Showing 21001 words to 24000 words out of 31290 words

Chapter 8 - Rayuwar Raihana Part 2 Hausa Novels by Takori Kabara.pdf

rungume jikin Baba Dacta ranar ‘graduation’ dinsa daga
MBBS. Kin kallon hoton ta yi, ta yi maza ta kunshe idonta cikin kafafunta.
Sai Juma ta yi dariya a ranta ta ce, “Kunya kamar Yalwati, ga rayuwar birni ba ta sa kin yi watsi
da ita ba. Ta soma tunano kuruciyar mahaifiyar Rayhanah, haka take da kunya da rashin wayo.
****

ASALINSU
Su ‘yan asalin Takai ne gaba da baya, basu da wata daukaka ko wani mulki ko suna
(reputation) kawai bayin Allah ne da suka fi karfin abin da za su ci, da wanda za su daura. Da
ita da Gwaggo Jummai kakar su Rahane uwarsu daya ubansu daya.
Lokacin da Malam Rashidu ya fito neman auren Rahane (Yalwati) dukkansu babu wanda ya
marawa al’amarin baya, ba don komi ba kuwa sai don cewa ba haifaffen Takai bane bakon
haure ne daga Tsangaya, wani kauye cikin karamar hukumar Albasu. Amma ba don karancin
samunsa ba. Ko da Rashidu ya yi alkawarin ba zai raba ‘yarsu da mahaifarta ba basu yarda ba, Babanta ne
ya yi musu bazata ya karbi sadakin Rahane daga Mal. Rashidu, ya ce ko bangon duniya ne ya
kaita, ba inda aure baya kai mace, balle ina Tsangaya ina Takai? Ban da neman zance irin na
mata? Sai kuma Rashidun ya basu mamaki da soyayyar da yake yiwa Yalwati. Ya je ya tattaro komi
nasa daga mahaifarsa, bai bar ko allura ba. Dama gaida mahaifiyarshi Iya Bilki ke kai shi
Tsangaya sai ya je ya dauko abarsa ya ajiyeta kusa da shi, uba ya jima da rasuwa, dangi sun
kare, ita kadai ta rage mishi. Ya kawo ta ya ba ta daki a gidan mahaifin Ado da yake haya a ciki. Bayan mahaifin Ado ya rasu, Ado ya gaji gidan. Zamane suka yi mai dadi shi da Rahane da

mahaifiyarsa, domin Iya Bilki ba tsohuwar banza ba ce ta san abin da take yi. Ashe zaman nasu
na dan takaitaccen lokaci ne (shekara biyu) Allah ya karbi ranta wajen haihuwar Rayhanah.
Don haka iyayen Yalwati (Rahane) basu ji ko dar wajen ba shi Zinaru ba, a lokacin da Iya Bilki
ta nemi hakan. Ta je ta zuba musu rashin mutuncinta ta fito ta koma gidan tsohon mijinta a
Albasu.
A lokacin da Iya Bilki ta rasu Inna Juma ba ta Takai tana birni tana wanke-wanke tsayin wasu
shekaru masu yawa tun bayan rasuwar mijinta Malam Saleh, ba ta kara jin duriyar Rahane ba
sai da ta dawo birni take tambayar al’ummar kauyen, su ma suka ce basu sani ba, amma dai
kowa ya san sunyi rikici da Ado, wanda shima ya dade baya kauyen sai da cutar zamani ta
dawo da shi jinyar dole gida.
A bakin Ado ne ya ce ta bincika gidan Hakimi shi can ya barosu. Inna Juma ba ta yi kasa a
gwiwa ba ta ci gaba da binciken Rahane da Zinaru har Allah ya hada su.
Ta kawo gwauron numfashi ta daga ido tana duban Rahane, wadda barci ya yi awon gaba da
ita. Ta mike ta kashe mata fitila ta kunna mata na’urar sanyaya daki, da yake ta yi rayuwar Birni
ba ta da duhun kai sam. Ta jawo kofar dakin ta nufi wanda aka ce shine nata.
****

