SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI 07030137870 *NA HUCE!* "SHIMFIDA ZAMFARA STATE, NAJERIYA" "Yamma lis, a wata ranar Lahadi, wadda tayi daidai da shida ga watan Yuli, ta shekarar alif dari tara da casa'in da tara da misalin karfe biyar na yamma, majalisarsamarin unguwar Kofar Jange ta hadu, ta cika ta batse cikin birnin ZAMFARAN Najeriya. Opposite wannan majalisa ta samari wani gida ne da za'a iya kira ginin masu kudin da, koko a ce 'yan bokon da, wanda aka yi wa renovation daidai da zamani, gida ne mai asali da tsohon tarihi a unguwar ta (Kofar Jange) da yayi fice sakamakon kasancewar mamallakin sa tsohon dan boko kuma dan siyasa da aka dama dashi a gwamnatin Zamfara tun daga state har federal." "Ita wannan unguwa KOFAR JANGE unguwa ce mai tsohon tarihi wadda ta samar da jiga-jigan 'yan boko da masu fada aji a jihar Zamfara. A dalilin maigidan tsohon dan siyasa ne wanda ya kare rayuwar sa cikin hidimar al'umma. Wadanda suka gudanar da siyasar su ta gaskiya da rikon amana tun duniya na kwance, lokacin mulkin Janar Abdulsalami Abubakar. Duk wani Bazamfare ya kwana ya tashi da sanin tarihin gidan Alhaji Mustapha Bilyamin Nahuche." """GIDAN NAHUCHE!""" Shine lakabin da ake kiran wannan gida a garin Zamfara. A saman gidan ma an rubuta hakan cikin rubutu na ruwan gwal. Gida ne mara tarin iyali domin matar aure daya ce tal tayi rayuwa a cikin sa ba tare da kishiya ba; su biyu ne kadai 'ya'yan gidan a wajen marigayi mahaifin su Hon. Mustapha Bilyamin da mahaifiyar su Hajiya Kaltume (Hajiyar Nahuche). "Wannan zama da samarin nan suka yi ba na komai bane na jiran isowar sa ne, shi kadai ran sa dan Nahuche jikan Nahuche. da suke matukar kauna, ya kuma zame musu role-model wato mutum abun koyi a halayya da dabi'a, da" "kuma yadda yake gudanar da kafatanin tsarin rayuwar sa, bi ma'ana, shi mutum ne da suka yiwa kyakkyawar shaida ta saukin kai da girmama matasa; ga sukuni Allah ya bashi, ga tarin kuruciya da zuzzurfan ilmi amma babu ashararanci ko kankani a tare da shi. Bai gaji mahaifin sa ba ta fuskar siyasa, amma ya gaje shi ta fuskar ilmin boko, shi kawai dan boko ne mai ci da gumin, biron sa." "Tun safe suke zaune, har zuwa yanzu da rana ta tasamma faduwa, suna da labarin ya shigo Zamfara a safiyar yau yana gidan sa na GRA, kuma duk ranar da ya shigo matasa da masu neman aiki na unguwar su sun warke, shi ba dan siyasa bane (business tycoon) ne mai kishin matasan yankin sa, sannan mai connections a birnin Tarayyah, suna da tabbacin dole zai zo ya gaida mahaifiyar sa Hajiya Kaltume komai dare, ba zai kwana cikin Zamfara ba, ba tare da ya zo ya ganta da tilon Dan sa ba." "Karfe nawa zai zo ne basu sani ba, in kuma zasu kwana dakon zuwan sa bazasu gaji ba, dalilin zaman su kenan a majalisar kofar gidan Hajiya Kaltume Nahuche." "Hira suke irin ta samari masu jini a jika masu burin da babu ranar cika shi; duka burin su dai shine su zama kamar sa a komai; a ilmi, a dabi'a, a halayya, a kasuwanci, a taimakon al'umma, a irin motocin da yake hawa, a irin simplelife- style din sa, a farin jini.....a kyawun sura a komai da komai. A cewar su dai, yana daga cikin masu sa'a a rayuwa in ka dauke gwaurantakar sa da bata dada shi da kasa ba." "Abin kamar hadin baki rediyon hannun daya daga cikin su ta soma kwararo muryar sashen Hausa na BBC (British Broadcasting Corporation) cikin shirin su mai taken: ""DOMIN MATASA. """ "Mai gabatarwa yayi sallama sannan ya ambaci sunan bakon mako, wanda ya sanya samarin baki daya sakin ihu cikin hargagi irin na samari harda masu mikewa suna daga juna. Shiri ne da sukeyi duk karshen sati wato ranar Lahadi domin tattaunawa da talentedbusiness tycoons masu jini a jika irin ""HABIBU NAHUCHE "". Domin karfafawa" matasa wajen neman na kai da neman ilmi. "Mai gabatarwa, AbdulHadi Taheer, wakilin BBC a jihar Zamfara, ya ce ""Assalamu alaykum masu sauraren muryar Hausa ta BBC, a yau muna tafe ne tare da ""NAHUCHE"", in nace Nahuche ina nufin HABIB, MUSTAPHA BILYAMIN NAHUCHE The propriator of NAHUCHE HOTELS & NAHUCHE GROUP OF HOTELS. Barka" "da zuwa wannan fili Engnr. Nahuche, matasan Zamfara na son sanin takaitaccen tarihin ka?""." "Zuzzurfar muryar sa kasaitacciya ta mazan da suka hantse cikin ilmin addini dana zamani ta kwararo sallama da Bazamfariyar accent din sa, wadda banbancin ta da sakkwatanci kadan ne....." """Assalamu alaykum, sunana Habibu Mustapha Nahuche, ni Bazamfare ne gaba da baya, nayi karatun firamare da sakandire duka a kauyen Nahuche kafin mahaifi na ya dawo birni a dalilin neman ilmi da neman abinci. Bayan kammala karatuna na sakandire na samu scholarship daga (Petroleum Technology Development Fund) da aka fi sani da PTDF zuwa kasar Germany, na karanci 'Hotels Administration' daga jami'ar Cologne, Germany. Nayi digiri na biyu duk a Cologne akan fanni guda. Na dawo gida a shekara ta 2000 na fara aiki da babban hotel din Najeriya na wancan lokacin (Nicon Noga) inda na rike manyan mukamai acan, daga baya na fara ginin hotel dina na farko a garin mu wato Zamfara, daga nan ne abubuwa suka mike har aka samar da NAHUCHE GROUP OF HOTELS a manyan jihohi na wannan kasa tamu mai albarka. Na taba aure, inada yaro""." "Abdulhadi Tahier yayi murmushi yace ""masu sauraro zasu so su samu karin haske akan kalmar ""na taba aure"" domin kalma ce mai harshen damo, har yanzu da auren ko babu?""" "Wani kasaitaccen murmushi ya saki, wani abu ya soki zuciyar sa, a lokacin da bafullatanar fuskarta ta gilma masa kamar walkiya, ""ta yaya zai mantata da lokutan kwanaki bakwai?"" A hankali kuma cikin karayar murya na tasowar wani tsohon miki yace." """Duk yadda anka fassara ta, daidai ne!""." "Abdulhadi Tahier bai ja tambayar da nisa ba don ya fahimci ya gama amsa ta. Sai ya dauko maqasudin tattaunawar, wanda shine abinda suke so matasa su amfana da shi." """Ko menene sirrin da ke karkashin nasarori da habakar 'Nahuche Hotels' akan sauran gidajen saukar baki da muke dasu a kasar Najeriya?""" "Bai bata lokaci ba ya amsa. ""Excellent Service Delivery!""" """Shin ina ne NAHUCHE? Domin banda Zamfarawa, ba kowa ya san garin 'Nahuche' da ake kiran ka da ita ba, wadda har ta boye asalin sunanka na yanka? A yanzun ana maganar kasarmu Najeriya ne in general da babu babban birnin da baka da Hotel, kana da masu kallon ka as a role-model suke kuma son jin wasu daga boyayyun sirrikan rayuwar ka""." """Nahuche karamin kauye ne a karamar hukumar Bungudu. Ainahin garin Nahuche gari ne dadadde, garin ne da mutanen garin hausawa ne. Mutanen garin bakake ne sid." "A wata shekara garin ya hadu da musibar hare-hare daga wasu garuruwan. An addabi garin da yaqi har suka rasa yadda za suyi. Ana cikin wannan halin ha 鈥檜 lin, sai wani shahararren mayaqi Ya zo daga Katsina, cikin kabilar Rumawa. Rumawa kuma ka san fulani ne kyawawan gaske." "Wannan shahararren mayakin tafiya ta biyo da shi ta cikin garin Nahuche, sai Kekun Nahuche (sunan ainihin sarautar Nahuche kenan) Ya roki wannan mayakin da ya taimaka masu kan hare-haren da su ke fama da su. Har yayyi mashi alkawarin idan har yacci wannan yaqin to zai bashshi rabin kassar shi da kuma sarautar Uban Dawakin Nahuche." "Aka yi yaqi, kuma aka samu cin nasara, shi kuma Kekun Nahuche bai manta da alkawarin da ya dauka ba, ya ba wannan mutumin sarautar Uban Dawaki (saboda ko da yazo a kan Doki yazo) ya kuma bashi rabin kasar shi Nahuche, shi kuma ya koma Katsina ya zo da iyalin shi suka ci gaba da zaman lafiya da mutanen garin, da Keku da Uban Dawaki sune ainahin sarautun da ke Nahuche kuma kowanne na mulki individually." "Har yanzu akwai rabe-rabe akan sunan wannan Bakatsinen amma mafi yawanci sun ce sunan shi Juli (sunan fulani ne). Juli ya sa 鈥榶 a 'yan shi sun yi makaranta, ciki har da kakanninmu, my grandfather (Bilyamin Nahuche) yana daga cikin dattijan wannan gari""." """Madallah da wannan kyakkyawan bayani na tarihi akan garin Nahuche, a karshe wane sako gare ka ga matasa masu burin zama manyan (business figures) irin ka a Najeriya?" Wannan karon da murmushi ya amsa. """Su duba organizational theory of business, kafin kafa kowanne irin kasuwanci. Gaskiya, rangwame da rikon amana shine sirrin nasarar kasuwanci, kada a raina riba komai kankantarta. A zama kullum cikin tunanin sababbin hanyoyin habaka kasuwanci a zamanance (technological innovation). Abu na karshe shine mai cin muguwar riba, baya taba nasara a kasuwanci kuma dukiyar sa bata albarka""." "Samarin nan banda ihu ba abinda suke yi lokacin da shirin ya kare, muryar shi kadai tsuma samarin Zamfara take yi, kaunar da suke mishi ba 'yar kadan bace. Da a ce shi mai bin ra'ayin wasu ne ba ra'ayin rikau ba, da ya dade da shiga siyasa ""........Allah ya taimaki Nahuche.......Allah ka bar mana Nahuche......."" kawai suke ambato cikin hargowa. Daidai lokacin da motar baka wuluk kirar PORSCHE ta sulmiyo ta shigo layin kamar yadda suka yi tsammani. Suke kuma dakon jira." "Dan sardidin matashi da shi. Habibu Nahuche. Yau ma kamar kullum ya fito yana takun nan nasa majestically, cikin farin danyen Voyel mara nauyi dan shafal, dinkin jikin sa (very simple) wanda aka yi shi dan siriri da farin zare, sai da ya baiwa kowannen su hannu daya bayan daya babu gazawa cikin far'a da sakin fuska, sannan ya kawo ihsanin da" "ya saba yi musu a dunkule yayi musu, addu'a iri-iri Habibu ya sha ta, bai tsaya sosai ba ya wuce kai tsaye zuwa cikin gidan iyayen sa." "Mahaifin Habibu Alhaji Mustapha Bilyamin Nahuche tsohon dan siyasa ne wanda ya rike manyan mukaman siyasa a jihar Zamfara a lokacin rayuwar sa, yayi dan majalisar dattijai mai wakiltar Zamfara ta kudu, yayi sanatan Zamfara ta kudu, yayi shugaban karamar hukumar su wato Bungudu wadda garin Nahuche ke karkashin ta. Ya rasu ya bar matar aure daya da 'ya'ya biyu mace da namiji." "Itace aunty Badiyya Nahuche, wadda ke aure a garin Kaduna, tanada yara hudu, sannan shi Habib, dake binta, daga kansu Allah bai kara baiwa Haj Kaltume haihuwa ba." "Da sallama ya shiga falon Hajiyarsa, tana kishingide akan tumtum, ta kunna rediyo tana sauraron hirar da ake yi da shi. Shigowar sa tayi daidai da karewar shirin. Ta kashe rediyon tana mai shimfida masa karamin center carpet, bakin ta dauke da murmushi, fadi take." """Habibu bazaka bari ka kwanta ka huta zuwa gobe sannan ka shigo ba? Ka taho tun daga Lagos? Ka san dai tunda samarin nan suka ganka ba bari zasu yi ka huta ba""." "Murmushi yayi yana zama akan shimfidar data yi masa, idanun sa cike da kewar ta, da ganin su zaka san akwai shaquwa da kauna ta musamman bayan ta iyaye da Allah ya riga ya assasa, cikin nutsuwa irin tasa ya sunkuya ya gaisheta, sannan yace ""bana taba gajiya dasu Hajiyar mu. They are part of me (su rabin jiki na ne), nima shekarun baya ai kamar su din nake; matashi mai buri. Ina Abdallah?""" "Hajiya Kaltume ta nisa, sannan ta ce ""Badiyya ta tafi dashi Kaduna hutu, amma gobe insha Allah nace a kawo shi don ku gaisa, kafin ka tafi Makurdi din da ka ce zaka wuce daga nan." "Anya Habibu ina amfanin a dinga yamadidi da kai a kafafen yada labarai ana fadin baka da aure sai kace wani dan siyasa? Shin ita ta kara tuna ka a duka wadannan shekarun nan ko bata san inda kake ba da dan ta? In tana da niyyar cigaba da rayuwa da kai ai da tuni ta nemeka. Tunda na tabbata ta san inda ka ke. Kai ne baka san inda take ba. Kai din a yanzu kuma fitacce ne kuma sananne a kasar Najeriya, bai yuwuwa ace bata san da wanzuwar ka ba koda a kafafen yada labarai ne. Idan har tana da muradin sake rayuwa da kai." "Mata na duniya babu irin wadanda iyayen su basa kawo min, babu 'yar wanda bazaka aura ba Habibu, ka hakura da yarinyar nan ka hakura da ita bisa umarni na!""." Hajiya Kaltume bata ankara da cewa hawaye ne ke zuba daga idon sa ba. sai da ta kai karshen maganar ta. A fili ta furta """Yaa Salamu sallim!""" Domin al'amarin Habib da uwar dan sa yafi karfin tunanin ta. "A duk lokacin da ta takura masa da zancen aure karshenta kenan, yayi mata hawaye. Don bai da abin cewa. Shin wacece wannan uwar Abdallah haka? Kuma me ta taka da har ta mallake zuciyar namijin duniya irin dan ta Habibu Nahuche???" **** "ABUJA, NAJERIYA" (Cikin Gidajen Likitoci na National Hospital 9:30 am). "Ta kashe rediyon a hankali, zuciyar ta na wani irinragaita, tana daga cikin wadanda suka fara aikawa BBC sakon appreciation din su ga wannan shiri na musamman. Abubuwa masu yawa da suka gabata a birnin Cologne din Jamani shekaru GOMA a baya na gilma mata. Wannan ita ce kaddarar su, da har gobe ba wanda ya san ta. Kuma kaddarar data hana ta AURE shekaru goma bayan rabuwar su. Kaddarar data maida rayuwar ta duhu didim; farin ciki bai kara gudana a cikin ta ba; ""Kaddarar auren kwana bakwai""." "Ta dauki hoton karamin kyakkyawan yaron mai kama da ubansa a komai tana kallo, hawaye na sauka akan fararen sumul-sumul din kundukukinta. Ta san yanzu ya girma, watakila aji hudu na firamare. Cikin kowanne hali dai ta san" "zai kula da shi. Damuwar ta ba akan kulawar da zai samu bane domin hakika Habib Nahuche zai kula da dan sa har fiye da yadda yake kula da Hotels din sa. Damuwar ta akan yadda har gobe ta kasa kallon kowanne namiji da idanun sigar aure, kowa ya zo sai ta ga bai kai shi ba, ko farcen kafar sa bai kama ba, koda kuwa ya fi shi komai na rayuwa. Duk da cewa ta san shi ne kawai a matsayin dalibin jami'ar Cologne ba'a matsayin sa na yanzun ba (mamallakin Nahuche Hotels) amma tana bibiye da duk wani fadi-tashin sa na rayuwa daga ranar da ya yi kidnapping Dan su. Dalilin bibiyar ne bata sani ba har yau, tunda ita tace bata son sa. Farin jini kam har bata san irin nata ba, manema ba irin wadanda Allah bai bata ba, kuma burin Dada shine tayi aure tun kafin Allah ya dau ranta, amma har gobe ta kasa kallon kan sauran maza da gashi sai dan mutanen Nahuche. The one that took away her pride na diya mace. Wanda ta tabbatar zuwa yanzu ya manta da ita, a irin shuhurar da Allah yayi masa cikin shekaru goma kacal da rabuwar su." Bata san hawaye take ba. Sai da ta ji dandanon gishiri a bakin ta. Hawayen da ta tabbatar bazata daina zubar dasu ba har zuwa karshen rayuwar ta. Idan har rayuwa bata koma yadda take a baya ba; with him by her side. """Auren Wucin Gadi"". ""Auren kwanaki bakwai kacal"". Wadanda abubuwan da suka wakana cikin su sun fi tsayin na shekaru bakwai. Wanda ya samar da kaddarar Dan da ke a tsakani, Dan da silar zuwan sa duniya ne yayi connecting komai, ya hada zukata ya kuma raba su cikin kwanaki bakwai. Jami'ar Cologne din Jamus ita ce tushe, mafari, ginshiki na dukkan walagigin rayuwar data samu kanta. Plus rashin cikakken gata da ya baibayeta a lokacin." "Shekaru goma a baya, suka soma tariyo kansu a idanun ta, tamkar a majigi." ***** NA HUCE IS NOT FOR FREE. IT'S N1000 VIA; 3094856450. SUMAYYAH KABARA FIRST BANK SHAIDAR BIYA 07030137870 SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI 07030137870 *NA HUCE!* (PAID BOOK) (FARKON LABARIN) SHEKARU GOMA A BAYA "Daga cikin bututun maganar cikin jirgin Boeing745 wanda ya tashi zuwa kasar Jamus a yau daga filin jirgin saman Murtala Mohammed dake Lagos, bututun sadar da sako na gaggawa ya karade kunnen fasinjoji, ""jirgi yana cikin hatsari, jirgin mu yana watangaririya, hazo ya lullube sararin samaniya gabadaya, direbobi sun rasa direction din su, a sabili da haka muke shawartar a sanya rigar hatsari, don komai na iya faruwa, sannan ta soma bayanin (how to escape a plane crash) cikin gaggawar magana." "Abinda ya gigita fasinjoji, ya firgita mata da yara, masu kuka na yi, masu salati na yi, bata san sanda ta kankame mutumin dake gefenta ba tana rusar kuka." """Ina da gyatuma, da Allah da ni kadai ta dogara, dama sai da tace min kada in taho karatun nan, don ba lallai mu sake ganawa ba, don Allah don annabi ka taimaka min kada in mutu, in koma wajen Daada""." "Za'a iya cewa shikadai ne bai razana a cikin jirgin ba, da ganin yarinyar ta gama tsurewa, kokari yake yasa mata rigar hadari amma ta bi ta cukuikuiye shi gabadaya." "Ta kankameshi kamar ta samu uwar ta. Duk da cikin tashin hankali suke sai da yaji wani iri a cikin jikin sa da ruhin sa. Da karfi ya yakice ta," """Hey! Relax, are you not a Moslem? Kiyi addu'a, ki cika ni insa miki rigar kubuta daga hadarin jirgi"". Ya soma ambaton ""innalillahi wainna ilaihi raji'oun "" a fili har itama ta kama eventually." "Cikin ikon Allah ba'a yi minti talatin ba kuma komai ya daidaita. Hazo ya yaye, jirgi ya daidaita akan hanyar shi, ba jimawa suka sauka a birnin Cologne, Germany." "Kunyar abinda ta aikata kuma ta zo ta lullubeta, ta kasa sake hada ido da shi, ta nemi hanya ta sulale abin ta, cikin nasihohin Daada kafin ta taho har da cewa kada ta yarda jikin ta ya rabi na kowanne namiji haramun ne in ba mijin auren ta ba, yau ba raba ba kadai ta kankame namijin da bata san daga inda yake ba, tana tafe tana waige-waigen neman abokan tafiyar ta." "Bafulatanar Adamawa ce kyakkyawar gaske, doguwa sambaleliya, siririya, shekarunta sha tara da haihuwa, tana cikin dalibai masu hazaka da gwamnatin jihar Adamawa ta zaba tayi sponsoring karatun su na likita zuwa kasar Jamus akan likitancin fidar kunne, hanci da wuya (ENT surgeon) wadanda sunyi karanci a Nijeriya, specialization din su shi ake kira (Otorhinolaryngology)." "Ta tashi ba tare da iyayen ta ba, sun mutu tun tana kankanuwa, a hannun kakarta Daada wadda ta haifi mahaifin ta ta tashi, don haka duk wani wayo irin na yaran da suka tashi gaban iyaye bata da shi, goyon kaka ce ziryan, mai tarin yarinta, wauta da shagwaba, amma a fannin karatu zaqaqura ce. Daada ita tasa ta a makaranta, hazakarta tun tana karama daban ce data sauran tsararrakin ta. Bata san kowa ba a danginta sai Dada, Dada ce kawar ta, uwar ta uban ta komai nata." "Hazaqarta ce ta sayo mata kauna a gun malamanta, bayan kammala sakandire wadda ta gwamnati ce, tafi kowa cin WAEC da NECO, B2 guda biyar rus, da A1 a biology, physics, chemistry da lissafi, wannan yasa hukumar makarantar ta bada sunanta a gurbin sukolaship na dalibai biyu masu hazaka 'ya'yan marasa karfi da gwamnatin jiha ta basu." "Komai za'a yi musu, sannan za'a dinga basu alawus na cin abinci, har su gama karatunsu a Jamus wanda zai dauke su tsawon shekaru biyar zuwa bakwai har specialization din da a ka tura su su yi. A karshen kowacce shekara zasu zo gida su yi hutu su koma." "Ba karamin dauki ba dadi aka yi da Daada ba, kafin ta barta tahowa Germany, sai da shugabar makarantar su ta zo har gida da kanta ta same ta, ta roketa ta kuma kwantar mata da hankali, ta gaya mata yara irin jikanyar ta ba'a wasa da talent din su, irin su ake nema don a farfado da harkar kiwon lafiya a Najeriya, sannan karatun da zata yi (Otorhinolaryngology) babu mai irin shi a fadin Najeriya a wancan lokacin, tayi wa jikanyarta addua ta bita da fatan alkhairi ta bar ta taje, ita kuma zata kula da rayuwar ta acan, akwai kanwarta dake aure a kasar." "Sannan ne Daada ta hakura, amma tace abu na halin rai da tsufa, ko a ina ta samu damar yin aure tayi, koda wanene, in dai musulmi ne, babba ko yaro, in dai zai rike maraicin ta, sabida bata da tabbacin zata dawo ta sameta a raye." "Don haka ne da jirgi ya kusa kifar dasu tafi kowa nadamar wannan tahowa, da ta yi hakuri ta yi zamanta bayan Daada, akan gadon bonon ta, da wannan ajali ya dauketa ne a bayan Daada cikin kwanciyar hankali. Don ta san mutum baya tsallake ajalin sa, saidai inda ajalin kowa yake ne daban." "Suna saukowa daga jirgi ta hau raba idanu, abokan tafiyar ta duk sun kama gaban su, taimakon da Allah yayi mata tana da adireshin jami'ar data zo da duk wasu muhimman takardunta a tare da ita." """RAHINA OMAR! RAHINAH OMAR!! RAHINAH OMAR!!!""" "Taji an kira sunan ta daga baya, da sauri ta juya don ganin mai kwala mata kira haka, nan da nan ta gane shi, shine agent wanda aka turo daga Embassy yayi musu jagora a komai har su gama registration dinsu. Kuma tana da hoton sa. Sannan principal tace shi zai kaita wajen kanwarta Dr. Laura wadda lakcara ce anan Cologne take aure. Gara ta zauna gidan ta madadin zaman (students hall of residence)." "Murmushi ya subuce mata, data hango abokan tafiyar ta tare da shi, suka rankaya cikin babbar mota suka wuce cikin gari." "Sunan ya cigaba da wata irin amsa-kuwwa a kwanyar sa, ba tare da sun ankara da shi ba, sabida a lokacin ya basu baya "".......Raheenah Omar "". Ya ji amsa-kuwwar wannan suna har cikin bargon sa. Kamar yadda har zuwa yanzu" "yake jin ta cukuikuiye a jikin sa. Surar ta bazata taba gushewa daga idanun sa ba, domin bai taba ganin kyakkyawar surar data manne a ruhin sa irin tata ba, sannan innocentlooks dake cikin fararen idanun ta wani sign ne daya makale a zuciyar sa." **** *FIRST ENCOUNTER (HADUWAR FARKO)* """The Cologne Public Library"" babban dakin karatu ne na jami'ar Cologne wanda yake lamushe dubunnan dalibai komai yawan su, yawanci daliban anan suke assignments din su, kuma idan kazo a matsayin sabon dalibi dole ne kayi register da Labirare, a matsayin ta na sabuwar daliba mai yin registration yau ta shigo labirare tunda wuri, bata kai ga tarewa gidan kanwar principal ba ta zauna tare da abokan tafiyarta a (hall of residence) har zuwa sanda zata kammala da registration." "Bayan ta kammala abinda ya kawo ta ta juya zata fita, accidently ta bugi mutum wanda ya juya baya yake jera littatafan Encyclopaedia Britannica a bookshelves na library din. Littafan hannunsa suka fadi kasa." "Da sauri ta sunkuya tana tsince masa, ta mika masa cikin cewa ""i'm sorry "" sorry din ta makale a makoshin ta" sakamakon ganin makwabcin ta na jirgi. Wanda ta sulalewa. "Ga dukkan alamu ma'aikacin library din ne. A very handsome figure din data zauna mata a rai sati biyu da suka wuce, ko na kwana daya bata fasa tuna shi ba." """You?""" "Ya fada yana nuna ta da dan yatsa. ""...... matsoraciya mai tsoron mutuwa"" ya sake fadi cikin harshen hausa. Murmushi ta yi tayi gaba tana fadin ""wa ke son ta? Da jirgin nan ya kifa da ni Dada na ma mutuwa zata yi"". Dariya yayi ya bi bayan ta har kofar labirare. ""Daga wane gari kika zo?"" Bata san meyasa ta samu kanta da kantara masa karya ba tace ""Benue"" kallon mamaki yayi mata don ko kusa bata yi kama da kabilu ba, face zallar fulani, bafullatana cikakkiya, ita kuwa ta fadi hakan ne sabida Dada ta ce mata never trust a stranger. Sai yayi tunanin watakila zama ne ko aiki ya kai su zaman Benue din." "Bai cika ta da tambaya ba, suka yi sallama ta wuce ya wuce, amma da ya koma dakin sa na accomodation din dalibai sai ya kasa zaune ya kasa tsaye. Ta yi masa karan -tsaye a zuciya a kan dalilin da bai sani ba. A kuma yadda ya lura bata da wayau, wayau na fahimtar abubuwa muhimmai irin wanda ya samu kansa akan ta, bai taba tunanin aure nan kusa ba, amma yau ji yayi in bai mallaki yarinyar nan ba bazai iya rayuwa ba. Ya manta da abinda ya kawo shi karatu ne kuma a yanzu ne ya fara masters din sa, ya samu part time job da labirare don ya taimaki kansa, kasancewar kudin da PTDF take basu ko kusa baya isar sa sabida tsadar student accomodation." "A yau da ya sake haduwa da Raheeenah, sai ya tuna cewa ashe shima namiji ne, ashe yana da bukatar mahadin rayuwa duka shekarun nan biyar da ya kwashe a Jamus, ashe bai taba haduwa da wadda zuciyar sa zata aminta bane, shiyasa bai taba son aure ba, sai akan Rahinah. Wadda ganin shi da ita bai fi a kirga ba. Gabadaya ya rikice ya birkice ya rasa inda zai sa kan sa. Aure kawai yake so yayi kuma ba da kowa ba sai Rahinah Omar." "Yana da Ubangida limamin masallacin musulmai na jami'ar Cologne wanda ke karatun doctorate, mutumin kasar Maghrib ne, shine ya samar masa aikin da yake yi a library yanzu, duk da albashin ba mai yawa bane amma bai nemi komai ya rasa ba, har ya bar cikin jami'a ya kama private gida karami a wajen makaranta." "Rigimar son aure data shige shi a yanzu harda kuruciya domin kuwa abinda bai sani ba infatuation ke damun sa akan Raheenah ba soyayya ba. Kyawun ta ne ya riba ce shi. He just wants to have her as a spouse at the age of 27 a lokacin da ya kamata ace karatun sa ne a gaban sa ba mace ba. Ga Hajiyar sa ta dade da samar masa mata a kauyen su, Nahuche. Wadda take matukar so, don 'yar kanin baban sa ne. Jira take ya kammala masters ya dawo ayi musu aure." "Amma haduwar sa da Raheenah ta rikita shi ta hargitsa shi, gabadaya ya rasa lissafin sa, bai taba tunanin yin zina a rayuwar shi ba duk da cewa ita tafi komai arha a Cologne, amma ji yake kamar zai iya raping Raheeenah in bata yarda ta aure shi ba, laifin da ya san zai iya kai shi ga hukuncin kisa a kasar turai, ji yake in bai yi aure da Rahinah ba a daidai wannan lokacin zai iya rasa ransa, al'amarin da ya kawo shi gaban ubangidansa at a smart pace (afujajan) yana neman mafita." "Dr. Sayyed ya dube shi sosai bayan ya gama jin damuwar sa, da yake malamin Psychology ne a take ya gama fahimtar halin da Habib yake ciki (infatuation/lust), yace masa ""ita yarinyar tana son ka, kuma ta amince zata aure ka? Annabi SAW yayi umarni da ayi wa samari aure a lokacin da suka bukaci hakan, in ba haka ba barna bazata gushe ba a doron kasa. Don haka in ta amince ni zan daura muku aure (ba tareda tunanin abinda zai biyo baya ba)""." "Cikin rauni Habib yace ""ni ko dosarta da zancen bazan iya ba, i'm sure ba abinda ya kawo ta kenan ba, she's very naive and innocent, ni kuma zan iya cutar da ita idan ta ki yarda ta aure ni, i just want to marry her or rape" "her in ba haka ba Dr mutuwa zan yi. Na yarda bayan dayan wannan in kare behind bars!""." "Dr. Sayed ya gama gane inda Habib ke fuskanta, infatuation ne mai tsanani ya kama shi ba soyayya ba, yace ""ba zaka mutu ba insha Allahu, kuma bazaka aikata zina ba har karshen rayuwar ka, sannan bazaka je kurkuku akan laifin fyade ba, kaje ka gwada sa'ar ka, in har ta amince ni kuma zan yi kasadar daura muku aure, ai karatu baya hana aure""." "Tun daga lokacin yake tunanin ta inda zai bullo mata, sun sha haduwa a wurare daban daban musamman labirare data ke yawan zuwa. Amma kwarjininta ya hana ya tunkare ta. Until that fateful day da ya ga an daukota ranga-" ranga a sume an yi asibitin jami'ar Cologne da ita a ambulance. "Abokan karatun ta sun tabbatar wa da likita cewa basu san me aka gaya mata a waya ba, ana cikin lecture ta ansa waya sai gani su kayi ta zuba kara ta zube a wurin a sume." "Ya makale a asibitin nan a kofar dakin da aka shiga da ita, ya ki matsawa ko nan da can, lokacin da likitoci suka yi nasarar dawo da numfashin ta shi suka ce ya zauna tare da ita kasancewar duk abokan karatun ta sun koma makaranta. Sun dauka shima coursemate din ta ne." "Tana bude ido da sunan DADA ta bude baki. tana kuka tana fulatanci, fulatancin da bai san me take fadi ba, a" karshe ya tsinci kalmar hausa. Dada ni da ke shike nan? Dada kema kin tafi kin bar ni ba uwa ba uba a kasar da "bani da kowa? Dada kin kyauta min kenan? Meyasa baki ce mutuwar ta dauke mu tare ba? Me yasa baki jira na zama Otorhinolaryngologist ba na saya miki gida mai kyau da mota?""" "Ta soma zabura tana fizge karin ruwan ta, da sauri ya rike ta ya kuma danna kararrawar kiran likitoci suka zo suka zurmuqa mata allurar barci." "Kwana uku cif Rahina na cikin wannan halin na tsananin firgita da dimuwar rasa Kakar ta. Ko na minti daya Habib bai bar asibitin nan ba, da nasiha da banbaki da janyo ayoyin Al'qurani masu tabbatar da kowanne mai rai mamaci ne ""kullu nafsin za'iqatul maut"" Habib ya samu ta soma dawowa hayyacin ta. A ranar data kwana biyar a gadon asibiti, cikin dare ta farka yana sallah, ta hada kai da gwiwa tayi kukan ta ta koshi, yana jin ta har ya gama nafilfilin sa ya juyo don ya kara bata baki." "Sai gani yayi ta mike, ta dauki mayafin ta ta yafa, tana shirin barin dakin. Yayi maza ya sha gaban ta ""Rahina ina zuwa? Likita bai sallame ki ba tukunna, ya ce sai gobe, kiyi hakuri ki kwanta ki kara nutsuwa zuwa gobe, ni da kaina zan maida ke gidan ku""." "Cikin kuka ta ce ""Najeriya zan koma na fasa karatun, passport dina zan je in dauko a gidan aunty Laura, dama sun tsane ni, a dole nake zaune a gidan, bazan iya rayuwa babu Daada ba, don Allah don Allah ka fadawa hukumar" "makaranta na koma gida""." "Wani matsanacin tausayin ta ne ya kama shi, yace ""Rahinah in kin bar karatun ki, kuma babu Dada, kin koma gida, menene madafarki a gaba? Gara ki karbi reality na cewa Dada ta rasu, ki tsaya ki gina future din ki, wanda ya riga ya" "mutu baya dawowa, kiyi hakuri zuwa gobe likita ya sallameki in raka ki gidan Antin ki, in kuma san gidan naku don yanzu ni Yayanki ne wanda bazai bari ki ragaita a rayuwa ba""." "Da haka ya samu ya kalallameta, da tausasan lafuza, har ta yarda ta koma gado ta zauna. Saidai yadda suka ga rana haka suka ga dare. Kowanne abinda yake sakawa a ransa daban ne. Ga Habibu, tunani yake wannan dama ce Allah ya bashi ta auren Rahinah cikin sauki, tunda bata da gatan da zai zame masa cikas, ba sai ya wahalar da kansa wajen neman soyayyar ta ba." "Raheenah kuwa tunanin ta irin zaman data fuskanta ana yi a gidan anty Laura ne; zama na kafirci da rashin tuna dokokin ubangiji, ta tsani zaman gidan don dai bata da yadda zata yi ne, sabida basu da kirki ko kadan, Anty Laura tana da wani Da Yasir fitinanne mai ruwan 'yan iska, wanda ta gama gane take-takensa na banza da wofi a kanta, don haka tunda ta yi sati a gidan ta fahimci zaman gidan bazai yiwu mata ba domin 'ya'yan anty Laura ko sallah basa yi. Yanzu tunanin ta shine taje ta kwashe kayanta ta dauki passport din ta ta koma makaranta da zama yadda ta fara tun farko. Tunda Habib ya ce komawar ta gida ba amfani." "Gari na wayewa likita ya sallame su, suka fito tare zuwa bakin titi, ya tare musu taxi suka hau zuwa gidan Dr. Laura wanda ba shi da nisa da makarantar su." "Cikin halin ko'in 'kula Dr. Laura ke tambayar ta inda ta tafi har kwana biyar, bayan an gaya mata kakarta ta rasu, shi kuma wannan saurayin ina ta samo shi?"" Kamala da kwarjinin Habib yasa ta kasa ci masa mutunci yadda tayi niyya, a take ya kara fahimtar cewa dan sauran gatan da yake tunanin tana dashi a kasar ma babu, wannan matar da gani ba jinin ta bace ba." "Nan yayi mata bayanin daga asibiti suke, ya gaya mata duk halin da Rahina ta kasance, ga mamakin sa sai ta kyabe baki, ""don tsohuwa ta mutu ne kike neman kashe kanki? Ai kawai yarinya ki zauna kiyi rayuwa mai 'yanci a Jamus ki tarawa kanki ilmi da dukiya, kin ganni nan tun da na bar Africa na huta da wahala, aure kuwa na yi ya kai goma, yarannan da kike gani duk uban su daban, bana daukar bakin cikin namiji, in kika samu kwalin Cologne kin gama tsallakewa, ki tsaya kiyi karatu ki nemi rayuwar 'yanci kawai""." "Rahina ta saki baki tana kallon ta, Shikuma Habib tsoron matar ne ya kama shi, ya tabbata barin ta da Rahinah hatsari ne babba, don haka ya yi gaggawar cewa shi yana son auren Rahina, a bashi auren ta." "Aunty Laura tace ""ai ba 'ya ta bace, ba kuma 'yar uwata bace, student din yayata ce kawai, don haka zan mata magana, in ta amince kuma kanada sana'ar da zaka rike ta ko gobe zan wakilta muji na ya daura muku aure""." "Abu kamar wasa karamar magana ta zama babba, domin principal cewa tayi Dada ta bar mata wasiyyar idan Rahina ta samu miji musulmi, wanda zai rike maraicin ta ayi mata aure shine babban kwanciyar hankalin ta a kabarin ta." "Dr. Laura tace ""ai gashi kam ta samu, har da tabon sallah a goshin sa karewa, kuma ga yadda na lura yana son ta sosai, zan gaya wa baban Nihal ya zama waliyyinta ranar jumaa a daura musu aure""." "Baban Nihal mijin Anty Laura da Dr. Sayed suka zaunar da Raheena suna nuna mata amfanin tayi aure shine martaba da kwanciyar hankalin ta, Rahina ta kasa musa musu sai kuka, daga Sayed ya dinga lallashin ta, daga bisani suka daura auren a masallacin Cologne bayan an idar da sallahr jumaah, akan sadakin da Dr. Sayed ya biya masa in Euros. Kudi tsababa masu yawa duk don ya taimaka ta amshi auren domin ta kafe kai da fata bayan daurin auren tace bata so, duk da convincing din ta da Dr. Sayed ya bata lokaci yayi, har mari ta sha a wajen anty Laura tace ""ubanki ya ce ki kwaso min shi? Ba tare na gan ku ba? To in baki son shi sai dai ki bar min gida na, ko ki auri Yasir ya sha cocaine dinsa ya lakadaki ba ruwa na""." "Ta debi kudin sadakin ta watsa mata, tace ""kije ki hada kayan ki da daddare zasu zo su tafi dake, Allah ya gani ni taimakon ki na yi, don nasan in bakiyi auren bama karshenta ki zama international prostitute." "A Jamus kike yarinya ba a Najeriya ba""." "Tana kuka tana komai Anty Laura dasu Nihal suka loda mata kayan ta a bayan taxi din da Habib ya zo a ciki, kamar dama zaman ta tare dasu ya takura musu don dai basu da yadda zasu yi da ita ne." "Tunda suka shigo motar take kuka, kuka tukuru tamkar zata fidda rayuwarta. Wannan wace irin rayuwa ce? Daga ganin mutum bata san komai a kan shi ba, don kawai musulmi ne kuma ya zo daga kasarta sai a aura mata? Kawai" don an ga bata da gata? Ita bata ce lallai sai ta zauna da Dr. Laura ba ta so ta koma hostel kawai tunda ko ta koma Najeriya babu Dada wajen wa zata je? "Tunda ta taso bata san kowa nata ba sai Dada, daga dangin uwa har na uba, ta rayu karkashin kulawar tsohuwa Dada a shekarun rayuwarta bakidaya. Yau ga rayuwar da rashin gatan Dada ya jefa ta a ciki; auren mutumin da bata sani ba, bata san asalin sa ba, bata san halayen sa ba, bata san manufar sa a kanta ba. Just haduwar kan hanya wadda bazata iya bada shaidar komai a kan sa ba, wannan taimako nasa ya zame mata masifa, duk yadda aka yi yana da target dinsa a kanta, amma in ba haka ba ta yaya daga ganin ta bai san asalin ta ba zai zabe ta ta zama matar auren sa?" "Ko da take goyon kaka, tana da hankalin ta. Bazata taba barin shi ya gurbata mata rayuwa ba." "Ta soma yi mishi kallon mutumin kirki tun daga haduwar su ta farko, amma ashe ba haka bane yana da mission dinsa da yake son cikawa a kanta." "Zata bashi mamaki, zata nuna mishi ka bar raina allura. karfe ce, komai kankantar ta." "Wannan take hakkin dan adam ne, a aure shi babu cikakkiyar yarda da amincewar sa." "Tana da damar da zata kai su ga hukuma daga su har anty Laura, amma bazata yi hakan ba, sabida ko yaya dukkan su sun taimaketa a Jamus. Kuma Dr. Sayed yayi iya kokarin sa wajen convincing din ta." "Amma ta gama kudurta mafita, mafitar da zata nemawa kanta ta kwatarwa kanta 'yanci....." """Bazata taba bari ya samu access din keta mata haddi ba, in ma kwadayin hakan ne yasa shi auren ta da gaggawa haka. Har sai ya gaji ya bata 'yancin ta na dalibtaka wanda shine abinda ya kawo ta Jamus ba auren sa ba""." ***** *Na Huce!* IS NOT FOR FREE. IT'S 1000 VIA ; 3094856450 SUMAYYAH KABARA FIRST BANK SHAIDAR BIYA 07030137870 : SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI 07030137870 *NA HUCE* (DAGA FUSHI NA. ) PAID BOOK "Kugin karshe da motar tayi, a kofar flat din Habibu ne, wanda ke shiyyar Klettenberg. Shi ya bude mata kofa da kan sa ya kuma rungumota barin jikin sa. Ji tayi kamar ya dala mata wuta, amma haka ta daure ta cije ta shiga gidan tana hawaye." "Dr. Sayed ya biyo bayansu har falon gidan, ya zauna yayi musu nasiha sosai, yace su taru su rufawa juna asiri su zauna lafiya, duk wata matsala da suke da ita su sameshi, shi uba ne a garesu, kuma Raheenah ta kwantar da hankalin ta Habib mai son ta ne, bai aureta da wata manufa ba sai bisa son cika sunnar Ma'aiki SAW." "Da wannan yayi musu doguwar addua'a sannan ya tafi, bayan Habib ya taka masa ya rufe gidan ya dawo." "A inda ya barta anan ya sameta, amma ta yaye lullubin fuskarta tana yi masa wani irin kallo, kallo irin na kamar ka ga makiyin ka, koko abunda zai cutar da kai. Da gaske zuciyar ta da dan kankanin tunanin ta basu bashi kowanne matsayi ba, face na mai mugun nufi a kanta." "Ya zauna dab da ita, har tana iya jin kamshin turarensa Carolina Herrera (Men). Da sauri ta matsa ta ja baya, sannan ta nuna shi da dan yatsa ta soma magana cikin hawaye." """Allah ya fi ka! Duk abinda kake nufi da ni Allah ya fi ka""." "Cikin madaukakin mamaki yake kallon ta, baki sake, ya ce ""Rahinah are you alright?""" """A'a a haukace nake, kawai daga ganin mace akan hanya baka san ko wcece ba sai kasa power ka aureta? Sabida ka fahimci bani da gata ko? Shiyasa ban cancanci ka nemi soyayyata ba, ka nemi dangi na ka aure ni cikin mutunci, ka taimaka min inyi abinda ya kawo ni sai kawai kayi min kutse a rayuwa ka raba ni da burika na?" "Ni na ce maka na zo Jamus don in yi aure ne?""" "Habib yayi mata wani irin kallo, domin ji yayi ya muzanta a gaban ta, yarinya tamkar mai gani har hanji! Da gaske yasa kaimi ya aureta ne don biyan bukatar ruhin sa da gangar jikin sa, bai taba fadawa a wani abu wai soyayya ba, kallon ta yake da jin ta as waste of time, burin sa da lokutansa na tunanin maida kobo ya koma dari ne, yana da manyan burika da suka zarce soyayya. In fact, bai dauki mace a bakin komai ba banda abar hutawar gangar jikin mijin auren ta." "Amma ita wannan inda bata bullo masa ta haka ba, da bata nuna ta san ba son ta yake ba, bayan target dinsa na auren ta yanada burin tallafar rayuwar ta da maraicin ta, tare da cigaba da zama da ita har karshen rayuwar sa." "Amma tunda ta nan ta bullo, ya san ta yadda zai yi maganin ta." "Daga sanda ya mike ya durfafe ta, da sanda ta soma ja da baya cikin tsoro, cikin abinda bai gaza sakan bane idanuwan su suka hadu, ta hango wani boyayyen al'amari cikin brown kwayan idanun sa, al'amarin da har gobe ta kasa mantawa, shekaru bakwai kenan; Babu soyayya a cikin a cikin kwayar idon Habibu ko kankani face lustfuldesire wanda ya kara darsa mata tsanar sa. Ta kuma kara yarda da cewa manufarsa kenan ta auren ta." "Da farko yayi kokarin lallashin ta, amma sai ya gane zai bata lokacin sa ne kawai, ga rashin kunya da tsiwa kala-kala na fita nau'i-nau'i daga bakin ta, sai ya ce." """Raheenah bari in yi maganin ki. ""." "Duk wani kokari na kwatar kai da neman ceto Raheenah Omar ta yi, kafin ta gane all her effort was futile (kokarin ta na banza ne), tamkar Habib Nahuche ya jima yana jiran wannan ranar, ya gama shirya mata. Abubuwanda suka wakana a tsayin daren bakidayan sa ba masu dadin fada bane. Saboda al'amarin baida maraba da 'rape' banda igiyar aure data suturta shi." "Kuma wannan ne abinda ya gina matsanancin tsoro da kiyayyar sa a zuciyar ta. She hates him with passion from their first night. Ta alkawartawa ranta koda jan ciki sai ta bar Jamus, gara ta dawo Adamawa ko bara ce ta yi ta ci da kanta, da dai ta zauna da wannan mugun mutumin mai halin dabbobi." "Tamkar ya san tunanin ta, washegari da zai fita makaranta saida ya kulle ta ta waje." ***** "Ba shi ya dawo ba sai yamma lis, tunda ya san ya bar mata komai da zata bukata. Amma ga mamakin sa a inda ya fita ya barta anan ya dawo ya sameta, a kwance akan marbles kamar kayan wanki, baya tunanin ko sallah ta tashi ta yi, balle akai ga wanka." """And your name is bride?"" Ya tambayeta cikin zolaya." "Hararar data ke masa tamkar idanunta zasu fado, wadanda suka kada suka yi jajazur kamar an gumbuda musu barkono. Da za'a bata dama zata iya kashe shi ta hanyar rataya, sabida tsanar data yi masa." "Ya tsugunna a gabanta ya ajiye mata ledar abincin McDonalds da lemun power horse mai sanyi, yana wani makalallen murmushi na tura haushi yace ""ki ci ki sha, ko kya wartsake kinji amarya ta! We're going for the second phase., what is the marriage meant for? I don't believe in what is called love. Ban sani ba ko in kika haifa min" "'ya'ya..... """"ta Allah ba taka ba..kada Allah ya nuna min wannan ranar""""ko?"" Ya tambaya yana kara hade filin dake tsakanin su kuma wannan karon ma kokarin ta da bijirewar ta, bai kwace ta da komai ba." """You goddam lunatic! I hate you kuma insha Allahu sai Allah ya saka mini, ta hanyar da baka taba zato ba. Abinda" "kayimin sai an wa 'yar ka, in baka haifa ba kanwar ka, in baka da ita UWARKA!""" "Bai san sanda ya daga hannu ya zabga mata mari ba, marin da Raheenah ta tabbatar taga wuta a cikin sa. Kafin ya kama hannun ya rike cikin nadama! Wai shine da dukan mace macen ma mai amsa sunan matar sa. Amma abu na" "karshe da bazai iya dauka ba shine raini, don abinda take gani a matsayin babban laifi daga gare shi shi ko kusa bai kalle shi hakan ba. A tunanin sa ana aure ne for sex only, kamar yadda ake cin abinci kullum. Baya jin a duniya zai so wata mace bayan mahaifiyar sa. Kuma baya comparing din ta da sauran mata. Talkless of Rahinah ta ambace ta ta zaga." """Duk rainin ki ya tsaya a tsakanin ni da ke, kada ki sake ki hada da uwata""." "Ya fada yana sake rugumota jikin sa ba tareda tausayi ba ya sake maimaita laifinsa, har da cewa ""ai sadaki na biya, ki jawomin ayar da tayi umarni da soyayya, aure Ubangiji yayi umarni mu yi ba soyayya ba""." "This man is unbelievable ga tunanin Raheenah bata san a rukunin mutanen da zata sanya shi ba, gashi dan boko mai matakin master, amma jakancin sa akan diya mace ko gardin kauye bazai yi ba. She hates him again and again for his wickedness." Tunanin ta gabadaya ya koma kan how to escape from this abusive marriage. "Amma har kwanaki suka nausa zuwa biyar, bata samu wannan damar ba." "Yayin da Habib ya dukufa ga morar sadakin sa, don bai taba tunanin abinda yake yi din ba daidai bane, ko zata iya tafiya ta barshi tunda bata da kowa." "(Akwai maza da yawa irin Habibu Nahuche, wadanda baza'a ce rashin ilmi ya hana su son matan su ba, ko kasancewa masu nuna soyayya da tarairaya koda fake ce. Suna aure ne for their own pleasure. Ita mace kuwa 'yar son lallashi ce da soyayya kuma har abada in baka iya tafiyar da ita ba, hankalin ta bazai taba nutsuwa da kai ba. Ita Rahinatu ma kallon Habibu take as rapist don bata yarda miji zai iya yiwa matar sa izayar da yake yi mata ba)." "A duka kwanakin nan bata ci bata sha, sai taji hanjin cikin ta na neman tsinkewa ne take shan ruwan bunu ko ta sha madarar kwali, wanka kuwa da sabulu rabon ta dashi har ta manta, iyakaci ta yi wankan sallah, watakila in yaji tana tsami, a yadda yake dan gayun nan mai son wanka da kamshi zai daina rabar ta." "Amma gogan nata ko a jikin sa, wani sabon abu ma ya tsiro da shi; fesa mata turaren sa 'Carolina Herrera' a duk sanda zai kusance ta, tana kuka tana tsine masa, amman kaman tana kara zuga shi." "Tsahon kwanaki shida ya tabbatar shi kansa ya samu lafiya daga masifar dake damun shi akan Raheenah, zamu iya cewa kanwa ce ta kar tsami kwannafi ya kwanta. Ya soma jin tausayin ta, kuma ya rage takura mata." ***** *RANAR KWANA BAKWAI* "Ranar da auren su ya cika kwana bakwai ne komai ya faru, haduwar da rabuwar masu kama da blink of an eye (kiftawar ido). Gabadaya haduwar sa da saninsa da Raheenah Omar, zuwa auren su da zaman auren watanni uku ne cif har kwanaki bakwai na aure data yi a gidan sa." "A safiyar ranar tun asubah ta faki idon sa ta dauke masa mukullai, neman duniya yayi musu bai gan su ba, kuma baya so ta gane abinda yake nema kenan, don haka yaja bakin sa yayi shiru, kada ta gane bai rufeta ba tayi tunanin guduwa, shi kuma daga ranar ya fara nadama, ya kuma alkawartawa ransa bazai kara kusantar ta ba sai bisa amincewar ta." "Sannan zai yi kokari ya koma yadda duk take son sa, wato namiji dan soyayya, mara gaggawa, loving, caring, romantic. Mai bin komai a sannu. Sex will be his last priority a rayuwar auren su. In ta kama zai je makaranta ya shiga aji ya zauna a koya masa yadda zai koyi zama da mata ne zai yi hakan, sakamakon wani irin pleasant feeling (so na hakika) tamkar maganadisu mai jan zuciya da ruhi da ya ji yana shigarsa a hankali akan RAHINAH OMAR daga daren jiya zuwa wayewar garin yau." Wayewar garin data cika kwanaki bakwai da auren su. "Bata taba yarda sun kwana gado daya ba, in suka gama damben su yayi galaba akanta anan kasan marbles da ya barta bata canza matsugunni, sai in ya fita ne taji yunwa zata kasheta take yunkurawa ta isa ga firji ta sha madara ta koma ta kwanta. Haka zata wuni kuka idan ta tuno karatun ta, da abokan karatun ta da Dadar ta. Yau ta dauke masa mukullai ne da niyyar zata gudu, kuma zata bar Jamus gabadaya." "Bai nuna mata bai ga mukulli ba, tana daga kwance inda take ya sunkuya ya ajiye mata kofin tea. Sai tiriri yake. Ta runtse ido hawaye na bulbula domin ko fuskarsa bata son gani. Kamshin turarensa duk ya mamaye ta. ""Kiyi hakuri sweetie, i promised to become a changed person, if you give me another chance (nayi alkawarin canzawa, in har zaki bani dama). Yanzu dai na makara, inna dawo zamu tattauna sosai""." """Allah yasa kafin ka dawo ka tadda gawata!""" Ta fada cikin rishin kuka. Tana mai addu'ar Allah ya dauki ranta ta huta kafin Habibu ya dawo. "Murmushi Habib yayi, sannan ya sunkuya ya sumbaci bakin ta lightly. Wani abu da bai taba wanzuwa tsakanin su ba (sumba). Ta tattaro miyau ta tofa masa a fuska. Maimakon ta ga ransa ya baci ko ya falleta da mari kamar yadda ya saba, sai taga yasa dan yatsa ya lakato miyan ya kai bakin sa ya lashe." "Ya kuma kasheta da murmushi yace ""i know that i offend you, and it's intentional as you expect, but i promised to become new HABEEB (masoyi) har sai kin koreni sabida soyayya." "Ki bani thirty minutes yanzu zan dawo we will discuss everything, in nace EVERYTHING ina nufin har ASALI NA da naki""." "Maimakon maganganun sa su farantawa Raheena, sai ma suka kara shafa masa shuni a idanun ta. Ba abinda zai ce ta yarda yana kaunar ta. Ya baro gini tun ran zane. zuciyar ta ta riga ta mace a tsanar sa." Abinda kuma zai farfado da matacciyar zuciyar nan ba kankani bane. Ya riga ya raunata zuciyar ya yi mata illah. Tsanar data yi masa ba 'yar kadan bace. Kuma zata nuna masa ita ba yar tsana bace duk rashin gatanta ta san 'yancin kanta. "Haka ya fita yana waiwayen ta, ita kam ko ido bata sake dagawa ta dube shi ba. Mintina goma sha biyar ta bayar bayan fitar sa, ta mike tasa jallabiyya, tasa jilbab, sannan ta tattara duk wasu muhimman takardun ta da passport dinta ta fice cikin zafin nama." ***** """Divorce ( *Scheidung* ) a kasar Germany: ba karamin abu bane. Domin tunda ke ke son sakin, sai kin dauki lawyer. Sannan zaki biya kusa 鈧฀3,000 kudin kotu dana daukar lawyer. Ki rubuta application for divorce (divorce petition) in kin tabbatar kina da gamsassun hujjoji. Sannan ne za'a shiga family court a gudanar da sakin under German-law. Tunda dukkkannin ku kuna kasar Jamus. The divorce will run in accordance with German law regardless of your nationality (sakin zai kasance ne karkashin kundin tsarin shari'ar Jamus batare da la'akari da kasancewar ku ba 'yan kasa ba)." "However, also in this case, sai kin jira end of the one-year-separation before starting the divorce procedure""." "Ambasadan kasar Najeriya a kasar Jamus yayi mata bayani cikin nutsuwa. Da gani yarinyar is desperate, sakin kawai take so ba tareda ta san aikin dake gaban ta ba, ""tun farko me ya kai ki amincewa da auren sa in kin san ba kya son sa?"" Ya tambaya calmly, Rahina ta sanya gefen jilbaab dinta ta goge gumi da hawaye, ""ranka ya dade basu bani damata ba, uwardakina ta kasar nan ita tayi min fin karfi, hujjarta kakata tace kowa aka samu a aurar dani gareshi. Ni kuma ba na son sa, ban san shi ba, ban san komai a kan shi ba""." "Ambasasada Shehu yace ""zaki iya gaya min hujjojin ki na rashin son zaman aure? Idan har akwai ci da sha da suttura?""" "Rahinah ta rasa inda zata sa kanta, da kunya ta fadi hujjojin ta, balle a gaban alkali. Me take so daga gareshi banda SOYAYYAH??? Asalin sa, da sanin dalilin sa na auren ta?""" "Kuma a yau ya ce, tayi hakuri in ya dawo zasu tattauna komai and he promised to become a changed person irin yadda duk take son sa. What else take so daga gareshi bayan wannan? Ya riga ya dasa kiyayyarsa a zuciyarta ne ta yadda babu wani repenting da zai yi ya wanke dattin laifukan da yayi mata." "Ambasada ya ga shirun ta yayi yawa, yace ""bazan iya tsaya miki ba, har sai na san hujjojin ki masu karfi ne, sabida Jamus ba Najeriya bace, karshe a kare da cin ki tara. A yanzu haka ma in zai sake ki sai kin biya shi kudi masu yawa, do you have any source of income bayan alawus din ki na cin abinci?""" "Rahinah ta kara rudewa, tace ""ka taimakeni yadda Allah ya taimake ka, banida komai da zan biya shi, bani da kowa da zai kwatar min 'yanci. Shin rashin so bai zama hujjah ba? Bana son sa ne, kuma bazan taba son sa ba""." "Ambasada Shehu yayi murmushi, ya gama gane wauta da tarin kuruciya a tare da ita, banda haka auren, ai shine rufin asirin ta. Kowanne iri ne kuwa. Don haka yace." """'Ya ta, zan tsaya miki kamar Babanki, domin hakkin walwalar duk wani dan kasar Najeriya dake Jamus yana wuya na, amma hujjar ki bata isa hujja da za'a kai kotun Jamus ba, sannan baki da kudin da zasu nema. Don haka in zaki bi shawara ta in ma sakin zaki nema to ki nemeshi ta hanyar sulhu saki na addini tunda auren musulunci kuka yi ba tareda kin kai shi kotu ba." "Ni zan kira yaron mu zauna mu uku, gara ya baki saki bisa doron musulunci tunda shi kika zaba amma ba ta hanyar kotun bature ba. Hakan zai jawo babbar matsala ga karatun ku ku duka, don dukkan ku ba abinda ya kawo ku ba kenan. Kuma in gwamnatin garin ki ta ji a inda kika kare a kotu zaki yi disappointing din ta ga kara sponsoring yara mata, sannan jami'ar ku zata shigo zancen wanda duka matsala ne ga karatun ku. Don haka ki barni in ganshi mu zauna mu duka." "Idan rabuwar ku ita ce mafi alkhairi ya sake ki ta ruwan sanyi bisa doron saki na addini""." "Jikin Rahina yayi sanyi sosai, kuma tana hango rashin yiwuwar hakan a idanun ta; Habib bazai yarda ya sake ta ta ruwan sanyi ba, ta gama gane mutum ne mai naci akan abinda yake so, kuma hargagi ko barazana basa razana shi. Shiyasa ta so ta kai shi kotu. But who is she to argue with this humble ambassador?""" """Na amince a kira shi in roke shi ya sake ni, a bisa hujja ta bana son sa""." "Ta fada cikin matsananciyar faduwar gaba, tana mai jin tamkar hukuncin data yanke bai yanku ba, kamar zai dawo watarana yayi ta haunting din ta (evocative feelings)." ***** NA HUCE is not for free. It's 1000 via; 3094856450 Sumayyah Kabara FirstBank : SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI *NA HUCE* (Daga Fushi na) PAID BOOK "Sati uku kenan tana karatun ta conveniently online. Natsuwa ta soma shigar ta yadda ya kamata. Tunda bata ganin Habibu A. Bilyamin Nahuche bata da bacin rai, kuma bata da damuwa." "Ciki dai har mantawa take yana makale a jikin ta, in banda mugun kwadayi da yake sa ta, kamar ta cinye Nene da Yafendo sabida dafa min kaza, dafa min kaza." "To haka rayuwa take, komai lalacewar zamani baka rasa mutane na kwarai masu zuciyar taimako saboda Allah, iyalin Ambasada Shehu Bichi, ba abinda zata ce dasu sai addua da fatan Alkhairi." "Hutun farko na summer mutanen gidan duka zasu je Paris, amma Ambasada yace banda ita da Yafendo, su zauna suyi kadin auduga a gida, ta sha jarabawa tana bukatar zaman waje daya ta nutsu, don su kam in sun tafi sai sun kwashe sati hudu suna yawo." "Sun tashi ranar lahadi, gidan ya rage daga ita sai Yafendo, don haka ta lokewa tsohuwar, ba hirar data ke so su yi sai ta garin Girei da mutanen cikin sa. Duk yadda Yafendo ke son ta nusar da ita gara ta koma gidan ta taga gara ta kyaleta, tana cikin walwala da farin ciki a gaban nasu, kamar bacin ranta shine ace ta koma gidan Habibu Nahuche." "Ita kuma haka kawai yaron ya shiga ranta, yana da wata irin Charisma da ba duka maza Allah ya mallakawa ba. Zuwan sa biyu gaida Daddy suna haduwa da Yafendon a falon saukar bakin Daddy, tayi ta zolayar sa wai biko yake zuwa a inda ba'a son sa. Shikuma baya shiru ramawa yake yi, yace yanada kamar ta me zai yi da wata Rahinah? Shi Yafendo ta ishe shi rayuwar duniya. Ya zo ne ya ji lafiyar dan sa a wurin Daddy he's not here for RAHINAH!" "Bata jima da dawowa daga dakin Yafendo ba ta ga wayar ta na haske, alamar shigowar sako text. Ta dauka ta duba sai taga cewa alert ne na kudi Euros 鈧฀3000. Daga Habibu Aminu Nahuche. Ya cika alkawari na farko da Daddy yasa shi ya dauka na ciyar da ita har sai ta haihu." Bata san ya aka yi ya aka yi ba kawai ta ji kwalla ta cika idanun ta. **** "Rayuwa ta cigaba da gudana yadda suka tsara ta, sai dai kuma sau tari ta kan zo wa dan adam da sauye-sauye; abin nufi, cikin ta na girma ra'ayin ta na canzawa akan sa. From negative to positive. A kullum ta ji shi yana wutsilniya sai ta ji gabanta ya fadi, sannan kauna irin ta UWA ta soma kanannade ta ba tareda ta yi shawara da ita ba. Bata son uban cikin, amma tana jin zata iya yin komai don tsira da wannan dan na cikin ta. Shi kadai ne ya rage wanda zata kalla ta kira jinin ta, tunda har gobe bata da wanda zata kira nata a gefen ta." "Ta yi sallama a dakin Yafendo, ta sameta tana murza goge a magogi tana hambudawa, Yafendo tace ""yau tun safe ban ji motsin ki ba, inji dai lafiya kuka tashi?"" Ta zauna gefen Yafendon, tace ""lafiya na tashi Yafendo ina wani group discussion ne da 'yan class din mu via zoom. Sai yanzu muka gama kuma dole yau zan shiga makaranta akwai littafan da zan karbo a library"". Yafendo tace ""a wannan yanayin da kike 'yar nan? Zaki niki hanya ki bar gari zuwa makarantar nan taku mai nisa?"" Tayi murmushi ta dora hannunta akan na Yafendo tace ""kada ki damu tawan, ina jin karfin jikina sosai, kuma direba zan kira mu tafi tare"". Yafendo tace ""in kin ga wannan naman da ake cusawa cikin fulawa ki sayo min, irin wanda kika kawo min wancan zuwan naki makaranta"" tayi dariya tace ""bakin Yafendon mu akwai son cin dadi, zan kawo miki shawarma, nima yau ita nake son ci"". Da haka suka yi sallama ta daga wayar ta ta kira Yohana direba." "Suna tafe akan titi tana nazarin wani practical da zasu yi cikin ipad dinta, tayi shigarta islamically cikin abaya ruwan makuba da mayafinta kirar kasar Oman, cikin ta ya fito sosai yayi toro don ta shiga wata na bakwai. Sake-sake take a ranta ko yaya haihuwa take? Is it painful? Shikuma raino da breast feeding ya suke? Kamar amsa ga tambayarta dan cikin ta yayi wani uban juyi da yasa saida tasa hannu ta dafe shi, tana mai addu'ar Allah ya raba su lafiya." "Ta nunawa Yohana inda zai ajiyeta, wato parking lot na Cologne Public Library. Ta bude kofa ta fito a hankali tana taku irin na masu ciki, ta shiga library din da kafar dama domin kuwa shima shigowar sa kenan. Kamar kullum yana cikin kayan sa na hausawan usul jamfa da wando na farin boyel, amma yau bai sa hula ba, ya tara suma mai yawa akansa ta yadda farin gilashin da ya sanya ya nitse cikin gashin kansa. Yana zaune a kujerar sa cikin wani dan cabin na glass inda yake kula da bangaren ajiyar littafai masu muhimmanci (reserve section) ya ga wucewar ta amma ita bata lura da shi ba, kuma gabadaya ta manta a wajen da yake aiki kenan." "Taje ta zabo littatafan da take bukata, amma bata samu guda biyu ba an ce suna reserve section." "Ta tako a hankali zuwa reserve din, ya juya baya yana fuskantar allon kwamfutar dake gaban sa, kwarai ya ga sanda ta taho, kuma ta taho ne tare da bugun zuciyar sa. Ta kara wani itin kyau da sulbin fata tabbacin tana cikin kwanciyar hankali, sabanin shi da rayuwar sa ta jirkice bakidaya tun shigowar ta cikin ta. Rahinah muguwa ce mai son kanta da la'akari da maslahar kanta kadai. Idan wani barin na zuciyar sa ya so kare ta, wani baya mata uzuri cewa yake bata da hujjar kin koma maka. tunda ka ce zaka canza zuwa yadda take so." Babu wani bangare na zuciyar sa dake yarda wai Rahinah bata son sa. tana amfani da kalmar ne don biyan bukatar kanta. """Hi, can you please check these for me?鈥฀;" -Diagnosis in Otorhinolaryngology -New Aspects of Fundamental Problems of Laryngology and Otology "Pediatric Otorhinolaryngology....Scott-Brown's Otorhino....."" sauran maganar ta makale gabadaya a makoshin ta sakamakon juyowar sa gabadaya. Saura kadan numfashin ta ya bar gangar jikin ta sabida wani mummunan kallo da Habib ya jefa mata. Dadi da cewa bata tsammaci ganin sa ba a daidai wannan lokacin. Sannan dadewar da ta yi bata ganshi ba ya dada haifar mata da faduwar gaban. Tayi kokarin maida numfashinta amma ya gagara isa huhunta." "Daga sanda ya taso daga mazaunin sa zuwa isowar sa gabanta Rahina bata farfado daga suman tsayen data yi ba. Haka kama hannun ta da yayi suka bar cikin library din bata iya ta kwaci kanta ba. Saboda gabadaya bakin ta ya mutu ta kasa saita kanta a gabansa, ta kasa kuma yin kowacce irin hobbasa ta kwace hannun ta daga cikin nasa." "A sanin ta da shi dai bashi da mota, amma ya bude bayan wata mota opel-astra ya sanya ta ciki ya rufe harda mukulli. Ya zagaya ta barin mazaunin sa ya zauna kuma ya tashi motar da wani irin mahaukacin gudu, bata raba daya biyun yau tata ta kare. Don ta san Habibu akan ta wani mahaukaci-mahaukaci yake komawa." "Har kofar flat dinsa ya shiga da motar, ya kashe ta sannan ya dube ta da idanun da suka kada, suka kuma sanya hantar cikinta kadawa. ""Ki fita mu je, magana kawai zamu yi in mayar dake inda na dauko ki""." "Rahinah ta soma hawaye, tace ""babu inda zani, nida shiga wannan gudan sai dai akai gawata""""ko? Zaki shiga ne kuma da ran ki da lafiyar ki, ko ta tsiya ko ta arziki, kina sane da cewa har yanzu matsayin matata kike?""" "Wani karfin zuciya ne ya zo mata, ta ce ""wallahi ko ka bude min na fita, ko nayi maka ihun da zaka fada hannun hukuma, nace bana yi, bana so kuma bana auren dole ne?""" "Ya kwantar da kai akan sitiyari yana kallon ta, masifa take yi tun karfin ta amma zakin muryarta kamar busar sarewa yake jin sa a kunnuwan sa. Haka mace mai cikin take komawa? Danya sharaf? Komai fresh? Idanuwan sa har wani kanakancewa suka yi suna dubanta da siga mai nuna bukatuwar miji zuwa ga matar sa......" """You can scream.... (kina iya yin ihun) amma ki sani nima inada nawa 'yancin da musulunci ya bani, kuma zan tabbatar miki shi yanzu"". Ya karasa maganr ta hanyar kamota da karfin gaske ya rungume ta, tana mutsu-mutsun kwatar kanta. Yace ""Rahinah ki dubi Allah ki tausaya mun my life is shattered without you. Ko me kike so zan" "miki, ko me kike so zan zama. Nayi alkawarin fin Romeo iya soyayya. One more last chance ko don albarkar dana" "dake karkashin marar ki. Rahinah ko a lahira wani kan ci albarkacin wani. In kika barni gabadaya bazan iya kara aure ba. Zan yi ta zama da dan ki ne yana debe min kewar ki har karshen rayuwata ""." "Rahinah ta ga cewa hargagin ta ko cika bakin ta bai kwatar ta hannun Habibu a yau, he's ready to face anything don ganin ya kusance ta a yau, wanda hakan na nufin maida hannun agogo baya. Tun farko ita wane tsautsayi ya kawo ta library bayan ta san anan yake? Ta soma kuka tana rokon sa ""don Allah ka amida ni inda ka dauko ni, kaga bani da lafiya, bazan iya wannan abun ba zan mutu, da na ma zai mutu, wallahi nayi alkawarin zan saurareka da duk abinda ka zo da shi amma bayan na haihu "". Habib ya sassauta rikon da yayi mata, shima bazai so wani abu ya samu dan" "sa ba, dan da yake jin duk duniya ba abinda yake so kamar sa in ka dauke Haj. Kaltume. ""Kin yi alkawari zaki saurare ni in kin haihu?""" Ya tambaya in a subdued voice. "Da sauri ta gyada kai, ba don ta yarda ta yi alkawarin a karkashin zuciyarta ba, fatan ta ta rabu da Habib lafiya ba tareda ya maida ita gidan nan nasa ba, data yi alkawarin ita da shi sai dai a kawo gawar ta." "Sai jin Habibu tayi yana dauke hawayen fuskarta da halshen sa, wani al'amari tamkar electrical shocking ya bakunce ta. Ashe ba a iya nan zai tsaya ba? Al'amarin da ya biyo baya mai tsauri da nauyi ne da ya shallake tunanin ta. He began to kiss her passionately wani abu da bai taba faruwa tsakanin su ba. Ko ya manta a inda suke, ko kuma ita ta manta cewa sakakkiya ce a wurin sa. Wani incident da ya dauki tsayin mintuna masu yawa da bazai taba gogewa daga kwakwalwar Rahinah Omar ba. Ya kuma goge tabon abubuwa masu yawa da suka samu muhalli tuntuni akan Habibu Nahuche a zuciyar ta....." Wayarta ce ta dauki tsuwwa....kira ake akai-akai. Da sauri ta ja baya. tana wani irin hararar sa tamkar idanun ta sa "fado kasa. Habibu ya shafa kai, yana kallon ta da dukkan kauna da soyayya na zuciyar sa, idanun sa har shigewa ciki suke sabida azabar soyayya. Shi kadai ya san azabar da yake dandana. Komai ya dawo masa sabo, ji yake tamkar bai taba kusantar Rahinah ba sai a wannan lokacin. Amma ya san ko shi maye ne Rahinah bazata sake bashi wannan damar ba, idan har ba ya ya yi yaqin kwatowa kansa soyayya ba." """Nene!""" Sunan da ya bayyana akan screen din kenan. Gabanta yayi wani irin faduwa. Me ta aikata? Me take aikatawa rayuwar ta? Dadin bakin namiji ne zai sa ta gurbata kyakkyawan ginin data faro? Ya su Nene zasu ji in suka ji tana tare da Habib ne a kofar gidan sa cikin motar sa ba tasu ba? Bayan ba yadda basu yi da ita ba kan ta koma masa amma tace a'ah? Me yasa ta yarda ta biyo shi? Shin idan Nene ko Ambasada suka san tana tareda Habibu ba zasu zargeta da raina musu hankali ba? "Da wani irin zafin nama ta bude murfin motar ta fice, Allah ya so ta ya saki lock din, ta leko ta window tace cikin muryar kuka." """Allah ya isa taba ni da kayi, Allah ya saka min!""." "Habib Nahuce. Bai san sanda dariya ta kwace masa ba duk da halin da yake ciki. Yace ""Allah ya saka mana tare Rahinatu! Akwai mugu a duniya irin ki? Kin ci albarkacin Baby na, na rantse da sai kin kunshi wani sabon cikin a yau kin haifo su tare sun zama biyu "". Bata tsaya sauraron mugayen kalamansa ba masu kama da sabon Allah a" kunnuwan ta ta nufi titi da mugun sauri tana tare taxi. "Yohana sai ganin ta yayi taxi ta sauketa a gefen sa, ita da tace library zata shiga ta karbo littafi ta fito. In ya kirga daidai ta kwashe akwalla awanni biyu kenan. Ba wannan ne ya bashi mamaki ba sai yadda ta bude motar ta afko kamar wadda aka biyo." """Are you okey Madame?""" Ya tambaya calmly. """I'm okey Yohana let's go, kada ka tsaya a ko'ina sai mun isa Frankfurt""." """Is someone following us? So that i report to police?""" """A'a babu mai bin mu, kaidai ka tafi da sauri ka bar harabar wajen nan""." "Ya ja motar suka bar wajen yana cewa ""alright Madame, but kowanne karamin abu ki dinga gaggawar sanar da police""." Ita dai tace masa ta ji. "Sun yi nisa sosai wayar ta ta sake kara, tayi ajiyar zuciya sai yanzu ta fara samun nutsuwa data tabbatar sun fita daga shiyyar birnin Cologne. Sun kama hanyar da zata kai su Frankfurt." Da ta duba sai ta ga 10 missed calls daga Nene. "A take ta kira ta jikin ta har rawa yake, ji take kamar Nene ta ga komai da ya faru, ita da Habibu a mota suna kissing. Wani hawayen bakin ciki ya zubo mata, ta ji ta tsani kan ta, ta tsani karatun da ya fiddo ta daga gidan Ambasada, in bata yi wasa ba Habibu na gab da sake rusa mata rayuwa." """Nene wallahi ina cikin library ne wayar kuma na barta a mota""" """Meyasa kika je makaranta baki jira ni na dawo mun je tare ba idan zuwan ya zama dole? Kinsan Dr. Yace ki daina zirga-zirga"" ta share wani uban gumi daga kan goshin ta, tace ""Nene i'm sorry littafai na je amsow na clinical assignment dina, kinga ma ban samo su ba, bazan ma kara zuwa ba har sai na haihu. Zan gayawa Daddy a nemomin na saya kawai"" Nane tace ""better, me zan dafa miki kan ki iso?"" Tayi murmushin samun relief tace ""anything traditional""""to shikenan zan miki tuwon alabo miyar ugu leaf da alayyahu da ganda da busashshen kifi, yayi miki?"" Wani hawaye ya bullo mata, ashe haka soyayyar UWA ke da dadi? Allah ya barta da danta itama ta bashi kauna irin wannan. Allah yasa kuma kada mutuwa ta raba su yana karami sai ya mallaki hankalin kansa ko da zata mutu. Ya zamo cewa ta gama bashi duk wata kulawa da tarbiyyar da ya kamata ya samu daga gareta." "A wannan daren, daga Habibu Nahuche har Rahina Omar, babu wanda ya iya ya runtsa. Dare ne mai matsanancin hazo, cikin watan Nuwamba, Habibu na nannade cikin bargo sanyin kasar Jamus na shigar sa, ba abinda yake so yake bukata a lokacin sai dumin matar sa Rahinah. Amma ta wace hanya zai bi ya dawo da damar da ya samu a baya? Masu iya magana dama sun ce opportunity comes only once in life! Ya bata komai, ya dade da bata komai, ya riga ya bata rawar sa da tsalle. Haduwar su a yau ta maida masa komai sabo in itsown special unique way girman" "Rahinah da soyayyar ta sun karu sun ninku sun hauhawa a zuciyar sa, ya fahimci abubuwa da dama wadanda a baya bai sani ba; Rahinah na daga cikin kasaitattun mata da samun kamar su sai an tona. Irin matan nan ne one in million wadanda duk namijin da Allah yayiwa baiwar mallakar su ya gama bashi rabin addini sa, ya gama bashi farin cikin rayuwa, da duk wani jin dadi dake cikin ta." "A yau ya amince da abinda a baya ya ki believing da gangan. Cewa zai iya rayuwa babu Rahinah, zai iya hakuri da rayuwar sa single ba tare da Rahinah cikin ta ba. A yau ya yarda ya amince rayuwar sa bazata taba zama straight ba ba tareda Rahinah a gefen sa ba. Ko zata yarda ta saurareshi idan ta haihun kamar yadda ta yi alkawari? Shi kuma zai yi komai don dawo da ita cikin rayuwar sa cikin martaba da mutuntawa, dadin dadawa soyayya mara yankewa har fiye da wadda bata tsammani. Daga wannan ranar yake bincike, wani irin bincike na yadda ake tafiyar da soyayyar mata. A rubuce-rubuce na masana ilmin psychology (self-help books and self-reflection). Ya samo wasu tips guda goma wadanda suka ce (How to keep your woman and make her love you forever). Marubucin ya ce; cikin abubuwanda zasu rike maka soyayyar matar ka sun hada da;" -work on yourself ; ka yiwa kanka self-evaluation; ka cancanci ta so ka ko a'ah? -listen to her (and i mean really-really listen); ka saurareta akan duk abinda ta zo da shi da cikakken attention ka bata hankalin ka a lokacin da take bukatar hakan. -learn how she prefers to be loved; ka duba abinda tafi so ka nuna mata soyayyar ka da shi. "-give her gifts (ka kasance mai yawan yi mata kyauta, kyauta tana kara dankon kauna)." -be honest with her (ka zamo mai gaskiya da kyakkyawar manufa akan ta). -respect her (ka girmamata) and treat her with this respect. -find creative ways to tell her that you love her (ka zama mai iya kirkirar hanyoyin gaya mata yadda kake son ta in your own special way). -allow yourself to be vulnerable; wato ka dinga nuna mata raunin ka. (Allow yourself to make mistakes and admit to them. Allow yourself to be real and true and not hide any of yourself from her. "Don't be afraid to cry in front of her. And don't be afraid to let her cry, too.