Showing 3001 words to 6000 words out of 14129 words
ce tayi fiskan tausayi tare da cewa "Dee, Leemah da Deeyah meyasa kukayi
dariya bayan kunsan yaya Jidderh da saurin fushi, yanzu ga shi kun ja ta ɓata rai,
kuma dai kunsan gwanda ita a kan yaya Soffy, ita ke zama a cikinmu ba ruwanta da mu
ƙannenta ta yi wasa da dariya da mu, in dai hauka ne da a gaban yaya Soffy kuka yi
wannan maganan ai da tuni kun gansa, da an bawa kowa sadakan bugu a baki."
Meelat ta ƙara mai da idonta kan Subby ta ce, "Kinsan halin yaya Soffy sarai a
kan shi, ni kuma duk ba dan komai nace na matsu ta dawo ba, wallahi nayi kewanta ne
kawai, kunsan muna shiri da ita nikam."
Subby taɓe baki tayi ta ce, "Ku kuka sani yanzu kuma" ta tashi ta shige toilet.
Wacce aka ƙira da Dee ta ce, "Ai kuwa nikam anjima zan dangana da gidan stoho na
bawa yaya Jidderh haƙuri dan nasan yanzu haka can ta wuce, bawa yaya Jidderh haƙuri
ya zama mini farilla ni da nake dakon wayan hanunta, naji wai wancan wahalallen
saurayin nata zai sauya mata kuma fa kunsan ba amsan na hanun nata zai yi ba."
Leemah ta ce, "Nima zan biki mu bata haƙuri dan gaskiya banason fushin yaya Jidderh
tamu."
Deeyah jin abinda suka faɗa sai ta kwashe da dariya ta ce, "Ke ma Leemah nasan abu
kika gani kike so tabaki, kunsan yaya Jidderh da kyauta, anyway ni banson komai
amma nima zan bata haƙuri."
Meelat murmushi tayi ta ce, "Da ya fi muku kam, kunsan dai yaya Jeeddeerh ita ce
idonmu a gidan nan, serious bai kamata muna ɓata mata rai ba, Subby ce kawai da ba
ta ji da ƙaton kan ta."
Subby da fitowanta kenan daga toilet, jin abinda Meelat ta ce sai ta aika mata da
harara."
Meelat ta ce, "ki harareni da kyau, amma ko menene dai ke ce kika fara maganan da
ya ɓata mata rai."
Dee ta ce, "Yanzu dai a matsayina na Auntynku in absence of yaya Jeeddeerh ni
yaya Fadeela na ce case close."
Dukkansu biyar ɗin dariya suka saka har da ita Dee ɗin da tayi maganan, Deeyah
ce ta fara hararanta ta ce, "Waye sa'anki a nan? dan kawai kin ga ba kya ce mana
yaya shi ne har da reni, wai yaushe ma kika cika 21year's ne Dee?"
Tura baki Dee tayi tare da faɗin, "To nidai naji ko nice ƙarama na ɗau matsayin
manya na ce a rufe babin maganan ya wuce."
Subby murmushi tayi ta ce, "Nikamma Deeyah kin tuna mini birthdayn mu ya kusa,
akwai cin kuɗi, kaiii gaskiya dole ma na bawa yaya Jidderh haƙuri nima."
Leemah ta ce, "za ma ki dawo hanya ai wallahi, indai yaya Jidderh ce ko wa ma
yasan yana cin albarkacinta kuma tana yi wa kowa kirki."
Meelat miƙewa tayi tare da buga stalle kaman ƙaramar yarinya ta ce, "kowa ya
tuba dan wuya ba lada, sai da ke yaya Jidderh tamu."
***
Juma'at Kareem.
MASU DARAJA HABIBTIEES NA UWAR BATOORL AKWAI GARAƁASA GUDA, A YANZU KAMUN MU
KAMMALA FREE PAGE'S TO KUƊIN LITTAFI DAI #300 NE, IDAN MUN KAMMALA KUWA #500 YAKE
INSHA ALLAH.
9161720046
Harira salihu isah
Opay
&
2220553988
Harira salihu isah
Uba
Shedar biya ta wannan layi 07015870735.
Mutanen Nijar ku ma ku yiwa wannan layi magana dan yin payment naku 07015870735.
# Hareeyh
# 09161720046
# 07015870735
# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚
SHAMEEKH
B̶̶O̶O̶K1
Officially
𝘽𝙮
Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)
اللهم صلى و سلم على سيد نا رسوللهSAW 🖤🤍
GARGAƊI: masu YouTube channels, masu yin Audion littafi, kada wacce ta ɗaura mini
littafi ba da yawu na ba, domin muddin na ci karo da haka to ko wacece/ wanene zan
ɗau mummunan mataki a kai, hukuma za ta rabani da mutum, A KIYAYE.
