Showing 42001 words to 45000 words out of 68809 words

Chapter 15 - JARABTA Compelet Book hausa novels by Maman Abdul Shakur.pdf

M Shakur   

14 Nov 2025

1076

mai kyau yace "mekike yi akasa haka" yakarashe maganan yana murmushi
wani karfi ne taji yadan zomata da kyar ta tashi tsaye tahau kan jikinshi ta yaye rigarta sama
tana wani irin lankwashewa tanuna mai cikin ta dan tamakasa magana, adan rude ya kalli cikin
ganin yanda yake wani motsi up and down da kyar tace "cikina Ya..." kasa karasa maganan tayi
tawani shige jikinshi tana bangarewa, fashewa tayi da kuka sosai ta kankameshi tana wani irin
mika, adan rude ya wawwaigawa baiga kowaba da sauri yaciro fuskarta daga jikinshi yace "ina
Farida?" kasa magana tayi saima wani kanannade shi data sakeyi tana wani irin lankwashewa
kaman macijiya tana kuka, hanunshi ya daura akan cikin wani irin motsi da kara yaji ba karamin
faduwa gabanshi yayiba ciro kanta yayi daga jikin nashi ya kwantar da ita anan kasa ahankali
da idanunshi dasukai jajir yace "am coming" tashi yay yay bedroom yana kwallama Farida kira
"Farida Farida" har bayi saida ya bude bata, hakan yasa yafito ya shiga kitchen da sauri nanma
bata harzai fito saiya hango farin leda dakuma farin marfi akasa kusa da bin, hakanan yaji
zuciyar shi bata kwantaba shiga kitchen din yayi yana kallon ko'ina dan wari warin magani
yakeji, digon wani abu daya gani akan fridge kaman mai yasa yasaka yatsa ya dangwala yakai
hanci ya shinshina warin magani yaji kaman kalanzir da sauri yakoma wurin bola inda yaga farin
marfi akasa ya daga yakai hanci same wari yaji tashi yayi yana kalle kalle bolan ya leka ganin
Goran sniper a kwance cikin bolan yasa yaciro yana kallon goran dan yasan babu irin goran
nan agidan, harda dan gudunshi yakoma falon plate din Indomie daya gani yaje yadaga
yanama abincin wani irin kallo, shinshina abincin yayi da sauri ya ijiye yadau juice din ya tsiyaya
a cup abu kaman maimai dayagani a kwance kan saman juice din cikin cup din yasa ya dafa
kirjinshi jin yanda ya buga da karfi yace "innalillahi wa innailaihi raji'un" harda dan gudunshi
yazo inda take kwance tana wani irin numfarfashi tana kuka yace "waya baki abincin chan
shikikaci?" kasa magana tayi saima wani irin kukkule ido datake yi tana bubbuga kanta akasa
danji take kaman ana tsitsinke hanjin cikinta, kama fuskarta yayi yay tapping kumatun ta da karfi
yace "wayabaki abincin chan" kara fashewa tai da kuka tana nunamai cikinta da kyar ta iya
cewa "Fa.. Far" wani irin ihu tayi ta buga kanta akasa sabida yanda cikinta yay wani irin kara
dahar shi saida yaji da gudu yay gaban tv danhar yana huge kafa da center table, key mota
yadauka ya dauke ta yafita tsakar gida da gudu yana kwalama gateman kira "budemin gate"
kwantar da ita yay abayan mota yarufe da gudu ya shiga gaba yatada suka fita agidan, yanda

