Showing 42001 words to 45000 words out of 69924 words
Chapter 15 - KURMAN BAKI HAUSA NOVELS WRITING BY HUGUMA.pdf
Tayi ado duk da baby kwalliya ko kadan saman
fuskarta amma adon dake jikinta zaka tsammaci bawai asibiti zataje ba
"Zunubi kam aikowanne bawa yana tattare dashi,saidai ka zama me neman yafiya wajen Allah"
ruqayya ta maida mata tana takawa a hankali tana barin wajen don ji takeyi kamar amai zai taso
mata
"Idan baka zalunci bayinsa bafa" zainab din ta fada cikin son maida raddi
"Ya isa haka,likita ya shigo?"
"Eh ai bazai zauna jiran zuwanku ba,yace qarfe sha biyu zai sallameni idan likitan rana yazo" ta
fada tana hade fuska.
"Sannu" ruqayya tace d jimmy sanda ta isa daura da ita zata zauna a kujerar da take a wajen.
"Yauwa sannu" jimmy ta amsa da fara'a sassanyan qamshin dake tashi jikin ruqayya na
burgeta(qamshi fa yana jawo maka farinjini a wajen mutane tabbas,ku zama masu qamshi don
Allah yan uwa mata). Haka kawai taji ruqayya ta burgeta,tuni kuma ta fahimci itace kishiyar
da zainab ke qorafi akai
"Kayyasa,wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa ai" ta fada can qasan ranta. Tazarace mabayyaniya
me dimbin yawa tsakaninta da ruqayya. Ko a yanzun taga dabbanci da hauka a wajenta. Sun
iso ruqayya na tattalinsa duk da tare suka kwana,ke anzo dubaki ba wani feleqe ba komai,jiya
baki wanka ba me makon yau kafin su iso ko fece jikinki ko yaji dadin kallonki amma kin zauna
kamar tsumammiyar jaka,sun iso da kayan abincin ba gaisuwa ba ya ka kwana ba sannu ba
godiya kin buge da qorafi ke 'yar sakin zuciya,kamar ke kikafi kowa zuciya,BA KISSA BA
SIYASAR ZAMA DA MIJI BA TSAFTA BA MAGANA ME DADI amma tsohuwar ballagazar dinki
take buqata ayi mata, tabdijan!,Allah yasa ranar farko ya balle matsiyaci!. Jimmy ta raya a ranta
dariya na balle mata har sai data toshe fuskarta da pillow.
Tunda ruqayyan ta fidda wayarta take danne danne abinta,ko sashen da suke bata
sake kalla ba bare taga abinda ranta zai baci. Yanayin basarwarta da kawaicinta ya sake burge
jimmy qwarai,ta tabbatar da wata ballagazar ce itama da tuni tana gabansu ta kafa ta
tsare,zainab zata yita yin abu da gayya ita kuma nata ran yana baci.
A hankali ta dafe qirjinta saboda taso mata da amai yayi. Jimmy daketa aikin jarida
tsakaninsu ta kula da haka,saita aje wayar hannunta
"Lafiya?" Dan murmushi ta sakar mata
"Lafiya ba komai,na gode"
"Kaman yunqurin amai naga kinayi,ga leda don kada yazo bagatatan ya bata jikinki" jimmy ta
fada tana cire wata leda da aka siyo mata gasashen nama a ciki ta bata.
Qamshin Naman da ya daki hancinta ya sanya tasowar amai din gaba daya,tasoma
kwarashi cikin ledar. Qarar aman ya jawo hanakalin saleem da Zainab,saleem din ya miqe da
wani irin gaggawa ya isota yana tallafeta. Zainab na zaune ko motsawa batayi ba,wani abu ne
kadai ke yawo mata cikin kai
"Ruqayya da amai?,tabbas amai na daya daga cikin manya manyan sign na samun
cikinta,cikine da ita?,ciki fa!!" Ta fada cikin zuciyarta wani tashin hankali yana zarto mata tun
daga tsakiyar kanta har zuwa yanzun qafafunta.
https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr
*_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫
*HUGUMA*
PAGE 20
_Wai Allah♀️♀️,da qyar na qwaci kaina nayi wannan,ayimin afuwa don Allah,zainabu na
gaisuwa ga jama'arta_
Gaba daya sai ta koma kamar mutum mutumi,ta dinga binsu da idanu harta gama
aman,jimmy da tafi kusa da ita ta bata ruwa ta kuskure bakinta,saleem ya karba ledar ya qulle
ya yar.
