Showing 6001 words to 9000 words out of 31076 words

Chapter 3 - HAUWA KULU Yar Cikin Badala Part 3 BY TAKORI.pdf

"Yau nake ganin sakarcin wofi. Lauyo!" In ji Inna,
"wato kin fi so mu ci gaba da zaman Kanon dai yana binmu da kulli yana illata mu, ko
saboda soyayyar da kike da dansa Jamilu ko? Ya ci gaba da yi miki naci yana zuwa azure yana
kalallame ki da shirme, ke kuma kina biye masa, tun farko ma ai ni so na yi mu bar Kanon gaba
daya tun ranar da ya rusa mana gida. Saboda Zakari abun gudu ne, kika dage kika hana ni sabida son Badalar ki, da kafiya da
naci kamar kuturwa, ni na san a Kano cibiyarki ta ke, mu duka ruhinmu ana yake, amma Manzo
(S.A.W) ma da kansa lokacin da Makkah mahaifarsa ta yi masa kunci saboda kiyayyar abokan
gaba da kafirai yayi hijira ya koma Madinah inda ya samu sababbin masoya, suka karbeshi
karbar da ahalinsa basu yi masa ba, sannan ne ya zauna lafiya. Ki duba tarihin Hijirar manzon
Alah SAW zuwa Madinah.
Banda wauta irin taki wai har bayan jin abin da Zakari ya aikata wa mahaifinki kina marmarin ci
gaba da zaman Kanon inda yake zaune taki kadan zuwa dan agundi, yo ni ai ko don in raba ki
da dan Zakari haihata-haihata na tafi Ghana, kurwata kur da iyalin Zakari da shi kansa. Zakari
abin neman tsari ne. Malam Bilyaminu kam ya sha mamakin Jamilu a kan Hauwa, wai yana son auren Hauwa,
koda yake tuntuni ya san halin Jamilu na kirki duk cikin ‘ya’yan Zakari shine kadai in ya hadu da
shi a hanya yake gaida shi, sai ya rage mamakinsa ya ce,
"ki mata a hankali, lallashinta za kiyi, sabo ne, amma Ghana dole mu tafi ba makawa muddin
muka kai kwana uku a raye, komai na rayuwata ya koma can, sannan ba zan kara rayuwa a
inda Zakari yake ba, na barshi da Allah, na bar shi da fitowar rana da faduwarta.
Amma tafiyarmu zuwa Kumassi (Ghana) ita ce mafi alkhairi a garemu, ko yaya ka gani Likita
Sarhamu?"
Dr. Sarham wanda tunda ya dukar da kai yana sauraron su bai ce komai ba, amma bai taba
jin tashin hankali irin wanda yake ji a zuciyarsa yanzu ba, musamman da Hauwa take wani irin
kuka kamar na fitar rai tana fadin bazata bar BADALA zuwa GHANA ba, tace gara abarta ita
kadai ta zauna zata iya rayuwa a gidan su ko babu dan jagora. Malam Bilyaminu wanda shi ma kukan Hauwa ya rikita shi, kalamanta kuma sun hautsina shi,
amma bukatarta na ya cigaba da zaman Kano ba mai yuwuwa bace, ya ce,
"Haba Hauwa-Kulun-Majadun, ‘ya daya tamkar da dubu!
Shin ke ba kya fatan yin aure ne kamar kowacce mace, sai fatan dauwama a cikin Badala ko
a gaban Innarta?
Ai ke yar gidan wasu ce Hauwa'u, don haka barinki Kano zuwa Ghana ba komai bane, don
idan ban da lalurar nan da na same ki a ciki, tuni na bada auren ki ga Salisu dan wajen Alhaji
Munkaila, to a yanzu na san ba lallai ya yarda da zabin mahaifinsa ba, in ya kasance sun ji kin
daina gani, ba kowa zai yarda ya auri marar ido ba sai mai soyayyar gaskiya, don haka na bar
wa Allah ya zaba miki abin da ya fi zama alkhairi ga rayuwar ki, amma hakika nafi so kiyi aure".
Inna ta yi sauri tace, "Mafi alkhairi ya fi a ce yaro mai nakasar ido yana tare da uwa da
ubansa a gefensa? Suna zama garkuwarsa da karfinsa a lokacin duk da yake bukatar su a
tare? Ka taimaki kanka Mallam, ka kuma bai wa kanka zaman lafiya ta hanyar cire wa ranka
batun son aurar da ita ga dan uwangidanka da kowa ma. Yau da a ce Hauwa da idanunta biyu, sai na fi kowa son ta yi aure a wannan matakin na

girma data shiga a rayuwarta. Amma da ya kasance haka Allah ya zaba mata rayuwa barin
maganar yi mata aure da kowa shi ya fi alkhairi Baban Hauwa".
