Showing 33001 words to 36000 words out of 46557 words

Chapter 12 - HAUWA KULU Yar Cikin Badala Part 2 BY TAKORI.pdf

ayi mata aiki a zuciya, domin ta samu rami (hole) a zuciyarta. Ai jin haka
Inna ta mike ta fice ta bar Hauwa da likita suna kiranta (again), Hauwa ta biyo bayan ta tana
kuka da roko, sai Inna ta dakata da tafiya tace da Hauwa.
“Idan kin manta haka aka ce min za’ayi miki aikin ido ki warke daga hakiya, amma kin warke
din?
To ni yanzu in aka yanka min zuciya kina da tabbacin zan mike?
Ba tsoron mutuwa na ke ba domin kuwa a shekaru hamsin me nake jira banda neman
hanyar dacewa da cikawa da Imani?
Ke nake ji Hauwa-Kulu, in babu ni, rayuwar ki zata shiga wani hali na garari da walagigi har
da da bara akan titi, don baki da mataimaki da mai yi miki jagora bata idanu kadai ba harma da
rayuwar ki gabadaya, sai Allah da ya halicce ki”.
Abinda Inna bata sani ba, ko babu ita Innar, ita HAUWA-KULU (modern makauniya ce), bata
bukatar dan jagora don zuwa wani waje, kanta tsaye take zuwa ko’ina, iyakaci kai in ka fahimci
bata gani kai ka kauce mata, wata irin brainlliant ce mai kaifin kwakwalwa da kaifin basira, gata
da ji mai karfi irin na wadanda suka rasa idanun su da kuruciyar su Allah ya bata. Don dai

UWA-UWA ce amfaninta yafi ga haka, wato ya wuce ta rayu don ta yi mata dan jagora, sai dai
don ta zama GARKUWAR ta a rayuwa bakidaya kuma cikon farin-cikinta ta.
Tun daga ranar bata kara yarda Hauwa ta ja ta asibiti ba, tayi ta kwanciya a gida suna cinye
dan jarin nasu a sayen abinci kullum, tunda ba juyawa ake ba yanzu kashewa ake yi yasa
kullum daurin kudin su sai kasa yake yi, kafin makwabcinta Malam Sani mai irin ra’ayin ta kan
traditional medicine ya ce da gaskiyar ta, tazo ya kaita gidan mai magani inda zata samu
magani na kowacce cuta ba tareda an tsaga kirjin ta ba.
​ Aka fito da Inna daga cikin gidan ranga-ranga da daurin kayan su a bakko, aka sa a
bayan motar Sarham, Tafada da Hauwa suka shiga, suka sa Innar a tsakiyar su, wadda bata
san ma ko su waye a kan ta ba lokacin. Rabin jikin ta na kwance jikin Hauwa. Malam Isa na
gidan gaba Sarham ya ja motar cikin nutsuwa da hanzari suka hau titin da zai maida su cikin
birnin Kano.
​ Suna tafe a hanya suka fahimci Inna ta farfado daga suman data yi, suka yi ta yi mata
sannu da jiki. Malam Isa nata yiwa Inna fada da dacin rai, na yadda ta shiga duniya ta bar
makwabtan ta masu kaunar ta, wai ace yanzu ta gwammace rayuwar sayar da abinci a tasha a
kan zaman gidan sa, yace to yanzu me kika tsinto a tashar duk sana’ar taki ban ga kinyi arziki
ba, ban ga kinyi kiba ba, na gan ki tsiya-tsiya rakace-rakace wutsiya a zage cikin ciwo.
Rayuwa bata raggo bace. Haka azzaluman mutane ba’a kyale su su cigaba da aikata zalinci
son ransu ga marassa karfi a doron kasa musamman mata da kananan yara kamar Kulu.