"Danqari!!,ana dara......." Zainab ta fada cikin zuciyarta wadda keyi mata suya
"Inaga kamar akwai likita ko?,muje ya dubaki karmu wuce gida abun yafi haka" saleem ya fada
cikin kulawa ganin yadda jikinta ya saki.
"Allah ya sawwaqe" jimmy ta fada tana komawa gadonta
"Ameen na gode" ruqayyan ta amsa mata tana fita a dakin. Batasan ya suka qare ba,ya kusa
mintuna uku sannan ya fito suka wuce karban file.
"Kinga irin zallar rashin adalcin da ake gwadamin ko?" Zainab da idanunta suka cika da hawaye
tace da jimmy
"Ummmm,na gani" ta amsa mata tana bata haushi saboda yadda ta karanceta,sam bata iya
mu'amala da miji ba,maganganun data gaggasawa saleem kafin ya fita ta tabbatar inda wani
namijin ne me saurin daukan mataki daga nan saidai tayi gidansu,kai koda a dadiro ko dandi ne
tabbas ba abinda zahana ya lakada mata na jaki har dai an qwaceta. Amma maganganun da ya
dasa mata a rai da me hankali ce ita ya kamata taji zafinsu ne ta kuma dauki haske.
"Banda aikin asiri.....kazo dubaninamma idanunka ya rufe ba tani kake ba?,don kawai tayi
amai?"
"Ai aman kawai ne?,bashi kikeyi ba ke sanda aka kawoki asibitin nan?"
"Eh amma ni harda gudawa"
"Baiwar Allah ai ciwo ciwo ne ko?,sannan nifa a nan banga aikin asiri ba,kawai dai ta fiki sanin
kanta ne da alama" kamar cakewar mashi haka maganganun jimmy suka tsaye mata a rai,ta
zuba mata fusatattun idanunta tana kallonta. Banda tana tsoron kada ta yiwa kanta sanadin
dinkin da za'a yi mata wallahi da sai ta gaggasa mata maganganu
"Ban gane nufinki ba"
"Maganata a bayyane take ai,baki iya kula da mijin ba,baki da lafazi baki da mu'amala,sannan ki
kalli jikinki da nata daya ne?" Jimmy ta fada kai tsaye tana kallon cikin idanunta. Dif sukayi su
duka, abinda ya kawo katsewar maganar tasu shigowar hajiyayye, jimmy ta dauke kai taci gaba
da harkokinta.
Bayan duka tambayoyi sai aka bata gwajin PT don alamu sun nuna hakan. Gwajin
kuwa ya fito da sakamakon da ake zargi na juna biyu. A take akayi mata scanning don duba
baby. Scanning din ko ya bada sakamako me ban mamaki.
"Cikinki ai yayi wata biyu harda rabi ma,kuma dukkan wasu alamu sun nuna twince ne,matso ku
gani" likitan ya fada yana zooming scanning din.
Wani mugun sanyi jikin saleem din yayi,ya dinga jin tsoron Allah yana ratsashi,anya
ruqayyan ba wani matsayi gareta wajen Allah ba da yakeson nuna masa ishara?. Duk wani
gwaji anyi ance ruqayyan sam bata taba haihuwa,amma cikin hikimar buwayi gagara misali sai
gashi yanata nuna ayoyinsa.