Rahane ba ta kara tsinkewa da irin kaunar da Baba Dacta ke mata ba sai a washe garin ranar
da safe. Safiya ta farko a gidan miji, wacce ke cike da sauyin rayuwa a gareta.
Ta tashi ne ta jita cikin wata irin nutsuwa da ba ta taba ji ba a kafatanin rayuwarta, ta daga kai
tana kallon dakin barcin nata. Fentin dakin fari tas, haka marbles din tsakar dakin. Ga wasu
ubansu English-Furnished Funiture bakake da ratsin silba, labulen ma silba ne da ratsin baki,
split na aiki. Katifar gadon ta ruwa ce kamar kana kan gajimare. Ba ta kara tsinkewa ba sai da ta shiga bandaki domin dauro alwala da wanka, inda ta ga
bakonta ya iso (period). Don haka wankan ta yi, cikin lokokin saman da aka yi a bandakin ta
samu pad da pantis ta gyara kanta, bayan ta yi wanka.
Ba ta da yawan ado, Pakistan ruwan toka kawai ta zura, ta fesa spray ko lotion ba ta shafa ba
kasancewar zafi ake yi. Ta yi tattaki ta fito falo. Duniyar Turawan da Daddy ya shirya mata ko
‘yar gwamna sai haka, komai cool ba harbatsiya, abin kayatarwa a ido, kujerun kansu yatsu ta
kai tana latsasu, domin kyansu da santsinsu ya isa (Leather Francaise) maroon da ratsin
makuba, haka labulayen ma kalarsu kenan.
Dakunan barci uku ne a falon, na Inna Juma yana falon kasa, shigifar duk da ta shiga kalar
kayan dakin daban ne. Musamman Baba Dacta ya taho da decorators din da suka gina gidan
daga Ireland, sune kuma suka shirya gidan.
Ta shiga nan ta fita can har ta jefa kanta dakin da Gwaggo Juma take, tana kan darduma tana
lazimi da carbinta mai ‘ya’ya dubu cunkus a gabanta. Ba ta katseta ba bayan sallamar da ta yi,
Juma ta daga kai alamar amsawa, sai ta fada gadon Juman kawai ba ta san sanda barcin
gajiya ya sake yina won gaba da ita ba. Tunda aka fara al’amarin nan ba ta samu isasshen
barci irin wanda ta samu yau ba.
Da Juma ta gama laziminta, kicin ta fada tana yi musu abin da za su karya da shi. Duk na’urori
ne fal da yawa ba ta san amfanin su ba. Amma ta san yadda ake amfani da Gass Cooker.
Nan ta bude store babu abin da ba a zuba ba ta fannin kayan abinci. Haka firij babu nau’in
nama ko kifin da babu dankare cikin kankara a freezer. Ta debi dankali (potatoes) ta soya musu