Da kin zauna mun tashi tsaye mun hada karfi da karfe mun kwato miki hakkin ki, yadda
makwabtanki suka fusata a lokacin da kin tsaya, in yafi karfin ki ai bai fi karfin shari’ah da Alkali
ba, cewa fa mukayi ki tsaya zuwa wayewar gari mu shigar da kararsa maimakon mu dau
Shari’ah a hannunmu. ​ Kuma ni da kin zauna kin yi gaiba, na rufa miki asiri na killace ki a gidana karkashin
inuwar aure in taya ki kula da ‘yar makauniyar ‘yar ki, amma ina! Ke ga ki kububuwa sarkin
masu zuciyar duniya, kika dauki ‘ya ba ido kika bar BADALA!”
​ Sarham ya rage gudun motar sa a dokar daji, a fusace yace “wallahi Malam Isa in baka
yi mata shiru ba zan cillar da kai a dajin nan in ja mota ta, da me kake so ta ji? Da ciwon jikin ta
ko da hayaniyar ka?”
​ Daga haka aka samu Malam Isa yayi shiru, bai kara magana ba har suka isa asibitin
Malam Aminu kano.
​ Tun kafin su iso dama Sarham yayi waya da Dr. Babangida, wani babban likitan zuciya
ne (cardiologist) abokin karatun sa a Jiddah da ya dawo yake aiki a nan AKTH, shi yasa aka
karbi Inna cikin kulawa daga shigar su asibitin, aka yi imajensi da ita. Kuma da taimakon
sanayyar sa da Dr. Babangida yasa ta samu attention din likitoci da yawa suka rufu akan ta, don
binciken hakikanin abinda ke damunta.
​ Sai da suka kwana suka wuni a A&E ana bata taimakon gaggawa kafin a basu daki a
kwantar da Inna, amma da Sarham ya zo asibitin a washegari sai yace a maidata dakin
‘Amenity’ ya kuma biya komai aka maida Hauwa da Inna kebantaccen daki wato ‘Amenity’ a
sashen mata. ​ A kwana uku sakamakon gwaje-gwajen da likitoci suka yi wa Inna ya fito, da gaske tana
da huda a zuciyar ta, wadda ke bukatar sai an yi mata aiki an cike ramin da zuciyar tayi.
Madinah na can gidan kakannin ta tana jego, Sarham na jelen asibiti dasu Inna daga nasu

gidan yake zuwa shi yasa bata san me yake ciki ba, sai dai duk sanda ta kira shi a waya zai ce
mata yana asibitin Aminu Kano yana da ‘patient’ yana ‘busy’, ta kuma san shi sosai da Dr.
Babangida shiyasa ta daga masa kafa, yau kwana uku bai zo Soron dinki ba balle ya ga Baby
Hauwa da take kira (Waheedah) tun ranar sunanta. ​ Kowa ya dauka saboda Haj. Kulu Sarham ya sakawa ‘yar sa suna Hauwa, shi kuwa zai
iya rantsuwa ya saka sunan ne don ya dinga tunawa da Inna da Hauwa a lokacin da ya neme
su ya rasa.
​ Hatta a gida sun gane yana zirga zirga, kuma ba a wajen masu jegon ba, ko jiya ya saka
Surayyah girki na hanta da koda da ‘vegetables’ da kunun gyada yace ta zuba masa madarar
ruwa a ciki, Surayyah ta dauka shi zai ci, bayan ta gama ta gaya masa ta gama, sai yace ta
shirya a basket ta kai masa mota, Mama ta bi Surayyah daki bayan fitar sa tana tambayarta ko
wa Sarham zai kaiwa abinci? Surayya tace bata sani ba, yace dai yana da mara lafiya a asibiti
ne.
Mama tayi wani dan tunani sai ta ce “in kika bibiya bazai wuce mutanen sa na Badala ya
gano ba. sune kadai zai dauka da muhimmanci irin haka ya kasa nutsuwa in suna cikin
matsala”.