聽 Vulnerability allows for deep connection and bonding 聽 in a relationship. If you can't be yourselves 聽 in your most raw forms, how are you supposed to feel safe building a whole life together?""" "Habeeb Nahuche sai ya ga cewa duka wadannan tips din da wannan masanin ya zano duk zurfin ilmin sa shi bai mallaki ko daya ba! Bai taba nuna wa Rahinah dayan su ba, yet yana blaming din ta da kasa son shi duk cancantar sa." "Ita soyayya ta gaskiya ba ta ta'allaka da appearance din mutum, but the way he demonstrates himself." "Ya yarda duk ilmin ka ilmi baya taba karew a a duniya, saidai ka dauki iya wanda zaka iya ka bar ragowar. Inama! Inama! Inama Rahinah ta yarda ta sake bashi dama koda sau daya ne a rayuwar su???" **** "*NA HUCE* is not for free," It's 1000 via 3094856450 Sumayyah Kabara FirstBank ": A daren bata yi wani isashshen barci ba sabida taraddadi da ya cika ranta, ashe tana da rabon ganin wanda zai ce ya san wani nata ma bayan Dada? Excitement ya cika zuciyar ta, ta dokantu shekara ta zagayo ta bi iyalin gidannan Najeriya." "Washegari da safe ta yi shirin makaranta, ta hada tea a dining din kitchen zata sha, kawai sai taji zuciyarta na tashi kuma ba abinda take so sai ramar Yafendo." "Da sauri ta suri jakar ta ta nufi dakin Yafendo. Ta idar da sallahr walha kenan, ta shigo dakin kamar an jefo ta, ""Yafendo don Allah don annabi ki sammin rama da kuli, in ban ci ba yanzun nan mutuwa zan yi""." "Yafendo ta katse lazimin ta jin abinda Rahinah ke cewa, kafin kuma ta bata amsa ta hau daddaga shirgin Yafendo tana neman Ramar, Yafendo tace ""Rama da safiyar nan 'yar nan? Ki tafi makaranta kafin ki dawo zan kwada miki, yanzu ki nemi ruwan dumi ki zuba a cikin ki""""na hada na kasa sha, tashin zuciya bambita yake sa ni, don Allah ki taimakeni""." "Da sauri Yafendo ta dauko ramar, tace ""jona ruwan dumi a butar can"" cikin minti biyar tayi mata kwadon ta bata. Nan ta hau ci ba kakkkautawa hannu baka hannu kwarya. Yafendo tana ta mamaki a ranta, anya lafiyar ta?" "Data dawo daga makaranta ma kai tsaye dakin Yafendo ta zarto. ""Na kwaso yunwa Yafendo, zan samu kwadin ramar ki?' Kawai sai ta ga Yafendo ta zaro kwano a rufe ta mika mata, already ta kwada tun kafin ta dawo""." """Allah ya kara nisan kwana Yafendo nagode"" ta soma ci a urunce. Yayin da Yafendo ta tsura mata ido." "Ta koma dakin ta ta sunce zata yi wanka, amma sai ta bige da kallon kan ta a mudubi, a take ta hango wasu bakin sauyuka a halittar jikin ta. Abinda ya fi daukar hankalin ta shine karuwar girman kirjinta sosai, sannan tayi wani irin fari dau! Kamar babu jini a jikin ta." "Rahinah bata damu ba ta cigaba da wankanta tana fadin mutum na kara girma ai dole kirjin sa ma ya kara girma. Tana fitowa Ahlan ya shigo da gudu, ""Aunty Rahina Nene tace wai yau baki ci abinci ba ko lafiya?"" Ta ce ""Ahlan ka gayawa Nene wallahi kwanan nan ban iya cin komai sai RAMA""." "Ba jimawa sai ga Nenen da kanta, tayi sallama ta shigo, tace ""Rahinah me kika ce a gaya min? Ban gane hausar Ahlan ba, Jamusanci ya masa yawa"" nan ta maimaita mata. Tace ""ke a ina kika ga Ramar?""""Wajen Yafendo, tana da ita mai yawa"" Mami ta tsura mata ido, a take ta hango sauyukan data ke son gani. Tace ""Rahinah kina yin period kuwa?"" Kanta tsaye ta amsa ""ai ni rabo na da shi har na manta, amma kin san i'm too busy to notice that ba don kin fada ba""." "Nene tayi mata kallon tausayi, sannan ta ce yanzu idan ramar ta kare ya za'ayi?""" """Nima ban sani ba Mami,na dai san in ina so ban samu ba mutuwa zan yi, yanzu kam na koshi sai kuma gobe in Allah ya kaimu""." "Mami ta juya ta fita tana fadin ""on weekends zaki raka ni asibiti, mutum baya period ai gara a duba shi a san dalili"". Cikin damuwa tace ""Nene, is there any problen with that?"" Nene ta dafa kafadarta tace ""don't worry"". Sannan ta fita. Nene ta ce kar ta damu, amma sai ta ji ta damun, ko wata cuta ce rashin yin period din?" "Nene na fita dakin Yafendo ta nufa, ta samu kujera ta zauna, tace ""Yafendo ko kin lura da abinda na lura da shi game da yarinyar nan?""" "Yafendo ta ce ""kwarai kuwa, kallon ta kawai nake, in kuma jira in ga ko zaki kula da kiwon da Allah ya baki. Shi aure dama in Allah bai nufi karewar sa ba wa ya isa ya karar da shi? Da zata ji shawara ta gara mata ta koma gidan mijin ta ta cigaba da hakuri irin wanda kowacce mace ke yi a gidan auren ta, ba namijin da yake cikakke a komai dukkan su suna da gibi, amma yadda na lura tafi jin dadin rayuwar ta da mu a haka bata ko so a dago mata zancen sa"". ""Kwarai wannan haka ne, bari in je in samu Daddy muyi magana a kan ta""." "Yana sauraron radio Jamus a 'yar karamar rediyon sa lokacin da Nene tayi sallama ta shiga. Ya amsa mata, sannan ta samu gefensa ta zauna." """Ranka ya dade magana ce ta kawo ni, akan yarinyar nan Rahinah""." "Ya rage sautin rediyon sa ya bata hankalin sa. ""Ina zargin ciki ke gareta"". Radeyon hannun Ambasada ce ta subuce kasa, tace ""wallahi alamu sun gama nunawa, amma duk da haka ban tabbatar ba""""kuje asibiti a tabbatar pls"" Mami tace ""insha Allahu, amma in ya tabbata cikin ne yaya zamu yi da ita ga karatun ta mai tsayi?"" Ambasada ya nisa yace ""yadda zamu yi da Safeenah, idan irin haka ta same ta""." **** "Rahinah bata san me ta rako Nene yi a asibiti ba, amma tunda suka zauna a gaban likita ya kuma ce ta bashi fitsarin ta komai ya fara kwance mata." "As a medical student ta san awon fitsari na nufin abubuwa da yawa.....awon cuta ko awon ciki! Don haka kafin sakamako ya taddasu, ta yi ligib cikin tashin hankali da tararradi." """She's two months pregnant"". Likita ta fadawa Nene ita kadai, bayan ta ce Raheenah ta je reception ta jira ta. Sannan ya bata shaidar hakan a rubuce." "Nene ta yi masa godiya, sannan ta fito ta tadda ita suka tafi, a hanya take gaya mata an ga shawara (jaundice) cikin fitsarin ta." "Raheenah tayi wani ajiyar zuciya, feeling relieved. Har suka zo gida zancen rama take wa Nene, wai yanzu idan ranar Yafendo ta kare ina zata sa kanta? Nene tace ""sai ki ci salad, ai shima ganye ne""""amma bai da dan tsami- tsaminnan kamar na rama"" murmushi Nene tayi, tace ""sai a masa vineger""." Suna sauka a mota kuwa ta tafi dakin Nene cin rama. "Kwana bakwai kenan bata iya cin komai banda ramar, har yau gashi rama ta kare, babu kuma inda za'a sameta a Jamus." "Don haka tun safe take cikin kunci, haushin kowa ta ke ji, da Ahlan ya shigo yana mata surutu sai ta shige toilet ta rufe kanta don bazata iya korar sa ba." "Nene ta shigo dauke da plate a rufe ta sameta, ""Rahinah yau bazaki makaranta bane? Yara duk sun fita sun barki, ga wannan ko a mota sai ki ci kada ki tsaya ci ki makara, kin dai san kina da nisa""." """Nene yau ban iya zuwa makaranta"" ta fada hawaye na ciko idon ta. ""Sabida me?""""I'm not feeling well, sabida tun jiya ban ci rama ba, Yafendo ta ce ta kare""""try this"" ta fada tana mika mata plate din hannun ta." "Bata yi musu ba ta karba ta bude, salad ne Nenen ta hada mata da kanta, yaji kuli da vinegar da tumatur, cocumbrr da albasa. Wani mugun yawu ya gudana a bakin ta, ta karba tun daga tsayen ta soma ci kafin ta zauna. Amma ko loma hudu bata yi ba ta dinga kwaro amai kamar zata amayar da hanjin ta." "Tun daga ranar komai ta ci sai ya dawo, ta galabaita matuka, karfin jikin ta ya yi kasa sosai. Ambasada yace da Nene ta kaita asibiti, koda taimakon da zasu yi mata abinci ya dinga zama a cikin ta." "Suna asibitin likita ya riketa, domin yace she's 60% dehydrated. Aka sa mata drip nan take. A ranar ne Ambasada ya kira Habib a waya." """In ka samu lokaci kazo 'Sachsenhausen Hospital' da daddare ina son ganin ka"". ""Insha Allah i will"". Ya fada cike da girmamawa." "Karfe takwas na dare a Sachsenhausen ta yi wa Habibu Nahuche. Yana sanye da Native Hausa Attire dinsa na shadda sharaton ruwan makuba, ya kafa hula a gaban goshin sa ruwan toka mai turuwa sosai (deep grey), yayi kyau kamar koyaushe amma kallo daya Ambasada yayi masa ya gane muguwar ramar da yayi cikin watanni biyu da yayi bai ganshi ba." "A wajen parking motoci suka hadu, direba ya sauke ambasada, shikuma taxi ta sauke shi. Ambasada ya bashi hannu sannan tare suka taka zuwa dakin da aka kwantar da Rahinah. Daga ita sai Nene a dakin. Kamshin turaren sa ne ya fara shiga hancin Raheenah, wani kamshi mai tasirin da bazata taba mantawa ba. da sauri ta juya kai zuwa bakin" "kofar shigowa. Idanun su suka hadu, wanda hakan ya haifar da wani irin shock ga Rahinah dake kwance, domin ta ganshi ne ba zato ba tsammani." "Yayin da Habibu Nahuche ya tsura mata ido, gabadaya ta zabge ta lalace, maimakon ya zo ya ganta very healthy and jovial tunda ta samu rayuwa yadda take so? Ta karbi 'yancin ta da take ikirarin ya danne mata? Banda girman idanun ambasada da yake gani babu abinda zai sa shi amsa wannan kiran, don bai ga dalilin sa ba. Tunda komai ya kare a tsakanin su." """To zauna mana kun tsaya kuna kallon-kallo kamar zakaru"" Ambasada ya furta masa sounding fatherly. Ya nemi guri can nesa da gadon da take kwance ya zauna. Wani irin abu na hankoro a zuciyar sa, ta shiga bugawa fat-fat-fat, bai san idanunsa sun yi kewar ta ba, sai yanzu da suka ganta kwance a gaban su, hatta zuciyar sa neman fitowa take daga tsakiyar kirjin sa. shikadai ya san halin ragaitar da ya samu kansa cikin wadannan watannin biyu masu kama da" jiran tashin alkiyama a gare shi. "Rahinah ta dauke kai daga kallon sa, ta mayar wani gefen daban, tunda suka rabu ko sau daya bata ji kewar sa ba. Bai bar mata wani abun tunawa a zaman da tayi da shi ba na kwanaki bakwai, banda kyakkyawar fuskarsa ta Rumawa data zauna a zuciyarta ta ki fita." """Na kira ka ne Habib, don in sanar da kai Raheenah na da ciki na watanni biyu""." "Daga Habib har Raheenah, a tare zuciyarsu tayi wani irin dokawa, ta doka ta sake dokawa ta ci karo da bango. Idanuwan Rahinah kamar zasu fado kasa.....jin maganar tayi tamkar saukar aradu a kunnuwan ta, zata rantse ko mutuwar Dada da aka gaya mata a waya bata firgitata ta ruda ta kamar abinda Ambasada Shehu ya fada yanzu ba..." "Yayin da Habib, Mustapha Nahuche ya wani irin lumshe idanunsa." Wani albishir ne zai ce ko bushara da ba'a taba yi masa kwatankwacin sa ba. Wani irin maganadisu ya ji yana fizgar zuciyar sa akan Raheenah da abinda ke cikin ta.. The feeling is so sweet da bai taba jin mai dadi a zuciyar sa kamar sa ba...nitsatstsen SO! "A hankali ya bude idanun sa akan Raheenah, wadda ta tamke nata idanun tamau, hawaye na zirara ta gefe da gefen su." "Which means she's not happy at all, she's mourning kaddar da ta afka mata rana daya. ta tabbata ta rasa farin cikin" "ta daga yau, bata ga amfanin sauran rayuwar ta ba.." Ashe dai ta yi gudun gara ne ta tadda zago Habib Nahuche bai shigo rayuwarta don ya fita a lokacin da take so ko yake so ba. "Kaddara bata kare tsakanin su ba, mai hada eternal dangantaka ya riga ya hada wato gamayyar jiki, wadda a yau ta maida ita matar Habib a karo na biyu har sai ta haife masa dan sa ko 'yar sa wanda take jin ba abinda ta tsana a duniya sama da kawo shi duniya..." "A fili ta fada "". bai yi sa'ar mahaifi ba, he's but selfish by nature wato mutum ne mai son kan sa da yawa (tana" nufin Habib din). "Muryar Ambasada Shehu ta cigaba da ratsa mugun shirun da ya ratsa kamar daukewar ruwan sama. ""My dear Son and Daughter isn't it high time you reconcile? Tunda kun ga yadda kaddara tayi daku, kowanne Da yana burin ya tashi tsakanin iyayensa biyu, broken home shine babbar matsala ga tarbiyya da rayuwar kowanne yaro, rayuwa duka 'yar afuwa ce, in kuka afuwantawa juna kuka kuma zauna kuka gano matsalolin ku i'm sure zakuji dadin zama da juna tunda har ga rabo a tsakani. ""." "Habibu yasa hanky dinsa ya goge gumin fuskarsa da hawayen da suka cika masa ido, wadanda yake da tabbacin na farin ciki ne. Ya dubi Raheenah wadda ta kautar da kai gefe tana jin tamkar Daddy na diga mata narkakkiyar dalma a kirjin ta da ya ce wai ta komawa auren Habibu. Ya ce ""ranka ya dade ni bani da matsala da hakan in har ta amince, abinda ba zanyi ba shine sake zaman aure da ita ba tare da amincewar ta 100% ba""." "Rahinah ta juyo a hankali zuwa side din da yake, a hankali ta ce ""to in dai ko amincewata kake bukata to har abada bazamu koma ba, once beaten twice shy. Ba ciki ba ko 'ya'ya goma ne suka bayyana tsakani zan baka abin ka, yadda bana son ka haka bana maraba da duk abinda ya fito daga jikin ka. """ """Rahinatu!""" "Ambasada ya kira ta sounding fatherly, ""banda cin fuska ga wanda ya girme miki, balle mijin auren ki, wanda har yanzu kike cikin zummar auren sa, har sai idan kin haihu bai ce ya mayar dake ba. Tunda baki amincewa komen ba shikenan, amma ki janye munanan kalaman da kika yi masa""." "Tana kuka sosai, kukan kaddarar da ta sameta, tace ""ka yi hakuri Daddy na maida kalamai na, amma har abada bazan koma masa ba""." """Shikenan zance ya kare, shima cewa yayi ai in kin amince. Kinga kuwa yasa tagociya kenan ga maganarsa. Don haka ki kwantar da hankalin ki kina hannun Daddyn ki, har Allah ya sauke ki lafiya""." "Ya juya ga Habib, wanda tuni ya mike tsaye ya zuba hannayen sa cikin aljihun caftan din shi yana nufin barin dakin don in ya cigaba da zama zuciyar sa na iya fashewa ko tayi bindiga, a yiwa uwarsa da 'yar uwar sa asara! Ya gama saduda Rahinah bata son shi, kuma har abada bazata so shi ba, tunda rabon bazata da Allah ya kaddara a tsakanin su bai sa ta so shi din ba. Ya sha jin ance mace na fara son mijinta ne daga lokacin da rabo ya gifta a tsakanin su. Wanda ke nufin ita Rahinah is exceptional and extraordinary daga sauran mata......." """Daga wannan watan zaka dinga raba albashinka biyu kana bata rabi don ciyarwa har sai ta sauka. Ba don bazan iya daukar dawainiyar su ba sai don in baka damar ka ta uba da addini ya baka. Ka kuma koyi daukar responsibility na iyali tun daga yanzu""." "Kansa a kasa idanunsa sun kada sun yi jazir yace babu damuwa insha Allahu. A turamin account number din ta"". ""Kana iya tafiya Habibu, Allah yayi muku albarka, yasa hakan shi ya fi alkhairi tsakanin ku""." "Hawayen da yake ta rikewa ne suka kwace masa, ya juya kadan ya dubi Rahinah wadda ke kallon bayansa a lokacin, suka kuma hada ido, ji tayi zuciyarta na son karyewa (rauni irin na diya mace) amma ta amince wannan shine decision mai kyau ga rayuwar ta." Sai ta maida idanunta ta lumshe su a hankali. Tana sauke ajiyar zuciya. "Shikuma yasa kai ya fita daga dakin, babu ko waiwaye. Kamar yadda yake ji a ransa bazai kara waiwayar RAHINAH OMAR a rayuwar sa ba." **** "Sai da ta kwashe kwanaki bakwai kafin ta samu karfin jikin ta, kuzarin jikin ta ya dawo ko ba duka ba. Har tana jin zata iya zuwa makaranta a gobe monday." "Tana canza kayanta na barci zata kwanta Nene tayi sallama a dakin. ""Rahinatu kin yi barci ne?""""Yanzu dai nake shiri Nene""""to zo mu yi magana irin ta uwa da 'ya"" tayi murmushi, don Nene ta canza mata bakidaya tundaga samun cikin ta, sosai take janta a jiki yanzu, tana tausaya mata, domin gani take tayi kankanta da haihuwa kashin jikin ta kamar bai gama kwari ba. Sabida bata da manyan barage." "Ta zauna daidai kafar Nene Bilki ita kuma tana daga saman gadon ta, tace ""Rahinah meyasa bazaki koma gidan mijin ki ba? Yaron nan ya bani tausayi sosai, da gani yana bukatar ki cikin rayuwar sa. Can you be open to me? Inaso in san meye matsalar ku? A matsayina na uwa zan iya bada shawara""." "Rahinah ta sunkuyar da kai, tana tuno irin rashin tausayi da rashin soyayyar da Habib ya gwada mata, kullum tana ji a littafai cewa aure abu ne na soyayya, miji tarairayar matarsa yake yana bi da ita ta hanyar da bazata cutu a shimfida ba, amma Habib Nahuche a wannan fannin sai dai a kira shi NOVICE. Don haka bata ga amfanin zama dashi ba gara tayi rayuwarta single." "Amma ta yaya zata iya gayawa Nene haka bata ga rashin kunyarta ba? Ita a ina tasan yadda ake rayuwar aure tunda ba taba yi tayi ba! She's just comparing and imagining. Don haka ta ga gara ta rike sirrin auren ta a zuciyarta, shi ciki ba anyi shi don cin tuwo ne kadai ba. Ta soma tunanin abinda ya kamata ta gayawa Nene, don ita duk wata shawara in dai akan ta komawa Habib ne to bata bukatar ta." """I don't love him Nene!""" "Ta fada tana hawaye. ""Sabida bai aure ni cikin mutunci da daraja ba, ya sameni a arha da yawa. Cigaba da zama dashi zai iya janyomin psychological depression""." """Allah ya sawwake"" inji Nene Bilki, amma daga nan zuwa ki haihu ki nutsu ki fahimci zuciyar ki. Maiyiwuwa wani bacin rai ya sanya miki wanda ya lullube soyayyar. Bazan takura sai naji ba don tsakanin mace da mijinta sai Allah da ya halicce su. Amma shi AURE is not all about love my dear so many cirmustances na sanya mu zaman aure." "Ni kinga so nake Saffenah ta samu mijin amma Allah bai bata ba, shikuwa Habibu har cikin kwayan idanun sa na hango SO mai yawa, wanda nake da yaqinin da zaki hakura ku koma zai isheku rabawa ku duka, ya yalwaci zuciyar kowannen ku." "Yanzu mu bar maganar kome, mu yi ta karatun ki." "Kinga dai position din jikin ki na da dana yanzu ba daya bane, ba zaki jure wannan zirga-zirgar tsakanin Frankfurt da Cologne ba. Don haka na kawo shawara me zai hana ki nemi iznin accessing lectures dinki online? In yaso lokacin jarabawa sai kije ki rubuta, doctor yace kina bukatar hutu sosai. In yaso in kika haihu sai ki cigaba yadda kike yi""." "Rahina bata so ya zamo cewa kowacce shawara da Nene ta kawo bata dauki ko daya ba, banda haka da ta gaya mata. gara ta cigaba da zirga-zirga yadda cikin zai jijjigu ya bare. Cikin da bata maraba da shi ko kadan cikin" rayuwar ta. """To shikenan Nene, insha Allah zan rubuta application na neman iznin hakan, sai a karbo takardar asibitin"" Nene tace ""hakan dai ya fi""." """Sai maganar abinci, duk abinda kika je shi kike so, shi zuciyar ki ta kwanta da shi, kada kiyi kauron baki ki gayamin, nikuma insha Allahu zan dafa miki muddin ina gida, in ma bana nan ga Yafendo, kada ki dinga zama ke kadai idan ba karatu kike ba"". ""Nagode, nagode Nene, Allah yayi muku sakayya da alkhairi, yadda kuka dubi maraici na Allah ya dubi haular ku a bayan ku""." **** : *SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI)* 07030137870 "A nata bangaren, Rahinah Omar, kwana tayi tunanin abinda ya faru a yau, tana mai tariyo komai dalla-dalla. Idan zuciyar jin tausayi ta kutso, sai zuciyar neman kwatar 'yanci ta hambare ta. Mutumin da bai ji tausayinta ba, ita akan me zata ji tausayin sa? Yana son ta koma ne don bukatun kansa amma bai taba tunanin ya tambayeta asalin ta ko na iyayen ta ba. Wanda ke kara tabbatar da cewa ba damuwar sa bace personal life din ta, abinda yake yimawa kawai shine a gaban sa." "Ita wannan soyayya ta Habibu ta kasa ganeta, domin ta hada biyu da uku bata bata ma'ana ba. Tana burin auren mijin da ke matukar son ta, wanda zai rungumi maraicin ta kada yayi amfani da shi ya cutar da ita, wanda zai so ta da dukkan zuciyar sa. Amma Habibu fa? Ta tabbata ba don cikin nan ba da daga ranar da ya sake ta bazai kara waiwayota ba tunda duk abinda yake so daga gareta ya riga ya same shi." "Tsaki tayi ta juya a hankali don taji dadin kwanciyar ta, sai taji gefen wuyan ta na kamshin Carolina Herrera (men) har zuwa lokacin. Abinda ya tuna mata da incidence din. Is what happened Haraam? Bata sani ba, in haramun ne tana neman gafarar Allah, domin kuwa bata da laifi, laifin ta shine kasa yi masa gardama wajen binsa tamkar rakumi da akala. ""Ya salamu sallim"". Ta fada a fili. Amma wani sako na zuciyar ta na gaya mata it's not haram din, tunda har yanzu cikin iddah take. Kuma abinda addini ke so a wannan tsakanin shine su yi sulhu. Sulhun da bata jin har abada zata yarda da shi." "Washegari Nene ta rakata anti-natal da suke zuwa duk sati, likita ta dubata sosai ta kuma ce baby is breach sai an gyara masa kwanciya. Haka ta daure aka gyara sannan ta karasa duba ta, tace tanaso tayi mata alfarmar zuwa dakin haihuwa tare da mijin ta, sabida suna so mata su dinga haihuwa akan idanun mazajen su, domin neman karin kauna da soyayya, jin kai da tausayi a garesu. Gashi bata taba ganin ta ta zo tare da shi ba." "Rahina dai bata ce komai ba, sai Nene ce ta ce baya kasar ne, amma in ya dawo kafin ta haihu da shi za'a shigo labour room." "Rahinah ta daga 'yan idanun ta taba kallon Nene kamar tace da ita akan me za ki mata karya! Mun rabu, short and simple. Sai ta tuna abinda Ambasada ya taba gaya musu cewa saki ba karamin abu bane a kasar jamus, and it should be abiding by German law. Don haka rufe zancen da Nene tayi kawai shine daidai." "Watanni biyu a gaba, ta shiga watan haihuwa, ta kuma gama shekarar farko ta karatun ta. Wato tsayin semester biyu. A haka take zuwa zana jarrabawa da tsohon ciki har ta kammala da kyakkyawan sakamako. Ambasada ya baiwa Nene kudi yace ta saya mata duk abinda zata bukata na haihuwa ba ruwansa da abinda Habibu zai bayar." "A daren ranar ne kuma sai ga tarin akwatuna shaqe da sitturun jarirai unisex daga Habibu Nahuche. Hatta pampas da feeding bottle sai da ya sayawa dan sa, amma ita ko tsinke bai saka da sunan ta ba. Wannan ya sosa mata rai ba don tana son abin hannun sa ba, a'a yadda ya nuna yafi son abinda zata haifa yanzu akan ta shine abinda ya sosa zuciyar ta." """To a kan me?""" Zuciyar ta tambaya. """A kan dalilin da nima ban sani ba!"" Ta amsawa kanta a fili." **** EDD dinta saura kwana biyar rannan da daddare suna zaune a dakin Yafendo suna cin tuwo taji damshi-damshi daga kasan jikin ta. Bata kawo komai ba sabida sabida bata ji ciwon komai ba. An ce mata kuma ciwo ake ji mai tsanani. Amma ba'a dauki wani dogon lokaci ba ta soma 'yan mutsu-mutsun da ya ja hankalin Yafendo kanta. """Yar nan lafiya kike yanka gumi haka?"" Tayi yake tace ""bakomai fa Yafendo, zafi kawai nake ji"" Yafendo ta gyada kai ba don ta harda ba suka cigaba da hira. Safeenah ta shigo ta gaida Yakumbo, sannan ta dubi Rahinah tace ""Nene ta ce kina da bako a falon Daddy "" amma kafin ta kai karshen maganar ta sai gani suka yi tana shure-shure." "Yafendo tace ""Aha! Ni na san abun ne ya zo, kika yi mirsisi ke ga jaruma. Ke Safeentu kira Nenen ku ki gaya mata haihuwa ta zo a kawomin reza"". Safeenah ta zaro ido sannan ta fita a guje, kada taje ayi haihuwar a gabanta." "Nene ta fado dakin da gudunta, tace ""Yafendo wace irin Reza? Ki rufa min asiri in mutu maza su kai ni, ba'a kasar mu muke ba inda ake haihuwar gida. Maza kwarara jikin ki Rahinah mu gangara asibiti, ga Habib nan yana nan ya zo sai ya kaimu tunda direba bai dawo ba har yanzu.""" "Tsananin halin da take ciki, shi ya hanata yin musun tafiya asibiti tare da Habibu kuma a cikin motarsa. Daga ita sai Nene a baya tana shafa mata kanta da bayan ta tana yi mata addu'a yayin da shi yake tuki cikin wani mawuyacin hali. Ji yake da zai iya da ya karba mata nakudar, kanar yadda ya zamo silar wahalar ta daga zuwa karatu." "Sun samu ganin Dr. Saliha Widad wato likitar data ke gani itace on duty, nan da nan ta karbeta akan gadon tura marasa lafiya daga hannun Habibu da ya sunkotota gabadaya daga cikin mota zuwa cikin reception. Dr. Saliha ta duba ta tabbatar haihuwa ce gadan-gadan sai ta fito tana kiran sa. Ta tambayi Nene shine mijin Rahinah? Nene ta gyada kai ba tareda ta ce komai ba, yayin da likitar tace ""kazo ka tsaya tare da ita, ka ga yadda dan ka/'yar ka zai iso duniya""." "Habibu ya hada kai da bango yana ce mata ""a'ah..."" tayi murmushi tace ""ashe raggo ne baban baby, Rahinah ta fika juriya. C'mmon ka biyo ni nace"". Ya juya yana kallon Nene sai ta gyada mai kai, don bata so a tsaya ana tone-tone. Ai har yanzu tana cikin zummar auren sa." "Tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki, haka ya daga kafa ya bi bayan Saliha Widad." **** """Dada!""" "Kawai take kira hadi da sunan Allah,ta yi gumi kashirban, kanta na bisa cinyoyin Habibu gashin kanta ya bazu jikin sa. Ya rike hannayen ta cikin nasa, ita take nakudar amma ya fi ta hada gumi, jikin sa har kyarma yake. Dr. Saliha na fadi tayi nishi baby ya kusan isowa. Da ta daddage ta saki nishin kuwa sai gashi ya fado tare da mabiyar sa. Ya kuma canyara kuka a hannun Dr. Saliha wadda bakin ta ya kasa rufo, shekarar ta kusan goma tana karbar haihuwa amma bata taba ganin haihuwar katon baby black beauty irin na Rahinah ba. Saidai bai dauko komai nata ba har duhun fatar sa na mahaifin sa ne." "Aka gyarata, aka gyara wajen haihuwar, aka dau baby ana gogewa da man zaitoon aka shirya shi tsaf cikin kayan sanyi, aka nannadeshi a shawul sannan aka kawo mata shi saitin kanta. Sai a lokacin ta soma dawowa hayyacin ta ta kuma ji kamar a jikin mutum take kwance. Tana so ta kalli fuskar babyn amma tana son ganin wanda ya baje mata jiki ta kanannade akai ta haihu haka. A hankali ta daga kanta, sai idanun ta cikin na Habibu, wanda hakan ya haifar mata da matsananciyar faduwar gaba. Kafin ta soma yunkurin tashi ta kuma fashe da kuka." """Amma Dr. Widad kin cuce ni. "" ta fada cikin kuka sosai, kamar Dr. Na jin harshen nata, tayi Allah ya isa da" "fillanci, tayi da hausa, tayi da German, tayi davduk yaren data iya. Duk akan Dr. Widad data shigo mata da Habibu dakin haihuwa. Nene tana ta bata baki kan ta yi hakuri. Shikuwa ya harde hannuwa a kirji yana kallon ta da wani irin murmushin SO. In da a ce zai iya, zai iya ciro zuciyar dake kirjin sa ya bata a halin yanzu don kawai ya nuna mata dimbin godiyar sa da soyayyar sa gareta. Bisa bashi farin cikin da wani a duniya bai taba bashi ba. Bisa maida shi UBA, bisa bashi precious gem din da kudi ko mulki basu isa su bawa dan adam ba." "Dr. Ta mika mata Babyn bayan ta gama kukan bakin ciki ta share hawayen ta, da sauri ta karbe shi tana kallo. Ba shiri ta daga ido ta dubi Habibu. Yaro kamar Ubansa yayi khaki ya tofar. Ya lumshe mata lumsassun idanun sa ya kuma daga mata girar sa daya, ""eh dani yake kama ba da ke ba, kamar ya san ba kya son uban sa"". Ta gatsina baki ta cigaba da kallon babyn tana tazbihi a zuciyar ta. Wata irin kauna ta da da mahaifi na keta ruhin ta da zuciyar ta. Her only relative, her only blood! Ta yaya bazata so shi sama da komai a duniya ba?" Bata yi aune ba ta ji Habib ya kashe su da hoto da camerar wayar sa. "Hararar sa tayi, duk wani abu da zai bakan ta mata ya san shi, yanzun ma Nene na bada baya ya matso gabanta, ""wai sabida kin haihu gabana kike wannan kukan? Yo wane dare ne jemage bai gani ba? Bani Da na nan in ji dumin sa, kin wani kama shi kin kankame kamar ke kadai kika yi nakudarsa"". Ya mika hannu, ta yi maza ta janye dan ta." """Ba zaka dauke shi ba!""" "Ya saki baki yana kallon ta da mamaki, Nene ta shigo jin sautun kukan ta, tace ""lafiya? Ki bashi yaron mana ya yi masa khutbah?""""Nene bazan bashi ba, da na ne nikadai, ba ruwan shi da mu ba ruwan mu da shi"" Nene tace ""Rahinah kin san abinda kike fada kuwa? Mahaifin sa ne fa? Yau na ji karfin hali wai barawo da sallama. Ki bashi yaron nan kafin raina ya baci akan hakan"". Rahinah ta saka kuka sannan ta mika masa yaron. Ya karbeshi da wata irin kulawa tamkar ya maida shi cikin sa. Yayi masa khutbah da sunan da ya zaba masa wato sunan mahaifin Manzo SAW. Ya tauna dabino (ajwa) ya sanya masa a baki, yaron ya hau motsa dan bakin sa gwanin sha'awa, Habib bai san lokacin da wasu irin zafafan hawaye suka zubo masa ba. Ya rungume yaron a kirjin sa. A haka Ambasada ya shigo ya same su. Safinah ta biyo bayan sa dauke da kwandon abinci. Ya yi wa Habib da Rahinah ""congratulations"" sannan ya karbi yaron yayi masa addu'a." "Washegari aka sallame su. Suka koma gida. Tun daga ranar Habib yake zarya, sayo banza sayo hopi, duk don ya farantawa Rahinah. Amma ina! Zuciyarta ta riga ta kekashe akan Habibu, babu wani repenting da zai yi ya burge ta." "Babban tashin haankalin sa shine Rahinah ta gama iddah, gashi yayi alkawarin bazai maida ita ba da amincewa da yardarta ba, shima Ambasada bazai taba amincewa ba yayi forcing din ta akan abinda ta nuna ta gama bashi baya." "Tsayin watanni uku tana shayar da Abdallah kasancewar suna cikin hutun summer. Ta saba da yaron sosai, bata barci sai yana kan kirjin ta, har fargabar komawa makaranta take, don ta san dole zai koma haunnun mai raino. Ita kam ba wanda take jin zata iya baiwa dan ta ya rike mata yadda take ji da abun ta. Ko Habibu bata bari ya dauke shi sai in Ambasada yana gidan yayi mata jan ido. Gabadaya Habibu Nahuche ya gama susucewa, ya fita hayyacin sa don zuwa yanzu ya tabbatar da ya rasa Rahinah." "Lokacin da suka koma hutu Nene tace zata samar mata mai raino, amma Rahinah ta fito fili tace da Nene zata yi deferring karatun ta zuwa shekara ta gaba don ta samu damar kulawa da Abdallah. Da bashi cikakken lokacin ta a lokacin da yafi bukatar hakan." "Nene da Ambasada na jinjina soyayyar Rahinah ga dan ta, amma a zuciyar su suna tausaya mata. Don sun san irin wannan kaunar sai ka samu a karshe iyayen da 'ya'yan basa rayuwa tare. Kaunar tata tayi yawa kuma silence din Habibu na nufin wani abu. Yafi watanni uku bai kara takowa inda suke ba tun wani wulakanci da Rahinah tayi masa, inda tace idan ba ita ce autar mata ba, kuma ba daga kanta an daina haifar mata ba, sannan shi ba maye bane to ya fita hanyar ta ya je ya nemi wani gantalallen auren amma ba nata ba, tun daga ranar bai kara takowa ba, amma sakon shigar kudi basa yankewa a tsakanin su." "A wannan watan da ake ciki ya kammala rubutun proposal din sa, ya karbi shaidar kammala masters din sa, aka yi musu convocation na graduating. A ranar da ya karbi kwalin sa ya hada komai nasa don barin kasar Jamus. In bai yi kuskure ba yau ne Abdallah ya cika shekara daya da haihuwa kuma yana gudun sa ko'ina. Don daga baya ya kan je ganin sa amma iyakar sa falon saukar bakin Ambasada, a kawo masa yaron suyi soyayyar su ta uba da da, ya bashi sayayyar da ya yo masa, ya tafi ya bar shi yana kukan sai ya bi shi. Sun yi wani irin sabo wanda in zaka ga sanda zasu rabu sai zuciyar ka ta motsa, ka kuma tambayi kan ka shin ita Rahina wace irin zuciya gareta? Anya ma tana da tsokar zuciya a cikin kirjin ta?" "A wani zuwa da yayi ganin Abdallah, ba tareda sanin ta ba ya fice da shi a mota, tun safe har yamma, a ranar Rahinah har dan karamin hauka ta yi, Nene na kwantar mata da hankali tana gaya mata bazai ki dawo mata da dan ta ba tunda nono yake sha. Yafendo kam haushin Rahinah ta koma ji sabida rashin kawaicin ta akan yaron, tace ita bata taba ganin mara kunyar bafullatana irin Rahinah ba, rashin kunyar tata shahararriya ce kuma a kan dan fari, inji Yafendo. Idan ta kaita bango kuma ta ce ""kinibabbiya, sanda tasa Uban sa a daki yayi mata cikin sa ai bata ce masa rowar sa zata yi masa ba idan sun haife shi, in da gaske take son yaron ta koma gidan ubansa mana?" Dukkansu basu san inda Habib ya kai Abdallah ya kuma dawo dashi ba. Rahinah kamar ta shide da Abdallah ya dawo don murna. **** "Yayi sallama a falon Ambasada Shehu, shi kuma ya amsa cikin sakin fuska da mutuntawa kamar yadda suka saba a kowacce haduwar su. Har kasa ya tsugunna ya gaishe shi. Shikuma ya soma yi masa fada akan irin ramar da yake yi, da kyar idan yana cin abinci yadda ya kamata. Ya ce ""shi mace bata isa tasa shi a wannan halin ba, don dukkansu daga karkataccen hakarkari aka halicce su. Yana da tabbacin Rahinah zata huce watarana kuma da kanta zata nemeshi ta nemi dawowa dakin ta. Haihuwa a tsakani ba wasa bace. Don haka ya kwantar da hankalin sa." "Habib sai yayi murmushi, his beautiful serene smiles. Ya ce ""ai komai ya zo karshe ranka ya dade, na kammala karatuna zamana a kasar Jamus ya kare. Nazo ne in dauki Abdallah bisa iznin ku, zamu koma gida Zamfara""." "Ambasada shiru yayi, hukuncin da yaron ya yanke yayi matukar impressing din sa. Da gaske gara yayi nisa da Rahinah ya kuma dauke dan sa, watakila hakan yasa ta yi gaggawar gano muhimmancin su cikin rayuwar ta." """Amma ka san mai raba ta da dan nan sai Allah ko? Kuma kana da wadda zata kula da shi kamar yadda mahaifiyar sa zata kula da shi? Idan babu, kai namiji bazaka iya rainon da ba, na gaya maka""." """Mahaifiyata tana raye ranka ya dade, sannan Yayata Badiyya, duk cikin su babu wanda bazai rike min shi kamar koma fiye da yana gaban mahaifiyar sa. Albarkar ku kawai nake bida, da fatan alkhairin ku""." Ambasada couldn't keep his tears wato ya kasa maida hawayen sa. Yayi saurin share su kafin Habibu ya gani. Ya kira Nene ya gaya mata ko me kenan. Itama Nene tafi mijin ta shiga rudun tunanin mai iya raba Rahinah da Abdallah. "Sai ga yaron ya shigo tinkis-tinkis, cikin tafiyar shi mara kwari, ya yi kyau cikin kayan sanyi, yana ganin Babansa ya tafi da gudu ya fada jikin sa. Habib sai ya ga kawai bari yayi amfani da wannan damar, kada dama ta biyu ta sake kubuce masa." """Zan tafi dashi yanzun nan ranka ya dade, ku gafarce ni""" "Nene ta soma kuka, ta saba da yaron ya shiga ranta da zuciyar ta duka. Daga ita har Ambasada aka rasa mai karfin halin hana Habibu wannan danyen aikin, har ya fice falon da yaron a kafadun sa. A lokacin da Rahinah ke dakin ta tayi dai-dai a tsakiyar gadon ta tana ta sharar barci abinta." """""""""" "Koda ta farka bata ga yaron ba bata damu ba, ta dauka yana wasan sa ne a dakin su Ahlan kamar yadda ya saba. Tayi wanka ta ci abinci ta koshi ta janyo littafanta ta karkade, gobe ne zata koma makaranta daga deferring din ta. Saboda haka tana bukatar dumama kwakwalwar ta, duk da cewa a son karatu irin na Rahina ko da bata zuwa makaranta kuma babu jarrabawa a gaban ta bata fasa bitar littafanta ba lokaci-zuwa lokaci." "Amma ga mamakin ta har tayi sallahr maghriba da Isha Abdallah bai shigo ba, bata kuma ji tashin muryar sa ba. Nene kuma tana sassan Daddy a irin wannan lokacin, watakila kuma ya bita can din ne." "Amma da lokacin kwanciyar su yayi bata ganshi ba dole ta fito tana kwala masa kira. Gaban Nene da ke daki ya bada dam! Tayi zamanta a daki ta ki fitowa, sai ga Rahinah ta shigo." """Nene ashe kina nan? Abdallah nake ta nema tun rana rabo na da shi"". Nene ta daga ido ta dubeta idon ta fal tausayi, ta ce ""yaki Rahinah, zo nan mu yi magana""." "Rahinah ta soma shiga tashin hankali, ta dafe kirjin ta da hannayen ta da karfi, ""ba dai wani abu ne ya same shi ba Nene?""""Ba abinda ya same shi Rahinah, he's healthy and vibrant, amma Baban sa ya ce mu gaya miki ya zo ya tafi da shi, idan kin canza ra'ayin ki kan zaman ku tare ku raini yaron tare ki fada masa zai dawo ku koma auren ku!""" "Rahinah ta dora hannuwa aka ta zuba ihu, sannan ta sulale a wurin babu yadda take, tamkar wata mai tashin jinnu ta koma tana kuka tana birgima a kasa tana kiran Abdallah "" wayyo da na, wayyo Abdallah!"" Nene sai da ta firgita" "ta kuma yi nadamar gaya mata ta wannan sigar, ita ta fada ne don Rahina ta ce ta amince zata koma dakin ta su kuma su yi wa Habibu magana ya dawo. Amma a yadda Rahina ta karbi lamarin babu zancen sulhu face Habibu Nahuche yayi mata kidnapping Da." "Data gaji da ihu da birgima hawaye ya hade da majina duk jama'ar gidan na kanta har Yafendo, hatta Safeenah da bata son ta yau ta tausaya mata. Nene na bata hakuri tana gaya mata abu ne mai sauki, ta yarda kawai ta koma dakin ta ta raini dan ta a gaban ta amma ina! Tunanin Rahina yayi fintinkau da tunanin kowa. It goes far beyond mere or casual assumption ta riga ta sanyawa zuciyarta tsanar Habibu kuma bata jin akwai abinda zai kankare wannan" tsanar ban da ikon Allah. "Hanya ta saba babu ko lullubi data faki idon Nene ta shiga sallah, Yafendo ma ta koma daki ta rabu da ita, bata manta nisan dake tsakanin Cologne da Frankfurt ba tafiyar awanni biyu ce kwarara a mota, amma ji take zata iya zuwa a kafa....." Tafe take a gefen titi tana kuka kamar mahaukaciya. Daidai lokacin da anka rufe kofar jirgin Lufthansa. wanda zai "tashi zuwa kasar mu mai dimbin albarka. Ba da jimawa ba ya soma rugugin sa mai gigitarwa kafin ya dauki hanya dodar, ya daidaita sosai, ya cigaba da keta hazo a sararin samaniya......" Ya tafi tareda duk wani farin cikin RAHINAH OMAR.....Ya kassara ta. ya raunata jarumtakar ta. A da tana ganin "ita jaruma ce zata iya fuskantar komai don ta kwaci 'yancin ta wajen Habibu Nahuche. Ashe wani 'yancin ba ya kwatuwa ta karfi duk yanda anka so, Habibu bai shigo rayuwar ta don ya fita a sanda take so ba. Ya shigo ne don ya dai-daita (shattering) farin cikin ta ya raba ta da sauran hope din da ya saura mata a rayuwa......" """Allah ya isa na. Allah ya isa tsakanina da kai Habibu! Kuma ko zan mutu ba aure, ko haka zan kare rayuwata" "single bazan koma gidan ka ba. mugu, magulmaci, maketaci, maha'inci, the rapist!""." "Ita kadai take tafiya tana hada hanya tana sakin zance kamar zautacciya. Habibu ya shammace ta, shammatar da da ace idanun ta biyu ko duk kotun duniya zata taru a kanta bazata raba ta da danta ba. Ai addinin ma da ya bashi wannan damar sai idan dan ya fara girman da zai iya kula da kan sa." """Jahilin banza jahilin hopi, algungumi munafiki, in ba tsoro ba ka dauke shi gabana mana? Ai faduwar gaba asarar namiji ce ""." "Babu wani mummunan suna da bata kira Habibu da shi ba, babu mugun alkaba'in da bata yi masa fata ba. A karshe ta fashe da kuka ta durkushe a inda take, data ga ta dauki hanyar barin Frankfurt kuma tafiya ta ki ci ta ki cinyewa." "Hankalin ta ya fara dawowa jikin ta ta tabbata bazata iya kai kanta ga inda zata riski Habibu ba kuma bata da kudin motar da za ta biya a kaita, haka babu katin bankin ta a tare da ita." Wannan ya tabbatar mata har yanzu tana cikin hankalin ta bakin cikin Nahuche bai haukatata ba. "Zata yi amfani da sauran hankalin da ya rage mata wajen gina rayuwar ta, ta ga cewa bata kamu da ciwon damuwa ba, da wajen ganin cewa bai yi amfani da soyayyar da take wa Dan ta ya karasa cin galaba a kan ta ba, ya kara kassara ta, ta hanyar maida ta kurkukkun auren sa, wanda babu komai a ciki sai biyan bukatar ran sa." "A tunanin ta har abada bata son Habibu, kuma har abadan bazata so shi ba. Abin da bata sani ba SO daban, haka bacin rai daban. Bacin rai is *mortal* and LOVE is *inevitable* . Watakila kuma ganin ta da shi na farko abinda ta ji akan sa wani abu ne daban ba so ba, wanda ta dinga fatan in sun zo mutuwa a jirgi...to Allah ya sa ta mutu manne cikin jikin sa." ***** *NA HUCE..* ..is not for freee. It's 1000 via 3094856450 Sumayyah Kabara Firstbank Shaidar biya 07030137870 ": Habibu Mustapha Nahuche ya sauka a filin jirgin saman Abuja daga Frankfurt ta kasar Jamus da misalin karfe shidda na safiyar Jumaah, yana rungume da dan sa Abdallah a kafadun sa na dama, wanda ke ta barci sadidan cikin gajiya tun suna cikin jirgi." "Kai in ka ga irin rikon tsantsenin da yayi ma dan na sa, gami da tsantsar kulawar da ya ke baiwa kankanin yaron, tsammani za ka yi cikin sa zai maida shi don tsananin So da kauna irin ta mahaifi. Mahaifin ma irin Habibu Nahuche wanda samun Uban da ke son dan sa kamar sa sai an tona. Har ila yau, tsatstsauran rikon da ya yi wa yaron, yana da nasaba da kasantuwar sa cikin fargaba da tsoron ko Raheenah za ta biyo bayan su afujajan kafin su kai ga sauka a kasar su ta haihuwa, Najeriya." "Duk da ya san hakan ba mai yiyuwa bane ba tare da shiri ba. Amma hanakalin sa bai kwanta ba har sai da ya gan shi a filin jirgin saman birnin tarayyah. Saboda yana da tabbacin abu daya: A yadda Raheenah ke son Dan ta, da yadda ta damu da kasancewa tare da shi ko barci bai taba raba su ba, da kuma yadda ya san ta wajen kafiya da naci akan abun data ke so, da bakin cikin shammatar da ya yi mata, ya tabbata za ta iya takowa ko da da rarrafe ne ko da akan gajimare ne tun daga Frankfurt, ta biyo bayan su ta cikin hazo don ta kwace dan ta Abdallah, shi ya sa bai je dauko Abdallah daga gidan Ambasada bama sai da ya kayyade ya kuma kintaci lokacin tashin jirgin su." "A yayin da jirgin ya karci kasa ya bar babban birnin Frankfurt din Jamus, sai ya ji tamkar ya nannade komai na Raheenah Omar daga zuciyar sa, tamkar yadda ake nade tabarma, ya baro shi a can. Ya cire ta kenan HAR ABADA daga rayuwar sa, ya hakura da ita, ko da ita ce autar mata a duniya, kamar yadda babu shi babu kara yin aure a duniya." "Raheenah Omar, ta kassara shi, ta raunata shi, ta ji masa ciwo mai muni a zuciya, bashi da sauran wata soyayya da zai iya baiwa wata diya mace, ta kashe duk wani burin sa a kan yaya mata (ko dama can bai da buri akan su, ita kadai Allah ya sallada zuciyar sa kan ta, ya jarrabce shi akan ta da mafi girman jarrabawa). Juya masa baya da ta yi da sulhun da ya nufa na alkhairi a gare su ya dauke duk wani farin ciki da walwalar sa, ta zagwanyar da farin cikin achievements din da ya dawo da su daga kasar Germany. Wato kwalayen sa guda biyu, masu daraja ta farko." "A kan ta ya san so, a kan ta ya fara so, haka a kan ta ya kare so, kamar yadda daga kan ta ya rufe SO. Ta tafi da dukkan (charming and amiable) Habibu Nahuche bata bar shi da ko guda ba cikin dabiun sa da halayen sa na baya." "Amma a matsayin sa na musulmi kuma haihuwar musulunci, ya san komai muqaddari ne daga Allah watakila Allah ya rubuta iya rayuwar auren da zai yi da Rahinah kenan ta kwanaki bakwai, watakila a rubutun kaddarar su; babu sauran zama a tsakanin su. Hakan ba zai sa ya kasa rayuwa a kasar haihuwar shi ba. Hakan ba zai hana shi godiyar Allah da ya bashi tsatso daga gare ta ba. Zai yi gammo ya dauki rayuwa a duk yadda ta zo masa, ba tare da Rahinah Omar a cikin ta ba." "Abin da zai sa a gaba yanzu shi ne: hanyoyin da zai bi ya maida kobo ya koma dari don tserewa bakin ciki da takaicin duniya, don samawa Abdallah kyakkyawan future, da kuma hanyar da zai bi wajen rainon gudan ran sa (ABDALLAH), zai yi duk yadda zai yi wajen ganin ya bashi rayuwar da ta dace da kowanne Da mai gatan UBA har ma da UWA (tunda Hajiya da Badiya na raye) da kuma ilmi mai inganci." "Ko a lahira ba ya fatan Allah ya sake hada shi ko a hanya da uwar Abdallah.. Infact, abinda ya lura a tare da Raheenah Omar; babu zuciyar imani ko kankani a cikin tsakiyar kirjin ta, babu compassion, babu love, babu affection, ita da sassakakken dutse basu da maraba. Taurin kai ko irin na mutanen farko, she has no love in her talk more of offering it to someone. To Idan so cuta ne. Hausawa suka ce hakuri ma magani ne!." "Zai hadiyi hakurin nan komin dacin sa, komin baurin sa, komin girman sa, zai kuma hada da addu'a da rokon Allah dare da rana kan ya fidda Rahinah da komai nata daga zuciyar sa da rayuwar sa bakidaya." "Daga Abuja shatar karamar mota ya dauka kai tsaye har garin su Zamfara, tun a wancan lokacin jihar Zamfara babu filin jirgi. Ya tsaya ya yi canjin kudin sa a Abuja daga Euros zuwa Naira, ya saya wa Abdallah abincin da zai rika ci a cikin mota har su isa Zamfara." "A lokacin Abdallah ya tashi daga barci sai faman kalle kalle yake na ganin sa a bakon wuri da bakin fuskoki, amma ko tari bai yi da sunan kuka ba, tunda dama ya saba da Baban sa sosai." ****** UNGUWAR KOFAR JANGE ZAMFARA STATE (GIDAN MARIGAYI ALH. MUSTAPHA BILYAMIN NAHUCHE) "Yau unguwar kofar Jange cike take makil da matasa, ana ta hada-hadar siyasa, unguwar ta cakude da hargowar samari da 'yan jagaliyar siyasa masu yawo da fastocin 'yan takara suna musu kamfen. Don haka da kyar direban da ya dauko su ya samu hanya suka kutsa suka isa har kofar gidan da ake kira 'GIDAN NAHUCE'." "Duk inda suka gifta cikin unguwar tasu sai Habibu ya bi wurin da kallo (with nostalgia) da tsananin begen gida, yana mai tuno wani abu na dabdalar kuruciya da ya yi a wurin, shekaru bakwai kenan da barin sa gida idan har lissafin da yake yi daidai ne." "Yau ga shi ya dawo gida lafiya, amma ba shi kadai ba kamar yadda ya tafi, ya dawo ne tare da wani replica din sa (photocopy of Habib Nahuce). Wanda kaddara ta tanadar masa, ta kuma ba shi ba tare da ya tsara ba." "Yana godiya da wannan kaddara tasa da hannu bibbiyu, domin kyautar Da sukutum! Rahma ce daga Ubangijin Talikai. Wadda ba kowa Allah yak e baiwa ba." Hajiyar Nahuce (kamar yadda kowa a dangi dama jamaar unguwar ke kiran ta) tana alwala da buta a gindin famfo lokacin da Habib ya yi sallama. Muryar sa ta dira a cikin kunnuwan ta kamar cikin mafarki. "Sai ta dakata daga wanke kafafun ta da ta ke yi, ta yi tsam! Da ran ta, tana son gasgata abin da ta ji. Kafin ta dago manyan idanun ta wadanda da gani ka san babu tambaya ita ce ta haifi Habibu Mustapha Nahuce. Alamun girma da ya soma kamata bai boye zahirin kamannin su ba na Rumawan Nahuche." "Bude baki ta yi cikin mamaki, da tuajjibi, don ko shekaranjiya sun yi waya dashi Habibun, amma bai ce mata yana tafe ba." """Wa nake gani kamar Habibuna? Habibullahi?""" "Duk yadda Da ya kai ga canjawa, cikin halin jin dadi ne ko akasinsa, to fa Uwa ba ta kasa gane abinta. Don haka komawar Habibu kyakkyawan Bajamushe kuma gogaggen bakin bature bai hana Uwarsa Hajiya Kaltume gane shi ba, daga kallo na farko da ta yi masa." "Har gabanta ya karaso ya sunkuya, cikin gajiya, sannan ba tare da ya ce komai ba ya mika mata Abdallah da ke hannunsa makale a kafadun sa. Amma sai Abdallah ya ki zuwa, ya makale sosai a jikin Baban nasa." Jikin Hajiyar Nahuche ya hau rawa da makyarkyata. """Ni Kaltume Nahuce! Habibullahi ina ka samo yaro mai kama da kai haka???""" "Ba jikin ta kadai ba, hatta muryar ta Hajiya karkarwa take yi." "Magana ya shiga yi wa Abdullah da harshen German""Abdallah Sie istmeine Mutter, geh zuihr (she's my mother go to her)"". Yaron ya make kafada cikin rashin yarda, tare da sake makalewa cike da tsoro da kyuya a jikin Abban sa." Yara suka soma shigo da jakunkunan Habibu manya-manyan trollies. Haj. Kaltume gabadaya mamaki da tsoro ya hana ta kokarin karbar yaron da yake ta faman son ta karba. Sai ta fara hawaye daga tsaye. Sakamakon abinda zuciyar ta ta hasaso ta kissimo mata. """Sai ka fara gaya min ina ka samo shi tukunna zan karbe shi, Habibu Allah ya sa ba shegensa ka yi ba a can kasar masu jan kunne"". Idanunta na zub da hawaye suna nuna tsananin kidima da fargabar da ta ke ciki." Da sauri Habib ya hau girgiza mata kai. Shima nasa idnun suka kawo kwallah. """Wannan ba rainon da ki ka yi min ba ne Hajiyata, ban taba yin zina ba, ban taba kusantar ta ba, tun ban san ma'anar ta ba kike nusar da ni illar ta, kuma har in mutu ba zan yi ba insha Allahu." "Ina baki hakuri Hajiyarmu, domin hakika na miki laifi, (na yi aure a Jamus ba da saninki ba)"". Dogon Salati Hajiyar Nahuce ta saki," """Aure kamar ya ya?""" "Habibu bai bata amsa ba, sai ya kara mika mata Abdallah, wannan karon ba musu ta sa hannayen ta biyu ta karba, tunda dai ta samu tabbacin ba shegen sa akai ba. Sannan kalmar aure ta gitta. Komai zai biyo baya a ganinta zai kasance da sauki." "Daki suka shiga, Habib ya shigo da jakunkunan sa, kafin ta yi komai flask ta jawo wanda dama ba ta rabo da kunun tsamiya a cikin sa, ta zuba a kofi ta saka dan suger ta motsa ta soma kokarin baiwa Abdallah." "Kasancewar Yafendo tana ba shi ya san kunu sosai, ya karba yana sha, ta dora shi a cinyoyinta tana rirriga shi, sannan ta maida hankalinta kacokam a kan Habibun, wani irin mabayyanin bacin rai kwance-kwance baro-baro a kan dattijuwar fuskarta." """Yanzu Habibullahi wuyan ka har ya yi kaurin da za ka yi aure kan gaban kanka babu sanin kowa naka?" "In Shafa'atu ce ba ka so ai ba sai ka yi haka zan san ba ka son ta ba, wane irin aure ni 'ya su sai ka ce wasan yara? Ina uwar dan da za ka dauko wannan dan tatsitsin yaron tun daga wata uwa duniya kai kadai?""" "Habibu Nahuche, bai taba barin weakness din sa ya bayyana a gaban kowa ba, amma wannan UWA ce MAHAIFIYA ce, kafadar da kowanne dan Adam ke iya sauke damuwar sa babu haufin komai. Don haka sanda ya fara hawaye bai san sun zubo ba, dacin tuno kiyayyar Rahinah gare shi, sai da ya ji saukarsu a kan kundukukinsa, da damshinsu a kan fuskarsa." """Na yi duk iya kokari na a kan ta so ni, ta zauna da ni mu raini dan nan da Allah ya bamu tare abu ya faskara. Ban san meye aibu na har haka ba da Rahinah ta ki ni. A karshe mun rabu, rabuwa ta har abada, ni kuma na dauke Dan ba da saninta ba, amma marikanta sun san na dauke shi""." "Ya kwashe gaskiyar komai, har sanadin auren ba-zatan ya gaya mata, sai dai wani sirrin ai bai faduwa, balle sirrin aure. Ya tsaya ya kafe a kan Raheenah ba ta sonsa kawai, sabida ya aure ta baa hannun iyayen ta ba, yace aurensu kaddara ne kawai da rabo rantsatstse daga Allah." "Haj. Kaltume ta rasa abin da za ta ce, amma sai ta ji ya fi mata a kan a ce Habibu zina ya yi ya kawo mata yaron nan. Ta rungume Abdallah sosai a kirjinta, wanda zuwa lokacin ya samu barci yana sauke ajiyar zuciya." "A daren ranar ta kira Badiyya wadda ke aure a garin Kaduna, ta ce duk abin da ta ke ta bari gobe ta zo Zamfara maganar ta fi karfin waya." "Sannan ta sa almajiri ya share wa Habibu dakinsa, ya wanke masa toilet dinsa, sannan ya shigar masa da dukkan kayansa." "Girki na musamman ta yi musu, tuwon shinkafa da miyar taushe da naman saniya zuku-zuku a ciki, ta yarfa man shanu sannan ta hadawa Habibu kunun zaki kasancewar yana son shi sosai mutumin sa ne, amma na gasara ziryan ba na farau-farau ba." "Da dare ya yi Abdallah ya rikice kan bai kwana tare da Hajiya, sai Momin sa, don haka tare suka tafi dakin sa dake zaure yana ta rarrashin sa, sai da ya yi barci ya dauko shi ya maido wa Hajiyar shi." "Hajiya Kaltume tana sallahr dare kamar yadda yake a aladar ta, jefe-jefi tana juyawa tana kallon kyakkyawan yaron dake barci cikin nutsuwa a gefen ta mai tsananin kama da Habibu, tamkar Habibun a lokacin da yana kamar sa, kaunar yaron na dada shiga ran ta, a cikin kowacce sujjadah data yi tana yi masa addua Allah ya raya shi rayuwa mai tsayi da albarka." "Cikin wannan daren mai dimbin tarihi a rayuwar Habib da Raheenah. Dukkan su babu wanda ya runtsa. Ya fidda layinsa na kasar Jamus ya karairaya shi, ya taune shi ya zubar, ya saka MTN NG da ya saya a filin jirgin saman Abuja. Yana fatan yadda ya karairaya shi haka ya zubar, zuciyar sa ta karairaya Raheenah Omar ta zubar, da duk abinda ya shafe ta." "Amma ko da ya so yin barci, sai barci ya ce dauke ni inda ka ajiye ni. Shin ko yaya rayuwa za ta ci gaba musu shi da Abdallah? Shi maraicin matar da yake so daya da daya a duniya? Abdallah maraicin uwar da ya budi ido da ita?" "Wata Tambaya ce mai wuyar amsawa farat daya, da ya kasa amsawa kan sa, ya ce bai son ta ma ya san wannan yaudarar kai ne. Raheenah Omar, ta shigo rayuwar sa da wani irin karfi, ta yi tasiri mai yawa a cikin ta cikin auren da bai gaza kwanaki bakwai ba. Tasirin da kafin ya yi nasarar cire ta kwata-kwata, shi ma ya san zai sha wuya, kuma abu ne da ba zai tabbata a lokaci guda ba." "But gradually, by trying to follow the path of reality; yana fatan canzuwar kaddararsu, yana fatan Raheena ta bar zuciyarsa ta sha iska haka, ta bar kwakwalwarsa ta sarara, ta bar gangar jikinsa da ruhin sa su huta. Ta bar sababbin abubuwa da suka fi ta muhimmanci su shigo." "Ba shi ya iya runtsawa ba sai da ya dawo masallacin Kofar Jange sallar asubahi, sannan ne barcin gajiyar da ya tara ta zaman jirgi da shirye shiryen dawowa da ya jima yana yi ta karkashin kasa suka taru suka danne shi bakidaya." ****** "Kukan Abdallah ne ya tashe shi wajejen takwas na safe, ya karade gidan da kuka yana kiran ABBANSA da MOMIN SA... cikin harshen Jamusanci. Zuciyarsa ta yi wani irin karyewa, anya cikin hukuncin da ya yanke babu zalunci a ciki ga yaron da ma uwar kan ta?" Yanzu haka yaron zai tashi bai san mahaifiyarsa ba alhalin tana raye a kololuwar duniya? "Da tsananin mutuwar jiki ya fito tsakar gidan hannayensa zube cikin aljihu. Ya zubawa yaron ido daga bakin kofar shigowa cikin gidan. Idanun sa sun kada Abdallah na ganin sa ya taho da mugun gudu ya rungume shi, sannan ya soma gaya masa cikin harshen da yafi iyawa ya maida shi gun Mummyn sa, tashi Mummy din ba wannan ba, yana nufin Hajiyar sa." Hajiya Kaltume ta fito daga daki tana ta mita. """Dan nema rigimamme, sakaltacce, ni bana son shagwaba ko kadan, da alama gidan ku can sun gama sangarta ka, in ba haka ba ta ya ya gotai-gotai da kai za ka saki kashi daga tsaye? A ba ka foo ka ki hawa?""" "Murmushi Habib ya yi, shima ya san da gaske gidan Ambassada sun sakalta Abdallah, ya karaso inda ta ke yana dauke da Abdallahn." """Ke da maigidan naki za mu gan ku a rana, Maman shi pampers ta ke saka mishi ba ta dora shi a wani foo""." "Hajiyar Nahuce ta ce, ""Au? Tunda irin 'ya'yan Badiya ne, to ba zan iya ba, ta zo ta dauki abin ta (Badiyar), su ma haka ta sangarta su da kin hawa foo, yaro dan shekara biyar sai ya saki kashi cikin auduga, mu ba haka iyayen mu suka raine mu ba, to ni ba zan iya wankin kashi a cikin pampers ba da girman yaro da komai""." "Karshe Habibu ya je ya siyo pampers gari guda ya kawo mata, yana rokon ta kan ta lallaba Abdallah, a hankali zai koyi hawa foo din. Shi zai dinga yi masa tsarkin ya fidda pampers din. Hajiya sai ta ji su duka sun bata tausayi." "Sai wajen la'asar Aunty Badiyya ta iso daga Kaduna, Aunty Badiya ba ta kama da Habeebu sam, bazaka ce ma cikin su daya ba, don ita mahaifin su sak ta dauko, fara ce ita Barumiyar Nahuce, sabanin Habeeb da yake wankan tarwada." "Aunty Badiya 'yar boko ce sosai, domin kuwa (PHD holder) ce. A wannan lokacin ita ce mataimakiyar Provost ta (Kad-Poly), yayin da mijin ta babban ma'aikaci ne a Abuja, sabida aikinta ta ke zaune a Kaduna sai karshen mako yake zuwar musu." "Yaran Aunty Badiya hudu ne duk maza ta karshen ce kawai mace, Zarah, wadda ba ta fi sa'ar Abdallah ba." "Zuwan Badiya gida da ganin kanin ta da ta yi da Da, da labarin da ta tsinkaya daga bakin mahaifiyar su ya bata mata rai ba kadan ba." "Ta yi fadan kamar ta yi ya ya! A karshe ta ce, ""Allah ya kara da ba ta son naka, Allah ya kara karawa, yanzu ai sai ka hakura ka zo ka auri mai son ka (tana nufin yar uwar sa Shafa'atu)""." "Ita babban bacin ran ta yadda ya boye musu maganar auren nasa a Jamus, kamar wani wanda bashi da kowa, amma Hajiya Kaltume da ta ga fadan Badiya ya yi yawa, duk hakurin da Habibu ke ta bata ta ki sauraron sa, sai ta ce." """Maman Zarah, hakuri za ki yi mana, laifi kam ya riga ya yi sai dai tunda ya bada hakuri kuma ya ce ya yi ne don ya ceci kansa daga aikata zina a can, ai ina ga wannan ya isa hujjah, ni tuni na dauki kaddara." "Yaro Allah ya raya mana shi, Ya sa Mahaddacin Alqur'ani ne""." "Badiya ta ce ""Hakuri na daya ne Habibu ya auri Shafa'atu, ban ce ta rike masa yaro ba, ni zan hada da na waje na in rike, amma auren sa da Shafa'atu ya zama tilas""." "Habib da yake neman a yafe masa, ba abinda ba zai yi ba a lokacin. Ya ce da Yayar sa Badiyya ""ki bari na gama NYSC sannan a yi maganar auren, ni yanzu da ba ni da abin yi, da me zan yi auren?""" "Badiyya ta ce, ""A can Jamus da me ka yi auren? Cewa nake karatu kake a inda baka da kowa ma? Balle anan da mu zamu rike maka matar. Ka yi auren ka dandani dadin sa da rashin dadin sa ne zaa kyale ka ka ci gaba da zama a haka?" "In dai Shafa'atu ce ba bakuwar zafi ba ce, za ta iya zama a gidan nan tare da Hajiyar mu, sai a gyara muku sassan Baba""." "Mikewa ya yi daga gurin yana kakkabe rigar sa, har da kunkuni kamar kuturu yana fadin." """Ke za ki dinga ciyar min da matar? An ce miki a Jamus ko kai dalibi ne kana rasa aikin yi da zai rike iyali? Nan kuwa fa? Ai ki ji da kan ki kawai Yaya Badiya, ki kyale ni in nemi kobo. In gwaninta za ki min, kawai ki kular min da Abdallah""." "Yaron da ya riga ya shige zuciyar Dr. Badiyatu Nahuce farat daya, har fiye da son da takewa Habibu, ta kara rike shi sosai a jikin ta tana hararar Habibu, a lokaci guda tana mamakin irin karfin jinin sa. Yaro kamar Habibu yayi kakhi ya tofar, bai da maraba da shi a lokacin da yana kamar shi. Addu'a ta ke cikin ran ta Allah ya ba ta lafiya da tsawon ran kula da Abdallah, kamar, ko ma fiye da yana gaban mahaifiyar shi." A washegari ta juya da Abdallah gidan ta a Kaduna. ****** NA HUCE Is not for free. It's 1000 via 3094856450 Sumayyah Kabara Firstbank Shaidar biya 07030137870 *SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI) 07030137870* PAID BOOK "Ba jimawa da dawowar sa ya yi registration na tafiya hidimar kasa. Aka tura shi Kwara State, ya tafi ya bar Abdallah hannun Yayar sa Aunty Badiya." "Haka yaro Abdallah ya rayu karkashin kulawar Kakar sa Hajiyar Nahuce da Yar mahaifin sa Dr. Badiyatu Mustapha Nahuce, suna zuwa Kaduna ta sanya shi a Kindergarten na (Kad-Poly) tare da diyar ta Zahrah, kullum sai ta sauke su sannan ta wuce aiki." "Sha biyun rana ta sa masinjanta ya dauko su, a can ofis din ta za su yi ta wasan su a gaban ta har ta gama abin da za ta yi su koma gida." "In aka yi hutu kuma ta kawo shi Zamfara ya yi hutu a hannun Hajiya Kaltume, sabida wayon yaron da kokarin sa a karatu da hikimar sa da saurin shiga rai a wajen malamai (double promotion) aka yi ta yi masa ya koma Nursery 3 daga Nursery 1. Sanan duk karshen zango shi yake zuwa na daya a aji, kuma sai ya dawo da prizes gida. Dr. Badiya (is highly proud of her son Abdallah) tana fada a koda yaushe. Yana tuna mata da kuruciyar Abban sa shima haka yake da yana kamar sa. Duk inda yayi karatu sai yayi tambari." "Zuwa wannan lokacin Abdallah ya manta da Raheenah, ya dauki Badiya a matsayin mahaifiyar sa. Hajiya Kaltume da yake kira ""Granny kuma ya san Kakar sa ce wadda ta haifi mahaifin sa. Yana kara girma yana fahimtar alaqar sa da kowa." "Tsakanin shi da 'ya'yan Aunty Badiya ba za ka taba iya bambance wanne ne nata wanne ne na kanin ta Habib ba. Yayyen nasu Musaddiq, Mubaraq da Mu'allim suna kula da shi sosai shi da Zarah, don kuwa Uncle Habib (yadda suke kiran Habibu) ba su ajiye shi nan kusa ba, suna matukar son shi, sabida yadda yake nuna musu kauna shima duk lokacin da ya zo ganin Abdallah daga Kwara. Kaunar jini ce ta cakude da kauna ta musamman wadda suke yi wa Uncle Habibu, ta shafi dan sa Abdallah. Ko kuda in suna da iko ba zai sauka akan Abdallah ba." "A haka ya kammala NYSC, sai Aunty Badiya ta karbi takardun sa ta baiwa Baban Musaddiq ya tafi da su Abuja don nema masa aikin yi." "Kasancewar Baban Musaddiq babban ma'aikaci ne a Federal Ministry of Commerce and Industry wadanda Federal Govt. ke damawa da su a lokacin. Ga shi ya san manyan ma'aikata a can Abuja domin ya dade yana aiki, sai bai sha wahalar samar wa Habibu aiki ba tunda abu ne na wa ka sani, gashi da (qualifications) na Cologne University, ya samu aiki mai gwabi a babban Hotel din NICON NOGA, a lokacin shi ne hotel din da babu na biyun sa a Nigeria. Kuma fannin da Habibun ya karanta kenan wato (Hotel Administration)." "Habib ya dade a Nicon - Noga, matsayi iri-iri a ya rike a cikin ta, daga karamin matsayi zuwa sama, promotion kan promotion akai-akai. Wani irin mutum ne shi mai nasibi akan duk abinda ya sa gaba. Ba don haka ba manyan mukaman da yake samu akai-akai a NICON cikin 'yan shekaru kalilan da bai isa ya same su a yan shekarun ba. Don akwai wadanda suka fi shi jimawa amma basu kawo matakin shi ba, abin kuma har da kwarewa da baiwa ta daban (exceptional talent) da Allah ya bashi." "A lokacin ne aka bude babban hotel din Najeriya watau TRANSCORP HILTON inda Habib da wasu daga cikin manyan ma'aikatan (Nicon - Noga) suka samu karin matsayin komawa (Transcorp - Hilton), inda Habeeb ya rike mukamin mataimakin manager, ba kananan kudi ke shigo masa ba domin kuwa a Nigeria gabadaya babu hotel din da ya kama kafar (Transcorp - Hilton) a birnin tarayyah." "Yawanci turawa, larabawa da sauran jajayen kunnuwa ke sauka a can idan suka zo Nigeria kan harkokin su, sai ko kusoshin kasar mu, da manyan 'yan kasuwanni, da ke yin conferences acan." ****** "NAHUCHE HOTELS, ZAMFARA" "Idea din mallakar hotel nasa na kansa ta dade da ginuwa a ransa. A hankali yake saving, har ya tada tubalin ginin karamin gidan saukar baki 'guest inn' a kasar shi ta haihuwa wato ZAMFARA." "Da nan ya fara kamar da wasa, sai gashi Allah ya sa masa albarka da ilhama a ciki, ya fadada guest inn din ya maida shi babban hotel mai zaman kan sa a jihar ta Zamfara cikin Gusau." "Sabida yadda ba ya tsauwalawa ne da kuma kyawun hotel din gami da nagartar ma'aikatan sa ya sa ya yi attracting customers da masu kudin Zamfara nan da nan, inda ya fara da yi masa branch a birnin Tarayya, daga nan sai Lagos, inda can ne ya zamo (headquater) na (NAHUCHE GROUP OF HOTELS)." "A cikin shekaru goma da dawowar sa daga kasar Jamus ya mallaki hotels manya-manya a duka manyan jihohin Najeriya. Ba ya wata sana'a sai wannan wadda ya karanta yake kuma da experience a kai, wato (Hotel Administration), ya san duk wata hanya ta bunkasa hotels (gidan saukar baki) a zamanance daga (Cologne) inda ya yi digirgiri da masta." "Daga nan ne kuma 'yammata suka ce salamu alaykum, ta hanyar budewa Habibu wutar so da kokon bara, kamar za su cinye shi danyen sa, ga kuruciya ga rufin asiri ta ko'ina ya samu, amma babu iyali." "Ga kyau na Zamfarawan usli tushen garin Nahuche. Ko marmarin aure ba ya yi, ba abinda baa cewa a kan sa a dalilin rashin aure, lokacin da sunan sa ya fara karade kafafan yada labarai a matsayin (Young Nigerian Hotels Owner) wasu ma sun ce neman maza ya hana shi aure." "Irin wadanan miyagun maganganu da aka soma yi a kan Habibu Nahuche suna dawowa kunnen Yayar sa Badiya, kasancewar ta mai taammali da mutane daban-daban, ta sha titsiye shi ta ce, sai ya gaya mata ko ba shi da lafiyar da zai iya aure ne?" "A irin wadannan lokutan, Habib Nahuche, dariya yake yi sosai, ya cewa Badiya," """Ba ni da lafiyar ki ka gan ni da Da na mai tsananin kama da ni?""" "Sai Badiya ta ce cikin kankantar da murya," """To Habibu ko dai da gaske kana deviating ne saboda bakin cikin Maman Abdallah ta ki ka?""" "A wannan karon ma murmushi ya yi wanda Badiya ta kasa fassarawa, yayi kasa da kai, sannan nan da nan murmushin ya bace daga kan kyakkyawar fuskar shi, sabida wannan ba shine karo na farko da yaji hakan ba (ana masa mummunan zargi), ya ce cikin Bazamfariyar Hausar shi mai dadin sauraro;" """Wannan kuma ai tsakkanin bawa... da Ubbangijin sa ne""." ***** "Zuwa yanzu kam Shafa'atu 'ya'yan ta biyar kenan, tana auren ta a Talata-Mafara." "Da farko ta gwada jiran sa kamar yadda Badiya ta kwadaitar da ita har ya gama NYSC ya samu aiki, amma tunda ya sa kafa a (Nicon - Noga) ba ta kara jin komai a kan sa ba. Bata kara jin duriyar Habibu ba. Zumunci ma ya yi rauni tsakanin iyayen su a dalilin hakan don iyayenta sun dauki laifin komai sun aza a kan Hajiyarsa, a ganinsu da ta takura masa da tuni ya auri Shafa'atu." "Ita kuwa Hajiya Kaltume kullum Allah ta ke kai wa kukanta a kan auren dan ta Habibu, shi kuma ta bar wa zabi. Baa shaidar dan yau, amma ita kam ta shaidi nata. Sabida yawan ibada da tsaida sallah yana hani dga aikata alfasha wanda kuma kowa ya san dabiun Habibu kenan, ga yawan azumin tadawwui. Ta dade da sanin akwai abinda ya kulle a zuciyar sa tun daga kan Maman Abdallah. Wadda ita tasa ya ki jinin mata. Duk ya hada su yayi musu kudin goro. Har ila yau, Hajiya Kaltume ta gama fahimtar ba ya son Shafa'atu, in ta takura masa ya aure ta zaa bata goma ne daya ba ta gyaru ba. A lalata zumunci kuma auren bazai dore ba. Sannan ta fahimci baya yin wani abu na banza duk da ba" "tare take da shi ba a yawancin lokuta amma ta fi kowa karantar sa, bata taba jin yana waya da 'yammata ba. Don ba wayar da ba ya iya amsawa a gaban ta." "Ta fahimci in ta takura masa ya auri Shafa'atuba zai kula da ita ba don kwata-kwata yanzu hankalinsa bai kan mata. A duniya abu uku ya sanya a gaba; (bautar Allah da neman kudi, sai rainon dansa Abdallah, Dan da Raheenah Omar ta haifa masa)." "Ita kan ta Dr. Badiya ba karamin gata ta ke samu a wurin Habibu ba, duk da kasancewarta mai albashi mai tsoka nata na kanta itama, to balle kuma mahaifiyarsa da Dansa. Wadanda duk abin da ya samo nasu ne, a cewar sa su yake nemawa. Duk fadi-tashin sa a rayuwa sabida su ne. Sau uku a jere Haj. Kaltume da Badiya na tafiya aikin Hajji duk shekara." "Tuni ya buge gidan su an zuba gini na zamani na gani na fada, kai ka ce gidan wani minista ne ba gidan tsohuwa Kaltume matar marigayi Bilyamin Nahuce ba, duk fadin unguwar Kofar Jange babu gida mai fasali da zubin zamani da ya kai kwatankwacin GIDAN NAHUCE." "Ga maaikata rututu Habibu ya zuba mata. Kullum zaka sameta zaune a tankareren falon ta akan kilishi mai taushi tana lazumi tana ibadah, don a cewar ta su kadai suka rage mata yanzu, sai ko ganin auren Habibullahi. Hajiyar Nahuche ta zama wanke goma ka tsoma biyar. Jawur da ita, tsafta da naira sun kama jikin ta. Ga hasken rikon addini. Gidan ta kullum cike da yan cin arziki daga jamaar unguwa dana garin su Nahuche." "Daga baya Hajiya Kaltume ta soma karbar tayin hotunan 'yammata da ake kawo mata daga Nahuche da Bungudu, sannan yayan masu da shi anan Zamfara da iyayensu ke son hada auren 'ya'yansu da Lucky Habibu Nahuce duk haka ake kawowa Hajiyar Nahuche. Eh, wasu kan kira shi 'Lucky' sabida kafin ka samu mutum mai sa'a a kan duk abin da ya sa gaba kamar Habibu Mustapha za a dade." "Komai ya sanyawa hannu na harkokin sa sai ya zama kamar magic sai ka ga ya bunkasa ya shahara ya yi albarka cikin dan lokaci. Wannan kuma albarkar bakin UWA ne da addu'o'inta da ba sa yankewa a gare shi. Kullum Haj. Kaltume a kan dugaduganta take kwana sallah, kuma duk yawancin addu'o'in ta akan Habibu ne." "Nasarar rayuwa, kariya daga sharrin Shaidan, albarka a dukiyar sa, da mata tagari (wadda zata kaunace shi saboda Allah ba don dukiyar sa ba) su ne abubuwan da kullum take roka masa." "Hotunan 'yammata iri-iri 'ya'yan manya a garin Zamfara da garin Bungudu da Nahuce an sha kawo wa Hajiya Kaltume, amma a duk lokacin da ta dumfari Habibu da su ko dubawa ba ya yi zai ce," """Ki yi hakuri Hajiyata, ni na riga na gama aure a duniya""." "In ta takura masa kan sai ya duba kuma sai ya fara mata yan kanan kwallah, da dole zata mayar dasu inda ta dauko cikin mutuwar jiki. In ya so tsokanar ta kuma sai yace." "Hajiya kada ki damu akwai (hurul eeni a aljannah, inshaAllahu)." "Bata taba daukar maganar sa a bakin komai ba, face lokaci ne bai yi ba, in lokacin yayi shi da kan sa zai kawo mata matar da yake so, bacin ran uwar Abdallah (Rahinah) ta yi amanna da cewa shi ke walagigi da shi har zuwa lokacin. Ya ke ganin don ita ta ki shi, ba zai samu mai kaunar sa ba. Ko kuwa an ce ita ce autar mata da za'a debewa sauran mata tsammani a kan ta??? A bisa wannan dalilin Hajiyar Nahuche ta ji ta fara tsanar wannan Rahinah duk da bata taba ganin ta ba ko a hoto." ****** "*MUTANEN JAMUS (BAYAN BARIN HABIBU FRANKFURT).* Tun daga lokacin da Habibu ya dauke mata Abdallah, rayuwa bata kara komawa yadda ta ke a baya ba ga Raheenah Omar. Sauran kadan ta zama depressed wato ciwon damuwa ya kama ta. Ita kadai sai ka same ta a dakinta tana magana cikin safah da marwah, karatu ta daina fahimtarsa kwata-kwata, zuwa makarantar tana yi ne kawai bisa tursasawar Nene da Ambasada Shehu, amma ta kasa concentrating a kan komai. Komai ya fice mata a ka. Hatta kasar Jamus bakidayan ta." A jarrabawar karshen zangon da suka yi Ambasada Bichi bai ji dadin sakamakon Raheenah ba ko miskla zarrah; ta fadi courses har biyar. Don haka ya kira ta falonsa don su yi magana ta Uba da Da. """Rahinatuh. Ina son sanin hakikanin abinda ke damun ki? Akalla in ban miki maganin sa ba a matsayina na Uba zan baki shawara wadda nake ganin ta dace. Wannan wane irin mummunan sakamako ne nake gani haka?""" "Raheenah ta share zufar da ta jika goshinta, cikin rauni da karaya ta ke wa Baban ta Ambasada magana. Ba tare da ta san maanar abinda take furtawa ba." """Ni kai na Daddy (ban san hakikanin abin da ke damuna ba), rayuwar ce kawai na gaji da ita. Na fi so in mutu in huta. Ji nake kamar ni kadai na yi saura a duniya, kamar rayuwata ta zo karshe........." "Kamar babu wani sauran farin ciki da zan cimma a karshen ta, kamar duniya ta ta kare. Ji nake kamar wani tsuntsu ko kuma shaho ya zo daga sama ya tattare dukkan farin ciki na da burika na ya tashi sama firrr! Da su""." "Wani irin murmushi Ambasada Shehu ya yi, irin nasu na manya da suka karanci halayyr dan adam, kafin ya ce," """Kuma wannan TSUNTSU ko SHAHO ba kowa ba ne, HABIBU ne!!!." He ran away with all your hopes and happiness... (ba tare da sanin ki ba ya tafi da dukkan fata da farin cikin ki). "Habibun da ki ke gujemawa da gangan, amma ruhin ki da zuciyar ki na tare da shi da Dan da ki ka haifa masa.." "It's either two options; ko dai ki yi hankuri ki ba wa zuciyar ki abin da ta ke so don samun farin ciki da kwanciyar hankali, ko kuma ki ci gaba da horar da kan ki da kan ki a bisa kuskuren ki." "Allah Ubangiji mai afuwa ne, Annabi (S.A.W) mai afuwa ne. Allah Ubangiji kuma yana son masu afuwa." "Amma Rahinatu ke kin ce ba za ki yi afuwa ga Habibu ba a kan kankanin laifin da ya yi miki. Wanda ku kadai kuka san abin ku. Don haka sai ki koya wa zuciyarki juriyar rashin su, in har kina nan a kan bakanki, ki fuskanci rayuwar da ke fuskantar ki." "Kina da babban aiki a gaban ki wanda ba ya son damuwa da rudani (karatun ta). A matsayi na na Baban ki, shawarar da zan ba ki ita ce ki koma addu'a, idan rabuwar ki da Uban dan ki ita ce mafi alkhairi, Allah ya ba ki zuciyar dangana." "Idan dawowar su cikin rayuwar ki shi ne alkhairi Allah ya sanyaya miki zuciya su dawo cikin rayuwar ki ba da jimawa ba""." "Raheenah ko kadan ba ta son yarda da abin da Ambasada ke fadi, wai- wai wai Habeebu ne tsuntsun da ya tashi da farin cikin ta. Za ta fi yarda in ya ce rashin dan ta Abdallah! Don haka ba ta ce komai ba, amma tana can tana kokawa da zuciyar ta a kan shin abin da Daddy Amb. ke fadi shi ne hakikanin damuwar ta ko kuwa?" Wato rashin Habibu Nahuce??? "Idan kuwa shi ne zuciya ba ta yi mata adalci ba, domin Habeeb bai bar wani (green momeries) ba cikin rayuwar ta da ya cancanci ta bishi da kewa, sai (black memories and black episodes...) wadanda da su ne kullum take kallon sa, suka kuma sa ta kasa bashi gurbin masoyi, wane irin rashin adalci na zuciya ne zai sa rashin sa ya dagula lissafin ta har haka, ya hana ta ci gaba da harkokin rayuwar ta?" "Daga wannan ranar Raheenah ta yi aniyar fighting da zuciyar ta, mai neman kai ta ta baro, har sai ta manta da Habibu da Dan sa, dan da bata taba zaton ma za ta so ba har sai bayan da ta haife shi. Wannan wani kudiri ne da ta ke fatan Allah ya ba ta nasara da iko a kan sa, wato gusar da duk wani burbushi da Habibu ya bari cikin rayuwar ta." "Daga wannan ranar, Rahinah Omar ta maida hankali a karatunta, don in ba karatun ba wa za ta kama? Ranar da babu su Ambasada? Habibu ko sunan garinsu ba ta sani ba, balle inda ya fito, bare ta sa ran watarana za ta je ta kwato danta." Abin da ta sani a kansa kawai shi ne dan kasarta Nigeria ne. Bayan wannan bata san komai akan sa ba. Sannan Nigeria kasa ce ba gari ba. "Da sabon zango ya zagayo. Ta sake maimaita takardun da ta fadi, kuma cikin ikon Allah ta haye wannan karon. Da taimakon nasihohin Yafendo, Ambasada da lallashin Nene Balki." *NA HUCE.