take juyejuye sabida azaba har saida tafado kasa daga kan kujeran juyowa yay da idanunshi
dasukai jajir yakira sunan ta "Islam, Islam" kasa amsawa tayi saima bubbuga kai datake yi a
jikin kujeran. Allah ne kawai ya kaisu asibitin lafiya dan yana tuki yana kallon bayane yanda take
nukurkusu akasa. Idan kaga Khaleel zaka zaci ya haukace ne sabida yanda yake ihu a asibitin, da gudu aka
karbeta Dr yace "maiya sameta" da kyar ya iya cewa "I think sniper aka bata" ganin yanda
tawani bankare zata Fado daga kan gadon da aka daurata yasa ya riketa yace "Islam Islam am
here babu abinda zai sameki kinji" cikin wani daki akai da ita ya bisu amma akace yafita.
Har sunkai layinsu itada me napep din daya dauketa sai kuma taji jikinta yay wani irin mugun
sanyi yanzu sabida namiji zata iya kashe Islam? Wata zuciyar tacemata amma ai idan ta mutu
zai aureki, dafe kanta tayi tana girgizawa da sauri tace "no no, I can't do dis, Islam jini tace " da
sauri ta kalli driver tace "malam komar dani GRA dan Allah kayi sauri" juyawa sukayi addu'a
kawai take ido arufe Allah yasa bataciba jikinta har wani bari yake, har suka kai sauka tayi
tacemai yajirata da gudun ta ta shiga gida mai gadi namata magana amma Kota kanshi batabi
ba, a bakin kofa ta tsaya ganin plate din Indomie andan ci kadan sanan ga dan kwalin material
dinta akasa maganan mai gadi taji tabayan ta yace "Hajiya basanan yanzun nan alaji yafita da
ita kaman hajiyar ba lpy ne" wani irin bugawa kirjinta yayi tai wani irin suman tsaye, da kyar ta
iya cemai to ganinan fitowa, wani luuu tayi zata fadi da kyar ta iya dafa bango tana kwalalo
idanu tareda dafe kirjinta kaman wata mahaukaciya tafara lalubar jakarta watsar da komi tayi na
jakan kasa ta ciro wayarta hanunta har wani barbar yake number Abba tai dailing ringing daya
Abba ya daga kafin yay magana tace "Abba, Abba, Abba na kasheta, Abba nakashe yar uwata,
wlh wlh bansan meyakai ni bata sniper ba, Abba na shiga uku shairin shaidan ne" maganganu
kawai take zaroma Abba kaman zarrara hakan yasa Abba hankalin shi yatashi kodai Farida ta
zarene ahankali yace "Farida mekike fadine haka wakika kashe?" "Islam, Abba kanwata, yar
uwata jinina nakashe yau, Abba..." katse wayar Abba yay jin yanda take xazzaro maganganu
kaman mara lpy number Khaleel dayaji kotaje gidan sune dan yasan batasan gidan bama, yay
dailing number saida ya kusa katsewa yay picking ahankali yace "Abba" tashi tsaye Abba yay
daga kan kujera dan yanda yaji muryan Khaleel yasa kirjinshi yawani irin mugun bugawa
"Khaleel meke faruwa yanzun nan Farida takirani" da kyar Khaleel ya iya cewa "muna general
hospital Abb..."wayarce tafadi kasa ta tarwatse sabida yanda jikinshi ke wani irin rawa, ganin
ankara gunguro Islam daga dakin datake, wani irin abu kaman babban straw abakinta wata
nurse kuma ta rike jakan ruwa da ake dura mata ta bakinta dan yay washing cikinta sunyi ICU
da ita, da gudu yabisu amma har an shige da ita anrufe kofar bubbuga kofar yake kaman zai
fasa yana kiranta, ahankali ya sulale ya cusa kanshi acikin kafafu tareda sanya hannu akan
wuyarshi yafi 15mins ahaka a wurin, bayanshi yaji andafa hakan yasa ya dago jajayen idonshi
Abba yagani da Anty Hindu dakuma Mum kana ganinsu kaga tashin hankali karara akan
fuskokin su.

Farida tafi minti 10 tsaye a wurin sanan ta daddafe bango tafito tana ganin jiri ta shiga napep
din tareda cemai muje, tafiya kawai suke dan gabaki dayanta bata hankalin ta da kyar tace
"kaini asibiti" "wani asibiti hajiya" Ahankali tace "kowanne" tafiya suka dingayi yay parking
agaban general hospital yace "kije wanan sunfi kwararrun likitoci Allah sawake" duka kudin

purse dinta taciro tabashi kaman wata tababba take tafiya har taje reception tana waige waige
Allah sa nan suke, hijabin Anty Hindu ta hango ta cikin emergency ward hakan yasa ta daga
kafa da kyar ta shiga ward din, tsayawa tayi daga ta wurin kofa tafashe da kuka sosai tana
kallon su yanda suka tsattsaya gaban ICU. Dago kai Khaleel yayi karap suka hada ido da ita, mikewa tsaye yayi kaman namijin zaki yana
kallonta hakan yasa Abba suka jujjuya suna kallon inda yake kallo, hannu ya daura akan belt
dinshi na jikin wando yana kwancewa batare daya dena kallonta ba, wani irin Fizgo belt din yayi
azuciye koni bantaba ganin Khaleel ahakaba wanan zuciya hmmm! Ko kallon fuskar su Abba da
mutanen dake ward din baiyiba yay inda take tsaye yana tafiya kaman wani mayunwacin zaki
jikake fui fui fui dukan Farida yake da belt Kota ina...

