Showing 27001 words to 30000 words out of 82745 words

Chapter 10 - Sakon So Complete Hausa Novels by M Shakur .pdf

M Shakur   

09 Nov 2025

1129

yana magana zan ma iya zanashi da pencil naganshi, ranan sabida shi
bokon ma bakiso zuwa ba dan kada yazo baki kalli video ba amman Allah bless yasa kikaje
makarantan, jibidai yanda nida idona da muna kallon video naga bayin dakiketa nema akasa ki
shiga baki ganiba domin Allah ya daukemiki idanun awajen so yake kije sama kihadu da
Imrana, kikaje saman kika bangajeshi kika bata mishi kaya da fanta amman fuskanki nakan
waya shaidanin nan kike kallo kika wuce bayi nafi kowa sanin yanda kike neman waje shiru ki
natsu duk sanda zaki kalli Mandawari dan ko ni nan idan zaki kalla uwardaka kike shigewa ko
nazo ina kwalamiki kira shiru kike ki kyaleni” shiru Gwaggo tayi sannan ahankali tace “Allah ne
ya aiko miki Imrana diyata, shima kuma Allah ne ya aikamishi ke rayuwanshi saikuma Allah
yakaddara cewa ba kaddara mai dadi bace zata fara hadakuba hasalima na batanci ne, na kalli
fuskan yaron nan nakara kallo babu abinda nagani kan kwayan idanunshi Sal dumbin alkhairai,
nasan baki sonshi shima bayi sonki, baki sanshi ba bai sanki ba amman kuma Allah yahadaku!
Allahandaya hadaku shinake roka ya dawwamar daku awanan rayuwan Auren har abada Allah
yasamishi sonki da kaunar ki dakuma tausayinki kema Allah yasamiki haka, koyau nafadi
namutu Alhamdulillah, kullum banda zullumin daya wuce wazaki aura wazai auri Lulu na,

amman kinga wannan mutumin yanada yara da sunma girma miki Dan haka ina mai kyautata
zato zai iya tafiyar dake da kyau” hannu tadaga ta tottafa addu’a sannan tashafama Lujain a
fuska kafin takashe wuta ta kwanta kaman jira Lujain take kankame Gwaggo tayi Gwaggo tace
“ahap aini nasani duk yanda takai ga bacci inhar taji dumin mutum saita kwakumeshi” kafin
kaceme Gwaggo tafara jan minshari.



Suna kaiwa gida Abee bai kula kowaba fita yayi daga motan dasauri yay flat dinsu Hajiya zata
kirashi Liman yace “kul Hajiya kubarshi, kubar yaron nan shi kadai yasan meyakeji” yajuya
yakalli su Ibro yace “ku kira likitanshi kuji” gyadamai kai yayi sannan Baba Liman yace “saida
safen ku” godiya duka sukamai yawuce, Musty da Harun ma sukama Hajiya sallama dan tun
ahanya suka sauke Abdul ya sauka a police station dinsu sukuma sauran suka shige gida.







Wuraren 2:30 wani kalan bakin yunwa ne yatadata daga bacci muryanta ya dishashe sosai
sabida kuka ahankali tace “yunwaaa” firgigit Gwaggo tafarka tocula tajawo ta haska dakin yay
haske sannan ta tashi zaune tana kunna wutan dakin tace “mussamman nasan yau dole kitashi
da wuri dan babu abinda kikaci kikai wannan wahalallen baccin, sauko ga abincin ki nan a tray”
Gwaggo tai maganan tana jawowani katon tray gaban gadon ta zauna tana bubbude mata
kulolin, sannan tadau wani babban kofi tana juye mata tea dayaji madara da Milo dake tiriri
akan a cup din, daidai nan ta sauko tana gyara kullin towel din kirjinta, Gwaggo tadauki cup din
shayin tabata ahankali takarba takai bakinta tana karban buredin da Gwaggo kebata data
yagomata kato ahannu, Gwaggo takai hannunta saman goshinta tace “kinga har jikinki yay zafi,
nida har sadaka saida nayi na murnan daina zuwa asibiti yanzu kuma zaki maidamu ne” shiru
tayi kawai shan shayin take da buredin da sauri da sauri tass ta shanye shayin tana mikama
Gwaggo kofi tace “karamin” karasa juyemata ragowan tea tayi shima yacika cup din takai
bakinta tanasha maganan su princess ne yadawo mata sabo aranta jitayi shayin da abincin
gabaki daya yafita aranta, ahankali tasauke cup din daga bakinta ta ijiye akasa dasauri Gwaggo
tace “menene kika ijiye shayin kuma keda ke shanye shayinki tass” ahankali takai hannunta kan
katon kumatunta tabuga tagumi dasauri Gwaggo tasa hannunta tacire tagumin tace “bana
gayamiki babu kyau tagumi ba” kaman jira take wani kalan rushewa da kuka tayi sosai tanuna
kanta tace “Gwaggo su princess sunce wai ni Yar iskace, ni karuwa Gwaggo ai kintuna lokacin
dana fara period kince min ko hannun namiji yarike zanyi ciki ko” Gwaggo ta gyadamata kai
itama kaman zatai kuka ganin yanda Lujain ke kuka bitterly, cikin mugun kuka tace “wlh
Gwaggo, wlh wlh ko yatsana bai tababa, baimazo kusadani ba, Gwaggo bantaba ganinshi ba
sai ranan, Gwaggo nida banda saurayi babu wanda kesona sabida ni katuwa ce inada kiba,
dawane zanyi iskanci? Gwaggo ni yanzu konaga mutumin ma bansanshi ba baranma ganeshi

