[02/02, 15:02] Ameerah Adam🌚: *GIDAN LIKITOCI* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA BAƘAR DAULA AN YA BAIWA CE? ƊAN BA ƘARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA SHAFI NA ƊAYA Jar mota ƙirar golf ce take tafiya a hankali, saboda tsufa da lodin magunguna tare ɗima-ɗiman manyan sifikun da suka yi mata nauyi. Ta baya boot ɗin motar a buɗe yake waɗansu matasan samari ne a zaune, hannuwansu riƙe da jarkokin magunguna suna ɗagawa. Tayoyi da gefen motar duk sun yi butu-butu, saboda ƙura da jar ƙasa. Mai maganin gargajiyar yana daga cikin motar, ya sake ƙara volum ɗin recording ɗin tallan magungun da yake yi. "Alhaji ko Hajiya idan har matsalarku sanyi ne ku zo ga babansa. Ni fa ba na rantsuwa a kan magungunana saboda sadidan ne, amma idan har kuka sha maganina bai yi muku aiki ba ku dawo na ba ku kuɗinku. Ina mai fama da sanyin ƙashi, sanyin mara da ciwon baya ku zo ga waraka ta zo muku har gida. Alhaji kai ne ake ganinka kullum cikin babbar riga, ana yi maka kallon cikakken namiji amma a baɗini kana jin kunya to ka zo mu saka labule don Allah." Mai maganin ya rage volum ɗin recording ɗin, sai ya zuro kansa ta window ganin ya ƙaraso wurin da jama'a suke zirga-zirga ya ce. "Al'ummar Annabi ina magidancin da yake son huce takaicin sanyin nan da muke ciki? Amma ɗan kanoma ya yi masa mugun kamu. Don Allah kada ya ji kunya, ya zo ya samu mai warakar sanyi matsalarsa ta kau da ikon Allah. Cutar rana, kumburin ciki, zafin bayan gida, basir da cutar sanyi duk ni ne likitan da ke magance su." Baba Inu da ke kishingiɗe a kan benci ya tashi zaune, ya ɗan ƙanƙance ido yana ƙarewa motar da mai motar kallo, saboda masu magungunan ba baƙinsa ba ne, don yana iya tantance duka masu magungunan gargajiyar da suke shigowa garinsu. Musamman yadda suke haba-haba da shi, duba da yadda ya zame musu babban costomer. "Kai mai magani, zo nan." Baba Inu ya kira shi yana yafito shi da hannu. Da sauri mai maganin ya gyara paking ɗin motar yana kaikaitata a daidai ƙofar gidan. "Babana da Innata ga ɗan baiwar masu magani ya sauka, mai warkar da matsalar sanyi ya zo kada a yi wasa." Mai maganin ya sake furtawa a loudspeakersa. Ƙuri Baba Inu ya yi masa ya ce. "Abokina amma dai kai baƙo ne a garin nan ko?" Mai maganin ya gyaɗa kai ya ce, "Yanzu ma wucewa na zo yi, duk mai matsalar sanyi ya zo muna bayar da taimako don Allah. Idan ya sake na tafi ba zan sake dawowa ba sai baɗi." "Miƙo mini wancan maganin na jarka, nawa ne kuɗinsa?" Baba Inu ya tambaya, yana nuna wata zungureriyar jarka da ke cike da jiƙaƙƙun itatuwa a ciki. Jarka biyu mai maganin ya miƙa masa yana faɗin. "Wannan da kake gani darr kenan, Mai gida ba kowa nake sayarwa ba sai mai sa'a. Ko kana shan kunya a wurin iyalinka, don Allah ka ɗaga roba ka sha rabi ka shiga wurin uwargida ka dawo ka ba ni bayani." Baba Inu bai jira cewarsa ba ya ɓalle murfin robar, ya ɗaga ta sama sai da ya ga maganin ya ƙare sannan ya wurgar da jarkar. Mai maganin ya zaro ido waje ya ce, "Master amma ka kwana a wannan layin ko?" Horn ɗin da Baba Ibrahim ya yi ne ya katse Baba Inu da yake shirin bayar da amsa. "Abokina ja motarka gefe ga masu iko da gidan sun ƙaraso." Mai maganin ya ja motarsa gaba, a daidai lokacin Baba Ibrahim ya ƙarasa da ta shi motar ya yi parking sannan ya fito daga ciki. Tun lokacin da mai maganin ya ƙarasa gaban Baba Inu ya shawo kwanar layinsu, a kan idonsa Baba Inu ya ɗaga ya shanye. Da sallama ya ƙarasa wurinsa haɗe da faɗin. "Yaya barka da hutawa." Baba Inu ya ɗan kalle shi a sheƙe ya ce. "Bokan turai yau kuma lafiya na ga ka dawo da wuri?" Baba Ibrahim ya ce, "Lafiya ƙalau Yaya." Ganin Baba Ibrahim ya tsaya ba tare da ya yi magana ba ya sa Baba Inu ya ce, "Iro ya aka yi? Ka saka ni a gaba ko kai ma a miƙo maka maganin ne?" Da sauri Baba Ibrahim ya ce, "Allah ya kiyashe ni, ni kam." Baba Inu ya dube shi a gwasale ya ce, "Yo dama ina abin yake maye ya ci jariri, mai mace ɗaya har ya bugi ƙirji ya saka kansa a sahun mazaje. Ai maza kam suna inda suke." Baba Ibrahim ya girgiza kai ya ce. "Yanzu Yaya hanyar da ka ɗauko wa kanka mai ɓillewa ce? Saboda Allah a ce kai kullum cikin shaye-shaye da jiƙe-jiƙen magunguna kake kala-kala. Kullum masu magani sai dai su dinga layi a ƙofar gidan nan, mutanen garin har sun fara gane ka? Magungunan fa yawanci waɗanda kake sha babu wata ƙa'ida kai tsaye kake hankaɗa wa cikinka, kuma mafi yawa masu haɗa magungunan nan da ka suke yi ba su da ilimin abin. Ko mu da muke likitocin asibiti, babu yadda za a yi mu ɗauki magani mu ba ka ba tare da mun duba ka ba." Baba Ibrahim ya sauke ajiyar zuciya cikin takaici ya cigaba da cewa. "Yaya da ace kuɗaɗen nan da kake kashewa a sayen magungunan tara su kake, da ko nauyin karatun yara ka rage da su. Amma ka bar yara haka, hatta makarantar allo ba duka ne suke zuwa ba. Kuma saboda Allah ga shi nan, kullum wasu ƙananan ƙwayayan ake sake ƙyanƙyashe maka." Baba Inu ya ɗago fuska a haɗe ya ce, "Ka gama ubana? Idan ba ka gama ba na yi shiru ka cigaba." Baba Ibrahim ya furzar da iska mai zafi ya ce. "Na gama." "To shige ciki ka ba ni wuri, ashe shi ya sa ka kwaso fuska kamar akwatin zaɓe ka zo ka tsaya mini a ka. Wallahi Iro ka fara ba ni tsoro, da ace kana da iko na tabbata da sai ka yi duk yadda za ka yi domin ka turmushe mini ƙwaiƙwayen haihuwa. Amma ka don kanka, na lura baƙinciki da hassadar ne fal ranka. Allah bai hore maka irin ƙwaiƙwayen haihuwa masu yawa da albarka kamar ni ba." Bab Ibrahim a fusace ya ce, "Wallahi gaskiya ka faɗa, yadda kake sakin jiki kai da matan da kake aura kana saki da ina da iko sai na farke ka na ƙone maka su kowa ya huta. Tun da haihuwar kawai ka sani ba ka san jidalinsu ba." A ɗan tsorace Baba Inu ya dafe ƙirji, yana bin Baba Ibrahim da wani irin kallo ya ce. "Kai dai Iro an yi mai mugun hali, mugun bakinka ya faɗa kanka. Sai ja je ka yi ta fama da 'ya'ya huɗu, ni kam haihuwa yanzu na fara tun da ban san mai jin ƙaina ba." Ganin Baba Inu bai ɗauki zugar Baba Ibrahim ba ya sa Mai maganin ya zuro kai ya ce. "Ai mai gida shi ya sa a kullum idan za mu fito, muke addu'ar neman tsari miyagu irinsu masu hana a yiwa bayin Allah ciniki." Takaici ya sa Baba Ibrahim ya shige cikin gida ba tare da ya tanka musu ba. Saboda halin yayan nasa ba ƙaramin ɓata masa rai yake ba. Baba Iro yana shirin yin magana daga soron gidan ya ji, gijif! Kwacakwar! Alamar ana jan kaya a buhu. Baba Saleh ne ya fito da ƙaton buhun magungunansa, ganin motar mai magani a ƙofar gidan ya sa ya murtuke fuska yana harare-harare cikin habaici ya fara waƙa. Komai baƙin cikin tsololon ƙato. Wallahi sai dai ya yi ƙototo. Na zama kainuwa a wannan loto. Ƙaryar mai baƙinciki ya ga bayana, har masu ƙin sayan maganina. Yana gama faɗar haka ya fizgo ƙaton buhunsa da yake ja da ƙyar, sai ga shi bisa tsautsayi ya fiszo da ƙafar bencin da Baba Inu yake kai. Bencin ya yi gaba shi kuma Baba Inu ya hantsila ta baya ji kake darr ya yi zaman 'yan bori a ƙasa. Kamar bai san da shi a wurin ba Baba Saleh ya saki buhun hannunsa yana rafka salati sannan ya ce. "Wai Yaya dama kana nan ƙofar gida? Ikon Allah sannu!" Ya ƙarasa maganar yana ƙoƙarin riƙo hannun Baba Inu, da sauri ya bige hannunsa rai a ɓace ya ce. "Wallahi duk baƙincikin mutum bai isa ya ga bayana ni Inusa don uban mutum! Haka zan daɗe na yi ƙarko shekaru irin na dabino, sai na ga bayan maƙiyana. Kai mai magani, ungo dubu biyar ka yi mini haɗin komai da ruwanka." Baba Inu bai yi niyyar sayen maganin dubu biyar ba, amma don ya ɓa ta wa Baba Saleh rai ya yi haka. Baba Saleh ya buga tsaki yana wurgawa mai maganin harara, ya nufi wata tsohuwar motarsa da yake tallan magungunansa, ya buɗe ya tura buhun maganin da ke cike da jarkokin magani sannan ya rufe. Inna ce ta fito daga gida a fusace hannunta riƙe da Laraba, ta dubi Baba Inu bayan sun yi sallama da mai maganin ta ce. "Inu na gaji da cin kashin da ake yi mini a cikin garin nan." Da mamaki Baba Inu ya dube ta ya ce, "Me aka yi miki Inno?" "Ba ni aka yi ba Laraba aka yi wa, kuma duk wanda ya yi wa Laraba ni ya yi wa. Mai gari ne yake son ganina da ita, wai Laraba ta tare Ɗahe ɗan gidan Sa'a mai ragadada ta cinye masa. Saboda Allah ina Laraba za ta kai ragadada cikin ɗan bokiti ban da son zuciya?" Jin haka ya sa Laraba ta juya gefe a fakaice ta sake suɗe hannunta da ya yi shanana da miyar ragadada. Baba Inu ya zuba mata ido ya ce, "Wallahi duk abin da aka ce mini wannan hatsabibiyar yarinyar ta yi ba zan musa ba, shi ya sa tun da satin nan ya kama nake jiran shigowar Uwar marayi garin nan. Wallahi babu abin da zai hana Laraba zuwa birni, ta je can ta yi aikatau ko na huta da takaicinta. Ni duk cikin 'ya'yana babu sai siffar 'ya'yan aljanu irinta." Wani irin haushin Baba Inu ya kama Inno, sai kawai ta ja hannunta suka wuce wurin mai gari. Tun daga nesa da aka hango Inno tafe da Laraba ƙananan maganganu suka fara tashi a fadar mai gari. Sanƙira ne ya yi magana sannan kowa ya yi shiru. Da sallama Inno ta zauna a kan tabarmar fuska a haɗe ta ce. "Allah Ya taimake ka, na ji wai kana nemanmu ni da Laraba!" Mai gari da tun da Laraba ta zauna yake bin ta da mugun kallo ya ce, "Wai ne ma Inno?" Ya mayar da kallonsa wurin Laraba ya ce. "Ke Laraba waye wannan?" Laraba ta yi kicin-kicin da fuska tana duban Ɗahe kamar ba ta gane shi ba ta ce, "Ban san shi ba, amma na ga yana yi mini kama da 'ya'yan Baraka mai hancin salansa." Haushi ya sake cika Mai gari ganin irin rainin hankalin da Laraba ta yi masa. Ya sake nuna Huwaila wacce ta kai ƙarar Laraba, a kan ta jefa mata bokiti da guga a cikin rijiya. Laraba ta sake ƙanƙance ido ta ce. "Wannan kam Lado ƙeya ne!" Sai kuma Laraba ta washe baki ta ce, "Lado ƙeya dama ka dawo daga Legas?" Haushi ne ya lulluɓe mai gari, mutanen wurin wasu suka fara dariya yayin da wasu kuma haushin Laraba ya cika su, don kusan duka mutanen garin babu wanda ba shi da tabon ɓacin ranta. Tsam mai gari ya taso ya zo gaban Laraba, a tunaninta tambayarta zai yi sai ji ta yi ya zabga mata gigitaccan mari, har sai da ta ga waɗansu taurari sun gilma mata. A razane Laraba ta dafe kunci saboda marin ba ƙaramin zafi ya yi mata, amma sai ta basar don ba ta san ta kunyata kanta a gaban mutanen garin. Ta sake basarwa ta sake ba shi irin amsar da ta ba shi da farko. A wannan karon ma haushi ya sa Mai gari ya sake ɗauke fuskarta da mari, abinka da farar fata lokaci ɗaya fuskarta ta yi jajir. Ganin haka ya sa ran Inno ya ɓaci ta dube shi a fusace ta ce. "Wallahi Sama'ila ka kiyaye ni, jikata fa ba jaka ba ce..." "Ai dama duk wani iskanci da yarinyar nan take yi ke ce kike ɗaure mata, wallahi mai gari sisina ba zai yi ciwon kai ba sai an biya ni ragadadata. Har kayan miya da mahaɗi kusan dubu biyar na kashe." Sa'a mai ragadada ta faɗa a ƙufule. Cikin tsoratarwa da burgagi Mai magari ya miƙe tsaye yana buɗa kafaɗu ya ce, "Inno tun da haka kika ce, bari na aika ku birni wurin hukuma ta yanke mata hukunci. Kin ga idan aiƙali ya ji irin tuhume-tuhumen da ake yi mata ƙila ma ya aikata gidan yari." Jin haka ya kaɗa hantar cikin Inno, hankali a tashe ta zungoro Laraba ta ce. "Ke Laraba ki yi magana." Laraba ta yi wa Mai gari ƙuri tana yi masa kallon ba ka daki banza ba, har sai da cikinsa ya kaɗa amma sai ya basar ya ce. "Laraba kin tare Ɗahe kin cinye masa ragadada kin tula masa ƙasa a ciki, ita kuma Huwaila kin jefa mata guga da bokita a rijiya yanzu da kin jefa ta ciki me za ki ce?" Laraba ta wurga wa Huwaila harara ta ce, "Kai Lado ƙeya tun da ka dawo garin nan yaushe muka haɗu da kai!" Huwaila ta fashe da kuka cike da takaici ta ce, "Mai gari kana ji tana mayar da ni Lado, yanzu Laraba ta rasa da wa za ta haɗa ni sai Lado ƙeya?" Mai gari ya kalli Sanƙira yace ya tsinko masa itacen dalbejiya ya zuge masa ganyenta. Jikin Sanƙira har rawa yake ya haye bishiyar da ke gefensu, ya fisgo manyan reshe ya zuge ya miƙa wa mai gari. Kafiya da taurin kan Laraba ya sa ko gezau ba ta yi ba, duk da gabanta sai faɗuwa yake yi. Rai a ɓace Mai gari ya shiga rafta mata ta ko ina, mutanen wurin suka marmatsa don kar a same su. Tun Laraba tana daurewa har dauriyarta ta ƙare ta fashe da kuka tana mutsu-mutsu. Inno ban da kuka da kururwar neman taimako babu abin da take yi. Yaran da suke zagaye da su ne suka fara tafi suna tsalle da waƙa, saboda tun da suke ba su taɓa ganin abin da ya saka Laraba kuka ba. Laraba mai kuka ye ye. Ga majina da yawu ahayye. Gobe ma ta ƙara ye ye. Ku zo mu yi mata ɓarɓaɗan tusa a tsakar ka. Idan suka kai baitin waƙar sai su ƙarasa su dunguro kan Laraba da ke shasshekar kuka. Mai gari sai da ya gaji don kansa sannan ya koma kujerarsa cike da son nuna birgewa ya ce. "Duk wanda ya sake aikata makamancin abin da Laraba ta yi, hukuncin da za mu yi masa kenan. Ina Inno take?" Cike da jin haushi a daƙile Inno ta ce, "Ga ni." "Za ki biya Huwaila da Sa'a kuɗin ɓarnar da Laraba ta yi musu." Inno ta yi tsagal ta ce. "Ai kuwa ba za ta saɓu ba, ya za a yi a daki yarinya sannan kuma na biya." Mai gari zai yi magana suka ga Laraba ta miƙe zumbur! Kamar wacce aka yi wa allurar doki. Don irin zaburar da ta yi ba ƙaramin tsoro ta ba shi ba, ba shi kaɗai ba, hatta ragowar mutanen wurin sai da suka ja da baya. Idanunta sun yi jawur saboda kuka, ta dube su ɗaya bayan ɗaya abinka da mai manyan idanu sai suka sake fito. Ta fara takawa a hankali wurin saitin fuskokinsu, ta cigaba da kallonsu ɗaya bayan ɗaya kamar wacce take haddace kamanni da sunayensu. Da ta je kan mai gari sai ta matsa dab da shi ta gwalalo masa ido waje har sai da ta ja baya, sannan ta cigaba da kallon mutanen gefensa Tana zuwa ƙarshe, sai kawai suka ga ta ɗiba a guje ta fice daga cikin fili ta nausa daji, hankali a tashe Inno ta rufa mata baya tana faɗin. "Laraba! Ke Laraba ina za ki je?" Tun ba a je ko ina ba Laraba ta yi wa Inno nisa, ganin Inno za ta tafi ya sa Mai gari ya ce. "Inno wai ni za ku yi wa dirama? Ke da Laraba wa ya ba ku ikon tashi daga wurin nan. Wallahi ba don ina duba darajar marigayi Baffa babba ba, da ke da jikarki tuni na kore ku daga garin nan." Mai gari yana rufe baki, suka hango Laraba ta tunkaro wurinsu a guje, hannuwanta ɗauke da wasu tafka-tafkan reshen bishiya. Ba ta yi wata-wata ba ta shiga tafka musu kan mai uwa da wabi a haukace tana wani irin ƙaraji. Lokaci ɗaya wurin ya hautsine, Mai gari saboda tashin hankali da rarrafe ya dinga tafiya, domin da farko da ya saka gudu sai da ya yi adungure sau uku babbar rigarsa tana taɗe shi. 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam🌚 [02/02, 15:02] Ameerah Adam🌚: *GIDAN LIKITOCI* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA BAƘAR DAULA AN YA BAIWA CE? ƊAN BA ƘARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA SHAFI NA BIYU Kamar wata fusatacciyar zakanya, haka Laraba ta cigaba da yin kan mutane tana fatka musu itacen da yake hannunta. Ban da wani irin gurnani babu abin da take yi, Inno da ke raɓe a can gefe jikinta ya shiga karkarwa saboda tsoro da tashin hankali. Don tun da take da Laraba ba ta taɓa ganin ta yi irin haka ba, Sanƙira ta hango maƙale a gefen bishiya. Ta yi wani irin zullo haɗe da ƙaraji ta tunkari wurinsa, kamar sabon marayan da ba shi da mafita. Haka Sanƙiran ya saki wani marayan kuka zai fita da gudu, Laraba ta tuna yadda Sanƙira ya dinga zuge ganyen bishiyar yana wurga mata harara sai kawai ya ɗaga hannu ta tafka masa itace a baya. Sanƙira ya gantsare cikin azaba ya ce, "Wayyo Mai gari bayana wash! Wallahi wannan ba dukan bil'adama ba ne." Mai gari da babbar riga ta sarkafe shi yana rarrafe yana dungurawa ya ce, "Wallahi na ajiya sarautar na damƙa maka yanzu kai ne mai garin." Laraba ta saki murmushin ƙeta ta riƙo babbar rigar Sanƙira ta baya, suna gudu tana tafka masa ice a baya. Ganin Larabar tana neman kai shi ƙasa, ya sa Sanƙira ya yi wani ƙaraji ya dara gaban rigarsa gida biyu, da yake dama rigar ta kwana biyu nan take ta rabe biyu. Sanƙira ya zuba a guje ya bar Laraba da babbar riga a hannu, filin wurin ya sake cakamewa da ƙurar ƙasar da take tashi. Mai gari ya hango Laraba tana tunkaro shi, cikin tashin hankali ya zuba kabbara kamar wanda yake filin jihadi. A wannan karon Allah Ya ba shi sa'a ya samu da ya miƙe bai sake faɗuwa ba, gudun kada babbar za ta sake ba shi matsala ya sa ya tuɓe ta ya wurgar. Ya taƙarƙare ya fita da gudu, takalmansa da hularsa sai tsalle suke yi suna tashi sama. Laraba ta so ƙyale shi amma da ta tuna irin marin da ya zazzabga mata sai ita ma ta rufa masa baya da gudu. A lokacin da Mai gari ya ƙarasa gida, Salame matarsa ta rako Inna mahaifiyarta da ta zo duba ta sakamakon rashin lafiyar da ta yi. Suna nan a soro ya shiga a guje, cikin neman maɓoya ya fisgi hijabin jikin Inna ya yi gaba da ita. Cikin tashin hankali Inna ta fara ihu tana kiciniyar ƙwace kanta, don Mai gari janta yake da gudu ga kanta ya cukwikwiye mata a cikin hijabi. Ragowar mutanen gidan suna jin ihu daga waje, da suka ga a yadda mai gidansu ya shiga yara da manya sai kowa ya nemi maɓoya. Laraba ce ta yi tsaye tana wani gurnani, ta ga tsakar gidan kowa ya fashe sai wani ɗan ƙaramin yaro da bai fi shekara biyu da rabi zaune a kan fo. Irin kallon da Laraba take yi masa tana gwalo ido, ga zungureren itacen da ya gani ya sa yaron ya miƙe a zabure yana ihu ya shige ɗakin mahaifiyarta. Tun da Mai gari ya fisgi hijabin Inna, ba shi ya tsaya a ko ina ba sai a uwar ɗakin Salame a can ƙarƙashim gadon ƙarfenta. Ya shiga sauke numfashi da ƙyar yana muzurai, hannunsa ya kai wurin wandonsa ya ji ya yi sharkaf. Jiki yana karkarwa ya zura kansa cikin hijabin Inna ya ce. "Salame ina jin fa gudawa na yi, wallahi har yanzu ji nake abu yana tsiyaya a jikina kamar an kunna fanfo." Inna da kunya, haushi da baƙincikin Mai gari suka cika ta murya a dakushe ta ce. "Ai kana da hannu ko?Sai ka yi ƙoƙari ka kashe fanfon." A razane Mai gari ya ɗago, sai a lokacin idanunsa suka sauka a kan fuskar sirikarsa. Ya fito daga ƙarƙashin gadon a guje, yana zuro kai ya ga Laraba ta ƙwalla wata irin ƙara ta yanke jiki ta faɗi. Daga Mai gari har ragowar mutanen garin da suke leƙowa tsaye suka yi suna kallonta, aka rasa wanda zai tunkare ta ballantana ya yi yunƙurin tashinta. Laraba ta ɗan jima a haka sai kuma ta fara buɗe idonta a hankali tana salati, tashi ta yi zaune tana kalle-kalle kamar mai neman wani abu ta ce, "Kai, waye ya kawo ni nan?" Shiru gabaɗaya suka yi mata, ta tunkari wurin mai gari a ɗan razane ta ce. "Mai gari me nake yi a nan?" Baki yana rawa Mai gari ya ce, "Ni ma tambayar da nake son yi miki kenan, amma yanzu ki fara zuwa gida tukunna." Laraba ta saki murmushi a fakaici ganin yadda duk ya birkice, sannan ta fito ta nufi hanyar gida. Kamar sun ga sabuwar hallita haka mutane suka dinga bin Laraba da kallo, ita kuwa ta maze tana tafe tana hura hanci tana buɗa kafaɗa har ta je gida. Baba Inu yana shiga gida kai tsaye ɓangarensa ya nufa, tun daga bakin ƙofa ya tsaya ya yi gyaran murya yana haɗe fuska, lokaci ɗaya yaran suka fara shiga taitayinsu. Iyayensu kuma suka shiga tsawatarwa 'yan ƙananun da ba su yi wayo ba. Larai ce da girki ranar, a tsakiyar gida ta ajiye tukunyar abincin rana sai ƙanana da manyan kwanuka birjik a gabanta. Waɗansu ƙananan yara ne kusan su huɗu waɗanda ba su wuce shekara ɗaya zuwa da rabi ba, biyunsu riƙe suke da kwanuka suna kukan yunwa suna kama zanin Larai. "Gaskiya Indo ba kwa kyauta mini, da wanne zan ji? Da aikin abinci ko da waɗannan yaran. Ke Kulu zo ki janye mini su don ubanki!" Ta ƙarasa maganar a fusace ta fisge kwanukan hannun yaran. Baba Inu ne ya ƙarewa tukunyar kallo, ya matsa gabanta a kausashe ya ce. "Ke Larai satar mini abinci kika yi? Kika ƙara a kan wanda na ɗebar muku, da na ga kin rafka wannan rafkekiyar tukunyar?" Jiki yana rawa Larai ta buɗe tukunyar ta ce. "Mai gida tukunyar girkin ce ta ɓule shi ya sa na ɗora wannan." Leƙa tukunyar ya yi ya hango abinci a can ƙasan tukunyar sannan ya sauke ajiyar zuciya ya wuce ɗakinsa. Mukulli ya saka ya buɗe, ya ɗauko wata 'yar madaidaiciyar tukunya ya miƙa mata yana daga tsaye ya ce. "Maza ɗumama mini miyar nan." Da sauri Larai ta karɓa ta ɗora a kan murhun, Baba Inu ya koma kan benci ya kasa ya tsare yana ganin yadda take rabon abinci. Kowanne kwano idan ta ɗauko bai fi ta yafita ludayi ɗaya da rabi ba, saboda idan da sabo sun saba a kullum abincin ba isarsu yake yi ba. "Mai gida a zuba maka kana marmarinsa?" Larai ta tambaya tana gyara goyon Fure da ke bayanta. "A'a ku ci kawai!" Baba Inu ya furta a daƙile. Larai ta ɗebi ragowar wanda ta rage masa cikin murna ta shiga ƙara wa kwanonta. "Ke Larai wallahi son zuciyarki yawa gare shi, ba za ta saɓu ba wallahi sai kin ƙara wa kowa." Hansatu ta yi caraf ta yi maganar ganin abin da Larai take yi. Babu yadda ta iya ganin Baba Inu yana wurin ya sa ta shiga ƙarawa kowanne kwano bai fi cokali ɗaiɗai ba. Bayan ta gama ta ce kowa ya ɗauka, a guje yara da 'yan matasan cikinsu suka ɗauka da sauri, wasu tun a tsaye suka fara zuba loma duk da abincin yana ƙona su. Ƙamshin ɗumamen miyar ne ya fara dukan hancinsu, Larai ta sauke har za ta kai masa ɗaki Baba Inu ya ce ta kawo gaban bencinsa ta ajiye. Abu da ke da tsohon ciki wani irin ƙwaɗayi ya taso mata. Kwanon abincinta ta ɗauka ya ƙarasa wurinsa cikin marairaicewa ta ce. "Don Allah mai gida ko man miyar ne, ka taimaka ka yafa mini na ci ko na samu sauƙin abin da nake ji. Wallahi ƙwaɗayi ne ya addabe ni." Wani banzan kallo Baba Inu ya yi mata ya ce. "Cewa aka yi idan ba ci ba za ki mutu?" Abu ta yi saurin girgiza masa kai, Baba Inu ya sake haɗe fuska ya ce. "To yanzu baƙincikin wanda zan ci kike yi? Idan kuma ba na cin mai maiƙon, ta ya ya zan iya samun ƙwarin jikin nemo muku abincin da kuke ci." Abu ta haɗiyi yawu tana kallon farantin da Baba Inu ya zuba miyar da ƙirjin kaza, sai da ya rufe tukunyar ya miƙa wa Larai ta mayar masa ɗaki sannan ya ce, "Wallahi ba don cikin jikinki ba, da idan ba ki matsa daga kaina ba sai na sheme ki. Dubi yadda kike ɗebo mini fuska kamar an matse lemon tsami." Abu babu yadda ta iya, haka ta ja jiki a sanyaye ta koma ƙofar ɗakinta ta zauna. Ƙaton biredi ya ɗauko ya gutsira sannan ya mayar ya saka kwaɗo ya rufe ɗakin nasa. Kan bencin ya koma ya fara yagar biredin yana dangwalar miyar da ita, daga yaran da suke wurin har iyayensu ban da haɗiyar yawu babu abin da suke yi. Wani ɗan ƙaramin kwanon sha ya buɗe kusan cike yake da nono, ya zura hannu a aljihu ya zaro wani ƙullin maganin ƙarin kuzari da ya saya a daren ranar. Ragowar ƙullin ya kunce ya zuba ya jujjuya ya ajiye shi a gefe, ya ci gaba da yagar kazar yana dangwalar biredi da miya. Baba Saleh sai da ya gama loda duka magungunansa a cikin mota sannan ya koma gida, domin ya yi wa Ɗan Bishir sallamar tafiya yawon tallar magani. Yana shiga sashensa, ya samu ɗan bishir yana tsanyara ihu kamar wanda ake ƙwaƙwalewa idanu. Wani irin bugu ƙirjinsa ya yi, kamar wanda ya yi tozali da gawar mahaifiyarsa. A hargitse ya janyo Ɗan Bishir ya rungume yana jin zuciyarsa tana zafi ya ce. "Ɗan bishiririna, waye ya taɓa ka? Me aka yi maka?" Ɗan Bishir ya sake narkewa yana wani tale baki irin na shagwaɓaɓɓun yaran da aka sangarta ya ce. "Innaaaaaa! Inna ce ta dungure mini kai. Wayyo Allah kaina." Jikin Baba Saleh har karkarwa yake, saboda a duk duniya idan da abin da yake ɗaga masa hankali ganin kukan Ɗan Bishir. Ya nuna Uwale idanu cike da masifa ya ce. "Sau nawa zan ce ki daina zalintar yaron nan Uwale? Ke wacce irin uwa ce kamar ba ke kika haife shi ba tsabar rashin imani, wallahi ba don kin ci darajar ke kika haife shi ba yau sai ranki ya yi mummunan ɓaci." Ran Uwale ya gama ɓaci ta nuna masa randar ruwan da suke sha ta ce. "Wallahi Mai gida wannan abin da kake yi ba soyayya ba ce, ɓata tarbiyyarsa kake yi. Dubi fa randar ruwan shan mu ya ɗauki omo da mai ya zuba mini, don na dungure masa kai kake yi mini wannan tijarar? To wallahi na gaji, na gaji da wannan abin da kake yi mini. Kai kuma don ubanka ko yau ka sake yi mini irin wannan ɓarnar sai na dungure ka." Uwale ta ƙarasa maganar tana sakarwa Ɗan Bishir ƙozo a ka. Wata irin gantsarewa ya yi yana canyara ihu tamkar wanda aka caka wa wuƙa, a fusace Baba Saleh ya kai wa randar duka ta bada tus! Ruwanta ya mamale a tsakar ɗakin, cikin ƙaraji ya ce. "Ba dai a kan randa za ki illata mini Ɗan Bishir ba? To wallahi idan ba ki da gaske ba, yadda na ragargaje randar nan kema sai na ragargaza ki." Baba Saleh ya yi furcin yana sunkutar Ɗan Bishir da zai yi shekara shida a tsaye, ya ɗauke shi yana shafa bayansa zuwa kansa yana lailaya shi kamar zai mayar da shi ciki. Ya rungume shi a ƙirji cike da so, ya waiga yana wurga wa Uwale mugun kallo. Har lokacin Ɗan Bishiri bai daina tale baki yana kuka a shagwaɓe ba, Baba Saleh ya kalle shi har lokacin zuciyarsa zafi take ya ce. "Me kake so ka ci Ɗan Bishirina." Ɗan Bishir ya wale baki yana duban mahaifiyarsa tana mata harara sannan ya ce. "Namaaaa!" Baba Saleh ya sauke shi ya ce, "Don nama banza Ɗan Bishir, bari na je na yanko maka na zabi ko kaji." "Na zabiiiiiiiiii." Ɗan Bishir ya faɗa a sangarce. Harara ya wurga wa Uwale sannan ya fice daga sashensu, yana zuwa ƙofar gida ya yi turus ganin abokinsa Sani yana ba wa yaro sakon a kira shi. "Ga ni na zo a daidai ya aka yi?" Sani ya ƙare masa kallo tun daga sama har ƙasa, sannan ya sauke idonsa a kan jakar wanzaman da ke rataye a kafaɗar Baba Saleh. "Karenka ya kai tsaiko ko Sale? Wai har ni za a kira na cire beli na yi wa jaririya aski, amma sai na ji labarin ka yi mini shigar ɓurtu alhalin ka sani ni ɗan gado ne a harkar wanzanci ba ɗan ka-ta-haye kamar kai ba?" Baba Sale ya saki tsaki cikin halin ko-in-kula ya ce. "To mene ne marabar dambe da faɗa? Don kana ɗan gado ka koya mini harkar wanzanci, na zo ni kuma Allah Ya saka mini nasibi duka costomers ɗinka sun dawo wurina wani avu ne? Wai ma da kake wannan abin, kai da kake jin ka ɗan gado da ni ta-ka-haye ba duka wanzamai za a ce mana ba? Kai matsa ka ba ni wuri Ɗan Bishiri ya aike ni, don aikensa ya fi mini wannan sokiburutsun banzan da kake yi mini." Baba Sale ya gegara ya wuce shi, ya nufi wurin Sadau mai nama. Bayan fitar Baba Saleh cikin takaici Uwale ta ɗauko zani ta shiga tsane ruwan tana matsewa. Mugun kallon da take jifan Ɗan Bishir da shi ya sa ya yi saurin ficewa daga ɗakin. Kai tsaye sashen Baba Inu ya nufa don tun da ya ji shiru ya san abinci suke ci. Ɗan Bishir irin kwaɗayayyun yaran nan ne da duk abin da suka ga ni, za su ce suna ci koda a hannun babba ne. Sangartar da Baba Sale ya yi masa ce ta sa ya koyi wannan mummunar ɗabi'ar. A lokacin da ya shiga sashen Baba Inu da bencinsa ya fara cin karo, ya hangi Baba Inu a can ƙofar ɗakinsa yana rabawa yaransa waɗansu ƙananun alewa. ragowar naman kazar da ya gani ya saka hannu ya ɗauka, ya kai ba ki ya fara zuge tsokarta yana lumshe ido. Sai da ya gama cinyewa tas, sannan ya ɗauki kindirmon nonon da Baba Inu ya zuba magani ya ɗaga kansa ya ɗaɗɗaka, a shagwaɓe ya wurgar da kwanon ƙasa bayan ya shanye ya ɗauki ƙashin kazar ya fara tauna. Ƙarar jefar da kwanon ce ta ja hankalin Baba Inu, da yara da suke gabansa. Ganin abin da Ɗan Bishir ya yi ya sa Baba Sale ya ƙarasa wurinsa rai a ɓace ya kai masa duka a baya. Ɗan Bishir ya tale baki a shagwaɓe ya saka kuka yana yi wa Baba Inu daƙuwa haɗe da faɗin. "Uwakaaaa!" Zuciyar Baba Inu ce ta fara tafasa, ya saka hannu zai dake shi da sauri Ɗan Bishir ya fita da gudu yana faɗin. "Allah Ya isa." Zucya tana tafasa Baba Inu ya rufa masa baya, suna zuwa mararrabar hanyar da take haɗa kowa da ke cikin gidan ya samu nasarar cafko shi, bai yi wata-wata ba ya tsinke shi da mari. A daidai lokacin Baba Sale ya ƙarasa wurin, ganin abin da aka yi wa Ɗan bishir ya sa shi wata irin zabura a haukace ya yi kukan kura ya tunkari wurin da suke tsaye. Share pls 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam🌚 [02/02, 15:02] Ameerah Adam🌚: *GIDAN LIKITOCI* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA BAƘAR DAULA AN YA BAIWA CE? ƊAN BA ƘARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA SHAFI NA UKU Jikin Baba Sale har karkarwa yake yi, ya ƙarasa wurinsu ya suri Ɗan Bishir da ya gantsare yana wani irin ihu da kuka, rungume shi ya yi tsam a ƙirjinsa ya shiga lailaya masa baya yana sasshafa shi. Lamo Ɗan Bishir ya yi yana sauke ajiyar zuciya don dukan da Baba Inu ya yi masa ba ƙaramin shigarsa ya yi ba, Baba Inu ya dube su rai a ɓace ya ce. "Idan ubanka bai koya maka tarbiyya ba, ni idan ka shigo gonata ladaftar da kai zan yi. Shashashan banza da wuri, yaro ya duk ya bi ya sangarce kamar tasowar gidan gwauro." Ran Baba Sale ne ya sake ɓaci, saboda dama ba ya ƙyale shi ba ne. Yana jiran ya gama lallashin Ɗan Bishir ne kafin ya dawo kansa. A hankali ya dire Ɗan Bishir, ya sunkiya ya yi masa raɗa a kunne. "Tsaya a nan zan rama maka ka ji Ɗan Bishiririna!" Ɗan Bishir ya kwaɓe baki a shagwaɓe ya ce. "Da ƙarfi za ka rama mini." Baba Sale ya gyaɗa masa kai, sannan ya tunkari Baba Inu da ya juya baya yana shirin shiga sashensa. Wani irin kukan kura ya yi haɗe da sufa sai ya yi tsalle ya ɗafe masa wuya, maƙure shi ya yi sosai ya shiga kai masa duka yana harbo shi da ƙafarsa. Jin irin shaƙar da Baba Sale ya yi masa ya sa Baba Inu ya zuciya ya wulwulo shi ya damfara shi da ƙasa, a galabaice Baba Sale ya yarfe hannu yana dafe ƙugu ya ce, "Wayyo Allah Uwale ki zo ya karya ni." Ihun da Baba Sale ya saki ne ya janyo hankulan mutanen gidan, ba a ɗauki lokaci ba mutane suka cika wurin kowa ya yi carko-carko. "Subhanallah me yake faruwa Sale?" Baba Ibrahim ya tambaya a razane, don irin ihun da Baba Sale ya yi za ka ɗauka farke masa ciki ake yi. Yana daga kwance ya ɗaga hannu yana fitar da numfashi da ƙyar ya ce, "Yaya Inu ne yake ƙoƙarin datse rayuwata da ta Ɗan Bishir, don Allah ku nesanta mu da shi kada ya hallaka mu." Ajiyar zuciya Baba Ibrahim ya sauke, Baba Inu ya yi kicin-kicin ya haɗe rai yana hura hancin yin galaba a kan Baba Sale. "Don Allah Yaya me kuke yi haka kamar ƙananan yara? Kai ne babba fa, ko me Sale ya yi maka ba sai ka rabu da shi ba ko ka yi masa faɗa. Amma yanzu ina daɗi a ce yara suna ganin irin wannan abin da kuke yi? Ta ina yara za su haɗa kansu?" Baba Ibrahim ya rufe su da faɗa, saboda lamarin gidan nasu a kullum ƙara taɓarɓarewa yake yi. Baba Inu ya dube shi a sheƙe ya ce, "Kai Iro, dube ni da kyau ka kalli ƙwayar idona." Baba Inu ya yi maganar yana ware dara-daran idanunsa da girma ya sa suka fara shigewa, sannan ya ɗora da cewa. "Wane ne wannan?" Ya tambayi Baba Ibrahim yana nuna Ɗan Bishir. "Ɗan Bishir ne!" Baba Ibrahim ya ba shi amsa. "Yanzu Iro ko Sale ya isa ya zage ni ballanta wannan yaron mai zubin buhun bagco!" Duka mutanen wurin suka girgiza kai cike da son ƙara ingiza Baba Inusa, saboda kowa ya san rashin kunyar Ɗan Bishir don haka yake da baƙin jini a wurinsu. Nan take Baba Inu ya ba su labarin abin da ya faru, da abin da Baba Sale ya yi masa. A razane Baba Sale ya miƙe jiki yana karkarwa, ya nufi hanyar sashensa da gudu ganin Ɗan Bishir ya yi hanyar, ya rarumo shi ya riƙo shi sai kawai ya ɓarke da kuka. Kallonsa suka tsaya yi suna mamakin kukan da yake yi, ya tako wurinsu a guje yana saɓule burmemiyar doguwar rigar Ɗan Bishir ya ce. "Jama'a ku taimaka mini Ɗan Bishir ya sha maganin ƙarin kuzari, wayyo Allah yaya don Allah ka kawo mini ɗauki." Ya ƙarasa maganar yana miƙa wa Baba Ibrahim shi sannan ya ɗora da cewa. "Don Allah ka yi masa wani abu yaya kai ne likita, Allah Ya sa ba ajali ne yake kiransa ba ban da haka ina Ɗan Bishiri ina shan maganin kuzari?" Yana gama maganar ya sake ɓarkewa da kuka. "Ka ga Sale kada ka ɓata wa kanka lokaci, idan har kana son rayuwarsa ka ba ni wani abin ni kuma zan ba ka lambar mai maganin sai ka nemi makarin maganin a wurinsa. Bokan turai ta ina ya san abin da aka haɗa?" Baba Inu ya yi maganar yana sakin murmushin ƙeta. Baba Sale ya yi zaman 'yan bori a wurin ya ce, "A kan Ɗan Bishir zan iya sadaukar da komai da na mallaka, Yaya nawa zan ba ka don Allah ka ba ni lambarsa." Baba Inu ya ɗauke kai gefe cikin basarwa ya ce. "Dubu ashirin!" A firgice Baba Sale ya ce, "Ashirin fa Yaya?" Baba Inu ya yi gaba abinsa cikin halin ko-in-kula ya ce. "Kada ka biya matsalarka ce, ni ko yanzu na mutu akwai masu yi mini addu'a da yawa." Jin haka ya sake ɗaga hankalin Baba Sale, ya janyo ƙafarsa yana ba shi haƙuri, babu yadda ya iya haka ya shiga cikin gida ya ɗauko dubu ashirin ya damƙa masa. Sannan Baba Inu ya karanto masa lambar mai maganin, jikin Baba Sale har rawa yake ya yi masa bayanin abin da ya faru. Mai maganin ya tabbatar masa da babu abin da zai faru da shi, sai dai ya ja hankalinsu a kan su dinga lura sosai saboda kar gaba a samu matsala. Ɗaya bayan ɗaya suka fara watsewa, Baba Inu ya koma sashensa zuciyarsa fes don shi wannan abin da ya faru ya zame masa alkairi. Yana nan zaune ya ji sallamar Malam Jibrin, jin haka ya sa ya dubi su Abu a kausashe ya ce. "Ke Abu da fatan kun haɗa wa yaran nan kayansu ko? Ga sallamar Malam Jibrin can na ji, bari na je mu gaisa." Tun da Baba Inu ya fara magana ta haɗe fuska, saboda Allah Ya sani ba za ta iya bayar da yaranta a kai su makarantar allo ba. Yana zuwa ƙofar gida ya samu Malam Jibrin, daga gefe wata ƙatuwar motar Bus ya gani kusan rabin motar cike take da yara waɗanda za a kai makaratar allo. Bayan sun gaisa Malam Jibrin ya ce. "Malam Inu ina fatan an gama kintsa yaran? Saboda direban motar sauri yake akwai sauƙon da ake jira zai bayar a hanya." Yaya Inu ya faɗaɗa fara'arsa yana jin kamar za a sauke masa wani gingimemen nauyi daga kansa ya ce. Malam Jibrin ba ka da matsala yanzu za su fito, amma fa an samu ƙarin yara uku." Shiru Malam Jibrin ya yi ya ce, "Yaran kuwa ba su yi yawa Malam Inu? A baya fa yara shida ka ce za a tafi da su. Idan mun yi gaba akwai 'ya'yan Malam Sallau guda biyu da za mu ɗauka." Duk da yana jin zafin fitar kuɗin amma sanin sauƙi zai ƙara samu ya sa ya zaro dubu uku ya miƙa wa Malam Jibrin ya ce, "A ƙara da wannan Malam Jibrin, ka sha ruwa a hanya, ka san yaran ne duk kansu ɗaya. Da su Barau masu shekara huɗu zuwa biyar ne zan bari amma su ma ai sun tasa, Allah na tuba abu da girman ɗan mutum babu wuya." Malam Jibrin ya kalmashe dubu ukun saka a aljihu yana murmushi ya ce, "Yo shekara huɗu mene ne ba za su iya yi wa kansu ba? Ai duka sun tasa, kuma Allah ai shi yake raya bawa ba mutum ba." A daidai wannan lokacin Malam Isiya ya ƙarasa da ɗansa Musbahu mai kimanin shekara goma sha biyu, hannunsa riƙe da ƙaton buhu wanda ya haɗa masa ƙanzo, garin kwaki, sabulu da omon wanki. Bayan sun gaisa da Malam Isiya, ya kawo 'yan kuɗi ya ba shi. Malam Jibrin ya ce, "Malam Isiya ya na ganka da ƙaton buhu bayan jakar hannunsa, akwai yaran da za mu ƙara a motar fa." Malam Isiya ya yi murmushi ya ce, "Kayan abincinsa ne a ciki, ai ba ka da damuwa Malam Jibrin zan biya kuɗin kujera biyu, don tare za mu tafi. Saboda na je na ga mkarantar da za a kai Musbahu, mu gaisa da malamin kafin daga baya lokaci zuwa lokaci na dinga zuwa ina gano shi ina kai masa kayan abinci." Malam Jibrin ya kalli Musbahu ya ce, "Lallai Musbahu kai ɗan gata ne, abin da iyaye da dama ba sa yi kenan! Kai ma Malam Isiya Allah Ya sa da gaske kake." Malam Isiya ya ce, "Me ka ɗauke ni Malam Jibrin? Ai yayansa Ɗahiru da ke garin Kaduna yana karatu, duk bayan wata biyar nake zuwa wurinsa, domin na ga halin da yake ciki kuma na kai masa kayan abinci da 'yan kuɗaɗen sayen abin buƙata. Kawai kuma saboda ka kai yaro makarantar allo sai ka manta da shafinsa? Yara fa amana ce da Ubangiji Ya damƙa mana kuma ranar Lahira sai ya tambaye mu a kan kiwon da ya ba mu." Malam Jibrin ya jinjina kai, Yaya Inu yana jin haka ya zame ya shige gida yana faɗin zai haɗo kan yaran su tafi. Saboda sho ko ɓarin gyaɗa babu wanda zai ba wa a cikinsu, abin da yake ciyar da su ma Allah amfana. Yana shiga tsakar gida ya ci karo da su Basiru kowanne ɗauke da ƙaton buhu a kansa, iyayensu ne suka ɗauko ƙanzo da garin kwakin da suka tanadar musu. "Ku yi sauri ku shirya su Barau, Idi da Iro ƙarami, su ma da su za a tafi." Sororo suka yi jiki a sanyaye Larai ta ce, "Don Allah malama..." "Wallahi sai an tafi da su, tun da na rantse babu kaffara. Idan sun zauna yaran uwar me za su yi musu? Kun fi son yara su zauna babu ilimi mutanen gari su dinga zagina." Sanin halinsa na kafiya ya su Larai suka shiga shirya ƙananan yaran kowacce tana share hawaye, ban da Abu da ta ja ta tsaya ta ki motsawa. "Ke ba ki ji abin da na faɗa ba ne?" Yaya Inu ya faɗa yana haɗe rai. "A gaskiya Malam ba zan iya bayar da Bukar da malami a tafi da su ba, dududu shekarar Bukar nawa? Ko biyar da rabi bai rufa ba. Shi kuma malami shekara huɗu, idan sun je wa zai kula da su ya ba su abinci?" Abu ta faɗa tana ƙanƙame Malami. Ran Yaya Inu ne ya ɓaci, suka shiga ja'inja yana jan Malami tana ja, daga ƙarshe ya ɗauke fuskarta da mari sannan ya fisgi hannunsu suna ihu da kuka Abu tana yi ya nufi hanyar fita. Da gudu Abu ta bi shi duk da tsohon cikin jikinta, ya waigo a fusace ya ce. "Wallahi Abu idan har kika tako zuwa soron gidan nan a bakin aurenki tun da ba ki da hankali." Abu ta yi turus, tana jin wani irin ɗaci a ranta. "Iyataaaa!" Malami ya faɗa cikin kururuwa, da gudu Abu ta rufa masa baya har ƙofar gida yana zuwa ya damƙawa Malam Jibrin su, ya fisge su kamar kaji ya watsa a cikin mota. A zafafa Yaya Inu ya koma cikin gidan Abu ta bi shi tana kuka, ya waigo a zafafe ya ce. "Daga nan ki wuce gidan ubanki, na warware ragowar igiyar kanki." Daga haka ya shige cikin gida. Ɗaya bayan ɗaya 'yan masu wayon suka fara fita cike da ɗoki, musamman da suka leƙa suka hango motar da take jiransu a ƙofar gida. Su Barau da yake ƙanana ne suka dinga kuka suna tirjewa iyayensu ma suna kuka. Jin kuka da ihu tare da hargagin Yaya Inu ya sa rogawar mutanen gidan suka fito suka yi carko-carko, Inno ce ta tambayi abin da ya faru a nan Yaya Inu ya sanar da su. Takaici ne ya kama Baba Ibrahim rai a ɓace ya ce. "Yaya wai saboda Allah wacce irin rayuwa kake yi haka? Yanzu don Allah kamar su Barau za ka kai birni makarantar allo? An ya kana tunanin goben yaran nan?" Yaya Inu yaji kamar Baba Ibrahim ya zuba masa ruwan zafi, rai a ɓace ya mayar masa da martani. "Kai Iro kada ka faɗa mini maganar banza da wofi, ba ɗazu ka gama faɗa mini magana a kan rashin iliminsu ba. Kai za ka faɗa mini na hango gobensu, akwai shege ɗaya a cikin gidan nan da yake ciyar mini da su? Tun da ni na samu kaina a gobena ai shi kenan! Daga yau ma kada wani ƙaton banza ya sake shiga hurumin iyalina." Yaya Inu ya ƙarasa maganar yana fisgar Idi da ko wando babu a jikinsa ya yi waje da shi. Su Larai suka durƙushe a wurin suna sakin kuka. Suna nan tsaye suka ji tashin motar, hakan ya sake ɗaga hankalansu, a daidai lokacin Yaya Inu ya dawo yana muzurai yana harare-harare. Bayan Sallar Isha'i Zaune yake a matsakaicin ɗakin da aka ware masa, daga gabansa wani ƙaton fulas ne cike da farfesun kaji. Sai da ya zuge tsokar cinyar kazar hannunsa, sannan ya ɗaga ƙaramar wayarsa ya danna wata lamba. Bugu ɗaya ta yi ya ji an ɗauka, ya yi ƙasa da murya ya ce. "Barka da hutawa 'Yar gwal!" Malam mai Yasin ya furta yana kurɓar romon naman, amsa masa ta yi sannan ta ce. "Ni fa na gaji wallahi..." Da sauri ya katse ta. "Haba 'Yar gwal, na faɗa miki kwantan ɓauna na yi wa mutanen gidan nan, har na samu na aure tsohuwar nan. Ni na san Inno ba za ta ba ni matsala ba sai dai 'ya'yanta, amma ina aure ta magana ta ƙare. Tatsarta zan ta yi har na tara mana kuɗin da za mu hole, kada ki ji muryata ƙasa-ƙasa har yanzu nuna musu nake ba ni da lafiya." Daga can ɓangaren 'Yar gwal ta saki dariya ta ce. "Shege Malam Gambo wallahi ko shaiɗan bai kai ka shaiɗanci ba." Malam mai Yasin ya saki dariyar shakiyanci, suka cigaba da hira sannan suka yi sallama. Ya kai kusan awa guda a zaune a bakin gadon yana yi mata firfita, saboda ko kaɗan ba ya son abin da zai dagula lissafinta. A hankali Rahina ta buɗe idanunta ta sauke su a kan mai gidanta Labaran, murmushi ya sakar mata ganin za ta tashi ya sa ya ɗago ta zaune sannan ya rungume ta sakar mata kiss a goshi. "Barka da tashi masoyiya!" Labaran ya furta cike da so yana jin kamar zai lashe Rahina. Fari ta yi masa da ido ta ce, "Wai tun da na kwanta kana zaune masoyi?" "Ina zan matsa daga wurinki ƙaunata. Yanzu dai bari na sirka miki ruwa ki yi wanka. Ya ƙarasa maganar ya fita daga ɗakin." Rahina ta bi bayansa da kallon soyayya tana jin tamkar ita kaɗai ta yi dacen miji a duniya. Tana nan zaune ya dawo ya riƙo ta, ganin za ta tuɓe kaya ya saka hannu ya fara rage mata. Rahina ta ɗaura zani ta yafa ɗan kwali a kanta, Labaran ya riƙe mata hannu ɗayan hannun nasa yana riƙe da kwandon wanka suka nufi hanyar banɗaki. Sai da ya ga ta shiga banɗakin, sannan ya koma domin ya zuba mata abincin da za ta ci idan ta fito. Rahina irin matannan ne masu tsayi da ƙiba, shi kuma Labaran ɗan tsamurmuri ne ko tsayin kirki ba shi da shi. Yadda yake son Rahina da kishinta ji yake zai iya aikata komai a kanta. Malam mai Yasin yana daga zaune a ɗakinsa ta labule ya hango wucewar Rahina, ya jima ransa yana biyawa da ita don haka bayan tafiyar Labaran ya yi zaraf, bayan ya ji ta fara sheƙa ruwa ya nufi banɗakin cikin sanɗa. A hankali ya tura ƙofar banɗakin, da yake dare ne sai Rahina ta yi tsammanin ko Labaran ne ya shiga domin ya tayata wankan. Malam mai Yasin yana shiga da sauri ya wara hannuwansa ya dadumo ta, cike da so da ƙauna Rahina ta ce. "Wallahi ba don kada na saka son zuciya ba, da sai na ce duk duniya babu matar da ta kai ni sa'ar miji masoyi." Malam mai Yasin don kar ya yi magana ta ji muryarsa sai kawai ya ce, "Ummmmm!" Ya cigaba daduma hannunsa a jikinsa. Rahina tana shafo fuskarsa ta ji gemunsa da gashin bakinsa sun yi mata ƙababa, a razane ta ja da baya da ta ce. "Wayyooo Allah! Masoyi ka zo kwarto a banɗakin nan." Da gudu Malam mai Yasin ya fice daga banɗakin ya faɗa ɗakinsa, Labaran da ke ɗaki jin ihun Rahina ya sa ya zaro wani kafcecen almakashi irin na aikin gona ya tafi da shi. Yana zuwa banɗakin ya shiga jera mata tambayoyi, ba ta tanka masa ba sai ji ya yi ta fashe da kuka. Ganin ba shi da wata mafitar ya sa shi ma ya rushe da kuka har da majina, sai da ta yi mai isarta sannan ta ce. "Kwarto ne ya shigo mini banɗaki, kuma tas ya gama lalube ni." Wani abu ne ya soki ƙirjin Labaran tsananin soyayya da kishinta ya rufe shi. "Sai da na laluba gemu da gashin bakinsa, na gane ba kai ba ne tun ba ka da shi." Rahina na ƙara faɗin haka ta sakin kuka. Jikin Labaran ne ya shiga karkarwa zuciyarsa tana zafi, cikin huci ya ce. "Na tabbata Ado ne! A cikin gidan nan shi ne tuzuru sako zaninki ki tafi ɗaki, wallahi yau sai na guntule shi da almashin hannun nan nawa. Nan gaba sai na ga da me zai nemi yin kwartoncin." Labaran yana gama magana ya fita a guje yana wani irin ihu kamar wanda zai tunkari maƙiya a filin yaƙi. 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam🌚 [02/02, 15:02] Ameerah Adam🌚: *GIDAN LIKITOCI* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA BAƘAR DAULA AN YA BAIWA CE? ƊAN BA ƘARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA SHAFI NA HUƊU Kasancewar yaya Ado dawowarsa daga wurin aiki kenan, ya sa ya shiga rage kayan jikinsa domin ya watsa ruwa ya gabatar da sallar Isha'i. Yana daga cikin ɗakinsa ya fara jiyo ihun Labaran, ya girgiza kansa cike da takaici, yana jin haushin yadda gidansu ya zama tamkar gidan haya saboda yadda zuciyar kowa take a kusa. Ihun da Labaran yake kurmawa ne ya janyo hankulan mutane wasu suka fito, wasu kuma suka tsaya suna leƙensa daga window. Yayin da wasu kuma suka rifa masa baya, domin su ga irin wainar da zai toya. Sashen Yaya Ado ya shiga, ya tsaya daga bakin ƙofa yana sauke numfashi cike da zafin rai. Yaya Ado ne ya leƙo da kansa daga shi zai gajeren wando, ya haɗe fuska ganin Yaya Ado da ragowar mutanen gidan a sashen ba tare da sun nemi izininsa ba. Saboda yaya Ado mutum ne mai tsattsauran ra'ayi, kuma yana da ƙa'idoji don haka suke cewa karatun boko ya mayar da shi mai aƙidar yahudawa. "Me ya sa ka shigo mini ba tare da izinina ba?" Yaya Ado ya tambaya fuska a haɗe, Labaran ya ji kamar ya watsa masa ruwan zafi mai haɗe da attaruhi, saboda ganinsa da ya yi da gajeren wando kaɗai ya sake harzuƙa shi, musamman da ya tuna Rahina ta ce kwarton yana ta shafe ta a banɗaki. A hankali Labaran ya fara takawa jikinsa har karkarwa yake, hannunsa riƙe da ƙaton almashi. Ganin haka ya sake ɓata ran Yaya Ado, saboda a duniya ya tsani wani ya raɓo ɗakinsa saboda muhimman takardunsa da ba ya son wani ya taɓa masa. A harzuƙe ya tunkari Labaran ya ce. "Kai Labaran ba magana nake yi maka ba?" Mutanen wurin carko-carko suka yi cikin mamaki suna kallon Labaran, cikin shammata Labaran ya yi kukan kura ya yi kan yaya Ado yana ɗaga almashin sama, kamar yadda sojoji suke yi a filim yaƙi ya ce. "Zuwa na yi na halaka ƙasurgumin fasiƙi da wannan almakashin." Yana gama magana ya kai hannu yana ƙoƙarin fisgar gajeren wandon Yaya Ado. Nan take suka shiga kiciniya, Yaya Ado yana ƙoƙarin kare kansa shi kuma Labaran ƙarfi da yaji yake ihu da kururuwar sai ya guntule shi. Ganin haka ya ɓata ran yaya Ado, ya fusata ya ɗaga Labaran ya damfara shi da ƙasa. Labaran bai daddara ba ya sake miƙewa duk da ya ji zafin buguwar ya ce. "Wallahi yau ko kashe ni za ka yi sai dai mu kashe juna, ko banza na san zan mutu a fagen shahadar kare mutumcin matata." Yana rufe baki sai kawai ya saka hannu ya zugo gajeren wandon ƙasa. Matan da suke wurin suka saki ihu suna fita waje a guje, yayin da Baba Ibrahim da Baba Sale suka yi kansu Labaran da gudu ganin da gaske yana shirin aikata abin da yake faɗa. Fitar Hansatu ya yi daidai da parking ɗin motar Fadil, da gudu da ƙarasa wurinsa cikin kururuwa ta ce. "Likita don Allah ku taimako wallahi kisa za a yi, Ado ne da Labaran." Cikin izza ya sauke baƙin gilashin idonsa, ya zuge gilas ɗin motar cikin golden voice ɗinsa ya ce. "Lafiya?" Ya tambaya saboda bai ji abin da ta faɗa ba, sakamakon gilashin motar da ke rufe. "Ado da Labaran ne za su kashe kansu har da makami, don Allah ku zo ku kawo ɗauki." Hansatu ta sake maimaitawa a hargitse, ganin yanayin da take ciki na firgici ya sake tabbatar masa da abin da take faɗ. Ya saka hannu ya dafe goshinsa cikin takaici, saboda a kullum danasanin sakancewar zamansa a wannan gidan gandun yake yi. Bai tanka mata ba, ya ajiye lapcoat ɗinsa ya buɗe murfin motar ya fito. Ƙamshin turarensa ya bugi hancin Hansatu, ita dai haka kawai rayuwar Fadil take birge ta don haka ma ta ci alwashin aura masa Badariyya, idan ta ƙara zama budurwa tun da dama namiji ai mijin mace huɗu ne. Kuma matar Fadil ko kaɗan ba za ta nuna wa Badariyya komai ba, sai kyau da iyayin da take taƙama da ita likita ce. "Suna ina?" Fadil ya katse mata tunanin da take yi. Da hannu ta nuna masa mangaren Yaya Ado. Da sauri Fadil ya shiga, a daidai lokacin Malam mai Yasin da Inno su ma suka ƙarasa. A lokacin yaya Ado ya samu nasarar ƙara ɗaga Labaran ya buga da ƙasa, hakan ne ya sake ɗaga hankalin Inno sai ta fashe da kuka, da ƙyar aka samu aka riƙe Labaran, shi ma yaya Ado aka riƙe shi kowannensu sai sauke ajiyar zuciya yake yi. Malam ya kwantar da murya kamar bai san abin da ya faru ba, ya shiga tambayarsu abin da ya haɗa su. Rai a ɓace yaya Ado ya ce. "Kun san dai a cikin gidan nan ba sabgar kowa nake shiga ba, saboda ba na ɗaukar raini ba zan ɗauki cin zarafi ba. Yanzu saboda Allah shekara nawa na ba wa Labara? ko Sale da yake bi na, ya isa ya zo ya yi mini iskancin daLaraban ya yi mini ballanta shi ƙanina na biyu? Wallahi ko da wasa ka sake kwatanta mini abin da ka yi sai na ba ka mamaki sakarai bawan mace." Daga haka yaya Ado ya fisge hannunsa ya shige ɗakinsa. Tun ba su ji ta bakin Labaran ba suka fara ba shi laifi a zuciyarsu, saboda kowa ya san yaya Ado shi kaɗai yake gudanar da rayuwarsa bai cika shiga shirgin kowa ba bayan gaisuwa. Don haka ma ake zargi da raɗe-raɗin ko aljana ce ta aure shi, tun da ga ƙannensa nan har biyu sun daɗe da aure amma shi shiru. "Kafin ku ji abin da ya faru don Allah zan tambaye ka Likita!" Labaran ya yi maganar yana kallon Fadil. Gyaɗa masa kai ya yi alamar yana sauraronsa Labaran ya ce. "Idan yanzu na saka almashin nan na guntule yaya Ado, akai wani dashe da za a yi masa a likitance?" Takaici da kunya suka hana Fadil yin magana, kamar dai ba zai magana ba sai kuma daƙile ya ce. "A'a" Labaran ya haɗiyi yawu mai ɗaci yana jin kishin Rahina yana nukurkusarsa ya ce, "Yaya Ado ne ya shiga banɗaki ya lalube mini masoyiya tana wanka, saboda ya ga dare ya yi kuma wallahi idan duk garin nan gatansa ne sai na gama da shafinsa." Labaran yana gama faɗar haka ya shamace su ya fisge ya faɗa ɗakin Yaya Ado cikin ƙaraji yana faɗin. "Gafara ga maza nan bisa kanka." Ganin haka ya sa su ma ragowar mazan da ke tsaye suka rufe masa gaya. Da ƙyar suka samu suka sake yage Labaran, sai da aka kai ruwa rana sannan aka ba wa Labaran haƙuri ya haƙura. Dalilin da ya sa Labaran ya haƙura, saboda Baba Inu da Baba Ibrahim sun tabbatar da yaya Ado a kan idonsu ya shiga sashensa, kuma suna tsaye Labaran ya zo yana cewa an shiga banɗakin da Rahina take wanka. "To kuwa idan haka ne akwai kwarto a cikin gidan nan, kuma ni da ma daga cikin ilimin da Allah Ya ba ni akwai na gane kwartaye. Kuma ni dama tuna zuwa ban yarda Ado zai aikata hakan ba. Za mu zuba aiki cikin ɗan ilimin da Allah Ya ba mu, Allah Ya sa mu dace." Malama mai Yasin ya yi maganar da wata irin murya, kamar irin waliyan bayin Allahn nan. Gabaɗaya suka amsa masa sannan kowa ya watse. Washegari Tun da asuba bayan da Inno ta tashi Laraba yin Sallar Asuba, ta tabbatar mata da ba za ta je makaranta ba, saboda irin cin zarafin da Mai gari ya yi mata a gaban mutane da yaran gari. Don haka har kimanin ƙarfe tara na safe tana kwace a kan gado tana bacci, daga ita sai rigar atamfa da ɗan kanfai a jikinta. Zanin ya zame ya faɗi gefen gado, yayin da ɗankwalinta ya faɗo ƙasa. Sallama ɗauke a bakinsa ya shiga ɗakin Inno, Inno tana ganinsa ta haɗe rai fara mita sama-sama. "Haka kawai a dinga tayar mini da zaune tsaye, ina dalili a ce duk bayan kwana uku sai an auna jinin mutum. Ni dai tun farko Burema ya cuce ni da ya sayo abin nan ya ce ka dinga auna jinina." Fadil ya zaune a gefenta bayan ya gaishe ta ya ce. "Ba ni hannunki!" Inno ta watsa masa harara ta ce, "Kai Boka ni fa na gaji da wannan ɗaurin hannun. Kaf zuri'armu babu mai ciwon hawan jini, sai da ubanka ya ƙaƙaba mini." Fadil ya sake haɗe fuska ya ce. "Inno sauri nake fa." Ya ƙarasa maganar yana riƙo hanunta, Inno ba don ta so ba Fadil ya gama gwada mata hannu. Kasancewar ta taɓa fama da ciwon hawan jini, yana shirin fita ya hango Laraba a kan gado tana sharar bacci. "Yarinyar can me ya hana ta zuwa makaranta?" Inno ta ɓata fuska don ta san yanzu sai ya tilasta mata zuwa. "Tun asuba ta ce mini jikinta yana ciwo ba za ta je ba, ka san jiya zanen zabuwa Mai gari ya yi mata. Ni ma kuma da ma ko ba ta faɗa ba, ba zan bari ta je makaranta da ɗanyan jiki ba." Fadila bai tankawa Inno ba ya ƙarasa ya buɗe firjinta, ya ɗauko ruwa mai sanyi ya ƙarasa ya kwara a kan Labara. A hargitse ta tashi cikin masifa ta ce. "Uban waye ya zuba mini..." Maganarta ce ta maƙale ganin Fadila tsaye a kanta, ya naɗe hannuwa a ƙirji fuska babu walwala. Ta shiga murtsuka fuska tana kawar da kanta fege. "Tashi ki yi shirin makaranta. Labara ta tura baki ta ce. "Ni ba za ni makaranta yara su raina ni ba!" "Idan na sake magana wallahi sai na karya ki biyu!" Fadil ya faɗa a tsawace. Jiki yana rawa Laraba ta tashi ya janyo kayanta a cikin drower, waɗanda suka cukukuɗe kamar an ƙwato daga bakin kura. Uwar ɗaki ta shiga ta sako kayanta duk sun yi ɗauɗa, wandonta kuwa saboda rashin guga duk ya tattare ta baya da kaɗan ya fi gwiwarta. "Ni fa yunwa nake ji!" Laraba ta faɗa cikin ƙunƙuni. "Ba dole mutum ya ji yunwa ba ƙarfe tara na safe, a gaskiya Boka kada ka tura Laraba makatanta ba ta ci abinci ba..." "Wuce mu je!" Fadil ya katse Inno. Labara har da hawayenta ta ɗauko jakarta wacce ta kasance ta ɗinki buhu ta rataya. A tsammaninta ita kaɗai za ta tafi, sai ta ga Fadil ya bi ta tana gaba yana biye da ita a baya. Laraba tana zuwa ƙofar ajinsu ta ja ta tsaya ganin Fadil ba shi da niyyar tafiya. Ɗagowa ta yi za ta yi magana, kallon da ya wurga mata ya sa ta shige cikin ajin jiki a sanyaye. "Ke daga ina kike?" Malam Sule ya wurga mata tambaya. Laraba tana shirin yin magana Fadila ya yi sallama a ƙofar ajinsu. Malam Sule ya ƙarasa ya miƙa masa hannu suka gaisa. "Ga yarinyar nan na kawo, don Allah malam a saka ido a kanta ba ta son zuwa makaranta. Kuma duk ranar da ta makara ko ba ta zo ba, matuƙar babbu wani ƙwaƙƙwaran dalili a hukuntata." Fadil ya faɗa. Malam Sule ya washe baki ya ce. "In Shaa Allahu Alhaji za a yi yadda kace." Fadil ya yi masa godiya, sannan ya shiga ofishin Headmaster ya sake jaddada masa maganar da suka yi da Malam Sule, Headmaster ya ji daɗi sosai domin yana son ya ga iyayen da suka tsaya a kan kula da shige da ficen yaransu. Daga ƙarshe Fadil ya yi masa godiya, sannan ya wuce gida a gurguje saboda ya kusa makara. Malam sule dama abin nema ne ya samu, saboda yana daga cikin malaman da suke hora ɗalibai. Yana shiga ya dubi Laraba ya ce ta je gaban allo ta tsaya, sannan ya ce mata idan ya gama biya musu darasi sai ta karanta masa abin da ya rubuta. Laraba ta wurga masa harara a fakaice, ta koma ta tsaya ta haɗa rai domin ko kaɗan ba ta san raini. Tana daga tsaye wasu daga cikin 'yan ajin suka dinga yi mata gwalo, wasu kuma suna tsokanar dukan da aka yi mata. Malam Sule subject ɗin English language yake ɗaukarsu. Kuma a ranar Comprehension ya yi musu, sai ya rubuta musu short story mai taken 'Tortise and the goat' kasancewar duk cikin ajin babu mai textbook. Sai da ya karanta da turanci sannan ya fassara musu da hausa, ya dubi Laraba da tun da aka fara karatun hankalinta yana kan ƙofa, tana kallon dukan makarar da ake yi wa sauran ɗalibai. Don ko bayanin da ya yi da hausa ba ta gama saurare. Malam Sule ya haɗe rai ya ce. "Maza biya mana, ki fara yi da turanci sai ki fassara." Shiru laraba ta yi tana bin allon da kallon, don ta tabbata da allon yana magana ƙila zai iya baya mata kansa saɓanin ita da babu abin da ta gane sai baƙaƙen a b c d, su ma idan da za a saka mata wuƙa a wuya ko guda goma ba za ta iya karantawa ba. Laraba ba ta yi tsammani ba ta ji ya zuba mata bulala a baya, don haka ta taƙarƙare ta fara yi masa wani irin yare wanda ita kansa ba ta san me yake nufi ba. Duk yadda Malam sule ya kai ga mazewa sai da ya kawar da kai ya saki murmushi, sannan ya ce ta fassara da hausa. A nan ma Laraba babu tsiyar da ta tsinana, sai sokiburutsu da ta dinga yi masa. 'Yan ajinsu kuwa suka shiga ƙyaƙyata dariya suna yi mata ihu, Laraba ta ƙulu sosai don haka ta yi kukan kura ta faɗa kan Suwaiba ta rufe ta da duka, don ta fi jin haushinta dama saboda har gwalo take mata tana raɗawa na kusa da ita abin da za su faɗa. Da sauri Malam Sule ya fisgo Laraba saboda ya yi mata maganar duniya ta ƙi ji, ya shiga dukanta da zafafe. Zuciya ta kuma ciwo Laraba ta sake cukumo Suwaiba, tana kai mata naushi a baki har sai da ya fashe. Malam Sule mari ya zabga kata, sai a lokacin Laraba ta ja da baya ta dube shi a haukace cikin ɓacin rai ta ce. "Kai malam kada ka sake dukana, wai ba kai ne ɗan gidan Bala mai satar agwagwa ba ko an faɗa maka ba mu sani ba." Wani abu ne ya caki zuciyar Malam Sule, saboda bai taɓa tunanin za ta yi masa wannan bankaɗar ba. Cikin borin kunya ya rufe ta da duka, sai da ya zane Laraba sannan ya riƙe hannunta ya dinga bin ajujuwa da ita, yana saka kowanne prefect ya yi mata bulala biyar kuma 'yan aji su yi mata ihu. Ranar zuciyar Laraba ta gama dagulewa, don haka ta ci alwashin ko sama da ƙasa ce zaata haɗe ba za ta ƙara zuwa makarantar ba. Kuma sai ta hukunta iyaye da 'ya'yan da suka ci zarafin, shi kuma Malam Sule ta ci alwashin sai ya yabawa aya zaƙinta a wurinta. Duk irin zaman doya da manjar da suke yi tsakanin matan Yaya Inu, sai da suka ji jikinsu ya yi sanyi a kan sakin da ya yi wa Abu. Duk da ba baƙon abu ba ne a wurinsu amma irin son da suka san Yaya Inu yana yi mata ne ya ba su tsoro domin ba su taɓa tsammani ba. Hansatu ta fi kowa shiga damuwa saboda duk matan da Yaya Inu yake saki, idan suna da yara ƙarƙashin kulawarta suke komawa, kasamcewar ita ce uwargida a wannan lokacin. Sun jima suna janjantawa da suka ji motsinsa sai kowacce ta shiga aikin gabanta. A yanzu Indo ita ce matar Yaya Inu ta uku, ita ce take bin Larai. A ƙalla ta kai shekara huɗu a gidansa, 'ya'yanta uku duka maza. Babban ɗanta Uzairu bai fi shekara uku da watanni ba, sai mai bin sa Ya'u mai shekara ɗaya da rabi. Sai kuma jaririn da take goyo mai wata shida Hannafi. A washegarin ranar da aka saki Abu akwai bikin da matar yayan Indo ta gayyace ta, a wani ƙaramin gari da ke gaban garinsu. Tun safe Indo ta katsa wanka ta ɗauko galleliyar atamfarta yadi ta saka, ta yi wa su Larai sallama tana jin kamar za ta je wata sabuwar duniya. Larai a ranta take jin dama ita ce take da 'yan uwa a birni, da suke biki har ake gayyatarta da ko babu komai ta samu abin yi wa su Hansatu gori. A gidan kamun bikin da Indo ta je ne, ta tarar da wata mata da aka ɗauko Hajiya Zanni mai gyaran aure tana yin lecture ma'aurata. Matar irin masu safarar magungunan mata daga Kano zuwa Saudiyya ne, ita take koyar da su kissa da dabarun jan hankalin miji wanda zai mallake zuciyar miji. Saboda yadda take yin lacture cikin batsa ya sa mata sai shewa suke, mafi yawa daga ciki suka ƙuduri niyyar yi wa mazajensu daga ciki har da Indo, da take ganin kamar ta mallake Yaya Inu ta gama. Daga ƙarshe Hajiya Zanni mai gyaran aure ta ɗebo magunguna ta fara tallatawa. Jikin Indo yana rawa ta zaro ɗan canjin jakarta ta sayi wani magani mai suna, kin yi wa kishiya fintinkau da idonka idona. Cike ɗoki Indo ta tafi gida, koda ta je gida haka ta dinga kallon su Larai a sheƙe tana yi musu kallon tausayi, mai tafe da izgilin na yi muki nisa don a yanzu sai yadda na yi da mai gida. Daɗin sai ya haɗe mata biyu sakamakon ita ce da girki ranar, tun kafin magriba Indo ta gama komai. Ta caɓa wanka, ta ɗauko wani turarenta na Binta sudan, ta bulbule jikinta da shi kamar yadda ta ji Hajiya Zanni ta ce namiji yana son ƙamshi. Indo har ƙaguwa ta yi a idar da sallar Isha'i Yaya Inu ya shigo gida, sai ga shi a ranar ya yi jinkirin shigowa don har kusan goma saura. Haka ta zauna a gefen gado har ta fara gyangyaɗi, sannan ta ji shigowarsa. Da sauri ta ɗauko Hannafi ta kai shi gefen Uzairu ta kwantar da shi, saboda ta ji Hajiya Zanni ta ce ba a zuwa turaka da yara suna takurawa uwargida da mai gida. Turarenta na Binta sudan haɗe da jan miski ta ɗauko ta sake bulbulawa, ta janyo wani fakeken gajeren wandonta a drower shi ma ta shafe shi da jan miski. Ta nufi ɗakin Yaya Inu hannunta ɗauke da tiren abinci, dama daga ita sai ɗaurin ƙirji wanda hakan duk yana cikin lecture Hajiya Zanni. Tana shiga ta ajiye masa abincin a gefe sai kuma ta ja ta tsaya a wurin, Yaya Inu ya ɗago fitilarsa ya haske ta yana shirin yi mata magana sai ya ga Indo ta saki zanin jikinta ya faɗi ƙasa. Saboda duk huɗubar da Hajiya Zanni ta yi musu ta haddace ta kanta. Da mamaki Yaya Inu yake bin Indo da ke tsaye tumɓur sai ɗan kanfai, da wata sakakkiyar rigar mama a jikinta wacce suk ta zuge ta saki kamar gugar jan ruwa saboda yawan sakawa. "Ke Indo lafiyarki kuwa?" Yaya Inu tambaya a tsorace. Indo ta ji daɗi har ranta, don ta ji Hajiya Zanni ta ce akwai wani shauƙi da miji yake shiga idan an yi masa haka. Indo ta fara harba ƙafa tana wani juyi ita a dole rawar India za ta yi a gabansa, Yaya Inu zai sake magana Indo ta wurga masa wannan burgujejen gajeren wandon da ta ɗauko, wanda ta jiƙe shi sharkaf da turaren miski da Binta sudan. Gajeren wandon ya sauka a saman fuskar Yaya Inu, ya yi sakatoto yana bin ta da kallon mamaki. Indo ta yi wani tsalle tana harba ƙafa haɗe da fisge rigar maman jikinta, kusan lokaci ɗaya ta kifar da kwanon miyar abincin Yaya Inu. Kuma a daidai lokacin rigar maman ta faɗa saman wuyan Yaya Inu da ya gama kai wa wuya. 