SHAMEEKH or SHAMIKH : is an Arabic name that is use interm of naming a muslim baby
boy, the name Shamikh is drive from the holy Qur'an chapter 77 verse 27, Shameekh
mean's HIGH, LOFTY and ABOVE ALL OTHER'S.
Yauwa waɗanda ke da mastala akan basu iya faɗan sunan ba, idan suka karanta ayar
za su fahimci yanayin yacce ake ƙiran sunan, a cikin suratul MURSALAT aya ta
ashirin da bakwai.
̶ ̶F̶r̶e̶e page
Page naku ne
Surryta
Habiba Muhammad Yusuf
PAID #500
Shafi
Na
Biyu.
⭐
ADAMAWA STATE.
FEDERAL MEDICAL CENTER YOLA.
Wata farar mata ce ta fito a ɗaya daga cikin ɗaƙunan malaman asibiti da ke
jere a floor ɗaya, office ne wanda yake a jerin na manyan likitoci masu duba
mastalan da ya shafi mata, dattijuwar matar da kana ganinta kasan ta manyanta,
sanye take da leshi baƙi ɗinkin dogon riga wanda yayi mugun amsarta, hijab nata
fari tass ɗan dai-dai, idanuwanta ta maƙala musu glasses fari, amma kana gani kasan
medicated glass ne ba na gayu ba, hanunta riƙe da labcoat, tafiya take cikin
nistuwa fiskanta yalwace yake da murmushi, jama'a sai ɗaga mata gaisuwa suke tana
amsawa tun fitowanta office nata har ta iso inda drivernta ke jiranta, tana isowa
wajan motan sai drivern yayi sauri zai buɗe mata ƙofa, amma sai ta dakatar da shi,
fiskanta da fara'a ta buƙaci ya bari za ta buɗe da kanta, drivern ba dan ya so ba
ya masta ta buɗe ta shiga tare da karanto addu'an hawa ƙarfe, ajiye abubuwan
hannunta tayi a gefenta tare da gyara zamanta tana hamdala ga Allah.
Driver ne ya ce, "Sannu da aiki Hajiya."
Tana murmushi ta amsa masa, tare da tambayansa nasa aikin, shi ma ya amsa mata,
counter(carbin irge) da ke maƙale a yastunta ta gyara tare da cigaba da yin
tasbihin da take yi, ƙira ne ya shigo wayanta dake cikin jaka, Jawo jakan ta yi ta
buɗe ta ciro wayan, sautin qira'a na Amanar-rasulu yana tashi, amma kamun ta gama
ciro wayan har ƙiran ya yanke, tana cirowa ta duba ta ga layin Alhaji ne, murmushi
kawai ta kuma yi tare da bin ƙiran, yana shiga ringing ɗaya kawai yayi aka ɗauka,
ita ta fara yin sallama cikin nistuwa da girmamawa ga wanda ta ƙira ɗin.
"Assalamu Alaikum Baba an wuni lafiya?"
"Lafiya ƙalau Alhamdulillahi Fatima, ya kike? ya aiki?" Faɗin muryan wani stoho a
ɗaya ɓangaren.
Matar ta ce, "Lafiya Alhamdulillahi Baba, yanzu haka ma tasowana daga asibitin
kenan ko gida ban ƙarisa ba."
Gaisawa suka yi ta tambayi stohon ƙarfin jikinsa, ya amsa mata da sauƙi sannan ya
ce, "Fatima wai ina labarin abokinane kam?"
Matar murmushi ta yi ta ce, "Ya na can lafiya baba, munyi waya ɗazu ma ya ce yana
gaisheku kuma in Allah ya yarda yana shigowa."
"To! To! Madallah, Allah kawo sa lafiya, Allah muku albarka duka ku da
zuria'anku."
Da "Ameen" matar ta amsa, sannan stohon ya faɗa mata ga Hajiya ya miƙa mata wayan
suka gaisa, Hajiyan ta ce, "Faɗimatu wai yaushe za ki shigo ne?"
Matar na murmushin jin tambayan mahaifiyarta ta ce, "Mama wai daman ina jiran
mai-gidanki ne, idan ya zo sai mu taho tare."
Hajiya a ɗaya ɓangaren ta ce, "Me haɗin Dubai da Adamawa?"