ba, Gwaggo nayi ihu daga ganshi bisa ka na abayi sabida nasaka earpiece banmaji karan
tafiyan da ba, ganinshi akaina yasa nai ihun nan ba wannan ihun wanda wanda….. wanda naji
aaaa……..” tawani kalan fashe da kuka sabida yanda abin kemata ciwo, hannunta Gwaggo
takai zata share mata hawayen cikin kuka kaman wanda ta tuna wani abue tace “shine suke
kirana fasika, karuwa da Yar iska, Gwaggo ni, ni ni Lujain ce karuwa” tanuna kanta tana wani
kalan kuka mai tsuma rai dayasa Gwaggo tafara matse hawaye tana kallonta takasa lallashinta
tace “Kola harda cewa wai zaiyi Iskanci dani ya siyamini shawarma guda biyar da Fanta goma
sabida nine mayyan abinci dazan iya iskanci idan zaa bani abinda zanci, wlh banyi komiba
Gwaggo ni danasani da banmaje excursion dinba dan dama banso zuwaba” yanda take kuka
yasa Gwaggo tahau matsar kwalla tace “Allah kaimu gobe wlh wlh har ajinku zanje sainayi
dambe da gantalallun yaran nan masu tallan bushahhsen gero, shegun yara wayanda ba’a
haifesu ranan juma’a ba, ai gasunan sune zasusha kunya tunda Imrana ai yanzu mijinki ne” duk
wani kuka da Lujain keyi tsayawa yayi ta kalli Gwaggo da rinannun idanunta tana zarosu tama
kasa tambayan komi wani kalan washe baki Gwaggo tayi ganin tana kallonta tace “ai wlh kinyi
goshi Lujain dakika sami miji irinshi ga kudi, ga kyau gakuma hankali jibi girman kampaninshi
barima kiga” Gwaggo ta tashi da sauri tayi falo ta kwaso mata kwalin giro dana sweet din tace
“kinga goro da sweet na daurin aure, jiya da daddare kina bacci aka daura gaban kawunanki da
duka dangin su Imranan anan falon babanki bakiga idanun Maman su Samira ba kaman zasu
fado kasa sabida bakin ciki taga Allah yabaki mai kudi daga sama ita dake cewa barama kisami
mai aurenki ba balle mai kudi yanzu ai gashinan ke kinyi miji nata zankadaddun yaran dabata
basu abinci suci su koshi sabida karsuyi kiba na nan agabanta” Gwaggo takara washe baki tace
“dazaran kin tare da yan kwana biyu nima zan tattaro yinawa inawane nadawo gidan naku ina
zan iya zama gidan talaucin nan ubanki na fama da saida atampopi akasuwa too wlh badani ba”
wani kalan mugun kuka Lujain tasaki tace “Gwaggo ninace muku ina sonshi ne dazan aureshi
dazu nadauka tsoratasu kawai kikayi akanme zaki auramin mutumin dabanma san kamannin
shiba? Mandawari na fa”? Wani mugun harara Gwaggo tamata tana tabe baki tace “kina ganin
yanzu da wannan video naku ya zagaye yanar gizo mandawari zai yarda ya aureki idan ma ya
kulankin kenan? Yau shekara nawa kina bibiyan yaron dabaimasan da zaman ki adoron kasan
nan ba” cikin kuka tace “eh nidai shinake so, ai dama celebrity basa amsa messages da wuri,
kinsan followers nashi nawa ne almost 400million global followers, baruwanki da ni da
Mandawari, wlh wlh banason Auren nan nibaran aureshi ba” dan dariya Gwaggo tayi tace “aure
kuma tuni ya dauru yarinya naki wasane, bakida hankali yanzu lamarin nan na manya ne
kimana shiru kawai ki kalli ikon Allah” wani kalan kukan datake yasa taji cikinta na hantsinewa
ta tashi da gudu tana kukan sai bayi Gwaggo tabita duka shayin datasha amayo dashi tayi
tadasa uban kuka tun Gwaggo na lallashi ta tana bata baki harta shareta ta kwanta akan gado
abinta tai bacci itama daga baya anan kasa baccin yay awon gaba da ita.