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam🌚 [02/02, 15:02] Ameerah Adam🌚: *GIDAN LIKITOCI* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA BAƘAR DAULA AN YA BAIWA CE? ƊAN BA ƘARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA SHAFI NA BIYAR Ko kaɗan Indo ba ta damu da ganin ɓarnar da ta yi masa ba, saboda ta ji Hajiya Zanni ta ce duk cikin sirrikan da ta ba su babu na yarwa indai a ɓangaren mallaka da saye zuciyar miji ne. Don haka ta yi wata girgiza ta cake a wuri ɗaya, ta fara miƙa masa hannu ɗaya irin yadda jaruman india suke yi, idan za su miƙa wa masoyinsu hannu domin su yi rawa. Ta miƙe ƙafa gaba da zummar ta yi tsalle ta dira a gaban Yaya Inu, ta yadda za ta ɗago shi ta manna a jikinta kamar yadda Hajiya Zinni ta kwatanta musu, bisa tsautsayi ƙafarta ta harɗo labulen ɗakin ya faɗo a kanta. Kukan Hannafi ta fara ji sama-sama da alama ya tashi daga bacci, amma sai ta basar ta tunkari Yaya Inu da zuciya ta gama cika shi. Don yadda yake ji ransa ya ɓaci kamar ya tashi ya shaƙe Indo, saboda wannan sabon iskancin da take ƙoƙarin kawo masa. A gabansa ta tsaya tana wani rangaji, iska ta fara kaɗo cikin ɗakin saboda sanyin da ake busawa. Burgujejen gajeren wandonta ya fara kaɗo fuskar Yaya Inu, Indo ta yi masa wani far da idanu ta ƙanƙance murya ta ce. "Taso mu yi rawa lantarkin zuciyata..." Kalaman Indo suka katse sakamakon fisgowar da Yaya Inu ya yi mata, ta faɗi ƙasa daɓas! Gwiwoyinta suka bugu da ƙasa. A tsammanin Indo shauƙin da Hajiya Zanni ta ce maza suna shiga ne ya fara kama Yaya Inu, don haka ta shanye zafin da ta ji ta sake wurƙila idanu da sunan fari tana wani banƙarewa kamar kazar mayu ta ce. "Na jima ina alla-alla kwanakin girkina su dawo, saboda na shayar da kai romon soyayya..." Takaici ya sake lulluɓe Yaya Inu, ya ɗaga hannu ya yi wa Indo mahangurɓa a fuska. Wani irin mummunan yanayi ya ratsa ta, don haka a gigice ta miƙe da niyyar ceton kanta. Yaya Inu ya shatalo ta da ƙafarsa ta faɗa kan miyar kukar da ta zubar. A fusace ya ɗaga hannu ya zabga mata mari cikin fusata ya ce. "Wannan iskancin a gidan uban wa kika koyo shi? Wallahi ko kukar bulukiya ce a kanki sai na sauke miki ita." Indo ta fashe da kuka tana jan jiki gefe ta ce, "Yanzu mai gida duk abin da na yi maka ban birge ka ba, saboda Allah duk wannan kissa da kisisinar..." "Au to, sai yanzu na gano! Wato saken da kika samu na zuwa cikin gari, shi ne kika haɗu da siraran karuwai suka koya miki wannan karuwancin ko? To ba a gidana ba, tun wuri ki watsar da abin da yake kanki idan ba haka ba ki ƙara gaba." Shiru Indo ta yi tana share hawaye. Daga can bakin ƙofa Hansatu da Larai suka ƙaraso suna tambayar abin da ya faru saboda sun ji ihun Indo, Yaya Inu bai tanka musu ba saboda har lokacin haushin Indo yake ji. Ita ma Indo ban da hawaye babu abin da take yi, don haka kowacce ta ƙunshe dariyarta cike da ƙeta suka koma ɗaki. Saboda dama haushin Indo suke ji, a kan shan ƙamshi da kallon wulaƙancin da ta dinga yi musu. A kunyace Indo ta tashi za ta fita Yaya Inu ya ce, "Kuma tun wuri ki gyara mini ɗaki tas, kika ɗebo siraran cinyoyi kamar tsinke ashana. Yo ni akwai wani iya shege da wata figaggiya za ta yi mini?" Takaici ya sake cika Indo, jiki a sanyaye ta ƙarasa ta zare rigar mamanta da ke saƙale a wuyansa. Ta ɗauki zaninta ta ɗaura sannan ta shiga kiciniyar gyaran ɗakin, a cikin ranta ta shiga tsine wa Hajiya Zanni da miyagun shawarwarin da ta ba ta. Washegari Tun kusan kimanin ƙarfe huɗun asuba ya farka yake sharɓa kuka, tun yana yin na zuciya har ya dawo yin na sarari. Sautin sasshekar kukan da Baba Sale yake yi ne ya farkar da Uwale daga baccin da take. Gabanta ne ya yi mummunan faɗuwa, da sauri ta zaro ƙaramar wayarta a ƙarƙashin filo ta haske ɓangaren da Ɗan Bishir yake bacc. Ganin yana bacci cikin kwanciyar hankali ya sa, ta dubi Baba Sale ta ce. "Me yake faruwa mai gida?" A maimakon Baba Sale ya ba ta amsa sai ya sake kallon wurin Ɗan Bishir ya fashe da kuka. Jikinta ne ya yi sanyi don rabonta da ganin kukansa, tun wata rashin lafiya da Ɗan Bishir ya yi kusan shekara ɗaya da rabi kenan. "Mai gida don Allah ka cire ni a cikin duhu, wallahi hankalina duk a tashe yake." Uwale ta furta jikinta yana rawa, don ta ayyana abubuwa da dama a cikin ranta. Baba Sale ne ya faɗa jikinta kamar wani sabon maraya, ya ja majina cikin kuka ya ce. "Kamar kin manta yau ne za a yi wa Ɗan Bishir shayi! Yau ne fa wa'adin kwanakin da za a yi masa kaciya ya cika." Baba Sale ya yi maganar yana share ƙwalla, haɗe da shigewa jikin Uwale kamar wani ƙaramin yaro. Ya ɗago murya a dashe saboda kukan da ya ci ya ce. "Uwale hankalina a tashe yake, wallahi duk wani abu da zai taɓa lafiyar Ɗan Bishir ba na son shi..." Kuka ya sake cin ƙarfinsa, takaici ya mamaye Uwale amma gudun kada su fara raba hali tun da asuba ya sa ta ce. "To ya za a yi, ai dama kowa da haka ya fara. Yanzu dai ka tashi ka je ka yi sallah na ji har an shiga masallaci." A hankali Baba Sale ya fita yana jan majina, ya ɗauro alwala ya wuce masallaci. A lokacin da ya ƙarasa masallaci a raka'ar ƙarshe ake, bayan an idar ya tashi ya ciko raka'a ɗaya sannan ya yi sallama. Baba Sale hannu ya ɗaga ya fara zazzago addu'a, mutane ba su yi tsammani ba sai ji suka yi ya fashe. Sororo mutanen wurin suka yi, Yaya Ado har zai fita ya koma ya zauna. Duka mutane suka yi carko-carko suna kallonsa, Malam Rabe ne ya yi ƙarfin halin zuwa kusa da shi ya ce. "Sale me yake faruwa ne?" Baba Sale ya sharce majina ya fara wata shassheka kamar wanda uwarsa ta mutu ya ce, "Ina buƙatar addu'arku. Domin kowa ya san ɗana ɗaya ne a duniya wato Ɗan Bishir! Kuma ina fatan ya haifa mini jikoki ashirin da huɗu sai dai kash..." Kuka ya sake cin ƙarfinsa. Gaban su Baba Labaran ya faɗi, don duk wanda ya ci karo da irin kukan da Baba Sale yake yi za ka ɗauka mutuwa aka yi masa. Cikin haɗin baki hankali a tashe duka mutanen cikin masallacin suka ce. "Sai dai me?" Baba Sale ya rungumo hannun Yaya Inu ya shiga goge fuskarsa da shi ya ce. "Ku yi mini fatan a yi a gama wa Ɗan Bishir shayi, an jima Bala wanzan zai zo ya yi masa don ni ba zan iya ba. Ba ni da ƙarfin zuciyar ta guntule Ɗan Bishir." Jin haka ya sa takaici ya mamaye su, a zafafe Yaya Inu ya fisge hannunsa ya ce. "Kai dai ka zama gantalalle ɗan wahala. Yanzu shayin da za a yi wa Ɗan Bishir ne kake wannan iskancin, kai Allah Ya tsine iskanci da magoya bayansa. Shi ya sa ka sakar mana murya kamar an kunna generator kana ihu, Allah wadaran naka ya lalace." Daga haka Yaya Inu ya fice daga masallacin rai a ɓace. Ɗaya bayan ɗaya haka mutane suka watse kowa yana mita, Baba Sale ya koma gida ya sake saka Ɗan Bishir a gaba yana lailaya shi kamar zai mayar da shi ciki. Tun da Ɗan Bishir ya tashi daga bacci Baba Sale ya ɗauke shi ya rungume, hatta abinci a baki ya dinga ba shi. Kimanin ƙarfe tara na safe Bala wanzan da yaransa suka ƙarasa ƙofar gidan, Uwale ce ta iya ɗaukar Ɗan Bishir ta miƙa masa. Domin Baba Sale uwar ɗaki ya shige ya haɗa kai da ƙarfen gado yana kuka. Saboda shekara ta uku kenan ana cewa za a yi masa shayi yana ɗagawa saboda soyayyar da yake yi masa. Yana nan zaune Inno ta aika kiransa, da ƙyar ya iya fita ya nufi sashenta fuskarsa ta kumbura saboda kukan da ya sharɓa. 'Yan'uwansa ya gani gabaɗaya a zaune, ya yi mamki matuƙa don haka ya zauna a gefe yana kallonsu. Inno ta dube su ɗaya bayan ɗaya, sai kuma ta saki wani murmushi zuciyarta fes ta ce. "Dalilin da ya sa na tara ku a wurin nan ba komai ba ne, illa na sanar da ku wani abin alheri kuma abin farinciki da ya tunkaro mu. Kuma na tabbata za ku ji daɗinsa, domin cigaba ne da zai iya kai ni aljanna da ku bakiɗaya." Fuskarsu ɗauke da fara'a gabaɗaya suka furta. "Ma Shaa Allah, gaskiya wannan abin farinciki ne Inno. Allah Ya sa mu dace." Inno ta sake washe baki fuskarta wasai kamar gonar auduga ta ce. "Amin Ya Rabbi." "Amma Inno wanne abin farinciki ne haka?" Baba Labaran ya tambaya. Inno ta rangwaɗa kai gefe ta ce, "Dama zan sanar da ku mun gama daidaitawa da Malam, don haka ma na ce zan sanar da ku a ɗaura mana aure ranar Juma'a mai zuwa." Sororo gabaɗaya suka suna kallonta cikin mamaki Baba Ibrahim ya ce. "Inno aure fa kika ce?" Inno ta haɗe rai ta ce, "Eh sunnar Annabi!" Ajiyar zuciya Yaya Inu ya yi ya ce, "Yanzu Inno tuntuni ba ki yi aure ba sai yanzu? Saboda Allah tun da ƙarancin shekarunki bayan da Baffa babba ya rasu ba ki yi ba sai yanzu da girma ya cim miki? Gaskiya Inno ki yi tunani." Inno ta yi wa Yaya Inu kallon sheƙeƙe ta ce, "Ka karanta mini aya ko hadisin da Allah Ya haramta wa tsohuwa aure! Yanzu Inusa sunnar Annabi kake ƙoƙarin daƙilewa?" Yaya Inu ya yi shiru don zuciya ta gama zuwar masa wuya. Saboda dama tun farko jininsa bai haɗu da Malam mai Yasin ba. "Yanzu Inno da za ki ce za ki auri mutumin nan mu da ba mu san asali da tushensa ba, babu wanda muka sani na shi fa. Abu ɗaya ne fa ya haɗa mu da shi taimakon da muka yi masa a airport, sanadin kamen da aka yi masa wanda har yau babu wanda muka sani a cikin danginsa. Gaskiya ko za ki aure shi sai mun san wani daga cikin danginsa." Baba Ibrahim ya yi maganar fuska a haɗe. "Wallahi kai ka ma yarda ta aure shi, na rantse da Allah yadda na tsani ƙyamusasshen tsohon can idan ban sheme shi ba Allah Ya tsine mini!" Yaya Inu ya faɗa jikinsa yana karkarwa. Inno ta yi karaf ta ce. "To wallahi ku shaida duk wanda na ji ko kallon banza ya yi wa Malam sai na ɗaga masa mamunana. Kuma dama na faɗa muku ne saboda na fita haƙƙinku na 'ya'ya atoh, don kada ku ji muna kashewa da binnewa ni da shi a ɗaki ku fara yi mana ɗan zargi. Duk da dai dama na faɗa masa auren ɗauko buta za mu yi." Inno ta sake kallonsu ɗaya bayan ɗaya ta cigaba. "To ku ban da abinku ace yau uwarku ta mutu da aure a kanta ba ya fi daraja a wurinku ba? Allah na tuba duk haƙurin da na yi da ubanku tsawon shekaru bai wadatar ba? Wallahi da shi ne ma ba zai ɗauki shekarun da na ɗauka bai yi aure ba, a toh a yanzu na samu wanda zai ba ni walwala da kulawa gwargwadon farincikina. Da ku ɗaura mini aure da kar ku ɗaura duk ɗaya, saboda yanzu zan tafi wurin Malam Liman ya zama waliyina shi kuma Malam Ladan ya yi wa Malam walicci ashafa mana fatiha." Shiru ta ji sun yi ba tare da sun tanka mata ba, ta kalle su rai a ɓace ta ce duka su fice mata daga ɗaki. Nan take duk suka fice, Baba Ibrahim zai fita ya waigo ya ce. "Idan Allah Ya kai mu zan ɗauki jininki da na Malam ɗin sai na yo muku gwajin da ake yi kafin aure." Haɓa Inno ta riƙe ta ce. "Kai Iro ka fita a idona na rufe, uban me zan yi da wani gwaji ni da zan yi auren ɗauko buta." Baba Ibrahim ya fita don ya lura Inno a fusace take, sai dai ya ci alwashin zai shawo kanta ya yi musu gwajin koda ba za ta haƙura da auren ba. Malam mai Yasin da yake raɓe abayan katanga yana jin duk abin da suke faɗa ya saki murmushi a fili ya ce. "Ashe na kusa ɓarje amarci tun da na tsinci dami a kala. Na ci mai kyau na sha mai kyau, nan gaba kuma na kwashi ganima son raina." Ya ɗaga kansa yana kallon tanƙamemen gidan gandun ya ce. "In Shaa Allahu har wannan gidan sai na mallaka, da ni kuke zancan dan ubanku." Yana jin motsin tafiya ya yi sauri ya faɗa ɗakinsa ya saki labule. Tun da Laraba ta dawo gida ta ci alwashin idan sama da ƙasa ce za ta haɗe ba za ta sake zuwa makaranta ba. Kuma ko da gari ya waye, sai ta yi shirin makaranta kamar wacce za ta je da gaske, amma sai ta nufi cikin gari ta shiga yawace-yawacenta. Ta jima tana tunanin hanyar da za ta ɓullo wa Mai garu da su Malam Sule, a kan cin zarafin da suka yi mata amma har lokacin ba ta samu mafita ba. Sai da ta daidaici lokacin tashi ya yi sannan ta kamo hanya ta fallo da gudu, a bisa tsautsayi za ta tsallaka wata hanya shi kuma wani matashi ya shawo kwana da motarsa ya ɗan make ta. Laraba tana ganin haka ta sake bajewa a ƙasa tana numfarfashi, a gigice matashin ya fito daga motar jikinsa sanye da uniform ɗin NYSC. Laraba ta ƙyallere ido a kaikaice bayan ta hango fitowarsa ta sake runtse ido tana ihu. "Wayyo Allah! Ƙafata da kaina za su ɓalle. Wayyo Allah." Ganin yadda matashin ya gigice ya sa Laraba ta sake narkewa. "I'am very sorry dear!" Ya furta a gigice yana ɗago ƙafar Laraba da ya ga ta dafa ta. Laraba ta yi shiru tana bin zara-zaran dogayen yatsun hannunsa, don dama ba ta fahimci abin da ya ce ba. "Lets go to hospital..." "Wayyooooo jama'a ya karya ni." Furucin Laraba ya sake katse shi. "Ki yi haƙuri please mu je hospital, a ga me ya faru da ke." Kallon da Laraba take wurga masa da dara-daran idanunta ya sa tsoro ya kama shi, a ransa yake raya ko dai aljana ya bige? Yana nan tsugunne ya ji ta bushe da dariya. Ta sake zaro masa ido ta ce. "Kai an gaya maka gadon gidanmu suna zuwa asibiti? Mu za ka nuna wa boko?" Cikin Mahmud ya kaɗa, gabansa yana faɗuwa ya ce. "Ku yi haƙuri me kuke so." Laraba ba ta tanka masa ba, ta nuna masa wata katuwar bishiyar kuka da ke gefe. Ganin haka ya sa shi zaro ido, sai kuma ta nuna masa hanyar fadar Mai gari. Shiru ya yi don bai gane abin da take nufi ba, ta ƙare masa kallo tun daga sama har ƙasa ta ga bai yi kama da ɗan garinsu ko maƙotan garinsu ba ta ce. "Mu gadon gidanmu ba a iya biyansu da kuɗi ko kadara, idan har aka cutar da su. Sai dai a tambaye su abin da suke muradi a yi musu." Bakinsa yana rawa ya ce. "Don Allah faɗi abin da kike so ko mene ne zan yi miki." Laraba ta ja ƙafa da rarrafe ta ce, "Matso kaji don kada aljani Karbu ya ji ka." Yadda Mahmud ya matso da sauri kamar zai faɗo kanta ya sa dariya ta kusa ƙwace mata. Ta maze a ta fara yi masa raɗa a kunne, da sauri ya zaro mata ido. Laraba ta gyaɗa masa kai sannan ta ce. "Wallahi idan ba ka aikata son raina ba sai na saka aljani batoyi ya babbake ka, kuma na sa ya bi har gidan iyayenka ya ƙone su ƙurmus. Sannan ya haɗa maka baƙin sharri a garin nan, gara tun wuri ka tafi zan biyo ka ta cikin iska duk abin da za ka yi ina ganinka. Idan ka faɗa ba daidai ba na hukunta ka ba." Kamar Mahmud zai yi kuka ya nufi hanyar fadar Mai gari da Laraba ta kwatanta masa, su Mai gari tun daga nesa suka fara hango shi don haka suka zuba masa idanu suna kallo. Mahmud yana zuwa ya taka har tsakiyar shimfiɗar Mai gari ya fara bin su da kallo kamar yadda Laraba ta tsara masa, yana yi yana waige don kar ya yi ba daidai ba ta sa a ƙone shi. Gabaɗaya a tsorace suke don sun yi tsammanin soja ne, Sanƙira ne ya yi ƙarfin hali ya ce. "Samari daga ina haka? Wa ya ba ku izinin taka shimfiɗar ranka shi daɗe..." Sanƙira bai gama magana ba, Mahmud ya ɗauke fuskarsa da mari. Saboda tsoro har ji ya yi marin yana yi masa yaji-yaji a fuska. Lokaci ɗaya suka shiga taitayinsu, cikin Mai gari ya shiga kaɗawa gumi yana keto masa. Malam Bukar ya yunƙura zai tashi ya tafi, Mahmud ya buga masa tsawa. "Ni da kuka ganni ba mutum ba ne, na zo muku da wannan surar ne domin ku bil'adama ne. Idan na kwashe ku na tafi da ku a can ne za ku yaba wa aya zaƙinta. An turo ni ne daga hukumar kare haƙƙin aljanu, domin na zo na bi diddigin cin zarafin da aka yi wa 'yar cikinmu wato aljanun da ke jikin Laraba." Mahmud yana gama faɗar haka mutane wurin suka shiga rige-rigen gudu, Mai gari tsalle ya yi ya haye bayan Sanƙira kamar wani ɗan biri. Saboda tashin hankali Sanƙira bai yi wata-wata ba ya damfara Mai gari a ƙasa, ya naɗe babar rigarsa ya take ƙafarsa ya bar wurin a guje. Mai gari yana shirin guduwa, taku ɗaya Mahmud ya yi ya cafko rigarsa. Duk yadda ya so ya ƙwacewa ya kasa, ga shi yawancin mutanen wurin sun gudu sun bar shi. Sai kawai ya taƙarƙare ya fashe da marayan kuka, ta ƙasa kuma gudawa ta ƙwace masa tana zuba. 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam🌚 [02/02, 15:02] Ameerah Adam🌚: *GIDAN LIKITOCI* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA BAƘAR DAULA AN YA BAIWA CE? ƊAN BA ƘARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA SHAFI NA SHIDA Wani irin ƙyanƙyami ne ya kama Mahmud jin yadda Mai gari yake ta sakin gudawa babu ƙaƙƙautawa, ya ɗan waiga bayansa cike da tsoro don su kansu da ace ba a tsorace suke ba, da sai sun fahimci tsoron da yake kwance a saman fuskar Mahmud. Mai gari hawaye da majina da suka gama wanke masa fuska ya dubi Mahmud ya ce. "Da wanne suna zan kira ka ranka shi daɗe, kuma cikin jinsinku ana iya kiranku da wannan sunan? Ka dubi Allah, ka dubi Muhammadur Rasulillahi ka yi mini rai ka yafe mini." Mahmud ya tsuke fuska ya ce. "Kada ka sake yi mini magiya, domin ni ma umarni na karɓa daga sama, a madadin hukumar kare jinsin aljanu ta ƙasa, sun wakilto ni na zo na tafi da kai da taƙadiran mutanenka zuwa fadar majalisar ɗinkin duniya ta aljanu. Amma tun da sun gudu da kai za mu tafi." Jin haka ya sake ɗaga hankalin mai gari sai kawai ya sake fashewa da kuka, don ba shi da wata mafita da ta wuce haka. Sai da ya yi mai isarsa sannan ya shiga yi wa Mahmud magiya, Mahmud ya tuna yadda suka yi da Laraba ya dube shi ya ce. "Za mu yi maka afuwa amma da sharaɗi, sharaɗin kuwa za ka ɗebo zabin gidanka guda huɗu ka yanka su a kan waccan bishiyar." Mahmuda ya nuna masa wata bishiyar tunfafiya, Sanƙira da ke laɓe a bayan katanga ya zaro idanu duk da ba da shi ake ba. Mai gari ya sauke gwauruwar ajiyar zuciya ya ce. "Zabin banza ranka shi daɗe, wallahi ko rago ka ce yanka shi zan yi." Ganin zai yi gaba Mahmud ya ce, "Ba mu gama ba ai, shi wannan jinin da zai sauka a kan bishiyar tunfafiya shi zai goge laifin da ka yi a ofishin shugaban ƙungiyarmu. Saboda ka san haka nan ma aljanu zubar da jini suke yi, gangar jikin kuma ka taho mini da buhu zan kai a kwankwantsa namansu, a madadin naman jikinka da za a yi kwatsa-kwatsa da shi." Mai gari ya shiga gyaɗa kai kamar na ƙadangare. Ya ƙalla wa Sanƙira kira ya ba shi umarnin da ya je gida ya ɗebo zabi guda huɗu. Sanƙira ya yi wuf ya sake ɓuya, don haka aka rasa wanda zai kawo wa Mai gari zabin da zai fanshi kansa sai Sahabi ne ya yi ta maza ya je gidan ya ɗebo. Kamar yadda Mahmud ya ba shi umarni, haka Mai gari ya ƙarasa bakin bishiyar tumfafiyar ya fara yanka zabbin ɗaya bayan ɗaya har ya yanke su duka. Bayan Mahmud ya karɓi zabbin ya cewa Mai gari. "Abu na ƙarshe da zan faɗa maka shi ne, ka kiyaye ɓacin ran Laraba. Wallahi tun wuri ka haɗa mutanen garin nan su nemi yafiyarta." Mahmud ya sake daidaita baƙin gilashin idonsa ya cigaba. "Idan ba haka ba sai mun tsotse romon kanka, kuma daga yau duk abin da kuka ga Laraba ta yi to ba yin kanta ba ne. Duk wanda ya yi gangancin sake taɓa ta zai mutu nan take, ko kuma mu ɗauke shi mu yi ta azabtar da shi." Mahmud ya gama magana ya juya kansa a ƙasa ya cigaba da tafiya, Mai gari yana ganin haka ya fice a guje ya nufi gida ƙafar wandonsa ta yi sharkaf da gudawa. Ga mamakin Mahmud yana zuwa ya tarar Laraba ba ta nan, a tsorace ya ajiye ɗan buhun zabbin ya yi sauri ya faɗa motarsa ya fisge ta da gudu ya bar cikin dajin. Tun da Laraba ta hango shi ya tunkaro ta, take ƙyaƙyata dariya tana da saman bishiyar dalbejiya har Mahmud ya ja motarsa ya yi gaba. Dirowa ta yi ta buɗe buhun tana dariya har da riƙe ciki, sai kuma ta yi shiru tana tunanin yadda za ta yi da zabi har guda huɗu. Mai daban-daban ne ya faɗo mata a rai, wani mai nama da yake can tsallaken ƙauyensu, wanda ya jima da cewa yana sonta. Da sauri ta suri buhun kamar marar gaskiya ta shiga bi ta cikin gonaki ya har ta isa wurinsa. "Larabayyo 'yar Larabatuwa! Yanzu Laraba sai ki dinga guduna, saboda Allah mene ne aibuna?" Mai daban-daban ya furta mata cike da so. Laraba ta maze ta ce, "Mai daban-daban ka san shi so makaho ne, to kwanaki shi ya lulluɓe mini idanu a kan wani mutumi amma yanzu ba ya gabana kai nake so!" Wani irin daɗi ya mamaye shi don haka ya ce. "Kai amma na ji daɗi Laraba, wallahi yau da ƙyar zan iya yin bacci yanzu faɗi duk abin da kike so a wurin nan a yanka miki." Laraba ta yatsina fuska ta ce, "Eh wancan balangun za ta yanko mini ko yanka sha biyar ne, amma kafin nan ga zabin Inno nan ta ce a kawo ka gyara ka gasa mata." Jikin mai daban-daban har karkarwa yake, ya fara yankawa Laraba nama. Ya kalli wani yaronsa ya buga masa tsawa a kan ya karɓi buhun hannun Laraba ya je ya gyara su. Bayan ya miƙa wa Laraba balangun ta ce. "Na gode sosai masoyina mai daban-daban, yanzu waɗannan zabin idan ka gama gasa su ka ajiye da daddare zan zo na karɓa." Mai daban-daban ya amsa mata yana washe baki. Laraba har ta yi gaba ta waiga ta sake jan kunnensa, a kan kada ya aika zabin gidansu za ta dawo ta karɓa da kanta. Mahmud bai yi tafiya mai nisa ba, isa bakin wani babban symbol ɗin sabulun wanka da ke gefen titi. Ya ciro waya ya kira abokinsa Muddasir, wanda suka yi da shi za su haɗu a adaidai wurin da ya kwatanto masa. Bugu biyu wayar ta yi ya ɗauka. Daga can ɓangaren ya ce. "Ga ni nan ina hango ka na kusa ƙarasowa!" Daga haka Muddasir ya katse. Cikin ƙasa da minti ɗaya mai adaidaita sahu ya sauke shi. Sai da Mudassir ya biya shi kuɗinsa ya ƙarasa wurin motar Mahmud ya ce, "Mutumina ashe ka gane kwatancen!" Cike da damuwa Mahmud ya ce, "Allah ka yi mana tsari da ƙauye, yanzu saboda Allah a nan za mu yi service?" Mudassir ya yi murmushi yana zama a sit ɗin gaba ya ce. "Kai kukan daɗi kake yi, da muka samu aka canza mana school zuwa ta garin Gangaren dutse? Da ace an bar mu a garin Rafin gurgu fa? Yanzu ba ga su Haidar can ba suna fama." Mahmud ya saki guntun tsaki ya ce, "Yanzu ina za mu bi mu ƙarasa garin Gangaren dutsen?" Mudassir ya nuna masa hanyar shiga garinsu Laraba, gabansa ne ya faɗi amma sai ya basar don ba ya san ya sanar da Mudassir abin da ya faru da shi ya yi masa dariya. Ganin sun tunkari hanyar garinsu Laraba ya sa Mahmud ya ce, "Wai ina ne garin? Mun kusa zuwa ko da saura. Mudassir ya ce, "Mun kusa zuwa, da ka miƙe za mu bi ta kan doguwar hanyar can har ƙofar gidan mai gari, ka san dole sai mun gabatar da kanmu a wurinsa tun da zama ne ya kawo mu. A hargitse Mahmud ya taka burki cikinsa yana kaɗawa, Mai garin da ya gama sakawa zawo a wando ne za su je wurinsa su gabatar da kanku? "Lafiya Mahmud?" Mahmud da gumi ya gama rufe shi kamar zai yi kuka ya ce. "Wallahi ba lau ba Mudassir." Ya ƙarasa maganar yana yin parking ɗin motar a gefen hanya, sai kawai ya kifa kansa a kan sitiyarin motar. Cike da shauƙi Mai Yasin yake kallon Inno jin amsar da ta ba shi, dangane da sanar da iyalanta a kan maganar aurensu. farinciki fal zuciyarsa ya ce. "Allah mai haɗa jinin mumini da mumini, Allah kaɗai ya san alkairin da yake ɓoye da silar haɗuwarmu a Saudiyya. Haka kawai na ji kin sake kwanta mini Inno, a gaskiya marigayi ya dace da mace." Inno ta saki murmushin jin daɗi kanta a ƙasa, ita dai nutsuwar Malam da daɗaɗan kalamansa waɗand ta rasa a baya suna birge ta. Har a cikin zuciyarta tana jin ina ma tun tana budurwa, Allah Ya aiko mata shi cikin rayuwarta, da babu yadda za a yi ta yi rayuwa da tsohon mijinta da ko kaɗan bai iya soyayya da tarairaiyar mace ba. Mai Yasin ya saci kallonta da gefen ido ya ce. "Innota ko ba kya jin daɗin yabon da nake yi miki? Ko da za ki ji babu daɗi sai dai ki ji, amma Allah Ya sani ƙaunarki ta jima da ɗamfaruwa a cikin zuciyata." Inno ta ɗago ta dube shi ta ce. "Haba Malam, ai duk macen da ta yi dace da kai a matsayi mace ta more a gidan duniya da Lahira." 'An zo wurin, dama nan nake ta jiran mu ƙaraso.' Malam ya raya a cikin ransa, yana murmushi mai ɗauke da manufa a ransa. Ya ƙanƙance murya cikin yaudara da karuwanci ya ce. "Wallahi tun da na wayi gari jikin nan yake son dawo mini Inno, ga bakina salam babu daɗi kamar yawun mage. Nace ko zan samu koda kaza ko naman kasuwa?" Inno ta sauke ajiyar zuciya, tana mamakin yadda Mai Yasin ba ya gajiya da murƙushe cinyoyin kaza, amma da ta tuna a kullum ya ci kazar ya kuma sharɓi romonta ƙara samun lafiya yake sai ta ce. "To Malam ka ga dai yaran nan ɗazu kusan baram-baram muka rabu da su dutse a hannun riga, kuma dama mai ƙoƙarin sayo maka Iro ne. Yanzu dai ban san cikinsu wa zan tunkara ba, tun da kazar jiya ma shi ya taho da ita." Mai Yasin yana gama jin haka sai kawai ya fashe da kuka, ya fara jan magina yana matsar ƙwallah. Sororo Inno ta yi jiki a sanyaye ta ce. "Lafiya malam?" Mai Yasin ya ja majina ya ce, "Kaico rashin haihuwa, kaicona Allah ka cigaba da ba ni dangana. Da 'ya'yan da na haifa ne ai duk tsiya za su kawo mini duk kuwa yadda muka yi da su, yanzu kamar dai garken wannan yaron Inu har sai na tambaye shi idan na yi niyyar ɗiban kaji ko zabi? Amma tun da ban haifa ba dole na yi haƙuri da rayuwa." Shiru Inno ta yi tana nazari don ta san mammaƙo irin na Yaya Inu, amma don ta kawar da damuwar Malam sai ta ce. "Daga yau kada ka sake faɗin yaran nan ba kai ka haife su ba, kai tamkar mahaifinsu ne kuma duk abin da kake muradi, ka yi kanka tsaye ko ka tambaye ni idan kana jin nauyi." Malam ya hau gyaɗa mata kai, Inno ta miƙe tsaye har ta je bakin ƙofa ta juyo ta ce. "Kaji kake so ko zabi?" Malam ya sake narkewa a katifa yana sakin murya a dole shi marar lafiya ya ce, "Idan da so samu ne a samo matasan samarin zakaru masu jini a jika, tun da ai muma a wannan satin ne tariyarmu!" Inno ta saka mayafin ta rufe fuska ta fice tana dariya, tana fita Mai Yasin ya buga tsalle a kan katifa yana rawar oya shake body. Kai tsaye sashen Yaya Inu Inno ta nufa, a lokacin da ta je ba ya nan sai matansa. Cikin girmamawa suka gaishe ta, bayan ta amsa ta ce su buɗe mata garken awaki da shanunsa. Kusan lokaci ɗaya suka kalli juna, Larai ta yi ƙarfin halin faɗin. "Inno amma bai ce za ki zo ɗaukar..." Cikin tsawa Inno ta katse ta. "Dama ban ce miki na faɗa masa ba, Malam ne ya ce mini yana sha'awar matasan samarin zakaru ni kuma na zo zan bincika masa, idan ya zo ki sanar da shi abin da na sanar da ku." Daga haka Inno ta nufi garken ta hankaɗa ƙofar zagayen da ƙafarta. Safare da Dubu 'ya'yan Yaya Inu ne suka taya Inno ɗiban zakarun guda uku ta fice da su, ta yi wa Malam magana da kansa ya fito zuwa bakin rariya ya yanka su. Inno ta ɗora ruwa ta shiga gyaran kaji, sai ga shi babu jimawa ƙamshin farfesun kaji ya cika gidan, ta zuba a babban food flask wanda ta saba zuba wa Malam ta kai masa. Ta ɗebi ɗan madaidaici ta ragewa Laraba a kai, ƙafa da wuya a cikin tukunya. Cikin sauri Yaya Inu yake tafe, hannunsa riƙe da baƙar leda wacce take cike da sababbin magunguna da ya taho da su daga bakin kasuwa. Saurin da yake yi La'asar ta ƙarato, ga shi mai maganin sanyin da ya saya ya sanar da shi ba a wuce ƙarfe huɗu na yamma ba tare da an dafa an sha shi ba, saboda ƙa'idarsa kenan. Shi kuma a ranar yake son yin amfani da shi kuma ba ya fatan lokaci ya ƙure, shawo kwanar da zai yi ne ya ci karo da Hajara tsohuwar matarsa wacce ya ji labarin mijin da take aure ya mutu. Dama tun da ya saki Abu zuciyarsa ta shiga wasu-wasi a kan ya dawo da ita. "Ranki shi daɗe, yau Hajara ce a gari?" Yaya Inu ya faɗa yana washe baki, Hajara ya ɗan yatsina fuska ta ce. "Eh ni ce sai aka yi yaya Inusa?" Yaya Inu ya fara gyara zaman hularsa ta tashi ka fiya naci, ya saka hannu yana gyara wuyan rigarsa yana murmushi ya ce. "Hajarata tun rannan nake ta so na zo mu gaisa, saboda kin san lamarin duniya komai ɗan haƙuri ne. Wallahi na so na zo na yi miki gaisuwa ma amma Allah bai nufa ba, na ce ƙila ma rabona ne ya yi gaba da marigayi." Hajara ta ƙanƙance ido cikin masifa ta ce. "Rabon me? Allah Ya tsare ni da komawa gidanka Inusa, ai ni babbar godiyar da na yi wa Allah da ya sa ban haihu da kai ba. Da zaman yunwa zan ji ko da rashin sutura, kai yanzu ba ka ga yadda na koma ba?" Yaya Inu ya yi shiru yana bin ta da kallo cike da so, don ta yi shar fatarta har ƙyalli take. Dama ya ji labari an ce a gidan tsohon mijinta ta haɓɓaka uwar gida. "Ai yanzu wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa na wuce ajinka wallahi Inusa, su dai waɗancan wahalallun matan naka sai su yi ta zama kafin layin saki ya biyo ta kansu." Tana gama maganar ta yi gaba, ran Yaya Inu ya ɓaci ga rashin samun haɗin kanta da na baƙaƙen maganganun da ta faɗa masa. Ya bi ta da sauri ya ce. "Banza 'yar wahala an faɗa miki ba zan samu wacce ta fi ki ba, ki zuba ki gani nan da kwanaki kaɗan zan ɓarzo wacce ta fi ki komai." Hajara ba ta kula shi ba ta yi gaba, shi ma Yaya Inu ya ƙarasa gida rai a ɓace. Tun daga bakin ƙofa ya fara yin ball da kwanika saboda yadda yake a fusace. Hakan ya sa su Larai suka sake shiga taitayinsu, yadda ya ga sun yi tsuru-tsuru ne ya sa ya fahimci abin da ya faru. "Lafiya kuka yi wani zumu-zumu da idanu kamar an shaƙe zakaru?" Indo da har lokacin haushinsa take ji, saboda abin da ya yi mata dariya ta kusa ƙwace mata amma sai ta danne ta ce. "Zakaru kam ai ba shaƙa kaɗai suka sha ba, karo suka yi da wuƙa yanzu ma sun wuce birnin tumbi." Yaya Inu ya haɗe fuska ya ce, "Abokin wasanki na zama Indo?" Indo ta fara tafiya irinta ta kai kajiyo, sannan ta sanar da shi abin da Inno ta yi. Jikinsa ne ya shiga karkarwa saboda duk duniya babu abin da yake saurin ɗaga hankalinsa irin a taɓa garkensa. Da sauri ya nufi sashen Inno ya same ta a ɗaki ya ce, "Inno na ji wani zance a kan garkena." Jin haka ya sa Mai Yasin da ya ke zaune a ɗakin Inno ya tauna wani ƙashi wanda ya ja hankali Yaya Inu, wani ƙululun baƙinciki ya tokare maƙoshinsa, ya haɗiyi yawu mai ɗaci yana sauraron Inno. "Ubanku ne yake marmarin matasan samarin zakaru, shi ne na lalubo 'yan matsakaita uku na yanka masa." Yaya Inu ya fara huci ya ce, "Amma Inno ko za ki ɗiba ai sai ki sanar da ni." Mai Yasin ya yi farat ya ce, "Kai Inusa kana neman albarka kuwa? Saboda mahaifiyarka ta ɗebi zakaru uku ka zo za ka yi mana tijara, kai yaro ka shiga hankalinka ka nemi albarkar uwa." Haushi ya sa yaya Inu ya tunkari Malam yana jin kamar ya murɗe masa wuya, da sauri Inno ta sha gabansa ta ce. "Ni ka dake ni Inusa ka ji! Ka dake ji na ce." Shiru Yaya Inu ya yi saboda yadda zuciya ta ciyo shi, sai kawai ya fice daga ɗakin. Malam ya jima yana zuga Inno ai kuwa ta cika ta yi fam, daga haka ya koma ɗakinsa ya zura doguwar riga ya tafi banɗaki zai yi wanka. Yaya Inu yana daga harabar gidansa ya hango shi, ganin Malam ya shiga wanka ya sa shi faɗawa ɗakinsa da sauri ya ɗauko wani ƙullin yajinsa, ya zura wata doguwar dorina a aljihu ya nufi banɗakin da Malam ya shiga. Sai da ya laɓe ya ji malam ya saɓa sabulu a fuska sannan ya banka banɗakin ya watsa masa yaji a fuska, Malam yana shirin yin magana saboda yadda ya ji an banko ƙofar banɗakin ya ji an zuba masa abu a fuska. Da sauri ya buɗe ido zafin sabulu da na yaji ya haɗe masa a ido lokaci ɗaya, cikin zafin zuciya Yaya Inu ya shiga zabga masa dorina ta ko ina. 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam🌚 [02/02, 15:02] Ameerah Adam🌚: *GIDAN LIKITOCI* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA BAƘAR DAULA AN YA BAIWA CE? ƊAN BA ƘARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page ɗin, ya taimaka ya yi mana Subscribe a youtube channel ɗinmu.👆🏻👆🏻👆🏻 SHAFI NA BAKWAI Tun da mahaifiyarsa ta kawo shi duniya bai taɓa jin azaba irin wacce yake ji ba, a tsammaninsa aljanu ne suke yi masa wannan izayar don haka Malam ya shiga karanto duk wata addu'a da ta zo bakinsa. Ban da kuka babu abin da yake yi, a zuciye Yaya Inu ya ce masa. "Wallahi koda wasa idan ka sake cewa za ka ci kaza ko zakaru a gidan nan, sai na yi maka abin da ya fi haka. Munafikin Allah dama ba ka san haushinka nake ji ba, ubanmu ya kwanta dama sama da shekara ashirin Inno ba ta taɓa marmarin aure ba sai a kanka. In sake jin ka saka ta, ta taɓa awakina wallahi sai na lahira ya fi ka jin daɗi." Daga haka Yaya Inu ya fice daga banɗakin kai tsaye ya wuce ɗakinsa ya sauya kayan jikinsa. Kai tsaye garken awakinsa ya shiga, wani sabon takaici ya mamaye masa zuciya musamman da ya tuna danƙwala-danƙwalan zakarun da Inno ta saka aka yanka. Tun da ya fara magana cikin gargaɗi Malam ya fahimci Yaya Inu ne, sai da ya ji ya fita daga ɓanɗakin ya yi ƙoƙarin buɗe idonsa ya ji wata azaba ta ratsa shi. Ruwa ya laluba ya shiga kwarawa, ai kuwa ya ji kamar yana zuba wa jikinsa ruwan zafi saboda raɗaɗin da yake ratsa shi. Malam bai wata-wara ba ya fito a guje yana ihu da neman taimako haɗe da faɗin. "Jama'a taimako, wani marar imanin zai hallaka ni. Jama'a ba kwa ji na ne ku kawo mini ɗauki." Ihun da Malam yake yi ne ya ja hankulan mutane yara da manya, sai dai manyan da sun yi arba da shi suke komawa a guje. Labaran da Rahina ne suka shigo ba tare da sun san abin da ya faru ba, Rahina da Malam suka yi gware tana yin arba da shi ta kurma ihu suka shige sashensu ita da Labaran a guje. Ɓaɓatun da Malam yake yi ne ya sa Inno ta fito a tsorace ta ce. "Malam lafiya kuwa?" Turus Inno ta yi ta zuba hannuwa a ƙirji cikin tashin hankali, shi kuma Malam jin muryar Inno ya sa ya tunkare ta da gudu yana faɗin. "Inno ki taimaka mini idanuwana za su makance, Innota jikina azaba yake yi mini kamar ana babbake ni." Inno ta zuba kabbara ta fita da gudu tana faɗin. "Malam ka yi mini aikin gafara wannan aikin ba nawa ba ne." Malam Ya rufa mata baya har sashenta yana faɗin. "Inno a gidan nan ke kaɗai ce kike ƙaunata, ki taimaka mini ki ce iyalina ta gobe." Inno ta banka ɗaki da yake sashenta shiru yake babu kowa, sai hakan ya sake ɗaga hankalinta ga Malam ya biyo ta a gigice. Ta danna sakatar ɗakin ta ce, "Ka gafarce ni wannan aikin na maza 'yan uwanka ne." Duk bugun da Malam ya yi Inno ba ta buɗe masa ba. Ana cikin haka Baba Ado ya shiga ya same shi, ko kaɗan bai ji daɗi ba domin tun a ƙofar gida aka fara ba shi labari. Towel ya miƙa masa murya a daƙile ya ce. "Ka suturce jikinka." A fusace Malam ya yi warci towel ɗin ya yi wurgi da shi ya ce, "Suturar banza da wofi, kai idan za ka taimaka mini ka ba matsa daga gabana, domin ni kaɗai na san bala'in da nake ciki." Tsaki Yaya Ado ya yi ya ce, "Wallahi idan ba ka ɗaura towel ɗin nan ba, zan tafi na bar ka. Darajar tsufanka na gani shi ya sa na zo taimaka maka, idan ba haka ba wallahi da sai dai ka yi ta zama a haka." Sanin halin nunkufurcin Yaya Ado ya sa da sauri ya fara lalubar towel ɗin ya ɗauka ya ɗaura a ƙugunsa, kamar ƙaramin yaro haka ya zaunar da shi ya shiga wanke masa fuska da ruwa da sabuli. Zafin ciwukan da dorinar ta ji masa ya sa ya dinga ihu kamar yaro ƙarami, a haka har Yaya Ado ya gama wanke masa sai dai har lokacin wani irin raɗaɗi yake ji. Har ɗaki Yaya Ado ya raka shi ya haye katifa yana rawar ɗari, nan take zazzaɓi ya rufe shi. Tun lokacin da Bala wanzan ya gama yi wa Ɗan Bishir kaciya ya shiga kiran layin Baba Sale, sai da ya yi ta maza ya ɗauka a nan yake sanar da shi an gana yi masa kaciyar. Jiki a sanyaye ya fita ƙofar gida, yana yin ido huɗu da Ɗan Bishir ya ji wasu zafafan hawaye sun zubo masa. Da ƙyar ya miƙa hannu ya karɓe shi, har zai shiga gida abokinsa Sani wanzan ya zo wucewa. Ya kalli Baba Saleh sai kawai ya tuntsire da wata irin dariya, wacce shi kaɗai ya san manufar yin ta. Haka kawai gaban Baba Sale ya faɗi, amma sai kawai maze ya wurga masa harara ya shige gida. Ɗan Bushir ban da yage baki yana kuka babu abin da yake yi. Yana zuwa ya kwantar da shi a kan gado, ya sa gefen rigarsa ya share hawayen ya ce. "Ɗan Bishiririna! Ɗan Bishiri ka yi haƙuri ban kyauta maka ba ko? Yanzu me kake so na sayo maka?" Ɗan Bishir ya kalli gabas da yamma, ya kalli mahaifiyarsa da ke gefe a zaune kalli mahaifinsa. Sai ya sake ɓarke baki ya saki kuka. Ƙirjin Baba Sale ya buga da ƙarfi ya jikinsa yana rawa, ya rungume Ɗan Bishir ya dubi Uwale fuska shaɓe-shaɓe ya ce. "Uwale tsoro nake ji, wallahi ina cikin tashin hankali." Uwale ta sauke ajiyar zuciya, saboda ta san za a yi haka ko ma fiye da haka. "Me ya faru mai gida?" Baba Sale ya ja gefen ɗan kwalinta ya share hawaye ya ce. "Ina tsoron ko dai an guntule Ɗan Bishir gabaɗaya, Uwale kada fa Bala wanzan ya nakashe mini ɗan ɗaya-ɗayana..." Kuka ya ci ƙarfinsa. "Yanzu mai gida duk yaran da ka dinga yi wa shayi, iyayensu ba su ce za ka nakasa musu 'ya'ya ba sai da abin ya zo kanka? Kamar ba ka san yadda Bala yake da ƙware a harkar wanzanci ba? Kar ka manta shi fa ɗan gado ne." A hassale Baba Sale ya ce. "Kowa ai nasa ya sani, ni gudan jinina kuma magajina na sani don haka a kansa zan yi magana..." Ita ma Uwale ta katse shi. "To ai ɗa na kowa ne, shi ya sa ɗa da dukiya ba a yi musu mugunta. Kuma hausawa suka ka ƙi naka duniya ta so shi, ka kuma so naka duniya ta ƙi shi. Wallahi wannan zazzafar soyayyar da kake yi wa Ɗan Bishir ba za ta kai ka ba. Don ba zan ɓoye maka ba a cikin gidan kowa haushinsa yake ji, ko kaɗan ba shi da farin jini a wurin yara da manya." Wani irin kallo ya shiga wurga mata, yana jin a ransa yadda ta caɓa wa Ɗan Bishir baƙaƙen maganganu da ace ba a yi masa kaciya ba, babu abin da zai hana bai kora ta gidansu ba. To don dai ya san idan ta tafi babu mai jinyarsa. "Baaabaaaa!" Ɗan Bishir ya furta a shagwaɓe, da sauri Baba Sale ya amsa masa sai ya ce. "Zan ci abincin Rahina, daɗi gare shi. Ni ba zan ci komai ba sai abinci ko shayinta." Zumbur Baba Sale ya miƙe ya ce, "Ai kuwa yanzu zan karɓo maka, zauna Ɗan Bishiririna ga ni nan zuwa." Ya ƙarasa maganar yana zuwa bakin ƙofa, ya waigo yana jifan Uwale da harara ya ce. "Shi Ɗan Bishir dai ya zama kabewar kan kabari baƙincikin mai taushe, duk wani mahassadi sai dai ya gan shi ya ƙyale." Daga haka ya fice daga ɗakin. Kai tsaye sashen Labaran ya wuce, daga bakin ƙofa ya tsaya yana sallama. A lokacin Rahina ta tsakar gida a zaune tana shan iska, Labaran yana wanka a ta bayan kitchen ɗinsu don ya ce kafin ya samu kuɗin da zai rufa musu banɗakin sashensu, a nan za su dinga wanka saboda abin da ya faru da Rahina. "Wa alaikassalam." Rahina ta amsa sallamar tana yunƙurin miƙewa domin ta saka hijabinta, daga can gefe ta ji Labaran ya ce. "Kada ki sake ki ƙara magana." Shiru ta yi saboda ta san zafin kishinsa, shi kuma Baba Sale jin an amsa ya saki murya ya ce. "Amarya mai daɗin tuwo da miya, angon na ki yana ciki?" Wannan yabon da Labaran ya ji ana yi wa Rahina ya sake ɓata ransa, don haka ya zura gajeren wandonsa ko kunfar jinsa bai wanke ba ya fita fururu ƙofar gida. "Lafiya Labaran me yake faruwa?" Baba Sale ya furta fuska ɗauke da mamaki. Labaran ya yarfe kumfar fuskarsa ya ce, "Ita ta kawo haka! Ka san dai abin da ka aikata haramci ne ko? Ka zo ƙofar gida ka zage muryarka kana magana iyalina tana sauraronka, ba ka tsammanin ta ji muryarka ta yi mata daɗi?" Ran Baba Sale ne ya ɓaci, amma da ya tuna Ɗan Bishir ya zo nemarwa abinci sai ya wayance. "Labaran kenan, yanzu dai duk ba wannan ba. Wallahi Ɗan Bishir ne yake son cin abincin Rahina, saboda zaƙin girkinta kasan na daban ne." Tun Baba Sale bai gama magana ba Labaran ya hau huci, rai a ɓace ya ce. "Allah Ya isa, wallahi ba zan yafe maka ba, da wannan yabon. Yanzu saboda Allah abincin Rahina ne wani zindiƙin sankacecen ƙato yake yabawa haka?" Zuciya ta fara ciwo Baba Sale ya ce, "Kai Labaran kada ka faɗa mini maganar banza da wofi, ban da aska da tasha jinin Ɗan Bishir ka isa na tako wurinka neman abinci ne? Ka faɗa mini ko nawa ne zan biya ka, ka sayar mini abincin nata." Labaran ya buga tsalle kamar mai shirin tashi sama, saboda yadda kishi ya tirniƙe shi ya ce. "Ba askar kaciya ba Allah Ya sa abba-tuwa ce a kansa, wallahi ba zai ci abincin Rahina ba. Yanzu ni kake kallo ka ce na sayar maka da abincin Rahina? Ko kasan sayar maka da abincin nan daidai yake da na sayar maka da wani tsagi na daga baiwar da Allah ya ba ta?" Haush ya sake mamaye Baba Sale sai kawai ya zuciya zai faɗa gidan, da sauri Labaran ya suri wani ƙaton itace. Ganin haka ya sa Baba Sale ya fice, shi kuma ya rufa masa baya yana faɗin. "Jama'a ku tare ga baƙin kwarto mai lasisi nan." Baba Sale yana faɗawa cikin gida ya danno ƙofar ya saka sakata, Labaran ya yi bugun duniya bai buɗe masa ba. Ganin yadda Mahmud ya yi zuru yana nazari ya sa Mudassir ya taɓo shi ya ce. "Wai me yake faruwa ne?" Mahmud ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Wallahi Mudassir na haɗu da wani iftila'i a cikin wannan ƙauyen, ina cikin damuwa kuwa matuƙar Mai gari ya gano ni." Mudassir ya bi shi da kallon mamaki don a iya saninsa da Mahmud, wannan ne zuwansa garin na farko, saboda har yana kan hanya shi ya dinga yi masa kwatance. A tsorace Mahmud ya kwashe duk abin da ya faru tsakaninsa da Laraba ya ba shi labari, tun bai rufe baki ba Mudassir ya dinga sheƙa masa dariyar ƙeta. Haushi ne ya kama shi, ya dube shi rai a ɓace ya ce. "Ka ma mayar da ni ɗan iska wato ga mahaukaci ko?" Cikin dariya Mudassir ya girgiza masa kai ya ce, "Wallahi a garin wannan tsoron naka watarana sai ka halaka kanka. Yanzu kai Mahmud aljanu ne za su kai ka su baro? An ma kuwa aljanar gaske ce? Ace aljanu su nemi ya yanka musu zabi su tafi da su? Gaskiya akwai ayar tambaya." Jiki a sanyaye Mahmud ya ce. "Wallahi a wannan dajin ba na jin za a samu bil'adama a cikinsa, kai ganin idona na fahimci ba mutum ba ce. Yanzu tun da ka ce dole mu gabatar da kanmu wurin mai gari sai dai ka wakilce mu." "Kai ka san yadda mutanen ƙauye suka ɗauki mai gari kuwa? Ai dole sai mun haɗu mun gabatar da kanmu ya san da zamanmu a garinsa, wallahi yadda ka ci ubansa shi ma haka zai ci na ka idan ya gano ka." Mudassir ya furta yana gimtse dariyarsa. Wata dabara ce ta faɗo wa Mahmud ya saki murmushi a fili ya ce. "Mu je gidan da ka ce za mu sauka, na san yadda zan yi da su." Mudassir ya shiga kwatanta masa hanyar, suka sauya akalar hanyar zuwa wani ɗan madaidaicin gida mai ɗaki biyu wanda babu kowa a cikinsa. Mudassir ne ya ɗauko mukulli ya buɗe musu ƙofar suka shiga da kayansu, a kan wani ɗan ƙanƙanin gas da Mahmud ya taho musu da shi suka ɗora ruwan wanka. Sai da suka yi wanka suka sha ruwan tea da Mudassir ya dafa musu, sannan ya ce su shirya zuwa wurin mai gari. Mahmud shadda ya saka fara ƙal, ya ɗauko hula ya saka. Sai kuma ya saka face mask a fuskarsa idonsa yana sanye da glass. Mudassir kuwa ya saka ƙananan kaya sun yi kyau sosai, duk hanyar da suka bi sai abi su da kallo ana ganin 'yan birni sun shigo garin. Lokacin da suka ƙarasa ƙofar gidan mai gari shiru suka ji shi kamar babu mutane, a ƙofar gidan suka tsaya duk da Mahmud ya rufe fuskarsa amma gabansa faɗuwa yake kada Mai gari ya gano shi. "Salamu alaikum!" Mudassir ya yi sallama yana zura kai soron mai gari. Shiru suka ji ba a amsa ba, da yake ɗakin Mai gari a soro yake yana jin duk abin da suke faɗa. "Na yi mamaki da na ji ba a amsa sallamar ba, ɗazu fa da na zo a kan idona ya shiga gida." Mahmud ya furta a hankali, shi kuma Mai gari jin haka ya sa cikinsa ya sake kaɗawa, don ya yi tunanin hukumar kare haƙƙin aljanun ce ta sake turo wakilanta. Yana daga cikin ɗakinsa gumi ya shiga keto masa, wani ɗan matsakaicin matashi da ya zo wucewa ganin su Mahmud a tsaye ya ce. "Wai Mai gari kuke nema?" Mudassir ya gyaɗa masa kai, don yaron ya yi musu magana da biyu ne saboda ya birge abokansa da ke can labe suna kallonsu. Ko babu komai dai ya san ya yi wa 'yan birni magana. "Idan kuka yi magana bai amsa ba, yana nan cikin ɗakinsa ku ƙwanƙwasa masa." Yaron ya furta yana niyyar wucewa, Mudassir ya ce masa. "Don Allah zo ka shiga ka yi mana sallama da shi, ka ce baƙi ne suka zo akwai muhimmiyar maganar da suke son tattaunawa da shi." Gaban Mai gari ya sake faɗuwa, nan take jikinsa ya shiga karkarwa. Jin furucin saurayin da kuma baƙin da suke ƙofar gidan, ya sa shi sake firgicewa musamman da ya kallo ƙauren ɗakinsa ya karye ba shi da damar rufewa duk abin da zai faru sai dai ya faru da shi. Doguwar rigar shaddar jikinsa ya cire, ya zame dogon wandonsa daga shi sai gajeren wando. Don haka ya wala ƙafafuwa ya saita bakin ƙofa, cikin shirin ko-ta-kwama. Don ya ci alwashin sai dai ya fice a guje amma ba zai zaune hukumar kare haƙƙin aljanun ta sake hukunta shi. Musamman da ya san idan suka ritsa shi a ɗakin babu mai ƙwatarsa sai Allah.. Cikin murna yaron ya shiga soron gidan Mai gari yana sallama, ya ƙarasa bakin ƙofar ɗakin zai yi magana sai ji ya yi Mai gari ya fito a guje ya baje shi a ƙasa. Ya tattakura ya fita da gudu, a daidai lokacin, yaron ya fasa ihu saboda zafin buguwar da ya yi. Su kuma su Mudassir ganin yanayin da Mai gari ya fita a guje su ma sai suka rufa masa baya suna gudu, don a tsammaninsu wani abin ne ya koro shi daga cikin gidan. Saboda yadda Mahmud ya fi tsorata shi ne yake biye da Mai gari, hularsa da glass ɗinsa sai da suka yi kusa tsalle uku sannan suka faɗi a ƙasa. Abin da ya sake ɗaga hankalin mai gari, yadda ya ga duk waigen da ya yi sai ya ga su Mahmud suna biyo shi a baya. Don haka ya tattakura ya ce. "Jama'a ku kawo mini ɗauki, hukumar kare haƙƙin wancan jinsin za su halake ni." A madadin a samu wasu su fahimci maganar Mai gari, sai dai duk majalisar da suka wuce su ma sai su rufa musu baya saboda tun da suke ba su taɓa ganin Mai gari da gajeren wando yana gudu ba. Sai da Inno ta bari jikin Malam ya sarara masa da zafi, sannan ta sake aikawa ɗaya bayan ɗaya ta kira iyalanta. Tun da suka shiga ɗakin suka fahimci ran Inno ya gama ɓaci, Malam kallo ɗaya ya yi wa Yaya Inu ya ji gabansa ya faɗi, don haka ya sauke kansa ƙasa. "Gabaɗaya na tara ku ne domin na yi muku godiya a kan cin mutumcin da kuka yi mini. Ba malam kuka wulaƙanta ba, ni kuka wulaƙanta. Idan har saboda na ce za mu yi aure da Malam ne kuka yi haka mu zuba ni da ku, a yau ba sai gobe ba zan yi wa Malam Liman magana bayan sallar Magriba a ɗaura mana aure." Gabaɗaya shiru suka yi Baba Ibrahim ya ya ce, "Har ga Allah Inno ni ban san abin da ya faru ba, hasali ma ba na gidan a lokacin da abin ya faru." "Dama ni ban ce kai ba ne Iro, jikina yana ba ni Inusa ne saboda na yanka zakarunsa na dafawa malam." Malam da ya tuna gargaɗin Yaya Inu ya yi sauri ya ce, "A'a Inno ba na jin Inu zai aikata mini haka." Inno ta sake ba wa Malam haƙuri, ta kuma ba su umarnin da su ba shi haƙuri tare da biyan kuɗin sadaki dubu hamsin. Babu yadda suka iya haka suka ba shi haƙuri sannan suka fice. Suna fita Inno ta aika aka kira mata Malam Liman, bayan sun gaisa ta kawo kuɗi ta damƙa masa na sadaki. Ta yi masa bayanin duk abin da ya faru, Malam Liman ya yi mata Allah sanya alheri sannan ya tafi. Bayan sallar Magriba kuma aka ɗaura auren Inno da Mai Yasin a kan sadaki naira dubu hamsin. Lokaci ɗaya gari ya ɗauka a kan maganar auren Inno, baƙinciki ya mamaye su Baba Ibrahim. "Magana ta gaskiya hankalina bai kwanta da wannan mutumin ba, na ɗauka maganar auren nan za ta kwana biyu har na yi musu gwajin jini saboda muhimmancinsa. Gaskiya duk kun jagula al'amarin nan." Baba Ibrahim ya furta cike da takaici. "Uwar me gwajin zai yi ne da ka addabe mu da zan can nasara, da tun can da ake yin aure babu gwajin me ya faru da mutanen baya? Ko shi Baffa lokacin da zai auri Inno an yi musu gwajin ne? Kai ni ba wannan ne agabana ba, fargabata kada tsohon nan ya sake gangancin taɓo garkena." Yaya Inu ya faɗa. Baba Ado ya tuntsire da dariyar ƙeta ya ce, "To garkenka kuma ai sai dai kar a kuma, ba ka ji labarin Inno ta sa an fita da matashin ragonka ba? Ɗazu nan fa aka wuce musu da shi wai Ali mai tsire ne ya gasa musu..." Tun bai gama magana ba Yaya Inu ya shaƙo wuyansa jikinsa yana rawa ya ce. "In ji uban wa?" Baba Ado ya zame hannunsa yana ci gaba da ƙyaƙyata dariya, jikin Yaya Inu ne ya sake sanyi don ya san Ado da miskilanci idan ka ga dariyarsa to wata ƙetar ya samu. Bai iya tankawa 'yan'uwansa ba ya faɗa cikin gidan da sauri, kai tsaye ɗakin Malam ya nufa don a can yake jin muryarsu sama-sama. Kamar wanda aka jefe haka ya faɗa ɗakin, Yaya Inu ya yi turus ganin wani shimfiɗeɗen gasasshen nama a gaban su Inno suna reɗa da wuƙa. Ta ci sabuwar atamfa sai murmushi take, Malam da bai san naman ragon Baba Inu suke ci ba, ya sake yanko wata shimfiɗeɗiyar tsoka cikin gadara ya tura a baki. Yaya Inu da ya rasa mafita sai kawai ya zauna a bakin ƙofar ya fashe da kuka, Sai a lokacin Inno ta lura da shi. Ta washe baki ta ce, "Kai Ɗan Inuna, a duniya me za ka yi wa kuka tun da kana faranta ran iyaye. Wai dama haka ragon nan ya kiwatu, ni fa lokacin da ka ce mini an taya shi dubu hamsin na yi mamaki. Ashe-ashe rabon mu sharɓi ganimarsa a daren tariya ta da babanku ne." 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam🌚 [02/02, 15:02] Ameerah Adam🌚: *GIDAN LIKITOCI* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA BAƘAR DAULA AN YA BAIWA CE? ƊAN BA ƘARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page ɗin, ya taimaka ya yi mana Subscribe a youtube channel ɗinmu.👆🏻👆🏻👆🏻 SHAFI NA TAKWAS Duk maganar da Inno take yi babu ɗaya da Baba Inu yake ganewa, saboda wata irin juwa da ya ji tana ɗibansa. Hankali a tashe Mai Yasin ya furzar da naman bakinsa, gabansa yana bugawa ya dubi Inno ya ce. "Inno kina nufin wannan ragon da aka gaso mana muke ci ragon Inusa ne?" Cike da son birgewa Inno ta saki murmushi ta ce, "Ragon Inusa ne, ai sau biyar ana taya shi yana ƙin sayar da shi, mutumin ƙarshe da ya zo ko sati uku ba a yi ba dubu saba'in ya taya shi." Inno ta kalli wurin Yaya Inu da har lokacin kuka yake yi kamar wanda mahaifiyarsa ta mutu, ta kalli Mai Yasin da ya gama firgicewa ta ce. "Na jima ban ci gashin nama da ya yi daɗi kamar wannan ba, ai wallahi Inusa Allah ne kaɗai zai biya shi saboda ko lokacin da na sa aka fita da ragon ba ya gidan..." Kukan da Mai Yasin ya saki ne ya katse furucin da Inno take yi, hankali a tashe ta dube shi haɗe da faɗin. "Malam lafiya kuwa?" Mai Yasin ya girgiza mata kai cikin kuka ya ce, "Babu komai Inno, kawai ina taya Inusa jimamin rashin ragon da ya yi. Gaskiya Inno ba ki kyauta masa ba, me ya sa ba ki nemi jin ta bakinsa ba kafin a yanka." Mai Yasin yana gama faɗar haka ya sake ɓarkewa da kuka. Sororo Inno ta yi jin abin da ya faɗa, saboda yadda ta san shi da son nama ba ta taɓa tsammanin zai faɗi haka ba. "Malam ai saboda wancan karon na ga ya ji haushin zakarun da aka yanka masa shi ya sa na ɗauki rago, yanzu da a zo duk bayan kwana biyu muna yanka zakaru ba gara mu yi mai gabaɗaya ba." Mai Yasin yana haɗa ido da Yaya Inu ya ga ya yi masa wani mugun kallo, mai ɗauke da manufar za mu haɗu da kai, sai kawai ya cusa kansa cikin cinyoyi kamar ƙaramin yaro ya sake ɓarkewa da kuka. Shiru Inno ta yi ta rasa bakin magana, kukan Yaya Inu da na Mai Yasin ya cika ɗakin. Jiki a sanyaye Yaya Inu ya miƙe yana dafa bango, don ji ya yi wata hajijiya tana yunƙurin taɗe masa ƙafarsa. A daddafe ya fice daga sashen su Inno ya wuce sashensa, su Baba Ibrahim suna wurin da ya bar su amma saboda halin da ya shiga ya sa har ya wuce bai tanka musu ba. Zazzafan zazzaɓi ne ya rufe shi don haka ya shige ɗakinsa ya ja bargo ya rufa, domin kusan a ƙasa da shekara goma sha biyar wannan ce asara mafi muni da ya tafka. Bayan Yaya Inu ya wuce sashensa, Baba Ibrahim ne ya shiga sashen Inno ya yi sallama daga tsakar gida, Inno ce kawai ta amsa masa ya yi gyaran murya sannan ya ce. "Inno dama wata 'yar magana gare ni idan babu damuwa." Daga can ɓangaren Inno ta ce, "Na taso ko za ka shigo ciki?" Baba Ibrahim ya ji daɗi yadda ya ji muryar Inno wasai, don haka yake fatan Allah Ya sa ta ba shi haɗin kai a game da buƙatar da zai je musu da ita. Ya matsa bakin ƙofar sannan ya ce. "A'a zan shigo ma, da yake maganar da ku duka za mu tattauna." Sai da Inno ta amsa masa sannan ya shiga cikin ɗakin ya zauna daga gefe, ganin har lokacin Mai Yasin bai daina kuka ba ya sa mamaki ya kama Baba Ibrahim don haka ya ce. "Inno lafiya? Me ya samu Malam?" Inno ta ɗan canza fuska ta ce. "Wai fa don ya ji na ce ragon Inusa na saka aka gasa mana, shi ne yake taya shi kukan jimami!" Baba Ibrahim ya yi ƙuri yana kallon Malam, saboda haka kawai ya ji bai yarda da hujjar yin kukansa ba. "Inno magana ta gaskiya ba a kyauta wa Yaya Inu ba, ina laifin ma ki sa a ɗebi kaji amma a ce rago guda ai kuma ya yi muku yawa." Baba Ibrahim ya furta, don ya san fiye da jinya ma ɗan'uwan nasa yana iya yi saboda soyayyarsa da abin duniya. "Mu ajiye wannan zancen a gefe Iro, yanzu me yake tafe da kai." Baba Ibrahim ya yi jim sannan ya ce. "AlhamduLillah! Haƙiƙa ina godiya ga Allah (S W.A) da Ya sa haɗuwarmu da kai Malam da zamo mana alheri. Tun da aka ce harka ta auratayya ta shiga tsakani, to kuwa ta wuce komai. Amma wani hanzari gare ni ba gudu ba Inno da kuma Malam!" Baba Ibrahim ya ɗago ya ɗan dube su sannan ya cigaba da cewa. "Dama maganar gwajin jinin da na yi rannan ita ce na zo zan sake maimaitawa. Don Allah ina son ka fahimce ni Malam, ba ina son a yi wannan gwajin don wata manufa ta ko saboda ba mu yarda da kai ba ne. A'a ina son a yi muku wannan gwajin ne saboda a tantance lafiyarka da ita Inno, saboda kada a cutar da ɗaya daga cikinku ko kuma gudun samun wata matsalar da ba ma fata a nan gaba." Tun da Baba Ibrahim ya fara magana Mai Yasin ya haɗe rai, Inno ta dube shi sheƙeƙe ta ce. "Kai Iro fita daga idona na rufe, yadda yahudanci ya ratsa ka so kake ni ma ka ribace ni ko? Wallahi tun ranar da na ji kana yi wa Inusa faɗa, a kan yawan haihuwa na fara zargin ka karɓo kwangilar yahudawa. Kai Iro ka ji tsoron Allah, yanzu lokacin da na auri ubanka akwai wani tsirfar gwajin jini kafin aure ne? Ni za ka haramtawa sunnar Annabi ina zaune ƙalau?" Baba Ibrahim ya sauke ajiyar zuciya cikin damuwa, don dama ya san za a rina an saci zanin mahaukaciya. Shi kuwa Malam zuciyarsa fes, duk da ya san lafiyarsa ƙalau amma shi kansa bai yarda da sabuwar al'adar da ta shigo ta gwajin jini kafin aure ba. "Wallahi Inno ba ni da wata alaƙa da Yahudawa kamar yadda kuke zargi, shi wannan gwajin jinin yana bayyana rukunin jinin da kika ɗauke da shi. Gwari-gwari bari na yi miki bayani, nau'in rukunin lafiyar jini na gado shi ake kira da Genotype. To kamar yadda muka sani Inno kowanne ɗan'adanm da Allah Ya hallita, yana tare da wasu ƙwayoyin halitta da suke gudana a jikinsa, kuma waɗannan ƙwayoyin halittar gadonsu ake yi. Misali idan iyaye suna da nau'in jini mai kyau sai su haifi yara lafiyayyu, idan kuma aka samu akasin haka sai a haifi yara masu ɗauke da matsalar amosanin jini wacce aka fi sani da sikila. Bayan wannan gwajin akwai kuma wanda yake bayyana cututtuka da dama kamar: Ciwon hanta, hawan jini, cutar damuwa (Depression) sai uwa-uba cutar ƙanjamau (HIV/AIDS) da ragowar cututtukan da ban lissafa ba. A gwaje-gwajen da ake yi kafin aure akwai cutukan da idan aka same su, ake haƙura da auren. Akwai kuma wanda ake yin auren sai a bayar da shawarwari." Baba Ibrahim ya faɗa cikin tattausan lafazi. "Innalillahi wa 'inna'ilahi raji'un! Yanzu Iro ni ko Malam a cikinmu wa kake yi wa fatan ƙanjamu? Mu za ka mayar 'yan iska, masu yawon kwararo? Idan na ce kana ƙoƙarin raba sunnar Annabi ka ce ba haka ba. Yanzu tun da ubanku ya rasu akwai ƙaton da ya sake taɓa mini hannu? Ta shi ka fice mini tun raina bai ɓaci ba." Inno ta faɗa a zafafe tana nuna masa hanyar fita. "Don Allah Inno ki fahimce ni, ba ina nufin zarginku nake yi ba. Ita cuta mai karya garkuwar jiki, ai ba sai an sadu tsakanin mace da namiji ake samunta ba, ana iya ɗaukarta ta hanyoyi da dama kamar amfani da reza ɗaya, burushin wanke baki, kibiya wacce mata suke kitso, kilifa ta masu aski, askar wanzamai, wuƙa, abin yankan farce, allura ta asibiti da allurar ɗinki. Duk ana iya ɗauka da su matuƙar dai jinin mai ɗauke ita zai taɓa abubuwan da na lissafa, wanda ba shi da ita idan ya yi amfani da su to tabbas zai iya kamuwa shi ma. Inno hanyoyin suna da dama fa, kuma gwajin jini na genotype yana bayyana rukunin jinin da ya dace su haɗu wurin aure da waɗanda ba su dace ba. Kin ga mai rukunin jinin AS ba zai yiwu ya auri mai irin nasa na AS ba, haka zalika mai jinin SS ba zai auri mai SS ko mai AS ba saboda gudun kada su haifi yaran da za su zo da lalurar sikila, su yaran su wahala haka su ma iyayen su wahala wurin ɗawainiya." Kallon da Inna take jifansa da shi ya sa ya tsahirta sannan ya ce, "Inno na ga kamar ba ki gama fahimtar bayanina ba. Ana sanin genotype idan anyi gwajin jini, kuma daga gwajin ake samun genotypes a jikin mutane cikin nau'i guda uku kamar haka: AA, AS da SS. AA sune masu cikakkiyar ƙwayar halitta, AS kuma su ake cewa carrier, akwai ɗan rauni a cikin ƙwayar halittarsu, sai kuma na ukun sune SS masu ɗauke da amosanin jini wato sikila. Saboda raunin ita wannan ƙwayar halittar ya kai maƙura. Shi ya sa muke yawan jan hankulan mutane, da su tabbatar da sun yi gwaji jini tun kafin soyayya ta yi ƙarfi. Muke kuma hankaltar da muhimman abubauwan da ya kamata a lura kafin aure, idan an duba genotype din sune kamar haka: Rukunin farko yana nufin mijin, ba biyun kuma yana nufin matar, sakamakon kuwa irin yayan da za a samu ne. 1. AA +AA = AA, AA, AA, AA (Za a samar da 'ya'ya masu cikakkiyar lafiya.) 