Showing 6001 words to 9000 words out of 14129 words

Chapter 3 - SHAAMEEƘH by Harira Salihu Isahl

fari tasss
da shi, sai da ta shafa wani ruwan turare mai haɗi, ta zauna a haka jikinta ya
bushe, sannan ta zo ta bi da man ta mai ƙamshi da Humra da kuma turaruka, iya abin
da tayi kenan bata tsaya wani kwalliya ba, domin Jidderh ba ma'abociyar ɗige-ɗige
ba ce.

A iya shafe-shafen turaren da Jidderh tayi kawai, kar ku ga haɗuwan da tayi na
kyau da baiwan da Allah ya mata, don jidderh kyakkyawa ce ta gaske, ita ba fara ce
sol ba har can, sannan kuma ba za'a ce mata baƙa ba, ba ta da jiki sannan ba
siririya ce sosai ba, tana da dirinta dai-dai wan da ya tafi da yanayin aukin
jikinta, ƙirjinta madaidaita Masha Allah, ƙugunta ma duka Masha Allah son kowa ƙin
wanda ya rasa, tana da dogon gashi har bayanta baƙi wuluk gwanin sha'awa, dogon
hanci Masha Allah, ga bakinta ɗan dai-dai kaman ramin asusu, idanuwanta manya-manya
waɗanda ake kira da golden eye's, a taƙaice dai jidderh kyakkyawa ce ta ƙarshe ma,
duk iya yacce ake buƙatan mace to ta kai wajan, dan Allah ya wadata da komi
Alhamdulillahi Masha Allah.

Shiryawa tayi cikin pink sleeping dress mai kauri sosai, amma kayan akwai laushi da
stansti, ga shi har ƙasa wandon ya kai mata, rigan kuma iya guiwa amma abuɗe gaban
rigan yake sai igiya kawai, kayan sosai ya amshi Jidderh kaman ka sace ta ka gudu
da ita.

Wani ƙaton zumbulelen hijab ta saka black color, wayanta ta ɗauka da duk abin da za
ta buƙata, sannan ta fice a ɗakin nata ta ja ƙofa ta rufe.

Ɗakin mummy ta shiga ta sameta tana ninke hijabi ta idar da sallah kenan, tana
kallonta ta murmusa tare da cewa, "Uwar masu gida sai ina haka da wannan hijabi
kaman matar limami?"

Murmushi Jidderh tayi ta ce, "Mummy za ni wajan takwarata na gaishe su da stoho,
wataƙila ma na kwana a can."

"Tom ki kula sosai-sosai, Allah ya tsare ki gaishe da baba Alhaji."

Sai da jidderh ta juya tana ƙoƙarin ficewa ta ce, "Insha Allah mummy za su ji, yau
zan je na ƙwace mijina."

Mummy murmushi tayi tare da ɗaga murya yacce jidderh za ta ji, ta ce, "Za ku yi ku
bari duk ku gama baba alhaji na hajiya mama ita kaɗai ce."

Jidderh Ficewa tayi a gidan nasu tana tare da jan ƙofan palourn ta rufe, hanyan
ficewa a gate na gidan nasu ta nufa, kusan cin karo suka yi da wani matashin
saurayi kyakkyawa da shi, murmushi ya saki yana kallonta ya ce, "Ke kuwa stohuwa
lafiya haka da ƙaton hijabi kaman mai zuwa ɗaukan darasi, ga shi sai sauri kike
kaman mai shirin tafiya sama, sai ina haka?"

Cunno baki jidderh tayi ta ce, "Allah yaya Faisal banaso nikam, ni ba stohuwa
ba."

Murmushi saurayin da ta ƙira da yaya Faisal yayi ya ce, "To naji Hajiya jidderh
an daina, sai ina da daren nan?"

"Yaya faisal gidan takwara zan je."

"Au ki ce soyayyan stoho ta mosta za ki je ganinsa."

"Ai kuwa kam kai da ka sani, idan ban ga wannan storhon ba ai babu bacci hankali
kwance, balle kuma cikin nishaɗi."

Murmushi Ya Faisal yayi tare da girgiza kai ya ce, "Faɗa ɗayan gaskiyan kada ki
yaudari stoho, dan munsan ba shi kike nufi ba, wancan na Dubai ɗin kike nufi."

Jidderh murmushi tayi kawai tare da kulle fiskanta wai taji kunya.

Ya Faisal ya ce, "Ga shi na zo gaishe da mummy ne da na raka ki."

