[29/03 09:54] MRS SADAUKI: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐 """"""""""""""""""""""" LoVe aNd HoRrOr StOry☠️ ```MRS SADAUKI```💫✍️ FCRW☀️ ____________________________________________ 01 Cikin duhun dusar ƙanƙara wata mata mai ƙusumbi ke ta ɗangala sanda cikin sauri har ta isa wani ƙaton kogo mai cike da hayaƙi kamar an yi gobara.Tana shiga kogon ya fara rawa yana fitar da wani sauti,baƙin bargon da ta luluɓe kanta da shi ta sauke kan kafaɗunta hakan ya bayyanar da shafafar fuskarta wacce babu ido,babu tsinin hanci sai iya baki kawai.Bakinta ta buɗe tana yin wani gurnani mai fitar da magana cikin wani yare na ƙarnin baya “ uleja naho kajulu ramhakaya fyayal!” cak kogon ya tsaya da rawar da yake tare da ɗaukar wani irin shiru kamar mutuwa ta ratsa,babu jimawa kuwa wasu fararen halittu suka fara shawagi ko ta ina. Da sauri ta zube kan gwiwanta tana mai buga gundulalun tafukan hannunta a ƙasa tana mai daɗa furzo wasu kalaman. “Za ki iya gabatar da abin da ke tafe da ke” wata murya ta ratso iska ta bata umarni. “Naomi!” ta furta cikin rawar murya. “Alƙaluman doka sun riga da sun ƙafe babu wani canji da za mu iya yi miki” aka bata amsa. “Ita ɗin yarinya ce ƙarama ƙwaƙwalwarta ba za ta iya ɗaukar wannan hatsabibin tashin hankali ba” tana gama rufe bakinta wata tukunyar ƙasa ta faɗo a gabanta ,“ki bata waɗannan ruwan ta sha daga nan komai zai tafi kan tsari” Tukunyar ta ɗauka kafin ta gyara luluɓinta sai kuma ta fito,bai wuce tako uku da ta yi ba sai ta furta wani furuci wanda ya haifar da wata hatsabibiyar guguwa tashi ta zo ta zagaye ta tana fitar da wani iska,sannu a hankali guguwar ke daɗa yin sama da ita a haka ta ɓace ɓat kamar walƙiya ba ta bayyana ko ina ba sai a ƙofar gidanta. Ina zaune ina ƙulla garin magunguna na ji motsi,da sauri na ɗago kai sai na hangi Maa na daidaita rufin ƙyauren gidanmu.Murmushi ne ya wanzu a fuskata ba tare da na ce mata komai ba na ci gaba da kallonta har ta ƙaraso ta zauna kusa da ni tana mai miƙo mini tukunyar hannunta.Na karɓa,sanyin haɗi da wani shock suka ratsa ni yayin da na ji kwaɗayin shan ruwan ciki.Baki na kafa na soma shan abin da ya kasance a ciki don sai bakina ne kawai ya iya tantance mini kallon kitse na yi wa rogo don kuwa ba zallar ruwa ne ba. Ina ajiye tukunyar sai na ji tamkar wacce aka yi wa wankin ƙwaƙwalwa,wasu abubuwa da suka keɓancin mahaifiyata nake son sani. “Maa me yasa ake kiranki da mayya?” “Saboda ababen bauta sun mallaka mini baiwar da ta keɓanta da ta sauran mutane” “Kina nufin makantar ido?” “Eh! ” “Amma ai kina gani duk da babu gurbin ido a fuskarki ” “Naomi??” muryar ƙawata ta katse zaren tambayoyin da nake yi wa mahaifiyata wacce ta kasance jigona,bango abin jiginata. Miƙewa na yi da sauri ina ƙara gyara zaman fatar dabba wacce ta suturta tsaraicina ina mai duben Debora wacce ke sanye da wani tsohon bargo duk ta yane jikinta da shi.Murmushi ta sakar mini kafin ta yi mini alama da hannu,Maa na duba ina mai cewa “zan yi wa Debora rakiya ne” “To kar ki jima saboda lokacin zuwa farauta ya kusa” Maa ta bani amsa,ba tare da na ce komai ba na kama hannun Debora muka fito ƙofar gidanmu wanda ya kasance na kara. “Ya meke labari?” na tambaye ta . Kamar munafuka ta yi ƙasa da murya ta ce “zo mu je na nuna miki wani abu” sai kuma ta fara ɗan gudu-gudu tana nufar bayan gari yayin da ni kuma nake take mata baya har muka isa bakin Teku .Da wani irin kallo na bi ta da shi ina mai cewa "me kuma za mu yi a nan?” Da hannu ta yi mini nuni da can tsakiyar ruwa,sai dai sam ban ga abin da take son nuna mini ɗin ba.Lura da hakan yasa ta ce “yi kamar za ki rufe idonki” hakan na yi na lumshe manyan idona kafin na ɗan buɗe su a hankali sai a lokacin na ga wani abin mamaki wanda tunani da hankali ba za su ɗauka ba.Dogon tsani ne a cikin ruwan tare da shata wata doguwar hanya da alamu za ta ɓulle a wani wurin.Umarnin zuciyata ƙafafuwana suka bi ba tare da na shirya hakan ba na ji sanyin ruwa ya ratsa ni.A hankali nake tafiya har na isa kan tsanin na fara taka matakalansa sai dai ban fi tako uku ba na ji kamar an tunkuɗo ni sai ganina na yi a wani wajen na daban ko kuma na ce wata duniyar wacce ta sha banban da wacce na taso na tsinci kaina a cikinta. Wasu halittu ne masu irin siffata sai dai yanayin launin fatarsu da kuma shigarsu ya sha banban da irin ta duniyarmu.A karon farko da na ji tsoro,don ban taɓa ganin irinsu ba .Ƙafata ta hagu na ɗan mayar a baya ina kallon yadda wani mutum ke musayar wuta shi da maƙarabansa,ina daf da na koma cikin ruwa muka yi ido huɗu da shi hakan ya haifar mini da matsanancin faɗuwar gaba tare kuma da rikicewar tunani.Mun shagala da kallon juna ,ƙarar wani abu da ban san me ake kiransa ba ya dawo da ni hayyacina.Sai da na yi dogon nazari sannan na fahimci cewa ta cikin ƙirjinsa ne aka halba masa abar kashe mutane.Faɗuwa yayi ƙasa,wanda hakan ya jawo hankalin tawagarsa kusan su duka na ji sun ce “yalaɓaiii?” kafin su yo kansa,ɗaya daga cikinsu ne ya zube ƙasa tare da ɗora kansa kan cinyarsa yana mai cewa “Naslam?” cikin tashin hankali yake kamar yadda fuskokin sauran suka bayyana. Abokan adawarsu ne suka fara yi musu sarƙa suna gargaɗarsu da su miƙa musu wannan mutumin kawai suke buƙata in kuma sun ƙi za su kashe su duka su tafi da shi. “Rayukanmu fansa ne akan shugabanmu babu gudu babu ja da baya don haka dakaru ku juya ku fuskance su” shi ne abin da ya faɗa yana mai shimfiɗe Naslam ɗin. A wannan gaɓar ce na ga wani al'amari mai shige da irin rayuwarmu ta can duniyar,yadda su mutanen da ke neman ran Naslam duk suka wani zazzalo harshe waje suna sarrafa shi,kafin ƙyaftawar ido sai gawarwaki nake gani suna faɗuwa. Idona na ji suna yi mini ƙaiƙayi ,babu jimawa suka furzo da wani hatsabibin haske wanda ya tarwatsa taron Mayun duk suka faɗi babu rai sai ɗaiɗaiku ne suka gudu. “Naomiiii?” na ji muryar Debora tana kirana daga ta can ɓangare,kamar kifi haka na faɗa ruwa na koma duniyarmu.Ko da na fito daga cikin ruwa jama'ar gari na tarar duk sun cika wurin suna jiran fitowata.Ko kaɗan babu wani damshi ruwa a jikina a bushe nake ƙamas,sai dai a akwai banbanci tsakanin lokacin da na shiga da kuma yanzu da na fito.Kaf illahirin jikina ya rine yayi baƙi yayin da kuma wani abu da nake tunanin ƙusumbi ne ya bayyana a bayana.Fuskokin wasu cike da mamaki yayin da wasu kuma na hango tsoro da hassada a tattare a ciki. “Naomi me kike yi ƙasan ruwa kusan kwana biyu ba ki fito ba?” ƙawata Debora ce ta zo gare ni tare da tambayata. “Kwana biyu ?” na maimaita yayin da kuma cike da mamaki,ɗaya daga cikin tsofin garin ta matso tana mai nuna ni da yatsa tana mai cewa “dama tun ranar da aka haife ki na hango ajalin mahaifiyarki a tattare da ke saboda kin tabbata butulu ki rasa wacce za ki kashe sai wacce ta kawo ki duniya” sai kuma ta juya ta fuskanci mutanen gari tana mai cewa “kuna ta tambayar wa ya kashe Maa to ƴarta ce” Normal mutane ne kawai suka tsorata da furucinta yayin da su kuma dangina masu ido uku suka rufo kaina suna mai cewa “ita ma a kashe ta” sai dai ko kusa da ni ban bari sun ƙaraso ba na yi wani furuci duk suka ƙame ƙyam a wuri guda kamar wasu bishiyoyi. Magana na soma yi sai dai abin mamaki ba muryata ba ce ke fita,ta mahaifiyata ce.Gargaɗi ne mai ban tsoro haɗi da bushara ga waɗanda suka yarda suka miƙa wuya a bisa sabuwar dokar da na shimfiɗa musu.Kamar yadda ake rusunawa sarki haka duk suka zube suna jinjina mini haɗi da gaishe ni,ƙawata Debora ce kawai a tsaye tana wani mayen murmushi mai fitar da tsantsar farin ciki. Hannunta na kama na ratsa ɗimbin jama'ar muka wuce,har muka isa gidanmu ni da ita babu wanda ya cewa wani kanzil.A ɗaki na tarar da gawar Maa a kwance tuni ta fara ruɓewa tsutsotsi na shige da fice ta bakinta.A lokacin ne na ji wata murya daga can cikin ruhina tana bani mafita da shawari,yayin da ni kuma na yi tako ɗaya na aiwatar da abin da na ji.Hannuna na ɗora a goshin Maa na soma yin wani furuci wanda ban koya ba,kawai zuwar mini yayi.Babu jimawa ta soma bajewa tana komawa hayaƙi a haka har ta baje gaba ɗaya sai sautin muryarta da ya soma yi mini bushara “ ina tare da ke a duk inda za ki kasance ƴata Naomi kar ki yi baƙin cikin rabuwarmu wannan shi ne matakin nasararki,hidimar da za ki yi kuma na san mahaifinki zai yi alfahari da ke.Zan tafi na koma asalina,a duk lokacin da kika yi kewata ki je magudanar ruwa ki cilla dutsen karlis zan jiyo sautin kiranki” tana gama faɗar haka aka kece da ruwa mai bala'in ƙarfi wanda rufin ɗakinmu bai iya tare shi ba.Na yi saurin lumshe idona ina jin sabuwar halittata na yi mini wani irin motsi haɗi da ƙara girma wanda silar haka na ji kafaɗata ta ƙara nauyi hakan ya haifar mini da ɗan rusunawa kamar dai yadda mai ƙusumbi ke yi. An ɗauki lokaci kafin ruwan ya tsaya cak ,sai a lokacin kuma na tsinci muryar Debora na cewa “haƙiƙa kin kasance mai babban rabo ƙawata,ina mai sanar da ke cewa nan ba da jimawa ba amon mulkinki zai ƙetare duniyarmu ta ruwa ya tsallaka duniyar turɓaya ” Sai da na haɗiye wasu yawu masu ɗaci kafin na ce “a yau na ga wata duniya ,wasu mutane na gani a siffar tawaga biyu,ɗayar tawagar ta kasance ta Mayu ce yayin da ɗayar kuma ban san ta mece ce ba abin da kawai na iya gani shi ne fuskokinsu na fitar da wani irin haske mai natsuwa haka ma hannuwansu.A goshin shugabansu na ga abin da ya kusan dakatar da numfashina,wani baƙin tabo ne wanda ya ƙawata goshin nasa ya kuma fitar da tsantsar hasken fuskar tasa” “A yadda kika siffanta su sak sun fito a al'ummar nan da ke bautar wani Ubangijin Ka'aba,sam ba su nuna tausayinsu ga matsafa da kuma waɗanda suka saɓa dokar Ubangijinsu” Zuciyata ce na ji tana wata irin tafasa hakan yasa na juyo a fusace ina kallon Debora wacce ita ɗin ta kasance ƴa ga babban malamin ilimin tarihin duniya.Tun da na ji ta ambaci haka tabbas kuma na san gaskiya ta faɗa ,“dama har akwai masu tsanar Magic a duniya? Shin ba su san tasirin tsafi ba ne ko kuwa sun jahilci lamarin ne?” “Ko ɗaya! Su ɗin sun yi imani a kaf duniya babu wanda ke tafarkin gaskiya sai wanda ya kasance ɗaya daga cikinsu.Wannan dalilin ne ma yasa suke shirya yaƙi duk shekara suna shiga ƙasashen matsafa.Kin ga mu bar maganar nan ma saboda ba ta shafe mu ba” “Ta ya za ki ce ba ta shafe mu ba alhalin kin san duniyarmu ba mu yarda da wani addini ba? In fa suka farmake mu?” ban san me yasa na ji tsoro da shakku dangane da mabiya addinin ba, musamman in na tuna fuskar mutumin nan Naslam. Debora ta riƙo hannuna tana mai cewa “masana tarihi sun tabbatar mana cewa yankinmu zagaye yake da ƙoramai ta yadda babu wata halitta da ta isa ta ƙetaro izuwa nan sai da izinin esprit ɗin ruwa,kina tunanin uwayen gijinmu za su lamunta a kawo mana hari ?” wani irin numfashi na sauke ko ba komai kalaman ƙawata sun ɗan rage mini fargaba amma duk da haka ban yi ƙasa da gwiwa ba na yi shela ina son ganin dukkanin matsafan garin domin zuwa kowacce kusurwar ruwa su kai saƙo zuwa ga aljanai da ruhikan ruwa....... [30/03 19:48] MRS SADAUKI: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐 """"""""""""""""""""""" LoVe aNd HoRrOr StOry☠️ ```MRS SADAUKI```💫✍️ FCWA☀️ ____________________________________________ 02 Ƙananun shekaruna ba su hana ni jagorantar tsoffi da kuma dattizai zuwa bakin kowacce kusurwar ruwa ba.A tsaye nake ƙiƙam ina kallon yadda ake masayar kalamai tsakanin aljanun ruwa da kuma matsafa,kamar yadda na faɗa musu tun farko ina son a bai wa garinmu kariya haka su ma suka faɗa sai dai aljanun sun ƙi lamincewa da ƙudirinmu kai tsaye sai da suka kawo nasu sharuɗan.Daga ciki akwai bayar da jinin baƙaƙen dabbobi duk ranar laraba, sannan a kowacce ƙarshen shekara ɗaya daga cikin mutanen yankin zai zama hadiya ta aljanai. Shiru wurin ya ɗauka suna kallona,suna jiran amsata a matsayina na shugaba.Ni ma shirun na yi ina nazari,wanda ban san ashe cewa tazarar lokacin da na ɗauka kafin na miƙa yardata ya fusata aljanun ruwan sun komawarsu. “Sun fusata ba za su sake yin magana ba sakamakon shirun da kika yi yayi yawa.A matsayinki na shugaba ya kamata a ce kina bada amsa ne a kai ba tare da nazari ba” ƙawata Debora ce ta yi wannan furucin idonta na kallon tsakiyar ruwa.Dukkan matsafan sun yi amanna da furucinta,ban ce komai ba sai taku da na fara yi ina ɗaga kafaɗata gefen da ke da ƙusumbi na shiga can tsakiyar ruwan.Tafin hannuna na hagu na kalla ina yin wani furuci nan take ya tsage jinina ya soma ɗiga a cikin ruwan.Duk ɗigo ɗaya ina iya jiyo wani nishi daga can ƙasan ruwa,na ɗauki kamar minti biyu a haka kafin na dakatar da zubar jinin sai kuma na soma yin magana cikin sauti ƙasa-ƙasa “joliho kuntahee namaruju kalmari hanaighar kashmuh balbilancaaaa!” babu shiri na lumshe ido jin yadda wata irin guguwar ruwa ta tashi tana tunkuɗo duk wani masarafin tsafi izuwa gare ni. “Ya ke ƴa ga Bazuka ki sani cewa kowanne tasiri da farashinsa,sannan mu halittun ruwa ba mu taɓa mance duk wata alaƙa da aka ƙulla da mu .Za mu bai wa garinki kariya kamar yadda kika buƙata sai dai ki sani a duk lokacin da kika take dokarmu za mu bayyana miki asalin me ake kira da masifa da annoba ” wata murya da ke kama da ta macijin ruwan ta yi mini jawabi. “Hakan ba zai taɓa faruwa ba,zan kiyaye dukkan sharuɗanku” wannan karon na bada amsa kai tsaye. “Mu ne za mu zaɓar hadiya da kanmu,a duk sa'ilin da lokaci ya yi