2. AA + AS = AA, AS, AA, AS, (Shi ma aure ne mai kyau, kuma babu matsala a lafiyar 'ya'yan da za a haifa, amma bai kai na saman ba.) 3. AA + SS = AS, AS, AS, AS, (Shi ma wannan auren ana iya yin sa, duk da akwai 'yar matsala kaɗan a kan 'ya'yan da za a haifa. Za su zama AS ne duka, ma'ana carriers) 4. AS + AS = AA, AS, AS, SS, (Akwai matsala, domin za a samu ɗa ko 'ya mai cutar sikila) 5. AS + SS = AS, SS, SS, SS (Akwai matsala sosai domin kusan kaso tamanin 80% na 'ya'ya za su zama masu cutar sikila) 6. SS + SS = SS, SS, SS, SS, (Akwai matsala mai muni, domin dukkan 'ya'yan da iyayen sikila ne, za su ƙare cikin tsanani da wahalar rashin lafiya..." A zafafe Mai Yasin ya katse shi, "Kai Iro ka kiyaye ni, kai yanzu mu za ka zaunar kana nusar da mu gaibu? Waye masanin gobe idan ba Ubangiji ba? Yanzu zurfin da ka yi a yahudancin har ya kai ka fara ja da hukuncin Ubangiji, kana yi masa shisshigi a kan halitar bayinsa? Wane ne kai ban da gajiyayye wanda fushin Allah kaɗai zai iya tarwatsawa, wallahi ka dawo cikin hayyacinka, don ba abin mamaki ba ne yanzu Ubangiji ya mayar da kai ragon sallah. Sakarai dube ka a ido kamar mutumin kirki, amma dai kai an yi zindiƙin bayahuɗe." Inno da takaici ya gama cika ta, ta nuna masa hanya rai a ɓace ra ce. "Fice mini daga ɗaki Iro! "Don Allah Inno..." "Na ce ka fita ko!" Ta katse shi a zafafe. "Shashasha, kai ni dai kam ban san ƙaddarar da ta saka na yarje maka ka yi karatun nasara ba tun asali, idan abin da ka faɗa haka ne me ya sa ku duk ban haife ku a nakashe ba?" Inno ta faɗa cike da masifa, babu yadda ya iya haka Baba Ibrahim ya fita jiki a sanyaye don ba haka ya so ba. Ko kaɗan auren Inno da Malam bai ɗaɗa Laraba da ƙasa ba, saboda mutuminta ne tun zuwansa gidan yake faran-faran da ita. A cewarsa 'ya'ya da jikiokin Inno tamkar nasa haka ya ɗauke su, dalili kenan da ya sa ya sake mamaye zuciyar Inno tun bai furta mata kalmar so ba. Laraba ganin Inno ta tafi ɗakin Mai Yasin ya sa ta yi zaraf ta ɗauki hijabinta ta nufi wurin mai daban-daban, a lokacin da ta je ya gama gashe mata zabin sun yi jar suya gwanin birgewa. Laraba ta basar kamar gaske ta ce masa. "Mai daban-daban Inno ta ce na tambaye ka, nawa ne kuɗin aikin naman sai a biya ka." Mai daban-daban ya washe baki cikin jin daɗin ganin Laraba tana sakar masa fuska ya ce. "Haba Laraba, yanzu saboda ni na fi kowa rashin kara sai na karɓi kuɗin Inno don na yi mata aikin zabi, ai a kanki Laraba babu abin da ba zan iya sadaukar miki ba." Laraba ta fakaice shi ta ɗan taɓe fuska sannan ta ce. "Ashe haka kake sona ban sani ba Mai daban-daban?" Mai daban-daban ya miƙa mata ledar da ya zuba zabin a ciki ya ce, "Tun farko dama ai ke ce kika ƙi ba ni haɗin kai Laraba, amma bakina ai ba zai iya furta irin soyayyar da nake yi miki ba." Laraba ta yi masa murmushi sannan ta tafi gida, sai dai fargaba ce fal a ranta tana tunanin me za ta ce wa Inno, idan ta tambaye ta a inda ta samo nama mai yawa haka. Tun da ta doshi kwanar layinsu ta ga wani matashin saurayi yana biye da ita, ita mamaki ma abin ya ba ta don idan aka cire Mai daban-daban babu namijin da ya taɓa cewa yana sonta, saboda duka mutanen garin kallon marar hankali suke yi mata. "Yan mata, don Allah ki tsaya ina da magana da ke." Matashin ya furta yana shan gabanta, Laraba ta ɗan haɗe fuska kamar ba ta fahimci me yake son faɗa mata ba ta ce. "Malam lafiya kuwa?" Sai da ya gyara gaban rigarsa ya saki murmushi sannan ya ce. "Tun ɗazu da kika wuce na ji kin kwanta mini a zuciyata, to na ga bai da ce na tsayar da ke a can ba shi ya sa na biyo ki zan ga gidanku." Laraba ta ɗan maƙale murya ta ce, "To gaskiya ni dai ina da masoya da yawa, amma ka san dai an ce mace allurar cikin ruwa ce. Kuma yanzu aike na aka yi, sai dai idan na kai aiken ka tsaya na fito." A fili ta lura da yadda matashin ya ɗan tsora ta jin ta ce tana da masoya, amma da ya ga ta ba shi dama sai ya sauke ajiyar zuciya. Laraba zuciyarta ƙal, don ita ma so take ta gwada yadda ta ga su Bushira yayyanta da suke uba ɗaya suke yi kafin su yi aure ko ta ji abin da ake ji. A ƙofar gida matashin ya tsaya Laraba tana shiga cikin gida ta zura da gudu ta nufi sashen Inno, har a ranta tana fargabar kada ya gudu kafin ta shiga ta fito. A uwar ɗakin ta ajiye ledar ta sake zurowa da gudu ta koma, sai da ta je soro sannan ta tsaya ta ɗan daidaita nutsuwarta tana mayar da numfashi. "Ɗan samari na dawo!" Laraba ta furta tana wani kanne ido. Martanin murmushi ya mayar mata ya ce, "Barkanki da dawowa sarauniyata, ni dai sunana Habu kuma ba a ƙauyen nan nake ba. Na zo ne daga maƙotan garin nan, ban sani ba ko kin san gidan Malam Lado mai itace?" Laraba ta yi murmushi ta ce. "Wallahi na gane shi, sam-sam ba shi da mutumci. Sau ɗaya na taɓa tsinkar masa mangwaro ya kai ƙarata har gaban mai gari, kawai dai na raga masa ne saboda na ga ƙafa ɗaya gare shi." Habu ya saka hanu ya rufe bakinsa ya ce, "Yayan mahaifina ne fa!" Cikin halin ko'in kula Laraba ta ce, "Ita gaskiya ai dama ɗaci gare ta." Shiru ya yi yana tsoron kada ya sake wata maganar ta ce ta fasa son shi, don ya lura kamar ba ta rufa-rufa. Don haka ya basar ya ce. "Na tambayi sunanki an ce sunanki Laraba, amma Laraba ai ba sunan ainahi ba ne." Laraba ta yi fuskar tausayi ta ce, "Sunana Aminatu, sunan mahaifiyata na ci kasan tana haihuwata ta mutu. Ana kirana da Laraba ne saboda ranar Laraba aka haife ni, ga kuma sunan Innata da na ci." Cike da tausayawa ya yi wa mahaifiyarta addu'a, sannan suka ci gaba da hira duk da mafi yawan hirar da Laraba take yi masa shirme da shirirta ne, amma haka kawai ya ji tana birge shi. Tun da ya shawo kwanar layin hasken fitilar motarsa ta haske su Laraba da ke tsaye a ƙofar gida, suna hira ita da Habu tana ta sheƙa dariya. Ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, cike da ɓacin rai ya ja dogon tsaki har sai da matarsa Nabila da ke gefe ta kalle shi ta ce. "Baby lafiya?" Kamar ba zai tanka mata ba, sai kuma ya furzar da iska mai zafi ya ce. "Nothing!" Shiru suka yi har suka ƙarasa ƙofar gidan, sai da ya fita ya buɗe gate ya koma cikin motar ya shiga da ita cikin harabar gidan, sannan ya yi hanyar fita a zafafe. Saboda ya lura koda Laraba ta gan shi babu wani tsoro ko shakku a tattare da ita. "Baby ina za ka je kuma?" Nabila ta furta, don ta lura da sauyinsa. "Get inside, i am coming back righ now." Bai jira cewarta ba ya fice. Shiru ta yi tana nazari, haka kawai ta ji ƙirjinta ya buga da wani tunani ya faɗo mata. Cikin sauri ta ce. "No! It can't be happen!" Ta buɗe motar ta ɗauko lapcoat ɗinta da jaka ta rataya sannan ta shige sashensu. "Shiga gida!" Dr Fadil ya furta wa Laraba a tsawace, ta wani kwaɓe fuska ganin zai yarfa ta a gaban saurayi ta ce, "Zance fa nake yi Ya Fadil." Ɗan zaro ido waje ya yi jin abin da Laraba ta faɗa masa babu ko shakku. "Idan na sake magana ranki zai ɓaci." Laraba ta fara hawaye rai a ɓace ta ce, "Wallahi Ya Fadil ka fiye shiga haƙƙina, kai lokacin da kake soyewarka wa ye ya hana..." Marin da ya sauke mata ne ya sa ta katse ragowar kalamanta, gefen bakinta ya fashe ganin irin ƙasƙancin da ya yi mata ya sa ta fashe da kuka tana faɗawa cikin gida da gudu. "Haba Malam wannan wane irin abu ne haka? Mene ne aibu a maganganun da ta yi da za ka mare ta..." A fusace Dr Fadil ya ɗauke Habu da mari, ya nuna shi da yatse cike da masifa ya ce. "Dama ku ne irin 'yan iskan samarin da suke hurewa ƙananan yara kunne ko? Idan na sake ganinka a ƙofar gidan nan, sai na karairayaka na watsar a ƙasa." Daga haka Fadil ya shige gida ya bar Habu riƙe da kunci, ƙwafa ya yi ya ja ƙafafuwansa ya bar ƙofar gidan, a ransa yana jin idan sama da ƙasa za ta haɗe ba zai daina zuwa wurinta ba saboda soyayyarta ta yi masa mummunan kamu. A harabar gidan Laraba ta yi zaman 'yan bori ta fasa ihu, kamar wacce ake ƙwaƙwalewa idanu. Mutane suka shiga fitowa daga ɓangare-ɓangare ciki har da su Inno, takaici ne ya cika Fadil ya yi tsaye ya harɗe hannuwa a ƙirji yana kallonta. "Ke Laraba lafiya kike ihu da daren nan kamar wacce ta taka 'ya'yan shaiɗanu?" Inno ta faɗa a ruɗe. Laraba ta sharce majina da ɗan kwalinta fuska shaɓe-shaɓe da hawaye ta ce. "Ba Ya Fadil ba ne ya koro ni ina zance da saurayina, haka kawai ya dinga falla mini mari duk ya zubar mini da aji a gabansa." Inno ta yi kicin-kicin ta haɗe rai ta ce. "Kai Boka ka fita idona na rufe, Larabar ce ba ta isa zance ko mene ne nufinka? Ina ce saba'ar watannan ta cika shekara goma sha biyar? Ga Lantan nan sa'arta ce haihuwa biyu za ta yi a ɗakin miji." "Wallahi idan na sake ganin Laraba a ƙofar guda sai na ci mutumcinta, dama duk iskancin da yarinyar nan take yi ke ce kike ɗaure mata Inno. Ni da ita za mu ga mai taurin kai." Dr Fadil ya furta a zafafe yana barin wurin, a daidai lokacin Nabila ta ƙarasa tana jin abin da yake faruwa. Inno tana shirin yin magana suka ji wani sabon kukan daga ƙofar shigowa. Salame 'yar gidan Larai ce ta ƙarasa cikin kuka, kowannesu fuska ɗauke da mamaki suka wurga mata tambaya. "Lafiya Salame?" Sai da ta share hawaye sannan ta ce, "Jamilu ne ya sake ni." Kusan lokaci ɗaya suka ɗauki salati, cikin kumfar baki Yaya Inu ya ce. "Uban me kika yi masa da zai sake ki a daren nan ga tsohon ciki a jikinki." Salame ta ja majina ta ce, "Saboda ya sayo shayi ruwan bunu da awara zai sha, ni kuma na ji sha'awarsu na ɗauki ƙwaya biyu da shayin na sha. Shi ne kawai ya sake ni." Ta ƙarasa maganar cikin kuka, takaici ya mamaye mutanen da suke tsaye. Yaya Inu a ƙufule ya ce. "Shayin banza da wofi da har zai sake ki a kansa, wannan ai rashin hankali ne. Bai ga halin da kike ciki ba ne?" Larai da ke tsaye ta saki murmushin takaici ta ce. "Dama gwano ai ba ya taɓa jin warin jikinsa, yanzu mai gida har kana da bakin magana don an sako maka 'yarka, kuma a kan dalilin da bai taka kara ya karya ba? Ai na sha faɗa maka, wannan auri sakin da kake yi ba zai haifar mana da samun ɗa mai ido ba, domin kai ma uba ne kuma duk abin da ka yi wa 'yar wani sai an yi wa ta ka. Idan ba ka manta ba fa, Raliya a kan ƙosai ka sake ta. Mariya kuma a kan man shanu, ga Abu kuma a kan kai yara almajiranci. Ni ma da kake zaune da ni saboda na zama kujera ce, duk tarkacen yaran da ake tafiya a bar maka ni nake riƙe su. Ka ga yanzu kai ma kana da zaurawa uku kenan a gida, wannan kaɗai ya isa ya zame maka izina..." A fusace ya katse ta. "Larai ni za ki yi wa rashin mutumci a gaban mutane?" Baba Ibrahim ya ce, "A duk maganganun Larai babu cin mutumci, sai zallar gaskiyar da har yau ka gagara gane ta Yaya Inu, ya kamata ka dawo cikin hayyacinka. Aure-auren da kake yi ya yi yawa wallahi, yanzu ko wuƙa aka saka mini ba zan iya lissafa adadin mata nawa ka aura ba. Ka gyara zamantakewarka da iyalinka, sai ka ga Allah Ya daidaita lamuranka. Duk da dama aure da mutuwa yana wurinsa, amma ka sani akwai jarabtar da Allah yake yi wa bawa a kan abin da yake aikatawa." Mai Yasin da ke gefe ya zuba wa Salame da kuka idanu yana lashe baki, saboda fara ce tas kamar Yaya Inu sai dai 'yar ƙibar mahaifiyarta da ta ɗauko. 'Yanzu wannan danƙwaleliyar aka saki, ai kuwa wannan mijin nata an yi sakarai.' Malam ya furta a cikin ransa. "To tsohon munafuki, ai babu kuɗin kowa a cikin auren da nake yi, kuma babu ƙaton da yake ciyar mini da su idan sun dawo gida. Ke shige gida muje." Yaya Inu ya ƙarasa maganar yana tasa ƙeyar Salame shi ma ya shige ciki, daga haka kowa ya watse. CIKIN DARE Tun da Mai Yasin ya ci karo da Salame ya kasa zaune ya kasa tsaye, haka kawai ya ji wani abu yana fisgarsa a kanta. Duk da tana yanayin kama da Laraba amma ta fi Labara zama cikakkiyar mace 'yar duma-duma kamar yadda yake muradi, Inno da ke gefensa ta miƙe za ta yi masa sallama ta ce. "To Malam ni zan wuce ɗaki ko akwai abin da kake buƙata a yanzu?" Wani munin Inno ya gani saboda yadda Salame ta mamaye zuciyarsa, haushinta ya kama shi don haka ya ɗan yi tsaki a hankali ya ce. "Babu komai za ki iya tafiya!" Inno ta yi mamakin yanayin furucin da ya yi mata, ganin haka ya sa Mai Yasin ya wayance da cewa. "Raina ne duk a ɓace wallahi, a ce ka saki mace da tsohon ciki wannan ai hauka ne." A fili Inno ta saki ajiyar zuciya cikin jin daɗi, don yadda Mai Yasin yake nuna wa zuri'arta kulawa abin yana burge ta. "Lamarin babu daɗi dai sam malam, ni bari na wuce sai da safe." Mai Yasin ya amsa mata yana alla-alla ta fice, shi kaɗai ya dinga zarya a ɗaki yana tunanin yadda zai ɓullowa halin da yake ciki. Wata dabara ce ta faɗo masa ya saki murmushi mai sauti, kamar wanda aka yi wa dole haka Mai Yasin ya zauna tunkur har ƙarfe biyun dare ta cika. Daga shi sai gajeren wando ya zare sakatar ƙofa ya nufi sashen Yaya Inu, wannan ne zuwansa na farko sashen don haka cikin sanɗa ya kama gajeriyar katangar ya dira. Sakatar ƙofar ya zare ya bar ƙofar a buɗe saboda koda rana ta ƙwace masa ba zai sha wahalar guduwa ba. Da yake da ɗan hasken farin wata, cikin sanɗa ya dinga bin ɗakuna yana leƙe, sai dai idan ya zura kai ba ya iya hango komai ta ciki. A haka har ya nufi ɗakin da Yaya Inu yake kwance ya shiga, domin jikinsa ya ba shi a nan Salame take a kwance. Tun dag bakin ƙofa Mai Yasin ya kwanta ya fara jan jiki a hankali, don kada a ji motsinsa a haka har ya haye kan katifar da Yaya Inu yake kwance. Cikin bacci Yaya Inu ya ji ana shafa masa jiki, da ɗan magagin bacci ya ce. "Hansatu ce!" Jin muryar Yaya Inu ya sa ƙirjin Mai Yasin ya buga da ƙarfi, amma don kar ya yi saurin gano shi sai ya ce. "Ummm." Tsaki Yaya Inu ya yi ya ce, "Ke dai kin cika jabara Hansatu, don masifa na ce miki zazzaɓi ne a jikina amma saboda ƙalata sai kin zo kin tsotse ragowar ruwan jikina." Mai Yasin ya yi shiru ya cigaba da kai hannun yana laluben Yaya Inu, shiru Yaya Inu ya yi yana mamakin yadda Hansatu ta iya irin waɗannan abubuwan don bai taɓa jin haka daga gare ta ba. Don haka sai abin ya birge shi duk da yana jin zazzaɓin jikinsa, ya shiga mayarwa da Mai Yasin martani yana faɗin. "Ke dai Hansatu wannan jarabar Allah Ya yaye miki, duk halin da mutum yake ciki ba za ki..." Maganar Yaya Inu ta maƙale, ƙirjinsa ya buga da ƙarfi jin ya shafo gashin baki da gemu buzu-buzu, sai kuma ya kai hannu ya shafo kai ya ji wayam babu gashi sai ma wani sulɓi da ya ji kan yana yi kamar bayan sulba. Mai Yasin kusan mutuwar tsaye ya yi, Yaya Inu ya yi kukan kura ya ce. "Ƙundun uba, jama'a kwarto a ɗakina zai haike mini." A yi mini afuwa da rashin update kwana biyu, na shiga rububi amma yanzu na dawo free. 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam [02/02, 15:02] Ameerah Adam🌚: *GIDAN LIKITOCI* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA BAƘAR DAULA AN YA BAIWA CE? ƊAN BA ƘARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page ɗin, ya taimaka ya yi mana Subscribe a youtube channel ɗinmu.👆🏻👆🏻👆🏻 SHAFI NA TARA A madadin Mai Yasin ya saki Yaya Inu ya yi ta kansa, sai ma ya sake ƙanƙame shi ta baya ya maƙale murya cikin ƙarfin hali ya ce. "Haba Mai gida me kake son mayar da ni?" Sororo Yaya Inu ya yi jin abin da Mai Yasin ya faɗa, sai ya fara zargin ko dai shi ne bai shafo daidai ba, ko kuma hannuwansa ne suke yi masa gizo. Don haka ya sake lalubo Mai Yasin ya ji ƙasunbarsa ta masa ƙabe-ƙabe, ya shafa gefen cinyarsa ya ji gajeren wando. A zafafe cikin zafin nama, ya kai masa naushi a fuska yana faɗin, "Mai gidan ubanka, ɗan iskan kwarto. Jama'a a kawo ɗauki." Ganin da gaske asirin Mai Yasin yana shirin tonuwa, ya sa shi fita a guje; shi ma Yaya Inu ya rufa masa baya. Sai da suka je tsakar gida Yaya Inu ya fisgo gajeren wandon Mai yasin, saboda babu riga a jikinsa idan ba haka ya yi ba zai iya kama shi har ya cim masa ba. Ganin dumu-dumu ya shiga hannu sai Mai Yasin ya zage iya ƙarfinsa ya barke wandon ya rabe biyu, ya fita a guje saboda tashin hankali a tsammaninsa sashen Inno ya nufa. Ba tare da ya ankara ba, ya haye katangar sashen Labaran ya dira. Cikin ɗakin ya faɗa a guje jikinsa har karkarwa yake yi, yana jin sa a kan katifa ya ja bargo ya rufa gumi yana keto masa. Labaran ne ya fito daga zagayen wurin da suke tsugunno, sai da ya ajiye butar a ƙofar ɗaki sannan ya shiga ya buɗe randa ya sha ruwa, ya ƙarasa gefen gadon Rahinatu. Murmushi ya saki a fili ganin mutum ya gangaro wurin kwanciyarsa, a tsammaninsa Rahinatu ce. Cike da shauƙin soyayya ya furta. "Rahinatuwa kenan! Bari na gyara ki da kaina, don kada na katse miki bacci mai daɗi." Ya ƙarasa maganar cikin tattausan lafazi mai haɗe da soyayya, sannan ya saka hannu ya gyara hannun Mai Yasin da gumi ya gama wanke shi, ya yi mamaki sosai da ya ji hannun kamar ba na Rahina ba saboda ita mace ce mai ƙiba sosai. Da yake ɗakin babu haske sai ya bar abin a ransa ya raɓa ta gefe ya kwanta, sauke hannunsa da zai yi a gefen Rahinatu ya ji ana karkarwa ga gumi ya jiƙe shi. Ƙirjinsa ne ya buga da ƙarfi, a sanyaye ya ce. "Rahinatu lafiya kuwa? Me yake damunki na ji kamar kina rawar ɗari " Daga can gaban Mai Yasin, Rahina ta ɗago tana ɗan yanutsa fuska ta ce, "Baby lafiya kake magana da tsohon daren nan?" Da sauri Labaran ya zaro ido waje, saboda Mai Yasin a tsakiyarsu yake. Labaran shiru ya yi ya sake saɗaɗa hannu ta cikin bargo ya shafo ƙafar Mai Yasin ya ji, don ya tabbatar da ba aljani ne ya jawo masa hari ba. Saboda a fitar da ya yi fitsari a tsammaninsa indai ba aljani ba, babu wanda zai shigo masa ba tare da ya ji ƙarar buɗe ƙofa. Ƙafar Mai yasin ya shafo ya ji 'yan yatsu irin na shi saɓanin kofato da ya yi tsammani, sai ya kai hannu ya shafo kansa. Mai Yasin ya maƙale murya ya ce, "Masoyi kada ka yarda da ita ni ce ainihin matarka." Ware ido Rahinatu ta yi don sai a lokacin ta lura da mutum a kusa da ita, jin furucin Mai Yasin ya sa Labaran ya shafo ƙasunbarsa, ya lalubo ƙirjinsa sai ya ji shi wayam. "Kai la'ananne sai na kashe ka, garsamemen ƙato a gefen Rahinatuna! weeeeeeeeee huuuuuuu." Labaran ya furta a haukace haɗe da yin gurnanin da ya razana Mai Yasin, hakan ya sa ya bankaɗe bargo ya fita da gudu Labaran ya rufa masa baya. Cikin shammata Mai Yasin ya juyo ya yi masa mahangurɓa a fuska, cikin tsananin jin azaba ya zube a wurin. Rahinatu ta fito tana ihu da kururuwa, a haka Mai Yasin ya samu ya cire sakata ya fice. Ya fita kenan Yaya Inu ya sako kai cikin sashen Labaran, ya shiga wuri-wuri hannunsa ɗauke da barandami da kokara. A haukace Labaran ya fisge daga hannun Rahinatu ya cakumi wuyan Yaya Inu yana faɗin, "Wallahi yau ko ni ko kai a gidan nan, tun da ka nemi gwada mini kwartanci." Yana faɗin haka ya kai wa Yaya Inu naushi a baki, jin zafin haka ya sa Yaya Inu ya watsar da kokarar hannunsa ya falla wa Labaran mari, nan take suka shiga kiciniya Rahinatu ban da ihu babu abin da take yi. Kafin wani lokaci tuni iyalan Yaya Inu sun cika sashen Labaran, da ƙyar aka raba su kowannensu yana mayar da numfashi. "Kai Labaran idan ka bari na riƙe ka wallahi sai na sumar da kai, shashasha wanda bai san ciwon kansa ba." Yaya Inu ya yi furucin yana buga tsalle, kamar zai ƙwace daga hannun su Bashar. Labaran ya ji wani takaici ya lulluɓe shi, don gani yake Yaya Inu ya gama cin tuwo a kansa, saboda maganar da yake yi masa kamar an dake shi ne kuma aka hana shi kuka. Ya zabura a hassale ya ce. "Ka dai yi asara Inusa, ka ajiye riɗa-riɗan mata amma kana bibiyar matan wasu, wallahi idan gabaɗaya mutanen garin nan gatanka ne, sai na ɗauki haƙƙin iyalina da ka shiga har cikin turakar sunna kake ƙoƙarin aikata fasadi." Shiru kowa ya yi, cike da mamaki Hansatu ta ce. "Kai Labaran kana nufin bayan sashenmu kai ma an shigo maka? Yanzu fa ihun Mai gida ne ya taso mu." Yaya Inu ya ɗago gajeren wandon Mai Yasin ya ce, "Wannan shi ne abin da na samu daga jikin kwarton, kuma wallahi sai na kai wa Mai gobe da nisa ya saka shi a bala'in da bai taɓa zato ba." Sai a lokacin jikin Labaran ya yi sanyi, kunyar yayansa ta kama shi, suna shirin watsewa suka jiyo ihun Inno a ɓangarenta. Kamar haɗin baki lokaci ɗaya suka bi sashenta sai dai ƙofar a rufe suka same ta, Yaya Inu ne ya kama katangar ya dire sannan ya buɗe wa ragowar ƙofa. A tsaye suka samu Inno butar hannunta ta tuntsire a bakin ƙofa ruwan cikinta ya zube, Inno tana ganin su Yaya Inu ta riƙe su jiki yana rawa ta ce. "Inusa wani ya shigo gidan nan, don yanzu haka na fita fitsari na ga giftawarsa da gudu. Babban tashin hankalin ma, gamo na yi domin zir ɗinsa haka yake ko bante babu." Ba su saurari jin ta bakin Inno ba suka fita da gudu suna haske-haske, Mai Yasin ya yi tsumu-tsumu a ɗaki yana saka kayansa, ya yi lakur a kan katifa yana mayar da numfashi. Sai da suka yi binciken duniya amma ba su gan shi ba, suna cikin haka Mai Yasin ya fito yana tambayarsu kamar bai san abin da ya faruba. Labaran ne ya yi masa bayani, bayan ya gama Yaya Inu ya ce. "Ai na yi mai wuyar tun da na samu tufafinsa, zan sa Mai gobe da nisa ya yi mini aiki mai zafi a kansa. Dama abin da yake buƙata takalmi ko wani abu da aka samu daga jikin ɓarawo ko kwarto, wallahi daga wannan karon ba zai sake haurewa gidan wani ba." Jin haka ya sa cikin Mai Yasin ya kaɗa, wani zazzafan gumi ya yanko masa. Ya ƙarasa gaban Yaya Inu ya riƙo hannunsa da ke karkarwa ya ce, "A'a Inusa ka bar mini komai a hannuna, ka san dai kamar yadda na faɗa muku zafin aikina ne ya sa ake kira na da Mai Yasin. To ni zan..." Kallon da Yaya Inu ya shiga wurga masa ne ya sa shi katse kalamansa, don yadda ya ga yana kallonsa har sai da ya sa shi tsarguwa. "Ka bar mini komai a hannuna, ni na san irin shige da ficen da nake yi a wurin malamai, don haka zan ji da shi." Jiki a sanyaye kamar zakaran da ya shuri wuƙa, Mai Yasin ya ja jiki gefe. Yaya Inu ya fice yana muzurai, babu jimawa kowa ya watse. Ganin duk irin gudun da Mai gari yake fallawa su Mahmud ba su daina bin sa ba, ya sa shi ɓarkewa da kuka yana gudu yana waigensu. Ba shi ya tsaya ba sai da ya ƙarasa tukubar tsiren Mai daban-daban, yana shiga rumfar a guje ya yi bayan su Haladu da ke zaune a kan benci. Zumbur! Suka miƙe, cikin damuwa Sallau ya ce. "Subhanallah! Ranka shi daɗe lafiya kuwa? Me yake faruwa daga kai sai gajeren wando?" Kafin Mai gari ya bayar da amsa su Mahmud suka ƙarasa cikin runfar, ganinsu ya sa bakin Mai gari ya shiga karkarwa hannu yana rawa ya nuna su ya ce. "Su... ne, wallahi ba... mutane ba ne. Ku taimaka..." Bai ƙarasa maganar ba ya yanke jiki ya faɗi, cikin su Mahmud ya sake kaɗawa don Mudassir tuni ya fara hawaye, ya dubi Mahmud ya ce. "Mahmud ka janyo mana masifa muna zaune ƙalau." Sai ya sake ɓarkewa da kuka, hawayen da Mahmud yake riƙewa ne ya ɓalle haɗe da wanke fuskarsa lokaci ɗaya. Sun juya za su fita da sauri Mai daban-daban ya danƙo wuyan rigarsu yana faɗin. "Billahillazi la'ilaha'illahuwa sai kun tsallaka mai gari, kai babu wanda fa zai bar wurin har sai mai gari ya dawo hayyacinsa." Su Mahmud suka yi tsilli-tsilli ƙirjinsu yana bugawa. "Wallahi a ɗaure su har sai ranka shi daɗe ya dawo hayyacinsa, idan ba haka ba sai sun tsallaka shi, dubi idon munafuka sun yi kama da baƙaƙen mayu. Wai ma ku su waye a garin nan!" Daga ƙarshe Sallau ya wurga musu tambaya. Daga Mahmud har Mudassir aka rasa mai magana, ba su yi aune ba Mai daban-daban ya fiszo wata ƙatuwar igiyar da yake ɗaure damin itace, shi da Haladu suka shiga ɗaure Mahmud da Mudassir. "Wallahi mu baƙi ne kuma ɗalibai, don Allah ku kunce mu. Wallahi ba mu yi gadon maita ba." Madassir ya faɗa murya tana rawa. Babu wanda ya kula shi, sai da suka ɗaure su tsaf sannan suka shiga yayyafa wa Mai gari ruwa. "Wallahi matuƙar ranka shi daɗe ya mutu gabaɗaya sai mun ƙone ku." Mai daban-daban ya furta, ganin sun gama juye ruwan buta guda a kan Mai gari ba tare da ya motsa ba. Mahmud da Mudassir kusan lokaci ɗaya suka kallo wutar tukubar naman Mai daban-daban, kamar haɗin baki sai kawai suka ɓarke da kuka; bayan zuciya ta gama raya musu Mai gari zai iya mutuwa tun da sun ga bai motsa ba. Dukan ƙirjin Mai gari aka fara yi ana shafa masa ruwa a fuska, sai a lokacin ya sauke ajiyar zuciya. Ya buɗe idanunsa a hankali yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya. "Su waye ku? Mu ne ko kuma su ɗin ne?" Mai gari ya faɗa yana raba idanu kamar ƙosan sadaka. "Allah Ya taimake ka Mai daban-daban ne, sannu ya jikin naka?" Mai daban-daban ya furta yana tallafo Mai gari. Tashi ya yi zaune ya sake kallonsu, sai a lokacin komai ya shiga dawo masa. "Mai daban-daban ni kaɗai kuka gani, ko kun ga wani jinsin bayan ni?" Mai gari ya tambaya a firgice. "Allah Ya taimake ka kai kaɗai ka fara shigowa, sai kuma waɗancen matasan." Ya faɗa yana nuna masa su Mahmud, da fuskarsu ta kumbure suntum saboda kuka. A zabure Mai gari ya miƙe jikinsa yana rawa, gudun kada ya sake fita da gudu ya sa su Haladu suka dafe kafaɗunsa. A madadin Mai gari ya yi musu bayani sai ya fashe da kuka, yana cusa kansa a cikin jinkinsu. Cikin tashin hankali ya ce. "Wallahi ba mutane ba ne, aljanun Laraba ne daga hukumar kare haƙƙin aljanu ta faɗin duniya." A razane suka dubi su Mahmud, Mai daban-daban ya bugi ƙirjinsa sannan ya zaro wani kwalli a aljihu ya saka a idonsa. Ya kalli su Mahmud na wani lokaci ya ce. "Waɗannan yaran mutane ne, domin babu wani aljani da ya isa ya yi mini kurari. Sa'a kuka ci na ji an ambaci sunan Laraba da tuni na sheƙa kurwarku ƙiyama." Mahmud ya ƙanƙame Muddasir ƙirjinsa yana bugawa. "Kai uban me ya kai ku razana Mai gari." Ya wurga musu tambaya yana zare ido. "Dama wannan ne..." Da sauri Mahmud ya katse Mudassir da yake son tona masa asiri, ya kwashe abin da ya faru tsakaninsu da Mai gari na aiken yaro da suka yi, don a yi musu sallama da shi su gabatar da kansu a wurinsa. Kunyar duniya ta lulluɓe Mai gari musamman da ya gan shi a yashe da gajeren wando, ya dubi Haladu cikin tsare gida da borin kunya ya ce. "Kai Haladu, a suturta mu ba ma son raini. Muna buƙatar babbar rigarku, wane irin iskanci ne za a gan mu a haka; kuma a ƙyale mu tsirara ana ƙare wa surarmu kallo?" Haladu ya gimtse dariyarsa, ganin yadda Mai gari yake cijewa yana haɗe rai, ya ciro babbar rigarsa ya miƙa masa. Mai gari ya dubi Mai daban-daban ya ce. "Ku kuma sai mun buƙaci hula za a ba mu saboda rashin girmama na gaba?" Tun bai gama magana ba, ya ciro hular kansa ya miƙa masa. Bayan ya saka ya dubi Sallau cikin kurari ya ce. "Ba tun yau ba, muka lura kuna da jiji da kai. Idan ba ku kwaɓo takalmanku ba, za mu yanke muku hukuncin noman gonar bayan gidanmu." Da sauri Sallau, ya sunkuya ya ce. "Tuba nake ranka shi daɗe." Daga haka ya miƙa masa takalmansa. Mai gari ya dubi su Mahmud yana baza babbar riga ya ce. "A kunce su yanzu, kuma su same mu a ƙofar fada idan Allah Ya kaimu." Daga haka ya yi gaba, har ya fara tafiya borin kunya ya sa sake juyowa ya ce. "Kai Haladu za a bi bayanmu ana yi mana kirari, ko sai mun tura ku birni gidan yari!" Da sauri Haladu ya koma gefen Mai gari, yana tafe a gefensa yana yi masa kirari. Shi kuma yana tafe cikin ƙasaita kamar ba zai tata ƙasa ba. Mai daban-daban ya kunce su Mahmud, suka fito daga runfar jiki a sanyaye kamar marayun zakaru, suka nufi hanyar gidan da suka sauka. Washegari A hankali yake bubbuga ƙofar sashen Inno, kusan minti ɗaya yana tsaye ba tare da an buɗe ba. Inno ce ta ƙarasa tana faɗin, "Waye haka zai ɓalle mini ƙofa? Saboda Allah mutum bai gina mini ba, da farar safiya ya nemi karya mini ita..." Ba ta ƙarasa maganar ba ta cire sakatar, ganin Fadil a tsaye ya sa Inno ta ɗan ƙanƙance ido ta kalle shi tana faɗin. "Wane ne haka kamar Iro?" Fadil ya saki murmushi don ya fahimci Inno rikici take ji, shi kuma ba zai biye mata ba. "Eh shi ne." Ya ba ta amsa yana gegarewa ta gefe ya wuce ciki. "Kai boka ni fa na gaji da ganinka a sashena, ita waccen figigiyar matar taka ban isa ta zo ta gaishe ni ba kenan? Kullum sai dai ka ɗebo doro ka shigo mini gida." Fadil bai tanka mata har ya shiga ya zauna, kasancewar ranar weekend ce ta sa koda da ya ga Laraba tana bacci bai tanka wa Inno ba. "Ina kwana Inno?" Ya furta mata. "Lafiya ƙalau boka ya mugun halin matarka? Don ni dai ba zan ce ga abin da ta yi mini na laifi ba, amma wallahi yadda take kwaɓe fuska kamar kunu kullum babu fara'a, ya sa nake mata kallon mai mugun hali." Ido ya zuba mata yana kallo, ya saki murmushin gefen baki saboda idan ba ka san halin Inno ba, sai ta ɓa ta maka rai a banza. "Inno wata magana na ji, a gaskiya ba zan lamunci ki yi zaman aure da mutumin da ba a tantance jininsa ba." Tun da ya fara magana take kallonsa a gwasale, sai da ya gama ta ce. "Ubanka Iro ma haka ya gan ni ya ƙyale ni, wallahi bokan turai ka shiga taitayinka tun ban yi maka iyaka da ɓangarena ba." Hannu ya saka a aljihu ya ɗebo wasu kuɗi masu kauri ya miƙa mata. Ino ta karɓa tana zuba kabbara. "Allahu akbar kabiran, wato boka ni fa inda kake burge ni kenan. Akwai ka da kyauta har ka fi uwarka miƙa hannu, dama ba zan saka Iro ba don babu abin da ubanka yake ba ni." Dariya sosai Fadil ya yi, musamman da ya kalli gwangwanayen madarar da ke kan firjinta, ya tuna gorin da Inno ta yi masa ta ce mahaifinsa ne ya kai mata. Yana shirin yin magana ta ce. "Ka ga idon nan, tun jiya yake yi mini rawa. Ni dama na san ko dai kuɗi zan samu ko kuma baƙi zan yi." Haɓa ya riƙe yana kallon Inno ya ce. "Kenan saboda fatar idonki tana rawa sai ki samu kuɗi ko ki yi baƙi? Inno me ya sa har yanzu ba za ki watsar da camfe-camfen nan ba? A kimiyance fa ba haka abin yake ba, babu dalili da zai sa don fatar idonki tana rawa ki samu kuɗi duk camfi ne. Kuma dama duk abin da ka camfa shi, za ka ga yana tabbata kamar yadda tsafi yake gaskiyar mai shi." Inno ta yi kicin-kicin da fuska ta ce, "Kana nufin ƙarya nake kenan? To ba ubanka Iro ba, ko yayan uban Inusa bai isa ya karyata ni ba, ku da komai na ku sai kun sako iyayi da tsurfar ƙaryace-ƙaryacan yahudawa." Fadil ya ɗan girgiza kai ya ce, "Allah da gaske Inno duk camfi ne, a kimiyance fa wasu dalilai ne suke haddasa haka. Har ka ji tsokar jikin mutum, ko wani sashe na jikinsa yana rawa wato (twitching) a kimiyance mu ce nervous ticks. Dehydration, wato bushewar jiki da ƙarancin ruwa a jikin mutum yana haifar da haka. Akwai yawan shan abubuwa masu ɗauke da caffiene , wasu a ɓangare ci ko sha zuwa yawaita shan magunguna hana zugi barkatai, ba tare da shawarar likita ba. Musamman magungunan da za ki ji ana kira da ciwo goma, ko ciwo takwas. Haka idan sinadarin ƙara ƙarfin ƙashi wato vitamin D, da vitamin E na rage dattin jiki zuwa calcium suka yi ƙaranci, duk zai iya janyo wani sashe na jiki ya dinga rawa. Akwai kuma rawar hannu, da za ka ji haka kawai hannunki yana rawa. (Neurological disorder) Ana iya gadon rawar hannu, kamar idan iyaye da kakannin suna yi. Shi ma kuma, akwai wanda wani dalili yake saka haka." Inno ta shiga tafa hannu a tsorace ta ce, "Wallahi ni dai a kaf zuri'ar dangin uwata da ubana babu maye ko mayya. Don haka babu ta inda Iro zai gaji maita, ballantana ya haifo maye sai dai ko a can dangin uwarka. Ni kake cewa ban da bitamin a jikina boka? An ya a makarantar da ka yi karatun likitancin nan, ba su sayar maka da maita ba?" Yadda ya ga Inno ta tsorata ne, ya tabbatar masa da gaske take faɗar maganganun har cikin zuciyarta. Ya saka hannu ya dafe kai ya ce. "Haba Inno don Allah ki fahimce ni, ni fa ba haka nake nufi ba. Ina yi miki bayanin abin da yake kawo motsin wani sashe na jiki ne, kamar yadda kika ce fatar idonki tana rawa." Shiru ta yi tana kallonsa a gwasale, ganin haka ya sa Fadil ya cigaba. "Inno har yawan rashin hutu ko wadataccan bacci yana haifar da haka, haka fargaba ko damuwa duk suna cikin abin da yake janyowa. A ɓangare ɗaya, yawan zuƙar taba da shan giya duk yana daga cikin abubuwan, da za su iya saka wani sashe na jiki ya dinga motsi, kamar ki ji hannu, ido ko tsokar cinya tana motsi. Idan kina son gujewa haka, sai dai ki kiyaye waɗannan abubuwan da na lissafa, yawaita shan ruwa, samun hutu da bacci da yawan cin kayan marmari. Masu zuƙar taba kuma, muna ba su shawarar guje wa zuƙar taba da shan giya, haɗe da takatsantsan wurin shan magunguna masu ɗauke da caffeine. Idan kuma matsalar ta ta'azzara sai mutum ya wuce asibiti, domin ya ga likita." A fusace Inno ta wawauro muhuci ya raɗa wa Fadil ta ce, "Fice ka ba ni wuri, mutumin banza da wofi. Yanzu ni kake zama ka cewa ina shan giya, giya fa boka..." Sai kawai Inno ta ɓarke da kuka, Fadil ya fice yana shafa kafaɗa don dukan ba ƙaramin shigarsa ya yi ba. Tun daga ɗaki su Hansatu, suka fara jin yadda Yaya Inu yake wurgo ƙullin kaya da kwanukansu tsakar gida. Kusan lokaci ɗaya Hansatu da su Indo suka yi carko-carko, a ƙofar ɗakin suna kallonsa. "Mai gida Lafiya wai? Dubu yadda kake jefo mana kaya tsakar gida." Hansatu ta faɗa tana tattarawa kayan wankinta. A daidai lokacin Yaya Inu ya sake wurgo wata tukunya da farantin Indo suka fashe lokaci ɗaya. Ranta ba ƙaramin ɓaci ya yi, ta kwashe cikin masifa ta ce." Malam mene ne haka muna magana ka yi shiru?" Yaya Inu ya tako yana kallonsu a wulaƙance haɗe da yamutsa fuska kamar ya ga kashi, ya dafa ƙofar ɗakin ya yi bake-bake ya ce. "Gabaɗayanku ku kwashe mini wannan tarkacen haukan, saboda gobe za a ɗaura mini aure. Kuma a yanzu ne na san zan yi aure, zan auri farincikina mai faranta mini rai. Wacce ta san mutumci da ƙimar aure, tun a yanzu ta fara shagwaɓa ni tana lailaya ni. Wallahi idan ta zo duk wacce ta koya mata ƙazanta da mugun hali sai na ci mutumcinta. Saboda a kullum idan na kalli ku fuskokinku kama kuke yi mini da sumammun birirrika." Da sauri Hansatu ta saka hannu ta rufe bakinta saboda mamaki da ɓacin rai. "Mai gida cin zarafin naka har ya kai ka kira mu da birrai?" Hansatu ta faɗa a zafafe. Indo tana shirin yin magana, suka ji muryar Abu ta shigo gidan tana faɗin. "Yawwa Goggo, mun zo a daidai ma ga shi nan yana gida." Ɓata rai Yaya Inu ya yi yana ƙanƙance ido ya ce, "Bayan na warware igiyar aurena da ke, uwar me ya kawo ki gidana da farar safiya Abu?" Abu ba ta tanka masa ba, tana zuwa ta ɗaga hijabi ta miƙa masa jaririya. Ba Yaya Inu ba, hatta su Indo zaro ido waje suka yi suna kallon yanayin kalar jaririyar. "Ke mene ne wannan? Kuma waye uban wannan abin?" Yaya Inu ya furta yana janye jiki cike da ƙyanƙyami. "Kai ne ubanta, kuma a haka ta zo duniya." Ganin kamar Yaya Inu ba zai karɓa ba, ya sa ta dire masa jaririyar a ƙasa. Kwana biyu na yi nisan zango, bayan na ɗanyi rashin lafiya sai kuma muka shiga biki. Na gode sosai da kulawarku, Allah Ya bar zumunci. 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam🌚 [02/02, 15:02] Ameerah Adam🌚: *GIDAN LIKITOCI* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA BAƘAR DAULA AN YA BAIWA CE? ƊAN BA ƘARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page ɗin, ya taimaka ya yi mana Subscribe a youtube channel ɗinmu.👆🏻👆🏻👆🏻 SHAFI NA GOMA A zabure Yaya Inu, ya buga tsalle ya dira a gaban Abu da Goggonta da suke shirin fita. Goggo ta haɗe rai ta ce, "Kai Inusa, ka ba mu hanya mu wuce. Ciki ne dai Allah Ya raba ta da shi lafiya, don haka muka kawo maka abarka." Yaya Inu saka hannuwa biyu, ya yi bake-bake a bakin ƙofar ya ce, "Ku je ina? Don Allah Goggo kada ki shiga gonata, saboda akwai ragowar mutumcinki a idona." Ya waiga wurin Abu ya ce. "Wallahi tun muna mu biyu, ki gaggauta ɗauke wancen abin daga cikin gidan nan!" Abu tana shirin magana Indo ta saki shewa har da guɗa tana buga cinya. "Ahayye! Allah na gode maka, ai dama Allah ba azzalumin bawa ba ne sai bawan da ya zalinci kansa. Yau ga shi muna ji muna gani, satar kwana da karya dokar Ubangiji ta bayyana a fili mun gani." Indo ta ƙarasa maganar tana sakin dariyar izgilanci. Hansatu ma dariyar take yi ta isa gaban Yaya Inu tana kallonsa a watse ta ce, "Yanzu don Allah mai gida ba ka ji kunyar abin da kuka haifo ba? Ke yanzu Abu ba ki ji kunyar iyayenki da sauran danginku ba? Tirƙashi! Yau ake yin ta a gidan nan, abin da muke hange a nesa ya zo kusa da mu. Yanzu mai gida jarabar taka har ta kai ka dinga kusantar Abu tana jinin al'ada?" Yaya Inu da ya gama zuwa wuya a zafafe ya ce, "A gidan uwar wa kika ga na kusance ta tana jini? Ko kin ɗauka ban san hukuncin addini ba." Su Indo suka kwashe da dariya kusan lokaci ɗaya, Hansatu ta kalli wurin da jaririyar take kwance tana mutsu-mutsu ta ce. "Ga shaida can mun gani, ko ba zabiya ta haifa maka ba. Ai an yi walƙiya mun ganku, duk munafuncin da kuke yi ashe Allah zai tona muku asiri ba ku sani ba. Ba ni kaɗai ba, kowa ya san sai an kusanci mace tana jinin al'ada ake haihuwar zabiya." Abin duniya goma da ashirin ya haɗe wa Yaya Inu, ya haɗiyi yawu mai ɗaci kamar zai yi kuka ya ce. "Billahillazi la'ilaha'ilahuwa ban taɓa aikata wannan ɗanyan aikin ba. Ni fa shi ya sa nake tantama, magana ta Allah a ce duk dangina babu zabiya sai yanzu zan haife ta. Wallahi tun ban kai ku wurin hukuma ba, Abu ki ɗauke yarinyar nan ki kai ta wurin ubanta. Da ma ni da ke babu kare bin damo." Hankalin Abu ya tashi, saboda babu abin da yake ɗaga mata hankali irin ta yi ido biyu da ɗansanda. Duk da tana da gaskiya, amma haka gumi ya shiga karyo mata, ta ƙarasa ta ɗauki jaririyar cikin ƙarfin hali da barazana ta ce. "Au haka ka ce ko? To kafin ka kai mu wurin hukuma, ni da kai na zan fara kai ƙararka. Ka san dai ko lokacin 'yan matancin na kai ne mutumin da nake kulawa. Don haka babu wani uban yarinyar nan, idan ba kai ba. Ai na sha faɗa maka ka daina satar kwana kana kirana turakarka amma sai ka ce ba haka ba. Ka dinga koɗa ni kana ce mini matar so, ni kuma ina jin daɗi domin na ɓa ta ran su Indo nake biye maka. Sai yanzu za ka ce ba ka san zancen ba, za ka yi bayani a gaban ƙuliya." Tana gama faɗar haka ta yi waje fuu! A fusace. Hansatu ta gyaran ɗaurin ɗan kwalinta, irin ɗaurin ture ka ga tsiya ta ce. "Kai yau Allah na gode maka da ka nuna mini wannan rana. Ayyiriri! Shagali wan dina. Ai gara da ta tafi da 'yarta don wallahi ba zan riƙe gayyar tsinuwa ba, yarinya an same ta a tsine ta rayu a ciki cikin tsinuwa sannan a ce za a dire mana ita. Haka kawai muna zaune a kawo mana annoba cikin zuri'a ta kwashe mana albarkatun cikin gida." Daga haka ta wuce cikin ɗakinta, su Indo ma haka. Yaya Inu jiki a sanyaye ya nufi ɗakinsa yana nazarin baƙin cikin da Zainab ta dasa masa. A ɓangare ɗaya yana fargabar abin da zai je ya dawo, saboda shi dai ya san bai taɓa kusantar mace tana jini ba, satar kwana dai kam ya san yana yi babu adadi musamman idan mace ta ɓata masa rai. Don ya rama abin da ta yu masa sai ya kira wata macen da ba girkinta ba, musamman Abu ta kwana a ɗakin. Babban tashin hankalinsa, ya yi mata barazana da hukuma kamar yanda ya san tana tsoron 'yansanda amma ya lura ko a jikinta. Zaune yake ya yi shiru yana kallon Ɗan Bishir da jijiyoyin jikinsa suka gama yin laushi, ya ja riga ya share hawayensa. Yana jin ina ma yana da ikon dawo da ciwon shalelensa kansa, da tuni ya dawo da shi. "Mai gida zaman nan naka fa ba zai kai mu ba, a ce yanzu tun da aka yi wa yaron nan shayi ba za ka fita kasuwa ba. Ita zara fa ba ta barin dami, don Allah ka tashi ga magungunanka can na haɗa maka su." Baba Sale ya ja majina ya ce, "Haka ne Uwale, amma gani nake idan na fita kamar wani abu zai faru da shi. Ban taɓa ganin kaciyar da ta lalace haka ba, ki duba fa ki ga yadda take yin ruwa. Yaron nan duk kuzarinsa ga shi nan ba shi da kataɓus." Ita kanta Uwale ƙarfin hali take yi, don tana nuna rauninta ta san abin da mijin na ta zai yi sai ya fi haka, don haka ta shanye hawayen idonta ta ce. "Haka ne, amma ko ka zauna ɗin ma abin da Allah Ya ƙaddara shi zai faru. Shi kuma idan mun ga ba ta daina ruwa ba, sai mu sake kiran wanzan mu yi masa bayani. Tun da maganin wurinka ma bai sa ta ƙame ba." A sanyaye Baba Sale ya miƙe ya shiga ɗaki, ya ɗauko wani ƙaton buhu da ke cike da magunguna. Ya ƙarasa gaban Ɗan Bishir ya ce, "Ɗan Bishiriri ni zan fita nema." Ɗan Bishiri da ya yi lugub, saboda yadda yake jin jiki ya kalle shi da shanyayyun idanunsa ba tare da ya amsa masa ba. Da ƙyar Baba Sale ya iya ɗaga ƙafarsa ya fita Uwale tana biye da shi. Suna fita Fadil yana fitowa bayan sun gaisa ya wuce ya shiga motarsa da ke gefensu. "Au Mai gida na manta ba ka bayar da maganin Shamsiyya ba, kada sai ka tafi ta aiko." Uwale ta furta. Buhun ya buɗe ya ɗebo wasu matsakaitan magunguna a cikin jarkoki guda huɗu, sannan ya ɗauko wata ƙaramar roba mai ɗauke da man shafawa na magani ya miƙa mata. Ya ɗago jarkokin guda biyu, ya nuna mata wurin da aka yi bayanin maganin a jikin takardar. "Wannan ki ce mata sai ta ci abinci za ta sha, maganin sanyin mara ne. Kuma sau biyu ake sha safe da yamma, duk lokacin da za ta sha murfi biyu za ta sha saboda yana da ƙarfi sosai." Ya sake ɗauko ragowar roba biyun da yake ba iri ɗaya da waɗancan ba ne ya ce. "Wannan kuma idan ta tashi biyu za ta raba shi, ta sha rabin roba yau gobe ta sha rabi. Shi kuma wannan man zafi ne, na ciwon bayan da ta ce tana yi ne. Za ta dinga shafa shi a bayanta safe, rana da dare. Amfaninsa iya baya ne. Kar ta ji ƙafa ko gwiwa tana yi mata ciwo ta shafa, ba zai yi mata aiki ba. Duka dai bayanan maganin suna jiki, na san kin fahimta abin da ba ta gane ba sai a bari na dawo, saboda ba na son na ba wa mutum magani ya sha ba daidai ba a samu matsala." Duk bayanin da Baba Sale yake yi Fadil yana cikin mota yana jin sa, ba ƙaramin birge shi ya yi ba. Don haka ya fito ya ƙarasa wurinsa cike murmushi ya ce. "Am Baba Sale na ji duk bayanin da kake yi mata, kuma AlhamduLillah ka birge ni matuƙa. Saboda yadda na ji kana bayanin magungunanka daki-daki cikin ƙa'ida, ta yanda ba zai haifar wa mutane matsala ba." A sheƙe Baba Sale ya dubi Fadil ya ce. "Kai yaro da me ka ɗauki masu magungunan gargajiya? Jahilai ka ɗauke mu ko yaya? Ka ɗebo tsila-tsilan ƙafafuwanka kamar ƙwailayen lawashi za ka yi mini iyayi." Kunnuwansa Fadil ya riƙe ya ce, "Allah Ya huci zuciyarka ba haka nake nufi ba, ka yi abin da ya dace ne shi ya sa na yabe ka. Saɓanin wasu masu magungunan da suke sayar da magani babu dosage, mutum ya sha yadda ransa ya so babu ƙa'ida." Baba Sale ya taɓe baki ya ce, "Da ka ɗauka maganin asibiti ne kaɗai yake da galihu? Masu magungunan ai wasu suna suka tara, kamar yadda a cikin likitocin akwai muna likita. Kai dube ni nan. Sana'ata ba irin ta sauran masu magani ba ce. A yanzu ma idan na samun jari, babban wuri zan buɗe na huta da gararanba a titi. Sai na sake inganta su, don ina da burin har jami'an lafiya zan zuba tun da ni dai ka san summun bukumin ne, zo na kashe ka da turanci ban sani ba ballantana na san harkar gwaje-gwaje." Fadil ya saki murmushi, ya yaba masa sosai da sabon tsarin inganta maganin da ya ɗauko, har zai tafi ya waigo ya ce. "Na ji Daddy ya ce an yi wa yaron nan shayi ya jikinsa?" Jin tambayar Fadil ta sa hawaye ya zubo masa, ya saka hannun rigarsa ya share. Mamaki ne ya kama Fadil yana shirin magana Baba Sale ya ce. "Ɗan Bishir dai ga shi can rai a hannun Allah, daga kaciya jikin yaro sai fitar da ruwa yake duk ya jagalgale abin ba kyan gani. Na saka masa magani a banza, haka wanzan da ya yi masa kaciyar ya aiko masa da magani amma sai ta fara kamewa sai ta koma 'yar gidan jiya." Ya ƙarasa maganar yana fashewa da kuka. "Subhanalla, kuma ka kai shi asibiti?" Kamar Baba Sale yana jira ya ce, "Kaciyar zan kai asibiti don lalacewa? Wai me ya sa a kullum, sai ka nemi wulaƙanta mana sana'ar wanzanci ne?" Fadil ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Ni fa ba da wata manufa na faɗa ba, yanzu mu je na ga yanayin jikin na sa." Babu musu Baba Sale ya yi gaba Uwale da Fadil suna biye da shi. Suna zuwa suka samu Ɗan Bishir a yashe a ƙasa, kudaje sun yi yamama a kan jikinsa. Da sauri Fadil ya ƙarasa ya fara karkaɗe masa, ya ɗago a ɗan zafafe ya ce. "Garin yaya kuka bari jikin yaron nan ya yi haka? Saboda Allah dubi yadda ƙudaje suka bin sa ko su ba su isa su saka masa wata cuta a jiki ba." Mai shirin kuka ne aka jefe shi da kashin awaki, jin kalaman Fadil ya sa Baba Sale ya saki wani wawan kuka har sa da ya tsorata Uwale da Fadil. Ya riƙo hannun Fadil jikinsa yana rawa ya ce. "Boka wallahi ban san yadda aka yi ba, don Allah yanzu mene ne abin yi?" Jim Fadil ya yi sannan ya ce, "Mafita kawai a ɗauke shi zuwa asibiti shi ya fi fa'ida. Don haka a yanzu muke bayar da shawara idan za a yi kaciya a san wuraren da ya dace a kai yara, ba zan kushe ta wanzamai ba. Domin tun daga shekarun baya zuwa kusan ɗan shekara ashirin da yake a yanzu, kusan yawancin duka kaciyar gida aka yi musu. Amma a inda gizo yake saƙar, rashin kula da tsaftace kayan aikin yin ta zuwa kula da ita bayan an yi wa yara, sune manyan ƙalubalen." "Wai boka da kake ta ƙafafa a kan shayin, asibiti shin tana da bambamci da ta gida ne? Duk dai ba abu ɗaya ake yi ba?" Uwale ta tambaya, don ta fara jin haushin yadda Fadil yake fifita aikinsa a kan sana'ar mijinta. Fadil ya cigaba da karkaɗe wa Ɗan Bishir ƙuda ya ce. "Gaskiya akwai bambamce-bambamce da dama. Kamar yadda muka sani shayi wacce a kimiyance ake kira (Circumcision) wata ƙaramar tiyata ce da ake cire fatar loba (Foreskin) wacce take zazzagowa ta rufe kan al'aurar namiji(Glans). Kaciya tana da dalilin da ya sa ake yin ta, daga ɓangaren addini zuwa al'ada. Mafi yawancin ƙasashen da suka ci gaba, suna yin shayi ne a rana ta farko da aka haifi jariri. Wasu ƙabilun kuma suna yi bayan suna ko idan an yaye yaro. To amma kin ga a irin yankin ƙabilunmu, yawanci ana yi wa yara daga shekara uku zuwa bakwai. Sannan rashin yin ta babbar barazana ga lafiya ne. Kamar yadda shayi ke da dalili akwai amafanin da take da shi, musamman a ɓangaren lafiya. Domin yin ta yana bayar da kariya daga saurin ɗaukar cutar infection, saboda cututtuka suna iya ɓoyewa a ciki idan ba a cire fatar ba. Tana bayar da kariya daga kamuwa da penile cancer, a ɓangaren mata kuma zai rage musu kamuwa da cervical cencer, har ma da matsalar saurin kamuwa da ciwon (Balanitis) kumburin saman al'aurar namiji. Da ma sauran cututtukan da ban lissafa ba." Jikin Uwale ba ƙaramin sanyi ya yi ba, Baba Sale ya zube a ƙasa kamar wanda aka zare wa laka ya ce. "Yanzu boka duk wannan bayanan a kimiyance ka karance shi? Shi Ɗan Bishir wannan ruwan da take yi na me ne ne?" Ganin yadda Baba Sale ya ɗaga hankalinsa, ya sa Fadil ya tsugunna a gabansa ya ce. "Ka kwantar da hankalinka Baba Sale, wannan ba komai ba ne In Shaa Allah za a kamo bakin zaren matuƙar aka je asibiti. Rashin kula da tsaftar wurin ya sa infection ya shiga, har ya haifar da zubar wannan ruwan da kake gani. Idan har aka je asibiti za su duba shi, su yi abin da ya dace su ba shi magunguna. Ni ma don dai ina da uzuri, da zan iya yi masa treatment. Amma ba zai yuwu, a bar yaro haka har tsawon lokacin da zan dawo ba. Sannan yana da kyau a kula da tsaftar raunin, kada a bari ƙudaje da wasu ƙwarin su dinga hawa jikinsa; saboda za su iya fesa masa ƙwayoyin cutar da ido ba zai iya gani ba. Rashin kulawa da tsafta, haɗe da takatsantsan zai iya haifar da kamuwar cutuka, har ya haifar da fiye da wannan da muke gani wanda ba ma fatan hakan." "Uwale maza ɗauki Ɗan Bishir mu tafi asibiti, wallahi ni babban tashin hankalina kada ma abin ya guntule ya faɗo ƙasa." Baba Sale ya faɗa cikin hawaye. Fadil ya jima yana ba su shawarwari da ƙwarin gwiwa sosai, sannan suka fito suka shiga mota ya sauke su a asibiti shi kuma ya tafi uzurinsa. Motar Fadil ta fita babu jimawa Mai adaidaita sahu ya sauke Baba Ɗanladi, hannunsa ɗaya riƙe da matarsa ɗayan hannun kuma riƙe da akwati. Sai da ta sauka sannan ya ɗauko musu akwatinan su ya ajiye a gefe. Kuɗi ya zaro ya biya mai adaidaita sahun, ya kamo hannunta yana shirin shiga gida Uzee gaye ya ƙarasa wurin bakinsa a washe kamar gonar auduga ya ce. "Oyoyo jirgin ceto, Oga murfi namu na gargajiya, uban gidan kowanne mai cin mushe. Duk wanda kwaɓarsa ta yi ruwa ya zo a ɗaure masa, ka suturta kuma ka rufa asirin gayu. Ina wanda ya samu 'yar shila ya bige aka samu matsala? In wanda bargon suturarsa yake son yayewa? Ya zo ga mai lulluɓe masa har ya yi bacci. Oga murfi wannan 'yar shilar ita ma zuwa ta yi a kifar da madafun ikonta ne?" Tun da Uzee guye ya fara maganar kan Baba Ɗanladi ya ƙara girma, ya faɗaɗa fara'arsa ya ce. "A dai dinga iya baki Uzee saboda tsaro ba don tsoro ba. Wannan da kake gani ba costomer ba ce, matar da na auro ce." Murmushi ta yi tana jifan Uzee da wani karuwan kallo, wanda kallo ɗaya kawai ya yi mata ya fahimci ita ma 'yar hannu ce. Uzee ya yi ƙasa da murya ya ce. "Wallahi Oga murfi ka zo a daidai, domin yanzu haka akwai wata yarinya da rana ta ƙwace mini. A taƙaice dai cikinta wata biyu kenan, don Allah ka rufa mini asiri kamar yadda ka saba ka ɓarar da shi." Baba Ɗanladi da irin su Uzee suke kira da Oga murfi ya ce. "Ka ga zuwana kenan, ko cikin gida ban shiga ba. Koda zan dawo bakin aiki sai zuwa nan da sati guda, domin shi kansa chemist ɗin yana buƙatar gyara." Uzee gaye ya yi masa godiya, sannan Baba Ɗanladi ya shige cikin gida hannunsa maƙale da na matarsa da yake jin ta kamar tsoka ɗaya a miya. Tun daga harbar gidan mutanen cikin gidan suka shiga yi masa barka da zuwa, sai dai kusan kowa bakinsa ƙunshe yake da magana kasancewar ganin Baba Ɗanladi rungume da wata mace mai zubin 'yan duniya. Amma da yake ba su ga fuska ba, sai kowa ya tsuke bakinsa. "Lale marhabun wa nake gani haka da hantsin nan?" Inno ta faɗa tana washe fuska, turus ta yi ganin Ɗanladi sarƙafe da mace a gefe. Inno ta ƙanƙance ido tana ƙare mata kallo ganin gashin doki ya yi mata yaro-yaro a fuska. "Ɗanladi daga ina ka samo wannan abin?" Inno ta tambaya tana miƙe wa tsaye rai a ɓace. Ɗanladi ya saki murmushin soyayya, ya shafo fuskar matarsa cikin so ya ce. "Inno wannan ita ce matar da na auro ai, so nake sai mun zauna na gabatar miki da ita." Inno ta fara bin ta da kallo, tun daga ƙafa har zuwa tsakiyar kanta. "Baby ina buƙatar hutu ka san na gaji. Mu je ɗaki ka yi mini tausa." Ta furta tana shafa jikin Ɗanladi. Inno salati ta saki tana tafa hannu ta ce. "Yanzu Ɗanladi, ƙaddarar da ka kwaso mana kenan wannan mai zubin alakwankwan ɗin?" Ɗanladi ya sunkuya ya sumbaci matarsa ya ɗago ya cewa Inno, "Wallahi Inno kamar kin sani wannan ita ce ƙaddarata. Jin ta nake har birnin zuciyata. Beb wannan ita ce Mom ɗina, you know i told you Dad ɗina ya jima da mutuwa." Ta ɗago tana taunar cingam ta ce, "Am so sorry Mom, ya kike?" Inno ta saki baki da hanci tana kallon ikon Allah. Jin maganganu a tsakar gida ya sa Mai yasin ya leƙo yana faɗin. "Inno ke da waye ha..." Maganarsa ce ta maƙale, sakamakon haɗa ido da suka yi, lokaci ɗaya wani irin tari ya turnuƙe shi. Daga can ɓangarenta ita ma ido ta zaro, amma sai ta daidaita nutsuwarta ta basar kamar ba ta san Mai yasin don kada su gano su. 'Me ne ne alaƙar wannan yaron da 'yar gwal? Ko dai aurensa ta yi ban sani ba, lallai kuwa dara ta ci gida idan har haka ne.' Mai Yasin ya raya a ransa. Ɗanladi ya zaro mukulli a aljihu, ya buɗe ɗakinsa ya fara jan akwatinansu ya shigar musu da su ciki. 'Yar gwal a wurin ta fara rage kayan jikinta, ta zame mayafinta ta wurga a kan igiya. Ta zamo hular gashin dokin kanta za ta wurga igiya a daidai lokacin Yaya Inu ya shigo cikin gidan, a bisa tsautsayi ta jefa masa a fuska. Warin gashin ya daki hancinsa, a tsantsance ya wurgar da shi gefe rai a ɓace yake kallonta, cikin tsawa ya ce. "Ke! Wace ce ke?" Daga cikin ɗaki Ɗanladi ya ce, "A'a Yaya Inu, kada ka sake ka sake yi wa 'yar gwal tsawa don ba zan lamunta ba." Da mamaki Yaya Inu yake ƙare mata kallo ya furta. "Za ki fice daga gidan nan ko sai na sumar da ke? Kai Ɗanladi, a gidan uwar wa ka samo wannan abar mai zubin surar Fir'auna?" 'Yar gwal ta bi Yaya Inu da kallo a ranta ta raya. 'Ni za ka yi wa barazana? Ai kuwa za ka ga aikin 'yan bariki. Sai na nuna maka sheɗan ne uban gidana ba Fir'auna ba.'' Yaya Inu yana shirin sake magana, 'Yar gwal ta yi wata wawar sufa ya ɗane shi. Na kusa kammala free page In Shaa Allah, ma su son cigaba za su fara payment daga yanzu. 500 Aisha Adam 3090957579 Firstbank evidance ta wannan no ba 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam🌚 [02/02, 15:02] Ameerah Adam🌚: *GIDAN LIKITOCI* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA BAƘAR DAULA AN YA BAIWA CE? ƊAN BA ƘARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page ɗin, ya taimaka ya yi mana Subscribe a youtube channel ɗinmu.👆🏻👆🏻👆🏻 SHAFI NA SHA ƊAYA "Innalillahi wa inna'ilahir raji'un! Ke! Wane irin iskanci kike yi haka? Ba za ki cika ni ba, sai na saɓa miki." Yaya Inu ya yi kalamansa yana kokawa da 'Yar gwal amma fir ta ƙi sakinsa, ta ƙadandane shi sosai kamar mayen ƙarfe. "Ke yarinya, ba ki da mutumci ashe ban sani ba, ba za ki sakar mini yaro ba." Inno ma ta yi maganar tana ƙarasawa wurinsu. Mai Yasin ya gimtse dariyar ƙetarsa, saboda dama a ciki yake da Yaya Inu. Kuma ya san fiye da haka ma 'Yar gwal za ta iya aikatawa. Ganin da gaske 'Yar gwal ba za ta sake shi ba, ya sa ya tattare iya ƙarfinsa da niyyar ya warɓo ta ƙasa, sai ta maƙale shi ƙam a madadin 'Yar gwal ta faɗo sai wata wawiyar tusa ce ta ƙwacewa Yaya Inu. "Subhanallahi! Inusa mene ne haka da sakin tusa?" Mai Yasin ya furta, sannan ya ce. "Ke yarinya kanki ɗaya kuwa? Kamar muna ƙasar kafirai za ki ƙadandane mutumin da ba muharraminki ba." 'Yar gwal ta ɗago tana bin sa da wani irin kallo, sai kawai suka ji ta saki jiki ta faɗi yaraf a ƙasa. Sai a lokacin Yaya Inu ya ja gefe yana kaɗe riga, ya cigaba da wurga mata kallon tsana kamar zai mata duka. "Sannu babyna, ko jikin ne ya dawo?" Furucin Baba Ɗanladi kenan. 'Yar gwal ta fara jera atishawa, Ɗanladi ya ɗago ya dubi Yaya Inu ya ce. "Shi ya sa tun farko na ce babu ruwanka da ita, saboda ni na san aljanun jikinta ba sa nisa da ita. Ina zaman zamana za ka rikita mini mata babu gaira babu dalili." Ɗanladi ya ƙarasa maganar yana ɗaukar 'Yar gwal ya shige ɗaki da ita. Inno ta shiga share hawaye ta ce. "Inusa yaushe ɗan'uwanka ya yi lalacewar haka? Wai Inusa saboda ya mayar da mu ba komai ba a wurinsa, har shi zai je wani wuri ya aurar da kan shi. Inusa ba za ku yi wani abu a kai ba?" Yaya Inu da ya gama cika da mamaki ganin ƙiri-ƙiri 'Yar gwal ta raina musu hankali ya ce. "Inno kin fi kowa sanin wane ne Ɗanladi, tun da rayuwar da ya ga ta fiye masa ba sai ya yi ba." Daga cikin ɗakin Ɗanladi ya ce. "Inno yanzu auren da na yi ne ba za ki saka mini albarka ba? A da kuna yi mini ƙage, kuna cewa ina lalubar yaran mutane a chemist ɗina. Amma yanzu kuma na yi auren ma ba za ku sarara mini ba? Sunnar Annabin ce kuke ƙyashi na raya?" 