* ...is not for free. It's 1000 via 3094856450 Sumayyah Kabara Firstbank Shaidar biya 07030137870 ": Ana gab da hutun summer Ambasada ya karbi passport din ta ya hada da nasu don yi musu shirin zuwa Nigeria hutu, kamar yadda suke yi duk karshen shekara." "Ta shiga dakin Yafendo a wani dare, sai ta tadda ita tana daure kaya. Tsibi-tsibi tana daurewa tana ajiyewa kamar in ta tafi ba za ta dawo ba. Raheenah ta ce," """Yafendo? Wannan kaya ina za ki kai su haka? Ai sai ki karar mana da kilo""" "Yafendo ta ce, ""Duk tsaraba ce da na ke tarawa tsayin shekara guda ta mutanen Bichi. Sannan ke ma na yi sayayya ta musamman don ki kai wa 'yan uwanki in Allah ya sada mu da su""." "Wani dadi ya ratsa Raheenah, sai ta ji tamkar Dadanta ce a tare da ita. Allah ya sa wadanda Yafendo ke hasashe su kasance su ne dangin nata. Da duk wasu matsaloli da damuwoyi sun karasa zama tarihi a gare ta. Habibu ya je ya dafa dansa ya cinye." "A washegari ita ma ta hada nata kayan, amma ba ta dauki sun fi kala bakwai ba. Don Daddy ya ce ita sati daya za ta yi ta dawo ita da Safeenah don ba ya so gidan ya zauna babu kowa. Safeenah kuma ba ta son zaman Bichi ko kadan, a cewarta zafi ke damunta." "Daddy Ambasada dan garin Bichi ne ta Jihar Kano, kowa ya san 'yan Bichi 'yan boko ne na ga-ni-kashe-ni. Gidan iyayensa har gobe yana garin Bichi, suna da family mai tsohon tarihi." "Sun sauka a Kano da daddare, daga filin jirgi wadanda suka zo tarensu kannen Ambasada ne su uku suka dauke su suka wuce dasu Bichi." "Kwanan su uku suna zaga dangi Yafendo da Nene na rabon tsaraba, suna kuma shan tambaya a kan bakuwar fuska Raheenah, cewa ta ke Daddy ke rikonta a Jamus, karatu ta zo. Sai da suka kwana hudu Yafendo ta kira Muqaddas kanin Daddy kuma cousin a gare shi, ta ce ya shirya mota gobe zai kai su Girei ita da Nene da Raheenah, Daddy Abuja zai wuce akwai taron da zai halarta na Ambasadodin Najeriya kafin nan da dawowar su daga Girei din." Ambasada ya yi musu fatan alkhairi na Allah ya sa a dace ya kawo kudin fetir da na kashewa ya babbasu. ****** "GIREI, ADAMAWA T" afiyar su daga Bichi zuwa Adamawa ta basu wahala ba kadan ba. Musamman dake tafiyar mota ce zuwa Adamawa daga Kano. Sun jigata sun jijjiga wuni guda sur don ma motar lafiyayya ce. "Sai magriba suka shiga garin Girei, inda Yafendo ta ce Muqaddas ya tambayi gidan sarkin Fulanin Girei can za su je. Raheenah sai rarraba ido kawai ta ke yi, tana jin wani irin nutsuwa da wani irin kwanciyar hankali na shigar ta, tun ma kafin a ce ga dangin Daadan ta. Kasar Girei da mutanen cikin ta kawai ta ke ta bi da kallo, irin feeling din da dan Adam ke ji lokaci na farko da ya taka fatherland din sa." "An kai su har gidan Sarkin Fulanin Girei mai ci a lokacin. Farin dattijo, siriri dan shafal da shi. Yana zaune a karkashin bishiyar darbejiya da ta yi wa kofar gidan sa rumfa. Suka sauko daga mota suka taka zuwa inda yake zaune, sai binsu yake da ido har suka karaso." Tun daga nesa Raheenah ta kura wa siririn dattijon ido gaban ta na tsananta faduwa domin sosai yake kama da Dadarta. """Jabbama-Jabbama (maraba-lale)"". In ji Sarkin Fulani, su kuma suka tube takalman su suka karasa inda yake zaune a kan makekiyar tabarmar kaba, suka gaida shi ya amsa da madaukakiyar fara'a, sai kallon Raheenah yake yi da mamaki, domin da ganinta ka ga Sarkin fulani mai rasuwa, wato Umaru Modibbo. Fuskar ta sak ta jikoki sa dake cikin gida." "Yafendo ta kara gaishe shi, sannan ta gabatar da su daya bayan daya," """Wannan sunanta Rahinatu, wannan Nene Balki, nikma Yafendo Mairama, mun taho tun daga Bichi ta jihar Kano don mu yi tambaya a kan tsohuwa (Rahin) da dan ta Modibbo Umaru Sarkin Fulani na nan Girei mai rasuwa shekaru kusan talatin da suka wuce." "Tunda na san shi ne a matsayin dan Rahin kuma sarkin fulanin Girei, shi ya sa kai tsaye na ce a nuna mana gidan sarkin Fulani mai ci a yanzu, wai an ce matambayi ba ya bata, hakane ko ba haka ne ba? Dadin dadawa muna da hoton ita marigayiya Rahin tare da mu""." "Har ta kai karshen bayanin ta dattijon bai katse ta ba, sai ya kalle ta sannan ya kalli Raheenah, sannan ya kalli Nene, sai da ta dasa aya sannan ya ce," """Allah mai iko, ikonSa da girma yake. Bana raba daya biyun wannan yarinyar jinin Adda Rahin ce. Don shi jinin mu karfi gare shi ba ya buya a ko'ina, balle a idanun mu." "Kwarai kun zo gidan su Adda Rahin, wadda ta kasance Yaya a gare ni. Kafin mu tattauna ku shiga cikin gida wajen iyali na a ba ku ruwa, ku yi sallah ku sha fura sannan mu zauna""." "Suka mike suna godiya, farin ciki fal zuciyar Raheenah, ta kasa tashi daga gaban dattijon sai da ya ce je ki bada farali tukunna kin ji? Suna tafe zuwa cikin gida amma ba ta bar waiwayen dattijon ba don tsoro ta ke kada su shiga su fito su neme shi su rasa." Har sai da ta ga ya dauko butar sa ya biyo bayan su sannan hankalin ta ya kwanta. Ta sa kai cikin gidan. "Matan aure hudu ne a gidan, Fulani duka farare sol da su kamar mijin su. Uwargidan na da tsagin kalangu a fuskar ta wadda Rahina ta ji an kira Dudu, sai Baba Amina da Goggo Tani da amaryar Sarki, Surbajo." "Cikin fulatanci ya yi wa matan nasa bayanin bakin, wadanda kowacce da aikin da suka samu tana yi a tsakar gida, ga yara da matasa suna ta shige da fice. Nan suka hau rige-rigen ba su ruwan alwala suna masu sannu da zuwa cikin karamci da girmama bako irin wanda Fulanin Girei suka gada." "A dakin uwargida Dudu aka shimfida musu karauni suka yi sallah, sannan kowacce cikin matan gidan ta shigo musu da kwanuka cike da kabakin abin da ta dafa wa iyalin ta, kasancewar 'yar tukunya ake yi a gidan wato kowacce tukunyar ta daban, Sarki kuma ya aiko musu da damammiyar fura ta ji kindirmo kwarya guda, da gasasshen nama mai laushi. Nan suka baje suna ci suna hirar karamcin mutanen gidan a tsakaninsu." "Rahinah kam farin ciki da doki sun hana ta iya cin komai, sun cika mata zuciya da ruhi taf! Sai furar ta sha bai fi ludayi uku ba da Nene ta matsa." "Sai da suka huta Sarkin Fulani ya shigo har tsakar gida aka shigo masa da kujerar shan iskar sa a waje tsakar gidan, ya zauna sannan ya ce Surbajo ta zo da bakin sa." "Sai da suka sake sabuwar gaisuwa sannan ya ce," """Ko me ye dalilin su na zuwa neman gidan su Rahin?""" "Yafendo ta nuna masa Raheenah da dan alin ta ta ce, ""Domin mu sada wannan yarinya da dangin ta na uwa da uba, jikar Rahin ce, ba ta san kowa nata ba bayan Rahin, Allah bai sa Rahin ta taba gaya mata asalinta ba. Ni ma zance ne ya yi zance...to ka ji""." "Ta ba shi labarin yadda aka yi ta yi zargin diya ce ga Umaru Modibbo, ta kwashe duk yadda suka yi da Raheenah shekarar baya ta fada masa, sannan ta dauko hoton Dada da Raheenah ta ba ta tun lokacin ta boye ta mika masa. ""Tsarki ya tabbata ga sarki Allah, wannan Yayata ce Rahin, uwarmu daya ubanmu daya. Ita ce ta haifi Umaru da Usmanu da Dije mai rasuwa." "Abinda ya faru shine, Umaru ya kasance bayan haihuwar wannan yarinya Raheenah uwar ta ta koma, sai ya auro wata mace daga zuwa ci rani Shagamu, ya taho da ita nan Girei, ya kawo ta gidan nan inda a da nan ne gidan da yake zaune tare da mahaifiyar sa (Rahin)." "Wannan mata da ya aura babu tarbiyyah ko kankani a tare da ita, ta yi ta azabtar da Rahin da 'yar marainiyar Allah ba tare da sanin Umaru ba. Ko abinci ba su da kwanonshi a gidan nan. Ni lokacin bana nan don sana'ar mu ce kai shanu kudu ni da Ummaru, kuma in mun tafi muna jimawa ba mu waiwayi gida ba sai mun sayar da shanun da muka kai tas! A kan hanyar Umaru ta dawowa ya yi hatsari sai gawarsa aka kawo wa mahaifiyarsa, a lokacin ba a jima da ba shi sarkin Fulanin Girei ba." "Har gobe cikin mu babu wanda ya san abin da ya shiga tsakanin matar Umaru da Adda Rahin, bayan rasuwar Umaru ta hada komai nata da na yarinyar nan ta yi asubanci ta bar Girei. Matar Umaru kuma mai suna Kulu ta hada bakidaya shanun Umaru ta sayar ta kulle kudin ta bar garin nan kafin dawowa ta, don haka Rahin da jikanyar ta ba su karbi gadon Umaru ko kwandala ba. Kulu ta san makarkashiyar da ta yi mata ta korata inda har yau ba wanda ya kara ganinta cikinmu, don kawai ta wawashe gado ita kadai." "Bayan na dawo matata Dudu ta gaya min abin da suke zargi, cewa Kulu ta yi wa Adda Rahin barazanar kashe jikanyarta Rahinatu muddin ba ta bar Girei ba. Don dai ta cinye gado ita kadai. Ta sayar da komai na Umaru ta gudu cikin dare ba tare da sanin kowa ba." Damuwar mu a lokacin ba ta ina Kulu ta tafi da dukiya ba ne ko dukiyar da ta handame sai ta ina Adda da Rahinatu suka fada? "Mun yi neman duniya ba mu same su ba. Abin kamar hadin baki, shi ma Usman bai kara zuwa ba tunda ya tafi Karatu Zaria." "In takaice muku zance, Usman bai waiwayi gida ba sai bayan shekaru biyar da barin Rahin Girei, a lokacin babu wayar tarho, san da ya dawo ya gama karatu har ya samu aiki a Kaduna." "Da ya dawo ya tadda tashin hankalin da muke ciki na mutuwar dan uwansa, da rashin sanin inda mahaifiyar su Rahin da Rahinatu suka fada." "Gari-gari haka muka dinga yawo neman su Rahin, ni da Usmanu, a lokacin babu kafafen yada labarai ban da radio duk wani gari da yake makwabtaka da mu mun je mun bincika ba mu same su ba." "Fadin halin da Usman ya samu kansa a ciki a wancan lokacin ba zai yiwu ba, don gara mutuwar iyaye a kan batansu da ransu. A karshe dole Usman ya koma Kaduna ya ci gaba da aikinsa, amma akai-akai yana zuwa muna kara bincikawa Allah bai sa an dace ba." "A shekaru biyu da suka gabata ne wani dan garin nan ya zo mana da labarin ya ga Rahin a cikin Adamawa a kasuwa, ko kafin ya yi mata magana ta bace masa." "Don haka na gaya wa Usman, wanda a halin yau ya zama babban ma'aikaci a gwamnatin tarayyah, ni kuma an jima da maida sarautar Modibbo Umaru a kaina. Wato dai ni ne sarkin Fulanin Girei tsayin shekarun nan bayan rasuwar Modibbo Ummaru." "Usman ya zo muka durfafi cikin Adamawa cike da bakin cikin ashe duk wahalhalun nan da muke sha wajen neman su Rahin ashe ba nisa ta yi ba, don dai bawa ba ya hada sani da UbangijinSa ne. Kasancewar zuwa lokacin an samu ci gaban zamani mun kai hotunan Rahin kafafen yada labarai na Adamawa, mun saka cigiya musamman a talbijin. Kuma ba a fi sati biyu ana cigiyar ba wani likita daga asibitin jihar Adamawa ya bayyana kansa a matsayin wanda tsohuwa Rahin ta mutu a hannunsa a dalilin cutar ciwon zuciya na farad daya. Ya bada dukkan shaidun da suka tabbatar mana cewa Rahin ce." "Daga nan ne muka yi ta bibiya har muka samo muhallin ta, makwabtanta sun tabbatar mana cewa ta rasun, kuma tana da jika budurwa wadda aka biya wa karatu a kasar waje ta tafi shekara guda kenan da tafiyar tata a lokacin binciken namu. Amma su basu san kowacce kasa ce ba." "Yau Allah cikin ikonsa ga Rahinatu ta dawo gidan su da kafafunta. Zan so ganin murmushin da zai bayyana a fatar bakin Usmanu, don haka tunda kun zo da mota, gobe in Allah ya kai mu za mu yi asubanci zuwa Kaduna, in sada Rahinatu ga Babanta Usmanu""." Raheenah ba ta san sanda ta karasa gaban dattijon ta rike kafafunsa tana kukan farin ciki ba. Yafendo da Nene sai kabbara suke yi suna gode wa Allah tare da yi wa Daada Rahin addu'ar neman rahma da gafarar Ubangiji. "Kafin su kwanta sai da Nene ta kira Ambasada ta gaya masa duk halin da ake ciki, cikin farin ciki ya ce shi ma zai same su a Kadunan don gobe zai baro Abuja, da sun shiga Kaduna ta shaida masa don za su tsaya a can su jira isowarsu." "A daren duk 'ya'yan Sarkin Fulani da ke gidan aure sai da iyayensu mata suka aika musu suka zo suka ga Raheenah duk da cewa dare ya yi. Nene ta yi alkawarin dawo musu da Raheenah in sun sake zuwa karshen shekara, idan kuma ta gama karatunta bakidaya za ta dawo Girei bakidaya ko wajen kanin Baban nata." "Godiya da fatan alkhairi gami da shi albarka su Yafendo sun sha shi daga Sarkin Fulani da iyalin sa, washegari bayan sun yi wanka sun karya kumallo daga tukwanensu Dudu suka kama hanyar Kaduna tare da Sarkin Fulani a gaban mota da babban dan sa Ilyasu." "Tun a hanya ya sanar da Alhaji Usman cewa ga su nan tafe tare da diyar Modibbo Ummaru ta hannun Adda Rahin, wadda aka ce ta tafi karatu ketare. A lokacin Alhaji Usman yana Abuja, amma haka ya ajiye duk ayyukan da ke gaban sa ya taho Kaduna a safiyar don su yi taho mu gama, ya kuma sanar da matar sa cewa ta shirya musu kyakkyawar tarba ta musamman." "Suna shiga Kaduna Nene ta kira Ambasada ta gaya masa, ya ce ai su tuni suna cikin kaduna suna jiran su, Ilyasu ne ya bai wa Nene lambar Alhaji Usman ta tura wa Ambasada don haka Alhajin da kan sa ya kwatanta wa direban Ambasada gidan sa wanda ke unguwar Sarki." "Alhaji Usman Girei na tsaye a kofar tankareren gidan sa yana jiran isowarsu. A gefensa babban dansa ne Musaddiq dan kimanin shekaru goma sha biyar. Suna fitowa daga mota Alhaji Usman na karasowa, burin sa kawai ya dora idanun sa a kan diyar dan uwansa." "Raheenah na fitowa daga mota ta gane shi ne Alhaji Usman kani ga mahaifin da ba ta taba sani ba. Ya buda mata hannuwa ta tafi da sauri ta shige, Nene sai da ta ji hawayen tausayi da farin ciki ya cika idanunta." "Daidai lokacin da motar su Ambasada ta iso, suka jira har direban sa yayi parking ya bude masa mota ya fito, sannan Alhaji Usman yayi musu jagora zuwa babban falon sa, tarba ta girma da karamci sun ganta gun iyalin Alh. Usman, bayan an gaggaisa Sarkin Fulani ya sake maimaita labarin da ya basu a Girei, Ambasada kuma ya dora nasa na yadda aka yi Raheenah ta zo hannunsa a kasar Jamus." "A lokacin maidakin Alhaji Usman ta fita, tana kitchen tana hada-hadar hada abincin alfarmar da ta tanadarwa bakin nasu. Don haka bata ji labarin da Ambasada ya bayar ba. Amma ta san yar Yayan sa ce mai rasuwa data tafi karatu ketare aka kawo masa. Wadda ta dade tana jin labarin batan su a bakin sa tare da mahaiyar sa." Hatta auren Raheenah da Habibu sai da Daddy ya labarta masa komai da yadda auren ya kare. Abinda ya hana Rahinah yarda da sulhun da komen ne shi har gobe bai sani ba. "Alhaji Usman ya ce ya zama dole su yi tracing Habibu, wannan ai zalunci ne, dauke yaron da ke shan nono daga uwar da ta haife shi ko kotu za a je sai ya kwatowa Raheenah dan ta. In ya koma wajen ubansa to ya balaga ne, yana bayan hukuncin da Rahinah ta yi wa aurenta da Habibu ta karbi 'yancinta, inda gaske yana son ta ya kasa hakurin ya nemi iyayenta ya nemi aurenta cikin mutunci a hannun su mana? Sai wata watsatsiyar mata Laura? Shi kwata- kwata bai ga laifin Raheenah ba. Maza-maza a ba shi lambar Habibu yanzu zai je ya karbo wa Raheenah dan ta." Amma me? "Lambar Habibu da Daddy ke da ita ta kasar Jamus ce, sai a lokacin ya tuna tunda Habibu ya zo Nigeria bai kira shi a waya da lambar sa ta Najeriya kamar yadda suka yi alkawari ba. Haka ya yi ta gwada ta Jamus din duk da ya san ba shiga za ta yi ba. A karshe ya gaya wa Alhaji Usman tunda ya taho bai kira shi ba, amma yana da yakinin zai kira shi komai daren dadewa, domin yaro ne mai hankali da biyayya, sannan da zuciya daya yake son Rahinah. Ya kwantar da hankalinsa ya sa a ransa cewa, Dan Raheenah yana a kyakkyawan hannu. Domin yaron Uba ne har da rabi." "Daidai lokacin da Hajiya Badiya ta shigo masu aiki biyu a bayan ta dauke da kabakin abinci, suka shirya komai tare da ita a kan tebirin cin abinci, ta zo tana tsokanar Raheenah wai anya ko tana jin 'ZO' da harshen Hausa? Ta gan ta sullubebiya kamar sai ka wanke hannu kafin ka taba. Yafendo ce ta tare mata da cewa ""ko jakar Kano nan ta ganta ta barta wajen jin hausa"". Hajiya Badiya ta gabatar mata da kannenta, Musaddiq da Mubaraq da Mu'allim da Zarah. Raheenah ta rungume Zarah sosai kaunar yaran na shigar ta, tana ta yi musu tambayoyi a kan karatun su, sun tattauna muhimman abubuwa a kan Raheena tsakanin Daddy da Alhaji Usman kafin su yi sallama tare da amsar lambobin juna." "Shi da su Nene washegari da asubah suka juya zuwa Bichi a motar da Daddy ya zo, direban su Nene kuma ya juya da mutanen Girei zai maida su. An bar Raheenah sai za su wuce Jamus jibi ita da Safeenah direba zai tsaya ya dauke ta a nan Kaduna su karasa Abuja su hau jirgin Jamus." **** : SUMAYYAH ABDULKADIR 07030137870 "Zaman Raheenah na kwana biyu a gidan Kawun ta tare da matar kanin mahaifinta Aunty Badiya da 'ya'yanta hudu gwanin ban sha'awa, ba ta bambanta Raheenah da Musaddiq ko magana za ta yi sai ta ce, sai Raheenah ta fara kaza sannan Musaddiq zai yi tunda ta girme shi. Jininta ya fi haduwa da na Musaddiq sabida ilminsa, ga Raheenah da son yara masu kwazo. Zarah ma suna shiri don sai ta ke kwatanta girmanta da na Abdallahnta a halin yanzu, ita in ba idonta ne ma ke mata gizo ba sai ta ce, Mu'allim yana mata yanayi da danta Abdallah. Sai dai yadda ta binne uban Abdallah a ranta a yanzu, haka ta ke so shi ma Abdallahn ta daina ko tuno shi duk da ta san hakan ba mai yiwuwa ba ne." "Lokaci-lokaci sai ta tsaya ta bar abin da ta ke yi tana tunanin Abdallah, ko me yake yi yanzu? Ko ya manta ta? Ko ya daina kiran sunanta? Wannan da wancan Amma ko ya ya tunanin Habibu ya kutso cikin kan ta da zuciyar ta sai" tayi kokarin yakice shi da dukkan karfin ta. "Ba shakkah ta ji dadin zama da Aunty Badiya da yaranta da Kawun ta, tsayin kwana biyun, ji ta ke kamar kada ta koma Jamus, but she want to be that Otorhinolaryngologist she promised to be. Wannan ne kadai ya sa ta yarda ta koma Jamus tare da Safeenah a washegarin ranar da suka biyo don tafiya da ita, inda suka tashi ta filin jirgin saman Abuja." "Kudi mai yawa Alhaji Usman ya ba ta, ya ce ta rage wa Ambasada nauyi, kuma ya yi alkawarin aika mata kwatankwacin su duk karshen wata." "(Ranar da Rahinah ta tashi Abuja da safe, da yammacin ranar aka dawo da Abdallah daga Zamfara inda ya je ya yiwa Hajiyar Nahuce hutu)." ***** *KOMAWAR RAHEENAH JAMUS* "Bayan sun koma Frankfurt ita da Safeenah, kowacce tana dakinta babu mai shiga shirgin kowa. Ko da ma can jininsu ba wai ya hadu ba ne, don haka kowa sabgar karatunta ta ke yi ita kadai a dakin ta. Ta kan dai ji wani lokacin Safeenah na waya da saurayin ta Muktar a barandar dakunan nasu. Raheenah Omar ta fuskanci karatunta da wani irin zeal saboda a halin yanzu ba ta da damuwa, tana cikin farin ciki na haduwa da danginta. Sai ta dauki hankalin ta da nutsuwarta kacokam ta mika wa MBBS dinta." "Har zuwa lokacin da su Daddy suka dawo, suka ci gaba da gudanar da rayuwar su cikin gidan yadda" suka saba. "Amma me? Ita diya mace a yayin da ta samu contentment na rayuwa, nutsuwa da kwanciyar hankali, abin da ya saura mata shi ne, DA NAMIJI a gefenta. A matsayin mijin aure ko manemin aure." "Wannan ne kadai gibin Raheenah a rayuwa. Somehow, wani bangare na zuciyarta kewar Habeebu yake yi, tana karyatawa da gangan. Tana bai wa tunanin rashin muhimmanci, tana ganin she can overcome it by force, amma a hankali sai tunanin Habib Nahuce da wata sabuwar kakkarfar soyayyarsa suka zo suka soma cin karfintaba tare da ta ankara ba." "Wannan wani sirri ne tsakanin ta da zuciyar ta, wanda daga ita sai Ubangijin ta suka san da shi. Bata kuma fatan wani cikin gidan ya san da shi." "Raheenah Omar ta gama MBBS a wannan shekarar, da sakamako mai madaukakiyar daraja, ta kammala ne (as the overall best student). A wannan lokacin Alhaji Usman Girei sai da ya taka kafafunsa har Jamus da taimakon cuku- cukun visa da Ambasada ya yi masa ya taya Raheenah murnar karbar kwalinta." "A wannan ranar Raheenah sai da ta yi kuka don farin ciki amma duk da haka; ta rasa dalilin da ya sa farin cikin nata ya zama incomplete, tamkar tana missing someone important, musamman da ya kasance kusan duk abokan karatunta mazajen su ne suka taya su karbar nasu kwalin, wasu kuma fiances dinsu. Ita ce kadai mai Uncle da Daddy a gefe, babu mijin da ya taya ta karbowa ya karba a nashi hannun bayan ta karbo ya bi ta da murmushin kauna." A hakan ma ta fi kowa godiyar Ubangiji domin ba ta taba tunanin haduwa da wani nata ba har zuwa sanda za ta bar Jamus kwata-kwata. Amma yau ga ta tare da kanin uban ta har Jamus din. "Kafin ta fara specialization dinta sai da ta zo Girei ta yi sati biyu da su Goggo Dudu, sannan ta wuce Kaduna can ma ta yi sati biyu. Ba tare da ta sani ba, a ranar da ta je Kaduna, a jiyan ranar Habibu Nahuce ya zo ya dauki Abdallah daga wajen Aunty Badiya zuwa Zamfara don ya yi hutun kirsimetin sa tare da Hajiyar Nahuce." Satin ta biyu ta koma Jamus ta fara specialization din ta a otorhinolaryngology. "Daga lokacin da ta fara specialization din kasancewar wahalar sa bata kai ta MBBS ba ta kan samu lokacin kan ta da lokacin tunani, a lokacin abubuwa suka fara rikice mata. Soyayyar (her ex Habibu) ta kada ita wanwar. Ta soma" "tunani da neman hanyar samun labarin sa. Ba don ta kula shi ba, sai don kawai shes curious ga son ta san me yake ciki shi da gudan ran ta, don haka ta soma sha'awar bibiyar Habibu Nahuce a kafafen sadar da zumunta, amma ko daya ba ya kai. As the busy person that he is, bashi da lokacin wadannan abubuwan (social media platforms). A karshe ta yanke shawarar duba shi a yanar gizo (google) ta san bazata kasa samun wani abu da shafe shi ba komai kankantar sa." "A wani marece ne ana tafka ruwan sama mai karfi a garin Frankfurt, ta rufe tagogi da kofar dakin ta, ta saki fararen curtains din dakin, sannan ta kunna (room-heater), ta dauko kwamfutar bisa cinya (loptop) ta shiga google kawai ta rubuta sunan sa HABIBU MUSTAPHA NAHUCE. Ita kuma googlesai ta kai ta LinkedIn. Kasancewar sa (professional platform). A can bata samu wani cikakken bayanin sa ba sai na profession din sa (as a Hotel Administrator), sai kuma a wani website na hotels din sa. A canne ta ga cikakken sunansa da cikakken bayaninsa a halin yanzu." """Habibu Mustapha Nahuce (Lucky), Young Nigerian Hotels Owner, the Proprietor of NAHUCE GROUP OF HOTELS, Excutive Director TRANSCORP HILTON, NIGERIA......." "(With so much interest) hadi da mamaki da dokantuwa, wani irin inquisitivity and curiousity, Raheenah ta ci gaba da surfing tana bin bayanan wadanda duk sun kunshi gwagwarmayar rayuwar Habibu ne, ta neman ilmi, ta fadi-tashi a Jamus, da ayyukan Hotels a gida Nigeria, saicurrent hotunansa wadanda suka kusan gusar da numfashinta." "Yana nan a handsome HABEEBUNsa, dan gayun nan wankakke, mai iya daukar wanka, mai iya sanya karin hula, kuma dan kwalisar shi yadda ta san shi a baya cikin birnin Cologne, sai wata 'yar kiba ta hutu da zaman naira a muhallin ta ya sabbaba kawai da ya kara, hadi da wani irin kwarjini da kamala wanda rikon addini ke haifarwa mutumin da ya rike addinin sa da gaskiya, ya kuma san ciwon kan sa (at approaching 40)." Numfashin Raheenah yayi balaguro na tsayin lokaci daga kirjin ta. "Ba ta iya ci gaba da karantawa ba, haka bata iya cigaba da kuma kallon hotunan tallbuildings din NAHUCHE HOTELS dake kasa ba ta kifa fuskar kwamfutar ba tare da ta kashe ta ba." "Numfashin ta na racing...cikin sassarfa, zuciyar ta na wani irin bugu cikin ragaita... So Habibu yana can kasar shi Nigeria yana progressingto such extent harya manta da ita. Ya manta an yi halitar ta. Mai wannan tarin achievements din ina zai tuna da wata halittar Allah mai suna RAHEENAH! Ya gama cimma komai na rayuwa, da duk wani buri da dan adam ke da shi, watakila ma har aure ya yi ya dau Dan ta Abdallah ya baiwa wata, in ba haka ba yaya zai yi da yaron???" "Wannan tunani ya dugunzuma zuciyar Rahinah. Kishi da bakin ciki matsananci suka lullube ta. Kawai sai ta ji hawaye na saukar mata duk da ba na regret bane, na tunanin ya dau dan da ta sha wahalar dakon cikin sa wata tara da nakudar sa ya baiwa wata ne. Watan da ta ke da tabbacin ba zata rike mata Da sabida Allah ba sai don wannan dukiyar HOTELS da aka tara." "Ba ta san lokacin da ta sake kunna kwamfutar ba ta koma kan browser din ta ta rubuta 'HABIBU NAHUCE'S WIFE', amma kuma no result matched her search, ta yi sau ba adadi ba ta ga wata mace associated with him as a spouse ba, sai Daractoci da manajoji na hotels din shi, wadanda duk kabilu ne." "Wata nannauyar ajiyar zuciya ce ta kufcewa Raheenah, amma sai wata zuciyar ta ce," """Kada ki yi saurin sauke numfashi Rahinah, watakila yana daga cikin mazan da ba sa exposing matan su a internet, ko da gani ma wadannan bayanan duka ba shi ya dora su ba, website ne na hotel din sa ya dora, ya kuma kunshi dukkan bayanan da suka shafe shi." "Da sauri ta soma binciken babban location na shedkwatar Nahuche Hotels, da kuma ainahin jihar da garin NAHUCHE yake, ba jimawa adireshin ya bayyana;" "'ZAMFARA STATE, NIGERIA'." Ta koma da baya ta jingina da allon gadon ta tana wani irin lumshe idon ta. So Habibu dan Zamfara ne kenan all these while ba ta taba sani ba. Yau har karamar hukumar da garin Nahuce ke ciki sai da Rahinah ta binciko (aiki ya samu manyan mata) Ranar dai baki dayan ta ta zama ta DAN NAHUCHE jikan NAHUCHE ce a wajen Raheenah..... "Gabadaya ta birkice a searching din komai da ya dangace shi, sai da ta binciko komai concerning Young Nigerian Hotels Owner Habibu Mustapha Nahuche. Ba kuma da nufin za ta taba neman sa ba; she is only infatuated and truely in LOVE... ba tare da ita kanta ta san soyayyar gaskiya ke dawainiya da ita a daidai wannan lokacin ba." Dankwalin kan ta yayi nasa wuri gashin kanta na fulanin usli duk ta hargitsa shi kamar yadda ta hargitsa zuciyar ta da tunanin ta. "Duhu na neman shigowa, har zuwa lokacin Raheenah na bisa kwamfuta ba tare da ta tuna da abincin rana ba. Wanda ta ce ma Nene in ta gama abinda take yi zata zo ta dauka." "Jin shiru har karfe shidda na yamma Rahinah bata fito ba sai Nene ta shigo mata da shi tana tambayar ko lafiya ba ta fito cin abinci ba gashi har an gama na dare? Idanun Nene Balki suka kai kan allon kwamfuta (screen) inda ta hango fuskar Habibun su ta cika screen din, da alama zooming hoton ta yi. Tana kara kallon kyakkyawar fuskar sa da kyau. Da sauri ta kife fuskar kwamfutar ba tare da ta kashe ta ba. Nene ta yi kamar ba ta gani ba, amma ta kusa sakin salati don mamaki, ta ajiye mata abincin da ta biyo ta da shi, ta ce." """Ki daure ki ci abinci ki koshi, sai ki fi jin dadin tada tsumin tsohuwar soyayyah""." "Raheenah ta yi maza ta rufe ido ruf! Tare da dora hannayen ta biyu a kai kamar ta ce, ""wayyo Allah kasar ta tsage ta shige"". Nene ta gani, ta gan ta da hoton Habibu cikin kwamfutar ta! Yau ina za ta sa kanta da wannan dingimemen abun kunya???" "Nene ba ta tsaya sauraron borin kunyarta ba ta juya ta fice daga dakin. Ba ta kuma tsaya ko'ina ba sai falon Ambasada, ta labarta masa abin da ta gani a kwamfutar Raheenah yau. Mamaki kamar ya kashe ta." "Ambasada Shehu Bichi murmushi ya yi, ya ce," """Shin ke Nene da can kin dauka wai ba ta sonshi ne? Ai ki bar bacin rai a lokacin da yake cin zuciyar diya mace. Sannan shi bacin rai (is mortal but love is inevitable). Amma kuma duk da hakan zuciyarta mai rauni ce a kan ta Da namiji. Bari ta gama karatun ki sha kallo, da kan ta za ta nemo shi duk inda yake." "A lokacin ne yake gaya mata shi ya san inda Habibu yake, (Habibu is now a successful business tycoon) a garin Zamfara, amma har gobe bai yi aure ba, me ye dalili? Wanda ke nufin uwar dan sa yake jira TA HUCE DAGA FUSHIN TA." "Ya kara da cewa, abin da ki ka ga tana yi yanzun, alamu ne na ta fara HUCEWA, sai mu ba su lokaci su duka, mu kuma bi su da kyakkyawar addu'a." "Amma a yadda na fahimta Habibu na da zuciya, soyayyah ba ta rufe masa ido ya kasa sarrafa kan sa." "Idan kin ga ya yarda ya maida Raheenah to fa sai dai idan ita da kanta ta neme shi, ta ba shi tabbacin amincewar ta a kan komawar ta dakin ta. Ya riga yayi zuciya da Raheenah. Yayin da ita kuma Rahinatu in kin lura akwai ta da ki- fadi (mawuyaci ne hakan ta kasance daga bangarenta)""." Nene ta dinga jinjina kai. Ta rasa abinda zata ce. ***** "*COLOGNE, ALUMNI*" "A yau ne jamiar Cologne ta kasar Jamus, jamia mai dadadden tarihi, ke bikin kammala karatun su Raheenah daga jami'ar wato (convocation ceremony). Duk inda ka duba dalibai ne daga kasashe daban-daban na duniya, tun daga Amurka, Birtaniya, Asia, Africa and Latin-America. Suna saye da bakar rigar kammalawa (convocation gown) da hular ilmi, farare sun cakude da bakake ba ka iya tantance nationality din kowannen su." "Dr. Raheenah Omar, ta fita da matsayin overall best student a department din ta (Otorhinolaryngology) ta karbi wannan kambu daga shugaban jami'ar Cologne. Ta karbi membership daga (AFHNS) wato (African Head and Neck Society) da kuma (ORLSON) wato (Otorhinolaryngocological Society of Nigeria)." "Kamar yadda ta yi wa kasar ta alkawari, wannan ne lokacin dawowar ta gida bakidaya domin ta taimaka wa kasar ta ta amfana daga ilmin da ta tsaya mata ta yi." "Yau gidan Ambasada Shehu Bichi komawa ya yi kamar gidan mutuwa don koke-koke, sakamakon cewa gobe ne Raheenah za ta bi Uncle din ta zuwa gida Nigeria. Wanda ya kara zuwa Jamus a karo na biyu don tafiya da ita. Ahlan kuka har da majina, Yafendo kuwa habar zani ta sa tana ta fyace hanci kamar an aiko musu da manzon mutuwa, Nene ce kadai mai lallashin kowa tana tuna musu suma kwanan nan za su koma Nigeria, sabida tenure din Ambasada Shehu ta kusan karewa." "Rabuwar Raheenah Omar da iyalin Ambasada wata irin rabuwa ce veryemotional. Wadda mai raguwar zuciya ba zai iya tsayawa a wajen ba. Abu daya ya kwantar musu da hankali, shi ne, su ma ahalin gidan na gab da dawowa Abuja bakidaya." "Suna sauka a Kaduna, Alhaji Usman ya sa direban sa ya wuce da ita Girei, kafin ta huta ta zo ta wuce NYSC, lokacin har an fara daukan batch A, don haka Uncle (yadda ta ke kiran sa) ya shigar da sunan Raheenah cikin masu tafiya hidimar kasa na wannan shekarar." Ba ta fi sati biyu da dawowa Kaduna ba ta wuce NYSC a Ibadan inda suka yi posting dinta zuwa asibitin koyarwa na Ibadan. "Duk inda Raheenah ta shiga farin jinin ta da kyawun ta ke sayo mata soyayyar jama'a. Ga ta nan kamar ka taba jini ya yi tsartuwa (jazir sumul da ita) bafullatanar usli, wadda ta samu gogewa cikin zuzzurfan ilmin zamani. Ta wanke ta yi sumul ba za ka taba tunanin bafulatana ba ce, ta fi kama da larabawan Oman, Qatar haka, ko kuwa na Maghrib." "A Ibadan Teaching Hospital ne wani babban likita dan uwanta ya like mata wai shi Dr. Aryan dan jihar Minna ne, aiki ne ya kai shi Ibadan kuma karkashin team dinsa ta ke aiki. Rahinah ta yi duk iya kokarin ta don ta nunawa Aryan ba auren sa za ta iya ba, amma ya ki ganewa, mutum ne mai nacin gaske kuma girman mukamin aiki da ke tsakanin su ya sa ba ta isa ta wulakanta shi ba don ba ya shiga hurumin aikin ta sam-sam ya san lokacin da yake damunta da nacin kira da zarya a inda duk ya san zai ganta kasancewar sa ya manyanta don ya jima yana aiki a nan, matarsa ta mutu da jimawa ba shi da Da ko daya." "Don haka da Allah ya kawo lokacin kammala NYSC din ta, ji ta yi tamkar an raba ta da kaya, ta dawo gidan su a Kaduna a ranar matsayin cikakkiyar Otorhinolaryngologist mai lasisin aiki tare da Hukumar Lafiya ta kasa, ba da jimawa ba aka tura ta National Hospital Abuja matsayin ENT Surgeon. Dr. Rahinah Omar ta fara gudanar da ayyukanta na likitancin kunne, wuya da makogaro cikin dumbin nasara." "Ita ce likitar kunne ta farko a Africa da ta gudanar da dashen dodon-kunne (cochlear Implant) a Nigeria gabadaya. Kuma kafafen yada labarai suka yada nasararta a wannan surgery na kunne mai hadarin gaske, wanda ya zamo na farkon yi a kasar Najeriya. Kuma wanda ta sanyawa din ya ji magana sosai. Don haka manyan asibitoci masu zaman kansu na birnin tarayyah da wajen ta suka ankara da ita, ta yi attracting asibitocin kunne masu yawa suna masu gayyatar ta aikin part-time job tare da su. Amma duk ciki sai ta zabi babban asibitin NIZAMIYE ta hada da aikinta na gwamnati a National Hospital Abuja." "An bai wa Raheenah gidan likitoci a cikin National Hospital. Uncle ya ce bai son ta je ta zauna ita kadai ba muharrami don haka Aunty Badiya ta samo mata mai aiki a nan kaduna suka tare tare, wai ita Sahura. bazawara ce da ba ta fi shekaru arba'in ba." "Daga lokacin da Raheenah ta gane dangin ta zuwa yanzu ta zo Kaduna ya kai sau shida, amma cikin wani hukunci na Ubangiji ba ta taba haduwa da Abdallah ba, duk lokacin da ta zo yana Zamfara ko wajen mahaifin sa a Lagos inda harkokin sa suka fi karfi yanzu. Sai dai cikin hirarrakin su da Aunty Badiya da su Musaddiq ta fuskanci akwai dan kaninta da ta ke riko tare da Zarah, Baban sa bai cika barin sa ya zauna a Kaduna ba cikin hutu wanda ita lokacin take zuwa sai lokacin makaranta. Haka a bakin su Musaddiq tana yawan jin sunan Junior sunan da duk jamaar gidan suke kiran Abdallah, kasancewar shi ne karami a cikin su." "Tun komawar su Abuja ita da Baba Sahura Raheenah ta zama ba ta da lokacin kan ta, sabida documentation na kama aiki. Tana jin dadin zama da Sahura don kullum kafin ta dawo ta gyare musu dan madaidaicin gidan su tsaf! Ta kunna turaren wuta, ta kuma dafa musu abinci. In Raheenah ba ta ra'ayi daga waje ta ke taho da abin da za ta ci. Uncle ya mallaka mata karamar mota KiaPicanto don ta samu saukin zirga-zirgar ayyukan ta." "Wannan ya taimaka ainun wajen kwashewa Raheenah hankali a wannan dan tsakanin. Ba ta da lokacin da za ta zauna ta yi tunani. Ko bibiyar lamuran dan mutanen Nahuce. Aiki ta ke tukuru da kwarewa da patriotism domin saka wa gwamnatin Najeriya da ta tsaya mata, ta tallafi ilmin ta da (scholarship)." "Ranar da ta fara daukan albashin ta na farko ko naira ba ta ci a ciki ba ta kasafta wa iyayen ta, bayan ta ware wa Ambasada kaso mafi tsoka, sannan Yafendo da Nene. Tana mai dakacen ina ma Daada tana raye?" "Wannan ihsani da girma da Raheenah ta bai wa iyayen dakinta ya kara mata martaba a idanun su, ba don ba su da shi ba, sai don ganewa da suka yi ita din mutum ce mara manta alkhairi. Bayyanar iyayen ta bai sa su ta daina kallon su da matsayin iyaye ba." Asibitin Nizamiye wani babban asibiti ne mai zaman kansa a birnin tarayyah. Suna matukar ji da Dr. Rahinah Omar wadda ke aiki part-time da su a matsayin ENT Surgeon (otorlaryngologist). "Nizamiye Hospital na nan a (Life-Camp). They have the latest technology for the treatment of most common ENT cases irin su Rhinitis, Sinusitis, Myringoplesty, Tympanoplasty, Mastoidectomy, Septoplasty da sauransu. The World Class Private Hospital wanda Turkawa suka kafa a birnin Tarayyah." Don haka Raheenah ba karamar sa'a ta taka ba a rayuwarta da ta samu kujera a Nizamiye. Kudi sosai ya soma shiga account din yar mutanen Girei. **** NA HUCE is not for free. It's 1000 via 3094856450 Sumayyah Kabara Firstbank Shaidar biya 07030137870 ": Wata ranar Litinin, Dr. Raheenah ta dawo aiki a gajiye likis, tana yin parking a apartment din ta Baba Sahura na fitowa za ta zub da shara. Da sauri ta aje kwandon sharar ta iso ta karbi jakar uwargijiyar ta tare da (lab coat) da ke hannun ta tare da yi mata barka da zuwa, Rahinah ta bata mukullin booth din motar ta ce ta fidda cefanen da ta yo musu ta sanya a freezer." Wayar Raheenah ta yi kara a lokacin da ta ke fidda leshin jikin ta za ta shiga wanka. Dakatawa ta yi ta dauki wayar inda ta ga Aunty Badiya ke kiran ta. """Maman Musaddiq ya ku ke?""" "Ta ce, ""Muna lafiya cikin alkhairi Raheenah, Uncle ne ya ce in tambaye ki yaushe za ki samu shigowa Kd? Akwai muhimmiyar magana da ya ke so ku yi""." "Raheenah ta ce, ""Aunty a wannan watan duka ba zan samu lokacin shigowa ba, due to my tight schedules, amma insha Allahu weekend din karshen wata zan shigo""." "Aunty Badiya ta ce, ""Ni kuma zan je gida Zamfara lokacin, zan dauko dan kani na Junior daga wajen Hajiyar mu, Baban sa zai dawo daga Belarus ina so kamin ya wuce Lagos ya gan shi, amma kwana daya zan yi. So, insha Allah za mu hadu kafin ki koma, a kula da aiki, a kula da mutunci. Allah ya kara wa rayuwar ku da nema albarka""." Sati biyu bayan nan Ambasada Shehu da iyalinsa da mahaifiyarsa Yafendo suka sauka a kasar Nigeria. Sun jima a Bichi cikin 'yan uwa da danginsu kafin su yi relocating a gidan da Ambasada ya saya a Abuja tun kafin barowar shi Jamus. Gidan yana nan a unguwar Maitama. "Raheenah na dakin tiyata, fitowar ta kenan ta samu kira daga bakuwar lamba. Sai da ta zauna bisa kujerar ofishin ta ta warware nadin mayafin da ke kanta, sannan ta bi bayan kiran." Muryar wa za ta ji? NENE! Sannan lambar ta kasar Nigeria ce. "Wata zabura da Raheenah ta yi daga kujerar ta tana kiran sunan ""Nene!"" Sai da ta bai wa Nene Balki dariya, ta ce," """Finally, ga mu a Abuja, kuka ya kare ko?""" "Hawayen farin ciki suka zubowa Raheenah, da ma kewarsu da kadaici sun addabe ta musamman da ta fara samun saukin ayyukan da ke gaban ta. Sannan ba ta da kowa a Abuja bayan Uncle Usman, shi kuma ba haduwa suke ba sai idan ta samu lokaci ta je ofis din sa ko shi ya zo nata." Don haka dawowar iyalin Ambasada Shehu Abuja ba karamin kwanciyar hankali ya kara wa Dr. Raheehah ba. A ranar a gidan Nene suka kwana dakin Yafendo ita da Sahura ana ta hirar yaushe gamo. "Daga wannan lokacin ne kuma rayuwar Raheenatu ta dauki sabon direction. Rayuwa ce ta 'yanci ta ke ciki wadda kowanne mai ilmin boko ita yake yi wa buri, ga aiki, ga gida ga albashi ga motar kan ta, ga kuma rayuwar Abuja. Don haka abu daya ya rage mata shi ne mahadin rayuwar diya mace, wato mijin aure. Mazan da har gobe ta kasa daga ido ta yi musu kallon maza, sai muna-maza, domin kowa ya zo gare ta da kalmar so ji ta ke tamkar ya daba mata mashi a kahon zuci, bai kai ba, bai isa ba. Wanda ta ke binnewa da gangan a karkashin ran ta, shi kadai ne namiji a idanunta a zahiri da badini, dan Hajiyar Nahuce (Habibu)." "Ta zama infatuated a kan Habibu kwarai, ta ci gaba da follow up a kan duk wani takunsa na rayuwa, da halin da yake ciki. Duk wasu nasarorin sa na rayuwa a kan kunnen ta, Amma ta yanke shawarar never to look for him ever! A wurin ta kaddara ta riga ta gama playing game din ta, tsakanin ta da Habibu Nahuche. Amma ta rasa dalilin da ya sa har gobe ta kasa daina bibiyar halin da yake ciki." Shin da gaske ne kaddarar ta gama playing game din ta a tsakanin su??? Ta tambayi kan ta a ranar da ta ji (live programme) din sa da British Broadcasting Corporation wato gidan rediyon BBC Hausa. Ta kashe rediyon ta koma jikin taga ta tsaya standstill tana kallon harabar gidan ta wanda shuke-shuken korran ciyayi suka yi wa kawanya. Abdallah ko yanzu in ya gan ta zai iya shaida ta? Ko ya taba gaya masa yana da uwa a duniya? Ko kuwa bacin ran ta ya sa bai taba gaya masa ba? Habibu kadai ya san duka amsoshin wadannan tambayoyin. ****** "Yau juma'a ba ta da aiki sosai a ofis don haka ta yanke shawarar tattara komai nata ta wuce Maitama wajen su Nene ta kare ranar yau tare da su. Ta kira Sahura a waya ta ce, kada ta dafa abinci da ita ta wuce wajen su Yafendo sai dare za ta dawo." "Rahina na tuki cikin nutsuwa kamar yadda ta saba, lokacin da direban sa Yohan dan kabilar Igala ya shararo motar su a guje kirar 'Discussion Contineous' saura kadan ya goga mata. Da sauri ta dauke kan motar ta tana mai Allah wadai da halin wasu direbobin, shi ko Yohan Ubangidan sa ke azalzalarsa a kan ya yi sauri, saura mintuna goma sha biyar meeting din zai halarta a Transcorp Hilton." "Amma me? Motar da ta kauce musu is a glimpse of her Fulani face. That magical beauty of her's, wanda cikin kowanne hali ba zai kasa shaidawa ba. Cikin hali na mafarki ko ido biyu ba zai taba mancewa da kamannin Raheenah Omar ba. Waiwaye wani abu ne da ba ya yi sam, amma yau ya yi waiwaye har ba adadi kamar wuyan sa ya karye amma motar ta bace masa. Abu daya ya gane, motar fara ce sol! Kirar kia picanto, kuma yana da tabbaci a kan-kan sa (self-assurance) na ko da ba ta bace masa ba, ba zai bi bayan ta ba. To ya bi ta yace mata me? Ko ya yi mata me?" "Ta bar shi da tabo a zuciya, it's a deep wound that can never be healed, watakila har sai ranar da Raheenah Omar ta nemi KOME zuwa auren su da kan ta da bakin ta." Wanda kuma yake da tabbacin abu ne mai matukar wuya a kafiya da taurin kai irin nata da ya dade da fahimta. Wannan na nufin ta dawo Nigeria... "Wannan na nufin she's progressing without him, shi da dan sa ta ba su baya, ta manta da su kwata-kwata." "A duk lokacin da ya tuna Raheenah, fada yake da zuciyar sa ta ci gaba da yin tauri, kada ta karaya, kada weakness din ta ya bayyana. Amma yau fa? Raheenah ya gani ba hotonta ba, her humble self bayan wucewar shekaru goma, which is hard for him to control himself domin kuwa ko meeting din da yake gaggawar zuwa har aka yi aka gama bai tsinci komai a ciki ba." "Ta iso gidan Nene wajejen karfe sha daya na rana. Da Ahlan ta soma cin karo suna wasan kwallon kwando da abokan sa a harabar gidan. Ya baro abokan nasa ya zo ya bude mata kofa yana fadin, ""Yayata tafi ta kowa, Yayata likitar da babu kamar ta'." Dariya ta yi suka rankaya zuwa ciki. "Nene na kicin tana girki lokacin da suka shigo. Ta kama mata suka karasa komai, suna aikin Nene ta ke gaya mata Yafendo ba ta jin dadi tun jiya." """An je asibiti?"" Ta tambaya cikin damuwa." "Ba yadda Daddy bai yi ba dazu su tafi asibiti ta ki, wai in mutuwa ce a bar ta ta mutu a cikin dakin ta. Ba ta son zakule-zakule, Raheenah sai ta bar komai ta nufi dakin Yafendo." "A kwance ta same ta tana lazimi ta tsaya daga bakin kofa ta ce, ""Yafendo me ya same ki?"" Yafendo ta sauke idanun ta da suka kada sabida zafin zazzabi, ta ce," """Ya ki 'yar albarka, da ma yanzu zan ce wa Ahlan ya danno min ke a waya, ki zo ki ba ni magani, bana son zuwa asibiti a yi ta jagwalgwala ni""." "Ai kuwa sosai Rahinah ta bincike ta, ta kuma ba ta treatment din da ya kamata, domin ta fahimci zazzabin typhoid ke son kamata, har allura ta yi mata wadda ta aika Ahlan ya sayo." "Zuwa la'asar Yafendo ta ji dadin jikin ta sosai, sai suka koma hira, Yafendo ta ce," """A yi magana cibi ya zama kari, amma bari Baban naki ya shigo""." "Raheenah ba ta gane me Yafendo ke nufi ba sai da Daddy ya dawo, ya kuma shigo don ya duba jikin Yafendon, nan ya ga Raheenah ya fadada fara'ar fuskar sa, yana fadin, ""Lale-maraba, da manyan otorlaryngologists""." "Yafendo ta ce, ""Ai gara da ka zo, da ma yanzu zan ce ta latso min kai. Shigo ka zauna, magana za mu yi ta gaskiya ni da ku""." "Ambasada ya samu wuri gefen Yafendo ya zauna, ita kuma sai ta fara magana cikin tsananin damuwa." """Yanzu saboda Allah haka za ku zuba wa Rahinatu ido ta kare rayuwar ta babu aure? Talatin ta ke nema fa rabin sittin ba ashirin ba. Ni ban ce lallai sai ta koma wa Baban Abdullahi ba, tunda wannan shi ta ga zai fishshe ta, amma ta fidda miji ta yi aure ko wane ne tunda ta ki komen mai kaunar ta da gaskiya." "Amma wallahi ku yi a hankali daga ku har ita, kada bokon ku ya kai ku wutar jahannama""." "Shi kam Ambasada murmushi kawai yake yi domin a yau din nan ya gano wani muhimmin al'amari, wato Yayar Habibu Nahuche Uncle din Rahinah Alhaji Usman Girei ke aure. Ya gane hakan ne daga hirar da suka yi da Uncle Usman yau a ofishin sa, inda yake gaya masa ai NAHUCHE HOTELS na kanin maidakin sa ne Badiya, lokacin da aka nuno sabon ginin NAHUCHE HOTEL da ya yi launching a jihar Rivers (PortHercourt) a talbijin din da ke cikin ofishin a gaban su lokacin da suke hirar. Shi kuma Ambasada bai gaya wa Uncle komai a kan sanin da ya yi masa yana dalibi ba, ko girman alakar da ke akwai a tsakanin su yanzu. Shi Uncle Usman din da Habibun (wato surakuta). Ya bar wa Allah ikon Sa ya ci gaba da yin hukuncin Sa a kan Rahinah da Habibu Nahuche, don ya gane ba karshen kaddarar su kenan ba, tunda har wannan babbar alaka ta sake bayyana kan ta a tsakanin su." "Da wannan Ambasada Shehu ya samu ya rarrashi tsohuwar sa Yafendo cewa, shi da Uncle Usman za su zauna da Raheenah don jin hakikanin halin da ta ke ciki, kuma za su yi duk mai yiwuwa su ga cewa ba ta kara shekara daya a nan gaba babu aure ba." """Ah toh ya rage naku kuma, ni dai aikina tunatarwa da tsoratarwa a inda na ga an yi ba daidai ba. Ya rage naku ku yi ta biye wa boko kuna bautar sa ba Allah ba. Ni rayuwata ta yi kyau, na kare ta cikin bautar aure har ya koma ga mahaliccin sa, shi ya sa nake mata kwadayi ita ma ta mutu karkashin igiyoyin aure, don ni rayuwata ta kare, rakawa muke yi, dole kuma mu yi muku tunatarwa a lokacin da ku ka nemi kauce hanya""." "Jiki a sanyaye Dr. Rahinah ta koma gidanta sabida irin maganganun da Yafendo ke yi sun karya mata zuciya, sai fada ta ke ita rayuwarta ta kare. Alal hakika ganinta ta ke kamar Daadarta." "Kamar yadda ta yi alkawari, a ranar asabar din karshen wata ta shirya suka kama hanyar Kaduna ita da Sahura don amsa kiran Uncle Usman." "Wajejen azahar suka shiga Kaduna, ba ta samu Anty ba sun wuce Zamfara ita da Zarah da Musaddiq sai Mu'allim da Mubaraq da mai aikin Aunty sai kuma Uncle da kansa kawai a gidan." "Dakin na gidan wanda anan ta saba sauka in ta zo a can ta sauka, amma yau jin duk jikin ta ta ke wani irin dizzy kamar zazzabi na son shigar ta." Uncle bai kira ta ba sai da ya dawo sallar isha'i. "Ta nutsu a gaban shi tana sauraron abin da zai ce mata, wanda muhimmancin sa ya wuce su tattauna shi a ofis sai ya kira ta har Kaduna." """Rahinatu yau na kira ki ne a matsayin mahaifin da ya damu da 'yar sa, ina so in san hakikanin shin me ya hana ki aure? Ko kusa kada ki ce min miji ne Allah bai kawo ba, don kuwa ko ta bangarena mutane hudu ne ke son ki ba su dama." Haka Chief-Medical Director na Nizamiye Dr. Irshad mutumin nan shi ma ya yi tattaki gare ni har ofishi na a kan maganar ki. "Ga wannan Aryan na Minna shi ma har gobe ba wai ya hakura ba ne, lokaci-lokaci yana kira na a kan batun ki." "Ya gaya min kin sanya layin shi ma a divert call sabida ba ki da lokacin sauraron shi. Shi ne nake so in san matsalarki ta hakika, wadda ta sa ki ke gudun masu kaunar ki, ko kuma ki gaya min gaskiya, har gobe Uban dan ki ki ke kwadayin komawa ko me?""" "Da sauri Raheenah ta cira kai ta dubi Baffan ta, me ya sa zai yi mata wannan hukuncin? To amma in ta kalubalanci Uncle za ta kalubalanci zahirin abin da ke karkashin zuciyar ta ne? Maza ba sa burge ta ko kadan, sai dan mutanen Nahuche... The one that took away her pride na diya mace. Ya san sirrinta ta san nasa, reality din shi ne ba za ta iya kara hada jiki da wani Da namiji bayan shi ba. Ba za ta iya kara hada rayuwar ta da kowa ba shi ba. Amma kuma ba za ta taba neman sa ba balle ya yi tunanin kome ta ke nema, ko tana so ya dawo mata da dan ta, har ya yi amfani da damar hakan ya gina wata sabuwar mu'amala a tsakanin su." "Yaro Abdallah Allah ya raya shi, ta tabbata duk inda yake yana cikin koshin lafiya, yana samun ilmi mai nagarta kamar na Bajamushen mahaifin sa, watarana da kafafun sa zai neme ta in har ita ta haife shi." "Uncle sai a lokacin ya ankara da cewa, Rahinah kuka ta ke yi tana share hawaye da gefen gyalen ta, kukan da in za a kashe ta ba za ta ce na hakikanin mene ne ba. Ta fi alakanta shi da cewa, kuka ne na tausayin kai, tausayin yadda Habibu ya yi shattering (daidaita) zuciyar ta da rayuwar ta bakidaya, ya hana ta jin dadin achievements din ta na rayuwa ko kadan. Tun rabuwar ta da Habibu Nahuche abu daya za ta ce ya sanya ta farin ciki (zuwan ta Girei) bayan wannan babu abin da ya kara faranta mata zuciya sai kunci maras dalili, har kuwa da kwalinta na Overall Best Otorlaryngologist." "A hankali ta ke kuka, sautin na ratsa zuciya da kwanyar Uncle Usman. Bai san sanda ya ce, ""Ki yi hakuri Rahinatu, I don't meant to hurt your feelings.But I must perform my role as a father in tabbatar da cewa a wannan stage din kin shiga gidan aure." "Na ji ba Baban Abdullahi ki ke jira ba, amma akwai abin da ke damun ki a karkashin zuciyar ki wanda nake so in sani yanzu?""" "Rahinah ta shiga girgiza kai tana fadin, ""Babu komai Uncle, I'm just finding life boring...""." """...Without him ko?"" Uncle ya karasa mata yana murmushi." "Za ta iya cewa ta firgita da wannan furucin na Uncle din ta. Me ya sa duk wani makusancin ta yake alakanta damuwar ta da Habibu Nahuche? Me suke gani suke fadar haka? Ita kawai har gobe ba ta ga wanda ya yi mata ba ne, amma ba shi ta ke jira ba." """Alright Rahinatu, je ki kwanta. Amma na ba ki kwana daya, wato zuwa gobe da daddare, tunda jibi da safe za ku koma, ki zo ki gaya min mijin da ki ka zaba cikin maneman ki, ko in bai wa duk wanda Allah ya tsaga da rabon sa auren ki. Idan ba ki gaya min mijin da ki ka zaba a gobe ba ya tabbata Baban Abdullahi ki ke jira. Wanda na tabbata duk inda yake zuwa yanzu shi ya manta da ke tunda har aka kai DECADE bai neme ki ba." "Bayan ya san inda ki ke, wanda ke nufin bai da sauran bukatar ki a rayuwar shi ke kadai ki ke dakon wahala"". Raheenah kuka ta ke yi ta ce, a hankali." """Uncle I'm not waiting for him...""" """To in ba shi ki ke jira ba wane ne? Na gaya miki kwana daya na baki ki zo min da abin da ki ka yanke ko in bai wa (Chief Medical Director of Nizamiye) damar fitowa""." "A hectic night for Raheenah, ta kasa barci a tsayin daren bakidayan sa, zaben miji a kwana daya ai ba mai yiwuwa ba ne, da ace ta san abin da kiran Uncle na yau ya kunsa kenan da ba ta zo Kaduna ba, da ta yi ta bada uzuri da aiki har sai ya gaji ya manta. Ya aura mata Dr. Irshad ta kai shi ina? Wannan mayen matan idon sa kullum a kan matasan likitoci mata masu tashen kwarewa a ayyukan su, bin mata kamar bunsuru. Ita farin mutum ma ba ya burge ta sam, this gentle handsome black man ya dusashe hasken fatar kowanne namiji a idanun ta." """Yaa Salamu Sallim!""" "Raheenah ta furta a fili, ko dai Habibu na da alaka da cin kurwa ne (Maita)? Ta yadda ya cinye kurwar ta bakidaya bai barta da ko guda daya na extra-space a zuciyar ta da za ta iya sanya wani a muhallinsa ba. Idan har mayen ne da gaske, hakika ta yarda ya gama lashe kurwar ta." "A washegari da safe Aunty Badiya ta kira ta, ta ba ta hakurin rashin samunta a gida ta ce, amma tana bisa hanyar dawowa daga Zamfara ta je kai Junior ne." """Ni wannan Junior wane ne ne? Babu ranar Allah da za ta fito ta fadi ban ji an ambaci sunan sa a gidan nan ba"". Rahinah ta tambayi Aunty Badiya cikin raha." "Murmushi ta yi, ta ce, ""Kada ki damu, yau za ki ga Junior Abdallah, dan kanina ne, gwauro mai gudun aure irin ki, da za ku taimaki juna ku auri juna da kun taimaki kan ku, mu ma kun taimaka mana""." "Nan da nan Rahinah ta yi fuska, kamar Anty na ganin ta, amma sunan yaron da Aunty Badiya ta ambata ya tsaya mata a rai, yana son tono da tsohuwar soyayyar nata Abdallah din, da ta bi ta sa block ta bibbinne a zuciyar ta." ******* Sumayyah Abdulkadir : Kafin Aunty Badiya ta iso Raheenah ta yanke shawarar barin Kaduna don dai ta guje wa haduwar su yau da daddare da Uncle. Bata da amsar da zata bashi. "Ta soma shirya karyar da ya kamata ta yi masa, amma da yake karyar ba dabi'ar ta ba ce, duk wadda ta kama sai ta kubce, ga shi ba ta shirya fuskantar sa a yau ba don ba ta da amsa ga umarnin sa." "Na farko ba za ta iya auren Dr. Irshad ba don halayen sa kwata-kwata ba su yi mata ba. Ba ta son namiji mai son mata, sannan ga shi foreigner ba kasa daya ba, ba kabila daya ba. Ko dan kasa ne ita kam farin mutum ba da ita ba, sannan ita ba Habibu ta ke jira ba, to me ta tanada da za ta gaya wa Uncle?" Ta iso kofar dakin mai aikin Anty ta tadda Sahura suna hira ita da Labo mai aikin Aunty Badiya. """Sahura taso tafiya za mu yi""." "Sahura ta ce, ""Tafiya ran ki ya dade? Yanzu Labo ta ce Aunty na hanya fa sun kusa shigowa Kaduna. Na dauka kin ce sai gobe za mu koma har ina shirin shiga Malali (gidansu) in dawo?""" """To na fasa kwanan, tafiya za mu yi, in kuma in barki kya taho a motar kasuwa ne to?""" "Da sauri Sahura ta mike tana janyo hijabinta tana fadin, ""A'ah uwargijiya ta, ba zan barki ki kama hanya ke kadai ba""." "Uncle ya fita bai nan tun safe, ta ji hakan a bakin Mu'allim, don haka ta jefa jakarta a bayan mota ta shiga ta tayar, Sahura ma ta shiga ta yi reverse ta durfafi get, maigadi ya bude musu za su fice sai ga Mubaraq na shigowa." "Ta dan dakata ta sauke glass ya ce, ""Aunty unguwa za ku je ne? Mummy sun kusa isowa har da Uncle din mu da Junior, ya dawo daga Belarus kuma anan gidan zai fara sauka ya ga Junior""." "Murmushi ta yi, ta ce, ""Mubaraq ana kirana da gaggawa a asibiti, so I must go now, na yi wa Daddy text, ka gaya wa Aunty zan kira ta in na isa Abuja. A gaida min Junior da Uncle din mu, wani lokaci za mu hadu ai insha Allah""." "Da haka suka yi sallama da Mubaraq ta ja motar da gudu suka hau kwalta. Da ta tabbatar ta yi nisa da Unguwar Sarki, ta hau titin fita garin Kaduna fintinkau, har wata ajiyar zuciyar samun kubuta ta saki." "Daidai lokacin da direban Habibu Mustapha Nahuche, ya karya kan motar su kirar Camero, onedoor, mai dauke da tambarin (NahucheHotels4) mai lambar jihar Lagos wadda a ciki ya dauko Habibu daga filin jirgin saman Kaduna ya shiga gidan Aunty Badiya, da yake suna waya shi da aunty da kamar mintuna biyar da isowar su yana cikin motar yana waya bai kai ga fitowa ba itama ta iso tare da nata direban, wanda ya daukota daga Gusau, Junior a gefen ta, Zarah a gidan gaban motar." "Yana kokarin parking Mu'allim na isko su da gudun gaske sabida jin dadin ganin Uncle Habibu, kusan watanni ukku kenan basu gan shi ba, shi ya bude bangaren (owners side) don Habibun ya fito, tun kafin direban sa ya gama parking, ya kuma karasa ya bude wa mahaifiyar sa tata motar. Yana yi musu oyoyo dukkan su." "Aunty Badiya ta fito tana mika, cikin tsabar gajiya tana, ""Wash Allah!"". Sabida gajiyar zaman mota tun daga Zamfara har Kaduna." "Mu'allim ya ce, ""Welcome Uncle, welcome Junior"". Tare da rungumo kyakkyawan dan uwan nasa Abdallah wanke hannu ka taba dan Habibu Nahuche. Wanda ke sanye cikin tsadaddun shirt da wando masu duhun kala samfurin (Dolce&Gabbana)." "Junior ya na fitowa ya ce, ""Yaya Mu'allim ina kwallona da na ba ka ajiya?""" "Hararar sa Daddyn sa ya yi, ya ce, ""Kwallo? Kwallo daga zuwan mu za ka fara ko Abdallah?""" """Afuwan Daddy, ka sani in ban yi kwallo ba bana jin dadi, ni so nake ma in na gama jarabawa ka kai ni Manchester in zama dan Manchester United""." "Dariya Aunty ta yi, ta ce, ""Karewar buga kwallo kenan, wallahi Baban Junior in ba mu yi da gaske ba Junior dan kwallo zai zama""." """Allah ya sauwaqe!""." "In ji Habibu cikin takaici, a ran sa kuwa cewa ya yi, ""Ranar da Alhuda-hudar uwar shi ta gan shi ya kare da zama dan kwallo da me zan mata tutiya da shi na cewa da na yi, zan fi ta iya kula da shi?" "Suna takawa zuwa cikin gidan Mu'allim ke cewa," """Aunty Rahinah ta tafi, ta ce in ta isa Abuja za ta yi miki waya, an kira ta on emergency a wajen aiki""." "Kwakwalwar Habibu ta tsaya cak! Da aiki, kamar yadda ya dakata da tafiyar da yake yi. Sakamakon ambaton sunan Raheenah da Mu'allim ya yi, but he didn't take it further, and he did not show any reaction. Rahinah nawa ce a" duniya kuma ba tun yau ba yake jin zancen ita wannan Aunty Raheenar a bakin su. Ya fahimci wata 'yar uwar su ce makusanciya ta bangaren mahaifin su. "Aunty ta ce cikin takaici, ""Amma Rahina ba ta kyauta min ba, sai fa da na ce ta tsaya yau za su hadu da Junior"". Takaicin ta daya ta so yau Raheenah da Habibu su hadu, ko Allah zai sa a dace su yi wa juna, don dai ta dade tana shaawar gwada wannan saar tata a ran ta, don a ganin ta Rahinah ba daya take da sauran mata da Habibu yake gudu ba, tafi karfin namiji yayi mata kallo daya." "Habibu ya yi gaba zuwa cikin gida ya bar su yana ta amsa wayoyin da ke shigo masa, bai saurari zancen da suke yi ba." "Bai tafi ba sai da Uncle Usman ya dawo, sun dade suna tattaunawa a falon Uncle a kan harkokin su. Suna cikin maganar sako ya shigowa Uncle daga Rahinah." "Uncle I'm so sorry, an kira ni on emergency ba zan iya jiran dawowar ka ba, yanzu har mun shiga Abuja, Uncle ba ni da amsa ga umarnin ka, I have no one, I have only myself"". Rahinatun ka." "Murmushi ya yi, ya san da ma za ta gudun, amma kawai sai wani bakon tunani ya shigo kan sa, a lokacin da ya daga ido ya dubi Habibu da ke cin abinci a dining din falon sa." -Wace ce uwar dan sa? Me ya sa ko zancen ta bai taba yi ba? "-Habibu ya rayu ne a Jamus, haka diyar sa Raheenah, Habibu na da Da Abdallah, Raheenah na da Da ita ma mai suna Abdallah, amma ko zancen dan ba ta yi." "-Habibu ba ya zancen tsohuwar matar sa, Raheenah ba ta zancen tsohon mijin ta. Ambasada ya ce mijin dan Zamfara ne...! Matar sa Badiya da kanin ta Habibu sun fito daga Zamfara ne..." "A fili Uncle Usman ya ce, ""Ya Jamilal Munzar! (Wato, Ya Mafi Kyawun Masu Gani) Ka taya ni duba al'amarin nan""." """Habibu!""." "Ya kira sunansa da karfi, wanda hakan ya sa Habibu dakatawa da cin abincin sa, ya dago lumsassun idanun sa yana kallon Uncle cikin mamakin karfin tone din da ya kira sunan sa da shi, Uncle ya mike jikin sa har rawa yake, ya isa ga dining din. Ya ja kujera wadda ke fuskantar Habibu ya zauna." """Ka gaya min sunan Babar Abdallah, da garin da ta fito""." "Da wani irin mamaki yake duban mijin Yayar sa, wanda yake tamkar ubangida a gare shi. Duk wasu achievements din sa a rayuwa Usman Girei shi ne sila, don haka yana da matsayin da ya zarta na siriki kawai, yana kallon sa ne a matsayin Yayan sa da suka fito ciki daya kamar matar sa Badiya. Yana da wannan kimar. Ban da haka shi tun barin sa Jamus harshensa bai kara ambaton sunan Rahinah Omar ba... In ya ji mutum dan Adamawa ne ma ba ya tsayawa a inda yake, kada tsautsayi ya sa ya kasance ya san Raheenah Omar ya yi masa zancen ta." "Muryar sa na rawa ya ce," """Uncle Usman me za ka yi da sunan ta da garin ta? Ina fatan ba neman ta za ka je yi ba? I don't need her in my life anymore...!""" "Girgiza masa kai Uncle yayi. ""Ba neman ta zan je ba, ba kuma bikon ta zan maka ba, hakkin haihuwa zan ba ta in kai mata dan ta ta gan shi ta san yana raye, kada hakkin su ya kama ka." Shekaru goma decade guda ka raba Uwa da Dan ta.... Yaa Subhanallah! Sai a yanzu Uncle Usman ya kara tabbatarwa yar sa Rahinar sa ce uwar Abdallah da ya tuna farkon bayyanar Rahinah gare su an gaya masa Habibu ya sato shi ne daga hannun ta yana dan shekara daya. "Kuma tabbas Junior ya zo hannun su ne bai fi shekara dayan ba, ina kwakwalwar su da lissafin su ya tafi tuntuni suka kasa gane hakan daga shi har Badiya?" """Ka gaya min sunanta na ce Habibu, da garin da ta fito""." Ya fada wannan karon cikin karyewar murya da karewar kuzari a jikin sa. Cikin in'ina da magana daga kasan can makoshi ya ce. """Rah...Rahinah Omar... Adamawa...!!!""" "Uncle Usman ya tsura masa idanu, ya kasa cewa komai. Hawaye suka cicciko a idanun sa, hawayen da bai san na tausayin Habibu ne ko na tausayin Rahinah ba? Shekaru goma suna dakon soyayyar juna da kuma Da a tsakanin su? Habibu bai gane halin da Baban Musaddiq ke ciki ba, kuma bai san dalilin ganin cikowar hawaye a idanun sa ba, sai gani ya yi ya tashi daga wajen, ya dauki wayar sa da hanzari ya yi waje." "Mikewa ya yi don ya kasa ci gaba da cin abincin ya nufi sassan 'yar uwar sa. Tana falo ita da su Junior sun kunna kwallo (ball) suna kallo shi da Mu'allim sai iface-iface suke. Tambayar da Baban Musaddiq ya yi masa ta sa duk ya birkice, idanun sa sun kada, afterten years yau ya ambaci sunan ta." "Kuma ba a fatar baki kawai ya fada ba, ya ne tun daga karkashin zuciyar sa, wanda hakan ke bankado rufaffen gyambon yana kaikayi da son neman agaji. A yadda Aunty Badiya ta gan shi ya shigo falon sai ta ce da karfi." """Junior, kashe kwallon nan ku tafi dakin ku, zan yi magana da Daddy""." "Mu'allim ne ya kashe suka fita, Junior na cewa da Abban sa, ""Don Allah kada ka je hotel ka kwana, ka zo mu yi sharing daki na"". Amma ga mamakin Junior Daddyn nasa bai iya ya ce masa komai ba, which is very unusual Junior ya yi magana ya ki kula shi." """Zai zo Junior, ka karkade masa shimfida"". Inji Aunty." "Da murnar sa ya fita yana cewa, ""Thank you Mummy. You know I love you ko? Ke da Daddy?""" "Murmushi Aunty Badiya ta yi, ta ce, ""I know Abdallah, and Mummy da Daddy loves you more""." Da haka ya fice yana tsalle. "Habibu ya zauna gefen Yayar sa, tamkar wanda ya dauki azumin rashin magana. Aunty Badiya ta ce," """Tsakani da Allah Habibu me ye reality na rashin auren ka? Habibu ko dai ka zama ba namiji ba ne bayan haihuwar Junior da ka yi?""" "Duk halin da yake ciki sai da Dr. Badiya ta ba shi dariya. Ta gefen ido ya kalle ta ya yi murmushi, ya ce, ""Auren ne kawai bana ra'ayi, tunda kuma ina azumin litinin da alhamis ina iya rike kaina. Stop all these silly thoughts. Yau ki ce wannan, gobe ki ce wannan." "Badiya ta yarfar da kai gefe, ta ce," """Tsakani na da Maman Abdallah Allah ya isa! Ita ta ki zama da kai, sannan ta hana ka auren kowa. Wa ma ya sani ko asirin su irin na fulani ta yi maka?""" Mikewa ya yi yana dan murmushi kafin ya ce da Yayar sa Badiya. """Ai ita ba ta so na ma ko kadan, balle ta yi min asiri. Masu yin asirin ina ce sai suna son zama da mutum suke yin sa? Ba ta taba so na ba, kuma har abada ba za ta so ni ba""." "Yana fadin hakan ya doshi kofa ba tare da ya juyo ba, kada Aunty Badiya ta ga kwayar idanun sa, ta hango weakness din da ya bakunce su." """Gobe ba zan biyo ta nan ba, daga Hotel zan wuce Lagos""." "Badiya ta yi masa Allah ya kiyaye hanya, ya wuce ba tare da ya kara waiwayowa ba, ya bar ta da hannu bisa haba." "A harabar gidan ya ga Baban Musaddiq zaune bisa fararen kujeru yana waya, ga yadda ya bada nutsuwar sa kacokam ga wayar za ka fahimci waya ce mai muhimmanci yake yi. Habibu na dosowa ya kashe ta, ba tare da ya gama ko ya yi sallama ba." """Baban Musaddiq zan wuce masauki, gobe zan wuce Lagos, ba zan shiga Abuja ba sai upper week""." Baban Musaddiq sai kallon sa yake kamar yau ya soma ganin sa yana kissima abubuwa masu yawa a cikin ran sa. "Ashe surukin sa ne... Ashe shi da Badiya har jini sun hada... Ashe shi ya sa yake matukar son ABDALLAH... Abubuwa da yawa yake kissimawa wadanda sai a yanzu suka samu damar dawowa suna warware kan su, yana kara mamakin ta yadda har ya kai tsayin wannan lokacin bai gane din ba." "Hannu kawai ya iya mika wa Habibun, ba tare da ya ce komai ba suka yi musabaha ya wuce zuwa motar sa. Ya shiga ya tayar da kan sa don ya sallami Solomon tun dazu, Baban Musaddiq bai bar wajen ba sai da Habibu ya fita daga get gabadaya." "Wayar da Uncle Usman ya fito waje yana yi, ba da kowa yake yi ba da Ambasada Shehu ne. Har kuka ya yi a cikin wayar, a lokacin da yake gaya masa ashe Habibu shi ne mijin Raheenah ba su taba ganewa ba?" "Murmushi Ambasada ya yi, murmushi mai sauti kafin ya ce." """Finally kai ma ka gano da kan ka kenan, kamar yadda na dade da ganewa. Da ma na ce ba zan gaya maka ba ne sai ranar da ka gano don kan ka...""." "Nan aka dauko tsohon tarihi, Ambasada ya warware wa Uncle Usman rikicin auren su a Jamus kaf! Ya kare zancen sa da cewa." """Har gobe daga ni har Nene Bilki da kawar ta Yafendo, babu wanda ya san hakikanin laifin da Habibu ya yi mata. Bata taba fada ba. Which means tana sirran ta sirrin sa. Amma kuma tana fushi da shi, ban yarda rashin so ne ba, kada ka takura sai ka ji, don tsakanin mace da miji sai Allah." "Yanzu neman hanyar sulhunta su za mu yi, in ba haka ba ina mai tabbatar maka Habibu da Rahinah za su yi furfura a kan su ba tare da sun yi aure ba""." "Uncle Usman da Ambasada suka ci gaba da kulla mai yiwuwa a tsakaninsu su biyu ba da sanin Aunty Badiya ba, haka ba da sanin Habib da Rahinah ba, sun aje kwanaki uku masu zuwa za su hadu su je Girei su samu Sarkin Fulani a san ta yadda za a shawo kan al'amarin. Bayan nan, sun yanke tabbas za su hada Habibu da Rahinah a gidan Uncle Usman ba tare da sanin kowannen su ba, don su ga irin reaction din kowannen su." "Don a cewar Ambasada Rahinah ta HUCE daga fushin ta tuntuni, ki-fadin ta ne ba zai bari ta nemi Habibu ba. Shi kuma Uncle ya musanta da cewa har yanzu ba ta huce ba, don ko jiya da ya matsa mata da zancen aure, kuka ta yi masa. Ta kuma gudu. Ba za su gane hakikanin abin da ke zukatan su ba har sai sun hada su sun ga juna unexpectedly." "Abin da dattijan biyu ba su sani ba shi ne, daga Habibu har Rahinah babu wanda bai san garin da dan uwan sa ke rayuwa ba... Babu wanda bai san duk wani taku na dan uwan sa ba. Babu wanda bai san ci gaba da nasarorin dan uwan sa ba. Abin da ba su sani ba shi ne, alakar da ke tsakanin su, wadda Badiya da Uncle Usman suka hada, wato kasancewar Habibu kanin matar Uncle din ta, da kasancewar Rahinah diya ta halali ga ubandakin sa, kuma sirikinsa Baban Musaddiq Alh. Usman Girei." ****** "Sarkin Fulani ya gama jin duk abin da ke akwai, ya yi kabbara takbir da tahlili cikin jinjina kudurar Ubangiji. A karshe ga bayanin da ya yi musu, a matsayin sa na babba, wanda dukkan su ya fi su shekaru da tsinkaye." """Bana bayan shawarar ku, ta a maida musu aure ba da sani da amincewar su ba. Kada ku manta Rahinatu na a matsayin bazawara ne a halin yanzu, addini ya ba ta damar zaben mijin aure. Alhamdulillahi tunda saki daya ne a tsakanin su, abin da za ku yi yanzu shi ne, ku yi kokari su hadu da juna, ta ga dan ta ta san shi ne. Ya gan ta, ta ganshi su san alakar zumuncin da ke tsakanin su." "Daga nan ku bar komai a hannun su, ni na gaya muku za su sulhunta kan su. A wannan lokacin addu'a ce tsakanin ku da su ba tirsasawa ba""." Daga Uncle har Ambasada sun yi na'am da shawarar Sarkin Fulanin Girei. ****** *SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI)* 07030137870 *NA HUCE!* (Paid Book) "Ta fito daga bedroom dinta a shirye tsaf, likita mai aji, rike da 'yan mukullayen motar ta ta tadda Sahura a falo tana kallo, ta ce, ""Sahura, yau in na fita sai Allah, don haka kada ki yi girki da ni, ki yi daidai cikin ki, za mu yi dashen dodon kunne har biyu (cochlear implant transplantation) a Nizamiye, don haka sai kin gan ni kawai""." "Sahura ta ce, ""Allah ya yi jagora, Allah ya bada sa'a uwar daki na, Allah ya bada ladan ceton kunnuwan al'umma""." Dariya ta yi ta wuce ta fita tana karanto addu'ar fita daga gida. """Ina so ki ba ni hankalin ki""." Baban Musaddiq ya ce da Aunty Badiya. "Ta gyara zaman ta tare da tattara masa kafatanin hankalin ta. Baban Musaddiq tun jiya ta ke ganin shi upset, ga waya akai-akai shi da wadanda ba ta san ko su waye ba, abu kadan ya dau waya ya fice ya gama magana sannan ya dawo, abin da ba halin sa ba, babu wayar da ba ya iya amsawa a gaban ta a baya." "Yanzun dai Nene Balki ce ta ba wa Ambasada shawarar ya kamata Badiya ta san komai, kuma a gidan ta ya kamata Habib ya ga Rahinah ba a Abuja ba, tunda a can Junior yake. Ba ta ga amfanin kin sanar da Badiya da wuri ba." "Shi kuma Ambasada ya gaya mata cewa, Badiya tana kullace da tsohuwar matar Habibu a kan ita ta hana dan uwan ta aure, da yadda ba ta taba neman ta ga dan da ta haifa ba inji Uncle Usman, Nene ta ce," """Akwai fahimta da kyakkyawar mu'amala tsakanin Rahinah da matar kawun nata, insha Allah komai zai zo da sauki""." "Don haka shawarar Nene Balki Uncle Usman ya bi yanzu. Ya ce," """Maman Junior I have something special for you, mene ne zai zama tukwici na?""" "Murmushi Dr. Badiya ta yi, ta ce, ""Duk abin da ka ke so shi zan ba ka Daddy""." "Ya ce, ""Shin wace ce babar Abdallah ne, kuma a ina ta ke?""" "Nan da nan Aunty Badiya ta canza fuska kamar ba ita ke ta fara'a yanzun ba, ta ce, ""Daddy da zan ganta Allah kadai zai raba ni da matar nan, na tabbata surkullen su na fulani ta yi wa Habibu ya kasa yin aure." "Ban san ta ba, ko sunanta ban taba tambayar sa ba, sabida ba ni da wata alaka da ita. Yaron da ta haifa ta yasar, babu ko waiwaye ga shi nan Allah ya raya shi." "Ita kuma Allah ya yi mana shari'a da ita a lahira""." "Uncle sai ya kama dariya, ya ce, ""Wato fulani surkulle gare mu? Kuma 'yan Nahuche ai fulanin ne in miki kirarin garin ku Zamfara GALMA UWAR RUFI, ko ba ku son mutum ba ku hwadi. Ke kam ba ki yi galmar ba kin hwadi ba ki son matar Habibu, ga shi kuma ta zame miki dole, sai ki dau na Annabawa ki soma tunanin hanyar sulhunta su, tunda kuwa ba kowa ba ce 'yar ki ce Dr. Raheenah""." "Kusan za a ce Aunty Badiya shidewar wucin gadin razana ta yi, sabida ta san Baban Musaddiq ba ya yin joke shi kai tsaye yake fadar komai. Ta kura masa ido ta kasa daukewa, shi kuwa sai lumshe mata ido yake yana gyada mata kai cikin ba ta tabbacin maganar sa. Da kyar Aunty Badiya ta iya cewa," """Wace Dr. Rahinar?""" "Shi kuma bai bata lokaci ba ya ce, ""Ya ta Raheenah""." "Ya kwashe labarin komai ya gaya mata, sak! yadda Ambasada ya labarta masa." """Idan Ubangiji ya lullube al'amari, babu dan Adam din da ya isa ya bankado shi, sai a lokacin da Ya nufa. Don haka ki sauke duk wasu makaman yakin ki a kan Maman Abdallah mu taru mu taimaki yaran nan su koma auren su, don zan iya yi miki rantsuwa kan cewa soyayyar juna ta hana su aure." """Yanzu me ye abin yi? Da me zan iya taimakawa?"" cewar Badiya cikin mutuwar jiki." Uncle Usman ya gyara zama. Tiryan-tiryan suka soma tsarawa. ****** """Kin kyauta Rahina, ni da ma na san kafin in dawo za ki gudu, to duk abin da ki ke yi ki bari ki zo karshen satin nan, I'msure ba kya aiki asabar da lahadi, Sarkin Fulani ma ya ce ki biya ku gaisa idan kin zo""." "Raheenah ta marairaice murya abin tausayi, ta ce, ""Uncle, bana son zancen aure, don Allah Uncle ka kyale ni, idan ka takura zan iya kamuwa da depression, I have a lot to do I can't put myself in any relationship... Zan iya rike kaina Uncle, don Allah kada ka sake yi min zancen aure""." "Murmushi Uncle ya yi, ya ce, ""Na yi alkawari ba zan sake ba, za ki zo din? Weve planned a get together dinner na kammala karatun Musaddiq""." "A hankali ta ce, ""Insha Allahu zan zo Uncle, tunda ka yi alkawari""." Murmushi ya yi yana kallon matar sa Badiya. """Finally, ta amince za ta zo din""." """To Allah ya sa shi ma ya yarda ya zo don ka san shi kamar tsuntsu yake, yanzu haka sai ka ji ya bar Lagos din ma"". Ta fada tana dialling number din Habibu Nahuche." Har ta yi karar ta ta gama bai dauka ba. Tana kokarin sake kira sakon sa ya shigo. """In a meeting, call later""." "Murmushi ta yi, ta tura masa nata sakon." """Call me da zarar ka fito""." Yana fitowa din kuwa ya kira ta. """Ya ya ku ke Aunty, ya Abdallah?""" """Sarki mai Abdallah, ni boarding zan kai shi in huta kallon kwallo. Za ka iya zuwa karshen satin nan? Baban Musaddiq ke gayyatar ka get together dinner iya mu i'mu na gama degree din Musaddiq and zaa yi hotuna da bidiyo don tarihi, don haka presence dinka is very vital""." "Habibu ya yi dan murmushi, zumunci da 'yar uwar sa ba ya hada shi da komai, don ba shi da wanda ya fita a duniya bayan mahaifiyar su. Ya ce, duk muhimancin uzrurrukan sa yana bari sabida hidimar Aunty Badiya da iyalin ta." """Zan yi squeezing time don ina da muhimman abubuwa a gabana a weekend din nan""." """A bar komai a zo mana, in babu kai abin ba zai yi armashi ba"". ""I know Maman Abdallah"". Da haka suka yi sallama." "Kusan a tare Habibu Nahuche da Raheenah Omar suka shigo garin Kaduna, shi a jirgi daga Lagos, ita a motar ta daga Abuja. Sahura na gefen ta tana zuba mata hira, amma ga mamakin ta ta kasa ce mata komai. Yau jin kan ta ta ke kamar an dinke mata baki, an cire dukkan kuzarin ta. Ba ta san hakikanin abin da ke damunta ba." "Raheenah ta riga Habibu isowa gidan Uncle, kuma kai tsaye sai ta wuce dakin ta na gidan ta kwanta, don duk yaran gidan Aunty ta kwashe su ta kai su gidan aminiyar ta a Malali, ta ce sai takwas na dare za ta turo a dauko su. Musaddiq ne kawai a gidan, don haka bayan sun gaisa da Aunty ta ce ba ta jin dadi, kwanciya za ta yi kamin Uncle ya shigo gida. Da ma kuma tana hutun sallah." "Ba a fi awa guda da kwanciyar Rahinah ba Habibu ya iso, karkashin rakiyar ma'aikatan Nahuce Hotel na garin Kaduna, wadanda suka dauko shi daga filin jirgi. Motoci uku jibga-jibga kamar su fashe don koshi da sheki, kowacce dauke da logo na NAHUCE GROUP OF HOTELS. Sanye yake cikin (black-grey-German-Suit) wadda ta fiddo zahirin ilhama da cikar zatin sa, kwarjininsa ya fiddo zahirin matashin miloniya mai tashe, HABIBU MUSTAPHA NAHUCHE wanda kallo daya za ka yi masa ka tabbatar Allah ya gama yi masa kowacce irin ni'imar rayuwa." "Kallo daya ba zai gamsar da idon ka a kan HABIBU NAHUCHE ba, ba tare da marmarin ka yi masa kallo na biyu ba. Idaniya ba sa taba gajiyawa da kallon sa sabida wani sassanyan sirrantaccen kyau da haiba da Allah ya yi masa." """The successful business tycoon of Zamfara""." Kamar yadda kafafen yada labarai ke kiran sa. "Habibu Mustapha Bilyamin Nahuche, ya fito daga motar hotel dinsa yana taku majestically, zuwa cikin gidan Aunty Badiya." "Musaddiq ne ya fara taren sa a bakin kofar shiga falon, da runguma mai karfi yana fadin." """Welcome Uncle Habib!""" "Muryar Musaddiq ce ta fiddo Aunty daga kicin, murmushi fal bakinta ta ce, ""Ban zaci za ka sauka haka da wuri ba. Musaddiq ka je ka taho da su Abdallah""." "Musaddiq ya ce, ""Aunty da kin kyale Abdallah sai Uncle ya ci abinci ya huta, yana zuwa zai ishe shi da zance da dumi ba comma ba full-stop""." "Aunty ta ce, ""Sai kuma Uncle din ya ce maka bai son ya cika shi da dumin? C'mmon je ka dauko su maza gidan Anty Hassu""." Habibu na jin su amma rabi-da-rabi don hankalin sa ya tafi ga wayar da yake ta amsawa akai-akai. "Kafin dawowar Musaddiq Uncle ya dawo, ita kuma Aunty da mai aikin ta ba su zauna ba sun dukufa shirya abinci bisa makekiyar darduma da aka shimfida a falon Uncle. Fita goma ko shiga goma za ta yi sai ta kalli Habibu ta yi murmushi, ba abin da ta ke tsananin so irin ganin reaction din da zai nuna idan ya ga Raheenah yau a gidan ta. Ko za a kashe ta ta san Raheenah ce ta farko, kuma ta karshe a zuciyar Habibun, ko da kuwa su duka a yau sun nuna musu ba su taba sanin juna ba." "Uncle Usman ya bi Aunty kicin ya ce, ""Tana ina ne?""" "Aunty ta yi dariya ta ce, ""Tunda ta zo, tana daki a kwance ba ta fito ba, kamar wadda aka yi wa duka""." "Uncle ya girgiza kai ya ce, ""Bari in je in yi serving din sa abinci ya ci, idan ya gan ta ba zai iya cin abinci ba, ga shi ban san yadda kowannen su zai karbi dan uwan sa ba""." "Ya juya ya fito, ita kuma Aunty ta hau kiran Musaddiq a waya don ta ji ko sun taho?" "Uncle da kan sa ya zuba ma Habibu duk abin da Aunty ta dafa a kan plate guda yana ta jan shi da zance yana loda abincin a kan faranti har sai da Habib ya ce, ""Abincin nan ya yi min yawa fa!""." "Uncle Usman ya ce, ""So nake ka tada komada daga wannan ramar taka, kai kenan kullum kamar a bushe ka fadi?""" "Murmushi ya yi, ya ce, ""Yaya dan Adam zai yi kiba alhalin rayuwar sa ba ta taba hutawa ba? Kullum cikin kujuba- kujubar nema yake, sannan babu iyali a gefe wadanda taimakon su zai sa ya yi kibar?""" "Baban Musaddiq ya ce cikin halin ko'in kula, ""I can relate, I see""." Sannan ya tura masa plate din abincin gaban sa. Bayan ya aza cokali da fork akai. "Gab da zai gama cin abincin Abdallah da Zarah suka shigo, Abdallah ya yi kan sa da mugun gudu yana," """Daddy na, oyoyo!""Ya rike shi sosai cikin jikin sa tamkar zai maida shi cikin sa yana sunsunar sa, ya ce, ""Junior, me ka ke ci haka? Ni girman ka tsoro yake ba ni""." "Dariya Abdallah ya yi daidai lokacin da Aunty ta shigo, ta ce, ""Junior, je ka dakin Zarah za ka ga bakuwa tana barci, ka taso ta, ka ce ta zo in ji Daddy ya dawo""." "Da gudu Abdallah ya fita don shi yaro ne mai bin umarni, yana fadin, ""Daddy kada fa ka je ko ina, yanzu zan dawo"". Aunty ta zauna gefen Habibu tana yanka mishi apple, Daddy kuma na diban sa da zance." "Barci ta ke sosai, lokacin da Abdallah ya shiga dakin. Yatsun kafarta ya hau ja yana fadi da karfi, ""Bakuwa ki taso ki zo in ji Maman mu, Daddy ya dawo""." "Kamar a mafarki 'yar siririyar muryar yaron ta ke ratsa kunnuwan *Rahinah Omar.* Jin muryar ta yi tamkar busar sarewa cikin kunnuwan ta, ga shi sai kara maimaitawa yake yi. A hankali ta ke bude fararen idanun ta, wadanda barci ya sa suka canza launi tana kallon kyakkyawan yaron. Har idanun ta suka gama washewa sosai a kan sa." "The cute face looks so familiar... and the feelings for him is not a strange feeling. Abin nufi ji ta yi ba yau ya ginu a zuciyar ta ba. Wani daddadden feeling ne wanda babu irin sa (maternal love) irin wanda kowacce uwa ke da shi a kan dan ta, walau ta san shi ko ba ta san shi ba." "Amma a halin da ake ciki, Rahinah Omar ta ji kaunar yaron ne kawai a ranta ba tare da ta san daga ina kaunar ta keto ta fito daga karkashin zuciyarta ba." "Murmushi ta yi masa, sannan ta yunkura ta tashi daga kwanciyar ta sa hannu ta yafito shi. Matsowa ya yi gaban ta ya tsaya, a kintacenta zai yi shekaru goma, amma ba ta taba ganinshi cikin gidan ba, don haka tunaninta ya ba ta shi ne Junior da suke yawan ambata. Hannu ta sa a kan lallausar sumar kansa ta ce," """Kai ne Junior?""" "Gyada mata kai ya yi, sannan ya juya zai fice. Raheenah sai ta samu kanta da cewa cikin rawar murya, ""Junior ya ya sunanka na gaskiya?""" "Sai da ya kai bakin kofa zai fice ya juyo ya ce," """Sunana Abdallah Habibu Nahuche!!""" """ABDALLAH NAHUCHE!!!" Rahinah ta maimaita a fili. A ina ta taba sanin wannan sunan? Tamkar wadda aka fizga a zuciya ko kuwa aka tsikara sai ta samu kan ta da mikewa wuf! Ta bi bayan sa ko kallabin ta ba ta tsaya daurawa ba. "Dakin Aunty Badiya ta fara zuwa, babu kowa! Da sauri ta fito zuwa inda ta jiyo tashin muryoyin jama'ar gidan, wato falon Daddy." "Nan ta tadda su complete family yadda sukan zauna koyaushe. Amma a kusa da Aunty a tall, giant, handsomeman, ya bata baya, wanda duk hayaniyar da ke tashi a falon babu tashin muryar sa. It's either kamar bai falon, ko kuma akwai abin da yake yi da ya hana shi magana. Waya ce a hannunsa yana daddannawa, sallamar Rahinah Omar ta sanya shi wani irin dagowa in a slow motion." "Ita kuma ba tare da ta lura da shi ba ta nufi inda Junior yake can gefen Musaddiq yana ta zuba masa zance. Tamkar wadda ake controlling da remote haka ta nufi gurin yaron absentmindedly ta tsugun na a gaban sa, tafin kafarsa ta kama tana son tantance abin da ke cin ta a zucci." "Tawwadar Allahn data ke son gani tana nan a kan babban yatsar kafar sa, sai girma da fadi da ta kara." """ABDALLAH!""" "Habibu ya fada da karfi tamkar ya ga wani abun da zai cutar masa da Da. Irin tsugunnon da ta yi a gaban yaron, irin sa ta yi a gaban Ambasada Shehu Bichi tana rokon sa ya karbar mata 'yancin ta daga hannun sa. Bafullatanar mai yawan sumar kai, da hasken fatar da ko a cikin farare ita fara ce lamba daya tsugunne gaban dan sa, wadda cikin kowanne hali ba zai kasa gane ta ba, image din kyakkyawar fuskar ta ba zai taba gushewa daga zuciya da kwakwalwar sa ba." "Balle ma cikin shekaru goman da suka gabata, canjin da Rahinah Omar ta samu na halitta ba wani mai yawa ba ne. Canji ne kawai irin wanda nauyin shekaru ke haifarwa diya mace ba tare da ya canza appearance na kuruciyar ta ba. She is still that ravishing, glowing and sparkling lady fiye da yadda ya baro ta a Germany." "Sai ma wata 'yar kiba-kiba da ta kara mai nuna sukuni, wadata da kwanciyar hankalin da ta ke ciki." "Kiran da Babansa ya yi masa haka da karfi ya firgita shi, don haka da sauri ya kwace kafar sa daga hannun Rahinah ya nufi baban sa yana buya a bayan sa." """Daddy boye ni, ni ma ban santa ba""." "Ya yi daidai da lokacin da Rahinah ta juyo, ta sauke ragaitattun idanunta a kan Habibu Nahuce, wanda ke kallonta babu ko kiftawa. Her Ex- Habibu ne! wanda ko mutuwa ta yi ta dawo ba za ta kasa gane shi ba, balle dan da ke tsakaninsu." "Kallon-kallo aka shiga yi tsakanin Habibu Nahuche da Rahinah Omar, kallon da ke rewinding duka incidents din shekarun can baya a Jamus, abubuwa da yawa da suka gabata na gilmawa a idanun su." "A take Rahinah ta soma ja da baya cikin tsoro da kidima. Tsoron da ya haifar mata da karkarwar jiki da ta zuciya, amma ga Habibun, ba zan iya cewa ba." "Domin kuwa bayan idanun sa sun farfado daga shock din ganin ta a inda bai taba tsammani ba, wato a gidan Yayar sa, ya kara yi mata kallo na biyu, kallon da ya tattaro duk wani kundi da ya lullube a karkashin zuciyar sa. Ya bude shafukan sa filla-filla, shafukan tun shigowar Raheenah cikin rayuwar sa, and the roles she played in shattering it (da rawar da ta taka wajen yagalgala ta)." "Eh, ya kira shigowar ta cikin rayuwar sa ba komai ba sai kacaccala ta (shattering dinta into pieces) tunda har yau ga shi nan a gantale bisa titi yana ragaita babu iyali, in an kuma bi salsala wannan bafullatanar ita ce sila." "Domin kuwa soyayyar ta ce har gobe ke azabtar da shi ko na second daya bai taba hutawa ba. The marital physical relationship din da ya wanzu tsakanin su, will forever remain green a zuciya, gangar jiki da kwakwalwar sa, wanda ya dusar da hasken duka sauran mata daga idanun sa yake musu kallon ba bambancin da nasa jinsin, sai ita kadai ce mace a idanun sa." "Ba zai gaji da cewa ba Rahinah Omar... ta tafi da dukkan farin cikin sa, sannan dawowar ta a yau ya san yana nufin abubuwa da dama in bai yi wa tufkar hanci ba." "Tunda ita tamkar mala'ikar daukar rai ta ke, ba ta zuwa ta tafi, ba tare da ta kashe zuciyar mutum ba." Ta zame masa tauraruwa mai wutsiya ganin ki ba ALHERI ba. "Yana cikin tattala 'yar ragowar rayuwar sa da ta riga ta kashe ya samu control din ta a yanzu, shi ne kuma ta dawo cikin rayuwar sa ta inda bai zata ba." "A wannan karon, a wannan lokacin, a wannan 'yan dakikan, Habibu Nahuche, ya kudiri aniyar yaki da dawowar Rahinah Omar cikin rayuwar sa. Ba zai bari ta sake yin galaba a kan sa ba. Ko da wacce ta zo zai tarbe ta kyakkyawar tarba irin ta yakin ceton rai." "Ko da ma can ya san tana existing a garin Abuja matsayin cikakkiyar *otorlaryngologist* din National Hospital da NIZAMIYE. Yadda aka yi ta zo gidan Yayar sa ne bai sani ba, watakila wani ya gaya mata ga inda dan ta yake shi ne ta zo, za kuwa ta sha mamaki in ya ce mamaki, yana nufin mamaki mai gigita kwanyar diya mace. Domin daga yau Abdallah zai bar gidan Badiya." "Hannu ya sa ya janyo Abdallah da ke faman buya a bayan sa, ya yi masa kyakkyawar mafaka a kirjin sa, ya rungume shi sosai idanun shi a lumshe." """Don't be afraid Abdallah, I'm here with you babu mai taba ka sai ruwan sama""." "Daga nan ya mike tsaye rike da hannun yaron, kyakkyawan kallo na biyu wannan Rahinah Omar ba ta samu daga gare shi ba," """Maza Abdallah debo kayan ka tafiya za mu yi""." "Daga Aunty Badiya har Daddy bin sa suka yi da kallo, kallo na mamaki. Domin ba haka suka yi zato ba." "Yayin da Dr. Raheenah ta sunkuyar da kai, hawaye fal idanun ta. (Between happiness and excitedness) ba ta san wanne ta ke dulmiyewa tana nutso a cikin sa ba. Abdallahnta... her only son Abdallah... after a decade, yau shi ne tsaye a gaban ta gidan Uncle din ta." "To ta ina ya zo? Wannan na nufin... shi ne Junior din, dan kanin Aunty Badiya... wannan na nufin Habibu Nahuche... shi ne kanin Aunty Badiya... Ta wani irin lumshe idanun ta a hankali, tsigar jikinta na tashi, ko kafin ta farfado daga shidewar wucin gadin da ta tafi, babu Habibu babu dan sa Abdallah a falon." Ta ina za ta bari Abdallah ya sake kubuce mata A KARO NA BIYU? Ai ko yakin duniya na biyu ( *World War II* ) za su yi ita da Habibu wannan karon sai ya ba ta dan ta!!!. "Da gudu-gudu ta bi bayan su tana kiran sunan ""ABDALLAH"". Yayin da jamaar falon duka suka bi su da kallo. Ba ta cimmasu ba sai a harabar gidan yana kokarin saka katuwar jakar kayan Abdallah a bayan jibgegiyar motar da ke ajiye a ma'adanar motoci." "Sai ta rasa kwarin gwiwar karasawa gare su, sabida kallon dibar karen mahaukaciyar da Habibu ya yi mata, ta tsaya daga bakin kofar shiga falon Daddy Usman tana kallon su kawai suna shiga mota, kaunar Dan ta na kara bunkasa a zuciyar ta kwatankwacin ta ranar da ya zo duniya, hanyoyin da zata bi ta karbi Abdallah ta take tunani, koda hakan shine *struggle* na karshe da zata gudanar a rayuwar ta. Daga nan har *supreme* *court* ! Wato kotun *daga ke sai Allah ya isa!!!