Showing 39001 words to 40544 words out of 40544 words

Chapter 14 - Aisha Saddiqa Part 4 hausa by Sumayya Takori Kabara .pdf

ya akayi sai ji mukayi Prince yace “get the hell out of my room Takori and
your CREW!” (Ashe-ashe Prince ya hango mu ta bayan labulen da muka buya muna dauko
muku rahoto).
Sauran al’amuran da suka biyo baya masu nauyi da girma ne daya shallake tunanin
kowannensu yafi karfin bironmu nida crew dina. A wannan lokacin Abdulrasheed is more than
bewildered. Gabadaya ya dauki Aisha ya kaita wata duniyar daban da bata taba mafarkin zuwa
ba ko cikin mafarki. Ya mika hannu ya canza musu launin fitila daga mai haske zuwa mai duhu.
Daga nan dai daga ni har Crew dina, bamu kara hango me ya faru ba, har zuwa sanda Petel din
Umma ta amshi certificate din girma da sallama da kuruciya irinna kowacce ‘ya mace, daga
bayeraben mijinta Prince Abdulrasheed (Kehinde). Bamu kara jin duriyar Aisha da
Abdulrasheed ba. Mun barwa mai karatu ya kissima abinda zai kasance a wannan muhimmin
daren a garesu bakidayansa.

Just imagine a 43 year old bachelor yau ya angwance da ‘yar 18 years.
A lokacin da soyayyar juna ta kai ta kawo ta tumbatsa a zuciya da gangar jikin kowannensu!.
**** **** ****

WASHEGARI
Prince Abulraheed Idris Kehinde Akanni, da matarsa Aisha Siddiqah Yunus, sun wayi gari
cikin farin cikin ma’aurata da bazai misaltu ba. ya sakawa Aisha albarka tafi cikin kwando. A yau
ya wayi gari da farin cikin zama cikakken magidanci da farin cikin halin da ya samu Aisha na
cikar mutunci da tarbiyyah, ya kuma wayi gari da farin cikin dabbaqa sunnar Ma’aiki SAW. Ya
zama cikakken miji a gidansa abin so da alfahari a wuri matarsa.
Amma kwarai ya tausayawa Aisha, but he is happy, more than a word can say. Don haka duk
wata kalar shagwaba ta Aisha ya jure ta, da kansa ya taimaka mata da dukkan taimakon da zai
iya, Aisha ko jariri a wannan ranar nan ya ganta ya barta wajen shagwaba da narkewa miji.
Hamma Prince ya rasa irin taimakon da zai bata da farko, domin kwarai yayi aika-aika, wadda
shi da kansa saida ya tausayawa Aisha.
Luckily to him, sai ga Dr. Taiwo ta kira, Aisha na kwance bisa kirjin Prince tana zuba
shagwaba, domin babu inda baya ciwo a jikinta. Prince ya amsa wayar Taiwo alhalin yana shafa
bayan Aisha da gashin kanta da dayan hannunsa. Yace “Taiwo, Aisha is sick, ya zanyi? Gashi
bazata iya takawa muje asibiti ba” Taiwo na jin haka ta gane Kehinde dinta sai yau ya
angwance, tace “take her to bathroom yourself, ka tara ruwan dumi ka sakata a ciki, for some
minutes, ta bata pain reliever”. Ta gaya masa duk abinda ya dace yayi mata, a matsayinta na
kwararriyar gyneacologist. Da sunan maganin da zai aika a karbo mata a pharmacy.
Prince duk yayi yadda Taiwo tace, har Aisha ta fara samuwa. Da kansa ya hada musu light
breakfast don ya hana Zaid zuwa yau. Haka yayi ta lallabata tana dada narkewa har ya samu ta
ware kafin dare.
Soyayya gangariya ‘yar usuli kuma mai tsafta ta cigaba da gudana a gidan Prince
Abdulrasheed Kehinde har zuwa zagayowar satin da suka daga zuwa kasar Singapore. A ka’ida
Prince aiki ne ya kawoshi Singapore, na tsayin wasu satittika, amma sai ya maida damar ta
koma masa ta hutun amarci zallah. Prince baya taba gajiya baya gundura da Aisharsa. Itama
kuma kullum son bayeraben mijinta Prince da tsananin kaunarshi karuwa suke, kasancewar
kullum sabunta girman son nasa da tasirinsa yake a ranta, da samfur-samfur din soyayyarsa ta
bayeraben miji mai tsananin son matarsa.
Basu dawo Qatar ba saida Siddiqah ta fahimci samuwar yaron ciki a tareda ita, aka dawo
Qatar da guzurin tattaba kunnen Sarkin Ilorin.
Dawowarsu Qatar keda wuya, Tosin Abdulnaseer ya kawowa Prince ziyarar ban girma, da
gaisuwar rokon iri har Qatar. Shikuma nan da nan ya hadashi da Baban Kiki a waya, a lokacin
ne Tofeeq yaji kunya sosai kan abinda yayima Taiwo, yayi tattaki zuwa Lagos ya roki iyayensu
Prince a kan a maida masa Maman Kiki, ya tuba. Dade yace da wa ya rike ta? ita tayi fushi ta zauna a gida. Amma kuma ya fito filiya bashi
laifin yin aure a boye da yayi. Yace Taiwo ai musulma ce na me zai boye mata? babu mai hana
shi aure inda yace zai yi ai su duka musulmai ne masu bin sunnar Annabi SAW.
Amma wannan iskanci ne kuma wulakanci ga uwargida, no matter what she deserves to
know and consent idan mijinta zai kara aure. Tofeeq yace shi wallahi tsoron bala’in Taiwo yake.