'Haƙiƙa na lura duk balaja'un Inusa ashe shi shafar mai ne a kan wannan. Tirƙashi, wannan Ɗanladin ai ya gama tashin kaina.' Mai Yasin ya raya a ransa. Yaya Inu ya kamo hannun Inno ya furta. "Mu je Inno, idan kika biye ta wannan yaron ranki ne zai yi ta ɓaci a banza. Yanzu mu je ciki ni ba wannan ce damuwata ba, wani tashin hankali ne yake tafe da ni da na garara samun nutsuwa." Inno ba ta musa ba, ta bi bayan Yaya Inu suka shiga ɗaki. "Inno ɗazu Abu ta zo, ta kawo mini jaririyar da ta haifa..." "Amma dai wannan yarinya an yi marar mutumci, yanzu ita saboda rashin hankali daga haihuwar yarinyar za ta ɗauko ta kawo maka? A kanta aka fara mutuwar aure?" Inno ta katse shi tun bai ƙarasa magana ba. "Don Allah Inno ki bari na dire maganata." Inno ta yi fakare tana jiran ya gama magana ta ɗora daga inda ta tsaya. "An samu matsala domin yarinyar zabiya ce. Ni kuma gaskiya ina zargin ba 'yata ba ce, saboda kowa shaida ne ban taɓa haihuwar zabiya ba." A razane Inno ta ja da ba ya tun bai gama magana ba, ta fara dubansa da wani kallo sannan ta ce. "Kada ka raina mana hankali Inusa, batun ka ce 'ya ba ta ka bace ai bai taso ba. Saboda kowa ya san ta yadda ake samun zabiya, sai da ka je ka gama saɓon Allah sannan za ka same ni kana yi mini 'yar murya? Me zan iya yi maka a yanzu? Bayan Allah ya yi ikonsa, ai sai dai ka ɗauki na Annabawa. Ka je can kai da Zainabun ku yi ta istigifari kuna tuba ga Allah." Inno ta yi maganar tana miƙewa, har za ta shige uwar ɗakinta ta waigo ta ce. "Yawwa dama daga yanzu kada ka sake ka shigo mini. Saboda kada zunubin da kuka kwaso Allah Ya jarabce ni da shi." Tana gama maganar ta shige ciki. Kamar Yaya Inu zai ɗora hannu a ka, haka ya fice daga sashen Inno abin duniya ya haɗe masa. Yamma ce sakaliya, sanyin la'asar tuni ya riga da ya sauko. Fadar Mai gari cike take da mutane ana zaune ana zaman fada. Mafi yawan mutanen da suke zaune gulma ce ta kawo su, a kan abin da ya faru da Mai gari. Shi ma da yake ya fahimci haka sai ya tsuke fuska, ya dubi su Mahmud da suke takure kamar zakarun da aka tsamo daga ruwa ya ce. "A madadinmu da na talakawan yankinmu muna yi muku barka da zuwa. Muna buƙatar ɗayan bayan ɗaya, ku gabatar da kanku a gaban mutane. Mudassir ne ya ɗan muskuta zai yi magana, Mai gari ya yi wa Mahmud ƙuri da ido ya ce. "Kai yaro, kamar na san fuskar nan taka?" Cikin Mahmud ya karta, amma sai ya yi ta maza ya ce. "A'a ranka shi daɗe, sai dai idan mai kama da ni ka sani. " Jin Mai gari ya yi shiru ya sa Mudassir ya furta, "Ni dai sunana Mudassir Najib, ɗaya daga cikin ɗaliban da aka turo daga babbar Jami'a yin bautar ƙasa (NYSC)." A fili Mai gari ya faɗaɗa fara'arsa yana jinjina kai, saboda ya ji ya ce bautar ƙasa suka zo don haka sai ya ci banza. Har ya fara lissafa kansa, a sahun mahajjatan da za su sauke farali a bana. Duba da irin aikin gonar da ya ayyana zai jibga wa su Mudassir. Shi ma Mahmud ya gabatar da kansa, sannan Mai gari ya fara baza babbar yana haɗe rai ya ce. "Tun da har Gwamnati ta aiko ku garin nan, na tabbata babbar Masarauta ƙasar nan ta san irin gudunmawar da nake bayarwa a ƙasata. A don haka, ya zame muku wajibi ku zage damtse ku yi mini noma yadda ya kamata." Mai gari ya zaro ido waje cike sa barazana ya sake dubansu ya ce. "Ku dube ni nan, bautar ƙasa ba wasa ba ce yara ina fatan kun gane. Domin shinkafar da kuke miƙe ƙafa kuke ci, ita ma sai da aka gama bauta mata sannan ta bauta muku a cikinku. "Ammm amma ina ganin kamar ba ka fahimce mu ranka shi daɗe. Service muka zo fa, ga wannan takardar za ka iya karantawa." Mahmud ya ƙarasa maganar yana miƙa masa takardar. Gaban Mai gari ya faɗi, da ya ga ya miƙa masa wata zungureriyar takarda mai cike da rubutun turanci. Sai da ya fakaice su ya sharce gumin fuskarsa, sannan ya riƙe takardar yana ɗan matse idanu ya fara karantawa. "Assalamu Alaikum. Ni Mai girma gwamna, na aiko waɗannan jajirtattu kuma haziƙan ɗaliban nan, domin su zo garin nan su taya Mai gari aikin gona wanda muke kira da bautar ƙasa. Kuma a don haka, muke jan kunnensu domin su jajirce wurin yin aiki tuƙuru. Idan ba haka ba, za mu zartar musu da mummunan hukunci." Mai gari ya ɗago yana muzurai, daga can ƙasa ya ga wani rubutu da lambar waya har da saka hannu, sai ya ce. "Ga lambar wayata nan ni mai girma gwamna, duk wani ƙorafi da kuke da shi kai tsaye za ku iya tuntuɓa ta. Kuma duk wanda ya yi ba daidai ba a cikinsu, muna bayar da umarnin Mai gari ya saɓa masa. Idan da hali ma ya ci tararsa." Tun da ya fara jawabin Mahmud da Mudassir, suka yi zuru suna kallonsa cike da mamaki. Mutanen da ke wurin suka ɗauki sowa cikin kambaba Mai gari suka ce. "Allah Ya ja zamaninka mai martaba. Haƙiƙa gado ba karanbani ba, duk wanda ya san gidanku ya san mane ne mulki." Mai gari ya fara zuba doro yana kalle-kalle cikin izza. Hambali da yake gefe cikin tsananin jin kunya ya ce. "Allah Ya taimake ka, idan na fahimce su fa kamar ba haka suke nufi ba. Duk da dai ni ma ba karatu na yi mai zurfi ba, iya ka ta diploma. Idan aka ce an tura ɗalibi NYSC wato bautar ƙasa, ana nufin ya hidimtawa ƙasa ta hanyar bunƙasata da ciyar da ita gaba. Kuma kamar wani ƙarin horo ne, da ɗalibai suke sake gogewa; domin su zama shugabanni ko al'ummar da za a yi alfahari da su a gobe. Amma a gafarce ni ranka shi daɗe, idan na faɗi ba daidai ba." Tun bai gama magana ba Mai gari ya fusata. Rai a ɓace ya nuna Shazali ya ce. "A kanannaɗe shi a hukunta shi, mu zai kawowa raini a gaban fada? Shazali, yaron nan yana nufin fada ba ta san me take yi ba ne?" "Allah Ya taimake ka, abin da bawan Allahn nan ya faɗa fa haka ne. Ba aikin gona muka zo ba, kamar yadda ka faɗa..." Da sauri Mai gari ya katse Mahmud. "Kai yaro ka iya bakinka. Shin ya bari mun gama fesar da maganganun bakinmu ne? Ko numfashinmu ya tara? Abin da muke shirin faɗa kenan ya yi mana katsalandan, don haka dole a hukunta shi." Kallon tsaf Mahmud ya yi masa, yana jinjina ƙarfinsa. Bayan Mai gari ya sallame su, suna tafe a hanya ya ce. "Na lura da Mai garin nan tsaf, ashe duk burgagin banza yake yi. Ba abin da ya sani wallahi, kawai su yake naɗewa." Mudassir ya yi murmushi ya ce, "Ai kuwa sai dai su ya naɗe su, don idan ya shiga tawa gonar sai na yi masa naɗin da ya fi na huhun goro." Gabaɗaya suka saka dariya. Baba Sale shi da Uwale ba su suka dawo daga asibiti ba sai yamma liƙis, saboda bayan likita ya gwada Ɗan Bishir sai da aka ba shi gwaje-gwaje. Bayan sakamakon ya fito aka yi masa dressing, sannan aka rubuta musu magungunan. Duk soyayyar da Baba Sale yake yi masa haka ya danne shi da ana wanke masa, saboda likita ya tabbatar masa da matuƙar bai samu kyakkyawar kulawa ba komai zai iya faruwa, tun da har wurin ya fara ruwa yana ɗan wari. Likitan ya gargaɗe su sosai, wurin kula da tsaftar sabon gyambo koda ba na kaciya ba ne, sannan ya ce bayan kwana uku su koma a sake duba jikin nasa. Bayan sun koma gida, ko zama bai yi ba ya nufi gidan Bala wanzan. A ƙofar gida ya tsaya ya ce a yi masa sallama da shi, yana nan tsaye yaron ya dawo tare da wani ɗan matashin saurayi. "Kai Tasi'u, ina mahaifinka yake?" Baba Sale ya furta fuska babu walwala. Matashin da ba zai wuce shekara goma sha uku ba, ya rausayar da murya cike da neman tausasawa ya ce. "An tafi da Baba ofishin 'yan sanda ɗazu." Da sauri Baba Sale ya ce, "Ofishin 'yansanda fa? Me ya yi aka kai shi can?" "Ban san takamaiman abin da ya yi ba, amma an ce wai Idi Naira ya yi wa aska, kuma wai ana zargin yana da cutar ƙanjamau!" "La'ilaha'illa'illahu Muhammadur Rasulillahi, Sallallahu alaihi wasallam. Ɗan Tasi me kunnuwana suke zuƙo mini? Kada ka ce mini Ɗan Bishiriri ya kamu, wayyo Allah Tasi riƙe ni da ƙarfi duhu nake gani." Baba Sale ya yi maganar yana jin wata irin hajijiya tana yin ɗiban karan mahaukaciya da shi. Da sauri Tasi'u ya riƙe shi yana kiran sunansa da ƙarfi, "Baban Ɗan Bishir lafiya." A hankali Baba Sale ya ɗago duk da ba ya gane abin da Tasi'u yake faɗa sosai ya ce, "Tasi'u maza kai ni ofishin 'yansandan." Kamar sabon ɗan maye haka suka tafi Tasi'u yana riƙe da shi, don har suka ƙarasa wani irin layi yake yi idanunsa suna yi masa gizo. Su Baba Sale suna zuwa, suka samu Bala Wanzan a tsaye yana bayani. "Wallahi tallahi yallaɓai ban taɓa sanin Idi Naira yana da cutar abar nan ba, ni ko sunanta ba na son faɗa. Kuma babban tashin hankalina yaran da na yi wa shayi, a ranar da wannan tsautsayin ya afku. Domin su ne masu tasowa ba su mori ƙuruciya ba..." Wata irin ƙara suka ji gijiiiiiif Baba Sale ya faɗa ta saman kanta, saboda tun a bayanin farko da ya ji Bala wanzan yana yi, ya ji ƙafafuwansa ba za su iya ɗaukarsa ba. Kalaman Bala na ƙarshe suka sa ya ga wani baƙin duhu ta lulluɓe idonsa, numfashinsa ya ɗauke. "Subhnallah! Waye wannan? Lafiya?" Wani kurtun ɗansanda ya ƙarasa kansa yana tambaya. Tasi'u ne ya yi musu bayanin abin da ya faru tsakaninsa da Baba Sale, har zuwansu cikin station ɗin. Ruwa aka ɗebo aka zuba masa, a hankali ya farfaɗo yana daga kwance yake kallon mutane ɗaiɗai. Ya yunƙura a hankali ya zauna sai a lokacin komai ya shiga dawo masa. "Yallaɓai Ɗan Bishir, kun bincika mini Ɗan Bishiriri." Wani Sergent da ya fahimci Baba Sale, ya dubi Bala Wanzan ya ce, "Kai Wanzan ka yi wa yaron wannan mutumin kaciya ne?" Da yake a lokacin an mayar da Bala cikin cell, yana daga ciki ya ce. "Eh na yi masa yallaɓ..." Tun Bala bai gama magana ba Baba Sale ya sake sumewa a wurin, haka suka sake zuba masa ruwa ya sake farfaɗowa. Sai dai su kansu abin da ya fi ɗaga hankalinsu, yadda Baba Sale yana farfaɗowa zai sake suma. Har sun lura ko ya farfaɗo ba ya zama cikin hayyacinsa. Don haka suka tattarashi hankali a tashe suka yi asibiti da shi, sai bayan sun je suka saka Tasi'u ya yi musu rakiya har gida aka sanar da Uwale da su Baba Ibrahim halin da ake ciki. Tun da suka fito daga asibitin yake zabga sauri, cikin sassarfa ta rufa masa baya ganin ya fara yi mata nisa ya sa ta fara ƙwala masa kira. "Masoyi! Masoyi don Allah ka jira ni saurin me kake yi kamar za ka tashi sama." "Ya muke da jirgin sama? Na ce ya muke da shi?" Baba Labaran ya furta a zafafe. Sororo ta yi tana kallonsa don har tsoro-tsoro ta ji, ganin yana yi mata faɗan da ba ta saba gani a tattare da shi ba. Hasali ma ba ta ga abin faɗa a maganarta ba. "Asibiti na uku kenan a yau muna zuwa suna yi miki gwaji, amma duk maganarsu ɗaya kamar haɗin baki. To magana ta gaskiya na fi son mace a haihuwar fari, saboda magaji nake nema. Haka kawai duka asibitocin sun ce mace suka gani. Wallahi da sake an ba wa mai kaza kai." Da mamaki ta dube shi ta ce. "Da sake fa ka ce Masoyi? Shin butulci za ka yi wa uabangiji ne? Mutane nawa ne suke neman haihuwar ba su samu ba, mace ko namiji mai albarka ya kamata ka roƙa." Maimakon ya ba ta amsa sai kawai ya saki tsaki ya yi gaba yana faɗin. "Kanki ake ji, ni na gama faɗar ra'ayina." Daskarewa Rahinatu ta yi, ta ɗora hannunta a kan ƙaramin cikin jikinta da bai fi wata uku da satika ba. Cikin sanyin murya ta ce. "Dama duk soyayyar da mutumin nan yake yi mini ta fatar baki ce? Haƙiƙa Labaran ya cika butulu." Daga haka ta fara takawa a hankali, ta rufa masa baya tana jin zuciyarta na suya. Damuwa haɗe da tarin ayarin tunaninnika ne suka cunkushe masa kwanya, saboda Indo da su Hansatu sun nemi mayar da shi kamar mahaukaci. Don da sun kalle shi sai kowacce ta gimtse fuska, yana bada baya sai su kwashe da dariya. Rumfar Tsalha mai kayan miya nufa, yana zuwa ya yi sallama amma babu wanda ya amsa masa. Kamar haɗin baki, lokaci ɗaya mutanen cikin rumfar suka watse . Turus Yaya Inu ya yi, yana shirin magana ya ji Tsalha ya ce, "A gaskiya malam Inusa ka dakata da zuwa cikin rumfata, saboda ka da ka kawashe mini albarkar cinikayyata. Ba zan ɓoye maka Inusa ka san dai ni abokinka ne, maganar haihuwar zabiyar nan fa ya karaɗe ciki da wajen garin nan don haka ka yi hattara." Daga haka Malam Tsalha ya koma kujera ya zauna yana haɗe rai, don kada Yaya Inu ya samu fuskar zama. Kamar zakaran da aka tsamo daga cikin ruwa haka Yaya Inu ya fito ya nufi hanyar gida, tunanin Zuly matashin kai ce ta faɗo masa. Ya saki murmushi ya nufi ƙofar gidansu. Ƙaramar wayarsa ya ciro ya kira ta, ba a ɗauki lokaci ba ta fito tana taunar cingam. "Haskena ashe kaine da yamma haka?" Yaya Inu ya saki murmushi ya ce, "Takanas na shiryo na zo na ganki domin na huce takaicin zuciyata, saboda ke kaɗai ce hasken da ke yaye duhun da ke ɗanfare a ciki." Sai da ta hura kwai da cingam ta ce, "Wani zance nake ji yana tashi, wai an haifar maka zabiya 'yan gidanmu har sun fara bala'i. Ni kuwa na ce duk bala'insu ba zabiya ba, ko rabi mutum rabi aljan aka haifa maka babu wanda ya isa ya han ni aurenka." Farinciki ya sa ta Yaya Inu ya zaro rafa kuɗi har dubu goma ya miƙa mata. "Ki sha lemo da wannan, masoyiyata kuma hasken zuciyar Inusa." Alewa ta buɗe ta wurga a baki ta tsotsa, sannan ta zaro ta miƙa masa cike da kissa. Cikin so da ƙauna Yaya Inu ya karɓi alewar, ya jefa a baki ya yi mata sallama. Yana gab da shiga gida ya hango wani mai magani, yana tafe da wata ƙatuwar Mp3 da wani faffaɗan kwando mai ɗauke da magungunan maza a ciki. "Ina mai matsalar kuzari? Ina namijin da ya rako maza? To ya hanzarta ya zo ga adamalmala. Maganina rabo ne, maganina sa'a ce. Alhaji sai mai tsananin rabo ne zai dace na ba shi, ina mazan da basir ya jima da yi musu illa? Alhaji ba ka nisan zango wurin tuƙa sitiyarin mota? Don Allah ka zo, ga mai adamalmala ya dawo. Idan na bar garin nan ba zan dawo ba, maza kaɗai nake ba wa magungunana domin na fi kishinsu a kan mata. Alhaji ko Malam kada ka ji kunyar karɓa, indai matsalarka a ɓangare iyali ne ta kau. Sabon aure za ka yi ne? Ko kuwa ka rasa gane kan matanka ne? To maza gangaro ka karɓa sadakar ƙalilance, ni dai ba na rowa domin burina na kankaro mutumci a wurin maigida." Yaya Inu ya tsaya a jikin bishiya ya yafito shi da hannu, Mai maganin ya ƙarasa wurinsa adaidai lokacin Na Balaraba ya ƙarasa ta wurin zai wuce. "Kai wa nake gani kamar Gambo, ko idanuna ne?" Cewar Gambo. Mai maganin ya ɗago yana kallon Na Balaraba da sauri ya ce, "Kai! Wa nake gani kamar Na Balaraba? Dama rai kan ga rai?" Yaya Inu ya washe baki, "Na Balaraba ka san shi ne?" Na Balaraba ya furta, "Na san shi farin sani, yanzu ne dai zumunci ya zama yanda ya zama, shekara biyar zuwa shida rabona da shi." Yaya Inu ya washe baki ya ce, "Ka ce faɗuwa ta yi daidai da zama, dama kiransa na yi zan sayi magani." Mutumin tun da ya yi tsaye yake ƙarewa Yaya Inu kallo, har sai da gabansa ya faɗi. Amma jin Na Balaraba ya ce ya san shi ya sa ya saki jikinsa. "Haba ba ka da damuwa Inusa, ka sayi maganinka wannan da kake gani ba na shakku a kansa." Yaya Inu ya nuna wani magani ya ce yana son saya, Mai maganin ya yi zaraf ya ce. "A'a mai gida bari na ba ka wannan, ai wannan shi ne gagara-badau an buga da kai an barka." Ya ƙarasa maganar yana miƙa masa wata roba ƙarama ya ɗora da cewa. "Yanzu kana komawa gida tun da magariba ta ƙarato ka shafa shi, sai bayan minti talatin ka wanke da ruwan ɗumi. Ka zuba wa sarautar Allah ido za ka ba ni labari idan na sake dawowa." Jiki yana rawa Yaya Inu ya zaro kuɗi ya biya. Bayan Mai maganin ya tafi Baba Ado da yake gefe ya ce masa. "Yanzu Allah Yaya, ba za ka raba kanka da gabzawa kanka waɗannan magungunan barkatai ba? Haka kawai maganin kare da doki kowa na ka ne, ba ka duba inganci ko ka je wurin masu magungunan gargajiya waɗanda suka san kansu ka saya..." A sheƙe Yaya Inu ya katse shi. "Kai dakata kada ka yi mini rashin kunya, tuzurun banza da wofi. Wai har da su kaza a cin danƙo? Kai da ko arzikin auren ba ka samu ba, shi ne har za ka zauna kana yi mini fi'ili? Tun da kai 'yan mata aljanu sun gama tsuƙe jijiyoyin jikinka, ai sai ka bar masu raya sunnar Annabi su yi. Da uwar kuɗina nake saya babu wani ƙato da yake saya mini, don haka kada ka sake shiga hurumina." Yaya Inu yana gama magana ya shige gida a fusace. Yana zuwa ɗakinsa bayan ya huta ya shafa man kamar yadda Mai maganin ya faɗa masa, bayan kamar minti biyar da shafa man ya ji wani irin zafi yana ratsa shi. A ɓangare ɗaya kuma ya fara jin kamar ana tsoma wurin a ruwan zafi, ba shiri ya tashi ya rage dogon wandon jikinsa. Ya ɗauki muhuci yake firfita, jin azabar ta yi yawa ya sa yaYaya Inu ya faɗa banɗaki a guje har yana ɓari da kwanuka. Ƙirjinsa ne ya buga da ƙarfi, bayan ya shafo jikinsa ya ji tamkar ba na shi ba. Yaya Inu yana kai kallonsa, ganin sauyin hallitarsa ya sa wani wawan kuka ya kwace masa. Saura na ji wani ya yi wa Yaya Inu dariya.😂 Littafin kuɗi ne 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan no 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam🌚 [02/02, 15:02] Ameerah Adam🌚: *GIDAN LIKITOCI* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA BAƘAR DAULA AN YA BAIWA CE? ƊAN BA ƘARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page ɗin, ya taimaka ya yi mana Subscribe a youtube channel ɗinmu.👆🏻👆🏻👆🏻 SHAFI NA SHA BIYU Indo tana daga bakin murhu ta fara jiyo numfarfashin Yaya Inu da shasshekar kukansa, da farko ba ta yi tsammanin shi ba ne. Saboda hayaniyar yaran da ke kai-kawo a cikin gidan, sai da ta kasa kunne sosai sannan ta fahimci kukan babba ne. Mamaki ne ya kama ta, don su Hansatu gabaɗaya suna nan ballantana ta ce wata daga cikinsu ce. Miƙewa ta yi ta nufi hanyar banɗakin tana zuwa ta ji yana faɗin. "Kaico wannan wanne irin tsinanna magani da mai maganin ne? Ai kuwa ni da magani irin wannan har abada." Sai ya sake ɓarkewa da kuka. Ƙirjin Indo ya buga da ƙarfi, ta ɗan buga ƙofar banɗakin ta ce. "Mai gida lafiya kuwa? Me yake faruwa?" Daga can cikin banɗakin Yaya Inu ya ja majina ya ce, "Shigo ciki Indo." "Cikin banɗaki fa Mai gida?" Ta tambaya da mamaki. Yaya Inu bai sake tanka mata ba saboda yadda abin duniya ya dame shi, tambayar Indo ma haushi ta ba shi, don haka ya ja baki ya tsuke. Jin Yaya Inu ya yi mata shiru, ya sa Indo ta faɗa banɗakin gabanta yana faɗuwa musamman da ta tuna bai taɓa yin haka ba, kada ko wani abin ne ya same shi a ɓanɗakin ba ta sani ba. "Mai gida lafiya kake kuka a banɗaki?" Indo ta yi maganar bayan ta samu Yaya Inu har lokacin a tsugunne. "Indo na haɗu da wani iftila'i, wallahi ina cikin tashin hankali komai ya canza mini, al'amarin ya munana." Muryar Yaya Inu kaɗai da ta ji ce ta tabbatar mata da tabbas babu lafiya, ta sauke ajiyar zuciya ta ce. "Me ya faru dai yanzu?" Yaya Inu ya zauna a kan wani ɗan dandamali da suke zama su yi wanka, ya dubi Indo da shanyayyun idanunsa da suka yi mitsi-mitsi saboda kukan da ya sha ya ce. "Ku je ku kori yara ɗaki, ki kira mini su Hansatu ku mayar da ni ɗakina. Saboda su kansu jijiyoyin ƙafafuwana sun yi sanyi, ji nake kamar da na wani aka zuba mini ba nawa ba." Jin haka ya sake ɗaga hankalin Indo, ta ja ƙafafuwa jiki a sanyaye ta samu Hansatu da ke ɗinkin mahuci ta furta. "Mai gida fa babu lafiya Hansatu." Da yake har lokacin Hansatu cike take da haushin Yaya Inu, kai tsaye ta ce. "Allah Ya sawaƙe, kowa ma fama yaka da rashin lafiya." "Wannan fa ba irin rashin lafiyar yau da gobe ba ce, don ya ce a tura yara ɗaki mu je mu ɗauke shi mu mayar da shi ɗakinsa." Furucin Indo ya sa Hansatu zaro ido, a razane ta ce. "Shi Mai gidan za mu ɗauka mu kai ɗaki? Innalillahi wa inna'ilahir raji'un!" Da sauri Hansatu ta miƙe, kowacce ta shiga ƙoƙarin tura yaranta ɗaki. Kafin wani lokaci tuni yaran sun shige ciki, Hansatu ce a kan gaba sauran suna biye da ita. A inda Indo ta bar Yaya Inu, a can suka koma suka same shi. Yana zaune ya haɗa kai da gwiwa. Abin da ya sake ɗaga hankalin matan nasa, ganin hawaye shaɓe-shaɓe a fuskarsa yana ambaliya. "Mai gida! Wai me yake faruwa haka?" Hansatu ta jefa masa tambaya a rikice, Yaya Inu da muryarsa ta shaƙe can ciki ya ce. "Ku yi tara-tara ku kai ni ɗaki. " Da yake Yaya Inu ba mutum ne mai ƙiba ba, ya sa su ukun suka haɗu suka ɗaga shii suka yi ɗaki da shi suka kwantar a katifa. Zani suka janyo suka rufe masa jikinsa, suka yi carko-carko kowacce tana saƙa da warwara a cikin ranta. "Ɗazu gabanin zan shigo gida na haɗu da wani matsiyacin mai magani, bayan na saya ya ce mini na shafawa ne. Ina shafawa kun ga abin da ya faru!" Yaya Inu ya ƙarasa maganar yana bankaɗe zanin rufar da suka rufa masa, wannan karon hankalinsa ya fi tashi don ya lura da ci bayan da yake ta samu a jikinsa. "Innalillahi! Malam mene ne haka a tsotse kamar hanjin ligidi? Wannan wane irin magani ne haka ka shafa?" Hansatu ta faɗa a ruɗe. Indo ta jinjina kai ta ce, "Gaskiya wannan abin akwai ayar tambaya, amma babu lambar waya a jiki da sai ka kira shi." Yaya Inu ya yi zaraf ya ciro robar maganin, cikin sa'a ya ci karo da lambar mai maganin. Yana kira bugu biyu ta yi ya ɗauka, nan take ya zayyane masa duk abin da ya faru. Daga can ɓangaren ya ce. "Allah sarki Mai gida, na manta ai tun farko ban yi maka wannan bayanin ba. Amma kada ka damu wannan ba komai ba ne, dama a rana ta farko dole za ka fuskanci haka. Amma zuwa gobe war haka komai zai dawo daidai." Yaya Inu da kamar zai yi kuka ya ce. "Yanzu har sai na kai gobe war haka? Yanzu fa ƙarfe takwas na dare, haka zan yi ta zama a zuƙe?" "Wannan ba wani abu ba ne, idan har maganin ya game duk jikinka, muna nan da kai sai ka nemo ni ka kawo mini kwastoma saboda kyawunsa." Kalaman mai maganin kenan da suka ɗan ƙara wa Yaya Inu ƙwarin giwa. Larai da ke riƙe da haɓa ta jinjina kai ta ce, "Magana ta gaskiya Mai gida lamarin nan fa ya ba ni mamaki, ba yau ka fara amfani da irin wannan maganin ba fa. Wallahi akwai dai magana, ka tuhumi tsakaninka da Ubangiji gaskiya." Yaya Inu ya zaburo ya ce, "Ke Larai me kike nufi?" Larai ta murguɗe baki gefe ta yi ƙasa da murya ta ce, "A'a toh, ga dai abu ya bayyana nan tun da har ka haifo zabiya. Ƙila fushin da Allah Yake yi da kai ne ya jarabce ka ta wurin, ba sai a ga ta saɓon Allah ba. Tun da Ubangiji da kansa Ya yi hani da kusantar mace tana cikin jini..." "Na rantse da Allah zancanki yana hanya Larai, kai duniya jama'a akwai darussa a rayuwar nan fa." Indo ta furta tana jinjina buwayar Ubangiji. Kalaman su Larai ba ƙaramin ɗaga hankalin Yaya Inu ya yi ba, yana daga kwance ya tashi zaune ƙirjinsa yana bugawa ya ce. "Na rantse da girman Allah ban taɓa aikatawa ba, Allah ne shaidata. Na shiga uku Hansatu ku taimaka mini, wallahi ina cikin wani yanayi." Larai ta yi hanyar waje ta ce, "Wallahi Mai gida ni kam a yanzu ma tsoron taɓa ka nake yi, kada na je ni ma wata hallitar tawa ta tsotse." Daga haka ta yi ficewarta. Kuka Yaya Inu yake iya ƙarfinsa, ya janyo zanin Hansatu yana ɗago mata hannu. Ba ƙaramin tausayi ya ba ta ba, saboda duk abin da zai saka Yaya Inu kuka ba ƙaramin tashin hankali ba ne. A sanyaye Hansatu ta zauna ta ce, "Mai gida! Yanzu mene ne abin yi?" Yaya Inu ya wara mata hannu alamar ba shi da mafita ya furta, "Sai abin da kika ce Hansatu." Indo ta gimtse dariya ta yi ficewarta, don ita ma a wani ɓangaren ya fara ba ta tsoro. "A'a kai ne mai faɗa aji ai, tun da kai rana ta ƙwacewa. Laifi dai ka riga da ka aikata, kawai dai ka yi ta isgifari. Sannan sai mu zuba wa sarautar Allah ido, zuwa washegari kamar yadda Mai maganin ya faɗa." Wata sabuwar soyayyar Hansatu ta mamaye shi, ya riƙo hannunta ya ce. "Hansatu dama haka kike sona, ke kaɗai ce ba ki guje ni ba a cikinsu." Hansatu ta yi wa Yaya Inu ƙuri da ido, tana tuna soyayyarsu tun ta saurayi da budurwa. Sannan ta tuna irin cin kashin da yake yi musu, musamman na ranar ta ce. "Ai wannan kalaman da kake faɗa na fatar baki ne ranka shi daɗe, mu da ka ce fuskokinmu kamar na sumammun birarrika? A'a za ka yi aure ai, ni ma abin da ya sa ka ga na tsaya a kanka, ina duba darajar da ka ba ni a cikin matanka da ba ka taɓa sakina ba. Tun da ni ma ka mutumta ni a matsayina na uwar gida." Shiru Yaya Inu ya yi kunya ta lulluɓe shi, Hansatu ta cigaba ɗebe masa kewa sai da ta fara jin bacci sannan ta wuce ɗakinta. Dai-dai da abincin dare Yaya Inu da ƙyar ya iya ci, haka ya kwana cikin tunani da bacci mara daɗi yana miyagun mafarkai kala-kala. Lokacin da su Uwale suka samu labarin abin da ya faru ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba, abin sai ya haɗe mata goma da ashirin ga halin da Ɗan Bishir yake ciki, da zargin da ake yi ya kwashi cuta mai karya garkuwar jiki ga kuma halin da mijinta yake ciki. Da yake dawowar Baba Ibrahim kenan daga wurin aiki, ko gidan bai shiga ba ya ce wa Uwale ta koma shi zai je ya ji abin da yake faruwa. Kai tsaye ƙaramin asibitin gwamnati ƙauyen nasu ya wuce, a can ya samu Baba Sale ana yi masa ƙarin ruwa . Da yake an yi masa allurar bacci sai ya zauna a gefensa yana jiran tashinsa. Kusan zaman awa guda Baba Ibrahim ya yi, sannan Baba Sale ya buɗe idonsa. "Sannu Sale, ya jikin naka?" Baba Sale ya tashi zaune yana dafe kansa da ya yi masa nauyi, ya dubi Baba Ibrahim murya tana rawa ya ce. "Yaya ka ji abin da ya faru ko?" Ya gyaɗa masa kai ya ce, "Sale ina son ka saurare ni da kyau don Allah. Na farko dai kai musulmi ne, ka yarda da ƙaddara mai kyau da akasinta. Sannan ka san Ubangiji ne ya ba ka Ɗan Bishir, a lokacin da ba ka yi tsammani ba. Don haka kenan ko a yau Allah Ya yi niyyar ɗauke abinsa zai iya. To me zai sa ka kashe kanka a banza da wofi, ko ka janyo wa kanka ciwo ya kwantar da kai. Lokacin da na zo likitoci sun tabbatar mini ko a asibitin nan ka yi suma ya fi bakwai, don Allah ka kwantar da hankalinka. Yanzu ina son daga nan zan wuce na je na samu Bala Wanzan, da shi Idi Naira na ji yadda aka haihu a ragaya. Idan na ji ta bakinsu sai mu wuce asibiti ɗungurungum a yi haihuwa da hanji, amma babu yadda za a yi a dinga faɗar cuta da fatar baki ba tare da an tabbatar ba." Da sauri Baba Sale ya riƙo hannunsa ya furta. "Yaya zan bi ka, gara a yi komai a kan idona." Baba Ibrahim ya sake haɗai rai ya ce, "Idan ka san za ka yi mini hayaniya ko ka je kana sume-sume gara ka yi zamanka a nan." Cikin sauri Baba Sale ya girgiza kai, Baba Ibrahim ya yi wa lokitocin bayani sannan ya biya su kuɗin ruwa da alluran da ake yi masa; suka wuce Police station. Bayan sun gaisa Baba Ibrahim ya gabatar da kansa sannan ya ɗora da cewa. "Yallaɓai zuwa na yi domin na ji kan zancen abin da ya faru, idan da yuwuwar zuwa asibiti a yanzu sai mu wuce gabaɗaya." Sergent ɗin da ke tsaye ya buɗe wani file ya zaro takarda ya ce, "Alhaji wani mutum mai suna Malam Shehu mai doya shi ya kawo ƙarar Bala wanzan, yana tuhumarsa da cin zarafinsa bayan ya je ƙofar gidansa. Sannan laifin da Bala ya yi har da zagin ɗaya daga cikin ma'aikatanmu, abin da kuma ya sake dagula case ɗin zargin cutar HIV da ake yi wa Alhaji Idi Naira. Yanzu haka shi ma Idi ya kawo Malam Shehu wurinmu, a kan zargin yana ɓa ta masa suna da wannan cutar." Ajiyar zuciya Baba Ibrahim ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Yanzu za mu iya ganin Bala Wanzan ɗin?" "Gaskiya sai dai zuwa gobe idan Allah Ya kai mu." Ɗansandan ya furta. Babu yadda suka iya haka suka wuce gida, sai dai kaso talatin a cikin ɗari na damuwar Baba Sale ta ragu, saboda ya ji an ce Alhaji Idi Naira ya yi ƙarar Malam Shehu zai ɓata masa suna. Mai Yasin tun da ya saka 'Yar gwal a idonsa soyayyarta ta dawo masa sabuwa fil a ransa, haka a ɓangare ɗaya kishinta ya mamaye shi, yana jin tsanar Ɗanladi a ransa don dai kawai yana shakkarsa ne. Yana daga ɗakinsa ya hango ta, ta nufi banɗaki da buta a hannu shi ma ya yi zaraf ya ɗauki buta ya rufa mata baya. Tana shiga banɗaki za ta turo ƙofa ta ji mutum yana ƙoƙarin turowa, suna haɗa ido ta saki murmushi irin na 'yan bariki ta ce. "Mai Yasin namu, ashe a wannan lungun ka lafe?" Mai Yasin ya riƙo hannunta ya ce, "Ga ni kuwa kin gani, wai dama 'Yar gwal za ki iya auren wani namijin ba ni ba?" 'Lallai wannan gafalallan tsohon naka wasa ne.' Ta raya a ranta, amma a fili sai ta ce. "Ka da ka sake kallona a matsayin matar aure, saboda wannan auren nawa shi da babu duk ɗaya. 'Yar gwal ta auri Ɗanladi ne domin ta yi masa tatsar mai, idan ta kwashe albarkar aljihunsa sai ta ƙara gaba." "Sai da ke 'Yar kunama!" Mai Yasin ya yi maganar yana dariya, sannan ya yi ƙasa da murya ya ce. "Yanzu ni ya za ki yi da ni?" "A'a ka ji da tsohuwar da ka samu, idan fa muka bari suka san alaƙarmu na rantse da Allah ni da kai sai dai mu yi biyu-babu. Kawai mu cigaba da sabgarmu, kowa ya wawuri abin da ya wawura ko a fakaice ma dinga haɗuwa." Guntun tsaki Mai Yasin ya ja, ya ce. "Wa yake ta wata tsohuwa? Ƙila dai a rashinki yau na waiwayi haƙƙina a wurinta." 'Yar gwal ta saki dariya, sannan ta ce ya yi maza ya tafi don kada wani ya gansu. Bayan 'Yar gwal ta koma a tsakar gida ta ci karo da Laraba tana 'yar carafke, tana shiga ta ɗebo wankin rigunan mama da ɗan kamfai ta wurga mata a fuska. Tsaminsu haɗe da warin man bilicin ɗin da 'Yar gwal take shafawa ya bigi Laraba, ta ture su tana yamutsa fuska. "Ke! Wanke mini su yanzu, ina son su fita sosai." Da mamki Laraba take kallon ta. "Ko ba za ki wanke ba? Kika zubo mini ido irin na marasa tarbiyya kina kallo." Laraba ta tashi ta ɗaga wani wargajejen ɗan kamfai, sai kawai ta tuntsire da dariya. Tun tana dariya a tsaye har ta tsugunna, ta janyo wata warɓeɓiyar rigar mama ta ɗago ta ta sake kwanciya tana dariya. "Don uwarki dariya ma za ki yi mini? Wato ni za ki mayar 'yar iska?" Laraba ta tsagaita da dariya tana ɗan tsuke fuska ta furta. "Kambu... Kada ki sake zagin uwata tana ƙasa, ki zagi kowa nawa ban ta uwata wallahi. Ehe, ba dole mutum ya yi dariya ba wannan ai ya isa na yi hijabi da shi." "Rashin kunya za ki yi mini?" 'Yar gwal ta ƙarasa gaban Laraba a fusace. Laraba ta juya mata baya tana ɗago ɗankwalinta gaba ta ce. "Faɗa wa ƙeya ɗankwali ya ba ki amsa 'yan mata." Laraba tana juyowa 'Yar gwal ta wanke ta da mari, a hargitse Laraba ta ɗago za ta yi magana Ɗanladi ya ƙarasa yana faɗin. "Kin yi mini daidai sanyin zuciyata, wato har yanzu kina nan da iskancinki ko Laraba? Maza wuce ki kwashe su ki wanke kada ranki ya ɓaci." Idon Laraba ya yi ja saboda ɓacin rai, ta harari 'Yar gwal a hankali ta ce. "Allah Ya isa ban yafe..." Tun ba ta gama magana ba, kamar haɗin baki Ɗanladi da 'Yar gwal suka make bakinta, nan take bakin ya fashe amma a dole ta kwashe kayan, ta fara wanki saboda yadda Ɗanladi ya ciro belt zai zane ta da shi. Sai da ta yi wa kayan ruwa kusan huɗu kowanne 'Yar gwal tana cewa bai wanku ba, sai a na biyar sannan suka bar Laraba ta fara shanya a lokacin har an fara kiran sallar isha'i. Jin shirun Laraba ya yi yawa ya sa Inno ta fito daga sashenta, tana zuwa harabar ta ci karo da ita tana shanyar kaya su Ɗanladi suna tsaye a kanta. "Laraba me kike yi haka da daren nan?" Murya tana rawa Laraba ta ce, "Wanki." Inno ta ƙanƙance ido ta ce, "Mene ne wannan kamar ɗan diras? Ke wuce ciki mu je." Da sauri Laraba ta saki na hannunta ta wuce ciki, Inno ta dubi Ɗanladi rai a ɓace ta ce. "Ba baiwa aka sayo muku ba, tun da ba ka da mutumci haka matarka ma ba ta gaji arziki ba wallahi ba za ku mori Laraba. Mun kwana a gida ɗaya, amma ban da mutumci da za ku zo ku gaishe ni." Inno ta wuce sashenta a zafafe. Ran Laraba ya ɓaci sosai, ita kanta ta san a banza ma tana dafa mutum da ruwan jikinsa har ya nuna, ballantana sun taɓo ta da kansu. Don haka ta ci alwashin yadda suka azabtar da ita sai ta rama. Tun da dare ya fara yi Laraba ta fara zarya, tana saka da warwarar abin da za ta aikata, tana wucewa ta ga 'Yar gwal a ƙofar ɗaki tana dama kunun gyaɗa. Da sauri ta faɗa ɗakin Inno, a can drower madubi ta buɗe ta ciro wani maganin hawan jinin Inno, mai saka bacci ta ɓallo guda takwas. A ƙa'ida Inno ɗaya take sha a wuni guda, kuma a hakan ma bacci yake saka ta sosai. Bayan jininta ya sauka ne aka sauya mata wani, don haka ta daina shansa. A cikin ƙaramar farar leda ta zuba su ta ɗebi ruwa kaɗan ta zuba, sai da ya narke sannan ta fita cikin sa'a kuwa ta ga 'Yar gwal ta shiga ɗaki. Da sauri ta matse maganin a cikin jug ɗin kunun, ta juya cikin sauri ta bar wurin. Tana laɓe a bakin ƙofar Inno tana leƙe ta ƙofa, ta ji lokacin da 'Yar gwal ta ɗauka ta shiga ɗaki. Zuciyar Laraba ƙal da haye katifa ta kwanta, tana shirya irin muguntar da za ta yi musu. A fili ta saki dariya, Inno ta wurga mata harara sannan ta ɗauki furar Mai Yasin ta nufi ɗakinsa. Saboda Laraba ta taki mugunta haka ta zauna tunkur, har kusan ƙarfe ɗayan dare. Sai da ta fito cikin sanɗa zuwa ƙofar ɗakin Mai Yasin, ta kasa kunne ta ji munsharin Inno da Mai yasin sannan ta saɗaɗa ta fice daga sashensu ta isa ɗakin Ɗanladi. A yadda ta fahimta sun jima da yin bacci, don lokacin da ta ɗaga labulen ɗakin a ƙasa ta gansu sun ɓingire suna bacci, 'Yar gwal tana jingine da bango da kofin kunnu a hannunta. Sai da Laraba ta saka ɗankwali ta rufe fuskarta, sannan ta ɗauki sauran kunun ta juye mata a fuskar. Wani tunani ne ya faɗo mata ta fita da sauri, ta ɗauko jarkar ruwa irin ta 'yan-ga-ruwa ta tuttule musu ruwan gabaɗaya a ɗakin. Ta janyo galan ɗin man gyaɗarsu ta sheƙa a ƙafafuwan 'Yar gwala da Ɗanladi, ta kai jarkar man ta saƙala mata a hannu. A hankali ta lalallaɓa ta ja ƙafar Ɗabladi sai ta ji ya tafi yaraf, daga shi da ma sai gajeren wando da singlet. Ta ɗauko ƙaton omonsu ta zazzage masa a jiki zuwa fuska, har ta je za ta fita ta hango belt ɗinsa da sauri ta ɗauka ta fara zabga musu ɗaya bayan ɗaya. Sai da ta ga sun fara motsi sannan ta fice daga ɗakin da sauri, ta nufi ɗakin Inno. Tana zuwa ta shige bargo ta kwanta tana dariyar ƙeta, babu jimawa bacci ya yi awon gaba da ita. Mai Yasin tun da ya sha fura suna hira da Inno ya ga bacci ya ɗauke ta, bai tashe ba don shi ma ba son tafiyarta ɗakinta yake ba. Yana gama shan furar babu jimawa shi ma bacci ya ɗauke shi, ba shi ya farka ba sai kusan uku saura na dare. Inno cikin bacci ta fara jin alamun ana lalubar mamanta, da yake bacci ya sha kanta cikin magagi ta ce. "Laraba wani wulaƙanci ne kike ji da shi haka?" Shiru Mai Yasin ya yi ya ci gaba da sabgar gabansa, Inno ta gyara kwanciyarta jin har lokacin ba a daina lalubarta ba, kuma har lokacin idonta a rufe yake da sauran bacci a kanta ta furta. "Laraba zan ci mutumcinki fa." Mai Yasin ya kashe murya, shi a dole yana son lallamar Inno don kar ta ba shi matsala ya ce, "Wannan Ɗanlami ne ba Laraba Innota." Firgigit Inno ta yi ta ware idonta, a rikice ta ce. "Malam mene ne haka?" Mai Yasin ya kashe mata ido ɗaya ya ce, "Haba Innoniyata, kamar wata 'yar sha uku duk kin firgice. Sharuɗɗan aure ne fa nake son cikawa." Inno tana shirin ture Mai Yasin ya murɗe 'yan hannuwanta, ta yi mamaki matuƙa yadda ta ji ta kasa kataɓus. Don ba ta taɓa tsammanin yana da ƙwari haka ba, Inno babu yadda ta iya haka ta zubawa sarautar Allah ido. Tun tana tsine wa Mai Yasin a zuciyarta har ta fito fili, don shi da ita sun yi yarjejeniyar auren ɗauko mini buta suka yi. In Shaa Allahu wannan shi ne shafi na biyun ƙarshe, gobe zan gama free pages. Littafin kuɗi ne 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan no 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam🌚 *GIDAN LIKITOCI* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA BAƘAR DAULA AN YA BAIWA CE? ƊAN BA ƘARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page ɗin, ya taimaka ya yi mana Subscribe a youtube channel ɗinmu.👆🏻👆🏻👆🏻 SHAFI NA SHA UKU Inno har gari ya waye ban da hawaye babu abin da take yi, da ta kalli Mai Yasin ban da kallon tsana babu abin da yake wurga masa. Shi kuma Mai Yasin ban da juyi a katifa babu abin da yake yi, saboda wani bacci da ya samu mai cike da kwanciyar hankali. Jin shasshekar kukan Inno ce ta farkar da shi, ya ɗago cike da shauƙi ya ce. "Innota! Haba Innota, me ya sa kike son ɗaga mini hankali da farar safiya haka? Maimakon ki zo na ninke ki a bargo, mu cigaba da baccin cikar fariciki amma sai ki ɓa ta ranki a banza. Ko me na yi miki ai soyayya ce, haba Innaniyota!" Inno ta share hawaye, a hankali Mai Yasin ya dinga fasa mata kai yana yabonta tare da nuna mata zallar soyayya. Saboda ya lura da abin da Inno ta fi so, ya kuma fi saurin sace zuciyarta da shi. Nan take ta saki jikinta, sannan ta miƙe za ta fita da sauri ya ce. "Inno me za ki fita ki yi, kina fama da kanki?" Inno ta jingina da jikin ƙofa ta ce, "Abin kari zan haɗa mana..." "Allah Ya sawaƙe ki fita ki haɗa kayan abinci, da kanki kina fama da ɗanyan jiki." Murmushi Inno ta saki har cikin ranta ta ji daɗin kulawar da yake ba ta. "Bari ki ga na je wurin Sule mai shayi, na kaso mana dubu biyar ɗin nan." Da sauri Inno ta ce, "Malam dubu biyar fa?" Cike da son nuna burga Malam Ya ce, "Dubu biyar ɗin banza, ni duk yawan kuɗi ba kin fiye mini su ba Innota." Kan Inno ya ƙara girma, za ta fara magana wayar ta ta fara ringing. Malam ne ya miƙa mata, sai da ta ɗauka ta kai kunnenta sannan ta gane muryar aminiyarta ce, kasancewar sabuwar wayar da Fadil ya sauya mata, ba a iya saving da shaidar mota ko jirgi da a baya ake yi mata. "Assalamu Alaikum, Hajiya Goggo barka da safiya." Daga can ɓangaren Goggo ta ce, "Wa alaikissalam, barka dai amarsu. Inno ga mu nan a tasha yanzu motarmu za ta taso." Cike da farinciki Inno ta ce, "Kai amma dai gaskiya kin yi mini bazata, Allah Ya kawo mini ke lafiya." Goggo ta amsa da Amin sannan ta furta, "To agaida mana angonmu kafin mu zo, don na ji muryarki ta sauya amarci ya karɓe ki tsohuwar nan." Inno da Goggo suka saki dariya lokaci ɗaya, daga haka suka yi sallama. Ba tun yau ba Mai Yasin yake jin labarin Goggo a wurin Inno, a lokacin aurensu ma ta so zuwa wani jikanta ya rasu don haka ta ɗaga zuwan sai daga ba ya. Tun bayan fitar Laraba sama-sama suka dinga yunƙurin buɗe idonsu, amma fatar idanunsu ta yi wani irin nauyi don haka suka gagara buɗewa. Sai dai wasu abubuwan da suka faru gani suke yi kamar a cikin mafarki ne. Ɗanladi da 'Yar gwal ba su suka farka ba, sai kusan ƙarfe tara na safe. Ɗanladi ne ya fara farkawa ya ji jikinsa duk ya yi tsami, a hankali ya buɗe idonsa ya ci karo da ɗakin ya yi jaga-jaga. Ransa ne ya ɓaci da ya ci karo da mai ya yi luntsum a tsakar ɗakin, ga jarkar man a hannun 'Yar gwal ta yi share-share a ƙasa tana munshari. A fusace ya ƙarasa wurin da take yashe, ya tsinka mata mari wanda ya sa ta miƙe tsaye a gigice. "Tsabar iskanci dama ba ki daina shaye-shayen da na hana ki ba? Dubi irin rashin mutumcin da kika yi mana?" Da mamaki 'Yar gwal take bin jikinta da ɗakin da kallo, ta dafe kumatu ta ce. "Ni ka mara?" A harzuƙe Ɗanlami ya ce, "An mare ki ko za ki rama? Da yake har lokacin maganin bai gama sakin ta, ta yi luuu da idanu ta furta. "Wallahi ba ka mari banza ba sai na rama." "Ashe kuwa zan yi miki ɓarin makauniya, tsabar rashin mutumci in saka sama da dubu goma sha na sayi jarkar mai ki rubar a ƙasa. Wallahi yau sai kin gane ke ƙaramar ƙwaya kike sha." A zabure 'Yar gwal ta miƙe tsaye tana kaɗa ƙugu ta ce, "Ƙwayar ma ai mataki-mataki ce, billahillazi sai na nuna maka ko a gidan giya akwai babba. Kai ba wani shege fa." Daga haka ta cakumi wuyan Ɗanladi, ganin haka ya sake ɓa ta ransa don haka ya shiga kai mata duka ita ma tana ramawa. Kasancewar ƙarfin namiji da mace ba ɗaya ba, ya sa 'Yar gwal ta fara laushi. Wannan ya sa, ta ɗauki wani burugali a bayan ƙofa ta ranƙwala masa a goshi, nan take goshinsa ya yi wani tsororo ya kumbure suntum. Azaba ta sa Ɗanladi ya kai mata naushi a ba ki, sai ga bakin 'Yar gwal ya fashe har haƙorinta ɗaya na gaba ya faɗo. Kafin wani lokaci tuni bakin ya kumbure sai sheƙi yake yi. Sai da suka jigatu don kansu sannan suka faɗi gefe, ba a ɗauki lokaci mai tsayi ba. 'Yar gwal ta fara tattara kayanta tana kuka, hakan ya sa jikin Ɗanladi ya yi sanyi. Ya tsugunna a gefenta cikin tattausan lafazi ya furta. "Me kike yi haka 'Yar gwal?" Ba ta tanka masa ba, ta cika akwatinta, ta fizgi mayafi ko wanke fuskarta ba ta yi ba saboda ɓacin rai za ta fita. Da sauri ya janyo ta, ta faɗo jikinsa ya ce. "Haba 'Yar gwal, don Allah ki yi haƙuri kin san dai ba zan iya rabuwa da ke ba. Wallahi ɓacin ran abin da kika yi mini ne ya sa haka, ke ma kin san ba ki kyauta ba." Har a ranta ta ji daɗi saboda ita ma dama ba ta yi niyyar tafiyar ba, ta yi hakan ne don ta tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro. Ta janye hannunsa fuska a haɗe ta ce, "To ai gara na ba ka wuri tun da hakan shi ya fiye maka, da ka dinga tuhuma ta a kan abin da ba ni da masaniya." Shiru ya yi yana nazari, don shi ma a iya saninsa dai 'Yar gwal ta daɗe ba ta shaye-shaye, kuma ko ta bugu ba ta irin wannan ɓarnar. "Yar gwal jiya bayan mun sha kunu me ya faru?" Ba ta ba shi amsa ba, ta taɓe baki. Wani irin tsoro ya kama shi, don ya ga jikinsa da na 'Yar gwal duk sun yi ruɗu-ruɗu. "An ya ɗakin nan babu aljanu kuwa?" Ya yi tambayar cikinsa yana kaɗawa, 'Yar gwal ta ce, "Ah to gidanku ne dai, ka fi kowa sanin yadda yake ai." Ɗaladi ya jima yana rarrashin 'Yar gwal, daga ƙarshe dai ta haƙura. Shi da kansa ya shiga gyaran ɗakin, don 'Yar gwal cewa ta yi ba za ta taɓa komai ba. Washegari tun da farar safiya Zuly matashin kai ta dokowa Yaya Inu waya, cike da kissa take yi masa kalaman tausasawa domin tana son sake karɓar kuɗi a wurinsa. Yaya Inu duk damuwar da yake ciki lokaci ɗaya ta yaye, ya miƙe a hankali ya saka wata jallabiyyarsa ya fice. Ƙofar gidansu Zuly ya ƙarasa, ya kai mata dubu goma sha biyar kamar yadda ta buƙata. Ta kashe masa ido ta ce, "Yanzu fa nan da awa biyu zuwa uku na zama taka. A gaskiya duk macen da ta yi sa'ar samunka ta yi dacen miji." Yaya Inu ya saki murmushi ya ce, "Waɗannan kalaman na ki suna sake birkita ni Zulyta. Yanzu dai bari na wuce gida na sallami waɗancan mutanen, na fara shirin tafiya ɗaurin aure." Zuly ta ɗan yamutsa fuska ta ce, "Tun yanzu baby?" Yaya Inu cikin tausasa lafazi ya ce, "Sai yadda kika ce." Zuly ta yi wani far da ido ta ce. "Ni na isa, Allah Ya taimake ka aje ayi yadda ya dace. Don na fi son mijina ya zama adali." Yaya Inu sai da ya yi da gaske sannan ya tafi daga wurin Zuly, yana tafiya ta wuce gidan Hajiya zuma mai magungunan mata. Ta kai mata dubu biyar cikon kuɗin magungunan da take bin ta. Saboda ba ƙaramin haɗi ta yi mata ba, don ta ci alwashin kafin ta fito daga gidan Yaya Inu sai ta tatike shi tsaf, domin ba da niyyar zama ta je ba. Don haka ta je aka saka mata inplan, don ma kada ta ɗauki ciki. Tun da hantsi ya yi suka ga shiru Mai gari bai fito ba, Azeema ce ta shiga ɗakin saboda dama girkinta ne. A zaune ta samu Mai gari ya haɗa kai da gwiwa yana hawaye, hakan ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya yi ba. Jiki a sanyaye ta zauna kusa da shi ta ce, "Ranka shi daɗe lafiya? Me yake faruwa da kai a farar safiyar nan kake kuka?" Mai gari ya ja majina yana sharce hawaye, ya saka hannu ya dafe saitin zuciyarsa da yake bugawa da sauri ya ce. "Azeem ina cikin wani yanayi mara musaltuwa, zuciyata tana cike da muradin da ban san lissafin da mutane za su lissafa a kaina ba." Azeema ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Tun shekaran jiya na fara lura da sauyinka ranka shi daɗe, amma na yi maka tambayar duniya ka ce mini babu komai. Mene ne a zuciyarka da yake damunka?" Kai tsaye Mai gari ya ce, "So ne, so ne yake nuƙurƙusar zuciyata kuma ban san a lokacin da ya yi mini kamun kazar kuku ba. Yanzu haka na takure kaina a ɗakina ne, saboda kada na fita fada zuciyata ta fisge ta zuwa gidansu." "Wace ce ita?" Ta wurga masa tambaya. "Laraba ce Azeema, wallahi zuciyata har wani tartsatsi take a kanta." A razane Azeema ta ce, "Laraba tsidigu dai? Eh lallai dole ka ce jarabta. Ranka shi daɗe ko dai mafarki kika yi, ka rasa wacce za ka so sai waccan sheɗaniya hatsabibiyar yarinyar Lara..." Ba ta gama magana ba, Mai gari ya gwaɓe mata ba ki ya fashe. "Kada ki sake danga ta mini Laraba da shaiɗanu, idan ba haka ba ranki zai yi mummunan ɓaci." Tsoro ne ya kama Azeema, jikinta a sanyaye ta fice daga ɗakin domin ba ta tantama akwai ciwon da ya samu mijin nasu. Kamar yadda suka tsayar da magana, a washegari Baba Ibrahim da Baba Sale har da Ɗan Bishir suka sake komawa police station. "Alhaji na yi mamaki ƙwarai da na ji an ce case ɗin naka ne? Me ya yi zafi haka?" Baba Ibrahim ya tambayi Alhaji Idi Naira. Alhaji ya furzar da iska mai zafi ya ce. "Wani zance ne ya fara yawo a cikin garin nan, wai ina ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki Dr, ni kuma a iya sanina ba ni da ita. Da na bi diddigin maganar, sai aka ce an samo zancen daga wurin Malam Shehu, don haka na kawo shi ƙara. Sai bayan na zo na ci karo da Bala wanzan a nan , ni kuma ba zan laminta ba har sai an bi mini haƙƙina. Daga nan ma kotu nake son a tura mu." Malam Shehu ya yi fiƙi-fiƙi cike da tsoro ya ce. "Wallahi tallahi ni ma ba ni na faɗa, jita-jita na ji ana yi kuma sai aka yi sara a kan gaɓa. Ni kuma ina ganin kamar Bala wanzan ya sani, amma ya munafurce ni." Bala wanzan ya zaburo yana faɗin, "Amma ai kai ka kawo hukuma har gida suka tafi da ni, ka ce na yi maka aski wai kai ma kana zargin ka kamu." Jin hayaniya tana neman kacamewa wani Sergent ya buga musu tsawa yana faɗin. "Ba ma son hayaniya, kai Bala tun da kai aka fara kawowa ka yi musu bayani." "Ni dai tun da nake ban taɓa yi wa Alhaji Idi Naira aski ba sai wannan karon, ya kira ni har gidansa na yi masa aski da gyaran fuska. To bayan na fito daga gidansa, sai na wuce gidajen iyayen yara da dama na yi wa 'ya'yansu kaciya, wasu ma har aski na yi wa iyayensu. Sai kuma jarirai biyu da na cirewa hakin wuya. Bayan kwana biyu, sai na fara jin surutun wai Alhaji Idi Naira yana ɗauke da cutar ƙanjamu. Kwatsam! Ina zaune sai ga jami'an tsaro su zo da Malam Shehu, su ka tattaro ni suka yi awon gaba da ni." Sergent ɗin ya gama rubuta jawabin Bala wanzan, sannan ya dubi Idi Naira. Idi Naira ya shiga wurga wa Malam Shehu harara ya ce. "Yallaɓai wannan mutumin ya ci mutumcina, ta hanyar yi mini ƙazafin da ban ji ba ban gani ba. Kawai saboda kwanaki na yi fama da rashin lafiyar farankama, shi ne aka fara yawo da ni wai ina da ciwon ƙanjamau. Har wasu suna cewa ƙurajenta sun fito mini." Ƙuri Baba Sale ya yi wa Alhaji Idi Naira yana kallo, saboda irin ramammun mutanen nan. Idi Naira ya ɗora da cewar. "Dr kai ne likita, saboda Allah ina haɗin cutar farankama da ƙanjamau? Ko saboda kullum sun ga ina lalacewa kamar ɗibana ake yi? Ni lafiyata ƙalau, masifar uwar gida da amaryata ne suka saka ni a gaba." Sai a lokacin Baba Ibrahim ya numfasa jin musu da hatsaniya ta fara kacamewa ya ce. "A'a gaskiya babu haɗi ma tsakanin cutar ƙanjamau (HIV) da cutar farankama/ƙarambau (CHIKENPOX). Tun da ita cutar ƙanjamau wato HIV (Human Immunodeficiency virus), cuta ce da take karya garkuwa da kariyar jikin ɗan'adam. Ta yadda za ta ba wa ƙwayoyin cututtuka damar shiga jikin salin-alin, ba tare da wata kariya ba. Alamomin cuta mai karya garkuwar jiki sun haɗa da: Ɓarkewar zawo, yawaitar kaluluwa, matsanancin zazzaɓin da ya ƙi jin magani har zuwa lokaci mai tsawo, ciwon maƙoshi, yawaitar fitowar ƙuraje babu dalili, gumin dare koda lokacin sanyi ne, ramewa da rashin cin abinci, tashin zuciya da amai sai tari mai ɗaukar lokaci ba tare da ya ji magani ba." Cikin Alhaji Idi Naira ya kaɗa sosai, saboda yana jin kusan kaso mai yawa na alamomin da ya ji Baba Ibrahim ya lissafa. "To amma wani hanzari ba gudu ba, koda mutum ya ji irin alamomin da na lissafa ba zai ce kai tsaye yana da cutar ba, har sai ya je asibiti an gwada shi kuma an tabbatar." Jin furucin Baba Ibrahim ya sa Alhaji Idi Naira ya sauke ajiyar zuciya, Bala Ibrahim ya cigaba. "Amma ita cutar farankama/ƙarambau (CHIKENPOX), ƙwayoyin virus na varicella-zoster ce take haifar da ita, cutar tana iya kama yara da manya. Kuma ana iya ɗaukarta ta hanyar shaƙar numfashin mai ɗauke da ita, cin abinci, makwanci ko wasanni tare.Tana saka ciwon ciki, zazzaɓi mai zafi, firgita, jajayen ƙuraje masu ɗurar ruwa, da matsanancin ƙaiƙayi. Mafita ɗaya ce a kiyaye haɗa mai cutar da wanda ba shi da ita, yin gaggawar zuwa asibiti domin bada agajin gaggawa. Killace mai fama da ita, da karɓar rigakafi." Baba Ibrahim ya dubi Idi Naira ya furta, "Ka ga kenan babu alaƙa tsakanin cutar ƙanjamau da farankama Alhaji, amma duk ba wannan ba, yanzu ku tashi sai mu wuce asibiti gabaɗaya a yi muku gwajinta domin kowa ya fita daga zargin." Cikin Alhaji Idi Naira ya ɗuri ruwa saboda shi kansa ba shi da tabbacin rashin cutar, sakamakon idan ya tafi Lagos har ya dawo da matan banza yake mu'amala. Ya haɗe fuska tamau ya ce. "Dakata Dr, babu inda zan je ni lafiyata ƙalau." Ganin borin kunyar da Idi Naira yake yi ya sa kowa ya aminta da tabbas biri ya yi kama da mutum, domin rashin gaskiya ya bayyana ɓaro-ɓaro a fuskar Alhaji Idi Naira. Yaya Inu yana komawa gida daga wurin Zuly matashin kai ya samu Hansatu da Larai sun riƙo Salame ranga-ranga za su tafi da ita asibiti. "Subhanallah! Hansatu lafiya?" Yaya Inu ya furta a razane. "Wallahi Mai gida jikin ne ya rikice ina jin haihuwar ce ta zo." "Allah Ya ba ta lafiya, yanzu ina za ku kai ta?" Kai tsaye hansatu a ce. "Asibiti, saboda jikin ya ba ni tsoro." A gwasale Yaya Inu ya ce, "Yanzu haihuwar ce har sai kun yayime ta zuwa asibiti? A can ɗin rage mata zafin ciwon za su yi?" Haushi ya sa Hansatu ta yi gaba ba tare da ta kula shi ba. Shi ma daɗi ya ji saboda ya san ƙarshen zance a ce ya kawo wani abin. Fadil ne ya ɗauke su a motarsa ya wuce da su asibitin ƙwararru na Malam Aminu Kano (AKTH). Kasancewar a can yake aiki, kai tsaye ɗakin haihuwa aka wuce da ita domin a duba ta. A gwaje-gwajen likitocin ne suka tabbatar da ba ciki ba ne, sai dai ba sa ganin komai a cikin nata. Hankali a tashe Hansatu ta kira Yaya Inu, a lokacin ya ci babbar rigarsa zai tafi ɗaurin aurensa. "Mai gida akwai damuwa ciki dai na jikin Salame ashe ba ɗa ba ne." "Mene ne idan ba ɗa ba? Hansatu kada ku janyo mini masifa a farar safiyar nan. Ni fa ba na son damuwa, yanzu haka ɗaurin aurena da Zuly zan tafi." Baƙin ciki ya sa ƙwalla ta zubo wa Hansatu a ƙufule ta ce, "Yanzu abin da za ka ce mini kenan? Mai gida kana nufin Zuly ta fi 'yarka Salame?" "Hansatu kada ki ɓata mini rai, kin san dai jiya a yadda na kwana. Auran nan da za a ɗaura ne kawai yake ba ni ƙwarin gwiwa, har kika ga ina walwala. Ke bari na wuce kada ki ɓa ta mini lokaci, saboda matashin kai ta ce mini waliyinta wutar ciki gare shi zai iya tafiya idan na makara." Daga haka Yaya Inu ya katse, ya tura waya a aljihu ya rufe ɗakinsa sannan ya fice. Yana kai kansa zai fita a ƙofar gida ya ci karo da Mai gari shi da su Sanƙira, cike da girmamawa mai gari ya russuna ya ce. "Barka da fitowa!" Hannuwa biyu Yaya Inu ya kai ya fara shafa idonsa, a ransa yana ayyana ko dai gizo idonsa ya yi yake nuna masa Mai gari ne yake tsugunna masa. "Ranka ya daɗe ya haka kuma?" Mai gari ya russuna ya ce, "Duk girmanka ne ai, ga wannan a rage da abincin yara." Sanƙira shi da Muzammil, suka shiga kiciniyar sauke buhunhunan kayan abincin daga cikin kura sannan suka tafi. Mai gari har zai juya da sauri Yaya Inu ya tsayar da shi. "Ranka shi daɗe ni fa ka saka ni a duhu, waɗannan ɗin na mene ne?" Mai gari ya shafa kai ya ce, "A da dai ban yi niyyar sanar da kai yanzu ba, amma na ga kana neman ƙarin bayani ne Baba. Magana ta gaskiya Allah Ya jarabce ni da son Laraba, kuma aurenta nake son yi." Yaya Inu ya bayyana mamakinsa a fili, saboda duk cikin yaransa babu mai baƙin jini da samari ba sa kulawa kamar Laraba. Amma ganin irin rawar ƙafar da Mai gari yake yi masa, da tarin arzikin da zai samu ya sa ya ce. "Idan ma yanzu a shirye kake, ka wuce mu je masallaci domin yanzu haka ni ma ɗaura mini aure za a yi!" Cike da shauƙi Mai gari ya ce, "A yi haka kuwa?" Yaya Inu ya washe baki ya ce, "Me ya rage Mai gari? Ni ma ai an sauƙaƙa mini wannan bidi'ar wunin bikin, da mata za su zo su yi ta cinye abinci." Godiya sosai Mai gari ya yi, ya ce zai je ya sauya kayansa sannan ya ƙarasa. Hakan kuwa aka yi, Mai gari yana zuwa masallaci ana gama ɗaurin auren Yaya Inu da Zuly matashin kai. Yana zama ya miƙa wa Malam Liman sadaki ya zama waliyinsa, aka ɗaura aurensa da Laraba a kan sadaki naira dubu ɗari. Fitar Yaya Inu daga gida babu jimawa Goggo ta ƙarasa, almajirai ne suka shiga da ƙullin kayanta. Inno tana hango ta, ta ƙarasa wurinta cikin farinciki ta rungume ta tana faɗin. "Lale marhabun yau ga mutanen Jibiya." Goggo ta saki murmushi ta ce, "Ga mu Allah Ya kawo mu, wai ina Laraba ban ji motsinta ba?" "Idan kika bibiya ta fita ta ɗauko mini magana, yarinya yadda kika san rainon ifiritu." Goggo ta saka dariya cike da zolaya ta ce, "Ni kam wai Inno hala yaron ciki gare ki? Irin wannan ƙyalli da kike yi haka." Inno ta saki guntun tsaki ta furta, "Wuce mu je ku gaisa da Malam, kafin mu shiga ki fara zuba mini labari." Tun shigar Goggo gidan da Mai Yasin ya ji muryarta, ƙirjinsa ne ya yi wata irin bugawa da ƙarfi. Haka kawai ya ji gabansa yana faɗuwa, jin muryar matar da ko a duniyar mafarki ba zai manta da ita ba. Da sallama ɗauke a bakin Inno suka shiga ɗakin, Mai Yasin yana ɗaga ido karaf ya sauka a kan Goggo da ta daskare a wurin. "Malam Jafaru! Dama tsawon shekaru a nan ka laƙe bayan ka halake mini dukiyar marayu? Allah na gode maka, tabbas addu'a ba ta faɗuwa ƙasa banza. Azzalumi maha'inci, ka ci amanata kuma ka tafi ka bar ni da ƙallagaggen aurenka a kaina." Mai gari ya jima bai yi farincikin da yake ciki a wannan ranar ba, saboda mallakar Laraba da ya yi ji yake kamar ya mallaka faraincikin duniyarsa gabaɗaya. Yaya Inu ne ya sanar da shi tariyar Laraba, za ta kama sati mai zuwa saboda 'yan saye-sayen kayan ɗaki da za a yi mata. Bayan sallar Isha'i Zuly matashin kai da wasu fanɗararrun ƙawayenta biyar, suka yi mata rakiya zuwa ɗakin miji. Dama da rana ma tare da ita aka yi jere, don haka da za a kai ta suna tafe suna hira. Zaune take a ɗakin ta, tana jiran shigowar Yaya Inu hayaniyar yaran ta cika mata kunne. Cike da izza ta fita tsakar gidan a gadarance ta ce. "Ku waɗanne irin dabbobi ne, ku da yaranku da za ki dinga tunɓele da dare?" Indo da dama zuciyarta take cike da kishi fal ta ce, "Yadda muka zama dabbobi, sannu a hankali ke ma za ki zama dabbar, har ki haifo balami a ciki gaba da yin tamɓelen da shi." A daidai lokacin Yay inu ya shigo, yana shigowa duka yaran suka nustu suna yi masa sannu da zuwa, ko ƙurarsu bai kalla ba ya wuce wurin Zuly ya kamo hannu ta suka wuce ɗakinsa. Sabuwar hira suka dasa suna ƙyalƙayala dariya, zuciyar Indo kamar za ta buga, tun tana tsakar gida tana jin hirarrakinsu har dare ya yi ta shige ɗaki ta kwanta. Ganin Yaya Inu ya ja filo da abin rufa ya sa Zuly matashin kai ta ce, "Yaya haka ne masoyi? Ban gane ba an yi gabas da kare." Ƙirjin Yaya Inu ya buga amma sai ya basar ya ce, "Na gaji ne kin san fa yau na sha baƙi." Zuly ta ɗan tsuke fuska ta ce, "A'a ai kuwa haka za ka yi haƙuri ka tashi, don ni in saluɓe namiji ba abu ne mai wuya a wurina ba." Tsoro da kunyar Zuly ya mamaye shi, saboda tun da yake aure bai taɓa auro fitsararsiyar mace irinta ba. A ɓangare ɗaya kuma bai san me zai ce mata ba, hasali ma wata irin kunyarta yake ji. Yana cikin nazari, ya ga Zuly ta miƙe tsaye tana warware ɗankwalin kanta ta ce. "Na ka wasa ne Malam Inusa, ai ni ba na sanya. Ba ka ji ma laƙabin sunana ba matashim kai? Bari ma ka gani." Zuly ta ƙarasa maganar tana fisgo siraran ƙafafuwan Yaya Inu. Ya auren Yaya Inu da matashin kai zai kasance? Shin Yaya Inu yana warkewa ko ya tafi kenan? Wacce badaƙalar za a yi a gidan Mai gari da Laraba? Shin za ta so Maigari ko shi yake wahalarsa? Ina matsayin auren Inno da Mai Yasin? Yaya Mai Yasin zai yi tun da asirinsa ya tonu? Zai zauna da Goggo da Inno ko yaya? Mene ne a cikin Salame idan ba ɗa ba? Ya matsayin gwajin da za a yi wa su Ɗan Bishir? Yar gwal da Ɗanladi zaman su zai ɗore? Duka waɗannan tambayoyin da ma waɗansu, amsarsu tana cikin cigaban littafin GIDAN LIKITOCI. AlhamduLillah, a nan na kawo ƙarshen free pages ga me son ci gaba za ta biya ta 500 Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan no 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam🌚 [05/06/2024, 16:52] Ameera Adam: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA ƊAYA Cikin karayar zuciya da ɗacin rai wasu tagwayen hawaye suka fara 'yar tsere a saman dakalin fuskar Baba Isuhu, ya kai kallonsa wurin mai sunan malam da ke wutsul-wutsul a hannun Lami ya ce. "Mai sunan malam ba zan iya rabuwa da kai ba, don Allah Lami kada ki azabtar da ruhina da rashinku." Kuka ya sake ƙwace wa baba Isuhu da ya sauke idanunsa a kan ƙullin kayan Lami da ke ɗaure a ɗankwali. Sai da ya sharce majina da gefen rigarsa sannan ya sake kwantar da murya yana faɗin. "Lami kin san irin so da ƙaunar da nake yi miki? Ko so kike ki mayar da ni marayan ƙarfi da yaji? Matuƙar za ki tafi gidanku sai dai ki tafi da ni Lami, domin ni na fi maye maita indai a kanki ne." Baba Isuhu ya janyo hannun Lami ya haɗa da na mai sunan malam ya rungume a ƙirji sai ya sake ɓarkewa da kuka. "Don Allah ki haƙura da yajin nan da za ki yi Lami. Matuƙar naman ƙauri ne zai datse igiyoyin so da ƙaunar da ke tsakaninmu ko sayar da kaina zan yi, amma na yi miki alƙawari duk inda zan shiga zan yi koma me ye na nemo miki abin ƙaurin nan Lami." Lami ta taɓe ba ki sannan ta ce. "Wallahi Isuhu ba abin da zai hana ni tafiya a daren nan, don in gaya maka na ce wa Goggo Sala ko awa guda ba za mu ƙara a gidan nan ba. Saboda Allah kamar a kaina tsiya ta ƙare, haihuwar fari a ce yau kwana biyu cir babu kajin ƙauri ballantana na saka rai da ɗan akuya ko tinkiya. Kai tir da halinka Isuhu, wallahi da Isa mai tsire na aure na san nama har sai na ci na ture..." Cikin sauri Baba Isuhu ya katse ta. "Me aka yi aka yi Isa ne Lami? Wai ko kin manta Isuhun Lamisuwa mai hadarin naira?" Lami ta sake taɓe baki ta furta. "Ai a banza man kare, tun da a haihuwar ɗanka na fari guda a ce abin ƙauri ya gagara, kenan haka zan zauna har hakikar sunan ita ma ta gagare ni. Wallahi ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa." Jin haka ya sake tsuma Baba Isuhu ya zabure haɗe da ɗaga hannu sama ya ce. "Sai ni isuhullen Lamisuwa mai hadarin nairori, sai ni Isuhun da ya sha gaban zaratan mazaje ya samu Lamisuwa." Lami ta ɗan saki murmushi sannan ya kalle ta ya ce. "Wai ina Lami take?" Da sauri Lami ta amsa. "Ga ni mana." "A yau ba sai gobe ba zan kayar miki da tinkiya." Sai da ya kalli hagu da dama ya yi ƙasa da murya sannan ya matsa saitin kunnenta ya ce. "Kin san Allah yau uwar garke zan girke miki." Da sauri Lami ta washe baki cikin zumuɗi ta furta. "Uwar garke fa..." "Ki yi ƙasa da murya mana haba Lami, ko so kike asirina ya tonu?" Baba Isuhu ya katse ta da sauri. "Ɗan Isuhullena ai sai yanzu na fahimce ka, Allah Ya ba ka sa'a kada hatsabibiyar yarinyar nan ta ganka lokacin da za ka ɗauke mata uwar garken nan." Lami ta yi maganar murya can ƙasa zuciyarta fes. "Ai maso abin ka ya fi ka dabara Lamisuwata, dare zan bi na san yadda zan yi da ita. Ke dai kawai ki zuba wannan ki sha kallo." Baba Isuhu da Lami suka kwashe da dariya. "Lami! Ke Lami ki fito mu wuce kin shanya ni ke 'yar daɗi miji, kin san dai idan ana jego ko kyakkyawan zama a wurin miji ba a yi ballantama wannan mijin na ki..." Lami ta yi saurin katse Goggo Sala, "Goggo zo mu je ciki ai tuni mun riga da mun gyaro ta ni da shi." Baki sake Goggo Sala ta bi ta da kallo sannan ta ce. "Hmmm namiji kenan! Ke yanzu daɗin bakin namiji har zai sa ki zauna..." Lami ta yi saurin yi wa Goggo Sala raɗa a kunne, da sauri Goggo Sala ta washe ba ki ta furta. "Ke 'yar nan da gaske?" Lami ta gyaɗa kai tana murmushe. "Haba ko da na ji wannan ita ce harkar arziƙi, ko ni ƙanwar uwarki ai na samu na lasa wa a bakin salati. Ni fa kin san ni dama na fi kwarkwasa kwaɗayi, duk wurin da ake samun mai maiƙo-maiƙo a nan na fi ƙarfi." Lami ta yi gaba tana tafiya cikin ƙwambo tana jin ita ma ta isa, kuma ta tabbata matuƙar aka wayi gari da an yi mata ƙauri da tinkiya ta san daraja da ƙimarta ta ƙaru a idanun facalolinta. CIKIN DARE A hankali Uwani ta buɗe idonta sakamakon jin fitsarin da ya zame mata kamar farilla cikin talatainin dare, sai da ta gama murtsike idanu sannan ta fara tashin Dada. "Dada! Dada don Allah ki tashi ki raka ni fitsari nake ji." Dada cikin takaici ta saki dogon salati sannan ta ce. "Ni kam wallahi Dijen Iro ta cuce ni da ba ta gashe miki mara tun kina zanin goyo ba, wallahi Uwani ki kiyayi haƙƙin tashina tsakiyar dare da kike yi..." "Dada kamar kukan uwar garke nake ji." Uwani ta katse Dada cikin sauri tana sake kasa kunne, don sama-sama take jin kamar kukan dabbobinta kasancewar suna da ɗan nisa da sashen Dada. Dada ta yi mata