Ita kanta a karan kanta sai ta dinga jin girman Allah da girman al'amarinsa yana sake
shigarta,ta dinga tasbihi a gareshi tana jin zuciyarta tana tsinkewa
"Ki yafemin don girman Allah,saboda bansan me ubangiji yake nufi da hakan ba" saleem ya
fada yana tsugunnawa a gabanta harda hade hannayensa biyu
"Na yafe maka fa,na yafe maka tuni,komai da ka gani muqaddarine daga Allah" ta amsa masa
tana jin nauyin duqa matan da yayi.
Kafin su dawo hajiyayye tayi parking kayansu gaba daya saboda anyi sallama,wanda
inda ta biyewa zainab motar haya zasu tara su wuce gida ba tare da sun jirashi ba.
Tanata kumbura tana wani babbankewa ta wuce gaban mota. Itakam ruqayya ma
dariya ta bata,yanzun ita kuma me ya rage mata?,Allah ya mata komai na rayuwa da mace
keda burin samun bakin gwargwado,saidai ci gaba da neman qari. A gidan duniya rashin zuriya
ne damuwarta,sai gashi Allah ya wanke mata hakan y bata ya bata ya sake bata wasu.
Koda suka wuce gida bangarenta ta wuce kai tsaye abinta saboda sam batajin qwarin
jikinta,gaba daya tunda tayi aman kamar laulayin aka zuba mata,zainab kuwa suka wuce da
hajiyayye nata sashen,wadda ta matsa ta biyota din,tunda daima tasan nan da dan kwanaki
saleem din zai wuce umra shi da hajiya. Tace dai iya yau zata zauna din,idan ya tafin ta dawo.
Tunda ta zube a kujerar falon nata take saqawa take kwancewa,gaba daya komai yana
neman qwace mata,wannan cikin na jikin ruqayya ya zame mata qadangaren bakin tulu,ya
akayi har ruqayya ta rigata samun cikin ita tana zauna?,bayan ta shigo ne don ta haihu?,don ta
cika gida da 'ya'ya ta yadda gida zai zama nata sai yadda tace?.
Duk yadda hajiyayye takai ga aiki sai data sare,da farko ta dauka lalurarta yasa sashen
nata yake kaca kaca haka,saita zage ta fara gyarawa. Saidai sai data fara gyaran ta fahimci
lallai shayi ruwa ne,don kuwa tsohuwa kuma tsumammiyar dauda ce danqare a sashen.
Iya dakinta da kitchen ta gyara ta dawo ta zauna tana maida numfashi,ta dubi Zainab
dake a jabe
"Gaskiya magana ta Allah muddin ba zaki gyara wannan annamimiyar qazantartaki ba to kin
shiga uku wallahi,aiki tun kana na marmari har ya koma maka na jaraba?,yanzu don manzan
Allah uban panties da kika tara a bandakinki cikin bathtub na meye?, harda me jini a jiki fa?"
"Don Allah kada ki qaramin tension akan wanda nake ciki,haba mana,ki barni naji da abinda
yake damuna"
"Kiji da abinda yake damunki nima zanji da nawa,don wallahi gida zan wuce,kuma ko ya tafi
indai kinsan baki kwashe kayan qazantarki kafin nazo ba kada ki kirani"
"Haba dan hajiyayye zo mana" zainab din ta fada tana sasaautowa,don tasan ba wanda
tafiyarsu zatazo daya da ita sai hajiyayyen
"Kiyi haquri raina ne a bace don Allah"
"Sakeni" ta fada tana zare hannunta ta koma kitchen din tana qunqunin mita
"Dadina dake shegiyar mita wallahi" zainab din ta sake fada tana jan tsaki hadi da hararar inda
hajiyayye ta wuce,saita gyara zamanta tana ci gaba da qulla wadda take ganin zata fishsheta.
Tunda ta zauna wajen ta gaza motsawa,gaba daya komai ji take ya dagule mata. Ba
irin tunanin da bata saqa ba akan cikin ruqayya,har addu'a take cikin ranta
"Ya Allah kasa zuwa gobe da safe ta hadu da mummunan tsautsayin da zai kawo sanadin
zubewar cikin". Duk zaman da tayi a wajen ta rasa wanne zata kama?. Dagewa zatayi tayi
ciki?,ko ta bawa banza ajiyar saleem din ta dage tayi ciki?,idan ta haihu sai a dinketa gaba
daya?.