*" "Ganin sa da ta yi yau matsayin kanin Aunty Badiya matar Baban ta, ta san Allah ke nufin farawar sababbin al'amura da dama a gare su, wadanda a iya kintacen ta da tsinkayen ta bata hango farkon su balle karshen su ba. Na baya duk shimfida ne, wato wanda ya faru a Jamus, yanzu ne zasu fara ta babu dadi ita da dan mutanen Nahuche. Domin ko sama da kasa zata hade sai ya bata dan ta." "Abu daya ta sani shine (maintaining self-esteem) din ta yanzu ta fara, ko da soyayyar ita ce ajalin ta, amma tana da right din ta na rikon Abdallah wanda addini da shari'ah suka bata har sai ya balaga in ya so ya zaba tsakanin ita da shi." "Idan a da bata da gata shi yasa yake walagigi da ita da dan ta yadda yake so to a yanzu tana da gata kamar koma fiye da kowa. Sannan ta tsaya da kafafun ta, ta wuce wargin kowanne da namiji. Wata fuskar yanzu ta fi gaban" Mari. Don haka ita da Habibu a je zuwa..wai mahaukaci ya hau kura "*SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI KE CEWA, MU KARASA LABARIN ""NAHUCHE. (DAGA FUSHI NA) A LITTAFI NA 3 NAN BA DA JIMAWA BA INSHA ALLAHU.*" 20/02/2022 : *SUMAYYAH ABDULKADIR* *NA HUCE* PAID BOOK "Daga wannan kallon shakulatin bangaron da ya yi wa Rahinah, Habibu ya ja hannun yaron ya saka shi a gaban mota ya rufe har da murza key, ya zaga daya bangaren ya shige ya rufe, ya yi juyi (reverse), ya ci taya sannan ya zugi motar da mugun gudun da ya sa Maigadi wangale masa kofar ba shiri, saura kadan ya bi ta kan yatsun Hashimu mai gadi.La-shakka da dai a ce ba (interlocks) ne a wurin ba da Habibu ya bule Rahinah da kura, kurar da watakila in ta koma cikin gida baza su gane ta ba. Shi kan sa Abdallah ya tsorata da wannan jan mota da Baban sa ya yi kamar za su tashi sama, kamar zai bar Kaduna dasu a mota zuwa birnin Sin." "Sai ta tsaya daga inda take tsaye cikin mutuwar jiki, da matsanancin bacin rai,gawaniirin sagewar guiwa da ya same ta duk a lokaciguda, tana mamaki da al'ajabin abin da Habibu ya yi mata kamar ko a hanya bai taba sanin ta ba." "Tadade da saninkobajimako ba dade watarana dole zasu hadu tunda Abdallah ya riga ya yi tying alaqar da bazata kankaru har abada ba, amma bata zaci in sun hadun irin reaction din da zai nuna kenan ba. Ai ko Habibu bai taba sanin ta ba yau ya fara ganin ta ba zai mata wannan wulakancin da tozarcin ba, ita da Dan ta! Wannan karfin hali zata ce ko fin karfi da me zata kwatan ta shi (Hausawa suka ce gwano ba ya jin warin jikin sa)." "Dr. Rahinah Omar ta yi ajizanci mai girma da ta manta baya, kalaman ta na shekaru goma a baya har kullum dada komawa danye kumakorre sharr suke sake yi a zuciyar Habibu Nahuche. Tsayin shekarun nan da suka gabata da canzawar zamani da yanayin rayuwa hadi da tarin nasarorin da ya samu a rayuwar sa, basu sa ya manta da zafi, daci da dafin da kowannen su ya zuba kamar digar dalma a zuciyar sa ba." "Rahinah na nan tsaye kamar an dasa ta a wurin. Daga karshe ta ga cewa in ta yi kuka a dalilin wulakancin dan mutanen Nahuche ta fadi babu nauyi, tana da tabbacin ya yi ne don ya bakanta mata, idan ta bari ran ta ya sosu irin haka Habibu ya ci nasara kenan? Don haka ta daddage ta hadiye wani mayataccen kukan bakin-ciki da ya yunkuro mata. Ta yarfe wasu zafafan hawaye da suka tsatstsafo mata." "Juyawar nan da za ta yi da nufin komawa cikin gida, sai ganin kafatanin jama'ar gidan ta yi tsaye a bayan ta. Sun zuba mata ido suna kallon duk abin da ke faruwa." "Rahinah ta rasa inda za ta sa kanta don kunya, bakin ciki da takaicin wulakancin da Habibu ya yi mata a bainar jama'a. Ga hawaye shabe-shabe a idanun ta. Ita ba shi ta biyo ba, dan ta ta biyo. Linzamin da ke zarge wuyan Uwa akan dan ta, shi ya zargo ta ya fiddo ta daga daki ta biyo bayan Abdallah ba tare da ta san lokacin da ta yi hakan ba.Yanzu kuma za ta ci gaba da bibiyar abin ta da karfin gaske, daga nan har kotun koli sai an ji su ita da Habibu Nahuche, sai ya ba ta abin ta in dai akwai shari'ah a duniya." """Lafiya Rahinah? Kin san su ne?""" "Daddy da Aunty har suna hada baki wurin tambaya. Sai ka rantse da Allah basu san komai ba. Ba kuma su suka hada komai ba. Maimakon ta ba su amsa sai ta girgiza kai ta russunar da jikakkun idanun ta, wadanda nan da nan sun kada sun yi jajir kamar gauta, abin ki da farar mace ita kanta tayi jazur musamman dogon karan hancin ta, ta sa kai ta wuce su zuwa ciki da dan banzan sauri, har tana hadawa da gudu-gudu da mugun cin tuntube." "Kai tsaya bata tsaya a falon ba. Dakin ta ta nufa ta soma kwashe komatsan ta data barbaza a kan durowar gefen gado tana dannawa a hand bag din ta, sannan ta janyo trolley din kayan ta ta fito rataye da mayafin ta bisa kafadun ta, idanun ta bakidaya sun kankance sun juye sun canza launi. Har wani hayaki-hayaki da yaji-yaji suke yi mata. Tsabar tukuki da bakin-cikin dake cin ran ta." "A bakin kofa suka ci karo da Aunty, ta saki baki tana kallon Rahinah. ""Ina za ki je haka Rahinah a daren nan?""" "Ba ta san lokacin da hawayen da take ta tattali suka balle mata ba, ta yi maza ta sadda kai don kada ta ba su damar zubowa a gaban Anty, raunin ta ya fito baro-baro wato (weakness) duk da yadda ta ke kokawa da shi, ta ce," """Aunty za mu koma ne, ina nufin Abuja""." "Aunty Badiya ta yi murmushi wanda ya tsirga har cikin ran ta, ta ce, ""Anya Rahinah? A wannan Najeriyar da muke ciki ne za ki kama hanyar Abuja after 8pm (bayan karfe takwas na dare)? Ido na ganin ido ma yaya aka kare da insecurity? Ki sake tunani dai. In dai don Baban Junior ne, ya tafi, kuma bana jin zai dawo gidan nan nan kusa. ""." "A firgice Rahinah ta kalle ta. Aunty ta sake yin murmushi wanda har hakoran ta sai da suka fito, ta kama trolley din ta maida mata dakin tare da kamo hannun ta suka koma ciki." "A gefen gado suka zauna hannun Rahina na cikin na Aunty Badiya. Ta rike Rahinah tsam-tsam kamar ta maida ita cikin ta don so da kulawa. Tana jin wata sabuwar kaunar Rahinahn na ratsawa a ran ta. Wadda ta zarta ta alaqar diyar miji dake tsakanin su a baya wadda mijin ta Uncle Usman Girei ya hada, a yau dangantakar ta kara matsayi mai girma dalilin kasancewar ta mahaifiya ga dan ta Junior. Dan ta Abdallah, da kanin ta kwalli daya a duniya ya haifa, kanin da bata da kamar sa a duniya, uban dan da take so har fiye da nata 鈥檡 a 鈥檡 an data haifa a cikin ta." "Rahinah, gaya min gaskiya, kin san Baban Junior ne a wani wurin?""" "Da sauri Rahinah ta cira kai ta dubi Aunty, sannan tayi saurin sadda kan ta kasa, ba tare da ta ce komai ba. Amma komai ya gama bayyana kansa cikin idanun ta. Idanun sun ce ""sani ba dan kankani ba!""" Aunty ta ci gaba da nacin tambayar ta. """In ba ki san shi ba ta yaya daga ganin sa za ki ce za ki tafi Abuja afujajan? Me ye ki ka bi su wajen mota daga ganin mutum da Dan sa in baki san su ba? Kuka fa muka ga kina ta yi har da sheshsheka Rahinah?""" "Nan ma Rahinah shiru ta yi kamar da dutse Aunty Badiya ke magana. Aunty ta jinjina kai cikin mamaki, ga dukkan alamu Habibu ya gamu da wadda ta fi shi iya zurfin ciki. Wadda ta fi shi taurin kai da wuyar sha'ani. Tambayar duniya Aunty Badiya ta yi amma Rahinah gumm! Ba ta ce komai ba. A karshe ma sai ta kifa kai akan cinyoyin ta ta fashe da kuka." """Ya sake tafiya da Abdallah for the second time (a karo na biyu) wannan karon ban san ina zai kai shi ba kuma..., I have no idea a kan abinda zai yi yau, don ya kara raba ni da shi...." "Aunty Habibu bashi da adalci ko kankani, bashi da tausayi bashi da imani a zuciyar sa in dai a kai na ne, ban san meyasa ba, ban san dalili ba, kan sa kadai ya sani da selfish interests din sa...." "Na tabbata yanzu zai yi duk abinda zai iya wajen kara nesanta ni da ABDALLAH, har fiye da wanda ya yi na shekarun baya tun da yau na gan shi a inda bai zata zan zo ba. He 鈥檚 good at kidnapping a son from his mother (ya kware wajen sacewa Uwa dan ta) da kuma raba zuciyar Uwa da ta dan ta. Wannan shine babban abinda HABIBU NAHUCHE ya fi kowa kwarewa a kai Aunty; ZALUNCI!""" "Magana 鈥฀. zarar bunu ta fito daga zuciyar Rahinah don bana ce daga bakin ta ba, irin maganar nan ta mutum da" "zuciyar sa. domin fatar bakin ce kawai ke motsi, amma zuciyar ta ce ke magana." "Amma hakan bai raunata ta ba kamar wulakancin da Habibu ya yi mata a idanun jama 鈥檃 r gidan, ta hanyar pretending kamar bai san ta ba, yayi mata kallon banza, ya kuma dauke dan sa yasa a mota suka yi tafiyar su, bayan ya bule ta da iskar motar sa." "Aunty ta rungumo ta a jikin ta cikin kauna, tana lallashin ta ta hanyar jijjiga kafadunta kamar tana rarrashin karamin yaro. Zuciyar ta bakidaya ta karye. Lallai abinda suke zato cewa karami ne tsakanin Rahinah da Habibu to ba karamin bane asexpected (yadda suka zata). Wadannan sunaye da Rahinah ta kira Habibu da su sun bata mamaki matuka, domin a iya sanin ta a duniya babu mai akasin su irin Habibu, bata taba ganin ko jin wani ya suffanta shi da su ba (zalunci). Karewa ma, ita bata taba ganin mutum mai kirki, mai saukinkai, mai tausayi da adalci a duniya irin kanin ta Habibu ba!" "Dankwalin Rahinah ya zame ta baya, wanda hakan ya sa sassalkan bakin gashin kan ta na fulanin usli ya kwanto lambam a gadon bayan ta ya rufe fuskar ta bakidaya. Aunty ta dauka tana daura mata bayan ta tufke mata jelar dogon gashin kan nata wuri guda. A lokacin Uncle Usman ma ya shigo dakin, tun daga waje ya ke kakabi yana fadin," """Me na ji ana cewa ne? Wai Rahinah zata tafi Abuja yanzu? To me yayi zafi?" "Ki kama hanyar Abujan a daren nan ki ga yadda za mu yi ni da ke Rahinah. Shin Mai sunan Dada, a ina ki ka san HABIBU ne ma???""" "A muryar Uncle babu wasa ko kadan yau, babu lallashi irin wanda ya saba yi mata, tambaya ce kawai yayi bisa umarni da ke tsananin bukatar amsa. Bai taba yi mata magana in a serious tone irin na wannan karon ba. Don haka kukan da Rahina ke yi ya katse kan sa da kan sa, ta soma shiga taitayin ta yayin da wata irin fargaba da tsoro suka rufto mata a lokaci guda.Me zata ce da su tunda itama har yanzu bata gama tabbatar da irin alaqar da ke tsakanin su da shi ba?" "Uncle Usman ya zazzaro ido yayi kan Rahinah kamar zai buge ta yana fadin," """Za ki gaya min inda kika san shi ko in kira shi da kaina shi ya fada min? Na ce a ina kika san shi?""" "Da sauri ta dago ido ta dubi Baban nata, ta yarda yau ya kauda duk wani wasa da farantawar diyancin da ke tsakanin su, amsar ta kawai yake bukatar ji ko yakai hannun sa jikin ta." Murya na rawa Rahinah ta ce. """I... I know him from Germany..."" (Na san shi a Jamus). Sai kuma ta kifa kan ta a kafadun Aunty wadda da ke kusa da ita. Ta soma wani irin girza kuka da ta tuno ranar da ya raba ta da diyaucin ta by force, abinda a turance ake kira (marital rape) da kuma ranar da ya dauke mata Abdallah ya janyo mata (maternal deprivation) tsakanin ta da dan ta. These are the worst parts of him da ba za ta yafe ba!Ta kuma kasa mantawa har gobe, har abada kuma bazata manta ba, baza ta yafe ba. Uncle ya ce," """Sai kuma aka yi yaya a Germany din?""" "Cikin kuka Rahinah ta ce, ""sunan sa HABIBU NAHUCHE... my ex-husband. Ya aure ni ne ba da cikakkiyar amincewa da yarda ta ba. Ba kuma hannun iyaye na ba. Ya aure ni a wulakance a hannun wata uwar daki na a Jamus mai suna Aunty Laura. Auren ya kare a kwanaki kalilan. Har muka samu rabon wannan yaron, sai ya sace min shi ya taho da shi daga yaye shi 鈥฀. 鈥฀." "(Tuno ranar da ya dauke mata Abdallah, ya kara rura kukan ta). Da yadda ta bi titi a Frankfurt kamar mahaukaciya zautacciya. Sai da ta yi mai isar ta tana yi tana fyace hanci, tayi jajir don kuka musamman hancin ta komawa yayi kamar jini ya kwanta. Daga Aunty har Daddy babu wanda ya sha numfashin ta, sai dai kuma kukan da ta ke yi yana ratsa su yana sanyayar da jikin Aunty, sai da ta yi kukan da ya samarwa zuciyar ta rangwame da salama." A yau Dr. Rahinah ta yarda da gaske kuka Rahma ne ga zuciyar dan adam wani lokacin. Kuka ne na tasowar tsohon miki da aka samu ya jima da yin healing. Sai da ta samu rangwame daga nauyin da zuciyar ta ta yi sannan ta cigaba da gaya musu cikin murya mai ban tausayi. "鈥淗 abibu ya yi min laifuffuka masu yawa Uncle, wadanda bazan iya fada ba, don ban san tsakanin ku da shi ba, zai cigaba da zama sirri ne tsakani na da shi har abada, kuma bazan iya yafe masa su ba har abada, in na ce zan gaya muku tun haduwa ta da shi da irin laifuffukan da ya yi mun, girman sa zai zube a idon ku, kuma zuciya ta bata da jarumtaka da juriyar tuna abinda ya yi mun, bazata dauka ba. Na riga na baiwa abin baya." "Shi ya sa na ki yarda in koma wa auren sa (no matter how much he repented). Duk da Daddy Ambasada, Nene har ma da Yafendo sun so hakan sosai (komen auren mu)." "Yanzu kuma ina so in karbe yaro na ko ta halin kaka. Ka taimaka min Uncle. , don Allah ka taimake ni in karbi" "yaron nan!"". Ta ci gaba da kuka mai ratsa zuciyar duk mai sauraron ta." "Wani irin hararar ta Uncle Usman ya hau yi, ya ce, ""Yaron da ba ki taba waiwaya ba tsayin shekaru goma ko? Yau ne kika san yana raye? Saboda kin gan shi kin tuna shi? Me ya ci ya rayu shi da dan sa baki sani ba? Yaya ya yi da kashin sa da fitsarin sa duk baki sani ba! Sai yau don kin gan shi healthy and vibrant karkashin kyakkyawar kulawar jajirtaccen Uban sa mai son sa da gaskiya?" Wace irin Uwa ce ke da zaki kasa waiwayar dan ki shekaru goma alhalin kin san yana raye a duniya? In baki waiwayi uban ba da hujjar ya yi miki laifi shi Abdallah laifin me ya yi miki? "Har kina da bakin cewa zaki dauki dan ki yanzu? Sabida kin gama da boko ko kin zama abinda kike son zama? Cewa nake uwa tagari tana iya sadaukar da komai, don ta rayu da dan ta?" "Yanzu ne kika san yana raye? Na dauka kin san da su a duniyar Subhana amma tun bayan dawowar ki baki kara yi mana zancen su ba mu iyayen ki, ko da da subutar baki ne, ko ki je a je a gano shi in ke baza ki je ba, sabida neman duniya ne a gaban ki babu neman aljannah? Ke Rahinatu, ki fita ido na in rufe, zan fyato ki in kika nemi bata min rai." Ke wacece da ba za 鈥檃 yi miki laifi ki yi afuwa ba? Kowanne irin laifi ne ba ya wucewa ke a wurin ki? Ina amfanin kullatar dan uwan ka musulmi irin wannan kullacin na shekara goma wanda aure ne ya taba hada ku ba shashanci ba har da albarkar yaro? In ji dai Habibu ko me ya yi miki ba shirka yayi ba? Ko Allah (S.W.T) ba hakuri Ya ke da mu dukkan mu bani Adam ba? "Da Allah ba ya hakuri da mu, tare da yi mana afuwa bisa tarin laifuffukan mu, da tuni ya kifar da mu kamar yadda ya kifar da al 鈥檜 mmar Annabawan da suka gabace mu sabida yawan laifuffukan mu da sabawar da muke maSa tare da rashin godiyar mu gare shi." "Kullum cikin saba masa muke da karkacewa umarnin Sa, amma afuwa Yake mana kullum da zarar mun roka." "Ke wace ce da ba za ki yi afuwa ga wanda ya saba miki ba, ya kuma dawo ya nemi gafarar ki? Ko kema Allah ya dube ki sanadin hakan ya yafe miki zunuban ki?""" "Rahinah kuka ta ke tana girgiza kai, ta ce," """Uncle Uncle ba za ka gane ba...... shi nasa daban ne, he 鈥檚 selfish by nature, kuma azzulumi ne na kin karawa"". ""Kwarai da gaske. Ba abin da zan gane cikin wannan dambarwar taku mai sunan Daada, face ke da shi duka masu zurfin ciki da taurin kai ne na rashin dalili, rashin afuwa da wahalar da kai siddan da kuma kafiya. In ba haka ba ki fada mana mu ji menene laifin? Mu gani in girman sa ya yi yadda kike kambama shi. Sannan kuma ku yarda ko kada ku yarda har gobe son juna ne yake wahalar da ku ya kuma hana ku yin aure a inda kuke, tunda bazaku ce kun rasa masoya ba." "Amma a wannan karon muddin mu muka haife ku, ba ku kuka haife mu ba, to kuwa za mu saka muku waigi cikin wannan rashin hankalin da kuke yi. Ke ba aure shi ba aure kun gwammace ku mutu gwauraye sabida son juna. To mu zuba mu da ku. Kafar wando guda zamu saka ni da ku bakidaya""." "Da fadin hakan ya juya ya fita cikin fushi. Aunty ma bin bayan sa ta yi zuwa falon sa, ta zauna daga gefen sa tana diallingnumber din Habibu, jikin ta duk yayi sanyi. Iya kintacen ta da hasashen ta da tsinkayen ta, ta kasa gano hakikanin laifin da Habibullahin Hajiya ya yi wa Rahinah haka." ***** A "lokacin suna cikin wani daki na musamman (VIP room) na NAHUCHE HOTEL na garin Kaduna shi da Abdallah, daga shi sai farar singlet da dogon wandon da bai kai ga canzawa ba, ya sirkawa yaron ruwan dumi a kwamin wanka (bathtub), ya ce ya yi wanka don ya ji dadin yin barci, don gobe asubanci za su yi zuwa jihar Lagos." "Kiran Aunty Badiya ya shigo cikin Thuraya din sa, da farko kamar ba zai amsa ba, don ya san tatsuniyar gizo bata wuce koki, haka ya kyale wayar ajiye daga gefen sinkdin toilet tana ta burari yana kallon ta ta gefen ido yana cigaba da sirka ruwan wankan Abdallah cikin rashin damuwa, wani abu da bai taba yi wa Badiya ba, ko dakin meeting ya ke baya kin daga kiran ta don ya san in har ta kira shi to sako ne mai muhimmanci take son ta isar, sai Abdallah ya juya ya dube shi yace." "鈥淒 addy, Mummy ce fa ke kira 鈥฀ kasancewar ringtone din da ya sanyawa Badiya daban yake, kuma Abdallah ya san shi, ala dole ya yanke shawarar amsawa, ko don kyawawan idanun Abdallah (Almond shaped eyes) masu kama da na uwar sa dake karakaina a kan sa kamar yana son karantar canje-canjen da yake ta gani na (facial expression) a tare da Baban nasa tun barowar su gidan Aunty Badiya," "鈥渒 a yi wankan Abdallah kafin na amsa wayar, ina zuwa, zan zo na cuda maka baya 鈥฀. 鈥淏 ar ni ma kawai Daddy ba sai ka zo ba, na iya da kai na ai yanzu 鈥฀. In ji Abdallah." "Ya fito gefen gadon dakin ya zauna, ya amsa kiran Yayar tasa cikin madaukakiyar nutsuwa. Muryar sa kuwa Anty bazata iya fassara yanayin ta ba." """Kuna ina ne Habibullahi?鈥฀" """At the hotel 鈥฀"". Ya ba ta amsa a matukar gajarce, kuma a takaice. Kamar mai fama da ciwon makogaro. Irin baya bukatar wasu tambayoyin daga wannan." """Wane hotel din? Daga nan sai ina kuma?"" Aunty ta sake tambaya, wannan karon murya cike da lallashi (mai nuna concern) fiye da ta baya." """ba sai kin ji kowanne hotel bane don da Assubah muka barin shi. Zuwa duk inda Allah yak-kai mu"". Habibu Mustapha Nahuche, ya amsa wa Yayar sa Badiya da Bazamfariyar accent din sa. Za ka iya jin helplessnessda hopelessdin da ke kwance cikin muryar sa." "Ajiyar zuciya Aunty ta yi, ta ce a raunane," """Will you do me the favour of coming back now (za ka yi min alfarmar dawowa gida na yanzu)?"" Da sauri ya girgiza kai, kamar tana ganin sa." """Ni da gidan ki har abada Maman Musaddiq!"". Daga haka ya kashe wayar sa." "Aunty da Uncle suka dubi juna, dama wayar a bude ta saka ta, Uncle na jin komai. Uncle Usman ya yi murmushi haka itama Badiya, ya ce, ""Tabdi! Yau nake ganin abin da ya fi karfin ji da gani na. Su kuma irin tasu nau 鈥檌 n salon soyayyar kenan? Ana so ana kai wa kasuwa karfi da yaji? Amma babu komai, mu basu lokaci mu gani, na tabbatar miki zasu nemi juna da kan su, ko da tsiya ko da arziki, tabbas daya zai nemi daya 鈥฀." "Uncle Usman kamar mai gani har hanji. Cikin daren Rahinah kasa barci ta yi, ta kasa sukuni akan gadon ta, daga karshe ma sauka ta yi daga gadon kamar mai aljannu sabon kamu sai safah da marwah take a dakin ta, tana tunanin ta ina zata fara? Ko ta halin kaka zata kwaci Abdallah a cikin watan nan ba sai an ja dogon lokaci ba. Ta yarda ta amince daga lokacin da ta sake dora ido akan Abdallah (her maternal love for him increased) wato KAUNAR UWA ta motsa fiye da kintatawa bazata kuma iya rayuwa babu shi ba." "Abu na farko, tana son lambar wayar Habibu Nahuche, a yau ba sai gobe ba, don aiwatar da kudirin ta na farko, wanda zuciyar hankali da kyakkyawan tunani ke halartowa. Idan ya ki, sannan sai ta aiwatar da kudiri na biyu, wanda shi ya kamata kawai ta dauka don huce takaicin abinda ya yi mata yau, da nuna masa da da yanzu fa ba daya bane. Wata fuskar.. yanzu ta fi gaban mari." "Amma zuciyar hankali da nutsuwa da Allah ya halicce ta da ita, har ma da bangaren adalci na zuciyar ta, sun ki amincewa da hakan; sun ce ta bashi dama ko sau daya ne ta ji amsar da zai bata 鈥฀. Once and for all." "Duk da zuciyar girman kan ta da jiji da kai irin na diya mace mai aji daidai da nata, har ma da ego din ta na tankwabe shi. Abin nufi anan; zuciyar hankali na fadin ta fara sauke kai, ta ajiye kullacin ta da shi a gefe, ta roke shi (alfarma), ta hanyar bin sa ta lalama da neman alfarmar karbar yaron ta cikin mutunci (in such a way that) babu cin mutunci ko tozarta juna da zai biyo bayako don albarkacin Aunty Badiya data tabbatar jinin sa ce yanzu, bayan wannan babu wani abu daban a tsakanin su da zai kuma wakana balle ya samu damar yi mata kallon banza." "Daga nan sai kowa ya kara gaba (in ta karbi Abdallah), ya cigaba da gudanar da rayuwar sa yadda yake yin ta. In dai yaron ta yana hannun ta falillahil hamdu, bata da sauran matsala kuma a rayuwa." Amma a ina zata samu lambar Habib Nahuche ba tare da Anty Badiya ta sani ba? "Kawai sai Musaddiq ya fado mata a rai. Dama dan gidan ta ne. Da sauri ta dauki wayar ta ta kira shi, karfe goma sha biyun dare ta gota lokacin, shi har ya fara barci tace ya kawo mata aron wayar sa, zuwa safe zata bashi." """Aunty Rahinah kin san bama shigowa cikin gida after 12 am?鈥฀" "Musaddiq ya fada cikin mamaki. Numfashin Rahinah na sassarfa, kamar yana shirin daukewa daga kirjin ta sabida azalzalar da zuciyar ta ke yi da cewa ""a yi ta ta kare ita da Habibu Nahuche, a yau ba sai gobe ba, kowa ya san matsayin sa, tunda hakkin haihuwa kowa da nasa, ba nasa ne shikadai ba, ta ce" """Musaddiq ka ajiye min a bakin kofar shigowa falo ka tafi, zan fita in dauka da kai na 鈥฀ da sauri Musaddiq ya amsa." """Rightaway Aunty Rahinah!鈥฀" "Duk da cikin zuciyar sa yana mamakin me Antin sa Rahinah zata yi da wayar sa, ba dai zata ce credit din kira ne bata da shi ba shine zata yi amfani da wayar tasa, a hakan dai ya bi umarnin ta domin ta wuce tayi masa umarni ya tsaya questioning din ta." "Cikin nutsuwar da take tattarowa da kuma baiwa kanta karfin guiwa ta saka suna 'HABEEB 鈥฀ a cikin wayar Musaddiq, ta kira." "Nan take kuwa sunan ""UNCLE HABEEB! Ya bayyana kan sa. Sai ta yi maza ta kashe, ta kuma kwafe lafiyayyun lambobin na gidan wayar mtn a tata lafiyayyar wayar. Kai da ganin su ka san lambobi ne na musamman (special numbers) da ba kowa mtn ke baiwa ba." NA HUCE is not for free It's 1000 via 3094856450 Sumayyah Kabara Firstbank Shaidar biya 07030137870 SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI 07030137870 *HABIBU NAHUCHE* "Ya bai wa kan sa hutu ne domin ya gama fahimtar a hargitse yake, ci gaba da ayyukan sa a wannan halin da ya ke ciki ba abin da zai haifar sai tarin nakasu da koma baya cikin harkokin kasuwancin sa. Domin hatta lissafi kowa da ke tare da shi ya san ya daina yin sa daidai." "Ya dauka komai nata ya tafi, tafiyar da babu dawowa, ya dauka ya riga ya binne ta a zuciyar sa ba don ta mutu ba, sai don ta gama taka rawar ta a rayuwar sa, ya dauka komai nata ya zama bygone? Tunda bai hana shi progressing ba. Amma ashe likimo ta yi wa zuciyar sa mai kama da kwanton Bauna!" "Daga lokacin da idanun sa suka shiga cikin those innocent fulani eyes din na Rahinah Omar, komai ya dawo masa sabo fil. Wai kunama ta harbi gyambo." "In ma ya ce har da kari ba zai yi karya ba. Yanzu ya gan ta ne a matsayin cikakkiyar mace (matured young lady in her late twenties fiye da yadda ta ke a baya. Yanzu ne ta ke amsa sunan mace sosai, ta ke amsa sunan (Dr. Rahinah Omar Girei Otorhinolaryngologist) ba 'yar yarinya budurwa mai tsananin kyau da ya sani a Jamus, mai amsa sunan Rahinah Omar ba." "Wannan kyan na yanzu hade yake da sanin ciwon kai, matured mind, contentment of life." A halin yanzu ka ganta tsammani za ka yi balarabiyar kasar Oman ce sabida yadda fatar jikinta ke glittering. "Dr. Irshad bai iya boye hakan a ran sa, a duk lokacin da ya ga Rahinah ko wani aiki ya kawo ta ofishin sa sai ya fada kasa-kasa cewa, 鈥楲 ooking Ravishing'." "A duk sanda ya fadi hakan ita kuma za ta yi kicin-kicin da fuska, don duk namijin da ya yabe ta haushi yake ba ta." "Habibu Nahuche has never praised her beauty, watakila bai ma san ya ake gaya wa mace abin da zai dadada mata rai ba. Yet shi kadai yake burge ta, shi kadai ta ke so ta ji ya yabi wani abu nata. Unfortunately bai taba ba, sunan ta 鈥渕 uguwa-azzaluma 鈥฀ a bakin sa." "Watakila wadannan muggan kalaman nasa da suka haukata ta a kwanakin nan, su za su cigaba da birkitata suna farautar farin cikin ta da nutsuwar ta har zuwa ranar da ta daina numfashi." ******* "Duk da bai san wace irin alaka ce tsakanin ta da su Uncle Usman ba, ya fahimci alaka ce ta kusa ba ta nesa ba. Maimakon ya samu hutu kamar yadda yake bukata cikin 鈥橬 ahuche Hotel 鈥฀ na garin Ikko, tun bayan da ya sada Abdallah da 鈥楤 oarding School 鈥฀ don ma kada Rahinah ta samu access din sake ganin sa, sai kadaicin ya bankado wa zuciyar sa tsohon kundi da tsohon miki na rayuwar KWANAKI BAKWAI a birnin Cologne din JAMUS." "Rayuwar da har yau bai kara maimaitawa ba, bai kara samun kwatankwacin ta a gardi ba, bai kara attemptingdin ta da kowacce 鈥檡 a mace ba tsayin shekaru goma, wato rayuwar auratayyah! For she left no space in him. Ta mamaye ko 鈥檌 na na zuciyar sa." "Ya rike kan sa ta duk hanyar da addini yayi umarni, ta hanyar maida kan sa busy kullum, da neman kudi da azumin tadawwu 鈥檌 don kada ya tuna ta. Don kada ya nemi mata. Ya sani ba irin mummunan zargin da duniya bata yi masa akan rashin aure." "Idan ya ce yana sufferinginternally a cikin wannan dan tsakanin, ya yi kadan ya bayyana irin halin da ya samu kan sa. Ganin ta ya tuna masa cewa shima NAMIJI ne mai lafiyar bukatar aure, don a baya ya dauka ya dade da komawa mace. Sabida kowacce macen kallon mata-maza yake mata sai ko yau da ya ga RahinahOmar ganin idanun sa, ya kuma ji muryar ta jin kunnen sa 鈥฀" ****** *ASHE RAHINAH BAKI SAN GATSE BA?* "Mr. Atiku wato PA din sa na Abuja ne ya kira shi, da bai same shi ba, sai ya kira PA din Lagos. Rasak. Cikin tashin hankali yake gaya masa ya hada shi da Oga, itisurgent. Shi kuma yace masa Oga fa ba ya amsa waya currently, yana hutu a Hotel, ajiyar zuciya PA din Abuja ya yi, yace." """Sai ka gaya masa hutu bai gan shi ba, an turo masa da SAMMACI daga Federal High Court, Abuja, kuma zance har ya bullawa media." He has to be in Abuja today or tomorrow a kashe zancen nan kafin 'Daily Trust 鈥฀ su shigar da jaridar da zasu fitar "jibi zuwa yanar gizon su, ko su fara sayar da ita a kan takarda." "Ban san wa ya kai musu zancen ba kuma ban san wa ya yi karar sa ba. Amma hakika a kan yaron sa ne, Abdallah. Har suna questioninglegitimacy din sa dalilin hakan. Ana neman sa nan da kwana uku a kotu!鈥฀." "Jeremy da ke kula da abincin sa shi ya shigo masa da jaridar yau da ya sayo tare da lunch din sa. PA dinsa ne ya ce ya kai masa jaridar tare da abincin rana, tunda sun yi-sun yi da shi akan ya daga waya don su gaya masa yayi wani abu kafin 鈥橠 aily Trust 鈥฀ su saki labarin, amma ko damar ganin sa bai basu ba balle ya san abinda ke faruwa." Headline na jaridar Sabuwar Najeriya (NEW NIGERIA) dauke ya ke da kanun labaru kamar haka 鈥฀.. """NAHUCHE 鈥橲 EX-WIFE DRAGS HIM TO COURT, ACCUSES HIM OF INJUSTICE ON THEIR CHILD 鈥" 橲 CUSTODY 鈥฀.DR. RAHINAH OMAR OF NIZAMIYE APPEALS THE COURT FOR JUSTICE... Yayin da Headline na 'Daily Trust 鈥฀ ya ce. """IS ABDALLAH NAHUCHE A LEGITIMATE CHILD???鈥฀" "A cikin kanun labaran kuma an yi bayanin zuwan sa Germany karatu, tare da dawowa da yayi tare da karamin yaron, ba tareda kowa nasa ya shaida auren sa ba." "鈥淣 o one knows how, and where Habibu Nahuche got his beautiful son Abdallah in GERMANY 鈥฀..not even his" Mother 鈥฀.鈥฀. "Ba da niyyar cin abinci ya fito falon ba, ya fito ne domin ya dauki wayar sa da ya bari akan diningtable din. Babban abinda ya fizgi hankalin sa kan jaridar da ke ajiye shine hoton Abdallah a fuskar jarida, sai na shi dana Rahinah, a kagauce ya bi headlines din. Wadanda suka sa wani irin gumi tsatstsafo masa." 鈥淚 ta kenan bata san gatse ba?! Ashe Rahinah bata da hankali da hangen nesa har yanzu tana nan yadda take da "kafiya da taurin kan ta? Nauyin shekaru ba su kara mata komai ba daga sanin da ya yi mata a baya, basu canza ta ba haka basu ishe ta yin hankali ba?" Har yanzu tana nan a sha yanzu magani yanzun ta! (not giving things a second thought)鈥฀. "Ya tambayi kan sa cikin tasowar wani matsanancin bacin rai, da bai taba ji a rayuwar sa ba, ba don yana shayin kotu zata kwace masa Abdallah ta bata ba, sai tunanin wannan tereren da ta ja musu, da Dan sa da ya ji ana kokarin sheganta masa!鈥฀" "A take ya yi waya yayi booking jirgi mai zuwa Abuja, da zummar zai je yau ya fuskanci Dr. Rahinah Omar da duk abinda take taqama da shi a duniya, sai ta gwammace bata yi karar nan ba 鈥฀ ai ta gwammace bata san shi ba, sai ta gwammace wata alaqa bata taba hada su ba. Yau za ta san ko waye ""REAL Habibu Nahuche 鈥฀ domin zai fiddo mata truecolour din sa." "Abdallah kuma sai dai ta daukaka kara zuwa SupremeCourt, (Federal High Court) ta yi tsararo ta kwatar mata shi, kai duk duniya bai ga kotun data isa kwatar Abdallah ba a kasar nan da wajen ta daga hannun sa 鈥︹€฀" "(Babban bacin ran Habibu Nahuche ba karar sa da Rahinah tayi gaban Alkali bane, kamar shegan ta masa Abdallah da ta janyo ake kokarin yi a kafafen yada labarai babu gaira babu dalili, sai don neman magana da neman suna irin na鈥檡 an jarida)." ****** *ABUJA* "Kafin ka ce meye wannan labarin ya bazu kamar wutar daji a media, musamman cikin birnin tarayyah, kowace jarida tun daga ta cikin gida wato LEADERSHIP har Daily Tribune da Sahara Reporters ta maida shi headline din ta na wannnan satin. FACEBOOK, TWITTER, WHATSAPP groups kuwa sun maida shi 鈥檛 opic of discussion 鈥฀ hotunan Habibu da Rahinah da kyakkyawan dan su Abdullahi ya baibaye wayoyin al 鈥檜 mmah. Kowa yana fadin albarkacin bakin sa mai dadi da marar dadi." "Duk wanda ya kwana da sanin Habibu Nahuche (Lucky), Hotelier, ya ji labarin tsohuwar matar sa ta maka shi a kotu kan ya bata dan ta, dan da ba 鈥檃 da tabbacin na halaal ne don a kasar Germany suka haife shi ba da sanin kowa nasu ba." "Washegari Aunty da Uncle suka bi bayan su zuwa wajen Hajiya, Aunty ta tabbatar wa Uncle babu inda Habibu zai je da Abdallah sai Zamfara, don ba zai iya yawon jihohin Najeriya da yake yi da yaron ba, don ba ya so jama'a suna tanka wa a kan tsananin kamannin da ke tsakanin sa da yaron." A cewar sa don kada baki ya kama shi. Yana guje masa kambun baka. Don haka Aunty ba ta raba dayan biyun tabbas Zamfara suka nufa. Ilai kuwa Hajiya Kaltume sai ganin Aunty da maigidanta ta yi sun yi sallama suna shigowa. "Suka zazzauna suna gaggaisawa da Hajiya cikin tsananin girmamawa. Hajiya ta ce, ""Ni laifin me kuka yi wa Baban Abdallah ne?鈥฀" "Dariya Aunty da Daddy suka yi a tare, Aunty ta ce," """Babu laifin fa da muka yi masa. Laifin mu daya kasancewar mu iyayen mahaifiyar Abdallah""." "Hajiya ta dan zamo jikin ta daga cikin kujerar ta, ta tattara hankalin ta kan babbar diyar ta, cikin rashin fahimta ta ce. ""Wace mahaifiyar Abdallahn?""" "Aunty ba ta bata lokaci ba, ta ce, ""Dr. Rahinah, mahaifiyar sa wadda ta haife shi, matar Habibu a Jamus, wadda ta guje shi." "Diya ta ke ta halali ga Baban su Musaddiq shi da mahaifin ta mai rasuwa ciki daya suka fito""." "Hajiyar Nahuche ba ta san sanda ta ce, ""Allahu Akbar!"" ba, ""Allah da iko Yake, to ya aka yi da can ba mu sani ba?""" "Aunty ta ce, ""Muna tare da Rahinah tsayin shekaru masu yawa, tana karatun likita a Jamus, sai dai ta zo ta kwana biyu ta koma. Yanzu ne ta dawo gida gabadaya ta fara aiki a Abuja. Circumstances ne ya sa muka gane cewa ita ce, ba don wani cikin su (ita ko Habibu) ya gaya mana ba." "Hajiya gudun juna suke yi, bayan kuma a fili yake dayan su bai iya sake aure ba da dan uwan sa ba." "Laifin da muka yi masa har ya kwace Abdallah shi ne, mun yi plan din da ya ga Rahinar sa a gidan mu. Ba don haka ba sun zabi har su tsufa ba su kara neman juna, while dukkannin su sun san inda junan su ke rayuwa. Alaqar da ke tsakanin mu ce basu sani ba." "Hajiya, Habibu da Rahinah suna bukatar interference na iyaye da masu iko da su, domin su taimaka wajen gyara rayuwar su, su kuma ci gaba da rainon dan da Allah ya ba su a tsakiyar su""." "Hajiya ta nisa cikin al'ajabi," """Ke nan 'yar family din Sarkin Fulanin Girei Habibu ya aura?""" "Daddy ya ba ta wannan tabbacin, sannan ya kara da cewa, ""Uban ta shi ya sha nono ya saki na kama. Abin da dukkanin mu ba mu sani ba, kuma muke son sani shi ne, laifin da Rahinah ta yi wa Habibu, da laifin da Habibu ya yi wa Rahina suka gwammace su rayu a tagayyare cikin soyayyar juna shekara goma ba tare da juna ba""." "Hajiya ta ce, ""Sha'ani na miji da mata ai babu yiwuwar sai an san abin da ya hada su. Hanyar gyara kawai za a nema a sulhunta su. Oh ni Kaltume Ya Allah ka nuna min wannan ranar... da Habibullahi zai sake aure a rayuwar sa ta duniya, duniya kuma ta shaida""." "Sai kawai ta soma matsar kwallah. Kwallan da ba ta komi ba ce face ta farin ciki, a dalilin sunsuno cewa lokacin auren Habibu ya zo. In dai da gaske 'yar su Aunty ita ce mahaifiyar Abdallah, ita shaida ce kan cewa babu wadda Habibu yake jira sai ita, ko da za ya soma furfura ba aure." "Uncle Usman ya ce, ""Ai sulhu ba zai yiwu ba tare da an san rootcause na matsalar ma'aurata ba. Ta hanyar sanin mene ne hakikanin matsalar su ne za a san hanyar magance ta da hana ta sake faruwa a gaba." "Don haka Hajiya komai yana hannun ki yanzu. Ke kadai za ki iya tankwara Habibu ya nemi sulhu da matar sa. Hajiya ta girgiza kai ta ce, ""Wani irin lallashi ne ban yi masa ba a kan aure? Wane irin nasiha ne ban yi masa ba? Wace irin addu 鈥檃 ce ban yi masa ba? Don haka tunda dai wannan din ita ce uwar Abdallah kuma mu duka shaida ne a kan cewa ita kadai yake so, sannan kai ne madaurin auren ta, to mu taru mu gyara sunnah, in ba su shirya don Allah ba sa shirya albarkacin dan su. Ku tashi yanzun nan komin dare mu wuce Nahuche in gaya wa madaura auren sa""." Ba karamin jin dadin shawarar Hajiya Daddy Usman da maidakin sa suka yi ba. A take ya kira Ambasada Shehu ya gaya masa duk abin da yake faruwa da hukuncin da Hajiya Kaltume ta yanke. "Ambasada sabida sanin da ya yi wa Habibu da Rahinah sai ya ga cewa shawarar su ba mai billewa ba ce idan har ba Rahinah da kan ta ta amince za ta koma wa Habibu ba, to fa baza 鈥檃 haifi da mai ido ba, don haka ya ce su ci gaba da abin da suka tsara, shi kuma zai zauna da Dr. Rahinah formally ya tattashe ta a kan komen ta gidan Habibu don ita ce mai babbar matsala ba Habibu ba. Duk suka yi na 鈥檃 m da shawarar Ambasada." ******* "A Nahuche, baffanin Habibu sun ji dadin batun da Uncle da Hajiya Kaltume suka zo da shi. To kowa a kan gwiwa yake da damuwar rashin auren Habibun. Dadin dadawa an ce uwar dan sa Abdallah. Don haka kowa ya yi na 鈥檃 m da a maida auren." "Amma zasu jira Ambasada tukunna kamar yadda yace sai ya zauna da Rahinah officially akan maganar komen nata, matsayin ta na bazawara wadda addini ya baiwa damar zaben mijin aure." "Suna kan hanyar dawowa Zamfara daga garin Nahuche wayar Ambasada ta shigowa Uncle Usman, da sauri ya amsa cikin fara 鈥檃 yana gaya masa nasarar tafiyar su Nahuche da matsayar da aka cimma idan Ambasada ya gama Magana da ita Rahinah. Ambasada Shehu sai ya sauke wata gwauruwar ajiyar zuciya sannan yace da Usman," "鈥渒 unna data ka duba WhatsApp, na turo maka wani abu yanzun nan da 鈥楧 aily Trust 鈥฀ suka fitar cikin makon nan 鈥฀." Da sauri Uncle ya hau duba dayar wayar sa. "Salatin da ya yi ba Aunty kadai ya firgita ba har Hajiya Kaltume. Sai ya kasa Magana kuma, sabida kunyar Hajiya Kaltume, a lokaci guda yana kissima irin yadda zai saka kafar wando guda da Rahinah, ana ganin ta mai ilmi ashe bata da hankali ko kankani? Kuruciya bata bar ta ba a shekaru 29?" "Kasa fada musu ya yi, yayi shiru, duk da tambayar sa ko lafiya da suke ta yi yake jera salati? Sai ya ga gara su ji a bakin sa akan su ji a media. Ya gaya musu Rahinah ce ta yi karar Habibu a kotu, gobe zasu shiga Federal High Court ita da shi su fara Shari 鈥檃 h akan dan su, amma su kwantar da hankalin su (he will never let this happen) insha Allah in dai yana raye kuma shine uban ta, zai yi maganin Rahinah." "Jikin su duka sai yayi sanyi, a lokaci guda kowacce ta soma tunanin ko dai a hakura ne? Allah kadai ya san abinda ya boye a karkashin wannan takun-sakar na Habibu da Rahinahr sa, sai kuma su da suka aiwatar da rayuwar su ta dan lokaci tare a Jamus." "Har suka iso gida jikkunan su a sanyaye suke. Aunty Badiya bata kai Uncle Usman jin ciwon abinda Rahinah ta yi ba, domin ya nuna bacin ran sa a fili, fada ya ke ta yi kamar Rahinar na ganin sa har suka isa Zamfara." "Hajiya kam ta fi kowa jin babu dadi, Habibullahi a Kotu! Wani abu ne da bai taba faruwa da shi ba, kuma wai da uwar Dan ka wannan terere da bankada da me ya yi kama. In Rahinah na son karbar dan ta ta bi ta maslaha mana ko ta zo ta same ta ta gaya mata sai kawai ta sa su a bakin duniya?" "Dama can Hajiya Kaltume tana jin haushin Rahinah, a bisa ganin cewa, sabida ita Habibu ya ki aure, balle yanzu da ta yi wannan danyen aikin, ana cikin kokarin gyara aure." "Sai Hajiya ta ji Rahinah ta kara sire mata, amma zata ci albarkar Usman don miji ne har miji ga 鈥榶 ar ta," "wanda ba 鈥檃 taba jin kan su da Badiya ba shekaru ashirin da doriya, sannan zata ci albarkacin dan ta. A yadda ta san Habibullahi, da son da ya ke wa Abdallah, to ba kotu ba, ko ina Rahinah zata je zata gaji ta bari babu mai iya raba shi da Abdallah." "Uncle Usman yayi kwafa 鈥渂 anda hauka irin na Rahinah? Wa ya gaya mata ana jayayya a kan Da? Da, na kowa ne kuma ajiyar Ubangiji ne ga iyayen sa, zamu gamu da ita, sai ta gwammace bata taba sanin Usman Girei ba 鈥฀. Ko da suka isa Zamfara, anan ya bar Aunty Badiya. A daren ya dawo Kaduna, washegari ya nufi 鈥榓 irport 鈥฀ ya bi jirgin 鈥楳 ax Air 鈥฀ zuwa Abuja don hanyar Abuja ta kazanta a wannan dan tsukin, ba 鈥檃 fiya bi da mota ba, balle shi da yake a kagauce da yin tozali da Rahinah, ko a waya bai kira ta ba, burin sa ya bude ido ya gan ta gaban sa, yana kuli-kulin kubra da ita. A sanin da ya yi wa Habibu ko kadan bai son tashin hankali balle abinda zai taba mutuncin sa." ****** *RAHINAH* "Abinci ta ke ci a dakin Yafendo, abinci mai rai da motsi da Nene Balki ta dafa mata na musamman, tana ci suna hira ita da Yafendo hankalin ta kwance ya tsumma a randa. Tana fadi cikin ran ta jibi I yanzu suna gaban alkali ita da dan Nahuche. Har Lawyer ta dauka mai zaman kan ta daga Chambar Lauyoyi masu zaman kan su na garin Abuja." "Sai ganin Daddy Ambassada ta yi tsaye a kan ta rike da jarida, tsabar bacin rai ko sallama bai yi musu" ba. Ya ce "鈥淩 ahinatu, me na ke gani haka?鈥฀" Ashe baki da hankali baki da tunanin dana ke ganin kina da shi?鈥฀ "Ya jefa mata jaridar 鈥楧 aily Trust 鈥฀ akan cinyar ta sannan ya ce 鈥渕 aza-maza ki je ki janye karar nan, kafin in kifta ido na, wa ya ce miki ana jayayya a kan yaro? Kina so Ubangiji ya yi hukuncin sa a kan sa? Kina son ku rasa shi gabadaya ko? In kina son rayuwa da yaron da gaske, me zai hana ki koma gidan uban sa?鈥฀" "Rahinah ta sunkuyar da kai, bata ce komai ba, ganin yadda Ambasada ke tafarfasa, ko wa ya kai wa 鈥榶 an jarida labarin kuma? Bata yi don ta bata ran iyayen ta ba da masu kaunar ta, ko don a yayata su a mediasai don kwatarwa kan ta 鈥榶 ancin ta da Habibu ya bi ya danne ya ke kuma kan dannewa, domin so ya ke har ta mutu ba ita babu dan ta." "Ita ba don a sa a media ta kai Habibu kara ba, ta kai shi ne don shari 鈥檃 h ta kwatar mata dan ta, tunda ta bi shi ta lalama ba wanda ya ji ba wanda ya gani amma ya bi ta da gatse da bakar Magana. Ya raina mata hankali." "鈥淢 aza-maza ina umartar ki da ki tashi ki je ki janye karar nan, yanzu yanzun nan kafin isowar Usman, ya gaya min ya taso a jirgi, zai saba miki yadda ba kya zato. Don ta ni kin sani mai sauki ne, har kullum Uba nake mai fahimtar ki da bin ra 鈥檃 yin ki, mai yawan yi miki uzuri, hadi da baki damar da Allah ya ce a baki. Amma a wanan karon bana bayan ki Rahinah." "Akwai muhimmiyar Magana da dama nake so mu yi a yau, kawai na ci karo da wannan shirmen naki ana sayarwa a hanyar motoci, tashi maza-maza ki je ki janye ki dawo kafin isowar Usman don ya gaya min kan azahar zai sauka a garin nan." "Rahinah ta dan tsuke baki da fuska cikin alamun gardama, karo na farko da zata yi wa Ambasada musu, Yafendo da bata gane akan me ya ke ta fadan ba ta ce." 鈥淢 e ke faruwa ne Jakada?鈥฀ "Nan Daddy yayi mata bayani a takaice 鈥淩 ahinah ta kai Habibu kara kotu, a kan ya bata dan ta!鈥฀." "Sai ga Nene Balki ma ta shigo, ta tsinkayi karshen maganar da yake fadawa Yafendo, salati suka hau yi a tare, Nene na fadin 鈥淩 ahinah kan ki daya?鈥฀ Yafendo ta ce 鈥渒 o kin fara shaye-shaye ne bamu sani ba? Don an ce min yanzu a kasar nan mata sun koyi shaye-shaye, kuma kika kunshe baki kika yi shiru kina sabgogin gaban ki hankalin ki kwance kamar kin kashe rai, sai zabga lomar abinci kike, Allah ya raba mu da kotu, ko makiyin mu kada Allah ya kai kotu balle Baban Abdullahi, 鈥榶 ar nema, ja 鈥檌 ra.鈥฀" "Nene kuma ta ce 鈥淩 ahinah ki komawa uban sa mana! In kin san kina son yaron ki da gaske? Ki rayu da su har abada cikin salaama da aminci, wannan taurin kan da girman kan ba naki bane a matsayin ki na 鈥榶 a mace, na rasa ina kika koyo su, ita 鈥榶 a mace da rauni aka san ta da yafiya ga mijin auren ta, ki tashi maza ki bi umarnin Abba Jakada, kin ga shi bai iya fada ba, kada ki sa yau a kan ki ya koya 鈥฀." Cikin bacin rai Ambasada ya ce 鈥渁 i ni bata dauke ni Uba ba shi yasa ina ta Magana tana ji na ta yi kunnen "uwar shegu da ni, ku bari uban ta na halali ya zo, shi in ya sa ta za ta yi, ya ce min har da dorina sai ya buge ta wallahi 鈥฀." "Kalaman Ambasada Shehu na 鈥渂 ata dauke ni Uba ba, ku bari uban ta na halali ya zo 鈥฀ sun taba zuciyar Rahinah sun kuma karya ta. Ta mike tana hawaye ta isa gaban Ambasada ta durkusa, cikin rawar murya take magana.鈥淏 a ni da uban da ya fi ka Daddy, ka yi min abinda kowanne uban halali yake yi wa 鈥檡 ar sa. Ka yi hakuri" zan je in janye yanzun nan. Saboda kai!鈥฀. "Ambasada ya juya ya fita sakamakon kiran sa da ake ta yi a waya duk akan maganar, wadda ke kara yaduwa kamar wutar daji a garin Abuja. Ita kuma ta dauki Jilbaab din ta da mukullin mota jikin ta na rawa ta fita." "Lawyer data dauka wato Barr. Hanifa Suraj Kumo (AMANATA) ta fara kira tana hawaye tana tuki, ta gaya mata Baban ta ya ce ta janye karar, so ta janye, amma kudin da ta riga ta bata ta bar su. Barr. Hanifa ta ce baza 鈥檃 yi haka ba, zata maido mata da ko rabi ne. Sannan ta karasa kotun, cikin dan lokaci ta janye karar." "Al 鈥檃 marin da bai yi wa 鈥榶 an jarida dadi ba, don sun so samun kudi sosai da issue din Nahuche da ex- wife din sa. Kasancewar Habibu Nahuche wani matashin miloniya mai farin jini a kasar Najeriya. Tana hanyar dawowa gida, Uncle Usman ya iso, Ambasada ya tura direban sa ya dauko shi daga filin jirgi, suna falon saukar bakin sa suna kara tattaunawa akan al 鈥檃 marin." 鈥淣 a tura ta yanzu kan ta je ta janye 鈥฀ inji Abba Jakada. "Sai ga wayar Habibu ta shigowa Uncle Usman, inda ya gaya masa 鈥済 a shi ya sauka daga Lagos shima yanzu, an aika masa SAMMACI, wai wata mahaukaciyar Likita ta kai karar sa, zai halarci zaman kotu jibi tare da ita 鈥฀. Uncle ya kasa gane halin da muryar Habibu ke ciki a wannan lokacin. Sai ya ji sunan da ya kira Rahinah da shi ya ba shi dariya, ya kuma dace da ita ya ce masa," "鈥渋 na gidan Ambasada yanzu haka, nima ban dade da shigowa garin ba, ka bar duk abinda ka ke, ka zo ka same ni a can. Maitama ne 鈥฀." "Habibu ya juya yayi wa PA din sa na Abuja Magana wanda shi ya dauko shi, ya bashi umarnin su fara zuwa gidan Ambasada Shehu kafin ya kai shi gidan sa na Abuja da ke a 鈥楲 ife-Camp 鈥฀." "A dai-dai wani shatale-tale (roundabout) na kan titin da zasu bi su dauki hanyar unguwar Maitama, danja ta tsayar da su." "Kusan a tare suka tsaya da motar da ke barin daman su kirar KiaPicanto fara sol, kamar an ce da shi ya kalli matukin motar, sai ya dan janye jaridar 鈥榙 aily trust 鈥฀ da ke hannun sa yana dubawa, wadda ke dauke da kanun labarun kai shi kotu. A gefen nasu mace ce fara sol ke jan motar, sanye da (Egyptian Jilbaab) ruwan kasa-kasa, hannayen ta biyu da ke dafe da sityari sun sha zobban zinare guda uku-uku, bai dauki 鈥榶 an sakanni ba kwakwalwar sa da kyawawan idanun sa suka gane ta; Dr. Rahinah Omar Girei." "Itama jin alamun idanu a kan ta, sai ta waiwaya kadan, motar su kirar bakar 鈥楥 hevrolet-Volt 鈥฀ wadda bata da yawa ko a cikin Abuja ba itace ta dauki hankalin ta ba, kamar HandsomeMan din, mai wani irin sassanyan kyau da aji na musamman, wanda ke kwance cikin lallausar farar shaddah Wagambari a bayan motar." "Ko mutuwa ta yi ta dawo wannan fuskar bazata taba bace mata ba, lumsassun idanun nan masu son shigewa cikin nata a yawancin lokuta, har yanzu suna nan yadda suke farare kal, a lumshe, cikin farin glasses tar-tar da shi kamar ba glass ne a idon sa ba sabida garai-garai din sa; Baban Abdullahi dan mutanen Nahuche, shi ke kallon ta cike da wata irin lumsassar 鈥榯 sana 鈥฀ kwance cikin kyawawan kwayan idanun sa." "Yatsun ta masu dauke da zobban zinare ta kai tana danna maballin dake jikin motar ta, glassai bakake suka maye gurbin masu haske su ka yi sama zuuu! Kamar yadda ta kautar da kai itama, cikin tsananin faduwar gaba marar misaltuwa." "Dai-dai lokacin danja ta basu hannu, ta wani irin zugi motar da gudu ta tsere musu. Ashe an yi ba 鈥檃 yi ba, an gudu ba 鈥檃 tsira ba." "Domin kuwa kusan a tare su duka suka isa gidan Ambasada Shehu Bichi da ke unguwar Maitama, ta riga su shiga, har ta adana motar ta a ma 鈥檃 danar motoci kafin su iso, akan idon ta mai gadi ya bude musu kofa suka sulalo cikin gidan kamar ita kan ta motar tasu tafiyar takama take yi tamkar Ba-Rumen ubangidan nata (dan kabilar Rumawa)." "Kafin PA Mr. Atiku ya gama parking ya fito don ya bude masa, ya bude da kan sa ya fito." "Rahinah bata tsaya ba, kusan da gudu-gudu ta karasa shigewa cikin gida, bata sani ba ko da ace ta tsaya din sun jera, ko alfarmar kallo ba zata samu daga Habibu ba." "Dakin Nene Balki ta fada ta shige toilet ta rufe, don ta san nan ne kadai waje na karshe da za 鈥檃 yi tunanin neman" "ta cikin gidan. Addu 鈥檃 r ta daya kada ya kasance wani ya ga dawowar ta, balle a neme ta." "Sai dai kuma tana shiga toilet din Nene na shigowa dakin, ta kuma ga rufo kofar toilet din data yi, sannan kamshin turaren ta 鈥楴 ina Ricci 鈥฀ shi ke fallasa ta a duk inda ta s higa." "Nane bata kawo komai ba a ran ta, ta dauka ta shiga ne don yin alwallar sallahr azuhur." ****** Is not for free. It's 1000 via 3094856450 Sumayyah Kabara Firstbank SUMAYYAH ABDULKADIR 07030137870 "Ga dai kiran ya shiga, ga wayar tana ta ruri, amma sai ta nemi dukkan karfin gwuiwar da ta tattara take tinkaho da shi na jin cewa zata iya tarar sa gaba da gaba ta rasa, ta nemi kalaman data harhada a fatar bakin ta don yin magana da Nahuche ta rasa, ta nemi boldness din da jajirtacciyar ego din ta suma ta rasa 鈥฀. A lokacin da ta ji calm, cool muryan nan ta Habibu Nahuche cikin kunnuwan ta tana kwarara mata sallama, kamar wanda dama ya ke jiran kiran nata ya amsa impatiently," """Hello, Ma 鈥檃 m, ina kan layin!鈥฀." Duk sai ta kara daburcewa ta rikice gabadaya. Ya ya san cewa ita ce ta kira shi? "A ka 鈥檌 dar sa bai amsa kiran da bai san ko na waye ba, amma already ya san Rahinah zata kira, psyche din sa ya dade da bashi zata kira din, da wacce fuskar zata kira ne bai sani ba; da tsiya ko da arziki." "Don haka tuntuni Habibu yana jiran kiran nata ne, shi ya sa yaki yin barci, yayi mamaki ma da ta kai har sha biyun dare bata kira ba, a yadda ya san ta da wutar ciki a kan Dan ta, ya san yadda ya kasa barci itama yau bazata iya ba, watakila har gara shi, tunda yana makale da dan sa rabin ran sa a gefe abin debe masa kewa (apple of his eyes), ya fi kyautata zaton kiran nata bana arziki zai kasance ba, kuma ya shirya mata da duk irin wacce ta zo masa." "Shi yasa koda ya ga bakuwar lambar da aka nuna daga cikin Kaduna kiran yake ya san cewa; ita ce. Dr. Rahinah Omar Girei. Don haka bai yi nawa ba wajen dagawa a ginshire, ya amsa a kagauce. Yana magana a kasaice." He is expecting her rigimammen call a daidai wannan lokacin orbefore. Jin dadin sa daya Junior ya yi barci. Zai ji dadin caccaba mata Magana yadda yake so. "Bayan ya sha jerin tambayoyi masu dimbin yawa daga wayayyen yaron nasa mai kaifin basira da wayayyen kai, da kalaman da suka bashi mamaki, akan BAKUWAR FUSKAR da ya gani ta gidan Mummy Badiya a yau, wadda ta biyo su har gurin mota." "Abdallah ya ce da Habib bayan ya fito daga wankan da ya sa shi dazu, yana goge sumar kan sa da karamin tawul." "鈥淚 just like her Daddy, and i don 鈥檛 know why I admire her from the first glance 鈥฀.. (Kawai na ji ina son ta, ban san kuma me yasa nake son nata ba, daga sanda na fara ganin ta, ta kwanta min a rai Daddy)." Wacece ita? A ina take? She 鈥檚 beautiful. Ina so in koma gidan Mummy don in kara ganin ta 鈥฀. "A wannan lokacin Habibu rasa amsar da zai baiwa Abdallah yayi, sabida ya san howsmart yaron nasa is, sai ya yi taka-tsan-tsan kwarai wajen gaya masa ko wacece Rahinah gare shi, dole ya bashi gamsashshen bayani, son samu ya gaya masa abinda zai dakusar da tasirin data samu haka nan da nan a ran sa, don kalaman da yaron ya yi amfani da su a kan ta sun bashi mamaki matuka, kasancewar sa wanda bai son bakin fuska bai kuma sakin jiki da su sam." "Sai ya shiga shafa kan yaron cikin wani hali na tausayin kai, tare da da tasowar wata irin KEWAR Rahinah Omar, ya samu kan sa cikin wani hali na kaka-ni-kayin SO mai wahalar da zuciya, da kuma bakuntar wadannan tsofaffin feelings dinnan da yake dasu tuntuni a kan ta, a dalilin ganin da yayi mata yau; (she 鈥檚 more beautiful and looking more ravishing than ever before)." "A baya ya dauka ya dade da rasa sha 鈥檃 war sa ta Da namiji a kan mace, tun daga kan ta, ya dade da rasa mazantakar sa a kan rashin Rahinah Omar, kudi kawai yake nema sune kadai bukatar sa a rayuwa. Har sai yau da ya ga RahinahOmardin ganin idon sa 鈥฀ a ji muryar ta jin kunnen sa 鈥฀. Ya gan ta more mature, more ravishing and more sexy than before." "Sai komai ya dawo masa sabo fil, ya ji shi ya koma yaro matashi danye mai tashen balaga da tashen kuruciyar nan, wannan Habibun dan kimanin shekaru ashirin da tara ba arba 鈥檌 n din da yake da su a yanzu ba, wato lokacin da ya fara ganin Rahinah a Jamus. Wani abu mai kama da tsoro kuma ya zo ya darsu a ran sa a dalilin maganganun yaron a kan Uwar sa." "Daga bisani ya ga bashi da mafita, domin Abdallah ya tsatstsare shi da Almondshapedidanun nan nasa irin na uwar sa, wadanda ke tado masa da tsofaffin abubuwa da ya riga ya manta da su, suka shude tun wani karni can da ya shude, amsar sa kawai Abdallah yake son ji. Sai yalumshe ido na tsayin lokaci kafin ya bude su a kan Abdallah ya ce. ""Ka yi hakuri sai gobe Abdallah, zan gaya maka ko wacece ita, amma in ka yi min alkawarin duk runtsi; ni zaka zaba a kan ta!鈥฀." "Cikin mamaki yaron ya kalli mahaifin nasa da kyawawan idanun sa sak na Rahinah, in da abinda Abdallah ya dauko a jikin ta guda daya kwakkwara, to kwantattun idanun ta ne masu gazar-gazar eye-lashes, har sai da Habibu ya ji wani irin abu ya tsirga a zuciyar sa da ruhin sa a dalilin kallon da Abdallah ya yi masa, domin exactly irin kallon da Rahinah Omar ta yi masa dazu ne yaron yayi yanzu. Wato kallon tuhuma, amma na Abdallah mai cakudeda kauna irin ta Da da mahaifi." "Sai ya tuna idanun ta dake kallon su dazun,a bakin kofar shiga falon gidan Uncle Usman,cikin ragaita da rashin sanin abin yi 鈥฀.. gani ya ke kamar Abdallah zai zabi Rahinah ya bar shi in ya ji ko wacece ita a gare shi, shine abinda ya ke tsoro, to gashi ya ce yana son ta (from the first glance) ba tare da ya san ko wacece ita ba, ina ga ya ce masa ita ce ta yi nakudar sa?" "Shi kuma yaron sai ya russunar da kwayar idon sa kasa, bai ce komai ba." "Bai ce komi bane saboda bai fahimci dalilin Baban sa na cewa hakan ba. Amma duk da kasancewar sa yaro to fa ya digawa maganar Baban sa a kan bakuwar matar nan katotuwar ayar tambaya. cewa da Baban nasa ya yi," 鈥฀ in ka yi alkawarin ni za ka zaba ba ita ba!鈥฀. "A haka Habibu ya samu yayi barci, ya karanta addu 鈥檃 r barci ya shafe shi sosai, lokacin ne kiran Rahinah ya shigo masa." """Hello!鈥฀" "Habibu ya sake fada, wannan karon da kwantar da murya, jin tana numfarfashi kawai cikin bala 鈥檌 ta kasa cewa komai. Ta rasa ta ina za ta fara. A yadda ya san ta da ego da boldness, bai zaci zata kasa voicingout maganarda ke cike a bakin ta ba. Wata irin mace ce mai tsayayyar zuciya." """In ba kira bane please zan ajiye in kwanta, ina da sammako gobe da safe 鈥฀ ya fada da harshenGerman. Maimakon Hausa ko Ingilishi. (German Language) shine harshena biyu da ya san Rahinah ta fi sabawa da shi. Wannan ya tada tsigogin jikin Rahinah, wani abu yamm! Kamar tashin tsigar jiki ya soma bin tafin kafar ta, sakamakon tuna baya. (The way he kept on 鈥฀. raping her daily a tsayin KWANAKI BAKWAI kamar ya samu kuyanga) ya dawo sharr! A zuciyar ta da yayi magana da harshen German. A wancan lokacin duk sanda ya kusance ta da harshen Jamusanci yake mata sambatu. Zuciyar ta ta tuna mata ko waye Habibu, don haka kada ta bari kwantar da muryar sa ya kassara ta ta fasa kudirin ta na kwatar Dan ta, zaluncin sa ya fi da haka." "Ba 鈥檃 kidnapping Da kawai ya kware ba, har da kidnapping zuciya da ruhin diya macen duk da ta yi hadarin fadawa hanyar sa." "Da wannan tunanin, Rahinah Omar ta kwarara kan ta, ta hanyar tattaro dukkan kuzarin ta da karfin zuciyar da ya rage mata. Hankalin ta da nutsuwar ta ta hada su wuri guda ta dunkule su cikin tafin hannun ta, ta sani kwarai cewa da babban mutum take magana a yanzu, mai amsa taken (Young Nigerian Hotelier) wanda ya kama kasa, ya ajiye Naira da kwalayen boko, ba dan saurayin dalibin nan na 'Cologne University 鈥฀ da ta sani ba. Don haka dole ta yi taka tsan-tsan. Ta kuma iya takunta." """Kana magana da Rahinah Omar!鈥฀." """I 鈥檓 aware"". (Wato ya sani)" "In ji Habib kamar cikin rada, muryar sa na nuna halin ko in kula." "A ran sa ya ce ""the happiness destroyer, the cruel lady in action, and also a heart breaker (mai tarwatsa farin ciki, muguwar mace mara tausayi ma 鈥檃 bociyar karya zuciya)!"". Rahinah ta hadiye bacin ran ta, tana kara baiwa zuciyar ta hakuri. Ita ke nema a wajen sa dole ya wulakanta ta yadda ya ga dama." "Zata shanye komai in dai eventually zai bata Dan ta, gudan ran ta Abdallah ta tafi da shi gidan ta a Abuja. Ta sanya shi makaranta, su kwana gado daya suna hira, tana koya masa karatun Alqur 鈥檃 ni daga kwance. Me zai fi wannan moment din dadi a zuciyar uwa? Ba abinda zai kara gama su ko a hanya (bayan ta karbe Abdallah) balle yayi mata wulakancin sa da ya gada nau 鈥檌-nau 鈥檌." """Ba Hotel nake so a bani in sauka ba Yallabai, balle a zaci bara ce ko maula suka kawo ni. I don 鈥檛 care ka gane" mai magana ko a 鈥檃 h? "Da na, Abdallah, wanda na haifa a kasar Jamus ba tare da taimakon kowa ba, wanda aka bi dare aka dauke mini, nake so a bani yanzu, kamar yadda Shari 鈥檃 h ta bani, cikin aminci da salama, ba tare da mun taba mutuncin juna ba ko wani thirdparty ya shiga." "In ya so idan ya balaga sai ya zabi wanda zai zauna da shi tsakanin ni da kai din, tunda haka shari 鈥檃 h ta tanadar mana 鈥฀." 鈥淎 llah ko?鈥฀ Habibu ya tambaya cikin izgili da shagube. Kai har da tsagwaron raini. Kafin ya ce. """Baki san hanyar kotu bane da zaki neme ni da salamar in baki Dan ki? Na dauka komai bisa doka da doron shari 鈥檃 hr yafi bada ma 鈥檃 na? Ai Dr. Rahane kike ko wa? Ba Otorlaryngologist ba ko shugabar likitocin Najeriya da Jamus aka baki kin yi kadan ki karbi yaron nan daga hannun Uban sa. Muguwa kawai, azzaluma!!!鈥฀." "Yana fadin haka ya kashe wayar sa. Ya cusa kan sa a karkashin filon da yake kwance a kai, zuciyar sa na hankoro a cikin kirjin sa kamar zata fito ta bakin sa." "Sabuwar soyayya ta zo ta lullube shi, tamkar numfashin sa zai bar gangar jikin sa. Tamkar ruhin sa zai bar cikin numfashin sa." "Ko me ya tuna? Sai ya dago kan sa daga karkashin filon, idanun sa sun kada sun rine, gara a ce hawaye yake da launin da suka koma. Ya dauki wayar sa ya rubuta sako (text) ya turawa lambar data kira shi yanzu." "鈥淒 elete my number from your phone Rahinah, don 鈥檛 ever attempt to call me again, daga ni har Abdallah we" don 鈥檛 need you in our lives anymore!鈥฀. "(Ki goge lambata daga wayar ki Rahinah, kada ki kara kokarin kira na, daga ni har Abdallah bama bukatar ki cikin rayuwar mu ko kadan)." Yana tura sakon ya goge lambar da sakon bakidaya. "(Saidai ashe ya goge lambar ne a kan fuskar wayar sa kadai, amma tuni kakkaifar kwakwalwar sa ta haddace lambar Rahinah Omar ba tareda yin shawara da shi ba, kamar yadda ya haddace karatun sallah a cikin kwanyar sa)." "Da asubahin washegari ta gan shi at a smart pace (afujajan) babu ko wankan safe ta san wani muhimmin al'amari ya taba zuciya da ruhin Habibullahin ta. Tabawar da aka dade ba 鈥檃 yi masa irin ta ba. Habibullahin ta dan gayu da kwalisa yau babu ko wanka ya kamo hanya. Idanun sa sun yi luhu-luhu na rashin barcin daren jiya, sun kada sun yi jajir dasu." Ilai kuwa suna gaisawa abin da Habibu ya fara fadi shi ne. """Hajiya, ga Abdallah nan na kawo miki shi ya yi miki sallama, zan kai shi makarantar kwana a duk garin da Allah ya nufa 鈥฀." "Da jin haka Abdallah ya dago da sauri, nan da nan ya soma turjiya yana shura kafa irin na 'ya 鈥檡 an gata shagwababbu ""...ni gaskiya Daddy ban yarda ba, bana son boardingschool, wallahi bana so, ni wajen Mummy zan koma gun su Yaya Musaddiq, kuma na ce maka zan koma in ga wannan balarabiyar matar baka maida ni ba 鈥฀." "Bai san sanda ya kai ma Abdallah duka ba, ji kake gab! Ya gabje masa baki, dama zuciyar a kusa take. Hajiya ta yi maza ta tare dukan don ya sauka a nata hannun amma tuni ya samu Abdallah, bakin sa saura kadan ya fashe. Habibu ya hau fada kamar ba shi ba, ta inda yak e shiga ba ta nna yake cfita ba." "Hajiya ta manta yaushe rabon da ta ji Habibu ya daga muryar sa irin haka, (he is always calm, cool and smart) amma yau ya ma manta da Hajiyar sa yake magana." """daga yau kada a kara kai shi gidan Yaya Badiya, na hana daga yau, in dai don makaranta ne zan nemi boardingschool da ta dace da shi in kai shi goben nan, amma ya gama zuwa Kaduna, yagama har abada ba zai kuma zuwa ba""." Hajiya da sakakken baki ta ke kallon sa. """Kan ka daya kuwa Habibullahi? Me Badiyar ta yi maka haka da zafi? Allah dai ya sa ba shaye-shayen zamani kuma ka fara ba""" "Mikewa ya yi yana balle links din hannun rigar sa yadda zai ji dadin yin alwala yayi sallahn nafila ko zuciyar sa ta lafa daga tafarfasar da take yi masa, wanda ba kowa ya janyo ba sai RAHEENAH OMAR, haka kawai -kawai yana rayuwar sa lafiya ta dawo ta hargitsa shi, ba tare da ya baiwa Hajiya Kaltume amsa ba, ya sa kai ya fita daga dakin." "Duk wanda ya yi wa Habibu Nahuche farin sani kamar Badiyya da Hajiyar sa, kallo daya za su yi masa su gane daga jiya zuwa yau har wata 'yar kwarya-kwaryar rama ya yi, sabida damuwa da azabar tasowar soyayyah, ramar da ganin Rahinah Omar ce ta haifar, ya kuma tada tsohon tsumi da tsohon miki wadanda suka dade da warkewa don haka a yanzu bai san ya ya zai yi da su ba." "Haka Hajiya Kaltume ta rabu da shi ya yi alwala shi ma Abdallah ya yi, don ya tsorata sosai da dukan da Daddyn ya kai masa, wanda wani abu ne da bai taba faruwa ba sai yau, don haka sosai ya shiga taitayin sa, suka tafi masallacin gidan tare (wanda shi ya gina wa al'ummar unguwar) don samun jam'i." "Kuma har suka je masallaci suka dawo suka zauna shi da Hajiya suna sallama bai gaya mata maqasudin dalilin sa na rabo dan sa da gidan Badiya ba, Badiyar da ta zame wa yaron UWA a lokacin da yake tsananin bukatar kulawar Uwa. Hajiya Kaltume ta dube shi sosai, alal hakika a matsayin ta na uwar sa, ba ta taba ganin Habibullahin cikin kwatankwacin irin wannan birkitaccen yanayin ba." """Ka ki gaya min me ya faru? Laifin me Badiyar ta yi muku da za ka ce haka? In duniya da amana har kana iya nuna wa Badiya iko a kan Abdallahi? In da alkawari ruwa ba zai dafa kifi ba""." Hajiya ta fada da sanyin murya. "Habibu ya yi kasa da ido, cikin kasalalliyar murya ya ce, ""In tana son ganin shi ta zo nan ko ta je Lagos ta gan shi, amma na raba shi da gidan ta daga yau. Ra'ayi na ne kawai hakan Hajiyar mu, ba don sun mana wani laifi ba, ita ko maigidan ta alkhairi ne kawai tsakani na da su. Allah ne kuma zai biya su alkhairin su ga Abdallah ba ni ba""." "Hajiya ta yi masa kallon, 鈥漷 o ba ka isa ba 鈥฀, sannan ta gyada kai ta ci gaba da jan carbin ta. Daga haka ba ta kara ce masa komai ba, don ita duk abin da zai raba kan 'ya'yan ta biyun nan (Badiya da Habibu) da Allah ya ba ta tana neman tsari da shi." Ba ta fatan 'ya'ya su raba wannan kyakkyawan zumuncin na Habibu da Yayar sa Badiya har bayan ran ta. So take su rungume juna 鈥檡 a 鈥檡 an su su dunkule su zama abu guda. Allah SWA ya yi gaskiya da ya ce (鈥檡 a 鈥檡 a da dukiya fitina ne). Bazata zuba ido 鈥檡 a 鈥檡 a su yi sanadin wannan zumuncin ba. "Washegari suka wuce Lagos a jirgin sama da zummar zai je ya yi masa cuku-cukun samun gurbi a (British International School) da ke Lagos. Gara shima ya hakura da ganin Abdallahn, da dai RAHINAHOMAR ta samu access din sake ganin sa!" ****** DR. RAHEENAH OMAR A "can Kaduna kuma ko kafin jama'ar gidan su tashi daga barci Rahinah ta kama hanyar Abuja a washegari. Ita kadai cikin motar ta kiapicanto, sai sharara gudu take yi kamar zata tashi sama, don tsabar rashin nutsuwa a can ta baro Baba Sahura ta manta ma tare suke. Hukuncin Allah ne kawai da kiyayewar sa ya kawo ta Abuja lafiya amma ba nutsuwar tuki ba." "Tana shiga Abuja gidan ta ta nufa, cikin gidajen likitoci na 鈥橬 ational Hospital 鈥฀, ta shige ta kulle kan ta. Ta kuma kashe dukkan wayoyin ta." "Nutsuwa ta ke so ta samu ko ya ya ne, kafin ta yanke shawarar abun yi, amma nutsuwar ta ki zuwar mata sama ko kasa." "Ta kwanta rigingine tsakiyar lallausar gadon ta da niyyar ta yi barci, ko ta samu rangwame, amma barcin ya ki zuwa shima. Gabadaya jin kanta ta ke wani irin a birkice, upset, kuma upside-down. Ko ta ki ko ta so, kuma hakan na da nasaba ne da muggan kalaman dan mutanen Nahuche a wayar da suka yi jiya, bayan wucewar shekaru goma." "To dama ita soyayya tana rikidewa ne farat daya ta koma kiyayya? A sanin ta har suka rabu bin ta yake da kokon barar SO. Yaushe wsannan son ya rikide zuwa kiyayya? Itace dai bata da tabbaci akan tata zuciyar, amma kalaman sa sun sa ta gano da gaske ba ya bukatar tata, amma ita tana da bukatar tasu (Uban da Dan sa) in su basa bukatar ta (kamar yadda yace)." "Sai dai kuma ko da bukatarta ta dawowar su cikin rayuwar ta ita ce zata yi ajalin ta 鈥฀ a haka zasu kare wutsiya a zage. This self-esteem da yayi takingfor granted a baya, yanzu ta fara maintaining din sa." "Ta tuno sunan da Habibu Nahuche ya kira ta da su a karshe, "". Muguwa-Azzaluma!!!鈥฀." "Rahinah kamar tayi hauka, kalaman sun rikita ta, ita kadai a uwardaki sai kai da komo take kamarf zararriya tana tambayar kan ta," """da gaske ni muguwa ce? Azzaluma ce ni? Me na yi masa na zalunci? Me na yi masa na mugun ta? Ni ban kira shi da duka wadannnan sunayen ba sai shi zai kira ni da su?" A wurin ta mata suna sarayar da ESTEEM din su akan 鈥檡 a 鈥檡 a da SOYAYYAH su bari maza su taka su son "rai, su keta alfarmar su. Su danne 鈥檡 ancin su da hakkokin su da addini ya basu. Hujjar su da taqamar su shine zasu zauna sabida 鈥檡 a 鈥檡 an su. Annabi SAW mai girmama matan sa ne da mutunta bukatun su, mai nuna musu soyayya ne, ya yi umarni ga mazan aure kada su zowa matan su ba tare da dan aike ba, kada su aure su bisa tursasawa, ya yi umarni da fahimtar juna kafin aure." "Wadannan su ne hujjojin ta na kin barin soyayyar Habibu ta yi galaba a kan ta, amma ba don bata son shi ko ba ta son Dan su ba. Ta fara son shi immediately bayan rabuwar su, ta yadda har ta dinga bibiyar al 鈥檃 marin shi, amma sai bata dauki soyayyar matsayin priority ba sama da goalattainment." A yanzu all her dreams have come true. The goals are well achieved and properly actualized. Abu biyu ya rage mata yanzu a rayuwa; soyayyar miji da soyayyar Dan ta (family life). "鈥淒 ole in yi amfani da kuduri na na biyu, da na ki da na so, in ba haka ba HABIB NAHUCHE zai sha ni basillah! Bazai bani Dana ba, sannan na cigaba da bin sa ta lalama zai cigaba ne da wulakanta ni ne da bata min lokaci." "Rahinah ta shigo garin Abuja ne daga Kaduna absent-minded don haka ta manta cewa ita ma'aikaciya ce da za a iya nema a kowanne lokaci, amma ta kulle kanta ta kulle wayoyi. Ta manta tana zuwa aiki kullum. Halin da ta ke ciki ya danne komai. Ita kadai ta ke suffering a zuciya da ruhi, ba tare da Habibu Nahuce ya san tana yi ba." A lokacin shi da Abdallah suna gidan sa dake Ikoyi. Har ya fara registration din makarantar Abdallah. "Daga wannan ranar, daga wannan lokacin daga Habibu har Rahinah babu wanda ya kara nutsuwa, babu wanda ya kara samun sukunin zuciyar sa, (they are internally suffering with concurrent love, hatred, and emotional torture). Habibu ya shiga tafka shirme a wajen aiki bisa rashin sani, haka a takardu muhimmai sai ya yi ta kuskure ana ankarar da shi." "Wannan ne yasa PA din sa na Lagos, Rasak, wanda bayerabe ne ya karbi komai daga hannun sa ya dauki hutu na tsayin sati uku." "Maimakon ya zauna a gidan sa na Ikoyi bayan ya kai yaron makaranta sai ya tafi NAHUCHE HOTEL, LAGOS, ya kama (Excutive VIP room). Ita kuma daga baya Dr. Irshad ya ba tahutudon ta gaya masa bazata iya aiki ba awannan dan tsakanin tunda ta san rayukan mutane ne hannun ta a NIZAMIYE kasancewar shi da kan sa yafahimci ba daidai ta ke ba a satin nan. Ta gaya masa tana neman wanda zai shige mata gaba on a legal issue zata maka wani kotu!" "Dr. Irshad ya dauka wasa take yi sai ranar da ta kira shi a waya ta roki alfarmar ya zo ya dauke ta a 'Federal High Court 鈥฀ baza ta iya tuki ba, tana fama da ciwon kan barin kai guda (migraine)." "Dr. Irshad ya dauko ta daga kotu zuwa asibiti ba tare da ya san abinda ta je ta yi ba, a hanyar su ta dawowa Rahinah tace ta bashi dama idan har yanzu yana son auren ta ya turo wajen iyayen ta." "Dr. Irshad dai ya san Dr. Rahina ba daidai take ba a satin gabadaya, wannan amsawar da ta yi masa ma ta farat daya bai gane mata ba, tana magana idon ta a rufe kamar mai ciwon baki, butkoma dai menene matsalar ta he will not miss this golden chance (wannan kyakkyawar damar data bashi wadda ya dade yana jira), yace insha Allah cikin satin nan zai turo magabatan sa daga Yemen." "Ita kadai cikin gida kamar sabon kamu, gabadaya ta birkice. Gashi dai ta ce da Irshad ya turo, amma duk da haka ta kasa nutsuwa, Habibu Nahuche ya kusa haukatata da mere kalaman bakin sa, wadanda basu fi kalma biyu ba." "鈥淢 uguwa-kawai-azzaluma!鈥฀, sune kalaman da ke haunting din ta." "Gashi ta baro Sahura a Kaduna. Da ta ga za ta mutu ita kadai a cikin gida don ko abinci ba ta iya girkawa sai dai ta sha madara, da dan abin da yake cikin firjin gefen gadon ta, sai ta tattara inata-inata ta nufi gidan su Nene." "Don ma kada kadaici ya sake tambayar ta wane ne Habibu Nahuche? Ko ya tuna mata kalaman bakin sa. Sai ta ki sauka a dakin ta na gidan kamar yadda ta saba, ta sauka a dakin Yafendo. Ta tabbata duk runtsi tsohuwa Yafendo ba za ta barta da damuwa da kadaici ba." "Ai kuwa Yafendo ta shiga hidima da kawar ta likita Rahin (yadda ta ke kiran ta) ta tashi musamman ta yi mata burabuskon shinkafa da miyar taushe tana cewa," """Mutumiyar Rama, ko a jika rama ne?""" "Ta yi dan murmushi ta ce, ""Komai ma na samu zan ci Yafendo, kwana na hudu kenan ban ci dafaffen abinci ba"". Yafendo ta kama haba, ta ce." """Kwana hudu? To a dalilin me? Haba, ni fa na ga duk kin yi wani zuru-zuru, firgai-firgai da ke""." "Ba ta bai wa Yafendo amsa ba ta mike tana rage nauyin kayan jikin ta. Laffaya koriya sharr da ta ji adon pinkflowers. Amma da zata iya da ta gayawa Yafendo cewa; A dalilin HABEEBUN su, a dalilin dan mutanen NAHUCHE, ba zuru-zuru firgai-firgai ba har dan karamin hauka ta tabbata ta san ya same ta a tsayin satin nan bakidayan sa, tunda" "kuwa an dakatar da ita daga ayyukan ta na fidar kunne, hanci da makogaro wanda tafi kowa kwarewa a kai a garin Abuja don shugaban ta ya gane ta fara zautuwa." ******* *SUMAYYAH ABDULKADIR* 07030137870 *NA HUCE* *ZAMFARA* "Dr. Badiya ta isa Zamfara yamma lis, domin su hadu ita da Hajiya da sauran 鈥榶 an uwa su shirya yadda tarewar" "Rahinah za ta kasance. Ta sha kiran Habibu a waya tun daga ranar da aka daura aure, ba don ta yi masa albishir din komai ba sai don ta ji lafiyar sa. Duk da ta san fushi ya ke da su daga ita har Daddyn Musaddiq tunda su ne silar komai, silar sake kulla masa Rahinah Omar a matsayin matar sa, amma duk sanda ta kira sai ta samu duka wayoyin sa a kashe suke." "A karshe ta kira PA din sa na Lagos wato Mr. Rasak, shi yake gaya mata Ogan sa ya dauki hutu baya ganin kowa kuma baya amsa wayoyi, tace ya kai masa wayar, ya ce daga gida Zamfara ne. Amma sai ya ce mata 鈥淚鈥檓 sorry Ma, bani da hurumin yin hakan, bai bani damar zuwa inda yake ba, in ba shi da kan sa ya neme ni ba." "Amma ki kwantar da hankalin ki lafiyar sa kalau, don Cook din sa ya tabbatar min yana dan cin abincin da yake kai masa""." "Aunty Badiya ta yi a jiyar zuciya, a zuciyar ta ta yi alkawarin sai ta ji abinda ya hada wannnan gabar tsakanin Habibu da uwar dan sa Rahinah daga bakin ita Rahinah, don ta tabbata Habibu ba zai taba gaya mata ba." Abinda Badiya bata sani ba shine har gara Habibu wani lokacin akan Rahinah wajen taurin kai da zurfin ciki irin na Fulani. "Badiya ta lura yau annurin da ke tare da Hajiyar su ma daban yake, alamu ne masu kyau na ta fara sakin ran ta a kan auren. Bayan sun gaisa ta ce ""me yasa bata zo mata da Zarah ba ta debe mata kewar Abdallah, tunda Juniour din uban sa ya dauke shi? Don ya gwada musu shi ke da iko da dan sa?