shiru saboda takaici. "Dada don Allah ta shi mu je ko wani abu ne yake damun su..." "Ai wallahi ko Umaru ne ya dawo daga Lahira bai isa ya fid da ni waje ba, tun wuri ki kama 'yan matan ƙafafuwanki ki yi gaba." Jin takaicin abin da Dada ta faɗa ya sa Uwani tashi fuuu ta suri buta ta yi waje. Tamkar sabon munafiki haka Baba Isuhu yake tafe cikin sanɗa yana waige har ya ƙarasa sashen da awakin Uwani suke, sai da ya karkace maƙogaro ya maƙe murya kamar yadda Uwani ke yin magana sannan ya ce. "Uwar garkeruruna tayya maza mu je ki ci dusa." Shiru ya ga uwar garke ta yi babu alamin za ta motsa, ganin za ta ɓata masa lokaci ya sa ya ɗago ta ya fara ja a hankali. Sai da ya ƙarasa bakin katanga sannan ya taka turmin da ke jingin, sama-sama ya ɗan fara jiyo motsi don haka ya yi kasake. A ɓangare ɗaya ƙirjinsa na bugawa don kada uwar garke ta yi kuka asirinsa ya tonu. Yana raɓe a gefen katanga ya ga Uwani ta wuce da buta a hannu sannan ya sauke gwauruwar ajiyar zuciya, tirmi ya taka a hankali ya leƙa ya hango Mai gari da ke tsaye yana jiransa. "Haba Isuhu tun ɗazu ɗauko tinkiya ya gagare ka, ko so kake asirinmu ya tonu mutumcina ya bi rariya ya tsiyaye tas a garin nan ina matsayin mai garin garin nan." Baba Isuhu ya yi ƙasa da murya ya ce. "Kai Talle ka san dai fita da uwar garke ta ƙofa ba zai yuwu ba saboda tsaro, yanzu ga ta ka matso zan cicciɓo maka ita." Da sauri Mai gari Talle ya matsa jikin katangar. Baba Isuhu ya koma wurin Uwar garke da ke cin dusa, ya tattaro iya ƙarfinsa ya ɗago ta sai ji kake ɓaaaarrrrrrr wata uwar tusa ta ƙwace masa. Uwani da kawo kanta kenan ta saki murmushi ta ce. "Kai da jin wannan tusar ka san su uwar garke bacci ya yi daɗi." Har za ta gota sai ta leƙa garkensu, sai dai haskarwar da ta yi babu uwar garke babu alamunta. Da sauri ta juyo tana shirin fasa ihu ta hango Baba Isuhu rungume da uwar garke, ita kuma uwar garke jin matsar da Baba Isuhu ya yi mata ya sa ta ware baki ta ce. "Meeeeeeeeehhh." Cikin sauri Baba Isuhu ya miƙa wa Mai gari Talle, Mai gari na karɓa ya fara kici-kicin hawa mashin. Uwani na ganin Baba Isuhu ya miƙa uwar garke ta yi caraf ta kama katanga, sai dai tana gani Mai gari shi da wani da ba ta gane fuskarsa ba suka haye mashin suka fita da gudun gaske. A haukace Uwani ta diro daga kan katangar ta ɗora hannu a kanta cikin tashin hankali ta ce, "Wayyo Allah uwar garkena." Sai kuma ta yi sashen Dada a guje. Ganin haka ya sa Baba Isuhu da sauri ya nufi sashensa. A tsakar ɗaki ya sami Lami don haka tana ganinsa ta ce, "Ya dai Isuhullena an dace kuwa?" Baba Isuhu da ke faman haki ya ce, "Maza ki tafi ɗaki ki kwanta, ni ma lamfo zan yi shegiyar yarinyar nan ta kama mu ni da Talle." Zaro ido waje Lami ta yi ta ce, "Mun shige su Isuhuna ya za ka yi?" "Babu lokaci Lami ke dai ki je ki yi yadda na ce miki." Lami ta yi saurin ficewa shi kuma Baba Isuhu ya faɗa uwar ɗaki ya haye gado sannan ya fara sauke numfashi kamar wanda ya jima yana bacci. "Wayyo uwar garke." Uwani ta furta haɗe da ɓarkewa da matsanancin kuka. Ganin Dada na sakin bacci har da minshari ya sa Uwani ta buga tsalle haɗe da faɗin. "Wayyooo uwar garkena!" Sai a lokacin Dada ta ji ihun Uwani. "Kai ni kam Mamman ya cuce ni da ya haɗa Uwani da kiwo tun tana ƙanƙanuwarta. Yanzu ban da masifa a ce yarinya har cikin bacci tana ambatar tinkiya, wannan bala'in da me ya yi kama..." Dada ba ta ƙarasa magana ba ta ji Uwani ta faɗi a gefen ƙafarta tim! Ta fashe da wani irin matsanancin kuka. A razane ta tashi zaune sannan ta kai hannu ta kunna fitilar ɗakin, hannuwa biyu ta sa ta dafe ƙirji a firgice Dada ta furta. "Uwani ke ce nake gani a gabana ko buɗe mini ido aka yi?" Uwani ta ji tamkar Dada ta watsa mata ruwan zafi, don haka ta fyace majina da gefen zaninta cikin ihu ta ce. "Uwar garkeeeeeena! Baba Isuhu ne uwar garkenaaaa." Dada ta zaro ido waje. "Ke Uwani ko dai gamo kika yi ne? Shi Isuhun ne ya zama uwar garke? An ya lamarinki Uwani babu jifa a ciki?" Dada na gama magana ba ta ji daga bakin Uwani ba ta fashe da kuka tana faɗin. "A'ubikalimatillahi tamma min sharrin ma kalaƙa. Aniya bi aniya wallahi aniyar kowa ta bi shi, Allah Ya kai mu wayewar gari wallahi sai na je gidan Sarkin aska na karɓo miki ƙaiƙayi, ni za a kashe da ƙullutun baƙinciki..." Uwani ta katse Dada daga dogon jawabin da take yi. "Dada wallahi ganin idona Baba Isuhu ya ɗauke mini uwar garke ya miƙa wa Mai gari ta katanga." "Ke yarinyar nan ki ji tsoron Allah, shi Isuhun nawa ne kike jifa da sata? Isuhun da ko yatsa ba za a saka masa a baka ya tauna ba?" Ganin haka ya sa Uwani ta fice daga ɗakin tana faɗin, "Wallahi ko sama da ƙasa za ta haɗe sai ka dawo mini da uwar garkena. Wayyo Allah garkeruruna!" Jikin Dada nan take ya ɗauki karkarwa don haka ta miƙe cikin sauri ta bi bayan Uwani. Kafin wani lokaci wasu daga cikin mutanen gidan suka fara fitowa, kowa ya tambayi Uwani amsa ɗaya take bayarwa 'Uwar garke, Baba Isuhu ya miƙa wa mai gari ta katanga.' Carko-carko suka yi domin ga dukkan alamu sun fara aminta da kalaman Uwani, sakamakon sun duba garken awakinta sun ga babu uwar garke. "Ina shi Isuhun ne?" Baba Idris ya tambaya. Kallon juna suka shiga yi don haka ya bayar da umarnin a je sashen shi a kira shi. Sahabi da Tasi'u ne suka nufi sashen Baba Isuhu, sun jima suna buguwa sannan ya buɗe ƙofa, yamutsa fuska ya hau yi tamkar wanda aka tasa yana bacci ya ce. "Kai waye a tsohon daren nan yake mana bugu haka?" "Baba Isuhu dama Baba ne ya ce a taso ko?" Suka amsa masa. "Ni kuma? A tsohon daren nan? Ko ciwon Yaya ne ya tashi?" Baba Isuhu ya jefa musu tambayoyi kamar bai san abin da yake faruwa ba. Girgiza masa kai suka yi, suka wuce gaba yana biye da su a baya. Yana zuwa ya samu mutane a tsaye carko-carko, tun daga nesa gabansa ke dukan uku-uku amma gudun tonuwar asirinsa sai ya yi hanzarin aro mayafin jarumta ya lulluɓa wa jikinsa. Ya sake aro fuskar mamaki ya ɗora a saman tashi, cikin mamaki ya furta. "Yaya lafiya na ganku haka a tsohon daren nan?" "Uwani ce ta zo mana da wata magana..." Duk abin da ya faru Baba Idris sai da ya zayyane masa sannan ya ɗora da cewar, "Ina Uwar garke take?" Duk da ƙirjinsa bugawa yake amma bai hana shi fututtukewa ba ya ce. "Haba Yaya yanzu duk faɗin gidan nan a rasa wanda za a laƙa wa sata sai ni? Me zan yi da wata uwar garke? Shekarar uwar garke nawa a gidan nan? Amma kawai don yarinyar nan ta shirya ƙaryarta sai a hau kai a zauna, shi kenan tun da ni ne ɓarawon da kuke zargi a faɗa mini nawa ne kuɗinta zan biya." Ganin yadda ran Baba Isuhu ya ɓaci ne ya sanyaya jikin ilahirin mutanen da ke wurin, Dada ta zauna daɓar haɗe da rushewa da matsanancin kuka. "Tsakanina da wannan ɓarawon ni kam sai na kai kukana gaban Ubangiji, ina zaman zamana zai haɗa mini husuma a cikin zuri'ata." Baba Mustafa ya ɗago Dada sannan ya ce, "Yanzu dai duka mu bar maganar nan ni nan zan sayo miki wata ƙatuwar tinkiyar da ta fi uwar garke girma kin ji Uwani." Jin haka ya sa Uwani ta rushe da kuka. "Wallahi ni uwar garke nake so, kuma ko kur'ani aka ba ni zan dafa ganin idona na ga Baba Isuhu da uwar garkena..." Baba Mustafa ya yi saurin katse ta don haka kawai ya ji ya yi na'am da kalaman Uwani, don haka ma ya ce. "To shi kenan ba tinkiya kaɗai zan saya miki ba, kina son ɗan maraƙin sa ko?" Ba don Uwani ta daina jin zafin rashin uwar garke ba ta amsa, sai don son da take wa ɗan maraƙin sa. Saboda haka ta gyaɗa masa kai tana goge hawaye, a gefe ɗaya tana kuma ƙudurtar irin fansar da za ta ɗauka a kan Baba Isuhu don ta yi rantsuwa da Allah jinin Uwar garke ba zai tafi a banza ba. Daga haka gabaɗaya kowa ya watse, Uwani da Dada suka yi sashensu sai dai buta ta sake ɗauka ta fito kamar za ta banɗaki kai tsaye ta wuce sashen Baba Isuhu cikin sanɗa, ta ci sa a bai rufe ƙofa ba don haka tana laɓe daga bakin ƙofar ɗakinsa ta ji Lami na faɗin. "Isuhullena ai ka birge ni da ka ƙaryata shegiya, haka kawai da tuni da tozarta ka a gaban mutane." Baba Isuhu ya saki dariya ya ce. "Ke zan cen da nake miki gobe warhaka mun riga da mun gama ɓarje dabgen kan uwar garke." A gefe ɗaya ta ji muryar Goggo Sala na cewa. "Yanzu dai tun da aikin gama ya gama ai sai ku ja baki ku yi shiru, amma dai Isuhu dole ka badda kama idan za ka shigo da uwar garke don ka san dole a saka maka idanu." Baba Isuhu ya fashe da dariya yana shirin yin magana daga can bayan ƙofa suka ji muryar uwar garke ta ce. "Meeeeeeeeh." A zabure suka kalli juna cikin tashin hankali. "Kukan uwar garke nake ji a tsakar gida Isuhu leƙa ka gani..." Lami ta faɗa da sauri. "Ba ki da hankali Lami, ya za a yi ganin idona Talle ya tafi da uwar garke kuma na ji muryarta ke ki leƙa mana..." Kalaman bakinsa suka katse sakamakon sake jin kukan Uwar garke ta ce, "Meeeeesuhuuuu." Wani abu ne ya tsargawa Baba Isuhu tun daga tafin ƙafarsa har tsakiyar kansa. "Isuhu kamar sunanka na ji a cikin kukan uwar garke." Lami ta faɗa a tsorace. "Meeeeeesuuuhuuuu." Uwani da ke laɓe ta sake maƙale murya ta faɗa da yanayin kukan uwar garke, tana gama faɗa ta dokon ƙauren ɗakin da suke ciki. A zabure Lami, Isuhu da Goggo Sala suka faɗa uwar ɗaki, Goggo Sala da ke ɗaure da ɗaurin ƙirji tun a falo zanin jikinta ya faɗi ba tare da ta sani ba. Goggo Sala da baba Isuhu suka shige bayan ƙofar uwar ɗaki ita kuma Lami ta maƙale a gefen gado, shirun da suka ji ba a ƙara kukan tinkiyar ba ne ya sa suka fara dawowa hayyacinsu. Goggo Sala ta kai idonta jikinta sai a lokacin ta yi ido biyu da tsurar ɗan fatarin (Under wear) da ke ƙugunta, ga ƙirjinta zube a saman kan Baba Isuhu da ke tsugunne a ƙasa. Sai a lokacin ta lura da hannuwan baba Isuhu da ke riƙe da ɗan fatarinta. Cikin matsananciyar kunya ta ce. "Kai Isuhu wanne irin iskanci ne haka saboda Allah za ka nemi shigewa cikin fatarina, ni fa ƙanwar mahaifiyar matarka ce ." Cikin rashin sani Baba Isuhu ya miƙe tsaye sai jin ƙirjin Goggo Sala ya yi a saman fuskarsa, yana ɗagowa suka haɗa ido da ita. Ganin abin kunyar da aka tafka cike da borin kunya ta ce, "Amma dai Isuhu yadda ka kwaso mini ƙirji ina a matsayin sirikarka Allah Ya kwashe maka albarka." 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 [06/06/2024, 10:23] Ameera Adam: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA BIYU Uwani da ke laɓe tana jin su sai da ta saki murmushi sannan ta wuce ɗakin da Lami da Goggo Sala suke kwana, tana shiga ta samu mai sunan malam yana kwance yana bacci. A hankali ta ɗauko shi sai da ta zo tsakar gida, ta saka shi a cikin ƙatuwar tukunyar da ake dafa wa Lami ruwan wanka amma babu ruwa a ciki. Ta saka hannu ta ɗan jijjiga shi don ya tashi, saboda dama ta jima da sanin Baba Isuhu matsoraci ne na bugawa a jarida, don haka ta gano lagonsa. Baba Isuhu ba ƙaramin ɗacin kalaman Goggo Sala ya ji ba, ya saci kallonta rai a ɓace ya ce. "Allah Ya kwashe mana dai, ni allan-musuru ne na san ke ce a wurin? Wallahi ni da na ji na ɗebo abu a kaina na ɗauka hannuwan Lami ne." Baba Isuhu ya ƙarasa maganar yana fitowa falo. Ya bar Goggo Sala a tsaye cike da takaicin abin ya faɗa. "Tsabar iskanci da wulaƙanci har ƙirjina ya yi lalacewar da za a ɗebo su aka a ɗauka hannuwa ne?" Goggo Sala ta ayyana a ranta. Yana zuwa ya ji mai sunan malam ya tsanyare da kuka. Kusan tare suka kalli juna shi da Lami, sai dai jin shiru babu kukan uwar garken ya sa suka ɗan saki jikinsu. Cikin sanɗa suka fara takawa a hankali har suka fita tsakar gida, suna yunƙurin tafiya ɗaki suka ji kukan mai sunan malam a cikin tukunya ga shi kuma tukunyar a rufe. Lami ce ta yi ƙarfin halin buɗewa nan take ta yi tozali da shi. "Isuhu akwai abin da yake shirin faruwa wallahi." Lami ta faɗa murya na rawa. "Lami ko dai a garin ɗaukar uwar garke ne na tako aljanu? Na shiga uku kada su taɓa mini mai sunan malam." Baba Isuhu ya ƙarasa maganar cikin kuka, Goggo Sala na ƙarasowa suka wassafa mata abin da yake faruwa. "An ya kuwa Isuhu uwar garken ka ɗauka ba aljanu ba kuwa? Gaskiya ruwa ba ya taɓa tsami banza." Cikin Baba Isuhu ya sake ɗurar ruwa, ya waiga a hankali yana kalle-kalle daga can kusurwar bango ya hango kamar mutum a tsaye, Uwani da ke raɓe ganin kar ya gano ta ya sa ta yi wata girgiza haɗe da cewa. "Meeeeesuuuuhuuuu zaaaaan cinyeeeeee idoooonnnnkaaaaa." Jin abin da aka faɗa ya sa Baba Isuhu da su Lami suka faɗa ɗakin da su Lami suke jego. Uwani ta samu ta saɗaɗa sannan ta wuce sashen Dada tana sakin murmushi, ko ba komai ta gano lagwansu da yadda za ta dafa su a ruwan sanyi. Su Baba Isuhu gabaɗayansu babu wanda ya samu sukunin rintsawa, don Baba Isuhu ko sallar asuba bai samu ya fita ba. Sai da gari ya yi haske tarwai sannan suka fito suka yi alwala suka yi sallah, Goggo Sala ta ɗora ruwan wankan mai jego. Ita ma Uwani idonta biyu har aka yi sallar asuba sannan bacci ya yi awon gaba da ita. Ko da gari ya waye babu wata damuwa a tattare da Uwani don ba ƙaramin jin daɗin mafitar da ta samu ta yi ba, ita kanta Dada ta yi mamakin ganin Uwani tana harkokinta. Sai dai a lokacin da ta ƙarasa garken awakinta sun ba ta tausayi musamman da ta ga tagwayen uwar garke sai koke-koke suke alamun suna neman ta, tana zuba musu abinci suka daina kuka sai tagwayen uwar garke da har lokacin ba su daina kuka ba. "Kai Talle asirinmu fa ya kusa tonuwa, kai Allah ne kaɗai ya tarfa wa garinmu nono." Baba Isuhu ya faɗa yana yin ƙasa da murya. "Ai na san za ka gyara komai, kai ma fa shaiɗanin kanka ne. Yanzu dai ya za a yi da kai da ƙafafuwan? Kuma cinyoyin baya ka san na ce maka ni zan ɗauke su." Mai gari Talle ya furta. "Ni yanzu kai da ƙafar 'yar akuya nake so ka samo mini, saboda zan kai wa Dada don na badda idonsu a kaina, cinyoyi dai gaskiya na gaba za ka ɗauka. Kuma sai yamma liƙis za ka aiko min, ka tabbatar an daddatsa komai don kada a fahimci naman babbar tinkiya ne." Mai gari Talle ya gyaɗa kai yana shirin magana ya hango Uwani a ɗan nesa da su tana haɗa tukwanen taɓo, idan ka ga yadda ta mayar da hankali tana wasa sai ka rantse da Allah ba ta san wainar da suke toyawa ba. Ganin ta ya sa Talle Mai gari ya ce. "Abokina ma yi magana anjima kawai, yanzu dai gaskiya sauri nake." Daga haka suka wuce, don shi kansa Baba Isuhu ya lura da Uwani duk da ta yi kamar ba ta san suna yi ba. Uwani na ganin Talle mai gari ya tafi gida ta watsar da kayan ƙasar hannunta, ta sake ɗaure ɗamarar da ta yi da ɗankwali wacce cike take da jelolin raguna da tumakai, da ta shiga kasuwar awaki ta samo. Tana daga jikin katangar ƙofar gidansa ta ga ya shiga soron gidan, da yake turakarsa a soro take don haka a kan idonta ya faɗa ɗakinsa. Tana nan tsaye ta ji ya sake fitowa a tsammaninta fitowa waje zai yi sai ta ji ya shiga cikin gida yana faɗin. "Amarsu ta ango mai daɗin tuwo da miya, wannan ɗan waken da kika shanana mini man ƙuli ai dole na bada tukwici." Da sauri Uwani ta faɗa ɗakin tana shiga ta samu sabuwar langar Zuwaira amaryar mai gari cike da ɗan wake, da sauri ta cakuɗa ta hau ci saboda tsabar ƙeta ta dinga haɗa uku-uku huɗu-huɗu tana ci, cikin ƙanƙanin lokaci ta cinye ɗan waken tas, sannan ta ɗauki ruwa ta sha, ta zaro jelar tumaki biyu ta saka a ciki. Tana shirin miƙewa ta ji alamar tahowar mai gari shi da Zuwaira yana faɗin. "Haba wane mutum ki dinga haɗa kanki da waccen ballagazar. Ke fa komai na ki na daban ne Zuwairatuna." Uwani da ke ɗakin cikin matsananciyar faɗuwar gaba ta shige uwar ɗakinsa, can bayan ƙofa ta ɓuya don ta tabbata matuƙar mai gari ya kamata sai ranta ya yi mummunan ɓaci. Zuwaira cikin kwarkwasa ta zauna tana fari da idanu, hannunta ɗauke da mufici tana yi masa firfita. Mai gari da ƙarfinsa ya ɗauko langa amma jin ta fayau ya sa shi mamaki don ɗan waken da ya gani cike da langa yake, yana ɗaga murfin ya ganshi fayau sai jelar tinkiyoyi a ciki. Wani abu ne ya tsarga masa tun daga tafin ƙafarsa har tsakiyar kansa, cikin faɗuwar gaba ya furta. "Zuwaira kina ganin abin da nake gani kuwa?" Zuwaira da mamaki ya sa ta hangame baki ta ce. "Mai gida me ye wannan kamar jelar tumaki? Ina ɗanwaken da na zuba maka?" Mai gari ya haɗiyi yawu mai ɗaci yana shirin magana daga can uwar ɗakinsa ya ji an ce. "Taaaaalleeeeeeeeeh." Zuwaira ta waiga cike da tsoro ta ce, "Kamar kukan tinkiya kamar kuma cewa aka yi Talleh." Kafin ta gama magana tuni gumi ya gama wanke Mai gari, Zuwaira na shirin sake magana suka ji ƙarar buhu sai kuma Uwani ta sake maƙe murya ta ce. "Ga uwar garke ta dawo ba ta mutu ba, na zo tafiya da talleh a cikin buhun mutuwa." Zuwaira da mai gari nan take suka shiga rige-rigen guduwa, Uwani da ta saka kanta a cikin wani ƙaton buhun gero ta biyo su buguzum-buguzum da gudu tana fisgar malun-malun ɗin mai gari. Mai gari kafin ya shiga cikin gida ya kifa ya kai sau uku, da ya tashi malun-malun sai ta sake harɗe shi. Ladiyo da ke tsakar gida sai ganinsu ta yi a guje. Zuwaira ta shige ɗakinta ta banke ƙofa, yayin da Mai gari ya faɗa ɗakin Ladiyo, yana tafe fitsari da zawo na bin wandonsa. Waige-waige Ladiyo ta fara yi don ita ba ta san gudun da suke yi ba, ganin haka ya sa ta shiga ɗakinta, a can ƙasan gado ta hango Mai gari gumi na yanko masa ta ce. "Mai gida wai me yake faruwa ne?" Mai gari ya sake jan zanin gado don ya rife kansa ya ce. "Ladiyo gamo muka yi a ɗakina, wallahi aljanu ne a ciki." Wani wari ne ya ziyarci hancinta, ta kai kallonta wurin ƙafar wandonsa ta ce. "Mai gida me nake gani kamar zawayi?" "Idan zawayin ne akwai uban da ya yi mini shi? Ba abina ba ne ki bar ni mana Ladiyo." Mai gari ya faɗa yana muzurai. "Don Allah ka taso mu je ka sauya kaya kafin yara su dawo gida." Shiru mai gari ya yi sannan ya ce. "Amma za ki tsaya a ƙofar banɗaki ko?" Ladiyo ta gyaɗa masa kai cike da mamakin wai yau ita Mai gari yake ce wa ta yi masa rakiya banɗaki. Da ƙyar da suɗin goshi Ladiyo ta samu kan Mai gari ya fito, Uwani da ke ɗakin Mai gari har ta fito za ta tafi gida ta ji suna maganar shiga banɗaki. Da sauri ta saki murmushi ta ɗauko buhun ta zagaya ta bayan gidan Mai gari, zuciyarta fes don babu mutane sosai sai waɗansu ƙananan yara da ba su wuce shekara uku ba suna wasa. Kasancewar banɗakin karkara a buɗe yake ta sama ya sa duk abin da Mai gari yake faɗa tana ji, sai da ta tabbata da Mai gari ya tuɓe sannan ta tsugunna ta saitin rariyar ta ce. "Shi kenan ma Talle ya zo masarautarmu da ƙafafuwansa yana wanka, buhun mutuwa zo ka kai Telle inda ya kai shugabarmu wato Uwar garke." Uwani na gama maganar ta watsa masa jelar tumaki biyu ta saman banɗakin, sannan ta wurga ƙaton buhun geron da ta fito da shi. Tana daga nan wurin ta ji Mai gari ya zuba ihu ya fice a guje yana faɗin. "Wayyo Allah! Za su tafi dani, wayyo Ladiyo ki taimaka mini buhun mutuwa ya biyo ni." Garin gudun da Mai gari yake yi ne ta ga takalminsa wari ɗaya ya faɗo ta bayan katanga. Dariya Uwani take yi kamar mahaukaciya sabon kamu, sai da ta yi mai isarta sannan ta ɗauki takalmin mai gari wari ɗayan ta ɗaure shi a cikin ɗankwalin da ke ƙugunta kai tsaye ta wuce gida. Yamma ta yi liƙis a lokacin tana tafe tana waƙoƙinta, da mamaki take bin galleliyar motar da ke ƙofar gidansu. A gaban motar ta tsaya ta isa gaban mudubin motar tana kallon kanta tana yatsine-yatsine, ta mudubin ta hango Salele hannunsa ɗauke da tulu ya ɗebo ruwa. Uwani ta ƙwalla masa kira, nan take jikinsa ya fara rawa, "Yar ƙashin gwiwa don girman Allah ki bari na kai wa Innata ruwan nan." Uwani ta tsuke fuska sannan ta ce. "Don uwarka wani abin na ce maka ne, kawai ka zo na ce ko." Jikinsa a sanyaye ya ƙarasa idonsa na zubar da ƙwallah don ya san yau kwanan tulun Innarsa ya ƙare. Duk abin da yake faruwa Jafar na daga cikin motarsa yana kallonsu, kamar ya yi mata magana sai kuma ya ce bari ya tsaya ya ga iya gudun ruwanta. Don ko ba a ce masa Uwani ba ce, kamaninta da na mahaifinsa ya alamta masa. "Sauke ruwan tulun nan." Ta furta fuska a haɗe. Babu musu Salele ya sauke, Uwani ta fara ɗiban ƙasa tana ƙwaɓawa a saman gilashin motar Jafar, domin baƙin gilas ne kuma ba ta taɓa tsammanin da mutum a ciki ba. A hankali ta fara zuba ruwan tulun tana wanke ƙasar wani wurin ya yi jurwaye wani ya wanku, ta ɗora tulun a saman motar sannan ta ce. "Salele tulun Innarku yau shi zai tuƙa mu zuwa garin Kano, ka san fa sabuwar motata ce da Dada ta sayo mini jiya." Uwani na sakin tulu ya faɗo ƙasa tush! Salele ya wage baki ya saki ihu cikin ɗacin zuciya. A hankali Jafar ya fara zuge gilashin motarsa, Uwani da ke gefe ta yi mutuwar tsaye saboda tsoro don ba ta taɓa tsammanin da mutum a ciki ba. Sai kuma ta maze ta fara harare-harare don kar ya raina ta, ta kalli wurin da Salele yake ihu ta buga masa tsawa. "Za ka yi mini shiru ko sai na mayar da bakinka ƙeya." Tamkar an yi ruwa an ɗauke haka Salele ya yi tsit yana goge ƙwallah. "Uban wa ya ce ki jiƙa mini mota." Uwani ta ji saukar maganar Jafar a kunnenta, ƙirjinta ya buga da ƙarfi saboda tsoro amma don kada ya gano ta sai ta haɗe fuska ta ce. "Ka ga malam bar ganinka da wasu kayan 'yan sanda ka ɗauka za ka tsorata ni, babana ma babban ɗan sanda ne. Wallahi yanzu ihu ɗaya zan yi ya kai ka caji ofis ya sa a kulle ka." Uwani ta ƙarasa maganar tana murguɗa baki, sannan ta yamutsa fuska ganin Jafar ya kafe ta da ido yana kallo ya sa ta ci gaba. "Kai ni fa ban ma yarda da kai ba wallahi, an ya ma kai ba ɗan sandan bogi ba ne? Dubi yadda kake raba idanu kamar shege a rabon gado. Wai ma uban wa ya ce ka jiye mota a ƙofar gidanmu..." Uwani ta haɗiye ragowar kalamanta sakamakon ganin Jafar ya buɗe mota ya fito, ba Uwani ba hatta Salele sai da ya tsorata da yanayin da ya ga Jafar. Uwani a dole don kar ta kunyata kanta ya sa ta cigaba da tsaiwa ta ce. "Ka ga malam tun kashinka bai bushe a hannuna ba ka..." Ta sake haɗiye ragowar kalamanta sakamakon jin Jafar ya damƙi hannunta da ƙarfin gaske. "Yeeeh Uwani ta shiga hannun ɗan sanda." Salele ya faɗa da ƙarfi cikin murna yana tsalle, tuni cikin Uwani ya kaɗa. Salele ya ja baki ya rufe sakamakon ganin bindiga saƙale a gefen aljihun Jafar. Da ƙarfin gaske Jafar ya fisgi hannun Uwani kai tsaye ya wuce cikin gida da ita. Tamkar raƙumi da akala haka Uwani take bin Jafar ƙirjinta na bugawa, zuciyarta na shelar neman agajin gaggawa. Don duk iskancin Uwani tana tsoron bindiga ɗari bisa ɗari. Lokacin da Jafar ya shiga ɗakin Dada babu kowa a ciki, don haka ya wurgar da Uwani gefe fuska a haɗe ya ce. "Maza tashi ki fara tsallen kwaɗo." Uwani jiki na rawa ta fara tsallen kwaɗo sai dai ba ta kai ko ina ba, ta fara hawaye shaɓe-shaɓe. Belt ɗinsa ya ciro yake lafta mata idan ta tsaya, don haka lokaci ɗaya Uwani ta fara fita a hayyacinta. Bayan ta gama tsallen kwaɗo ya saka ta tuƙin babur, da kansa ya gwada mata yadda za ta yi, tana daga tsaye ban da numfarfashin kukan Uwani babu abin da yake ta shi. "Allah mai yau da gobe, wato yau kukan Uwani nake ji a gidan nan? Tabbas gaba da gabanta wai aljani ya taka wuta, Uwani yau wa kika taɓo wanda ya fi ƙarfinki haka..." Kalaman Dada suka maƙale sakamakon ganin Uwani a ƙobare da ƙafafuwa tana tuƙin mashin. Baki a sake Dada ta ce. "Ke Uwani wane sabon iskanci ne kuma haka? 'Ya mace da ke ki hau wani ƙobare ƙafafu kuma kina kuka." Uwani jin abin da Dada ta faɗa ya sa ta faɗi ƙasa ta sake fashe wa da kuka. "Wallahi idan na ƙirga uku ba ki tashi ba sai kin maimaita har da tsallen kwaɗo." Jafar da ke zaune a gadon ƙarfen Dada ya furta fuska a haɗe. A yatsine Dada take kallon wurin ta ce. "Waye haka kuma da baƙaƙen kaya? Na san dai na ba wa Mamman tarbiyya ba zai yi wannan rashin imanin ba, domin ni musulma ce kuma ina sallah a ɗakina amma dubi garsameman ƙato ya shigo mini da waɗannan takalman kalar na arnan Lagas har cikin ɗakina. Wai Jafaru za ka fito ka cire mini takalmi a waje ko sai na kira ubanka mamman ya fitar da kai?" "Dada kada ki sake ɓata mini rai!" Jafar ya furta a takaice. "Ran naka ya fi na ran ƙuda ɓaci, ke Uwani ta shi ki tafi wannan zalinci ba za a yi shi a ɗakina ba. Ni kam wallahi Sa'idu ya gama cutata da ya haɗa mini zuri'a da aikin kaki." Dada ta furta ƙwalla na zuba. Bindigar aljihunsa ya zaro yana juya ta, ganin bindigar ya sa daga Uwani har Dada suka zabura. Hawaye bibbiyu na bin fuskar Dada ta ce, "Yanzu harbe mu za ka yi Jafaru? Ni kam ko ana sauya muku zuciya daga ta musulmai zuwa ta kafirai a wurin tirenin ne?" Jafar ya sake haɗe fuska ya ce. "Ta kanki zan fara ma, Dada sai yau kika san ana sauya mana zuciya?" Ganin yadda ya sha kunu ya sa jikin Dada ya fara karkarwa, Jafar ya fara takowa a hankali kafin ya ƙarasa sai gani ya yi Dada ta zube ƙasa a sume. Murmushin gefen baki ya saki, Uwani na ganin haka ta wage baki ta ƙwalla ihu, a daidai lokacin Malam na madina ya kawo kai yana faɗin. "Wallahi Uwani sai Allah ya yi mana hisabin wannan ihun da kike yi mana babu ji babu gani." Jafar ya hango a tsaye ya mayar da bindigarsa aljihu, yana shirin magana ya hango Dada a yashe a ƙasa. "Na Madina wallahi Jafaru ne ya sa bindiga zai harbe mu shi ne Dada ta faɗi." Uwani ta faɗa fuska da hawaye shaɓe-shaɓe don ba ƙaramin tsorata ta yi ba. Ganin haka ya sa Malam na Madina ya yi wani irin ihun da jaruman indiya suke yi, cikin kukan kura ya yi wata irin sufa ya cukumi wuya Jafar haɗe da maƙale shi yana faɗin. "Wiiiiihuuuuuuhuuuu gafara ga maza nan bisa kanka." 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 [07/06/2024, 10:48] Ameera Adam: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA UKU Ilahirin ƙarfinsa Malam na Madina ya ware yana cakumar Jafar, idan ya dunƙule hannu sai dai ka ji dum! Ya kai masa dundu a baya. Shi kansa Jafar ya yi mamakin ƙarfin dattijon duk da ba fin ƙarfinsa ya yi ba. Na Madina da ya ga ya ɗauki lokaci bai kai Jafar ƙasa ba, ya zuba wata uwar kabbara tamkar wanda yake tsakiyar yaƙin musulmai da arna yana faɗin. "Allahu Akbar." Da ya yi kabbara sai ya sauke wa Jafar wani dundu a baya. Uwani na ganin haka ta ɗebo ruwa a randa ta fara yayyafawa Dada, babu jimawa Dada ta fara sauke ajiyar zuciya sannan ta buɗe idonta. Jafar tun yana ganin dukan da Na Madina yake yi masa wasa ne har ya ga ya cukwikwiye masa wuya, har wani zullo yake yana kabbara yana kai masa duka tamkar mai jifan shaiɗan. Jafar ya haɗa hannuwan dattijon wuri ɗaya ya murɗe su sannan ya ce. "Wallahi Na Madina ko ka sauko daga kaina ko na bi yatsun hannunka ɗaya bayan ɗaya na tsike su kamar yadda ake tsinkar mangwaro." Jin matsar da Jafar ya yi masa da kuma furucinsa ya sa cikin Na Madina ya karta, yana shirin yin magana ya ji Dada na salati daga kwance. Tamkar ɗan biri sai ga na madina ya yi tsalle ya faɗo ƙasa, Jafar ya gyara wuyar rigarsa ya fice daga ɗakin. Kai tsaye ya wuce ɗakinsa da Dada ta sa aka gyara masa. Malam na Madina ya tsugunna a daidai kan Dada ya ce. "Sannu da farkowa Kulu." Dada ta dube shi luuuu da idanu a shanye sai kawai ta ɗaga ɗan yatsa ɗaya ta ce. "Ashhadu anla'Ila'ha'illahu wa anna Muhammadur Rasulillah." Malam na Madina ya sake cewa. "Mun auna arziƙi Dada wannan yaron ashe harbe ku ya so yi?" Dada ta sake yin luuuu da idanu fuskar na Madina na yi mata gizo ta ce. "Ismi Hauwa kulu wa ana musulima." Jin haka ya sa Na madina ya fashe da kuka, kukan da Dada ta ji ne ya sa ta ɗan wartsake sai a lokacin komai ya fara dawo mata. Zumbur ta tashi zaune ta fara bin su Uwani da kallo. "Uwani kina jin maganata ko kuma da gaske Jafaru ya harbe ni na mutu?" Uwani ta saki dariya ta ce. "Ina jin ki mana Dada ga Na Madina ma a zaune." Dada ta kalli na Madina suna haɗa ido kamar haɗin baki suka fashe da kuka a tare. "Uwani maza ɗauko mini wayata."Dada ta furta cikin kuka. Da sauri Uwani ta ɗauko mata don ta san ba ya wuce ta ce a kira mata baba Mamman. "Maza kira mini Mamman." Uwani ta karɓi wayar ta gama dube-dubenta sannan ta ce, "Lambarsa ce mai hotan zuciya ko?" Da sauri Dada ta gyaɗa kai. Uwani ta kira tana jin an ɗauka ta miƙa wa Dada. "Assalamu Alaikum. Hajiya Dadata yau ke ce da kira da kanki..." "Dakata Mamman! Kiranka na yi ka gaya mini waye shugaban 'yan sanda na duk faɗin duniya?" Dada ta katse Baba Mamman a zafafe. "Shugaban 'yan sanda na duniya? Dada me ya faru kuma?" Ya tambaya a sanyaye. "Me ye ma bai faru ba Mamman? Ka gaya mini shugaban 'yan sanda na duniya da inda zan same shi, domin a yau ba sai gobe ba wallahi zan ce ya tube Jafaru daga wannan aikin kakin. Kai ni dai Sa'idu ya gama cutata, a ce 'ya'ya duka babu mai aiki ƙwaƙƙwara daga Soja, Rosafti sai Ɗan sabda. Wai kamar ni 'yar limamai jikar limamai ace duka 'ya'yana babu limami ko malamin makarantar allo." Sai da Dada ta fyace majina sannan ta cigaba. "Mamman ko ka sa a tube Jafaru ko kuma wallahi sai dai ku nemi wata uwar ba ni ba..." "Don Allah Dada me yake faruwa?" Baba Mamman ya katse ta hankali a tashe. Nan take Dada ta zayyane masa duk abin da ya faru, ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba. Cikin kwantar da murya ya fara lallashinta har ya samu ta daina kukan sannan ta ce. "To yanzu Mamman yadda aiki yake wahala, idan aka tube Jafaru daga aikin nan wacce sana'a zai fara? Tsorona Allah tsorona kada ya fara ɗauke-ɗauke, ni dai na san Jafaru da tsoron Allah ko mage ba zai iya kashewa ba, to ko dai a Lagas ɗin nan ya fara 'yan zuƙe-zuƙe ne da ya zo zai harbe mu?" Murmushi baba Mamman ya yi ya furta. "Dada da ya kashe mana ke ai gara a tube shin kawai, amma dai ba na jin Jafar yana shaye-shaye ki bar ni da shi zan kira shi yanzu a waya wallahi ransa sai ya ɓaci." Dada ta ɗan yi jim sannan ta ce. "Ni fa Mamman ban ce ka kira shi ka yi masa tijara ba, ina zaman zamana Jafaru ya zo ya cika ni da nunkufurcin tsiya. Ni ban san ma lokacin da Saratu ta koya maka masifa ba, yara irinsu Jafaru sai addu'a da lallashi. Kai kanka Mamman ba don tsayuwar da na yi a Harami ba ai da ban san abin da za ka zama ba, Allah dai Ya shirya mana zuri'a." Baba Mamman ya yi murmushi ya amsa mata sannan suka yi sallama. Uwani sam ba haka ta so wayar ta kasance ba, don haka ta miƙe har za ta fita sai kuma ta wuce uwar ɗakin Dada tana sakin murmushi. A can ƙarƙashin gado ta ciro bankinta ta ƙwaƙulo kuɗaɗen da suke ciki, sai da ta ƙirga su kusan dubu ɗaya da ɗari biyar ne. Ta ɗaure su a ɗankwali haka kawai ta fara sakin murmushi, Dada ta bi ta da kallon mamaki baki a sake. Baba Mamman na kashe waya ya kira Jafar ya yi masa faɗa sosai, tare da nuna masa illar tsoratar da Dada da ya yi musamman da shekarunta suka tura. Jafar ya fahimci mahaifinsu sai dai shi tsokanar Dada yake da ya ce harbe ta zai yi. Can ƙasan akwatinsa ya je ya tura bindigar ya ajiye sannan ya shiga banɗaki ya watsa ruwa ya wuce ɗakin Dada. A nan ya shiga tsokanarta suka fara hira har Malam na Madina kamar ba shi ne ya gama kabbara yana naushinsa ba. Uwani na fita can kantin Ɗan bala ta wuce ta sayo alawa irin da raɗin suna leda biyu, sai ta ƙarasa wurin Ali mai dabino shi ma ta sayo gwangwani uku. Sai da ta tsaya a gefen hanya ta kunce kowacce leda ta zuba kofato biyu da ragowar jelar tumaki ɗai-ɗai sannan ta ɗaure. Tana tafe tana sakin murmushi har ta ƙarasa gida, kai tsaye sashen Baba Isuhu ta nufa za ta shiga kenan ta gan shi ya fito da alama masallaci za shi don an kira sallar Magriba. "Sakaryar banza ke ba kya ganin mutane ne?" Baba Isuhu ya furta yana wurga wa Uwani harara. "Ga shi wata mata ta ce na kawo maka." Uwani ta faɗa tana miƙa masa ledar hannunta. Da mamaki ya karɓa ya furta, "Wata mata kuma? Ba kuma Lami aka ce ki kai wa ba?" Uwani ta girgiza kai cikin alamun tsoro ta ce. "Kai ta ce a kawowa kuma ni fa idanun matar ya ban tsoro wallahi, Baba Isuhu dama mutane suna da kofato ne ban taɓa sani ba sai yau?" A firgice Baba Isuhu ya saki ledar alawar ya ce. "Kofato fa? A ina kika ga kofaton?" Uwani na ganin yadda ya firgice sai ta basar ta ce, "Bari dai na wuce wurin Dada..." "Don ubanki za ki tsaya ki mini bayani ko kuwa?" Baba Isuhu ya yi magana jiki na rawa, don bai jima da barin gidan Talle Mai gari ba, da yaje duba shi sakamakon yana kwance sharɓan. Kuma a dubiyar da ya je ne yake shaida masa abin da ya faru da shi a banɗaki da kuma ɗakinsa. "Eh matar ce na ga ƙafarta da kofato, sai ta miƙo mini ledar nan ta ce na ba ka. Kuma ta ce na faɗa maka idan ka wurgar da saƙon nan a kan mai sunan malam za ta fanshe."Da sauri Baba Isuhu ya tsugunna ya fara tattaro dabino da alawar, a nan idanunsa suka ci karo da kofato, tuno abin da Uwani ta faɗa ya sa jikinsa na rawa ya haɗa ledar ya sa a aljihu ya dubi Uwani ya ce. "Ina matar take yanzu." Uwani ta zuba hannu biyu ta yi tagumi ta ce. "Ni fa tana ba ni ledar nan da na waiga sai ban ganta ba, wallahi ina jin ɓacewa ta yi don kamar ƙiftawar ido haka na neme ta na rasa." Wani irin sanyi ƙafafun Baba Isuhu suka yi, Uwani ta yi kamar ba ta gane yanayin da yake ciki ba ta shige cikin gidansa. Baba Isuhu yana nan tsaye har zai fita ko me ya tuna da sauri ya faɗa cikin gida, yana tafe hawaye na zuba don jikinsa ya gama ba shi ta shi ta zo ƙarshe. Uwani na daga ɗakin Lami ta hango shi nan da nan ta ƙunshe dariyarta, yana shiga ɗakin ita kuma Goggo Sala na sirka ruwan wanka don aiki ne ya hana ba ta yi wanka da wuri ba. "Lami ni kam na shiga uku!" Da sauri Lami ta kalle shi, Uwani na jin haka ta muƙe ta fice. Da yake ta lura hankalinsu ba ya kanta kai tsaye ta bi hanyar banɗakin da Goggo Sala ta bi domin yin wanka. Lokacin da Uwani ta je wurin banɗakin Goggo Sala ta riga da ta tuɓe har ta fara wanka, a hankali ta saɗaɗa ta janye kayan da ta cire. Sannan ta fara wani irin gurnani tana kukan tinkiya. Goggo sala ta riga da ta saɓa sabulu a fuska da sauri ta dakata, jin ta daina wankan ya sa Uwani ta yi wani gurnani mai ɗan tsoratarwa sannan ta maƙe murya ta ce. "Gani gare ki Goggo Sala, ki nutsu ki saurari abin da zan faɗa miki domin zai yi miki amfani a matsayinki na jinsin bil'adam." Nan take jikin Goggo Sala ya ɗauki karkarwa kamar mazari, hannu biyu ta sa ta fara kiciniyar goge kumfan fuskarta amma yajin sabulu ya hanata buɗe ido. "Nan wurin da kike wanka masarautarmu ce, kuma kina tsaye ne akan karagar shugabarmu ga hadimanta nan sai zagaye ki suke yi. Wani abin haushi kin saka su kallon tsiraici, don ma Allah Ya taimake ki aljani Manu ɗan kwarto ba ya kusa da tuni ya haike miki." Jin haka ya sa Goggo Sala ta fashe da kuka, Uwani ta gimtse dariyarta ta cigaba da cewa. "Ni ce uwar garke wacce kika dafa namanta, to yanzu haka na dawo domin ni dama ba tinkiya ba ce. Kuma namana da kika dafa a tukunya na ɗauke shi na kai garkena, sannan zan kafa miki wani sharaɗi matuƙar kika saɓa masa zan ɗauke ki zuwa duniyarmu." Goggo Sala baki na rawa ta ce. "To Babata uwar garke faɗi kowanna sharaɗi ne ni mai biyayya ce a gare ki." Uwani ta sa hannu ta toshe dariyarta ta ci gaba da cewa. "Sharaɗin shi ne kullin za ki dinga goya Isuhu sau uku a rana, safe, rana da kuma dare. Idan kika zo goya shi ki dinga yi kina lasar baki, kuma idan kika kuskure koda na lokaci ɗaya ne ba ki yi ba take zan ɗauke ki ko kuma na tsotse romon kanki." "Wallahi zan yi ba dai goyo ba, ko har da Lami aka ce zan haɗa na goya su." Goggo Sala ta faɗa cikin kuka. "Kin taimaki kanki, yanzu kayan da kika cire zan kai shi garkena amma zan bar miki ɗankwali, kuma kada ki kuskura ki fito sai an kira sallar Isha'i domin anfara tattaunawar fadar aljanu da ke. Sannan ɗan autan shugabanmu ya ce da baya da baya za ki tafi ɗaki kina cewa nasara a kanku Isuhu da Lami." Goggo Sala ta amsa, a zuciyar tana da-na-sanin zuwanta zaman daɓaro gidan Lami. Uwani na gama maganar cikin sanɗa ta koma har lokacin baba Isuhu yana ɗakin don ta hango shi ta cikin labule, ta raɓe a gefen ƙofar ɗakin ta karkace murya ta fara kukan tinkiya. Shiru ta ji sun yi sannan ta yi wani gurnani tana yi tana buga ƙafa irin tsalle-tsallen da awaki suke yi. "Shi kenan Lami ta zo ina jin tafiya za ta yi da ni." Baba isuhu ya faɗa cikin kuka. "Ba zan tafi da kai yanzu ba. Ni uwar garke ni ce na aiko maka da saƙo ɗazu. Ku buɗe kunnenku da kyau, uwar garke ba mutum ba ce. Na zo na kafa muku sharuɗɗana idan kuka bi su zan yafe muku zunubin da kuka aikata mini, idan ba haka ba kuma a gabanku zan yi farfesun mai sunan malam na saka ku cinye shi kuma ku shanye romonsa." "Wallahi ko mene ne kika ce mu yi za mu yi miki biyayya." Lami ta faɗa a tsorace. "Kai Isuhu da farko taimakonka za mu fara yi kafin ka ji sharaɗinmu. Ƙanwar mahifiyar matarka babbar matsafiya ce a ɓoye, kuma dama da biyu ta zo zaman daɓaro gidanka. Idan kuma ka yi yunƙurin korarta za ta halakaka da iyalinka gaba ɗaya. Daga gobe ne wa'adin aikin da take yi a kanka zai fara, don haka yanzu ma za ku ga ta fito tana tafiya da baya-baya tana ambatar sunanku don haka kada wanda ya tanka mata. Kuma gobe za ta zo da sassafe ta ce maka za ta goya ka. Duk rintsi kada ka bari ta taɓa maka jikinka." A zabure Baba Isuhu ya ce. "Goyo fa? Ni Isuhu za a goya da giramana ban da iskanci?" Uwani ta katse shi. "Idan muna magana ba a tankawa. Sannan Sharaɗin da za mu kafa maka ya zama wajibi ka ɗauki rigunan mama na Lami guda uku ka kai wa mahaifiyarka Dada ka ce ta saka su..." "Dadar ce za ta saka bireziya..." Baba Isuhu ya furta cikin suɓutar baki. Uwani ta buga masa tsawa cikin gurnani ta ce. "Idan ka saɓa mana wallahi sai mun hallaka ka da kisa mafi muni." Nan take Baba Isuhu ya ce. "Duk abin da kika ce na bi Inna uwar garke." "Na dawo gare ki Lami. Ke kuma akwai dafin da Goggo Sala ta saka miki a ruwan wanka wanda wa'adinsa gobe zai cika, ko ba kya ganin irin maganin da take zuba miki a ruwan wanka kullin?" Da sauri Lami ta gyaɗa kai. "Idan kika sake shayar da ai sunan Malam daga gobe ke da shi mutuwa za ku yi, domin dodonta zai zuƙe jininku tas." Da yake Lami ta san Goggo Sala da shegen bin malamai nan take ta aminta da kalaman Uwani. "Sharaɗin da zan kafa miki ya zama dole daga gobe ki dinga ɗaukan mai suna Malam kina kai wa Jafar shi yana shayar da shi a sashen Dada." Cikin haɗin baki Lami da Baba Isuhu suka ce. "Jafaru kuma? Shi zai shayar da mai sunan Malam?" "To kada ku kai shi dama ɗan autan Goɗiya kwaɗayin romon jariri yake ji sai na dafe masa shi." Uwani ta faɗa cikin wata irin murya, don ita kanta dagewa take da tuni dariya ta kwace mata. "Wallahi za mu kai shi, Allah Ya kai mu gobe." Gabaɗaya suka amsa. "Kuma ya zama wajibi a gare ka, kai Isuhu ka saka ƙarfi ka danne Jafar domin a shayar da mai sunan malam idan ba haka ba komai zai iya biyo baya. Kuma sharaɗin da zan kafa muku na ƙarshe ko da wasa kuka faɗi abin da ya faru tsakanina da ku, sai na sa wuƙar aljanin mahauta ya yaɗe fatar jikinku sannan na ɗauke ku zuwa duniyarmu a azabtar da ku kamar yadda kuka azabtar da ni." Uwani na daga tsaye ta fara jiyo shasshekar kukan Baba Isuhu. Sai da ta lallaɓa ta ɗauke tukunyar naman da aka yi farfe su ta ajiye a soro sannan ta ce. "Tukunyar namana da kuka dafa ku same ta a wurin garkena, kada wanda ya fito har sai an kira sallar isha'i domin tuni an zauna zaman fadar aljanu da ku. Kuma idan kuka bari namana da kuka dafa ya kwana a garkena cikin dare zan gayyato tawagar jinsinmu su ɗauke mini ku." Uwani na gama maganar ta fara kukan tumaki tana wani irin dire-dire sannan ta ɗauki tukuyar ta tafi a hankali, kai tsaye ta wuce garken awakinta. Da yake duhu ya yi awakin Uwani duka sun kwanta, a hankali ta isa turken uwar garke ta ajiye tukunyar. Ta janyo igiyar uwar garke ta saƙale a jikin ƙafar tukunyar, zuciyarta fes ta wuce sashen Dada don ta yi sallar magriba tana tafe tana dariya kamar sabuwar kamu. Har alla-alla take gari ya waye ta ga irin diramar da za a tashi da ita. A lokacin da ta shiga ɗakin Dada Jafar na zaune ta kofin shayi a gefensa , ga laptop a gabansa yana dannawa, dawowarsa daga masallaci kenan. Uwani na ƙare masa kallo ta tuntsire da wata mahaukaciyar dariya, domin yanayin zaman da ta ga ya yi ne har ta hango yadda Baba Isuhu zai danne shi a shayar da mai sunan malam. Ɗagowa ya yi ya kalle ta sai kuma ya ci gaba da danna laptop ɗinsa, Uwani ta sake kallonsa ta ga yadda yake jin magani sai kawai ta tsugunna a wurin tana sheƙa uwar dariya. "Uban me kike yi wa dariya?" Jafar ya furta a daƙile. Tamkar wacce ya sake ingizawa, sai Uwani ta sake fashewa da dariya har da hawaye da ta tuna duk irin haɗe fuskar da yake yi wai shi za a danne a shayar da mai sunan malam. "Ba tambayarki nake yi ba?" Jafar ya buga mata tsawa. "Dama wani wasa ne muka fara bugawa ni da ƙawata Lantana shi ne na shirya mata yadda zan cinye ta gobe." Uwani ta yi maganar tana ɗan murguɗa baki. "Ba na son shashanci idan wannan iskanci za ki yi ki fice mini ba na son hayaniya." Uwani ba ta kula shi ba ta gimtse dariyarta ta shige uwar ɗakin Dada. Ku kawo wa Jafar ɗauki zai shayar da mai sunan malam🤭🏃🏼‍♀️😂 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 [08/06/2024, 11:39] Ameera Adam: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA HUƊU Tun da Uwani ta fito daga gidan baba Isuhu daga shi har Lami babu wanda ya kuma motsin kirki, baba Isuhu ya sharɓe hawaye ya dubi Lami cikin kallon tsana da jin haushi ya ce. "Tsakanina da ke Allah Ya isa Lami, kin cuce ni kin cuci rayuwata. Ni ban san ƙaddarar da ta sa na auro ki ba, duk wannan ƙaton bakin na ki ko ina ya je da ban gan shi ba sai yanzu?" Lami ta wurga masa harara ta ce. "Mun dai cuci juna malam ka gyara maganarka. Ni kaina ban azal da kuma rabo me zan yi da kai? Ka san dai duk a samarina kai ne faƙiri matsiyaci." "Wallahi aurena da ke bai ƙare ni da komai ba sai masifa, ina zaman zamana kin jefa ni a jafa'i muguwa mai ƙashin tsiya..." "Dakata malam, kada ka raina mini hankali. An gaya maka ban san dama can kana 'yan sace-sacenka ba? Ko ka manta kajin Yaya Haladu da muka taɓa soyewa?" Shiru baba Isuhu ya yi yana nazari, shi kam ya ci alwashin daga uwar garke har abada ba zai ƙara taɓa kayan wani ba. Dama tun da yake 'yan ɗauke-daukensa ba a taɓa kama shi ba, don haka zai ajiye sata salin-alin ba tare da ta tona masa asiri ba. Suna nan zaune suka ji an rafka kiran sallar Isha'i, babu jimawa suka ji takun Goggo Sala tana tafe da baya-baya, taku ɗaya-biyu idan ta yi sai ta ci karo da kwanuka sannan ta furta. "Nasara dai a kanku Isuhu da Lami." Da hannu Lami ta yafito baba Isuhu ta cikin labule take nuna masa ita, cikin gasgata maganar da Uwani ta gaya musu suka saki baki suna kallonta, a ɓangare ɗaya kuma tsoron Goggo Sala ya kama su. Tana shiga ɗakin da suke kwana da Lami ta banko ƙofa, can ƙuryar bango ta zauna sai kawai ta rushe da wani irin kuka mai cin zuciya. "Kaico kwaɗayina bai amfane ni da komai ba, Allah ka fitar da ni daga wannan gidan annobar. Wallahi nan gaba idan duniya Lami za ta haifa har abada ni da gidanta." Ganin ta shige ɗaki ya sa baba Isuhu ya fita a hankali domin cika umarnin uwar garke, kai tsaye garken Uwani ya nufa yana haskawa kuwa ya yi ido biyu da tukunyar farfesun naman. Nan take ƙirjinsa ya buga, jikinsa ya fara karkarwa sai da ya yi ta maza ya ɗauko tukunyar ya nufi sashensa. WASHEGARI Baba Isuhu tun da ya yi sallar asuba ya gagara runtsawa saboda fargabar goyon da Goggo Sala za ta yi masa, yana zaune a gefen gado ya kallo Lami da ke kwance ita da mai sunan malam. Motsi ya ji a tsakar gida yana leƙawa ya hangi Goggo Sala tana kaiwa da kawowa, abin duniya ya dame ta saboda gari ya fara haske amma har kawo lokacin babu Isuhu babu motsinsa. Cikin sanɗa ta nufo ɗakin da suke ciki baba Isuhu ya leƙo ta windo ya ce. "Munafukar Allah ta'ala ina ankare da ke, wato fakona kike za ki hallaka ni ko?" Goggo Sala ta washe baki tana basarwa ta ce. "Isuhu barka da safiya." Baba Isuhu da ya tuna gargaɗin da aka masa, aka ce kar ya yi mata kora da hali shi ma sai ya yaƙe baki ya amsa. Amma a zuciyarsa ji yake tamkar ya fashe da kuka. Mai sunan malam ne ya motsa Lami ta yi fitgigit ta tashi zaune. "Maza tashi mu je ki kai shi wurin Jafaru." Ba musu Lami ta tashi ta saka hijabinta, baba Isuhu ya manta Goggo Sala da ke waje tana fakonsa ya sa hannu ya buɗe sakata suka fito. Har zai yi gaba ya tuna bai ɗebo rigunan maman Lami da aka ce ya kai wa Dada ba, dama tun a daren ya sa Lami ta ɗebo masa guda uku daga cikin na ta. Komawa ya yi ya ɗebo ya zuba a aljihu sannan ya fito. Yana fitowa Goggo Sala ta yi wata uwar sufa za ta cafko baba Isuhu, a firgice ya zuba a guje yana faɗin. "Wayyo Lami ki zo za ta cafke ni, wallahi tsaf za ta sa a tsotse romon kaina." Goggo Sala na ganin rana ta fara fitowa ga shi ba ta cika umarnin uwar garke ba, ya sa ta rufa wa baba Isuhu baya yana gudu tana bin sa. Da yake ya gama tsorata da ita har gani yake kamanin Goggo Sala kamar har rikiɗe masa suke yi, Goggo Sala irin dogayen matan nan ne, shi kuma baba Isuhu ba shi da tsayi kuma ba shi da jiki. Don haka Goggo Sala ta kusa kama shi amma Allah ya taimake shi ya fice daga gidan, Lami ta rufa masa baya da sauri ya tura ƙofar ya datse ta. Wata gwaruwar ajiyar zuciya ya sauke yana ayyana shi kenan da tuni an bayar da jininsa. Ɓangaren Dada a buɗe yake don haka ba su sha wata wahala ba suka nufi ɗakin da Jafar yake ciki, Lami ce ta fara ƙwanƙwasawa sun ɗan jima sannan Jafar ya buɗe da alama bacci yake yi. Daga shi sai singlet da gajeren wando ya buɗe ƙofar yana murza idanu. Da mamaki yake bin su Baba Isuhu da kallo ya furta. "Ina kwana baba." Baba Isuhu ya washe baki. "Jafaru an tashi lafiya?" Jafar ya amsa sai baba Isuhu ya ce. "Wurinka muka zo Jafaru amma ko za mu ƙarasa ɗakin Dada?" Zuciyar Jafar fes ya ce. "Ok to bari na saka kaya ga ni nan zuwa." Lami da baba Isuhu suka wuce ɗakin Dada a lokacin tana zaune tana jan carbi. Tana ganinsu ta shafa addu'ar, sai da ta cire hijabin ta ajiye carbin ta ce. "Isuhu lafiya na gan ku da farar safiyar nan?" Cikin haɗin baki suka gaishe ta. Baba Isuhu ya ciro rigunan maman hannunsa ya miƙa wa Dada ya ce. "Dada ga wannan a saka." Dada ta karɓa tana yamutsa fuska. "Kai kuwa Isuhu kamar wanda ya kwana da Uwani a rai, tun da farar safiya ka kawo mata wata rigar mama. Wannan dai rigunan ai na manyan mata ne, ina Uwani ina wannan lalacewar." Baba Isuhu ya ɗan sosa kai ya ce, "Ai dama ba na Uwani ba ne, ke na kawowa Dada..." Tun bai ƙarasa magana ba Dada ta katse shi, "Ni fa Isuhu? Ni kuwa me zan yi da rigar mama tsofai-tsafai? Amma dai ka ci mutumcina Isuhu, wai ko dai ka fara 'yan zuƙe-zuƙe ban sani ba?" Idanun baba Isuhu suka ciko da ƙwalla sai da ya share hawaye ya ce. "Don girman Allah Dada ki ɗiba ki shiga ɗaki ki saka." Baki sake Dada take kallonsa, ta rafka salati haɗe da faɗin, "Maza kwashe mini lalatattun kayan nan kafin ranka ya ɓaci. Ni Kulu uban me zan saka a ciki? An ya Isuhu shaɗanu ba su dafa maka kai a cikin bacci ba?" Uwani da ke uwar ɗaki ta sunne kai ƙasa tana dariya. "Haba Dada da farar safiya ki cika wa mutane kunne da ihu." Jafar ya faɗa yana sako kansa cikin ɗakin. Uwani da ke ɓoye a ɗaki ta yi ƙasa da murya ta ce, "Kai ma naka ihun yana tafe." "Ba dole ka ji ihuna ba Jafaru yanzu kamar ni tsofai-tsofai." Sai kuka ya ci ƙarfin Dada sai da ta share hawaye sannan ta watsa wa Jafar rigunan a fuska ta ci gaba. "Wai Isuhu ya rasa me zai kawo mini sai baraziya wai na saka. Yanzu saboda Allah Jafaru ko uwarka Saratu me za ta yi da baraziyya ballantana kuma ni?" Tun Dada ba ta gama magana ba Jafar ya watsar da rigunan sakamakon wani tsami da bashi-bashi da ya ji ya doko hancinsa. "Haba Dada me kike yi haka ne?" Jafar ya faɗa a ƙazance. Kafin Dada ta yi magana mai sunan Malam ya sake tsanyarewa da kuka, Lami ta dubi Jafar ta miƙa masa shi. Kamar Jafar zai yi magana sai kuma ya basar ya miƙa hannu ya karɓe shi, yana bin su da kallon mamaki. "Don Allah Jafaru ka taimaki yaron nan ka ba shi mama ya sha ko ya yi shiru." Lami ta faɗa a ɗan kunyace. Jafar ya kalli Lami cikin sauri ya ce. "Wane Jafarun?" Jafar ya tambaya a hargitse. "Kai mana Jafaru, don Allah ka yi ka ba shi kada ya shiɗe don tun ɗazu yake kuka." Baba Isuhu ya furta. Ran Jafar ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, ya haɗe fuska ya dubi baba Isuhu. "Baba wannan wacce irin magana ce babu tsari, yanzu idan na faɗa maka magana a ce na yi rashin kunya. Idan har ni zan iya shayar da shi me ya hana kai ba ka shayar da shi ba?" Dada ta saki baki da hanci tana kallon baba Isuhu a tsorace, don ita a yanzu ya fara ba ta tsoro shi da Lami. A hankali ya ajiye mai sunan malam a gefe sannan ya miƙe, yana shirin tafiya Lami ta ce. "Isuhu sai fa mun danne shi..." Tun Lami ba ta ƙarasa magana ba baba Isuhu ya sa ƙafa ya shatalo ƙafar Jafar sai ga Jafar a ƙasa. Dada na ganin haka ta fara tafiya da rarrafe don ta tabbata yau su Isuhu babu lafiya, shi ya sa ta nemi guduwa kafin ita ma su dawo kanta su danne ta su saka mata rigar mama. Jafar ya yi mamakin yadda ya gagara ƙwace kansa a hannun baba Isuhu, don haka jin baba Isuhu ya fara ɗaga masa riga sama ya fara kiciniyar kare kansa, garin yunƙurin danne rigarsa sai ga Jafar yana sakin tusa. Uwani kuwa me za ta yi ba dariya ba har hawaye saboda mugunta. Ganin haka ba zai kai Jafar ba ya sa ya fara ihu. "Wayyo Dada ki kawo mini ɗauki. Wayyo Allah! Mutanen gidan nan ku kawo min ɗauki su Lami za su haike mini." Uwani na daga ɗaki ban da dariya babu abin da take sheƙawa, saboda tsabar dariya har kwanciya ta yi ƙasa. Suna cikin haka sai jin muryar Goggo Sala suka yi a bakin ƙofa ta fara lashe baki tana faɗin, "Allah na gode maka da har yanzu lokaci bai ƙure mini ba." A zabure baba Isuhu ya ɗaga Jafar, take jikinsa ya fara karkarwa ta fara tunkaro shi yana ja da baya. "Wayyo Allah Dada ki zo Goggo Sala za ta sa a cinye ni." A madadin Jafar ya gudu tun da ya samu ya tsira sai ya bi baba Isuhu da kallo, saboda ba ƙaramin mamaki ya ba shi ba. Dada da ke cikin ɗaki ta kai wa Uwani duka tana ce wa. "Dariyar me kike yi Uwani mu da ya kamata mu fara yunƙurin ƙwatar kanmu." Kafin Uwani ta yi magana suka ji baba Isuhu ya zuba ihu. "Wayyo ta shanye mini ƙafafu, Jafaru, Dada ku zo ku kawo mini ɗauki." Goggo Sala ba ta bi ta kan baba Isuhu ba ta shatalo ƙafafuwansa za ta sunkuta shi a baya sai ga baba Mustafa da baba Idris sun shigo. "Subhanallahi kai Isuhu lafiya kuwa?" Suka ƙarasa maganar suna ƙarasawa wurin Goggo Sala, baba Isuhu da yake ya gama tsorata sai ji suka yi sharaf ya faɗo jikinsu da alama ya suma. Suka kama shi suka kwantar a ƙasa sai kawai Goggo Sala ta fashe da kuka. "Yanzu shi kenan rayuwata ta zo ƙarshe." Da mamaki suke bin ta da kallo, Baba Mustafa ya dubi Jafar da ya yi laƙwas a gefe ya ce. "Kai Jafar wane sakarci ne haka ake yi kai kuma kana zaune?" Jafar ya sauke ajiyar zuciya ya ce. "Baba ni ma ta kaina nake da tuni sun haike mini, dube ni wai fa ni zan shayar da mai sunan Malam." "Gara da Allah Ya kawo ku Idirisa, wallahi Isuhu shi da matarsa sun haukace. Ashe ba su kaɗai ba har da Salamatu ita ma, an ya ba gamo suka yi a cikin gidan ba. Ban da haka wai ni Isuhu zai kawowa rigar mama ya ce na saka, sannan su dubi garjejen ƙato kamar Jafaru su ce ya shayar da me sunan malam." Baba Mustafa ya yi farat ya ce. "Shi Jafarun ne zai shayar da jariri?" Dada ta wara hannuwa ta furta. "Ta ya ni ji dai Muɗɗafa, ka ga dai a kan idona aka haifi Jafaru. Kai ƙarshe ma dai ni na yi jinyar shayin da aka yi masa ballantana na ce ko Jafaru ya koma mata-maza, Jafaru ko ka sauya daga baya zuwa mata-maza ne ban sani ba." A ƙufule Jafar ya ce, "Wallahi Dada kar ki ƙara ce mini mata-maza." Kukan da mai sunan malam yake tsanyarawa ne ya sa baba Idris ya yi wa Lami magana, sai da ta share ƙwallar idonta ta ce. "An ce daga jiya kada na ƙara shayar da shi." A daidai lokacin baba Isuhu ya farfaɗo sakamakon ruwan da aka yayyafa masa. "Waye ya hana ki shayar da shi?" Shiru gabaɗaya suka yi, baba Isuhu ya dubi Lami ita kuma ta kalli Goggo Sala sai kawai suka fashe da kuka lokaci ɗaya. Shiru ɗakin ya yi kowa yana bin su da kallon mamaki, ban da Uwani da ke sakin murmushi a fakaice. Sai da suka yi me isar su sannan aka samu da ƙyar Goggo Sala ta ce. "Ni kam na san wannan jawabin da zan yi ƙila shi ne na ƙarshe a rayuwata don na san kashe ni za su yi." Baba Isuhu ya yi tsammanin bayanin 'yan ƙungiyar asirin da take ciki za ta faɗa, don haka ya zuba mata ido sai ya ji ta ce. "Dama dai uwar garke ba..." Kamar haɗin ba ki Lami da Isuhu suka ta fi da gudu suka toshe mata baki, da mamaki mutanen ɗakin suka bi su da kallo. "Ƙarya take yi makira haɗa ni da 'yan uwana za ta yi." Baba Isuhu ya faɗa yana haki kamar wanda ya ci gasar tseren gudu. "Ba ma son shashancin banza da wofi Isuhu, sakar mata baki kada ranka ya yi mummunan ɓaci." Baba Mustafa ya faɗa a fusace. Babu yadda suka iya haka suka koma suka zauna jiki a sanyaye, baba Isuhu ya sunkuyar da kai ƙasa gabansa na faɗuwa. Goggo sala ta fara wassafo jawabi tiryen-tiryen tana hawaye. Tana gama jawabi gabaɗaya ɗakin suka ɗauki salati. "Kaico rayuwa ni Kulu me na haɗa da sata da Isuhu zai janyo mini mugun hali cikin zuri'ata." Dada ta furta tana zubar da ƙwallah. Malam na Madina da ke gefe ya ce. "An ya Isuhu yanzu rayuwar da ka ɗauko mana kenan? Wallahi ka yi gaggawar yin istigifari kuma ka nemi masu kaya ka mayar musu da abin su. Idan ba haka ba muna cikin Firdausi kana Hawiya, atoh faɗar Allah ce ba ya yafe haƙƙin wani a kan wani." Shiru ɗakin ya yi kunyar duniya ta mamaye baba Isuhu shi da su Lami. Baba Idiris da baba Mustafa suka rufe shi da faɗa sosai, don haka ya nuna nadamarsa a fili. Sannan baba Mustafa ya juyo wurin Dada. "Dada ki gafarce ni a game da abin da zan faɗa amma tun farko ke ce kika ɓata Isuhu, saboda Isuhu yana ɗan autanki kika ɗauki son duniya kika ɗora masa. Hatta makaranta da Baba Sa'idu ya saka shi daina zuwa ya yi kuma kika goya masa baya, duk cikinmu shi kaɗai ne bai samu karatun arabi da boko mai zurfi ba. Ga shi nan sana'o'in ma wacce ce ba a nuna masa ba amma kullin a tsalle-tsalle yake ba shi da aiki sai kame-kame, tun wuri ka yi wa kanka faɗa domin kullin girma kake ƙara yi." Dada ta sharce ƙwallar da ke fuskarta ta ce. "Yanzu dama Muɗɗafa ka na da tarin nasihohin nan tutuni ba ka yi mini ba? Ni dai wannan maganar a rufe ta a nan kada Sa'idu ya ji don wallahi sai ya kusa cinye ni ɗanya." Gabaɗaya suka amsa mata. "Dama wannan abin kunyar ai ba za mu bari ya fita ba Dada, yanzu dai a tambayi Uwani tun da haƙƙinta ne ta yafe masa?" Uwani da ke gefe ta saki murmushin ƙeta ta yi saurin cewa, "Ni dai Baba na riga da na yafe musu baba Isuhu ai tamkar mahaifina na ɗauke shi." Da sauri Jafar ya dube ta don haka kawai ya ji bai yarda da kalaman Uwani ba. "Allah Ya yi miki albarka Uwani, dama ɗa ba sai wanda ka haifa ba kaico rayuwa Allah Ya gafarta wa Yaya Umaru." Baba Isuhu ya faɗa yana sharce ƙwallah. Uwani ta saki murmushin ƙeta a ranta ta ce, "Za ka ga ɗa ba sai ka haifa ba." Baba Idris ya yi musu nasiha sannan ya ce shi da kansa a ranar zai kira su Aramma na gangare su yi saukar Alƙur'ani a gidan gabaɗaya. "Baba ni fa gani nake wannan abin da aka yi musu kawai tsoratarwa ne wani ke yi musu, idan aljanun gasken ne ai da tuni sun ɗauki mataki. Kada a yi wasa da hankulan mutane a dai duba lamarin." Jafar ya yi maganar yana zuba wa Uwani kallon tuhuma, don yadda ya ga tana sakin murmushi ya ji sam bai yarda da ita ba. "Koma dai mene ne ai babu abin da ya fi ƙarfin Ubangiji Jafaru. Allah Ya yi mana maganin wannan masifa." Baba Mustafa ya faɗa, gabaɗaya suka amsa da Amin. Uwani na haɗa ido da Jafar ta sakar masa harara, haɗe da murguɗa masa baki. 