Surayyah ta ce cikin mamaki “ba sun bar Kano ba? Ba sun bace masa ba tuntuni?” Mama
tayi dariya tace “ko a ina suke in dai a fadin Najeriya ne na tabbatar miki sai Sarham ya nemo
su, ki bar Sarham akan abinda yasa kan sa, ko yake kuma kauna da son taimakawa da zuciya
daya”. ​ Surayyah ta kwana abun yana bata mata rai, na yadda ta zage ta shirya masa abincin
nan da kyau, don ita bata son zancen su ma, yadda aka sakata girkin wahalar wasu kauyawa
wai su su Innar Hauwa, tarkacen BADALA, don haka washegari da ya saka ta girkin again tayi
maza ta ce kanta na ciwo bazata iya ba, dole sai Nancy sabuwar mai aikin Mama ya saka tayi
masa ‘potatoe porridge’ da yaji ganyen alayyahu. Da dafaffen kwai.
Ita Hauwan ma da ake kaiwa garar abincin mai dan gina jiki, don a samu ta murmure ta tada
komada daga muguwar ramar data yi da mokadewar da kashin wuyan ta yayi a Albasu, sam
bata iya ci, bakin ta ya kasa karbar dandanon abincin don bata saba da cin mai lafiya da dadin
dandano irin sa ba. Ruwan bunu (lipton) ko na Milo kawai take iya zubawa a cikin ta ya zauna da dadin rai, ta
zama kamar ka bushe ta ta fadi don kamar ma bata da lafiya, nan kuwa yunwa ce kawai ta
zaman Albasu ta zauna a jikinta tayi mata illah. Abu daya ke faranta mata in ta tuna Inna na
bisa karkashin kyakkyawar kulawar asibiti yanzu, kuma ana tabbatar mata da tana jin sauki
kasancewar idonta a rufe yake kuma kullum ana mata karin ruwa kafin ranar da za’a yi mata
aiki tazo.
​ Sarham ya biya komai ranar aikin, ya kuma saka hannu aka yiwa Inna aikin zuciya. Aka
yi lafiya cikin nasara ba kamar yadda Inna ke tsoro ba.
A lokacin ne ya samu ya koma cikin hayyacin sa tun daga ranar da ya dauko su Inna sai yau
ya samu nutsuwa, bayan an gama aikin an kai ta dakin hutu, inda Hauwa ta cigaba da jiran
farfadowar ta.
Sai ranar ya samu ya leka su Baby Hauwa. Madinah bata iya fushi da Sarham ba, ko me
yayi mata kuwa, komai girman laifin, amma yau a kwayar idonta ya gane tayi fushin,
musamman da yaga tana ‘avoiding eye contact’ da shi, ya san tayi fushi mai ban mamaki ko

bata furta ba.
​ Ya sa hannu ya dauki Hauwa cikin dan kyakkyawan gadon ta tana barci, ya zauna dab
da Madinah yace “Likita matar Likita barka da yau, ya kuka kwana? Ya kukan daren uwar
bil’adama?” Madina ta amsa fuska ba yabo ba fallasa, sai yace “ba sai an gaya min ba, na san
nayi laifi wa GIWAR SARHAM, kuma na karbe shi tun ba’a bani ba (laifin), tun kwanaki uku
baya ma fa ya kamata ace na koma Jeddah, amma inada uzurin da ya rike ni mai muhimmanci,
kiyi hakuri kin ji Madindin din Sarham! Madinatul-Munawwarah my shelter, my eternal
happiness, my home peace, my safety and my security, in sha Allahu nama fasa komawa, sai
kin gama wankan jegon ki sai mu koma tare, zan yi amfani da lokacin (as annual leave) dina”.
​ Amma har ga Allah ya fasa komawa ne saboda lafiyar Inna, yana kuma son daukan
‘measures’ din da ya dace akan rayuwar su Inna kafin ya koma Jeddah.