za mu nuna miki mutumin da muke buƙatar jininsa ta mafarkinki ” “Na amince!” “Sannan kuma haramun ne shiga ruwa ranar Laraba ” “Na amince!” ina furta haka kawai sai yanayin garin ya canza ya ɗauki wani irin launin duhu amma ba sosai ba,sararin samaniya ya cika da baƙaƙen giza-gizai yayin da kuma kukan tsuntsaye da kaɗawar bishiyoyi ya tsaya cak. “Aroroke! Aroroke! Aroroke!” shi ne abin da sauran mutanen da muka zo suka fara faɗa cikin murna saboda dukkan alamomin nan da suka bayyana na nasara ne. A hankali na fito daga cikin ruwan ina mai fuskantar su sai duk suka yi shiru tare da sauke idonsu ƙasa don nuna girma a gare ni. “Daga yau na sama wa garinmu suna za a dinga kiransa YANKIN MUTUWA,duk wanda ya shigo sunansa gawa ba wai mutum ba ko dabbar da ba ta wannan garin ba ta shigo na bada izini kafin a zo a faɗa mini a kashe ta” nan ɗin ma jin daɗinsu suka bayyana a fili kafin na wuce gaba su mara mini baya muka koma can tsakiyar gari inda na sa aka ƙara ƙawata gidanmu. Kan shimfiɗar da gawar Maa ta rushe na hau tare da yin kwanciya.Ina lumshe idona fuskar Naslam ta dawo mini da wani mugun sauri na buɗe su tare da tashi zaune ina jin zuciyata na harbawa da sauri.A fili na ja wani tsuki ina jin tsanarsa da su kansu mabiya addininsa.Yatsun hannuna na murza tare da furta kalmar tsafi nan take ragayar da ke maƙale a tsakiyar iccen rufin ɗakinmu ta yo ƙasa ta zo daidai inda nake wata ƴar ƙaramar takarda na gani mai ɗauke da haruffan tsohon asiri.Ban yi wani dogon bincike ba na fahimci cewa wannan takarda daga mahaifina take,mutumin da daidai da sakan ɗaya ban yi rayuwa da shi ba.Rubutun bai da yawa a ido,amma ma'anoninsa sun isa a rubuta dogon labari.Tsam na miƙe bayan na maƙale takardar a ƙuguna,daidai ƙofar da za ta ba mutum damar shiga uwar ɗaga na zube tare da shafar wurin nan take ya ɗau wani haske yana mai bayyanar mini da jan rubutu wanda aka rubuta da jinin mahaifina. “Finstako Bazaku enfinstako naheee” ina furta haka ƙasar wurin ta tsaye sai ga wata ƴar madaidaiciya wuƙa ta bayyana mai ɗauke da sunan mahaifina,nawa da kuma na Maa.Sai da na tsaga jinina ya ɗiga a kai sannan na samu damar ciro ta.Wani mummunan iska ne ya taso daga sama ya cilla ni gefe kafin guguwa ta fara haɗuwa daidai wurin da na ciro wuƙar.Wata siffa ce ta bayyana a gare ni,tun a kallon farko na ga ne shi ɗin mahaifina ne duba da fuskarsa sak irin tawa ce.Hannu ya miƙa mini,daga wurin da nake zuwa inda yake da ƴar tazara amma hakan bai hana ni ɗora hannuna kan tafinsa ba sai ya janye ni muka ɓata cikin iskan guguwa.Wata tsohuwar maƙabarta ce mai zubin ta kiristoci,kowanne kabari da nasa sunan. “Wannan ce hanyar da matsafa ke bi don kawar da maƙiyinsu ba tare da sun sha wahala ba.Da zarar kin ginawa mutum kabari to lissafin mutuwarsa zai dawo hannunki ,ke ce za ki zaɓar lokaci da kuma yanayin da zai bar duniyar bil'adama zuwa ta matattu” shi ne bayanin da Abbana ya yi mini ba tare da na tambaye shi ba. Kallonsa na yi ina mai cewa “ni banda maƙiyi ko ɗaya” “Shi kuma Prince ɗin da kuka haɗu fa? Kin yi tunanin cewa haka kawai ne kika fita daga duniyarmu ta tsakiyar ruwa zuwa duniyar turɓaya? Ya ke ƴata ki sani daga ranar da muƙamin iko na prophecy ya fara aiki a kanki to abu na farko da uwayen gijinmu suke nuna maka shi ne babban maƙiyinka” Shiru na yi ina nazarin furicinsa ,so nake na san ta ya aka yi Naslam ya zama maƙiyina,don na fahimci sarai a kansa ne yake magana. “Dalilin da yasa kika zama maƙiyiyarsa saboda ta silarki ce aka yi galaba a kansa,ba don a ce ya shagala da kallonki ba to da tabbas magauta ba za su harbe shi ba” ya ƙara faɗa kai ka ce shi ke sarrafa tunanina da har yake sanin abin da ban furta ba. “In dai duk abin da ka furta gaskiya ne,to zan so a ce a duk lokacin da yake tsakiyar fafatawa da maƙiya ya zamana ni kuma na bayyana a wurin ta yadda zan zamo rauninsa,ya gane ya kuma fahimci cewa wutsiyar raƙumi ta yi nisa da ƙasa.Ta hakan ne kawai ba zai taɓa sha'awar farmakar yankina ba” Bai ce mini komai ba sai wuƙar nan da ya cire daga gidanta ya miƙo mini tare da nuna mini wani buɗaɗen kabari wanda a jikinsa aka rubuta sunan Prince Naslam. Hannuna na tsaga jini ya zuba a cikin ramen kabarin,babu jimawa wuta ta soma ci balbal.Daga nan kuma kawai sai tsintar kaina na yi a ɗaki,ba tare da na san alƙawarin jini ne na ƙulla Ni da aljanai ba. ★DAULAR ABU NASLAM Tutar daular ce aka juye alamun babu lafiya a yankin.Dakaru haɗi da hadimai sai faman kai komo suke yi suna jiran tsammani na farfaɗowar jagoransu,madubi kuma gun babbar masarautar musulinci. Sarki Haroon mahaifi gun Prince Naslam a tsaye yake a wata kusurwa wacce ta yi daidai da alƙibla.Idonsa a rufe suke,yayin da kuma ya haɗe hannuwansa wuri guda domin nuna ladabi ga Ubangijinsa.A hankali yake motsa bakinsa,duk da ba a jin furucin amma za a iya fahimtar abin da yake cewa shi ne “Ya Hayyu! Ya Ƙayyum! Wato ma'ana Ya Rayayye! Ya dawamamme!” iya shi kaɗai yake furtawa bai dakata ba kuma sai da ya ji murya jakariya Ali yana cewa “shugaba cikin amincin Ubangiji ka'aba Prince Naslam ya dawo hayyacinsa ” “Shukuran Ya Rabb!” shi ne kawai abin da ya furta kafin yake juyowa yana kallon Ali wanda duk ya fita hayyacinsa tun ranar da suka dawo daga yaƙin tsibirin Mayu. Murmushi sarki ya sakar masa wanda ya haifar masa da samun wata ajiyar zuciya nan take kafin cike da girmamawa ya ce “yarima na buƙatar ganinka” “Mu je!” ya furta kafin sarki ya shiga gaba shi kuma Ali na take masa baya har suka shiga ɗakin yarima Naslam inda yake kwance yayin da kuma tsoho Barham ke kula da lafiyarsa. Suna haɗa ido da mahaifinsa ya yi saurin yunƙurowa da niyyar tashi,sai dai raunin ƙirjinsa ya dakatar da shi da wani mugun sauri ya koma ya kwanta yana mai yin wani irin nishi. Barham ya ce “na yi nasarar cire dattin garin mahalbiya,nan da kwana uku in sha Allah zai iya tsayuwa kan ƙafafunsa” Sarki ya ce “Ubangin ka'aba ya albarka ce ka ya ƙara maka ɗimbin ilimin sanin magani” Barham ya amsa da “ Amin ” kafin kuma ya yi wa Ali alama suka fice suka bar sarki shi da yarima. “Ya jikin naka?” sarki ya tambaye shi yana mai dafa goshin Naslam ɗin.Maimakon ya basa amsar tambayarsa sai cewa ya yi “Abih aljanar da nake baka labari ita ce silar raunin da aka ji mini,na gan ta a zahiri tana tsaye gaɓar teku sanyen da kayan arna,ƙusumbin tsutsotsi maƙale a bayanta,idon sharrinta na fitar da gubar tsafi ” “Naslam na sha faɗa maka ita ɗin ba aljana ba ce,wakiliyar duk wasu sheɗanun Mayu da matsafa ce.Ita ce aka damƙawa kundin prophecy domin cika wani baƙin ƙuduri nasu.Amma da ka gan ta wane yunƙuri ka yi?” “Abih ta ya zan iya yin wani abu? Yanzu dai ina so a shirya dawakan yaƙi su ƙara komawa can domin binciko mini ita” Shiru sarki yayi kafin kuma ya fita,cike da bayar da umarni ya sa aka shirya dawakai majiya ƙarfi da kuma dakarun yaƙi . Jakariya Ali shi ne ya shugabanci tawagar,sai dai sama da awa biyar suka kwashe ko kusa da ruwan sun kasa zuwa saboda tsantsan tsaron da aka shimfiɗa musu a dole ya jawo su suka dawo gida a lokacin tuni yarima Naslam ya kasa sukuni ya sa an kawo masa farin ƙyalle haɗi da abin zane haka ya zauna ya zana Naomi kai ka ce ta gasken ce . Ido ya tsura mata cike da tsana yana tambayar kansa a zuci ‘ wace ce ke? Me yasa tun da na shiga zangon balaga kika addabi rayuwata?’ Jin an banko ƙofa yasa shi barin zancen zucin tare da maida idonsa kan ƙofar shigowa.Jakariya Ali ne sanye da kayan yaƙi,zanen ya fara kallo kafin ya cewa yarima “babu wata nasara dangane da tekun can,amma wai don Allah me yasa ka damu? ” Cikin zafin rai ya ce “aljanar mafarkina ce” “Amma fa ita ce ta cece mu lokacin da Mayu suka fara sarrafa tsafi ” jakariya Ali ya faɗa . “Bayan ta yi silar cutar da ni,Ali na tsani aljanar nan tun ba yau ba na fahimci cewa ita ɗin rauni ce a rayuwata” “Yarima a duk lokacin da na ji kana irin wannan zantukan sai na dinga jin cewa kai ma fa tamkar kana ɗauke da ikon prophecy ” Kafin yarima Naslam ya kai ga yin magana wani irin iska mai sanyi ya fara ratso ɗakin yana shigowa,babu abin da ya motsa sai zanen hoton Naomi shi ma ɗin cike da abin al'ajabi yadda bakinta ke ɗan buɗewa tana murmushi..... [05/04 11:18] MRS SADAUKI: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐 """"""""""""""""""""""" LoVe aNd HoRrOr StOry☠️ ```MRS SADAUKI```💫✍️ FCWA☀️ ____________________________________________ 03 Zanen fuskar Naomi bai gushe yana murmushi ba suka jiyo sautin wata waƙa wacce yarima Naslam ne da kansa ya haramta ta saboda kalaman da ta ƙunsa na tsafi da kuma kirari zuwa ga tawagar dabar Mayu da matsafa. Jakariya Ali ne yayi saurin tsayuwa kusa da window ta inda ya fi jin sautin na fitowa.Wata makauniyar tsohuwa ya gani a durƙushe riƙe da sanda tana rera waƙar tana wani jinjina kai haɗi da murmushi. “Ina ga mun yi baƙuwa ne ,ba don haka ba ai ka haramta raira waƙar nan” jakariya Ali ya faɗa . Yarima da ya cika yayi fam kamar zai fashe ya ce “a kama ta” Da wani irin gudu kuwa jakariya Ali ya fita ,babu jimawa yasa wasu dakaru biyu suka damƙe matar tare da kai ta can ɗakin ajiyar masu laifi ya kuma bada umarnin a ƙara tsaro sosai. Shi kuwa yarima Naslam zanen ya naɗe tare da adana shi ƙarƙashin pilow .Sai a lokacin kawai ya tuna akwai sallolin da suka hau kansa waɗanda bai yi ba,tsuki ya ja a fili yana cewa “duk sharrin aljanar nan ne” Cikin ikon Allah sai ga jakariya Ali ya dawo ,shi ne ya taimaka masa zuwa banɗaki ya yi ɗahara haɗi da alwala sannan ya fito ya soma gabatar da sallolinsa. Bayan ya gama ne,mai magani Barham ya ƙara shigowa ya duba shi tare da basa maganin sha da kuma na shafawa wanda cikin hukuncin Ubangiji sai ya ƙara jin ƙarfin jikinsa. “Zuwa bayan sallar asar zan haɗa maka ruwan magani a bahon wanka sai ka shiga ka yi,amma ina so don Allah ka cire duk wani tunani akan yarinyar da ka zana ” Barham ya faɗa . Yarima Naslam ya ɗago manyan idonsa masu firgita maza ya ɗora kan Barham kafin ya ce “me ka sani game da ita?” Barham ya gyara tsayuwarsa kafin ya ce “ita ɗin ba kamar sauran mutane take ba,an haife ta bayan ɗaukar ran mahaifinta,an raine ta cikin gata da soyayya sannan kuma an damƙa mata muƙamin prophecy a ranar da mahaifiyarta ta yi gushewa wannan dalilin kaɗai ya isa ya tabbatar maka iya tunaninta ma kaɗai ba alkhairi ne ba ga Sarkin goben masarautar nan” “ Ban fahimce ka ba,kana nufin ita ɗin annoba ce ga duniya baki ɗaya?” “A'a! Ita ɗin fa shugaba ce,kamar yadda kake kare Yankinka to ita ma haka jininta ke tafarfasa in aka ce an taɓa ahalin mugaye.Tana da ƙarfin ikon maitar ido,ga kuma baƙar maita ta baki wadda da za a ce ta tofa yawunta a tekun wani yanki da ba nata ba to tabbas da ruwan sun haramta saboda tasirin ƙwayoyin cutar da ke ciki.Na yi magana da jakariya Ali ya shaida mini duk yadda komai ya faru,kuma na gaskata sarauniya Naomi ce saboda abin da na tsinta a yayin yi maka magani” “Me fa?” yarima Naslam ya tambaya. Shiru Barham ya yi kafin ya tako ya iso gun yarima,cikin muryar raɗa kamar mai jin tsoro ya ce “ta jefa maka cutar ayni wato maitar ido, wannan ne ya hana ka motsi ya juye maka tunani ka manta cewa filin daga kake har sai da magauta suka yi nasarar harbin ka” Zuciyar Naslam ce ta fara tafasa kamar za ta faɗo,yana jin ina ma zai ga Naomi a yanzu da babu shakka tabbas da hannunsa zai kashe ta.Haka ya danni zuciyarsa,ya yi ƙoƙari sosai wurin manta wa da ita sai dai kamar abin isimi lokacin yin wankansa na yi na magani idanunsa suka fara yi masa gizon yadda ta kafe shi da idonta masu matuƙar girma da kyawu don tamkar gwal haka suke sheƙi. Jakariya Ali ne ke taimaka masa har ya samu ya shiga ya kwanta cikin bahon wankan,kamar jira ake yi kuwa wani al'amari ya riske shi.Ji yayi kamar an rufe shi bai numfashi kafin ya soma jin wani yanayi wanda sam ba zai iya misalta irin abin da yake ji ba.Jikinsa ne ya ɗauki wata irin kyarma sakamakon wasu halittu da yake gani dishi-dishi waɗanda ya yi imani cewa ba Mala'iku ba ne.Can kuma ya soma wani abu kamar mafarki yana tare da Naomi yana tarayya da ita kamar sauran mafarkansa na baya. Jakariya Ali da ke gefensa tuni ya fahimci abin da ke faruwa,muryarsa na ɗan rawa ya kira sunan yarima Naslam kafin ya ce “innalillahi wa'inna ileyhi raji'un!” nan take komai ya tsaya cak.Yarima Naslam yayi wata irin zabura haɗi da nishi bakinsa na fitar da baƙin jini.Jakariya Ali ne ya yi hanzarin goge masa jinin kafin ya taimaka masa ya yi wankan,da ya fito ma shi ne ya taimaka masa wurin saka kaya marar nauyi kafin kuma a gabatar masa da tafasasshen shayi wanda suke yi ko wane dare.Har ya yi sallolinsa bai dubi kofin shayin ba saboda abin da ke damun ransa,bayan sallar isha'i ne sarki ya shigo da kansa ya duba shi. “Gobe ka tura dakaru zuwa bakin Teku su ƙara binciko mini aljanar nan” yarima ya faɗa yana wani kawar da kai gefe. Sarki ya ce “zan so ka manta da batun yarinyar nan ka fuskanci sabon al'amarin da ke shirin tunkaro masarautarmu Naslam.Sanin kanka ne duk abin da ya cika naci to babu alkhairi a tattare da shi,ba tun yau ba kake faɗa mini kana yin mafarki da aljana to ka sani shigowa da ita masarautar nan daidai yake da ruguza duk wani ginshiƙi da ka gina tsawon shekaru” sai kuma ya yi shiru tare da zuwa ya ƙara ɗaukar wani kofi ya zuba masa shayi sannan ya saka cokali yana juya shi tare da miƙa masa ,ba don ya so ba ya karɓa ya soma sha.Sai kuma a wannan lokacin ne sarki ya ci gaba da cewa “gimbiya A'ishah na waje tana jiran fitowar ka ,zan so a ce ku daidaita kanku tun a yau don a samu a wuce wurin,na san daga lokacin da aka ɗaura maka aure shi kenan matsalarka za ta kau”. Ambaton sunan gimbiya A'ishah shi ya wanzar masa da nutsuwar zuciya,don yana mugun ƙaunarta har cikin ransa saboda ba ƙaramar gudunmawa ta bayar ba wurin haɓaka musulunci a masarautar nan ba. A hankali ya sauko daga gadon da yake,sai dai sam ya kasa jurar tsayuwar a dole ya koma ya zauna.Cikin ɗan ɗaga murya sarki ya ce “Ali?” shi kuwa kamar mai jira haka ya buɗe ƙofar ya shigo tare da ƙamewa. “Ka fito da yarima zuwa waje” ya faɗa tare da ficewa.Jakariya Ali ya ɗauko kujera ya taimaka wa yarima ya hau ya zauna sannan ya soma tura shi zuwa can falo wanda ya cika da ahali da kuma aminnan arziki.Tun daga nesa suka haɗa ido da ita,da wani mugun sauri ta yi ƙasa da kanta cikin kunya tana yin wani sihirtacen murmushi.Har aka ƙaraso da yarima ba ta ɗago kanta ba,haka aka shiga jera masa sannu yana amsa wa amma idonsa na kanta. “A'ishah zo ki gaishe da yarima mana kin wani tsaya wuri guda kina sunne kai kamar ba ke ce a yanzu ki ƙi cin abinci ba saboda shi” mahaifinta ya faɗa yana wani murmushi haka ma duk sauran mutanen wurin fuskarsu cike take annuri in aka cire mahaifiyar A'ishah ɗin da take jin kamar ta je ta kama wuyar yarima ta shaƙe shi har sai ya mutu. Gimbiya A'ishah ba ta ko motsa daga inda take ba,sai da mutanen suka dinga fita zuwa babban falo suka bar su iya su uku don duk inda yarima yake jakariyarsa Ali na tare da shi.