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 [09/06/2024, 12:01] Ameera Adam: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA BIYAR Kasancewar sunan gidan baba Isuhu ya zo a lokacin hutun zangon karatu ya sa ilahirin zuri'ar gidan sun hallara, musamman da ya kasance baba Mamman ya dawo gida ne gabaɗaya domin lokacin ritayarsa ta kusa. Kuma a wannan kwanakin ne yake shirin tarewa a katafaren gidan da ya gina a nan cikin Unguwar rijiyar zaki da ke jihar Kano. Hajiya Saratu da iyalanta sai shan ƙamshi suke yi suna kallon mutane ɗaiɗai, don ko maganar arziƙi ba ta cika haɗa ta da sauran facalolinta ba. Sanin halinta na raini da wulaƙanci ya sa suma sauran mutanen gidan suke kama mutumcinsu ba tare da sun shiga sabgarta ba. Asalin Tarihinsu Malam Haruna mai shanu shi ne ainihin cikakken sun marigayi malam mahaifin su baba Isuhu. Asalinsa mutumin garin Rigana ne da ke cikin ƙauyen lambar ƙunci, ɗaya daga cikin ƙananan ƙauyukan da ke jihar Kanon Dabon Najeriya. Sunan mai shanu ya samo asali ne tun a wurin mahaifinsa kasancewarsa fitaccen bafulani a wannan ƙauyen, duk girman garin Rigana babu mai albarkar shanu da dabbobinsa. Yana da matar aure ɗaya da 'ya'ya biyu sakancewar duka maza, Malam Haruna shi ne babba sai ƙaninsa mai bin sa Sa'idu wanda bayan su mahaifinsu bai sake haihuwa ba. Bayan mahaifiyar su malam mahaifinsu ya auri mata biyu sai dai ko ɓatan wata babu wacce ta taɓa yi. Mahaifiyarsu ta rasu tun suna samari yayin da mahaifinsu ya rasu bayan da kowannen su ya yi aure a lokacin Malam haihuwarsa biyu. Baffajo tun da ƙuruciyarsa yakan ɗebi shanu da awakinsa su tafi garuruwa kiwo bayan wani lokaci sai ya dawo gida, hakan yake yi har zuwa lokacin da su Malam suka zama samari suma yake nuna musu hanyar kiwon shanu. Sai dai tun suna yara ya fahimci sam ba su da ra'ayin kiwace-kiwacen shanun da yake yi, bayan da mahaifinsu ya rasu sai suka ɗora daga inda ya tsaya sai dai su ba kamar Baffajo ba. Don tun bayan da ya rasu bai fi sau uku zuwa huɗu suka fita da shanu zuwa wasu garuruwan ba. A wannan lokacin ne kuma watarana bayan malam ya fita da shanun su da suka gada a wurin mahaifinsu, ya yi nisa sosai da garinsu sai ya faɗa tarkon wasu 'yan fashin daji. Kasancewar kuma sarkin yawa ya fi sarƙin ƙarfi sai suka yi masa ƙwacen shanu da yawa, kaɗan ya rage ba su hallaka shi ba ya dawo gida da tsirarun shanun da ko goma ba su kai ba. Wannan yanayin da suka shiga wasu sun dasa zargin har da saka hannun mutanen garinsu, yayin da wasu kuma suka ce jarabta ce kawai daga wurin Ubangiji. Dalili kenan da ya sa bayan da malam ya warke suka haɗa kai shi da ɗan uwansa suka bar garin gabaɗaya tare da sayar da shanunsu, suka dawo wani ɗan ƙauye a nan garin Kura suka kafa kasuwancin su. Kuma cikin hukuncin Ubangiji sai Allah ya saka musu albarka. Hauwa kulu Ibrahim mai allo shi ne cikakken ainihin sunan Dada asalinta mutuniyar garin Bauchi ce, baƙar bafulatana ce tana da kyau daidai gwargwado. Mahifinta Malamijo ɗan gidan malamai ne domin a rigarsu gidan su Dada ba ɓoyayyan gida ba ne. Mahaifinta yana da mata biyu da 'ya'ya bakwai. Musa shi ne ainihin sunan malam na Madina, kuma shi ne babban yayansu Dada uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Ya auri matarsa bayan zamansu mai tsawo Allah Ya yi mata rasuwa, sai dai bayan ita ya yi aure-aure da dama bai taɓa samun haihuwa ba. Dada ita take bin shi sai kuma Fatsime take bin Dada sai dai akwai tazara sosai tsakanin Dada da Fatsime. Fatsime ta rasu a wurin haihuwa, ta rasu ta bar 'yarta Abuwa dalilin da ya sa Dada ita da na Madina kaɗai suka rage waɗanda suke uwa ɗaya uba ɗaya. A lokacin da mahaifiyar su Dada ta haifi Fatsime har ta cire rai da sake samun haihuwa. Hasiya, Safare, Sule da Gali sune sauran 'yan uwan Dada da suke Uba ɗaya. Malam ya haɗu da Dada ne a lokacin da suka tafi kiwo garin Bauchi tun mahaifinsu na raye, don haka ba a ɗauki lokaci ba aka tsayar da maganar aure bayan wani lokaci aka ɗaura musu aure. Da yake Dada nesa da garinsu za a kai ta sai mahaifinta ya haɗa ta da ƙanwarta Fatsime, a kan bayan wani lokaci idan Dada ta saba sai Fatsime ta dawo. Sai dai ko da Malamijo ya buƙaci Fatsime ta dawo malam da kanshi ya je har garin Bauchi ya roƙi arziƙin a bar musu Fatsime a wurin su. Ganin yadda malam ke kula da Dada da kuma girman da yake ba shi sai ya kawar da kai ya haƙura ya bar masa ita. Dada da malam sun haifi 'ya'ya tara bakwai maza sai biyu mata. Baba Yunusa (Soja ne), baba Mustafa (Road safety ne), baba Idris (Malamin makarantar secondry ne), baba Mamman (Ɗan sanda), baba Rufa'i (Likita), Atika, Halimatu, marigayi Umaru wato mahaifin Uwani sai kuma Baba Isuhu (Sayar da itace yake yi). Baba Sa'idu (Ƙanin malam) Yana da mata ɗaya da 'ya'ya biyar. Biyu maza sai uku mata. Ya auri matarsa ne tun a garin Rigana, kuma tin bayan komawarsu Kura da suka fara kasuwanci shi da ɗan'uwansa, sai ya fara tafiye-tafiye zuwa garuruwa. Sannu a hankali sai nemansa ya fi ƙarfi a garin Zaria, don haka ya ɗauki iyalinsa suka koma can da zama. Cikin ikon Allah kowannensu ya ci gaba da zama da iyalinsa. Da yake Dada kwanika ta dinga yi gabaɗaya 'ya'yanta tazarar su babu yawa, kuma a lokacin da take da cikin Baba Isuhu ne Allah ya yi wa malam rasuwa. Kafin rasuwarsa ne ya biya mata Makka, zuwan farko umara ta je ta yi sai zuwa na biyu da suka je tare suka yi aikin Hajji. Malam Sa'idu ya kaɗu da rashin ɗan uwansa domin ko mutuwar mahaifinsu ba ta bige shi haka ba, daga nan kuma ya riƙe dukiyar ɗan uwansa da amana yana juya musu. Kuma ya ci gaba da tallafa wa Dada ita da yaranta, ya tsaya musu kai da fata suka samu ilimin addini da na zamani kuma har Allah ya ci da su suka samu aikin yi. Sai dai ba da aikin Gwamnati kaɗai suka dogara ba domin suna harkar kasuwancin kayan robobi da harkar kayan abinci. Baba Mamman yana da matar aure ɗaya Hajiya Saratu da yara biyar. Jafar shi ne babba, Ibrahim, Shukra, Jidda, sai Mufida wacce suke kira da Auta. Hajiya Saratu 'yar aminiyar mahaifin baba Mamman ce, ba ta da son mutane ko kaɗan. Mace ce mai faɗin rai da taƙama uwa-uba tana da son kanta, ga ta da tsananin kishi sannan akwai ta son hulɗa da matan masu kuɗi. Wannan halin na ta ya sa ko kaɗan ba ta jituwa da Dada, kuma kusan halayenta ne su Shukra suka kwasa gabaɗaya. Jafar da Ibrahim ne ba su da irin halinta sai Auta don haka har sun fi su Shukra sabo da mutanen cikin gida. Gidan marigayi malam Haruna mai shanu gidan gandu ne da ya haɗa kakanni, iyaye, jikoki da kuma 'ya'yan jikoki. Baba Mamman da Baba Yunusa ne kaɗai ba sa zaune a cikin gidan, kasancewar yanayin aikinsu da sauye-sauyen garuruwan da ake yi musu a wurin aiki. Amma kowannensu yana da ɓangarensa a cikin gidan, idan suka zo hutu suna sauka da iyalansu a ciki. Marigayi Umaru Haruna Mai shanu shi ne mahaifin Uwani, ya rasu tun mahaifiyar Uwani na da cikinta wata bakwai sakamakon hatsarin mota. Maryama Shu'aibu shi ne ainihin sunan mahaifiyar Uwani, dalilin mutuwar mahaifin Uwani ya sa Dada da su Baba Mamman suka ci gaba da kula da ita. Bayan wata tara Allah Ya sauke ta lafiya ta haifi jaririyarta, ta ci burin idan namiji ne ta mayar da sunan mijinta Umaru. Amma da ta haifi mace su Dada suka tambaye ta sunan da take son a raɗa wa jaririyar, da kanta ta ce a saka sunan Dada saboda irin karamcin da suka nuna mata, sai ake kiranta da suna Uwani. Bayan da aka yaye Uwani ne mahaifin Maryama ya nemi da ta dawo gabansa da zama, domin zawarawa suna ta zuwa kai masa gaisuwa da nuna ƙoƙon bararsu a kan aurenta. Ranar da za ta tafi ne Dada ta nemi da ta bar mata Uwani saboda soyayyar da take yi wa mahaifinta, idan tana ganinta za ta dinga jin daɗi. Bayan komawar mahaifiyar Uwani gidansu ko shekara ba ta rufa ba aka ɗaura mata aure da wani mutum, a lokacin yana da aure da mata ɗaya da yara huɗu. Maryama ta aure shi ne ba don tana son shi ba, sai don kawai ta yi wa mahaifinta biyayya amma har lokacin zuciyarta na ga mahaifin Uwani. Garin da take aure yana nesa da garin su Uwani sosai, kuma ta haifi yara biyu da malam Salihu mace da namiji, sai dai ko kaɗan ita da kishiyarta ba sa jin daɗin zama da shi sakamakon mugun halinsa. Uwani ta taso a hannun Dada cikin kulawa da nuna tsantsar soyayya, tun bayan tafiyar mahaifiyarta baba Mamman ya so a ba shi riƙon Uwani amma fir Dada ta hana shi, lokacin da Hajiya Saratu ta ji ba ƙaramin daɗi ta ji ba. Shekarun Uwani goma sha huɗu a duniya kuma irin fitinannun yaran nan da suke fita zakka ko a cikin unguwa. Rashin ji, rashin tsoro, kafiya, naci, tsokana rashin yafiya sune halayen da suka mamaye Uwani har mutanen garin suka saka mata suna 'Uwani 'Yar Ƙashin Gwiwa' saboda hatsabibanci da rashin jin ta. Duk cikin gidan mai shanu Dada ce kaɗai ba ta ganin laifin Uwani, don haka ma duk wurin da ta shiga sai dai su bi ta da harara. Jafar ma'aikacin ɗan sanda ne mai ɗauke da muƙamin ASP, shekarunsa talatin da biyu cif a duniya. Ya yi karatunsa tun daga primary har zuwa matakin degree a jami'ar Bayero University. Miskili ne bai cika surutu ba, sai dai wani lokacin bauɗaɗɗan hali gare shi. Yana da kirki ga wanda suka fahimci juna sai dai wani lokacin yana da saurin fushi. Ba ya son raini ko kaɗan kuma yana da kykkyawar mu'amala da abokan aikinsa. Lokacin da ya fara aiki jihar Kaduna aka tura shi bayan wani lokaci ne ya samu sauyin aiki zuwa garin Katsina daga baya aka mayar da shi garin Lagos, ya kwana biyu a Lagos don bai cika zuwa hutu sosai ba. Ko da ya zo ma a gurguje yake kawo wa Dada ziyara shi ya sa Uwani ba ta wani san shi farin sani ba. Tana yawan jin labarin irin kulawar da Jafar ɗin ya dinga ba ta a lokacin da take yarinya, sai dai a wannan karon sam ba ta ga kalar mutumci a tattare da shi ba. Wannan hutun da Jafar ya samu kusan wata guda zai yi kafin ya koma, kuma ya ji labarin zuwan mahaifansa hutu da tariyarsu don haka shi ma ya yada zango a nan sashen Dada. Mu Koma Labari Tamkar sabuwar munafuka ko ɓarawon da yake sanɗa a daidai gaɓar da yake ɗaukar abin da ba na shi ba, haka Uwani ta shiga cikin ɗakin saɗaf-saɗaf tana tafe tana waige. Sai da ta kai ga ƙuryar ɗakin sannan ta sauke gwauruwar ajiyar zuciya. "Uban 'yan iyayi ashe ba ya cikin ɗakin, da tuni yana nan a naɗe a kan katifa kamar mai karyayyan ƙugu." Ta furta cikun salon kwaikwayon muryarsa. Motsin da ta ji a bayanta ne ya sa ta yi mutuwar tsaye, zuciyarta ta fara harbawa tamkar za ta bijirewa zama a ƙirjinta, cikinta ya shiga juyawa yayin da zazzafan gumi ya shiga keto mata. Caran zakaran da ta ji a bayanta ne ya sa ta sake sauke ajiyar zuciya, ta saki murmushi a fili sannan ta furta. "Lawan wallahi ka cika binbinin tsiya, yanzu ɗakin Ofisa ma sai ka biyo ni. Idan kuwa ya kama mu wallahi sai ya kusa murɗe maka wuya." Tamkar zakaran ya san da shi take ya ci gaba da takawa yana tafe yana sakin kashi a tsaftataccan ɗakin da ya sha gyara ta ko ina sai zuba ƙamshi yake.   Kafin Uwani ta ƙarasa kan katifar ɗakin tuni zakaranta da take kira da Lawan ya yi mata jagora zuwa kan luntsumemiyar katifar da ta sha gyara, a ɗame take da zanin gado kamar gadon sabuwar amaryar da za a kai ɗakin miji. "Lawan ina ka baro Fanteka, uwar 'ya'ya na san tana cen tana yawo ita da 'ya'yan iya." Uwani ta yi maganar kamar da mutum ɗan'uwanta take yi. A saƙale ta hango uniform ɗinsa na kayan 'yan sanda masu bulun riga da baƙin wando. Da sauri ta janyo ta hau kwaɓe kayanta kafin wani lokaci tuni ta saka a jikinta, sai da ta gama soshe kanta da ya cukurkuɗe sannan ta kafa baƙar hularsa a kanta. Cikin ƙwambo ta fara taku ɗaiɗai sannan ta cake a wuri ɗaya. "Ba na son hayani matsa daga kaina, ƙazama mai kwarkwata." Ta yi maganar cikin kwaikwayar maganar Jafar, tana faɗin irin maganganun da yake faɗa mata.  Ta jima a tsaye tana surutanta sannan ta ƙarasa gaban mudubin da ke can gefenta, kamar a mafarki haka ta hange shi tsaye ƙyam kamar wanda ya haɗiyi falwaya. Fuska a haɗe kwatankwacin ta fusataccan bujumin sa. Nan take yawun bakinta ya ƙafe, ƙafafuwanta suka ɗauki rawa ƙirjinta ya shiga harbawa. Sai dai dakiya da ƙarfin zuciyar Uwani ya sa ta basar kamar ba ta gan shi ba. "Iya iya iya." Ta ji 'ya'yan kazarta na faɗa yayin da zakaran da ya gama kasaye ɗakin ya fara cara, da sauri kazar ta tunkaro ɗakin da niyyar shiga a fusace Jafar ya sa ƙafa ya yi ball da ita. Wata azababbiyar ƙara Uwani ta ƙwalla kamar da ita Jafar ya yi ball, ta fara tafiya wandon uniform ɗin yana zamo mata. "Innalillahi kashe mini fantake za ka yi..." Uwani ta yi maganar tana shirin fita daga ɗakin, yayin da Lawan (Zakaranta) ya firgice yana tsalle-tsalle a ɗakin, yana jefo masa kwalaben turare. "Gidan uban wa za ki?"Jafar ya wurga mata tambaya rai a ɓace. "Ina da gidan da ya wuce ɗakin Dada..." Jafar ya katse maganarta ta hanyar bige bakinta da ƙarfi. "Wallahi na ba ki nan da minti goma ki gyara mini ɗakin nan, sannan ki yi gaggawar cire mini uniform tun ranki bai ɓaci ba. Kuma idan kin gama zan gauraya da ke." "Sai ka fita na canza kaya." Sororo ya yi yana kallon Uwani don bai san lokacin da ta raina shi ba. Yana shirin sauke yatsunsa biyar a fuskarta wandon uniform ɗin ya zamo mata, gajeren wandon da ke jikinta ya bayyana. Fari ne amma dauɗa da jirwaye sun sa ya dafe saboda ƙazanta. A ƙazance ya kawar da kai gefe haɗe da tofar da yawu. "Ka san dai kallon tsiraici haramun ne, ka fita na sauya kaya. Kuma ni dai ba 'yar iska ba ce..." "Idan ba ki rufe mini baki ba wallahi sai na haɗa miki jini da majina a wurin nan. Sakarya fuska kamar ta aljanu, daga yau ko wani ne ya aiko ki ɗakin nan ba za ki ƙara marmarin shigowa ba." Tun da Jafar ya fara magana Uwani take kallonsa sheƙeƙe tun daga sama har zuwa yatsu biyar na ƙafarsa. Ba ta yi aune ba ta ji ya zuba mata rankwashin da ya sa ta gagara gane muhallin da take tsaye. Cikin sauri ta fisge hular kanta, ta zame dogon wandon uniform ɗinsa da ke jikinta. Jafar na nan tsaye ya ji tuuush! Lawan ya jefo sabuwar kwalbar turarensa, a firgice yake miƙa wuya yana cara haɗe da ci gaba da taka kayan da ke saman mudubin. A zuciye Jafara ya jefa masa takalmin kanbas ɗinsa. Firgitar da Lawan ya yi har cikin ran Uwani don haka cikin ɓacin rai ta ce, "Allah dai ba ya zalinci yana kallon baƙaƙen azzuluman duniya masu baƙaƙen kaya." A fusace Jafar ya yo kanta rai a ɓace, ganin haka ya sa Uwani ta zuba a guje kai tsaye ta wuce sashen Dada Jafar ya rufa mata baya. A daidai lokacin da Jafar ya nufi sashen Dada shi kuma malam na Madina ya kawo kai, cikin rashin sani Jafar ya bangaje shi kaɗan ya rage gemunsa ya taɓa ƙasa. "Jafaru! Kai Jafaru kana ji ka angije ni kamar ka angije dabba? Wallahi duk laifin Kulu ne ni take nunawa 'ya'ya da jikoki sun fi ɗan uwa." Ya ci gaba da tafiya har bakin ƙofar Dada yana kiran sunanta. "Kulu! Kulu kina ina ne..." Cikin sauri Malam na Madina ya datse ragowar kalaman bakinsa jin furucin da Jafar ke faɗa.   "Wallahi tun wuri ki wuce mu je ɗakina don har kan katifa..." Uwani ta yi farat ta katse shi. "Amma dai ai ka bari na saka kayana yaya Jafaru, wallahi na fita a haka ka san dai mutanen gidan nan kowa sai ya san abin da yake faruwa." Jafar ya yi ƙwafa yana shirin ba ta amsa daga can waje ya ji muryar Malam na Madina yana sallallami. "Yanzu Jafaru dama munafurcin da kuke aikatawa kenan? Shi ya sa saboda sauri har ka angije ni ko waige na ba ka yi ba. Ba da ni ba, wallahi ba zan zauna ana aikata alfasha ina kallo ba, lokaci ɗaya Ubangiji ya halakar da mu." Sai da Jafar ya fito daga ɗakin Dada ya samu Malam na Madina da ke bin shi da ƙazantaccan kallo. Ficewa ya yi daga sashen Dada ya faɗa ɗakinsa, akwatin kayansa ya janyo ƙiiiiii yana kokawar fito da ita Dada ta sako kai ciki. Jin motsin ya yi yawa ya sa ta fara mita. "Waɗannan dabbobi na Uwani yadda kasan tare aka shayar da su saboda duk hatsabibancinsu iri ɗaya ne..." Ganin Malam na Madina ya janyo akwatinsa ƙiiii ya sa Dada sakin baki, "Wai Muda ne a wurin nan ko Usumanu?" Ta wurga masa tambaya tana ɗan ƙanƙance ido. Sai da Malam na Madina ya fito sannan ya ce. "Ki yafe ni Kulu don kar na tafi da haƙƙin wani a kaina." Baki sake Dada ta ce, "Yaya wani abin aka yi maka ne?" Malam na Madina ya share ƙwallar idonsa, ta waiga wurin da Jafar yake tsaye a bakin ƙofa ya jefa masa mugun kallo sannan ya furta. "Ubangiji aka yi wa laifi, ni dai tsakanina da mutanen gidan idan na ce an yi mini wani abu na ɗauki haƙƙinsu. Amma ni kam ba zan zauna ina ji ina gani a dinga saɓon Allah ba, gara na mutu salin-alin da a tashi idanuwa su bada shaidar baɗala ranar Lahira." Malam na Madina na gama magana ya fara jan akwatinsa ƙiiiii, da sauri Dada ta sha gabansa don tuni hankalinta ya tashi idonta ya fara ciko da ƙwalla. A duniya idan akwai abin ta tsana shi ne a ɓata ran Malam na Madina. Jafar ya kafe Malam da kallo yana jin kamar ya ƙarasa ya shaƙe shi ko ya rufe shi da duka. "A duniyar nan dai Yaya ka san mu biyu kaɗai muka rage, kuma kai ne uwata kai ne ubana kai nake gani na huce rashin su marigayi, (Iyayensu) don Allah ka faɗa mini abin da yake faruwa."Dada ta yi maganar tana share ƙwalla. "Waye wancan a tsaye?" Na Madina ya nuna Jafar a daidai lokacin Uwani ta leƙo don jin abin da yake faruwa daga ita sai gajeren wandon jikinta, ta tuɓe riga ta rufa hijabinta a saman ƙirjinta. Dada ta kai kallonta wurin ta ce, "Jafaru ne sai Uwani da ta fito." "Amma a rigar kwasam na san ba za ki manta Iron Alto ba?" A firgice Dada ta kalle shi, ba ita ba hatta Jafar ya san labarin Iron Alto a bakin Dada. Dada na shirin magana Malam na Madina ya katse ta. "To Ta'adar Iron Alto na ji waɗannan yaran suna aikatawa..." Tun bai rufe baki ba Dada ta saki butar hannunta wacce ta ɗauro alwala da ita jiki na rawa. Yau dai bari mu tsagaita dariyar na ga jiya har da masu shiɗewa 😂 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 [10/06/2024, 10:59] Ameera Adam: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA SHIDA Dada ta zuba musu ido ganin yanayin da Uwani take ciki ya sa ta aminta da kalaman ɗan'uwanta, ta san dai ba zai taɓa yi musu ƙarya ba. Runtse idonsa Jafar ya yi yana fesar da iska mai zafi, ya buɗe idanunsa da suka rine jawur kamar gauta ya sauke su a kan malam Na Madina. A fusace ya ƙarasa gabansa ya cukwikwiyo babbar rigarsa ya riƙe shi wuri ɗaya rai a ɓace ya furta. "Wallahi ba don ina duba tsufanka ba, da yau sai na bambamce maka tsakanin zuma da maɗaci." Jafar ya sake shi sannan ya wuce ɗakinsa, saboda tsoro tuni malam Na Madina ya yi mutuwar tsaye. Dada ta bi bayan Jafar da kallon tsoro baki a sake. "Yaya an ya Jafaruna ne ba aljanu ne a kansa ba..." Kuka ya katse maganar da Dada take yi. "Sharrin ƙwaya ce Kulu, na sha faɗa miki wannan aikin ɗamarar ba zai haifar da samun ɗa mai ido a cikin zuri'armu ba. Yanzu wa gari ya waya? A ce Jafaru bai san Kano garin Musulunci ba ne? Ya ɗauka rayuwar da yake yi a Legas ita zai yi a gidan nan. Kin ga dai abin da ya faru a gabanki. Da fa dukana zai yi, kaico rashin haihuwa ne ya ja mini haka." Na Madina ya fashe da kuka, Uwani da ke gefe ko a jikinta ta shige ɗaki ta ci gaba da sauya kaya. Don ita hakan da ya faru ma daɗi ta ji, ko ba komai ta san Jafar da zuciya ba lallai ya sake shiga sashen Dada ba sai bayan kwana biyu, ballantana ya hora ta a kan laifin da ta yi masa. Tana gama sauya kaya ta fice a nan harabar gidan ta ga Lawan da matarsa Fanteka, 'ya'yan ta ɗibo ta yi hanyar keji da su uwar ta rufa musu baya. Sai da ta dawo ta ga Lawan yana tsince-tsince a wurin akuyoyinta. "Kai dai Lawan ka cika ɗan kishiya riƙon mai haƙuri, wallahi da kiwon ka aka ba ni da ka ja mini zagi a ce na bar ka da yunwa." Uwani ta yi maganar tana ƙoƙarin kama shi, Lawan ya yi tsalle zai dira a kan katangar gidan Baba Isuhu da ƙyar ta kama shi tana sakin murmushi. Kai tsaye sashen Dada ta wuce tana shiga ta ci karo da Jafar ya fito ɗauke da jaka a kafaɗa.   "Marar gaskiya ko a ruwa gumi yake. Yaya ka ga yaron nan saboda ya san tsiyar da ya shuka fita zai yi ya bar mu, ni dai wallahi Sa'idu ya cuce ni duk wannan abin da yake faruwa Sa'idu ne sila." Jafar bai bi ta kan su Dada ba ya fice daga gidan har yana hankaɗe Uwani. "Kulu Allah Ya ba mu alheri, wallahi Jafaru ba zai yi mana turun jeka ka mutu ba. Ya shuka bishiyar tsiya mu da ba mu ji ba, ba mu gani ba mu girbe masa." Malam na Madina ya sake jan jaka ganin haka ya sa Dada ta ce. "Ka jira ni yanzu zan kira Inusa dole ya tara mini 'yan'uwansa a gidan." Dada ta yi maganar tana faɗawa ɗaki domin ɗauko wayarta. "Inusa a yanzu ba sai gobe ba ka tara mini 'yan'uwanka, wallahi idan ba haka ba zan bar muku gidanku na shiga duniya. Kuma ku yi gaggawar kiran Jafaru ku ce ya dawo don zaman nasu ne, shi da Uwani ne suka ƙulla tsiyar da bakina ba zai iya furtawa ba." Daga haka Dada ba ta sake cewa uffan ba ta kashe wayarta, da kashe wayar babu jimawa Baba Yunusa ya sake kiranta, Dada na ɗauka ta ce. "Yunusa wai wa muke yi wa Sallah da azumi?" Daga can ɓangaren Baba Yunusa ya ce. "Allah." Dada ta sake haɗe fuska kamar yana ganinta ta ce. "Da ma saboda na fita haƙƙinka a matsayinka na babba shi ya sa na kira na sanar da kai, wallahi idan ba ka haɗo mini kan 'yan uwanka ba sai dai ku nemi wata uwar ba ni ba." Dada za ta katse da sauri Baba Yunusa ya ce. "Shi kenan Dada ga mu nan zuwa yanzu In shaa Allah." Ta amsa masa sannan ta katse wayar, sai da ta lallami Na Madina sannan ya mayar sa akwatinsa. Falon tsit ya yi da ka kalli fuskokinsu ka san kowanne yana cikin damuwa, Baba Yunusa ne ya yi  ƙarfin halin cewa. "Dada gaba ɗaya ga mu mun hallara." Jafar tun da ya sunkuyar da kai ƙasa zuciyarsa ke tururi, Uwani na raɓe a gefe sai raba ido take kamar ƙosan sadaka. Ganin haka ya sa jikinsu ya sake yin sanyi, don sun tabbata banza ba ta kai zomo kasuwa.   Sai da Na Madina ya kalli Jafar da Uwani sai ya sake fashewa da kuka, ganin haka ya sake raunata zuciyar Dada ta ja gefen mayafi ta fara sharce hawaye sannan ta fara magana. "Gabaɗayanku na tabbata idan za ku yi mini shaidar Allah da Annabi, za ku yarda da abin da zan faɗa." Suka amsa mata cikin haɗin baki. Dada ta ci gaba da ce wa. "Wallahi ƙanin mahaifinku Sa'idu ya cuce ni cutar ta har abada, amma ya je ba ni ya yi wa ba zumuncin Allah ya yi wa kuma ranar gobe ƙiyama sai igiyar zumunci ta zarge shi. Ni dai ba zan shiga tsakaninsa da Ubangiji ba amma sai mun tsaya a gaban Ubangiji ni da shi." Sororo gaba ɗaya suka yi hankali a tashe suna kallonta. Baba Yunusa ya ce. "Dada me yake faruwa haka ne Baba Sa'idu fa? Baba Sa'idu da ya zame mana bango madafa kuma majingina, mutumin da ya maye gurbin mahaifinmu..." "Inusa wa ya samar maka aikin Sojan nan? Kuma wa ya samarwa ɗan'uwanka Mamman aikin Ɗansanda, shi kuma wancan Rosofti?" Dada ta Katse shi. "Duka Baba Sa'idu ne ya samar mana Dada wani abu ne ya faru?" Ya tambaye ta a sanyaye. "Aikin ɗamarar ba shi ya kai Jafaru Lagas ba?" Duka suka amsa mata, jin furucin Dada ya sa Jafar ya ɗago a fusace. Dada ta cigaba da faɗin. "Silar haka ai ga shi muna shirin samun Iron Alto na biyu a cikin gidan nan." Jin kalaman Dada ya sa gaba ɗaya suka ɗauki salati hankali a tashe. Baba Isuhu ya wurga wa Jafaru wani mugun kallo cike da ƙyama, yana riƙe da haɓa hannunsa ɗaya kuma na riƙe da mai sunan Malam. Sai da ɗakin ya lafa da hayaniyar da ake yi sannan Na Madina ya ce, "Wallahi ba tun yau ba shi ya sa magana ta a kullin yaran nan a aurar da su, amma da yake nasara ya hure muku kunne sai ku ce yara sai sun yi karatu. Yanzu dubi garsamemen ƙato kamar Jafaru a ce bai yi auren fari ba, ni wallahi ina kamarsa da Allah Ya ba ni haihuwa da na yi 'ya'ya uku. To yanzu me ya fi wannan haushi? Wa ya sani ma a Lagas ɗin ko 'ya'yan ƙedarai ne suka suke buɗe masa idanu, yake wartar ɗaya bayan ɗaya yana sakayewa a gefe. Ga shi nan yanzu ai ya gagara haƙuri ya ja Uwani ɗakin Kulu suna watsa wa sunnar Ma'aiki ƙasa a ido." Kamar haɗin baki gabaɗaya mutanen ɗakin suka furta. "Innalillahi Wa'inna ilahirraji'un."   Duk budurin da ake yi ko a jikin Uwani ita babbar damuwarta ba ta wuce ta samu ta tsira daga horon Jafar ba, don ta san yadda ransa ya ɓaci idan ta shiga hannunsa sai Allah. Ran Jafar ya kai matuƙar ƙololuwar ɓaci don haka a zuciye ya buga tsaki haɗe da miƙewa zai fice daga ɗakin. "Wallahi matuƙar Jafaru ya fita daga ɗakin nan Mamman sai ka bi ɗanka, tun da ni da ɗan'uwana ba mu isa da shi ba." Dada ta yi furucin rai a ɓace. "Koma ka zauna Jafar." Mahaifinsa ya furta murya a dashe saboda ɓacin rai.   "Daddy wai ba ka ji me waɗannan mutanen suke faɗa ba ne? Wannan wanne irin abu ne. A ce a rasa ƙazafin da za a yi mini sai na zina, kuma na rasa da wa zan yi sai Uwani yarinyar da ƙazanta ta samu gurbin zama a ilahirin jikinta..." Na Madina ya katse Jafar sakamakon rarrafowar da ya yi, ya dafa ƙafarsa. Kwanciya na Madina ya yi a gabansa sannan ya fashe da kuka. "Don Allah kada wanda ya hana Jafaru ya rufe ni da duka, dama ɗazu ka so dukana to ka saka bindiga ka tashi kaina a kan waɗannan magangun da kake faɗa mana ni da 'yar uwata." Na madina ya furta ƙwallah na zuba, idan ka ga yadda yake rusar kuka sai ka rantse da Allah wani abin aka yi masa. "Ba na son sakarci ka koma ka zauna Jafar." Mahaifin Jafar ya buga masa tsawa. Sai da ya haɗiyi yawu mai ɗaci sannan ya koma ya zauna yana wurga wa su Na Madina harara, ya sunkuyar da kai ƙasa cikin ɓacin rai. Baba Inusa da kansa ya ƙarasa ya tashi Na madina ya koma mazauninsa sannan shi ma ya koma ya zauna.    Baba Rufa'i ya gyara zama, sannan ya fara magana. "Dada duk mun ji abin abin da yake faruwa amma don Allah ku gafarce ni a maganar da zan faɗa." "Kayya Rufa'i muke wa Ubangiji laifi ma ya yafe mana, ballantana ɗan'adam abin banza." Cewar Dada. "A iya sanin tarbiyyar da yaran nan suke da ita ba mu taɓa tsammanin haka za ta taɓa faruwa ba, sai dai kuma ɗa ne ka haife shi ba ka haifi halinsa ba." Dada ta jinjina kai jin kalaman Baba Rufa'i yana shirin ci gaba da magana ta katse shi. "Ai albasa ce ba ta yi halin ruwa ba Rufa'i, wai a rasa wurin da za a yaye wa sunna labulen albarka sai a ɗakina. Kaico ni Kulu." Sai da Dada ta yi shiru sannan ya ɗora. "Kai Jafar ina maka kallon mai hankali ya aika yi haka ta faru?" Kai tsaye Jafar ya nuna su Dada murya a shaƙe ya ce. "Baba a tambaye su ni kaina sama ta ka na ji abin da suke faɗa." "Ba ni da ɗan uwana ka ƙaryata ba, uwarka Saro da ubanka Mamman su ka ƙaryata ka ji Jafaru." Dada ta furta tana wurgawa Jafar taƙuwa. "Ka shiga taitayinka Jafar? Idan na kuma jin magana mara daɗi daga bakinka sai ranka ya yi mummunan ɓaci, ke Uwani shin yau wannan abin ya taɓa shiga tsakaninki da Jafar ne?" Baba Rufa'i ya jefa mata tambaya. Zuciyar Uwani ɗaya ta share ƙwalla ta ce, "Wallahi ni kam azalce ta kai ni ɗakin Ya Jafar, ashe Lawan yana laɓe a bayana ban san ya biyo ni ɗakin ba." Cikin haɗin baki duka suka ce, "Waye Lawan? "Mijin Fanteka ne." Uwani ta faɗa cikin kuka. "Ashe ba ki da hankali Uwani? Ashe sakarcin na ki da ake faɗa gaskiya ne? A ina Lawan ɗin yake kuma ɗan gidan uban waye a ƙauyen nan? Da har zai shigo cikin gida ya bi ki ɗaki." Baba Yunusa ya yi maganar rai a ɓace. "Ban gan shi ba Baba, duk neman da na yi ban gan shi ba ma ɗazu, kuma wallahi ganin idona ya fito daga ɗakin ya Jafaru. Sororo suka yi suka gagara gane kan maganar Uwani. "Shi Lawan ɗin ne zai ɓata a gidan kamar wani zobe? Kin san me kike faɗa kuwa Uwani?" Cewar Baba Mamman. Ganin duka ba su fahimci inda maganarta ta dosa ba ya sa Dada ta ce. "Lawan ɗin da Uwani ke faɗa ba kowa ba ne fa face zakaran da take kiwo, ko ba Lawan mai wake-wake ba Uwani?" Da sauri Uwani ta gyaɗa kai.   "Ba maganar zakara muka yi miki ba, muna magana ne akan tsakaninki da jafar." Baba Yunusa faɗa. Jin haka ya sa Uwani ta kwashe duk abin da ya shiga tsakaninta da Jafar ta faɗa musu, shiru duka suka yi Dada ta dubi Na madina ta ce. "Yaya wai haka ne abin da ta faɗa? Don gaskiya shedar zir haramun ce kar Mamman ya fusata ya ce mun yi wa ɗansa ƙazafi ya kaimu kotu, alƙali ya yanke mana bulala tamanin mu shiga uku." Jikin Na Madina ya yi sanyi don shi kasan ya san zargin ne yake yi idanunsa ba su gani ba. "Ni dai Allah Ya sani ban kama Jafaru da Uwani turmi da taɓarya ba, amma na ji waɗansu kalamai da suke yi a cikin ɗakin Kulun. Don Allah me zai sa su keɓe idan ba warware mutumcin sunna suke ba?" Sai a lokacin iyalan wurin suka fahimci gabaɗaya inda maganar su ta dosa. "Amma dai Yaya ka ci zarafin zuri'ata, yanzu saboda Allah wacce ƙiyayya kake yi wa Jafaru da Uwani da za ka nemi  ka haɗa su da hali irin ta'adar Iron Alto, ni dai ku zama shaida ta daga yau ba zan sake haɗa inuwa ɗaya da Yaya Musa ba." Dada ta yi maganar cikin kuka, ta mayar da kallonta wurin su Jafar ta ci gaba da cewa. "Ban da ƙarfin alƙawari ma me zai haɗa Uwani da Jafaru? Yarinya kyakkyawa kamar Uwani a ba ta Ɗansanda, Ɗansandan ma kamar Jafar mai zuciyar masifa. Ni tsorona ma kada watarana Uwani ta yi masa laifi ya sa bakin bindiga ya bindige ta..." "Allah ya tsare ni, ni kuwa me zan yi da Uwani wallahi ko a ƙafa aka ɗaura mini ita ba zan ja ba, kai ko abokina ba zan yi wa hanyar aurenta ba, haka kawai a ce na yi sanadin auren ƙazama kamar Uwani." Jafar ya faɗa a ƙazance kamar zai yi amai. "Idan kai ba ka so ba ai tuni alƙwari ya ba ka aurenta Jafaru, shafa Fatiha kaɗai ya rage muku. Amma fa wallahi faɗi kanka tsaye Jafaru ƙazantar uwani tun da na zo duniya ban taɓa ganin ƙazama irinta ba."  Jin tonan asirin da Dada take mata ya sa Uwani tura ba ki gaba. "Rigar mama wannan Uwani ba ta san ta canza ba sai dai idan na tilastata ta sauya, ban da ma Allah Ya kawo mu zamani yaushe yarinya za ta fara saka rigar mama a gaban iyayenta? To haka take zama da tsamin hammata, rannan ina kwance a saman kaina na ji tsami ya cika min hanci wallahi ina dubawa na ga ashe ɗan diras da kanfanta ne a ajiye. Ni ina tsoron ma kar a aurar da Uwani ta shafa wa Jafaru kwarkwata, don wallahi ko gorin kwarkwata aka yi wa Uwani sai haka. Amma dai tun da Hajiya Saro (Mahaifiyar Jafar) ta daina ƙazanta Uwani ma za ta daina, don bara war haka sai da na roƙa wa Uwani addu'ar yayewar ƙazantar nan a Harami." Dada ta mayar da kallonta wurin su Baba Rufa'i sannan ta cigaba. "Yanzu dai ba za mu tashi daga wurin nan ba sai mun kammala maganar yaran nan. Kun dai ga yadda Uwani ta zama budurwa ni tsorona ma kada ta fara baƙon wata a gabana na shiga uku..." "Subhanallah wannan wanne irin mummunan fata ne haka Kulu? Yanzu saboda Nasara ya gama wanke wa su Mamman hannu a ka sai su bar yaran nan haka?" Jafar ya saki murmushin takaici don shi gani yake duk sokiburutsun tsofaffin ne. "Don Allah ku dubi fuskar Jafaru washar yadda yake sakin murmushi, ko wannan miskilancin da yake yi fa aure yake so, kuma yanzu ya samu an soso masa wurin da yake yi masa ƙaiƙayi." Na Madina ya ƙarasa maganar yana sakin murmushi. Baba Rufa'i ya yi gyaran murya sannan ya furta. "Dada dama ba mu ƙi ta ku ba, amma gaskiya shekarun Uwani sun yi ƙanƙanta a aurar da ita yanzu Ina laifin ta gama sakandire ma..." "Sakandi me? Kana nufin zan zauna ina ganin Uwani a gabana har tsawon shekara biyar? Wallahi da kunci amanar zumunci, yanzu saboda kun ga ƙasa ta lulluɓe idon mahaifin yarinyar nan shi ne za ku watsa mata ƙasa a ido. Kaico mutuwa mai yankan ƙauna. Allah Ya jiƙanka Umaru, ni na san da Umaru ne ba zai taɓa yi wa bayanku haka ba." Shiru suka yi Baba Mamman na shirin magana Na madina ya katse shi, "Amfanin me karatun bokon zai yi mata? Aure fa shi ne sunnar Ma'aiki. Yanzu Dada ba ga su Safare nan ba kowacce tana ɗakinta da 'ya'yanta, ina ce firamare kawai suka yi. Ko kuma mu iyayenku da ba mu yi yi bokon ba sai a ce ba mu ji daɗin rayuwar aure ba?" Dada ta ware hannuwa cikin gamsuwa ta ce, "Gane mini hanya Yaya, so suke yadda fitsararrun yaran can suka rasa miji ita ma ta gandame mini a gabana." "Dada domin fa mu inganta rayuwar Uwani muke son mu tsaya mata ta yi karatu kamar yadda sauran yara suka yi, amma ba don wata manufa ba. Don Allah ku fahimce mu Uwani yarinya ce, har yanzu fa ba ta cika sha biyar a duniya ba duk fa girman jiki ne." "Ni dai Baba kawai a aura mini Ofisana, kar na je Furaira ta riga ni gabatar da kanta a wurinsa. Don wallahi Furaira masifar son shi take. Ka ga ni ma sai na dinga gayu irin nasa, Allah ko su Fanteke sai sun zama 'yan gayu..." Da sauri Jafar ya katse Uwani. "Ke ba na son shashanci da rashin hankali an gaya miki ni sa'anki ne? Tun wuri dama ki nemi mijinki don ni tuni akwai wacce zan aura a Lagos..." "Lagas? Yanzu Jafaru ka rasa wacce za ka auro sai ƙedarun Lagas, wallahi ni kam dole na je Zariya na samu Sa'idu." Dada ta faɗa cike da damuwa. "Jafar wannan daɗaɗɗan alƙawari ne da na ƙulla shi shi tun ranar da Uwani ta zo duniya, kamar yadda ka sani mahaifinta ya rasu tun tana ciki sakamkon hatsarin da ya yi. Ba ta taɓa sanin fuskar mahaifinta ba sai mahaifiyarta. Tausayinta ya sa na ɗauki alƙawarin aura maka ita matuƙar kuka kai munzalin aure, tun da a lokacin ba ka fi shekara goma sha uku zuwa sha biyar a duniya ba. Daga kai har ita mu muke da iko a kanku babu wanda ya isa ya bijire wa umarninmu." Baba Mamman ya yi wa Jafar jawabi fuska a haɗe. Dada ita da na Madina suka washe baki cikin farinciki ya ce, "Wallahi ka jima ba ka faranta mini rai irin na yau ba Mamman." "To yanzu dai duk ba wannan ba, abu ɗaya zan yarda da shi. Ba zan zuba wa Uwani ido ba a yi mata aure ba har nan da shekara biyar ba. Watan Maulidin nan me zuwa ne bikin su Shukra ko?" Baba Mamman ya gyaɗa mata kai. "Nan da watan maulidi nake son a ɗaura musu aure idan ya so nan da wani lokaci sai a yi maganar tariya. Ko dai mutuwa na yi kafin lokacin na sauke nauyin da muka ɗauka, ko ba haka ba Yaya?" Dada ta furta tana kallon Na Madina, cikin gamsuwa ya amsa mata. Duk yadda su Baba Mamman suka so shawo kan Dada don ɗaga maganar fir ta ƙi amincewa. Don haka suka haƙura suka tashi daga taron, Jafar tun ba su kai ga tashi ba ya fice fuuu daga ɗakin. Ganin haka ya sa Malam na Madina ya saki murmushi ya furta. "Ja'irin yaro wannan doron da ya yi yana yin aure zai miƙe, na san yau kwanan farinciki zai yi yoo aure wasa ne." Dada ta bushe da dariya. 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 [11/06/2024, 13:08] Ameera Adam: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA BAKWAI Kamar Jafar zai tashi sama haka ya nufi sashen mahaifiyarsa saboda ɓacin rai ko gabansa ba ya gani sosai, da ƙarfi ya doka ƙofar falon Mami da su Shukra na zaune. A zabure duka suka miƙe Mami ta dube shi ta ce. "Hankalinka ɗaya kuwa Jafar? Saurin me kake yi haka?" Jafar bai tanka mata ba ya wuce kan kujera ya zauna yana furzar da iska mai zafi. Sai da ta ƙare masa kallo sannan ta ƙarasa kusa da shi ta furta. "A kullin ina gaya maka ka dinga rage wannan baƙar zuciyar taka. Me aka yi maka?" "Mami me ya sa Daddy ba ya son farin cikina ne?" Shi ma ya jefa mata tambaya. "Me ya sa ka faɗi haka?" "Yanzu Mami da girmana ni ba ƙaramin yaro ba a ce za a wani nemar mini matar aure, saboda Allah an yi mini adalci kenan? Atleast ko shawarata ai sai a nema." Nan take Mami ta haɗe fuska sai da ta sauke ajiyar zuciya ta furta. "Ina tunanin dai wasa yake yi maka, amma kuma ban da abin ka Jafar ka sani ko 'yar manya ce ita ma. Duk da dai na san kun gama daidaitawa da Safna ai ita ma wannan sai mu ji waye ubanta." Tun da Mami ta fara magana wani ƙululun baƙin ciki ya tokare masa maƙoshi, "Mami ko 'yar gidan uban waye ni fa idan ba na sonta ba zan aure ta ba. Kuma Daddy ya rasa wa zai haɗa ni da ita sai waccen kucaka, sakarya kuma ƙazamar yarinyar can Uwani." A zabure Mami ta miƙe tsaye har ba ta san lokacin da wani ashar ya suɓuce mata ba. "Uban waye zai haɗa ka da wata Uwani? Yarinyar da ko a mai aiki ba zan ɗauke ta ba. Ba zai taɓa yuwu ba wallahi, wannan ma ai shiga haƙƙi ne ina kai ina wata jakar yarinya Uwani." Jin haka ya ƙarfafa gwiwar Jafar nan ya kwashe duk yadda aka yi ya sanar mata, tun ba ta gama jin jawabinsa ba ta dakatar da shi tare da faɗin. "Bari na je na samu Dada wallahi ba zai taɓa yuwu ba wankan kuturu da sabulu." Fuuuu Mami ta wuce su Shukra na daskare mamaki ya mamaye su. "Waye haka mai ƙirar samudawa ya yi mini gandandan a tsaye?" Dada ta furta tana ƙare wa Mami kallo da ta yi tsaye a bakin ƙofa. Mami ba ta amsa ba ta wuce ta zauna a kan hannun kujerar Dada, tana cika tana batsewa. "Sannu da gida Dada." Mami ta furta a daƙile. Dada ta bi ta da kallo sai da ta taɓe baki sannan ta ce. "Sannunmu dai." "Dada a gaskiya ba a yi mini adalci ba, saboda Allah wai a rasa da wa za a haɗa Jafar sai da wata Uwani. Yaron nan fa namiji ne ko mace ba za a yi wa dole ba, gaskiya a duba lamarin nan don ko kaɗan ba su dace ba. Wai Jafar ne da Uwani yarinyar da ko wanka ba ta yi, ga rashin nutsuwa yarinya kamar rainon gwaro, ko tashin gidan mahaukata." Mami ta yi maganar tana haki. Baki sake Dada ta bi Mami da kallo har ta gama jawabi sannan ta ce. "Uwata kin gama magana ko da saura? Ke Saro amma dai ba ki da kunya kuma ko kaɗan ba ki da mutumci, yanzu ni kike gaya wa haka?Maganar auren yaran nan tamkar yau kika san da ita? Ina ce tun ranar da Uwani ta zo duniya aka ajiye ta. Ki saurare ni da kunnen basira, wallahi ko mutuwa na yi ban amince su Mamman su aura wa Uwani wani mijin ba Jafaru ba. Ke har kya yi zancen ƙazanta Saratu? Kin manta lokacin da kike fama da tsamin kai da na hammata? Ko kin manta lokacin da Mamman yake tasa ki zuwa banɗaki da soso ya tilasta miki ki yi wanka?" Mami ranta ya yi ƙololuwar ɓaci, a fusace ta ce. "Koma dai mene ne ni na ɗauki cikin Jafar na haife abina, don haka babu wata ƙatuwa da ta isa ta yi mini iko da shi wallahi duk ƙarfin ikonta..." Cikin sauri Dada ta katse ta. "Iyeee rashin kunya za ki yi mini Saro? To ni kuma ni na haifi Mamman kuma zan nuna miki ƙaryar gadarar da kike yi. Wallahi idan har ni na ɗauki cikin Mamman wata tara na haife shi sai an ɗaura auren Jafar da Uwani a yau, idan kin isa ki sa Jafar ya warware shi a yau ɗin nan kema." Dada ta ƙarasa maganar cikin ɓacin rai. Mami ta miƙe tsaye jikinta har rawa yake saboda ɓacin rai ta ce. "Ke kin haifa kuma kin isa ki yi gadara da ɗanki to wallahi ni ma zan nuna miki Jafar ba rainonsa na yi ba, naƙudar abina ni ma na yi na haifa don haka mu zuba mu gani." Daga haka Mami da buga wa Dada cinya haɗe da tsaki ta fice daga ɗakin. Daidai lokacin da Mami za ta fita Uwani ta kawo kai, duk da Uwani ba wani shiga sabgar Mami take ba amma ganin ta ya sa ta ce. "Ina wuni Mami." Ko ƙurar da ta ajiye Uwani Mami ba ta kalla ba ta wuce sashenta, Uwani ta taɓe baki ta faɗa ɗakin Dada. Tana shirin yin magana Dada ta katse ta. "Ke Kulu maza je ki kira mini Mamman shi da 'yan uwansa." Jin yadda Dada ta kira sunanta da Kulu ya sa ta sha jinin jikinta don ta lura ran Dada ya ɓaci sosai. Kai tsaye Uwani ta wuce sashen su Mami da sallama ta shiga ɗakin sai dai gaba ɗayansu babu wanda ya tanka mata, sai ma wani kallon tsana da suke bin ta da shi. "Dada ta ce Baba Mamman ya zo." "Sai ki neme shi a ɗakin uwarki." Mami ta furta. "Uwata fa? Me na yi miki za ki zage ni?" "To ko za ki rama ne? Mami ta katse ta. "Ba zan rama ba amma wallahi kada ki sake zagina ban yi miki komai ba, don uwa ba ta fi uwa ba..." Kafin ta rufe baki Shukra ta sauke mata tagwayen mari biyu a fuska. "Rashin kunya za ki yi wa Mami don ubanki, shegiya ƙazama baƙa mai baƙar aniya." Uwani riƙe da kumatu ta ce. "Kan uba marina kika yi?" Uwani na cikin magana Shukra ta sake sauke mata wani marin a fuska. Jin zafin marin ya sa Uwani ta yi tsalle sai ji kake tass a fuskar Shukra Uwani ta rama. Cikin ɓacin rai Mami ta fisgo Uwani da ƙarfi, ita kuma Shukra ta yi mutuwar tsaye tana mamakin marin da Uwani ta yi mata. Kamar haɗin baki Mami da Shukra suka rufe Uwani da duka tun tana ihu tana kuka har ta ja bakinta ta yi shiru saboda galabaita, sai da suka gaji don kansu sannan Mami ta koma kujera tana haki. Shukra na kan Uwani Daddy ya shigo cikin gidan, ganin irin dukan da take yi wa Uwani ya sa Daddy ya ɗauke Shukra da mari. Da kansa ya ɗago Uwani lokaci ɗaya fuskarta har ta sauya saboda kukan da ta ci. Ya lallashe ta sosai sannan Uwani ta faɗa masa saƙon Dada, a haka ta fara dafa bango ta wuce wurin Dada. Shi ma Dadday bai tsaya bi ta kan su Mami ba ya rufa wa Uwani baya. Ganin a yanayin da Uwani ta koma ya sake ɓata ran Dada, nan take ta sa Baba Mammam ya kira mata sauran 'yan uwansa. Suna zama ta wassafa musu duk abin da ya shiga tsakaninta da Mami, ta kuma nuna musu Uwani da irin dukan da suka yi mata. Daga ƙarshe ta ɗora da jawabin ɗaurin auren su Uwani a ranar, duk yadda suka so shawo kan Dada a kan a bari zuwa nan da watan Maulidin ma fir ta ƙi yarda. Sai ma ta nuna musu ana idar da sallar Isha'i su tabbata da sun ɗaura wa Uwani da Jafar aure. Dada ta dubi Baba Mamman ta ce. "Kai Mamman tun da ka zama sakarai sai ka bari Jafaru ya saki Uwani tun da uwarsa ta yi rantsuwa ba zai aure ta ba, to ka sani matuƙar Jafaru ya saki Uwani wallahi sai dai ka nemi wata uwar ba ni ba. Kuma a take kai ma ka miƙa wa Saratu takardarta ta saki. Na gama magana ku tashi ku ba ni wuri." Babu wanda ya iya tankawa haka suka fice ɗaya bayan ɗaya kowa zuciya babu daɗi. Uwani tun da ta kwanta zazzaɓi mai zafi ya rufe ta har sai da Dada ta ba ta magani ta sha, don haka da dare ko fita wasan dare ba ta yi ba. A ɓangaren Jafar ma tun da ya tashi daga falon Mami ya biya wasu almajirai suka gyara masa ɗaki, tun da ya shiga ɗakinsa sallah ce kaɗai take fito da shi. Daddy kuwa ko da ya fito daga sashen Dada sun jima suna tattaunawa da 'yan uwansa sannan kowa ya kama gabansa. Lokacin da aka idar da sallar Isha'i a masallacin gidan marigayi Mai shanu har mutane za su fara watsewa, malam Liman ya yi shelar akwai ɗaurin aure da za a yi. Nan take aka gabatar da waliyai daga kowanne ɓangare, aka ajiye sadaki dubu ɗari da hamsin da alewar ɗaurin aure. Jafar da ke can kusurwar bango da mamaki yake bin malam Liman, a zuciyarsa yake ayyana wanne irin aure ne za a ce za a ɗaura shi da daddare? Ganin su Daddy a gaba-gaba ya sa gabansa ya yi mummunan faɗuwa, ya yi saurin kawar da tunanin da ya faɗo masa a rai har yana neman tsari da shi. Wayarsa ya ɗauko ya fara latsawa, saƙon Safna ya ci karo da shi yana shirin buɗewa ya ji Liman ya furta. "Ga waliyin Jafaru ga waliyin Hauwa kulu an kawo sadaki dubu ɗari da hamsin lakadan ba ajalan ba. A bisa duka shaidun da ake buƙata sun kammala kowa ya shaida an ɗaura auren Jafar Mamman mai shanu da amaryarsa Hauwa kulu Umaru mai shanu, a kan sadaki naira dubu ɗari da hamsin lakadan ba ajalan ba." Daga haka ya fara rattabo addu'o'i ana ta saka albarka. Baba Isuhu ya ƙarasa yana yi wa Jafar Allah sanya alheri, ganin shi ne angon waɗanda ba su san shi ba suka ƙarasa suna masa fatan alheri. Tamkar butum-butumi haka Jafar ya ƙame a wuri ɗaya, ta cikin hayaniyar mutane ya sulale kai tsaye ya wuce gida. Na Madina sai ƙwala masa kira yake amma ya yi banza da shi, Jafar kai tsaye ɗakinsa ya shige ya datse yana kai wa da kawowa. "Ga alewa da dabinon ɗaurin auren ɗanki, ki saka albarka domin addu'arki na da muhimmanci a wurinsu. Bayan mun idar da sallah aka ɗaura auren Jafar da Uwani." Daddy ya furta wa Mami bayan ya shiga gida. A fusace Mami ta suri ledar dabinon ta yi wulli da ita, cikin ɓacin rai ta furta. "Daddyn Jafar yanzu tozarcin da za ka yi mini kenan? Wannan tsinannan auren zan saka wa albarka? Wallahi a daren nan sai Jafar ya saki Uwani." Murmushin takaici Daddy ya yi ya ce. "Na riga da na gama magana da Jafar, ki sani idan kika tilasta shi ya saki yarinyar nan wallahi sai na sauke miki igiyar aurenki uku daga kaina." Baki sake Mami ta bi Daddy da ya wuce ɗakinsa da kallo, saboda takaici sai kawai ta fashe da kuka. Su Shukra ne suka ƙarasa suka fara lallashinta. Cikin ƙanƙanin lokaci garin ya ɗauka 'Yar ƙashin gwiwa ta yi aure, wasu masu ƙarfin halin har gidan suka shiga yin tsegumi. Uwani duk wainar da ake toyawa ba ta sani ba sai daga baya Dada take sanar da ita, babu wani abu da ya ɗaga mata hankali abin da ya fi damunta ciwon jikin dukan da su Mami suka yi mata, wanda ta ci alwashin gabaɗaya za ta ladaftar da su ɗaya bayan ɗaya. Washegari ne ya kama sunan gidan Baba Isuhu sai dai tsamin jikin da Uwani take fama da shi ya hana ta walwala, don ta ci burin ko yaya ne ta tarwatsa 'yan taron suna. Yamma liƙis Uwani da ƙawarta Kubra na tafe suna hira Kubra ta ce. "Oh 'Yar ƙashin gwiwa yanzu dai aurenku da Ɗansandan nan ya tabbata, to kema 'yar sanda za ki zama?" Uwani ta yi jim sannan ta ce. "Da dai tuƙin jirgin sama nake son koya na dinga lulawa a jirgi ta cikin gajimare, an ce fa idan ka na jirgi har taɓo gajimare ana yi da hannu idan aka zira hannu. Amma dai yanzu tun da na auri Ɗansanda gaskiya ina jin ni ma 'yar sanda zan zama, ko ba komai Yaya Jafar ba zai mini baraza da bindiga ba tun da kar ta san kar..." Maganar Uwani ta maƙale sakamakon hango Shukra da saurayinta a ƙofar gida, suna jingine a jikin mota Shukra sai karairaiya take masa tana fari, a can gefen wata bishiya ta hango wani mahaukaci da ake yi masa laƙabi da 'Ba ka da nauyi.' Ɗabi'arsa ce ya ɗauki mace ko namiji ya dinga yawo da kai a gari yana ce wa ba ki da nauyi, kuma ba zai dire ka a ko ina ba sai tsakiyar kwata. A fili Uwani ta sheƙe da dariya Kubra ta ce. "Lafiya kike dariya 'Yar ƙashin gwiwa?" Gyaɗa marau ɗin hannunta ta kalla sannan ta ce. "Zo mu je wurin ba ka da nauyi." Kubra ta zaro ido, da sauri Uwani ta haɗe fuska. "Malama tsaya a nan wallahi kika ɓata mini shiri sai na sa shi ya ɗauki Baffanki gobe." Kubra ta ja baki ta tsuke don ta tabbata Uwani za ta aikata fiye da haka. "Baka da nauyi za ka ci gyaɗa marau?" Uwani ta faɗa tana kaɗa ledar gyaɗar a gaban mahaukacin. Washe baki ya yi cikin katuwar muryarsa ya ce. "Anci gyaɗa." "To bari kaji ina da gyaɗa marau soyayyiya da yawa, idan kana son na baka to ka ga waccen saurayi da budurwar ka je ka ɗauki budurwar ka zaga gari da ita, duk wanda ya zo cetonta ka haɗa masa jini da majina ni na sa ka. Na maka alƙawari zan ƙara maka wata, ƙila ma ba baka kwano guda..." Tun Uwani ba ta gama magana ba, Baka da nauyi ya fisgi ledar gyaɗar hannunta ya saka a aljihu, kai tsaya ya nufi wurin su Shukra ya tsaya a gabansu yana sakin shashashar dariya. A yatsine Shukra ta dube shi ganin yadda kayan jikinsa suke duƙun-duƙun ya sa Shukra ta tsartar da yawu sannan ta ce. "Malam mene ne haka ka zo ka saka mutane a gaba? Haka kawai ka saka mu tashin zuciya, dalla matsa daga nan." Ta yi maganar a yatsine ita a dole ta yi birga a gaban Salim. Salim ya kaɗa mukullin motarsa yana shirin yin magana sai gani ya yi Baka da nauyi ya suri Shukra yana dariya, da mamaki Salim ya dube shi fuska a haɗe ya ce. "Kai Malam wannan wane irin iskanci ne..." Tun Salim bai rufe baki ba Ba ka da nauyi ya sa gwiwar hannunsa, ya yi masa mahangurɓa a fuska ya kusa haɗa masa jini da majina. Wani haske Salim ya gani ya gifta masa kansa ya yi wani irin nauyi dum. Cikin gigita ya faɗa cikin gidan da gudu, da yake sashen Dada shi ne yake kallon ƙofa da sauri ya faɗa ciki a guje cikin fitar hayyaci, Dada na tsaye da ɗaurin ƙirji za ta sauya kaya sai ganin mutum ta yi ya shigo a guje yana wuri-wuri da wawure-wawure. "Hasbunallahu wa ni'imalwakeel kai wane gansamemen ƙaton ne haka..." Kalaman Dada suka maƙale sakamakon jin Salim na fisgar zanin jikinta ta ƙasa yana tura kai don shi maɓoya yake nema. "Kai don ubanka ba ka ganin ni tsohuwa ce, wai me kake nema a ciki ne?" Salim ya sake hankaɗe kansa yana shirin bankaɗe Dada ta faɗi a ƙasa, ganin haka ya sa Dada ta saka kuka tana faɗin. "Yau wane salon kwartanci ne haka ido biyu tun dare bai yi ba." Dada ta furta tana fisgar zanin shi ma Salim yana ja. Ganin Salim da gaske tura kansa yake yana yunƙurin sauke zanin Dada a ƙasa ya sa ta fasa ihu tana faɗin. "Jama'a ku kawo mini ɗauki ku ceci tsohuwa a hannun kwarto." "Don Allah ki ɓoye ni zai sauke mini fuskata daga jikin kaina." Salim ya faɗa cikin tashin hankali, yana sake fisgar zanin Dada yana tura kansa ciki. "Don Ubanka ka rasa a ina za ka ɓoye sai a cikin zanina, kai amma dai yau Allah Ya haɗa ni da lalatattun kwaratan zamani." Salim bai bi ta kan Dada ba ya sure zanin jikinta ya yi uwar ɗakinta a guje, sai ga Dada daga ita sai ɗan tofi shi ma ya zazzago ƙasa saboda kiciniyar da suka sha da Salim. Shukra ban da ihu da zille-zille babu abin da take yi, don Ba ka da nauyi ya sauke ta amma ya ƙi, yara kuwa sai bin su suke a guje suna masa waƙa da tafi. Wannan ya sake ingiza shi ya ci gaba da gudu da Shukra a saman kansa, ɗankwali da mayafinta tuni suka cire tun a ƙofar gida. Sai da ya gaji don kansa ya je wata ƙatuwar kwata ya tsoma ta a ciki. "Allah Ya isa tsakanina da kai." Shukra ta furta cikin kuka. Hannu ya zira a aljihu ya ciro wata ƙatuwar goruba ba ta yi aune ba sai ji ta yi ƙwal ya buga mata a goshi, ya juya ya ci gaba da tafiya. Azaba ta sa Shukra ta rushe da kuka, ga zurfin kwatar ya mata nisa ba za ta iya fitowa ba ga zafin dukan goruba a goshi. Kafin wani lokaci tuni goshinta ya yi wani malolo a daidai wurin da ya ƙwala mata. Cike da takaici Dada ta rushe da kuka sannan ta ce, "Jama'a ku zo ya ƙwace mini zanin jikina, ku kawo mini ɗauki kwarto har uwar ɗakin tsohuwa." 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 [12/06/2024, 12:03] Ameera Adam: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA TAKWAS Uwani saboda dariya har kwanciya ta yi a ƙasa, Ba ka da nauyi ya ƙarasa wurinta tun bai yi magana ba ta miƙa masa ɗayar ƙullin gyaɗar. "Ba ki da nauyi ta yi malolo." Haka yara suka dinga yi wa Shukra waƙa suna tafi, ban da kuka babu abin da take yi saboda tsananin kunya da ɓacin rai. Da ƙyar wasu matasa suka kori yaran suka yi kama-kama suka tsamo ta a cikin kwata. Tana tafe ruwan kwata na ɗiga wasu daga cikin yaran suka fara yi mata wata waƙar. Ɗoyi, ɗoyi ɗoyi. Ɗoyi damalma kashi. Ɗoyi tukunyar kashi. A haka Shukra ta ƙarasa gida nan ma wasu daga cikin tsurarin yara suka bi ta Uwani na take musu baya, Shukra na shiga sashensu ta ɓarke wa Mami da wani irin kuka. "Yaya Shukra lafiya? Me ya same ki a goshi? Mene ne wannan yake wari a jikinki kamar kwata? Ina shi Yaya Salim ɗin?" Auta ta jero mata tambayoyi, sai dai babu ɗaya da ta iya amsawa ban da hawaye da ke shatata a fuskarta. Mami da Auta suka taimaka mata ta gyara jikinta sannan ta faɗa musu abin da ya faru, suka shiga zagin Ba ka da nauyi suna mamakin in da Salim ya je bayan motarsa na ƙofar gida. Jin ihun Dada ya sa su Atika shiga sashenta da sauri, ganinta a daskare daga ita sai ɗan tofi ya ba su mamaki domin Dada ba ta taɓa sauya kaya a gaban mutane. "Dada lafiya?" Hannu na rawa ta nuna uwar ɗakin. "Wani tabbataccan kwarto ne ya fisge mini zani ya yi uwar ɗaki. Ni Kulu ban san uwar me zai laluma a jikin tsohuwa ba." Da sauri su Atika suka leƙa ɗakin, ba su iya hango komai ba sai 'yan idanun Salim da ke duƙe a ƙarƙashin gado. Fa'iza ce ta kira Baba Isuhu, da sauri ya ƙarasa hannunsa ɗauke da ƙatuwar gora ya fisgo Salim. Sai dai sororo ya yi yana bin yadda halitar fuskar Salim ta sauya. "Wa nake gani kamar Salim? Kai uban me ya kai zanin Dada hannunka?" Salim da gefen baki zuwa fuskarsa ya kumbure sundundun ya ce, "Baba wani mahaukaci ne zai sauke mini fuska don Allah ku ɓoye ni. Ya ɗauke Shukra a ka ma ya tafi da ita." Sai a lokacin suka fahimci wurin da maganar Salim ta dosa, Baba Isuhu ya miƙa wa Dada zaninta. Ya kama hannun Salim suka fice Salim sai tirjewa yake, a zuciye baba Isuhu ya waigo ya furta. "Me kake yi haka ne wai? Ka san Allah ka ci sa'a na gane kayan jikinka don mun gaisa ɗazu kana ƙofar gida, wallahi da don ta wannan sukunbiyar fuskar taka ne ba zan gane ka ba. Dubu fa yadda ka koma fuska kamar ta sumammiyar akuya. Mu je na raka ka ƙofar gida ka tafi don indai Ba ka da nauyi ne fiye da haka ma zai yi maka." Sai a lokacin Salim ya saki jiki suka ƙarasa, da sauri ya shige mota ya fusge ta da gudun gaske ko waige ba ya yi. Su Dada suna tsaye suna mayar da yanda aka yi wayar Dada ta fara ringing, da sallama ta ɗauka jin muryar Maryama mahaifiyar Uwani ya sa ta furta. "Ke kuwa Maryama da ƙuruciyarki amma waya ta nemi ba ki wuya, tun daren jiya nake kiranki na sanar da ke abin alheri amma waya a kashe." Maryama cikin shasshekar kuka ta ce. "Dada hankalina ne ba a kwance ba." "To Allah ya rufa asiri ai ni dama tun da na ga yanayinki na san Aramma na zalintarki, ki ci gaba da haƙuri Maryama komai ya yi don kansa." Maryama ta saki kukan da ke cinta, Dada na son Maryama shi ya sa duk lokacin da suka yi waya take tausarta. "Kin ga ki yi shiru 'yar nan su maza fa haka suke, ni tsorona ma kada Aramma ya zo ya ji kina mini kuka ya ce ko Umaru kika tuno. Yanzu dai ba wannan ba jiya da dare dai an cika alƙawarin da aka ɗauka, Uwani dai an ɗaura aure ita da Jafar. Abin ne ya zo a gaggauce, amma dai tariya sai nan da watan maulidi." Maryama ta ji daɗi don ta san waye Baba Mamman, amma har a ranta ta so a ce Uwani ta yi hankali kafin ɗaurin auren. Sai da ta kwararo addu'a sannan ta sanar da Dada dalilin kiranta. "Dada dama kiranki na yi na faɗa miki Me sunan Iya ce ta rasu (Babbar 'yarta ta gidan Aramma.)" Salati Dada ta rafka sannan ta yi mata gaisuwa ta kuma yi mata alƙawarin washegari za su shiryo su zo mata gaisuwa. Bayan sun gama waya Dada ta miƙa wa Uwani waya, suka gaisa sannan ta yi masa sallama. Kimanin ƙarfe goma na safe su Dada suka isa ƙauyen da mahaifiyar Uwani take aure, sun yi kara sosai don har su Baba Yunusa gabaɗaya suka je mata da matansu. Tun da suka faka motoci yara ke zuwa kallonsu, mazan suka zauna a tabarmar da ke ƙofar gida suka tambayi mijin Maryama aka ce musu ya shiga cikin gida. Su Dada kuma suka shiga ciki. "Gata nan da ran Allah ita ta san inda ta kai mini yarinya aka cinye ta, amma idan ta zauna ta ishi mutane da kukan munafurci. Daga zuwanta garinsu ta dawo da yarinya ba lafiya, wai muna zuwa aibitin gangare da suka tura mu babban asibiti a binni aka ce sikila ce, yo ban da ƙaryar likitoci lokacin iyaye da kakanni aka san wata sikili? Ta kai mini yarinyar dai mayu sun cinye kawai." Shigar su Dada gidan suka samu Aramma na zazzaga wa Maryama masifa yana kumfar baki, tana durƙushe a gefen yayan Aramma da ya zo yi mata gaisuwa. A lokacin Aramma ya zo wucewa ya shi ne yake yi mata sababi. Ganin su Dada da yanayin shigarsu ya sa ya hau yashe baki. "Barkanku da zuwa Hajiya." "Barka dai." Dada ta amsa a daƙile. Jin muryar Dada ya sa Maryama ta miƙe tana goge hawaye ta shiga yi musu sannu da zuwa. "Ai kuwa wannan mutumin sai na gyara maka zama." Uwani ta faɗa a ranta. Maryama jiki a sanyaye ta miƙe za ta wuce da su ɗaki. "Ke Maryama wanne irin rashin hankali ne haka kina ganin baƙi ba za ki kai su ɗaki ba." Aramma ya faɗa cikin faɗa shi a dole sai ya birge su Dada. Ɗaki ta kai su bayan sun gaisa suka yi mata gaisuwa cikin jimami, Dada har cikin ranta ba ta ji daɗin irin zaman da Maryama take yi da Aramma ba, domin mace ce mai sanyin hali da haƙuri. Duk wanda ya santa idan ya san Uwani dole zai ce albasa ba ta yi halin ruwa ba. Aramma jikinsa har rawa yake ya sa aka sayo musu ruwa, ba su jima sosai ba Dada ta kawo kuɗin sadaka dubu biyar ta bata. Sauran sirikan Dada kuma mai ɗari biyar mai dubu ɗaya duk suka haɗa mata, lokacin da za su tafi ne Dada ke ce wa Maryama Uwani za ta zauna har sai an yi sadakar uku za ta tafi. Har ƙofar gida Maryama ta raka su, su Baba Idris suka yi mata gaisuwa, suma suka kawo abin sadaka suka ba ta da shi ma Aramma. Har sun ɗauki hanya za su tafi Dada ta dawo ta ja Maryama gefe tana yi mata raɗa. "Dama kuɗin da aka ba ki ko da wasa kada ki ba wa wannan mijin naki kin ji Maryam!" Maryama ta gyaɗa kai jiki a sanyaye sannan ta raka Dada bakin mota tana ɗaga musu hannu. "Dada gaskiya zan yi kewarki kwana biyu an ya ba biyo ku zan yi ba?" Uwani ta faɗa tana tura ba ki gaba. Dada ta watsa mata harara sannan suka wuce. Tun da suka koma cikin gida Uwani ta lura da mahaifiyarta sam ba ta da nutsuwa, suna nan zaune sai ga Aramma ya shigo. "Ke Maryama kawo abin sadakar nan da aka ba ki zan haɗa a yi abincin rana." Tamkar kazar da ƙwai ya fashe wa a ciki haka Maryama ta miƙe jiki ba ƙwari ta kunto kuɗin wurin su Baba Idris ta miƙa masa. "Ke ba na son shashanci da rainin hankali, kina nufin su matan ba su ba ki komai ba? Wai Maryama me ya sa kin fiye baƙin halin tsiya ne." Ran Maryama ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, ganin irin tozarcin da Aramma yake yi mata a gaban Uwani da kuma sauran mutanen da suka zo gaisuwa. Don haka rai a ɓace ta ce. "Wai Aramma ya kake so na yi ne? Me ya sa..." Tun ba ta gama magana ba Aramma ya ɗauke ta da mari, yana shirin kai mata duka Uwani ta shiga tsakaninsu ta furta. "Baba bari na miƙo maka kuɗin a cikin jakar can ta ajiye dama na ji ta ce za a auno garin masara a yi tuwo, amma bari na miƙo maka." Jin haka ya sa Aramma ya washe baki ya ce. "Ka ji yarinya mai hankali maza miƙo mini, ke dai kin yi asarar hali Maryama." Babu musu Uwani ta zuge jakar da ta ga mahaifiyarta ta zuba kuɗin a ciki, ta ɗebo su duka ta miƙa masa. "Kai Allah wadaran naka ya lalace wallahi Maryama kin ji kunya ace wai har 'yar cikinki ta fi ki hankali." Wasu daga cikin ƙannen Aramma suka bi mahaifiyar Uwani da baƙaƙen maganganu. Ba ta tanka musu ba sai ma ruwan hawaye da ke tsiyaya daga fuskarta. Uwani na daga gefe ta ci gaba da kallonsu ɗaya bayan ɗaya, kowanne tana zana gashin azabar da za ta yi musu daga baya. Sai da mutane suka ragu a ɗakin sosai daga Maryama sai 'yan uwanta ta dubi Uwani ta ce. "Me ya sa za ki ɗebi kudina ki ba shi." Ta ƙarasa maganar fuska a haɗe. "Gobe da safe zai dawo miki da su Inna rance na ba shi!" Uwani ta furta cikin rashin damuwa. "Rance fa? Ta ya ya zama rance bayan a kan idona kika ba shi?" "Allah Inna kada ki damu zai dawo miki da kuɗinki har ma ya ƙara miki wasu." Jin sokiburutsun Uwani ya sa Maryama ba ta sake bi ta kanta ba saboda takaici. "Maryama yaya aka yi kika bari har ya ga lokacin da aka ba ki kuɗin nan? Kin fa san halin mutumin nan sarai, ba shi da tausayi ko kaɗan." Indo kishiyar Maryama ta furta ƙasa-ƙasa. "Ai kin san tun da ya gan su ya san za su ba ni wani abu, kuma ragowar ma ba ni na ba shi ba yarinyar nan ce ta ba shi." Maryama ta furta. Suka gama jajantawa juna, don zaman da suke yi sam babu kishi a ciki saboda dukkansu ba wani daɗin zama da shi suke ji ba. Wuni ɗaya da Uwani ta yi a gidan ta fahimci irin zaman ƙuncin da mahaifiyarta da kishiyarta suke yi a cikin gidan, a kan idonta ta ga Aramma ya yo cefane har da nama ya ce a yi masa jar miya da shi. A yadda ta lura hatta abinci ma daban ake yi masa, su kuma duk kwamacalar da ya ga dama sai su dafa. Don abincin dare sai da ƙyar Uwani ta iya cin miyar kukar da aka kaɗa, saboda haka ta ci alwashin gyara masa zama kafin ta bar gidan. Tun da doshin magriba Uwani ta hangi wani ludayin silba a kwandon wanke-wanken mahaifiyarta, a fakaice ta ɗauke shi ta ɓoye sai da dare ya tsala kowa ya yi bacci sannan ta saci jiki a hankali. Har za ta fita ta hangi wani zumbulelen farin hijabin Inna Suwaiba, wani tunani ne ya faɗo mata da sauri ta saki murmushi. Ta figi hijabin a hankali ɗayan hannunta ɗauke da ludayin sulba, can hanyar soro ta nufa da yake a baki-bakin ƙofa turakar Aramma take, daga ɗakinsa kuma sai ɗakin da suke ajiye kayan abinci. Toka ta ɗiba ta bursune fuskarta da ita sannan ta saka zumbulelen farin hijabin, ta leƙa ɗakin ta hango Aramma a kwance ya sharɓe sai sakin munshari yake yi daga shi sai gajeren wando. Da yake irin mutanen nan gajeru masu ƙiba ga uban tumbi. Tana shiga ɗakin ta tsaya a kansa, sai da ta gimtse dariyarta sannan ta daidaici gefen goshinsa ta ba shi raaaal da ludayin hannunta. A firgice Aramma ya miƙe yana dafe da goshi, "Wane ɗan iskan ne a tsohon daren." "Tawagar fatalwar 'yan iskan lahira ne!" Uwani ta faɗa da wata irin murya, ta sa hannu ta cikin hijabin ta buɗa shi, sai ta ƙara faɗi ta cikinsa. A razane Aramma ya ja da baya ganin hallitar da ke tunkaro shi. "Mu sababbin ƙawayen 'yarka da ta baƙunci lahira ne. A cikin fatale ma mu tawagar shaiɗanu ne domin fatattaka ɗan adam muke yi da kulkin lahira. Ita da bakinta ta gaya mana irin zalincin da kake yi wa iyalinka, don haka muka zo domin mu tsintsinka hanjin cikinka, ko kuma mu gayyato 'yan uwanmu mu yi daga-daga da kai." Uwani ta yi magana tana wani miƙa wuya gaba. Jin kalaman Uwani ya sa Aramma ya fashe da wani irin kuka mai cin zuciya, cikin tashin hankali ya ce. "Ku dubi Allah ku yi haƙuri wallahi zan daina duk abin da nake yi..." Da sauri Uwani ta katse shi. "Zo nan maza-maza, matso nan." "Don Allah ku yi mini rai." Aramma ya faɗa fuska haɗe da hawaye da majina. "Za fa ka taka ɗan tsiti a bayanka, wallahi tawagarsa ta fi ta mu bala'i ka matso na ce maka." Da sauri Aramma ya matsa tiɓi-tiɓi sai haɗa gumi yake. Yana zuwa ya tsugunna a ƙasa, hannun Uwani mai ɗauke da ludayin da ke cikin hijabi ta ɗaga da sauri ta sake ba shi raaal a ƙeyarsa. A zabure Aramma ya miƙe sai da ya yi tsalle uku ya faɗi a can gefe cikin azaba. "Fatalwar 'yarka ta gaya mana duk abin da matanka suke samu karɓe musu kake yi, a jiya ma ka karɓe wa uwar marigayya kuɗaɗenta to ko ka mayar mata da abin ta ko kuma mu mayar da kai kuɗi. Domin muna cikin irin fatalwar da ke yi wa 'yan ƙungiyar asiri aiki, za ka zama kuɗi wayyo kuɗi, kuɗi masu daɗi." Uwani ta yi maganar tana wani tsalle tana ɗaga hannu ta cikin hijabi kamar mai shirin tashi sama. "Na rantse da Allah ko wasu aka ce na ƙara mata yanzu zan ƙara mata su." Uwani ba ta bi ta kansa ba ta ce. "Da ma ga hantarka da zuciyarka nan muna gani manya ne, ko su kaɗai muka tsaface za ta kawo mana miliyoyi." Da sauri Aramma ya dafe cikinsa da hannuwansa biyu, ya sake ɓarkewa da kuka. "Idan ka sake ka tona mana asiri wallahi a yanzu za mu hallaka ka." Jin haka ya sa Aramma ya haɗiye kukansa, ya sa hannu biyu ya toshe bakinsa. Uwani ta sake jingina da bango ta furta. "Ganin yadda muka ga ka yi nadama za mu ɗaga maka ƙafa na kwana biyu mu ga idan za ka sauya halinka, kuma ka gaggauta mayarwa da mahaifiyar 'yar uwarmu kuɗinta. Sannan ita da kishiyarta dole ne ka ƙara musu dubu hamsin-hamsin. Kuma ya zama wajibi duk sati ka dinga ba su dubu uku-uku na kashewa." "Duka na ji kuma na yi alƙawari zan yi yadda kuka ce, na gode muku Allah Ya biya ku." Aramma ya yi maganar yana rissinawa. "Ba ma buƙatar godiya, yanzu dai za mu tafi da kai ka je ka ga makwancin 'yarka, sai mu baro ka a can bayan sadakar uku sai mu dawo..." Tun Uwani ba ta gama magana ba ya katse ta cikin kuka. "Wallahi na haƙura da ganin ta, Allah ba sai na ga halin da take ciki ba. Na san mai sunan Iya tana da halin na gari." "To kuwa ya zama wajibi ka zaɓi ɗaya, ko mu ɗauke ka ta ƙarfin tsiya mu tafi da kai. Ko kuma ka zo ka ku yi sallama da shugabar tawagar 'yan iskan fatale." Jin haka ya sa jiki na rawa ya matsa gaban Uwani ya ce. "Zan gaisa da ita..." Maganar bakinsa ta katse sakamakon jin saukar ludayin da ya yi a gaban kansa. Wannan karon kasa motsi ya yi ganin haka ya sa Uwani ta sake sauke masa na biyu aka sannan ta ɗora da cewa. "Yanzu haka za mu fita mu ba ka wuri, sauran tawagarmu na tsakar gidan nan. Kuma duk abin da ka ji ko kuma duk hukuncin da ka ji muna aikatawa matuƙar ka leƙo to zai dawo kanka. Sannan saura idan gari ya waye ka ce ga abin da ya faru da kai." Daga haka Uwani ta fice tana wani shagiɗewa gefe tana tura wuya gaba. Kusan duk abin da ya faru tsakanin Uwani da Aramma, Yaya ƙarama da su Rahane 'yan uwan Aramma sun ji, sakamakon ɗakin da suke kwance a jikin na Aramma yake. Da yake dama idan wani abin taro ya kama a gidan to duka danginsa a wannan ɗakin suke sauka. Kowannensu na daga kwance cikinsa ya ɗuri ruwa ko motsin kirki babu mai yi, babban abin da ya ɗaga hankalinsu yadda suka dinga jiyo kukan Aramma ƙasa-ƙasa, da ita kanta saƙon fatalwar da take faɗa. Suna nan kwance suka ji motsin Uwani a ƙofar ɗakinsu tana ɗan wani gurnani, take fitsari ya jiƙe zanin Yaya ƙarama. Uwani na ɗaga labulen ɗakin ta hango yadda aka jere yara a ƙasa, ɗaya bayan ɗaya haka ta dinga jidar yaran tana kai wa tsakar gida. Yaya ƙarama na daga kwance ta ji Uwani ta dafa ƙafarta, jiki na rawa ta ce. "La'ilaha'illahu Muhammadur Rasulillah." "Ba za ki mutu yanzu ba sai mu fafe ƙwayar idonki." Uwani ta faɗa da wata irin murya, har ta juya za ta fita ta ce. "Su kuma waɗancan yaran zan ba wa ƙananan fatalenmu umarni su gama da su." Uwani na ƙarasa magana ta wuce wurin yaran da ke kwance a tsakar gida, idan ta ɗauko yaro ɗaya sai ta gasa masa mintsini ta tura shi cikin ɗaki. Ganin yadda yaran ke shigowa a firgice cikin kuka ga magagin bacci ga kuma zafin mintsini, ya sa su Yaya ƙarama suka banka uwar ɗaki a guje. Uwani ta yi wata irin sufa ta rufa musu baya tana faɗin. "Ya Ahalul fataleeee ku zo ga nama mun samu." 