Showing 9001 words to 12000 words out of 28936 words

Chapter 4 - Amani 3Hausa Novels by Takori Kabara .pdf

ga dai mutumin nan tare muka zo,
kuma don shi muka zo, ai ya kamata ya dinga zuwa ganin lafiyar mu, in bai
zo don ni da ya raina ba ya zo saboda ku da yake ganin girman ku” “ni kike cewa na raina miki hankali? Wato har yanzu bazaki gyara
halshen ki ga na gaba ba ko? To lafiyar ku ke da wa? A’a Uwa, ki cire mu

cikin lissafin ki da rashin kunyar ki, mu kam ai muna gaisawa da shi a waya,
bai banzatar da mu a kasar sa ba, ko dazun nan ya kira Jal’an, yace ko tana
son wani abu, ta ce cukui take so sabon yi, a kawo mata, kuma yasa an kawo
shi faranti guda mai laushi.” Haushi ya kara turnike Amani, ita din dai ita kadai Mukhtar ya raina,
kuma baya son ganin ta ko jin yadda take rayuwa a garin su mai shegen zafi,
ta tashi ta bar mata wajen cikin kunan rai. Baba Sahura na kara kyakyatawa
kyal-kyal-kyal don ta gano damuwa sosai a tare da ita. Tun daga ranar kuwa duk sanda Baba Sahura ta ga Amani ta yi tagumi
sai ta fashe da muguwar dariya.
Ummami kuwa, yanzu ta mayar da hankalin ta ne kacokam! Ga shirin
tariyar diyar ta Amani, shiri na musamman take yi wa Amani, shiri irin
wanda ake yi wa ‘ya’yan sarakai in zasu dakin miji, masu yi mata gyaran jiki
daga Maine-Saroa har su biyu ta kirawo ta ce daga yau har sati daya su gyara
amaryar Maina, gyara na musamman fiye da wanda suke yi matai ta
Ummamin, Sarki kuma ya saka ana ginin bangaren su a gefen nasa, wani irin
kasaitaccen gini shiyasa har zuwa lokacin basu tare ba.
Amani a daya daga dakunan sassan Ummami take zaune, an bata bayi
mata masu kula da komai nata har su biyar, amma in suka nemi yi mata wata
hidima ma korar su take yi saboda haushi, haushin kowa take ji, saboda
Mukhy bai neme ta ba ko sau daya, mai hali dai da baya fasa halin sa. Sahura da Mamma ma dakin su guda, Sarki ya hana su komawa
Katsina yace sai sun raka Amani ta tare a dakin ta tukunna.
Ginin Maina zai dauki sati biyu ana yi don gini ake ba na wasa ba
wanda duk masarautar Diffa babu ginin da ya zanu, ya kuma zamanantu
kamar sa.
Duk da rashin ta idon Amani sosai ta samu kan ta da jin kunyar
Ummami, bata sani ba ko sabida yadda take jan ta a jiki ne, ta ce kuma ita ‘ya
take da ita ba suruka ba, don haka ba karamin tanadi take yi wa tariyar ta
ba. Da nata, ‘ya tata, komai tuwon ta man ta, farin cikin hakan har ya so yayi
mata yawa. Shi yasa take yin komai da karsashi.
To amma yadda Mukhtar ya share Amani tun zuwan su, ko zancen ta
bai kara yi ba ya damu Mamma Jal’an a kasan ran ta, bata dai nuna ba, don
ta san yayi hakuri iya hakuri da Amani, yanzun lokacin sa ne, amma bata
fatan ya ce zai rama wulakancin Amani gare shi, don ko babu komi ‘yar uwar
sa ce, ta san idan ma Amani ta ce tana son sa yanzu, ai wata fassara zai yi
mata daban, don hankali ba zai kama ba.
Don haka ta shiga rokon Allah a boye a kan ya daidaita tsakanin su ba
tare da sauran mutuncin Amani ya zube daga idanun Mukhtar ba.