Ɗan gefe kawai ya koma yana kallonsu,shi dai ko kaɗan bai ga dacewar yarima da ita gimbiyar ba duk da kuwa cewa ita ɗin kyakkyawa ce ta ajin ƙarshe. “Amincin Allah ya tabbata ga shugaban gobe” ta furta tana mai takowa inda yake tana ɗagowa haɗi da yi masa wani kallo mai tsayawa a rai wanda a can da babu abin da ke matuƙar girgiza yarima irin kallon nan amma yanzu sai ya ji sam bai burge shi ba,hasali ma na Naomi ya tsinta a fuskarta. Da sauri ya lumshe ido yana mai amsawa tare da cewa “shi ne ba ki zo kika duba ni ba tsawon kwana biyu ina a kwance” Murya na ɗan rawa ta ce “subahanallahi! Meke damunka yarima? Ai ban san ba ka jin daɗin jikinka ba,saboda tun ranar da ka haɗa ni da matan nan nake koya musu karatu daidai da ɗaya rana ban taɓa leƙowa waje ba” Wani numfashi ya furzar yana mai buɗe idonsa ya dube ta,iliminta yana ɗaya daga cikin abin da yake so a tattare da ita,“kar ki damu ai na samu lafiya” Shiru ta yi tana mai ɗagowa ta dube shi,ita sai yanzu ne ma ta lura cewa kan kujera ne yake.Sai kuma ƙwaƙwalwarta ta tariyo mata lokacin shigowar su shi da jakariya Ali, kasancewar kwanyarta dama can ba kullum take tafiya daidai ba shi yasa ne ba ta fahimci hakan ba. Rikicewa ta yi ta zube a gabansa tare da soma jero masa tambayoyi,wanda kuma in akwai abin da yarima ya tsana a tare da ita shi ne yawan tambayoyi da kuma wannan haukan da take yi a duk lokacin da wani abu na ƙi ya same shi. Da wani irin sauri jakariya Ali ya matso yana mai dakatar da ita,yana cewa “don Allah ki yi shiru mana” sai ta ɗago kai tana yi masa kallon tsana saboda tun tuni ta san cewa Ali bai ƙaunarta. Yana yi mata wani mugun kallo ya je ya kama kujerar da yarima ke zaune ya soma tura shi tare da mayar da shi ɗakinsa.Har Ali zai tafi sai kuma ya dakatar da shi yana mai cewa “kai ni wurin matar da aka kama ɗazu” Jakariya Ali ya ce “tana da matuƙar hatsari yarima ,da bari ka yi zuwa gobe in sha Allah ka ga lokacin ka ƙara samun ƙarfin jikinka” “Mu je dai ka kai ni ” ya sake faɗa ,ba don ya so ba ya tura shi zuwa kurkukun har suka isa ragar da aka killace ta. Tana kwance a duƙunƙune cikin wani tsohon bargo,hatta kanta a rufe yake amma hakan bai hana ta ganin yariman ba.Cikin wata irin murya ta ce “barka da zuwa yariman musulmai,ka sani killace ni a nan ba shi ne maganin matsalarka ba.Hakan ma babban kuskure ne ka tabka,ko da yake ba ka san ko ni wace ce ba” ta ƙarashe faɗa tana yin wani nishi sai ga bargon da ta rufa a shi ya yi wani irin sama tare da buɗe ta. Yarima da jakariya Ali suka kalli yadda bargon ya maƙale can sama cikin iska.Su duka biyun sun yi imani cewa tsafi ne ta yi,sai dai a yanayin da yarima yake a yanzu ba zai iya ɗaukar wani mataki ba a hannunsa sai kawai yasa jakariya Ali ya juya da shi. ★ A cikin abin da bai wuce kwana uku ba mulkina ya tsaga kowacce kusurwar yankinmu.Tuni na yi ƙaurin suna yayin da kuma gogaggin matsafa daga garuruwan ƙetare ke kawo mini tayin aure duba da yanayin shekaruna ina buƙatar abokin rayuwa musamman don gudanar da mulki yadda ya kamata sai dai ko kaɗan babu wanda ya kwanta mini a rai. Muna zaune kan kututuren icce ni da Debora ,sai kuwa ga wata baƙar mujiya ta soma shawagi haɗi da yin wani kuka. Debora ta furta kalaman tsafi tana mai buɗe tafin hannunta,sai mujiyar ta sauko tana mai sakar mata wata takarda ita kuwa jikinta har rawa yake yi wurin buɗewa.Rubutu ne reras da manyan baƙi,sai dai harufan na tsafi ne kuma ba su yi mini wuyar karantawa ba.A tare muka kalli juna,kafin na miƙe tsaye ina cewa “to a wane yanki ne aka kama ta?” “Ba ta faɗa ba a cikin wasiƙar,amma ina zaton ɗaya daga cikin garuruwan da suka kawo miki tayin aure ne ba ki amince ba” Shiru na yi ina tunani kafin kuma na karɓi takardar,ina furta tsafi rubutun ya goge sai na soma juya ido ina yin magana cikin raɗa rubutun ya soma rubuta kansa ina gamawa sai na umarci tsuntsuwar ta kai wa mahaifiyar Deborah .Ido na birkice suka koma farare tas ta haka ne nake iya hango gudun tsuntsuwar tana keta sararin samaniya tana wuce ƙauyuka tana shiga wasu garuruwa sai dai tana daf da ƙetara wata tutar wani yanki na ga wata kibiyar haske ta jefe ta ita kuma ta faɗi ƙasa ,duk kuma yadda na ƙware a tsafi ban ƙarashe ganin sauran abin da ke faruwa ba...... [06/04 08:01] MRS SADAUKI: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐 """"""""""""""""""""""" LoVe aNd HoRrOr StOry☠️ ```MRS SADAUKI```💫✍️ FCWA☀️ ____________________________________________ 04 Hankalin Debora sosai ya tashi saboda ta lura da abin da ya faru.Ko kaɗan ban ga laifinta ba saboda na san yadda mutum ke ji in mahaifiyarsa ba ta tare da shi, wannan yasa na damƙo hannunta tare da yin wani irin kalar tsafi na gushe mata da damuwar tare da saka mata nutsuwa na danne ƙuncin zuciyarta. Idonta da suka kaɗa suka yi ja na duba karin na ce “ki sani cewa babu wani sarki da zai gagare ni,ki sa a ranki ummarka tuni ta kuɓuta” Muryarta na fitar da wani irin amo take cewa “ya ke shugabata in ba ki manta ba irin haka ne mahaifina ya tarar da wa'adinsa,silar zaƙulo bincike domin rubuta tarihi ya haɗu da wasu mabiya addini mabanbanta suka kashe shi a ƙarshe sai mahaifiyata ce ta maye gurbinsa domin ci gaba da rubuta littafin kudin binciken duniyar ruhaniya” tana kawowa nan da zancenta sai ta ɗan yi shiru kafin ta ci gaba da cewa “ina jin tsoron kar a ce ita ma Umma nata ajalin ne ya zo” Kai na girgiza mata ina mai cewa “muddin ina raye hakan ba zai faru ba” Rungume ni ta yi tana sauke wata irin ajiyar zuciya,yayin da ni kuma na shiga tunanin hanyar da zan bi na ƙwato Umma ɗin saboda a duniyar nan a halin yanzu banda wani masoyi da na fi so da ƙauna sama da Debora.Cikin hikima na mayar da ita cikin gida gabanin ni kuma na fita zuwa can cikin baƙin jejin garinmu mai cike da aljanai da fatalwa. Cikin tafiyar rauni ta masu larurar ƙusumbi nake tafiya ana take mini baya,ko kaɗan ban san su wane ne ke take sawuna ba kuma ban jin tsoro ko fargaba wani abu.A haka na isa bakin wata iraciyar kuka mai zubin halittar mutum don da baki da hanci gare ta.Ina gama daidaita tsayuwata sai kuwa bisashin ganye suka fara zubowa a kaina kamar ana ruwa kafin ɗanye ƙwaya ɗaya ya faɗo a gabana.Ɗaukarsa na yi tare da tofa yawuna a kai,sai na soma juya ido babu jimawa yawun suka rikiɗa zuwa rubutu.Sai a lokacin na miƙawa itaciyar ganyen mai ɗauke da bayanin abin da ya kawo ni nan ɗin.Tafin hannuna na ji ya cika da wasu duwatsu,ina dubawa sai na ga suna sheƙi akan kowanne dutse an rubuta karlis .Ban yi jinkiri ba na nufi ɗaya daga cikin magudanar ruwa na je na yi tsaye ina kallon yadda ruwan ke a kwance sun nutsu ko motsi ba su yi.Dutse ɗaya na cilla ina sauraren yadda ƙararsa ya ratsa ruwan tare da soma yin gudu har zuwa inda nake son ya isa. Ba a ɗauki wani lokaci ba wata iska mai sanyi ta soma kaɗawa tana fitar da wani ƙanshi irin na gawa.Can sai ga Maa ta ratso ruwa ta fito,fuskarta ta yi wani fari fat kana ganinta ka ga matatta ga kuma fararen kaya a jikinta. Cike da soyayya na je da gudu na rungume ta,sai dai kamar na jimƙi iskan gas haka na ji babu wata alamar gangar jiki.Da sauri na ja da baya ina kallonta tana wani fitar da murmushi,wani irin tausayin kaina na ji wanda ko ranar mutuwarta ban ji shi ba. “Me kike buƙata Nao?” don haka take kirana a duk lokacin da take shauƙi ko kuma take son isar mini ƙaunar da zuciyarta ke ƙumshe da ita. “Maa shi kenan ba zan ƙara jin taushin gangar jikinki ba?” ita ce tambayar da na yi mata madadin na sanar da ita matsalar da ta kawo ni. Ta ce “Naomi a zangon da nake na fita daga sawun duniyar bil'adama na koma cikin duniyar matattu,ki kira ni da ruhi kai tsaye” Kallonta na yi,tabbas ita ɗin ruhi ce kamar yadda ta faɗa ɗin.Na kai hannu na shafi kumatuna da nake jin wani damshi,wanda na yi imanin cewa ruwan hawaye ne .Murya na ɗan rawa na ce “mahaifiyar Deborah ta faɗa hannun mugaye shi ne nake son sanin ta ya zan ceto ta?” “Babu buƙatar yin haka,saboda ita ɗin ba kanwar lasa ba ce.Za ta iya fitar da kanta kar ki wani damu kanki” Maa ta faɗa . Na ce “amma kuma ita ce da kanta ta aiko da takarda domin sanar da mu” “Ta yi haka ne domin ku ci gaba da rubuta littafin bayanai ba wai don kawo mata agaji ba.Ki sanar da Deborah cewa lokaci ya yi da ita ma za ta ɗauki muƙaminta na rubuta tarihi kamar yadda mahaifinta ya karɓa gun mahaifinsa,ita kuma mahaifiyarta ta karɓa daga mahaifinta,yanzu kuma ƙaddarar littafin tarihi ta dawo hannunta” Maa na gama furta haka sai ta soma nitsewa cikin ruwa haskenta na tarwatse wa haɗi da disashewa.A gaban idona ta ɓata,na lumshe idona ina mai furta kalaman tsafi tare da buɗe su kuma a nan na tsinci kaina a ɗakina. Deborah na kwance amma ba bacci take yi na.Kallonta na yi kafin a takaice na sanar da ita abin da Maa ta shaida mini,da wani irin sauri ta miƙe ta zauna tana kallona can kuma ta soma furzo da wani irin furuci sai na ji tsafin da take yi ba irin nawa ba ne yana da banbanci kamar yadda Hausar wani gari ba ɗaya take da ta wani garin ba. Babu jimawa sai muka soma jiyo kukan jemage yana wani tsala shi kamar zai fasa gidan,a tare muka fita nan muka yi gamdakatar da wani baƙin jemage baƙi ƙirin da shi ga kuma wani irin girma na ban mamaki. Kan ƙafafunsa ya sauka bayan ya cillo wani tsohon littafi ya dira a tafukan hannun Deborah. Kallo ɗaya na yi masa na fahimci cewa shi ne wanda aka wakilta domin tsare littafin ya basa kariya.A hankali ya soma yin tsalle har ya isa gun Deborah,babban farcenta na ƙafar hagu ya kama ya fasa shi tare da soma shan jininta irin sosai ɗin nan don har sai da ta soma yin wani irin haske irin na rashin jini amma ko kaɗan ban yi yunƙurin tsayar da shi ba har sai da ya gama sha sannan ya tashi sama,sai dai bai yi wani nisa ba ya ɓace ɓat. Sai a lokacin na je na kama ta na ja ta zuwa ciki na zaunar da ita,magani na ɗauko na soma rufe mata yatsan da shi wanda har yanzu yake ɗigar da jini. “Ki kwanta ki huta na san kin gaji” na furta. “Ki soma karanta littafin kafin ni na karanta miki ” ta furta tare da miƙo mini,kamar ba zan karɓa ba sai kuma na kai hannu na karɓi littafin na ajiye a gefe.Ido ta lumshe ta soma yin bacci mai kama da mutuwa,wanda na yi imani cewa a cikinsa ne za a miƙa mata wasu asirai da kuma power kariyar kai da kuma ta abin da aka damƙa mata amanarsa. A cikin wannan daren ne na soma karanta littafin tarihi wanda ya ƙunshi rayuwar jarumai da kuma irin gwagwarmayar da suka yi fama a kai.Na samu sirrika dayawa,na yaƙi da kuma yadda ake sarrafa maita ta sigogi daban-daban. Wannan littafin ya ƙara saka mawa zuciyata cewa duk inda babu magic to lalle babu rayuwa mai inganci, Magic shi ne komai na duniya a cikinsa ne za ka samu ƴanci da kuma gata.Rufe shi na yi tare da raɓawa gefen Debora na kwanta,ina lumshe idona na soma jin wani irin motsi a cikin kunnena tamkar ƙwaro na tafiya.