da kwai, ta dafa musu shayi a filas, kayan shayin ma duk gasu nan a cikin irin kwandon nan mai
tayoyi, ta hado komai ta dawo dakin nata.
Har zuwa lokacin Rahane na barci. Sai ta ci gaba da ‘yan kintse-kintsen tsummokaranta cikin
kwabar jikin bango. Ba ita ta tashi ba sai karfe goma da rabi, ta koma dakinta ta yi brush ta
dawo suka fara karyawa.
Haka suka ci gaba da zamansu cikin kwanciyar hankali. Alal hakika Rahane ba ta iya komai da
ya shafi girki ba, domin Mami ba ta sa su girki, ita take yi in tana gida ko kuku.
Haka Iya Bilki Allah ya ji kan rai ba ta bata tukin tuwo sai kwashewa da rabawa. Don haka Juma
ta fuskanci hakan, sai ta dage wajen koya mata girki, mafi yawa na gargajiya don ita ma ba ta
iya na zamani ba. Ta koya mata kunun tsamiya, na kanwa da na gyada dana farar shinkafa. Ta
koya mata tuwo na alkama, na semo da na shinkafa. Ta koya mata sinasir da miyar ganye,
waina da taushe, fankaso, dambun shinkafa, moi-moi (Alala), gashin kaza cikin oven da soya
ta, dambun nama and much more. Yau ga shi har sun kwashi wajen watanni uku.
Daddy kan zo wani zubin in ya taso aiki su gaisa, ya ji ko suna da damuwa ta kudi ko ta cefane,
kuma ka’ida ne muddin ya zo sai ya ba ta kudi ko tana bukata ko ba ta bukata, bai taba yi mata
zancen angon ba, ita ma ba ta tambaya ba, sai dai ta fuskanci Daddy cikin damuwa yake yana
dai yin kokari ne na boyewa amma har ya rame shi bai san ya rame din ba. Kamar dai yau da ya zo ya kawo mata computers sabbi gal har guda biyu, laptop da Ipad, da
conecction dinsu da komai, tana ta godiya duk da bai bata waya ba. Tata a can gidan Mami ta
barota ba ta dauko ba tun ranar da Mamin ta kore ta. Ba ta damu ba, farin cikin wadannan
computers yasa ta manta da komai. Haka ya tafi babu kuzari a jikinshi. Damuwar Dr. Mansur kuwa shine, Ibraheem na neman ba
shi kunya. Tun maganar farko da suka yi, inda ya ce mishi ya zaba masa matar aure ba tare da
ya gaya mishi ko wace ce ba, ya ce dai wadda hankalinsa ya kwanta da ita.
Ya tattaro ya dawo gida Najeriya haka, ya bar aikin da yake yi a Chicago kasarmu ta fisu
bukatar Nephrologists, Jami’ar ta rike shi yana part-time lecturing, haka yana aiki a babban
asibitin koyarwa na Chicago (Illinois Teaching Hospital).
Abinda Ibraheem ya cewa Daddy shine, kowacece ya zaba mishi din ya karba, in dai ba auren
zumunci bane. Zai duba bukatar mahaifin nasa ta dawowa gida cikin satin ko da bai dawo gaba
daya ba.
Tun daga wannan maganar da suka yi, bai kara samun wayar Ibraheem ba. Idan ya kira ba ta
shiga, babu shi a social network don shi dama baya sanya kansa cikin wannan abubuwan na
asarar lokaci. Daddy ya buga ya buga ya kasa samun Ibraheem wata da watanni. Ga yarinya ya
ajiye babu future plan na ci gabanta. Mami da ta gaji da ajiyar amaryar Khalipha sai tasa ta a gaban mota ta bishi da ita Abuja. Anyi
sa’a ya dawo daga Hurghada inda ya yi sa’ar samun kakanshi mahaifin Mukhlis da
‘yan’uwanshi.
An tafka shari’a a kotun Muslunci ta Hurghada tsakanin Khalipha da dangin mahaifinsa, inda ya
yi kararsu a kan sun sheganta shi, ba dukiyar da suka lamushe ba ce a gabansa, a’a,
tabbatuwar identity dinsa.
Madaura auren Mukhlis da Asma’u a Jos duk sun bayyana a babbar kotun Hurghada, inda
sarkin Jos ya ba da shaidar komai, hotunan da aka yi da Mukhlis ranar daurin aurensa da
Asma’u, har (vedio casette) da aka yi a lokacin da Mukhlis an kunna a kotun kowa ya gani.