"Babu mama" faɗin matar tana murmushi dan tasan za'a yi haka daman.
"To idan har kin yi niyan zuwa kawai ki zo, shi kuma idan ya ga dama kar ya zo za
mu haɗu ne, ni da shi ɗin" Hajiya ta ƙarishe maganan da ƙwafa.
"To shikkenan Mama, Insha Allah za mu taho ranan asabar tare da kishiyanki."
"Allah kai mu, Allah miki albarka, Allah kawo ku lafiya dukanku."
"Ameen Mama."
Suna gama magana suka yi sallama ta kashe wayanta, dai-dai lokacin sun iso gidan
su dake anguwan Abuja road, buɗe musu gate aka yi suka shige, bayan driver yayi
parking ta fito dan shigewa cikin gidan, sai ga wata kyakkyawar yarinya budurwa,
yar kimanin shekara sha takwas ta zo da gudu, tana faɗin, "ayoyoo Ummiy sannu da
dawowa", ta rungume ta.
Ummiy na murmushi ta ce, "sannu babyn Ummiy, ɗauko jaka na da labcoat a mota", ta
faɗa tare da raba yarinyar da jikinta.
Yarinyar ta ce, "To Ummiy na."
Shigewa cikin gidan Ummiy tayi da sallama, Talatu yar aikin su dake goge palourn
ne ta amsa, stugunnawa tayi har ƙasa ta ce, "Sannu da dawowa Hajiya."
"Yauwa Talatu sannunki kema da aiki", Ummiy na gama faɗan haka ta wuce ta haura
matakalan da zai kai ta sashinta da ke sama, sannan ta nufi ɗakinta.
Shiga ɗakin tayi da sallama duk da ba kowa a ciki,(Ku zama masu yaɗa sallama ko
da kuwa babu mutane a wajan, domin akwai salihan bayi mala'ikun da ke amsawa, kuma
suke jira ka yi sallama dan su rubuta maka ladanka), hijab nata ta cire ta wuce
banɗaki direct.
Yarinyar da Ummiy ta ƙira da Baby ce ta shigo ɗakin da sallama ita ma, jin shiru
ba wan da ya amsa mata sai ta turo ƙofan ta shigo, jin ƙaran sauƙan ruwa a banɗaki,
shi ya tabbatar mata da Ummiy na ciki, ajiye mata jakan tayi da labcoat nata a
ma'ajiyarsu, sannan ta nemi waje ta kwanta a kujeran dake cikin ɗakin daga gefe,
tana jiran Ummiyn nata, bayan mintuna Ummiy ta fito.
Wucewa tayi wajan dressing mirrow ta shafa mai da turaruka masu qamshin gaske
( lallai anan Shamikh yayi gadon stafta, son ƙsmshi da komai ma).
Bayan ta gama shiryawa dogon riga mara nauyi ta ɗauko ta saka, sannan ta zauna
a bakin gadon nata, sai da tayi hamdala na daɗin jikinta da ta ji, sannan ta ce,
"Baby ina ga dai bakinki akwai magana."
Baby tashuwa tayi tana murmushi ta ce, "Ummiy nayi missing na big bro ne wallahi."
Ummiy ta ce, "Ikon Allah! Baby anya magananki akwai gaskiya?"
Turo baki tayi ta ce, "Da gaske fa Ummiynmu, yauwa Ummiy yaushe za mu je Maiduguri
ne nikam?"
"Yauwa kin tuna mini ɗazu mun yi waya da Hajiya Mama na faɗa mata za mu shigo
ranan Asabar in Allah ya yarda."
"Wayyooooo! Allah bar mana ke Ummiy, Allah nayi missing na Maiduguri barin ma
aunty Jidderh ta, shiyasa nake son wannan family meeting ɗin, saboda lokaci nayi za
ka kalli kowa, gaskiya Allah sambaɗawa stoho albarka, da ya kawo wannan
ingantacciyar shawara."
Murmushi Ummiy tayi tare da amsawa da Ameen, an ce Allah ya yiwa stohonta albarka,
sannan ta ce, "Ki tabbatar dai kin shirya kamun ranan idan ba haka ba kuma tafiya
zan yi na barki dan ina son mu tafi da sassafe ne."
Zaro ido baby tayi ta ce, "Ummiy dan Allah mu bi Flight wallahi nikam bazan iya
zaman mota ba."
Kallonta Ummiy tayi, tare da yin murmushi ta ce, "Daman so nake naji me za ki ce
baby, kekam ko stunstu ya ganki ya barki da son firewa, ke da jirgi kam inaga pilot
zan bai wa aurenki."