Ƙara nutsuwa na yi sai na soma jin tamkar ana yi mini magana ne,amma ta ina? Ban sani ba.Ji na yi ana danne ni ana saukar mini nauyi,na furzar da huci mai zafi jin wasu kalmomi daga wata murya da ban san mamallakinta ba. “ A duk inda kike a faɗin duniyar nan sai na nemo ki,ni ne nan zan kashe ki da hannuna ƙaramar matsafiya muguwa mai idanun maciji” muryar namiji ce amma ban san wane ne ba, sannan ban fahimci abin da yake nufi ba har ya ƙara yin wani furucin “ina ma ace annabi sulaiman bai yi wafati ba,da na roƙi alfarmarsa ya tura rundunar aljanu su gana miki azabar da ta fi ƙarfin tsafinki ” Saurin buɗe idona na yi,ina mai tambayar kaina “wane ne kuma Annabi Sulaiman?” sai dai banda amsar wannan tambayar,in akwai wanda zai faɗa mini ita to bai wuce Deborah ba wannan yasa na kasa haƙuri na kai hannu na shafi fuskarta.Ta buɗe idonta tarau a kaina,sai dai babu ɗigon baƙi a cikinsu da alamu har yanzu ba ta dawo daga balaguron ruhi ba. “Wane ne Annabi Sulaiman?” na tambaye ta,idanunta ne suka dawo normal nan take ta tashi zaune sannan ta bani amsa da cewa “ ya kasance ɗa ga Annabi Dawuda shi ma kuma annabin Ubangijin Ka'aba ne.Yana da matuƙar power don a tarihin annabawa shi ne kaɗai ya mulki mutane da kuma aljanai,sannan kuma yana iya yin magana da dabbobi da kuma jarirai waɗanda bakinsu bai buɗe ba.Ya yi mulki cikin hikima da adalci ga al'ummarsa” Zuciyata ce na ji tana wani irin bugawa na jin bayanin da Deborah ta yi mini.Kamar mai tsoron sake jin wata buwayar na ce “amma me Annabin ke nufi?” “Mutum mai isar da wahayi daga Ubangijin Ka'aba zuwa ga al'umma ” ta bani amsa kai tsaye.Ban ce mata komai ba sai tashi da na yi na fito waje ina kallon taurari ina kuma juya kalamanta. Ƙofar gidan na ji ana bugawa,na je na buɗe sai na ga gungun matsafan garin ne da alamu sun fito maitar dare ne suka biyo. “Ranki shi daɗe mun samu baƙuwar fuska a yankin nan,wani mutum ne maharbi mun tsince shi a wata gona yana bacci.Mun ɗaure shi da duk wata igiyar tsafi amma ta ƙi yin tasiri a kansa saboda girman tsafinsa wannan dalilin ne yasa muka zo zuwa gare ki” ɗaya daga cikinsu ya faɗa . Raina a mugun ɓace na ce “me yasa ba ku kashe shi ba?” Kallon juna suka yi kafin wani kuma daga cikinsu ya ce “ kamar dai yadda ya faɗa miki ɗin ne,tsafinsa nada matuƙar ƙarfi da dukkan alamu mutum ne na daban ko a duniyar ruhaniya” Ban ce komai ba na yi gaba a fusace yayin da su kuma suka take mini baya.Tun kafin na isa gonar nake jiyo numfashin baƙin tsafinsa,ina isa ya yi saurin tashi tsaye muna fuskantar juna.Ɗan saurayi ne da ba zai haura shekara ashirin da takwas ba,sanye yake cikin kayan maharba ya rine gefen fuskarsa da baƙin abu yayin da kuma ƙirjinsa aka zana wata baƙar kunama. Ban tsaya tambayar wane ne shi ba na kai masa farmaki,ya tare kafin kuma mu shiga masayar kalaman tsafi muna haɗawa kuma da yaƙin gangar jiki.Kamar yadda suka faɗa ɗin tabbas shi ɗin na daban ne,ban ida fahimtar haka ba sai da ya kai ni ƙasa ya saita kibiyar tsafinsa daidai idona. Yana jan wani numfashi ya furta “kafin a farmaki baƙo a fara tambayarsa da wace aniya ya zo,duk waɗannan matakan tsaron na ruhikan ruwa da kika saka ba su iya tare ni na shigo yankin nan ba sai ke ce kike tunanin za ki hana ni yin abin da na zo yi?” shi abin da ya furta,amma duk da haka ban saurare shi ba na fito da wuƙar mahaifina na daɓa masa ita a ƙirji daidai kunamarsa yayi wata irin kururuwa da ta saka dajin amsa wa kafin ƙyafta ido sai ganin kunamu muka yi suna zubowa kamar ana ruwa..... [08/04 12:12] MRS SADAUKI: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐 """"""""""""""""""""""" LoVe aNd HoRrOr StOry☠️ ```MRS SADAUKI```💫✍️ FCWA☀️ ____________________________________________ 05 Yadda baƙaƙen kunamun suka dabaibaye jikina shi ya fi komai ɗaga mini hankali,ga shi kuma masarafin tsafina ya ƙi aiki.Idona ƙurrr kan mutumin da na cakawa wuƙa yana tsaye ƙyam kan ƙafafunsa,yayin da kuma kunamun suka buɗe hannuwansu da alamu umarninsa suke jira su shiga harbata. Tafin hannunsa ya buɗe ya soma yin furuci cikin Yaren tsafi wanda ya sha banban da nawa,a hankali duk kunamun suka yi ɓata dabo sai a lokacin na yunƙura na tashi zaune ina kallonsa cike da mamakin me yasa bai kashe ni ba kamar yadda na yi yunƙuri. “Wane ne kai?” na tambaye shi.Bai bani amsa ba sai nuni da yayi mini da wuƙata wacce har zuwa yanzu tana nitse a cikin ƙirjinsa.A hankali na miƙe tare da zuwa na ciro wuƙar,abin mamaki sam babu ko da ɗigon jini da ya zuba illa kawai alamun an huda ƙirjin. “Banah!” ya bani amsa,na maimaita sunan a bayyane kafin na ce “me ya kawo ka YANKIN MUTUWA?” “Ke!” ya bani amsa kai tsaye,kallon ban gane ba na yi masa kafin na ce “ni kuma?” Kai ya jinjina mini kafin ya ciro wata sarƙa da ke a wuyansa mai tambarin gumki ya miƙo mini,na karɓa tare da juya ta sannan na ɗago na dube shi. “Ba ki ga komai ba?” ya tambaye ni. “Me kake son nuna mini?” “Duba da kyau dai” ya sake faɗa ,sai na nutsu da kyau nan ne na ga gumkin jikin sarƙar zanen mace ne da ƙusumbi a bayanta. Na shafi ƙusumbin da ɗan yatsana,nan take ya kawo wani haske kamar an kunna ƙwan lantarki.Banah ya matso kusa da ni shi ma ya ɗora nasa yatsan kan nawa sai hasken ya ƙaru a hankali kuma muka fara yin sama ƙafafuwanmu suka bar ƙasa muka lula can cikin iska. Mutanen gari ne suka fara fitowa,sai kuma suka shiga yin kiɗa da bushe-bushe yayin da wasu kuma suke rawa.Ban taɓa tunanin cewa wai hakan aure ne muka ƙulla ni da Banah ba sai da wasu ruhika suka bayyana a gare mu suka yi mana bushara da hakan tare kuma da ƙara mana power. Sarƙar nan mai hoton gumkin mace da ƙusumbi ita ce kabancin sadakina,ita Banah ya saka mini a wuya kafin mu sauko ƙasa. Gefe na koma ina kallonsa,ba mummuna ne ba amma kuma ba za a kira shi da mai kyau ba.A kallon farko za ka tabbatar da cewa shi jarumi ne a fagen tsafi,kumatuna da ya shafa shi ya katse mini ɗan guntun nazarin da nake yi a kansa. “Tunanin me kike yi?” ya tambaye ni,da sauri na juya masa baya ina mai basa amsa da cewa “ ban san wane ne kai ba,daga ina kake kuma amma kai tsaye ka zo ka aure ni ba tare da neman shawarata ba” “Naomi ba fa ni ne na tsara haka ba,allolin prophecy suka ga dacewar mu haɗu ni da ke domin mu cika alƙawarin da magabatanmu suka ɗauko” Da sauri na juyo ina kallonsa na ce “to ka riƙe ni matsayin abokiyar aiki kawai” ina gama faɗar haka na soma tafiya cikin rangaji saboda yanayin larurata.Ina jin yana take mini sawu har muka isa gida,Deborah na tarar a tsaye kamar mai jiran zuwana. Da ido ta tambaye ni shi kuma wancan na bayana? Na juya na dube shi da sauri ya ƙaraso ya gabatar da kansa ga Deborah sai na ga yanayin fuskarta sam babu annuri. “Zo ina son yin magana da ke” ta faɗa tare da kama hannuna muka shiga cikin ɗaki. “Ta ya aka yi ya zama mijinki alhalin tarihi bai nuna za ki yi aure ba a doron duniya?” Deborah ta tambaye ni tana wani tsure ni da ido. Ni ma ɗin kallonta na tsaya yi saboda gaskiyar da ta fito daga bakinta wacce na san ita kanta ba san ta faɗe ta ba. “ Ba zan yi aure ba?” na tambaye ta,sai a lokacin kuma na ga ta sha jinin jikinta tare da soma yin kame-kame . “ Tun yaushe kika gano haka?” na sake jefo mata wata tambayar. Ta yi ɗan ƙasa da murya tare da sauke idonta daga cikin nawa ta ce “tun ranar da Umma za ta bar garin nan zuwa neman tarihi a wasu guraren , ta shaida mini cewa ba za ki taɓa yin aure ba muddin alamomin prophecy sun bayyana a gare ki.Ita ce da kanta ta nuna mini tsanin nan da ke cikin ruwa,ni kuma na ja ki muka je” Sosai na ji ɗaci har ƙasan raina jin wai ba zan yi aure ba alhalin a duniyar nan babu abin da na fi so kamar na yi aure na haifi yara.A daidai wannan lokaci ne kuma na ji wani abu game da Banah,ko da a ce auren bogi ne to zan karɓe shi ko ba komai dai za a kira ni sawun ma'aurata kuma zan haifi ƴaƴa. “Ƙusumbin da ke gare ki ba zai taɓa barin maza su yi sha'awarki ba,in akwai waɗanda da za su so ki to ki sani mata ne ƴan uwanki ” Deborah ta faɗa tare da kamo hannuna alamun rarrashi. “Wannan furucin naki duk ƙarya ne,kin faɗi haka ne saboda kin jima kina sha'awarta wannan dalili ne ma yasa kika tunzura ta har kika kai ta karɓa muƙamin iko alhalin wa'adin karɓarsa bai yi ba.Kin san cewa muddin Maa nada rai ba za ki taɓa samun Naomi ba” Banah ya faɗa yana mai shigowa ɗakin. Kallon tsana Deborah ta soma binsa da shi kafin ta ce “muddin ina raye ba zan taɓa bari ka cutar da Nao ba” Ya yi wani murmushi kafin ya ce “na gode da tunatarwa ” sai kuma ya maido dubansa gare ni yana jefo mini kallon so da ƙauna ya ce “ ki sa a ranki Banah yana sonki kuma zai zauna da ke ko da kuwa dukkan jikinki ciwo ne” Wata ajiyar zuciya na sauke jin furicinsa ,kafin na dubi Deborah na ce “ba zan so ki tsani Banah ba saboda shi ɗin murfin rufin asirina ne.Deborah ki sani zuciyata ba za ta taɓa lamunta rashin miji ba” Kai ta girgiza mini tana mai cewa “Banah ba mijinki ba ne,in ma dai akwai shi to ba na ce a jinsinmu ba ne don kuwa tarihi bai nuna hakan ba” Da sauri Banah ya zo ya shiga tsakiyar mu yana mai ɗan ture Deborah ya ce “dama ba tun yau matsafan tarihi ke ƙirƙirar ƙarya ba domin cimma manufarsu” kallona ta yi,sai na kawar da kai ita kuwa da sauri ta fita. ★ “Ba zan taɓa lamunta ki auri ɗan maƙiyiyata ba,ki sani cewa ko bayan raina kika auri Naslam ban yafe miki ba“ Dadda ta faɗa tana yi wa A'ishah wani mugun kallo. “Ki haƙuri Dadda amma ina son yarima fiye da raina,ki sani cewa in kika hana ni aurensa to tamkar kin yi mini shamaki da duk farin cikin duniya” A'isha ta faɗa tana hawaye. Dadda ta yi mata mugun kallo kafin ta ce “da dukkan alamu har yanzu ba ki warke daga cutar haukan naki ba,ɗan matsafiya kike sha'awar aure ki haɗa zuri'a da shi?” Ta dubi mahaifiyar tata da jajayen idonta kafin ta ce “ Dadda babu wanda ya tabbatar cewa Ummi Naslam na yin tsafi,kawai ƙage aka yi mata wannan dalilin ne ma yasa ta bi dare ta bar masarautar nan” “Wato ƙage na yi mata? Don ubanki da idona na gani tana tsafi.Tashi ki ɓace mini ko na sabauta ki ” ta ƙarashe cikin tsawa,da wani irin sauri kuwa A'ishah ta fita daga ɗakin direct can baya ta nufa inda tantabarun yarima suke.Tana zuwa ta yi tsaye tana kallonsu yadda suke ciyar da junansu da kuma yadda suke yin wanka, murmushi ta soma yi tana jin sonsu ba don komai ba saboda yadda ta san muhimmancinsu a gun yarima.Daga bayanta ta ji muryar Barham yana mai cewa “har sai yaushe ne za ki bayyana asalin fuskarki? ” Ba tare da ta juyo ba ta ce “ ranar da ka bar ɓoyen taka!” “Amma ai kin san ni da ke ba ɗaya ne ba,magani nake bayarwa domin sanin wasu tsirrai dole sai na haɗa da Magic ” A'ishah ta juyo tana wani murmushi kafin ta ce “me yasa kake saka mini ido a lamurrana? Bayan ni ai ka san waɗansu masu ɗauke da kambun baka me yasa ba za ka takura musu ba ?” “Ki iya bakinki ko kuma...” ta yi saurin katse shi da cewa “ko kuma me? Ka je ka sanar da sarki? Hahaha! To bari ka ji abin da har zuwa yanzu tsafinka bai nuna maka ba,hatta yarima Naslam maye ne,yana ɗauke da kambun baka ” Cikin zafin rai Barham ya ce “ ki sani cutar kambun bakan yarima daga Ubangijin Ka'aba take ba wai ta tsafi ba ce,ke kuwa uwarki ce ta saka miki ita.A kullum cikin yin ƙoƙarina nake na ganin na magancewa Yarima cutar nan saboda na san hankalinsa zai tashi muddin ya farga” Shiru A'ishah ta yi tana nazarin kalamansa,wai ita Dadda ce ta saka mata maitar baka hakan na nufin kenan hatta Dadda matsafiya ce? Ba tare da ta ce masa komai ba ta yi saurin barin wurin ta koma can sashensu.Sai dai tana shiga ta tarar da Dadda cikin wani irin yanayi wanda da ace normal mutum ce ita da tabbas har taɓin hankali za ta iya samu. Dadda ce cikin siffar maciya tana a tsaye gaban madubi idonta a rufe tana furzo kalaman tsafi tana haɗawa da sunan mahaifiyar yarima Naslam. A'isha ta yi tsaye tana kallon cikin madubin wanda yake ta fitar da tiriri tamkar an ɗora shi kan wuta har wani hazo-hazo ke tashi. Ummi ce ta gani wato mahaifiyar yarima Naslam tana zaune kusa da ruwa da alamu so take yi ta wuce amma ta kasa shiga ruwan.A kallon farko da za ka yi mata za ka fahimci cewa kaf illahin jikinta dabaibaye yake da mugun baƙin tsafi. Dadda ta yi wata mahaukaciyar dariya tana mai fito da harshe waje tana yin wani tsafin A'isha sai gani ta yi Ummi ta faɗa ruwan,ba ta san lokacin da ta fasa ƙara ba ta ce “Ummiii?” hakan ya jawo hankalin Dadda matsafiya ta kuwa juyo da kanta ta kalli A'ishah tare da juya idonta suka fitar da wani haske ya je ya shiga A'ishah nan take ta faɗi ƙasa a sume. Dadda ta yi saurin komawa normal kafin ta je ta dubi ƴarta,hannuwanta ta kama ta soma janta ƙiii har ta kai ta kan shimfiɗa. Wata kwalba ta ɗauko ta gubar tsafi ta buɗe tare da dangwalo maganin ta shafawa A'ishah babu jima ta buɗe idonta tarau sai dai babu ɗigon baƙi. Dadda ta soma sarrafa tsafi babu jimawa kuwa duk maganar da A'ishah ta yi ita da Barham ta shiga tariyo kanta.Dadda ta naushi iska tana mai cewa “ wato dai mugun tsohon nan ba zai taɓa fita hanyata ba” sai kuma ta luluɓa bargo ta fice ta bar masarautar. A ɓangaren yarima Naslam kuwa a daren ranar haka ya kasa sukuni,yana kwance yana tunanin Naomi haɗi da yin surutunsa ba tare da ya san cewa ba zanen hotonta da ke ƙarƙashin pilow yana naɗar duk wata magana da zai yi ta yadda ita kuma za ta ji komai cikin ƙwaƙwalwarta. Sai wuraren ƙarfe biyun dare ya samu bacci mai nauyi ya ɗauke shi,mafarkin Naomi yayi.Wannan karon ba mu'amala suke yi ba,a'a takobi yasa zai sauke mata kai bayan an ce ta miƙa wuya ta karɓi shahada ta ƙiya.Yana datsa mata takobin ta yi kururuwa wacce kai ka ce a gaske ne sai ya ji abin har kunnensa.Daidai nan ya farka yana jan numfashi tare da soma yin magana shi ɗaya. ★NAOMI Duk da ban ji daɗin abin da ya faru ba tsakanin Banah da Deborah hakan bai sa na wani damu sosai ba saboda a ganina kowanne yana da hujjar da zai kalubalanci ɗan uwansa.Ita matsafiya ce mai rubutun tarihi,yayin da shi kuma matsafi ne mai ilimin jeji don maharbi ne. Washegari haka muka zaga gari ni da Banah a matsayinsa na mijina,kafin kuma yasa shela mutane suka taru a ƙofar gidanmu.Sabbin dokoki ya ƙara kafawa kafin kowa ya kama gabansa,haka muka zauna ni da shi ina basa