Ita kuwa Ummami yawan sabgogin dake kan ta na mijin ta da bayi da
tariyar Amani yasa bata fahimci cewa Maina ko gaisawa baya yi da Amani
ba. ba kuma ya zuwa inda ya san a can take.
Allah kadai ya san me ke zuciyar Mukhy a kan Amani, don har zuciyar
sa baya mararin sake ganin ta, duk da cewa ‘he’s absolutey busy’ kuma ‘busy’
din da yake ciki da jama’a da iyaye da ‘yan uwan sa ne ya hana shi zuwa inda
suke, amma yana kiran Mamma Jal’an a waya akai akai, har Baba Sahura
ma, kuma dai duk da hakan Amani tana nan a like a ran sa, yana tuna ta a
yawancin lokuta in ya kadaice domin kwanciya barci, amma bai damu ya gan
ta ko ya neme ta don ya gan ta ba, duk a kan kalaman ta na Saliyo, da har
zuwa lokacin ya kasa manta su, ya kasa yafe su, ya kasa share ‘effect’ din su
daga ran sa, kuma in ya tuna suna masa maqaqi a rai, amma ba don wai ya
dawo cikin gatan sa da take masa gori bane ko don halayen ta da ya riga ya
sani bane ya sa bai neme ta ba.
Aka fara yima amarya ‘Hamam Hallawa’ daga shi aka yi mata ‘Dilka
Gomage’ irin na matan Diffa, washegari aka yi mata wankan madara da
wankan lalle. Sai kunshi, wanda ya zama shine na karshe a gyaran amarci da
aka yi wa Amani a Diffa. Yau da yamma da aka gama kunshin, aka cire ya kama radau, kamar
ka sace kafar da hannun ka gudu, mai gyaran jiki ta ce ta je ta yi wanka da
ruwan turaren data sirka mata a toilet din Ummami, sun gama gyaran yau
kenan sai kuma na gobe in Allah ya kai mu. Mukhtar yana son ganin Ummami ya duba inda suka saba haduwa bai
gan ta ba, dole ya shig sassanta har addu’a yake Allah yasa kada ya hadu da
Hajjajun nasa.
Mukhy ya shigo dakin Ummami ne don ya gaya mata zasu tafi Burkina
Faso yau, domin kai Daddy wajen wani mai maganin shanyewar barin jiki na
gargajiya da Sarki ya ce a kai shi. Bisa umarnin abokin sa sarkin Burkina
Faso da ya tambaay ko akwai masu irin wannan maganin na wannan lalurar
ta shanyewar barin jiki a kasar shi bayan na asibiti? Shi kuma yace tabbas
akwai, kuma shi zai dauki nauyin maganin, da duk masu raka Alhaji har sai
ya samu lafiya. Don haka suka gama shirya tafiyar Alhaji Usman da ‘yan
rakiyar sa karkashin jagorancin dan sa kuma surukin sa Maina Mukhtar.
Da sallama ya shiga har kuryar dakin Ummami don bai gan ta a falon
data fi zama ba, sai hadimanta suna ta ayyuka a falon wajen tsaftace shi da
turare shi, bayan an gama kunshin amarya, ya duba duk inda zai gan ta har
turakar Mai bata can, kuma dole yana so yayi mata sallama saboda zasu kai
sati biyu a Burkina Faso in sun tafi gobe ana yi wa Daddy gashin kashi na
gargajiya, don har Mamma Jal’an zasu tafi, kuma ya gay mata ta waya cewa
ta shirya, don ta dinga kula da Alhajin sosai da daddare.