Ahankali Islam ta rike hanun Dr yake daddane cikinta tana amayar da ruwan dasuka duramata
ta baki, wani irin hawaye ne ya gangaro daga gefen idanunta da kyar ta iya magana tace
"please stop abinan dakekemin yamafi min azaba kan komi, please I want to see my husband"
yanda tai maganan yasa jikin Dr yay sanyi sosai, wani irin tari tayi hakan yasa ruwa yakara
fitowa daga bakinta tace "please I want to see him" ahankali Dr yajuya yafita daga dakin hango
Khaleel dayayi yana chasa Farida ga mutane duk antaru ana kallo su Abba dai na tsaye danko
yunkurin kwatota basuyiba Mum ce ke kuka sosai, da gudu Dr yay wurin yana "subhanallahi"
rike belt din yayi yana kallon yanda Farida ke kuka kaman zata mutu, dawani irin ido Khaleel da
kallai, girgiza mai kai Dr yayi tareda janshi yace "kayakuri, Matar ka nason ganinka" bin bayan
Dr yayi aka budemai dakin ya shiga kadan tabude idonta tana kallonshi da sauri yay kanta yana
shafa kanta hawayen daya gangaromai ya share yama forehead dinta kiss yama kasa magana
hanunshi yaji tarike gam hakan yasa ya dago kai yana kallon fuskarta, twisting jikinta tayi tareda
fito da ruwa sosai daga bakinta tashi yayi zaije yakira Dr yaji takara kamkame hanunshi da sauri
ya kalleta, dan murmushi tamai sanan ta bude bakinta da hakoran ta dasuka dan hade tafara
magana, da sauri yakai kunen shi saitin bakinta yaji tace "Yaya Khaleel inaso Kamin alkawari"
tadanyi shiru tana numfashi sama sama tace "inasonka sosai, I love you so much Muhammad
Khaleel" daura fuskarshi yay akanta ahankali ya lumshe ido wani irin zazzafan hawaye ne suka
zubo daga idonshi suka sauka agoshin n
ta da kyar yace "and I love you more than anything Islam, please stop talking, kidena magana
kinji u will be fine lemme go and call d Dr" yajuya zai tafi hanunshi takara kankamewa tana
kallonshi da idanunta dasuka kankance tafara magana, kai kunenshi yayi saitin bakinta ahankali
yaji tace "Kamin alkawari, promise me zaka auri Farida idan namutu, Farida na sonka so na
gaskiya, promise me" Ahankali ya dago kanshi dudda bata da lafiya bai hana ya mata wani irin
mugun kalloba ya fizge hanunshi daga nata yana goge wasu hawayen bakin ciki dasuka zubo,
da kyar ta iya daga hannu ta mikamai idanunta na fitar da hawaye ta gefe, ahankali ya tako
zuwa gabanta yarike hanun gam zatai magana yadaura yatsan shi akan lips dinta ya girgiza
mata kai idanunshi sunyi jajir, idanunta yaga sunsoma jujjuyawa wani irin nishi tayi tafara wani
irin nannade kanta tana bankarewa sabida yanda cikin nata yafara wani iri kaman ana kakkatse
duk wani hanji naciki, ihu Khaleel yay yace "Doctor".
[6/23, 11:35 PM] Maman Jedda: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

53...