鈥฀ Badiya ta bata hakuri tace 鈥淶 arah na da (common entrance exams) shi ya sa basu taho tare ba 鈥฀." Hajiya ta ce 鈥渕 e kika tsara game da tarewar 鈥榶 ar taki? Ta wani fannin kanwar taki? Kuma yaushe zaku je ku dauko ta?鈥฀ Badiya ta langabar da kai cikin damuwa ta ce 鈥淗 ajiya ina naga Habibun balle mu tsara tarewa? Ko waya ya daina amsawa tun daga ranar da aka daura aure 鈥฀. Hajiya ta jinjina kai ta ce 鈥渟 hin wai ni menene hakikanin matsalar su ne? Sama da shekara goma kullum magana "daya yake yi a kan ta 鈥渂 a ta son shi 鈥฀ ku kuma kun dage sai ita, tunda 鈥榶 ar ku ce. Amma ai gara ka auri wanda ke son ka, a kan ka auri wanda kake so, ba ya son ka 鈥฀." "Badiya ta ce 鈥渁 i ki bar maganar rashin so a tsakanin su Hajiya, tsabar iya shege ne kawai. Sabida son junan su" "suka kasa aure kowa ya shaida wannan. Manema ba irin wadanda Allah bai baiwa Rahina ba, har da 鈥榶 an asalin kasasshen larabawa, shikuma Habibu wadanne irin mata ne ba 鈥檃 kawo masa ba? Ko bai gani a duniya ba?" Don haka ni bana regretting maida auren nan da su Daddy suka yi kuma har abada ba zan yi nadamar hakan ba. "Sannan Daddy ya gaya min da amincewar ta suka maida auren, ba tursasa ta suka yi ba." "Sanda suka hada kan su a can wata uwa duniya suka yi aure har suka haifi da ai bamu sani ba, basu yi shawara da mu ba, to haka yanzu ma, sanda zasu daidaita kan su, su yi wa kan su maganin matsalar da suke da ita baza mu sani ba Hajiya. Ko labari ba zamu ji ba. Tunda dukkan su ba yara bane." "Abinda yake hakkin mu shine mu tabbatar Habibu ya zama cikakken mutum ta hanyar cika sunnar Manzo SAW, haka itama Rahinah, abinda ya ragewa Baban ta kenan, ya sada ta da dakin aure don cika amanar dan uwan sa marigayi." Don haka ta fannin mu mun sauke nauyin da ya rataya a wuyan mu. A dai wadannan shekarun na Habibu da ya dace ace yana da 鈥榶 a 鈥榶 a hudu ko biyar. "Don haka Hajiya ki daina fargaba kan duk wani nunkufurci da zai nuna, ina mai tabbatar miki a zuciyar sa farin ciki ne zallah, jin zafi ne kawai akan abinda ta yi masa wanda su kadai suka san shi, kuma a hankali bacin rai mai gushewa ne. Amma soyayya ba mai gushewa bace, da sannu zan binciki ko ma wace irin matsala ce a tsakanin su don a magance ta 鈥฀." "Hajiya Kaltume ta ji dadin bayanan babbar 鈥榶 ar ta Badiya, hankalin ta ya kara kwantawa. Domin hakika a baya ta shiga rudani akan auren, sabida yadda Rahina ta fita fit! Daga ranta, yanzu kuwa Anty ta dan kankaro mata mutunci tunda ta ce da ita tana son Habibullahi itama, bacin rai ne ya sa ta kai shi kotu, sannan ba shi kadai yake koshin wahala ba, itama kuma ta dandana rashin auren na shekara goma a kan sa ba don ba ta da manema ba." 鈥淭 o yanzu ta yaya kike ganin tariyar zata kasance tunda kin ce ko waya ba ya dagawa? Nima bai kira ni ba. Bana so iyayen ta su gane baya murna da komen auren 鈥฀. "Hajiya ta fada cikin damuwa, Badiya ta ce 鈥渢 attaki zamu yi har Lagos din mu same shi, ni da ke da Baban Musaddiq, sai dai kawai ya gan mu a gidan shi, in ya so ayi wacce za 鈥檃 yi ya fadi duk inda yake son ta tare. In gidan shi na Abuja ne? In kuma Lagos din za 鈥檃 bi shi da matar shi to duk ya fada, ba zai mai da mu kananan mutane a idon surukai na ba." "Habibu yayi kadan ya dinga juya mu, wanda yayyi a baya ma ya isa. Hajiya sanyin ki yayi yawa a kan Habibu shi yassa yakke yin yadda yagga dama 鈥฀. Murmushi Hajiya Kaltume ta yi ta ce," 鈥渢 o Badiya in ban tausasa masa ba wa zai tausasa masa shi ba mata a gida ba? Mu bi komai ta nutsuwa. "Kuma a hankali, abinda lallashi bai bayar ba tursasawa ba zata bayar ba." "Ni babu Ikkon da zan iya zuwa, kafafun nan bazasu jure hawa jirgi ba don kwanannan ba dadin su nake ji ba, ku dai je ke da mijin ki amma don Allah ku lallabashi ku lallashe shi 鈥฀." "Dariya Aunty Badiya ta yi, ""Habibullahi autan Hajiya!"" Hajiya tace ""na ji din""." "A haka suka tsayar da maganar, cewa a gobe, kwanaki hudu da daurin auren, Uncle da Aunty zasu bi jirgi zuwa Lagos domin su tadda Habibu a gidan sa." ****** "Rahinah na kwance rigingine a dakin ta bisa gado, cikin dakin ta na gidan Ambasada Shehu, ita ba barci ba ita ba ido biyu ba, Allah kadai ya san abinda ta ke sakawa tana warwarewa a zuciyar nan tata. Wadda ke cunkushe taf da al 鈥檃 mura daban daban duk a kan komen ta gidan Uban dan ta Habibu Nahuche." "Nene ta yi sallama a dakin, biye da ita wata bakar babarbariyar mace ce, ta yunkura kadan ta tashi zaune tana amsa musu da kyar, kallo daya Nene ta yi mata ta gane tun safe bata yi wanka ba. Ta ce 鈥渁 nya Rahinah? Wannnan wace irin amarya ce? To tashi maza in hada miki ruwan dumi ki yi wanka, ga Yagana ta zo zata fara miki gyaran jiki yanzun nan 鈥฀." "Kamar mai fama da ciwon baki ta motsa bakin ta kadan tana tambayar Nene 鈥渨 ane irin gyaran jiki Nene?鈥฀鈥渋 rin wanda ake yi wa amare 鈥榶 an gata mana! Wadanda ake so mijin ya so su, ya gigice a kan su, balle mazan duniya irin Habib Nahuche wadanda ba irin matan da basa gani suna zarya a hotel 鈥฀." "Murmushi ta yi mai ciwo, ta ji ta kara tsanar auren bakidaya, har gara mata sanda yake dalibi akan yanzu da ya zama mai budadden ido, tace," "鈥淣 ene ki yi hakuri ki sallami Haj. Yagana domin bana bukata, bazan yi ba 鈥฀." "Nene ta ce, 鈥渨 annan ne kuma baki isa ba, in kika yi min musu in kira Yafendo yanzu ta wanke min ke tas. Wawuya kawai ana nuna mata abinda ya dace tana shirme 鈥฀." "Ala dole ta mike cikin dacin rai ta zuro fararen kafafun ta kasa, sumul sumul da su tamkar bata taka kasa. Suka nufi toilet tare da Nene." "Nene Balki ta hada mata ruwa mai zafi a kwami ta yi wanka da kyau sannan ta fito, hatta cikin ruwan wankan ta saida Yagana ta zuba turarukan humra wadanda take tafe dasu." "Lokacin da Rahinah ta fito daga wanka sai mai gyaran jikin ta hau aikin ta a kan ta, ta yi mata Dilke da Halawah ai kuwa ta ci kwakwa kasancewar ta mai yawan sumar jiki, a zuciyar Yagana mamakin kyawun jiki da kyawun fata irin na Rahinah take yi tana tazbihi ga Sarkin halitta. ""Rahinah matar manya ce, Allah SWA ya kyautata halittar ta. Tana ta tsokanar ta da cewa" 鈥淎 mma Anti Rahinah angon ki ya more!鈥฀. Bata san bakanta mata ta ke da wadannan kalaman ba. Wai angon ta! Don haka ta zabga mata harara kasa- kasa. "A daren ranar Ambasada ya kira Rahinah falon sa, ga Nene a zaune, yayi mata nasiha mai ratsa jiki da bargo irin wadda ta dace kowanne uban kwarai ya yiwa diyar sa da zai kai gidan miji, don ko Safeenah iyaka abinda ya gaya mata kenan da zai kaita gidan nata mijin shekaru biyar a baya (da jimawa an yi wa Safeenah aure a Jos, ta auri wani Navy Officer Suhail Sajoh a can amma bata haihu ba har yanzu). Sannan ya kawo mukullin sabuwar mota irin tata ta baya ya bata, yace ta barwa Musaddiq tata." "Rahinah sai da ta yi hawaye, a zamanin nan samun mutanen kirki irin Ambasada da iyalan sa masu halin maida dan kowa na su zai yi wuya. Mutane yanzu kowa dan sa ya sani bale wanda baku hada alaqar jini da shi ba sai ta mutunci. A karshen nasihun sa Ambasada ya ce." "鈥淚 na fatan matsalolin ku da kuka kunshe cikin cikin ku, ku kawo karshen su yanzu da kyakkyawar fahimtar juna. Allah yayi muku albarka, ya albarkaci dan ku da sauran kannen sa masu zuwa a gaba 鈥฀." "Ta rasa ina zata sa kanta yau, don yanzu ta gama saddaqarwa ta tabbata matar Habibu Nahuche a karo na biyu." "Washegari suka kama hanyar Adamawa duk gidan, har da Safeenah wadda ta zo tun jiya daga Bukuru, tafiya ce su ke yi mai dadi yau, domin hatta ruwn da zasu sha a hanya da abincin da zasu ci sun tanade shi tun daga gida sun zuba a kuloli sun tafi dasu domin tafiyar wuni guda ce curr. Raha kawai suke suna tsokanar Rahinah wadda bata iya tankawa kowa." "Safeenah ta ce 鈥渟 ai ni babbar kawar amarya, amara kirjin biki 鈥฀ bayan a baya sam bata shiga harkar Rahinah har zuwa sanda aka yi mata aure, amma yau kam ta ware sai tsokanar ta take yi don ta fahimci bata son komen." "Sai bayan isha suka isa Girei, a dakin Uwargida Dudu su Yafendo suka sauka, Rahinah da Safeenah suna dakin Surbajo amaryar Sarkin Fulani." "Duk 鈥榶 a 鈥檡 an Sarkin Fulani da da ke gidan aure a washegari suka zo gidan tun da safe suka taya iyayen su dora tukwane. Sarkin Fulani yasa aka kada shanu har biyu don a yi hidimar abincin biki dasu. Ya kuma gayawa Usman ya gayawa matar sa cewa duk hidimar aure da ake yi na al 鈥檃 da a garin Girei bai yarda ba sai an yi wa Rahinah, don haka yana umartar sa da ya gayawa angon da iyayen sa." "Uncle Usman ya gayawa Badiya sakon Sarkin Fulani, ya kara da cewa ya ce ba zai basu Rahinah su tafi da ita ba sai sun sauke duka wannan nauyin na al 鈥檃 dar su." Na farko tunda an daura aure gabanin kawo wadannan kayayyaki na al 鈥檃 da to sun zama bashi dole ango da iyayen sa su kawo. "Kayan aure wato 鈥榣 efe 鈥฀ shi ne na farko, sannan zasu kawo 鈥榮 uddaje 鈥฀ ga dangin amarya, wato turamen Atampha guda dari, sai akwatin Uwa da na Uba duka za 鈥檃 hada a kawo mana su tare da kayan aure." "Mu kuma zamu yi wa dangin ango 鈥榩 aute 鈥฀ kwatankwacin yawan kayan auren d suka kawo mana (Paute shine kaiwa dangin miji kwanukan samiru, kuloli, gado da katifa da kayan abinci kamar 鈥榞 ara 鈥฀ a harshen Hausa amma ya banbanta dana Hausawa) domin su rarraba a tsakanin su. Ana yin paute ne iya yawan kayan aure da dangin ango suka kawo." "Bamu sani ba ko a taku al 鈥檃 dar ta Zamfarawa kuna yin 鈥楩 ansar Ido 鈥฀ wato (budar kai) a hausance, wanda shi dangin ango ne su ke shiryawa washegarin kai amarya gidan ta, a family house din su inda dangin sa da nata za su tara musu kudi daidai karfin su da iyawar su. Mu anan har yanzu muna yin shi madadin 鈥榸 aman Ajo鈥฀ da ake yi a baya, in kuma baku yi a can Zamfara to ya rage naku." "Mu dai 鈥榶 ar mu yanzu ne muka san zamu yi mata aure ba ruwan mu da wancan gantalallen auren da suka yi, don haka duka binda ake yi wa budurwa shi zamu yi mata. Bamu dauke muku komai ba 鈥฀." "Ai jin haka a wuni guda Aunty Badiya ta hada lefe na gani na fada, ko dama can tana da niyyar lefen, ta bari ne sai bayan tarewar Rahinah lokacin ta nutsu, amma tunda ga abinda Kakanta ya ce ai bata ga ta zama ba." "Ta kuma gayawa Hajiyar su komai, a take suka fidda makudan kudi don gudanar da komai ko ta kan Habibu basu bi ba, har ninkin abinda sarkin Fulani ya lissafo suka yi. Daga Nahuche suka hadu suka wuce kai tsaye zuwa garin Girei ita da kafatanin matan family din su, cikin su har da kanwar Habibu da ya ki aure wato Shafa 鈥檃 tu wadda ta taho tun daga Talata-mafara ta tadda su a Nahuche bisa umarnin mahifin ta, don dai a gyara zumuncin da ya samu tangarda na shekaru masu yawa." "Kasancewar mahaifin Habibu baya raye, Baban Shafa 鈥檃 tu da ke bin sa shine matsayin mahaifin sa a yanzu kuma" madaurin auren sa. "Ai kuwa sun ga karba ta girma wajen iyalin sarkin fulanin Girei, fura da nono kindirmo sabuwar tatsa, soyayyun zabbi da kaji, faten achcha da yaji ganyen rama, gudun kurna da miyar taushe sune abinciccikan da aka sauke su da su. Uncle Usman kuma ya kama musu gidan saukar baki na Girei Motel inda zasu sauka har a gama biki. Baza su wuce ba sai tare da amarya." "An yi biki na al 鈥檃 da cikin karamci, karramawa da mutumta juna, sarkin Fulani da rigima, ya ce shi fa bai gane ba, har yanzu bai ga ango ya zo ba, to bai basu amarya (su Aunty Badiya) sai angon ya tako da kafafun sa ya zo duk mukamin sa." Duk da uzurin ayyuka da Uncle Usman da Aunty Badiya suke ta bayarwa a kan Habibun don basa son bada wata kafa da mata zasu san somethingisfishy tsakanin Habibu da Rahinah. Daga nasu dangin na Nahuche da dama suke kullace da shi tun a kan Shafa 鈥檃 tu har dangin ita Rahinah. "Amma sarkin Fulani ya san komai, duk shawarwarin da ya baiwa Usman da Ambasada na kada a turasasa su da su suka yi amfani, sun bi shawarwarin daya bayan daya, sun basu dama don su yi sulhu kafin su maida musu auren, sun kuma nemi yarda da amincewar Rahinah." "Duk da Uncle Usman da Ambasada sun san ba wai tsugunne ta kare bane tunda ba wai sun daidaita bane baka da zuci, amma a hakan ma suna masu farin ciki matuka, Ambasada ya san with time, a irin son da ya san su duka suna yi wa dan nasu, zasu yarda su manta komai su kuma manta baya su hada kai su raine shi." "Tun kafin a kammala bikin Uncle Usman da Aunty Badiya suka zare jiki don tafiya Ikko su tadda Habibu, don sun san Sarkin Fulani da gaske yake, ba zai bada Rahinah ba sai ya zo da kan sa. Duk da cewa cikin raha ya fadi umarnin nasa, bafillace ne mai Magana guda daya a duk yadda ya fade ta." "Cousins da Nieces din Rahinah da 鈥榶 a 鈥檡 an Inna Dudu su biyu ana kiran su Kubra da Ladi su suka yi mata kwalliya ranar yini da fararen kayan saki, murjani da sauran duwatsun da Fulani ke ado da su, kada ki so ki ga yadda Rahinah ta bada wata irin kala a yau, ita ba balarabiya ba ita ba bafullatana ba haka ita ba ba 鈥檌 ndiya ba." "Safeenah sai daukar ta a hoto ta ke da digital camera da wayoyin ta, tana fadin 鈥渄 a inada lambar wayar Uncle Habeeb, da yau ya sha kallo, don da duka sai na tura masa 鈥฀ Ladi ta ce 鈥渂 a an ce kanin Aunty Badiya bane matar Baba Usmanu?鈥฀ nan Ladi ta ce zata karbo lambar sa wajen Maman Musaddiq a tura masa wadanan hotunan. Rahinah ta galla mata wata muguwar harara ba tare da ta kula ba." "Amma Ladi ta nemi Badiya sama da kasa a gidan ta rasa, da ta tambayi mahaifiyar ta Inna Dudu sai ta ce ta tafi unguwa, itama bata san inda ta tafi ba. Dole zancen turawa Habibu hoto ya sha ruwa. A lokacin Uncle da Aunty suna cikin (Arik-Air) mai zuwa Lagos." ******* "*LAGOS, NIGERIA*" "Uncle Usman Girei da mai dakin sa Aunty Badiya Nahuche, sun sauka a garin Lagos da yammaci, da taimakon waya da suke ta yi da PA din sa na Lagos watau Mr. Rasak. Shi ya zo da daya daga cikin motocin daukar baki na" *NAHUCHE HOTEL (LAGOS)* ya dauke su kai tsaye zuwa gidan Habibu da ke Ikoyi. Don daga baya ya baro hotel din ya koma gidan sa. "鈥淧 ls Uncle, don 鈥檛 mention my name 鈥฀." "Mr. Rasak ya roki Uncle Usman, wato kada ya sa da shi kan taimakon da yayi musu na kai su gidan sa. Don kuwa bai basu damar gayawa kowa yana gida ko yana hotel ba, shi kuma yayi duba ne da cewa Aunty Badiya ce, da mijin ta Uncle Usman wadanda matsayin iyaye na halali suke ga maigidan nasa." "鈥淜 ada ka damu Rasak, ka koma bakin aikin ka 鈥฀, inji Uncle. Yayi musu sallama ya juya bayan ya nuna musu kofar falon da Habibu ke ciki, wadda dakin barcin sa ma yana ciki." "Ginin gidan Habibu na Ikoyi ya burge su ba kadan ba, domin yafi gidan sa na Abuja kyau da tsari nesa ba kusa ba. Sosai Badiya ke bugun kofar babu sassauci da hannayen ta biyu, Uncle kuma ya hau rafka saallama. A lokacin Habibu na kwance rigingine bisa makeken gadon bedroom din sa. Shi ba barci ba shi ba ido biyu ba." "A hannun sa carbi ne dan karami yana ja, don bai dade da idar da sallahr maghriba ba." "Bugun kofar da ya ji ana masa ya bashi mamaki, don ya san ma 鈥檃 ikatan sa baza su yi masa wannan rashin hankalin ba. Sai kawai ya mike ya kunna CCTV camera din sa don dai ya ga ko wanene, ya tabbata dai ba kukun sa bane don lokacin cin abincin daren sa bai yi ba ko mai yi masa share-share. Mr. Rasak bai zo ma a ran sa ba don ba lokacin zuwan sa bane kuma ba ya zuwa sai ya neme shi." "Wadanda ya gani a bakin kofar ya sa shi saurin sauya sutturar jikin shi daga pjs zuwa jallabiyya ruwan madara mai santsi, ya tako cikin nutsuwa irin tasa zuwa falon, daga nan ya bude kofar da Badiya ke neman ballawa." "鈥淓 asy mana Maman Musaddiq, kin san bana son hayaniya 鈥฀ ya fada yana bude kofar yana yamutsa" "fuska, Aunty ta balla mai harara, a lokaci guda tana mai bin sa da kallo daga sama zuwa kasa." "Sai ta ji duk jikin ta yayi sanyi kuma, a lokacin da ta ga irin ramar da kanin nata yayi, Habib Nahuche, wanda yake healthy and energetic a kullum, yau tamkar wanda ya kwanta jinyar sati biyu." "SO, a harshen hausa, LOVE a harshen turanci, HUBB a luggar larabci ba karya bane, it 鈥檚 human nature, wato halittar ubangiji ne a zukatan 鈥榶 an adam da babu dan adam din da ya isa yayi yadda ya ga dama da shi ya kuma zauna lafiya." To Habibu da Rahinah sun ce zasu iya yin yadda suka ga dama da SO. Ko shiyasa dukkannin su suka kasa zama lafiya? "Uncle Usman ya ce 鈥淎 ngo ne haka!鈥฀ Sai ya basu hanya suka wuce zuwa ciki, yana yi musu sannu" "da zuwa cikin girmamawa, fuskar shi babu murmushi he looks moody, babu far 鈥檃 ko kankani haka babu alamun yayi maraba da zuwan su a lokacin da ba abinda yake bukata fiye da kadaicewa." "Suka zazzauna kujerun alfarmar da ke falon har da shi, Aunty na karewa kayataccen falon kallo daga sama har kasa, sai ya dauki wayar land-line wadda iyakacin ta cikin gidan, yayi wa kukun sa Lawrence Magana kan ya shirya wa su Uncle abinci da gaggawa." "鈥淏 a abinda ya kawo mu ba kenan ka bar abincin ka, mun zo ne takanas don ka gaya mana inda Rahinah zata" "tare, Abuja ko Lagos ko kuwa Port Harcourt? Ka kuma bamu mukullan inda ka zaba mata a hannun mu, sannan mu tasa ka a gaba zuwa Girei, ka je ka amshi auren ka da kan ka 鈥฀." "Inji Aunty Badiya, Uncle Usman kuma ya ce" 鈥渋 na Abdallah da ka dauke mana??鈥฀ "Sai ya rasa wa zai fara amsawa cikin su, don kowannen su a kage yake da son jin amsar tambayar sa, tunani daya ne ya zo wa Habibu a wannan lokacin kuma kyakkyawan tunani ne;" "Cikin abubuwan da Rahinah ke kullatar sa a kai, har da rashin zuwa neman auren ta hannun iyayen ta cikin daraja da mutunci sai wasu banzaye can, for the second time, sai ya ji ba ya son maimaita wannan kuskuren kamar yadda Aunty ta ce ne ya kamata ya je GIREI, yayi duk abinda ya kamata mai neman aure na hakika yayi wajen iyayen Rahinah, sannan ya nemi gafarar su a kan auren ta da yayi a baya a urunce, ba da yawun su da cikakkiyar yardar su ba." "Ko meye ke kwance tsakanin sa da Rahinah Omar (this one is a compulsory duty) da yake tamkar nauyi a kan sa da dole ya sauke. Maganar ya ce baya son Rahinah, ko ya daina son ta, ko ya cire ta bakidaya daga ran nasa is a fable. Wani abu ne da yafi kama da yaudararkai. Abinda yake zahiri inreality shine ya na jin zafin ta, ya hakura da ita ne sabida wulakancin ta, rashin afuwa da kafiyar ta. Da kuma tursasa shi da ta yi ya sake ta ba da son ran sa ba." "Ya hakura da ita ne sakamakon ta kasa yi masa adalci shi da dan sa Abdallah, ta zauna da su ta yafe masa, maimakon hakan sai ta dubi maslahar kanta kadai ta ki karbar kaddarar da ta fada musu su duka." "Shima bai je Jamus don yayi aure ba, ya je ne don yayi karatu kamar yadda ta je yi, amma bai isa ya kori kaddarar sa ba da kuma rabon da ya rantse a tsakanin su." Da wadannan laifuffukan zai cigaba da challenging Rahinah Omar daga nan har karshen rayuwar su. A wurin sa ta zalunce su shi da Abdallah zalunci na deprivation. Idan har ba ita ta san yadda ta yi ta wanke kanta daga cikin su ba (laifuffukan da yake tuhumar ta a kan su) ta hanyar da kowacce macen kwarai ke yi wa mijin ta da dan da ta Haifa. "Wanda ya san ba abu ne mai yiwuwa ba daga Rahinah Omar, a irin girman kan ta da izzar ta, taurin kan ta da ji da kan ta. Sannan da kafiya da tsayuwa a kan ra 鈥檃 yin ta." "Bakin alkalami ya riga ya bushe a tsakanin su, don haka ya san ta inda zai bullo mata da wadannan baudaddun halayen da dabi 鈥檜 n nata." "Da wannan tunanin ya yankewa zuciyar sa zai je Girei, ya karbi auren Rahinah, kamar yadda kowanne mijin kwarai ke zuwa gun surukan sa ya yi duk abinda ya kamata tunda ya amince, ya yardarwa kan sa har gobe YES! Yana son Rahinah a duk yadda Allah ya halicce ta." "Ita kadai yake so, ita kadai yake bege. Daga kan ta ya rufe so, daga kan ta ya dade da jingine so a muhallin sa." "Rahinah Omar. Za ta ci albarkaci mai yawa a yanzu; albarkacin dan su, da albarkacin iyayen ta. Da gaske iyaye da dangi martaba ne kuma sutura ne, domin a baya da tana da su ya san da bai samu damar da ya samu a kan ta ba." Sai ya ji duk jikin sa ya yi sanyi da tunanin sa ya zo nan. ****** NA HUCE is not for free. It's 1000 via 3094856450 Sumayyah Kabara Firstbank. SHAIDAR BIYA 07030137870 *BAKO DAGA IKKO* """Karaso daga ciki Habibullah 鈥฀." "Ambasada ya fada cikin kulawa. Ya taka a hankali zuwa cikin kayataccen falon na tsohon Ambasadan, kyawawan kafafun sa na nitsewa cikin lallausar kilishin falon, har kasa ya tsugunna yana gaishe su, Uncle Usman ya nuna masa kujerar da ke fuskantar su, amma sai bai hau ba, ya zauna akan kafafun sa daga nesa da su." Sun dauki dan lokaci su duka ukun babu wanda yayi magana a falon bayan gaisuwar data gudana. Zuwa can Ambasada ya ce 鈥測 a hanya? Kuma ya kokari? Ya a ka ji da jama 鈥檃?鈥฀ "Uncle Usman bai bari ya amsa ba ya yi kwafa, sannan ya ce." "鈥淜 ayi hakuri Habib, wannan mahaukaciyar ta taso ka daga wajen neman abincin ka, amma yanzu" Ambasada yake gaya min ya sa ta taje ta janye karar. "Na zo da zummar zane ta da dorina kan wannan rashin kan gadon nata, sai shi Baban nata ya bani hakuri ya ce yanzu haka ta tafi ne ta janye karar 鈥฀." "Shi dai bai ce komai ba, amma a cikin ran sa cewa yake 鈥淜 ash! Ai da kun bar ta, an goge rainin da ke tsakani na" "da ita a kan idanun duniya, watakila da ta fi hankalta, in ta gane ni ba sa 鈥檃 n yin ta bane. Ambasada ya kira sunan sa a hankali," 鈥淗 abibu!鈥฀ Bai amsa ba amma ya dago ya dubi Abba Jakadan. 鈥淗 ar yanzu kuna nan a kan bakan ku na cewa bazaku sulhunta ba ko saboda yaron nan? Wa ya gaya muku ana jayayya a kan yaro?鈥฀ "Uncle Usman ya ce 鈥渁 i su duka ya kamata su zauna yau a gaban mu, mu yi magana ta gemu kuma ta karshe mu da su, babu yaro cikin mu, kuma babu sa 鈥檃 n ku, wasa da hankalin da kuke yi mana ya isa haka 鈥฀." "Ambasada ya dauki wayar sa yana kiran layin Rahinah, tana kallon wayar na ringing kamar yadda hantar ta da hanjin cikin ta ke kadawa suma, bata iya ta daga ba har ta katse. Sai ya kira Nene Balki." 鈥淜 i zo min da Rahinah falon saukar baki yanzu 鈥฀. "Nene ta hau kwankwasa mata kofa, ai kuwa Rahinah ta kara tsurewa. Bata son fuskantar kowa a cikin su sabida kallon da Habibu ya yi mata dazu a danja ya lalata dukkan karfin zuciyar da ta ke ji da shi. Ga shi bata san kiran me aka yi masa gidan ba." "Nene kawai sai ta murda kofar toilet din don ta fahimci ba wani abu take yi a ciki ba, ta ce 鈥淩 ahinah lafiya?" Buya ne kuma a toilet? To ki wuce Abba Jakada na kira 鈥฀. "Koda ta dago ido yau Nene sai ta ga rauni a cikin idon ta, kafin a yi haka she 鈥檚 always bold akan duk wani al 鈥" 檃 marin ta da Habibu Nahuche. "Nene sai ta kamo hannun ta, ganin idanun ta sun cika da kwallah, ita kuma sai ta bi ta tamkar Rakumi da akala." "Shigowar su falon tare da Nene bai sa Habibu ya dago ido daga sunkuyawar da yayi ya dube su ba, but her presence overwhelmed him (ya ji kasantuwar ta a wurin acikin jikin sa). Amma hakan bai sa ya nuna ya san da shigowar su ba." "Gefen Habibu Uncle Usman ya nuna mata ya ce ta je ta zauna, zaman ta daura da inda ya ke zaune, da dan motsawar da yayi kamar ya kara zakudawa (ja baya) ya sa ta shako sassanyar kamshin 鈥楥 arolina Herrera 鈥฀ wanda ya tuna mata haduwar su ta farko a cikin jirgi, ranar da ta fara mannuwa da shi ta shaki wannan kamshin. Sannantheir second encounter at Cologne Public Library (haduwar su ta biyu a labiraren jami 鈥檃 r Cologne) ranar da ta barar masa da littatafai ta shaki the same perfume, the subsequent encounters (sauran haduwarwakin da suka biyo baya har zuwa firstnight din su (ranar daren farkon su na aure)." "A take ta ji dukkan karfin zuciyar ta ya dawo, kwanan nan ya kira ta muguwa, azzaluma. Shin tsakanin ita da Habibu idan aka dora a sikeli wanene mugu kuma azzalumi?" "He took away her pride by force, sannan a arha, with no love nor affection. Wannan duk bai ishe shi ba, ya mayar da ita bazawarar shekara goma (ta manta ita ta nemi sakin by all means) ya kuma dauke dan ta kwalli daya da Allah ya bata tun yana zanin goyo ta hanyar sacewa." "Don haka wannan mutumin ba abun tausayi bane, selfishness and rudeness din sa are in style, sun barranta (banbanta) da kamannin sa na zahiri na kamili kuma salihin mutum." "Uncle Usman ya soma Magana cikin bacin rai. Bacin rai irin wanda daga Habibu har Rahinah, babu wanda ya taba ganin sa cikin kwatankwacin sa." 鈥淵 au na ke fatan komai ya kare a tsakanin mu da ku. Ya kuma kare a tsakanin ku. Kodayake tsakanin ku ba zai "taba karewa ba tunda zuri 鈥檃 ta hada, amma bazamu zuba ido ku zubar da mutuncin junan ku a idon duniya ba, shi kuma yaro ku sa bakin duniya ya lalata shi." "Wannan shine zama na karshe da zai guda na, mun baku dama kowa ya fadi abinda ya sa ya kasa yafewa dan uwan sa da abinda yasa kuka zabi zama shekara goma babu aure 鈥฀." "Dukkan su kan su na kasa, amma Rahinah gumi ta ke kashirban. Habibu ya dago a hankali ya dubi Ambasada idanun sa sun kada, sannan ya dubi uban Rahinah, kuma ubangidan sa sannan surukin sa Alh. Usman Girei. Murya babu karsashi yace," "鈥淣 i ba abunda ta yi mun, ni ne ma na yi mata laifi kan laifi, na kuma roki afuwar ta tun a wancan lokacin. I" 鈥檓 not sure (bani da tabbas) ta yafe din ko bata yafe ba. "Rashin aure na shekara goma kuwa mai yuwuwa ne wannan ce kalar kaddarar mu. Amma ni ba don ita na ki aure ba, sabida ba ita ce autar mata ba." "A bayan haihuwar ta da kafin haihuwar ta an haifi dubunnan mata wadanda suka fi ta duk abinda ta ke takama da shi. Kawai bana ra 鈥檃 yi ne. Don na san zan iya rike kaina. Amma yanzu na baku wuka da nama, ni Habibu Mustapha Nahuche, na amince ku aura min kowacce 鈥榶a kuke da ita, tsohuwa ko yarinya, budurwa ko bazawara, ko daga ina ta ke, komai munin ta, akan dai ku mayar min da wannan 鈥฀. Ya nuna Rahinah da bakin sa cikin" "izgili, disgustingly da son tura haushi." "Ta dago a tsanake, idanun ta sun kada, domin sosai kalaman nasa sun buge ta, sun tura mata haushin har fiye da yadda yake so su tura. Maimakon ta dube shi ta maida masa martani, sai ta dubi Baban ta Usman Girei." "鈥淯 ncle, ba ka dade kana min maganar CMD ba? (Chief Medical Director) na Nizamiye, ina cewa ya dakace ni? Ai" "tuni na bashi damar fitowa kuma ya ce cikin satin nan zai je Yemen ya zo da Baffannin sa, su karbi auren. Ni wannan mutumin (ta nuna Habibu da baki) ba abinda ya yi min. Dan da ya shiga tsakanin mu kadddara ne. Amma ba don shi na ki aure ba." "Ban samu wanda ya kwanta min bane tuntuni sai yanzu, ina so ne in yi settling sosai da ayyukana kafin na yi aure. Kuma alhamdulillahi lokaci ya yi yanzu, na baiwa Dr. Irshad damar fitowa already 鈥฀." "Ta kare da sunkuyar da kai sabida hawayen da ke son bada ita. Daga Uncle Usman har tsohon Ambasada sakin baki suka yi galala! Suna kallon su, sun rasa mai ya kamata su ce kuma, ko ta ina kuma za su bullo musu?" "Sai Uncle Usman ya ce 鈥渢 oh-toh, yanzu kin yarda da auren bakon hauren kenan duk da baki ko san al 鈥檃" "dun kasar shi ba balle irin mutanen da yake tare da su? Nasaba, halayya da dabi 鈥檃 duk baki sani ba?鈥฀" "Rahinah ta runtse ido ta ce 鈥淯 ncle shi na zaba, na dade da sanin wasu daga cikin halayen sa musamman" "neman mata, amma wallahi ya fi min wannan sau dubu 鈥฀.鈥฀ (ta sake nuna Habibu da baki). Kuma tunda kun hana ni kai shi kotu sharia 鈥檃 h ta kwatar mun Da na, to ku karba ku bani. 鈥฀." "Kawai sai ta fashe da kuka, ta jingina kai a jikin kujerar da Habibu ke jingine tana ta yi riiii-riii-riiiii 鈥฀." "Ambasada ya ce 鈥渁 i na sha gaya miki muddin ina raye Rahinah, babu mai yi miki auren dole, not evenyour" "father (ya nuna Uncle Usman). Na tsaya miki Rahinah, and I will foreverstand by you (kuma har abada zan cigaba da tsaya miki a matsayin ki na marainiya 鈥฀." "Sai dai kuma Rahinatu bana son yadda kuke ta jayayya akan yaron nan, Allah da ya halicce shi ya fi ku son sa, kada ku tabo fushin sa. Yau da iyayen da suka haife ki suna raye, na tabbata zasu maida ke gidan uban dan ki ne ko ba tare da yardar ki ba." "Mu da mu ke matsayin iyayen ki a yanzu muna neman 鈥淎 LFARMA 鈥฀. Ki yi mana alfarma ki koma gidan mijin ki, zai je har GIREI ya nemi auren ki cikin mutunci, adalci da girmamawa yadda duk ya kamata a hannun iyayen ki, sadaki kuwa sai abinda kika yanke." "Bayan auren kuma, za mu cigaba da bibiya mu tsaya mu ga cewa ya rike ki da amana, adalci, soyayya, daraja da mutumtawa." "For our sake! For Abdallah 鈥檚 sake, for your late Daada 鈥檚 sake, for the sake of the love you have for your son" "鈥︹€฀(sabida mu, sabida Abdallah, sabida marigayiya Dadan ki, sabida kaunar ki ga dan ki) ki manta komai, ki komawa Baban sa. In na ce komai ina nufin KOMAI 鈥฀." "Ya hada hannayen sa biyu cikin alamun roko. Kafin Ambasada ya kai karshen maganar sa kukan Rahinah ya cika falon, ya nunka na baya. Ta rasa inda zata saka kanta. Habibu ban da jibi (zufa) ba abinda yake yi." "A wannan lokacin ya rasa takamaimai a matsugunin da zuciyar sa take, wani irin duka zuciyar sa ke yi tana lugulgude a tsakiyar kirjin sa. Addu 鈥檃 yake Allah yasa kada Rahinah ta amince da rokon Ambasada Shehu, don bashi da gurbin da zai saka ta cikin rayuwar sa yanzu." "Ya riga ya gama binne ta daga zuciyar sa ba don ta mutu ba! Yana jin dadin rayuwar sa a haka, ba tare da Rahinah Omar a cikin ta ba." "Ita kuwa Rahinah nata tunanin daban yake, Abba Jakada, wato Ambasada Shehu ya fi karfin ya nemi kowacce irin alfarma daga gareta. A irin kalaman da ya yi mata amfani da su, babu tursasawa, a irin lallashin da ya yi mata babu bada umarni, face tsagwaron bata hakkin ta da addini ya ce a bata." "Sannan Ambasada ya ce za 鈥檃 je neman auren ta ne cikin mutunci hannun iyayen ta karkashin tushen ta da asalin ta, babban abinda ya sa ta kullaci auren Habibu na baya kenan; auren ta da ya yi ba a hannun kowa nata ba, wannan kadai ya rankwafar da zuciyar Rahinah, amma ba don matsayin da ta aje Habibu ya canza ko kankani daga zuciyar ta ba." "Ba don feelings din ta a kan sa ya canza ba, har gobe yana nan a Habibun sa, dan mutanen Nahuche da har abada bazata yafewa ba. Aure ne a je a yi ta mayarwa tunda ta yarda ta amincewa ran ta tana son ABDALLAH, baza kuma ta iya rayuwa ta nutsuwa yanzu ba tare da shi ba, daga lokacin da ta dora ido a kan sa bayan wucewar shekaru goma. Bata kuma da wata hanya ta rayuwa tare da Abdallah yanzu, bayan komawa gidan su." 鈥溾€橸 a ta Rahinatu kin min alfarmar? Kin amince a mayar da auren ku ki koma zama gida daya da dan ki Abdullahi karkashin inuwar auren mahaifin sa?鈥฀ "Sai ta gyada kai sama cikin hawaye, wasu na korar wasu. A fili Ambasada ya jero Hamdala, Uncle Usman kuma a zuciyar sa yake yi, don shi ya so ba 鈥檃 tsaya yi wa Rahinah wannan irin lallashin ba, kawai a maida auren in ya so ta kashe Habibu don kiyayya. Ya amince Habibu ba ya kin Rahinah, tata kiyayyar ta fi yawa." "Amma a yanzu ko shi ya fi jin dadin hakan, da bai zama cewa auren tursasawa ne zai kara gudana a tsakanin su ba, a zo a koma 鈥榶 ar gidan jiya." "Duk da haka Uncle Usman na tsoron Rahinah. Ya fahimci ba wai ta amince bane 100%. Ta amince ne kan ba yadda zata yi albarkacin Ambasada, albarkacin ya fi karfin kowacce alfarma daga gareta." "Sai a lokacin ya magantu, 鈥渋 n ma akwai abinda kika kudurta a ran ki ki sani Allah yana kallon ki, in" "ma ba don Allah kika amince ba duka ya rage naki, da hannu na dai bazan dauki 鈥榶 a ta in baiwa bakon haure ba." "Mu za mu dan fita, ku yi amfani da wannan damar ku yi maganin matsalolin ku domin insha Allahu rabbi, sati mai zuwa za 鈥檃 maida auren ku. Saura kuma ya rage naku. Duk wanda ya zalinci dan uwan sa ko da da kalaman fatar baki ne shi da Allah. Ubangiji SWA ya ce 鈥淲 as-sulhu khair!鈥฀." "Da fadin haka, suka mike shi da Ambasada suka bar falon. Motsin kirki wannan babu wanda ya yi tsakanin Habib da Rahinah." "Kowanne zuciyar sa ta yi nauyi da sabon al 鈥檃 marin da ke shirin samun sa, wato sake zama da juna a karo na" biyu. "Rahinah ji tayi bazata iya cigaba da jurewa zama a inda Habibu yake ba. Gara ta tashi ta bar wurin kafin zuciyar ta ta yi bindiga da bakin cikin da ke cin ran ta. Ta san yanzu bakin alkalami ya riga ya bushe bata da sauran abun yi, bata isa ta dawo ta ce da dattijan nan ta janye alfarmar da ta yin ba. Amma cigaba da zaman ta a falon nan zai iya sawa ta yi hakan (tace ta janye din)." Gara mata zama waje daya da bakin maciji a kan zama kusa da Habibu Nahuche. Don haka ta mike cikin azama ba tare da ta dube shi ko ta ce da shi kanzil ba ta nufi kofa. Da zuzzurfar muryar shi ya dago idanun shi da suka canza launi ya dubi bayan ta tana ficewa. Ya daga murya yadda za ta ji shi sosai. "鈥淕 ara miki ki koma ki warware musu fake yardar taki, na gaya maki, ina kara gaya miki we don 鈥檛 need you" in our lives anymore daga ni har Abdallah. "Bar ganin na yi shiru, ki dauka nima na amince ne, a 鈥檃h, su biyun nan suna da wata irin kima ne a idanu na da" bazan iya yi musu musu ba. Amma wallahi gara duk matan duniya da ke Rahinah! Gara a aura min kowace ce da in kara hada rayuwa ta da ke 鈥฀. Wani lalataccen murmushi ne ya subuce a siririyar fatar bakin ta. Ta juyo gaba-gadi ta fuskanci Habibu. "鈥淣 i da nace na amince, ce maka na yi har zuciyata ne? I just want to be with my son and nothing more," "sabida bana so in kara jayayya a kan sa. Ka kwana da sanin Rahinar da ka sani da, ba ita ce yanzu ba, wadda ka ke raping a duk sanda ka so,wannan sai dai ku yi wrestling, ka shirya zama da sabuwar Rahinah mai 鈥榶 anci, mai gata, tsayayya a kan kafafun ta. Auren ka ko rashin sa, ba zai kare ni da komai ba, banda Da na da zai dawo kusa da ni 鈥฀." "Habibu ya yi murmushi wanda Kalmar ta ta wrestling ce sanadin sa, wasu irinbeautiful serene smiles, ko kadan kalaman ta basu yi masa ciwo ba, (as he expects words like these from her) domin ya tsammaci kalamai kamar su, ko ma fiye da su daga bakin ta, a duk ranar da suka sake haduwa. Don ta huce haushin ta." Yace cikin ginshira. "鈥淩 ahane kike ko wa? Ki tuna yaron nan bai san ki ba, ni ya sani matsayin uwa da uban sa, don haka zuwan ki" "gidan su wai saboda shi, ba abinda zai sa, ba abinda zai hana." "Zan tabbata na gaya masa Uwar sa muguwa ce, azzaluma ce akan Uban sa, wadda bata cancanci yafiya da soyayya daga gareshi ba. Bata taba waiwayar sa ba tsayin shekara goma sai don ta gan shi a akan hanya." "My boy is smart, kuma da wayon sa da hankalin sa, ba kowacce karabiti ce zata zo ta ce da shi ita ta haife shi ba ya yarda 鈥฀.鈥฀." "Yatsunta biyu ta sa ta toshe kunnuwan ta, sannan ta karasa ficewa da ga falon da dan banzan sauri. Har tana cin uban tuntube tare da sa hannu ta toshe bakin ta daga azababben kukan da ke son kubuce mata." ******* *ME YE ABIN YI?* "Dakin Yafendo ta nufa tana kuka wiwi, ta soma hada komai nata da zummar komawa gidan ta. Yafendo, bata ce mata ko uffan ba domin cike take da farin cikin maida auren da Abba Jakada ya ce mata za 鈥檃 yi ranar Juma 鈥檃 h mai zuwa." "Nene ce ta shigo dakin ganin Rahinah ta sunkuto Jakar ta tace 鈥淩 ahinah, babu inda zaki koma fa, daga nan" "gidan sai gidan mijin ki, za 鈥檃 je a kwaso komai na gidan gobe da safe insha Allahu 鈥฀." "Ta fada jikin Nene tana kuka 鈥淣 ene wallahi har gobe ba ya so na, nima bana son shi, Da na kawai nake so" 鈥฀. "Nene abin sai ya koma bata dariya Yafendo kuwa haushi ne ya kama ta, tace 鈥渟hi SON ya ci uwatar, ya ci" "Uba nai, mu da iyayen mu suka yi mana aure bamu taba ganin mijin ba fa sai a gidan sa? Ba gashi mun haifi wadanda suka haife ku ba babu soyayyar? Aka bar duniya ana begen juna, ku kuka dauki soyayya wata tsiya, ba kya son shi kika hada shimfida da shi har kuka haifi Da?" Ina ce karewar so kenan ka hada shimfida miji?鈥฀ "Nene na ta dariya ta ce Yafendo wannan ai ba sai da so ba, kaddara ne, umarnin Ubangiji ne, amma ni in zata dau lasifika ta hau duro tana yekuwar bata son Habibu ba zan taba yarda ba, domin na sha kamata tana searching (browsing) din sa a yanar gizo, har da saving hotunan sa cikin wayar ta da kwamfutar ta, in babu so me ya kawo wannnan? Wanda ba ka so meye naka na bin kwakkwafin sa?鈥฀" "Rahinah ta rasa inda zata sa kanta don bakin cikin abinda Nene ke fada, kamar ta dora hannu aka ta saka ihu, Nene ta cigaba da baiwa Yafendo labarin ranar data kama ta da hoton sa cikin kwamfuta tun suna Frankfurt." "Yafendo ta ce 鈥渁 hap! Ai shi munafurci dodo ne mai shi yake ci, aure kuma an mayar an gama da iznin Allah 鈥" ฀. "A fusace Rahinah ta bar dakin zuwa nata dakin da ke gidan, ta shige ta rufe har da key. Nene da Yafendo basu kara bi ta kan ta ba a gidan. A take Nene ta kira Aunty Badiya." "Suka gaisa, suka taya juna murna na maida auren da za 鈥檃 yi, amma jikin Aunty Badiya a sanyaye yake," "don a lokacin tana can tana fama da Hajiyar Nahuche wadda ta ce gara Habibu ya hakura da Rahinah, don bata hango masa kwanciyar hankali a sake zama da ita ba. Matar da zata kai ka gaban Alkali tabbas bata son ka, Aunty ta ce," "鈥淗 ajiya ki rabu da Rahinah ba halin ta bane, bacin rai ne ya kai ta ga hakan. Amma ba don bata son Habibu ba" 鈥฀. "Don haka da Nene ta bugo yanzu suka yi wa juna murna sai ta ke yi wa Hajiya Haj. Kaltume bayanin marikiyar Rahinan ce ta bugo, komai ya daidaita ta bangaren su sai jiran ranar daurin aure." Kuma dama Uncle Usman ya kira su ya gaya musu sati mai zuwa za 鈥檃 je Girei a maida auren don Hajiya ta "sanar da iyayen sa maza da zasu je su karba masa auren daga garin Nahuche, Hajiya dai kadaran-kadahan ta amsa don Rahinah ta gama sire mata, da ta yi wannan danyen aikin, kamar wadda bata da mafadi ko mashawarci." "Don ta ita a hakura da Rahinah a nemawa Habibu wata, abu daya take tunawa ta hakura wato Abdallah. Tana matukar son ya cigaba da girma karkashin kulawar iyayen sa biyu, ya daina walagigi tasakanin Zamfara da Kaduna." "Amma maganar soyayya irin ta uwar miji da surukar ta tsakanin ta da Rahinah Omar babu ita. Kamar yadda at the same time babu kiyayya. Watau bata kin ta haka bata son ta. A yadda ta ke son Habibullahi, kamata yayi a ce matar sa ta fari ta zame mata 鈥榶 ar gaban goshi, wadda zasu kashe su rufe tare, amma banda wannan Rahinar mai jin kan ta kamar wani dutsen yaqutu." "Washegari suka je suka kai goron tambaya da kudin aure. Aka sa ranar daurin aure Juma 鈥檃 h bayan masallaci, tun" "ranar Alhamis Ambasada da 鈥榶 a 鈥檡 an sa maza Abbas da kanin sa wadanda suka dawo karatu daga Frankfurt, Uncle Usman da nasa samarin 鈥榶 a 鈥檡 an hudu wato su Musaddiq suka kama hanyar Adamawa." Sun dauki hanya tun da sanyin safiya daga Abuja amma basu isa Girei ba sai dare. Kai tsaye gidan Sarkin Fulani suka sauka bayan sun je sun kama Guest Inn din da zasu kwana anan cikin garin Girei. "Kafin isowar su mutanen Nahuche sun riga su isa, kannen mahaifin Habibu ne da wasu dattijai daga family din su har da Baban Ex budurwar sa Shafa 鈥檃 tu wanda shine madaurin auren sa duk sun isa Girei kamar yadda aka tsara. Alh. Usman shi yayi musu masauki a inda suma suka sauka (Girei Motel)." "Washegari misalin karfe uku na rana bayan an sakko masallaci duk suna zaune zauren Sarkin Fulani, manyan 鈥" "榶 a 鈥檡 an sa su Ilyasu, Dagacin garin Girei, makwabta da dattijai abokanan arzikin Sarkin Fulani, abokan mahaifin Rahinah na kuruciya da abokan Uncle Usman na garin Girei da duk wani mai fada a ji a garin Girei, jama鈥檃 r gari 鈥榶 an gayyar sodi ma ba 鈥檃 bar su a baya ba." "Iyayen Habibu (Baffannin sa) suka mika sadakin su mai daraja wanda ya fito ne daga aljihun su da aljihun Hajiyar sa da suka yi karo-karo suka hada ba tareda sun bi ta kan sa ba, kasancewar kowannen su a kage yake kan yayi auren kawai koma da wacece, to balle da aka ce uwar dan sa Abdallah." "Don haka kowannen su cikin farin-ciki yake yin komai, ba bata lokaci aka daura auren HABIBU MUSTAPHA NAHUCHE da DR. RAHINAH OMAR GIREI. Wani aure da ya bar tarihi cike da farin cikin kowanne bangare. Ana yi ana raha da annashuwa. Limamin masallacin Juma 鈥檃 na garin Girei ya bi auren da addu 鈥檕鈥橧 na musanman, tare da rokawa ma 鈥檃 uratan zaman lafiya da kwanciyar hankali na har abada a tsakanin su." "Washegri Asabar kowa ya kama hanyar komawa garin da ya fito, tarewa sai Habibu ya zo da kansa inji Sarkin Fulani. Ya ce Usman ya kawo masa Rahinah nan gidan sa, daga nan Girei za 鈥檃 dauke ta zuwa gidan mijin ta bayan sun yi biki irin na al 鈥檃 dar garin Girei. Usman ya gaya masa tana gidan Ambasada yanzu haka, amma Nene Balki da Yafendo zasu dauko ta su kawo ta, in ya so, su rankaya daga nan Girei zuwa duk inda Habibu ya zaba mata ta zauna." "Kwanaki biyu kenan da daurin auren, ba tare da Habibu ko Rahinah wani ya kara neman dan uwan sa ba ko a waya, amma suna sane da cewa an daura din. Ita tana dakin ta na gidan su Nene a kwance kawai, ba abinda ke tada ta sai sallah." "Ta kashe wayoyin ta bakidaya tana wani irin jinyar zuciyar ta, da jinyar matacciyar gangar jikin ta kamar wadda ke fama da cutar paralysis, sabida yadda ta bi ta rafke akan gado, kokwakkwaran motsi bata yi, sallahr ma bata sanin lokaci yayi har sai Nene ta leko ta shaida mata cewa an yi kiran sallah." "Tun daga ranar da aka kara daura musu aure uffan bata kara cewa ba, domin kalaman Habibu na ranar da ya zo, sun yi wa zuciyar ta lahani da barna mai yawa." "Idan ta yi tunanin wai yanzu ya kara zama mijin ta na sunnah, sai duk wani kyakkyawan tunani ya subuce mata." Ta rasa wanda za ta kama. "Bata da tsumi ba ta da dabara a halin yanzu, sai na irin zaman da za ta fuskanta nan ba da jimawa ba a gidan Nahuche, a karo na biyu!" "Ita dai ta san trial din ta da Habibu bai kare ba, akwai sauran manyan kalubale da ya tanadar mata, wadanda suka fi na baya. Domin ya rama abinda ya ke ganin ta yi masa. Abinda za ta rike a matsayin makamin ta yanzu shine kadai (maintaining self-esteem) din ta, na cewa ta fi gaban duk wani wargin sa a halin yanzu, za ta nuna masa cewa wata fuskar yanzu ta fi gaban mari. In Rahinah ya sani, wannan Rahinatu ce, warki daidai kugun kowanne da namiji." "Daga ita har shi sun kasa kulla komai sai tunani, wanda ya kasa basu mafita ga tarin damuwoyin su da tarin kalubalen da suke hangowa sake zama da juna, tunda dai har yanzu basu kai ga cimma matsaya kwakkwara wadda za ta yi maganin matsalolin su da rashin fahimtar da ke tsakanin su ba." "A nasa bangaren, Habib Nahuche, ya kudurce a ran sa ko kadan ba zai dauki rabin abinda ya dauka a baya daga Rahinah da sunan rashin SO ba, tunda dai yanzun ita ta amsawa kanta ba wani ya tursasata ba, don haka babu hannun sa a ciki. Nan kusa ma bai shirya mata tarewa ba ko inda zata zauna, don kamar yadda yace din ne da gaske bashi da bukatar ta cikin rayuwar sa ta yanzu." "Da dai Uncle da Ambasada sun sani da sun bar bygone a muhallin ta, don basu gama sanin ko wacece 鈥榶 ar" "su Rahinah ba har gobe, shiyasa suke tsammanin da zuciya daya ta amsa, shi kam ya dade da sanin cewa ya riga ya bata baya. Ya manta da ya taba auren ta, ya dade da karbar rayuwa a yadda ya same ta, kuma yana jin dadin ta a hakan. Da Rahinah, da babu ita, ba zai kasa rayuwa ba, insha Allahu." Me jiya ta yi bare yau? Abin nufi me rashin ta na shekaru goma ya kara musu ko ya hana musu shi da Abdallahn? "Da wannan jinyar zuciyar kowannen su ke jibge akan gadon sa, ya dakatar da kowanne ayyuka na cigaban rayuwar sa da dailyactivities din sa." "Amma ga iyayen su da masoyan su abin ba haka yake ba, aunty Badiya, a ranar don farin cikin an daura wa Habibu aure da Rahinah, sai da ta kai goshin ta kasa ta yi sujjadar shukr, ta kuma dafa abinci mai rai da motsi ta rabawa mabukata sadaqah." "Hajiya Kaltume kuwa, ko da bata maraba da Rahinah, farin cikin yau Habibullahi yayi aure da azumi ta tashi a bakin ta." "Itama ta sa an dafa abincin sadaqa an raba a Kofar Jange har gidajen makwabtan ta, ko dama duk Juma 鈥檃 h tana" "bada sadaqar naman saniya, da ake kayarwa a rabawa mabuqata na Kofar Jange, ranar da Uncle Usman ya tabbatar mata sun dauro auren suna kan hanyar dawowa Shanu uku ta sa aka kayar don yin sadaqah." "Nene Balki da Yafendo kuwa suna can suna yi wa Rahinah kyakkyawan shiri irin na iyayen kwarai masu shirin kai 鈥榶 ar fari daki, Nene tayi ordern kayan gyaran mata 鈥榶 an gaske tafiyayyu tun daga Nijar. Ta kuma yi Magana da Yagana 鈥榶 ar Maiduguri mai yi mata gyaran jiki kan ta zo a washegari ta fara gyara Rahinah." "Sahura mai aikin Rahinah tana Kaduna, da Anty Badiya ta yi mata waya ta ce su fara shirin tarewa har rawa sai da ta taka. Don haka duk wani masoyin su cikin farin ciki yake, ya kuma ci wa auren nan alwashi da buri sabanin ma鈥檃 uratan, wadanda ke ganin tamkar Alkiyamar su ta matso." "Kowanne gani yake an katse masa rayuwa an kuma hada shi da alaqaqai, tunda kar ce ta san kar, kowanne da irin alwashin da yake ci wa zuciyar sa a kan dan uwan sa." "Shi dai Habibu alwashi ya ci ba zai bari Rahinah ta shiga tsakanin sa da dan sa ba, tunda tare ta gan su, ta sake kutsowa cikin rayuwar su don ta kara tarwatsa ta." "Ita kuwa Rahinah abu daya ne yake sassauta zuciyar ta in ta tuna yanzu zata samu kusanci da Abdallah. Za ta maida hankalin ta ne kacokam kan cike wawakeken gibin da Habibu ya samar a tsakanin su wanda ta san ba zai yiwu a lokaci guda ba, sai ta yi da gaske wajen kwatowa kan ta soyayyar dan ta, ta cike ratar da Habibu ya janyo a tsakanin su." Wannan shi ne kadai abin da zai zaunar da ita a gidan Habibu Nahuche amma ba Habibu ba; soyayyar dan ta Abdullahi! "Uwa uba farin cikin iyayen ta da kwanciyar hankalin su wato Ambasada da Uncle Usman. Ita kan ta Aunty Badiya Rahinah tana darajja ta, bata jin Habibu ya isa ya farraqa tsakanin su." Domin Badiya ta kaunace ta kauna ta hakika tun kafin ta san alaqar da ke tsakanin su. A lokacin da ta ke neman dangin da za su rungume ta. Don haka ko wanene Habibu ga Badiya alaqar su mai kyau tana nan bazata taba canzawa ba saboda shi. ****** *Na huce* is not free. It's 1000 via 3094856450 Sumayyah Kabara Firstbank Shaidar biya 07030137870 PAID BOOK "Tunda ta soma maganganun nata har da kuka ba kalaman nata Habibu Nahuche ke saurare ba, a 鈥檃 h, yanayin" "motsawar dan bakin ta ne cikin tsiwa jazir da shi (pink lips), lookingkissable, shi yake ta kallo, yana tuna wani lokaci can da ya shude a Jamus, a cikin motar sa a lokacin da take da cikin Abdallah da ya sato ta daga Library, abinda ya faru cikin motar wanda har abada bazai gushe daga zuciyar sa ba." "Wannan tunanin ya tada tsohon kwantaccen tsumi, domin ya tuna masa kowacece Rahinah a kan gadon auren sa. Dadin dadawa kewar shekara goma! Ba wasa bace ga muminin da ya rike kan sa. Su suka hadu suka tado masa wata gigitacciyar sha 鈥檃 wa wadda soyayyar da yake yi wa Rahinah ta jagorance ta, suka mantar da shi cewa fada su ke yi, sabani ne mai girma a tsakanin su." "All of a sudden idanun sa suka lumshe a cikin kallon ta, hannayen sa kuma suka kai kan su gare ta suka zagaye ta. Rahinah sai jin ta tayi bakidaya kwance lamau a jikin Habib. Wani al 鈥檃 mari tamkar haduwar chemistry din gravity ya bakunce su su duka, shock ne na bazata na wata irin sha'awa ya bakunce shi a take." "Wata irin tsuma jikin sa da zuciyar sa suka shiga yi lokacin da ya soma kissing Rahinah, wani irin lafiyayyen kiss, wanda ya gigita Rahinah Omar, ya kuma fidda ta a hayyacin ta nan da nan, (as it happened abruptly) ba tareda ta shirya ko ta yi tsammani ba. Kuma ba tare da ta kawowa ranta hakan zai kara gudana a tsakanin su nan kusa ba." "Ta dade da sanin rana irin wannan na zuwa, tunda auren ne dai suka kara yi, sannan a wannan fannin ba shi da hakuri, amma bata zace ta nan kusa ba, yanayin yanda yake sumbatar ta ya mantar da ita komai da ke tsakanin su. Hatta sunan ta na yanka a wannan lokacin bazata iya tunawa ba." "Ko me Habib Nahuche ya tuna? Sai ya nemi kuzarin jikin sa ya rasa. Yayi maza ya tsayar da sumbar da yake mata tare da janye jikin sa daga gare ta, ya shiga cusa yatsun sa cikin sumar kan sa cikin nadamar abinda ya aikata." "Ya yarda akan Rahinah Omar ba shi yake sarrafa gangar jikin sa ba, yana runtse ido yake fadin," "鈥淚鈥檓 sorry, it wasn 鈥檛 intentional 鈥฀ (kiyi hakuri ban yi da niyya ba)." "He doesn 鈥檛 want to be that abusive husband again, sabon Habibu yayi alkawarin komawa. Wanda ba zai kara forcing matar sa akan shimfidar sa ba. Ya yarda wannan shine deadlymistake din sa a duniya a idon Rahinah wanda ya shiga tsakanin sa da Rahinah Omar. Rahinar da ya tabbatar ba zai iya cikakkar rayuwa ba tare da itaba. Kuskure" "ne wanda ko Rahinah bazata kara son sa a gaba ba a dalilin sa, yana fatan ya gyara shi, yana kokarin ya goge shi daga zuciyar ta yadda ya kamata. Yayi repenting in har za ta bashi dama." "A kan ta bashi da zabin yadda yake so su rayu yanzu, zaman nasu zai kasance ne yadda ta zaba musu." "Rahinah durkushewa ta yi akan kafafunta tana kuka na bakin cikin abinda Habibu yayi mata. Sanda ya bar dakin bata sani ba, ta dai ji lokacin da ya rufo mata kofar silently." "Daga shi har Rahinah haka kowa ya kwana ya kuma wuni a dakin sa sukuku, ba wanda ya fito, ba wanda ya kara shiga dakin dan uwan sa, haka ba wanda ya ci abinci, kowa tasa ta ishe shi. (Jinyar zuciya da ruhi)." "A satin duka ba wanda ya zo musu, sai wayar 鈥榶 an uwa da abokan aikin ta da take ta karba, suna masu tayata murnar aure da suka samu labari ta kafafen yada labarai da jaridu. Jaridar Sabuwar Najeriya cewa ta yi 鈥淔 rom Court Issue to Love Reunion (Habibu Nahuche and Ex-Wife).Sai hoton su itada Habibu wanda ta rasa a ina aka same shi. Duk Safeenah ta turo mata ta waya ta gani." "A ran ta tace 鈥渟 u dai 鈥榶 an jarida akwai tada zaune tsaye, ko wa ya ce musu tun da can soyayya ce tsakanin ta da Habib Nahuche balle yanzu? Me jiya ta yi bare yau?鈥฀" Da daddaren ranar da suka cika sati da tarewa ta kira Aunty Badiya. "Tana jin muryar Badiya na amsawa ta sa kuka, kuka sosai mai cin rai, hankalin Badiya ya tashi, ta shiga tambaya 鈥渓 afiya Rahinah? Me ya faru? Habibu ne ko?鈥฀" "Cikin kuka ta ce 鈥淎 unty tunda na zo gidan ban ga Abdallah ba, Anty bazan iya zaman gidan babu shi ba, kin dai san komai, saboda shi na yarda na dawo 鈥฀." "Aunty Badiya ta nisa, cikin lallashi ta ce ki yi hakuri Rahinah, ki rabu da shi ki nuna baki damu ba, ya dauke shi ne don ki damu, wallahi ko ni ban san inda ya kai shi ba, amma na tabbata yana lafiya kuma yana kula da shi har fiye da yadda yake kula da Hotels din sa. Da za ki kwantar da hankalin ki ku zauna lafiya Habibu ya fi ruwan sha saukin sha 鈥฀." "Haka Aunty ta yi ta lallashin ta, a karshe ganin Rahinah ta ki daina kukan ta ce za ta sa Hajiyar su ta shiga maganar, ya dauko shi daga duk inda ya kai shi ya kawo mata shi." "Wayar mahaifiyar sa Hajiya Kaltume ta same shi a washegari, yana kwance a daki ya kasa ko zuwa kofar daki, don kada yayi kacibus da Rahinah cikin gidan. Ya yarda in har zai ke ganin Rahinah to kuwa burin sa na son zama SABON HABIBU ba zai taba cika ba, ba zai iya sarrafa kan sa ba dole ya kai kansa gare ta in one way or the other. Baya so ya kara lalata komai, zai daure, zai cije by becoming achangedperson, har zuwa ranar da Rahinah zata nemi wannnan don kan ta. Amma anya hakan mai yuwuwa ne daga Rahinah Omar? Ko dai mafarki yake yi? Rahinah ce watarana zata nemi wannan daga gare shi? Ashe kuwa ranar za'ayi ruwa har da kankara. Abin yi guda daya ne, shine ya kaurace mata ya nisance ta har sai ta nemeshi don kan ta." "Sai kawai ya tashi ya hau tattara abubuwan bukatar sa, da nufin booking din jirgi a yau ya koma Lagos. Sai kuma ga wayar Hajiya ta shigo." "鈥淗 abibullahi ina fatan kuna lafiya"", Hajiya ta tambaya da muryar uwa, 鈥渓 afiya muke cikin alkhairi Hajiya ta 鈥฀ Hajiya Kaltume tace 鈥渢 o bisa umarni na ba neman jin ba 鈥檃 si ko naka ra 鈥檃 yin ba, ko wata tashin tashina, ka je ka dauko Abdallah daga inda duk ka boyeshi, ka kawowa uwar sa." "Habibullahi ina jiye maka kada hakkin su ya kama ka, tana da hakki babba a kan sa, har fiye da kai. Shekaru goma ka raba ta da danta bata san komai a kan sa ba balle halayen sa da irin tarbiyyar sa, ta dawo gidan ta don ta samu kusanci da dan ta amma ka dauke shi wannan ya zama mugunta." Bana so Allah ya kama ka da hakkin wani ko wane iri balle hakkin iyalin ka 鈥฀. "Murya can kasa Habibu ya amsa da 鈥淚 nsha Allahu Hajiya ta zan dawo mata da shi, makarantar kwana na kai shi a Lagos 鈥฀." "Hajiya ta ce 鈥淎 bdallah yayi kankanta da makarantar kwana, kuma ya gaya maka ba ya so, kusanci da uwa yake bukata ba makarantar kwana ba, da saka idanun ta akan tarbiyyar sa a wadannan shekarun na rayuwar sa, kai dai kawai ka ce ka so yin mugunta ne shi yasa ka dauke shi amma in banda haka ko zaka kai shi makarantar kwana ai ka bari ya isa shiga babbar sakandire""." """Insha Allahu Hajiyata zan cika umarnin ki""" """madallah, ko kai fa, Allah ya karawa rayuwa, iyali da nema albarka""." "Sai da ya kammala shirin sa na tafiya tsaf, yayi booking jirgi online, ya yi matukar kyau cikin wani tsadadden yadi filtex mai hasken sararin samaniya, ya fito a handsome Habeebun sa, dan Nahuche jikan Nahuche, shalelen Hajiya da Aunty Badiya, sanan ya rufo kofar dakin sa zuwa dakin Rahinah don yi mata sallama irin wacce addini ya rataya a wuyan sa." "Sallahr walha ya iske tana yi, bai zauna mata a daki ba, daga tsaye ya tsaya yana karewa komai na dakin kallo yana mamakin yadda iyayen ta suka shirya mata shi gwanin ban sha'awa, har ta idar da sallahr. Jikin ta ne da numfashin ta suka bata yana cikin dakin a tsaye sabida yadda atmosphere na dakin bakidaya ya canza da sassanyar kamshin Carolina Herrera wanda shi ke fallasa shi a koyaushe, hannayen sa biyu zube cikin aljihu ya taka sannu a hankali zuwa gaban ta, da ya tabbatar ta yi sallama." """Shin Rahinah me ag-gamin ki da Da na ne? Ni ban taba jin inda akke son Da haka amma ba'a son uban sa ba, Dan da kinka jawo anka kussa sheganta min a media sabida rashin hankalin ki da rashin tunani, yanzu kuma kin kai kara ta wajjen Uwata kan dole sai nak kawo miki shi, me zaki masa Me zaki bashi wanda Allah bai masa ba bai kuma bashi ba tsayin shekarun da yayi ba tare da keba?" "Rahinah sai ta rasa amsar da za tabashi, ita kanta ta yi nadamar shigar da kara kotu daga lokacin da ake tantamar halarcin dan su, da ta san abinda hakan zai haifar kenan da ko kusa bata fara ba, it became something that they are all bitter about (wato wani abu ne da ya zo su duka biyun ya musu ciwo) amma yanzu ba rigima da Habibu ce a gaban ta ba, yadda za ta samar da kyakkyawar dangantaka ta mu'amala da soyayya tsakanin ta da Abdallah shine a gaban ta, yana da damar fadin duk abinda yake so bazata tanka ba, in dai a karshe zata yi winning ya dawo mata da Abdallah. ""Alright, kin ci darajar masu daraja (Hajiya da Badiya) Abdallah zai dawo. Amma bayan na gama gaya masa how cruel his mother is, how selfish sheis da ta zabi boko akan rayuwa da shi da uban sa." "Sai bayan ta gama watangaririyar ta a boko ne ta san da shi, ta zo da mayaudariyar soyayya a gare shi don ta shiga tsakanina da shi kamar yadda ta shiga tsakanina da farin ciki na na baya." "Sai in ce mu je zuwa Dr. Rahinah tsakanin ni da ke yaron da kan sa zai gane wa ke son sa da gaskiya. Ni dai na san ba ka taba son Dan da ka san ba ka son uban sa kaddara ce ta samar da shi a tsakanin ku. Sabida su 'ya 'yan da aka haifa ta hanyar soyayya daban suke""." "A wannan karon ma bata tanka masa ba, domin yau azumin magana ta ke yi in dai da Habibu ne. Ya gama fadin duk bakaken maganganun sa tana jin sa bata ko tada kai ta dube shi ba, ta lura kallon bakin ta yana motsi ko yana magana yana da tasiri sosai a kan sa." "Ita kuma bata zo gidan nan don sake zama abar hutawar sa ba, ko sex toy din sa kamar baya, ko kissing utensil din sa, ko matar sa, ko partner din sa a komai ba, sai don gyara tsakanin ta da dan ta, da nemowa kan ta soyayyar Abdallah da ta rasa shekara goma. Don haka shi yanzu ta dauke shi ta ajiye shi a gefe, ya gama duk bakaken maganganun shi ya kara gaba in dai a karshe Abdallahnta zai dawo gidan." "Haka ya karaci mitar sa ya gaji ya tafi, sosai ya so ta tanka din don ya samu damar sumbatar ta ko yaya ne, kamar ta san kudirin sa da abinda yake yi mawa sai bata tanka din ba har ya fice." Tana kallo ya aje mata ATM card tareda rubuta pinnumbers din a jikin complimentary card din sa mai dauke da dukkan lambobin wayoyin sa ya ajiye mata sannan ya juya yana fadin. """Gara in bar miki gidan ki, kafin kuma ki yi waya ki ce da Hajiya na yi raping din ki""." "Da ta tabbbatar sun shiga mota sun bar gidan shi da PA din sa da wasu daga ma 鈥檃 ikatan sa da suka zo tafiya da shi filin jirgi, ji tayi kamar an zare mata kaya a kafa, kamar an raba ta da dutsen da ya danne mata zuciya, sai ta mike ta shiga sha'anin ta cikin gidan." "Da farko kicin ta shiga ta shirya cefanen kayan abinci a inda take son kowanne ya kasance, sannan ta dafa noodles, da ruwan blacktea, ta zauna akan island din kicin din tana ci, da ta gama ta fito zuwa upstairs wato inda dakunan barcin su yake, dakin da ke tsakiyar nata da nashi ta bude domin mukullin yana jikin kofar, nan ta kara sakankancewa da kaunar da Habibu yake yi wa dan sa Abdallah." "Komai da ke cikin dakin (light blue and yellow) ne, ga gadon yara yan shekara sha biyu haka zuwa kasa mai gadon sama da na kasa, an kawata dakin da duk abinda yaro mai wadannan shekarun zai bukata, a gefe ga study- table na yara wanda aka jera masa littafai kala kala akai na daidai shekarun sa. Ga Alqur'ani mai hizfi dai - dai zuwa goma mai manyan rubutun hafsu, na'ura mai kwakwalwa ta yara bisa tebirin ta. Da kuwa ta bude wardrobe din dakin sai da ta ajiye ajiyar zuciya." "Sittirun sa ne dankare a ciki rukuni rukuni, bangaren dinkakku (traditional attire) daban haka na englishwears shima daban, ga takalma kala kala an jera masa a shoerack din sa." """Abdallah dan gata!""." "Ta fada a ran ta, sai ta ji duk damuwar ta ga son dawowar sa cikin gidan ta karu, da gaske uban sa ya gama saye shi da kowacce kalar kauna, duk wanda zai zo da wata kaunar daga baya sai dai ya bi bayan sa kamar yadda ya ce." "Amma zata yi kokarin ganin cewa ya gane ba rashin kauna ya sa ta bar shi ba. Har karatun nata ta jingine na shekara guda don ta kula da shi (in his first year of life). Yaudarar ta yayi ya dauke mata shi, ita kuma ta yi zuciya ta bar masa." "Amma daga sanda ta sake ganin shi ai bata sake nutsuwa ba, bata sake komawa cikin hayyacin ta ba sai tunanin ta hanyar da za ta dawo da shi gareta, wanda shine sanadin dawowar ta gidan su a yanzu." "Kasa fita tayi daga dakin Abdallah a ranar kusan a dakin ta wuni don yana da toilet din sa karami makale da dakin, har sallolin ta na farillah na ranar a kan dardumarsa ta yi." ****** D "a Habibu ya sauka a Lagos al'amuran gabansa ya shiga, sai bayan sati biyu ya je makarantar su Abdallah ya bada hakuri kan cewa zai cire yaron kasancewar Kakar sa bata amince ba." "Malaman British International School basu ji dadin tafiyar Abdallah Nahuche ba domin a yan satittikan da yayi tare dasu hikimar sa da hazakarsa sun fito fili, yaro ne mai kokari don haka yake da shiga ran malamai gashi da bin maganar malaman sa don Badiyya ta tsaya sosai akan tarbiyyar yaranta ciki har da Abdallah." "Amma shi ko da aka ce masa Daddynsa ya zo tafiya dashi murna yayi ta yi, don dama bai son makarantar kwanan." "Duk inda Habib yasa kafa suna tare a Ikkon tsayin sati guda. Yana gudanar da harkokin business din sa na hotels yadda ya saba, in suna gida kuma musamman lokacin da zasu kwanta barci sai ya dinga sako masa zancen mahaifiyar sa, sai dai kamar yadda ya alkawarta mata, ba alkhairi yake gayawa yaron a kan ta ba." "鈥淎 bdallah wannan Antin ta dawo gidan mu fa, tana Abuja, Hajiyar Nahuche Ta ce in kai ka wajen ta 鈥฀.鈥淲 ace Antin Daddy?鈥฀" "鈥淲 adda ka gani a gidan Mummy, ka dame ni kana son sake ganin ta 鈥฀." Yaron ya fadada far 鈥檃 r sa 鈥渁 i kuwa I like her 鈥฀. Cikin takaici Habibu ya ce. 鈥淎 bdallah za ka so wanda ba ya son Baban ka?鈥฀ 鈥淜 amar yaya bata son Baba na?鈥฀ "Habibu ya mike zaune, shima yaron sai ya tashi daga kwancen da yake. Seriously yake kallon yaron sannan with a serious tone yake magana." "鈥淣 a yi alkawarin gaya maka ko wacece ita, idan ka yi alkawarin bazaka zabe ta akai na ba 鈥฀.鈥淣 a yi alkawari Daddy, ta yaya zan zabe ta a kan ka?鈥฀" 鈥淪 aboda MAHAIFIYAR KA ce!鈥฀. "Shiru mai yawa ta ratsa tsakanin uban da dan. Dan na kokarin 鈥榙 igesting 鈥฀ maganar uban yadda zai fahimce ta cikin dan kankanin tunanin sa, domin ta yi masa girman da ta gagare shi ganewa." "鈥淒 adday, ina da wata uwa bayan Mummy ne? (Badiya)鈥฀ yaron ya tambaya cikin karyewar murya. Bai bata lokaci ba ya amsa masa." "鈥淢 ummy su Musaddiq ta Haifa, Yaya ta ce, uwa daya uba daya, ita kuma wannan din ita ta haife ka a Jamus mun je karatu muka yi aure. Amma wallahi bata son mu, tunda ta iya barin mu shekaru goma, muna watangaririya da ragaita cikin maraicin ta, bata taba neman mu ba." "Da wannan nake gaya maka ko mun koma gidan ba ruwan ka da ita, ko me zata yi maka kada ka yarda da ita, bata zo don ta zauna da mu har abada ba, sai don ta kwace ka dagahannu na ta kara gaba." "Imagine Abdallah har kotu ta kai ni, don a kwace ka daga hannu na a bata. Wannan abun ya mun ciwo, it really hurts me!鈥฀." "Haka yayi ta turawa yaron negative thoughts a kan mahaifiyar sa Rahinah, of course ya san abun da yake yi dinnan ba daidai bane, bai kuma kamata ba, ba 鈥檃 raba hanta da jini, amma ta wannan hanyar kadai zai bi ya rama bakin cikin da Rahinah Omar ta cusa masa ya rayu da shi tsayin shekaru goma, tunda ya bayyana gare shi ba abinda ta ke so ta rayu da shi a halin yanzu sai Abdallah, kamar yadda shima a wancan lokacin ba abinda yake so ya rayu da shi sai ita, bata duba Abdallahn ba, a wancan lokacin da suka fi bukatar ta, ta ajiye kowanne laifi ta ke ikirarin yayi mata, ta sadaukar da nata farin cikin da burukan don ta rayu da dan ta???" Sai yanzu da dan ya zama gotai-gotai da shi karkashin tashi kulawar da nashi tashi-fadin shi kadai? A duniya akwai mai SON KAI (sunan littafin TAKORI mai zuwa) irin Rahinah Omar?鈥฀ "Gabadaya ya rikita yaron ya hargitsa masa tunani akan mahaifiyar sa Rahinah, ta yadda yaron ya koma ganin ta da wata fuska ta daban, tun kafin ya ganta." A washegari suka bi jirgi mai zuwa Abuja. ***** Y "au tunda ta tashi da kewar komawa aiki ta tashi, duk da cewa sun kara mata kwanakin hutun a matsayin hutun aure da na karshen shekara, amma kadaici yayi mata yawan da take bukatar zuwa asibiti. To amma ya kyautu ne ta fita" "batare da sanin sa ba? Da da yanzu akwai banbanci, duk da takun sakar da ke tsakanin su, bazata so fitaba da iznin sa ba." "A bisa rashin sanin ta a lokacin ma su tuni sun sauka a Abuja, suna cikin mota sun taho zuwa 鈥楲 ife 鈥฀" Camp 鈥฀ daga filin jirgi. "Kamar daga sama ya ga kira daga bakuwar lambar da bai yi saving ba tun a wancan lokacin da ta fara kiran sa, amma ga mamakin sa duk da bai yi saving ba lambar ta dade da zama a cikin kan sa." "Cikin ginshira da shariya yaki dagawa, ya sake kishingida a kujerar sa, cike da mamakin yau Rahinah ta kira shi ai kuwa za 鈥檃 yi ruwa har da kankara, koda yake ita kiran ta ba alkhairi bane don kuwa ta riga ta zame masa tauraruwa mai wutsiya ganin ki ba alheri ba. Ko dai tata ce ta kawo ta, ko ta kira don ta gaya masa bakar Magana, ba kuma ya so ta san sun taho sai dai kawai ta ga Abdallahn." Da ta tabbatar ba zai daga kiran ta ba sai ta daure ta tura masa gajeren sako (text). 鈥淶 an shiga NIZAMIYE 鈥฀..鈥฀. "Ji ya yi tamkar ta caka masa mashi a kahon zuci da ya tuna a NIZAMIYE din nan wanda ta kira da Dr. Irshad yake, kuma he 鈥檚 ahead of her a mukamin aiki." "Bai san sanda hannun sa ya bi bayan kiran nata ba, ita kuma bata bata lokaci ba ta daga, don ta gama shiryawa tsaf hatta labcoat din ta na rataye a hannun ta." "Muryar da ke kassara ta a kullum sabida coolness din ta da zurfin ta, ta kwararo cikin kunnnuwan ta babu ko sallama." "鈥淜 i rubuta resignation letter ki kai musu ki dawo, ina jiran ki 鈥฀." "Rahinah ta kankance ido ta rasa mezata ce, sakamakon wani irin bacin rai da ya yunkuro mata." 鈥淢 e kake nufi?鈥฀ 鈥淚 na ce da Hausa nayi Magana? Ko sai nayi da Jamusanci?鈥฀ "Rahinah ta cizge mini hijab din ta ta ajiye, sakamakon jin gumi ya yanko mata, ta bar aiki fa ya ce, a sanin ta he 鈥檚 frank and straight forward baya fadin abinda ba haka yake a zuciyar sa ba, kuma baya wasa da furucin sa." "鈥淜 in gama aiki a Nizamiye, daga ranar da kika yi kuskuren sake amsa sunan MATAR HABIBU NAHUCHE, shima na gwamnatin ina tantamar cigaba da yin sa, zan iya biyan su scholarship din da suka biya miki, ki zauna ki yi bautar aure da kula da yara kamar kowacce mace." "Ba kin ce don ki kula da danki kika dawo ba? To gashi nan na kawo miki. Sai ki zaba ko shi ko aiki, don ni ba na barin da na a hannun 鈥榶 an aiki. I come in peace!鈥฀." Yana gama fadin hakan ya kashe wayar sa. Ya yi daidai da jin dirin shigowar motoci da ta yi harabar gidan. Da sauri ta karasa ta daga labule bayan ta wancakalar da lab-coat din ta. Kamar ta yi hauka sabida yau ta kara tabbatarwa Habibu Nahuche ya fi ta iya mugunta. Ta hango su shi da ABDALLAH suna fitowa daga mota..... "The tall, slim, chocolate complexioned boy, Abdallah Nahuche, looking so handsome and obviously cheerful like the replica of his father. Ya kara tsayi da kyau gwanin sha 鈥檃 wa da shi har fiye da ganin farko da ta yi masa bayan wucewar shekaru goma." "Fatar jikin sa lub-lub a kwance kamar ba girman kasar nan ba, kamar yadda sumar kansa ta ke kwance lub-lub itama ba tare da aski ko saisaye ba, daga gani tana samun kula ta musamman da tsadadden mai na gashin maza Arganavita, gashinan dai exactly yadda Habibu ke barin nasa gashin kan ba aski ba saisaye sai taza. Ita a rayuwar ta bata taba ganin kamanni na kwabo da kwabo irin na Habibu Nahuche da dan sa Abdallah ba." "Babu ko digo nata da Abdallah ya dauko banda almond shaped eyes din ta, wadanda suka taimaka wajen karawa yaron cikar halitta da cikar zati." "Ta saki labulen a hankali jin takun su suna hawowa upstairs din a tare, da taku na energy wato na sassarfar tafiya cikin koshin lafiya da kuzari, suna tafe suna hira har da dariya cikin nishadi irin na Da da mahaifi, kai da ganin su ka san basu da sauran matsala a rayuwa, hannun su makale cikin na juna kamar abokai ko Wa da kani. Dukkan su sanye da (Black-Grey German Suit) wadda ta dace da launin fatar jikin su mai salki da sheki." "Tsigar jikin ta ta ji ta soma tashi da jin sautin muryar ABDALLAH NAHUCHE, wadda ke tsirgawa tana ratsawa tana shiga cikin kunnen ta har zuwa cikin brain din ta, tana hudo wani irin sabon son Dan ta da kaunar sa a zuciyar ta, cikin wani yanayi na soyayyar uwa da bazai fassaru ba, irin feeling din da uwa kadai ke iya jin sa a kan Dan ta" kwatankwacin koma fiye da na ranar da ta kawo shi duniya tana kwance kane-kane cikin halin nakuda a kan cinyar Habibu Nahuche. NA HUCE is not for free. It's 1000 via 3094856450 Sumayyah Kabara Firstbank "A hankali ya sunkuyar da kai, kafin ya dago ya dubi Yayar sa da mijin ta." "鈥淜 u yi min alfarma ku ci abinci ku yi sallah ku natsa 鈥฀ yace da su finallycikin muryar sanyi, bayan ya dawo daga duniyar tunanin da ya lula, daga Aunty har Uncle basu katse masa hanzari ba sun bashi dama yayi tunanin sa positively." 鈥淏 a zan iya cin wani abinci ba sai ka tabbatar min zaka bi mu zuwa Girei Habibu 鈥฀. Inji Badiya. "A hankali ya gyada mata kai alamar zai bi sun. Uncle ya ce, 鈥渢 o alhamdulillahi, ina Abdallah? Cikin kunkuni ya ce." 鈥淏 a zan gaya muku inda yake yanzu ba don ban shirya ba da shi ga uwar shi ba 鈥฀. "Dariya Aunty ta yi, sabida farin cikin ya yarda zai bi su zuwa Girei kadai ya karbi auren sa da kan sa ya wadatar da ran ta." "鈥淐 an ta matse muku, a bamu masauki mu je mu huta 鈥฀. Inji Aunty." "Waya yayi wa mai kula da share-sharen gidan ya zo ya tafi dasu sassan baki, Kuku kuma tuni ya shirya musu abinci ya kai, ya san ba wanda zai yi masa wannnan karambanin na kawo su Anty Ikoyi sai Mr. Rasak." "Amma bai ce masa komai ba don shima yanzu ya ji dadin zuwan nasu, domin ya yaye masa damuwar da yake ciki kaso tamanin cikin dari 80%. Kuma shine babbar maslaha ga mutuncin sa aidanun iyayen Rahinah, dama ita Rahinar kan ta." "Ba wai sulhu yake nema da ita ba, illa shi mutum ne mai yawan submissiveness, wanda idan yayi laifi ya kuma gane daga baya yayi laifin, ko aka nusar da shi, yake gaggawar mika wuya nan da nan ga gyara wannan laifin." "Sun tattauna sosai a daren shi da 鈥榶 ar uwar sa. Duk abinda suka kashe ita da Hajiya da Uncle da su Baban Nahuche wajen hidimar auren sai da ta kwashe ta labarta masa, don ya san ba a banza ya samu Rahinah ba wannan karon." "Tace atampopin 鈥榮 uddaje 鈥฀ kawai daga Super sai Holland muka zuba, sauran da suke kanana 鈥榶 an uwa ne suka baka gudummuwar su har da Shafa 鈥檃 tu""." "He felt loved! Sabida ko kana da shi, idan 鈥榶 an uwan ka da iyayen ka suka yi maka aikin zumunci da kara irin wannan dadi ka ke ji. Ya ce da Anty zai maida mata kudin kayan suddaje din da na lefe cikin account din ta, Aunty ta harare shi nan ta hau shi da fada, inda ta ce," "鈥渒 a ji min yaro, lefe ai gudummuwata ne dama, suddaje gudumuwar Hajiya, Paute gudummuwa ne daga gare mu zuwa ga zuri'an amarya, sauran hidimdimun kuwa duk daga 鈥榶 an uwa na Nahuche suka fito, fatan mu Habibu kada ka bamu kunya, ka zauna lafiya da uwar dan ka, domin dukkan ku kuna bukatar juna 鈥฀." "Bai ce komai ba, domin duk jikin sa ya yi sanyi, sai ya samu kan sa yana mai tambayar kan sa da gaske yana bukatar Rahinah Omar cikin rayuwar sa ta yanzu ko kuwa Anty ta dai fada ne don ta ji dadin bakin ta???" "Daga can kasan ransa sai ya ji wani sako na amsawa da cewa ""YES! Har gobe yana bukatar Rahinah Omar cikin rayuwar sa. Irin bukatar da nisan shekaru ko tsufa ba ya taba canza ta." "Iyayen sa da 鈥榶 an uwan sa basa bukatar komai daga gare shi duk da Allah ya bashi wadata, burin su kadai ya zama cikakken mutum ta hanyar yin aure da wadda suka tabbatar ita kadai yake so." "Ko don albarkacin Hajiya, Yayar sa Badiya da Uncle Usman zai sassautawa zuciyar shi, zai karbi Rahinah da duk irin fuskar da ta zo masa; da tsiya ko da arziki. Wato duk irin rayuwar da ta zaba musu ita za su gudanar." Aunty ce ta katse masa tunani da cewa 鈥渋 n aka zaba mata ta zauna?鈥฀ "Ya dan zakuda kafada yace 鈥淚 have no idea. The choice is her 鈥檚 (wato zabin nata ne). Tunda ni ba mazauni bane na wuri guda ba 鈥฀, Aunty ta ce," "鈥渘 a san ma Abuja za ta zaba, ko don saboda ayyukan ta 鈥฀. Dan kyabe baki yayi irin na ba matsalar sa bane wannan." "A daren yayi musu booking din jirgin da zai juya da su Adamawa a washegari har da Mr. Rasak wanda ya nemi alfarmar halartar auren Ogan su, don Aunty ta gaya masa tun jiya da ya dauko su." 鈥淗 alan bai gaya muku cewa shi ango bane ko? Maman Abdallah za ta dawo!鈥฀. "鈥淐 ongratulations Oga, congratulations Boss!鈥฀ Inji duka ma 鈥檃 ikatan gidan." """May yours be among the best!""