labarina yayin da shi kuma ya yi mini alƙawari sai da dare sannan ya bani nasa labarin.Wannan yasa ko da daren yayi a ƙage na ce masa “ina saurarenka bani labarinka ” Maimakon yayi abin da na ce,a'a sai ma fatar dabbar da na suturce jikina da ita da ya yane ya soma yana shirin kai hannu kan jikina na zabura sakamakon kalaman nan irin na jiya da na soma ji suna ziyartar kwanyata ba tare da na san daga ina suke ba. “Ya Rabb! Ka taimaka ka kuɓutar da ni daga dukkan wani tarkon sheɗanu da mabiyansu.Ya Ubangijin al'arshi ka bani kariya a duk lokacin da na fuskanci uƙubar mushrikai kamar yadda ka bai wa Annabinka Ibrahim.Ya Hayyu ! Ya Ƙayyum ! Ya zul...” da wani mugun sauri na toshe kunnuwana ina mai yin wata ƙara don tamkar ana ɗiga mini dalma haka nake ji, wannan dalili ne ma yasa ban bari na ji ƙarashe ba.Jikina na yin ɓari na ɗauki suturata na mayar kafin na buɗe ƙyauren ɗakin,sauri-sauri haka nake tafiya har na isa ƙofar gidansu Deborah . A zaune na tarar da ita kan wani kututturen icce tana kallon sama,da alamu aikin nata ne take yi wato lissafin taurari.Gefenta na zauna ina mai cewa “ki yi haƙuri” “Ki yi tambayarki kai tsaye” ta faɗa ba tare da ta dube ni ba. “Wane ne Annabi Ibrahim ?” na tambaye ta a raunace don hatta faɗar sunan ma yana yi mini wani irin raɗaɗi. “Yana ɗaya daga cikin masu isar da wahayin da Ubangijin Ka'aba ya umarce su da shi.Kamar yadda tarihi ya zo Annabi Ibrahim ya fito daga cikin al'ummar da ke bautar gumaka amma duk da haka shi tun tashinsa bai taɓa bautar wani Ubangijin ba sai na Ka'aba.Al'ummarsa sun so hallakar da shi ta hanyar jefa shi a cikin wuta amma sai Ubangijinsa ya cece shi ya mayar da zafin wutar sanyi mai daɗi ba mai cutarwa ba” Shiru na yi ina nazarin bayanin da ta yi mini,ina shirin tambayarta wane ne shi Ubangijin Ka'abar sai ga Banah ya bayyana a gabanmu kamar walƙiya.Hannuna ya kama yana yi wa Deborah mugun kallo kafin ya ce “ina mai yi miki kashedi na ƙarshe ki fita idona na rufe” Debora ta miƙe tsaye tana cewa “abin da nake da niyyar faɗa maka kenan ka guji wasa da wuta” Tamkar wata sokuwa haka na tsaya ina kallonsu,sam hankalina ya ƙi tsayuwa wuri guda abin da nake son sani shi ne wane ne Ubangijin Ka'aba?????????? [09/04 17:18] MRS SADAUKI: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐 """"""""""""""""""""""" LoVe aNd HoRrOr StOry☠️ ```MRS SADAUKI```💫✍️ FCWA☀️ ____________________________________________ 06 Maimakon Banah ya kai mu gida a'a daga nan sai ya wuce da mu gaɓar ruwa. “Shawoli narat kohi jayi!” ya furta kalaman tsafi cikin wata irin murya,babu jimawa wata irin ƙara ta karaɗe wurin kafin ruwan ya soma darewa yana fitar mana da hanya.Haka Banah ya ja ni muka shiga muka fara tafiya,ko tsakiya ba mu kai ba aka soma yin ƙasa da mu har muka dangane da ƙasan ruwa.A nan ne na yi arba da tsoffin garinmu waɗanda suka mutu,wasu tun banda wayo a labari ne na ji mutuwarsu yayin da wasu kuma da hankalina suka yi mutuwar. Kamar yadda ake yi wa baƙo in ya zo a wuri haka suka karrama ni,a wannan lokaci ne na ida ganin ainihin ɓoyayyar fuskar Banah shi ɗin ba iya mutum ba ne a'a jinsi biyu ne. Wani abu aka shayar da ni wanda ya dagula mini lissafi ya juye mini hankali na ji tausayi,so,ƙauna da duk wani abu da ya shafi mutumci sun fita daga zuciyata.Sai dab da za mu fitowa ne sannan aka kawo Maa zuwa gare ni,tana tsaye cikin siffar nan ta matattu sai dai yanayin fuskarta ya nuna tana cikin damuwa kamar ba ta jin daɗin rayuwar wannan duniyar. “Maa” na kira ta ina mai shigewa jikinta,yadda na ratsa ruhin nata na fita shi ya sa ni saurin janye wa na koma kan ƙafafuna. “Naomi me yasa har zuwa yanzu ba ki yi wani aikin bajinta ba wanda zai sa ruhina ya mori aikinki? Dube ni yadda na rame har yanzu ruhikan ruwa ba su yi amanna da ni ba” ta faɗa cikin wani irin yanayi. “Maa sam ban gane abin da kike nufi ba” na faɗa . Ta ce “Ta hanyar kashe mutane ne kawai zan samu abinci Naomi ” ta bani amsa ,wato so take yi na fara sarrafa maita ina damƙe kurwar mutane ina kawo mata jininsu. Tana gama bani amsa aka zo aka tafi da ita,Banah ya kamo hannuna muka fito daga ƙasan ruwan.A lokacin da muka isa gida tuni gari ya soma yin haske,cikin son sake kasancewa da ni Banah ya soma yi mini wasu abubuwan amma na dakatar da shi ta hanyar yi masa wani kallo da idona da nake jin tamkar an yi mini musayarsu.Cikin wata shakkata ya janye daga gare ni kafin ya koma gefe yana kallona,murya a dake na soma magana “ka nemo baƙar akuyar da za a yi hadaya da ita,yau laraba ruhika na buƙatar jini” sai kuma na yi shiru kafin can kuma na ci gaba da cewa “ina son jinin mutum domin shayar da mahaifiyata” Sai da na kai karshe sannan Banah ya ce “domin samun jinin mutum ya zama dole ki fita farautar dare,don yin maita da rana tsaka ba halayyar shuwagabanni ce” sai kuma ya taso ya matso kusa da ni ya tallabo haɓata yana mai ci gaba da cewa “matata zafafa ce,na san ta kowanne fanni jaruma ce kuma ƙwararriya.Zan baki shawara mai kyau amma sai in kina so” “Ina jinka ” na faɗa a dake. Ya ce “ki shirya gagarumin yaƙi domin samo tataccen jini mai tsabta wanda ba a gurɓata shi da maita ba” “Su wa zan yaƙa kenan?” “Garuruwan da ke maƙwabtaka da mu mafi akasarinsu ba su sarrafa tsafi ballantana maita,in muka yaƙe su sosai za mu samu alkhairi ” A cikin bayaninsa sosai na tsinci kishin garinmu da kuma son ci gabansa, wannan dalili yasa na ce “bayan an gama ƙaddamar da hadaya,zan so ka haɗa hankulan dukkan mutanen garin nan sannan ka shaida musu a yau ba sai gobe ba za mu je farauta ruhika” Banah ya yi wani murmushi yana mai cewa “an gama” sai kuma ya fice. Ido na lumshe ina tunanin yadda na ga shugaban nan NASLAM da tawagarsa suna yaƙar Mayu.Da wani irin sauri na buɗe idona ina mai yin magana a fili “ yaƙi cikin tsakiyar dare ya fi ɗaga hankali kan da safe,don haka farmakin dare za mu kai musu” sai kuma na yi wani murmushin mugunta wanda hakan ba ƙaramin sanyaya mini zuciya ya yi ba. Kamar yadda na umarci Banah haka ya kawo mini baƙar akuya har da ma zakaru su ma duk baƙaƙe ne.A gaban al'ummar gari muka je muka shayar da kogi jinin dabbobin kafin kuma mu juyo,Banah ya laƙanci tsafi sosai wannan yasa bai sha wuya ba wurin aiwatar da shirinmu na kai farmaki a garuruwan da babu maita. Dab da shigowar duhun dare Deborah ta zo inda nake,haka kawai na ji ban buƙatar ganinta duk da kuwa wani sashe na zuciyata yana tune da ƙawancenmu. “Abin da kike shirin yin sam bai dace ba! Babu wani sarki da ya zo mana a tarihi cewa ya nuna ƙarfin tsafi ya janyo wani yanki izuwa nasa” Deborah ta faɗa ,ba tare da na kalle ta ba na ce “wannan garina ne,ni ce ke da ikon yin duk abin da ya dace ga al'ummar ciki ba ke ba.Ruwanki ne ki rubuta tarihina a cikin littafinki,in kuma ba ki ra'ayi za ki iya barinsa” “Naom...” ban bari ta kai ƙarshe ba na juyo a harzuƙe cikin hargowa,sai kawai ganin Deborah na yi ta yi sama tare da faɗowa ƙasa cikin rauni.Na nuna ta da yatsa ba tare da na ce mata komai ba,amma sosai ta gane kashedi nake yi mata. Wani irin kallo ta soma jefo mini kafin ta ce “ta yaya kika yarda har wani baƙon haure ya raba mu? ” “Shi ɗin mijina ne,don haka na san ba zai yi abin da zai cutar da ni ba kamar yadda ke kike ƙoƙarin danganta ni da masifar rashin yin aure” Hawaye suka zubo kan kumatunta ba tare da ta goge su ba ta ce “na san kin karanta littafin tarihi,kin gani da kanki muddin shugaban tawagar Mayu ta fito a mace babu ƙaddarar aure a rayuwarta,in kuma ta yi shi to ki sani akwai ranar da mulkin sai suɓuce mata.Sannan yadda tarihi ya nuna ke dai babu aure a tarihinki da ya zo da wanda ma zai zo gaba, sannan na faɗa miki sharaɗi in ma kin yi auren to ki sani ba a wannan duniyar ta ruwa ba” Cike da tsana da takaici nake sauraren jawabinta.Da a ce za a tambaye ni babban maƙiyina a duniyar nan a yanzu to babu makawa zan ce Deborah ce,saboda duk wanda ke da ja da lamarin aurena to ban ɗauke shi masoyi ba. Baya na juya mata a karo na biyu kafin na ce “ina shawartar ki da ki bar gidan nan kafin na yanke miki ɗanyen hukunci” Ba tare da ta ce komai ba ta tafi,babu jimawa kuma shi Banah ya shigo hannunsa riƙe da ƙwallon kwakwa ƙwaya ɗaya.Tsakiyar ido ya dube ni kafin ya ce “muddin kina gama baki da matsafin tarihi to mulkinki ba zai taɓa ci gaba ba saboda a kullum so suke su canza maka ra'ayi akan abin da kake buri” “Me za ka yi da kwakwa?” na tambaye shi ba tare da na bai wa abin da ya gama faɗa muhimmanci ba. “Jirgin dare ne na Mayu ,a cikinsa za mu tafi” ya bani amsa.Kallon mahaukaci na yi masa don sam ban san komai ba game da maita saboda ban taɓa gwada yi ba.Sai da dare ya zo tsakiya ne na ga abin al'ajabi yadda Banah ya mayar da kwallon kwakwa jirgi,kuma ma ni ce farkon shiga bayan shi sai kuma ya soma zagayawa da mu yana ɗibar jama'ar gari waɗanda ke ɗauke da kambu maita ko tsafi. A wani gari jirgin namu ya yi dirar angulu,tsit garin yake kowa na yin bacci .Haka muka zagaye shi kafin mu soma sarrafa mugunta muna fito da su daga gidajensu muna cillawa cikin jirgi,duk wanda ya yi gardama a nan take muke aika ransa ga ruhikan ruwa.Cikin ƙanƙanen lokaci garin ya hargitse da ihuce-ihuce da kukan mata da ƙananun yara,gefe ɗaya kuma wuta ce ke tashi. Har mun shiga jirgi za mu koma sai idona ya sauka kan wani gida,shi kaɗai ne ba mu rogaza ba.Kukan jinjiri na soma ji,cikin azama na dire tare da zuwa na ratsa bango na wuce saboda yadda duk ƙwayoyin tsafi suka game jinina. Wata mata ce na tarar a ciki,gefenta jinjiri ne sabon zuwa duniya don ko cibi ba a yanke masa ba.A hankali na duƙa na ɗauki yaron,sai a lokacin kuma na ji muryar matar na cewa “kar ku kashe mini yaro ” yadda na ga soyayyar uwa da ɗa a cikin ƙwayar idonta shi ya tuna mini tawa mahaifiyar. Ban kai ga cewa komai ba Banah ya shigo,kafin ƙyaftawar ido ya soma jan ragamar ruhinta.Cikin gargardar murya na ji tana cewa “ Ash-hadu an la'ilaha illallah! Wa'ash-hadu anna Muhammadu Rasulullah!” wata irin walƙiya ce haɗi da zubar ruwa suka zo a nan take,yayin da kuma ni da Banah muka zabura muka yi baya saboda ɗacin amon sautin abin da ta furta yayin da shi kuma yaron da ke rungume a hannuna ya ci gaba da canyara kuka. “Mu bar wurin nan yi sauri kafin alƙawari ya karye” Banah ya furta cikin wani irin tsoro wanda ban san dalilinsa na yin haka ba.Ina ɗaga kafaɗa haɗi da sake rungume jaririn a ƙirjina na fito,ina shiga cikin jirgin Banah ya jefo mini wani mugun kallo yana kallon jaririn.Na ƙankance ido ina mai ce masa “kar ma ka fara,ka tuƙa jirgi mu tafi” Ba don ransa ya so ba ya ja ragamar jirgin namu na matsafa har muka isa yankinmu,a ƙofar gidanmu aka zube dukkan mutanen da muka kwaso kafin ni na shiga can ciki na bai wa sauran umarnin su tsaya su tsare mutanen. Kan gado na shimfiɗe jaririn,ina shirin kwanciya na ji wata murya a cikin ƙwaƙwalwata tana shaida mini an samu baƙon haure a yankina. Ba tare da na fita ba na yi surkulle na aika Banah can gaɓar ruwan,bai dawo ba sai da gari ya yi haske sai ga shi saɓe da wata mata. Kan tabarma ya shimfiɗe ta,kallo ɗaya na yi mata tal na ji ƙaunarta ba don komai ba sai don na hango tabon ruhaniya a jininta. Fuskarta na shafa nan take ta buɗe idonta,sai kuma ta tashi zaune tana mai kallona da kuma inda take. “Su wane ne ku? ” ta yi tambayar tana ajiye idonta kan gado inda na shimfiɗe jariri.Da sauri kuma na ga ta miƙe tana cewa “me yasa har yanzu ba a yanke cibi ba?” “Ban san ya ake yi ba” na bata amsa. “Bani wani abu mai kaifi” ta furta,na zaro wuƙata na miƙa mata,da ita ta yi amfani ta yanke cibin kafin kuma ta ciri suturar jikinta ta kulle daidai wurin da ta yanke ɗin. “Gefen cikin jaririn duk yayi baƙi saboda mahaifa ta taɓa shi,a kawo ruwa na yi masa wanka” ta sake faɗa . Banah ya ɓata rai yana shirin magana amma na dakatar da shi,na je na kawo mata ruwan.Sai dai tana saka hannunta ciki ta ce “waɗannan ai masu sanyi ne,masu ɗumi nake so” idona kawai na juya ruwan suka soma tafasa suna fitar da tiriri.Sai ta yi ƙuri tana kallona kafin ta ce “wannan tsafi ne kika yi kuma sarki ya haramta haka” Sai muka kalli juna ni da Banah tare da haɗin baki wurin tambayar “wane sarki?” Kai ta girgiza sai kuma ta soma yi wa jaririn wanka,ta saki murmushi ta ce “mace ce ashe” sai ta fito da ita daga cikin ruwan,ta cire uban kallabin da ta yane kanta da shi ta saka jaririyar a ciki. “Wace ce ke?” na tambaye ta. “Ni kaina ban sani ba,amma sai nake jin tamkar an aiko ni nan ne saboda isar da wani saƙo” ta bani amsa tana mai ɗago kai ta dube ni.Idona ya sauka kan goshinta nan na ga irin tabon nan da ke a goshin NASLAM ita ma yana fitar da haske sai dai bai cutar da ni ba,hakan kuma sai ya yi mini daɗi na ji a raina cewa ko da a ce ita ma wannan Ubangijin Ka'aba take bauta ma zan iya zama da ita. ★ Wuraren ƙarfe tara na safe daular abu NASLAM ta samu wani rikitacen labari.Cikin ƙarfin hali da dakiyar zuciya yarima ya miƙe kan ƙafafunsa bayan ya yi wanka da magani ya kuma sha a cikin shayi. Cikin tafiyar jarumta ya soma ratsa dakarun har ya isa inda Sarki ke tsaye yana jawabin yadda komai zai kasance,kamar kuma yadda Sarkin ya tsara jakariya Ali ne zai jagoranci tafiyar. “Zan tafi ni ma don haka a shirya dokina” ya faɗa yana mai kallon mahaifinsa cikin ido.Sarki ya kawar da kai,don ya san ko da a ce ya yi yunƙurin hana shi ba zai ji ba. Haka duk suka fito kowanne ya hau doki,da yarima zai hawa kan nasa sai da jakariya Ali ya taimaka masa amma a haka suka tafi. Tun a bakin ƙofar shigar garin suka fara cin karo da kayan tashin hankali,babu shiri yarima ya diro yayin da kuma jakariya Ali ya soma take masa sawu. Gawarwakin mutanen da aka kashe,Ali ya kalla sai ya ga duk kusan kalar mutuwar iri ɗaya ce.Ya kai hannu ya damtsi ƙasa sannan ya kai kusan hancinsa ya sunsuna,yarima ya dube shi tare da cewa “me ka fahimta?” “Farmakin Mayu ne” ya basa amsa,ran yarima ya ƙara ɓacewa amma a haka suka ci gaba da duba ko ina har suka shiga gidan da matar nan ta haihu. Cak jakariya Ali ya tsaya yana kallon ustaza Jamila,wacce ta bayar da dukkan lokacinta domin yin hidima ga addininta.Yarima ya ƙarasa yana mai cire rigarsa ta sarauta ya luluɓe ta,tare kuma da baiwa dakaru umarnin a ɗauke ta a kai ta can masarauta tun yanzu ba sai an jima ba...... [10/04 08:51] MRS SADAUKI: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐 """"""""""""""""""""""" LoVe aNd HoRrOr StOry☠️ ```MRS SADAUKI```💫✍️ FCWA☀️ ____________________________________________ 07 Ustaza Jamila ƙanwa ce ta jini ga jakariya Ali,mijinta ma ya mutu ne a wajen yaƙin haɓaka musulunci sai ga shi ita ma ta mutu wurin da'awar jawo hankulan waɗanda ba musulmi ba.Kamar yadda tsarin masarautar yake,suna aika maza da mata garuruwa don koyar da mutane karatu. Yarima NASLAM ya dafa kafaɗar jakariya Ali yana mai cewa “ dukkan rai zai ɗanɗani mutuwa,ka sa a ranka lokacinta ne ya yi.Mu ma muddin namu yayi babu makawa a duk inda muke mutuwa za ta riske mu” Idon Ali sun kaɗa sun yi ja sosai,muryarsa ma cikin wata irin sarƙaƙiya take fita.