“Kina wasa ne kema, lalura ce zata hana aure sunnar Annabi SAW?”
Kamar daga sama kawai sai suka ji Sarham ya ce (cikin rawar murya ta tangardar harshe),
rudani da rawar murya,
"Har da ni Inna? Ina nufin ko nine na nemi auren nata? Har ni ma idan na bukaci hannun
Maijiddah zuwa aure ba za ki bani ba?"
Ya kuma tsareta da ido yaki dauke idanunsa da suka rine da damuwa da tausayin kukan
HAUWA daga kan Inna, sosai yake casa zuciyar Inna da kaifin kwayar idanunsa, masu haske
da wata nasaba ta musamman da ba duk Maza keda ita cikin idanunsa ba.
Yanayin kallon da yake mata, irin kallon nan ne na hana ta kawo kowanne irin uzuri ko
togaciya ko rashin yarda ne, a kan bukatarsa.
Dakin ya bada wani irin shiru. Daga Inna har Hauwa duk sun firgice da jin abinda likita
Sarham ke cewa, Inna ta diririce ta rikice hau kame-kame ta rasa inda za ta sa kanta. Hauwa
kuwa idanu ta firfitar waje kamar zasu fado kasa a soya su a cikin mai.
Malam Bilyaminu kuwa murmushin manya ya yi, ya ce. "Da shi ke nan ka raba gardama, ka
raba rigima tsakanina da Hauwa, da tsakanina da Innarta mai shirin ajiyeta a kwibinta har
karshen duniya. ka Kuma yi Tuwona - Maina, wato dai ta kwana gidan sauqi idan yau aka ce
LIKITA YAYAN HAUWA ya dauke abarsa, ya kai ta gidansa na aure ya killace ta sun tara zurri’a
mai albarka, in yaso, ki yi ta karata da son Kanon naki, tunda kowa ya shaida ke 'yar Badala ce
ba ‘yar Inna ba da ba’a dinga jin kanku ba, babu kuma wanda ya kai ki son zaman cikin ta.
In yaso ni da Inna mu koma Ghana ki yi zaman aure kamar kowa.
Yo kai mai abu maganin a kwabe ka, ai ba sai ka tsaya tambayar Innarta ba, sadaki kawai za
ka kawo in har da gaske ka ke, kuma iyayenka sun amince ka auri Hauwa da zuciya daya duk
da lalurarta, to nikuma in hakan ta faru, tuwon girma miyarsa nama! Na baka auren Hauwa
duniya da lahira. Ka sani ko aurenta na baka ba tare da na karbi komai naka ba bayan sadaki da Ubangiji yace
na karba, tofa ban biyaka ko rabin-rabin abin da ka yi min ba na kulawa da rayuwarsu, da
abinda kayi mata ita Hauwa din, tsayin lokacin da na dauka bana nan tare dasu baka bar su sun
wulakanta ba sun tozarta ba. Inna duk ta rude, rudewar ta ta kasa boyuwa fadi ta ke, "A’ah Malam, kada ka biyewa da na
Sarhamu, kada yi gaggawa, bi maganar nan a hankali don Allah, na tabbata likita Sarhamu
zolayarka yake, kukanta ne ya daga masa hankali, amma babu makamanciyar wannan
maganar a tsakaninsa da Hauwa. Na rantse da Allah babu soyayya. Ai ba yau muke tare ba, ko Sarhamu? Ba ka taba ce min kana rikon auren Hauwa ba koda da
subutar baki ne.
Idan muka baka ita alhalin bata da ido, hakika mun kware ka. Kada ka bari tausayi ya rinjayi
zuciyarka ka aikata abinda zaka zo kana dana-sani.
Hakika ni uwarka ce da ba zan so ka yi auren wahala ba, kuma ba sai ka auri Hauwa bane zan
san kana kaunata, ni shaida ce Allah kuma shaida ne".
Ta soma share hawaye tana cewa,
"Malam ba ka san wasa ba ne? Ya daga wasa zaka Maida allura garma? Daga ganin sarkin
fawa sai Miya tayi Zaki mallam???"

Rudewarta da rikicewar ta ya kai intaha. Sarham sai ya mike tsaye yana dan murmushi yana
shafar kansa, rikicewar Inna ce ta sa shi dariya, ya san dama za'ayi haka, ta sha fada ta
maimaita a gabansa bazata taba yiwa Hauwa aure ba, koda kuwa da dan shugan kasa ne, don
ma dai shine, wato don shine ya furta ba wani daban ba, tabbas da an ga dan karamin yakin
sunkuru! Idonsa a kan Hauwan da ke ta ta kokarin kai kanta daki tana cuno baki tana
zumbure-zumbure wai Inna wulakantata, ta kuma yi mata gorin ido tunda ta ce (ba ta da ido
aurenta wahala ne). Cewa ta ke cikin turo baki gaba irinna shagwababbu.