." "Kowa sai da ya fadi irin fatan alkhairin sa, domin hakika sun yi farin ciki. Washegari tun sassafe gabadayan su suka biyo Arik-Airdaga Ikko zuwa Adamawa." ****** "ADAMAWA, GIREI A" "saukar sa a Adamawa, ba abinda ya fara zuwa ran sa illa, da ya samu nutsuwa abu na gaba da zai sa a gaba shine zai samar da Nahuche Hotel a jihar Adamawa, tunda Adamawan ta zama wani bangare nasa yanzu." "Ita ce tushen mahaifiyar Abdallah kuma garin kakannin sa na wurin uwa, ko don su samu wurin sauka idan suka zo garin. Ilyasu Uncle ya yiwa waya, ya dauko motar sa da ya bari a Girei ya zo ya dauke su zuwa Girei. Basu tsaya a ko 鈥檌 na ba sai kofar familyhouse din su Rahinah, wato gidan Sarkin Fulani." "Tuni labari ya riski jama 鈥檃 r gidan, da ma ita Rahinar kan ta, cewa Angon Rahinah ya iso daga Lagos. Safeenah ce ta shigo mata da wannan labarin, wanda ya sa ta saurin runtse idon ta a ahankali tana ambaton sunan Allah. Ba don ta yi farin ciki da zuwan nasa ba sai don faduwar gaban da ta bakunce ta." Tana so ta tambayi Saffeenah ko tare da yaro Abdallah suka zo? Sai dai ta daure ta yi fulako ta yi shiru. "Yau wace rana ta gwada kawaici akan Abdallah. For the first time a tarihin rayuwar su da ta ji zuciyar ta ta dan rankwafa akan Habibu Nahuche, tunda dai har ya sauke girman kan sa ya biyo ta garin iyayen ta." ***** S "ai biki ya koma sabo dal sakamakon zuwan Angon. Dan Nahuche jikan Nahuche. Habib, Mustapha, Bilyamin Nahuche. Biki yayi biki, biki irin na fulanin Girei wadanda suka hade da Zamfarawa suna nuna musu irin nasu culturesandtraditions din, wannan ya sa mutanen Nahuche suka dauki aniyar in suka dau amarya zuwa Zamfara sai sun kai ta har garin Nahuche ta gaida Kekun Nahuche da Uban Dawakin Nahuche suma su nuna irin nasu al 鈥檃 dun. Tunda burin iyayen Rahinah shi ne su nuna ita 鈥榶 ar asali ce 鈥榶 ar dangi ce suma dole su nuna Habibu dan asali ne dan dangi ne, ba 鈥檃 fi su jela ba baza 鈥檃 fi su iya taka rawa ba, kamar yadda ba 鈥檃 fi su kwarkwata ba baza 鈥檃 fi su iya susa ba." "Allah kadai ya san irin farin cikin da duk family din nan ke ciki na kowanne bangare. Habibu kuma da zuwan sa ya bude bakin aljihu ga dangin amarya da iyayen ta, komai sai da aka sauke mota guda tun daga kan ruwan sha. Lemo kuwa kamar a wanke gidan sarkin Fulani da shi. Kaji da zabbi kamar a tuka a yi tuwon su. Mutanen Girei sun dade basu ga biki irin na Rahinah ba, gashi dai a al 鈥檃 dance aka yi komai babu surkin modernity, amma komai ya wadata sannan tun daga fara bikin har zuwa karshen sa traditionalattire wato kayan saki na gargajiya Rahinah ke sawa irin na Fulanin usli, wadanda cousins din ta 鈥檡 ammata sa 鈥檃 nnin ta suka kakkawo mata matsayin gudummuwar su." "Habibu da Rahinah basu hadu ba ko sau daya a garin Girei, sai ana I gobe za su wuce Zamfara. Aunty Badiya ta yi kokarin su hadu, ko sau daya ne su gaisa a Girei, kowanne ya nuna mata ba ya bukatar hakan." "Yau kuma da suka hadun, Sarkin Fulani ne ya kira kowannen su da kan sa zuwa turakar sa, kusan a tare suka iso, Rahinah ta sha ado, sanye da wata guntuwar rigar Karen miski ruwan hanta, ta yi dauren zanin daga can saman cikin ta ta yi lullubi da yalwataccen mayafi fari, an yi mata wadansu irin kananan kitso wadanda aka lankwaso jelar su ta gaban goshin ta zuwa bayan kunnen ta, kitson ya saka fuskar ta tayi fresh tayi cute da ita ya fito da kyawun fuskar ta na halitta. Kan ta babu kallabi sai lullubin babban mayafin da ta yi." "Habibu sanye yake da yadin voyel mai taushi fari sol, da gani yau ya soma saka su, 鈥榶 ar ciki da babban riga wanda aka yi wa sassaukan aiki da farin zare. Komi nasa a saukake, kwalliyar sa mai sanyaya idanu, amma kallo daya zaka yi masa ka san ya kama kasa, kuma komai da yake sanye da shi mai daraja ne. Sassaukar rayuwa ra 鈥檃 yin sa ce kawai amma kada kaso ka tona tsadar sittiru da takalmin da agogon da ke jikin sa." "Tana saka kai a kofar dakin sarkin Fulani shima yana sawo kai, saura kadan su yi karo da juna, itace ta yi saurin ja da baya ta bashi hanya ya fara wucewa bayan sun jefi juna da mummunan kallon da kowanne ya kunshe cikin idanun sa." "A ran ta ta ce 鈥渦 mh, mutum har mutum, fuska da zubi irin na salihai amma halin sa da zuciyar sa irin na mutanen farko (jahiliyya period)." "Shi kuwa Habibu gani yayi gabadaya Rahinah ta canza a idanun sa, kuruciya ta karu mata, duk ta danyance masa kai bazaka ce ta taba haihuwa ba, balle katon yaro kamar Abdallah mai neman cika shekaru goma sha biyu." "Kwatankwacin abinda ta fada a tata zuciyar shima haka ya fada a nasa ran, kamannin ta, innocent fuskar ta, zubin halittar ta duk basu yi kama da behaviours din ta na rashin tausayi ga mijin auren ta, na rashin compassion a zuciya da rashin karbar kaddara." "Ta fi kama da salihan mata masu sanyin rai, masu tausayawa da tallafawa mijin auren su, ba kamar nata halayen na zahiri ba. Ga ta stubborn ga ta unforgiving and wicked." "鈥淜 u shigo daga ciki 鈥฀ inji sarkin Fulani, suka zauna suna fuskantar sa shi yana daga gaban su, sai da ya tabbatar sun bashi dukkannin nutsuwar su sannan ya fara da addu 鈥檃 suka shafa, kafin ya maida hanklin sa kan Habibu Nahuche." "鈥淒 uk abinda ya faru da ku a baya, mun ji labarin sa, Ambasada ya gaya mana. Ina so ku dauka kaddarar ku kenan ta haihuwar wannan yaron, don haka ku maida komai ya zama tarihi, ku fusknci rayuwar da zaku fara yanzu." "Habibullahi na aika an kirawo ka ne domin in baka amanar marainiyar Allah RAHINATU wadda Allah ne ya hada ku ba mu muka hada ku ba, bata da uwa bata da uba a duniya sai mu da muka rage a raye, idan ka cutar da ita Allah ba zai barka ba." "Ke kuma Rahin, kin gama sanin gidan nan ba 鈥檃 yaji, ba 鈥檃 kawo kara, sannan ba 鈥檃 zawarci. Don haka ne ma bana gaggawar aurar da 鈥榶 a 鈥檡 a na sai ga mazan da na tabbatar suna son su kuma zasu rike min amanar su ko bayan rai na. Sannan ya zamanto cewa soyayya ta hada su ba tursasawa ba." Saboda haka na hore ki da yi wa mijin auren ki biyayya da zama uwa ta gari ga 鈥檡 a 鈥檡 an ki. Mahaifiyar ki matar kwarai ce mutuniyar kirki ce da har ta koma ga mahaliccin ta babu wanda ya taba jin kan su ita da Modibbo Ummaru. "Bai taba kara aure ba sai a bayan ranta, inda ya auri Kulun da ta yi sanadin barin ku gida har duka wadannan kaddarorin suka faru 鈥฀." "Habibu ya muskuta kadan, murya cikin sanyi yace 鈥漺 acece Kulu?鈥฀ Sarkin Fulani ya bashi labarin komai daga farko har karshe har yadda Rahinah ta hadu da su ta sanadin Yafendo, Habibu ya saci kallon ta kadan, (she have never know her parents), sai yaji tausayin ta kadan ya kama shi, gara shi ya girma da Hajiyar sa har gobe yana jin dadin ta, ya dukar da kai yana magana a hankali," "鈥渘 a karbi amanar ka da hannu bibbiyu Baba sarki, Allah ya bani wuyan dauka da hannun saukewa 鈥฀." Kawai sai Rahinah ta ji kuka ya zo mata. Wanda tun fara bikin bata yi shi ba. Don a baya komai ganin sa take kamar almara ko mafarki wanda anjima kadan za ta bude ido ta ga ba haka ba. Amma yanzu da Habibu yayi Magana da bakin sa ta yarda ta amince zahirin kenan. "Ta sake zama matar Hotelier (Habibu Mustapha Bilyamin Nahuche). Bambancin shine wannan auren ba irin na baya bane, wannan auren na mutunci da daraja ne, ya aure ta ne a hannun iyayen ta da kakannin ta, aure na adalci da martaba, to amma anya sauran tabban nasa da lahanin da ya yi wa zuciyar ta zasu taba gogewa daga zuciyar ta?" "鈥淜 u ta shi ku je, suna jiran ku za ku wuce. Allah yayi muku albarka 鈥฀." "Nene Balki da Inna Dudu ne suka shigo dakin sarkin Fulani suka tafi da ita, a motocin Nahuche Hotels zasu wuce zuwa Zamfara wadanda tuni PA Rasak ya sa an kawo su manya-manyan Highlanders har guda 4. Sai wadanda 鈥榶 an Nahuche suka zo a ciki dama ba su koma ba." "Wadanda Mr. Rasak ya kawo matan sarkin Fulani su duka hudun aka dauka a ciki da 鈥榶 a 鈥檡 an su mata, cousins din Rahinah da sauran 鈥榶 an uwan su aka dauka a ciki. Rahinah da Nene da Aunty Badiya da Inna Dudu suna mota guda, a gidan gaban motar kuma matar Baban Nahuche ce haka suka kama hanya daga Girei zuwa Zamfara." "Habibu da PA din sa tare da Uncle da yaran sa suka wuce, suna tafe a hanya yana ta buge bugen waya yana bada order na yadda yake so PA Mr. Atiku ya tsaya a kan gyaran gidan sa na 鈥楲 ife Camp 鈥฀ duk da gidan baya bukatar komai, amma yanzu mace ce zata zauna a cikin sa akwai bukatar abubuwan da babu cikin gidan. Su Uncle kuma sun ce ya basu dakuna zasu zuba kayan gado da kicin zasu zuba mata kayan girki. Yana ta gargadin PA Atiku kan ya tsaya ya ga cewa komai (is in place). Uncle na ta sauraron sa a fakaice yana ta mamaki, in ya ji kudaden da ake ta ciniki na abubuwan da za 鈥檃 sa a cikin gidan. Murmushi yayi, a ran sa ya ce," "鈥渟 annu sannu ai bata hana zuwa saidai a dade ba 鈥檃 je ba, yaro wa ya gaya maka Borno gabas take? Wa ya gaya maka ana yi wa matan gidan mu pretending?" ****** "KOFAR JANGE, ZAMFARA U" "nguwar Kofar Jange ta karbi bakin motocin wajen guda goma a jere da yammaci lis, lokacin da majalisar samarin Kofar Jange ta ke cikke taf! Kamar kullum. Nan da nan samarin masoya Habibu Nahuche suka soma tambayar junan su ko me ake yi? Don kafin isowar motocin wani makwabcin Hajiyar Nahuche ya kawo musu labarin akwai fa kishin-kishin din cewa NAHUCHE ya yi aure duk suka karyata shi, ta yaya zai yi aure bamu ji a media ba? Bayan kwanannan suka gama shari 鈥檃 da tsohuwar matar sa a Abuja?" Sai ga wadannan bakin motocin nata fakewa a kofar 鈥淕 IDAN NAHUCHE 鈥฀. "Mata ne suka rika fitowa kafin su fito da amarya nannade cikin alkyabba, suna shiga gidan Hajiya Kaltume, ai kuwa nan suka gasgata labarin da Kalla ya kawo suka gwale shi, nan wajen ya kaure da sowa da surutun su." "Dai-dai da isowar sa cikin motar karshe, motar Alh. Usman Girei. Suna yin fakin samarin na yanyame motar fadi su ke;" 鈥淎 llah ya bar mana NAHUCHE 鈥฀ 鈥淎 llah ya taimaki NAHUCHE 鈥฀ shi kuma sai murmushin da ya "saba ya ke yi (broad smile) cikin ginshira irin tasa. Ya kawo ihsanin da ya saba yi musu ya yi musu bayan ya basu hannu daya bayan daya, abinda suka samu yau ya zarta na kullum shikan sa bai san dalili ba, don ba zai ce farin ciki yake ba.....addua suka shiga yi a kan auren da suka samu labarin ya yi, tare da roka masa zuri 鈥檃 mai albarka." Wannan daban. Kasancewar Gidan Hajiya Kaltume babban gida ne mai wadatattun dakuna don haka tsaf ya dauke bakin Nahuche da na Girei. Aunty Badiya bata zauna ba suka shiga hidima ta bajinta da surukan su. Sabida yadda gidan ya cika da mata Habibu bai samu ganin Hajiyar sa ba suka wuce Hotel shi da su Uncle da PA Rasak. "Har dakin Haj. Kaltume su Nene suka kawo Rahinah, aka bada amana ta ce Allah ya taya mu riko. Yau ga Hajiya ga Rahinar Habibu! Duk da bata yi nasarar ganin fuskarta ba daga goshin ta da sumar ta ka san kasaitacciyar mace ce dole Habibu ya kasa aure akan wannan bafullatana." "Duk yadda suke boye maganar auren don kada 鈥榶 an jarida su samu a daren ranar ta yadu a garin Zamfara, kasancewar Habibu sananne kuma fitacce wanda kiris a ke jira a kan sa. Washegari bayan kowa ya karya ya kuma kimtsa motocin suka sake kwasar su zuwa Nahuche." "A Nahuche 'yan Girei sun ga karramawa inda aka kai ta gidan su mahaifin sa kowa nasa ya zo ya gan ta, ya sa albarka, kowa sai Masha Allah yake ambato matar Habibu ta kai ta kawo, daga nan suka wuce fadar Nahuche suka gaida Kekun Nahuche wanda amini yake ga Kakan sa Bilyamin Nahuche." Kwanan su daya a Nahuche suka wuce da amarya gidan ta. ****** ABUJA (Life-Camp) G "idan Habibu na nan a sabuwar unguwar Life-Camp wadda ke gaba kadan da Gwarimpa. Madaidaicin gida na zamani zubin (Pent House) mai hawa biyu wato sama da kasa, Habibu ya dauko samfur din sa ne daga kasar Jamus bai jima da kammala ginin sa ba. Ba kasafai yake zama agidan ba idan yana garin Abuja rayuwar sa ta fi yawa a 鈥楴 ahuche Hotel 鈥฀ na garin Abuja. Rahinah could 鈥檛 believe cewa yau ita ce a gidan miji, mijin kuma ba kowa ba face her ex husaband; Baban Abdullahi dan mutanen Nahuche. Wanda ta sha cin alwashin har abada bazata koma masa ba." To an ce kana naka Allah na nasa kuma na san shine gaskiya. Bawa bai isa ya tsarawa kan sa rayuwa yadda yake fatan ta ba. "A yau da ta daga kai ta yi duba ga al 鈥檃 muran duniya bakidaya, sai ta ga cewa (nothing is constant), komai canzawa yake kamar wahainiya, kuma rayuwar kanta garawa take da gudu kamar gare-gare abin wasan yara. To haka al 鈥檃 marin ta da uban dan ta ke nasa juyin cikin hikima da iradar Ubangiji. Yanzu kam ta yarda ta amince a cikin kundin kaddarar su, har da na sake zama da juna." "Abinda bata da idea a kai yanzu shine irin zaman da zai gudana tsakanin ta da Habibu Nahuche. Wani kwayan mutum guda daya da ke ta walagigi da duniyar ta (for almost a decade) tun haduwar ta da shi a jirgi. Har gobe, har jibi har gata zuciyar ta ta ki aminta da shi, ta ki kwanciya da shi a kan nakasu guda daya, a kan laifin baya, ta ki yarda soyayyar sa isgenuinekuma soyayya ce yake mata ta tsakani da Allah." "Kullum da abubuwan da baudaddiyuar zuciyar ta ke gaya mata daban - daban akan sa, wanda laifin sa na farko duk shine sila, mafari kuma tushe na sanya duhun sa a zuciyar ta, duhun da ya lullube soyayyar da ke kwance lambam, ta zabi su kare rayuwar su cikin challenging juna." "Su Nene da sauran 鈥榶 an uwan ta na Girei basu kwana gidan ba duk suka juya gidan Ambasada a daren, inda a can za su kwana, washegari kowa ya koma inda ya fito, cike da farin cikin an yi biki lafiya an kare lafiya." "Ita kadai tsakiyar makeken gadon ta wanda Uncle Usman ya yi mata, ta saka ta kwance, ta kasa kukan da amare suke yi sakamakon rashin nutsuwar da rashin ganin Abdallah har lokacin ya haifar mata." "Abdallahn da ta dawo domin sa, ta yi matukar kokari ta yi fulatanci (alkunya) bata tambayi kowa yaron ba har aka yi biki aka kare daga jama'ar Girei har zuwa na Zamfara zuwa Nahuche bata tambayi kowa ina Abdallah ba, ta dauka da ta zo gidan da shi zata fara tozali, ga 鈥榶 a 鈥檡 an Aunty Badiya babu wanda bata gani ba, kada dai ace tun dauke shin da yayi akan idon ta bai dawo da yaron daga inda ya kai shi ba? To ina ya kai shi?" "Ita ba abun ta dauki waya ta kira Badiya ta tambaya ba, fillancin da ta daure ta yi a baya ya tashi a banza." "Daman dai bata yi tsammanin ganin Habibu ba. Shima kuma koda ya dawo gidan daga gidan Ambasada karfe goma sha dayan dare inda acan ya ci abincin dare bai yi tunanin neman ta ba. To yace mata me? Shekara goma da doriyar watanni masu yawa yayi babu ita cikin rayuwar sa, don haka, a ganin sa, dawowar ta yanzu ba abinda zai kare shi da shi, ba abinda zai sa ba abinda zai hana, ita da babu duk daya." "Data ga barci yaki zuwa alwala tayi, tayi sallolin shafa 鈥檌 da wuturi da bata yi ba, ta zauna bisa darduma tana lazimi, anan barcin gajiya ya sace ta." "Da asubah sautin kira'ar Minshawy da ya karade gidan cikin suratul Dalaq shi ya tashe ta, ta rasa daga ina karatun yake fitowa. Sai ta tashi ta fada toilet tayi wanka da brush ta dauro alwalah sannan ta fito." "Data fito tsayawa tayi tana kallon yanayin tsarin komai na dakin, kyan ginin gidan kadai ya isa, tana mamakin irin dukiyar da ya tara cikin dan lokaci kankani da dawowar sa. Hatta marbles din gidan sa bata taba ganin shi a ko 鈥檌 na ba. Tsaki ta ta yi a fili ta ce." 鈥淎 llah ya sa halal yake ci 鈥฀. "Bayan ta idar da sallolin ta na farillah da na nafila da kayan da ta zo da su tun jiya ajikin ta ta koma gado ta nade cikin duvet, kayan duk sun bi sun dame ta amma ta kasa cire su ta huta don ba ta so ma ta saki jikin ta in ta tuna a gidan Habibu take, tana sauraron karatun da yake ta tashi a gidan, yanzu kuma Suratul Tagabun ake karantawa. Sai ta lumshe ido tana bin kira 鈥檃 r a hankali da fatan barci ya zo ya dauke ta, ko ya mantar da ita a ina take, ko ya maida reality din ya koma mafarki, burin ta a lokacin bai wuce a ce tare da Abdallah take kwance ba tana biya masa wannan karatun, tana yi masa tambabyoyi akan rayuwar sa da bata sani ba, amma barcin kamar ya san neman sa Dr. Rahinah ke yi ruwa a jalloh sai yayi kememe ya yi kemadagas yaki zuwa. Idanun ta dai suna rufe bata bude su ba, tana cigaba da bin karatun cikin Suratul Tagabun." "Ya dawo masallaci ne zai shiga dakin barcin sa ya ji tashin sassanyar muryar ta, tana bin karatun da ya kunna kafin ya fita." "Dakin da aka sauki Rahinah wato bedroom din ta opposite din nasa ne, a kusa da natan na Abdallah ne wanda yasa aka shirya shi da duk wani abun da yaro mai shekarun sa zai bukata, an narkar da dukiya ba kadan ba a dakin Abdallah, katifar sa kadai water mattress ce." "Tsayawa yayi kasake! A kofar dakin sa yana sauraron ta. Bata son abinda zai tuna mata a gidan Habibu take, a gadon auren sa take kwance, don haka karatun ya tafi da bacin ran ta ya wanke wannan damuwar, ya sanya mata nutsuwa da confidence din jin cewa zata iya sake zama da Habib Nahuche, da So ko babu So, Albarkacin Abdallah, dawowar ta gidan sa baya nufin karshen rayuwar ta." "Karatun ta ya mishi dadi ba dan kadan ba domin ya maida gidan lively. Duk da gari bai gama wayewa ba, sai ya tuna jiya bai bata komai ta ci ba, a matsayin ta na bakuwa a gidan sa wadda bata kai ga sanin ko 鈥檌 na na gidan ba, sannan bai duba ta ya ga yadda ta zo ba ko da bazata kula shi ba." "Tun jiya ya sallami kukun sa na gidan, ba zai jure wata mu 鈥檃 mala ko yaya ta shiga tsakanin Rahinah da wani namiji ba bayan su Musaddiq shaqiqan ta, bai san yana da kishi na fitar hankali ba sai ranar da Rahinah ta ambaci ta zabi wani Irshad a kan sa. A daren ranar ya san ba bakaken maganganun Rahinah ne suka hana shi runtsawa ba face wannan subul da bakan da ta yi a gaban sa. Har da cewa ta gwammace shi (Irshad) duk da kasancewar sa womanizer a kan sa." "Yanzu kam yana tantama a kan cigaba da aikin ta, ina amfanin tarin dukiyar da ya mallaka idan matar sa bata zauna a gida ta kula da Abdallah da kannen sa ba? Duk da ya san ita wannan Rahinah daban ta ke da sauran mata a kan boko zata iya barin komai, son Dan kawai ta sani, amma baya jin ta san yadda ake kula da yara da tarbiyyar su." "Yunwar da yake ji shima ta sa ya bar tunanin komai da sauraron karatun Rahinah ya nufi kitchen. Ya bude freezer, an zuba komai na amfani kamar yadda yayi wa Atiku umarni, one regrettable thing shine ya sallami Kukun gidan, don kada ya kalle masa mata, shi kuma ko suyar kwai bai iya ba." "Sai kawai ya jona kettle din dafa ruwan zafi ya dafa shayi ya hada shi sosai da peakmilk da lipton ya zuba a kofuna guda biyu, ya dora su akan karamin faranti, ya dauko sabon cake a firji ya aza bisa, da pizza wadda ya san Atiku ne ya ajiye masa su don baya rabo da cin su koyaushe. Kai tsaye ya koma sama, so yayi ya zauna ya ci a kicin din amma wata zuciyar ta ce a 鈥檃 h, akwai hakkin ciyarwa yanzu a wuyan ka." "Don haka ya nufi dakin Rahinah kan sa tsaye, an ce faduwar gaba asarar namiji ce, kamar yadda yayi tsammani dakin a bude yake, sakaya kofar kawai aka yi. Don duk mukullan gidan suna hannun sa jiyan da dare Nene ta damka masa bayan sun koma." "Sallamar da yayi ciki ciki yayi ta kamar an tilasta shi, don ya sa a ran sa ba Rahinah yayi wa sallama ba, a 鈥檃 h, mala 鈥檌 kun da ke tare da ita ne. Bata ji sallamar da yayi ba haka bata ga shigowar sa ba domin ta dora filo akan ta ta rufe fuskar ta tana cigaba da bin karatun ta cikin taushin murya, sanye yake da kayan barci pajamas samfurin 鈥楤 loomingDale 鈥檚鈥฀. Jin kamshin turaren sa yasa ta janye filon daga fuskar ta a hankali." "Yana nan a handsome HABEEBUNsa! Dan gayun nan wankakke, rashin wadatar haske ne ya hana mata ganin yanayin kyakkyawar fuskar sa wadda ko cikin duhu kyakkyawa ce." 鈥淪 orry for the interruption Ma 鈥檃 m 鈥฀ (ya nemi afuwar katse mata karatun ta). 鈥淚 brought tea for you 鈥฀ (na kawo miki shayi ne) ya sake fada. Tare da dora mata farantin akan bedside din ta. Wanda yake dab da inda kan ta yake. "Kamshin tsadadden lipton din ne ya tuna mata rabon ta da abinci, amma ko wannan shi ya saura shayi a duniya da garin Abuja bakidaya bazata sha shi ba." "鈥淒 auki tsiyar ka ka fita min a daki, bana son ganin mummunar azzalumar fuskar ka 鈥฀ maimakon kalaman ta su bashi haushi kamar yadda ya san ta fada ne don ta bakanta masa, su yi irin wacce suka saba, sai ya hada hannuwa cikin salama yace," 鈥渢 he ugly wicked man comes in peace. Maida wukar Ma 鈥檃 m. Albarkar haihuwa kike ci har gobe kuma ita za ki cigaba da ci har karshen rayuwar mu 鈥฀. "Da fadin hakan ya juya akan takun sa zai bar dakin, yana kokarin fita ya ce, ""Welcome to your humble abode!鈥฀." Sai ji yayi kamar daga sama ta ce 鈥淗 abib!鈥฀ "Bai juyo ba amma ya dakata, hannun sa akan marikin kofa, sai ji yayi taratsatsa! Ta hada kofin shayin da shayin da bango, 鈥渢 o hell with your tea, wannan ya zama lokaci na karshe da zaka kuma shigo min daki, kuma ka gaggauta kawo min Da na 鈥฀." "A wannan lokacin duk yadda ya so ya hakurkurtar da zuciyar sa ya kasa, juyowa yayi ya dubeta a gicciye da sexyeyes din shi, wadanda a kullum su ke gilma mata tamkar shifcin gizo." "鈥淣 a dauka kin fi kowa sanin hanyar kotu, ko kin ji nace da ke ki janye karar ki? Ba 鈥檃 gaya miki na amsa sammaci na zo ba? Don in tsaya da ke a kotu a kan kwatar Da?鈥฀" "Ya karasa fucewa daga dakin. Tare da cewa ""kina bukatar komawa islamiyya ki kara koyo tarbiyyah, Kura da fatar Akuya kawai 鈥฀." Kafin ya kai ga bude kofar ta yi maza ta sha gabansa. "鈥淜 ayi kadan kace min jahila, tunda duk jahilcin nawa a haka ka like mini, ka hana rayuwa ta sakat tun haduwa ta da kai, bayan na samu mun rabu meyasa ka ki yin auren ka da wadda ke son ka, har sai da ka janyo aka sake lika min kai?" "Wallahi ka sayar da maza, mara zuciya kawai wanda bai yarda bakin da ya furta rashin so har abada ba zai taba dawowa yayi furucin so ba. Na tsane ka Habibu Nahuche, na fada na kara bana son ka, Dan da na Haifa da kai kaddara ce ta yi min sanadin sa amma ba so ba." "Don haka ka sa a ran ka don shi na dawo, kuma zaman sa nake yi. Ka dauko min Da na duk inda ka kai shi ko in koma kai karar ka wurin Allah 鈥฀." *SUMAYYAH ABDULKADIR 07030137870* NA HUCE PAID BOOK "Tana shiga yana shiga, kafin ta juyo ya maida kofar ya rufe har da key. Ta daga idanun ta cike da masifa da hawaye ta dube shi." """Me ka zo yi min daki? Ko kana bina bashi ne? Ko ka zo raping din ne irin wanda ka saba tun kana cikin kuruciyar ka?""" Kawai sai ya hau undressing kan sa ba tare da ya ba ta amsa ba. Rahinah ta yi maza ta rufe idon ta ga kunya da ta kama ta kamar ta ce kasar wajen ta tsage ta shige. Ya Subhanallah Habibu menene haka? "A lokacin har ya gama undressing din, yace." """Ban so zan maimaita laifi na ba, amma bazaki daina kira na rapist ba ko na bari ko ban bari ba, sabida ke abu ba ya taba wucewa a wajen ki, na ga alama ke kam da dutse ba ku da maraba, ko kuwa in ce baki da lafiyar da yan adam ke da ita, ga shi tsufa na kwankwasa min kofa ban tara masu yi min addu'a da yawa ba." "Dan kwaya daya tal da Allah ya bani so ki ke ki kwace min shi ta karfi da yaji, da kissa da kinaya da nunkufurci irin wadanda kika kware a kai, don haka ina son yin ajiya a nan yau dinnan ko da tsiya ko da arziki 鈥฀." "(Ya nuna cikin ta). Yana kara takowa slowly zuwa gaban ta kamar mai tausayin kasa, lumsassun idanun sa da suka canza launi na gaya mata zahirin bukatuwar sa zuwa gare ta, abinda yake fadi haka ya ke har zuciyar shi kuma yau mai kwatar ta hannun Habibu sai Allah, ya kara da cewa," "In ma ya kasance ta hanyar rape din ne again ina ganin babu laifi don ke kika ja, tunda hakan kika zaba mana mu rayu, mu kuma cigaba da rayuwa, kuma ai na ga yayan rape din sun fi son iyayen su maza a kan ki, kamar sun san hobbasar uban su shi kadai ce ta samar da su ba tare da taimakon uwar su ba....." "In haka ne ni kuwa akan me zan ki haifuwar yayan rape tunda zasu so ni su kauna ce ni fiye da uwar da ta haife su? Dr. Rahinah Omar Allah ya gani na yi hakuri iya hakuri a kan ki, irin wanda ba kowane namiji ne kama na mai shekaru na zai iya ba. Shekaru goma kenan baki bar zuciyata da gangar jiki na sun huta ba, kin dawo cikin rayuwa ta again kina azabtar da ni da muguntar ki, bayan ban roke ki ki dawo ba tunda na fi kowa sanin wacece ke, tunda dai ni din mutum ne dan adam mai jini a jika kamar kowa ba daga sassake aka halicce ni ba dole yau in nemawa kai na mafita. Don haka yau daga ni sai Allah sai ke a dakin nan zaa goge raini da duk wani guntun munafunci da ke tsakani na da ke Rahinah ......" "Ta wara dukkan idanun ta da gabadayan girman su tana kallon sa cikin sabon tsoron da kwayar idon ta ce kawai ta bayyana shi banda action din ta. Wato a idon ta tsoro ne karara, a zahiri kuma ego din ta da pride din ta na nuna akasin hakan. Habibu ya karanto hakan, ya hango tsananin tsoron abinda ya tunkaro ta shi din tsakiyar (almond shaped eyes) din ta, kwatankwacin na shekarun kuruciyar ta." "Sai Habibu ya sassauta murya ya koma lallashi da ban baki. Irin wadanda shi kan sa bai san iya iya su ba ko a ina ya koyo su ba, ya yarda circumstances na rayuwa yana koyawa dan adam komai. Murya can kasa ya soma bayani cikin lallashi." "Tafiya zan yi zuwa Portharcourt wadda za ta debe ni har sati hudu, kin ga kuwa ai akwai babbar matsala alhalin na san yanzu ina da mata wadda ke zaman bukatu na. Azumin kamar kamar ya daina aiki a jikina a kwanakin nan" "Rahinah, wallahi ba na iya barci, a duk dare nikadai na san ya na ke wayar gari cikin soyayyar ki. Alhalin na san wannan karon ban tursasa ki ga aure na ba yardar kan ki da ta iyayen ki ce ta kawo ki cikin sa?" "Don haka ga zabi; ko dai mu tafi tare mu yi honeymoon wanda bamu taba yi ba sai rikici da balai wanda ni na fara gajiya da su, rayuwa mai maana nake bukata yanzu, in yaso Abdallah a kai shi gidan Ambasada har mu dawo; ko kuma please yau daya kar ki yi kokawa da ni. Give me this night, I don't want it to be hurting only loving and" "romantic!""." "Da fadin hakan ya yi maza ya hada ta da jikin sa ya rungume ta tsam-tsam, wata irin kyakkyawar runguma tamkar zai tsaga kirjin sa ya sanya ta ciki ko ya samu sa'idah daga azabar da yake dandana na kauna da soyayyar ta, Rahinah Omar, na iya jin yadda sautin bugun zuciyar Habibu ke dokawa, tana harbawa da karfin gaske a nata kirjin da nauyin soyayyar dake addabar sa cikin ta." "At the same time da Habibu Nahuche ya soma kissing din ta a zafafe, kamar kuma a yunwace, koko ta ce a urunce (hungrily) sannan in perfect style. Sumbatar ta kawai yake yadda ran sa ya ke so (tun daga sama har kasa. )!" "Ko ta yi kokarin gocewa ko nokewa a zuwan pretending a wannan karon, a wannan dan tsukin, a wadannan yan dakikan gangar jikin ta bata bada goyon bayan hakan ba 鈥฀, domin ta kasa yin hakan ko yatsar ta ta kasa motsawa da nufin kwatar kai, sakamakon ruhin ta da ya yi accepting komai (with a warm welcome) gangar jikin ta kuma ta amsa kyakkyawan kiran mijin nata Habibu, wanda abinda ta jima tana buri tana fata tana kuma mafarki kenan daga gare shi wato (soyayyah)." "The way and manner da Habibu yake sumbatar nata in style bai taba yin irin hakan ba, it's so soothing. Hatta babbar yatsar kafar ta ta tabbata yau Habibu bai bari ba, sai da ya kama ya tsotse in a soothing romantic manner, yana gaya mata wasu irin kalamai cikin kunnuwan ta da suka zam sirri ne a tsakanin su su biyu, wadanda duk na ban hakuri ne" "da neman hadin kai, wadanda suka gigita Rahinah Omar, suka kuma hautsina kwanyar ta, suka gusar da hayyacin ta na wucin gadi." "Wani tunani ne ya zo wa Rahinah a wannan lokacin, wato Habibu ya dauka ya ci banza raba ta da aikin ta da ya yi? Aikin da ta kwashe shekara goma tana karantawa don ta tsaya da kafafun ta. Ta zama abar hutun sa kawai daga yau tunda ta dage sai ta zauna da dan sa ko? An ce babu kyau kawo wani issue ga maigida a irin wannan lokacin, amma ita kam, ba ta da hanyar ramawa sai ta nan din. In yaso daga baya zata yi istigfari. Har kuma in da ahali ta nemi gafarar sa. Amma yau dinnan bata shirya karbar sa a matsayin miji ba, bata gama amincewa da canzawar sa ba, sannan ban hakurin sa bai gamsar da ita ba tunda yayi ne a lokacin da yake cikin halin bukatuwa." """Shin ka manta cewa zaman Da na na zo ba zaman ka nake ba? Ai zaman kula da Da nake yi babu wannan responsibility din cikin ajandar mu""." Idanun Habibu ko buduwa ba sa iya yi a wannan lokacin. Cikin rikicewa da gigicewa ya soma ya daga ido ya dube ta ya soma begging....... """Ki yi wa Allah ki yi hakuri ki yi min rai Dr. Rahinah, likitar zuciya ta. likitar kunnen duk duniya, na kara fadi with" "respect Dr. Rahinah ba Rahinah ba, wallahi za ki ci gaba da aikin ki amma ban da Nizamiye...... sabida wancan" CMD din ne ba zan iya jurewa ba. "Tuntuben harshe ne ya sa na ce kin bar aiki ba nufi na kwatakwata ba, kin san na san muhimmancin ilmin ki ba zan hana ki aiki ba no matter what ""." "Ya durkusa a gabanta ya rungume kugun ta, ""I'm very sorry Dr. Rahinah, for everything, for all the past inconveniences......" "Yanzu dai ki dubi girman Allah ki bar maganar komai kada ki shiga fushin Ubangijin ki, wallahi a bukace nake, na yi alkawarin daga baya zan saurare ki a kan duk abin da ki ke so ""." "Rahinah ta tabbata kalaman da Habibu Nahuche yake amayarwa yau ba cikin hayyacin sa yake yin su ba, amma yau kam ta rantse sai dai ya mutu. Duk da ta tabbatar wannan din SABON Habibu ne, ba her Ex-Habibu ba. !!!" "Juyawa ta yi da azama za ta fice daga dakin, ya yi maza ya sha gaban ta, murya a wahale ya ce." """Yau shekara goma sha daya da watanni rabon jiki na da naki Rahinah, rabon sa da na kowacce mace ma, rabon sa da wannan rayuwar, don duk wadda na kalla bata burge ni balle ta ban sha'awa sai ke kadai nake mafarki kullum." Kin tafi ne tare da gangar jikin Habibun bakidaya ba zuciyar sa kadai ba. Da wannan na gane cewa don ke kadai aka halicce ni..... "Don Allah Rahina. ki ci gaba da hukunta ni bayan haka, amma ki ba ni wannan hakkin ko na yau ne kadai, in ki ka" "so daga yau ki shata min layin shekara guda na amince, please and please ki ji tausayi na Dr. Rahinah ""." Ya tsugunna a kan gwiwoyin sa ya rungume kafafun ta. In tace zuciyar ta bata yi laushi ba ta yi karya. A take ya tuno raping din ta da ya rika yi babu ko tausayi at a very tender age sai ya ji hawayen nadama na zubo masa. "Ita ma abin da ta ke tunawa kenan tana nata kananan hawayen. Wanda ya zo yayi fatali da kalaman sa na karshe da ke son kassara ta. Suna a haka suka ji Abdallah na buga kofa da sauri da sauri yana kiran sunan mahaifin sa. ""Daddy where are you?""" "Da sauri Rahinah ta janye jiki daga gare shi ta shige bandakin ta ta rufe, shi kuma jiki ba kwari ya mike ya bude wa Abdallah kofar, bayan ya maida kayan jikin sa." """Daddy, dakin ta kuma ka zo? Tana ina? Ba ka ce ba ruwan mu da ita ba?""" "Rahina na bandaki tana jin su, ya kasa bai wa Abdallah amsa sai diri-diri ya ke yi, duk da hawaye ne makale a idon ta sai ta ji dariya ta kwace mata. Ah to, yaro sarkin gaskiya, mai magana daya shi, in ba ruwan ku da ita me ya kawo ka dakin ta har da rufo kofa kuma?" "Tana ji suka fice yana ta borin kunyar sa wa yaron, wai A.C din ta ce ta ke wuta shi ne ya gyara mata kada gobara ta kama musu gida." "Abdallah ya ki yarda ya koma dakin sa, ya ce shi yau tsoro yake ji, lallai-lallai tare za su kwana. Ita da ma haka ta ke so Abdallah ya cece ta a wannan daren kuma sai haduwa ta gaba, all thanks to Abdallah." Suna fita ta rufe kofar ta ba ta kuma zare mukullin daga jiki ba. "Ta yi shirin barci ta kwanta kenan, ba ta dade da soma barcin ba ta ji Habibu na knocking kofar ta, yana kuma hadawa da rokon ta da murya kasa-kasa kan ta bude. Rahinah ta ce cikin murmushin keta," """ka manta ne halan? Ni fa muguwa ce, kuma azzaluma ce already, don haka mu je a haka Malam Habibu, zan cigaba da amsa wadannan sunayen in practice (a aikace), har zuwa ranar da ka canza min suna""." """Idan kuma na ce na janye kalamai na fa Dr. Rahinah?" "In kin so daga yau kada ki kara kebewa da ni sai bayan wata shekara goman na amince, in ki ka bar ni a yau zan cutu, zan halaka, wallahi ba zan iya jurewa ba. Zan nema wani wajen ko ta halin kaka""." "Jikin ta ne ya hau rawa, ta ce, ""Wallahi Habibu ba zan bude maka ba, in ka yi forcing dina kuma zan tada Abdallah""." """Rahinah, don Allah... ki yi min rai. Na tuba na bi Allah na bi ki"" Ya fada cikin karkarwar murya da tsananin nadama da tashin hankali. Ganin da gasken ta ke bazata bude ba. Ga shi ya yi alkawarin babu shi babu sake forcing Rahinah a kan komai ma baa kan shimfidar sa kadai ba daga nan har zuwa karshen rayuwar su." "Da ya tabbatar ba za ta bude din ba sai ya juya zuwa dakin sa zuciyar sa, ruhin sa da gangar jikinsa baki daya na wani irin tukuki da azabtuwa." "A wannan daren daga shi har Rahinah babu wanda ya runtsa, ita (guilt) ne ya hana ta barcin don ta san ba ta kyauta ba, tana cikin fushin mala'iku in har ba ta nemi afuwar wannan zunubin ba, amma ba ta da courage (karfin zuciya) din da wani al'amari mai girma makamancin na baya zai sake gudana a tsakanin ta da Habibu Nahuche." "Ta kuma gane wani abu, kamar ita din ba ta da sha'awa irin ta auratayya sam, ba ta sani ba ko duk mata haka suke a kan mazajen su? Ko kuwa memories din abin da ya faru a baya ne yake farautar ta har yanzu? Ya cire mata kaunar abun ma gabadaya?" Ita kadai ce hakan ke faruwa da ita ko kuwa duka sauran mata ne??? "Ga shi ba ta da kawa balle aminiya ta jiki sai abokan aiki, wadda za ta iya tattauna irin wannan masalar da ita. Ta dade da gane hakan cewa ita bata da sexual desire, ko kuma kadan ne da ita? Ko kwatakwata ne babu ba ta gama ganewa ba har yanzu." Yayin da Habibu ya samu kan sa da kwana yana nema wa Rahinah Omar gafara a wurin Ubangijin ta. Yana cewa a fili; "Na yafe mata ya Allah, laifin da ta yi min komin yawan sa, wanda ta yi min a baya da duk wanda zata yi min anan gaba. Im the culprit. Komai ta yi min nine mai alhakin sa domin nine sila." "Ya fi dauka nervousness din abin da ya yi mata a baya, shi yake haunting din ta har yanzu kuma shi ya hana ta appreciating love-making gaba daya shekarun girman ta, a gabadayan rayuwar ta ta yanzu." "Duk sai ya ji ya tsani kan sa, ya kuma dorawa kan sa laifin komai." Domin ya tabbatar ya riga ya yi wa zuciyar ta illah mai yawa. Don haka maganar yayi fushi da ita akan hakan ma bata taso ba. Ya dauki alhakin komai ya dora a kan sa. At the end of all these yana son sanin consequences na forced sexual relation. Yau sai ya samu kan sa da yin bincike a kan (psychological effects na forced sexual relation\marital rape) kawai don neman karin ilmi a kai ba don komai ba. "Abubuwan da ya gani sun kara sa masa tausayin Rahinah, da nadamar abinda ya aikata mata a baya." A binciken sa ya gano cewa forced sexual relation ko kuma a ce marital rape yana haifarwa da mata abubuwa masu tarin yawa psychologically. Sun hada da; -Inferiority complex -Depression "-Feeling worthless and unloved, with no sense of dignity or pride" -Fear of intimacy between couples. A wasu lokutan mara karfin imani tana iya zama suicidal. "Daga nan ya kara samun dalilin fushin Rahinah, dalilin ta na kasa yafe masa, why she is bitter with him and how he will try to overcome it." A karshe ya yanke shawarar idan ya isa Portharcourt daga gobe zai fara yi wa Rahinah 鈥榯 exts messeges 鈥฀ na ban hakuri da nuna soyayya. Ba don ta bashi amsa ba. Zai kuma ci gaba da azumi da rokon Allah ya kare shi daga duk wani sharrin shaidan da ke giftawa a zuciyar sa. ****** WASHEGARI "Da wuri ta tashi don ta shirya wa Abdallah abincin makaranta, duk da yana cewa ba ya son abincin ta ta dauki alwashin shirya masa abincin tafiya makaranta kullum. Sanda yunwa za ta kama shi a makarantar ya bude ya ci ai ba sani zai yi ba." "Habibu ya fito cikin shirin sa tsaf na (Black Japanese Suit) mai jan neck tie, kafar shi rufe cikin rufaffen bakin takalmi da socks samfurin Armani, ya sanya siririn glasses din sa fari kal. Dakin Abdallah ya nufa don bayan ya yi barci jiya can ya maida shi, kuma sai direban ya sauke Abdallah ne zai wuce da shi filin jirgi ya wuce Fatakwal." "Shi ya taimaka wa yaron ya yi wanka ya saka uniform din shi, sai ga ta ta shigo rike da (food-basket), rigar barci ce a jikin ta da hula, ta dora zanin atamfa a kan rigar. Habibu bai daga ido ya kalle ta ba, ta ce," """Abdallah ga abincin ka, hope you will today eat Momma's food, (da fatan yau zaka ci abincin Maman ka) a yi karatu mai yawa, ban da guje-guje""." "Daga dan har uban babu wanda ya tanka mata, daga bisani Habib ya dago cikin harara." """Please Ma'am, koma da abincin ki, ba ya bukata. Wannan wane irin naci ne? Ko da can ke ki ke ba shi?""" "Ya fada cikin tsawar da ta firgita su ita da Abdallah. Ta san dalili, don haka ta juya tana kada masa bom-bom (irin kanka ake ji din nan) don ta san dole za su dauki abincin in ta bar wajen." "Tana tafiya kuwa ya ce, ""Abdallah dauki mu je ka ji? Ai ba nata ba ne tunda ba ita ta saya ba""." "Ya ba shi mukullai na gidan da na motocin gidan da cheque na kudi, ya ce ya kai mata da gudu ya ajiye kada ya ce komai ya zo su tafi." Tana canza kaya za ta shiga wanka Abdallah ya shigo da gudu ya ajiye mukullai da cheque ya fice da gudu ba tare da ya ce mata komai ba. "Ta ce, ""Ka daina gudu kada ka yi tuntube ka fadi"". Tana ji daga bakin kofa Habibu na ce da Abdallah." """Ko ina ruwanta in ka fadin? Na ga dai ba ta da asara?""." "Abdallah ya ce, ""Wallahi kam Daddy. Shes annoying na ce ta daina kula ni amma ta ki"". Dariya suka yi kamar wasu abokai suka sarke hannun juna suna sauka zuwa wajen mota." "Ba karamin jin dadin tafiyar Habibu PortHarcourt Rahinah ta yi ba, ko babu komai wannan ce damar da ta samu domin canza tunanin Abdallah a kan ta. Da ya riga ya gurbata masa. Tana tufka yana mata warwara kullum. Babu ko tsoron Allah ka dinga hada da da uwar sa. Gashi yace zai dade bai dawo ba." "Kafin ya tafi ya aje masa direban da kullum zai kai shi ya dauko shi, wai shi Sani, amma tunda ya ba ta mukullin motoci da na gidan duka sai ta sa a ranta kullum ita za ta kai yaron da kan ta, ta kuma dauko shi. Hakan zai taimaka wajen sanya shakuwa ko ya ya a tsakanin su, kafin kanwa uwar gami ya dawo." Ta rubuta takardar ajiye aiki ta kai asibitin Nizamiye. "Barin Dr. Rahinah Nizamiye bai yi wa masu asibitin da ma abokan aikinta duka dadi ba. Musamman Dr. Irshad. Ta ba su hakuri ta gaya musu ta yi aure ne ga hidimar iyali ta dawo wuyan ta, hada ayyuka biyu yanzu zai mata wahala, amma da yardar Allah tana nan a National Hospital in sun cimma conclusion a kai da maigidan ta, kuma za ta dinga kawo musu ziyara." "Ta yi shawara da Nene ta waya kan tana son kai Abdallah islamiyyah, Nene ce ta zabi islamiyyar da za a kai shi, wato (I Scholars), ita da kanta ta je ta yi masa rijista a nan kusa da su makarantar ta ke, wato Gwarimpha, tunda uban sa boko kawai yake masa fata ita ba za ta bar shi ba karatun addini ba. Ba ta san cewa yana da niyyar kai shi idan ya dawo ba." "Duk da haka uwa ta fi uba kulawa akan komai, uwa mafi uba ko da uban Sarki ne. Amma dai in reality Habib Nahuce bai da ragowa a kan kulawa da dan sa, yana kula da shi da komai nasa har fiye da yadda yake kula da Hotels din sa, kai dai bar shi da sangarta shi da jika shi da gata don a cewar sa don shi kadai (Abdallah) yake neman kudin." ****** NA HUCE PAID BOOK ABDALLAH Ya tattara hankalin sa duka a kan calculations din da yake yi da karamar kwamfutar sa lokacin da Maman sa Rahinah ta shigo dakin. """Abdallah lokacin kwanciya ya yi, ka kashe komai ka zo mu tafi daki na mu kwanta, tunda dai yau Daddy ba ya nan""." Ya tsuke fuska cikin gardama. """Daddy zai min fada in ya ji na kwana a dakin ki""." "Ta zauna dab da shi, ta kai hannunta bisa tarin sumar kan sa da tarin kauna fal cikin idanun ta, tattare da kulawa irin ta uwa, ta ce, ""Abdallah ka kwantar da hankali da ni ka ji? Don kai na dawo gidan nan idan baka sani ba, bana jin dadi kana biye wa fada na da Baban ka, ni mahaifiyar ka ce wadda ba ka da kamar ta duk duniya, ka ji?""" "Muryarsa na rawa ya ce, ""Ke ce ba kya son Baba na, ke ce ki ke wa Babana fada, in ya dau abincinki ki ce Allah ya isa, ni kuma bana so""." "Rahinah ta yi maza ta ce, ""Ba ka ji daidai ba Abdallah, wallahi shi ne yake min laifi, shiga fadan iyaye babu kyau, ko yi musu labe, saboda kai na aje karatu na a baya, don in baka kulawa a shekarar farko ta rayuwar ka, yanzu ma kuma na aje duka ayyuka na don dai in rayu tare da kai, in cike kewar ka da na yi ta shekaru goma"". Ta soma matsar kwallah." """Allah ya yi umarni da a bi Uwa, a bi Uwa, a bi Uwa kafin ya ce a bi Uba Abdallah""." Kalamai na kashe zuciya da sanya soyayya iri-iri Rahinah ta yi amfani da su a yau wajen brain-washing yaron da kwanyar sa ta riga ta gurbata a kan ta. "Bai ce komai ba, amma sun sanya shi a rudani, ya shiga tunanin shin tsakanin ita da Daddy waye mai gaskiya? Waye yake cutar da dan uwan sa ko da da kalaman fatar baki ne? Bai taba jin sun gayawa junan su kalma mai dadi cikin murmushi da lumana ba." "Duk yadda ta yi kokari don ya kwana a dakin ta bai yarda ba. A karshe ta ce," """To shi ke nan Abdallah, amma ka yarda daga yau in dinga kai ka makaranta ina dauko ka? Ka yarda in sa ka a islamiyya? Ka yarda in ringa koya maka karatu?""" "Sai ya gyada kai a hankali, exactly yadda Habibu ke gyada kan sa, wato ya amince da wannan. Amma ba zai kwana a dakin ta ba sai ta daina fada da Daddy." "Tun daga ranar Rahinah ta ci gaba da kai shi makaranta tana dauko shi, girki iri-iri ta ke musu suna ci, aikin gwamnatin ma ta sanya wa ranta ta hakura da shi saboda Abdallah." "Da daddare kafin su kwanta za su biya karatun da aka koya masa a islamiyya ta yi masa kari, ta yadda kafin su zo wajen a aji shi ya iya tiryan-tiryan. In sun gama sai ta taimaka masa ya yi home work din sa wato aikin gida na makarantar boko." "Duk weekend kuma sai ta kai shi Children's Park, su biya (Dominos) su ci pizza ta saya masa ice cream sannan su dawo gida. Duk dai abinda ta san zai sanya shi nishadi da farin ciki da sakin jiki da ita. A kullum kuma tana gaya masa how much she loves him." Yau da Abdallah ya dawo makaranta ya ci karo da dirkeken BIKE a kofar dakin sa. An makala greeting card a jiki ana yi masa murnar kammala jarrabawa lafiya. *From MUM Rahinah Nahuche.* "Wani tsalle Abdallah ya saka yana murna, ya ce," """Mummy you are the best, thank you so much. I love you!"". Don haka kafin Habibu ya yi sati hudun sa a PortHearcourt ya dawo, Rahinah ta gama janye dan ta tas, ya saki jikin sa da ita, sannan ne ta ba wa Sahura damar dawowa gidan. Don ta rika taimaka mata da ayyukan gida." ****** *NA HUCE is not for free. It's 1000 via 3094856450 Sumayyah Kabara First Bank* "Daga inda ta ke tsaye tana iya jiyo tashin dariyar yaron suna takowa da sassarfa a tare zuwa upstairs din, dariyar da ta tafi tare da sautin bugun zuciyar Rahinah Omar, ta tabo can kasan ruhin ta da wani irin sabon son Dan ta, wani shaukin soyayyar uwa ya debe ta da gudun gaske ya kai ta bakin kofa, ta bude kofar gabadaya ta wangale ta tana jiran hawowar Abdallah, daidai lokacin da suka hawo saman, Abdallah na fadi da accent din sa na Zamfarawa." """Is she really inside?"" Wato (da gaske tana ciki)?" "Sai ta ji duk damuwar ta ta yaye, damuwar da ya sanyata a ciki yanzunan, bakin cikin duniya da Habibu ya gama cusa mata na hana ta aiki a Nizamiye ya gushe nan da nan, wani farin ciki mara misaltuwa ya maye gurbin sa sakamakon jin dariyar Abdallah da sautin muryar sa kawai cikin kunnen ta." "Habibu yana takawa da sassarfa zuwa saman benen, yana amsawa Abdallah." """Yo wa ya sani ne ko tana nan din? Ko kuma ta tsallake magana ta ta zame ta tafi Nizamiye din nata?""" "Yana rufe baki idanun sa suka sauka cikin nata, wadanda ta ke kokarin lumshewa don kauda bacin ran da ke kwance kasan jijiyoyin su, da Habibun ya gama dasa mata yanzun nan ta waya." "Yaron ya tsaya kawai yana kallon ta da kallo na rashin sabo, ita ma tana kallon sa with so much adoration cikin fararen kwayan idanun ta. Ta tuno shi yana karami, yadda baya iya barci sai ya ji shi cikin jikin ta, ta tuno dabdalar sa gidan Ambasada ya shiga nan ya fita can tare da su Ahlan. Ta tuno rana ta karshe da ta rabu da shi daga kwanciya" "barcin laasar sai ta ji kwalla ta taram mata. Habibu ya cuce ta da yawa Allah ne kadai zai musu alkalanci amma don cuta ya gama cutar ta. Abdallah bai zurfafa kallon da yake mata ba ya kauda kai, ya bi bayan Baban sa wanda ya bude dakin sa ya shige ba tare da ya ce mata komai ba. Haka bai kara yi mata kallon arziki ba." "Abdallah yana gab da shigewa shima, ta bude baki a hankali ta ce da shi cikin shaukin da bazai misaltu ba; ""Abdallah!!!""." "Sai ya dakata kadan, shi bai dawo ba shi bai juyo ba haka shi bai shige dakin ba. Murmushi Rahinah ta yi wanda bai gama karade fuskar ta ba ta ce da shi." """Im saying Welcome Abdallah"". (Ina yi maka barka da zuwa)." "Yana so ya amsa, because he dont know why he likes her, amma kuma sai ya tuno abubuwan da Habibu ya gaya masa a kan ta daren jiya a Lagos." """Wallahi ba ta son mu, tunda ta iya barin mu shekaru goma muna watangaririya cikin maraicin ta, ba ta taba neman mu ba." "Ba ta zo don ta zauna da mu har abada ba Abdallah, sai don ta kwace ka daga hannu na ta kara gaba. Imagine Abdallah har kotu ta kai ni don a kwace ka daga hannuna a bata...""." "Sai kawai ya yi mata wani irin kallo da ya fi kama da na rashin yarda da jin haushi zallah, ya sa kai zuwa dakin Baban sa ba tare da ya ce da ita ko uffan ba." "In ta ce ran ta bai sosu ba, da biris din da Abdallah ya yi da ita, hakika ta yi karya. Amma sai ta ce a ran ta ""Da dai ba Habibu ne ya haife ka ba, shi ne za'a yi tsammanin halin ku ba zai zo daya ba""." "Duk da gwiwar ta ta yi sanyi da irin karbar da dan ta Abdallah ya yi mata, for the first time na zuwan ta gare shi a matsayin mahaifiyar sa a tsayin rayuwar sa ta yanzu, kuma tana da tabbacin yaron ya san da hakan, don ta san zuwa yanzu ba zai kasa gaya masa gaskiyar wacece ita a gare shi ba, hakan bai hana ta tunanin me za ta ba shi ya ci ba. Daga yau zata fara rayuwar motherhood, zata dasa tubalin irin rayuwar da kowacce uwa take yi da yayan ta." "Kitchen ta shiga ta soma tunanin me za ta dafa masa, ba ta san komai a kan likes and dislikes din sa ba wannan ma cuta ce mai zaman kanta da Habibu ya yi mata." "Musaddiq ya fado mata a rai, da sauri ta latso shi a waya. Bayan sun gaisa da tambayar mutanen gida, ta ce, ""Musaddiq ni me ye favourite food din Junior ne?""" "Musaddiq ya yi dariya, ya ce, ""Wannan ai shazumamu ne, kawai ki ba shi cornflakes din Kelloggs ya ji madara da suga zau, shikenan kin gama masa komai." "Wasu lokutan kuma Mummy (Aunty Badiya) tana yi masa danwake ta sa shi a gaba ta ce sai ya fara ci zai sha Kelloggs""." "Ta yi wa Musaddiq godiya, ta ce a ran ta, ""To ni kuma daga yau abincin da zai gina masa jiki ya kara masa girma zan koya masa ci (carbohydrate). Ni ba zan biye masa ba, gashi nan da jiki lange - lange kamar na Uban sa""." Girki sosai Rahinah ta zage tana yi har da sanya apron. Farin cikin ganin sa ya sa ta maida tension din da Habibu ya hada mata a kan maganar aikin ta a ba komai ba. Za ta ba shi mamaki kuma. Wannan karon da gaske ta gama da BOKO; motherhood din ta ke so. Shine kuma ya saura mata yanzu. In ma da gatse ya fada don yana ganin bazata iya ba to ya yi sara a kan gaba. "Ta kammala girkin ta mai rai da motsi tana kwashewa a sundukin abinci na zani (warmers), cous-cous ne ta yi wa wata irin dahuwa da 鈥榲 eggies 鈥฀ da 鈥榮 pices 鈥฀ masu sanya kiran yunwa, ga hanta ta wadace shi. Duk kitchen din da ma area din benen nasu ya dauki kamshin girkin Rahinah." "Habibu ya shigo karamin kitchen din wanda anan upstairs din nasu yake, bayan yayi wanka yana sanya maballan wuyan rigar shi TommyHilfiger fara sol. Bakin wandon Jeans ne mai kauri a jikin sa. Kitchen ne na zamani mai aji da mukami da ya ji komai na na'urorin zamani amma karami ne. Ya shigo ne da niyyar daukar ruwan FARO mara sanyi domin ya hada wa Junior Kelloggs. Ko kusa bai kawo a ran sa Rahinah zata yi musu girki ba. Kai shi ba ya jin ma Rahinah ta iya shiga kicin banda rike allura. Ta wutsiyar ido ya hango lafiyayyen abincin da ta ke kwashewa a food warmers wanda kamshin sa kadai azaba ne ga mai jin yunwa kamar sa. Rabon sa da abinci tun na daren jiya a Ikko." "Ya dauki ruwan da ya zo dauka har zai wuce ya yi wani tunani, in ya bar abincin nan bai ci ba bata da asara, ita gaba ma ta kai ta, kuma ya tabbata ba da shi ta dafa ba, bari kawai ya yi wa kan sa gata in ba haka ba da yunwa zai kwana, ya juyo gabadaya ya yi facing dinta hannun sa daya cikin aljihun wandon shi, daya rike da gorar ruwan Faro, ya ce cikin tsokana." """Sabbeni mu ina namu?""" "Hararar sa ta yi son ran ta, ba tare da ta tanka ba, tamkar idanun ta zasu fado kasa, wata zuciyar ta ce ta rabu da shi shiru ma amsa ce, wata ta ce dan yaba masa mara dadi wadda zai kwana tana nukurkusar sa." """Na yi kama da kukun gidan ka ne? Aikin banza!""." "Takowa ya yi zuwa gaban ta a hankali, ya tsaya dab da ita, har numfashin sa na dukan fuskar ta, ya kankance ido ya hade giran sama da na kasa tare da yin kasa da murya yadda ita kadai za ta ji shi ya ce." Waye mai aikin banzan?鈥฀ Ta murguda baki ta ce duk wanda ya tsargu..... "Kafin ta rufe baki ya kai hannu zai dauke warmer din gabadaya, ta yi maza ta danne hannun sa da iyakacin karfin ta ta rike foodflask din tamau." """Idan ka ci min abinci Habibu Allah ya isa!""" "Karaf! A kunnen Junior da ke shigowa kicin din, don shirun Baban sa ya yi yawa daga zuwa dauko ruwa a firji, shine ya taso ya biyo bayan sa, jin abinda Rahinah ta fada, sai ya dan dakata cikin jin tsoro, ya rakube a jikin kofa jin yadda ta yi maganar cikin tsiwa kuma da daga sauti sannan ga uban sa ta dannewa hannu kamar zata karya shi. Da sauri ya juya ya koma daki kirjin sa na bugawa lokacin da ya ji Baban sa na fadin." """ina rokon ki Rahinah. Ki cigaba da yi min Allah ya isa, because it 鈥檚 turning to BLESSINGS upon BLESSINGS. Allah ya isan ki ba ta tsiro, da tana tsiro da ban kawo yau ba, don Allah ki cigaba da yarfa min ita, shekaru goma ki kai kina jefo min ita tun daga Jamus zuwa Zamfara don na dauke miki Da, kin ga wani abu ya same ni ban da progresses da tarin achievments?" "Ke kuwa yau ga ki kin kare a gidan auren da ki ke gudu. Qualifications sun zama na banza! Tunda na hana aikin. Na fada, na hana!" "Da ma kin yi zaman aure na shekaru goman da ya fi miki alkhairi, da yanzu kin tara 'ya'ya biyar wadanda za su ji kan ki a tsufanki, at the very long last auren da ba kya so da shi ki ka tsira""." "Ta yi maza ta dauke hannun ta daga kan nasa, sakamakon wani irin shock da ya bakunce su su duka. Lokacin da Habibu ya matse nata hannun shima da dayan hannun sa. Har yanzu tana ignoring kallon cikin idanun sa da ya ke binta da su ba tare da ya sani ba, ta ce," """Idan kai ka dauki nauyin karatun nawa sai ka hana ni aikin in gani. Yaro kuma ya zo kenan hannun mahaifiyar sa, da shi da aikin al'umma duk zan iya hadawa in kula da abina. Babu ruwan ka." "Me ye naka a ciki? Auren da aka maida da wannan ka'idar ta hana ni aiki aka mayar da shi? Ko ko salon muguntar ka da zaluncin ka da ba ya taba karewa a kai na?""" "Habibu ya kara matsawa zuwa gaban ta sosai, kirjin sa da nata na bugawa wani irin fat-fat, ya kai hannu ya dago habar ta. Ta yi maza ta runtse ido gam! Tare da doke hannun nasa daga habar ta. Da azama ya matsa ya sumbaci eye-lashes din ta, sannan ya sauko a hankali kan karan hancin ta ya dora lips din sa a kai shima ya bashi kyakkwar sumba. Rahinah ta yi maza ta ja da baya tana hararar sa, domin hakika ya shammace ta, ya kawo sumbar a lokacin da bata zata ba, bata tsammana ba. Shi ko ido lumshe yake kallon ta tamkar ya hadiye ta ya huta da azabar soyayyar da ke kwance kasan kirjin sa, ya ce cikin sassanyar murya wadda ta samu rauni sanadin sumbar da ya yi. Kamar kuma baya so Abdallah ya jiyo su." """Aiki a Nizamiye na hana, na soke shi bakidaya daga yau. Idan kuma kina ganin ban isa ba, ko wasa nake, ko na yi kadan in yi umarni ki bi, to ki sake sa kafa a Nizamiye ki ga abin da zai faru 鈥฀." "Ya dauki flask din abincin gabadaya da plate da cokula biyu ya kama hanyar ficewa. Kasa ko motsi ta yi har ya fice daga kicin din. Bai ga Abdallah a dakin sa ba, don haka ya sauka zuwa downstairs inda main falon gidan yake." "A can ya tadda shi ya yi zugum da remote din talabijin a hannu, amma hankalin sa ba ya kan cartoon din da ya kunna, ya yi nisa a tunani. Da sauri ya karasa gare shi, ya ce," """Abdallah, what's up?""" "Firgigit yaron ya juyo ya dube shi, shi bai taba jin wani ya yi wa Baban sa Allah ya isa ba, ko ya daga masa murya, everyone treats his father with utmost respect including Hajiyar Nahuche da ita ta haife shi, in tana so yayi mata abu lallashin sa take yi with love and respect, sabida son da take masa, ma'aikatan sa kuwa kamar su yi masa sujjada sabida ladabi, don haka sosai abin da Rahinah ta yi wa Daddyn sa ya tsaya masa a rai." "Habibu bai kula da halin da yaron ke ciki ba ya hau zuba masa abincin yana cewa, ""Daure ka ci Abdallah, sai mu sha kelloggs din ko?""." "Girgiza kai ya yi da sauri. Kamar mai kyamar abincin. ""Ni ma ba zan ci ba!""." """Saboda me Abdallah?""" "Sai ya kasa gaya masa sabida ya ji ta yi masa Allah ya isa ne a kan abincin, kuma ta yi masa tsawa. Baban zai ce ya yi labe, bayan kullum yana hana shi sauraron zancen da ba nasa ba, kuma zai masa fada sosai." "Don haka ya yi shiru, Habibu ya debo abincin a cokali zuwa bakin sa. Dole ya bude baki yana ci. Ga mamakin Habibu yau Junior ya ci abinci yau sosai, cin har ya wuce daidai cikin sa. Ko shi da ya yi loma daya da cous-cous din Dr. Rahinah, sai da ya ji hatta fatar kunnen sa yana wani irin motsawa. Sai ya gyara zama ya shiga ci sosai da wani irin shauki, ko kuwa santin hannun da ya sarrafa girkin ne? Ba zai iya cewa ba." "Ko da ta koma daki kasa tabuka komai ta yi, sai safah da marwa da ta hau yi, yar sumbatar ta da Habibu yayi lightly duk ya birkitata ya kashe mata kuzari, ta fahimci Habibu zai iya barin komai a rayuwar sa amma banda kusantar jikin ta ko da accidently, wanda shi ma bai san lokacin da hakan ke faruwa da shi ba." "Hakan ya faru sau biyu kenan daga zuwan ta gidan nan zuwa yau. To ashe da ma ya iya kiss din ne har haka a baya yayi mata kwauron sa, ko ko yanzu ne ya je ya koya tunda ya gane ire-iren abinda take so kenan? A sanin ta dai a hawan kawara kawai Habibu Nahuche ya iya yi wa matar sa yadda zata cutu. Sannan ya bi ta da bakar magana. Bai iya wannan sanyaya murya da lallashin ba irin wanda ya yi yanzu har abin ya tsirga a zuciyar mutum, ya wuce ya bar shi da tunanin abun. Tsaki tayi a fili." "Haushin tunanin da ta ke yi din ne kuma ya zo ya kume ta, me ta zama ne haka? Me ya ke kokarin samun ta? Kada dai fa Habibu ya karya lagon ta cikin dan lokaci kalilan irin wannan ta tashi a tutar babu daga kan perception din ta. Yes, ta dade da gane shes romantic by nature, tana romance daga mijin auren ta, tana son romantic husband ba irin Habibu ba, tana son lallashi da tarairaya. Kuma akan haka ne ta tsani Habibu Nahuche, gashi tun baa je koina ba ta ga yana kokarin canzawa daga yadda ta san shi zuwa yadda ta ke son shi." "Neman tsari ta shiga yi da shi a zuciyar ta, domin dama can ta sani, baa kidnapping Da kawai Habibu ya kware ba; har da sace zuciyar diya macen duk da ta yi kuskuren hawa kan hanyar sa." Ta mike ta bi bayan su zuwa kasa don dai ta tabbatar Junior ya ci abincin da don shi ta girka ba don Uban sa ba. "A ran ta ta yanke shawarar hakura da aikin Nizamiye din, don ta tabbatar masa da ba bokon ne a gabanta ba yanzu, kuma ba shi kadai ya ke son Abdallah ba, don ta gane kamar yana kokarin ya nuna wa yaron hakan, kamar ma ya zuge shi a kan bata son shi, amma aikin gwamnati ba za ta daina shi ba ko da hakan zai kai ga ta gurfanar da shi a gaban Baba Ambasada, tunda a maida auren su da aka yi ai babu wannan yarjejeniyar ta son zuciyar sa." Uwa uba ta ci amfanin scholarship na gwamnatin kasar Najeriya wanda take fatan ta biya kasar ta wannan bashin ta hanyar cin moriyar ta. Tunda aikin ta halastacce ne a addinin muslunci. "Ba ta daddara ba da shareta din da Abdallah yayi dazu, ta fito falon ta isa kusa da shi ta zauna. Da sauri ya matsa gefe kamar ta tsikare shi, yana ta faman sunkuyar da kai ga barin kallon ta, cikin mamaki Rahinah ta ce," """Abdallah gudu na ka ke yi?""" "Ya yi mata shiru, ya sunkuyar da kai kasa, ta ce, ""To tashi ka je ka yi sallah maza""." "Ya yi kamar bai ji ta ba, don haka abin ya soma taba ran ta, ta tabbatar ba haka Habibu ya bar shi a kan ta ba kamar yadda ya ci mata alwashi. Tana iya ganin tsanar ta muraran cikin idanun yaron." "Haka ta rabu da shi zuciyar ta na kuna ta koma daki, Habibu bai taba bakanta mata ba a tsayin dambarwar su irin yau, don me zai sako innocent yaro cikin rikicin su? Allah kadai ya san abinda ya gaya masa a kan ta. Ba haka yaron ya yi mata a gidan Aunty Badiyya ba. Amma babu komai baa san maci tuwo ba sai miya ta kare. Ita da shi zata ga wa yafi son Abdallahn." "Ba ta daddara ba da daddare ta sake yi wa Abdallah girki. Wannan karon tuwon semo ne ta yi masa da miyar agushi, ta shirya abincin a kan tray ta nufi dakin Abdallah." "Yana sauya kayan jikin sa zuwa na barci, lokacin da ta shigo da sallama. Abdallah a can cikin cikin sa ya amsa mata sallamar, don ya san muhimmancin amsa sallama a addini, ko ta waye balle ta iyaye, sannan duk ya bi ya bata rai, Rahinah ta langabar da kai rike da farantin da ta shiryo abincin da ruwa da lemo," """Abdallah its time for dinner"". Wato Abdallah lokacin cin abincin dare yayi. Ya yi wani kicin-kicin da fuska, tare da turo baki gaba irin na yayan gata, ya ce," """Na gode. Amma ba na ci""." "Bata bata ran ta ba duk da kamar ya gwale ta ne (in a polite manner), kuma ta ji babu dadi, murmushi tayi ta ce. ""Ko da na ba ka a baki da hannu na?""" Ta zauna a gefen sa ta bude plate din ta debo tuwon ta shafo miya da yatsun ta ta nufi bakin sa. "Kin karba ya yi, ya kauda kai, sai da ta ce, ""Please Abdallah!"". Tare da yin narai-narai da idanun ta." "Sai ya ji ya kasa tankwabar da wannan kyakkyawar kulawar tata, at least da girman sa dai ba wanda ya taba cewa zai bashi abinci a baki, har wata kunya ya ji, ya karbi plate din abincin daga hannun ta, ya ce a hankali kamar cikin rada." """Ki bari zan ci da kaina! Kada Daddy ya zo ya ga kina bani abinci a baki""." """That's my boy!""" In ji Raheenah. "Tana zaune har ya kammala ci, sai ta tattara kwanukan ta ce. ""Ka zo mu tafi daki na mu kwanta ko Abdallah? Kada mu makara sallar asubahi"". (Duk a kokarin ta na son ya sake da ita)." "Ya dage kafada cikin rashin yarda. ""Ni ba zan kwana a dakin ki ba, sabida ban san ki ba, ina jiran Daddy na ya dawo ne, a dakin sa zan kwana, tare muke kwana in yana gari""." """ And I'm also your Mum Abdallah"". ""Na sani!""." "In ji yaron cikin kosawa," """Amma don Allah ki daina shigowa daki na, don Allah""." "Raheenah ta ji jikin ta ya fara yin la'asar ganin yaron ko hada ido da ita ba ya son yi, Allah kadai ya san irin hudubar da ya yi masa a kan ta." "Sai ta mike zuwa dakin ta da sauri ba tare da ta iya daukan kwanukan da ya ci abincin ba, jin takun Habibu yana hawowa benen. Ya ga sanda ta shige daki da sauri, ita kuwa ko waiwayowa ba ta yi ba sakamakon kwallah da ta cika idanun ta." "Ta dade ba ta samu barci ba yau, tana tunanin ta wace hanya za ta bi ta dawo da zuciyar dan ta gare ta? Gaskiya ba karamar cuta Habibu yai mata ba. Ya gama nesan ta ta da dan ta Abdallah." "A dakin sa Habibu ya same shi ya yi tagumi da kwanukan abinci a gefe. Ya ce Abdallah ya ne? Wa ya baka abinci? Ita ce ta kawo ya amsa a gajarce, kuma Habibu ya gane wa ya ke nufi, amma sai ya ce ita wa? Abdallah ya yi shiru bai ce komai ba." "Well Abdallah shes your Mum, and her food is nice, just eat, don ba ita ta kawo abincin ba ai ni na kawo, ita girkawa kawai ta yi, gyara zama mu cinye shi tas! Allah ne ya ce ta dafa ta bamu." "Da safe ba ta gaza ba, ta sake shirya masa karin kumallo. Tana kokarin saukowa daga bene zuwa dining dake kasan bene don ta aje masa abincin, tunda dai don shi kadai ta ke girkin ta, ta ji muryar sa yana gaya wa Baban sa shi ba zai kara cin abincin ta ba, duk da cewa da dadi, ya tashi su tafi Eatry ko restaurant su samu abin da za su ci, tunda ta masa Allah ya isa a kan food (he will never love her)." "Yana maganar (with a bitter tone) a kan harshen sa, shi kan sa Habibu ya yi mamakin maganganun yaron, daga yadda Abdallah yake maganar zaka fahimci abun ya tsaya masa a rai ya kasa wucewa, irin yaran nan ne da baa taba musu iyaye su kyale kuma yana da sanya abu a ran sa." "Maganar da ta sa Rahinah komawa sama da gudu, shi kuma Habibu ya yi sakale yana kallon yaron, kafin ya ce, ""Junior kada ka kara labewa idan muna magana, ba Allah ya isa ta ce ba, ba ka ji daidai ba ne. Tashi mu tafi restaurant din""." "Yana kokarin gayawa Habibu ba labewa ya yi ba shigar sa kicin din kenan ya ji tana fade Habibu ya yi masa tsawa..Cmmon, lets go i said. Dole yayi shiru yana kakkarwa. Ya saka takalmin sa ya bi bayan Baban nasa." "Kwanansu uku kenan a haka, kullum sai ta musu girki sau uku a rana, ba ta damuwa don Junior ya ki ci, yaro sai zucciya kamar tsohon kuturu, tana samun wani irin pleasure ne a ranta idan tana hidimta masa. Ko kaya ya cire ba ta saka su a kwandon kayan wanki ita ke wanke masa su da kanta a injin wanki. Ta kuma shanya a toilet din sa." Ya ki yarda ya kwana a dakin ta ko sau daya sai a nasa dakin. Duk lallashin data ke masa kuwa. Don haka da ta idar da sallar isha ta ke kulle kofar dakin ta ta bar mukullin a jiki. "Abin da ba ta sani ba shi ne, ko da ta bar kofar a bude in dai Habibu ne ya dade da sallama ta ta wannan fuskar. Sex is now his last priority. Azumin tadawwu'in da yake yi duk Litinin da Alhamis har yanzu bai fasa ba. Musamman yanzu da yake tare da Rahinah Omar kullum, cikin gida daya, abubuwa ke neman canza masa a matsayin sa na namiji mai lafiya wanda ya san yana da iyali na halali, duk irin dauriyar sa wata rana baya iya barci, kusan kullum yanzun ya farlantawa kansa azumin nafilah baya shifting din ma. Duk ya kara ramewa dama ga jikin ba wani jiki ba. Sai ya kara nesanta kan sa da it aba ya bin ko hanyar dakin ta, ko motsin ta ya ji ta fito to kuwa zai kara zama a daki har sai ya ji ta koma dakin ta ta rufe." "Sannan ba sa haduwa ma sam in ba a dakin Abdallah ba da safe. Yana da sabgogi masu yawa da yake gudanarwa a cikin Abuja da kuma Hotel din 'Transcorp Hilton' da suke dauke masa hankali daga Rahinah, ba ya zaman gidan ko kadan. Ko ba shi da abin yi a waje da dai ya zauna yana jin motsin ta yana kissime-kissimen da ba samu zai yi ba ya gwammace ya tafi gidan Ambasada ya karasa daren sa wajen su Yafendo. Ya ci abincin dare gun Nene tare da Abba Jakada." Sanda zai koma zai tarar ta yi barci sai ya shige dakin sa bayan ya duba Abdallah wanda shi daman da wuri yak e barci. "Satin su uku kenan da dawowar Abdallah Abuja har yau babu wani improvement tsakanin dan da uwar sa. Tana iya kokarin ta wajen jan sa a jiki da cusa masa akidu masu kyau, madadin na gata da ya tashi cikin su." "Habibu bai gaya mata yau zai kai yaron makaranta ba. Ta makara ba ta fito da wuri ba, sai jin tashin motar su ta yi suna ficewa daga gidan. Da sauri ta daga labulen dakin ta sai ta hango su direba ya fita da su, Abdallah da kayan makaranta a jikin sa." "Ya kamata a ce shi da ita sun zauna sun yi magana kafin yaron ya fara zuwa makaranta, amma sai ya ce wa kan sa ta yi kadan ya tsaya shawara da ita, don zai kai Abdallah makaranta." Da can da yaron ya yi primary tana ina? Ba tana can tana gina kan ta ba? Don haka yanzu ma da ta ke cikin gidan in dai a kan al'amarin Abdallah ne ba ta da wani amfani a wurin sa. ******* """Pace-Setters Collage"" ya kai shi ya nema masa gurbi, aji daya na karamar sakandire, makaranta ce ta 'ya'yan masu ido da kwalli da ke wajejen Wuye, Life-Camp da Gwarimpha a Abuja." "Can Habibu ya kai Abdallah, ya kuma ware direban da zai dinga kai shi yana dauko shi kasancewar shi ba mazauni ba, ko yana gari ba zai jure kai shi da dauko shi ba." "A tsarin ayyukan hotels din sa bai iya sati guda cikakka a gari daya, don haka yanzu ma shirin wucewa Porthearcourt yake yi, kan ba yadda zai yi ne zai bar Abdallah daga shi sai Rahinah a gidan nan, wadda ya san neman duk hanyar da za ta samar mata kusanci da Abdallah ta ke yi." "Tafiyar sa Portharcourt kuma a wannan dan tsakanin, daidai ta ke da ya bata filin da zata samu damar kanainaye masa yaro. Don kuwa shi yake kara zuga Abdallah kullum da cewa yayi a hankali da ita. Ba zama ta zo yi ba, in ya bari ya saba da ita ta zo ta kara gudar su shi zai sha wahala shi ba ruwan sa." "Don haka da dacin rai yau ya shigo dakin ta, domin tilas zai yi tafiyar, an samu matsala tsakanin hotel din sa na PH da gwamnatin jihar ta Cross-Rivers suna so zasu saye filin wajen don amfanin gwamnati, don haka dole ya je ya daidaita komai in sayar musu zai yi ya sayar in ya so a sake gina wani a wani filin daban." "Ya shiga dakin ne da niyyar gaya mata abinda zai bata mata rai, wanda har ya dawo zai hana ta shiga harkar Abdallah, ana-i-gobe zai tafi PH." "Bai gan ta a dakin ba, har ya juya zai sauka kasa kuma sai ya jiyo maganar ta a dakin Abdallah. Don haka can ya bi su 鈥฀" "Yana gab da shiga dakin ya ji tana dungure kan yaron tana cewa, ""Mai bakin hali da kuturwar zuciya kawai irin na Uban sa""." "Yaron ya yi kicin-kicin da fuska, ya wani irin manne idon sa cikin takaici da bakin cikin kalaman ta, ya ce, ""Baban nawa ne mai bakin hali, mai kuturwar zuciya? Baba na!""" "Rahinah ta ce, ""Exactly! Like father like son, ba ka baro shi a komai ba tun daga kamanni har halayya, ban da haka sau nawa zan gaya maka Abdallah ba'a yi wa uwa haka, ko ka ki ko ka so dai ni din nan dai, ni na haife ka, sai in gani in zaku iya sake ni, Allah ya ce a bi UWA sau uku, kafin ya ce A bi UBA, kuma ban gaya maka baa kwanciya da uniform ba? Da an dawo ake cirewa amma kullum sai na maimaita?""" "Sai Abdallah ya ce cikin kunkuni, ""To ke Antyn gidan nan me ye damuwan ki da ni ne? Na roke ki ki daina shigowa daki na kin ki. Na fada miki I'm not your son, I'm Daddy's son!""." "Sai jin sautin tafi suka yi daga bayan su, raf-raf-raf irin 'sound claps' dinnan. Habibu ya shigo dakin yana taku dai-dai cikin kasaita yana cewa," """Ka haifu Abdallah! Ai ka san wasu mutanen ba su da zuciya kare ya cinye, in ba haka ba ban ga dalilin da za ta dinga shiga sabgar ka ba, bayan ta jefar da kai a zanin goyo ta rungumi boko""." "Wannan karon a fusace ta ce, ""Ka daina yi min haka, ka daina fadin kowacce magana ta zo bakin ka a gaban sa... shi yasa yake kara tsana ta." "Na jefar da shi ko ka sace shi? Ka dinga yi kana tsoron Allah cikin al'amarin ka""." "Ta juya ta fice daga dakin hawaye fal idon ta. Ga ta da qi-fadi, ba ta son nuna raunin ta ko kadan a gaban Habibu Nahuce, shi yasa ta fice, kafin hawaye su gangaro mata, yaron sai ya ji dan tausayin ta ya kama shi yau, ganin tana hawaye da girman ta. Habibu kuwa ko a jikin sa, juyawa ya yi ya bi bayan ta zuwa dakin ta." "8/24/22, 10:35 - Bilkisu Adam 馃暩锔忦煈฀: U" "ncle Usman ne ya yi mata waya yana neman karin bayani a kan barin aikin ta, don abokan aikin ta sun bi ta kan sa a kan ya roke ta ta dawo aiki. They cannot afford to lose such a golden Doctor like her, inda ya sanar da su ba shi da masaniya a kan barin ta aiki, amma zai yi wa mijin ta magana, mai yiwuwa ne shi ya dakatar da ita." "Ko da ya kira Habibu yana tambayar ba'asin maganar, sai ya yi shiru. Wannan ya tabbatar wa Uncle Usman zargin sa na cewa shi ya hana ta din, kuma ba abin da za'a iya yi wa Rahinah barazana da shi ta bar aikin ta na likita a yanzu in ba dan ta ba." "Uncle Usman ya yi wa Habibu fada sosai ya ce," """Aikin ta bai da alaka da rigimar ku Habibu, ko da ka gan ta da karatun ta ka same ta, kuma ta sanadinsa ne har ka samu damar auren ta, har ku ka haifi Dan da ka ke mata barazana da shi Habibu." "Don haka ka bar ta ta yi aikin ta tunda aiki ne na taimakon al'umma. Bana son zuciya ba ne ko na rashin godiyar Allah""." "Habibu ya yi mamakin jin Rahinah ta bi umarnin sa ta bar ayyukan ta duka, shi iya na Nizamiye ya ce, wannan ya kara tabbatar masa Rahinah ta fara canzawa daga kafaffiyar da ya san ta a baya, kuma da gaske ta ke za ta yi wa Abdallah goyon da ya kubuce mata na shekaru goma ba da laifin ta ba, sai ya ji tausayin ta ya kara ya tsirga masa." "Amma ko da ya dawo gidan a washegari daga PH, bai nuna mata hakan ba. Bai nuna mata cewa ta fara karya lagon sa ba. Ya sha tura mata 鈥榯 ext masseges 鈥฀ yana PortHarcourt amma ba ta taba replying ba, ko tana gani ko ba ta gani? Allah masani." "Ko da ma ba masu bukatar reply ba ne, yawanci na ban hakuri ne kawai da alkawari kala-kala, a kan ya yi alkawarin zai canza, zai zama miji abin alfahari a gare ta. Zai koma irin yadda duk take son shi. Zai zame mata Mijin marainiya kuma loving and caring husband." "Bai tsammaci da ma za ta kula shi ba, kamar ya san a duk lokacin da ta gani ba ta bata lokaci ta ke share su daga fuskar wayar ta duk da a lokuta da dama kalaman suna taba ta, suna sassauta fushin da ke zuciyar ta." Amma still ta kasa sakewa da shi wholeheartedly. Ta kasa yarda duk abinda yake fadi haka yake har zuciyar shi. A ganin ta he needs time wato yana bukatar lokaci. "Ba tare da ta san cewa yau zai dawo ba, tana kicin tana juya lafiyayyar miyar Talo-Talo (Turkey) da ta ke soyawa mai yawa ta saka a firji. Sai jin takun sa ta yi ya nufo kitchen din. Kasancewar shi mijin ta, Habibu Mustapha Nahuche, mutum ne mai takun kan sa (duk inda ta ji takun sa sai ta gane), yana ta hayaniyar cigiyar Abdallah cikin gidan bai san yana can bayan gidan yana fama da dirkeken 'Bike' din sa ba." Abdallah where are you? Im here now! "Daga bakin kofa ya tsaya hannayen sa biyu zube cikin aljihu yana kallon bayan ta da wata irin siga, yana jin wani irin contentment da wata nutsuwa ta musamman suna baibaye shi. Samun mace kamar Rahinah kadai matsayin matar aure is a BLESSING da bawa domin sai wanda Allah ya zaba ya ga damar ba shi, a ganin sa ko da ba za ta amfana wa mijin ta komai a shimfida ba, kallon kyakkyawar fuskar ta kadai da fararen idanun ta sun isa sanya shi farin ciki kullum." "Ga shi ta yi wani abu da ya tsaya masa a rai, ya kuma lankwasa zuciyar sa yau, wato ayyukan ta da aka ce da gaske ta bari saboda Abdallah." """Good afternoon Dr.\Mrs NAHUCHE""." "Habibu ya fada da lallausar muryar da Rahinah ta kasa amincewa tasa ce. Sabida a kullum yana mata magana ne harshly and loudly da sigar tonon rigima, amma yau ba abin da muryar sa ke dauke da shi sai lislama, ni'imtacciyar soyayya da kulawa tsantsa." "Banza ta yi da shi ta ci gaba da soya miyar ta, sai ya tako a hankali tamkar mai tausayin kasa zuwa inda ta ke. Ba ta yi aune ba ta ji ya rike ludayin, ya kuma kashe cooker din." """Ki ba ni attention daga tafiya na dawo. Kuma kin san cewa I missed you ko?""