“Na yi imani ga Ubangijin Ka'aba,dukkan wata ƙaddara mai kyau da akasinta daga gare shi take.Sai dai babbar damuwata ɗaya ce ,cikin jikinta sam babu shi a yanzu hakan yana nufin kenan ta haihu in kuma ya tabbata haka ina jinjirin yake?” Shiru yarima Naslam yayi na wani ɗan lokaci kafin ya ce “a duk inda yake Ubangijin Ka'aba ne zai tsare shi,ka dai kawai ka sa kyakkyawan yaƙini ga ubangijinka ” kalamansa suka yi tasiri a zuciuar jakariya Ali, wannan ya basu damar ci gaba da binciken ko ina. Bayan sun gama haka suka haƙa rame aka rufe sauran kafin su juyo su dawo masarauta inda Sarki Haroon da sauran al'umma ke dakon jiransu. Suna shigowa sarki ya je ya tarbi yarima tare da soma tambayarsa abin da ke faruwa. “Farmakin Mayu ne,duk sun kashe mutanen gari da alamu kuma sun tafi da wasu.Babban baƙin cikin shi ne ba su bar wani sawu ba da zai sa mu gane ta ina suka fito ” Barham da duk ya ji abin da yarima ya faɗa sai ƙara matsawo yayi yana mai cewa “a yadda ka yi bayanin ya tabbata cewa wannan rundunar Mayun ta samu jagoranci Banah maharbi” Sarki da yarima Naslam sai duk suka maido dubansu ga Barham ɗin,shi kuwa kai ya jinjina kafin ya ci gaba da cewa “tarihin da ya fara zuwa na wannan ƙarnin ya bada labarinsa,Banah maharbi ne kuma babban matsafi wanda ya fito daga tsatson aljanar ruwa.Mahaifinsa ya kasance masinci ne,ya iya ruwa sosai a irin alƙawarin da mutane ke ƙullawa da ruhikan ruwa mahaifin Banah ya yi gamo da wata aljanar ruwa har yayi tarayya da ita suka same shi.Tun da aka haife shi a cikin jeji ya tashi tare da fatale da aljanu,kafin mahaifinsa ya mutu ya koya masa farauta da kuma baƙin tsafi na ƙarnin baya sannan kuma ya ɗora shi kan turbar yi wa aljana ZAƘUMA bauta” Barham na kawo nan da zancensa masarautar ta ɗauki wani salo,guɗa ce kamar an kawo amarya ta karaɗe ko ina kafin kuma iska ya soma tashi babu jimawa kuma aka soma yin wasu yayyafin jini. Hankali a matuƙar tashe Barham ya ce “Attakbirrrr!” Dukkan mutanen da ke wurin suka amsa da “Allahu Akbar!” nan take yayyafin jinin ya tsaya cak wanda duk ya ɓata fuskokin mutane.Sai kuma sararin samaniya ya soma ɗaukar launin ja yana nuno inuwar wata halitta marar kyawun gani can ita ma ta ɓace komai ya dawo normal. Ran sarki da na yarima ya ɓace,saboda ba tun yau suka saba ganin ire-iren waɗannan surkullen ba. Barham ya ce “ Aljana ZAƘUMA ce,wato uwar gijiyar Banah da ita yake tsafi.A kullum yana shayar da ita jinin mutane,ita kuma tana basa ƙarfin iko ” “Ina zan samu shi Banah ɗin?” yarima ya tambaya. Barham ya ce “Ubangijin Ka'aba ne kawai ya san daidai ina yake a yanzu,saboda tamkar guguwa haka Banah yake bai zama wuri ɗaya yawo yake yi gari-gari yana shanye jinin al'ummar yankin” Yarima zai buɗa baki ya sake yin magana amma sarki Haroon ya dakatar da shi ta hanyar cewa “yanzu abin da ya fi muhimmanci shi ne yi wa ustaza Jamila sutura,don haka a kira gimbiya A'ishah ta yi mata wanka” Sai a lokacin ne kawai Ayyub ƙanen sarki Haroon kawai ya saka bakinsa,“ gimbiya A'ishah tana kwance babu lafiya tun jiya,na so na sanar da kai sai kuma wannan al'amari ya danne niyyata ” Hankali a tashe yarima ya ce “meke damunta?” “Ciwon ido ne mai tsanani ,idanunta sun zama kamar gauta ” Ayyub mahaifi ga gimbiya A'ishah ya faɗa . Yarima bai ƙara cewa komai ba ya shiga can ciki,direct kuma sashensu gimbiyar ya wuce. A kwance ya tarar da ita don tun lokacin da Dadda ta fice ta bar ta take nishin azaba idonta sai ƙara ciwo suke yi saboda ta ga abin da bai kamata a ce ta gani ba. Tana jin muryar yarima ta yi ƙarfin halin buɗe idon nata sai dai tamkar mai ɗauke da sabuwar makanta haka take ji dole ta ja su ta rufe. “A'ishahhh?” ya kira sunanta cike da tausayinta.Murya na ƴar rawa ta amsa da “na'am yarima” “Mene ne ya shiga idonki?” ya sake jefo mata tambaya,sai dai ba ta kai ga amsawa ba jakariya Ali da Barham suka shigo. Barham ya matsa kusa da kanta yana ajiye jakar kayan aikinsa,bai ɓata lokaci ba ya soma zuba magani yana wanke mata idanunta duk da yana haɗawa da Magic babu wanda ya sani in ba ita gimbiya A'ishar ɗin ba. Cike da aminci ta buɗe idonta da suka dawo normal tana kallon Barham da yake yi mata ta idanu. “In yau na wanke miki ido kin samu lafiya ki sani gobe ba zan yi ba,zan bar ki da mugun halinki ” “Ban taɓa ganin inda maye yake gorantawa ɗan uwansa ba sai kai Barham” ita ma ta basa amsa ta ido. Ya ce “ni ba maye ba ne,ban taɓa yin maita ba hasali ma ina adawa akan duk masu yinta.Ke ma kin san cewa iya Magic kawai nake yi shi ma ba don komai ba sai don ci gaban masarauta” “Me yasa dole sai ni kake son na bayyana kaina? Don me shi yarima ba ka damu da tasa maitar ba?” ta tambaye shi,sai dai shi Barham ɗin bai bata amsa ba ya juye kansa ya mayar da dubansa ga yarima Naslam yana mai cewa “ba wani babban abu ba ne ya same ta,kawai wani ɗan tsautsayi ne” Yarima NASLAM ya dube ta yana mai cewa “ki kwanta ki huta” sai kuma ya fice jakariya Ali na take masa baya. Wasu mata aka samu suka yi wa ustaza Jamila wanka.Sai da aka ma fito da gawar ne sannan gimbiya A'ishah ta san abin da ke faruwa,sosai ta ji zafin mutuwar har da zubar da hawaye.Ana yi mata sallah aka kai ta gidan gaskiya,sai kuma a wannan lokacin ne jakariya Ali ya nuna rauninsa ya soma yin hawaye waɗanda zubar da su ba ƙaramin sanyaya masa zuciya suke yi ba. Sai da aka yi kwana uku ana jimamin mutuwar ustaza Jamila kafin kuma lamurra su ci gaba da tafiya. A yau ne yarima yasa aka fito da matsafiyar nan da ta raira waƙa tsafi.Gaban sarki aka gurfanar da ita,tare da umartar ta da ta faɗi laifinta. Amma ta yi shiru ta ƙi cewa komai sai yariman ne ya shaidawa sarki yana mai ƙara wa da “a yanke mata hukunci nan take ban son ajiyar mayya a cikin masarautata ” Sarki Haroon ya kafe ta da ido yana kallo kafin ya ce “ki amsa laifinki sannan ki tuba ki rungumi addinin Musulunci domin tsira da ranki” “Babu wani addini da zan shiga,na fi son zama babu alƙibla.Sannan kuma ni ba mayya ba ce duk da ina da ilimin sarrafa maitar,maganar ƙarshe kuma ita ce zan koma gida” Rai ɓace yarima Naslam ya zaro takobinsa da niyyar sauke mata kai amma jakariya Ali yayi saurin riƙe shi yana cewa “ka nutsu yarima kar ka yi saurin yanke mata hukunci jira na kira Barham” Zuciyarsa na ƙuna ya ce “ba ka ji yadda take magana ba sam babu ɗa'a?” bai ma kai ga cewa wani abu ba Barham ɗin ya shigo. Kallo ɗaya ya yi wa matar ya gane wace ce ita,hakan yasa ya ƙarasa gun sarki yana mai yin ƙasa da murya ya ce “kar ku kashe ta,za ta yi mana amfani a nan gaba” sosai sarki yake ɗaukar shawarar Barham saboda shi ɗin aminin mahaifinsa ne sannan kuma dattijon arziki na masarautar. “Ku mayar da ita” sarki ya faɗa wanda hakan sam bai yi wa yarima daɗi ba sai kawai yayi zuciya ya fita daga wurin. Jakariya Ali ya bi bayansa yana mai cewa “ gaggawa aikin sheɗan ne,matar can tana ɗauke da wani ɓoyayyen sirri wanda nake jin cewa ita ce makullin da za mu yi amfani da shi wurin buɗe duk wata ƙofa da ta yi mana wuyar shiga” Ba tare da yarima ya ce masa wani abu ba ya soma cire kayansa na sarauta yana ajiye wa.Toilet ya shiga ya soma yin wanka ko zai ji sassauci,har ya fito jakariya Ali na nan.Shi ne ma ya taimaka masa wurin tsane jikinsa ya saka kayan zaman gida,daga nan sai suka wuce can inda tantabarunsa suke. Yana son tsuntsaye, wannan yasa ko ƙunci yake sai ya ziyarce su yake jin daɗi.Jakariya Ali ya buɗe su,da gudu kuwa duk suka shiga fitowa suna nufo shi,ɗaya ta sauka kan kafaɗarsa ya kai hannu ya damƙo ta yana shafar jikinta yana murmushi. Sai ya ji kamar ana kallonsa,ido ya baza cikin tantabarun nan idonsa ya sauka kan baƙuwar tantabara idonta ƙurrr kansa.Kasancewar bai yarda da canfi ba sam bai kawo komai a ransa ba,haka ya ratsa ya je ya ɗauko ta wani irin shock ya ratsa shi nan ɗin ma bai sa a ransa wai lamari ne da ya shafi sprituality ba. Jakariya Ali ne kawai ya farga da abin da ke faruwa,amma kuma sai ya ja bakinsa yayi shiru.Duk yadda yarima ya so tantabarar ta saki jikinta amma abu ya cuttura kawai sai ya wuce da ita can ɗakinsa yana mai cewa “ban san daga ina ita wannan ta zo ba,da alamu ta ƙi sabawa da sauran ne” Jakariya Ali ya ce “ dama ai kullum cikin samun baƙi tantabaru ake yi,ita ma za ta saba” Cikin ɗakinsa ya sake ta,ai kuwa sai ta shiga yin walwalar. A can ɓangaren gimbiya A'ishah kuwa abubuwa ne duk suka dagule mata,ga rashin ƙawarta Jamila ,ga ɓatan Dadda kusan kwana uku har yanzu ba ta dawo ba,ga kuma yanayin jikinta da take jin ya sauya.Zaune ta yi cikin halin ƙaƙanikayi tana wasiƙar jaki,sai ta ji ana magana ƙus-ƙus ba ta jin abin da ake cewa, da ta nutsu sosai sai ta gane a cikin drower kayanta.A hankali ta je ta buɗe,ɓerayen da suke gurgurar kayanta suka saki ihu a tare wannan karon sarai ta ji abin da suka ce. “Wayyo an kama mu yanzu an yi ƙoƙarin kashe mu” shi ne abin da ɓerayen suka faɗa kafin su fara gudun tsira,har kan ƙafarta ɗaya ya faɗo amma ta kasa yin motsi saboda shock.Ita maitarta iya ta juya baƙi ya dawo fari ce,sai ga shi yau ta ƙara samun matsayi.Jikinta ne ya hau rawa,babu shiri ta nufi ƙofa don zuwa wurin Barham ta sanar da shi sai kuma ta yi kiciɓis da Dadda wacce ta dawo daga jejin Mayu.Da sauri ta ja baya,ita kuwa murmushin mugunta ta sakar mata tana mai cewa “Allah yasa dai ba ƙoƙarin tonawa kanki asiri kike yi ba? To ki sani muddin yarima ya ji labarin ke mayya ce to zai fasa aurenki, ba kuma zai yi jinkiri sauke miki kai ba kin fi kowa sanin halinsa fiye da ni yadda bai da tausayi akan mayu” Idon gimbiya A'ishah ya kawo ruwa,yanzu ne kawai ta yarda da maganar Barham .Tabbas a matakin da take a yanzu ta riga da ta makaro babu ta yadda za a yi ya cece ta. Dadda ta ci gaba da yi mata gargaɗi mai ban tsoro,“ in kuma kin shirya yin mutuwar kare sai ki je ki faɗa ,sanin kanki ne hatta sarauniya Sarat ta bar masarautar nan saboda laifin maita ballantana ke karan kaɗa miya ” “Amma Dadda ni ban ce miki ina son zama mayya ba,don me za ki bani kambunta?” gimbiya A'ishah ta faɗa . Dadda ta bata amsa da “saboda duniyar nan muddin babu maita da Magic to tamkar miya ce babu magi,ki zo na nuna miki mece ce ainihin rayuwar Mayu na tabba in kika ga irin shagalin da ake yi ke kanki za ki ji daɗi ki kuma gane gata ne na yi miki ” shiru gimbiya A'ishah ta yi kafin ta je da gudu ta rungume Dadda. ★YANKIN MUTUWA Zuwan baƙuwar haure daga duniyar turɓaya shi ya canza mana yanayin shigarmu.Na ajiye fatar dabba na koma saka kaya,waɗanda Banah ne da kansa ya shiga duniya shi da sauran matsafa suka kwaso su a can duniyar tuɓaya.Kai tsaye za a iya cewa suka sato,saboda dare ne suka bi suka dinga shiga kanti suna ɗebo kaya bayan an kawo haka aka zube su aka rabawa kowa ciki kuwa har da ƴar jaririya da na samo wacce har zuwa yanzu ba a saka mata suna ba. Ummilo shi ne sunan da nake yi wa matar wacce duk ƙoƙarin Banah na son saka mini tsanarta bai yi nasara ba. Zaune na yi ina kallon yadda take bai wa baby madarar da aka tatso daga dabbobi.Hannu na kai na shafi fuskar Babyn ina mai cewa “Ummilo wane suna kika zaɓa mata?” Ta yi wani murmushi mai ƙayatarwa kafin ta ce “ina son sunan Jamila saboda na riƙi ƴa mai irin sunan nan” sai kuma ta yi wani irin shiru kamar mai yin nazari,a nan ne na fahimci cewa kamar ƙwaƙwalwarta na son tuna wani abu da ya danganci rayuwarta. Ina shirin yin magana sai gani na yi gari ya ɗau wani irin duhu,yayin da kuma mutanen da na zube suna yi mini hidima suka soma yin ihu.Duk yadda na so yin tsafi abu ya cuttura,kamar minti biyar sai komai ya dawo normal.Idona na sauke ƙasa sai na ga duk ɗigon jini ne ta ko ina kamar an yi ruwansa,ina ɗago kai kuma muka haɗa ido da Banah fuskarsa kicin-kicin kafin ma na kai ga tambayarsa sai cewa yayi “ tun da kika shigo da jaririyar nan a yankin nan bala'i ya soma sauka,don haka mun yanke shawara ni da sauran matsafa za mu bayar da jininta matsayin hadaya ga ruhikan ruwa........ [11/04 17:07] MRS SADAUKI: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐 """"""""""""""""""""""" LoVe aNd HoRrOr StOry☠️ ```MRS SADAUKI```💫✍️ FCWA☀️ ____________________________________________ 08 “Ta ya za ka ce a ɗauki jaririya a kai wa Teku matsayin hadaya? Wannan sam ba mai yiyuwa ba ne.Wannan al'amarin da ya faru kuma ko kaɗan bai da haɗi da da jaririya Mila wani baƙin ƙulli ne daga maƙiya kuma zan binciko na gani duk masu hannu a ciki” na faɗa . Banah ya ƙanƙance ido yana kallona,na je da sauri na ɗauki Mila daga kan cinyar Ummilo na goge mata fuskarta da yayyafin jini ya ɓata.Can ɗaki na yi tsinke,ina daidaita mata kwanciya ya shigo yana mai cewa “ita kuma Ummilo sai yaushe za ta tafi tun da kin karya doka kin ce ba za a kashe ta ba” Ba tare da na juyo ba na basa amsa da “ nan ɗin masarautata ce,Ni ke da ikon barin wanda zai zauna da kuma wanda zan kashe,ka tsaya iya matsayinka na mijina in ina son shawarinka ni ce da kaina zan neme ka” Cike da takaici Banah ya fito daga ɗakin ya jefi Ummilo da wani mugun kallo wacce yake jin tsanarta sai dai fa alƙaluman tsafinsa sun kasa rubuta sunanta .Direct can bayan gari ya nufa,bai yi nisa ba ya soma furzo kalaman tsafi nan take busashen ganyen da ke zube a ƙasa ya soma tashi sama kafin kuma ya haɗa wata baƙar guguwa wacce ta yi ambaliya da gangar jikinsa ya ɓata .Cikin wani kogo ya bayyana mai ɗauke da kunamu baƙaƙe ƙirin kuma ga su manya-manya.Suna ganinsa duk suka soma basa hanya,shi kuwa haka ya dinga ratsa tsakiyarsu har ya isa can ƙarshen kogon inda wata halitta ke kwance tana ƙyafta ido kamar mai jin tsoron buɗe su ɗin. Zubewa yayi yana mai yi mata sujuda ba tare da kuma ya ɗago ba yake cewa “kin ce in na dinga shayar da ke jini za ki ɗaga martaba ta fiye da duk wani mai iko a duniyar nan,amma me yasa Naomi ke yi mini gardama akan hukuncin da na zarta alhalin hatta maganin laƙani na sa an shayar da ita shi” Ba ta basa amsa ba,sai fara saukowa da ta yi daga kan dutsen da take kwance ta zo ta fara hawan bayansa tare kuma da laulaye shi da bindinta.A hankali ta zagayo kanta kan ƙirjinsa,babu ɓata lokaci kuma ta buɗe bakinta tare da kafa masa haƙoranta masu mugun tsini ta soma tsotsar jininsa na wani lokaci kafin ta tashi sama tana wani irin kuka kamar jiniya.Dukkan kogon ne ya tsaya cak kamar babu wata halitta mai numfashi,muryarta ta soma fitowa “ka karya dokata,na faɗa maka duk wacce za ka aura to ya zama dole ka yi tarayya da ita a wannan daren sannan ka bani jinin budurcinta.Tun da har ka bijire to ya zama dole a gare ka da ka yi haƙuri da wasu ƙananun al'amurra.Sannan ita wannan mata da kake tsana ta kasance shugaba ce a wata mazaɓar duniyar ruhaniya muddin ka yi kuskuren cusa kanka a lamarinta to za ka tsinci litininka a laraba ” Sai da ta dire kalamanta sannan Banah ya ɗago,idonsa sun kaɗa sun yi ja kamar na baƙin maye.Aljana ZAƘUMA ta soma saukowa daga can saman ta zo dab da shi ta na hura ƙirjinsa wanda ya fitar da sawun haƙoranta,sai kuma ta ci gaba da cewa “a jefa jiragai cikin ruwa domin fara saye da sayarwa tsakaninku da wasu garuruwa,ta wannan hanya ce zan samu yadda nake so” tana gama faɗar haka ta cillo shi tsakiyar gari.Bai ma koma can gida ba ya wuce gaɓar ruwa,sai ya tarar da manyan jiragai guda biyu.Tsaye yayi ya lumshe ido tare da soma yin magana da ruhikan ruwa,bayan sun amsa masa ne ya tsaga yatsansa jini ya zuba a cikin ruwan da kuma jiragen. ★Naomi Bayan fitar Banah kalar nawa tsafin na yi don binciko su wane ne suka fara yi mini zamba cikin aminci,sai dai babu wanda aka nuna mini fuskarsa illa aljana ZAƘUMA.Banda ilimin tarihi wannan yasa ban san wace ce ita ba,haka na fito na samu Ummilo na tambaye ta. “Babu matsafin tarihi a wannan yanki naku?” ita ce tambayar da ta yi mini. Na ce “akwai sai dai mun yi kare jini,biri jini da ita kwanan baya” Ta ce “ke ce shugabar duk wani da ke garin nan,don haka ki aika kawai ta zo” na yi shiru na wani ɗan lokaci kafin na ga kuma eh ta yi gaskiya. Takarda na nemo da tawada na soma yin rubutu,bayan na gama sai na dinga murza ta ina yin furucin tsafi a hankali babu jimawa kuwa takardar ta fita daga hannuna ta yi sama.Ido na birkice ta yadda komai zai wakana ina gani,cikin aminci Deborah ta samu wasiƙar na yi tunanin ba za ta zo ba sai ta bani mamaki kuwa yadda ta ɗauko hanyar zuwa nan tana tafe iska na ƙara yin gaba da ita. Tana isowa ciki sai na ga ta yi tsaye tana kallon Ummilo kafin da sauri ta buɗe kuɗin da ke rungume a ƙirjinta.Sai ta rufe shi tare da sake kallon Ummilo cikin wani irin yanayi ,kamar wacce ba ta son taka ƙasa haka ta ƙaraso tare da yin tsaye. “Ranki shi daɗe ga ni na samu saƙonki ne a yanzu” ta faɗa cike da ladabi,sai kuma na ji babu daɗi yadda ta zubar da duk wata dangantaka da ke tsakaninmu ta bani matsayin shugabarta. Da ido na yi mata nuni da ta zauna,ta cire takalminta na fata ta zauna tare da maida hankalinta a gare ni. “A cikin tarihi wace ce aljana zaƙuma?” “Aljana ce mai matuƙar santsi da farin fata,tana ɗauke da kambun Maitar shan jini.Lokutan da ta fitowa shi ne dare musamman wuraren jeji ko kusa da rijiya.Tana jan hankalin mazaje musamman maharba don su ne suka fi shiga jeji,tana fitowa cikin siffar barewa haka za ta yi ta wasa da hankalin maharbi har sai ya faɗa tarkonta sai ta ja shi izuwa duniyarta” Deborah ta faɗa tana mai buɗe littafinta sai ta nuno mini hotonta,kallo ɗaya na yi masa na kawar da kai.Sosai ta fito a siffar mayyar shan jinin kuwa don bakinta kaca-kaca yake da jini. “Kika ce maharba sun fi shiga tarkonta ?” na tambaya. “Eh haka tarihi ya zo da shi” “Meke faruwa bayan ta kama mutum?” “Tana kai shi wani kogo ne,sai ta basa zaɓi biyu.Na farko zai bauta mata,in kuma ya ƙi zaɓi na biyu shi ne za ta kashe shi” Ummilo na duba ina mai cewa “dukkan alamu sun nuna ita ce ta zo yau don har yayyafin jini aka yi” “Hakan na nufin tana son jan ra'ayin wasu mazajen ne ,don haka mu zama cikin shiri” Ummilo ta faɗa . Deborah ta girgiza kai tana mai cewa “ Aljana ZAƘUMA ba ta taɓa bayyana a wurin da ba a ambace ba ko kuma sunan ɗaya daga cikin waɗanda ke baƙin tsafi da ita.Tun da kuka ga ta zo to tabbas a garin nan akwai mai yin aiki da ita” Da wani mugun sauri na dube ta,a cikin ƙwayar idonta na hango tana zargin mijina Banah da wannan ɗanyen aikin.Ban san me ta gani ba ita a nawa idon sai ci gaba ta yi da cewa “ta yiyu kuma wucewa ne kawai ta zo yi,don haka za ki iya yin watsi da lamarin mu gani in za ta sake dawowa” Numfashi na furzar tare da jinjina kai,Ummilo ta karɓi littafin tarihin tana mai cewa “ina mugun son labarun tarihin ƙarnin da ya wuce musamman a kan maita,shin a page lamba ta nawa ce zan samu tarihin Mayu da kuma yadda suke rikiɗa daga bil'adama zuwa dabbobi?” Deborah na shirin yin magana Banah ya shigo hannunsa riƙe da manyan kifaye,da dukkan alamu kuma ya ji tambayar da Ummilo ta yi duba da yanayin yadda fuskarsa ta cika da tsantsar mamaki. “Jira na zo na fayyace miki komai Ummilo ” ya faɗa yana mai miƙawa wata hadima kifin ya zo kusa da ni ya zauna sannan ya karɓi littafin tarihin ya mayar wa Deborah da kayanta sannan ya kamo dukkan hannuwan Ummilo ya ce “a duk lokacin da mutum yake son rikiɗa zuwa dabba da farko zai ɗan rage tsayi sannan ya furta kalaman tsafi yana mai tsayar da ƙwayar idonsa wuri guda ba tare da ya ƙyafta ba.Bari na nuna miki ta yadda za ki gane sosai” sai ya saki hannuwanta tare da yin tsugunne ya soma magana a hankali amma duk muna iya jiyo sautin.Cak kuwa ya tsayar da idonsa suka bar motsi,babu jimawa ya koma narkeken kare baƙi ƙirin yana wani fito da harshe waje. Duk da ni ma yau ne karon farko da na ga canjin siffa sam ban ji wani tsoro ba sai ma burge ni da lamarin ya yi na soma yin murmushi. Cikin firhici Ummilo ta furta “ Ya Ubangijin Ka'aba ka tseratar da ni daga sharrin wannan halittar” sai kuma ta soma yin ihu tare da tashi za ta zuba a guje,ni da Deborah muka yi saurin taro ta yayin da Banah ya yi baya yana haushi cikin hassala. Hakan da yake ba ƙaramin ƙara firgita ta ya yi ba,ni kuma lura da hakan yasa na juya na yi masa tsawa sai a lokacin kawai ya dawo cikin siffar bil'adama. Ummilo ta soma furzo wani zance “kar ki cutar da ni Ummu A'ishah ki sani ban taɓa aikata maita ba,wacce ke maƙale a ruhina ba sayenta na yi ba kyauta ce daga wasu ruhikan da ke zuwa mini cikin MAFARKI (MRS SADAUKI akwai littafin nan na MAFARKI complet mai so zan barsa shi a 700 maimakon 1k) .Ban so ki bari in ba haka ba zan tona miki asiri na faɗa kowa ya sani ke ce mai yin Maitar dare” tana kawowa nan sai numfashinta ya tsaya cak sai da muka tallabe ta tare da shimfiɗe ta. Deborah ta ce “ da dukkan alamu ita ma ta fito a yanki da ke maita duk da dai a yadda take furuci Maitar ba ta yi ƙarfi ba.Sannan ita wannan Ummu A'ishar tana ɗaukar siffar kare ne a duk lokacin da za ta yi maita ” Banah ya matso yana cewa “ai da na san haka ne da na ɗauki wata siffar,amma sam ban yi haka da wata manufa ba” Na ce “kar ka damu na fahimta,daga yau sai ka kiyaye” ya jinjina kai. Deborah ta ce “ni zan koma,in ta farka ki ce ina yi mata sannu da jiki” haka muka rabu. ★ Yarima NASLAM ne kwance yana yin bacci yayinda tantabarsa ke tsaye ƙiƙam tana kallonsa sai da ta gaji don kanta kafin ta ɗaga fukafukinta ta je ta sa ƙafafunta ta ciro shi sama tare bi ta window da shi ta fita.Haka ta dinga zaga duniyar ɓoye da shi yana cikin wani yanayi wanda shi ba bacci yake yi ba kuma idonsa ba a farke ba. Cikin wani jeji mai cike da dragon ta sake shi ,shuuu yayi kamar zai faɗi amma sam jegaran ba su bari hakan ta faru ba haka suka buɗe fukafukinsu wuri ɗaya ya faɗo a sama. Kafin kuma su kai shi kan wata lafiyayar shimfiɗa da aka yi da ganyen furen floris. Yarima NASLAM ya ja wani dogon numfashi tare da ɗan ware idonsa,nan ne ya yi arba da sarauniya Naomi cikin shigar ganye,ta rufe ƙirjinta da fatar lemun zaƙi kugunta kuma ta suturta shi da bayan albasa.Gashin kanta kuwa ya ci ado da ganyen lemu,tafiya take yi cikin yanga da jan hankali har ta zo gare shi.Kan shikinsa ta kwanta tare da yi masa rumfa kafin wasu lamurra su biyo baya waɗanda suka kusan sheƙa shi lahira.Yana gama samun nutsuwa ya farka daga baccin,a kan shimfiɗarsa ta asali ya samu kansa ƴar tantabarsa na can gefe tana bacci. Ya dafe kansa yana jin wani irin takaici na rufe shi,saboda shi babu wacce ya tsana irin aljanar mafarkinsa.A gajiye kamar wanda yayi mu'amalar a gaske ya ƙoƙarta ya tashi tare da shiga toilet,sai dai fa babu ruwa ba ciki babban bokitin ruwan ba.Ya ja tsuki ya fito kafin ya soma ƙwala kiran sunan jakariya Ali,dama ɗakinsa yana kusa da nasa babu jimawa kuwa ya shigo hannunsa riƙe da sharɓeɓiyar takobi duk a tunaninsa farmaki ne aka kawo musu. Turus yayi ganin iya yariman ne kawai a ɗakin,ya yi saurin ajiye takobin yana mai cewa “ranka shi daɗe me kake buƙata?” “Babu ruwa a banɗaki” yarima ya faɗa yana jin ƙyanƙyamin kansa,da sauri jakariya Ali ya fita babu jimawa ya dawo jaye da baro an lodo ruwa a ciki.Banɗakin ya shiga ya juye ruwan kafin ya fito,sai a lokacin yarima ya shiga sai ya ga hatta bahon wankan Ali ya cika masa shi da ruwan. Kwanon da ake zuba ruwa a ciki domin yin alwala ya ɗauka ya soma wanke hannunsa sau uku bayan ya ɗauki niyyar wankan.Daga nan yayi ɗahara sai ya wanke kansa tasss kafin ya game jikinsa duka,daga ƙarshe ya kurkure bakinsa ya kuma yi shaƙar hanci.Sai a lokacin kawai ya ji nutsuwa ta ratsa shi sai ya shiga bahon wankan ya kwanta a ciki,tunanin gimbiya A'ishah yake son yi amma da zarar ya fara cankar surarta sai fuskar Naomi ta zo ta yi fakan-fakan a dole ya haƙura ya fito ya ɗaura alwala ya zo ya fara yin sallar nafila. A ɓangaren gimbiya A'ishah kuwa tsakiyar dare Dadda ta tashe ta,tana shirin yin magana amma Dadda ta toshe mata baki tare da janta suka je bakin window suka yi tsaye suna fuskantar farin wata da ke wasar ɓuya cikin giza-gizai. Dadda ta soma yin magana a hankali tana cewa “a wurin Mayu dare shi ne lokaci mafi tsaro domin farauta,duk da cewa ana iya sarrafa maita safe ko rana amma irin wannan lokutan an fi yinta a cikin siffar bil'adama yayin da ita kuma ta dare ake ɗaukar ɓoyayyar siffa.Yau zan nuna miki romon da muke sha duk dare ni da sauran Mayu na wannan Daular ” Cike da mamaki gimbiya A'ishah ta ce “dama bayan ke akwai wasu Mayu a cikin daular nan?” Dadda ta yi wani irin murmushi kafin ta ce “idonki za su yi matuƙar mamaki in ki ka ga wasu mutanen” tana gama faɗar haka sai ta jimƙe hannun gimbiya A'ishah tana furta wasu surkulle nan take suka sama wasu ƴan ƙananu kamar sauro tare da tashi sama suka bi ta window..... Za ku iya fara yin payment domin shiga paid group . 