Koda Gwaggo ta idar da sallan asuba da jan charbinta tashi tayi tafito falo tareda bude kofa ta
taho bangaren su Mama bude kofa tayi uwa an biyota tazauna akan kujera daidai Mama tafito
daga dakinta ganin Gwaggo taso tafirgita saikuma tace “lafiya Gwaggo da asuban nan” kallon
banza tamata tace “lafiyan ce takawo haka” tabe baki Mama tayi tawuce tashiga kitchen abinta
bata wani jima afalon ba saiga Babatareda Yayansu kafinma ya gaisheta hannu tamikamai tace

“bani kudin sadakinta” dan kallonta yayi da mamaki yace “Gwaggo dama zan cika kudi ne
namata kayan daki” cikeda daga murya tace “bakaji ance yanzu anan gidansu zasu zauna ba
baa gama gidanshi ba lokacin daya gama gidanshi anemo wani kudin amata kayan daki” zama
kawai Baba yayi yana kallon mahaifiyar tashi ganin haka yasa tace “ko baraka bani bane”?
Ahankali yace “zan baki mana Gwaggo amman mezakiyi dahar dubu dari biyu gabadaya”
cikeda ihu tace “yoo gyaran Amarya mana dudda ma babu wani lokaci mai tsawo yau kwana
hudu yarage atafi da ita gidan mijinta amman dai abinda zanyi kenan” Mama dake tsaye cikin
kitchen tanajinsu ahankali tace “fitinanniyan tsohuwa inama tamutu ahuta” kallon Yayan su
Samira Baba yayi yace “jeka kawo kudaden nan adakina Auwal” tashi Auwal yayi yawuce dakin
Baba baijimaba yafito da bandir na yan 1k guda biyu yakawoma Gwaggo yage takardan guda
tayi sannan takalli Auwal din tace “kaine Babban jikana kaito ga dubu biyu sadaka kasama
Auren kanwarka albarka” gudun fitina yasa yasa hannu yakarba yace “Allah basu zaman lpy”
kwalama su Samira kira tayi tace “nasan kuna jina to kuzo nan” kaman munafukai suka fito
suka gaida Baba da Gwaggo dake kallonsu tace “nasan kunsan kaddaran daya fada kan
kanwarku Lujain, koma baku sani nasan farfesan uwar ku tariga ta fesa muku labarin daga
tushe zuwa iri to yanzu dai Alhamdulillah Allah yabata miji nagari son kowa kin wanda yarasa
da ake cewa bazata taba samin wanda zai sotaba da wannan kiban babu kalan gorin da baku
mata ba to yanzu dai ga sa’an datayi dan haka nan sadakin tane zan muku sadakan dubu dai
dai duk ku sanya mata albarka” dubu dai dai tazaro tabasu amsa sukayi kowannensu yace
“Allah sanya alheri” tace Ameen, sannan takalli Baba tace “kake kallona kokaima nabaka ne”
girgixamata kai yayi tace “bari naje namata abincin kari zan fita anjima, da daddare tarinka amai
inhar naji jikinta da zafi zaka kaita asibiti” Gwaggo na maganan tana daga zaninta tana tura
kudaden a cikin lalita tawuce tafita tana kaiwa dakin akan dadduma taga Lujain din tai salla
takifa kanta akafa tana kuka hararanta Gwaggo tayi tace “aisaikiyi” kitchen tashiga tahau
dumamata shinkafan jin kukan kuma taji takasa daurewa fitowa yayi tashiga uwardakan zama
tayi agabanta tabuga tagumi tana kallonta tace “wai Lujain saikin kasheni tatas kinga bana
numfashi zakiji dadi iyye? Yanzu mikikeso fadamin”? Ahankali batare data da go kanta daga
kafanta ba tace “ni banason Auren nan ban isa aure ba kumani Mandawari nikeso” shiru
Gwaggo tayi tana kallonta saikuma tace “kikace baki isa aure ba inace nannan Aisha har ajinku
ta Islamiyya dake shekaru sha shidda tai aure har anko saida kika tasani agaba namata, su
Zainab ma dake sha bakwai ba suna zana jarabawan gama sakandire aka musu aure ba kema
inda rashin lafiya yabarki kinfara makaranta da wuri da yanzu kin tsufa da gama sakandire,
kawayenki kadai yan layin nan dasukai aure sunkai hudu yanzu da akazo kanki ne zakice baki
isa aureba, shikuma Mandawarin yasan ki? Yasan dake? Yamasan sunanki? Ke yarnan ki kiyayi
kanki da auran calamburuti ina gayamiki barinma Mandawarin nan mai kamada shaidanu har
kitso yakema gashin kanshi” sosai take kuka still bata dago kanta ba tace “wlh shiba shaidani
bane Gwaggo yanada kirki, yana bada taimako har gidan marayu yake zuwa, yarabama
guraguma keke” Haba Gwaggo takama tace “to akace miki shi kadaine mai kirkin duniya” tai
maganan tanajan hanci jin kauri natashi tace “nashigesu wannan yarinya tasa na babbaka
abinci” tai maganan tana fita daga kitchen da sauri kashe rishon tayi dan arisho take girki
tadawo zama tayi kusada Lujain din ahankali tadagota tace “haba Yar jikata Yar lukutata Yar
bulbul Yar kyakkyawa yimin murmushi ingani” ashagwabe hawaye na gangarowa daga idanubta
tamakema Gwaggo kafada irin baratayiba, washe baki Gwaggo tayi tace “naji to zan miki