"Ni dai Inna a yi min gorin komai zan jure, amma ban da gorin idanu. In ma makantar ce ai
shi ya bani lasisinta don haka don ta kare a kansa ba laifi bace.
Allah ma ya sauwake in auri likitanki Inna, wushe nan inji dan fillo, ya yimin tsufa, bayan
yanada matarsa har da goyo. Yo Allah na tuba ba gara min Yaya Jamilun ba yaro danye shar
kama na?"
Ai ba ta kai ga rufe baki ba Inna ta mike ta sauke hannunta a bakinta, jikake bumm! Da sauri
Sarham ya kauda kai, ganin har ta fasa mata baki, ya hau saka takalmin sa absent-mindedly.
Malam ya ce, "Haba Safiyya, in rai ya baci hankali ke nemo shi, ki rasa abin duka da fiddawa
jini sai Hauwa abin Allah sarki wadda ko ganinki ba ta yi da idanunta?"
Da kuka da wiwi Hauwa ta ta karasa dakinta tana tafiya tana dafa bango har ta shige daki. Ta
rufo kofa ta kifa kai a jikin kofar tana kuka.
Ba kukan dukan da Inna tayi mata a gaban Sarham take yi ba, kukan Malam yace “ita abun
Allah sarki ce tunda bata da ido”. Bazata taba karbar kaskanci akan nakasarta ba amma zata
karbi kwarin guiwa.
Sarham ya yi musu sallama cikin sanyin jiki zai tafi, bayan ya roki Malam Bilyaminu ya daga
komawarsa zuwa Ghana sai sun gana da mahaifinsa tukunna.
Yace zai dawo da daddare ya kai shi gun Abban nasa kamar yadda ya bukata.
Da haka Sarham ya juya ya bar gidansu Hauwa yana jin kansa kamar duk abin da ke faruwa
din nan a cikin mafarkiyake gudana. Baban Hauwa ya dawo, har ga shi ya bashi aurenta da
kansa. Duk abin da ya tsara wa ransa a kan matakan da zai bi ya auri Hauwa, da yardar Allah
za su tafi cikin sauki fiyeda yadda ya zace su tunda mai kankat (Baban Hauwa) yayi amanna
nan take, Innar Hauwa dama yake ji kuma ga mai tausa matai ta ya dawo. Sai ya gane har da
daukin Ubangiji a cikin al'amarin nasu.
Daga nan gidan su Hauwa, ofishin Abbansa ya wuce cikin makaranta, don ya san a daidai
wannan lokacin a can ne kadai zai same shi.
Abba Prof. na shan shayi a kujerar ofishinsa dake cikin tsohuwar jami’ar Bayero, babban dan
sa, shalelen Abba (Dr. Sarham) ya yi sallama cikin rashin nutsuwa.
Abba ya bashi izinin shiga idonsa a kansa. Kallo daya ya yi masa ya lura da cewa Sarham
duk kwalisar shi wadda bata barinsa ya fito koda falon gidansu ne ba tareda ya dauki wanka na
musamman ba ga dukkan alamu yau ko wankan safe bai yi ba ya fito har ofishinsa.
A nitse yake kallonsa har ya zauna a kujerar gabansa, ya ce, "Lelen Abba, what's wrong with
you haka? Daga kwanaki bakwai a baya zuwa yau, you are upset? Duk ka canza daga yadda
na sanka anya kana auna bp dinka?".
Kai tsaye Sarham ya ce, "BP na lafiya lau Abba. Amma Abba aure nake so ka karba min, nan
da kwanaki uku kafin su bar kasar nan.
Abba alfarma nake so ka yi min, irin wadda ba ka taba yi min ba!

Abba ban taba rokon ka wani abu ka hanani ba, amma na san wannan zaka iya hana ni,
nikuma bazan iya fasawa ba, sabida dalilai na masu yawa ne Abba. shiyasa ka ganni a haka,
ba kuma zan kara nutsuwa ba sai ka yi min auren, Abba na zo neman amincewar ka da
taimakon ka da albarkar ka don Allah Abba na, ni na san a komai kana fahimtata Abba”. "Aure Sarham? Duka-duka yaushe ka yi auren fari?” Abba Prof. ya tambaya cikin tsoro da
mamaki. “Wannan karon kuma ina ka debo auren? Namamajo sarkin mata, yau shekarata
talatin da biyar da mahaifiyarka ita kadai. Kaji na taba sha’awar karawa?