Bai ga Ummami a dakin ba, sai wani fitinannen kamshi da ya baibaye
dakin ta ko’ina, can kuma sai ya jiyo karar ruwa a shaya, daga toilet din
Ummamin, nan ya gayawa kan sa Ummami tana wanka ne, don haka ya samu
kujerar ‘sofa’ kwalli daya dake dakin barcin Ummami ya zauna yana jiran
fitowar ta, hankalin sa bakidaya a kan wayar sa da wannan kamshi da yake ji
yana fitowa ta toilet ne ko ta falo ne dun sun bi sun rikita gidan, da wani
turare mai tada hankalin ‘yan maza.
Zuwa can Mukhy yaji an bude kofar toilet din, sannan a hankali ta fito
daure da faffadan tawul, gashin ganta ya sha wanki don kitso za’a yarfa mata
gobe, dagowar nan da zai yi sai ga Hajiyar tasa ce tana fitowa daga wankan
turare data shiga, ta zama tamkar hurul-eenin larabawan Diffa. Mukhtar ya
samu kan sa da fara tazbihi a cikin ran sa da sauri da sauri. Gabadaya iskar
dakin ta debi kamshin sihirtaccen turaren da Ummami ta sa aka hada
musamman saboda Amani, yau kwana bakwai da shi take wanka, wanda
Ummami tun daga T’Chad ta aika aka kawo mata shi, daga ita sai dan
faffadan towel wanda ko guiwar ta bai kai ba, tayi wani irin sumul ta yi jazur
kai har wata ‘yar kyakkyawar kiba ya ga ta yi kamar ba Amanin da ya sani
kamar a bushe ta ta fadi ba don rashin kauri. Yo kam ta ci Dawisun Diffa ta
koshi.
Da farko ita bata gan shi a dakin ba sam, har rausaya take tana rera
wani baiti cikin wakar mutuniyar ta wato “Nancy Agram’, da harshen larabci,
a haka ta isa ga mudubi domin ta sharce jikakakken gashin kan ta data
wanke, nan ta hango Alhajin nata zaune yana kare mata kallo, ta cikin
mudubin ta hangoshi, sosai ta tsorata duk ta firgice, don bata san da shi a
dakin ba. Mukhy ya dan rikice da kama shi da tayi yana mata kallon kurillah,
duk ya zama wani ‘upset’ don bai taba ganin ‘real Amani’ irin yadda ya gan ta
yau ba, ita ma ta diririce don bata san tana da kunya ba sai yau, tana kokarin
komawa bandakin don suturta jikin ta ya daure fuska sosai ya ce “ke da Allah
malaam! Tsaya, tambayar ki zan yi, ina Ummami? Ba wajen ki na zo ba balle
ki yi min yanga” idon Mukhy na walainiyar da basu san suna yi ba a kan
kirjin ta wanda ya dago sosai kamar an an kara hura mata shi ya zama
kamar balloon, sai zagin idanun sa suke ta cikin kakkauran towel, da
zara-zaran hannayen ta da suka sha jan lalle da hallam hallawa, suka zamar
da fatar ta tamkar na jaririya don taushi, wadannan abubuwan guda biyu,
gabadaya sun gama tada nutsuwar Mainan Diffa, ya kasa dauke ido a kan ta
tsayin lokaci, Amani ta juya don komawa toilet ba tare da ta amsa masa ba.
Mukhtar bai san lokacin da ya mike ya soma taku zuwa gaban Amani ba, ya
sha gaban ta yana cewa “ba tambayar ki nake ba?”
Nan da nan ta fara rawar jiki don dadin ganin sa da ta ji, ga kuma
kunyar yadda ya gan ta, sannan a gaban ta ya tsaya yana fadin, “shin sai