abinda kikeso” dasauri tace “zaki raba Auren ki nema mini Mandawari”? Gyadamata kai
Gwaggo tayi wani kalan murmushi tayi dayasa dimples dinta suka lotsa tai bala’in kyau tawani
rungume Gwaggo Gwaggo na dariya tace “to jekiyi wanka nima fita zanyi amman bari nafara
hada abincin ki” tashi tayi tawuce bayi tsaf Gwaggo tahada mata abincin kari da shayi wani
green towel ta daura tazo ta zauna tafaraci Gwaggo tadauki mayafi tace “tonatafi kiyi zamanki
adaki kada kije konan da chan kinji” gyadama Gwaggo kai tayi.
Tun safen nan sai wuraren 4 na yamma Gwaggo ta dawo da buhu buhu na itace da saiwowi
saikuma zabi kaji da tantabaru da aka hadesu aka kullemusu kafafu, wasu yara takira tasa suka
yanka mata aka gyara tafito dasu karfi da yaji sukazo suna aiki Gwaggo tun tana yarinya tayi
gadon iya hada magunguna lafiyayyun tsumi tayi anan tsakar gida akan ittace daya hada da
zuma da mazankwaila babu suga ko digi, sai farfesun su zabin datayi na magungunan hada su
Samira tayi da Lujain din duk sukaci sannan tashiga hada farfesun jijjibi wasu magunguna kuma
ta shanyasu, sai wajajen shadaya suka gama komi su Samira suka koma dakinsu itada Lujain
suka koma dakinsu tsumi tazuba cikin kofi tabama Lujain tasha sannan tahada mata wani
ruwan zafin wasu itace data dafa, Lujain dake zaune tana kallon cartoon a falo tanashan tsumin
kadan kadan tace “Gwaggo wai magungunan menene” batare da Gwaggo takalleta ba tana
saka farfesun daban daban datayi dasuka jera a robobi a dankareren freezer ta tace “shawara
tamiki yawa baki gankiba Saura kadan kizama zabiya tsabagen haskenki” yatsine fuska tayi
tana gyara daurin towel dake jikinta tun Gwaggo namata mitan tawul harta barta dan bata taba
ganin mutumin daya tsani kayaba irin Lujain.
Gwaggo bata kara mata maganan auren ba sai uban magungunan datake loda mata na safe
daban na rana daban na dare daban, ita dakeson yogurt saida Gwaggo tasa tasani yogurt
sabida yanda take zubamata garin magana a yogurt din daban daban.
****