Likitoci sun debi jini sun tabbatar. Shima Abu-Arab kakan Khalipha ya bada diary na marigayin
wanda ke rubuce da bayanin aurensa da Asma’u da niyyarshi ta kawota Hurghada cikin
shekarar. Ga hotunansu nan kala-kala shi da Asma’u da zungureren cikinta, dole dangin suka yi
saranda suka karbi diyaucin Khalipha. Amma sun nemi da ya yafe musu dukiya kam babu, sama ko kasa sun lamusheta. To dama
haka cin dukiyar maraya yake kamar cin wutar auduga. Allah ka kara mana imani da arziki na
halali ameen.
Khalipha ya yafe musu, ya kuma tabbatar musu shi ba dalilin neman shi dasu kenan ba.
Abu-Arab ya hana shi tahowa sam-sam sai da ma’aikatar Foreign Affairs ta tsoma baki sannan
kakan ya yarda ya koma bakin aikinsa.
Sai dai kuma tare da santaleliyar Balarabiyar amarya (Mimtaaz) ‘yar kanin mahaifinsa. Khalipha
yaso ya turje, suka ce bai isa ba. Ya gaya musu Mamanshi ta yi mishi wani auren ko tarewa ba
ayi ba, suka ce ai al’adarshi ta yarda ya zauna da mata hudu ma ba biyu ba, duk bayanin da ya
yi kokarin yi musu mai nuni da cewa zai shiga matsala da mahaifiyarshi kakansa ya ki yi masa
uziri.
A karshe ma kuka yasa masa, ya ce a yanzu shi yake gani kamar Mukhlis, zamanshi tare da
‘yar’uwarshi Mimtaz shine kawai alfarmar da yake so ya yi mishi kafin Allah ya dau ransa, ya
tsufa sosai, amma hakan bai hanashi hada kan iyalinsa ba, ta hanyar kulla auratayya a tsakanin
matasan jikokinsa. Don haka Khalipha ya yi tubus, ya kara neman alfarmar Mimtaaz din ta zauna a Hurghada ya je
ya yiwa mahaifiyarshi bayani tukunna ya dawo ya tafi da ita, zai dauki nauyinta.
Nan ma tsoho ya ki yarda, ya ce kafarshi-kafarta in yaso uwar tasa ta yi gunduwa-gunduwa da
ita tasa a miya. Rigimar wannan tsoho da yawa take...... in ji Khalipha. Sai ya sako sullubebiyar
matarshi a gaba suka sauka a gidan shi na Abuja.
Rayuwar Khalipha da Mimtaaz ta watanni biyu kacal sai ta zamo abar alfahari a zuciyar
kowannensu. Mimtaaz ta ci sunanta Mimtaaz wato (excellent). Kaunar jini mai karfi ta haifar da
tasirin da ya fi soyayya karfi. Yarinya danya shataf mai tarin baiwarwaki da falaloli da yawa daga
indallahi. Sai ga Khalipha yasa Mimtaz dinsa a barin damansa sun cilla Birnin Manzo yin umarah, daga
nan suka wuce Sweden suka kwashi sati biyu suna (honey-mooning). Sai ga bakin cikin dake
zuciyar Khalipha yana yayewa, haske ya cika shi farin ciki ya maye gurbin bakin ciki.
Sai dai kullum ya kan tuna Rayha, ko wane hali take ciki? Addu’a yake mata ba dare ba rana
Allah ya zama gatanta kamar yadda ya yi mishi gata ba don ba shi da shi ba. Sai don ya dubi
zuciyarsa mai kyau ce a kan kowa, mai son farantawa uwa mahaifiya don gamawa da duniya
lafiya. Haka yake kyautata zato a kan ita ma Rayhanah. Kwanansu biyu kenan da dawowa daga Sweden Mami ta iso da amarya Radhiyyah a gaban
motar ta, maigadi bai hana Mami shiga ba don ya santa. Ma’auratan na falo Khalipha na
karantawa Mimtaz wani novel mai suna (Surgeon’s Wife) na Azizah Idris Gombe, kasancewarta
mai son labaru. Haka yake bata lokaci ya yi ta karanta mata in ya dawo ofis, da yake tana jin Turanci sosai don
a jami’ar Coventry take karatu aka tsigeta aka yi mata auren. Witness to Tears ma na Abubakar
Gimba duk ya karanta mata tun a Sweden, The Burden of Memory na Wole Soyinka da wasu
daga cikin na Babansu William Shakespear da yake Literature take karanta, ita kuma tana kusa