Cunna baki tayi ta ce, "Ni dai Ummiy koma me in dai Flight za mu bi shikkenan
komai dai-dai ba mastala, kuma maganan big bro ma nafasa sai ya zo", daman har ta
miƙe tsaye sai ta koma ta zauna kusa da Ummiy ta ce, "Ayya Ummiynmu, dan Allah
idan big bro ya zo ki faɗa masa ya sauya mini waya, dan Allah dai kin ji Ummiyna."
Ummi cewa tayi, "Ai daman nasan kwanar zancen, ba zai wuce wani abun kike so ba,
ban da dai haka kawai baby ki ce kina kewan Shamikh, amma dai baby duk yaushe ya
sanja miki wayan? ki din ga jin tausayin yayanki fa baby, akwai mutuwa, akwai
jarabawar ubangiji, yau kana da shi gobe ba ka da shi, bana so ki saba da irin
rayuwar nan, domin Allah na jarabtar bawansa a ko da yaushe, idan babu mu wa zai
jure miki haka?"
Sunkuyar da kan ta tayi ta ce, "Insha Allah Ummiy zan zama mai yarda da ƙaddara a
duk lokacin da hakan ya samemu sannan zan kasance mai haƙuri da akwai ko babu."
Murmushi Ummiy tayi ta ce, "To Allah ya miki albarka, ki shirya da wuri ko, insha
Allahu kuma idan ya dawo zan saka shi ya sanya miki, ai ya zama dole a sauyawa
autar Ummiy abin da take so, kuma autar Ummiy ma tasan yayanta yana ƙaunarta, mai
mata komai ne ko babu Ummiy, muddin yana da halin mata."
Murmushi mai kyau baby tayi tare da cewa, "Ameen Ummiy, Allah ya ja kwana ya
barki da Daddy."
Murmushi kawai Ummiy tayi, tare da faɗin Ameen ɗin a zuciyanta.
"Ummiy bari na je nayi assignment da wani lecturer ya bamu tun jiya, amma fa
Ummiy ki fito ki ci abinci kamun ki kwanta, kin ji Ummiyna" ta faɗa tare da tashuwa
ta nufi ƙofa.
Tashuwa Ummiy tayi ta bi bayanta, suka fito tare, dinning Ummiy ta wuce, ita Baby
kuma tayi ɗaki ta ɗauko system nata, ta ajiye a kujera a palourn ta wuce dinning,
samun Ummiy tayi tana shan kunun gyaɗa da ya ji haɗi.
langwaɓar da kai baby tayi ta ce, "Yanzu Ummiy kunun kawai za ki sha fa na sani, ba
za ki ƙara komai ba, bayan kinsan big bro baya son hakan Ummiy."
Ummiy ta ce, "Sarkin surutu Ummiy bata jin yunwa, sai zuwa anjima."
Ɗiban kunun tayi ita ma ta ce, "to Ummiy Allah ya kai mu anjiman, kamun na gama
assignment ɗin sai mu miki favorite food naki."
"To a gama lafiya, daman dai shi nake sha'awan ci."
Baby cikin Palourn ta wuce riƙe da kofin kununta, system nata ta jawo ta buɗe
tana assignment tana kurɓan kunun.
Ummiy dake dinning ɗin ƙira ne ya shigo wayanta, ɗauka tayi tana amsa sallaman da
aka mata a ɗaya ɓangaren tana faɗin, "Mamana kuna lafiya?"
Shiru tayi da alama magana ake a ɗayan bangaren, can kuma ta kuma cewa, "Duk muna
lafiya muma mamana, ga ƙanwarki lafiyarta lau ko ɗazu sai da tayi magananki."
Murmusawa wa ummeyh tayi ta kuma faɗin, "Allah ya miki albarka Mamana, Insha
Allahu muma muna zuwa ba jimawa."
Juyawan da Ummiy za ta yi ba sai ta ga baby a gefenta ba tana faɗin, "Please Ummiy
ki bani mu gaisa nasan Aunty Jidderh ce."
"Mai anguwan garinku baby, ba dai kina da wayarki ba, to ƙira ta da naki ba zan ba
da nawa ba."
Jidderh ce tayi murmushi ta ɗaya ɓangaren ta ce, "Ayi haƙuri Ummiynmu a bata naji
muryan ƙanwata."
Ummiy miƙawa baby wayan tayi ta ce, "Karɓa ba dan halinki ba, kin ci albarkacin
Mamana."