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 [13/06/2024, 13:37] Ameera Adam: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA TARA Sai a lokacin Uwani ta fahimci ashe ba iya su Yaya Ƙarama ce kaɗai idonsu biyu ba, hatta mutanen da ke cikin uwar ɗakin lakur suka yi sai da suka ji Uwani ta yi sufa za ta faɗo uwar ɗakin suka fara ihun neman ceton rai. A daidai bakin ƙofar uwar ɗakin Uwani ta tsaya sai ta hango wata wuƙa a gefen randa, ta janyo ta ta fara wasawa. Naziru ɗan wurin Sa'a da a lokacin ya wartsake ya kafe Uwani da kallo, ganin haka ya sa Uwani ta kalle shi tana zare ido ta ce. "Ga wani ɗan ƙwage da shi za mu fara." Uwani ta ƙarasa maganar tana fusgar hannun Naziru da bai wuce shekara huɗu ba. "Wayyo Iyata! Wayyo Iyata." Ya fara ihu hankali a tashe don ƙiri-ƙiri ya ga wuƙar hannun Uwani. Sa'a na ganin haka ta fara jan hannun Naziru Uwani na jan ɗaya, Sa'a ta waiga wurin su Yaya ƙarama ta ce. "Ƙarama don Allah ku kawo mini ɗauki Naziri zai tafi." Yaya ƙarama da ke ƙuryar uwar ɗaki ta ce. "Sa'a ki haƙura da Naziru tun da ba wuce haihuwa kika yi ba, wallahi a yanzu ko Habibu (Shi kaɗai ne ɗanta) suka ja sai dai na bi shi da addu'a." Sa'a na shirin magana Uwani ranƙwala mata ludayi a ka, a guje ta saki hannun Naziru cikin kuka ta faɗa uwar ɗakin tana faɗin. "Wayyo Naziru." Shi ma Naziru sai tirjewa yake yana faɗin. "Iyata wayyo Iyata." Yaya ƙarama ce ta yi sauri ta banka ƙofar ɗakin ta danna sakata tana sauke ajiyar zuciya. "Idan kun rufe ƙofa za mu ɓullo ta ƙarƙashin ƙasa, mu dama ai daga kabari muke. A wannan lokacin babu buƙatar mu yi muku bayanin mu su waye, domin hukunta ku muka zo yi ɗaya bayan ɗaya, a kan cin zarafin da kuke yi wa mahaifiyar 'yar uwarmu da kishiyarta. Mu tawagar fatale sai mun saɓule fatar jikinku sannan mu tsotse romo da ɓargon jikinku. Amma za mu ɗaga muku ƙafa zuwa nan da ɗan wani lokaci, don mun lura kun fara nadama. Sai dai muna mai tabbatar muku babu wanda zai tafi gidansa sai an yi sadakar uku, idan kuma mutum ya yi kuskuren tafiya gida gobe, to a daren ranar sai dai ya kwana a ƙiyama." Uwani ta furta a lokacin da ta fita da Naziru tsakar gida da ke ƙwala ihu. A yadda ta lura kusan ilahirin mutanen gidan duka sun tashi, wata dabara ce ta faɗo mata don haka ta buga tsalle a tsakar gidan ta ce. "Waɗanda kuke leƙenmu muna gano ku, ke wato har da ke ko. Wallahi ɗaya bayan ɗaya za mu bi ku mu ƙwaƙwale idanunku idan ba ku koma kun kwanta ba." Ta saki hannun Naziru ai kuwa da gudu ya faɗa ɗaki yana ihu, sai ta tafi da gudu ta nufi ɗakin mahaifiyarta, a guje ta ji mutanen ɗakin suna shigewa uwar ɗaki wasu na hantsilawa. Nan ma ta nufi ɗakin kishiyar mahaifiyarta ta razana su, sai da ta tabbatar da sun gama tsorata kowa ya shige uwar ɗaki sannan ta lallaɓa ta isa banɗaki ta wanke fuskarta. Ta duƙunƙune hijabin Inna Suwaiba ta soke a hammata, sai da ta shirya sosai sannan ta nufi ɗakin mahaifiyarta da gudu tana faɗin. "Wayyo Allah! Ku taimaka mini za su ƙara janye ni." Tana shiga ɗakin ta tarar falon mahaifiyarta babu kowa an banke uwar ɗaki sai ƙananan yara da ke kuka suna buga ƙofa, saboda kada a gano Uwani ita ma ta fara bubbuga ƙofar tana ihu. Da ta lura ba za su buɗe mata ba sai ta janyo ƙofar falo ta datse. Har aka yi assalatu babu wanda ya yunƙurin fitowa daga ɗakin, duk da duka baƙin gidan a zuciyarsu kowa ya ayyana gari na wayewa tafiya zai yi. Amma da sun tuna kashedin da aka yi musu a kan kada wanda ya bar gidan har sai an yi sadakar uku sai jikin kowannensu ya yi sanyi. Sai da gari ya yi tangararan sannan Indo ta yi ƙarfin halin buɗe ƙofa, kamar sababin munafukai haka mutane suka dinga leƙowa ɗaya bayan ɗaya suna fitowa suna yin alwala suna sallah. Duk wannan abin da ya faru bayan da gari ya waye babu mutum ɗaya da ya jajantawa kowa, domin kowa a tsorace yake. Su Uwani suna zaune sai ga Aramma ya shiga ɗakin kansa ya yi waɗansu ƙulalai sun fi biyar, daidai tsakiyar hancinsa har wani ja ya yi yana maiƙo. Da mamaki suka bi shi da kallo, Aramma ya zauna daɓar jikinsa zafi zau da zazzabi. Gaishe shi mutanen ɗakin suka yi, suna son jin abin da ya faru da shi suna tsoro. Hannu ya sa a aljihu ya zaro kuɗin ya ce. "Ungo wannan Maryama, kuɗinki na jiya ne. Wannan kuma kyautar dubu hamsin ce na ba ki ita ma Indo zan miƙa mata nata." Baki sake Maryama ta bi shi da kallo, ta ce. "Malam dubu hamsin fa? An ya ba mantawa ka yi ba?" Aramma ya dube ta a fusace da ya tuna gargaɗin fatalwa sai ya wayance ya sassauta murya ya furta. "Maryama shaidar da za ki yi wa mijinki kenan? Kyautatawa ce kawai ta sa na ba ku." Maryama hannu na rawa ta sa ta karɓa tana zuba masa godiya, Aramma har ya miƙe zai fita Inna Suwaiba ta ce. "Aramma ungo shafa-shafa sai ka shafa a malolon nan na ka, Allah dai ya sawaƙe sanyi haka yake lokaci ɗaya ka ga wuri ya luluye. Ko kuma bige wa ka yi ne da dare?" Aramma da ba ya son a ja doguwar magana ya karɓa ya yi gaba ba tare da ya amsa mata ba, ɗakin Indo ya faɗa ita ma ya sallame ta ya koma ɗakinsa don ilahirin jikinsa ciwo yake masa. Aramma na shiga ɗaki sai ga Indo jiki na rawa ta shiga wurin Maryama suka fara tattaunawa cikin mamaki, ba su ƙara nutsa wa a tekun mamaki ba sai da suka ji Aramma ya ce a yi shinkafa da miyar dage-dage da rana. Wannan sabon sauyi da suka samu daga wurin Aramma ba ƙaramin daɗi ya yi musu. A na gobe Uwani za ta koma gida wurin ƙarfe goma sha biyu na dare ana zaune ana ɗan hira, ta hangi Aramma ya suri buta ya yi banɗaki. Sai da ta tabbatar da hankulan mutane ba ya kanta ta saci jiki ta nufi banɗaki, da yake banɗakin ya yi nesa da ɗakuna don haka ta laɓe a can kusurwar bango ta fara magana. "Baba ga tawagar 'ya'yanka sun dawo. Kada ka tsorata mune dai fatalen nan." Aramma da ke tsugunne a kan masai sai abin ya yi masa a daidai, saboda wata sabuwar gudawa ce ta tsarge shi. Gumi ya fara tsattsafo masa ya ce. "To 'ya'yana don Allah kada ku taɓa lafiyata, wallahi har yanzu ban warke ba." "Ba za mu sake cutar da kai ba, domin ƙawarmu wato matacciyar 'yarka ta ce ta ga irin kyautatawar da kake yi wa iyayenta da 'yan uwanta. Ki yi masa magana ya ji sabuwar muryarki ta cikin jinsin fatalwa." Uwani ta yi maganar tana wani fuffuka, sannan ta maƙale murya ta furta. "Baba ni zan tafi da kai na fi so na dinga ganinka." Tamkar an buɗe fanfo haka cikin Aramma ya birge, ya ci gaba da sakin gudawa babu ƙaƙƙautawa. Cikin tashin hankali ya ce. "Na yafe don Allah ki je ki ɗauki mahaifiyarki." "Shi kenan Baba zan dai dinga kawo muku ziyara a ɓoye duk dare ina ganin rayuwar da kuke yi, idan na ga saɓanin abin da ka fara yi wallahi cikin tumbinka zan shiga, na kannaɗe hanjinka ita kuma kodarka na fansarwa shugaba." Uwani ta furta tana gimtse dariyarta. "Wallahi komai zan ci gaba da yi idan na saɓa ki mini duk abin da za ki yi mini." "Mu zamu tafi Baba sai mun sake zagayowa." Uwani na gama faɗar haka ta fara wata fuffuka tana gurnani sannan ta saɗaɗa ta bar wurin. Saboda yadda Aramma ya razana bayan da ya gama uzurinsa a duƙe ya dinga tafiya, saboda yadda ya ji ƙafafuwansa sun yi sanyi har sun gagara ɗaukar nauyin gangar jikinsa. Ranar da aka yi sadakar uku dai tun da safe wasu daga cikin 'yan gaisuwa suka fara watsewa, domin dama wasu tamkar a kan ƙaya suke. Ita ma Uwani sai da aka yi sallar la'asar sannan Aramma ya zo ya sanar da Maryama an zo ɗaukan Uwani, ta so Uwani ta ƙara kwanaki amma babu yadda ta iya haka ta danne. Wasu daga cikin 'yan uwan mahaifiyarta sai tsokanarta suke suna amarya sai sun zo biki. Kafin Uwani ta fita sai da Maryama ta sata a gaba ta yi mata nasiha sosai. Fakare Uwani ta yi tana sauraronta kamar nasihar na shigarta, sai gyaɗai kai take tana amsawa. Sai da ta gama sauraron mahaifiyarsa sannan ta ce. "Ni kam Inna don Allah zan faɗa miki wata magana amma don Allah kada ki faɗa wa kowa." Take gaban Maryama ya faɗi amma sai ta basar ta ce. "Ina jin ki babu wanda zai ji Uwanina." Duk abin da ya faru tun daga farko har ƙarshe ta sanar da ita tana dariya, ita kanta Maryama dariya take sheƙawa sanna ta riƙe baki ta furta. "Allah Ya shirye ki Uwani ni dai wallahi ban san halin wa kika ɗauka ba, mahaifinki dai har ya fi ni sauƙin kai. Allah Ya shirya ki ko ba komai kin samar mana 'yanci." Suna cikin haka suka ji ƙarar horn da sauri Uwani ta sungumi jakar kayanta, ta ɗauko hijabinta ta saka. Sai da ta yi wa mutanen gidan sallama da Aramma sannan ta ƙarasa bakin motar cikin murna, don tun daga nesa ta hango motar baba Mamman. Don haka da saurinta ta buɗe motar tana faɗin. "Daddy wallahi na yi kewar Dada, ƙila ma ita tana can ko a jikin..." Kalamanta suka maƙale a maƙoshi sakamakon ido biyu da suka yi da Jafar. Wata uwar harara ya banka mata, ta yamutsa fuska tana ƙare masa kallo ta ce. "To kai kuma ina motarka ka ɗauko ta Daddy?" Jafar bai tanka mata ba ya fisgi motar da gudun gaske har sai da wasu yara suka matsa a guje. Suna cikin tafiya babu wanda ya tanka wa wani sai Uwani ta fashe da dariya har da ƙyaƙyatawa, a fusace Jafar ya waigo ya zuba mata manyan idonsa. Sai kuwa Uwani ta sake kwashewa da dariya, gangara motar ya yi ya faka ya ɗauke kai gefe a daƙile ya ce. "Fice mini daga mota." Uwani ta gimtse dariyarta sannan ta ce. "Kamar ya na sauka ai ba motarka ba ce." "Uban me kike wa dariya?" Uwani ta yi murmushi ta ce, "Wallahi dariya ka ba ni, ni dai ba baƙuwa ba ce a wurinka atoh. Kuma dai komai na ka Dada ta ba ni labari tun kana jariri har fa tunbiɗin da ka dinga yi kana yaro. Sai kuma na ga ka fafaki mota kana yin wani irin tuƙin 'yan Kaduna-Zaria, to wai ni birgar me za ka yi mini?" Jafar ya haɗiyi wani yawu mai ɗaci haɗe da fusgar da iska mai zafi, jin irin maganganun da Uwani ta faɗa masa. Yana shirin yin magana Uwani ta sake sakin wata dariyar tana faɗin. "Kasan Allah yadda ka iya fafakar motar nan da Inuwan Toyota zai ganka tsaf zai ɗauke ka kwandasta, saboda wataran idan ya gaji ya ba ka ɗani..." "Fice mini a mota." Ya furta mata cikin tsawa. "Wallahi ba zan fita ba ai motar Daddy ce, malam kada ka yi mini gori ni nan gaba ma jirgin sama zan tuƙa." Kalamanta na ƙarshe suka kusa ba shi dariya. 'Yarinyar da cikakkun sentence na hausa ma ba ta iya haɗawa ba ita ce za ta tuƙa jirgin sama.' Ya raya a ransa. Ganin za ta ɓata masa lokaci ya sa ya fisgi motar ya ci gaba da sharara gudu, har suka ƙarasa gida wani bai sake kula kowa ba. Tun Jafar bai gama faka motar ba Uwani ta suri jakar kayanta ta ɓalle murfin motar ta fice a guje ko rufe motar ba ta tsaya yi ba, tun daga soro ta fara ƙwalla wa Dada kira tana washe baki. Mami da ta rako aminiyarta Hajiya Falmata ganin Uwani ya sake tado mata da wani malolon baƙin ciki. "Ƙwata wannan abar ce fa aka aura wa Jafar, imagine a ce wannan ce sirikata." Hajiya Falmata ta ƙare wa Uwani kallo sannan ta saki wani malalacin murmushi ta furta. "Haba ƙawata wai da wannan 'yar abar ce ke barazana da aurenki? Tun da ƙuruciya ba ki yi yaji ba sai yanzu? Babu inda za ki, matuƙar kin bi duk tattaunawar da muka yi wallahi na faɗa miki da ƙafarta za ta kori kanta babu boka babu malam." Sai a lokacin Mami ta ƙara jin ƙwarin gwiwa, Hajiya Falmata ta ci gaba da biya mata miyagun shawarwari sannan suka yi sallama. Da murna Dada ta tarbi Uwani don ita kanta ba ƙaramin kewarta ta yi ba, dalilin da ya sa tun safe ta sa baba Mamman ya ɗauko ta. Shi kuma ya ce a bari zuwa bayan azahar sai Jafar ya ɗauko ta. Kuma ya yi haka ne domin so yake kafin lokacin tariyarsu su ƙara samun fahimtar juna. Sai da aka yi sallar Margriba kamar yadda Baba Yunusa ya ce za a zauna ya tara 'yan uwansa, Dada, na Madina, Uwani, Jafar da kuma Mami. Sai da ya buɗe taron da addu'a bayan kowa ga gama sannan ya fara magana. "Alhamdu Lillah! Na san wasu daga cikinku sun san dalilin wannan zaman yayin da wasu kuma ba su sani ba. Maƙasudin zamanmu a kan kai Jafar da kuma ke Uwani ne." Jafar ya sunkuyar da kai ƙasa rai a bace. Tsabar takaici ya sa Mami yin ƙwafa a fili, Dada ta dube ta haɗe da taɓe fuska ta ce. "Aure dai Allah Ya haɗa duk mai hassada sai rabo ya kashe shi, yara su haihu kuma a mayar da sunansa." Mami ta shiga aika wa Dada harara a fakaice. "Jafar a yanzu wani nauyi ya hau kanka domin aure ba wasa ba ne, ka riƙe yarinyar mutane amana don a yanzu da kake gani komai nata ya dawo ƙarƙashin ikonka. Ke kuma Uwani wannan da kike gani aljannarki na ƙarƙashin ƙafarsa, ki bi mijinki sau da ƙafa yi na yi bari na bari. Duk abin da kika san zai faranta ran mijinki shi za ki yi, abin da ba ya so sai ki haƙura da shi don zaman aure ɗan haƙuri ne." Sai da Baba Yunusa ya numfasa sannan ya ci gaba. "Mun tattauna ni da 'yan uwana a kan za ku tare tare da Mahaifinku tun da an riga an ɗaura aure babu fa'idar a ce za a zauna har sai nan da wata biyu idan auren su Shukra ya zo. A don haka idan Allah Ya kai mu ranar Laraba mai zuwa ne mahaifinku Mamman ya ce za a ƙarasa gyara komai da saka komai na gidan, tun da akwai wadataccen wuri za ku zauna a ƙaramin part ɗin da ke gefen na Maminku." Wani irin tuƙuƙin zafi ne a zuciyar Mami har za ta ƙi amimcewa da hakan sai kuma ta tuna da huɗubar ƙawarta Hajiya Falmata. "Saboda haka muka yanke shawarar idan Allah Ya kai mu juma'a mai zuwa ne tariyarku, kuma bayan nan za a nema wa Uwani wata makarantar za ta ci gaba da karatunta. Idan ya so bayan sun yi hutu sai ka ɗauki matarka ku wuce wurin aiki." Jafar ya yi shiru ba tare da ya amsa ba. Wannan maganar ta ƙarshe ba ƙaramin daɗi ta yi wa Mami ba, don a wannan lokacin ne za ta ci karenta babu babbaka a kan Uwani. "Ni iya abin da zan iya ce wa kenan, Dada kafin mu zo kan ki ko akwai mai magana a cikin?" Gabaɗaya suka girgiza kai ban da Baba Mustafa da ya ce yana da abin cewa. "Sannu da ƙoƙari Yaya Allah Ya ƙara girma, duk bayananka a kan tsari suke. Amma abin da nake gani me zai hana a ɗaga tariyar ta su zuwa nan da kamar sati biyu zuwa uku, duba da yanayin ragowar shirye-shiryen da ya kamata a yi musu. Daga haɗa lefe har zuwa wani shirye-shirye na su na mata, sannan a wannan lokacin mahaifiyar yarinyar na cikin halin rashin 'yarta. Amma bayan wannan lokacin ita kanta za ta samu nutsuwar gudanar da bikin yadda ya kamata." Dada ta jinjina kai sannan ta furta. "Wallahi Mustafa ka yi kyan kai, saboda Allah kamar gajiya na yi da Uwanin da za a ce nan da kwana huɗu a kai ta ɗakin miji." Baba Yunusa ya yi murmushi ya furta. "Wannan haka ne, Dada me za kike ganin ya dace bayan haka." Dada ta yi jim sannan ta furta. "Ni dai kam nasiha ce zan yi wa Jafaru da ita Uwani, amma kam ba yanzu zan yi musu ba sai ranar da za su tare. Don ina gudun na tofar da yawun bakina a banza, su barbaɗar da nasihar da na yi musu tun kafin tariyarsu." Tambayar Mami aka yi ko tana da abin faɗa ta ce babu, don haka suka ƙarƙaren zaman tun ba a gama addu'a ba Mami ta sa ƙafarta ta fice rai a ɓace. 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 [11/06/2024, 13:08] Ameera Adam: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA BAKWAI Kamar Jafar zai tashi sama haka ya nufi sashen mahaifiyarsa saboda ɓacin rai ko gabansa ba ya gani sosai, da ƙarfi ya doka ƙofar falon Mami da su Shukra na zaune. A zabure duka suka miƙe Mami ta dube shi ta ce. "Hankalinka ɗaya kuwa Jafar? Saurin me kake yi haka?" Jafar bai tanka mata ba ya wuce kan kujera ya zauna yana furzar da iska mai zafi. Sai da ta ƙare masa kallo sannan ta ƙarasa kusa da shi ta furta. "A kullin ina gaya maka ka dinga rage wannan baƙar zuciyar taka. Me aka yi maka?" "Mami me ya sa Daddy ba ya son farin cikina ne?" Shi ma ya jefa mata tambaya. "Me ya sa ka faɗi haka?" "Yanzu Mami da girmana ni ba ƙaramin yaro ba a ce za a wani nemar mini matar aure, saboda Allah an yi mini adalci kenan? Atleast ko shawarata ai sai a nema." Nan take Mami ta haɗe fuska sai da ta sauke ajiyar zuciya ta furta. "Ina tunanin dai wasa yake yi maka, amma kuma ban da abin ka Jafar ka sani ko 'yar manya ce ita ma. Duk da dai na san kun gama daidaitawa da Safna ai ita ma wannan sai mu ji waye ubanta." Tun da Mami ta fara magana wani ƙululun baƙin ciki ya tokare masa maƙoshi, "Mami ko 'yar gidan uban waye ni fa idan ba na sonta ba zan aure ta ba. Kuma Daddy ya rasa wa zai haɗa ni da ita sai waccen kucaka, sakarya kuma ƙazamar yarinyar can Uwani." A zabure Mami ta miƙe tsaye har ba ta san lokacin da wani ashar ya suɓuce mata ba. "Uban waye zai haɗa ka da wata Uwani? Yarinyar da ko a mai aiki ba zan ɗauke ta ba. Ba zai taɓa yuwu ba wallahi, wannan ma ai shiga haƙƙi ne ina kai ina wata jakar yarinya Uwani." Jin haka ya ƙarfafa gwiwar Jafar nan ya kwashe duk yadda aka yi ya sanar mata, tun ba ta gama jin jawabinsa ba ta dakatar da shi tare da faɗin. "Bari na je na samu Dada wallahi ba zai taɓa yuwu ba wankan kuturu da sabulu." Fuuuu Mami ta wuce su Shukra na daskare mamaki ya mamaye su. "Waye haka mai ƙirar samudawa ya yi mini gandandan a tsaye?" Dada ta furta tana ƙare wa Mami kallo da ta yi tsaye a bakin ƙofa. Mami ba ta amsa ba ta wuce ta zauna a kan hannun kujerar Dada, tana cika tana batsewa. "Sannu da gida Dada." Mami ta furta a daƙile. Dada ta bi ta da kallo sai da ta taɓe baki sannan ta ce. "Sannunmu dai." "Dada a gaskiya ba a yi mini adalci ba, saboda Allah wai a rasa da wa za a haɗa Jafar sai da wata Uwani. Yaron nan fa namiji ne ko mace ba za a yi wa dole ba, gaskiya a duba lamarin nan don ko kaɗan ba su dace ba. Wai Jafar ne da Uwani yarinyar da ko wanka ba ta yi, ga rashin nutsuwa yarinya kamar rainon gwaro, ko tashin gidan mahaukata." Mami ta yi maganar tana haki. Baki sake Dada ta bi Mami da kallo har ta gama jawabi sannan ta ce. "Uwata kin gama magana ko da saura? Ke Saro amma dai ba ki da kunya kuma ko kaɗan ba ki da mutumci, yanzu ni kike gaya wa haka?Maganar auren yaran nan tamkar yau kika san da ita? Ina ce tun ranar da Uwani ta zo duniya aka ajiye ta. Ki saurare ni da kunnen basira, wallahi ko mutuwa na yi ban amince su Mamman su aura wa Uwani wani mijin ba Jafaru ba. Ke har kya yi zancen ƙazanta Saratu? Kin manta lokacin da kike fama da tsamin kai da na hammata? Ko kin manta lokacin da Mamman yake tasa ki zuwa banɗaki da soso ya tilasta miki ki yi wanka?" Mami ranta ya yi ƙololuwar ɓaci, a fusace ta ce. "Koma dai mene ne ni na ɗauki cikin Jafar na haife abina, don haka babu wata ƙatuwa da ta isa ta yi mini iko da shi wallahi duk ƙarfin ikonta..." Cikin sauri Dada ta katse ta. "Iyeee rashin kunya za ki yi mini Saro? To ni kuma ni na haifi Mamman kuma zan nuna miki ƙaryar gadarar da kike yi. Wallahi idan har ni na ɗauki cikin Mamman wata tara na haife shi sai an ɗaura auren Jafar da Uwani a yau, idan kin isa ki sa Jafar ya warware shi a yau ɗin nan kema." Dada ta ƙarasa maganar cikin ɓacin rai. Mami ta miƙe tsaye jikinta har rawa yake saboda ɓacin rai ta ce. "Ke kin haifa kuma kin isa ki yi gadara da ɗanki to wallahi ni ma zan nuna miki Jafar ba rainonsa na yi ba, naƙudar abina ni ma na yi na haifa don haka mu zuba mu gani." Daga haka Mami da buga wa Dada cinya haɗe da tsaki ta fice daga ɗakin. Daidai lokacin da Mami za ta fita Uwani ta kawo kai, duk da Uwani ba wani shiga sabgar Mami take ba amma ganin ta ya sa ta ce. "Ina wuni Mami." Ko ƙurar da ta ajiye Uwani Mami ba ta kalla ba ta wuce sashenta, Uwani ta taɓe baki ta faɗa ɗakin Dada. Tana shirin yin magana Dada ta katse ta. "Ke Kulu maza je ki kira mini Mamman shi da 'yan uwansa." Jin yadda Dada ta kira sunanta da Kulu ya sa ta sha jinin jikinta don ta lura ran Dada ya ɓaci sosai. Kai tsaye Uwani ta wuce sashen su Mami da sallama ta shiga ɗakin sai dai gaba ɗayansu babu wanda ya tanka mata, sai ma wani kallon tsana da suke bin ta da shi. "Dada ta ce Baba Mamman ya zo." "Sai ki neme shi a ɗakin uwarki." Mami ta furta. "Uwata fa? Me na yi miki za ki zage ni?" "To ko za ki rama ne? Mami ta katse ta. "Ba zan rama ba amma wallahi kada ki sake zagina ban yi miki komai ba, don uwa ba ta fi uwa ba..." Kafin ta rufe baki Shukra ta sauke mata tagwayen mari biyu a fuska. "Rashin kunya za ki yi wa Mami don ubanki, shegiya ƙazama baƙa mai baƙar aniya." Uwani riƙe da kumatu ta ce. "Kan uba marina kika yi?" Uwani na cikin magana Shukra ta sake sauke mata wani marin a fuska. Jin zafin marin ya sa Uwani ta yi tsalle sai ji kake tass a fuskar Shukra Uwani ta rama. Cikin ɓacin rai Mami ta fisgo Uwani da ƙarfi, ita kuma Shukra ta yi mutuwar tsaye tana mamakin marin da Uwani ta yi mata. Kamar haɗin baki Mami da Shukra suka rufe Uwani da duka tun tana ihu tana kuka har ta ja bakinta ta yi shiru saboda galabaita, sai da suka gaji don kansu sannan Mami ta koma kujera tana haki. Shukra na kan Uwani Daddy ya shigo cikin gidan, ganin irin dukan da take yi wa Uwani ya sa Daddy ya ɗauke Shukra da mari. Da kansa ya ɗago Uwani lokaci ɗaya fuskarta har ta sauya saboda kukan da ta ci. Ya lallashe ta sosai sannan Uwani ta faɗa masa saƙon Dada, a haka ta fara dafa bango ta wuce wurin Dada. Shi ma Dadday bai tsaya bi ta kan su Mami ba ya rufa wa Uwani baya. Ganin a yanayin da Uwani ta koma ya sake ɓata ran Dada, nan take ta sa Baba Mammam ya kira mata sauran 'yan uwansa. Suna zama ta wassafa musu duk abin da ya shiga tsakaninta da Mami, ta kuma nuna musu Uwani da irin dukan da suka yi mata. Daga ƙarshe ta ɗora da jawabin ɗaurin auren su Uwani a ranar, duk yadda suka so shawo kan Dada a kan a bari zuwa nan da watan Maulidin ma fir ta ƙi yarda. Sai ma ta nuna musu ana idar da sallar Isha'i su tabbata da sun ɗaura wa Uwani da Jafar aure. Dada ta dubi Baba Mamman ta ce. "Kai Mamman tun da ka zama sakarai sai ka bari Jafaru ya saki Uwani tun da uwarsa ta yi rantsuwa ba zai aure ta ba, to ka sani matuƙar Jafaru ya saki Uwani wallahi sai dai ka nemi wata uwar ba ni ba. Kuma a take kai ma ka miƙa wa Saratu takardarta ta saki. Na gama magana ku tashi ku ba ni wuri." Babu wanda ya iya tankawa haka suka fice ɗaya bayan ɗaya kowa zuciya babu daɗi. Uwani tun da ta kwanta zazzaɓi mai zafi ya rufe ta har sai da Dada ta ba ta magani ta sha, don haka da dare ko fita wasan dare ba ta yi ba. A ɓangaren Jafar ma tun da ya tashi daga falon Mami ya biya wasu almajirai suka gyara masa ɗaki, tun da ya shiga ɗakinsa sallah ce kaɗai take fito da shi. Daddy kuwa ko da ya fito daga sashen Dada sun jima suna tattaunawa da 'yan uwansa sannan kowa ya kama gabansa. Lokacin da aka idar da sallar Isha'i a masallacin gidan marigayi Mai shanu har mutane za su fara watsewa, malam Liman ya yi shelar akwai ɗaurin aure da za a yi. Nan take aka gabatar da waliyai daga kowanne ɓangare, aka ajiye sadaki dubu ɗari da hamsin da alewar ɗaurin aure. Jafar da ke can kusurwar bango da mamaki yake bin malam Liman, a zuciyarsa yake ayyana wanne irin aure ne za a ce za a ɗaura shi da daddare? Ganin su Daddy a gaba-gaba ya sa gabansa ya yi mummunan faɗuwa, ya yi saurin kawar da tunanin da ya faɗo masa a rai har yana neman tsari da shi. Wayarsa ya ɗauko ya fara latsawa, saƙon Safna ya ci karo da shi yana shirin buɗewa ya ji Liman ya furta. "Ga waliyin Jafaru ga waliyin Hauwa kulu an kawo sadaki dubu ɗari da hamsin lakadan ba ajalan ba. A bisa duka shaidun da ake buƙata sun kammala kowa ya shaida an ɗaura auren Jafar Mamman mai shanu da amaryarsa Hauwa kulu Umaru mai shanu, a kan sadaki naira dubu ɗari da hamsin lakadan ba ajalan ba." Daga haka ya fara rattabo addu'o'i ana ta saka albarka. Baba Isuhu ya ƙarasa yana yi wa Jafar Allah sanya alheri, ganin shi ne angon waɗanda ba su san shi ba suka ƙarasa suna masa fatan alheri. Tamkar butum-butumi haka Jafar ya ƙame a wuri ɗaya, ta cikin hayaniyar mutane ya sulale kai tsaye ya wuce gida. Na Madina sai ƙwala masa kira yake amma ya yi banza da shi, Jafar kai tsaye ɗakinsa ya shige ya datse yana kai wa da kawowa. "Ga alewa da dabinon ɗaurin auren ɗanki, ki saka albarka domin addu'arki na da muhimmanci a wurinsu. Bayan mun idar da sallah aka ɗaura auren Jafar da Uwani." Daddy ya furta wa Mami bayan ya shiga gida. A fusace Mami ta suri ledar dabinon ta yi wulli da ita, cikin ɓacin rai ta furta. "Daddyn Jafar yanzu tozarcin da za ka yi mini kenan? Wannan tsinannan auren zan saka wa albarka? Wallahi a daren nan sai Jafar ya saki Uwani." Murmushin takaici Daddy ya yi ya ce. "Na riga da na gama magana da Jafar, ki sani idan kika tilasta shi ya saki yarinyar nan wallahi sai na sauke miki igiyar aurenki uku daga kaina." Baki sake Mami ta bi Daddy da ya wuce ɗakinsa da kallo, saboda takaici sai kawai ta fashe da kuka. Su Shukra ne suka ƙarasa suka fara lallashinta. Cikin ƙanƙanin lokaci garin ya ɗauka 'Yar ƙashin gwiwa ta yi aure, wasu masu ƙarfin halin har gidan suka shiga yin tsegumi. Uwani duk wainar da ake toyawa ba ta sani ba sai daga baya Dada take sanar da ita, babu wani abu da ya ɗaga mata hankali abin da ya fi damunta ciwon jikin dukan da su Mami suka yi mata, wanda ta ci alwashin gabaɗaya za ta ladaftar da su ɗaya bayan ɗaya. Washegari ne ya kama sunan gidan Baba Isuhu sai dai tsamin jikin da Uwani take fama da shi ya hana ta walwala, don ta ci burin ko yaya ne ta tarwatsa 'yan taron suna. Yamma liƙis Uwani da ƙawarta Kubra na tafe suna hira Kubra ta ce. "Oh 'Yar ƙashin gwiwa yanzu dai aurenku da Ɗansandan nan ya tabbata, to kema 'yar sanda za ki zama?" Uwani ta yi jim sannan ta ce. "Da dai tuƙin jirgin sama nake son koya na dinga lulawa a jirgi ta cikin gajimare, an ce fa idan ka na jirgi har taɓo gajimare ana yi da hannu idan aka zira hannu. Amma dai yanzu tun da na auri Ɗansanda gaskiya ina jin ni ma 'yar sanda zan zama, ko ba komai Yaya Jafar ba zai mini baraza da bindiga ba tun da kar ta san kar..." Maganar Uwani ta maƙale sakamakon hango Shukra da saurayinta a ƙofar gida, suna jingine a jikin mota Shukra sai karairaiya take masa tana fari, a can gefen wata bishiya ta hango wani mahaukaci da ake yi masa laƙabi da 'Ba ka da nauyi.' Ɗabi'arsa ce ya ɗauki mace ko namiji ya dinga yawo da kai a gari yana ce wa ba ki da nauyi, kuma ba zai dire ka a ko ina ba sai tsakiyar kwata. A fili Uwani ta sheƙe da dariya Kubra ta ce. "Lafiya kike dariya 'Yar ƙashin gwiwa?" Gyaɗa marau ɗin hannunta ta kalla sannan ta ce. "Zo mu je wurin ba ka da nauyi." Kubra ta zaro ido, da sauri Uwani ta haɗe fuska. "Malama tsaya a nan wallahi kika ɓata mini shiri sai na sa shi ya ɗauki Baffanki gobe." Kubra ta ja baki ta tsuke don ta tabbata Uwani za ta aikata fiye da haka. "Baka da nauyi za ka ci gyaɗa marau?" Uwani ta faɗa tana kaɗa ledar gyaɗar a gaban mahaukacin. Washe baki ya yi cikin katuwar muryarsa ya ce. "Anci gyaɗa." "To bari kaji ina da gyaɗa marau soyayyiya da yawa, idan kana son na baka to ka ga waccen saurayi da budurwar ka je ka ɗauki budurwar ka zaga gari da ita, duk wanda ya zo cetonta ka haɗa masa jini da majina ni na sa ka. Na maka alƙawari zan ƙara maka wata, ƙila ma ba baka kwano guda..." Tun Uwani ba ta gama magana ba, Baka da nauyi ya fisgi ledar gyaɗar hannunta ya saka a aljihu, kai tsaya ya nufi wurin su Shukra ya tsaya a gabansu yana sakin shashashar dariya. A yatsine Shukra ta dube shi ganin yadda kayan jikinsa suke duƙun-duƙun ya sa Shukra ta tsartar da yawu sannan ta ce. "Malam mene ne haka ka zo ka saka mutane a gaba? Haka kawai ka saka mu tashin zuciya, dalla matsa daga nan." Ta yi maganar a yatsine ita a dole ta yi birga a gaban Salim. Salim ya kaɗa mukullin motarsa yana shirin yin magana sai gani ya yi Baka da nauyi ya suri Shukra yana dariya, da mamaki Salim ya dube shi fuska a haɗe ya ce. "Kai Malam wannan wane irin iskanci ne..." Tun Salim bai rufe baki ba Ba ka da nauyi ya sa gwiwar hannunsa, ya yi masa mahangurɓa a fuska ya kusa haɗa masa jini da majina. Wani haske Salim ya gani ya gifta masa kansa ya yi wani irin nauyi dum. Cikin gigita ya faɗa cikin gidan da gudu, da yake sashen Dada shi ne yake kallon ƙofa da sauri ya faɗa ciki a guje cikin fitar hayyaci, Dada na tsaye da ɗaurin ƙirji za ta sauya kaya sai ganin mutum ta yi ya shigo a guje yana wuri-wuri da wawure-wawure. "Hasbunallahu wa ni'imalwakeel kai wane gansamemen ƙaton ne haka..." Kalaman Dada suka maƙale sakamakon jin Salim na fisgar zanin jikinta ta ƙasa yana tura kai don shi maɓoya yake nema. "Kai don ubanka ba ka ganin ni tsohuwa ce, wai me kake nema a ciki ne?" Salim ya sake hankaɗe kansa yana shirin bankaɗe Dada ta faɗi a ƙasa, ganin haka ya sa Dada ta saka kuka tana faɗin. "Yau wane salon kwartanci ne haka ido biyu tun dare bai yi ba." Dada ta furta tana fisgar zanin shi ma Salim yana ja. Ganin Salim da gaske tura kansa yake yana yunƙurin sauke zanin Dada a ƙasa ya sa ta fasa ihu tana faɗin. "Jama'a ku kawo mini ɗauki ku ceci tsohuwa a hannun kwarto." "Don Allah ki ɓoye ni zai sauke mini fuskata daga jikin kaina." Salim ya faɗa cikin tashin hankali, yana sake fisgar zanin Dada yana tura kansa ciki. "Don Ubanka ka rasa a ina za ka ɓoye sai a cikin zanina, kai amma dai yau Allah Ya haɗa ni da lalatattun kwaratan zamani." Salim bai bi ta kan Dada ba ya sure zanin jikinta ya yi uwar ɗakinta a guje, sai ga Dada daga ita sai ɗan tofi shi ma ya zazzago ƙasa saboda kiciniyar da suka sha da Salim. Shukra ban da ihu da zille-zille babu abin da take yi, don Ba ka da nauyi ya sauke ta amma ya ƙi, yara kuwa sai bin su suke a guje suna masa waƙa da tafi. Wannan ya sake ingiza shi ya ci gaba da gudu da Shukra a saman kansa, ɗankwali da mayafinta tuni suka cire tun a ƙofar gida. Sai da ya gaji don kansa ya je wata ƙatuwar kwata ya tsoma ta a ciki. "Allah Ya isa tsakanina da kai." Shukra ta furta cikin kuka. Hannu ya zira a aljihu ya ciro wata ƙatuwar goruba ba ta yi aune ba sai ji ta yi ƙwal ya buga mata a goshi, ya juya ya ci gaba da tafiya. Azaba ta sa Shukra ta rushe da kuka, ga zurfin kwatar ya mata nisa ba za ta iya fitowa ba ga zafin dukan goruba a goshi. Kafin wani lokaci tuni goshinta ya yi wani malolo a daidai wurin da ya ƙwala mata. Cike da takaici Dada ta rushe da kuka sannan ta ce, "Jama'a ku zo ya ƙwace mini zanin jikina, ku kawo mini ɗauki kwarto har uwar ɗakin tsohuwa." 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 [12/06/2024, 12:03] Ameera Adam: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA TAKWAS Uwani saboda dariya har kwanciya ta yi a ƙasa, Ba ka da nauyi ya ƙarasa wurinta tun bai yi magana ba ta miƙa masa ɗayar ƙullin gyaɗar. "Ba ki da nauyi ta yi malolo." Haka yara suka dinga yi wa Shukra waƙa suna tafi, ban da kuka babu abin da take yi saboda tsananin kunya da ɓacin rai. Da ƙyar wasu matasa suka kori yaran suka yi kama-kama suka tsamo ta a cikin kwata. Tana tafe ruwan kwata na ɗiga wasu daga cikin yaran suka fara yi mata wata waƙar. Ɗoyi, ɗoyi ɗoyi. Ɗoyi damalma kashi. Ɗoyi tukunyar kashi. A haka Shukra ta ƙarasa gida nan ma wasu daga cikin tsurarin yara suka bi ta Uwani na take musu baya, Shukra na shiga sashensu ta ɓarke wa Mami da wani irin kuka. "Yaya Shukra lafiya? Me ya same ki a goshi? Mene ne wannan yake wari a jikinki kamar kwata? Ina shi Yaya Salim ɗin?" Auta ta jero mata tambayoyi, sai dai babu ɗaya da ta iya amsawa ban da hawaye da ke shatata a fuskarta. Mami da Auta suka taimaka mata ta gyara jikinta sannan ta faɗa musu abin da ya faru, suka shiga zagin Ba ka da nauyi suna mamakin in da Salim ya je bayan motarsa na ƙofar gida. Jin ihun Dada ya sa su Atika shiga sashenta da sauri, ganinta a daskare daga ita sai ɗan tofi ya ba su mamaki domin Dada ba ta taɓa sauya kaya a gaban mutane. "Dada lafiya?" Hannu na rawa ta nuna uwar ɗakin. "Wani tabbataccan kwarto ne ya fisge mini zani ya yi uwar ɗaki. Ni Kulu ban san uwar me zai laluma a jikin tsohuwa ba." Da sauri su Atika suka leƙa ɗakin, ba su iya hango komai ba sai 'yan idanun Salim da ke duƙe a ƙarƙashin gado. Fa'iza ce ta kira Baba Isuhu, da sauri ya ƙarasa hannunsa ɗauke da ƙatuwar gora ya fisgo Salim. Sai dai sororo ya yi yana bin yadda halitar fuskar Salim ta sauya. "Wa nake gani kamar Salim? Kai uban me ya kai zanin Dada hannunka?" Salim da gefen baki zuwa fuskarsa ya kumbure sundundun ya ce, "Baba wani mahaukaci ne zai sauke mini fuska don Allah ku ɓoye ni. Ya ɗauke Shukra a ka ma ya tafi da ita." Sai a lokacin suka fahimci wurin da maganar Salim ta dosa, Baba Isuhu ya miƙa wa Dada zaninta. Ya kama hannun Salim suka fice Salim sai tirjewa yake, a zuciye baba Isuhu ya waigo ya furta. "Me kake yi haka ne wai? Ka san Allah ka ci sa'a na gane kayan jikinka don mun gaisa ɗazu kana ƙofar gida, wallahi da don ta wannan sukunbiyar fuskar taka ne ba zan gane ka ba. Dubu fa yadda ka koma fuska kamar ta sumammiyar akuya. Mu je na raka ka ƙofar gida ka tafi don indai Ba ka da nauyi ne fiye da haka ma zai yi maka." Sai a lokacin Salim ya saki jiki suka ƙarasa, da sauri ya shige mota ya fusge ta da gudun gaske ko waige ba ya yi. Su Dada suna tsaye suna mayar da yanda aka yi wayar Dada ta fara ringing, da sallama ta ɗauka jin muryar Maryama mahaifiyar Uwani ya sa ta furta. "Ke kuwa Maryama da ƙuruciyarki amma waya ta nemi ba ki wuya, tun daren jiya nake kiranki na sanar da ke abin alheri amma waya a kashe." Maryama cikin shasshekar kuka ta ce. "Dada hankalina ne ba a kwance ba." "To Allah ya rufa asiri ai ni dama tun da na ga yanayinki na san Aramma na zalintarki, ki ci gaba da haƙuri Maryama komai ya yi don kansa." Maryama ta saki kukan da ke cinta, Dada na son Maryama shi ya sa duk lokacin da suka yi waya take tausarta. "Kin ga ki yi shiru 'yar nan su maza fa haka suke, ni tsorona ma kada Aramma ya zo ya ji kina mini kuka ya ce ko Umaru kika tuno. Yanzu dai ba wannan ba jiya da dare dai an cika alƙawarin da aka ɗauka, Uwani dai an ɗaura aure ita da Jafar. Abin ne ya zo a gaggauce, amma dai tariya sai nan da watan maulidi." Maryama ta ji daɗi don ta san waye Baba Mamman, amma har a ranta ta so a ce Uwani ta yi hankali kafin ɗaurin auren. Sai da ta kwararo addu'a sannan ta sanar da Dada dalilin kiranta. "Dada dama kiranki na yi na faɗa miki Me sunan Iya ce ta rasu (Babbar 'yarta ta gidan Aramma.)" Salati Dada ta rafka sannan ta yi mata gaisuwa ta kuma yi mata alƙawarin washegari za su shiryo su zo mata gaisuwa. Bayan sun gama waya Dada ta miƙa wa Uwani waya, suka gaisa sannan ta yi masa sallama. Kimanin ƙarfe goma na safe su Dada suka isa ƙauyen da mahaifiyar Uwani take aure, sun yi kara sosai don har su Baba Yunusa gabaɗaya suka je mata da matansu. Tun da suka faka motoci yara ke zuwa kallonsu, mazan suka zauna a tabarmar da ke ƙofar gida suka tambayi mijin Maryama aka ce musu ya shiga cikin gida. Su Dada kuma suka shiga ciki. "Gata nan da ran Allah ita ta san inda ta kai mini yarinya aka cinye ta, amma idan ta zauna ta ishi mutane da kukan munafurci. Daga zuwanta garinsu ta dawo da yarinya ba lafiya, wai muna zuwa aibitin gangare da suka tura mu babban asibiti a binni aka ce sikila ce, yo ban da ƙaryar likitoci lokacin iyaye da kakanni aka san wata sikili? Ta kai mini yarinyar dai mayu sun cinye kawai." Shigar su Dada gidan suka samu Aramma na zazzaga wa Maryama masifa yana kumfar baki, tana durƙushe a gefen yayan Aramma da ya zo yi mata gaisuwa. A lokacin Aramma ya zo wucewa ya shi ne yake yi mata sababi. Ganin su Dada da yanayin shigarsu ya sa ya hau yashe baki. "Barkanku da zuwa Hajiya." "Barka dai." Dada ta amsa a daƙile. Jin muryar Dada ya sa Maryama ta miƙe tana goge hawaye ta shiga yi musu sannu da zuwa. "Ai kuwa wannan mutumin sai na gyara maka zama." Uwani ta faɗa a ranta. Maryama jiki a sanyaye ta miƙe za ta wuce da su ɗaki. "Ke Maryama wanne irin rashin hankali ne haka kina ganin baƙi ba za ki kai su ɗaki ba." Aramma ya faɗa cikin faɗa shi a dole sai ya birge su Dada. Ɗaki ta kai su bayan sun gaisa suka yi mata gaisuwa cikin jimami, Dada har cikin ranta ba ta ji daɗin irin zaman da Maryama take yi da Aramma ba, domin mace ce mai sanyin hali da haƙuri. Duk wanda ya santa idan ya san Uwani dole zai ce albasa ba ta yi halin ruwa ba. Aramma jikinsa har rawa yake ya sa aka sayo musu ruwa, ba su jima sosai ba Dada ta kawo kuɗin sadaka dubu biyar ta bata. Sauran sirikan Dada kuma mai ɗari biyar mai dubu ɗaya duk suka haɗa mata, lokacin da za su tafi ne Dada ke ce wa Maryama Uwani za ta zauna har sai an yi sadakar uku za ta tafi. Har ƙofar gida Maryama ta raka su, su Baba Idris suka yi mata gaisuwa, suma suka kawo abin sadaka suka ba ta da shi ma Aramma. Har sun ɗauki hanya za su tafi Dada ta dawo ta ja Maryama gefe tana yi mata raɗa. "Dama kuɗin da aka ba ki ko da wasa kada ki ba wa wannan mijin naki kin ji Maryam!" Maryama ta gyaɗa kai jiki a sanyaye sannan ta raka Dada bakin mota tana ɗaga musu hannu. "Dada gaskiya zan yi kewarki kwana biyu an ya ba biyo ku zan yi ba?" Uwani ta faɗa tana tura ba ki gaba. Dada ta watsa mata harara sannan suka wuce. Tun da suka koma cikin gida Uwani ta lura da mahaifiyarta sam ba ta da nutsuwa, suna nan zaune sai ga Aramma ya shigo. "Ke Maryama kawo abin sadakar nan da aka ba ki zan haɗa a yi abincin rana." Tamkar kazar da ƙwai ya fashe wa a ciki haka Maryama ta miƙe jiki ba ƙwari ta kunto kuɗin wurin su Baba Idris ta miƙa masa. "Ke ba na son shashanci da rainin hankali, kina nufin su matan ba su ba ki komai ba? Wai Maryama me ya sa kin fiye baƙin halin tsiya ne." Ran Maryama ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, ganin irin tozarcin da Aramma yake yi mata a gaban Uwani da kuma sauran mutanen da suka zo gaisuwa. Don haka rai a ɓace ta ce. "Wai Aramma ya kake so na yi ne? Me ya sa..." Tun ba ta gama magana ba Aramma ya ɗauke ta da mari, yana shirin kai mata duka Uwani ta shiga tsakaninsu ta furta. "Baba bari na miƙo maka kuɗin a cikin jakar can ta ajiye dama na ji ta ce za a auno garin masara a yi tuwo, amma bari na miƙo maka." Jin haka ya sa Aramma ya washe baki ya ce. "Ka ji yarinya mai hankali maza miƙo mini, ke dai kin yi asarar hali Maryama." Babu musu Uwani ta zuge jakar da ta ga mahaifiyarta ta zuba kuɗin a ciki, ta ɗebo su duka ta miƙa masa. "Kai Allah wadaran naka ya lalace wallahi Maryama kin ji kunya ace wai har 'yar cikinki ta fi ki hankali." Wasu daga cikin ƙannen Aramma suka bi mahaifiyar Uwani da baƙaƙen maganganu. Ba ta tanka musu ba sai ma ruwan hawaye da ke tsiyaya daga fuskarta. Uwani na daga gefe ta ci gaba da kallonsu ɗaya bayan ɗaya, kowanne tana zana gashin azabar da za ta yi musu daga baya. Sai da mutane suka ragu a ɗakin sosai daga Maryama sai 'yan uwanta ta dubi Uwani ta ce. "Me ya sa za ki ɗebi kudina ki ba shi." Ta ƙarasa maganar fuska a haɗe. "Gobe da safe zai dawo miki da su Inna rance na ba shi!" Uwani ta furta cikin rashin damuwa. "Rance fa? Ta ya ya zama rance bayan a kan idona kika ba shi?" "Allah Inna kada ki damu zai dawo miki da kuɗinki har ma ya ƙara miki wasu." Jin sokiburutsun Uwani ya sa Maryama ba ta sake bi ta kanta ba saboda takaici. "Maryama yaya aka yi kika bari har ya ga lokacin da aka ba ki kuɗin nan? Kin fa san halin mutumin nan sarai, ba shi da tausayi ko kaɗan." Indo kishiyar Maryama ta furta ƙasa-ƙasa. "Ai kin san tun da ya gan su ya san za su ba ni wani abu, kuma ragowar ma ba ni na ba shi ba yarinyar nan ce ta ba shi." Maryama ta furta. Suka gama jajantawa juna, don zaman da suke yi sam babu kishi a ciki saboda dukkansu ba wani daɗin zama da shi suke ji ba. Wuni ɗaya da Uwani ta yi a gidan ta fahimci irin zaman ƙuncin da mahaifiyarta da kishiyarta suke yi a cikin gidan, a kan idonta ta ga Aramma ya yo cefane har da nama ya ce a yi masa jar miya da shi. A yadda ta lura hatta abinci ma daban ake yi masa, su kuma duk kwamacalar da ya ga dama sai su dafa. Don abincin dare sai da ƙyar Uwani ta iya cin miyar kukar da aka kaɗa, saboda haka ta ci alwashin gyara masa zama kafin ta bar gidan. Tun da doshin magriba Uwani ta hangi wani ludayin silba a kwandon wanke-wanken mahaifiyarta, a fakaice ta ɗauke shi ta ɓoye sai da dare ya tsala kowa ya yi bacci sannan ta saci jiki a hankali. Har za ta fita ta hangi wani zumbulelen farin hijabin Inna Suwaiba, wani tunani ne ya faɗo mata da sauri ta saki murmushi. Ta figi hijabin a hankali ɗayan hannunta ɗauke da ludayin sulba, can hanyar soro ta nufa da yake a baki-bakin ƙofa turakar Aramma take, daga ɗakinsa kuma sai ɗakin da suke ajiye kayan abinci. Toka ta ɗiba ta bursune fuskarta da ita sannan ta saka zumbulelen farin hijabin, ta leƙa ɗakin ta hango Aramma a kwance ya sharɓe sai sakin munshari yake yi daga shi sai gajeren wando. Da yake irin mutanen nan gajeru masu ƙiba ga uban tumbi. Tana shiga ɗakin ta tsaya a kansa, sai da ta gimtse dariyarta sannan ta daidaici gefen goshinsa ta ba shi raaaal da ludayin hannunta. A firgice Aramma ya miƙe yana dafe da goshi, "Wane ɗan iskan ne a tsohon daren." "Tawagar fatalwar 'yan iskan lahira ne!" Uwani ta faɗa da wata irin murya, ta sa hannu ta cikin hijabin ta buɗa shi, sai ta ƙara faɗi ta cikinsa. A razane Aramma ya ja da baya ganin hallitar da ke tunkaro shi. "Mu sababbin ƙawayen 'yarka da ta baƙunci lahira ne. A cikin fatale ma mu tawagar shaiɗanu ne domin fatattaka ɗan adam muke yi da kulkin lahira. Ita da bakinta ta gaya mana irin zalincin da kake yi wa iyalinka, don haka muka zo domin mu tsintsinka hanjin cikinka, ko kuma mu gayyato 'yan uwanmu mu yi daga-daga da kai." Uwani ta yi magana tana wani miƙa wuya gaba. Jin kalaman Uwani ya sa Aramma ya fashe da wani irin kuka mai cin zuciya, cikin tashin hankali ya ce. "Ku dubi Allah ku yi haƙuri wallahi zan daina duk abin da nake yi..." Da sauri Uwani ta katse shi. "Zo nan maza-maza, matso nan." "Don Allah ku yi mini rai." Aramma ya faɗa fuska haɗe da hawaye da majina. "Za fa ka taka ɗan tsiti a bayanka, wallahi tawagarsa ta fi ta mu bala'i ka matso na ce maka." Da sauri Aramma ya matsa tiɓi-tiɓi sai haɗa gumi yake. Yana zuwa ya tsugunna a ƙasa, hannun Uwani mai ɗauke da ludayin da ke cikin hijabi ta ɗaga da sauri ta sake ba shi raaal a ƙeyarsa. A zabure Aramma ya miƙe sai da ya yi tsalle uku ya faɗi a can gefe cikin azaba. "Fatalwar 'yarka ta gaya mana duk abin da matanka suke samu karɓe musu kake yi, a jiya ma ka karɓe wa uwar marigayya kuɗaɗenta to ko ka mayar mata da abin ta ko kuma mu mayar da kai kuɗi. Domin muna cikin irin fatalwar da ke yi wa 'yan ƙungiyar asiri aiki, za ka zama kuɗi wayyo kuɗi, kuɗi masu daɗi." Uwani ta yi maganar tana wani tsalle tana ɗaga hannu ta cikin hijabi kamar mai shirin tashi sama. "Na rantse da Allah ko wasu aka ce na ƙara mata yanzu zan ƙara mata su." Uwani ba ta bi ta kansa ba ta ce. "Da ma ga hantarka da zuciyarka nan muna gani manya ne, ko su kaɗai muka tsaface za ta kawo mana miliyoyi." Da sauri Aramma ya dafe cikinsa da hannuwansa biyu, ya sake ɓarkewa da kuka. "Idan ka sake ka tona mana asiri wallahi a yanzu za mu hallaka ka." Jin haka ya sa Aramma ya haɗiye kukansa, ya sa hannu biyu ya toshe bakinsa. Uwani ta sake jingina da bango ta furta. "Ganin yadda muka ga ka yi nadama za mu ɗaga maka ƙafa na kwana biyu mu ga idan za ka sauya halinka, kuma ka gaggauta mayarwa da mahaifiyar 'yar uwarmu kuɗinta. Sannan ita da kishiyarta dole ne ka ƙara musu dubu hamsin-hamsin. Kuma ya zama wajibi duk sati ka dinga ba su dubu uku-uku na kashewa." "Duka na ji kuma na yi alƙawari zan yi yadda kuka ce, na gode muku Allah Ya biya ku." Aramma ya yi maganar yana rissinawa. "Ba ma buƙatar godiya, yanzu dai za mu tafi da kai ka je ka ga makwancin 'yarka, sai mu baro ka a can bayan sadakar uku sai mu dawo..." Tun Uwani ba ta gama magana ba ya katse ta cikin kuka. "Wallahi na haƙura da ganin ta, Allah ba sai na ga halin da take ciki ba. Na san mai sunan Iya tana da halin na gari." "To kuwa ya zama wajibi ka zaɓi ɗaya, ko mu ɗauke ka ta ƙarfin tsiya mu tafi da kai. Ko kuma ka zo ka ku yi sallama da shugabar tawagar 'yan iskan fatale." Jin haka ya sa jiki na rawa ya matsa gaban Uwani ya ce. "Zan gaisa da ita..." Maganar bakinsa ta katse sakamakon jin saukar ludayin da ya yi a gaban kansa. Wannan karon kasa motsi ya yi ganin haka ya sa Uwani ta sake sauke masa na biyu aka sannan ta ɗora da cewa. "Yanzu haka za mu fita mu ba ka wuri, sauran tawagarmu na tsakar gidan nan. Kuma duk abin da ka ji ko kuma duk hukuncin da ka ji muna aikatawa matuƙar ka leƙo to zai dawo kanka. Sannan saura idan gari ya waye ka ce ga abin da ya faru da kai." Daga haka Uwani ta fice tana wani shagiɗewa gefe tana tura wuya gaba. Kusan duk abin da ya faru tsakanin Uwani da Aramma, Yaya ƙarama da su Rahane 'yan uwan Aramma sun ji, sakamakon ɗakin da suke kwance a jikin na Aramma yake. Da yake dama idan wani abin taro ya kama a gidan to duka danginsa a wannan ɗakin suke sauka. Kowannensu na daga kwance cikinsa ya ɗuri ruwa ko motsin kirki babu mai yi, babban abin da ya ɗaga hankalinsu yadda suka dinga jiyo kukan Aramma ƙasa-ƙasa, da ita kanta saƙon fatalwar da take faɗa. Suna nan kwance suka ji motsin Uwani a ƙofar ɗakinsu tana ɗan wani gurnani, take fitsari ya jiƙe zanin Yaya ƙarama. Uwani na ɗaga labulen ɗakin ta hango yadda aka jere yara a ƙasa, ɗaya bayan ɗaya haka ta dinga jidar yaran tana kai wa tsakar gida. Yaya ƙarama na daga kwance ta ji Uwani ta dafa ƙafarta, jiki na rawa ta ce. "La'ilaha'illahu Muhammadur Rasulillah." "Ba za ki mutu yanzu ba sai mu fafe ƙwayar idonki." Uwani ta faɗa da wata irin murya, har ta juya za ta fita ta ce. "Su kuma waɗancan yaran zan ba wa ƙananan fatalenmu umarni su gama da su." Uwani na ƙarasa magana ta wuce wurin yaran da ke kwance a tsakar gida, idan ta ɗauko yaro ɗaya sai ta gasa masa mintsini ta tura shi cikin ɗaki. Ganin yadda yaran ke shigowa a firgice cikin kuka ga magagin bacci ga kuma zafin mintsini, ya sa su Yaya ƙarama suka banka uwar ɗaki a guje. Uwani ta yi wata irin sufa ta rufa musu baya tana faɗin. "Ya Ahalul fataleeee ku zo ga nama mun samu." 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 [13/06/2024, 13:37] Ameera Adam: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA TARA Sai a lokacin Uwani ta fahimci ashe ba iya su Yaya Ƙarama ce kaɗai idonsu biyu ba, hatta mutanen da ke cikin uwar ɗakin lakur suka yi sai da suka ji Uwani ta yi sufa za ta faɗo uwar ɗakin suka fara ihun neman ceton rai. A daidai bakin ƙofar uwar ɗakin Uwani ta tsaya sai ta hango wata wuƙa a gefen randa, ta janyo ta ta fara wasawa. Naziru ɗan wurin Sa'a da a lokacin ya wartsake ya kafe Uwani da kallo, ganin haka ya sa Uwani ta kalle shi tana zare ido ta ce. "Ga wani ɗan ƙwage da shi za mu fara." Uwani ta ƙarasa maganar tana fusgar hannun Naziru da bai wuce shekara huɗu ba. "Wayyo Iyata! Wayyo Iyata." Ya fara ihu hankali a tashe don ƙiri-ƙiri ya ga wuƙar hannun Uwani. Sa'a na ganin haka ta fara jan hannun Naziru Uwani na jan ɗaya, Sa'a ta waiga wurin su Yaya ƙarama ta ce. "Ƙarama don Allah ku kawo mini ɗauki Naziri zai tafi." Yaya ƙarama da ke ƙuryar uwar ɗaki ta ce. "Sa'a ki haƙura da Naziru tun da ba wuce haihuwa kika yi ba, wallahi a yanzu ko Habibu (Shi kaɗai ne ɗanta) suka ja sai dai na bi shi da addu'a." Sa'a na shirin magana Uwani ranƙwala mata ludayi a ka, a guje ta saki hannun Naziru cikin kuka ta faɗa uwar ɗakin tana faɗin. "Wayyo Naziru." Shi ma Naziru sai tirjewa yake yana faɗin. "Iyata wayyo Iyata." Yaya ƙarama ce ta yi sauri ta banka ƙofar ɗakin ta danna sakata tana sauke ajiyar zuciya. "Idan kun rufe ƙofa za mu ɓullo ta ƙarƙashin ƙasa, mu dama ai daga kabari muke. A wannan lokacin babu buƙatar mu yi muku bayanin mu su waye, domin hukunta ku muka zo yi ɗaya bayan ɗaya, a kan cin zarafin da kuke yi wa mahaifiyar 'yar uwarmu da kishiyarta. Mu tawagar fatale sai mun saɓule fatar jikinku sannan mu tsotse romo da ɓargon jikinku. Amma za mu ɗaga muku ƙafa zuwa nan da ɗan wani lokaci, don mun lura kun fara nadama. Sai dai muna mai tabbatar muku babu wanda zai tafi gidansa sai an yi sadakar uku, idan kuma mutum ya yi kuskuren tafiya gida gobe, to a daren ranar sai dai ya kwana a ƙiyama." Uwani ta furta a lokacin da ta fita da Naziru tsakar gida da ke ƙwala ihu. A yadda ta lura kusan ilahirin mutanen gidan duka sun tashi, wata dabara ce ta faɗo mata don haka ta buga tsalle a tsakar gidan ta ce. "Waɗanda kuke leƙenmu muna gano ku, ke wato har da ke ko. Wallahi ɗaya bayan ɗaya za mu bi ku mu ƙwaƙwale idanunku idan ba ku koma kun kwanta ba." Ta saki hannun Naziru ai kuwa da gudu ya faɗa ɗaki yana ihu, sai ta tafi da gudu ta nufi ɗakin mahaifiyarta, a guje ta ji mutanen ɗakin suna shigewa uwar ɗaki wasu na hantsilawa. Nan ma ta nufi ɗakin kishiyar mahaifiyarta ta razana su, sai da ta tabbatar da sun gama tsorata kowa ya shige uwar ɗaki sannan ta lallaɓa ta isa banɗaki ta wanke fuskarta. Ta duƙunƙune hijabin Inna Suwaiba ta soke a hammata, sai da ta shirya sosai sannan ta nufi ɗakin mahaifiyarta da gudu tana faɗin. "Wayyo Allah! Ku taimaka mini za su ƙara janye ni." Tana shiga ɗakin ta tarar falon mahaifiyarta babu kowa an banke uwar ɗaki sai ƙananan yara da ke kuka suna buga ƙofa, saboda kada a gano Uwani ita ma ta fara bubbuga ƙofar tana ihu. Da ta lura ba za su buɗe mata ba sai ta janyo ƙofar falo ta datse. Har aka yi assalatu babu wanda ya yunƙurin fitowa daga ɗakin, duk da duka baƙin gidan a zuciyarsu kowa ya ayyana gari na wayewa tafiya zai yi. Amma da sun tuna kashedin da aka yi musu a kan kada wanda ya bar gidan har sai an yi sadakar uku sai jikin kowannensu ya yi sanyi. Sai da gari ya yi tangararan sannan Indo ta yi ƙarfin halin buɗe ƙofa, kamar sababin munafukai haka mutane suka dinga leƙowa ɗaya bayan ɗaya suna fitowa suna yin alwala suna sallah. Duk wannan abin da ya faru bayan da gari ya waye babu mutum ɗaya da ya jajantawa kowa, domin kowa a tsorace yake. Su Uwani suna zaune sai ga Aramma ya shiga ɗakin kansa ya yi waɗansu ƙulalai sun fi biyar, daidai tsakiyar hancinsa har wani ja ya yi yana maiƙo. Da mamaki suka bi shi da kallo, Aramma ya zauna daɓar jikinsa zafi zau da zazzabi. Gaishe shi mutanen ɗakin suka yi, suna son jin abin da ya faru da shi suna tsoro. Hannu ya sa a aljihu ya zaro kuɗin ya ce. "Ungo wannan Maryama, kuɗinki na jiya ne. Wannan kuma kyautar dubu hamsin ce na ba ki ita ma Indo zan miƙa mata nata." Baki sake Maryama ta bi shi da kallo, ta ce. "Malam dubu hamsin fa? An ya ba mantawa ka yi ba?" Aramma ya dube ta a fusace da ya tuna gargaɗin fatalwa sai ya wayance ya sassauta murya ya furta. "Maryama shaidar da za ki yi wa mijinki kenan? Kyautatawa ce kawai ta sa na ba ku." Maryama hannu na rawa ta sa ta karɓa tana zuba masa godiya, Aramma har ya miƙe zai fita Inna Suwaiba ta ce. "Aramma ungo shafa-shafa sai ka shafa a malolon nan na ka, Allah dai ya sawaƙe sanyi haka yake lokaci ɗaya ka ga wuri ya luluye. Ko kuma bige wa ka yi ne da dare?" Aramma da ba ya son a ja doguwar magana ya karɓa ya yi gaba ba tare da ya amsa mata ba, ɗakin Indo ya faɗa ita ma ya sallame ta ya koma ɗakinsa don ilahirin jikinsa ciwo yake masa. Aramma na shiga ɗaki sai ga Indo jiki na rawa ta shiga wurin Maryama suka fara tattaunawa cikin mamaki, ba su ƙara nutsa wa a tekun mamaki ba sai da suka ji Aramma ya ce a yi shinkafa da miyar dage-dage da rana. Wannan sabon sauyi da suka samu daga wurin Aramma ba ƙaramin daɗi ya yi musu. A na gobe Uwani za ta koma gida wurin ƙarfe goma sha biyu na dare ana zaune ana ɗan hira, ta hangi Aramma ya suri buta ya yi banɗaki. Sai da ta tabbatar da hankulan mutane ba ya kanta ta saci jiki ta nufi banɗaki, da yake banɗakin ya yi nesa da ɗakuna don haka ta laɓe a can kusurwar bango ta fara magana. "Baba ga tawagar 'ya'yanka sun dawo. Kada ka tsorata mune dai fatalen nan." Aramma da ke tsugunne a kan masai sai abin ya yi masa a daidai, saboda wata sabuwar gudawa ce ta tsarge shi. Gumi ya fara tsattsafo masa ya ce. "To 'ya'yana don Allah kada ku taɓa lafiyata, wallahi har yanzu ban warke ba." "Ba za mu sake cutar da kai ba, domin ƙawarmu wato matacciyar 'yarka ta ce ta ga irin kyautatawar da kake yi wa iyayenta da 'yan uwanta. Ki yi masa magana ya ji sabuwar muryarki ta cikin jinsin fatalwa." Uwani ta yi maganar tana wani fuffuka, sannan ta maƙale murya ta furta. "Baba ni zan tafi da kai na fi so na dinga ganinka." Tamkar an buɗe fanfo haka cikin Aramma ya birge, ya ci gaba da sakin gudawa babu ƙaƙƙautawa. Cikin tashin hankali ya ce. "Na yafe don Allah ki je ki ɗauki mahaifiyarki." "Shi kenan Baba zan dai dinga kawo muku ziyara a ɓoye duk dare ina ganin rayuwar da kuke yi, idan na ga saɓanin abin da ka fara yi wallahi cikin tumbinka zan shiga, na kannaɗe hanjinka ita kuma kodarka na fansarwa shugaba." Uwani ta furta tana gimtse dariyarta. "Wallahi komai zan ci gaba da yi idan na saɓa ki mini duk abin da za ki yi mini." "Mu zamu tafi Baba sai mun sake zagayowa." Uwani na gama faɗar haka ta fara wata fuffuka tana gurnani sannan ta saɗaɗa ta bar wurin. Saboda yadda Aramma ya razana bayan da ya gama uzurinsa a duƙe ya dinga tafiya, saboda yadda ya ji ƙafafuwansa sun yi sanyi har sun gagara ɗaukar nauyin gangar jikinsa. Ranar da aka yi sadakar uku dai tun da safe wasu daga cikin 'yan gaisuwa suka fara watsewa, domin dama wasu tamkar a kan ƙaya suke. Ita ma Uwani sai da aka yi sallar la'asar sannan Aramma ya zo ya sanar da Maryama an zo ɗaukan Uwani, ta so Uwani ta ƙara kwanaki amma babu yadda ta iya haka ta danne. Wasu daga cikin 'yan uwan mahaifiyarta sai tsokanarta suke suna amarya sai sun zo biki. Kafin Uwani ta fita sai da Maryama ta sata a gaba ta yi mata nasiha sosai. Fakare Uwani ta yi tana sauraronta kamar nasihar na shigarta, sai gyaɗai kai take tana amsawa. Sai da ta gama sauraron mahaifiyarsa sannan ta ce. "Ni kam Inna don Allah zan faɗa miki wata magana amma don Allah kada ki faɗa wa kowa." Take gaban Maryama ya faɗi amma sai ta basar ta ce. "Ina jin ki babu wanda zai ji Uwanina." Duk abin da ya faru tun daga farko har ƙarshe ta sanar da ita tana dariya, ita kanta Maryama dariya take sheƙawa sanna ta riƙe baki ta furta. "Allah Ya shirye ki Uwani ni dai wallahi ban san halin wa kika ɗauka ba, mahaifinki dai har ya fi ni sauƙin kai. Allah Ya shirya ki ko ba komai kin samar mana 'yanci." Suna cikin haka suka ji ƙarar horn da sauri Uwani ta sungumi jakar kayanta, ta ɗauko hijabinta ta saka. Sai da ta yi wa mutanen gidan sallama da Aramma sannan ta ƙarasa bakin motar cikin murna, don tun daga nesa ta hango motar baba Mamman. Don haka da saurinta ta buɗe motar tana faɗin. "Daddy wallahi na yi kewar Dada, ƙila ma ita tana can ko a jikin..." Kalamanta suka maƙale a maƙoshi sakamakon ido biyu da suka yi da Jafar. Wata uwar harara ya banka mata, ta yamutsa fuska tana ƙare masa kallo ta ce. "To kai kuma ina motarka ka ɗauko ta Daddy?" Jafar bai tanka mata ba ya fisgi motar da gudun gaske har sai da wasu yara suka matsa a guje. Suna cikin tafiya babu wanda ya tanka wa wani sai Uwani ta fashe da dariya har da ƙyaƙyatawa, a fusace Jafar ya waigo ya zuba mata manyan idonsa. Sai kuwa Uwani ta sake kwashewa da dariya, gangara motar ya yi ya faka ya ɗauke kai gefe a daƙile ya ce. "Fice mini daga mota." Uwani ta gimtse dariyarta sannan ta ce. "Kamar ya na sauka ai ba motarka ba ce." "Uban me kike wa dariya?" Uwani ta yi murmushi ta ce, "Wallahi dariya ka ba ni, ni dai ba baƙuwa ba ce a wurinka atoh. Kuma dai komai na ka Dada ta ba ni labari tun kana jariri har fa tunbiɗin da ka dinga yi kana yaro. Sai kuma na ga ka fafaki mota kana yin wani irin tuƙin 'yan Kaduna-Zaria, to wai ni birgar me za ka yi mini?" Jafar ya haɗiyi wani yawu mai ɗaci haɗe da fusgar da iska mai zafi, jin irin maganganun da Uwani ta faɗa masa. Yana shirin yin magana Uwani ta sake sakin wata dariyar tana faɗin. "Kasan Allah yadda ka iya fafakar motar nan da Inuwan Toyota zai ganka tsaf zai ɗauke ka kwandasta, saboda wataran idan ya gaji ya ba ka ɗani..." "Fice mini a mota." Ya furta mata cikin tsawa. "Wallahi ba zan fita ba ai motar Daddy ce, malam kada ka yi mini gori ni nan gaba ma jirgin sama zan tuƙa." Kalamanta na ƙarshe suka kusa ba shi dariya. 