​ Madinah da bata iya dogon fushi da Sarham ba jimawa ta yarda da uzurin sa ta kuma
saki rai suka shiga hirar arziki da hirar soyayyar su da bata kodewa, suna yi suna kallon
kyakkyawar fuskar ‘yar su Hauwa (Waheedah) wadda suka saka a tsakiyar su tana barci da
sauke numfashi cikin koshin lafiya. A lokacin Madinah da Sarham suka hau musu akan wanda Hauwa tafi kama dashi, shi yace
da shi take kama completely, ita tace kalar su da gashin su ne kawai iri daya amma fuskar da
yatsun, duk nata ne.
​ Madinah a idon sa kadai ta fahimci ya jima bai ci abinci ba, amma da yake a dabi’ar shi
baya dorawa matar sa nauyin ta tashi tayi masa girki a duk sanda yake so, sai bai mata
complain ba, ita da kanta da yake ta san kan kayanta, ta gane sosai yake cikin gajiya da yunwa,
don tun haduwar sa dasu Inna bai samu nutsuwar cin kyakkyawan abinci ba sam, don haka ta
tashi ta hado masa abinci mai rai da motsi, sai da yaci ya koshi suka gaisa da Kakarta Haj.
Lailah, wadda ke falo, sannan yayi musu sallama ya wuce asibiti don ya tadda su Hauwa ya ga
farfadowar Inna, don haka daga nan Soron dinki can ya nufa.
​ Saida ya tsaya a hanya ya yi musu sayayya sosai kamar yadda ya saba duk da ya lura
Hauwa bata iya ci, yau sai ya saya mata fresh milk da yawa (unsweetened) kafin ya wuce
aibitin. Da sallama ya murda kofar ya shiga dakin, bayan Inna tayi masa iznin shigowa, amma
Hauwa a ciki ta amsa masa kamar yadda ta saba amsa sallamarsa tun fil azal, ya tadda su tare
da Malam Isa ya zo dubata shi da dan gidan Inna wato Saleleh.
​ Malam Isa har gidan su Salele ya je ya gaya musu an ga Innar Hauwa, shine fa Salele
ya biyo shi. Inna ta dubi Sarham tana daga zaune jikin filo. Ba don ba karamin sani tayi masa
ba da bata gane shi ba, don ya canza gabadaya daga yadda ta san shi, dan siririn saurayin
likitan nan na Murtala, ya girma ya kara cika ido cikin shekaru kalilan, ilmi da kwarjinin addini
sun kara bayyanar da cikar zatin sa. Tayi murmushi a hankali, ta ce.
“Inda rai da rabo, likita Sarhamu! Ashe Allah yayi zamu gana?”
Sarham ya ja kujera a gaban ta ya zauna, yana kallon Hauwa tana shafa hoda irin mai like
da mudubinnan a jikinta, saura kadan ya fashe da dariya, kasa amsawa Inna maganar data yi
yayi saboda dariya dake cinsa, ya nuna wa Inna ita da baki, itama tayi dariya, tace “kuma ayi
magana cibi ya zama kari ba!”. Malam Isa ya juyo garesu yace “dariyar me kuke haka?” Inna tace “kai dai abar kaza cikin
gashin ta, daga jiya zuwa yau na kirga shiga wankan ta ya kai goma! Wai biyan bashin wankan
kwana bakwai da bata yi ba a kauyen Albasu take yi yanzu, tunda ta samu ruwan dumi da

sabulu mai kamshi ai shikenan, har da yi wa Malam Sani Allah ya isa da yayi mata sanadin
komawa zaman kauye”. Sarham yayi dariyarsa mai isarsa, har da sunkuyawa da rike ciki, sai
lokacin Hauwa ta gane da ita suke.
Ta dan dakata da shafa hodar, duk ta sha jinin jikinta, ga mudubin a hannun ta, kai sai ka
rantse tana ganin fuskar ta cikin mudubin, jin sun kara ninka dariyar ta ji haushi, ta mike ta fita
daga dakin sai Sarham ya mike ya bi bayan ta don ya bata hakuri.
​ A jikin barandar dakunan ya same ta a tsaye fuskar ta ta hade kamar kunun kanwa.