"Lahh! Ya Faisal kar ka wani damu zan je ni kaɗai, kuma may be zan tafi da motana
idan ƙuya ya bai hanani ba."

"Okay sis Allah ya stare hanya ki gaishe da su nikam basu ganina sai ɗan Dubai ya
shigo."

Murmushi jidderh tayi kawai dan tasan stokana irin na ya Faisal, ta ce, "Byee Yaya
Faisal."

Wucewa jidderh tayi, tana isa bakin ƙofan, sai mai gadi ya taso zai ya buɗe mata
ƙofa, ita kuwa tana murmushi ta ce, "lah! a'a baba wallahi ka bari zan buɗe da kai
na, ka huta abinka."

Baba mai gadi yana murmushi ya ce, "Hajiya Uwar masu gida ina za ki je da daren
nan haka kinsan Alhaji ya hana fitanku, muddin aka yi Magriba."
"Gidan takwara zan je baba, zan kwana a can ma."

"To amma ai ke ɗaya bai yi ba kuma ga shi da ƙafa, ai ya kamata ki ɗau mota uwar
masu gida, tun da dai kin iya", baba mai gadi ya faɗa yana murmushi, dan duk cikin
jikokin wannan family a mata dai babu ya Uwar masu gida(sunan da ake ƙiranta da shi
kenan), jidderh tana da hali mai kyau, ga kirki ga haƙuri, ga girmama manya, da
sanin ya kamata, ba ruwanta da rena mutum dan yana aiki a gidansu, ba za ka taɓa
jin ga jidderh tayi faɗa da wani ba tun tasowanta, shiyasa manya da yara ba wan da
baya son ta a familyn, dan ta fita Zakka, kirkinta na daban ne(Wannan kuma hali ne
na masu suna Hauwa'u kulu mai jidda).

jidderh ta ce, "Bakomai baba, insha Allah zan je lafiya", suna cikin magana sai
ga Faisal har ya fito daga wajan mummy, yana murmushi ya ƙariso wajansu tare da
cewa, "Stohuwa har yanzu baki tafi ba?"

"Eh Ya Faisal, inji baba mai gadi ne sai na ɗau mota ni kuma ƙuyan driving nake
ji, daga nan zuwa gidan takwara kam."

"Ai da gaskiyan Baba, uwar masu gida ba abar wasa ba, amma tun da har na fito sai
muje na ajiyeki ba."

"To Yaya Faisal."

Baba mai gadi murmushi yayi tare da faɗin, "Alhaji Faisal ai zuwanka ya fi zuwan
gomna, dan gwanda a kai ta, da daren nan gari ya kusa fara duhu tafiyanta ita ɗaya
kuma a ƙafa bai yi ba, Allah ya kai ku lafiya, a gaishe da su Baba Alhaji."

Amsawa Ya Faisal yayi yana murmushi, suka shiga motan nasa da jidderh, Baba mai
gadi ya buɗe musu wangamemen gate ɗin suka fice, suna fita Ya Faisal na driving ba
tare da ya kalli jidderh ba ya ce, "A gaskiya baba mai gadi ɗan amana ne sis, kalli
fa ai irin wannan kulawan ko ƴar cikin ka iya haka za ka kula da ita, Allah dai ya
kare masa zuri'ansa shi ma."

"Ameen Ya faisal, Baba mai gadi kam ai ɗan aljanna ne, da amana da gaskiys yake
aikinsa, amma meyasa naga ka fito da wuri?"

"Daddy bayanan Mummy ce kawai kuma mun gaisa", faɗin Faisal da ke driving nasa.

Suna zuwa ƙofan gate na gidan baba alhaji ya tsaya ya ce, "Ni ba shiga zan yi ba
sis, ki sauƙa anan zan juya gida lokacin zuwa masallaci ma yayi."

Murmushi jidderh tayi ta ce, "Nikam ai nagode hakan ma ya Faisal, Allah ba da ladan
rage mini hanya", ta faɗa tare da ficewa a motan, suka yi sallama ta wuce ƙofan
gidan, Faisal yana tsaye ta ƙwan-ƙwasa ƙofa, mai gadin ya tambayi waye? Ta faɗa
kamun ya buɗe ta shiga bayan ta ɗagawa ya Faisal hannu, murmushi shi kuma ya sakar
mata sai sannan yaja motansa yayi gidansu shi ma.

Mai gadin ne ya gaidata da fara'a, dan kowa yasan kirkin jidderh ta kyawun
halinta, yana murmushi ya ce, "Uwar masu gida sannu da shigowa."