'Yarinyar da cikakkun sentence na hausa ma ba ta iya haɗawa ba ita ce za ta tuƙa jirgin sama.' Ya raya a ransa. Ganin za ta ɓata masa lokaci ya sa ya fisgi motar ya ci gaba da sharara gudu, har suka ƙarasa gida wani bai sake kula kowa ba. Tun Jafar bai gama faka motar ba Uwani ta suri jakar kayanta ta ɓalle murfin motar ta fice a guje ko rufe motar ba ta tsaya yi ba, tun daga soro ta fara ƙwalla wa Dada kira tana washe baki. Mami da ta rako aminiyarta Hajiya Falmata ganin Uwani ya sake tado mata da wani malolon baƙin ciki. "Ƙwata wannan abar ce fa aka aura wa Jafar, imagine a ce wannan ce sirikata." Hajiya Falmata ta ƙare wa Uwani kallo sannan ta saki wani malalacin murmushi ta furta. "Haba ƙawata wai da wannan 'yar abar ce ke barazana da aurenki? Tun da ƙuruciya ba ki yi yaji ba sai yanzu? Babu inda za ki, matuƙar kin bi duk tattaunawar da muka yi wallahi na faɗa miki da ƙafarta za ta kori kanta babu boka babu malam." Sai a lokacin Mami ta ƙara jin ƙwarin gwiwa, Hajiya Falmata ta ci gaba da biya mata miyagun shawarwari sannan suka yi sallama. Da murna Dada ta tarbi Uwani don ita kanta ba ƙaramin kewarta ta yi ba, dalilin da ya sa tun safe ta sa baba Mamman ya ɗauko ta. Shi kuma ya ce a bari zuwa bayan azahar sai Jafar ya ɗauko ta. Kuma ya yi haka ne domin so yake kafin lokacin tariyarsu su ƙara samun fahimtar juna. Sai da aka yi sallar Margriba kamar yadda Baba Yunusa ya ce za a zauna ya tara 'yan uwansa, Dada, na Madina, Uwani, Jafar da kuma Mami. Sai da ya buɗe taron da addu'a bayan kowa ga gama sannan ya fara magana. "Alhamdu Lillah! Na san wasu daga cikinku sun san dalilin wannan zaman yayin da wasu kuma ba su sani ba. Maƙasudin zamanmu a kan kai Jafar da kuma ke Uwani ne." Jafar ya sunkuyar da kai ƙasa rai a bace. Tsabar takaici ya sa Mami yin ƙwafa a fili, Dada ta dube ta haɗe da taɓe fuska ta ce. "Aure dai Allah Ya haɗa duk mai hassada sai rabo ya kashe shi, yara su haihu kuma a mayar da sunansa." Mami ta shiga aika wa Dada harara a fakaice. "Jafar a yanzu wani nauyi ya hau kanka domin aure ba wasa ba ne, ka riƙe yarinyar mutane amana don a yanzu da kake gani komai nata ya dawo ƙarƙashin ikonka. Ke kuma Uwani wannan da kike gani aljannarki na ƙarƙashin ƙafarsa, ki bi mijinki sau da ƙafa yi na yi bari na bari. Duk abin da kika san zai faranta ran mijinki shi za ki yi, abin da ba ya so sai ki haƙura da shi don zaman aure ɗan haƙuri ne." Sai da Baba Yunusa ya numfasa sannan ya ci gaba. "Mun tattauna ni da 'yan uwana a kan za ku tare tare da Mahaifinku tun da an riga an ɗaura aure babu fa'idar a ce za a zauna har sai nan da wata biyu idan auren su Shukra ya zo. A don haka idan Allah Ya kai mu ranar Laraba mai zuwa ne mahaifinku Mamman ya ce za a ƙarasa gyara komai da saka komai na gidan, tun da akwai wadataccen wuri za ku zauna a ƙaramin part ɗin da ke gefen na Maminku." Wani irin tuƙuƙin zafi ne a zuciyar Mami har za ta ƙi amimcewa da hakan sai kuma ta tuna da huɗubar ƙawarta Hajiya Falmata. "Saboda haka muka yanke shawarar idan Allah Ya kai mu juma'a mai zuwa ne tariyarku, kuma bayan nan za a nema wa Uwani wata makarantar za ta ci gaba da karatunta. Idan ya so bayan sun yi hutu sai ka ɗauki matarka ku wuce wurin aiki." Jafar ya yi shiru ba tare da ya amsa ba. Wannan maganar ta ƙarshe ba ƙaramin daɗi ta yi wa Mami ba, don a wannan lokacin ne za ta ci karenta babu babbaka a kan Uwani. "Ni iya abin da zan iya ce wa kenan, Dada kafin mu zo kan ki ko akwai mai magana a cikin?" Gabaɗaya suka girgiza kai ban da Baba Mustafa da ya ce yana da abin cewa. "Sannu da ƙoƙari Yaya Allah Ya ƙara girma, duk bayananka a kan tsari suke. Amma abin da nake gani me zai hana a ɗaga tariyar ta su zuwa nan da kamar sati biyu zuwa uku, duba da yanayin ragowar shirye-shiryen da ya kamata a yi musu. Daga haɗa lefe har zuwa wani shirye-shirye na su na mata, sannan a wannan lokacin mahaifiyar yarinyar na cikin halin rashin 'yarta. Amma bayan wannan lokacin ita kanta za ta samu nutsuwar gudanar da bikin yadda ya kamata." Dada ta jinjina kai sannan ta furta. "Wallahi Mustafa ka yi kyan kai, saboda Allah kamar gajiya na yi da Uwanin da za a ce nan da kwana huɗu a kai ta ɗakin miji." Baba Yunusa ya yi murmushi ya furta. "Wannan haka ne, Dada me za kike ganin ya dace bayan haka." Dada ta yi jim sannan ta furta. "Ni dai kam nasiha ce zan yi wa Jafaru da ita Uwani, amma kam ba yanzu zan yi musu ba sai ranar da za su tare. Don ina gudun na tofar da yawun bakina a banza, su barbaɗar da nasihar da na yi musu tun kafin tariyarsu." Tambayar Mami aka yi ko tana da abin faɗa ta ce babu, don haka suka ƙarƙaren zaman tun ba a gama addu'a ba Mami ta sa ƙafarta ta fice rai a ɓace. 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 [21/06/2024, 12:32] Ameera Adam: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA SHA UKU Jin yadda jikin Uwani yake karkarwa ya sa Jafar ya kwantar da ita a jikinsa ya sa hannu ya fara bubbuga bayanta, nan take idanunsa suka yi jawur saboda ɓacin rai. Ya dubi mutumin murya a dashe ya furta. "Ka san wa ka taɓa kuwa? Ka san wanne irin kuskure kake yunƙurin aikatawa. Wallahi sai na nuna maka bakin rijiya ba wurin wasan makaho ba ne." Jafar ya ƙarasa maganar yana yunƙurin cire Uwani daga jikinsa, cikin kuka Uwani ta furta. "Tsoro nake ji Ya Jafar don Allah kada ka sake tafiya." Ajiyar zuciya Jafar ya sauke ya riƙe hannunta suka fara tafiya rai a ɓace, ganin haka ya sa Alhajin ya zuba a guje ya faɗa ɗakinsa ya datse ƙofa. Ɗakinsu suka wuce sai da Jafar ya sa key ya buɗe suka shiga, ya kai ta kan kujera ya zaunar da ita sannan ya ce. "Ki jira ji yanzu zan dawo." Fuska da hawaye Uwani ta furta. "Ya Jafar kada ka tafi ya shigo mini." Sunkuyawa ya yi daidai fuskarta ya ɗan hura mata iska ya furta. "Ba abin da zai faru da ke yanzu zan dawo kin ji." A hankali Uwani ta gyaɗa masa kai sannan ya fice. Ɗakin Alhajin ya koma ya yi bugun duniya ya ƙi buɗewa, shi kuwa Alhaji tumbin kuɗi jin ana buga ƙofar ɗakin abokinsa da ƙarfi, ya sa ya ƙara wa tashi ƙofar key sannan ya wuce banɗaki a guje jiki na rawa ya ɓuya. Ganin ba shi da niyyar buɗewa ya sa Jafar ya zaro waya ya danna lambar DPO ɗin unguwar Zoo road, da yake abokinsa ne. Nan take ya sanar da shi abin da ya faru tsakanin Uwani da Alhajin. Sannan Jafar ya sauka ƙasa ya sanar da ma'aikatan reception abin da yake faruwa da kuma ɗakin da Alhajin yake ciki. Wata mata da ke gefe nan take ta furta. "Kai malam Allah Ya yi maka albarka. Wallahi ni ma jiya da dare na ɗan fita unguwa na dawo haka wani ya dinga mini ɗan kira, da na shiga ɗaki har buga mini ƙofa ya yi ƙila ma shi ne." Jafar ya furzar da iska mai zafi ya ce. "Daga yau ai ba zai ƙara ba." "A toh ai wasu mutanen gani suke idan suka ga mutum ya kama hotel kowa ma ɗan iska ne, Allah Ya kyauta." Ba a ɗauki lokaci ba sai ga motar 'yan sanda ta ƙaraso, lokacin da suka je bakin ƙofar Alhaji sai da ƙyar ya buɗe musu ƙofa. Har ƙasa ya tsugunna yana ba wa Jafar haƙuri amma fir ya ƙi sauraronsa, yaran D.P.O bayan sun saka masa ankwa Jafar ya ce su wuce da shi zai zo daga baya. A wurin da ya bar Uwani a nan ya koma ya same ta, fuskarta ta kumbura saboda kuka. Tana ganinsa ta yi zumbur! Ta miƙe tsaye. Bai kula ta ba ya koma can gefen gado ya zauna ya dafe kansa, wani irin ɗaci yake ji a maƙoshinsa ya ɗago murya can ƙasa ya ce. "Ya aka yi mutumin nan ya biyo ki ke da na bar ki a ɗaki?" Zuciyar Uwani ɗaya ta fara masa jawabi. "Ni fa kasan ƙafata ba ta saba zaman wuri ɗaya ba, gajiya na yi da zama shi ne na fita can ƙasa na sha iska. Da na dawo sai na rasa ɗakin nan, bisa tsautsayi na faɗa ɗakin wani ɗan iska..." Uwani ta kwashe komai ta gaya masa amma ba ta gaya masa irin azabar da ta yi wa Alhaji tumbin kuɗi ba, ta dai ce masa Allah ne ya ƙwato ta bayan ta fito wannan Alhajin ya biyo ta. Tass! tass! Jafar ya sauke wa Uwani wasu tagwayen mari biyu a fuska, cikin ɓacin rai ya furta. "Uban waye ya ce ki fita? Ba ki da hankali za ki fita da waɗannan kayan?" Ganin yadda Jafar ya hargitse mata lokaci ya sa nan take jikinta ya fara karkarwa, ya rufe ta da faɗa tamkar zai rife ta da duka daga ƙarshe ya faɗa toilet ya bar ta a zaune. Bai jima ba ya fito har lokacin ransa a ɓace yake ya furta. "Ki shiga ki yi wanka za mu wuce gida yanzu." Zani uwani ta ɗauka ta faɗa ban ɗaki kafin ta fito har Jafar ya gama shiryawa, gefe da gefen fuskar Uwani har ya ɗan kumbura don har lokacin ba ta daina hawaye ba. Jafar na zaune a gefen gado ya hango Uwani ta fito don ita ta manta ko hula ma ba ta saka ba, a razane yake bin ta da kallo baki sake. Ganin irin kallon da Jafar yake bin ta da shi ya sa Uwata ta sha jinin jikinta, tana sake tunkaro shi Jafar ya zabura a guje ya nufi ƙofa yana faɗin. "Wayyo Allah! Jama'a ku taimaka mini sun biyo ni nan ma!" Da yake ya manta ya datse ƙofar haka ya yi ta murɗawa ta ƙi buɗuwa. Cikin rashin fahimta Uwani ta ɗan waiga ta ce. "Wai ya Jafar me yake faruwa ne?" Laƙwas Jafar ya yi ya zauna a ƙasa kamar mutum-mutumi yana kare mata kallon, tamkar ya ga sabuwar hallita. Uwani ta shiga goge kanta da towel ko a jikinta ta ce. "Malam ka fita zan shirya." Har lokacin Jafar mamakin Uwani yake, ya shiga tariyo abin da ya dinga faruwa a cikin dare. Uwani ta fahimci sarai in da Jafar ya dosa, ta fito da kayan da za ta saka ta sake furta. "Don Allah ka fita zan shirya." "Uwani ina gashinki?" Cikin halin ko in kula ta ce. "Dada ta aske mini tun rannan." Miƙewa ya yi ya tako gabanta sannan ya furta. "Wato iskanci ne ya sa kika dinga tsora ta ni ko? Wallahi za ki shiga hannuna da ni kike zancen." Take dariyar da Uwani ke gimtsewa ta suɓuce mata. Jafar ya saki wani malalacin murmushin mugunta yana ayyana irin azabar da zai yi mata cikin ruwan sanyi ba tare da Daddy ya gane ba. Daga haka Jafar ya fice daga ɗakin, Uwani ta saka kayanta sannan ta haɗa ragowar kayanta da ke warwatse ta saka a jaka. Ba su ɗauki lokaci ba suka shirya suka fito Jafar ya ƙarasa gaban ma'aikatan da ke reception ya biya duk abin da ya suka kashe, sannan ya yi musu sallama suka fita da yake akwai Manajan wurin da shi a ka kai Alhaji can police station. Domin a cewar Manajan Alhajin na ƙarƙashin kulawarsu dole ne su san halin da yake ciki. Lokacin da su Uwani suka ƙarasa gida mommy ta rako ƙawarta Hajiya Binta bakin gate, ganin su Uwani ya sa Mami ta yi turus tana faɗin. "Ya aka yi Jafar?" Jafar ya ɗan sosai, sannan ya gaida Hajiya Binta da ke bin sa da kallon tuhuma. "Ƙawata wai kar dai raɗe-raɗin da nake ji a kan auren Jafar haka ne?" Hajiya Binta ta tambaya tana satar kallon Uwani. Ras! Gaban Mami ya faɗi, ta ɗan basar tana ƙirƙiro murmushin yaƙe ta ce. "Haba Hajiya Binta kina ganin akwai yarinyar da Jafar zai aura a duniyar nan bayan Safna? Ai me aiki ce ya taho mini da ita daga Lagos, a bakin gada take kwana shi ne ta roƙe shi Allah-Annabi wai ta dinga yi masa aiki. Da ya sanar da ni na ce idan zai taho ya kawo mini ita, kin san ɗa na kowa ne ƙawata." Cikin gamsuwa Hajiya Binta ta bi Uwani da wulaƙantaccen kallo ta furta. "Ban da taɓarɓarewar zamani yanzu wannan yarinyar har ta isa kwanan gada, mtsww Allah Ya sawaƙe." Mami ta furta. "Amin dai, yo yaran da maza ke ba su ɗari biyar suna sa su a ɗaki ina za ki yi mamaki?" Kalaman Mami da ƙarshe da ta jefi Uwani da su ba ƙaramin zafi suka yi masa ba, don haka ko sallama bai yi wa Hajiya Binta ba ya wuce. Ita kanta Uwani kusan daskarewa ta yi a wurin jin irin munanan kalaman da Mami ta jefe ta da shi, tunanin da ta zurfafa ciki ne ya sa Jafar ya wuce ba tare da ta sani ba. A ɗan tsawace Mami ta ce. "Tsawar me kike yi a gabanmu ne?" Babu yadda ta iya haka Uwani ta ja jaka jiki a sanyaye ta wuce ciki, kai tsaye sashensu ta shiga idanunta cike da ƙwallah. Sanin Daddy ba ya gidan ya sa Mami kai tsaye ta wuce sashen su Jafar, a falo ta same su duka ta dubi Jafar ta ce. "Wai fasa tafiyar ka yi ne Jafar?" Bai ɗago ya kalle ya ba ya furta, "Eh Mami." Jim ta yi tana nazartarsa ta furta. "To haka za ka zauna ana tsorata ka har a sabauta mini kai?" Jafar ya furta. "Ai na biya ta Islama Islamic Center na karɓo magani, kuma ya ce mini za a dace In shaa Allah." Jafar shi kansa ya yi mamaki yadda ya tsara wa Mami wannan jawabin, Mami ta wurga wa Uwani mugun kallo ta ce. "Wuce mu je akwai aikin da za ki yi mini." Babu musu Uwani ta bi bayan Mami, Jafar ya kwanta a kan doguwar kujewa. Haka kawai ya ji yana kewar Safna, don haka ya zaro waya ya kira ta suka fara hira. Mami na shiga sashensu ta haɗo wa Uwani wanki duk da a lokacin magriba ta fara kawo kai, bayan gida ta zuba mata wankin ta yadda koda an yi a arashi Daddy ya dawo ba zai ganta ba ballanta ya yi mata faɗa. Kuma dama ta san ba ya gari, don haka za ta ci karenta babu babbaka akan Uwanin. Cikin wankin da Mami ta haɗo wa Uwani har da labulaye da zannuwan gado, tun Uwani na wankin cikin daɗin rai har ta fara galabaita tun da ko a wurin Dada ba ita take yin wankin kayanta ba. Lokacin da aka kira sallar magriba Uwani wucewa ta yi sashenta don ya gabatar da sallah, tafiyarta babu jimawa Mami ta zagaya ta ga wurin wayam. Sai tsirarin kayan da ta shanya ga waɗansu nan a cikin ruwa. Uwani na zaune tana zaman tahiya Jafar ya shiga ya zaune yana kallonta, a yadda ya lura da Uwani duk hatsabibanci da ƙiriniyarta ba ta wasa da sallah ko kaɗan. Hakan ba ƙaramin birge shi yake ba, yana nan zaune Mami ta shigo ko shi ba ta yi wa magana ba ta rufe Uwani da duka. Ganin dukan da take wa Uwani ba zai ƙare ba ya sa Jafar ya yi saurin shan gaban ta. "Lafiya kuwa Mami? Me ta yi miki haka?" Jafar ya furta hankali a tashe. "Lallai Jafar wannan abar har kake tarewa?" Mami ta faɗa tana sauke numfashi. Ban da kuka babu abin da Uwani take yi, ga gefen bakinta ya fashe jini na ɗiga. Saboda yadda ta galabaita kukan da take yi ko fita ba ya yi, Mami ta sake zuba mata ranƙwashi a ka tana shirin yin magana Jafar ya ce. "Mami wai me ta yi miki?" "Wanki na saka ta don iskanci za ta zube mini ta zo ta saka miji a gaba, idan uwarki ce ta saka ki za ki ajiye mata." Mami ta yi maganar tana dungurin Uwani, cikin kuka Uwani ta ce. "Sallah aka kira shi ne na zo na yi..." Da sauri Mami ta sake doke Uwani nan take bakinta ya sake fashewa. "Haba Mami, ina ce Haladu ne yake yin wanki. Kuma sallah fa ta ce ta zo..." Tas! Mami ta ɗauke Jafar da mari, ba ta tanka masa ba ta figi hijabin Uwani ta fara janta a ƙasa, ba shiri Uwani ta miƙe ta bi Mami. Saboda ɓacin rai tun ba su gama fita ba Jafar ya gegare su ya fice daga gidan zuciyarsa na suya. "Iyeee Allah Jafar watsa mini ƙasa za ka yi a ido yaushe har ka san zafin mace. Wallahi dole kai ma na ɗauki mataki a kanka." Mami ta yi maganar a ɗan tsorace don ta yi tsammanin ko wuta za ta jefa Uwani sai dai Jafar ya taya ta ba dai ya hana ba. A cikin duhu ga sauro haka Uwani ta wanke ragowar kayan da ba ta ƙarasa ba, kanta ban da ciwo babu abin da yake yi. Bayan ta gama ne ta nufi sashen Mami har ƙasa ta zube ta furta. "Na gama wankin." A yamutse Mami ta dube ta tana shirin sallamarta Shukra ta shiga ɗakin tana taunar cingam ta ce. "Ke zan saka ki aiki yanzu saura ki yi mini hauka." Uwani ta ɗaga kai a galabaice ta amsa wa Shukra. Auta da ke zaune a gefe duk sai ta ji babu daɗi, tana son ta yi magana amma tana tsoron faɗan Mami. "Kina ji Shukra na yi miki magana ba za ki iya amsawa ba?" Mami ta yi maganar tana haurin Uwani. Sai da ta goge ƙwallar idonta sannan ta rarrafa gaban Shukra ta tsugunna. "Ga Salim nan ya faka motarsa a cikin gate, za ki je ki wanke masa kuma wallahi idan ba ta wanku ba sai kin sake." Da sauri Auta ta furta. "Aunty Shukra wankin mota fa?" Shukra ta sake shan kunu ta ce, "Waya na yi da shi zai kai wankin mota ya ce ba zai samu zuwa yau ba, so don haka na ce ya zo gida za a wanke masa saboda ina son magana da shi." Cikin tausaya Auta ta ce, "To shi kenan zan ta ya ki Uwani..." "Waye ya gayyace ki? Uwar iyayi da kankanba?" Mami ta katse Auta. Shukra ce ta yi gaba Uwani ta bi bayanta a lokacin zazzaɓi har ya fara rufe ta, lokacin da suka ƙarasa Salim na cikin mota. Da ya hango su ne ya fito yana sakarwa Shukra murmushi. "You are welcome dear." Shukra ta furta tana fari da ido. "Beb an ya zan iya jiran sati ukun nan masu zuwa kuwa? Kin ga yadda kika yi kyau." Salim ya furta cikin shauƙin soyayya, Shukra ba ƙaramin daɗi ta ji ba kin kissa ta ce. "Well mu je mu zauna, ga 'yar aikin Mami za ta wanke maka mota." "Za ta iya kuwa Baby? Na ga mata ba sa wankin mota." Salim ya faɗa yana bin Uwani da ke rakaɓe a gefe. Shukra ta dubi Uwani a tsawace ta ce. "Ke ba ki iya gaisuwa ba ne?" Jikin Uwani na rawa ta tsugunna ta gaishe da Salim, sannan Shukra ta ɗan yi murmushi ta furta. "Ai in gaya maka daga motar Daddy har ta ya Jafar ita take wankewa za ka sha mamaki." Shukra da Salim suka wuce wurin wasu fararen kujeru, daga wurin da suke zauna suna iya hango Uwani da duk abin da take yi. Sai da ta goge ƙwallar idonta sannan ta ɗauki bokiti ta fara ɗebo ruwa, da yake wurin ɗiban ruwan yana da ɗan nisa da wurin wankin motar a galabaice ta fara wankin motar har ta gama. Gaban Shukra Uwani ta je ta tsaya ta ce, "Na gama wankewa." Shukra ta bi ta da harara sannan ta ce. "Matso nan." Ba musu Uwani ta matsa gaban Shukra, da ƙarfin tsiya ta fisgo Uwani har sai da ta bugu da ɗan ƙaramin table ɗin da ke gabansu ta ce. "Don ubanki ke ba ki da ladabi ba za ki iya tsugunnawa ba?" Shukra ta ƙarasa maganar tana zuba wa Uwani ranƙwashi. "Haba Beb da kin ƙyale ta kin san irin yaran nan ba wani tarbiyya suke samu ba, so don sun yi haka ni ba zan yi mamaki ba." Salim ya faɗa a ɗan ƙyamace yana duban Uwani da ta gama jiƙe wa da ruwa sharkaf. "Dallah tashi ki ba ni wuri kina tafe da baƙi kamar na zunubi." Dariya sosai Salim ya yi jin abin da Shukra ta faɗa ya furta. "Wai yaushe kika koyi masifa ne love?" "Haba ka rabu da ni na tsani yarinyar nan wallahi." Uwani na laɓe a ta bayan fulawiyin da ke zagaye da harabar gidan, takaici ya mamaye zuciyarta. Wani tunani ne ya faɗo mata don haka da sauri ta zagaya can bayan gidan, ta ɗebo irin manyan bokitan fentin nan guda biyu waɗanda ta gama wanki da su. Sai da ta yagi wata igiya ta haɗa hannuwansu ta ɗaure, sannan ta saki murmushin mugunta. Cikin sanɗa ta fara tafiya ta cikin fulawoyi, a daidai bayan su Shukra ta tsaya ta ji Salim yana faɗin. "Haba ke dai Baby ba kya mantuwa, wannan fa mahaukacin ma shammatata kawai ya yi amma yadda nake ƙaunarki akwai abin da zan ga zai cutar da ke na gudu ban taimaki rayuwata ba, ke ce fa rayuwata ke ni fa idan za ki rayu da farinciki zan iya sadaukar da komai ciki kuwa har da numfashin da nake zuƙa." Shukra ta rangwaɗa kai cikin farinciki, tana shirin ba shi amsa Uwani ta saki murmushi duk da zazzaɓin da ke jikinta. Sai da ta daidaita saitin kansu sannan ta ɗaga bokitan fentin hannunta, ta kifa musu a kansu ta saka iya ƙarfinta ta danne saman ta yadda ba za su iya fisgewa ba. Salim da abin ya haɗe masa biyu ga zafin hula ga na bokiti ya ware murya cikin ihu ya ce. "Wayyo Allah wuyana!" "Wayyo kaina, Baby kana ina!" Shukra ta faɗa a ɗimauce. Daga Salim har ita sai ɗaga hannuwa suke cikin neman taimako. Sai da Uwani ta ga sun fara galabaita sannan ta fisgo hannun bokitin ta baya, da yake ƙafafuwansu na ƙasan table ɗin da ke gabansu faɗuwar da za su yi ta baya sai suka taho da table ɗin da ƙafafuwansu. Uwani na ganin za su kai ƙasa ta yi saurin matsawa a guje, sai ji kake rugugum! kacacar kofuna da ruwan jarkar duka sun watso kansu. Ga bokiti ya sarƙafe su ga kuma ƙafafuwasu sarƙafe a cikin table, Uwani ta laɓe a cikin shukoki tana dariya ƙasa-ƙasa don duk ƙwaƙwar mutum ba zai gano da mutum ɓoye a wurin ba. Da ƙyar Salim ya samu ya zaro ƙafarsa daga cikin Table, ya tashi zai zuba a guje Uwani da ke laɓe ta sake fisgo shi da yake igiyar tana hannunta. Daɓar Salim ya koma ya faɗi hankali a tashe ya ce. "Jama'a a taimaka mana wallahi jana ake yi." Shukra ce ta yunƙura ta tashi a guje saboda tashin hankali ko yunƙurin cire bokitin ba ta yi ba, ita da Salim suka zuba a guje a daidai lokacin Jafar ya shigo harabar gidan. Turus ya yi ya ɗan fara ja da baya ganin ƙafafuwan mace da namiji suna tafe da bokiti a kai, da yake ba sa ganin gabansu yana ganin sun tunkaro shi ya zube takalmansa shi ma ya shige a guje yana ihun. "Wayyo Allah! Lado kana ina?" Jin ihun Jafar ya sake ruɗa su Salim, a wannan lokacin Lado ya zagayo da buta a hannu shi ma turus ya yi yana kallon ikon Allah. Da ƙyar Salim ya samu ya cire bokitin kansa, hular ta faɗi can gefe. Dama takalminsa na cikin ƙasan table ya jima da fita, iya ƙarfinsa ya tattara ya fita a guje yana faɗin, "Jama'a ku duba mini kaina idan yana gangar jikina." Sai a lokacin Lado ya gane shi, ya bi bayansa yana faɗin. "Alhaji ka bar motarka." Lado na ƙarasawa bakin gate ko ƙurar Salim bai gani ba sai agogonsa da links ɗin hannun rigarsa da suka zube a wurin. Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki turo ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank sai shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 idan littafi ya kammala za ki turo 800 Free pgs ɗinmu ya kusa ƙarewa🫠 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 [22/06/2024, 13:32] Ameera Adam: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA SHA HUƊU *BOJUWA HERBAL'S & SCENTS* *Suna kawo Saiwowin da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.* *Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah* *Saiwowin tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru* *Saiwowin matsi gangariya* *Original gadalin mata* *Ƴaƴan gadali na asali* *Original gumba* *Tsumin Saiwowi* *Tsumin kwakwa da Dabino* *Igiyar alkairi* *Zumar goran tula* *Hakkin daka na musamman na asali* *Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*. *Akwai bridal package* *Mai jego package* *Ƴar gata package*. *Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.* *A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne* *Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi* *08032773332* *Iyah Basiru na gaisuwa*😅 A sanyaye Lado ya ɗebo agogo da links ɗin Salim ya dawo cikin gidan, sai dai yana shiga ga wutar harabar wajen ta ɗauke. Ga kuma ƙarar duka da ake yi wa Shukra tana ihu, zuwa can kuma sai ya ji an yi wurgi da bokiti an zuba cikin gida a guje. Gudun kada abin da ya same su, shi ma ya zo kansa ya sa Lado ya shige ɗakinsa ya danno ƙofa ya rufe don shi kansa bai manta abin da aka yi masa a tsakar dare ba. Da gudu Uwani ta bi bayan Shukra tana gurnani tana zabga mata igiyar a baya har Shukra ta fara kama ƙafar bene Uwani ba ta daina dukanta ba, tana hawa sai ga Shukra na rarrafe tana kuka saboda tashin hankali. Sai da ta ga Shukra ta shige sannan Uwani ta yi saurin ɗebe bokitan ta mayar da su wurin da suke, ta je ta ɗaga table ɗin ta mayar da ruwan jarkokin kai sannan ta koma ta kunna ƙwan fitilar harabar wurin ta wuce sashenta. A lokacin da ta shiga sashenta shiru babu motsin Jafar, ta zube a kan kujera kanta na matsanancin ciwo kamar zai tsage gida biyu. Uwar ɗakinta ta wuce don ta sauya kayan jikinta saboda rawar ɗarin da take yi, ɗrower kayanta ta buɗe tana shirin miƙa hannu ta yi ido biyu da Jafar tsugunne a cikin. Uwani ta basar kaman ba ta san abin da ya faru ba ta ce, "Kai kuma Ya Jafar mene ne haka?" Jafar ya fara wuri-wuri sannan ya ce. "Wai Uwani ke ce kika zama biyu ko ya aka yi?" Jafar ya wurga mata tambaya. "Wai me ka mayar da ni ne ya Jafar? Ni fa yanzu na gama yi wa saurayin Shukra wankin mota bayan na gama yi wa Mami wanki..." Cikin sauri ya katse ta. "Wankin me? Ke kika wanke wa Salim mota? To su waye na gani da bokiti a kansu suna ihu?" Uwani ta wara hannu ta ce. "Ni kam ban sani ba, ƙila dai mutanen gidan ne suke son buɗe maka ido." Jafar ya yi fakare yana nazari, abu ɗaya ne ya fi tsaye masa a rai wai Uwani ce ta wanke wa Salim mota. A fili ta ji ya furta, "Dole sai na ɗauki mataki a kanta." Uwani ta yi saurin tambayarsa. "Wace ce?" Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya furta. "Babu komai." Saboda tsabar gajiya Uwani na sauya kaya ta ɗauro alwalar Isha'i ta gabatar da sallah, a nan kan dadduma bacci ya yi awon gaba da ita. A yadda ya ga tana sauke numfashi sama-sama ba ƙaramin tausayi ta ba shi ba, ya ƙarasa ya cire mata hijabin ya ji jikinta ya ɗauki zafi zau! Cikin jakarsa ya duba ya ɗauko Paracetamol, ya jima yana tashinta sannan ta tashi ya ba ta magani. Duk yadda ya yi da ta tashi ta ci abinci ƙi ya yi, ya rabu da ita ya haye gado ya kwanta. Shukra da rarrafe ta ƙarasa falon Mami, babu ɗankwali ballantana mayafi ko takalmi, a razane Mami ta fara tambayar Shukra. "Ke Shukra lafiyarki kuwa?" "Mami ki ɓoye ni bokiti ne, wallahi bokiti ne ya danne mu ni da Salim." Da mamaki Mami ta ce, "Kamar ya bokiti ne Shukra? Shi bokiti mutum ne da zai iya motsi har ya danne ku. Wai ma ina ɗankwalinki?" Shukra fuska da ta gama jagulewa da makeup da hawaye ta zayyanewa Mami duk abin da ya faru, Cikin damuwa Mami ta ce. "Ni fa wallahi ina zargin yarinyar nan tana da Aljanu, mu dai tun da muka tare babu wani abin tashin hankali da muka taɓa gani. Amma tun ranar da yarinyar nan ta zo gidan nan masifar yau daban ta gobe daban, yanzu bala'in har ya kai kina hira ke da Salim ana razana ku? Gaskiya dole a san abin yi." Daga haka Mami ta shiga lallashin Shukra, da ƙyar a daren ranar Shukra ta yarda ta kwana a ɗakinsu. Da yake Daddy ba ya gari ya sa asubar fari Shukra ta koma ɗakin Mami bayan ta yi sallar asuba ta koma ta kwanta. Washgari Tun bayan sallar asuba Uwani da Jafar har sun koma bacci, suka ji bugun ƙofa. Jafar ne ya je ya buɗe da mamakin mai buga musu ƙofa da farar safiya. Karo ya kusa yi da Mami a ɗan duburburce ya ce. "Mami ke ce tun yanzu?" Mami ta ƙare masa kallo ta ce, "Eh ni ce, ina Uwani take?" Jafar ya ɗan sosa kai ya ce. "Tana ciki bacci take yi." "Ciki ina? Uwar ɗaki?" Jafar ya gyaɗa kai. Cikin sauri Mami ta ce, "To kai kuma a ina ka kwanta?" A ɗan kunyace Jafar ya ce, "Ni ma a ciki na kwanta..." "Laha'ilaha'illallahu Jafar tun ba a je ko ina ba?" Salatin Mami ya katse shi. A ɗan duburburce ya ce. "Am ai ita a ƙasa take kwana ni nake kwana a kan gado." A fili Mami ta sauke ajiyar zuciya tana murmushi ta wuce cikin ɗakin. Yadda Jafar ya faɗa mata haka abin yake, bacci Uwani take sosai a ƙasa saboda gajiya. Mami ta ɗauki ruwan jarkar da ke kan mudubinta ta sheƙa mata, a zabure ta tashi tana waige Mami ta taɓe baki ta ce. "Ki zo ki wuce kitchen za ki taya Inna haɗa breakfast, kin saki baki kina bacci ai duk gidan nan babu bawanki da zai dafa miki ki dinga ci." Jafar kamar ya yi magana sai dai kuma ya yi shiru, tun da yake bai taɓa samun saɓanin da mahaifiyarsa da har za ta mare shi ba, don haka ya kawar da kai har Uwani da Mami suka fice daga ɗakin. Suna tafe Mami ban da masifa babu abin da take mata, kai tsaye kitchen suka wuce. A lokacin Inna har ta fara haɗa kayan breakfast, suna shiga Mami ta dubi Inna ta furta. "Inna daga yau Uwani za ta dinga zuwa tana ta ya ki haɗa kayan breakfast." Inna ta washe baki cikin jin daɗi ta ce. "Allah Ya taimaki Hajiya, ina matuƙar godiya. " Uwani da har lokacin bacci bai gama sakinta ba, ta fara murza ido. Ba ta yi aune ba sai jin ranƙwashin Mami ta yi a kanta ta furta. "Kin ga dai ta hanyar da na biyo da ke, wallahi kika kuskura kika bi ta ƙofar ciki daidai da rana ɗaya kika haɗa ni da Dadyn yara sai ranki ya yi mummunan ɓaci." Cikin damuwa Uwani ta amsa mata, Mami har za ta fita ta juyo ta ce. "Idan kuma kin gama ki same ni a falo." Mami na fita Uwani ta jingina kai da bango, lokaci ɗaya hawaye ya fara ziraro mata. "Yarinya a wannan lokacin kuka ba na ki ba ne, shi wannan aikin da kika ga Hajiya ta kawo ki mu dinga yi gata ne take yi miki. Saboda duk macen da ba ta iya girki ba wallahi ta faɗo a wurin miji, ki ci gaba da haƙuri watarana sai labari." Inna ta yi maganar ƙasa-ƙasa. Kukan da Uwani take yi ya yawaita jin kalaman Inna ya sa ta furta. "Wallahi ni kam na gaji Inna, gara na koma wurin Dada ni ban saba da wannan wahalar ba." Sai da Inna ta ɗan leƙa bakin ƙofa sannan ta sake ƙasa da murya ta ce. "Ita dama rayuwar aure ai takan zo wa bawa da al'amura mabanbanta. Ni na ɗauke ki tamkar jikata duk abin da yake damunki ki dinga samuna a fakaice kina gaya mini, amma kada ki bari kowa ya fahimci haka don gudun mu samu matsala ni da ke." Uwani ta ji daɗin yadda Inna ta amshe ta hannu bibbiyu, don haka ta share hawayenta ta fara taya ta duk abin da ya dace. A cikin aikin da suke yi ne Inna ta fahimci sam Uwani ba ta iya wani girki ba, hatta aikin ma wani abin sai ta koya mata. Sai kusan tara saura sannan suka kammala komai, don har wanke-wanke babu abin da ba su gama ba. Uwani ce ta bi Inna dianing tana ganin yadda take yin komai, lokaci ɗaya Uwani ta nemi duk ƙuncin da take ciki ta rasa. Suna gab da barin kitchen ɗin ne Mami ta dawo tana bin Uwani da harara, ta dubi Inna ta ce. "Idan kun ƙarasa aikin ki ɗebo mata gero kwano ɗaya ta surfa, ta niƙe mini shi yau furar daka nake sha'awa." A sanyaye Inna ta amsa, Mami ta wuce ta buɗe tukwanen wurin, ganin abincin da Inna ta rage kusan na mutum bibbiyu ne ya sa Mami ta furta. "An kai wa Lado abincinsa ne?" Da sauri Inna ta amsa. Mami ta sake haɗe fuska ta ce. "Wannan abincin ai ya yi miki yawa Inna zuba mini a wancan plate ɗin." "Dama ni da Uwani na rage mana..." Mami ta yi saurin katse Inna. "Uwani idan ta gama za mu rage mata abincinta a wurinmu." Inna babu yadda ta iya haka ta ɗauki plate ta zuzzuba kamar yadda Mami ta buƙata, kusan shekararsu Takwas tana yi wa Mami aiki ba ta taɓa ganin ta yi mata iyaka da abinci ba sai yau, a ranta ta jinjina ƙarfin ƙiyayyar da take yi wa Uwani. Uwani tana kuka haka ta karɓi geron ta nufi harabar gidan tana dakawa, tun ba a je ko ina ba hannunta ya fara kanta ga turmin dakan ba shi da girman kirki don a surfe ma sai da ta raba shi gida huɗu sannan ta gama dake shi. Tun Uwani na cikin inuwa har rana ta same ta don sha biyun rana a lokacin ta kusa, tana nan tana daka su Shukra suka fito cikin shirinsu gwanin birgewa. Auta ce ta ƙarasa wurinta da sauri ta ce. "Uwani me kike yi haka ne?" Uwani ta share hawayenta. Tausayin Uwani ya kama Auta, a sanyaye ta ce. "Ki yi haƙuri Uwani In shaa Allah Mami za ta gane abin da take ba ta kyautawa, unguwa za mu yanzu wallahi da na taya ki." Uwani ta gyaɗa mata kai sannan ta wuce wurin su Shukra da har sun fita bakin gate. Fitar su Shukra ba jimawa ita ma Inna ta zo ta yi wa Uwani sallamar za ta je kasuwar Garu, Mami ta aike ta yin cefane. Ita kanta Inna ta so taya Uwani sai dai tana tsoron kar ta je ta yi abin da za ta bar aikinta, don da kuɗin albashinta take samun na rufin asiri. Lokacin da Uwani ta gama ta gama galabaita, ga yunwa ga kuma gajiya. Can kitchen ta je ta ajiye wa Mami garin geron saboda ba ta san yadda za ta sarrafa shi ba, ta fito za ta shiga ta ƙofar falo ta hangi wani tafkeken jangwalagwada. Har a fili sai da Uwani ta saki murmushi, ta ɗauko tsumma a kitchen da sauri ta ƙarasa wurinsa ta yi A'uzubillahi sannan ta damƙe shi da hannunta, a wannan karon ta ci alwashin yadda Mami ta azabtar da ita to ita ma sai ta rama. Har ta gama tsara komai koda ta kwaɓe mata tana gamawa Kura za ta yi wurin Dada, kuma ko kashe ta za a yi ba za ta dawo gidan ba. Cikin sanɗa take tafiya har ta shiga falon babu motsin kowa daga can ɗakin Mami ta fara jiyo muryarta sama-sama da alama waya take yi. Ta matsa a hankali da niyyar ta buɗe ƙofar ta zura mata ƙadangaren ta ji Mami na faɗin. "Haba Hajiya Karima kin gan ni fa na tuɓe kaya yanzu haka wanka zan shiga, don Allah ku jira ni. Kin san yadda nake bala'in son haɗuwa da matar DC kuwa? Kin san fa duk in da harkar manya take ba ma sanya da ita." Uwani ta saki murmushi da ta tuna tsiyar da za ta ƙulla wa Mami. A kan kunnen ta Mami ta gama wayar ta faɗa banɗaki, sai da ta tabbatar da wankan Mami ya fara nisa sannan ta buɗe ƙofar ɗakin a hankali ta shiga. Ƙofar banɗakin ta nufa sai ta fara murɗa ƙofar da sauri-sauri, daga ciki Mami na saɓa sabulu a fuska ta ji ana murɗa ƙofar. Mamaki ne ya kamata don ta san su Shukra ba sa nan, kuma ko suna nan ba za su buɗe mata banɗaki tana ciki ba. "Waye a nan?"Mami ta tambaya a hassale. Uwani ta kausashe murya ta ce, "Sarki ne ya zo da kansa ba aike ba." Da mamaki Mami ta furta. "Sarki wane iri? Kai waye da har za ka tsallake ko ina ka shigo ɗakin matar aure, kuma har ka nemi buɗe ni a banɗaki." "Sarautar ce haka! Kuma na aure ki daga yau, tun da na samu sukunin mai gidanki ba ya nan. Dama tun ranar da aka yi maganar auren ɗanki Jafar ni ma na kai kuɗin aurenki, yanzu haka kuma na biyo ki ne domin na ɓarje amarci." Uwani ta ƙarasa maganar dariya na son ƙwace mata. A hargitse Mami ta ce. "Kai malam wai waye kai ne ma? Ba ka da hankali za ka ce ka na son matar aure?" Uwani ta sake kausashe murya ta ce. "Ni dai babban burina ki ba ni haɗin kai domin ni matashin saurayi ne dal, soyayya ce kawai ta sa na tsaya a kanki. Amma kada ki yi mamakin kasancewa ta wata halitar da ba irin taki ba." Uwani na gama faɗar haka ta buɗe ƙofar a hankali ta wurgar wa Mami Jangwalagwadan sannan ta janyo ƙofar da ƙarfi ta rufe, da yake da key a jikin ƙofar nan take Uwani ta murza key ɗin ta cire shi ta ajiye a gefen gadon Mami. Lokacin da Mami ta ji abu ya sauka a kafaɗarta da sauri ta hau kiciniyar wanke kumfar fuskarta. Hannunta ta kai ta shafo kafaɗarta bayan ta wanke fuskarta, wani irin ƙadabarbar ta ji take jikinta ya hau karkarwa. Ta yi ta maza ta yi wurgi da shi, sai a lokacin idonta ya sauka akan tafkeken ƙadangaren. Da yake shi ma ya galabaita nan take suka fara 'yar tsere da Mami a banɗaki, duk yadda Mami ta so buɗe ƙofar sai ta gagara. Cikin Kuka Mami ta ce. "Wayyo Allah Lado, Jafar kana ina ka kawo mini ɗauki." Uwani ta gimtse dariyarta, ta sake matsa wa jikin ƙofar ta ce. "A yanzu babu mai iya taimakonki domin amarci na zo ci. Kuma daga yanzu ni fa zan dinga rikiɗa har zuwa surar mutane ina kawo miki ziyara." Uwani na gama faɗar haka ta sulale ta fice daga ɗakin, cikin sauri ta zagaya ta wuce sashenta. Jafar ta gani ya yi ɗaiɗai a falo yana bacci, da alama kallo yake yi bacci ya yi awon gaba da shi don ga remote nan a gefensa. A hankali ta wuce cikin ɗakinta ta faɗa kan gado tana sauke ajiyar zuciya, ƙugin da cikinta ke yi ne ya sake ankarar da ita yunwar da ke cin ta. Kitchen ta faɗa ta fara duba tukwane, ta ci karo da guntuwar Indomie da Jafar ya ci ya rage. Tukunyar ta ɗauko ya zuba shayi ta koma falo ta zauna ta ci, sannan ta buɗe bokitin dubulan ɗin ta ta ɗebo alkaki da dubulan na gararta ta baje a ƙasa ta ci gaba da loda wa cikinta. Tana cikin ci suka ji bugun ƙofa kamar za a ɓalle ta. "Ranka ya daɗe! Ranka ya daɗe akwai abin da yake faruwa a sashen Hajiya." Jafar shi da Uwani kusan lokaci ɗaya suka miƙe a zabure, da sauri Jafar ya buɗe ƙofar ya ga Lado da Baba tsoho, a ɗimauce ya ce. "Lafiya Lado?" "Ranka ya daɗe bugun ƙofa nake ji a sashen hajiya kuma idan aka buga bayan wani lokaci sai na ji shiru, kuma sama-sama nake jiyo muryar Hajiya kamar tana kuka." Jafar tun bai gama jin kalaman Lado ba shi da Uwani suka zuba a guje suka yi sashe ta, ganin haka ya sa Lado da Baba tsoho suka rufa musu baya. Jafar na zuwa ɗakin Mami ya nufa, abin mamakin komai tsaf yake babu wata hayaniyar tashin hankali. Wani rin numfarfashi suka ji a cikin banɗaki, da sauri Jafar ya dinga buga ƙofar yana kiran sunanta. Bugun da Jafar yake yi ne ya sake farfaɗo da Mami daga suman da ta yi, wanda ta yi suma a cikin banɗakin babu adadi. "Jafar! Wayyo Jafar ka shigo ka taimaka mini, wallahi ƙadangare ne zai haike mini." Mami ta yi maganar a galabaice don saboda wahalar da ta sha ko motsin kirki ba ta yi. Da ƙarfi Jafar ya dinga buga ƙofar amma a ƙame take ƙyam ta ƙi buɗuwa, "Ranka shi daɗe wannan ba shi ne mabuɗin na?" Lado ya ɗago key ɗin da ke kan gadon Mami. Da sauri Jafar ya karɓa ya buɗe yana buɗewa ƙadangaren ya yo bakin ƙofar a guje, ganin haka ya sa daga Lado har Jafar suka ɗiba a guje. Sai da suka ga ya shige ƙarƙashin gado sannan suka fara leƙowa, Mami da rarrafe da jan ciki ta fara tahowa Baba tsoho ya tunkari ƙofar banɗakin da niyyar taimaka mata, yana leƙawa ya hangi Mami tumɓur da sauri ya juya da baya yana faɗin. "Kai a'uzubillahi wannan lamari da muni yake." Baba tsoho ya nufi bakin ƙofa su Jafar na ganin yadda ya dawo jiki a sanyaye Lado ya je zai shiga da sauri Baba tsoho ya girgiza kai ya furta. "Ummm-ummm ku dawo Lado abin babu kyawun gani." Lado na zuwa ya ci karo da Mami na jan ciki, Mami da take a yunwace da neman taimako ta fara jan ƙafar wandon Lado tana faɗin. "Ku fitar da ni daga gidan, idan ba haka ba za su kashe ni." Ganin yanayin da Mami take ciki ya sa Lado ya fisge a guje yana faɗin. "Subhanallahi wannan lamarin ya munana Baba tsoho me ya sa ba ka buɗan aiki ba? Haka kawai zan ƙone idanuna." Jafar ya nufi wurin banɗakin, kamar haɗin baki Lado da Baba tsoho suka yi wata uwar sufa suka dafe kafaɗun Jafar suna faɗin. "Wallahi al'amarin akwai muni Jafar kada ka shiga." A ƙufule Jafar ya fisge ya ce. "Ni da uwata ne za ku yi mini iyaka? Duk halin da take ciki ni ba zan guje ta." Jafar ya fisge da ƙarfi ya tunkari wurin da Mami take. Cikin hukunci Ubangiji gobe ne za mu kammala Free pages ɗinmu, idan kina buƙatar ci gaba za ki biya 500 ta wannan Acc Aisha Adam 3090957579 First bank sai shaidar ta wannan lambar 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 [23/06/2024, 12:50] Ameera Adam: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA SHA BIYAR *BOJUWA HERBAL'S & SCENTS* *Suna kawo Saiwowin da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.* *Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah* *Saiwowin tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru* *Saiwowin matsi gangariya* *Original gadalin mata* *Ƴaƴan gadali na asali* *Original gumba* *Tsumin Saiwowi* *Tsumin kwakwa da Dabino* *Igiyar alkairi* *Zumar goran tula* *Hakkin daka na musamman na asali* *Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*. *Akwai bridal package* *Mai jego package* *Ƴar gata package*. *Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.* *A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne* *Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi* *08032773332* *Iyah Basiru na gaisuwa*😅 Jafar na shiga da ya ga a halin da Mami take ciki turus ya yi, da sauri ya juya cikin damuwa ya dubi Uwani ya ce. "Maza ki shirya ta za mu wuce asibiti." Uwani da ke gimtse dariyarta ta wuce sumi-sumi kamar sabuwar munafuka ta ƙarasa wurin Mami da ke sharɓe a ƙasa. Baba tsoho shi da Lado dama tuni suka fito harabar gidan, suna nan tsaye Jafar ya fito abin duniya ya dame shi. "Kai Jafaru, wai ya aka yi ƙadangare ya shiga har banɗakin mahaifiyarka? Ko dai ture aka yi mata?" Jiki a sanyaye Jafar ya ce, "Wallahi Baba tsoho ban da masaniya, ka na gani dai kune kuka kira ni ina ɗaki." Daga haka gabaɗaya suka yi jigum-jigum. Abin ka da mai ƙiba Uwani da ta ɗago Mami sai dai ka ji ta sake komawa sharaf, kuma har lokacin idanun Mami a rufe suke. Da ƙyar Uwani ta samu ta ja Mami a ƙasa kamar rago, ta ƙarasa da ita bakin gado tana zaunar da ita a kai ta sake tafiya sharaf, kayan da ta gani a gefe wanda Mami ta ɗauko za ta sa su ta fara dubawa. Rigar maman Mami ta ɗauko ai kuwa Uwani tana ɗaga wa ta faɗi a wurin tana ƙyaƙyata dariya saboda girmanta, sai da ta yi mai isarta sannan ta miƙe ta fara kiciniyar saka wa Mami. Da ƙyar Uwani ta samu ta shirya Mami sannan ta leƙa waje ta kira Jafar, yana zuwa nan take ya kama Mami ita ma Uwani ta kama ta suka fita ita. A kujerar baya suka saka Mami, Jafar ya kunna motarsa suka wuce asibiti. Suna zuwa asibiti da sauri aka karɓi Mami aka shiga da ita, aka fara ba ta agajin gaggawa. Sai da Jafar ya ga Mami ta samu bacci sannan ya samu sukunin kiran Daddy ya sanar da shi halin da ake ciki, a nan take yake sanar da shi yana hanyarsa ta dawowa. Lokacin da Mami ta farka gabaɗaya iyalanta na wurin, Daddy ne ya matsa gaban gadon ya fara yi mata sannu. Da wani irin kallo take bin sa ta yunƙura ta cukumo wuyan rigarsa a zabure tana faɗin. "Wallahi ba zan aure ka ba, ni ina da aure har da 'ya'yana!" Da sauri Daddy ya riƙo ta, Mami ta ɗago kai tana ƙare masa kallo sai gani suka yi Mami ta sake tafiya luuuu a sume. Har rige-rigen fita kiran Likita suke yi, babu jimawa Dr Nura ya shiga cikin shigarsa ta likitoci. Sai da ya gama jin bayaninsu sannan ya ce gabaɗaya su fita, don yana son ba ta kulawa babu buƙatar hayaniya. Daddy ya so zama don ciwon na Mami ba ƙaramin tsoro ya ba shi ba amma Dr ya ce ya fita. Wata allura ya yi wa Mami ba ta fi minti ɗaya ba ta sake farfaɗowa, tana daga kwance ta ga Dr Nura tsaye a kanta cikin fararen kaya ga farin gilas maƙale a idonsa. "Wato wannan karon rikiɗe mini ka yi zuwa wannan surar kenan? Wannan fa idan ba da gaske na yi na ƙwaci kaina ba sai ya illata ni ya cuci iyalina." Duk waɗannan maganganun Mami na yin su a cikin zuciyarta ne, ta dai kafe Dr Nura da kallo ko ƙiftawa ba ta yi. Ta fara motsa baki a hankali tana biya Ayatulkursiyyu. "Sannu Hajiya! Yanzu yaya kike jin jikin na ki?" Dr Nura ya tambaye ta yana gyara tsayuwarsa. A hankali ta yunƙura ta tashi zaune tana ɗan dafe kanta, cikin shammata Mami ta suri dogon ƙarfen nan da ake maƙala ledar ƙarin ruwa a jiki ta shiga zungura masa tana kwaɗa masa. Idan Mami ta karanta Ayatulkursiyyu ta tofa masa sai ta ɗaga ƙarfen ta ba shi ƙwal. Hankali a tashe Dr Nura ya shige can kusurwar ɗakin yana faɗin. "Help! Help! Help!" Mami ta sake zungura masa ƙarfen tana faɗin. "Wato don ubanka har surar Nasara kake rikiɗewa ai wallahi yau ko ni ko kai." Dr Nura ganin neman agajin da yake yi da harshen turanci ba zai kai shi ba, ya sa ya taƙarƙare cikin ihun tashin hankali ya ce. "Wayyo Allah! Jama'a Patient ɗin nan za ta halaka ni." Su Daddy na daga waje suka jiyo ihun Dr Nura, da gudu suka taho za su buɗe ƙofar, sai dai da yake Mami na jingine da ƙofar tana jin alamun za a buɗe ta sake danna ƙofar da ƙarfi tana zungurin Dr. Ganin Mami na niyyar illata shi ya sa ya faɗa ƙarƙashin gadon asibitin, da ƙyar su Daddy suka turo ƙofar suna ganin ta da ƙarfen suka shiga kallon-kallo suma suna ja da baya. Daddy ne ya murɗe hannun Mami ya karɓe ƙarfen ya ajiye, sororo ta yi ta fara kallonsu ɗaya bayan ɗaya sannan ta ce. "Daddyn yara da gaske kune? Ina ne nan?" Kafin Daddy ya ba ta amsa tuni Dr Nura ya yi wata irin sufa irin ta jaruman indiya ya fice daga ɗakin, glass da takalmansa kusan lokaci ɗaya suka yi tsalle sama suka zube a tsakar ɗakin sai dai hakan bai sa ya tsaya ko waige ba ballana ya ɗebi abin sa. Kan gado Daddy ya zaunar da ita yana yi mata sannu, sai ji suka yi ta fashe da kuka tana faɗin. "Daddyn yara ni dai daga nan ka wuce Kura da ni, har abada ba zan sake kwana a gidan can ba." Kamar ƙaramar yarinya Daddy ya shiga lallashinta sai da ta yi shiru sannan ya tambaye ta ainihin abin da ya faru. Tiryan-tiryan Mami ta sanar da shi abin da ta ji da kuma shigowar ƙadangaren, don ita ko shigar su Jafar ba ta sani ba saboda ta yi suma ya fi bakwai a cikin banɗakin. A yanzu shi kansa Daddy ya fara yarda da cewar gidan ba su kaɗai ba ne, saboda ya sake kwantar mata da hankali ya ce ya amince za su koma can da zama. Uwani na rakuɓe a gefe ta yi zuru tana ƙarewa fuskar Mami kallo, tana mamakin yadda Mami ta zabge ta zuƙe a wuni guda, suna haɗa ido ta doko mata harara ba shiri Uwani ta janye idonta gefe. Daddy da kansa ya koma kiran likitan da zai sake duba Mami duk da ya lura ciwon ba na asibiti ba ne, da ƙyar ya samu Dr Samira ta je ta duba Mami ta saka mata ƙarin ruwa da allurai bayan wani lokaci aka sallame ta. Su Shukra ko kaɗan ba su so komawa Kura ba don dai babu yadda suka iya ne, ita kuwa Uwani murna fal ciki. Daddy ne ya kwashe su suka ɗebo kayan sakawarsu. Mami kuwa fir ta ƙi yarda ta shiga gidan sai a mota suka bar ta. Su Shukra sun ɗauki hanyar Kura babu jimawa Salim ya kira ta a kan zai je ya ɗauki motarsa, bai dai gaya mata ba amma a cikin ransa ya ƙissima ba zai sake zuwa gidansu ba har zuwa lokacin da za a ɗaura musu aure. Adaidaita sahu ne ya sauke shi a ƙofar gidan Daddy, gaban Salim ne ya fara faɗuwa a hankali ya yi ta maza ya ƙarasa jikin gate ɗin ya fara ƙwanƙwasawa. Daga cikin gidan Lado ya furta. "Waye nan?" "Lado ni ne." Zuro kai Lado ya yi yana ganin Salim ya washe baki ya ce, "Allah Ya taimake ka, yau kaine da rana tsaka." Salim ya miƙa masa mukullin motarsa ya ce. "Shiga ka tuƙo motata ka fito mini da ita." Sororo Lado ya yi ya furta. "Ranka ya daɗe ni da ko mashin ban iya tuƙawa ba, ina ni ina tuƙa mota?" "Lado amma gidan nan ba ku kaɗai ba ne a ciki, ka na gani dai rannan aka so tafiya da mu a bokiti ban da ƙarfin addu'armu da ta iyaye da tuni wani zancen ake ba wannan ba." Lado ya yi jim sannan ya ce. "Ranka shi daɗe naka ai mai sauƙi ne." To yau dai in faɗa maka tik da ka sani haka ƙadangare ya tarfa Hajiya tumɓur tana wanka. Kai yanzu haka ma suna can hanyar Kura don gabaɗaya Hajiya ta rikice, ban da sha'anin iska ina ka taɓa jin ƙadangare ya auri mutum? Wai ƙadangare ne fa yake ce mata amarci zai sha da ita, ina ka taɓa ganin ƙadangare na magana?To Kai kuwa ma a shekarun Hajiya ban da neman cika wa da imani me take nema a wurin namiji ballantana ƙadangare? To ɗazun nan sun zo ɗiban kaya za su wuce Kura Uwani ta kwashe komai ta faɗa mini." Take cikin Salim ya sake kaɗawa, ganin ya ɗan fara ja da baya Lado ya ce. "Ni ma fa Baffa nake jira ya zo a yi wacce za a yi, idan har ƙadangare zai auri Hajiya ni waye da ƙangaruwa ba za ta aure ni ba. Haka kawai ina zaune ta murƙushe ni cikin dare babu mai ceton rai." Salim ya zaro ido ciki a tsure ya ci gaba da ja baya. Lado ganin haka ya sa ya ce. "Ranka shi daɗe ina za ka je ne? Ka shigo ka ɗauki motarka mana." Salim ya zabura a razane ya furta. "Allah Ya tsare ni wallahi, zan aiko a ɗaukar mini ita daga baya don ita kanta motar kafin na fara hawa sai an yi mata sauka biyar." Daga haka Salim ya juya ko sallama bai yi wa Lado ba yana zuba sauri. Da zuwan su Mami Kura ba a ɗauki lokaci ba, labarin abin da ya faru da ita ya watsu cikin gidan gabaɗaya. Facalolinta sai zuwa suke duba ta, wanda yawanci zuwan da suke yi da biyu suke yi. Domin masu yi mata dariya a bayan fage sun fi yawa saboda irin habaicin da ta dinga yi musu a lokacin da za su tare. Sai daga baya Dada ta shiga a lokacin yawancin mutane sun watse daga Daddy sai su Jafar, Uwani kuwa dama tun da ta shiga gidan ta yi sashen Dada daga nan ta wuce wurin turken awakinta. Sannu a hankali jikin Mami yake ƙara samun sauƙi, ganin yadda Mami ta yi laushi ya sa Uwani ta yi tsammanin ko Mami sauya halinta ne. A haka sai da suka shafe kusan kwana goma a cikin gidan, kuma a wannan kwanakin kullin sai Daddy ya sa an yi saukar karatun Alƙur'ani. Wannan saken da Uwani ta samu ya sa hankalinta ya kwanta, ta manta da matsalar Mami gabaɗaya. Don tun da suka koma Kura sau biyu ta shiga duba Mami, kuma ba wata kyakkyawar fuska take samu ba. Su Mami ba su suka koma gidansu ba sai bai fi saura sati guda bikin Shukra ba, da ƙyar Mami ta yarda ta koma kuma kafin ta koma sai da suka yi musayar ɗaki da Daddy, ita ta koma ɗakin Daddy shi ya koma ɗakinta. A kwalemar fitar da kayan ne aka fitar da Jangwalagwadan da ya shiga ɗakinta, don shi kansa ya galabaita. A lokacin da za su tafi ne Uwani ta saka kuka don cewa ta yi fir ba za ta koma ba, sai da Dada ta lallaɓa ita da Daddy ta amince amma sai cewa ta yi sai dai idan da awakinta za ta koma. Ba musu Daddy ya amince ya ce zai yanki wani wuri a cikin farfajiyar gidan a yi wa awakinta wuri, amma sai bayan bikin su Shukra. Cikin farinciki Uwani ta bi Jafar suka wuce duk da shi ma ba wata fuska take samu a wurinsa ba, amma ba ya zagin ta ko cin zarafin ta. Shirye-shirye sun fara kankama a wurin su Mami da wurin iyayen Salim, da yake Mami na zirga-zirga sai tsangwama da takurar da take yi wa Uwani ta yi sauƙi. Haka kuma Uwani ta fara gogewa da aikin da suke yi da Inna, don wani lokacin ma idan Inna ta gaya mata yadda za ta sarrafa abu ita take yi. Tun ana gobe kamun bikin Shukra hankalin Mami yake a tashe sakamakon wayar da suka yi da mahaifiyar Safna, a kan cewar za su zo ranar Juma'a da safe su tafi ranar Lahadi bayan ɗaurin aure. Sakamakon biyo jirgin da za su yi daga Lagos zuwa Kano. Tun da suka gama wayar gumi yake keto wa Mami. Ganin ta rasa mafita ya sa ta kira Shukra ɗaki. "Shukra ina tsoron asirinmu ya tonu, ina gudun duk plan ɗin da na shirya ya wargatse. Kin san dai matuƙar Safna da mahaifiyarta suka zo gidan ko yaya ne za su iya fuskantar Jafar na da aure, alhalin ni kuma ban sanar da kowa ba bayan Hajiya Falmata." Shiru Shukra ta yi sannan ta ce. "Hanya ɗaya ce, mu nemo abin da zai sa Yaya ya sake ta kawai." "Ta wace hanya kenan?" Shukra ta zuba tagumi tana nazari, da sauri ta dafa Mami ta ce. "Na samo mafita, kin san me za a yi Mami?" Mami ta girgiza kai da sauri. "Sata kawai za mu laƙa mata, ba kin ce Daddy ya ba ki ajiyar wasu kuɗi masu yawa ba? To da su za mu yi amfani." Shukra ta yi ƙasa da murya tana tsara wa Mami yadda za su yi, lokaci ɗaya suka saki dariyar samun mafita. Suna gama tattaunawa Mami ta ɗebo damin kuɗin ta damƙa wa Shukra, Shukra ta ɓoye su a cikin jakarta kai tsaye ta nufi sashen Uwani ita da ƙawarta Fatima. Kuma ko Fatima ba ta san da plan ɗin su Mami ba. Tun da Uwani ta tare sau ɗaya Shukra ta taɓa shiga sai a wannan ranar ta yi na biyu. Shiru ta ji falon babu kowa, sallama ta rangaɗa daga cikin ɗaki ta ji Uwani ta amsa. Ita ma Uwani dawowarta kenan daga sashen Mami don tun da Dada ta zo kusan wuni guda a cen take yi, idan ta dawo ɓangarenta sai dai ko wani uzurin ne ya dawo da ita. Uwani na fitowa Shukra ta ɗan saki fuska tana murmushi ta ce, "Ki je Mami tana kiranki. Sannan kuma ƙawata Fatima za ta yi Sallar Walha, sashenmu hayaniya ta yi yawa shi ya sa na ce ta zo nan." Uwani sakato ta yi tana mamakin yau rana ɗaya da har Shukra ta sakar mata fuska, a sanyaye ta amsa mata sannan ta wuce kiran da aka ce Mami tana yi mata. Uwani na fita Shukra ta faɗa ɗakin Uwani bayan da Fatima ta fita yin alwala, ta janyo drowar madubin ta saka kuɗin a ciki ta mayar ta rufe. Ba su wani jima sosai ba suka fice daga ɗakin bayan Fatima ta idar da Sallah, a ɓangaren Shukra dama kuma buƙatar maje Hajji Sallah tun da buƙatarta ta biya ba ta ga amfanin zaman nasu ba. Uwani na zuwa ta samu Mami a falo ta tsugunna har ƙasa, a lokacin Mami zaune take da matan Baba Mustafa sai ƙawarta Hajiya Falmata. "Uwani ku je ke da Auta ki taimaka mata ku ciro mini wayata ta faɗa bayan gado." Babu musu Uwani ta yi wa Auta magana suka shiga ɗakin Mami, sun sha wahala sosai kafin su samu damar ɗauko wayar tun da can ƙarshen gado ta faɗa. Abu ɗaya ne ya tsaye wa Uwani a rai, a iya sanin ta tun ranar da ta zo gidan Mami ba ta taɓa saka ta aiki tare da Auta ba. Amma sai ta sa a ranta ko don ganin mutane ne ya sa Mami ta yi hakan, don kar a ce har yanzu ba ta ƙaunarta. Wurin sallar Azahar bayan Mami ta yi sallah ta fito falo ta fasa kukan an sace mata maƙudan kuɗin da Daddy ya ba ta ajiya har kimanin raina miliyan biyu da rabi, nan da nan hankulan mazauna gidan ya tashi. Dada na jin haka ta fara sababi rai a ɓace. "A gaskiya ni kam idan aka kwashe kuɗin nan an cuci Mamman, saboda Allah a tara mutane domin harkar arziƙi su ɓige da harkar tsiya? Shi dai ɓarawo bai ji daɗin halinsa ba, ba don sai Hajji zan je Saudiyya ba da babu abin da zai hana na kai ƙarar ɓarawon nan wurin Ubangiji a ɗakin Allah ba." Haka dai kowa da abin da ya dinga faɗa, daga ƙarshe aka ce su waye suka shiga ɗakin Mami a ranar su za a bincika, nan take aka bada shedar Uwani ce da Auta suka ɗauko waya. Kiransu aka yi aka tambaye su kowacce ta ce ba ta ga kuɗi ba, Mami ta bada shawarar a duba ɗakunan kowaccensu, haka aka kasu gida biyu wasu suka yi ɗakin Auta wasu suka wuce ɗakin Uwani. Falonta aka fara dubawa har da ƙasan kujeru, sannan suka wuce ɗakinta, masu duba drower saka kaya na yi, wasu kuma har da leƙa ƙarƙashin gado suke. Kwatsam ana duba drower madubi sai ga kuɗi, nan take mutane suka ɗauki salati. Aka wuce wurin Mami da kuɗi, saboda tashin hankali Uwani jikinta har karkarwa yake yi. Duk yadda Uwani ta so fitar da kanta abin sai ya gagara, ta yi kuka ta yi rantse-rantse babu wanda ya yarda da ita. Hatta Dada a wannan karon ba ta yarda da ita ba, Uwani ta rarrafa gaban Dada tana kuka cikin takaici Dada ta wanke ta da mari sannan ta hankaɗa ta gefe. Daddy ne kaɗai da ya zo ya lallashi ta, a ransa yana wasu-wasin wannan abin da ya faru. Lokacin da Jafar ya dawo ya ji labari ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, nan take kuma Mami ta birkice a kan sai Jafar ya saki Uwani a cewarta ba za ta zauna a ɓata mata tarbiyyar yara ba. Shi kuma Daddy ya sake jaddada wa Jafar umarninsa na ko bayan ransa bai amince ya rabu da Uwani ba. Abin duniya goma da ashirin ne ya haɗe wa Uwani don haka ta koma sashenta, ta faɗa kan gado ban da rusar kuka babu abin da take yi. Lokacin da Jafar ya shiga ya same ta kallon tsana ya wurga mata sannan ya ce. "Wallahi ni dai an gama cutata, a ce wai matata ta rasa wa za ta yi wa sata sai mahaifina, me aka rage ki da shi ci ko sha? Ƙanƙanuwar yarinya da ke ko a ina kika san kuɗi da har za ki sa hannu ki kwashe miliyan biyu da rabi. Ni kam na yi dana-sanin aurenki, ni dai aurenki wallahi bai amfane ni da komai ba sai tsiya. Ya zame mini dole na yi gaggauwar auren Safna, don ba zan zauna ɓacin rai da takaicinki ya kashe ni ba. Shashasha ɓarauniyar banza da wofi." Jafar ya yi tsaki ya fice daga ɗakin. Uwani ta ci kuka kamar babu gobe, tana nan ɗaki Auta ta je ta same ta. "Uwani Allah Ya sani har yanzu ba na jin ke kika ɗauki kuɗin nan, tare fa muka yi komai muka gama." Rai a ɓace Uwani ta ce. "Auta fice mini a ɗaki kada na sauke fushina a kanki." "Don Allah ki saurare ni kada ki yi mana jama'u..." Cikin tsawa Uwani ta katse ta. "Ki fice mini a ɗaki na ce." Auta ta tsorata sosai da yadda ta ga Uwani ta birkice lokaci ɗaya, bayan fitar Auta Uwani ta fara nazarin shigowar Shukra da kiran da Mami ta yi mata. Murmushi ta saki ta share hawayenta a fili ta furta. "Wallahi wannan ƙwallar da na zubar ba za ta tafi a banza ba. Ni Uwani za ku laƙa wa sharri, ai ko kura ta rame ta fi ƙarfin gawurtattun karnuka." Daga haka Uwani ta shiga banɗaki ta wanke fuskarta, ta koma can sashen su Mami. Yadda mutane ke bin ta da kallo ita ma Uwani sai ta murje idonta ta fara bin su da kallo, hatta Dada fushi take yi da ita don haka ita ma ta yi kamar ba ta san da Dada a wurin ba. Duk in da Uwani ta gifta sai dai ka ji ƙus-ƙus na tashi. Auta ta nema ta ba ta haƙurin abin da ta yi mata, ita ma dama Auta ba ta ga laifin Uwanin ba don idan ita ce ma za ta yi fiye da haka. A cikin dabara Uwani ta tambayi Auta Event ɗin da za a yi kamu, Auta ta nuna mata ai sai su tafi tare tun da ba ta san wurin ba. Yamma liƙi jama'ar gidan ana ta hada-hadar tafiya wurin kamu, Uwani ma atamfarta ta saka da mayafi sai dai tun rana Auta ta hana ta yin wannan ɗige-ɗigen kwalliyar. Ita ta biya musu kuɗin make up aka yi muku kwalliya sai ga Uwani ta fito shar kamar ba ita, lokacin da Uwani ta saka ƙafa a cikin hall ɗin ne ta saki murmushin ƙeta da mugunta. Ta zura hannu cikin aljihun doguwar rigarta ta ji fakitin sabuwar rezar da ta saya tana ciki a fili ta furta. "Uwani ce fa 'yar ƙashin gwiwa, ai yanzu za mu fara wasan da ku tun da haka kuka zaɓa." AlhamduLillah a nan free pages na wannan labarin ya ƙare🫠 idan kina buƙatar ci gaba za ki turo 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 First bank sai shaidar biya ta wannan lamber 07062062624 Sai mun haɗe a shafin gobe idan Allah Ya kai mu domin mu ji tsiyar da Uwani za ta shuka, Fakitin Reza a cikin Hall ɗin kamu na san akwai ƙura.😂 #Ummou Aslam Bint Adam🌚