Baby amsa tayi tana murmushi ta shagwaɓe murya kaman tana gaban Jidderh ɗin ta
ce, "Yaya Jidderh ni fushi nake dake kwana biyu ba ki ƙirana shi kuma yaya inaji
ya manta da ni ma kwana biyu shi ma bai mini recharging ba balle na ƙira ki."
Jidderh ta ce, "Amana afuwa babynmu.'
Ƙara tura bakin tayi ta ce, "Ni dai naƙi yaya Jidderh."
"Haba dai in-law ta kuma ƙanwata."
murmushi ne ya kuɓuce wa baby har da gyaɗa kai irin ta ji daɗin sunan, ta ce,
"Insha Allah kuwa yaya Jeeddeerh ta, daga ke ba wata bayan ke ba ƙarii Allah bar
mana ku."
Jidderh ta ce, "Ameen ƙanwar kirki, yaushe za ku shigo?"
"Ranar Saturday yaya Jeeddeerh, kuma ni awajanki zan sauƙa, bro Yusuf yana nan
ai?"
"Eh baby yana nan, Allah ya kawo mana ku lafiya."
"Ameen yaya jeeddeerh", baby ta faɗa tana murmushi.
Wayansu suka yi tana faɗin a gaida mata kowa da kowa, sannan suka yi sallama ta
kashe wayan.
Ummiy da already taga call nasu bame ƙarewa bane wucewa tayi sama dan ta huta kamun
lokacin sallah yayi.
Baby da ta juya taga ba Ummiy a dinning kuma bata palourn, ajiye wayan tayi a
gefenta bata je kai mata ba dan ta san hutawa Ummiy taje yi, assignment nata ta ci
gaba da yi.
⭐
Jeedderh ce a ɗakin da yake mallakinta, komai na ɗakin blue colour ne sai white,
kwance take akan haɗaɗɗen gadonta, tana riƙe da wayanta ta zuba masa idanuwanta
gaba ɗaya, da alama wani abu mai muhimmanci take yi duba da yacce hankalinta duka
ke kan wayan.
Wani sihirtaccen murmushin da jeedderh ke saki, wan da ya ƙara mata kyau, shi ya
sanya ni leƙa wayan dan ganin abin da ke sanya ta, irin wannan sansanyar murmushin.
Message Jidderh ke rubutawa, wan da na tabbata santin message ɗin ke sanya ta
wannan haɗaɗɗen murmushin.
Tana gamawa ta tura wa mallakin saƙon ba ɓata lokaci, turawanta kuma yayi dai-dai
da shigowan ƙira a wayan nata, "SAFWAN" shi ne sunan da ya bayyana ɓaro-ɓaro, akan
layin da ya ƙirata, Jidderh tura baki tayi kaman ba za ta amsa ƙiran ba, tana ji
yana ringing amma sai da ta tabbatar ya kusa stinkewa, sannan ta ɗauka a hankali
cikin nistuwa ta kai wayan kunnenta, muryanshi ta jiyo yana faɗin, "Hello baby ya
kike?"
Cunna baki tayi kaman yana gabanta ta ce, "Uhmn lafiya."
"Masha Allah babyna ya labari?"
Jidderh da ke jin kaman ta shaƙesa, a hankali ta ce, "Please Safwan zan yi
sallah, idan na idar zan ƙiraka."
"Okay baby am waiting a saka mu a addu'a, Allah kuma ya mallaka mini ke."
Sai da Jidderh ta harari wayan, dan jin ya ce wani Allah sa ya mallaketa, sannan ta
ce, "Okay byee", tana faɗan haka a taƙaice ta kashe wayanta.
Sai da ta daste ƙiran sannan ta tura baki tana ƙun-ƙuni, can kuma ta tuno da
maganan da suka yi da baby na katin waya, dafe kai tayi a hankali cikin sanyin
muryanta ta ce, "Bari nayi sallah tukunna, zan tura miki babynmu ƙanwar miji", ta
ƙarishe faɗa tana murmushi ita kaɗai.
Sai da tayi dialling wani number da ta rubuta "ZAWJ", amma har sau uku tana ƙira
ba'a ɗauka ba, haushi taji ta jefa wayan kan gado, tana tura baki har da bubbuga
ƙafa ta yi hanyan toilet.
Jidderh alwala ta ɗauro ta zo ta saka hijab tayi sallah, ta jima tana addu'ointa
sannan ta shafa, tare da mayar da darduman da hijab ɗin mazauninsu.
Banɗakin ta koma tayi wanka ta fito ɗaure da towel mai madedecin girma,