." "Ta daga ido ta dube shi a fusace ta ce, ""Ina ruwana da tafiyar ka? Na aike ka? Ko na ce ina bukatar dawowar ka? Na bi I missed you din da gudu na tattake da takalmi mai tsini a kafa ta!"" Ta fadi tana tattaka kafar ta a kasa." "Dariya ya yi. Rahinah ko tsufa ta yi baya jin zata bar ki-fadin ta da tsiwa. Amma kwayar idanun ta sun fallasa cewa ta ji dadin 鈥淚 missed you 鈥฀ din, ita haka Allah ya halicce ta son soyayyar miji." """Ba ki ce ba, amma kin iya kai kara ta gun Baban ki ki ce na hana ki aiki, kin manta cewa yanzun ba ikon Baban ki ba ce, iko na ce (ya nuna kirjin sa da dan alin sa) To na hana din, ki yi duk abin da za ki yi, tunda na ce zan biya scholarship din da aka biya miki ga duk wanda ya bukata""." "A kufule ta dube shi, sabida kalaman sa sun bata mata rai matuka. Shi da ya ke neman shiri amma ba zai bar gadara da fadin rai ba. Hausawa sun yi gaskiya da suka ce Mai hali ba ya fasa halin sa don shi hali kaman zanen dutse ne. ""Ba ka da arzikin da za ka fanshi ilmi na, domin shi ilmi ba a sayen shi da dukiya, wadannan kudin naka da babu tabbacin ba na haram ba ne sun yi kadan su fanshi karatu na""." "Ba zan kara cewa ka sake ni ba, don I'm now matured enough ga bukatar hakan, amma har abada ba za ka samu zuciya ta tare da amincewar gangar jiki na ba. ""." "Sai juyawa suka yi su duka suka ga Abdallah a bayan su, hankalin sa a tashe da fadan da ya tarar suna yi kamar za su tada kicin din." "Kafin Habibu ya yi masa magana Abdallah ya juya da sauri, da sauri ya sakar mata ludayin ya bi bayan sa, sai kuma ya juyo yana kallon ta a kaskance. Domin kalaman ta sun masa ciwo ba dan kadan ba. (Cewa da tayi ba zai taba samun zuciyar ta da amincewar gangar jikin ta ba)." """Ki jika komai naki ki shanye don Allah Rahinah, I'm going for a second wife, wadda ta fi ki duk abin da ki ke takama da shi. Za ki ga ranar da kudin haram za su yi wa dan halal""." """Ka dade ba ka yi ba! Tunda ka kwashe shekaru goma ba ka yi ba sai yanzu, in ka yi yanzun gaskiya zai fi zama fashionable, sai ana son mutum a ke kishin sa""." "Ta karasa cikin karkarwar murya da ita kanta ta ba ta mamaki. Da gaske yake? Ko kuwa barazana ce irin wadda ya saba? In ma da gaske ne bai kamata ta ji faduwar gaban da ta ji a kan maganar sa ba, in har da gaske sai da so ake kishi." "Duk abin da suke fadi a kunnen Junior wanda ke bakin kofa ya kasa tafiya daki yana ta tsuma, zazzabi ne ya zo ya rufe shi sabida a rayuwar sa ba ya son fada, kuma ya tsani hargagi da tashin hankali. Amma dukkan su are talking bitterly to each other ba tare da sun san ya dade tsaye yana jin komai ba." "A daren wannan ranar an yi drama ba 'yar kadan ba, hakurin Habibu ya gaza, yayi lallashin duniya Rahinah ta ki, musamman tunda yayi maganar gatsen zai kara aure, hakan ya kara fusata ta, ya kara gishiri akan danyen gyambo, bayan a da ta fara dan sakkowa." "Shi kuma Rahinar sa yake son kasancewa da, anyhow, wanda abinda ya sanya shi dawowa daga PH kenan ba tare da ya gama abinda ya kai shi ba, ba don alkawarin da ya yi wa kan sa ba, na har abada bazai kara ba, ba akan Rahinah kadai ba, akan kowacce diya mace, sabida tunanin nasa yaya matan da zai iya Haifa a gaba, (after knowing the consequences of marital rape), da babu abin da zai hana shi maimaita laifin sa a yau, sai dai ko me zai faru ya faru." "Ya yi kwanan bacin rai ba dan kadan ba, yau ko gafarar bai roka mata ba, bacin ran da ya sa da asubahin washegari ya buga wa Aunty Badiya waya." "Wayar sa a daidai wannan lokacin ta fadar mata da gaba, idar da sallahr Asubar su kenan ita da Uncle, sai ta fito daga inda Uncle Usman yake zuwa dakin ta, ta amsa wayar tasa a nitse, don ba ta san ko me ta kunsa ba." "Suka gaisa shi da Badiya, amma ba'a kai karshen gaisuwar ba Habibu ya ce, ""Maman Musaddiq aure nake so zan kara. Ina neman taimakon ki""." "A zaune Aunty ta ke, amma sai ga ta tsaye a kan kafafun ta." """Amma ba karamar yarinya ba, bazawara nake so wayayya ba mai karatun boko ba, wadda ta doshi shekaru arba'in haka""." "Aunty ta nisa, kafin ta ce," """To Habibu za a bincika, amma ba yanzu ba. Duka-duka yaushe wannan ta koma? In ka kasa zama da guda daya zama da biyu ba naka ba ne. Find the root cause of the problem first, tackle it then, I'm sure ba dadi ne ya kawo bukatar karin auren ba sai akasin sa." "Daman ina da niyyar zuwar muku cikin satin nan in ga lafiyar ku, amma yanzu gobe zan zo insha Allah." "Ka ba ni sati biyu zan gana da Rahinah tukunna. Bayan nan in karin auren shi ne solution na tabbatar maka zan mara maka baya""." Da wannan suka yi sallama. Kamar yadda ta alkawarta masa a washegari Musaddiq ya dauko ta zuwa Abuja. "Ba ta gaya wa Rahina za ta zo ba, yau din ma suna tsaka da rikicin su a falon kasa, wanda duk rikicin Habibu da Rahinah kashi tamanin cikin dari in ka bincika a kan Dan su ne""." """Ni na ce ki dinga kai shi makaranta? Ko ko salon samun hanyar gantali a kan titi? Ban ajiye masa direba ba?"" Cikin tsananin zafin rai yake magana. Wanda kin sa da ta yi daren jiya shi ne sila." "Rahinah ta ce, ""Ka ajiye, kaishin da nake yi ganin dama ta ne. Wai me ka ke nufi da ni ne Malam a gidan nan?" "Auren kulle za ka koma yi min? Ka ce aiki, na bari, sannan ka ce ba inda zan je don in mike kafa ta sai dai kawai in zauna in sharba kiba a cikin daki?""" """Za ki rantse da Allah sabida ki motsa kafa ki ke kai shi ba don ki yaudare shi ba? In motsa kafa ne ina gymnasium din gidan? Kawai so kike ya saba da ke, ya so ki, ya so ci gaba da rayuwa da ke, ki zo ki sake guje masa!" "Ai mumini maciji ba ya saran sa a rami guda. Mun dade da sanin wace ce ke, mayaudariyar Uwa, muguwa, azzaluma. !""" "Fushin nasa ba a kan kai yaron makaranta da ta keyi bane kawai, har da kwalelen talalar data yi masa daren jiya." """Habibu!""" "Ya ji muryar Aunty Badiya daga bayan sa cikin fushi. ""Me nake gani haka? Me nake ji haka? Ku kalla nan...""." "Ta nuna Abdallah da ke mannewa a bayan labule jikin sa yana ta rawa da karkarwa, ko kadan ba ya son fadan nan da suke yi kullum, ba abinda ya tsani gani irin sa'in sar su, da sunan nan da Habibu ke kiran Rahinah a duk sanda ya bushi iska; muguwa-azzaluma." "Don a dan zaman sa da ita su biyu a cikin gidan ya fahimci abubuwa da dama a kan ta, tana son shi ita ma, kwatankwacin yadda Baban nasa ke son shi, har ya fi jin dadin kulawar ta a kan ta Baban sa." "Bai ga mugunta ba, bai ga zalinci a Maman nasa ba!" Daga shi har Rahinah ba su san yaushe Abdallah ya zo gurin ba. A tunanin su sun kaucewa idon sa tunda yana dakin sa yana barci. "Aunty ta karaso cikin falon tana cewa, ""To tunda kalar rayuwar da ku ke yi kenan, ni a ba ni yaron in tafi da shi, da ma ba ku san kalar kashin sa ba balle na fitsarin sa, bayan na haihuwa. Kada ku bata masa tarbiyyah a banza""." Aunty Badiya ta fadi a hassale tana janyo Abdallah jikin ta daga bayan labulen. "Rahinah sai ta haye sama da sassarfa. Tana ji Aunty na ta yi wa Habibu fada, ta inda ta ke shiga ba ta nan ta ke fita ba." "Ga shi kuma yana jin nauyin ta, yana kuma kare sirrin auren sa, ba don haka ba da ya gaya mata dalilin da ke tunzura shi a kan Rahinah ba Abdallah ba ne, the more mace ta yi denying husband dinta in bed, the more zuciyar sa ta ke a kusa, the more ya ke zama frustrated, duk wata kyautatawa da zata yi masa ba ya gane ta in ba wannan ba." """Ki yi hakuri""." "Kawai ya ce kan sa a kasa, sannan ya ce cikin sanyin murya, ""Ni zan fita, ina fatan a nan za ki kwana?""" Badiya sai ta ji kanin nata Habibu ya bata tausayi. Ta ce. """In kwana gidan da babu fahimtar juna da kwanciyar hankali cikin sa a kan me? Ka san dai ina da masauki na, me zai kai ni kwana gidan ku alhalin har gobe ba ku gama sanin ciwon kan ku ba? Ba ku iya rike amanar Da guda daya da Allah Ya ba ku ba sabida wautar ku?""" "Kan sa a kasa ya ce, ""Hakurin nan dai nake kara ba ki Maman Musaddiq, ba za ki gane ba ne. Kuma maganar aure da na yi miki I'm very serious yanzu nake son sa ba gudu ba ja da baya""." "Aunty ta ce, ""Tau! ai ka san inda zawarawan suke sai ka je ka bincika da kan ka. In ji dai Rahinar ma ba ni na gano maka ita ba?""" "Ta haye sama ta barshi a nan tana fadin, ""In ka so ka bai wa Musaddiq daki ya huta yana waje yana fidda kaya a boot""." "Ta kama hannun Abdallah suka bi bayan Rahinah zuwa dakin ta. Sai ta same ta ta hada kai da gwiwa a gefen gadon ta, ita ba kuka ta ke ba, amma idanun ta sun kada sun yi jajir." "Abdallah ya ce, ""Mummy, ki yi hakuri""." "Sai ta yi dan murmushi ta gyara zaman ta, ta ce, ""Aunty sannu da zuwa, ya hanya?""" "Ta mike don ta dauko mata ruwa a firjin gefen gadon ta, Aunty ta ce, ""Bar ruwan ki Rahinah. Yau tafiyar nan tawa takakkiya, taki ce. Na rantse ban barin gidan nan sai na ji tun farko mene ne matsalar ku ke da mijin ki. Me ya hada ku kuma me ya raba ku shekara goma?""." "Ta dubi Junior, ta ce, ""Junior maza tafi wajen Musaddiq yana dakin baki, ga choculates din ka na zo maka da su. Har da kelloggs""." "Ga mamakin Aunty Badiya, yaron bai nuna zumudi ko farin ciki ba, kamar yadda ya ke yi a duk lokacin da ta bashi chocolate ko kelloggs din, jikin sa a sanyaye ya ke idon sa sai kallon Rahinah yake yi wani iri, domin ba ya son ganin ta a irin yanayin nan da ta ke ciki tun dawowar Baban sa gidan." "Hatta fara'ar da ta ke wuni ciki yanzu ta dauke, koyaushe cikin yanayin da ta ke kenan; ido jajir babu fara'a." """Maza je ka Abdallah, ka ce ina gaida Yaya Musaddiq""." "Da wannan ya juya ya fita jikin sa duk a sanyaye, ko ledar tsarabar da Mummy ta kawo masa bai dauka ba." "Aunty ta maida hankalin ta kan Rahinah, ta ce, ""Rahinah, ba komai ya sa na ce ina son sanin hakikanin matsalar ku ba sai don Habibu da ya kira ni jiya yana batun yana so ya kara aure, shekara goma da ba kwa tare bai yi auren ba sai yanzu da ku ke tare Rahinah? And he sounds serious ban ji alamun wasa yake yi ba, don na fi kowa sanin sa." "Idan ki ka bari Habibu ya auri irin matar da yake nufi, kin kade har ganyen ki""." """Aunty ko kyankasassar 'yar bariki yake so ku aura masa don Allah ku aura masa..."". Sai kuka ya kubuce mata. Aunty ta ce, ""Rahinah may I know your problem as a mother not an inlaw? Na yi alkawarin ko Baban ki ba zai ji ba, ba zan saka third party a tsakanin mu ba." "Ciwon 'ya mace na 'ya mace ne, na tabbata rashin SO ba shi ne matsalar ku ba, akwai wani boyayyen dalilin amma ba shi ba." "Ko ban kawo solution ba ko ban hana shi kara aure ba zan taimaka miki da shawarwari matsayi na na mace yar uwar ki wadda ta fi ki yawan shekaru da sanin halin maza, wadanda insha Allah in muka bi su za mu yi maganin matsalolin komin yawan su. Hausawa suka ce barin kashi a ciki baya maganin yunwa Rahinah""." "Lokaci na farko da Rahinah Omar ta ji zuciyar ta ta amince ta fada wa wani abin da Habibu ya yi mata. Wanda ya sanya mata tsanar sa, ya kuma lullube soyayyar sa wadda ta zo ta same ta bayan rabuwar su. Ko babu komai ita wannan shakikiyar sa ce, 'yar uwar sa ce ta ciki daya, duk wani mataki da za ta dauka ko shawarar da za ta bayar wanda zai amfane su ne su duka, kuma ba ta taba mutuncin sa a idon wani ba. Idan kowa zai kalli da abin da ya yi din a baya ya hada shi da matsayin sa na yanzu da wani ido na daban, Badiya ba za ta kalle shi da haka ba." Sai ga Rahinah yau tana voicing out damuwar ta ta shekara da shekaru tana yi tana kuka. """He has been sexually abusing me in my adolscent ages da sunan aure. Auren da aka yi ba da cikakkiyar yarda ta ba, a gantale babu martabar iyaye a ciki." Abin da na fahimta ya saka karfi ya aure ni ne kawai a lokacin don biyan bukatar gangar jikinsa. "A lokacin da ni kuma ina da abin da na saka a gaba, abin da ya kai ni kasar Jamus. Ban gama sanin hakikanin me aure ya kunsa ba sai a hannun sa." "Sannan bai tsaya ya fahimtar da ni ta hanya mai kyau ba. Bai samar da fahimtar juna da kyakkyawar dangantaka ko kankani a tsakanin mu ba. Abinda ya sanya a gaba a wancan lokacin kawai shine ya sadu da ni anyhow, disregarding my feelings, my well being, my health and my humanity" "A yanzu kuma da na girma na mallaki hankalin kai na da tunanin kaina, sai na gane cewa, a rayuwa ta ina son miji ma'abocin soyayyah (I want my husband to be loving, caring and romantic who is not given sex priority), don" na fahimci ina da karancin bukata. Na fi danganta hakan da psychological trauma din da Habibu ya gina a kwakwalwa ta a baya. Kwatakwata yanzu bana so ya kusance ni duk da na fahimci yana son canzawa ne... To Anty kin ji abinda ke sanya mu samun sabani. "Ta karasa fadin hakan cikin tsananin jin kunya da runtse idanun ta, tana mai sunkuyar da kai tana share hawaye. Amma yau sai ta ji ta sakayau, tunda ko ba komai ta amayar da abin da ba ta taba amayarwa kowa ba, abinda ta dade tana fama da shi ita kadai a ran ta, sai ta ji tamkar an zare mata kaya daga zuciyar ta." "Aunty Badiya ta yi mamaki a kan labarin da Rahinah ta bata, kuma a kasan ran ta ta ji kunya sosai kamar ita ce Habibu Nahuchen, eh, dole Habibu Nahuche ya yi gummm da bakin sa in aka ce Rahinah ce autar mata da ya ki yin aure sabida ta ki shi, har wani lokacin ya bige da hawaye, ashe shi ya san danyen aikin da ya aikata mata, alhaki kuma yasa alamarin ya rikide masa zuwa soyayyah ta ce," """In kin duba shekarun sa a wancan lokacin za ki gane sha'awa ce ta sa shi auren ki, irin ta tashen balaga, a irin wadannan lokutan maza kalilan ke tsallakewa hadarin zina ko masturbation. An gode Allah da ya bada sadaki aka daura muku aure bai bi ta wata hanyar ya same ki ba, kin san kuma in a can kasashen da ku ke ne hakan ba wani abu ba ne, na tabbata addu'ar UWA da tsayuwar daren ta a kan sa ne ya sa a ka kare a haka." In kuma da ace yayi raping dinki ne ba auren a can Jamus yadda suka dauki rape case da muhimmanci fiye da kasar mu hukuncin sa a shariance mai girma ne. Banda hukuncin da yafi na kowanne wato na lahira. "Amma a addinance mijin ki bai aikata haramun ba tunda a wani kaulin karbar sadaki na nufin amincewa, but zamu kira abun deviance tunda ya saki kyakkyawar koyarwar sunnah. Ayar da tace matan ku gonakin ku ne bata nufin ku afka musu babu dan aike babu amincewar su. (Allah shine mafi sani)" "Don haka don Allah don Annabi Rahinah ki bar wannan ya shige daga zuciyar ki, na yarda Habibu yayi laifi kuma na tabbata duk da bai gaya min ba a halin yanzu da girma da hankali suka game jikin sa yana ta nadama, ki dubi Allah kani na ya ci darajar aure da ta alfarmar ya biya sadaki, ki ba shi dama ki ga irin repenting din sa." "Allah Ubangiji muna masa laifin da ya fi wannan, amma kullum cikin afuwanta mana yake in mun nemi gafara. Allah ya ce ka yi wa musulmi uzuri sau sabain kafin ka kamashi da yi maka laifi, ki yi masa uzuri da tsoron Allahn da ya ji bai nemeki da zina ba a inda yake da duk wata dama ta samun hakan." "Maimakon haka sai ya alkinta ki a dakin aure domin ya zama garkuwa kuma suttura a gare ki. Ki yafe masa Rahinah, ba don ni ba, ba don shi ba. Ki duba albarkar dan da Allah ya ba ku a sanadin hakan ki yi hakuri, ki sa a ran ki kaddarar zuwan Abdallah duniya ne ya janyo auren naku ma gabadaya""." "Rahinah ta sa habar zanin ta tana share hawayen ta cikin shessheka, ta ce," """Na hakura Aunty, wallahi daga yau na yafe masa, ba zan kara tada zancen nan ba""." "Aunty Badiya ta rungumota jikin ta. ""Na ji dadin jin wannan. Allah ya yafe miki ke ma, tare da mu bakidaya, da iyayen mu da suka kwanta dama. Kuma ki nemi gafarar sa kan hakkin sa da ki ke ta dannewa ba tare da ya san me ye hakikanin matsalar ki ba." "Yanzu ai Rahinah zamani ya ci gaba, bayan psychological trauma na abinda ya faru a baya akwai magunguna na zamani da na gargajiya da zasu gyara wannan matsalar, baa barin irin wadannan kananun matsalolin sakaka su hana zaman aure armashi, tuni ake maganin su." "Mostly cutar sanyi ita ke kawo karancin sha'awa, akwai magunguna na gargajiya da na Bature wadanda za su daidaita sexual behaviour din ki, musamman na kasashen Indonesia da Asia." "Nan Africa ma kasashenmu irin Nijar, da garuruwan Sokoto da Katsina suna sarrafa su don amfanin ma'aurata. Na yi alkawarin kawo miki wadanda za su daidaita wannan sabanin." "Shi kuma Habibu ki ba shi dama, ki kwantar da hankalin ki da shi, don ta haka ne kadai za ki gane ya canza ko bai canza ba. Amma kina ta rikici da shi kullum a kan Da, yaushe ki ka san yadda yake in bed a yanzu? Bana ko tantamar har da bakin cikin hakan yake tunzura shi yake tono abin da zai sa ku hau sama ku fado a kan yaro, wanda babu ruwan sa. Maza a wannan fannin basu da ragowa Rahinah kuma ba sa uzuri." "Dubi yadda walwalar Abdallah ta canza, amma ba ku kula ba, kun fi maida hankali ga tonon juna babu gaira babu dalili, yaro na ba haka yake ba, duk kun canza min shi. (He is healthy and energetic) kan ya zo hannun ku""." "Murmushi ta yi, a ranta ta amince ta karbi duka shawarwarin Aunty Badiya, da niyyar za ta ba shi dama ta gani ya canza ko bai canza din ba?" "Idan ta yarda ya canza din, sannan ne ita ma za ta yi amfani da daya shawarar ta Aunty, wato yin amfani da taimakon da za ta kawo mata." "Tare suka shiga kicin da Aunty kamar kanwar miji ba Yar miji ba. Girki na musamman suka shirya suka aza a dining, sannan suka yi wanka suka yi sallah, suka zauna a falo suna kallo suna jiran dawowar sa." "Amma sai waya ya bugowa Aunty ya ce, ba zai samu dawowa ba, ya wuce Lagos. Ran Aunty ya baci ta hau fada, ""Haba Habibu? Wannan wacce irin rayuwa ce? Da da yanzu da ka ke shawagin ka duk inda ka ke so babu notice din kowa da yanzu da ka aje iyali daban." "Kada ka kara tafiya wani gari ba tare da cikakken sani da cikakkiyar sallama da iyalin ka ba, this is sheer nonsense"". Murmushin da ya yi har ta cikin wayar ta ji sautin sa. Ya ce," """Maman Musaddiq ke nan! Matar da ta ke son ka, ta kuma damu da kai ita ke damuwa da zaman ka a gida, sometimes gara ma ka tafi inda ayyuka za su mantar da kai cewa ka aje iyalin. A bar kaza cikin gashin ta, amma 'yar ku duk ilminta na nasara ne kawai, tana bukatar training na UWA, a kan zaman aure saboda goyon Kaka ce..."" Aunty ta ce, ""Na sani Habibu, kuma na yarda da kai, as far as I'm concerned now zan yi iyaka kokari na a kawo karshen matsalolin nan duka, idan har ka bar maganar auren da ka rakito""." """Kun makara Aunty, its too late! Don har na samu mata a Bidda mun daidaita da Yayan ta yanzun nan, wanda tare muke da shi a Transcorp Hilton, in na dawo zan je Biddan in ganta ku kai kudin aure. Sunan ta Zeena""." "Ya kara da cewa, ""Kada fa ki damu, ba zan hada ta gida daya da 'yar ku mai halin mutanen farko ba, ko don kada ta lalata min tarbiyyar ta da rashin sanin darajar aure""." "Aunty ta ce, ""Yaa Salam! Habibu me yayi zafi? Ina raba ka da matan zamani, wallahi Allah duk wadda za ta aure ka a halin yanzu ba soyayyar Allah ba ce, abin hannun ka ta ke hange, ka fara dawowa gida tukunna ka bamu wata uku, daga nan in komai bai canza ba, na yarda ko uku za ka karo ka yi ta karowa""." Bai san sanda ya ce. "''Wata ukun zan kara nan gaba babu mace? Ai sai dai in mata sun kare a duniya ne. In ba za ki hado min lefe ba Maman Musaddiq ina da masu hadowa fa. Wannan da kudi na ma zan hada, in wancan gudunmawa ki ka ba ni don ki san cewa I'm serious""." "Da ta ci gaba da turzawa kan sai ya bar maganar karin aure ya dawo gida tukunna, in ya so nan nan da wata uku sannan ya sake tado maganar (hausar ta zuwa lokacin ya ga irin canjin da aka samu sun daidaita da Rahinah), sai ya ce mata," """Maman Musaddiq, bana jayayya da ke kin sani, amma yau kam, na yi." "Ba zan kara sati biyu babu matar aure ta hakika a gida na ba. Ita 'yar ku tana Abuja, ita Zina tana Lagos ba shi ke nan ba? Kowacce ta zauna da irin halin ta da irin tarbiyyar ta a inda ta ke. I can handle them both""." "Aunty Badiya sai ta kashe wayar ta, ganin Rahinah na hawaye. Bata san bakaken maganganun da zai cigaba da antayowa ba in ta cigaba da sauraron sa. Sabida Rahinah na jin komai." "Duk abin da suke fadi a kunnen ta ne, don Aunty a fili ta saka wayar don dai Rahinah ta ji ta kara sanin matakin da za ta dauka." "Washegari suka juya zuwa Kaduna. Ta ce nan da kwana uku za ta turo Musaddiq ya dawo ya kawo sakonnin nata, za ta gaya mata (Procedures) din ta waya. Kada kuma ta yi masa maganar auren da ya kafe a kai, ta rabu da shi." "Ita kanta Aunty ta lura Rahinah ta yi sanyi, ta kuma yi laushi, ko magana ba ta iya yi sosai. Alamu ne na TA HUCE DAGA FUSHIN TA." "A daren ranar da kyar ta iya yin barci. Washegari ba ta kai Abdallah makaranta da kanta ba, ta sa direban sa ya kai shi, tunda ya nuna ba ya son fitar tata kai Abdallah makaranta. Ita kuma daga yau duk abinda Habibu bai so ta daina shi duk son ta da abun kuwa." ***** "PACE-SETTERS COLLEGE, WUYE, ABUJA T" "sananin kulawa irin ta malaman wannan makaranta ya sa suka gane canzawar yaro Abdallah Nahuche. In ana karatu ba ya fahimtar komai yanzu, sannan in an fita break sai ya daina fita sai dai ya kwanta a kan tebir ya yi shiru." "Performance din sa na contineous assessment very poor. Haka walwalar sa cikin yara 'yan uwan sa ta karanta. Abincin da ya zo da shi haka yake komawa da shi ko ya zubar, don kada Rahinah ta gani ta yi masa fadan maiyasa bai ci ba." "Mrs. Easther Dekini wato classmistress din su ita ce ta lura da wadannan sauye-sauyen nasa, Mrs. Dekini sai ta hau jan yaron a jiki da wayo da tambaya tana son jin abin da ke damun sa. Rannan ta kawo katuwar ball ta ba shi, ta ce ya tashi ya shiga cikin yara 'yan uwan sa su yi wasa, sai ya bi ta da ido bai ce komai ba." "Mrs Dekini ta zauna kusa da shi a kan desk din sa, ta ce, ""My dear Abdoulayi what's bothering you? Ka gaya min na yi maka alkawarin ba zan gaya wa kowa ba""." "Yaron sai ya kama kuka. Ya yi kukan sa mai isar sa har yaba uku lada. Ta yi ta lallashin sa har ta samu ya yi shiru. Ta bude masa abincin sa, amma sai ya ce mata a'ah. Sai Daddy da Mummy sun daina fada zai dinga cin abinci." Ba ya jin dadi kullum suna fada a kan sa. A matsayin ta na malamar makaranta kuma mai ilmin psychology nan ta ga symptoms na kamuwa da depression a tare da shi. "Da aka kada kararrawar tashi ya mike ya dauki jakar sa zai fita, kawai sai ya yanke jiki ya fadi, wata irin kumfa na fita daga bakin sa." "Yara 'yan uwansa suka hau ihu suna fadin, ""Abdallah ya fadi"". Wanda hakan ya janyo hankalin malamai a kan sa. Lokacin direban sa bai iso ba, don haka a motar makarantar aka wuce da shi asibiti, sannan aka kira lambar Habibu aka gaya masa yaron sa yana National Hospital." "Da direban sa ya je daukan sa ne a ka gaya masa an tafi da shi asibiti ba lafiya. Ya tambayi wane asibiti ne, aka gaya masa. Da gudu ya dawo gida ya sanar da Sahura don ta sanar da Rahinah." """Abdallahn da ya fita lafiya kalau?""" "In ji Rahinah, cikin dimauta da gigita, irin wadda ba ta taba yi a rayuwar ta ba. ""Wallahi kuwa dai sun ce faduwa ya yi haka kawai""." "National Hospital ba bakon ta ba ne, don haka kai tsaye (emergency paeditric unit) ta nufa gudu-gudu sauri-sauri har tan cin karo da mutane. Likitoci uku ta samu a kan sa, sun rufu a kan sa. Domin saita bugun zuciyar sa da ke yi rapidly. Wajen awanni biyu suna kan yaron kafin a samu kan sa, a kuma maida shi aminity." "Awanni biyun da suka kasance tamkar shekaru biyu a idanun Dr. Rahinah Omar, domin ta gama sakankancewa dan ta Abdallah ba zai tashi ba." "Sun samu sun ba shi dukkan taimakon da ya dace sun masa allurar barci a karshe, yana ta barcin sa sadidan, ana masa karin ruwa kansa bisa cinyoyin Rahinah sai sharar hawaye ta ke yi babu kakkautawa, wasu na korar wasu." "Da sanyin safiya Habibu ya sauka a Abuja domin boarding flight ya biyo daga Lagos. Kuma ko gidan sa bai biya ba daga filin jirgi sai National Hospital afujajan da shi, domin zai iya cewa wannan ne karo na farko da aka ce Abdallah ya kwanta a asibiti a kan lalurar da bai san mece ce ba." "Yana yin ciwo sama sama amma bai taba kaiwa ga kwanciya ba. In ka ce tashin hankali ga Habibu, to daya kenan domin kuwa lokacin da aka kira shi a kan maganar, meeting yake yi da ma'aikatan sa duka na Nahuche Hotel Lagos amma sai cewa ya yi," """Excuse me...!""." "Daga haka bai kara cewa komai ba. Ya tashi ya fita da sauri, sai Rasak ya bi bayan sa, ba su tsaya ko'ina ba sai filin jirgi." "Cikin rashin sa'a jirgin Abuja bai jima da tashi ba a lokacin, sai kuma wanda zai tashi sha biyun dare, amma haka ya zauna a lounge din bai koma gida ba, don gani yake in ya koma za a kira shi kawai a ce babu Abdallah." : *SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI 07030137870 NA HUCE* PAID BOOK "Jiran lokacin tashin boarding flight din da ya zame wa Habib Nahuche tamkar jiran ranar busa kaho, finally, jirgin ya zo ya kuma dauko su zuwa Abujan, sun bata lokaci sosai don sai shidda na safe suka samu baro filin jirgin zuwa cikin gari, daga nan zuwa National Hospital." "Rahinah ba ta son tuno abin da likitan da ya jagoranci duba Abdallah ya fada mata, Abdallahnta is too young da samun wannan lalura, don haka yanzu ma da suke zaune su duka a gaban sa, ita da Habibun, ya kuma maimaita wa Habib Nahuche abin da Rahinah ta rigaye shi ji, Habibu bai san sanda ya juya ya kankame Rahinah ba." """Depression and Anxiety Disorder, sannan zuciyar sa ta fara tabuwa." "Daga bayanin da Mrs Dekini ta makarantarsu ta bayar sanda aka kawo shi, mun tattara mun gano musabbabin matsalar sa." "Ya dade yana ganin iyayen sa cikin halin da ba ya so. Me ya sa ku ke yin abin da zai daga masa hankali a gaban sa? He's too young da daukar matsalolin ku. Kwakwalwar sa karama ce, you all have to pay for that"". In ji likitan cikin bacin rai da matsanancin fushi." "Rahinah ba ta san sanda ta daddage ta ture Habibu da ya kankame ta ba, dukkan su jikin su rawa ya hau yi. A fusace ta ce." """Duk ba kai ka jawo ba? Sau nawa zan gaya maka ka daina hantara ta a gaban sa, ka daina daga min murya a gaban idon sa?""" """Really? Ni na jawo ko ke ki ka jawo? Do you have the guts na fadar hakan? Shekara goma bai san ki ba sam sai yanzu, ina ya wani damu da ke har haka? Ciwo ne kawai daga Allah""." """In ma ba ku kuka jawo ba you all contributed immensely to it"". In ji likita Mansur. Yana buga tebirin gaban sa. Cikin kuka Rahinah ta ce," """Tun farko ai kai ka fara poisoning mind din sa, da abin da shekarun sa, tunanin sa ba su isa ya gane, ko zuciyar sa ta dauka ba." "Ni kokari na kullum shi ne ya saki jiki da ni kawai, ya dauke ni mahaifiya ban taba zaunar da shi na gaya masa laifuffukan ka ba, amma kai hum!! Allah kadai ya san iya abin da ka gaya masa, ban taba gaya masa cewa ka yi min wata rashin kyautawa ko guda daya ba""." "A fuskar sa akwai nadama tsantsa, duk da haka bai yi admitting gabadaya ba. Hararar ta ya yi ya ce. ""Amma ai da kunnen sa yana ji kina min Allah ya isa in na debi abincin ki. Kuma ya gaya miki ba ya so""." "Dramar ta su sai ta koma baiwa likita Mansur dariya, wadannan wadanne irin iyaye ne? Gasu duka educated and matured, amma suna behaving kamar yara." "Haka suka yi ta mai da wa juna martani ba kakkautawa, likita Mansur na kallon ikon Allah. Suka yi suka gaji kamar zasu baiwa hammata iska, kuma a karshe suka bar ofishin sa zuwa dakin da yaron ke kwance a Aminity. Rahinah na hawaye." "Bayan ya gaya musu a yanzu dai Abdallah yayi kankanta da shan antipsychotics, counselling yake bukata daga gare su iyayen nasa da sauran clinical treatments a nan asibiti, wanda zai kwantar masa da hankali ya koma cikin hankalin sa." WA KE DA LAIFIN? "Habibu da Rahinah sun tambayi kan su wannan tambaya har babu iyaka. A lokacin da suka tasa Abdallah a gaba suna kallo. Ya tashi daga baccin sai kallon ceiling yake, yana mamakin a ina yake haka? Shi da yake cikin ajin su? Kwana daya kacal duk ya rame." "A tare kuma a sukwane suka isa gaban gadon sa har suna hada baki wajen tambaya. ""Abdallah ka tashi?""" "Ta zauna tana matsar kwalla rike da hannun sa, yayin da Habibu ya zauna daidai kafafun sa ya dauki kafafun ya aza bisa cinyoyin sa yana matsa masa su sannu a hankali." """Sannu Abdallah na, Daddy is here, ba zan kara tafiya in barka ba Abdallah, duk inda za ni da kai da Mummy zan tafi." "Mummy ai za ki bi ni Lagos ko?""" Da sauri Rahinah ta gyada kai idanun ta a kan sa tana kakalo murmushin dole. """Sosai ma Dad, kafar ka-kafar mu ni da Abdallah, ai mun daina fada tuntuni ko Daddy? Abinda yasa ma ban bi ka PortHearcourt ba sabida makarantar Abdallah ne""." Ta karasa fada tana gallawa Habib harara ganin Abdallah ya lumshe idanun sa yana sauraron su. "Habibu ya ce ""ni ai na manta yaushe rabon mu yi fada, kin ga yau har zobe na sayo miki, yana mota in mun koma gida zan ba ki, ko kin fi so in saka miki da kai na?""." "Likita Mansur na ci gaba da auna yaron yana jin su yana ta dariya a cikin sa. Iyaye da yawa ba su san cewa zaman lafiyar su ko akasin sa na affecting yaran su psychologically and morally ba. Daga Habibu har Rahinah babu wanda ya taba kawo wa ran sa wai Abdallah yana lura da abin da suke yi, yana kuma ajiye abin a ran sa." "Nan suka wuni, kowanne da irin kulawar da yake yi wa Abdallah, a lallai sai sun nuna masa jiya ba yau ba, lafiya suke zaune. Amma duk sanda suka hada ido sai Habibu ya balla mata harara. Itama ta rama." "Mr. Atiku ne ya kawo musu takeaway daga (Dominos) bayan azahar, suka ci tare a kan gadon Abdallah suna ba shi a baki suna masa hira, sai ga Nene da Sahura sun turo kofar sun yi sallama sun shigo, Sahura rike da basket din abinci. Rahinah kunya kamar ta nitse a wurin. Domin sun bararraje akan gadon ita da Habib sun sanya dan a tsakiyar su kamar zasu maida shi ciki. Ta yi maza ta diro daga gadon tana yi wa Nene barka da zuwa." "Da sauri Nene ta iso jikin gadon ta kama hannun Abdallah ta ce," """Sannu Abdullahi, me ke damun ka? Dazun nan Sahura tai min waya wai duk kuna asibiti an kwantar da Abdallah"". Rahinah da Habibu aka rasa mai bada amsa domin duk sun karaya, sai Habibu ne ya yi ta maza ya ce da Nene Balki, ""Sun ce Anxiety ke damun sa""." "Nene ta yi salati, ta ce, ""Depression and Anxiety ba ciwon manya bane, ina Abdallah ina damuwar da za ta sa shi zama cikin Anxiety? To ikon Allah ya fi ga haka, ina fatan an dauki duk matakin da ya dace?""" """Sun yi iya kokarin su, amma sun ce, counselling ya fi bukata a kan kwayar magani sabidda karancin shekarun sa, sai Therapy da zai karba na sati biyu""." "Zuwan Nene ya sa dole ya fita ya bar musu dakin, masallacin asibitin ya tafi don yin sallah. Nene Balki bakin ta bai yi shiru ba, sai kakabi ta ke kan me ya hada Abdallah da anxiety? Daga baya ta kira Aunty Badiya ta gaya mata." "Badiya bata yi mamaki ba ta ce, ""Allah ya ba shi lafya, amma ai su suka jawo masa Nene, Habibu da Rahinah, sun ki yarda Annabi ya faku. Kullum kananan yara su ke maida kan su. In suka sabauta dan ai shi ke nan sun huta""." Ta soma kwallah saboda ba karamin so ta ke yi wa Abdallah ba. "Uncle Usman yana garin don haka da daddare ya zo duba Abdallah. Nan suka hadu da Ambasada a parking lot suka jera zuwa ciki, suna tafe suna hira wadda duk ta Habibu da Rahinah ce, da dan su Abdullahi. Maganar aikin Rahinah ya roki Ambasada ma ya saka baki Habibu ya bar ta ta koma. Ambasada ya ce," """A'ah Usman, ka barshi ya yi cikakken iko da iyalin sa, in ya amince don kan sa, fine, in bai amince ba ta hakura babu rashin ci babu rashin sha, we are not to be interfering tunda dai mun yi mai wuyar mai kuma muhimmancin""." "Sun duba Abdallah sun jajanta kafin su bar asibitin su duka. Direba ya maida Sahura gida, dakin daga Rahinah sai Abdallah." """Mummy zan sha Kelloggs"". Ya fada kan sa na bisa cinyar ta." "Ta shafa kan sa ta ce, ""To Abdallah bari Daddy ya zo sai ya sayo ko?"". ""Ki masa waya mana! Yanzu nake so!""." "Jiki na rawa ta zaro waya ta hau zakulo lambar sa, ashe ba ta yi saving ba, kawai sai ta shiga inbox din ta inda ta ga sauran sakonnin sa rututu da ya turo mata yana PortHearcourt, ba ta ko kai ga budewa ba, balle ta goge. Kawai sai ta yi sha'awar yau ta bude duka sakonnin Habib ta karanta da nutsuwa kafin ta kai ga kiran sa, don ya kawo sakon Abdallah." Ga abin da Habibu ya rubuto wa Rahinar sa. "1- ""Kin yi tasiri mai yawa cikin rayuwata, tasirin da a tarihin soyayya a rayuwar Bahaushe ban ga irin nawa ba RAHINAH. Kin jijjiga rayuwa ta tsayin shekaru goma da doriya, amma duk da haka ban fidda rai watarana na" "zuwa da zamu koma daidai ba, har mu zama ma'aurata ababen misali. An ce abinda hakuri bai bayar ba rashin sa bai taba bayarwa, zan ci gaba da hakurin nan na wasu shekaru goman a gaba su zamo (two decades). Watakila sai a shekarun furfurata ne zan ci ribar hakurin nawa?!""" "2- ""Ni Habibu ina mai ba ki hakuri Rahinah, da guiwowina a kasa.. a bisa duka laifuffukana na baya, wanda na sani da wadanda ban sani ba, irin hakurin da ban san yawan sa ba, ban san adadin sa ba, ban san iyakar sa ba." "Na yi kuskure ina mai rokon a ba ni dama in gyara shi, ko da wannan ce dama ta karshe a gare ni. Na yi alkawarin zan goge tabon AUREN KWANA BAKWAI of the past Decade in only one night. idan kika bani dama!" "Nayi alkawarin zan biya bashin soyayyar shekara goma da muka yi missing in only one night""." "A hankali Rahinah ta wani lumshe idanun ta, kafin ta kai ga bude su daga lumshewar da ta yi musu, Habibu ya bude kofar dakin ya shigo da sallamar sa ba tare da ya san me ta ke yi ba." "Sai ta kasa bude idanun har ya iso jikin gadon yana tambayar Abdallah," """Ya ya dai apple of my eyes?""" "Abdallah ya ce. ""Mummy na ce ta kira ka ka kawo min kelloggs tun dazu. I guessed she don't have your phone number, (na fahimci bata da lambar wayar ka), kai ma ba ka da lambar wayar ta?""" "Da sauri ta bude ido ya sauka cikin nasa, duk suka kalli juna a tsorace. Habibu ya ce, ""Inquisitive Abdallah I have your mother's phone number, amma a nan (ya nuna saitin zuciyar sa) in ba ka yarda a yanzu in karanto maka ka ji"". ""Daddy na san ba ka karya, Mummy ke fa? Kina da number din Daddy na?""" "Rahinah ta rasa abin da za ta ce, kafin ta tuna Abdallah is now a sick person, a mental patient wanda abin da yake bukata kawai shi ne a yi masa abin da zuciyar sa ke so, wanda ba komai ba ne sai shiryawar su." """Abdallah, I've your Daddy's phone number, yanzu ma ya turo min message da ita, kana so ka gani?"" ""A'a, ki dai karanto min in ji""." "Da sauri ta dubi Habibu da idanun neman agaji, shi kuma ya kau da kai ya yana 'yar dariya, ya san yau Abdallah ya saka ta a kwana." """Abdallah zai fi kyau shi da ya turo sakon,ya karanta maka ko?""." "Habibu ya ce me ye a cikin sakon banda I really-truely LOVE YOU? And I promised a changed person?""" "Ya fada yana kallon cikin idon ta, kwayar idanun sa sun kada zuwa love colour bakidaya, wanda hakan yasa Rahinah jin kunya mai yawa, ba shiri ta hau rufe fuska da tafukan ta kamar wasu saurayi da budurwa, domin Habibu ya ki dauke rinannun idanun sa a kan ta, wanda hakan yasa Abdallah tuntsirewa da dariya yana fadin." """Mummy ki bude idon ki, we love you!""" Likita Mansur ya turo kofar dakin ya shigo yana clapping hannayen sa. Don tun daga waje yake jiyo dariyar Abdallah. """Abdallah and parents, what a good scene? Ina fata sun daina fada Abdallah?""" "Abdallah ya yi wani iri da fuska ya ce, ""Doctor sun daina ka sallame mu mu koma gidan mu, kuma ka roke ta ta karanta min text din da ta ce Daddy ya turo mata daga PH""." Dariya likitan ya yi yana shafa kan yaron. Sosai ya ji yana son sa sabida wayon sa. Hes really smart. "Ya ce, ""Abdallah this is their secret, ka ji? (Wannan sirrin su ne). Ba ruwan ka da abin da Daddy yake rubuta wa Mummy a waya, what matters most... (abin da ya ke muhimmi) shi ne su daina fada saboda ba ka so, su zauna lafiya har abada for you to stay healthy""." "Ya gyada kai cikin fahimta, likita ya ce, ""That's my boy. Amma ba zan sallame ka yanzu ba Abdallah sai nan da sati uku, in na tabbatar (heart beat) din ka ya koma normal""." "Bayan fitar likitan, Habibu ya dubi Rahinah ya ce," """Abdullah abin da na tura wa Mummy ko ni ban san me na tura mata ba. I just texted her to check on you sanda ina PortHearcourt""." """Ina fatan ta ba ka amsa?""" """Sosai ma, na ba shi amsa tun a lokacin""." "Habibu ya dago lumsassun danun sa ya yi mata wani irin kallo, da ya sa bakidaya ta nemi nutsuwar ta ta rasa ta rikirkice, sabida ita ba gwanar karya bace da ta yi ake gane ta. La shakka da a tsaye ta ke ba a zaune ba, ba abin da zai hana ta faduwa kasa sabida yadda Habib yake hukuntata da sexy idanun sa." """Mai karya dai, dan wuta!""." "Rahinah ta juya kai gefe tana 'yar dariya a kan kalaman sa, ba tare da ta shirya yin hakan ba. Dariyar da ta shagalar da Habibu a cikin kallon ta da duk ya bi ya maida Rahinah unease, ta soma tunanin abin da zai tada ita daga gadon. Gashi kan Abdallah na cinyoyin ta, shi kuma yana zaune a daidai kafafun sa. Abdallah ya ce," """Zan sha ruwa""." "Tun bai rufe bakinsa ba uwar da uban suka mika hannu domin dauko masa a kan (bed-side drawer), hannun ta ya riga na Habibu sauka a kan gorar ruwan Faron, kasancewar ta fi shi kusa da lokar, sai hannunsa ya sauka a kan nata." "Another unbearable chemistry like electrical shocking ya bakunce ta, wanda ya sa ta saurin dagowa ta dubi maigidan ta Habib Nahuche, sai aka yi sa'a idon ta ya sauka cikin nasa." "Habib sai ya samu kansa da cure yatsun ta da ke kan robar Faro a cikin nasa hannun, wanda hakan ya sa Rahinah saurin runtse idanun ta. Tana karbar wasu sababbin pleasant feelings a zuciyar ta da ta kasa gane ko na mene ne, ko daga ina suke yunkuro mata." "Habibu ya yi azamar dauke hannun sa daga kan nata sakamakon cewa abinda ya bakunce ta shima kwatankwacinsa ya ji, sannan ya dauki ruwan ya bude wa Abdallah." "Kunya ta ji sosai kan irin reaction din da ta nuna. Kawai daga Habibu ya rike hannun ta. Dare ya fara yi sosai, dakin ya yi shiru domin Abdallah ya yi barci. Su kuma kamar masu ciwon baki sai zukata da ke adungure a cikin kirjin kowannen su." "Rahinah na so ta ce ya tafi gida, tana so ta gyara gadon ta kwanta, ta rasa da bakin da za ta gaya masa hakan. Ya tattara hankalin sa kacokam ya dora a kan wayar sa, ga dukkan alamu chatting yake yi, kawai sai zuciyar ta ta gaya mata da mace ne, bazawarar da yake nema in ba haka ba da wa zai ke chatting karfe goma sha biyun dare? Kawai ta ji tsuka (tsaki) ya kubuce mata. Wani matsanancin kishi ya zo ya lullube ta." "Habibu ya ji tsakin, amma bai zaci nasa bane, sai ya dago shanyayyyun idanun sa ya dube ta da idanuwan bidar bayani," """Shin tsakin nan nawa ne ko na wani ne daban?""" "Juyar da kai ta yi gefe, ciki-ciki ta ce, ""Don Allah ina son filin gadon, zan kwanta kusa da Da na. It's almost past twelve yanzun""." "Kin dauke ido ya yi a kan ta, wanda hakan ya sa ta ji duk ta takura. Ya ce," """Ni kuma yau till down zan yi a zaune ina kallon kyakkyawar fuskar bafulatanar mata ta Rahinah Omar. She's indeed a heroine. Domin a rayuwa ta ban taba ganin mace mai aji, mai kullata, rashin afuwa, rashin yafiya da kafaffiyar zuciyar ta ba." "I wanted to ask Rahinah since, shin zuciyar ta ta dutse ce? Ko kuwa kurmar zuciya gare ta? Shin Rahinah ke a wurin ki lokaci ba ya maganin kullata, a tunani na time heals everything! It's almost a decade and above, amma har gobe Rahinah na nan a yadda na san ta." "Ni Habibu Mustapha Nahuche, dan adam ne kamar kowa, mai tarin nakasu (flaws), kuma mai zuciya da gangar jiki irin na kowanne lafiyayyen dan adam." "In haka ne ta ya ya ba zan kasance cikin masu aikata kuskure ba? In ankara, in so gyarawa, amma a hana ni damar gyarawar?" "I'm not saying all these to own your body, I'm saying it because I want you to know that I'm human, not a saint, or a Prophet (ba ina fadar duka wadannan don in mallaki jikin ki da zuciyar ki bane, ina fada ne don ina son ki san cewa nima mutum ne kamar kowa, dan adam ajizi, ba waliyyi ba ba kuma Annabi ba, wadanda ko su ba su tsira da aikata kuskure ko sau daya ne a rayuwar su ba)." "Allah shi kadai yake PERFECT a komai Rahinah. I'm saying SORRY for all that happened, a decade ago, from the bottom of my fragile heart." "Sorry for all the grievances and inconveniences that I caused to you Dr. Rahinah, na yi miki alkawarin zama na soyayya da farin ciki mai dorewa har zuwa karshen rayuwar mu. I promised to be far-away from your body tunda" "wannan shine babban abinda ya janyomin bakin jini a wajen ki""." "Da sauri Rahinah ta shiga girgiza kai, ammma ta kasa cewa komai, domin kalaman dake fita daga bakin sa a yau bata taba zaton su ba. Anya Habibun ta ne? Her ex Habibu ne? ko wani mai tsananin kama da shi ne??" "Bata fita daga wannan mamakin ba, Habib Nahuche, ya sake gigitata da sabon mamaki. Ta hanyar kamo hannayen ta ya rike su tsam cikin nasa." """Rahinah KIN HUCE?""" "Tunda ya fara maganar zuciyar ta ke luguiguita tana kakkaryewa tana kara HUCEWA, domin ta yarda da dukkan kalaman da ke fita daga bakin sa, haka suke har kasan zuciyar sa." """Ni na ce maka ina fushi ne? To Habibu NA HUCE"". Ya yi mata kyar da ido." """In ba fushi ki ke ba, me ya hana ki biyo bayan mu? Ban taba tunanin zan isa Nigeria lafiya ba tare da kin tara min mutane a kaina ba da sunan na sace miki Da, bayan nan ki ka dawo ki ka kama ayyukan gaban ki ko sau daya ba ki taba tunanin ki neme mu ba." "In ni ba ki neme ni ba don na yi miki laifi Rahinah, which I'm sure daga baya kin huce kin yi kewata yadda na rayu cikin kewar ki, abinda kike nunawa a zahiri ba haka ba ne a zuciyar ki ba, ai kya nemi dan ki ko? Ki binciki rayuwar sa ko lafiyar sa? Ki ga shin ya ya muke rayuwa? Amma ko sau daya! Baki yi hakan ba." "In gaya miki gaskiya wannan shine babban abinda yayi min ciwo bayan rabuwar mu har fiye da takuramin sakin da kika yi. Kullum a tunani na da tsinkaye na shine zaki dawo da kan ki ki nemi mu koma saboda dan mu, a yayin da kika yi achieving goals din ki. Sai kika nuna min kashi ma ya fi mu daraja ko bayan actualizing goals din""." "Ba ta san sanda ta yi dariya ba, ta ce, ""Ko? Bari in gaya maka abin da ba ka sani ba..." Duk wani step further da ka taka a rayuwar ka bayan dawowar ka Nigeria ina bibiye da shi. I'm the first to send an appreciation message to BBC HAUSA a shirin nan na DOMIN MATASA.... I'm the first to send an appreciation message zuwa ga jaridar NEW NIGERIA a kan shirin 'A ROLE MODEL NIGERIAS HOTELS OWNER.... "Ni ce ta farkon aika sakon jin dadin shirin ""The Legend of the Sahara... HABIBU NAHUCHE na gidan Radiyon Jamus a shekarun da suka gabata. ""." Sakin baki ya yi galala! Yana kallon ta domin ta gama mamakantar da shi. Ta shammace shi da abin da bai taba sani ba. """Abin da kawai ban sani ba a kan ka cikin shekaru goman shi ne, kasancewar ka kanin Aunty Badiya, wadda nake tare da ita sama da shekaru shidda, tun zuwan mu daga Jamus na farko lokaci da na hadu da dangi na." "Had I know ita ke rike da Junior kai ma ka san da tuni wani labarin ake ba wannan ba""." "Tasowa ya yi daga inda yake zaune, ya zo ya durkusa a gaban ta daga gaban gadon, ya dora tafin hannun sa saman tafin kafar ta." """That is what I don't know either. Had I know da tuni ni ma wani labarin ake ba wannan ba"". 'Yar dariya ta subuce mata jin yana yi mata tausa a kafafun a hankali har da tafiyar tsutsa . Ta ce," """Da wane labarin ake to zuwa yanzun?""" "Yatsun sa biyar ya daga ya wara mata a kan fuskar ta. ""Da yanzu su biyar ne ba shi kadai ba""." "Ta gane abin da yake nufi, wanda hakan ya sa ta murmushi (serene smile) amma sai ta nuna bata gane din ba. ""Su su wa kenan?""" "Ya ce, ""Abdallah da kannen sa mana""." Hira mai ban mamaki da ratsa zuciya ta ci gaba da gudana (heart to heart) wato daga zuciya zuwa zuciya tsakanin Habibu Nahuche da mai dakin sa Rahinar sa. Hira ce irin wadda ba su taba yi a tsayin rayuwar su ba. Ta ba shi labarin duk halin da ta shiga bayan tahowar su. A karshe ta ce. """...And evetually I moved on, kafin na gane rayuwar diya mace bata taba cika cikakka idan babu SOYAYYAR MIJI, sai dai hakan ba ya nufin faduwar diya mace warwas, in dai za ta iya kare mutuncin kan ta ta ribaci lokutan rayuwar ta da neman ilmi da neman lahira." "Sabanin sauran mata da ke bata lokutan su wajen kuka da halin maza na sun musu, sun musu kaza da kaza, har hakan ya taba kwakwalwar su ya hana su cigaba. Ni Rahinah I'm apparently a strong woman, wadda ta dauki goal attainment (self-actualization) da matukar muhimmancin da ya danne soyayya." "Shi ya sa na zauna lafiya kalau, in na ce lafiya kalau, ina nufin fa lafiya kalau...""." "Irin kallon da Habibu ke mata ya sa ta saurin toshe bakin ta tana dariya. Domin kallo ne na karya kike yi, in fact, you are not well at all." "Ya ce, ""Wallahi ba lafiya kalau ki ke ba, sabida ita soyayya barin rayuwa ce, kuma halittar Allah tsakanin Adamu da Hauwa'u." ABRAHAM MASLOW (1970) (psychologist) wanda ya samar da 鈥漈 heory of Self-Actalization. Ya sanya ta cikin "jerin rukunin bukatun rayuwar dan adam guda bakwai, wadanda ba zai iya rayuwa babu su ba (HIERARCHY OF NEEDS THEORY OF MOTIVATION)." MASLOW ya ce; """As long as the more urgent and pressing need is satisfied, another urgent need will emerge and become operative, and a currently satisfied need will become unimportant and underestimated and no longer controls or dominates behaviour...""." "-(Abraham Maslow, 1970)." "Dariya ta yi cikin matsanancin nishadi, kace ka tashi da 'Hotel Administrator' ka koma malamin 鈥楶 sychology""." """Ko daya, ni ba ni da alaka da psychology amma na san wannan, na kuma kawo miki misali da theory din ne don ki san cewa, bayan self-actualization din ki ya gamu, dole ki dawo daga baya ki nemi soyayyar miji da ta 'ya'ya (Love and Belonginess Need). Wannan a rubuce yake, sai dai kuma idan Rahinah waliyya ce ba mu sani ba""." """Yanzu ka bar maganar Maslow a gefe, na yarda da kai with no temptation, amma don Allah me ya sa ka aure ni a yadda ka aure ni a Jamus?""" "Ya rausayar da kai ya yarfar da hannu ya ce, ""Only men in mid - twentieth can relate. I have no option a wancan lokacin, in ba so ki ke in kare da raping din ki ba kuma in kare (behind bars) ban da babbar azabar Allah da za ta jiraye ni ranar gobe kiyama""." "Ta kai kyawawan yatsun ta ta rufe fuskar ta, ""Habeeeebu you are too much""." """Har na kai ki? My sweet sixteen my Bafulatana Rahinah Omar Girei. Duk da na sha wahala, ina kuma kan shan ta har yau ina alfahari da wannan gantalallen auren." Ga kyautar Allah wadda bani da tamkar ta (Abdallah). "And by so doing, i then came to realized the worth of a WOMAN, inda na gane abubuwa da dama a kan mata, na gane ba duka mata suka taru suka amsa suna daya ba na cewa su duka raunana ne a kan soyayyah, akwai masu kare鈥檚 elf esteem 鈥฀ din su koda soyayyar zata yi ajalin su, wadanda basu dauki soyayya da namiji shine rayuwar su ba, a typical example of my Bafulatana Dr. Raheenah Omar Girei. I salute!!!." (Ya fada yana yi mata gaisuwar sojoji). Kan ta yayi gingirin-gin. A fili ta ce (cikin shauki). Baban Abdullahi kana fasa mun kai! "Ba maganar fasa kai bace maganar gaskiya ce. Wanda hakan ya kara sawa na girmama ki, na kara daga darajar ki a zuciyar Nahuche." Amma don Allah ina rokon alfarmar daga yau dinnan in tashi daga HABIBU in koma HABEEBEE. "Rahinah sai dariya ta ke. Cikin matsanancin nishadin da bata taba tsintar kanta ba. In wani ne ya gaya mata watarana irin wannan na zuwa, da Habibu Nahuche zai tsaya a gaban ta ya bude baki yayi mata magana mai tsayi har haka za" "ta karyata. Sabida karancin maganar sa. Habibu ya mike daga durkuson da yayi a gaban ta ya koma jikin gadon ya jingina, tare da harde hannayen sa a kirjin sa." "鈥淭 o yanzu dai kin gane ko Maam? Ke da Dan ki ku gyara min waje in kwanta, yanzu zaki ji an kira asubahi bamu runtsa ba, barci nake ji sosai""." """Ai gadon ya mana kadan mu uku Habeebi. Ba ka ganin ba shi da fadi?""" """A haka za mu yi maneji, rayuwa sai da maneji da abunda ka samu. A baya ina na samu wannan alfarmar?." "A hakan suka kwanta. Rahinah a barin dama, Habibu a barin hagu, Abdallah a tsakiyar su, 鈥渟 uch is life my dear wife, yadda ta zo wa bawa a haka ya kamata ya karbe ta"". Ya fada yana gyara wa Abdallah kwanciya, suka sanya shi a tsakiya suka rungume, suna fuskantar juna suna kuma kashe juna da ravishing smile." """This is pure contentment of my life"". Habibu Mustapha Nahuche, ya fada a ran sa yana sarke yatsun kafar sa cikin na Rahinah, wani irin jin dadi na tsirga masa. Rahinah ta rungume Junior da hannu daya, hannun ta daya cikin na Habibu, idanun ta cikin nasa suna yi wa juna kallo na kauna da soyayya." "Da zasu iya, hakika da, sun rike wannan moment din daga motsawa kada gari ya waye, wani abu ya zo, ya gifta a tsakanin su." "Sai ya mika hannu ya latsa makunnin fitila shudiya ta maye gurbin mai haske (dim light), ta cikin dan hasken shudiyar fitilar suke hango kyallin hawayen da ke kwance yana tsatstsafowa cikin idanun kowannen su." "Hawayen so da farin ciki, wanda kwanciyar hankali kadai ya yi sanadin sa cikin idanun Habibu da Rahinah." Tun tana tsammanin Habibu zai yi kalar wani motsi bayan wannan (ya nemi taba ta ko kissing din ta) har ta ji saukar numfashin sa a hankali mai nuna ya yi barci. "Da ace wani ne ya gaya mata za ta kwana gado daya da Habibu watarana ba za ta taba yarda ba. Da dai wani ne ya gaya mata Habibu zai iya kwana gado daya da ita bai nemi komai daga gare ta ba, ba za ta taba yarda ba." "Da asubah shi ya fara tashi sakamakon kiraye-kirayen sallah a masallacin asibitin. Junior ya motsa ya ji an matse shi a gadon sa, sai ya bude ido a hankali ya gan shi tsakiyar iyayen sa biyu. Wani abu da bai taba faruwa ba tun dawowar Rahinah cikin rayuwar su." "Sai ya sa hannu daidai ya rungume kowannen su, ya ci gaba da barcin sa a haka." Habibu da dabara ya zame daga rikon da Junior ya yi masa a hankali ya sauka zuwa toilet wanda ke makale a cikin aminity room din. "Motsin sa ne ya tada Rahinah ita ma, ya fito daure da alwallah. Lokacin ta tashi ita ma ta kunna fitilar dakin. Suka dubi juna sai ta sunkuyar da kanta cikin jin kunya." """Dauro alwallah mu yi jam'i kawai, sai in wuce gida in yi wanka""." "Ta bi umarnin sa, shi ya ja su jam'in suka yi raka'atainil fajr, sannan suka bada faralin asubahi. Suka kara da sallahr nafilah." "Suka yi addu'o'i masu yawa a kan su da zuri'ar su, iyayen su da suka rasu da wadanda ke raye har ma da masoyan su, sannan Habibu ya mike don tafiya gida yin wanka, har ya kai bakin kofa ta ce." """Ka dauko min wani bedsheet din in canza wannan, da man shafawa ta a kan mudubi na"". ""An gama Habeebty, me ku ke son karyawa da shi?""" """Kada ka damu da wannan, Nene da Sahura duka za su kawo"". ""Kwalliya kuma fa? Wace iri za'a yi min? Kalli idanun ki, duk sun jeme""." "Yar dariya ta yi ta ce, ""kai kuwa dan kwalli daya kwal ya tsoka daya a miya aka ce min kwakwalwar sa ta tabu fa! Ai in da akwai abinda yafi jemewa da ramewa duk zan yi su. Allah shine shaida. This the terrible moment of my life bayan na sace shi da kayi 鈥฀." "Habibu ya gyada kai ya ce umh. I can relate, sai son dan kawai aka sani, baa san ta ya zaa nuna masa soyayyar ba. Mu bar wannan zancen. Ka zabo duk kayan da ka ke so in saka a wardrobe dina, ka dauko min turare Yves Saint Laurent a kan mudubi na""." "Ya ce, ""Da kuma mascara da wet-lips ko? Bakin duk ya bushe"" Dariya ta yi ta ce," """Anything that will beautify me Habibi""." "Sai kuma ta rufe ido ta ce, ""kai ma yau ka sako kananan kaya, don in gan ka dan saurayin ka yadda ka ke a Jamus, dan saurayin nan nawa na cikin jirgin 'Boeing' da na rungume cikin rashin sani, wanda ya sanya wa Rahinah Omar, rigar kubuta daga hadarin jirgi""." "Dariyar da Habibu ya yi sai da ta fiddo fararen hakoran sa, ya kada kai ya sumbuci Junior da ke barci. Rahinah ta saki baki da kunci tana jiran tata sumbar har da lumshe idanu, sai ta ji shiru, wayam." "Kafin ta ankara ta ji shi ya kai bakin kofa yana fadin, ""Sai na dawo!""." "Wai kuma sai ta ji duk babu dadi, Habibu na nufin ya daina kai hannun shi jikin ta kenan ko me? Tun zuwan sa ban da a ofishin likita da ya kankame ta saboda razana, ko sau daya bai kai hannu shi jikin ta ba." "Da gaske yake kenan da ya ce ta jika komai nata ta shanye, he is going for a second wife ko me?" "Wani abu da a halin yanzu ta san ko sama da kasa za su hade ba za ta taba yarda ba, (kara auren Habibu) don yanzu ne ta san tana son mijin ta uban dan ta! Tana kuma hakikanin kishin sa." : HAJ. KALTUME HAJIYAR NAHUCHE B "a da sanin Habibu ba, Aunty Badiya ta kira Hajiyar Nahuche ta zayyana mata halin da Habibu da Rahinah suka sanya Abdallah. Lokacin sun yi sati guda a asibitin saura sati a sallame su." """Ki duba ki ga Hajiya, wautar su ta janyo wa karamin yaro lafiyayye irin Abdallah mental instability. A da ina blaming Rahinah ne ita kadai, amma wallahi yanzu na gane Habibu ya fi ta laifi, don shi yake biye mata a matsayin sa na namiji, mai hankali kuma babba sama da ita." Karfe daya ba ya amo. Don haka zan maida yaron hannu na da zarar an sallame shi daga asibiti in ya so su je su haukata kansu su kadai. "Na yi nadamar sa wa ki ba su yaron, ban san shirmen da suke aikatawa cikin gidan su kenan ba sai da na je na gani da ido na""." "Hajiya Kaltume ba ta iya ta ce komai ba, bayan, ""Allah ya kyauta. Allah ya ba shi lafiya""." "Amma can kasan ranta abun ya dame ta sosai, domin tana tsananin son Abdallah. Abdallah dan lelen Hajiya ne. Wunin ranar zungur da abun ta wuni yana damun ta a rai, tana ta sake-sake, ba ta yi niyyar zuwa gidan Habibu nan kusa ba, sabida rike girma da dattijantaka irin nata, amma ta yanke shawarar gobe dole ta je ta gano lafiyar Abdallah." "Ga Hajiya Kaltume ba ta iya sa abu a rai ba, in ta sa abu a ran ta ya yi ta damun ta kenan, wannan damuwar ce ta tada hawan jinin ta ba tare da ta sani ba. Wuni ta yi kwance a daki." "Ta shiga bayan gida da asubahi ta daura alwala duk da yadda ta ke jin jiki, ta dawo kenan za ta shiga daki sai kawai ta zame ta fadi bisa kofar dakin ta. Faduwar da sai gadon asibiti aka nufa da ita gari na dan yin haske da taimakon masu aikin ta." "Habibu da Rahinah, wadanda a ranar ma sun yi kwanan zaune ne cikin rayuwa ta 鈥檋 eart to heart talk 鈥฀, wadda" "ita suke kwana yi duk dare a gadon asibitin Abdallah, wadda a yanzu ta samar da mashahurin kusanci da aminci ga zukatan su. Hatta sallahr asubahi kullum tare suke yin jamin ta a dakin asibitin, sai gari ya waye ne Habibu ya ke zuwa gida ya yi wanka ya dawo." "To yau ma kamar kullum, dawowar sa daga wanka kenan ya shirya cikin babbar shadda getzner mai hasken sararin samaniya, suka tsinkayi wannan mummunan labari na faduwar Hajiya da kwantar da ita a babban asibitin Zamfara da sanyin safiyar ranar a bakin mai aikin Hajiyar wato Larai, wadda ta dau wayar Hajiya ta kira Habib din, bayan ya dawo asibitin daga wanka da ya je ya yi." "Rahinah dai ta ji Habib yana salati, sai kuma ya mike ya hau neman takalman sa da mukullan motar sa bayan ya sanya hular sa a gicciye, ya dau makullin mota, Abdallah na barci lokacin bai tashi ba." """Lafiya Habibi?"" (Sabon sunan da ya farlantawa Rahinah kiran sa madadin Habibu). Ta tambaya cike da damuwa cikin sanyin murya." "Habibu na takawa zuwa kofa ya ce ""Hajiya ce wai babu lafiya, zan wuce yanzu, ki kula da Abdallah please, zan tsaya Kaduna in dauki Maman Musaddik mu wuce Zamfara""." "Cikin damuwa sosai ta yi wa Hajiya addu'a, sannan ta yi masa addu'ar sauka lafiya. Har ya kai bakin kofa zai fita, ta ce, ""Habibi""." "Sai ya dakata, sannan ya juyo yana duban ta da manyan kyawawan idanun sa." "Ta taka a hankali zuwa gaban sa, ta sanya hannu a wuyan rigar sa tana sanya masa maballan da rudewa tasa bai balle su ba, a hankali Habibu ya dan rufe idon sa jin sanyin hannun Rahinah a wuyan sa, sannan ta makala masa links din hannun rigar shi da shima yake a bude. Ta yi kamar za ta sumbace shi, ko me ta tuna? Sai ta ji kunya, ta fasa. Ta yi maza ta ja da baya." "Murmushi Habib ya yi, sannan ya sa kai ya fita daga dakin, ba tare da ya yi mata abinda take so din ba, ya fice yana fadin." """Sai na kira Ummu Abdallah, ki zauna da waya a kusa da ke don in ke jin lafiyar ku""." "Bayan fitar Habibun, Rahinah kasa komawa ta zauna ta yi har sai da ta ga fitar sa, ta ci gaba da safah da marwah a dakin, tana kallon dan su Abdallah da ke barcin sa peacefully. Idan ta tuna kwakwalwar Abdallah yanzu ba daidai ta ke ba, duk sai ta ji ta daina jin dadin komai na duniya." A wani gefen tana jajanta rashin lafiyar Kakar sa don ma ba ta san musabbabin sa ba. Bata san cewa a kan Abdallah bane Hajiya ta fadi. Hajiya Kaltume bata aje kaunar Abdallah anan kusa ba sabida shakuwar da ke tsakanin su wadda ta samo asali tun yana yaro. Ta yi addu'ar ko me yake damun Hajiyar Allah ya ba ta da sauki. "Da Abdallah ya tashi ta yi masa brush ta yi masa wanka, sannan ta sa shi ya yi sallah. Sai ga sallamar Sahura ta kawo musu karin kumallo. Ba jimawa Nene da Ahlan ma suka zo, sai dakin ya yi albarka, nan ta ke gaya musu maganar rashin lafiyar Hajiyar Nahuche." "Nene da Sahura duk suka yi wa Hajiya addu'a, nan suka taya Rahinah wuni a asibitin kasancewar karshen mako ne." ****** "ZAMFARA GALMA UWAR RUFI, KO BAKU SON MUTUM BAKU HWADI!" S "un isa garin su na haihuwa wato Zamfara shi da Badiya dukkan su ba cikin nutsuwa ba. Aunty Badiya ta yi nadamar gaya wa Hajiya rashin lafiyar Abdallah, ta manta shaf da halin ta na sanya abu a rai fiye da kima. Habibu ma ta sha fada a wurin shi kamar shine wan ita kanwar. Da ta gaya masa tana tsammanin abinda ya tada ciwon Hajiya kenan." "Sun samu an ba ta gado a Aminity 'yan aikinta suna ta kula da ita. Amma ganin halin da Hajiya ke ciki ya rikita Habibu, tsufa ne ya hadu da dadadden ciwo da damuwa, sai ya ce da Badiya zai dauke Hajiya ne kawai zuwa Jamus cikin satin nan don ta samu kulawa yadda ya kamata. Ya fi yarda da hospitalization din su fiye da na ko'ina." "Tun a lokacin ya soma tuntubar likitocin ta akan shawarar da ya yanke, duk sun ce ya bar ta zasu iya shawo kan matsalolin ta amma ina! Habibu gani ya ke basu iya komi ba, ba ya hada lamarin Hajiya da komai, a take ya kuma soma shirin tafiyar tasu ta yanar gizo, washegari suka tafi da Hajiya daga Zamfara don shigar da neman visa." "A hanya suke shawarar wadanda ya kamata su tafi da Hajiyar asibiti cewa bai kamata su tafi dukkan su ba, dole daya ya tsaya sabida Abdallah da ba'a sallama ba. Habibu ya ce shi zai zauna tare da Abdallah har a sallame shi, in ya so sai ya biyo bayan su daga baya, Badiya kuma ta ce zai fi kyau su tafi har da Rahinah tunda likita ce, kuma a can ta yi karatun ta ta iya harshen German, she will have more rapport da likitocin can tunda ita Badiyan ba ta iya Jamusanci ba, sannan again Rahinah can play the role of a support doctor ga Hajiya, za ta taimaka dai ta kowanne bangare. (Badiya ta kawo wannan shawarar ne don tana son dinke 'yar barakar da ke tsakanin Hajiya da Rahinah). Don ta samar da 'yar shakuwa da fahimatar juna tsakanin su ko yaya ne." "Ba bata lokaci ya amince da shawarar Yayar tasa, don haka suka bar Abdallah tare da Nene, suka dauki Rahinah a asibiti suka wuce 鈥橤 erman Consulate 鈥฀ har da ita wanda ke a garin Lagos don neman 鈥橦 ospital Visa 鈥฀. Masu abu da abun su, babu bata lokaci cikin sati aka yi musu komai da taimakon Ambassada Shehu, likita ya ki sallamar Abdallah ya ce sai ya gama karbar treatment." "Sahura ce ta hada wa Rahinah kayan da ta ware don tafiya da su Germany. Ta sanya a ran ta in ta samu dama kuma Hajiya ta samu lafiya za ta nemi Aunty Laura a Germany don kawai ta gaishe ta, ko babu komai ita ce silar duk abubuwan da suka faru dasu a Jamus, tsakanin ta da Habibu Nahuche har zuwa inda yau ke motsi." "Tunda ita tayi uwa ta yi makarbiya ta kulla auren su. Auren mai tsohon tarihi da dabaibayin zukata iri-iri. Har aka samu Dan da silar zuwan sa duniya ne ya yi connecting komai. ta wani bangaren, ba ta san dalili ba; a yau sai ta" "samu kan ta tana mai gode wa Aunty Laura, tunda ita ta yi silar dukkan kaddarorin su; masu dadi da marassa dadi. Laura ta cancanci abinda yafi godiya yau daga gare ta in akwai, tunda ta mallaka mata Baban Abdallah (Habibu Mustapha Bilyamin Nahuche)." ****** JAMUS S "ai da ya gama musu komai a filin jirgin saman Murtala Mohamed dake Lagos ya kuma ga tashin su, sannan suka koma gida shi da P.A din sa Atiku, yana tafe yana waiwayen jirgin da ya daga da Yayar sa, Mahaifiyar sa da Matar sa; mata ukun da bai da ya su a duk fadin duniya, wadanda su ne farin cikin sa, kuma komai na sa." "Habib Nahuche, sai ya ji tamkar shi kadai ya rage yanzu a fadin duniya in ka dauke dan sa Abdallah da ke gadon asibiti. Nene Balki na asibiti wajen sa ita da Sahura, sai dare zai koma musu." "Dr. Rahinah Omar a Jamus a karo na biyu. Wannan karon ba a daliba ba a matsayin mai jinya. Ita ta rinka jagorantar su a komai har suka sauka a masaukin su. Asibitin da aka yi wa Hajiya booking yana 'Bonn City' wato St. Josef Hospital, Bonn. Rahinah ce tsaye a kan komai har aka ba su daki, cikin kwanaki uku da zuwan su Hajiya ta ga duk likitocin da ya kamata ta gani. Babu irin binciken da basu yi mata ba (complete check up) na duka abinda ya danganci lafiyar ta." "Kuma a binciken su sun gano sugar (diabet) ma a jikin ta, sannan ciwon kafar Hajiya na da alaka da hawan jinin ta, treatment na kwararru kawai ake ba ta iri-iri." "Tun zuwan su asibiti Rahinah ta ajiye komai ta ke hidima da Hajiya, ita ke kula da komai nata, wanka take mata da tawul kullum, kula da cin abincin ta irin na masu hawan jini wanda asibitin ne ke ba ta da kan sa, kula da shan maganin ta a kan lokaci da communicating da likitoci, Habibu sai dai kawai Badiya ta yi masa waya ta ba shi labarin abin da ake ciki da irin kokarin da Rahinah ke yi. Tace ita zaman kashe zani take yi kawai. Rahinah ce ke jinyar." "Ita kanta Hajiya da ta ke a kwance ta san Rahinah a tsaye ta ke tsayin daka a kan lafiyar ta, ta baro nata yaron wanda shi ma kulawa yake bukata amma kacokam hankalin ta yana kan Hajiya. Duk abinda ya shafi lafiyar Hajiyar da ita likitocin ke tattaunawa." "Wannan kokari na zuciya daya da kulawa kamar ita Hajiya ta haifa ba Habibu ba, ya wanke Rahinah a zuciyar Hajiya Kaltume, ta kuma fahimci abubuwa masu yawa a tare da Rahinah da a baya ta kasa fahimta, wato dai ta gane Rahinah mace ce mai saukin kai da dadin mu'amala akasin yadda ta ke kallon ta kuma dai tana son Habibullahin ta, ta sani in har da a ce ba ta son Habib din, ba za ta yi wannan tsayuwar dakan a kan ta ba." "Balle kuma tana jin su cikin dare suna waya, wata irin waya da du kwakwar ka ba zaka gane me suke fada ba, a zaton Rahinah Hajiyar na barci ne, lokacin da Habib ke mata (midnight call), amma duk da kuskus din na su ta kan fahimci wasu daga kalaman Rahinan ga mijin nata Habibu a waya, duk na ban hakuri ne da tausasawa a kan kewar su da watakila yake cewa Rahinar yana yi, da kuma tambayar yaushe za ta dawo da Abdallah ke ta yi masa." "A kwana goma da zuwan su Jamus Hajiya ta fara samun sauki sosai, tana zama sosai a yi hira da ita, ana i-gobe za su cika sati biyu a Jamus Badiyya ta ce, Habibu ya yi mata booking za ta koma gida, sabida yara da kuma aikin ta, don excuse din sati biyu ta dauka dama." "Ta ce ""ka ga zaman nawa bai da wani amfani tunda Dr. Rahinah ke yin komai, ni 'yar taya su hira ce kawai. Asibitin kuma sun ce sai Hajiya ta yi sati uku za su sallame ta""." Don haka Habib ya yi ma Badiya shiri ta dawo Kaduna. "Badiya ta taho a washegari, shi kuma Habib ya yi booking din tahowa domin an sallami Abdallah daga gadon asibiti, Nene ta tafi da shi gidan ta wato gidan Ambassada." "Ko a daren ranar sun yi waya har tsakar dare ita da shi, amma bai gaya mata cewa yana (on transit) ba ne ma lokacin a kasar Neitherlands, ya dai gaya mata an sallami Abdallah yana gun Nene Balki." "Ta ko'ina yanzu Raheenah ta wanke kan ta a dan tsukin a wajen Hajiya Kaltume, ta saki ran ta da Rahinah, ta cire wa kan ta shakku a kan surukar tata, ta yarda ita ce daidai da rayuwar Habibullahin ta, wadda ya ke so saboda Allah, take kuma auren sa ba don wani abu da ya mallaka ba, in ka ji su suna hira da rigima a kan shan magani itada Hajiyar Nahuche kamar Yaya da kanwar ta." "A yanzu kam Hajiyar ta amince za ta iya baiwa Rahinah amanar da a baya ta ke ganin ba za ta bata ba, wato zamowar ta abokiyar sirrin da za su kashe su rufe a kan komai na Habibu tare, ba zancen surukuta ko shakku a tsakani." "Ta maida Rahinah 'yar cikin ta, ba maraba da Habib da Badiyya." ****** BAKON BAZATA """" "Daure ki sha Hajiya, daga yau zan roke su su rage yawan kwayoyin nan, tunda dai ba kya son hadiyar su, kullum sai mun fafata har waje ana jiyo mu akan shan maganin nan""." """Ke ko Rahinah shan maganin bature ai sai dole, dolen ma sai dole, amma ina ya ga dadi? Nafi gane in yi jikon sassake tunda alhmadllh babu cutar da bamu da maganin ta na gargajiya amma kun ki""" "Hajiya ta koka, tana yamutsa fuska." """To in ba kya sha a kan kari Hajiya ai bazaki warware da wuri ba su sallame mu a kan lokaci, ki koma wajen maigidan ki Abdallahn ki da kullum ki ke damu na da zancen sa""." "Hajiya ta dungure mata kai, ta ce, ""Abdallahn da ku ka sabauta min? Bawan Allah! Allah kadai ya san irin izayar da ku ke gana masa da sunan soyayya""." "Dariya Rahinah ta hau yi. Wai izaya. Fada kawai suke yi shi kuma Abdallah ran sa baya so, ya sanyawa ran sa damuwar hakan har hakan ya taba masa kwanya. Amma ai lelen sa suke yi ba ita ba ba Uban ba, wannan na wane" "wannan a son Abdallah, kowanne so ya ke ace shine gwarzon mahaifi a wajen Abdallah dayan ya gaza; wato dayan ne a baya." Kuskuren da suka yi shine kwakwalwar yaron ta yi kadan da daukar matsalolin su. Rahinah na wannan tunanin taba ballewa Hajiya magani ta sunkuya domin dauko gorar ruwa a firji sai ji suka yi an murda kofar dakin nasu tare da sallama a natse. "Muryar da ta ratsa har kasan zuciya da ruhin Rahinah Omar, ta sanya ta dagowa abruptly kuma cikin (slow motion). Baban Abdullahi dan mutanen Nahuche ya bayyana a dakin asibitin sanye cikin (Black - Grey German Suit), wadda ta taimaka ainun wajen kara fito da ilhama da cikar zatin sa na cikakken Bazamfare mai jini a jika. Kafar sa cikin rufaffen takalmi (cover) samfurin (Bloomingdale's) wanda ya dace da launin sutturar jikin sa, wato black/grey. Agogon rolex dake daure a damtsen hannun sa ma (Bloomingdale's) dinne na bakar fata. Agogon ya kwanta luf ya nitse cikin tarin lallausar sumar dake kwance a hannun sa ta Zamfarawan usli. Fatar jikin sa lub-lub mai nuna yanayin hutu da kwanciyar hankalin da yake ciki." "Wannan sardidin matashin bazamfaren da a kullum ta gan shi ko ta ji muryar sa tun daga kuruciyar sa har zuwa matakin da ya ke kai a yanzu (at his fourteith), sai ya tafi da kafatanin numfashin ta na wucin gadi ya kuma tada tsigogin jikin ta." "Daga ita har Hajiya babu wanda ya yi tsammanin ganin sa a wannan lokacin, don haka suka bi shi da kallo na mamaki da al'ajabi, na Rahinah cakude da boyayyen farin cikin ganin sa har kasan ran ta. Irin farin cikin da ta dade bata yi ba, kuma idanun ta sun nuna hakan. Ta saki wata siririyar ajiyar zuciya." "Sai da Habib ya tabbatar ya sanya kwayan idanun sa cikin na Rahinah duk da yadda ta yi kokarin kaucewa hakan saboda Hajiya da ke zaune a gefen su, sannan ya karasa gaban gadon Hajiya da sassarfa." "Hajiya ma ta kasa boye farin cikin ta na ganin sa, ta ce," """Baban Abdullahi zuwa ba sako ba sanarwa? Amma ka shammace mu""." "Hannayen ta duka biyu ya kama ya rike cikin nasa ya dora a kan kwantaccen sajen fuskar sa, ya ce, ""Hajiya ina sane na ki gaya muku zan zo, don cewa za ki yi ba sai na zo ba kin warke""." "Hajiya Kaltume ta yi murmushi ta zare hannayen ta daga cikin nasa, Habibu ba ya girma in dai a gaban ta ya ke, ta ce," """To ai shi ke nan, ka zo lafiya ya ya hanya, ya Abdallah da jiki?""" "Suka koma gaggaisawa irin ta Da da mahaifi. Yana gaya mata rikicin Abdallah na cewa sai ya biyo shi. Hajiya ta dubi Rahinah da duk ta kasa sakewa ta takura a dakin sakamakon kallon da Habib ke mata na kurullah duk lokacin da tayi kuskuren dago kan ta sai idanun ta sun fada cikin nasa ta ce," """Ke kuma haka ake karbar bako babu sannu da zuwa babu ruwan sha?""" "Murmushi ta yi cikin jin kunya, kan ta a kasa ta kara nutsuwa hadi da takurewa, murya can kasa ta ce, ""Sannu da zuwa Baban Abdallah""." "Habibu ya yi mata kallon tsaf, kafin ya ce. ""Rike sannu da zuwan ki tunda sai da a ka roka min"". Ya fadi hakan ne cikin gimtse fuska da nuna rashin jin dadi." Yadda ya gimtse fuskar sai ta ga ya kara wani irin kyau a idanun ta. Ko kuwa ita kadai ta ga hakan don tana murna da zuwan sa? Ba zan iya sani ba. "Tana murmushi ta nufi firij ta rasa lemon da za ta dauko masa, sai ta tuna ya taba cewa ba ya shan zaki, kawai sai ta bige da dauko ruwan roba mara sanyi da tambulan ta kawo masa." Gabadaya ta rikice ta rude sosai da zuwan Habibu. Amma tana kokarin sarrafa kan ta saboda idon Hajiya da nasa idanun da ke ta bin ta. Tana bashi ruwan ba tare da ta bari sun hada idanu ba ta juya musu baya ta tada sallah. "Bai sha ruwan ba ya mike yana fadin, ""Hajiya zan karasa masauki in yi sallah sai dare zan dawo in ga likitocin ki"". Hajiya ta dubi Rahinah da ke ninke sallayar ta bayan ta idar da sallahr ishai da idanun kulawa da kauna, kamar mai magana da karamin yaro cikin lallashi ta ce." """Rahinatu sai ki raka shi masaukin ko, kun dawo tare zuwa goben, ni bana bukatar komai alhamdulillah kullum lafiya karuwa take yi, barci ma zan yi yanzu haka, Allah ya yi miki albarka yasa yayan ki su yi miki ninkin abinda kika yi min""" "Rahinah ta zaro ido ta ce, ""Hajiya ba za mu barki ke kadai ba...""." Kallon da Habib ya yi mata ya sa ta hadiye sauran maganar ta har ta kware. Domin kallo ne da bata taba gani a idanun sa ba. "Hajiya kuwa sai ta hau fada," """To in kin zauna goya ni za ki yi? Kin bani magani kin bani abinci barci kawai ya rage min. Mijin naki da ya taso kasa ya kasa ki ce ba za ki raka shi masauki ba, haka ake yi Rahinatu? Bayan ni bana bukatar komai? Duk wata kulawa kin gama bani, shima kulawar ki ya ke so. Tashi maza ku tafi, Allah ya yi muku albarka""." "Shi tuni har ya kai bakin kofa ran sa kal da farin cikin kalaman mahaifiyar sa. Da tace da Rahinah shima kulawar ta ya ke so. Da gaske ne Hajiya ta fi kowa son sa, ta kuma fi kowa sanin sa da fahimtar sa." "Ba abinda yake so a lokacin sai kadaicewa da Rahinah Omar. Ba kuma wai don wani abu ba, kawai so yake ya gan su daga shi sai ita a kebantaccen muhalli shine babban abinda yake sa masa nutsuwa a yanzu. Son samu ya dan runguma ta cikin jikin sa ya ji dumin da ke kasan dogon wuyan ta, wanda ya san ba mai yuwuwa bane." "Rahinah ta gama 'yan mutsu-mutsun ta na jin kunyar Hajiya, sannan ta dauki kayan ta kala daya ta sanya a leda da rigar barci daya, da duk abin da ta san za ta bukata a daren zuwa gobe ta bi bayan sa kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki. Tana ficewa daga dakin tana ce da Hajiya 鈥滺 ajiya ki kunna waya ki bar ta a kunne 鈥฀. Hajiya tace," "鈥漷 o Rahinatu, ga nurses din nan ma suna ta bakin kokarin su ai, bana jin sai na kira ki, mu kwana lahiya cikin alheri 鈥฀." "Direban hotel din da ya sauka wanda da ya dauko shi zuwa asibitin yana waje yana jiran sa bai tafi ba, shi ya bude musu gidan baya na motar duk suka shiga, ya mayar ya rufe ya ja su a hankali suka shiga cikin garin Bonn." "Bonn City makociyar Cologne ce. Daga ita har shi, ba mai iya kallon dan uwan sa. Wata bakuntar juna ce ta zo ta lullube su. Zukatan su kadai ke aiki da wani irin emotion na zama jikin juna a kujerar baya na motar. Kwakkwaran motsi wannan daga shi har ita ba wanda ya yi har suka iso hotel din da Habibu yayi masauki." "Meriotte Hotel, Bonn." Shi ne hotel din da Habib ya yi masauki. "Ta lifta suka haura zuwa dakin da ya sauka a hawa na goma. Abin da Rahinah ta gani shi ne, Habib bai cika kallon ta ba tunda suka taho, karewa ma, ignoring haduwar idanun su yake yi, ko mai ya sa? Ko Habib ya daina son ta ne shine dalili?" "Tun shigowar su dakin yake sabgogin sa, ya yi wanka ya sauya kayan jikin sa zuwa na barci, ita kuma ta haye saman kujera ta yi zugum, kamar tsohuwar da ta yi wa Sarki karya. Tana kallon sa ya jona kettle ya dafa shayi ya sa lipton din 鈥橳 etley Tea 鈥฀ mai kamshin na 鈥檃 na 鈥檃 da kanimfari ya zauna a gefen gadon dakin yana sipping (kurba) a hankali, yana yi yana amsa wayoyin da ke ta shigo masa a kai a kai daga ma'aikatan sa na gari-gari a Najeriya da sauran abokan kasuwancin sa. Ta raja 鈥檃 sosai a kallon sa yadda yak e yin komai nasa cikin nutsuwa da class burgeta ya ke yi." "Tana bukatar wanka, don haka ta hakura da kallon mijin nata wanda ya nuna bai san da wanzuwar ta ba, ta mike da kayan ta cikin leda zuwa bathroom din dakin cikin mutuwar jikin yin biris din da Habib ya yi da ita, kamar bai san tana cikin dakin ba." Ai ko laifi ta yi masa tunda ta kashe kunyar Hajiya ta biyo shi masaukin sa ya sassauta mata yayi mata kallon rahma su yi celebrating ganin juna. Watakila bayan tahowar ta komai ya gama kankama tsakanin sa da bazawarar sa. Shiyasa yau Habibin ya ke share ta. Kawai sai ta ji idon ta sun cika da kwallah. Ta gaban sa ta wuce tana tafiya kamar macijiya. Ta kasan idon sa ya bi ta da kallo har ta shige ta rufo kofar. "A hankali Habib Nahuche ya sauke kwayar idanun sa kasa, daga kallon bayan matar tasa Rahinah, yana jin wani irin nutsuwa da kwanciyar hankali har da gamsuwa na ratsa shi. Ji yake kamar ya bi ta toilet din amma hani kan sa yin hakan, domin hakika ya azabtu da rashin ta a kwanakin nan duk da ko suna taren ba wani abu ke shiga tsakanin su ba, amma atleast yana ganin ta ko fada suke yi dadi yake ji, idan ya tuna Rahinah Omar ce ta dawo cikin rayuwar sa. Amma haka ya daure ya hana kan sa bin nata, domin ya riga ya alkawarta wa ran sa komawa SABON Habibu a gare ta daga yau har karshen rayuwar su, sabon mijin Rahinah wanda komai nasu sabo zai koma wato (from the beginning)." "A yanzu sabuwar rayuwa yake musu kwadayin ginawa wadda babu komai sai zallar soyayya, kauna da fahimtar juna a cikin ta. Ta baya ta riga ta shude. Sabon gini ya ke musu fata mai inganci da karko mai kuma meaningful direction. A sabuwar rayuwar da ya shirya musu shi da Rahinah, ya kuma ke musu fata yanzu; fahimtar juna da soyayya zallah ne zasu jagorance ta, sex will now be their last priority at the convenience and desired time of each other." Love and mutual understanding will prevail. "Tunanin da Habib Nahuce ke ta yi ke nan har Rahinah ta fito daga wankan ta, sanye da wata lallausar nightie (pusher pink) a jikin ta. Amma rigar doguwa ce sosai har kasan idon kafar ta, hannun ta ne kamar na shimi, suka hada ido, tayi saurin kawar da nata. Rauni irin na diya mace na son mamayar ta, ya fallasa halin damuwar da biris din da Habibu ya yi da ita ya sanya ta a ciki duk da yadda take daurewa, ruwa na yarari daga cikin lallausar gashin kanta ta fulanin usli da ta wanke da kumfar (head&shoulder)." "A hankali kamar wadda aka yi wa umarni Rahina ta tako zuwa gaban sa, kawai sai ta samu kan ta da tsugunnawa a kan gwiwoyin ta, sannan ta sunkuyar da kai, ta kasa cewa komai. Hawaye na son bada ita." "Habib ya ajiye kofin shayin da ke hannun sa, ya kai makura wajen shariyar da yake mata shima ba da son ran sa ba, sai don dai kawai don ya koyawa kan sa hakuri da yakanah, ta yadda zai tabbatar mata da cewa ya canza zuwa yadda take son sa, take fatan ya koma." "Yau Rahinah ce tsugunne a gaban sa a cikin yanayin da shi mijin ta kadai zai iya ganin ta, this scenario touches him to such an extent. Ya dube ta sosai cikin raunin murya wadda har shakewa da sarkewa ta ke yi, jikin sa na dan rawa ya ce," """Ya ya aka yi Maman Abdallah? Irin wannan durkuso haka kamar mai neman gafara? Baki yi min komai ba kin ji? Im only too much tired. Na kwana zaune a jirgi sannan tun da na sauka ban zauna ba. Tashi dawo nan daga gefe na.."" ya nuna mata saman cinyoyin sa. (Ba ya son ya yi wani action wanda zai nuna cewa bai canza daga yadda take so ya koma ba)." Don haka ya ke cigaba da kaucewa idanun ta kada su lalata masa ajin da ya shiga. "Maimakon ta ba shi amsa, kawai sai ta samu kan ta da kwantar da kai a kan gwiwoyin sa, ta rungume kafafun sa ta fashe da kuka." "Kuka sosai mai sauti Rahinah Omar ke yi mai taba zuciyar masoyi, masoyin kuma ba kowa ba ne HABIBU ne, wanda ba narka zuciyar Habib kadai ya yi ba, hatta jikin sa rawa ya hau yi, tsigar jikin sa ta mimmike duka, share tan da ya yi fa daurewa yake yi gas hi tana so ta lalata komai." "Ya sa hannu ya dago habar ta daga kan gwiwoyin sa, ya dubi yadda hawaye ke gudu bisa fararen kundukukin ta, wadanda nan da nan suka koma jazur, ya ce," """Rahinah... why? Rahinah dube ni... don Allah""." "Ba ta iya ta dube shi ba kamar yadda ya bukata, ya ke kuma kan cigaba da rokon ta yi hakan, sai ma kara sautin kukanta da ta yi tana kara kankame kafafun sa." "Ta sani ta azabtar da shi da yawa kuma yayi hakurin da har ya kai shi makura yanzu ya daina damuwa da ita irin da, ya daina sha 鈥檃 war tama bakidaya." Ta rasa ta ina za ta fara cewa Habib ya yafe mata. Ta rasa ta ina za ta fara cewa tana so su canza akalar rayuwar su daga rana irin ta yau. "Tana so ta gaya masa cewa ta mallaka masa ranar yau baki dayan ta, ya yi yadda ya ga dama da gangar jikin ta, ruhin ta da zuciyar ta bakidaya a yau ta mallaka masa su, ranar yau bakidayan ta tasa ce, tana so ta yi amfani da ita ta wanke dattin data jima tana yaba masa tsayin shekaru goma a daren yau bakidayan sa." "To amma ba za ta iya fadin hakan kai tsaye ba, banda kasancewar ta bafullatana har gobe ba su yi irin wannan sabon ita da shi ba har yau. Sannan har gobe ita Rahinah ce mai aji da kiyaye darajar ta." "Babbar yatsar sa sabbab ya sa yana dauke hawayen da ke sauka a kan fuskar ta wanda hakan ya sa Rahinah wani irin lumshe idanun ta, tare da sauke ajiyar zuciya, da kyar ta ce," """Habib ka yafe min!""