yaushe zaki yi hankali ne ke? Ko gaisuwa ga miji har yau baki iya ba, gaida
miji ma sai an ce ki yi? Ni kam anya Alhaji ya san irin shashashar matar da
ya bani?”
Mukhy yana maganar nan cikin takaici mai yawa, muryar sa na
canzawa cikin ‘yar in’ina, ta dalilin tasowar wani kwantaccen ‘feelings’ daga
kasan ran sa, duk kuwa da cewa gashi korafi yake akan halin ta, ya yarda
yana son Amani har gobe, duk da pretending din nasa, amma baya son
halayen ta ko kadan, don haka yanzu ma kokawa yake da kan sa na kada ya
sake kai hannun sa gare ta, komai zai faru da shi gara ya faru amma ba zai
kara sake mata ba.
Mukhtar ya kara taku ya tsaya a gaban Amani hannayen sa biyu cikin
aljihun Caftan din jikin sa, ya ce “Hajjaju ina fatan zafin kasar mu ta
talakawa bai saka ki ciwo ba? Na san ‘ya’yan Qaruna basa son zafi da rana da
sauro”. A yanzun yana maganar ne fuskar shi dab, da nata, a fakaice yana
sunsunar wannan sihirtaccen kamshin ne dake neman bugar da shit un dazu,
wanda yanzu ya gane daga jikin ta ya samo asali, mai neman bugar da
numfashin sa, ya rasa inda suka same shi. In bai manta ba irin sa ne tayi
amfani da shi a Saliyo ya kusa mutuwa a kan ta ba don kwanan sa yana gaba
ba.
Ta rasa me zata ce da shi, don kamar bakar magana ce ya gaya mata,
shi kuwa tsakanin sa da Allah ya san garin akwai zafi, akwai Sauron ma at
times, tana rokon Allah a ran ta yasa kada yau ma Mukhy ya tada zancen
“Shege!” Har yayi abinda zai yi bar dakin nan. Zuwa wannan lokacin Mukhy ya kusan hade dan space din da ya saura
tsakanin su, ban da makyarkyata ba abunda Amani take yi daga tsaye. Yace
cikin tsananin takaici “wai ashe ke kanwa ta ce duk wanan lokacin ban sani
ba, na tsaya kika yi ta yi min rashin kunya a banza a wofi, kina kunsa min
bakin ciki kina cin bulus, kina tada kai da bulus, to daga yanzu kika kara yi
min rashin kunya ko hararar nan taki ta raini, na rantse da mai samada mai
kasa gwabje bakin ki zan yi sai jini ya fito” ta yi wani sunkuye da kai, sannan
ta yi kasa da idanun ta bata ce komai ba, jikin takanwa y agama yin la’asar.
Mukhtar ya kara matsowa jikin ta don kamar wani magnet ya ji yana
jan sa zuwa gare ta, abinda bai tsara bane yake neman zuwa da kankanuwar
murya ya ce “ba zaki koyi gaisuwa ba?” Ya kara nacin fade, wannan karon
cikin shakakkiyar murya, Amani sai ta soma kokarin gocewa kusancin su, ta
yi gaba zuwa wardrobe don ta saka kaya a jikin ta, tana cewa cikin ran ta,
“Allah yasa kai ne Sarkin kasar Nijar bakidaya, ba mai jiran gado ba,
ba zan gaishekan ba, tunda ta karfi ake saka gaisuwar, ayi mutum ba
maganar arziki tsakanin sa da wadda yake kira matar sa amma babu lallashi
a bakin sa kullum. An yi sati biyu ma ba’a hadu ba, yau an hadu tana mararin