Tafi gasgata wannan shawarar kuma tafi yarda da ita,don haka dab da magariba ta
miqe daga wajen data jabe ba azahar ba la'asar,duk da yadda hajiyayye keta fama da ita ta
miqe din,ta wuce bedroom dinta ta wawwatsa ruwa don sauri takeyi kafin ayi kiran sallah ya
zamana ta fito kafin salim din ya shigo gurinta.
A gurguje ta biya bashin sallarta,sannan ta bude locker dinta tayi hadin
magunguna,tana ji a ranta zata sake dagewa da gyara,don ta shirya samun ciki a wannan dan
tsukin,idan so samu ne ma kafin yakai ga wucewa umra.
Wata rigar shadda ta saka,wadda wuyan da fadin yadanyi mata yawa saboda sanda
akayi dinkin tana da ciki tayi qiba sosai,yanzun kuwa ta zazzage ta koma ainihin jikinta. Ko
kadan bata fiya damuwa da sauyawar fadin rigar ba saima jinta sakayau da takeyi saboda
wankan da take jin tayi,sannan kuma aka dace shaddar wankakkiya ce,duk da babu shaidar
guga a jikinta ko na gamin gafara.
Parlor ta fito ta samu hajiyayye tare da yaran tanata fama dasu wajen gyara musu
yanayin cin abincinsu,yau sashen fes yake hakanan abincin yau da hankalinsa,saita hakimce
saman kujera tana dakon shigowarsa,a hankali tana jin maganin yana mata aiki,cikin qasan
ranta take fatan inama ace a wannan daren ta samu rabo itama?, tabbas a yanzu 'yan biyu
sune burinta,kai idan da hali ma guda uku zata roqa,so take ruqayya ta tabbatar da cewa da
gaske fa gida ya zama nata,qila hakanne kadai hanya guda daya da zata saka ta saduda.
*Kuyi manage,mu hadu gobe in sha Allah,na gode da haqurin jirana*
*_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫
*HUGUMA*
PAGE 21
Kusan tunda ya ajjiyesu ya fita yake fama da ciwon kai. A haka dai a daddafe ya zauna a
kasuwar saboda lissafin shago sukeyi na qarshen sati,dole kuma akwai buqatar ya zauna din
gudun rubuta kuskure.
Sanda ya qaraso yaran suka baibayeshi suna masa sannu da zuwa. Bai taba shigowa
gida bannu haka ba komai,duk qanqantar abu sai ya kawo musu tsaraban kasuwa(wannan
halayya ce me kyau,tana qara danqon soyayya tsakanin iyaye da 'ya'yansu,iyayenmu na da
zaiyi wahala kaga sun shigo gidansu haka,koda ma'aikata bare 'yan kasuwa).
Kai tsaye ya kama hannun iftee suka wuce sashen ruqayya yana tambayarsu mamar
tasu
"Daddy tana kwance tun da safe,mommy kamar bata da lafiya" iftee ta fada cikin karyar da
muryar
"Batajin dadi amma zata warke very soon in sha Allah" ya fada yana murmushi.
Sanda suka shigo ta gama alwalar sallar magariba dake gabatowa tana sanya hijabinta
"Sarkin tsafta"ya fadi a ransa,duk da batajin dadi amma sashen fes yake kamar kullum.