Ihu yake yana kiran Dr tareda danna alarm din gefen bed nakiran Doctors, hakan yasa Abba
yana ganin Doctors din sunzo zasu wuce dawayan su nurses suna gudu yabisu hankali atashe
suka shiga dakin...
Wani irin mugun rawa da jijjiga jikinta keyi tana kallon sama idanunta na kakkafewa tawani irin
bankarewa dan kumfa kumfa na fitowa daga gefen bakinta ta rike zanin gadon gam, riketa gam
Khaleel yayi yana wani irin ihu "Islam-Islam stay with me" yanda yaga jikinta ko ina narawa tana
wani irin mimmikewa yasa yafara "innalillahi wa innalillahi raji'un, innalillahi wa innalillahi raji'un,
Allahumma ajirni fi musibati" harda gudu Doctors da nurses din suka karaso wajen gadon da
sauri wani babban Dr dan tsoho nema ya kalli wata Nurse yace "kunna Defibrillator, her heart is
over racing" handglove ya dauka daga gefen gadon yasa da sauri yadau paddles din
defibrillator ya rike yay robbing dinsu together sanan yadaura akan kirjin Islam dake kakkarwa
yay ihu yace "clear" kaman electric shock wani irin bangarewa Islam tayi sanan takara komawa
kan gadon bam, cirewa yay yana kallon machine din yana reading abunda yake nunawa sanan
yakara putting dinsu together ya daura akan chest dinta yay shouting "clear" kara bangakarewa
tayi tayo sama sanan takoma kan gadon idanunta na kukkulewa wani irin kara machine din
yafara "diiiiiii
, din, din, din, din" ahankali Khaleel yafara komawa da baya da baya yana kallon fuskarta yana
dafa bango, sama sama yakejin Dr yana "cewa one more time we can't loose her" dumm yaji
kunenshi yayi sanan ya dauke, ganinshi yay duhu, yay baki, chan sama sama kaman daga
nesa yaji machine din yay kara sosai sanan kuma shiru, sama sama yaji likitocin suna "we are
loosing her.. Time of de... " dip yaji kunenshi ya dauke yadena jin komai idanunshi suka rufe ruf.

Good morning lovelies
[6/23, 11:35 PM] Maman Jedda: *JARABTA*


Maman Abd Shakur

54...

Ahankali yake bude idanunshi dasuka mai mugun nauyi ga kanshi dake mugun sarawa, da kyar
ya iya bude idanun duka ya sauke su akan wani Dr dayaga ya rikemai hannu yana shafa tafin
hanunshi yana bubbugawa, sama sama yakejin doctor nacemai "can u here me, I need you to
tell me your name" kadan kadan idanunshi ke kukkulewa ganin gabaki dayan dakin na juyamai
in a circle, kara bubbuga tafin hanun nashi Dr yayi yana rubbing tsakiyar yana kallon fuskar shi
da kyar yasake bude idon yadan kallai kadan yace "can you hear me? Me sunanka?" da kyar ya
iya bude bakinshi sabida wani irin nauyi dayamai sosai yace "Islaaam, I want to see her" yana
maganan yana kukkule ido har suka rufu tass, murmushi Dr yayi ya juyo ya kalli su Ammi harda
Goggo dasuka tsattsaya kowannen su hankali tashe yay murmushi yace "Alhamdulillah ya