Murmushi jidderh tayi ta ce, "Yauwa baba nagode, sannu da aiki", ta faɗa ta wuce
cikin gidan har ranta tana jin daɗin wannan suna, da suke ƙiranta da shi manya da
yara, musamman ma'aikatan familyn nasa, jidderh Uwar masu gida.

Ƙatoton gida ne wan da faɗan yacce yake ma ɓata baki ne, domin har kaman ya fi
gidansu jidderh girma, da sallama ta shiga cikin gidan, bata bi hanyan da zai sada
ta da babban palourn ba, ta ɓj hanyan da zai kai ta palourn takwarar tata, ta shiga
bakinta ɗauke da sallama.
Amsa mata dattijuwar yar aikin da ke jera abinci a dinning tayi, tana sakin
fara'a ta ce, "Maraba lale da uwar masu gida."

murmushi jidderhnma tayi ta ce, "Barka Baabaa larai."

Wucewa tayi ɗakin Hajiya mama direct, ta sameta tana kan sallah, cire hijab ɗin
jikinta tayi ta faɗa kan gadon kamn yarinya ƙarama, wayanta ta bude ta shiga ta
turawa baby recharge card na 5k, sannan ta tashi ta ɗauro alwala ta mayar da
hijabinta ta tada sallah.

Baabaa larai ce tayi sallama a ƙofan ɗakin, gyaran murya Hajiya mama tayi alamun
tana lazumi, jin haka sai baabaa larai ta juya.

Jidderh bayan ta idar da Sallan ta ja carbi, ita ma tayi nata addu'an ta shafa,
sannan ta cire hijabin ta ɗaure igiyan gaban riganta ta rufe.

Komawa kan gadon tayi ta kwanta, tare da ƙara yin dialing numbern ɗazu, yanzun
ma dai kaman ɗazu ne har ƙira uku tayi amma ba a ɗauka ba, ƙaramin tsaki ta ja tare
da dialing numbern Safwan, yana shiga aka kashe aka ƙirata.

"Wahalalle", haka ta faɗa kamun ta ɗau ƙiran, ba laifi yanzu dai ta sauraresa,
sun yi hira amma sama-sama take amsa masa, shi kam Safwan da alama ko a jikinsa.

"Babe yaushe za ki barni na zo na ganki? seriously am eager to see you, and ina
so na turo magabatana ayi maganan auran mu, i can't wait to see dis beautiful
diamond lady a gidana a matsayin halal wife tawa, kullum ki ce ba yanzu ba, dan
Allah babe ki yanke rana."

Jidderh tana jinsa har ya gama zancensa, ta taɓe baki ta ce, "Allah ya tabbatar da
alkairi Safwan."

Addu'ar da tayi ba ƙaramin daɗi ya masa ba saboda ƙaunarta da yake yi, wanda
hakan ya sanya shi cewa, "Babe guess what!"

Cike da zaƙuwa da kuma gajiya da wayan ta ce, "Yes am getting you."

"Wayanki ya iso Insha Allahu, zan iya yin komai dan farincikinki, duk lokacin da
kika ce a kawo ba ɓata lokaci zai iso gare ki."

Taɓe baki jidderh tayi ta ce, "An gode Allah ya ƙara budi."

Safwan na murmushi ya ce, "Ameen wife material, mace mai godiya da iya addu'a ai
ita ce macen da ko wani namiji ke fatan samu, Allah ya miki albarka."

"Ameen, am please Safwan ina jin bacci", faɗin Jidderh da ke jin kaman ta saka
kuka.

"Okay Babe Allah ya tashe mu lafiya, ki kula mini da kanki sosai kin ji."

"Insha Allah."

Safwan ya ce, "To Allah ya tashe mu lafiya, ina matuƙar sonki."

Kittt! haka Jidderh ta kashe wayanta, tana taɓe baki tana faɗin, "Yen yen yen! ka
bi ka dame ni, sai ka ce an ce maka ko ina sonka ne, mutum shegen naci kai ba zaka
fahimci ba'a sonka bane, ba abin da ban faɗa ba amma ka maƙale kaman chewing-gum,
idan kuka ka ji wani labari nan gaba sai ka ce yaudararka nayi."

Hajiya Mama da ta idar da addu'anta ta shafa ne, ta aiko wa jidderh dan-ƙwalo ta
ce, "Gidanku cubulle, na faɗa miki ba a yiwa namiji haka amma sam ke bakya ji,
wulaƙanta mutum ba abu ne mai kyau ba, tun da kin faɗa masa gaskiya ya ƙi ji, ai
sai ki kiyaye kawai ki bisa yanda yake so ku rabu lafiya, maza fa sai a hankali, a
wannan zamani ba iya mata ke shige-shige ba, har namiji ya iya bin malamai dan haka
ki bi a sannu a rabu lafiya bana son damuwa."