Yau Friday tun ranan Monday bayan an daura auren nan dasuna shigowa gidan Abee yawuce
dakinshi dagudu rabon kowa dayaganshi ko masallaci baya fita, Ya kulle dakinshi baya karban
abinci yanda za’a kawo abinci a ijiye gaban dakin haka zaa dawo adauka, shigowa gidan Musty
yayi afalo ya zauna yana kallon yanda Hajiya dakowa yay jugum ahankali yace “har yanzu bai
fitoba Hajiya”? Wani kalan ijiyan zuciya Hajiya ta sauke tace “ai inhar ciwon nan yatashi
saikuma yanda tayu, har yanzu likitan nashi”? Ahankali Musty yace “gashinan zuwa Ibraheem
yadaukoshi daga airport” shiru dakin yasakeyi babu wanda keda walwala Kausar da Abdallah
yakalla sun bashi tausayi yauma basuje makaranta ba, jin karan gate yasa Musty yaleka yace
“Alhamdulillah gasunan” Dr na shigowa falon baima tsaya gaidasu ba yace “give me his room
key” ciro key Hajiya tayi daga Yar purse na hannunta yawuce sama kowa na zaune akasa,
kusan 30min yayi aciki sannan yasauko kowa tashi tsaye yayi yana jiran abinda zaice dan
murmushi Dr yayi yace “ku kwantar da hankalinku he is fine” ajiyan zuciya kowa yayi, Mustafa
dake kallonshi yace “Dr maisa yake kulle kanshi yaki fitowa duk yanda Imran yakaiga son
bautan Allah jam’i baya wuceshi zakaga hatta masallacin baya fita yaje, yaranshi dayakeso
baya yarda yagansu baya ganin kowa, why is it like that”? Ahankali Dr yace “kasan patient
nawa aka rasa to PTSD post traumatic stress disorder? I applaud Imran bakaramin jarumi bane
mai kwazoba he’s fighting it with all of his strength, PTSD nakama mutum ne Idan mutum yay
experiencing a shocking event, mutuwan matarshi, yanda akai hanging nata sun harbeta a

goshi, aka kashe yaranshi in cold blood shine abinda yasa PTSD yakamashi, symptoms nashi
shine magrine, da mutum ya tsani kanshi yayita bama kanshi laifi akan abinda yafaru, mutum
yay isolating kanshi daga mutane kaman yanda yake yanzu dasauransu irinsu rashin yawanyin
magana, gashinan gashinan ne, for 13yrs I’ve been managing him da little medication su Anti
depression dakuma psychotherapy, yana zuwa har office dina he talks to me I talk him out of all
the guilt the experience dakomi dayake feeling, for a long time now kusan shekara daya kenan
baitasomai ba sai ranan Monday din nan shima sabida wannan dan he’s traumatized sabida
kazafin da akamai aka kuma yada aduniya yanar gizo, saikuma this sudden Marraige, Auren
nan dan gani yake he’s betraying his late wife, yanzu dai I assure you komi yazo karahe, Hajiya
inason kije kiyi magana dashi but before then dukku zazzauna inason magana daku gabaki
daya” zama dukansu sukayi shima Doctor yazauna yace “all abinda patient na PTSD ke bukata
is love and support from close family nasu and friend, ku nunamai kuna sonshi he means a lot
to you, sannan kununamai ku bama kusan yana ciwo ba koyanada wani ciwoba duk randa
yabude kofan nan dakanshi yafito kuyi mu’amala dashi kaman bakumasan yashiga daki ya kulle
kanshi na kusan kwana biyarba baci basha kungane”? Dasauri kowa yace “eh” Dr yace “sannan
karkumai kuka, don’t show him pity rather show them love, idan yaga kuna nunamai pity
kunamai kuka zaiyi worsen condition nashine dan he will feel yana causing muku pain, karku
nunamai kowani abu instaed ma zai iya idan yafito kuce mai babu kaza kaza kaza agida, Abee
inada assignment kaza kaza kungane engage him in something life moves on” yakalli Hajiya
yace “idan kinje dakin nan ba danki mai lafiya ke magana ba, ba Imran dinki zakigani ba, this
one is Imran mara lafiya, PTSD mess with brain Hajiya, so no matter mezaiyi don’t show
weakness kokuma kiyi kuka agabanshi, as his mother handle him kaman jariri tell me
kinasonshi he’s your everything, sannan idan kin shiga dakin daidai da hasken screen na
wayanki kada kisake ki kunna bayason haske bayason hayaniya bayason kuka at this time cus
all of that nakara tunamai da traumatic experience na lokacin memory nadawo mishi fresh, idan
tadade adakin ku aikamata da abinci kar wanda yashiga dakin abakin kofa zaku ajiye kutafi,
babu abinci acikinshi sannan he’s dehydrated, ga weakness kungane” atare duk sukace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login