Ba zan taba hana ka yin aure ba, don ba'a hana namiji aure, don in an hana shi aure baza’a
hana shi zin aba, ban san yanayin halittarka ba, amma ka sani ka dauko hanyar saya wa kanka
rashin kwanciyar hankali muddin ka hada wa kanka mata biyu da kuruciyar ka to 35 baka kai
ba, alhalin kana zamanka lafiya da matarka har ga albarkar haihuwa Allah ya fara ba ku. To karin auren na mene ne kuma? Ni dai nasan ba sha'awa bace, don nasan kaina kuma
nasan ni ka gada, ba kuma rashin gamsuwa da iyalinka bane ya saka wannan rigimar".
Sarham ya yi maza ya ce da Abbansa, "Auren da zan yi yanzu na kwakkwaran dalili ne,
wanda idan ka ji shi kuma kanada zuciya a kirjinka Abba zaka mara min baya, bana son zuciya
ba ne, bana soyayya bane. Sannan ba sha’awace ta saka ni yin sa ba Abba.
Auren jihadi zan yi Abba wanda dalilai masu yawa suka yi sanadinsa".
Duk ya saka Abba cikin rudu, ganin haka ya gyara zama ya shiga kwancewa Abbansa
labarinsa da HAUWA, wato tun daga ranar da ya yi wa Hauwa aikin ido, abubuwan da suka faru
bayannan, har zuwa dawowar Malam Bilyaminu jiya.
Matakin da Inna ta dauka a kan Hauwa, da yadda ya ce shi a ba shi aurenta zai iya zama da
ita da lalurar tata. Kai hatta rayuwar dasu Hauwa sukayi a baya ta sayarda abinci a Tasha Bai
boyewa Abbansa komai ba.
Abba Prof, sai ya dan zakuda kadan a cikin kujerarsa, sau tari kana haifar Da har ya girma ya
fika halin kwarai, in baka yi wasa bama sai ya riga ka shiga aljannah.
Yana alfahari da Sarham akan halin kwarai da nagartarsa wajen darajja al'ummar Annabi,
amma rayuwar Tashar nan da su Hauwa sukayi in ya tuna sai yaji ransa baya so, ace dansa ya
auri ‘yar mai abinci a tasha, sai hya kada baki ya ce,
"Lelen Abba na dade ina jiran ranar da za ka zo min da wannan bayanin akan Hauwa dinnan
ai, na kuma san dama da wuya in ba karshen alewa kasa ba.
Ni ban yarda wai ba son Hauwan nan ka ke yi ba, ka cire maganar wani JIHADI da ka ke
fakewa da shi, don jihadi kala-kala ne in shine akwai wanda yafi wannan lada ma, amma ka
sani ni ba yaro ba ne kamar ka. Da zan tsaya yaudarar kaina da kaina.
Ka saka sa a ranka kawai tuntuni, ko recently, ka fara son yarinyar nan ka fara developing
interest a kan ta yanzu, ko ba yanzu ba.
Well, ba ni da hujjar hana ka, amma ka shirya daukar dala babu gammo daga matarka, wai
makauniya da auren nesa.
Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Na yarda wadannan mutanen suna cikin kaddararka, don haka ba
ni da ja cikin abin da Allah ya hukunta. Kawai dai bana so ka gurbata zaman lafiyan gidanka da
auren rainon tasha. Ka san rayuwar sayarda abinci a Tashar mota kuwa? Da kallon da akewa
mai yin ta? Hummm. Amma tunda ka ga za ka iya ka kuma yarda da tarbiyyarta ni shawara ce kawai tsakaninmu.
Zan tura insha Allahu a karba maka auren kafin iyayen nata su koma Ghanan.

Ko babu komai ni ma ban san yaya karshen rayuwar nawa 'ya'ya matan zai kasance
watarana ba, ba wanda aka gama yiwa halitta sai ranar da ya koma ga mahaliccinsa".
Wani irin relief ya sauka a zuciyar Dr. Sarham. Tunda har ya samu hadin kan Abba ya san na
Mama Maishari’ah ma ba zai zamo mai wahala ba. Mai wahalar da ma Innar Hauwa ce, ita
kuma ya gane ba ra'ayinta daya da maigidanta akan Hauwa ba don haka nata ra’ayin ba zai yi
tasiri ba, yana da tabbacin malam Bilyaminu din zai iya janyo masa ra'ayinta. Kenan matsalar in
ma zai sameta to zata fi karfi daga matarsa uwar 'yar sa Dr. Madinah ne. Madinah zata fahimci
komai amma banda lamarin kishiya ya sani. Inda shine babban weakness dinta.
Kamar Sarham ya sani kuwa, don kuwa Malam Bilyaminu yau wuni ya yi yana ganar da Inna,
yana fadakar da ita don Hauwa ta rasa ido ba yana nufin bata da feeling ba, don Hauwa bata da
ido baya nufin bazata so daukar yaran data haifa ba, ya kuma ce Allah ya halatta mata yin aure
wanda sunnar kowanne musulmi ne don kare kansa daga dattin zina. Bata da hujja har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login