Dade yayi masa fada sosai yace ai sun wuce wannan stage din shi da ita. Ya kuma nuna musu
su duka sun girma, irin haka ba nasu bane, alhalin suna shirin kai Kiki dakin aure. Tofeeq yayi
nadama sosai yayi ta baiwa Taiwo hakuri. Aka lallaba Taiwo da kyar ta yarda ta koma gidanta
na Lagos. A satin da Aunty Taiwo ta koma gidanta aka saka auren Kiki da footballer Tosin Abdulnaseer
sati biyu masu zuwa.
Bayan bikin Kiki ne Aisha ta fara karatun jami’a a Qatar inda take karantar Pastry Art.
A lokacin kuma cikinta ya bayyana sosai kamar ya zarta watanninsa, cikin da Kakanni da
iyaye keta lelensa kamar ba’a taba haihuwa a zuri’ar Sarki Abdurasheed Akanni ba. sai akan
cikin Prince da Aisha.
Dangi sun yaba kwarai da rawar da Aisha da Prince suka taka a auren Kiki. Prince yayima
Kiki abinda ko Toafeeq bai yi mata ba a lokacin aurenta. Haka Aisha ta taka rawar gani wadda
ko Taiwo saidai tace ita ta haifeta.
Duk da Aunty Taiwo tayi nadamar abinda tayiwa Aisha, ta kuma koma zaman lafiya da ita,
lokuta da damaa tana dan dana halayenta na fada da shiga sharo ba shanu. Sabida shi halin
mutum hausawa suka ce zanen dutse ne. baya goguwa gabadaya. Aunty Taiwo is forever
Kehinde’s twin (Taiwo). Amma bata yarda koda kuskure ta dana halin nata akan Aisha wai
hausawa suka ce wargima wuri shika samu. Wata fuskar tafi gaban mari.
Ban taba ganin ‘yar gatan mace a gun miji da iyayensa irin AISHA INDO SIDDIQAH ba!.
**** **** ****

Haihuwarta ta farko ‘yan biyu ne maza wadanda nan take aka mayar da sunan Sarkin Ilorin
da Sarkin Gombe mai rasuwa. Addu’a suke nan gaba Allah ya basu wasu saitin twins din mata
a samu mai sunan Nenne da Umma Haj. Zainab.

Rayuwar Hamma Abdulrasheed (The Prince of the Ilorin Emirate) kacokam dinta,
bakidayanta, is an inspiration ga maza irinsa, sannan darasi ce babba ga mazan da suka samu
kansu a yanayi na jinkirin aure, mudubi ce mai nuni da cewa, rashin aure da wuri, matsayin
sarauta, mulki, da wadatar arziki ba tikitin zaman namiji “Dan Akuya” bane. Cikar kamalar namiji
kuma shine ya zamanto cewa ya iya ‘controlling desires’ din shi.

SADAUKARWA NE GA MAZAN DA SUKA SAMU KANSU CIKIN KADDARAR JINKIRIN YIN
AURE BA TAREDA SON RAN SU BA!!!
SADAUKARWA NE GA DUK BAHAUSHIYA/BAFULLATANAR DATA CIREWA RANTA
KABILANCI AKAN KABILAR “YORUBAWA” DA SAURAN KABILUN NAJERIYA TA DALILIN
KARANTA LABARIN |AISHA SIDDIQAH YUNUS|
-SUMAYYAH ABDULQADIR
MAY, 2024

07030137870
LITTAFINNAN NA SAYARWA NE IN KIN TSINTA KIN KARANTA KI JI TSORON ALLAH KI
BIYA (1000) TA WANNAN ACCOUNT DIN (2089357770 SUMAYYAH K. ZENITH BANK)

INA TALLATA MUKU AISHA LAME (ORIGINAL ORIFLAME AMBASSADOR)
Kina neman jakadiyar oriflame ta kwarai? Kinason mayuka da zasu dace da launin fatarki a
wannan lokacin na zafi kona sanyi? Kinason kamshi na alfarma? Kinason supplements
ingantattu na wellness and meal replacement ga masu bukatar weight loss and weight control?
Kayan kwalliya na kerewa sa’a? Kina bukatar zama Dawisu sarkin ado? Kawai tuntubi AISHA
LAME a lambar waya 07036662633 zaki samu duka wadannan cikin farashi mai inganci da
kyakkyawar mu’amala. Aisha lame karshe ce wajen baiwa faat hakkinta ku tuntubi Aisha ku zo
ku bani labari.
-Takorinku

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login