Tana tsaye kawai harde da hannuwa a kirji. Ya lallaba ya tsaya dab da ita shima ya harde nasa
hannuwan a kirji irin yadda ta yi. Ya ce.
“Kuluwa, ni fa ba ke nake yiwa dariya ba, labarin da Inna ta ke bayarwa ne ya bani dariya”.
Hauwa tayi narai-narai da idanu kiris ya rage ta fashe da kuka, tace “idan makanta abin dariya
ce ai bata wuce kan kowa ba, idan gorin ido abun yi ne, ba komai ku cigaba da yi min”. Sarham
ya kama baki cikin jin wani iri a ransa yace “kina nan a Kulun ki, Kululu, Kulun Majadun sarka
mai rikicin gangan, har gobe baki canza ba, dama Inna ta ce ayi magana cibi ya zama kari.
Yanzu saboda Allah ba dama muyi dariya sai ki ce rashin idon ki ake wa gori?
Idanun nan fa mun fi ki son su dawo, ta yaya zamu yi murna da halin larurar da suke ciki?
Kawai dai kina ji da rikicinki ne na gangan.
Kullum addu’ar mu shine su dawo da gani kamar na kowa, idan masu dawowa ne, idan
kuma ba masu dawowa bane Allah ya sa rashin su ya zama silar kaffara a gare ki da iyayen ki,
ya baki aljannar Firdausi a madadinsu”.
​ Hauwa ta dan saki rai, sai Sarham yace, “Maijiddah, tunda muka hadu bamu gaisa ba,
bamu zanta ba, bamu yi fadan namu ba, koda yake yau mun dan taba. Anyway, nayi kewar ki
MAIJIDDAH, bayan a baya na zaci bazan taba yin kewar ki ba, tunda baki damu da ni ba”.
​ Hauwa ta yi murmushi ta ce a ranta,
“kwarai kuwa, don ni dai kam in ba na dauko littafin makaranta ba, sam-sam bana tuno ka,
gara-garama a lokutan da kalamanka masu haska min rayuwa ke sawa in tunaka”.
Unfortunately, bata san cewa a fili ta fada ba.
Sai ji tayi Sarham yace cikin rashin jin dadi da sosuwar rai, “I know, ba tun yau ba na sani ai,
Inna ce kawata, uwata, kuma ita ta damu dani. Ni din a wurinki ba kowa bane face…”.
Yayi shiru cikin tsananin damuwa da rashin sanin ta yaya zai yi ya kankare wannan tunanin
daga zuciyar Hauwa-Kulu? Wanda ba tun yanzu ba ya lura yayi mugun samun muhalli a cikin
ranta?
Hauwa tace “kaima da ita kadai ka damu (Innar), daga zuwan ka ai ko la’akari da halin dana
ke ciki baka yi ba ka fara tsokanata a kauyen Albasu, wai idona kamar ana soya kosai cikin mai,
baka san cewa kukan farin cikin ganin ka nake yi ba, baka san halin dana ke ciki ba a lokacin,
don ji nayi kamar Yayana Zulkifilu ya dawo, kamar farin-cikin rayuwa gabadaya ya dawomin,
duhun zuciya ya gushemin, haske ya dawo a cikinta”.
Da mamaki da jin dadi a muryarsa Sarham yace “to kiyi hakuri Maijidda, mu ajiye wannan a
gefe, I’m happy to be your sourse of happiness, koda wannan kadai yau kin karramani, yanzu
inaso ki bani labarin bayan rabo, da rayuwar ku gabadaya daga farkon tafiyata har ranar zuwan
ku Albasu gidan mai magani”. Hauwa ta nisa, kafin tace “dogon labari ne likita, amma mun sha wahala wajen neman na
kan mu a tashoshin mota, mun yi girki iri-iri ba hutu tamkar injin girke-girke a kowacce rana

daga safe har yamma hakarkarinmu bai hutawa, ba don komi ba sai domin kada mu yi bara.
Allah ya sani, ba abinda nake gudu da nakasata irin bara! Alhamdulillah for being alive, and

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login