Abin da wasu matan ba sa ganewa kenan, maganan wulaƙanta najimi amma sam basa ji,
kuma wannan na ɗaya daga cikin abin da ke damun yaranmu mata a yanzu, sai ka ga
yarinya ta kwana biyu ba aure, tun tauraronta na haskawa har ya disashe, tabbas an
sani komai sai Allah ya nufa ya kuma ƙaddara idan lokacinsa yayi, amma wasu da yawa
makamancin iriyar wannan dalili ita ce mastalarsu, mu kiyaye, Allah kuma ya bai wa
kowa miji nagari, masu aure Allah ya karo zaman lafiya da haƙuri da juna ya kuma
raya zuri'a ya shirya mana su.

Turo baki Jidderh tayi ta ce, "To Hajiya na jiiiiiii."




***

MASU DARAJA HABIBTIEES NA UWAR BATOORL AKWAI GARAƁASA GUDA, A YANZU KAMUN MU
KAMMALA FREE PAGE'S TO KUƊIN LITTAFI DAI #300 NE, IDAN MUN KAMMALA KUWA #500 YAKE
INSHA ALLAH.

9161720046
Harira salihu isah
Opay
&
2220553988
Harira salihu isah
Uba

Shedar biya ta wannan layi 07015870735.

Mutanen Nijar ku ma ku yiwa wannan layi magana dan yin payment naku 07015870735.


# Hareeyh
# 09161720046
# 07015870735

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚, SHAAMEEKH ,
B̶̶O̶O̶K1

Officially


𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)


‫ اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله‬SAW 🖤🤍
GARGAƊI: masu YouTube channels, masu yin Audion littafi, kada wacce ta ɗaura mini
littafi ba da yawu na ba, domin muddin na ci karo da haka to ko wacece/ wanene zan
ɗau mummunan mataki a kai, hukuma za ta rabani da mutum, A KIYAYE.


̶ ̶F̶r̶e̶e page
Billy Ammin Safwan, masoyiya bealkysou Allah Ubangiji ya miki albarka ya nuna mana
bikin nan da rai da lafiya, ƙanwar aunty Ummi kiyi yacce kike so da page ɗin nan.


PAID #500
Shafi
Na
Uku.


Ƙwafa Hajiya Mama tayi ta ce, "Ni ban ma san me ya kawo ki ba takwara, kin zo
dare-dare kaman mara gaskiya za ki addabi rayuwan mutane."

Jidderh na daga kwance ta ce, "Ni bansan ma me yake kawo ni gidan stohuwar nan ba,
bana iya haƙuri sai na zo, idan nazo kuma ki ta mini gori kaman ɗauke mijin zan yi
na tafi da shi, laifi nane ma da nake zuwa ma gidanki ai", ta ƙarishe zancen
muryanta na rawa, kaman mai shirin kuka dan har idanuwanta yayi ƙwalla.

Hajiya Mama haɓa ta kama ganin ikon Allah, ta ce, "Eh samun waje kare da rawa a
bakin ramin kura, mai arahan hawaye, yanzu me abin kuka anan? To Allah ya azurtaki
da Manzon sauƙi takwara, mutum sai son hawaye da kuka kaman wacce mijinta ya mutu,
wai haka za ki dinga yi wa mijin ko nice da kike ganin damana kike min wannan
taɓaran? Sai ka ce daman ni na ce ki zo."

Tura baki tayi ta ce, "Ni dai Hajiya banaso, zan tashi na koma gidanmu,
alhamdulillah muma muna da gida."

Hajiya tana ƙoƙarin miƙewa ta ce, "Na kan ga rasulu idan nayi hali na gari, yanzu
ke takwara ni kike faɗa wa kuna da gida? To naji daman nasan kuna da shi ai ba a
daji kuke kwana ba, amma a haka kika zo mini gida dan ki takura wa mijina, to kin
zo kenan ba in da za ki koma, ke da barin gidan nan ai kuma ba yau ba, abin da ya
sanya ki zuwa dare-dare, shi zai zaunar da ke ki kwana dole, dan ƙafan gwoggonki
Fatu."

Jidderh tura baki ta kuma yi, kaman mai shirin yin kuka ta ce, "Nidai ba ruwan
gwoggona."