ganin sa amma ba maganar arziki, ai kuwa bata isa ga wardrove din ba ta ji
Mukhtar ya riko gefen tawul din, sai ganin tawul din ta tayi a hannun sa ya
rataya a wuyan sa, ta bude baki domin yin ihu, yayi maza ya toshe bakin da
hannun sa yana zaro manyan idon sa, ya ce, “baki da hankali zaki yi min ihu ki tara min mutane? Meye haka sai
kace yanka ki nayi? Zaki jawo a zaci wani abun nake miki? Daga kawai na
zare tawul?”
Amani ta rufe dukkan idanunta kamkam, cikin matsananciyar kunya
da gigita, tana ambaton Allah a ran ta, domin Mukhtar ya damke bakin da
kyau da hannun daman sa yadda bazata iya ihun da ta yi niyyar yi ba don
Ummami ta kawo mata agaji. Shi kuma rufe idon da ta yi sai ya bashi damar
karewa kyakkyawar halittar matar ta shi kallo, yana tazbihi a ran sa har ya
fito fili.
Amani bata san yaya aka yi ba daga nan, don idanun ta suna rufe, gara
mata rufe idon da ta hada ido da shi cikin wannan situation din, ta san dai
Mukhy ya tallafe bayan ta ya hanata kai wa kasa daga nauyin jikin ta da da
kafafun ta suka gaza dauka, daga nan kuma sai saukar bakin shi ta ji a kasan
dogon wuyan ta yana sunsunar ta, kafin ya saki wani wahalallen kiss, a asan
wuyan nata ba tare da shi kan sa ya shirya ba, ya gangaro a hankali ya saka
fuskar shi saman kirjin ta, bai san lokacin da yayi hakan ba domin tun dazu
yake kokawa da kan sa a kan yin hakan, amma zuwa yanzu duk wata dauriya
da duk wani azanci da ya san ya mallaka ya kwace masa, jaruntaka da ‘ego’
da ‘pride’ din sun subuce masa, wannan yasa ya yarda hakan wani ‘miracle’ ne
da Amani ke da shi a kan sa.
Wato duk irin fushin da yake da ita baya jin zai kasa kusanta kan shi da
ita, in har sun kebe.
Mukhy ya tafi da yawa, Hajiyar kuwa da ke guilty na damun ta yanzu
bata yi wani hobbasa na hanawa ba, ya manta cewa a dakin Ummami suke sai
faman…… wannan smooth lallausar fatar da taji wankan madara dana lalle
yake yi, yana hadawa da sunsunar ta kamar ba zai daina ba, sai dai kamar
wancan karon, yanzun ma sai da kwakwalwar sa ta tuna masa AMANI
FASKARI ce fa! Sarkin rashin mutuncin duk duniya, har yanzu bata yi
hankalin da zai sake mata ba irin haka, balle yanzu da take matsayin kanwa a
gare, shi tana bukatar ya bar ta ta kara hankali har zuwa lokacin da zata
kara sanin ciwon kan ta afin ya soma irin wannan rayuwar da ita.
Mukhtar ya saki Amani ta hanyar komawa bisa ‘sofa’ din da ya tashi, ya
kama kan sa da dukkan hannayen sa yana jin haushin kan sa, ya nutsa yatsun
sa cikin tarin sumar kan sa ya runtse idon sa, ya tuna abinda ta gaya masa
ana ‘I gobe zasu taho nan, cewa tana regretting abunda ya shiga tsakanin su a
Saliyo, me yasa yake bari ajin sa ke barewa muddin ya kebanta da Amani?

Me yasa yake kasa controlling emotions din sa a kan ta, a irin wadannan
lokutan???
Amsar da baya son samu daga kasan zuciyar sa dole ita ta soma
‘pumping’ a cikin kan sa, wato “duk da halaye da dabi’un Amani Usman
Faskari marassa kyau da baya so, wadanda a yawancin lokuta suke saka
masa tsanar ta, ya fahimci duk da hakan still yana matukar son ta da kaunar
ta.
So kuma kwakkwara guda daya, mara algus, wanda ya san daga Allah
ne ba don Alhaji ba.
Shi kawai tun sanin sa da ita a gidan su yake da wani ‘extra feeling’ a
kan ta, ko ganin ta yayi daga nesa sai gaban sa ya fadi duk da kasancewar ta
maras tarbiyya maras mutunta mutane. Idan kuwa ta matso kusa da shi, to
kuwa sai ya ji hakan a dukkan jikin sa. Kunya ta sa Amani sanya doguwar rigar Ummami a baibai, wadda ta
yayibo daga wardrove din ta, tana jin wata irin kunyar Mukhy, wadda a baya
bata da ita a kan sa, tana zuwa tana baibaye ta. Da kyar Mukhtar ya samu ya
koma daidai, ya mike yana faman daure fuska kamar yadda ya saba, ya ce, “na tambaye ki kin min banza, nace wai ina Ummami na ta shiga ne?”

A kokarin ta na son ‘adopting’ kyawawan dabi’u daga yanzu, wadanda
ta fahimci ‘gaisuwa ga miji’ na cikin su a gidan sarautar Diffa, kamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login