farka, anytime from now zai farfado full.. " "Islam" da Khaleel yakira yasa dukansu harda Dr
sukai kanshi wanan karan yabude idon duka saidai kanshi dayaji yana mugun ciwo, Ammi ne tai
maza ta rike hanunshi tana share hawayen dataji yazo mata, ahankali ya kalleta yace "Ammi
ina Islam?" shafa goshin shi Ammi tayi tana girgiza mai kai tace "kafara hutawa tukunna Son,
kasan yau kwanan ka Uku unconscious ko" ta kalli Dr dake checking pulse dinshi tace "Dr
yayake yanzu?" murmushi Dr yay yace "Alhamdulillah he's pulse is stable, blood pressure din
kuma yadawo normal, ku taimaka mai yay wanka da lukewarm water it will really help him"
kokarin tashi yake amma yakasa sabida yanda kanshi yaji kaman zai fadi ahankali ya kalli
Abban shi da Umma da Yusuf da Goggo dake wajen dakuma Anty Hindu da idanunta sukai jajir
sabida tausayi hanunshi ya daga da kyar yay pointing Anty Hindu ahankali yace "ina Islam
dina?" bude kofar dakin akayi hakan yasa dukansu sukabi kofar da aka bude da kallo
wheelchair din asibiti yafara gani, dan dago kanshi kadan yayi da taimakon Mum yana kara
kallon kofar, Abban Islam yagani ya gunguro Islam dake zaune akan wheelchair ta duke kai
sosai dan bata iya dagowa complete sabida cikinta, lips dinta sun kumbura sosai sunyi jajajir
bakinta nata dilallar da miyau, kasa dauke kanshi yay daga kanta har Abba yakawota jikin
gadon dayake ya tsaya, kokarin tashi yake Yusuf yayo kanshi zai taimakamai ya tashi dagamai
hannu, alamun yabari, rike kanshi yay ya sakko daga kan gadon da kyar kaman zai fadi, da
kyar ya iya ya tsugunna agabanta ya mika hannayen shi ya daura akan fuskarta ya dago kanta
yana wani irin kallonta idanunta alumshe, ahankali dawata irin murya mai taba zuciya yace
"Islam" shiru tayi batare data bude idonta ba batare datace mai komiba, ahankali Abba yace
"Muhammad Khaleel Ummi tasamu nakasu guda biyu, na farko dai tana fama da wanan
uncontrollable zuban miyau wato drooling, nabiyu kuma tunda ta farfado ko uppan batace ba,
Dr yace yana tsammani Sniper yamata dameji a wuya ne amma basuyi concluding ba, sanan
bata iya mikewa tsaye sabida intestine dinta wai basu warkeba tukun, and kaga bakinta yanda
yakoma" Abba yadanyi shiru sanan ahankali yace "banason na daurama dawainiya aka, after all
yar uwarta ce ta maida ita haka, to Khaleel idan baka sonta, idan bazaka iya zama da itaba wlh
bazan taba ganin munin kaba, bazan ji haushi ba, zaka iya sauwake mata" tunda Abba yake
maganan yakasa dauke ido daga kanshi gawasu jijiyo yi dasuka fiffito a forehead dinshi, da kyar
ya iya janye idanunshi daga kan Abba sanan ya kalli Islam dahar lokacin taki bude idonta,
ahankali yasake matasawa kusa da ita yadade yana kallon fuskarta da bakinta dake dulalar da
miyau ya daura kanshi akan cinyar ta ya fashe da kuka sosai, Yusuf ne yafara fita daga dakin jin
idanunshi sun kawo ruwa, hakama sauran iyayen da Dr suka fita daga dakin yarage daga shi
sai ita, yafi 5min yana kuka sanan ya dago kanshi ya share idanunshi da kyar dan muryanshi
ma ta dishe yace "Wife" ahankali ta bude ido ta sauke su akan nashi, ganin yanda yake kallonta
yasa ta daga hanunta ta rufe fuskar ta tana wani irin kuka mara sauti dan kunyan fuskarta take
sosai, hannu yasa yakamo hanun ya saukar dasu yana girgiza mata kai, hanunta ya daura akan
kirjinshi daidai wajen zuciyar shi ya goge kwallar data zubomai yace "kinga wanan zuciyar, only
beat for u" ahankali yace "koma yakike, koma yakika koma, koma menene you will always be
my Islam, my one and only wife, wacce nakeso wholeheartedly" sosai yaga take kuka ahankali
ya kai hannu ya share mata hawayen dake zubowa yace "am sorry, am sorry Islam is all my
fault" hannu tasa ta kara kare lebenta tana kawad dakai dan ba karamin kunya takeji ba idan
yana kallonta, wani hawayen yasake gogewa ya juyo da fuskar nata tareda saukar da hanun
nata yana girgiza mata kai ganin yanda take kuka mai cin rai, ahankali yakai bakinshi ya daura

akan katon lips dinta dake fitar da miyau.

Guys yau weekend am a little busy ne so manage this I love you all.
[6/25, 2:17 PM] Maman Jedda: *JARABTA*


Maman Abd Shakur

57 & 58

Batare daya dago kaiba yace "Islaaam" kadan ta kallai dan wahalan bude idanunta duka takeji
sosai, murmushi yay ya matso da kujeran saitin fuskarta yasa hannu yana shafa kitson kanta
ahankali ya sumbaci forehead dinta sanan ya shafa wurin yana kallon fuskarta murya chan ciki
yace "I have to go yanzu 7 ake koran mutane but da sassafe zanzo gobe" shiru yay yana kallon
fuskar ta ganin kaman tai bacci danta lumshe ido, addu'an bacci ya tofa mata sanan ya matsar
da kujeran baya yatashi, yadade a tsaye kafin ya juya da zumin tafiya hanunshi yaji takama da
sauri ya juyo ya kalleta, girgiza mai kai yaga tanayi da dan idanunta data bude kadan ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login