Murmushi Hajiya Mama tayi ta ce, "To naji masu gwaggo, mu da bamu da su a raye
Allah bamu haƙuri, kuma na kowa ma zai tafi indai mutuwar yanzu ne, taso muje mu ci
tuwo dan nasan daman kwaɗayi ya kawo ki gidana."

Jidderh ƴar dariya tayi jin wai kwaɗayi ne ya kawo ta, miƙewa tayi daga kwancen da
take tana faɗin, "Eh koma menene dai na zo ne dan na ci tuwo da sakwarata."

"Sai dai sakwara kam, ni rabani da halinki, bansan abin da ya kai Sama'ila saka
miki sunana ba, dan ni ba haka halina yake ba", Hajiya Mama ta faɗa tana ƙoƙarin
ficewa a ɗakin.

Jidderh sauƙowa tayi ta naɗe wa Hajiya Mama sallaya da hijabinta, sannan ta ɗauki
wayanta ta bi bayanta a niste, suka fice a ɗakin, palour suka nufa dai-dai Baba
Alhaji na shigowa shi da wani matashin saurayi.

Stohon da suke cewa Baba Alhaji murmushi ya saki ganin jidderh, ya ce, "Ah!
Amaryata ce da daren nan."

Jidderh na murmusawa ta ce, "Nice dai angona mai ran ƙarfe, ka ƙi zuwa hatta ɗaukan
amaryan shiyasa na taho abina da naga dare tayi."

Baba Alhaji ya ce, "To Masha Allah! Amaryata ta kyauta, Allah ya miki albarka."

Amsawa da "Ameen", jidderh tayi, sannan ta ce, "Yaya Sabeer an wuni lafiya?"

Matashi mai suna ya Sabeer murmushi yayi ya ce, "Lafiya alhamdulillah stohuwa
amaryan stoho."

Jidderh kallon Hajiya Mama tayi, tare da turo baki ta ce, "Allah kuwa sakwara ki ce
musu su daina ce mini stohuwa, ƴar gangariyan budurwa da ni haka kawai a rage mini
farashi."

Hajiya Mama haɗe fiska tayi tare da kallon Ya Sabeer ta ce, "A daina faɗa wa
takwarata stohuwa, ita ba stohuwa ba kuna ganin yarinya ƴar jinjira da ita, kuna
stofar da ita."

Ya Sabeer dariya yayi tare da riƙe bakinsa, da kunnensa alaman yaji ya daina, ita
kuma jidderh murmushi tayi ta ce, "Yauwa Hajiya Mama ta."

Baba Alhaji ne ya ce, "To azo aci tuwo kubar shirmen nan, dan Hauwa'u rigimanta
ya mata yawa."

Duk akan centre carpet suka zauna, Jidderh ce tayi serving nasu, ta saka wa baba
alhaji tuwon biski da miyar zogale da ya ji kifi kasancewan yana da ciwon sugar,
Hajiya Mama kuma ta saka mata tuwon shinkafa da miyar zogale da kifin ita ma, ta
saka wa Ya Sabeer tuwon shinkafa da miyar kuɓewan da yaji man shanu ga namomi,
sannan ta saka wa kanta tuwon doya(sakwara) da miyar egusi shi ma ya ji bushashshen
nama.

Abincin suke ci wajan shiru ba ka jin ƙaran komai, sai na taunan abincin nasu,
jidderh bata wani ci sosai ba ta cire hanunta, ɗiban ruwan zafi tayi ta haɗa black
tea ta sha, gefe ta matsa tana duba wayanta hankali kwance ciki ya ɗauka.

Hajiya Mama kallon jidderh tayi tare da girgiza kai, ta ce, "Ke dai takwara Allah
ya yaye miki rashin cin abincin nan, watarana har gwanda mai sunan Alhaji da ke
kam."

Murmushi kawai jidderh tayi ba ta ce komai ba.

Ya Sabeer ya ce, "Ai Hajiya Mama dai-dai kenan, kin ga an haɗa su perfect match,
amma dai nikam ina namiji ban ci ba wa zai ci? Ni fa na nemo abincin, ai gwanda ace
mace bata ci sosai akan a ce namiji ne baya ci sosai, don ita mace hakan ma ado ne
gare ta."

"Kubar damar mini amarya da surutu, tun da ta ƙoshi to a ƙyale ta", faɗin baba
alhaji.

Jidderh murmushi tayi tare da cewa, "Yauwa mijin ka gama ci kai ma sai muyi fira",
ta faɗa tana komawa kan kujera ta zauna.

Alhaji baba ne ya mayar da dubansa kan Ya Sabeer ya ce, "Nikam

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login