Fuskarta dauke da murmushin nan take dubansa
"Sannu da zuwa" ta fada
"Yauwa,ke za'a yiwa sannu maman wasu twince din in sha Allah" yaran tadan kalla ta gefan ido
tana bude baki kadan
"Daddy,bakaso na huta"
"Hutun me?,me ya rage banda ki cikamin gida da yara,inaso na ganni da yara masu yawa Allah
ma ya sani,sai gashi Allah ya qaddara zaki zama uwar 'ya'yana"
"Uhmmm,yau kuma ni za'a baiwa wannan matsayin kenan" tayi maganar tana zura hannun
hijabinta. Dan kallonta yayi sai ya basar,yasan gori takeson yi masa
"Baki da mantuwa" ya fadi qasa qasa sanda yake zama hannun kujerar dake daura da ita,saita
daga kanta,har zatace wani abu kuma sai ta fasa
"Baka da lafiya" ta fada a hankali. Idonsa ya lumshe yana jin qaunarta har qasan ransa,ita daya
ke da qarfin maganadisun iya karantar kowanne motsi nasa
"Kaina" ya fada a taqaice
"Subhanallah,daddy bakason shan magani,tsaya kasha magani don Allah" ta fada cikin nuna
maqurar damuwa
"Ki barshi idan na huta zan koma normal " kai ta girgiza cikin narkewa
"Kada muyi haka da kai daddy,yanzun idan wanine yace hakan sai kayita fada,mu shikenan ba
zamu kula da lafiyarka ba?,waye muke dashi mu da yaranmu sama da kai?" Idanunsa da ya
zuba mata ya lumshe gami da sakin murmushi
"Shikenan ranki ya dade" yadda ya kalletan taji kallon har cikin jikinta,idanunsa mada matuqar
tasiri har yanzu ga zuciyarta.
Ba jimawa ta dawo da maganin ta balla ta miqa masa hade da gorar ruwa,baikai ga
sha ba saiga haneefa Ibrahim yana biye da ita suna raba ido. Koda basuce komai ba tasan
turosu akayi suyi CID,don haka tana gama bashi maganin ta juya daki dasu,shi kuma ya
waiwaya yana dubansu. Kallon shi kadai yasa suka gane laifinsu,suka koma da baya suna
sallama,ya amsa yana miqewa,ruqayya ta qaraso da abun sallah
"Na gode" yace yana yin waje
"Wajibina ne" ta amsa masa tana shimfida abub sallar.
Yana sallama da ita ya fara cin karo,sai cika takeyi tana batsewa hadi da kumbura. Yi
yayi kaman bai ganta ba,yayi sallama yana saka kai falon. Hajiyayye ce ta amsa ta miqe tana
masa sannu da zuwa,ya amsa yana zama cikin kujera,har zuwa sanda hajiyayye tabar musu
gurin.
"Sannu da zuwa" ta fada ciki ciki kamar wadda aka yiwa dolen faden
"Yauwa,ya jikin?"
"Ka damu ka sani ne?,tunda tunda ka tafi baka ko kirani ba,ka dawo kuma kaje ka zauna a
wajen wadda ba girkinta bane" ta fadi cikin hasala. Idanu ya zuba mata kafin ya janyesu
"Wannan qorafin idan da sabo ya kamata bakinki ya gaji da fadinsu,kullum ke kenan cikin qorafi
akan na shiga ganinsu?,bayan ita ko sau daya bata taba qorafi akan shigowata wajenki ba?"
"Eh dama mana ai bazatayi ba tunda tasan tana cutata" ta fada tana gyara zamanta da alama
da gaske ta shirya tayita zabgo qorafin. Ganin hakan sai ya miqe tsam kawai abinsa yana
wucewa bedroom dinsa,cikin ransa yana mamakin yadda yau sashen yake fes. Amma yana
shiga dakinsa ya tabbatar ba itace tayi gyaran gidan ba,don bedroom dinsa yadda ya tafi ya
barshi ranar data fita a girki haka ya dawo ya sameshi. Da hannu ya tattara tarkacen ya zauna
gefan gadon yana jira maganin ya ratsashi. Tsahon wasu mintuna zuwa sanda yaji an fara kiran
sallah ya miqe ya wuce toilet ya daura alwala sannan ya fito don wucewa masallaci.
A inda ya barta a nan ya sameta ita da hajiyayye,dama ita din tun da batasan wai tabi
miji daki ko ta kebe dashi idan ya dawo daga aiki ko wani guri ba,saidai ya qaraci gararambarsa