da shi tana fifita masa shayin da yaji suga da na’a-na’a, daga shi sai singlet da wando
short-nicker Mami ta yi sallama a falon, hannun Radhiyyah cikin nata.
Sai ta tsaya kawai kamar an dasa ta ana kallon-kallo tsakaninta da Mimtaaz, ba fuskar kowa
take gani a fuskar Mimtaaz ba face fuskar Mukhlis (mijinta na fari), Balaraben Hurghada Mukhlis
Abu-Arab. Don haka ta tsaya stand still ta kasa gaba ta kasa baya, amma bakinta ya mutu ta
kasa yin ihun da da farko taso ta yi na ganin Khalipha da macen da ba tashi ba. Duk da haka ba komai bane kuma ba abin mamaki ba a wurin matasan yanzu, musamman
wadanda ke jike cikin naira suke kuma jan ragamar rayuwarsu irin su Khalipha. Sai dai tana da
yaqinin nata dan, ba zai taba yin hakan ba tunda ita dai bata taba yin zina ba a rayuwarta ko
kafin ta Musulunta. Shekaru talatin da biyar a baya suka shiga dawowa suna giftawa a idanunnta tamkar majigi.
****
[12/24/2019, 21:47] Takori: RESHE YA JUYE DA MUJIYA!
“Anzo Takai, ina na Takai ku sakko!”
Kwandastan yake ta fadi, yana bubbuga kofar motar.
Rahane ta daga ido tana kallon mahaifarta wadda har gobe ba ta canza a idanunta ba, duk da
dadewar da ta yi ba ta zo ba tun rasuwar Babanta.
Ga tafasa ta nuna, gero da masara sunyi yabanya kore sharr dasu, da yake lokacin na damuna
ne. Da kyar ta cira kafa da ta yi mata tsamin gaske ta fito daga motar.
To gata ta dawo gida, amma wajen wa za ta a Takai? Ba uwa, ba uba balle dangi. Ko gidan
gado ba ta da shi, balle ta je ta share ta zauna.
Wata zuciyar ta ce, “Ki tafi gidan Hakimi”. Wata kuma ta kalubalance ta da cewa, “A sanadin wa
kika san Hakimi da iyalansa? In kika je gidan Hakimi kin je rokon a mayar dake gidan Dr.
Mansur ne, a hada Mami da Daddy fada a kan gaskiyarta, ba ta yi isar da za ta hada mu’amalar
jini da ita ba. Don haka ba ta ga laifin Mami ba don ta raba danta da ita, sai ma laifin ita kanta
da ta gani, da ta bari zuciya ta rudeta ta mance da reality na rayuwa na dai-dai ruwa dai-dai
tsaki ta amince da soyayyar Khalipha.
Har zuwa yanzun kuma babu abin da ya canza daga soyayyar da take yiwa Khalipha, domin
soyayyar ba shigar sauri ta yi mata ba, balle ta fita fit! Farat daya. Circulating ta yi a hankali cikin
jini da tsoka har ta huda kashi ta shiga cikin bargonta. Sai dai ta amincewa kanta ko soyayyar
za ta kasheta, har abada ita da Yaya Khalipha.
Ta kai gefen hijabinta ta share hawayen da suka zubo mata a wannan lokacin. Ba wanda ta
tuna a wannan lokacin sai Zinaru kanwar mahaifiyarta Yalwati da Malam Rashidu ya aura ya
saki, rabonta da Zinaru tun ranar da ta bar gidansu.
Ta sani cewa duka kakanninta na wajen uwa sun rasu, amma Zinaru tana raye, za kuma ta iya
sadata da wasu daga cikin dangin Yalwati in akwai, idan ita ba za ta zauna da ita ba har zuwa
lokacin da Allah zai ba ta miji a nan Takai dai-dai da rayuwarta, wanda ba zai kalli tushenta,
asalinta da tsohuwar lalurarta ababen kyama ba, tunda tushe da asalinsu daya. To yanzu ina za ta nufa neman Zinaru? Shekarun da yawa, Takai da girma. Abin da ya kara
ruruta wutar kukan da take yi kenan.
Ta bi gefen titi ta soma tafiya tana kukan, amma ta toshe bakinta da hijabin. Tafiya take cikin
zafin nama ba tare da ta san inda take jefa kafafunta ba.

Horn din mota ta ji a bayanta ba kakkautawa, amma ba ta juyo ba ta ci gaba da tafiyarta, tunda
ta san ita dai ba a tsakiyar titi take tafiya ba balle a ce ta matsa. Sai ma ta kara azama ta soma
shigewa cikin gonakin masara.
Fakin din motar aka yi a gefe aka biyota da kafafu. Muryar da ta ji na kiran sunanta da karfi ya
sata juyowa cikin razana da firgici. Baba Dacta ne da Sha’aban dan wajen Hakimi. Ya fi karfin ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login