." """Da ki ka yi min laifin me?"" Ya tambaya yana dago ta daga durkuson da ta yi a gaban sa irin na mai neman gafara ya azata saman cinyar sa, ta rasa inda za ta sa kan ta da soyayyar sa da ke kara-kaina a tsakiyar kirjin ta." "Habib bai ankara ba kawai ya ji Rahinah ta shige jikin sa a hankali bakidaya ta kanainaye shi, ta cusa kan ta a kirjin sa da iyakacin karfin ta." Ta saki kakkarfan kuka mai tsananin sautin gaske wanda ya tafi ya ratsa har cikin brain din sa. "Shidewa ya yi na wucin gadi domin hakika rungumar ta zo mai bagatatan, wani abu ne da bai taba tsammanin samu daga Rahinah Omar ba, sai ko cikin sa mafarkan sa da hasashen en sa masu yawan gaya masa cewa rana irin wannan na zuwa komai daren dadewa...." "Ita kan ta Rahinah ba ta san lokacin da ta yi hakan ba, shauki ne ya debe ta, ta bi umarnin zuciyar ta da gangar jikita ne kawai, wadanda a wannan lokacin ba abin da suke so suke marari kuma, face kasancewa cikin jikin mijin ta Habibu Mustapha Nahuche." "Ji ta ke duk wani ban hakuri na duniya ya yi kadan ya nuna nadamar ta. Ta hakan ne kawai zata iya nuna masa ta yi nadama she 鈥檚 begging for change. Kwarai Habib ya yi mata laifi, laifi kan laifi yayi mata a baya, but her punishment to him is severe." "Yau watanni nawa da maida musu aure ko sau daya bata taba bashi hakkin sa na aure ba, yet yana jin dadin zama da ita a hakan don dai ya nuna mata ya canza...." "Habibu na son rike Rahinah cikin jikin sa, wata zuciyar na hana shi. Rahina a wasu lokutan Zuma ce ga zaki ga harbi, kada ya yi saurin nuna weakness din sa ta bashi zuma ta dawo ta harbe shi (ta guje shi). Wannan tunanin da ya yi ne ya sa tsaya mata kamar gunkin da ba ya motsi, bayan kuma ji yake tamkar zuciyar sa za ta fito daga kirjin sa with excitedness, ita kuma bata san hakan ba sai kara kankame shi ta ke yi tana sakin kuka mara sauti tana bashi hakuri. Tsigar jikin sa ce ta soma tashi sanadin jin ta lambam cikin jikinsa....." Zuciyar sa ke gaya masa... """Rahinah Omar ce fa!""" "Wadda ko na sakan daya bugun zuciyar sa bai taba gudana ba tare da ita a ciki ba. Rahinah ce Maman sanyin idaniyar sa wadda ta yi nakudar nan a kan idanun sa, ita ce wadda tsayin shekaru goma sha biyu daidai da rana daya zuciyar sa ba ta taba hutawa a kan ta ba." """Please hold me Habibi!"". Ta fada cikin tsananin kuka, wato ""ka rike ni Habibi!""." "Yana son ya rike tan, amma yana hana kansa hakan, sabida sanin ko wace ce Rahinah, bakidaya ta tado tsofaffin al'amura cikin jikin sa da a baya yake zaton sun gushe, sun shude, they are no longer alive in him. A lokacin da ta kwantar da kai a masagalin wuyansa sai komai ya karasa kwance masa......" "Da kyar ya iya cewa cikin sarkewar murya da sarkewar numfashi," """If I hold you today, will you hold me forever? Will you stand in our lives ni da Abdallah till eternity?""" "Muryar Habib Nahuche karkarwa kawai ta ke a lokacin da yake wannan furucin. Rahinah sai kawai ta yi azamar sanya bakinta cikin nasa, ta rufe duk wasu kalaman bakin sa, ta soma sumbatar Habibin in a gentle manner." "Habibu couldn't control himself amma ya ki taimaka mata da komai. Kyale ta ya yi ta yi mai isar ta, kissing dinsa ta ke from head to toe, kamar har abada ba za ta daina ba, sannan a hankali ta sabule rigar barcin da ke jikinta. tare da" "latsa makunin lantarki da ke jikin gadon, fitilu shudaye suka maye gurbin masu haske." "Habibu ya rasa duniyar da Rahinah ke shirin jefa shi a yau sai ninkaya yake cikin wata irin korama ta farin ciki da cikar buri.... fitilar da ta kashe Habib ya sake kunnawa, haske mai karfi ya wadaci dakin, ya ga Rahinarsa cikin yanayi da sigar da bai taba ganin ta a rayuwar sa ba, sannan sumbatar da ta ke masa ba ta fasa ba wai don ya kunna fitilar da ta kashe. Ya tabbatar ita din ce ba mai kama da ita ba, matar sa abin kaunar sa ce Dr. Rahinah Omar Girei. When theres life theres hope in ji bature.So always expect success in the future no matter how worst things seem to be in your past 鈥฀" "Tun Habibu yana shaida komai yana kuma gode mata bisa hobbasar ta, da wannan goma sha tara na arziki da take masa, har sai da duniyar sa da tata bakidaya suka kasa daukar su......" "80% na incident din daren bakidayan sa hobbasar Rahinah Omar ne ita kadai ran ta, Habibu sai ya zama dan gatan matar sa, sai yadda Rahinah ta yi da shi a wannan daren da babu irin sa a tarihin rayuwar su, ba abinda yake sai sambatun kiran sunan Rahinah.... yana rokonta ta bar shi da ran sa...." "Wani dare ne na musamman, wanda daga Habib Nahuche har Rahinah Omar, ba su taba mafarkin kwatankwacin sa ba." It's a night of majesty a rayuwar auren Habib da Rahinah. Ta yadda a wayewar garin ranar Rahinah ba ta iya hada ido da Habibu ba. Habibu da yake namiji shima bai iya ya hada ido da Rahinah ba. Zukata kadai ke magana. Sakamakon cewa an yi quenching kishirwar soyayyar shekara goma in only one night. ": Sosae Ammah tayi farin ciki da zuwan su,ta kalli Aliyu tana fadin""yanxu nake xancen Nooriyah a raina,na xata ma jikin har yanxu.""Basu dade da xama ba sai gasu Khaleel waxeer shida Laylah,itama kwana biyu bata shigo wajen Ammah ba ulcer ta sakota gaba.gaisheda Ammah sukayi dukan su,Ammah ta kalli laylah tana fadin""Ya jikin nata hop ta samu sauqi.""ciki-ciki laylah ke fadin taji sauki," "Sai da sukayi ishaai Ammah tace su tsaya suci abincin dare tare daita,ta kalli noory tana fadin""zata iya cin tuwon semo ko a girka mata wani??""girgixawa Ammah kai tayi dama can tuwon semo ba cimarta bace,Ammah ba sai anyi ba inada pizza gida idan naje ita xan ci da yougout ,,Kin tabbata zai kosar dake??""daga kai tayi cike da jin kunyar Ammah,typing Khaleel waxeer ya shigayi a wayarsa ya turawa Aliyu...""mekake jira buddy ka kashe boss Dan Allah" ",wai meke damunka idan Ammah ta gano akwai matsala kasheka xata yi babu ruwana.""jin sako ya shigo a wayar Aliyu yayi saurin duba wayar,da sauri ya kalli Khaleel waxeer ya ware masa ido gamida bude hannuwa,kallonsu kawai laylah keyi.Nooryn ce ke serving kowa,da gangan laylah ta kwantar da bottle water a dai-dai wajen da nooryn take,noory ta daga kafa dan isa ga Aliyu waxeer taji ruwa ya jata,da wani irin sauri Aliyu ya tarota ta fado kansa gaba daya.Ammah na dafe kirji take fadin""meye haka meyasa bakya bin A hankali Nooriyah,Aliyu yabi ruwan dake kwance kan marbles da mamaki lokaci daya ya kalli laylah ta sha toka gamida dauke kai,da sauri Ammah ta kama hannun nooryn ta zaunar daita,ta kalli laylah tana fadin.""ta tashi tayi serving Aliyu Nooriyah ta xauna ta huta,bakin ciki tamkar xai kashe laylah waxeer a wajen Haka suka karasa cin abinci tana kunci,sai kusan goma kowa yayi" "shirin tafia,suka yiwa Ammah sai da safe,A mota dukkan su shiru suka xauna,sai ga kiran Farhaan Shagari ya shigo a wayarsa ,kin dagawa yayi dan har yanxu bai sauko daga fushin da yayi da Farhaan Shagari ba,wani irin barci takeji yau duk taji bata jin ddin jikinta haka gabanta taji yana yawan faduwa,wanka kurum tayi tabi lafiar gado,shima a bangaren Aliyu wanka yayi ya duba sako a email dinsa,sai kusan 12 ya kwanta.shima bai dade ba yayi barci,harbin bindiga kawai sukeji kusan lokaci daya mami da daddy suka bude ido,cike da tashin hankali mami ke fadin""daddy bakaji karar bindiga ba,da sauri Alh.omar Shagari ya sauka kan bed yaje ya leka ta window,da sauri yaja da baya yana xare ido,mami ta dafe kirji tana fadin yan fashi kou daddy??""da sauri ta nufi kofa tana fashewa da kuka tashin hankali take fadin""Daddy Farhaan da Jamila, daddy ya jawota Yana fadin"".ki natsu Maryam,hawaye na xubar mata cikin tashin hankali take fadin""Jamila daddy.""da sauri daddy ya dauko wayarsa ,ya shiga kiran commissioner da yake abokin sane," "Kira wajen 3 yana yi masa bai daga ba,cikin tashin hankali mami ke fadin""bai dauka ba daddy.""ta fada tana rufe bakinta," "Da sauri mami ta saka Hijab ta bude kofar batareda ta jira mai daddy xai fada ba,shima akwai jallabiya a jikinsa ,yabi bayan mami da sauri dakin Jamila suka shiga bugawa a hankali,dama kuma Jamila bata dde da kwanciya ba.so barcin nata baiyi nauyi ba,ta bude kofa tana kallon mami da daddy gabanta na faduwa take fadin""mami meya faru??""Barayi jeki ki canja kayan jikin ki da sauri Jamila ta koma daki cikin minti biyu ta xura Hijab ajikinta babu inda baya rawa cikin jikinta,daddy ya kalleta yana fadin""maryam ki tsaya tareda Jamila bara naje na duba Farhaan, Cikin tashin hankali mami ke girgixa kai take fadin""baxan iya ba daddy pls muje tare. Yarda mami yaga ta daga" "hankalinta ," "Yasa duka suka nufi bangaren Farhaan zuciyarsu na bugawa," "Su bahago na hango tahowar su dashi da sauran yaransa suka fito daga mabuyar da sukayi a bayan flower's ,suka zagayesu da manyyan bindigogin su a hannu," "Kowane ya rufe rabin fuskarsa da bakin kyalle,cikin karfin hali mami ke fadin""dan Allah kuyi hakuri ko me kuke so zamu baku,Ina yaron gidan nan wajensa muka xo.""cikin rawar murya mami ke fadin""Bayana yayi tafia,lokaci daya bahago ya fisgo Jamila wacce ke bayan daddy,yasata cikin jikinsa yana fadin.""xaki fadi inda yake ko sai na yaga mutunci yarki a gabanta,lokaci daya hawaye suka wanke fuskar mami,cikin rawar murya take fadin.""dan Allah kuyi hakuri kar kuyi mata komai,haka suka saka su gaba har part din Farhaan,tsaye suka samu Farhaan acikin parlor Shima karar bindigar da yaji ya hanasa kwanciya,koda akayi harbin yana parlor ,baiyi zaton harbin ta cikin gidan su bane.""A fusace ya karaso gabansu ganin sun rike Jamila,daga hannu yayi xai kaiwa bahago duka ,bahago ya rike hannun nasa,Fashewa da kuka mami tayi ta xube a gabansu tana rokonsu da Allah kar su taba mata ya'yah,bahago ya mikawa Farhaan Shagari hannu yana fadin ya basu wayar hannunsa,wani kallo ya shigayi masu .mami ta daka masa tsawa tana fadin""kaba su mana," "Mika masu wayar yayi dama tana hannunsa," "Laptop Dinka??har dakin barcinsa suka tasa shi gaba ya dauko laptop acikin dakin barcin nasa ,suka rufe mami,daddy da Jamila.suka tasa Farhaan gaba har tsakiyyar parlorn suka 蓷 ora masa bindiga da mugun shock Farhaan ke kallonsu,xai yi magana yaji bullet gefen kirjinsa,jin tashin bindiga yasa mami ta fashe da mugun kuka,tana dukan kofar da duka karfinta, sun kashesa daddy sun kashesa .""!""Addu'a kawai daddy yake a ransa gashi garin sauri ya baro wayar daki,suna ganin Farhaan din ya fadi sukayi takansu ,na daina jin motsin su" "Farhaan mami ta shiga kwalawa kira da dukkan karfinta tana fadin yaxo ya bude kofar,sulalewa mami tayi a wajen a sume. cike da wani irin tashin hankali Jamila tayi kanta,wani key ya shiga nema a dakin na Farhaan dakyar daddy" "ya samo sa, addu'a yake Allah yasa basu bar key jikin kofar ba," "Shi kansa daddy jikinsa bbu inda baya rawa,yana jin key din ya shiga ya sauke ajiyar xuciya,da gudu ya nufi parlor sai dai turus ya tsaya a wajen ganin Farhaan din kwance cikin jini. zuciyarsa yaji tana bugawa , jin yyi wani abu na tsaya masa a wuya.........kusan karfe shidda na safe mutuwar Farhaan babu inda bata xaga ba,tun karfe hudu na Asuba commissioner yake gidan daddy shida yaransa,sosai ya ta baiwa daddy hakuri na rashin daukar wayarsa ,ya sata a caji barci ya daukesa,shima baya gari a ranar ya dawo.duk wani bincike sunyi basu samu komai akan mutuwar Farhaan Shagari ba,sai dai commissioner din ya tabbatar da turosu a kayi,ta yaya zasu karbi wayar hannun Farhaan da kuma laptop kadai,tambayoyi ake yiwa daddy sosai wasu ya bada amsa wasu yayi shiru,shi kansa daddy dauriya kawai yake ga mami kwance gadon Asibiti ,wacce har yau bata san inda kanta yake ba,Yarda Ammah taga ya shigo mata a gida da safe yayi mugun daga hankalinta,Ammah ta kalli Agogo kusan karfe 7,ya xube a gaban Ammah duk dauriyarsa ya kasa rike hawayensa,ammah ta shiga girgiza sa tana fadin""meya faru ina Nooriyah meya sameta ,yana girgiza kai yake fadin Ammah.""Besty Farhaan, cikin tashin hankali Ammah ke fadin meya samu Farhaan din''" ".Ammah ki cemin barci nake ki tashi ne dan Allah baxan iya daukar rashin sa ba,ki fada masa yanxu yaxo xan sakar masa noory ki bani biro da takarda Ammah.,,salati kawai Ammah keyi maganganun Aliyu din na taba ta,open ur eye's Aliyu..''Ammah ta fada tana daka masa tsawa,ya kalli Ammah yana girgiza kai yake fadin.''xan hakura daita saboda farin cikin sa Ammah .rungume Ammah yayi yana fashewa da wani irin kuka mai fitowa tun daga karkashin xuciyarta,sai jikin Ammah yayi sanyi bata ta 蓳 a ganin Aliyunta haka ba bata ta 蓳 a ganin sa haka ba," Shima Khaleel waxeer agigice ya shigowa Ammah ta kallesa tana fadin.''kayi min bayani Khaleel kar yasa zuciyata ta buga . "Ammah dama barayine suka kashe Farhaan Shagari.""kabbara Ammah tayi Aliyu ya nufi Khaleel ya rikesa yana fadin Yah leel pls ka fada mata bani ne sanadin mutuwarsa ba,ka fada masa dan Allah ya dawo xan saki noory ya Aureta baxan iya jure rashin sa ba,wai Aliyu ka haukace ne da kake maganar sakin matarka sabida abokinka.""Khaleel waxeer na girgiza kai yake fadin""kara ya fadawa Ammah gaskiyya kowa ma ya huta ,cikin minti goma Khaleel ya mata bayanin komai,kallon su kawai take, Khaleel ya rike hannayen Ammah yana fadin""dan Allah Ammah ki dauki abun nan da sauqi Ammah na girgiza kai tana masa wani irin kallo take fadin""wannan abun kake fadin na dauka da sauki ,mikewa tsaye Ammah tayi jin tayi dakin na juya mata saurin riketa Khaleel yayi ya zaunar daita gefen bed,jeka zo min da Nooriyah yarda Ammah yaga tayi yasa ya juya baiyi gardama ba Yabar Room din,tana moping" "parlor taji ana Danna door bell,Sama ta koma ta sako Hijab taxo ta bude kofar ganin Khaleel waxeer yasa xuciyarta tayi wani irin bugawa.ta gaishesa da ladabi,bai kalleta ba yake fadin""taxo Ammah na neman ta," "Talkami kawai ta xura a kafarta tabi bayan Khaleel wanda har ya nufi motarsa,tun a falon Ammah taji xuciyarta na tsinkewa, kasa ta xube tana gaisheda Ammah,Ammah ta amsa tana kallonta." "Karfin hali Ammah tayi na fadin""Abokin Aliyu ne ya rasu nasan bakiji labari ba,ga mijinki nan duk yabi ya daga mana hankali," "Dafe kirjinta tayi tana xare ido hawaye na taruwa a idonta take fadin.""Farhaan !""Farhaan ,sai kuma ta fara ihu,ganin su ukkun sun tsaya kallonta ta 蓷 ora hannu akae tana fadin""dan Allah ku fadamin ta yarda xan gane kuce wasa kuke," "Wlhi Ammah xan fada Maki gaskiyya,komai da komai na Aurenta da Aliyu ta fadawa Ammah,har cikin da ake karya tana dashi duk bata da,baki bude Ammah ke kallonta kenan da gaske ne??""ta nufi Aliyu da wani kalar" "tashin hankali tana fadin""kace wasa ne dan Allah ,na san yayi komai cikin fushine Amma ba halinsa bane,kai ka sani ba halin sa bane.""Ammah ta sauke ajiyar xuciya cike da jimami,ta kalli Khaleel waxeer tana fadin yaje da Aliyu su shirya dan samun jana'iza ,suma zasu shirya suxo gidan gaisuwar,ta kalli Aliyu cikin kakkausar murya tana fada masa ya dawo hankalinsa yanxu,kar kuma ace shine ya tura aka kashe Farhaan din tunda har sun samu sabani,kana jina Khaleel karka barsa ya daga daga inda kake,ka tabbata kana tare dashi.noory ta bisu da ido hawaye na xubar mata,wani irin zafi xuciyarta keyi mata da gaske Farhaan Ya rasu.""??wani xaxxabi taji yana cin karfinta,kusan karfe takwas da rabi tana kwance kan gadon Ammah,ta dunkule cikin duvet Ammah ta shigo dakin,da mug a hannunta,ta kalli Nooriyah wacce idanunta har sun canja sabida kuka." "Ammah ta xauna gefen bed tana fadin""ta tashi ta daure tasha tea,da sauri noory ta shiga girgiza kai hawaye na kara tarar mata ,take fadin""na koshi Ammah ,to mekika sha zaki ce wani kin koshi.""bana son musu tashi ki shanye kibani cup,Bata son yiwa Ammah musu ,ta karbi cup din ta kafa kai bata sauke ba sai da ta shanye duka tea dake cikinsa,da sauri ta koma xata kwanta Ammah ta dakatar daita,tana fadin ta bari ta huta sa'annan ta kwanta.har kusan 12 tana kwance a gadon Ammah,sai da akayi sallar axxahar suka shirya duka familyn waxeer suka nufi gidan gaisuwa,laylah sai kallon noory take dake famar sharar kwallah ta tabe Baki," "Tayi bakin cikin rasuwar Farhaan Shagari, kenan yanxu noory ta samu auren Aliyu waxeer a bagas," "Ammah na rike da hannun nooryn cikin mota take fadin""so kike mutane su fahimci wani abu a fara zargin ki kuma?''da sauri ta shiga goge hawayen idonta,ki natsu dan Allah Nooriyah kar mutane su fara zargin wani abu ki samu a matsala,da haka suka fita daga motar suka nufi cikin gidan,kai tsaye part din Mami suka nufa,yan uwanta kawai ne da yan uwan mijin sai Salma Shagari,mami har yanxu tana kwance a gadon asibiti,Ammah har magrib suna a gidan sai da akayi sallah suka tafi,kowa cike da al'ajabin rasuwar Farhaan din," "Dakin Ammah ta wuce kai tsaye,batareda ta tsaya parlor ba kukan da taji yana shirin taho mata yasa ta rufe bakin da gudu ta nufi toilet. Ammah ce ta tsare Aliyu da plate a hannunta na white rice da stew ,da sauri ya shiga girgiza wa" "Ammah kai yana jin zuciyarsa nayi masa wani iri ,Ammah bana jin yunwa idan naci xanyi amai.""Ya fada babu wani walwala a fuskarsa,Ammah ta daure fuska tana fadin""ina wasa da kaine??""girgiza kai yayi buda baki yyi Ammah ta shiga basa,kusan rabi yaci ya fadawa Ammah idan ya cigaba daci xaiyi amae,kusan karfe goma ya shigo gidan Ammah ,kallonsa Ammah tayi tana fadin""baka kwanta ba." "Ya girgixa kai yana fadin""baxan iya kwana acan ba Ammah ,toh ka shiga ciki matar ka na nan ,itama xaxxabi take tun safe ,amma ta sha magani.gabansa ya fadi shi sai yanxu yama tuna da Nooriyah yana ta zama a parlor tareda Ammah har Kusan goma da rabi Ammah tace yaje ya duba matarsa,tura kofar dakin yayi can tsakiyyar bed ya sameta ta dunkule waje daya,rufe kofar yayi ya nufi kan bed .duvert din ya shiga ja,sukayi ido biyu dashi da sauri ta Runtse idonta xuciyarta na harbawa," "Murya can kasa yake fadin""Ya jikin ki??""kin ci abinci murya can ciki take fadin""ta samu sauqi kuma taci abinci da haka ta Runtse idonta ta matsu Yabar gaban ta" "Shima kamar yasan abunda ke ranta bai takura taba yayi kwanciyar sa akan duguwar soofa din dake dakin,ya rage hasken fitila.dukan su cikin wannan daren babu wanda yayi barcin kirki,washe gari koda ta tashi bata gansa a dakin ba. har kusan 10 bata ga alamar shigowarsa ba,itama kanta dake ciwo tana ta kwanciya a daki." "Areefa tana ta kallon Siddiqa mansoor cike da takaici,wai na tambayeki mana Aunty Siddiqa Wai Farhaan kun hada jini dashi ne,xaki dauki mutuwarsa duk kisa Aranki,Ni dai wlhi bana jin dadin haka,bana son matsala ko kadan dan na girmi kowace irin matsala a rayuwar nan,idan kin shirya ki fito muje gidan gaisuwa ,sai mu wuce wajen malamin.""tayi maganar in I don't care manner's!""ita dai Siddiqa batace komai ba ta koma daki ta dauko Hijab dinta,ta dawo parlor tana kallon Areefa din daga sama har kasa take fadin""ba dai haka xaki gidan gaisuwa ba ,na rokeki ba danni ba ki saka Hijab,Areefa tayi wani irin juya ido nacin Aunty Siddiqa na damunta take fadin""mayafin da na saka fa.""gidan gaisuwa fa gidan gaisuwa Areefa.""tayi maganar da karaya a muryarta ,bakya tunanin a gidan mutuwa kema Allah ya dauki ranki..""tsaya anan dan Allah karki karasa ki daina yimin fatan mutuwa sabida saka Hijab,ki bani naki na saka dan kin san ko acikin kayana babu Hijab,sallah ma da dogayen riguna nake yinta.har suka isa gidan Gaisuwa Areefa na mitaa...." "Take Note.!""" "Team# bati Reader's ban San ku ba ban san a wace dunia kuke ba,kuna karanta hakkin da ba naku ba batareda ko sisin ku ba,ba sai ku Rufe bakin ku ba sai kuka kasa yin haka sai xagi da cin mutunci,nida hakkina ku hanani magana,baku san ya nake squzzing duk wani free tym da nake dashi dan nayiwa wanda suka biyani dan faranta masu ba.sun san wahalar da ake sha shiyasa suka biyani hakkina tun kafin su karanta,idan na xalinci duk wacce take karanta min book batareda ta biya ba,tana kuma xagina a banxa Allah ya isar mata idan kuma kuka xalince Ni ya Rabbi ka saka min tun a duniya," "Haka wallahi tallahi duk wacce ta karanta koda kalma daya na book din nan,banda wanda na bayar a matsayin kyauta Allah ya isa ban yafe ba.." Littafin waminal Hoob na kudi ne #500 Account Details 0004157137 Jaiz Bank Asma'u Buhari Aliyu Katin wayar MTN.ta wannan layin..09060259200 Shaidar biya ta wannan layin#08086207764.. TEAM#WM TEAM#NOORYALI FOREVER 鉂わ笍 ": Basuyi minti goma gidan makoki ba suka fito,sabida ko sun tsaya babu wanda ya sansu,sun dauki hanyar wajen gari Areefa wacce itake driving ta kalli Aunty Siddiqa tana fadin""shi malamin naki ya rasa inda xaiyi gida sai a karshen gari,gaskiyya wannan da sake,barazana ne ga rayuwar mu to idan aka sankame mu a hanya fa.""wai Aunty Siddiqa haka kike dauriya kina xuwa har Nan tun daga unguwarku??gaskiyya na jinjina maki,kinyi kokari haka hakurinki yayi maki Rana,tunda shegen mijinki yanxu ya daina bin matan waje,an riga an kame maki Abar sai yarda kika yi daita.Areefa ta fada tana sakin dariar shakiyan ci.""wanda dole sai da Siddiqa ta saki mumurshi,sunyi sa'a sun samesa sai dai akwai layi. Baki Areefa mansoor ta bude tana kallon manyyan motocin da sukayi parking a kofar" "gidan da bai wuce daki biyu ba aciki,manyyan hajiyoyi taga suna shiga suna fita.da sauri ta kalli Siddiqa aunty Siddiqa duk wannan manyyan hajiyoyin da nake gani wurinsa suka zo?tayi maganar sounding so very confused.""kadan ma kika gani in dai akan aekin malam mai bushasha ne,baya ma harka da kananan mutane,yafi son manyyan hajiyoyi masu kaisa aekin Hajji da umra,auhhh dama zai iya zuwa aekin Hajji kuma yana xuba wannan shirkar,shegen kudi ne dashi har manyyan motoci yana da,to meye Amfanin haka yana zaune cikin irin wannan matsiyaci gidan.""Siddiqa ta tabe Baki tana fadin""Ni dai mu shiga kar ayi mana cin layi.da haka suka kutsa kansu cikin gidan,kallonsa kurum Areefa keyi tsoho ne Sosae sai shegen gemun da ya kusa sauka har a kirjinsa fari sol.""wata big hajia taga ta aje masa jikar kudi,ya girgixa kudin yana fadin miliyan biyu ne aciki hajia,idan aeki yayi zaki dawo ki cika sauran ladarsa,hajiar ta russuna a gabansa tana famar xuba masa godia,jiki sanyaye Areefa mansoor taja Siddiqa gefen tana fadin""naji yana fadin manyyan kudi aunty Siddiqa nida iyakar kudina baifi dubu dari ukku ba,ki kwantar da hankalin ki,da haka tajasa gaban malam mai bushasha,ya kalli Siddiqa yana fadin.""wannan itace kanwar taki??cikin girmamawa take fada masa itace,ya kalli Areefa yana fadin""ta basa hannunta na dama,da sauri ta mika masa hannun ya dade yana kallon hannun," "Kafin ya Runtse ido ya shiga jan tasbahar hannunsa,yafi minti biyar a haka kafin ya bude,yana fadin mekike bukata?""da sauri Areefa ke fadin""dama ina son na shiga familyn waxeer ne,kuma inada ciki so nake duka familyn su yarda da Aliyu yayi cikin,haka ina so na xauna cikin su har lokacin da xan haihu ,ina son na juya yaron da uwarsa,haka ina son a dauki son dunia a 蓷 orawa cikin jikina musamman uwarsa,ina so Aliyu ya rinka bin duk wani umurnina. ""kallonta malam mai bushasha ya tsaya yanayi kafin ya Runtse idonsa ya shiga jan doguwar casbahar" "sa wacce batayi kama da ta sallah ba ko kadan,dan tashi tana dauke da karafuna a cikinta ,ya shiga ambaton wasu kalaman tsafi ya bude idonsa yana kallon Areefa mansoor yace ladan aekin miliyan daya da dubu dari biyar,ta xare ido tana kallon Siddiqa mansoor xatayi magana Siddiqa ta rigata tana fadin toh Malam xamuje mu hada kudin nan da kwana biyu xamu dawo,daga kai yayi alamar ya gamsu.suna fitowa ta kalli Siddiqa mansoor hankali tashe take fadin""kin haukace ne Aunty Siddiqa Ina xan samu wannan kudaden yanxu??""Ni dai na fasa gaskiyya ," "Baxan iya wannan hasarar ba,xanje kawai na fadawa Ammah.nasan baxata goyi bayan zalunci ba.""Siddiqa ta fashe da daria tana fadin""Ashe kuwa xaki rasa sa,wannan karon Siddiqa mansoor ce mai tukin,tana fadin""ban san baki da hankali ba sae yau Areefa kina tunanin kinga sirrinsa kuma kice kin fasa aeki dashi baxai ma yuyu ba,kibari xanyi" "magana da Ahmad ko aron1 miliyan zamu samu a wajen sa ,bakin ce kina da dubu dari ukku a hannunki ba,ba'a rasa dari biyu a hannun na ba sai a hada ba.ta gama da matsalar Aliyu sauran Sufyan mansoor da Abbanta,tasan taurin ran Sufyan mansoor xai iya kashe Aliyu waxeer idan yaji akwai cikin Aliyu waxeer a tare daita,hanyar tsayar dashi kawai xata nema.har suka kai gida ta rasa madafa,har Farhaan ya cika kwanakki ukku da rasuwa kullum su Ammah na zuwa gidan gaisuwa basa dawowa Sai da magrib haka sun samu zuwa ganin mami A asibiti itama Alhmdullh tana karbar sauqi a wajen Allah .sai dai har yanxu bata magana sai dai ta rika bin kowa da kallo ,sai kuma hawayen da basa gajia da sauka a kan fuskarta,ranar da Nooriyah taga mami a matsayin mahaifiyar Farhaan Shagari wandda Farhaan din gaba dayan sa mami ne,mutuwar Farhaan ya dawo mata sabo ,mota ta koma da gudu.ta shiga rera sabon kuka.cikin kwana biyu suka gama hada kudin suka damkawa malam mai bushasha yana kara tabbatarwa da Areefa mansoor bbu ita babu da nasanin aeki tare dashi,wani bakin kwaliyya ya bata yace kartayi wasa dashi duk ranar da ta shirya shiga familyn waxeer kai tsaye xata shiga ta tabbata ta shafa kwallin nan acikin idanunta,Haka duk bayan kwana bakwai zata rika shafasa, karta yi kuskuren ketare ranar shafasa," "Damke kwallin tayi a hannunta tana yimasa godia,tun kafin su shiga mota ta wani rungume Siddiqa mansoor tana fadin""ina farin ciki ina farin ciki.""Aunty Siddiqa ,ta fada sounding so very happy,Siddiqa mansoor taja cheek's dinta tana ware mata ido,itama murmushi dauke a fuskarta,shirin tafia Abuja sukayi dan tun karar Abba da kuma Sufyan mansoor." "Zuciyar Areefa ta riga da ta bushe ko Sufyan mansoor bai isa ya dakatar daita ba,da murna Aunty ta tarbesu wacce ke auren mahaifinsu tun bayan rasuwar mahaifiyarsu,Aunty ta kalli Areefa tana kama baki take fadin""kin ga yarda Kaduna ta kar 蓳 e ki naga kinyi wani uban kiba da kumatu," "Me Siddiqa mansoor ke baki, murmushi kurum Areefa tayi tana fadin""Aunty Yah Safwan fa,tun safe bamu hadu ba.daga waya tayi ta kirasa bai daga ba ta kara kira nan ma bai daga ba,duk tabi ta shiga damuwa,tana kallon kofa sukayi ido biyu da Sufyan mansoor ,wanda da ka gansa kaga fuskar Areefa mansoor shima fari ne sol""tamkar balara be," "Ya bude hannuwa gamida ware mata ,ido murmushi tayi gamida make kafada ya karaso cikin parlorn yana fadin.""ku wannan irin tafiya haka,kuma kina ta kirana a waya ,muna tare da Adee shiyasa ban daga ba. toh fadamin yar" "gidana meya faru ina son Jin good news,shi wannan mutumen da kika bi kika nacewa ya shirya yanxu ko har yanzu.""hawaye yaga suna cika idon Areefa mansoor tasan sune weakness din Sufyan mansoor,ke lafia meya faru??""duk yabi ya rude,siddiqa Mansoor ta kallesa ido cikin ido tana fadin""Yaya cikine jikin Areefa kuma cikin Aliyu waxeer.""girman kalma Sufyan mansoor yakeji tana masa nauyi cikin kirji,cikin shege ajikin kanwarsa.""ya mike a fusace ya xsbgawa Areefa shegen mari ya shakota lokaci daya,tana jin sha 茩 ar da yayi mata tana tabata Amma ko kadan baxata karaya ba,mekake yi haka yaya akwai ciki ajikinta kayi hakuri ka saketa kar kayi mata illah,jikin Safwan mansoor babu inda baya rawa,haka tana hango soyayyarta da kuma tashin hankali lokaci daya acikin idanunsa,sakinta yayi ya juya Yabar dakin ba tareda ya kara kallon su ba,na gama da matsalar Sufyan mansoor bana tunanin Abban,sabida nasan xai fadawa Abban har ishai basu kara saka sufyan mansoor a idonsu ba," "Har washe gari,hakurin Areefa har ya kare da safe ta gaisheda Abba sai dai bai nuna mata komai ba,,hakan na nufin Sufyan mansoor baiyi magana da Abba ba," "Wlhi na gaji ki tashi kawai mu kama hanya na karasa saurin aeki na,,meyasa bakya bin komai a hankali.""komai kiyi tayi masa gaggawa.""Siddiqa ta fadawa Areefa tana kallonta ta dakune fuska tana fadin""na gaji da wannan jiran Aunty Siddiqa kawai mu koma Kaduna idan ya gama fushinsa sai ya samemu acan,abu daya ne baxan iya dauka ba,yace xai taba Aliyu ""baxan iya daukar hakan ba ina son kayana a haka,kuma bana son yace xaiyi Shari'a da Aliyu Dan" "wallahi duka arzikin gidan nan xai kare Ni kawai ki fada masa kamar yarda muka tsara ba shikenan ba.""wayar Siddiqa mansoor ce ta fara ring ganin me kiran ta kalli Areefa da sauri tana fadin""Yaya ne da sauri Areefa tace ki" "daga kiji me xai ce,ku same mu a parlorn Abba da haka ya datse kiran," "Toh tashi muje maybe ya fadawa Abba komai,sun samu Aunty a parlorn tana ha 蓷 awa Abba tea,ko kadan Areefa bata so hakan ba,duk harkar ta bata son yinta da Aunty,kafafunta taji suna rawa ganin irin kallon da taga Abba nayi mata,haka ta kasa karasawa cikin parlorn,Sufyan mansoor ya daka mata tsawa yana fadin""akwai sa'anki anan da baxaki karaso ba,da rarrafe Areefa ta karaso ta xauna akan carpet,cikin rawar murya Abba ke fadin""da gaske ne da gaske ne Areefa akwai cikin shege jikin ki??""dagawa Abba kai tayi,ya kalli Siddiqa mansoor yana fadin""baxata zauna min a gida ba da dan shege ya kalli Aunty fuska bbu walwala," "Yake fadin a hada komai nata yau baxata kwanar min a gida ba," "Ku kaimin shegiya kauye kai Safwan ka fara shiri yanxu,ihu Areefa ta fasa tamkar mai jinnu take fadin""baxan je kauye ba Abba !!""kauye kauye fah.""ta fada tana fashewa da kuka," "Cikin sanyi murya Aunty Siddiqa ke fadin""Abba ae idan aka kaita can asirin mu xai tonu kasan mutanen kauye da saka ido,Ni xan bada shawara,mexai hana akaita gidan su wanda yayi mata cikin,suyi renon tsiyarsu acan idan ta haihu dole ya yarda ya Aureta.""haka ya kamata ayi Abba dan baxai ci bulus ba wallahi .""Sufyan mansoor ya fada yana kallon Abba,daga kai Abba yayi yana fadin""ku fara shiri har saratu tabiku ku damka masu ita,kar ta dawo min a gida har sai ranar da naganta da auren yaron nan akanta.Alh.mansoor ya fada da bakin ciki a muryarsa,har suka isa" "Kaduna acikin motar sufyan mansoor kallonsu kurum Aunty keyi,haka kawai take ji ajikinta ba gaskiyya Areefa da Siddiqa suka fada ba,yarda tasan Aliyu waxeer da mutunci sa da martabarsa,xaiyi wuya ace dan cikin jikin Areefa nasa ne,sai dai yawon da takeyi da maxan banxan da ta saba hurda dasu,suka yi mata ciki ita kuma ganin manyyan kudin dake ga Ali da familyn su xatace cikin jikinta nasa ne ,a gidan Siddiqa Safwan ya saukesu yana fadin""sai da dare suje familyn waxeer,da dare shine dai-dai haka kuma yafi sirri," "Saiti daya tayi na kayan da xata tafi dasu gidan waxeer ,sauran tarkace tasan daga baya xata mallaki fiye ma da irin su a familyn waxeer,ko abincin ta kasa ci duk da cikin bai bata wani wahala sai dai yana yawan sakata cin abinci da kuma kwalama.tun bayan Rasuwar Farhaan take zaune a gidan Ammah,suna ta xuba ido suga me Ammah xata yanke akan auren su,har yanzu taki magana haka ta hana nooryn ta koma dakinta,Matakin farko da Ammah ta dauka shine hukuncin rabasu da junan su,daga ranar da akayi sadakar ukkun Farhaan,ta hana Aliyu kwanar mata a gida," "Shi kuma yaki bude baki ya fadawa Ammah matarsa yake so,xuba ido kurum Khaleel waxeer yayi yana ganin sabon salon da Ammah ta dauko,da taga Aliyu ya shigo mata parlor inhar noory na xaune a wajen xata mata umurnin ta tashi ta wuce daki.ba karamin hurting dinsa hakan keyi ba,ko dan kisising din da yake samu yana rage zafi Ammah ta rufe ko wace kofa," "Itama a bangaren nooryn hakane,sosai take kewar mijinta,duk da mutuwar Farhaan yasa ta dan rage kula Aliyun,Haka karya take tace batayi missing kowane happy moments dinsu da sukayi enjoying tareda Aliyu ba.""ko yanxu tana kitchen Bayan magrib suna shirya abinci dare itada Ammah,mai aekin ta" "Nana ta shigo wacce ke yiwa Ammah wanke-wanke kwata-kwata yarinyyar baxata wuce shekaru goma sha ukku a dunia ba,da ladabi take fadawa Ammah tana da baki.Ammah ta kalli noory tana fadin.""bari taje ta duba da haka ta fice daga kitchen din,Jin tayi anyi hugging dinta ta baya,wani irin ihu ta saka da sauri ya rufe bakinta cikin sanyi murya yake fadin""ke nine fah.""Jin kamshin turarensa yasa ta sauke ajiyar xuciya ,ya dawo gabanta yana kallonta da idonsa da suka fada lokaci daya," "Da sauri ta kalli kofa tana tunanin ta ina ya shigo,dan Allah ka tafi kar Ammah taxo pls,ta fada tana kallon kofa,make kafada yayi yana hadata da jikinsa,yake fadin""Yaushe kika xama muguwa haka.""ta bude ido tana kallonsa,ba sai ki fadawa Ammah gidan mijinki xaki koma ba," "Kinji yarda nayi missing manyyan kayana,ya fada yana tsare kirjinta da ido," "Gabanta na mugun faduwa take fadin""dan Allah ka rufamin Asiri Aliyu kar Ammah taxo ta ganmu,zo muje gida.""ya fada yana jan hannunta ,fisge kanta tayi cike da tashin hankali take fadin ka rufamin Asiri Aliyu.""wai meyasa kake haka?""ya girgixa kai yana fadin""so kike na mutu kenan?ya isa ga gas ya kashe gas din ya dawo gabanta ya shiga kokarin cire botin farar shirt din jikinsa yake fadin""babu damuwa ko acikin kitchen xan iya shan kayana kin ga idan Ammah taxo ta ganmu a haka ,sai tayi tunanin bani matata .da gudu taxo xata bar kitchen din ya wani fisgota ya hade ta da bango,yana kaima wuyanta wani irin deep kisses,lalubar xip din rigarta ya shigayi ya xugesa iya karfinsa,xatayi masa musu ya hade bakinsa da nata,Haka hannunsa ya sa cikin rigarta ya shiga murxa abunda yafi kauna da so a dunia,wani irin rikesa tayi tana jin leg's dinta na kasa daukarta.sunfi minti goma a haka babu abunda ke tashi acikin kitchen din sai saukar breath dinsu,a haka Ammah tayi mugun gani.da sauri taja da baya tana buga kofar, Fisge kanta tayi da sauri tana fashe masa da kuka,tana girgixa kai take fadin""shikenan Ammah ta ganmu,Ya shafa sumar kansa yake fadin""duk ddin da kika gama sha yanxu sai ki bude baki kina kuka,ya dage kafada yana fadin""Allah yasa Ammah ta ganmu na fison haka,ya fita daga kitchen din Yana fadin""ta hado masa black tea Yan......kasa karasawa yayi ganin irin kallon da Ammah keyi masa,juya kaxo da matarka muna da baki da haka Ammah ta juya tabar wurin....." "Littafin waminal Hoob na kudi ne#500 Idan baki biya ba kika karanta ban yafe ba.""" Account Details 0004157137 Jaiz Bank Asma'u Buhari Aliyu Katin wayar MTN.ta wannan lambar#09060259200 Shaidar Biya ta wannan lambar#08086207764 "*The game has just started now,who is ready for d actual Journey???""*" ": Kallon Areefa mansoor Yake with so much shock,tashin hankalin da yake ciki baya faduwa,ba zato suka ga Aliyu waxeer ya fisgota ya bata mari Hagu da dama kafin ya shakota,kara ya kasheta da ta cinnawa familyn waxeer wuta,da sauri Sufyan mansoor yayi kansa sai dai sha 茩 ar da yayi mata bana wasa bane,tamkar ba namiji ba haka ya" "zama ya kasa kwatar kanwarsa a hannun Aliyu waxeer,ya isa ga Ammah yana fadin""ki yiwa mahaukacin yaronki magana rai biyu zai kashe idan wani abu ya sami kanwata shima sai na kashesa baxan jira hukuma ba," "Lokaci daya Ammah ta share hawayen idonta ta nufi Aliyu ta fisgosa lokaci daya ta wanke fuskarsa da mari,xaiyi magana ta Kara xabga masa wani marin.wani irin ciwo kirjinta keyi mata dauriya kawai take a gabansu, fadamin gaskiyya da gaske cikin dake jikin Yarinyyar nan naka ne ko bana naka bane.??""Juya girman 茩 addarar da ta canja masa rayuwa yanxu -yanxu yake har Abada baxai yafewa Areefa mansoor girman laifin da tayi masa ba,Kallon noory kawai yake wanda ko zai samu hop a wurinta tana zaune akan rug,da alama tafi kowa shiga tashin Hankali,baxa kayi magana ba??""Ammah ta fada tana daka masa tsawa,sau kusan ukku yake so ya buda baki yayi magana ya kasa ," Ga maganar yana jinta aransa fitar ta ya kasa. "Hawaye yaji suna cika idonsa lokaci daya,meke damun sane??""""Kar ya dauki girman laifin xina ya 蓷orawa kansa,kallon Ammah ya shigayi yana girgiza kai, kallon sa kawai Noory keyi addu'a kawai take aranta ya 茩 aryata ba cikin sa bane,shurun sa ya tabbatar mata da Areefa mansoor gaskiyya take fada,wani irin ciwo taji kirjinta nayi ciwon da duk wata macce wacce ke son mijinta da kishinsa xatayi duk lokacin da taji Aliyu waxeer ya ambaci sunan Areefa mansoor a gabanta take jin wannan ciwon,haka ta sha jin yarda Aliyu waxeer ke fadin""Yana son Areefa a gabanta ko a bayan idonta,baya shakkar fadin haka .hawayen Ammah sun kasa tsayawa tana gogesu wasu na xuwa,shurun Aliyu ya tabbatar mata da gaskiyya Areefa ta fada,Ammah ta kalli Aunty wacce ta dan ji tausayin Ammah,wanda uwa kawai ce xata ji irin wannan ciwo.""ku taso muje gidan baffan sa," "Ammah ta kallesa ido cikin ido take fadin""ka wuce muje kayi masu jagora su maimaita a gaban uban naka.Wani irin kuka yaxowa noory lokaci daya Rufe bakinta tayi da hannayenta tana girgixa kai kishi na cin xuciyarta, Addu'a take Allah ya cire mata son Aliyu waxeer daga yanxun nan ta huta,daki ta shige ta shiga rera kuka mai ban tausayi,Bayan sun gaisa da baffa dakyar Ammah tayi karfin halin fadin""wurinka suka zo danka ya jawo magana.""Ammah ta kalli Areefa mansoor wacce gaba daya hankalinta na akan Aliyu ,take fadin""fada ma mahaifinsa gashi zaune a wajen ,nan ta fada masa akwai cikin Aliyu waxeer a jikinta." "Kallonta kawai baffa yake tamkar wanda keson ya gano wani abu cikin fuskarsa kafin ya maida kallonsa ga Aliyu,da gaske cikin dake jikin Yarinyyar nan naka ne??""Baffa yayi maganar cikin karyewar murya shiru yayi masu tamkar yarda yayi a parlorn Ammah,hawaye yaji suna cika idonsa lokaci daya,ka buda baki kayi magana dan Allah Aliyu karka karyamin zuciya.......Baffa ya fada cike da karaya a muryarsa ,Ammah ta kalli Baffa tana fadin""baxai yi magana ba fa,tunda yasan ya aekata.""wannan Yarinyyar xata xauna tare dani harta haihu," "Daga ranar da ta haihu tayi Arba'in Aliyu xai Aureta,haka kuma dayan matarsa ya shirya bata takardarta, Baxata kara zaman Aure da maxinaci ba.""" "Baffa ya katseta yana fadin""kiyi hakuri kar abubuwa suyi masa yawa,idan yana son matarsa fa??""Ammah ta mike tsaye ta kalli su Aunty tana fadin""suje,a parlorn Baffa suka bar Aliyu tamkar an dasa sa a wajen,hawaye kawai ke xuba a idonsa," "Meyasa ya kasa 茩 aryata Areefa mansoor agaban baffansa,meyasa ya karbi cikin da shi yasan baida alaka dashi,me Areefa take nema da zata yimasa irin wannan sakayyar??"".,tashi kaje Aliyu Allah ya sauwakke,wata irin kunyar Baffa taxo ta rufesa wacce bai san yana yimasa ita ba sai yau.bai san yana kewar Khaleel waxeer ba sai yau da baya tare dashi,da yake Khaleel waxeer baya gari yaje Sokoto kan wani business dinsu,haka itama laylah tana Abuja ana bikin kanwarta,a wannan daren noory kawai yake son kasancewa tare daita," "Shi kawai xai sata jikinsa ya rarrasheta ya fada mata ba laifin sa bane,baya da alaka da cikin Areefa mansoor,yasan a duk inda noory take yanxu tana can cikin tashin hankali ,yasan kalar kishinta da yana da dama da ya dauketa daga gidan Ammah," Sai dai yasan hakan ba mai yuyuwa bane. acikin daren Ammah tasa aka gyara dakin da Areefa xata xauna harta "haihu,su Aunty godia sukayiwa Ammah,har suka bar gidan suna jinjina karamci irin na Ammah,ko kadan basuyi tunanin haka abubuwa zasu xo da sauqi har haka ba,Sufyan mansoor na driving Yana fadin""dama kun daina mamakin saurin karbar ku da sukayi.ko kadan basa so a taba mutuncin gidan su.idan ma sunki karbarta baga yan jarida da media ba. a wannan daren mutum ukku sunfi kowa shiga tashin hankali da jimami,Ammah Aliyu,da kuma" "noory idan sunce sunyi barci acikin daren nan,sunyi karya,tunda tayi sallar Asubah take zaune akan carpet idonta sun kumbura sabida kuka,duk lokacin da ta tuna akwai dan Aliyu waxeer kwance acikin wata sai taji duniar na birkice mata,idan tace bata kishin Aliyu waxeer xatayi karya,idan ta Runtse idonta hango Aliyu waxeer take tareda Areefa mansoor cikin wani irin moment da kwalkwalwar kanta baxata iya dauka ba,baxata iya sharing dinsa da wata macce a duniya ba,tunaninta ma yanxu yafi karkata da koda ma can Aliyu na neman wasu matan ,tasan Areefa budurwarsa ce wani irin rashin hankali xai saka Aliyu su aekata irin wannan babban xunubin,turo kofar dakin da take akayi.Ammah ce itama tareda Hijab din sallah ajikinta kallo daya xaka yiwa Ammah zaka san bata cikin natsuwarta,sallamar Ammah ta amsa tana tare hawayen idonta da suka kasa tsayawa," "Ta gaisheda Ammah cikin rawar murya,Ammah ta amsa cike da jin nauyin Nooriyah,da wani irin tausayin ta ." """Ban san kalaman da xanyi amfani dasu wajen baki hakuri ba Nooriyah ,ba kowace macce ce xataji abinda kika ji ba a jia kika kwana dashi acikin ranki,sai maccen da 茩 addarar ta fada kanta,baxan iya cewa komai akan wannan lamarin ba,shurun Aliyu ya tabbatar min da Yarinyyar nan gaskiyya take fada,haka baxan yarda ki cutu da Aurensa akan ki ba,dama Auren contract ne wanda akayi Auren dominsa ya riga yabar mana duniar meyayi saura,kara ya dauke maki wannan Auren kowa ma ya huta xan tsaya maki,Koda yaushe ina bayanki. ""kiyi hakuri Nooriyah dan" "Allah kiyi hakuri,hawayen idon noory suka kasa tsayawa itama Ammah hawaye ne a idonta,cikin rawar murya take fadawa Ammah meyasa take bata hakuri da laifin da ba ita ta aekata sa ba.hukuncin Ammah na karshe ne yafi taba mata xuciya ,baxata iya Rayuwar Aure da wani inba Aliyu waxeer ba,shine komai nata haka baxata iya kallon idon Ammah ta fada mata ta yarda ta raba Aurenta da Aliyu ba,A ganinta Ammah duk ta girmi waya'nnan Abubuwan a wajenta," "Amsar ki nake jira Nooriyah amsar ki kawai ce xata natsar da xuciyata ,dan Allah karki ce kin amince zaki cigaba da zama da Aliyu a matsayin miji,dan Allah karki bani kunya Nooriyah ," "Yanxu ne xaki nunawa Aliyu asalin ko ke wacece??''Haka nayi farin cikin da baki baiwa Aliyu budurcinki ba,sai nayi mugun koya masa hankali," "Ki kwanta ki huta ban Amince kafarki ta taka kofar kitchen ba tunda dukan mu muna azumi Areefa kawai ce xa'a ha 蓷 awa break fast,dagawa Ammah Kai kurum tayi.bayan fitar Ammah ta kwanta nan a kasan carpert tana tunanin maganganun da sukayi da Ammah.""" "Kusan karfe tara na safe har daki Ammah taje ta duba Areefa wacce har tayi wanka taci uban kwaliyya sai kaice mai shirin zuwa party,ta 蓷 ora kafa daya kan daya tana danna waya,ga kayan marmari nan ajeye an yanka su cikin madaidaicin tray ,Kallonta Ammah kawai keyi ta tashi xaune tana kallon Ammah tana fadin""Ammah ina kwana,Ammah ta amsa da lafia tana fadin""a kawo mata break fast ko zata je a dinning area tayi ,dan murmushi Areefa tayi tana fadin""muje nayi acan Ammah dama duk zaman ya isheni,Ammah tasa mai aeki tayi serving din Areefa." "Areefa ta kalli Ammah tana fadin""Ammah ke baxaki xauna muyi ba, Ammah ta girgiza kai take fadin""ina azumi ne kin san yau Litinin," "Shiru Areefa tayi tana kallon Ammah wacce ta koma cikin parlor ta xauna tana ta kiran wayar Aliyu a kashe," "Har Areefa ta gama break fast ta dawo cikin parlor tana jan Ammah da hira,dai-dai lokacin Nooriyah ta shigo cikin parlorn suna hada ido da Areefa ta wani dauke kai,taxo ta xauna kusa ga Ammah,Ammah ta kalleta cike da kulawa take fadin""har kin tashi barci,ta daga kai tana fadawa Ammah ta tashi ta gaji da kwanciya a daki.da yake itama ta dauki azumin tamkar yarda ta ga Ammah nayi litinin da Alhamis Ammah ta kalli Areefa tana fadin ga matar Aliyu" "ku gaisa Areefa,wani kallo Areefa ta yiwa noory ,kafin tace ya kk" "ganin yarda Ammah ke kallonsu yasa Noory tayi karfin halin fadin""ina lfy ya jikin ki.""babu abunda tace ta shiga danna wayar hannunta,Aliyu ne ya shigo parlorn dauke da sallama a bakin sa," "Tunda ya shigo parlorn idonsa ke kan noory,wacce kallo daya tayi masa ta dauke kai xuciyarta na bugawa da sabuwar soyayyar sa,Areefa na ganin sa ta shiga sakin murmushi,ya gaisheda Ammah ta amsa can ciki fuska babu walwala ,Ammah ta kalli Areefa tana fadin.""kin taba zuwa Asibiti??Areefa ta girgiza kai tana fadin"".sau daya tun lokacin da mukaje tare da Aunty Siddiqa,Ammah ta kallesa tana fadin" "Ya kamata kuje Waxeer hospital a Buda Mata file,a dubata a san watannin cikin.""Ammah muje yanxu ma dan ina jin yana yimin wani iri.""Areefa tayi maganar tana kallon Aliyu wanda ya hade rai lokaci daya,jin haka yasa Nooriyah tabar masu parlorn Ammah ta dan yi murmushi tana fadin""toh kije ki shirya ki fito,shi dai Aliyu yyi tsaye a parlorn yana so yabi noory A daki sai dai ganin Ammah ya kasa,Ammah ta hade wani abu da ya tsaya mata arae kafin tayi breaking silent dinsu da fadin.""ina jiran takardar Nooriyah nan da kwana ukku,Ni har nayi mata miji.""a wani irin haukace ya juya yana kallon Ammah," "Xaiyi magana sai ga Areefa ta fito da dan mayafinta wanda ta axa a kafadanta sai kuma bag dinta,ta mikawa Aliyu bag din fuska bbu walwala take fadin""rika min Captain wani irin kallo yake yimata itama ta tsaresa da idanunta ,wani abu yaga yana fitowa cikin nata idanun,tamkar walkiya haka gabansa yayi mugun faduwa,karbar jakan nata yayi da sauri hannunsa ta kamo ta saka cikin nata,ta kalli Ammah da jikinta yayi sanyi lokaci daya tana fadin""Ammah sai mun dawo pls Ammah ki saka noory tayi min sakwara da stew na egusi,nasan ta iya girki sosai kisa tayi min dan Allah xanfi jin dadin nata fiye da na yan aeki.""Ammah ta sauke ajiyar xuciya tana fadin insha Allahu ,da haka suka fice daga parlorn tana sakin wani murmushi,Ammah xuciyarta na harbawa tabisu da kallo.Haka ya rika driving tana masa hira wani ya amsata wani yayi shiru,ta kallesa shaye da toka tana fadin""Yaushe xaka saki wannan Yarinyyar ba naji Ammah na fadin ka saketa ba .""me kake jira kuma.xan saketa Areefa ta bude masa ido tana fadin da yafi dai ,dan Ni bana sonta ko kadan," "Nasan kaima haka ??""ko ba haka ba ta fada tana tsaresa da idonta dake saka sa shiga cikin wani irin yanayi,muga wayar ka, mika mata wayar yayi tana fadin.""" "Yanxu nake so kayi sakin nan a waya.""" "Bari kawai na saketa tunda kai baxa ka iya ba,Ammah tana ta fadin ka saketa ka wani nace mata ko ka fara sonta ne??""tayi maganar cikin daga murya tana kara tsaresa da idanunta,cikin rawar murya yake fadin""ban fara sonta ba, typing ta shigayi a wayarsa" "Tana fadin""idan Ammah ta tambayeka kai ka saki Yarinyyar nan,ka fada mata Ehhh kana jina??""da sauri ya daga kai, Zuciyarsa na bugawa." "Taya xai saki noory ya Rabbi kana gani," "Typing ta shigayi cikin minti biyar ta tura ta basa wayar tana fadin""mu tsaya ka siyamin mitpie,bana awa biyu ban ci wani abu ba, ta fada tana rike da hannunsa tana murxawa,tun fitarsu Aliyu da ta shige daki take famar rera kuka, Wanda ta rasa ko na menene.xuciyarta take jin tamkar xata fita sabida kishi,tana kokarin cire Aliyu daga ranta,sae kara sonsa takeji a xuciyarta ," "Xata fadawa Ammah ta amince Aliyu ya sauwake mata wannan Auren ,idan ta fita daga Rayuwarsa A hankali xataji soyayyarsa xata fice daga ranta batareda ta sani ba. Wayarta ta dauko taga sako ya shigo a wayarta,kuma da sunan" "Aliyu .da sauri ta buda sakon," "Abun da ta gani a wayar ya saka ta fasa wani irin ihun,da Ammah na zaune a parlor sai da taji ihun,girgixa kai ta shigayi tana fadin""pls karkayi haka Aliyu Dan Allah karkayi haka,banyi fushi ba hakama ina sonka a yarda kake ina sonka.""" "Na amince ko mata ukku xaka aura a lokaci daya xan xauna da kai a haka,Ammah ta riketa tana girgixa ta take fadin""meye haka noory meya faru??""so kike kiyiwa Kanki illah sabida soyayyar da namiji," "Hannunta na rawa ta mikawa Ammah wayar hannunta,tana murmushi take fadin""kice idona ne Ammah ba gaskiyya bane,,kice soyayyar Aliyu da kishinsa suka mai dani a haka..." "Littafin waminal Hoob na kudi ne# idan kika karanta min book baki biya ke ba yar halak bace,Allah ya isa!""""Allah ya isa!!!" Account Details. 0004157137 Jaiz Bank Asma'u Buhari Aliyu Katin wayar MTN.ta wannan lambar#09060259200 Shaidar biya ta wannan lambar#08086207764 SUMAYYAH ABDULKADIR 07030137870 PAID BOOK NA HUCE "Tana shiga dakin ta Habibu yana shigowa shima, da azama ya tura kofar ya rufe su har da key, da wata irin sasssarfa ya cimmata. Gabadaya ya shige cikin jikin ta yana kiran ta da sunan da bakin sa ke son kiran ta da shi a kullum wato RAHEENAH OMAR!" 鈥滲 a zaki gaya min abinda ya canza ki ba? You are looking additionally ravishing!. "Ya dago habar ta da yatsun sa biyu yana kallon kyakkyawar fuskar ta, wadda ta zama fresh kuma jajir irin ta mai yaron ciki, kafin a hankali ya sumbaci saman dogon karan hancin ta." "Ba shiri Rahinah ta lumshe idanun ta yayin da lips din Habibu suka sauka saman nata, ya soma kissing din ta very gently wanda hakan yasa ta saurin kai hannun ta cikin sumar kan sa, dragging herself closer to him in a gentle" "manner ba tare da ta san lokacin da ta yi hakan ba, ta hade ratar da ke tsakanin su. Habibu da Rahinah suka dunkule suka koma abu guda tamkar curin alkaki." "Jikin ta ke gaya mata wannan itace kauna da soyayya na zahiri da badini wanda Allah kadai ya san iyakar sa, wato iyaka son da take wa mijin nata Allah kadai ya san iyakar sa. Jikin ta har rawa yake yi domin sumbatar da Habibu ya ke mata babu sauki a cikin ta." "Kusan tunani iri daya suke yi shi da ita, domin ya tabbata Rahinah Omar cikon farin cikin rayuwar sa ce, wadda ba zai iya rayuwa cikakka kuma mai maana ba tare da ita ba." "Bata iya ta ce masa komai ba a kan abinda yake son ji din, duk da nacin tambayoyin da yake mata a kan canzawar ta, har sai da suka samu nutsuwar da suke so su samu. Sannan ne Rahinah ta kwantar da kai a kafadun Habibu, ta ce." Menene tukuici na in na gaya maka cewa i 鈥檓 pregnant?鈥฀ "Da wata irin azama ya dago fuskar ta cikin tafukan sa, ya dube ta sosai cikin idanun ta 鈥漅 ahinah ki ce kawai har yanzu ina nan a 鈥榮 harp-shooter 鈥฀ dina. Kuma na sake saka kwallo na a raga a Jamus yadda na saba 鈥฀. Ya kankameta gabadaya yana gaya mata cewa." "鈥漅 ahinah na wahala, na wahala a dalilin rashin ki, shekara goma ina ragaita a cikin soyayyar ki, da baki dawo cikin rayuwata ba na tabbata hakan zan kare ta incomplete and shattred." Kina dawowa kuma kin zo min da BLESSINGS upon BLESSINGS..... Hotels dina sai kara bunkasa suke a kasar Najeriya. Wannan shine albishir na biyu da yafi kowanne muhimmanci a rayuwa ta bayan na cikin Abdallah. Me kike so in yi miki a rayuwa don in nuna godiya ta da farin ciki na ga wannan albishir? "Rahinah ta sake narkewa a jikin Habibu. Cikin jin dadin maganganun sa ta ke fadin 鈥滺 abibi? Ka san bana son komai sai kai ko? Ka san kai kadai nake so ko? To tukuici na shine ka cigaba da son mu ni da 鈥檡 a 鈥檡 a na, ka bamu lokacin ka yadda ya kamata, duk da cewa kana kokari wajen hakan to ka kara." "Kada neman kudi yasa ka dinga tsallake mu na lokacin da bazamu iya jurewa ba 鈥฀. Habibu na shafar sumar kan ta ya ce," 鈥渋 n don wannan ne kin dade da samu Dr. Rahinah. Ni na dauka ma cewa zaki yi in bar ki ki koma aikin ki a NIZAMIYE?鈥฀ Ta girgiza 鈥漦 ai tunda baka so na dade da baiwa aikin nan baya tunda hankalin ka bai kwanta da shi ba 鈥฀. Habibu ya rungume Rahinah tamkar zai tsaga kirjin sa ya sanya ta 鈥漬 i kuma na yi miki alkawarin gina miki asibitin dashen kunne naki na kan ki a nan Abuja inda bazaki zama a karkashin kowa ba sai dai kowa ya zama a karkashin ki 鈥฀. "Da na fi kowa farin ciki Habibi, because I so much like my career." ******* "A daren ranar, suna zaune suna cin abincin dare a kan dining din su dake kitchen mai cin kujneru uku kacal, Habibu ya ce da Abdallah 鈥淪 on, gobe zaa kara kujera a nan. Abdallah ya ce sabida me zaa kara kujera Daddy ba mu uku bane a gidan?鈥฀ 鈥淪abida mu fara shirin tarbar kannen ka da ke kwance a cikin Mummy Abdallah ya yi saurin kallon ta 鈥渨 ai haka Mum? Da gaske zaki haifa min kanne muma mu zama da yawa a gidannan?鈥฀" Kafin ta samu zarafin amsa masa an kira Habib a waya ya daga yana sallama. "A ka 鈥檌 dar Habibu Nahuche, bai daukar bakuwar lamba, don haka zamu iya cewa wannan da ya amsawa kai tsaye yayi babbar sa 鈥檃." Muryar kamar ta larabawa haka da bata kware da hausa ba sosai ta yi masa sallama. "Habibu ya amsa ba yabo ba fallasa, sai mutumin ya ce kana magana da CMD na Nizamiye Hospital Dr. Irshad Salih" 鈥฀. "Habibu ya yi saurin duban Rahinah da ke cin abinci kamar yana son karanto wanene Irshad din a kan fuskar ta, don dai ya tabbata ta fannin ta ya san wannan sunan. Bai samu karanto abinda yake son karantowa ba Irshad ya cigaba da magana cikin ladabi da girmamawa." "鈥滿 r. Nahuche na kira ne domin in baka shawara ta wani fannin in roke ka, kan ka bar Dr. Rahinah ta dawo bakin aikin ta, in ma albashin ya yi kadan ne asibiti zai nunka mata, hakika barin Dr. Rahinah Omar aiki babban gibi ne ga Nizamiye sannan babbar asara ce ga alummah." A madadin dukkan abokan aikin ta na Nizamiye Hospital muke rokon ka wannan alfarmar. "Habibu ya saci kallon ta numfashin sa da kishi yayi wa illah yana sassarfa, kamar Irshad ya san halin da ya ke ciki sai ya ce ""in kuma sabida ni ka hana ta aiki sai in ce ka yi kuskure, ina mai tabbatar maka bani da wani sauran buri a kan ta tunda ta koma gidan mijin ta." "I congratulate you for that"". Habibu ya hadiyi miyau da kyar, a wahale ya ce ""to madallah da shawarar ka Dr., zamu duba""." "Daga wannan ya yi maza ya kashe wayar sa zuciyar sa na wani irin zabalbala kamar ta fito ta bakin sa. Kallon da ya sakarwa Rahinah saura kadan ta saki fitsari a jikin ta sabida zafin sa, wani irin zazzafan kallo ya yi mata wanda ya fi karfin harara. Ta yi maza ta ajiye cokalin hannun ta ""Habibi? Lafiya? Kai da waye?""" "Mikewa ya yi ya fasa cin abincin nata, da kyar in ba ita ta bawa bazawarin ta lambar wayar sa ba, in ba haka ba a ina ya samu?" Wani mikakken tsaki Habibu ya yi wanda Rahinah bata taba jin ya yi irin sa ba. Kai shi a ya tsaki ma domin ya kan ce dabi'a ce mummuna. Ya doshi hanyar ficewa daga falon. "A wannan lokacin ya zabi yayi nisa da Rahinanh ne don kada yayi abinda zai zo yana nadama. Ta bi bayan sa, amma bai tsaya ba, ko kafin ta cimmasa ya bude mota ya shige ya rufe ya tayar." "Irin kurar da ya bula mata a gidan Badiyya yau ma ita ya bula mata da ace da kasa a harabar gidan su. Maigadin gidan kan sa ya tsorata, ba shiri ya bude masa kofa ya fita saura kadan ya bi ta kan yatsun sa." "Rahinah ta dade tsaye a kofar shiga falo kafin ta koma cikin gida cikin tashin hankali, ta rasa abinda aka gaya masa a waya da ya fusata shi haka, koma menene ta gane yana da alaqa da ita, ta soma kiran wayoyin sa amma suna ta ringing bai daga ko daya ba." "Ba shi ya dawo gidan ba sai karfe sha biyu na dare abinda bai taba yi ba, ya zauna ne don kada ya dawo gidan sai Rahinah ta yi barci, wanda hakan ya fusata Rahinah kwarai kuma bata yi barcin ba, kwance take lamo bisa gado ta kurawa kofa ido tana jiran ganin ta inda zai bullo. Ta sha gaya masa ba abinda ta tsana irin yayi dare a waje." "Sadaf-sadaf ya shigo dakin kamar mara gaskiya ya dauka barci take yi. Yana rufe kofar tace ""Habib daga ina kake?"" Batare da ya juyo ba yace ""daga inda kika aike ni"". Ya canza kaya ya kuma fice daga dakin. Bata yi zuciya ba ta bi shi nasa dakin." "Yana kokarin jan duvet ya rufa ta rike duvet din. Idon ta cikin nasa amma sai yayi kokari ya kauda kan sa. ""if you dont mind, pls go to your room, i want to be alone"". Rahinah ta sakar masa duvet din ta ja gefe ta kwanta a daidai kafafun sa tace ""babu inda za ni saidai in ka gaji da ni ne ka san yadda zaka yi da ni""." (Rana ta farko da suka kwana kai da kafa a gado daya tun bayan shiryawar su). "Washegari ma bai ce mata komai ba akan wayar Dr. Irshad, sai fushi yake kamr ya ci babu, har ya je Transcorp Hilton ya dawo. Sannu da zuwan data yi masa ma bai amsa ba. Har suka zo kwanciya barci baya kula ta. ""Duk me yayi zafi Habibi?"" Rahinah ta tambaya cikin damuwa tana share hawayen da suka cika mata ido. Yace ""pls leave me alone i want to sleep"" tace to Baban Abdullahi ko na minti daya baza mu yi magana ba? Haka zamu kara kwana kana jin zafi na akan laifin da ban san na yi ba?"" Sai hawaye." Bai tanka mata ba ya ja duvet har kansa ya rage karfin iya kwandishin da remote. Har zuwa wayewar gari da ya je masallaci yayi sallahr asubah ya dawo. "Rahinah bata kara gane kan Habibu ba har tsayin kwana hudu, this is the hidden side of him da bata sani ba, dama an ce wasu halayen baka sanin su sai zama ya yi zama. A kan kishin Rahinah yana ji a ransa zai iya komai da zai zo yana nadama ko da zai kare a karkashin kanta. Domin zuciyar sa har cewa ta ke da shi ya je ya take Irshad da mota in ya so ko me za'ayi masa ayi." "Shi da kan sa ya soma jin tausayin ta sabida yadda damuwa ta sukurkuta ta, ta ramar da ita cikin kwana hudu kacal, ya soma addu'a akan karan kan sa kan Allah ya sassauta masa." "Ba karamin yaki ta yi da zuciyar ta ba kafin ta iya fita harkar Habibin nata, a ganin ta ya fara gajiya da ita ne, in ba haka ba daga yin waya sai ka tsiri sabon hali? Matsalar ta guda daya ce sun yi mugun sabo da juna tun bayan dawowar su Jamus jinyar Hajiya, ta yadda basu kara raba daki ba, shi ya sanya canzawar da yayi mata da sabon halin da ya tsira na fita harkar ta da rashin yi mata magana cikin kwanaki hudunnan ya dagula lissafin ta ba dan kadan ba. Addua Habibu da yake ta yi da kokarin sanyawa ransa salama ko ta halin kaka shi ya sassauta zuciyar sa. Sabida ya fara tuhumar kansa da over-reacting. Yau da daddare ya shigo dakin ta, sai ya same ta tana gyaran gashin kan ta." Har wata munafukar ajiyar zuciya Habibu ya saki don tun safe bai sanya ta a idanun sa ba itama ta yi fushi ta rabu da shi. Ta bar bin ko hanyar dakin sa. Sai ya hau takalar magana. """Ban ga abinci a dining ba, ko har yanzu baki gama ba? Ga Junior yana shirin yin barci." "Habibu Nahuche ya fada cikin dakewa, shi a dole ga wanda aka yi wa laifi ya kasa hakura kuma bai hakuran ba. Ba tare da ta bar abinda take yi ba, kuma ba tare da ta juyo ta dube shi ba Rahinah ta amsa." """Ban girka ba!" "A lokacin ta lura ya gama saukowa neman hanyar shiri yake yi girman kan sa na hana shi, ita kuma a lokacin take son aza harsashin nata rikicin, Habibu Nahuche, ya wahalar da zuciyar ta a kwanaki hudunnan babu gaira babu dalili a kan laifin da shi kadai ya san shi." """Kamar yaya baki girka ba? Me zamu ci kenan? Ga Abdallah ya fara gyangyadi a falo. Rahinah ta kyabe baki ta ce ""sai ku sanya apron ku shiga kitchen." "Kwafa yayi ya juya yana fadin ""namiji mijin mace hudu me ya kai shi sanya apron don shiga kitchen? Alhalin matan duniya basu kare ba?" Murmushi ta yi ta cigaba da tazar gashin kan ta ta manta da shi. Shi kuma ya juya ya bar mata dakin. "'Cornflakes ya hadawa Abdallah ya sha, shi kuma ya zauna a falon kasa yana kallon labaran Aljazeera. Amma duk ya kasa nutsuwa da tunanin ta. Misalin karfe goma lokacin Abdallah ya dade da bingirewa yana barci a kan littatafan sa daga yin homework. Habibu ya duba rantsatstsen agogon 'Swatch Blustery da ke daure a damtsen hannun sa na hagu, lokacin kwanciyar su ya yi amma har lokacin bai ga gilmawar uwargida Dr. Rahinatu ba." Ga dukkan alamu ya kara iza wutar fushin ta da furucin sa na dazu da ya ce namiji mijin mace hudu ne ana me zai sa rigar shiga kitchen? Tuni ya gama nasa fushin so ya ke a shirya ego din sa ke hana shi ba da kai warwas. Ita kuma yanzun ne ta dora nata akan nasa. Ta rantse sai ta rama! "Duk nauyin Abdallah haka ya sunkuya ya dauke shi a kafadun sa zuwa dakin sa. Ya kwantar da shi a gadon sa sannan ya karanta addua ya tofe shi kamar yadda ya saba kullum, ya rage masa hasken lantarki tare da kashe iya kwandishan." "Dakin sa ya koma sai bai ganta a can ba kamar yadda ya yi tsammani, ko jiya da yake fushi bata fasa kwanan dakin ba illa sun kwanta kai da kafa, ko yaya ta rabe shi sai ya janye ya matsa nesa da ita." "Yanzu da ya dawo hayyacin sa sai ya ke tambayar kan sa ita meye laifin ta don Irshad ya kira shi a waya ya ce ta koma aiki? Zai iya rantsuwa kan ba ita ta baiwa Irshad lambar shi ba, to akan me ma? A kan me zata yi waya da shi bayan ta ajiye musu aikin su har ta kai ga bashi lambar wayar mijin ta?" "Zama ya yi a gefen gadon sa jikin sa duk ya yi sanyi, wata kewar Rahinah Omar ta zo ta lullube shi. Sai kawai ya hau Safah da Marwah a dakin yana jiran shigowar ta, ya yi wanka kamar yadda ya saba kafin ya kwanta, ya sha turaren sa Carolina Herrera (Men) duk don tarbar uwargida Rahinah da yin abinda zai sanyaya mata zuciya, Pajamas din da ya sanya yau bai taba amfani da su ba su yan gidan Ralph Lauren farare sol, ya hau bisa gadon sa yana amsa sakonni cikin wayar sa yana kuma duban kofa yana jiran shigowar ta, duk zafin kan ya sauka, lallashi yake so ya yi amma har karfe sha biyun dare babu Rahinah babu alamar ta." "Ya dauki wayar da ita kadai yake kira da ita ya soma kiran layin ta, tana daga kwance tsakiyar gadon ta tana kallon kiran sa nata shigowa akai - akai yana katsewa cikin wayar ta dake gefen filon da ta ke kwance a kai amma ko kyakkyawan kallo bata yi wa wayar ba balle ta daga." Ta yi rantsuwa da Allah sai ta rama itama na kwana hudu daidai. "Kiran na ta shigowa yana katsewa. Habibu ba ya so ya zo kofar ta ya yi mata knocking sabida kada ya tada Abdallah. Bunch of keys na gidan gabadaya ya dauko cikin durowar gadon sa ya fito, ya brufo dakin sa zuwa nata." "Haka ya yi ta gwada mukullan har kofar dakin ta bude. Har wata siririyar ajiyar zuciya Habibu ya saki, sannan ya sanya kai a dakin." "Kwan fitilar da ta kashe ya kunna dakin ya wadata da haske. Idanun ta a lumshe suke tamkar mai barci, amma da ya shigo ya kunna fitilar sai ta yi maza ta rufe su ruf bakidaya. Bai yi wata magana ba kawai ya hau gadon ya cakumota yana kokarin , sai kokawa ta kaure sosai tsakanin su, Rahinah ta ki bada go ahead ko kankani, kokari take ta ture" "duk wasu sakonnin soyayyar sa masu zafin gaske, da kokarin sa na wanke laifin sa. A karshe ma da ta ga bai da niyyar hakura, domin sosai ya yi kewar ta kuma ya gaji da fushin daman shi ya sanya kansa ba wani ya sanya shi ba, sai ta saka kuka mai nuna maraicin ta." """Ka rabu da ni kawai kowa ya yi harkar sa cikin gidannan Baban Abdallah (yau ta cire Habibin) tunda 'yammata masu bugo waya sun iya hada mu fada"". Dariya ce ta kama Habibu, ya sanya fuskar ta cikin tafukan sa karan hancin sa na gugar nata ya ce ""kafin in baki amsa, pls allow me to kiss this impertinence mouth a little, because i desperately missed its tasty juice.... Ya soma sumbatar Rahinah with great passion in such a way that, duk fushin ta bata san" lokacin da ta bada kai borin ya hau ba. Aka koma kan light blue cloud (kan gajimaren) soyayyah kamar ba su ne masu fadan ba kuma. Kowanne kokari ya ke ya nuna wa dan uwan sa zahirin kaunar da yake masa. Wadda ya ke imanin zai iya fansar da ran sa don farin cikin dan uwan sa. "Habibu Nahuche da Rahinah Omar, wasu ajiyar Allah ne masu son juna saboda ALLAH. Wadanda suke fatan ko a gidan aljannah su tashi tare matsayin ma'aurata kuma abokan rayuwar juna. Soyayyar su extraordinary ce. Komai fushin da zasu yi da juna suna son junan su, kuma ba sa iya jan fushin da tsaho sabida intimacy da ke tsakanin su. Tun daga lokacin da suka samu daidaito na fahimta a auratayyar su." "Suna kwance wajejen asubahi cikin duvet, tamkar masu tsoron kada wani iftilain ya kara ratsawa ya raba su! Rahinah dai bata kara tada zancen waya ba. Shi da kan sa yanzu ya tado zancen, kansa na bisa kafadun ta. Yana kallon kyawawan idanun ta cikin dan hasken dim light." """Rahinah idan kodadden bazawarin kinnan ya kara shiga harkata zan je har Nizamiye a gaban maaikatan sa in masa kamshin mutuwa. Ina ruwan sa da hukunci na akan iyali na? Banda har yanzu yana kawa zucin ki? Da zai wani bugo min wata munafukar waya wani wai in bar ki ki koma aiki zasu ninka miki albashi. Ko dai don kawai ya dinga kalle min mata kullum? In ba don hakan bane mene ne zai sa ya bi ya damu kan sa sai kin koma aiki asibitin su?" "Sai a wannan lokacin Rahinah ta san wa ya bugo wayar da kuma abinda ta kunsa. ""Umh kawai ta ce. Don bata da abun cewa. A zuciyar ta ta ce." """An gaida HABIBU NAHUCHE!" "Habibu ya cigaba da mita da korafi yana aman kishin sa son ran sa, bata tanka shi ba, a karshe kuma ya buge da bata hakuri ganin ta soma hawaye. A hankali ta ce ""ni meye nawa ne a ciki Habibi? Tsakani da Allah ko baka ce in bar asibitin nan ba na yi niyyar bari da kai na. Don in samu cikakken lokacin iyali na. Amma sai kayi punishing dina har kwana hudu ko murmushin ka na rabu da gani." "Wannan zalunci ne babba ma kuwa, kuma rashin adalci ne ga wanda bai ko san laifin da yayi ba." "Dariya ce ta kama Habibu amma ya san bai isa ya yi ta ba, a yadda Rahinah take fusacen nan da shi, don haka ya hadiye kayar sa. Yace ""to ai gara dana huce a kan ki, akan dai in je har ofishin sa in masa one blow one die, a zo a samu a jarida ana ""Habibu Nahuche Runs Mad 鈥฀. Tunda dai ni kin san yan jarida kadan suke jira a kai na sai kace wani dan siyasa." "Im sorry once again and again, Mrs. Nahuche bazan sake ba!." "Ire-iren wannan ta sha faruwa tsakanin ta da Habibu in dai akan kishin sa ne, in har yana da flaws cikin muamalar su to bakin kishin sa na tsiya ne, wanda ya wuce kima, dama kuma an ce zo mu zauna zo mu saba, kuma tsakanin harshe da hakori ma ana sabawa balle maaurata." Soyayyar da tasirin ta baya hana sabani da kananan rashin fahimta wadanda a karshe kuma kusanci suke karawa zukatan su idan aka samu fahimtar juna eventually. "Watanni shidda rus a tsakani lokacin cikin ta ya isa haihuwa. A wani dare ta haifo santaleliyar diyar ta mai kama da ita a komai a sibitin 'National Hospital'. Ranar suna sai kowa ya ji Habibu ya ce sunan yarinya Daada watau (RAHINATU). Kwallar farin ciki ta zubowa Rahinah Omar, a kan wannan karamci da Habibu ya yi mata." "Rahinah ta rike Daada Rahin a kan cinyoyin ta ta tallafo kan ta a hannayen ta, tana kallon ta with so much affection, bakin Babyn irin na Habibu ne amma da ita take kama sak, har hasken fatar." "Wata irin kaunar jaririyar na hankoro a zuciyar ta sai smiling take tana hadawa da blushing. Habibu da ke gefen ta ya ce ""baiwar Allah kada ki cinye min ya, irin wannan kallo haka?" "Ni dai addua ta ita ce ta dauko halin Dadar Adamawa (mai rasuwa) ba halin Dadar Jamus ba (Rahinah Omar) mijin ta ya zo ya shiga uku da tsiwa, da kafiya da rashin yafiya." "Dariya ta yi, wadda ta fiddo fararen hakoranta masu kama da kankara don haske, ""Habibi, shaidar da zaka yi min kenan? Shaidar miji fa shaidar Allah." "Yace ""of course wannan halin ki ne (tsiwa, kafiya da taurin kai) shikuma hali zanen dutse ne, shiyasa nake nemawa diya ta tsari da irin sa." ******* Kafin Rahinah ta yaye SAMHA Habibu ya aza harsashin ginin asibitin ta a Katampe. Sabuwar unguwa ce akan hanyar shiga FCT Abuja. "Abdallah na ji da Samha, ko kuda baya bari ya sauka a kanta yana gani bai kore shi ba. Ta saba da shi sosai in ya tafi makaranta ya dawo har faduwa take tana fasa baki wajen kokarin fitowa yi masa sannu da zuwa." "Shekarar Samha uku ginin asibitin Dr. Rahinah ya kammala a Unguwar Katampe (Main). Habibu ya bata zabin sunan da zata sanyawa asibitin nata, sai ta ce a sanya masa suna;" """NAHUCHE OTORHINOLARYNGOLOGISTIC SPECIALIST HOSPITAL." "Farin cikin Rahinah a wannan ranar da ake bude asibitin ba zai misaltu ba. Ga Habibun ta duk inda ta sanya kafa nan ya ke mayar da tasa, ga yayan ta biyu a gefe Abdallah dan saurayi mai shekaru sha biyar da kanwar sa Samha rike a hannun sa karkashin kulawar Sahura, ga iyaye da masoyan ta duk sun hallara, Anty Badiya, Nene, Safeenah da matan sarkin Fulani sune a kan gaba, da sauran cousins din ta da nephews na Girei, a bangaren maza kuwa Sarkin Fulani ne tare da Uncle Usman, Musaddiq da kannen sa, Abbas da su Ahlan yayan Nene." "Abba Jakada (Ambassador Shehu Bichi) shi ya bude asibitin ta hanyar yanka dan kyallen da almakashi kowa ya shiga kayataccen karamin asibitin wanda specifically na matsalar kunne, wuya da makogaro ne." "Yawancin maaikatan da ta dauka abokan karatun ta ne a Jamus da suka dawo Nigeria tare, sai professionals daga Nizamiye da National Hospital wadanda zasu dinga aiki part-timely tare da ita." "Asibitin ya fara cikin dimbin nasara kuma burin Habibu ya cika, Rahinah ta zama bata karkashin kowanne CMD da zai rika bata umarni sai dai ita ta bayar." "Asibitin ta mata likitoci sun fi yawa. Ta samu membership da kungiyar likitocin Kunne, wuya da kokon kai na Africa, Najeriya dana Jamus da aka fi sani da African Head and Neck Society (AfHNS), Otorhinolaryngolocical Society of Nigeria, German Association of Ear, Head and Neck Surgeons da wasu da dama." ***** (SHEKARU GOMA A GABA) "Burin Abdallah Nahuche shi ne ya zama cikakken sojan sama, kamar yadda burin iyayen sa shi ne su hada aure tsakanin sa da Zahran Aunty Badiyya a shekarun girman su, duk da ba wata rata ce mai yawa a tsakanin su ba." Dr. Rahinah ta ci gaba da aiki karkashin gwamnati bisa yarda da amincewar maigidanta Habibu Mustapha. A gefe tana kula da nata private hospital din. NAHUCHE HOTELS sun bunkasa sun shahara ta yadda suka zama akwai rassansu a ko ina a jihohin Najeriya talatin da shida (36 States of the Federation). "Ya dukufa wajen aikin alheri da taimakon marassa karfi da matasa masu buri kamar sa a baya da tsaftatacciyar dukiyar sa ta hanyar yin amfani da connections din sa wajen samawa matasan Zamfara ayyukan yi, sunansa da na hotels dinsa ya ci gaba da yin tambari a kasar Najeriya, Nahuche Hotels ya zamo lamba daya a duk inda aka ambaci masaukin baki a Najeriya. Zuwa wannan lokacin Dr. Rahinah ta kai matsayin consultant a fannin ta na Otorlaryngology a babban asibitin kasa (National Hospital) lokacin da ta ke da yara biyar; maza biyu; Abdallah da Mustapha, da mata uku Samha, Suhaima da kanwar ta Sumayyah." WABILLAHI TAUFEEQ NA HUCE IS NOT FOR FREE. IT'S 1000 VIA 3094856450 SUMAYYAH KABARA FIRST BANK Masha Allahu laquwwata illa billah. Nan muka kawo karshen labarin Habibu&Rahinah. Kuskuren dake ciki ku taya ni rokon Allah ya yafe mini. Abin Alkhairin da ke ciki Allah ya raba mana ladansa ni da ku bakudaya. Sai mun hadu a goron sabuwar shekara insha Allahu. *_Sumayyah Abdulkadir*