500 ta wannan account: 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank Shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 [12/04 19:22] MRS SADAUKI: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐 """"""""""""""""""""""" LoVe aNd HoRrOr StOry☠️ ```MRS SADAUKI```💫✍️ FCWA☀️ ____________________________________________ 09 Yana ɗaya daga cikin tabi'un Mayu yin yawon dare a lokacin da mutane ke yin bacci,saboda babu dare yana ƙunshe da sirrika dayawa.Gimbiya A'ishah baki da hanci ta buɗe tana kallon duniyar ƙasa,cike kuma da burge wa da ban sha'awa take ware idonta tana kallon gidajen da aka rufe babu bismillah.Kamar misalin tukunya ce babu murfi,haka idon Mayu ke gane gidajen da ba a ambaci sunan Allah ba a lokacin da ƙafa ta tsana za a kwanta. Suna cikin shawagin suka yi ta haɗuwa da jiragen dare na Mayu, waɗanda suka kasance na tsafi ba wai zahiri ba. “Duk ina za su je Dadda? Ya na ga mutane cikin gwangwanin kifi?” gimbiya A'ishah ta tambayi mahaifiyarta sai dai kafin ma ta bata amsa wani jirgin na tsintsiyar tsaye ya bi ta gabansu shuuu yana ɗauke da wata tsohuwa da kuma ƙaramin yaro. Dadda ta yi murmushi tana mai cewa “A'ishah a duniyar ɓoye abubuwan da ba za su taɓa faruwa ba ne a duniyar zahiri suke gudana a nan ɗin.Muna amfani da duk wani abu da kika sani matsayin jirgin farauta,kamar irinsu turmi,jan zanen isimi,tsintsiyar tsaye da sauransu.Ke ma in kina sha'awa ai za ki iya hawa madadin ki yi yawo kamar leda” “To mene ne banbancinsu Dadda?” “Sauri! In kin hau jirgi kin fi saurin zuwa inda kike so,ko ba ki lura yadda mutane ke ta wuce mu ba?” “Na gani,amma me yasa mu ba mu shiga ba?” “Dama ina son fayyace miki komai ne,amma yanzu da zarar wata tawagar mayun za ta wuce zan tsayar da su don rage mana hanya” Ai kuwa babu jimawa sai ga wata tsohuwa zaune kan baƙar akuya mai ƙahonni dogaye.Dadda ta tsayar da ita tare da neman alfarma,tsohuwar ta ƙara matsawa gaba gimbiya A'ishah ta fara hawa sannan Dadda daga ƙarshe.Kamar wani babur haka akuyar tsafin ke keta hazo da su. Gimbiya A'ishah wacce duniyar ɓoye take sabuwa a wurinta sai cewa ta yi “ita ma akuya tana cikin jerin jiragen yawo?” Wannan karon tsohuwar ce ta bata amsa bayan ta yi ƴar dariya mai fitar da zallar tsufanta,ta ce “ jikata ita akuyar nan protector ɗina ce,suna da banbanci da jirgin dare saboda ita tana numfashi sannan kuma tana kare ni daga dukkan sharri” gimbiya A'ishah ba ta kai ga cewa wani abu ba tsohuwar ta yi ƙasa da ƙahonnin akuyar sai ta yi shuuu ta fara yin ƙasa har ta sauka a wani babban gawo wanda ya cika tanƙam da Mayu da kuma matsafa. Girki ake yi kan wata tunkunya wacce ke da zanen ƙwarangwal ta buɗe baki.Gimbiya A'ishah ta sauko daga kan akuyar tana wani riƙe Dadda ,ita kuwa sai cewa ta yi “ wannan ita ce TUKUNYAR MAYU ( ga mai son complete na Tukunyar Mayu yayi mini magana zan yi masa discount) duk dare muna haɗuwa a nan mu ci abin da wasu daga cikinmu suka yo farauta” Sai kuma Dadda ta ja ta suka ƙarasa,hannu ta saka cikin tukunyar da ke ta faman tiriri ta tsamo wani abu mai kamar zare amma su a wurinsu nama ne,bakin gimbiya A'ishah ta kai ita kuwa ta buɗe ta saka mata sai ta soma ci tana jin wani irin yanayi na ratsa ta. Dadda ta saki murmushi tana jin wani sanyi na luluɓe ta,a yanzu shirye take tsaf wurin tursasa ƴarta ta auri yarima Naslam ba don komai ba don ta san a cikin tabi'ar Mayu babu kara babu jin kunya,hatta uwar da ta kawo su duniya suna iya damƙewa ita kuma babban burinta shi ne ta bayar da yarima NASLAM a dafa shi kowa ci kamar yadda yasa aka yanke wa Ummarta hukunci kisa daga kawai asirinta ya tonu ta damƙe kurwar iyayen jakariya Ali. Bayan sun gama cin naman sai idanun gimbiya A'ishah suka ƙara buɗewa ta soma gani tarau ,babu abin da ba ta iya gani da ke jikin mutum ko dabba.Rawa suka soma yi suna zagayen wuta,duk da mutane sosai hakan bai hana ta gane wasu fuskokin ba sosai kuma ta yi mamaki kamar yadda Dadda ta ce mata tun kafin zuwansu. Alfijir na dab da ketowa suka koma gida,ta inda suka fita ta nan suka shigo.A gajiye duk suka zube suka ta yin rankon baccin da ba su yi ba. A ɓangaren yarima Naslam kuwa tun bayan sallar asubah ya je ya samu sarki da maganar aurensa da gimbiya A'ishah.Ya yi haka ne duk don ya bar mafarkin Naomi,ba tare da ya san alƙaluman ƙaddara sam ba su rubuta masa auren wata mace ba bayan maƙiyiyarsa. Gari na yin haske sosai sarki ya bada shelar baikon yarima zai kasance a yau bayan sallar asar in sha Allah. Jakariya Ali ne ya dinga taimaka masa wurin shiryawa,yana daidaita masa hullar sarauta a kai ya ce “kana ganin kun dace kai da gimbiya A'ishah?” “Me ya ja ra'ayinka wurin yin wannan tambayar?” cewar Yarima yana kallon mai tsaron lafiyarsa Ali . Shi kuwa kai tsaye ya ce “na ga ba sonta kake yi ba” “Haka kuma ban ƙinta“ “Duk da haka dai ya kamata a ce ka yi dogon nazari,na fi yi maka sha'awar auren soyayya gaskiya” “Ita ma ina sonta tun da har na damu da ita” yarima ya faɗa yana mai zuwa bakin gado ya yi zaune,jakariya Ali ya duƙa ya soma saka masa takalmi yana mai cewa “in kana son mutum bai kai sai ka faɗa ba,ayyukanka ne za su bayyana hakan” “Ko ma dai mene ne na yanke shawarar zan aure ta,kuma ta dace da ni tun da tana da addini sosai iya wannan ya wadatar” yarima ya faɗa yana tsayar da idonsa kan tantabarsa wacce ta yi wani saƙo kamar mai sauraren hirar da suke yi. Jakariya Ali ya juya ya dubi inda yake kallo,sai ya saki ɗan murmushi kafin ya je ya ɗauko ta ya miƙawa yarima.Ya karɓa tare da soma shafar kanta,“zan je na duba na gani in sun gama shirya wurin taron” Ali ya faɗa tare da ficewa. Yarima ya miƙe tsaye tare da zuwa bakin window yana kallon yadda ake ta kai komo cikin masarautar.Ko ina yayi kyau,hatta dawakai an yi musu ado na sarauta .Dokinsa wanda yake hawa a duk lokacin da zai fita yayi wani irin kuka,tantabarar hannunsa ta fizge tare da fita a guje tana kaɗawa yarima iskan fukafukinta da sauri ya lumshe ido kafin kuma ya ware su yana kallon yadda ta je ta hau kan dokin,duk wannan ɗin ma bai sa ya zargi wani abu ba kawai murmushi ya yi tare da fita. Masjid ya fara zuwa,bayan an gama sallah ne duk aka dugunzuma zuwa wurin da aka ware domin gudanar da shagalin bikin baikon. Zinare sarki ya ware masu yawa ya bayar matsayin kyautar mun gani muna so.Ayyub wanda ya kasance mahaifin gimbiya A'ishah da matuƙar farin ciki ya shaida wa dukkan taron jama'ar ya bai wa yarima damar auren ƴarsa,duk sai aka yi kabbara tare kuma da yin addu'o'i kafin a fita zuwa can inda za a yi wasar dawakai. Ta madubin tsafi Dadda ke kallon komai,tun lokacin da aka yi shelar yin baikon ta shirya baƙin tsafi mai ƙarfi ta tura domin hallaka yarima.Ita dai gimbiya A'ishah cike take da farin ciki duk gajiyar nan ta jiya sai ta neme ta duk ta rasa,duk da cewa kuwa ta sha bacci sosai sai wuraren goma na safe ta farka.A bakin mahaifiyarta kuma ta ji abin da ke faruwa,sosai ta so a ce ta fita ta ga yadda komai ya wakana sai dai hakan haramun ne a masarautarsu zuwan mata a irin wannan taron. Cikin rangaji ta ƙaraso ta zo ta yi tsaye ita ma tana kallon yadda ake wasar tseren .Wani irin murmushi ya suɓuce mata lokacin da ta ga yarima Naslam ya je kusa da dokinsa za su yi wasar tseren shi da wanda ya yi nasara akan dukkan dakarun da aka tsara wasar da su.Ita ma Dadda nata murmushin ta saki tana jin cewa saura ƙiris burinta ya fara cika don ta jefa kibiyar tsafi akan dokin yarima saboda in ya hau shi sai ya masakance. Yarima ya hau kan doki yana mai ambaton sunan Allah tare da yin kabbara,Dadda ta ɓata fuska tana mai ɗan satar kallon gimbiya A'ishah wacce har yanzu murmushi ya ƙi barin fuskarta. “Dadda dube shi ki ga yadda yake da ƙwarjini da cikar zati, wannan shi ne mijin A'ishah ” “Haka ne ki yi fatan Allah yasa ya ci gasar kar ya kwabsa abin ya zama abin goranta miki” Dadda ta faɗa tana mai shafar madubin haɗi da yin wani surkulle daidai nan su yarima suka fara gudun.Ƙafar dokin ta ƙure da ido ta na shirin aika masa wata gubar tsafin kawai sai ganin bakin tsuntsuwa ta yi ya caki madubin ya tarwatse. A tare suka ja ba,kafin su kalli juna.Da wani irin gudu kuma gimbiya A'ishah ta fita don jikinta ya bata babu lafiya,mayafinta ta ja ta rufe fuskarta lokacin da ta isa filin sukuwar. Yarima NASLAM wanda ya lashe wasar tseren dokin ya juyo yana kallon inda take a tsaye,suka haɗa ido da sauri ta sunne kai tana wani murmushi kafin ta juya da sauri ta koma.Ya ja numfashi yana jin a ransa ya yi dacen mata. ★ An ɗauki tsawon lokaci kafin Ummilo ta farfaɗo wannan karon ma tana yin wasu kalamai a cikin Yaren da ban fahimci me take nufi. “Alhamdulillahi lazhi ahayana ba'ada ma'amattana wa'ileyhi nushur” ta furta tare da ware idonta a kaina,na sakar mata murmushi na ce “sannu Ummilo” ba ta amsa ba sai martanin murmushin da ta maido mini tana mai shafar gefen fuskata kafin kuma ta miƙe ta fita.Haka na take mata baya sai na ga ta shiga banɗaki,can kuma ta fito ta soma wanke hannuwa da baki da fuska da hannuwanta hatta kai da kunne sai da ta shafa haɗi kuma da wanke ƙafafu. Mayafinta ta gyara kafin ta zo ta fara yin wata irin bauta da ban san ta mece ce ba,ni dai ido kawai na tsura mata da na ga ba ta da niyyar idawa kawai na je gun baby Mila na ɗauke ta dama tun ɗazu ta tashi.Madara na soma bata tana sha tana kallona cikin ido, murmushi na saki ina jin sonta na ratsa ni. Banah wanda tun bayan abin da ya faru ya koma can ƙofar gida yayi tsaye,sai yanzu ya shigo yana mai tambayata “mene ne can Ummilo ke yi?” “Ina kifin har yanzu ba a gama dafawa ba?” na tambaye shi ,don sau tari in yayi mini tambayar da raina bai so ba nuna masa nake yi kamar ban ji ba sai na ɗauko masa wani zancen. Fita ya yi ba tare da ya ce mini komai ba,can kuma sai ya dawo riƙe da kwano yana tiriri.Kamshin kifin ya daki hancina,nan take yawuna ya tsinke sai na shimfiɗe Mila na karɓa na soma ci shi kuma Banah yana aukin kallona.Ina gama ci na ji wata kasala ta rufe ni,sai na kwanta ni ma sai a lokacin kuma Ummilo ta shigo. Banah ya ce “ga kifi nan da Naomi ta rage ki ci” Da fara'a kuwa ta karɓa tare da gyara zama ta sa hannunta,sai dai fa ta gagara ci sai yamutsa fuska take haɗi da yunƙurin kai shi bakinta.Can dai ta haƙura tare da ajiye kwanon tana mai girgiza kai ta ce “in na ci wannan ai tamkar na cinye kaina ne,a'a sam maita ai ba hauka ba ce da zan ci jinsina ” Banah ya ƙanƙance ido yana kallonta kafin kuma ya fice ya bar mu.Maƙoshina ne na ji yana wani irin zafi kamar ana hura wuta,murya kamar ta mai koyon magana na ce “Ummilo sanyi nake ji ki rufe ni” sai kuwa ta miƙe ta ɗauko bargo ta luluɓa mini.Daga wannan kwanciyar ban ƙara farkawa ba sai washegari da zakara ya fara cara,na buɗe idona da suka yi mini nauyi kafin na yunƙura zan tashi sai dai na kasa sakamakon bayana da na ji ya riƙe kafaɗata ta ƙara nauyi. “Banah?” na kira sunansa kasancewar ni da shi ke kwana a ɗaki ɗaya,Ummilo kuwa cikin jerin ɗakunan da aka yi daga baya take kwana ita da Mila. Shiru ban ji motsinsa ba,sai na ƙara yunƙurin tashi a wannan karon gangar jikina ta baro shimfiɗar sai dai na gagara tsayuwa kan ƙafafuna na faɗi kwacaaa.Jeren kwanukan da ke ɗakin duk ya baje,ƙarar ta jawo hankalin Ummilo ta shigo tana tambayar lafiya sai dai muna haɗa ido da ita ta ɗau haske.Da sauri ta zo ta taimaka mini na miƙe tsaye tare da riƙe ta gam,murya na ɗan rawa na ce “ki kai ni banɗaki na yi wanka” ita ce ta kai ni,sannan kuma ba ta fito ba sai da ta yi mini wanka.Bayan ta saka mini kaya sai ta miƙo mini wani icce ta ce na riƙe,na karɓa ina jin ƙusumbina da ya ƙara girma ya rinjaye ni na yi mini wani motsi..... My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 [13/04 09:45] MRS SADAUKI: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐 """"""""""""""""""""""" LoVe aNd HoRrOr StOry☠️ ```MRS SADAUKI```💫✍️ FCWA☀️ ____________________________________________ Daga yau discount ya ida. Last free page 10 Wata rusunawar dole ce ta zo mini saboda girman ƙusumbina ya wuce a yi kwatance sam tsayuwa ko tafiya babu sanda ba zai yiyu a gare ni ba.A haka na fito daga banɗakin ina jin wasu canje-canje na daɗa ƙaruwa a jikina,ban zame ko ina ba sai a ƙofar gida inda mutane birjit ke a wurin dukkansu kuma a ƙarƙashin ikona suke.Tamkar sun ga ubangijinsu haka duk suka tsaya da abin da suke yi suka zube ƙasa tare da yin kwanciya suna yi mini wani irin kirari da ba a taɓa yi mini shi ba.Idona na ƙanƙance ina kallon Banah da ke can ɗan nesa da ni yana wani irin murmushi da ban san mene ne ma'anarsa ba,don ko kaɗan ban zargi cewa a cikin kifin da ya bani na ci ba ne wannan girman ƙusumbin ya ƙaru. “Sabbin dokoki sun sauka,don haka al'ummar gari ku kasance cikin shiri ga dukkan abin da shugaba za ta zartar” Banah ya faɗa yana mai takowa yana doso inda nake hannunsa riƙe da kwari da baka. Sai da ya zo dab da ni sannan ya saita kibiyarsa a sama yana mai furta ɗalasiman tsafi,ji kake shuuu kafin wata wuta ta baje a sama.Babu kuma jimawa sauran jama'ar gari suka fara ɓullowa ta kowace kusurwa,tuni wurin ya ɗauki harama ya cika tanƙam.Sai kuma a lokacin ne na soma yin magana,“daga yau an zartar da yin hadaya duk ƙarshen mako,ruhikan ruwa su ne ke da alhakin zaɓar wanda suke so ko dai mu ɗauke shi mu bayar ko kuma su da kansu su kira mutum zuwa can domin ɗaukar ransa.Abu na gaba shi ne duk wani jinjiri da za a haifa sai an kai shi bakin kogo uwa gijiya ta saka masa albarka tare da ƙa'ide masa adadin shekaru ko watannin da zai yi a duniya” Yanayin fuskokinsu duk sun nuna ba su ji daɗin wannan sabon tsarin ba,sai dai babu wani mai zarrar yi mini magana duba da irin ƙarfin ikon da ya ƙara hawa kaina ba tare da ni kaina na shirya masa ba. A haka aka watse na koma ciki na tarar da Ummilo a zaune ta yi uban tagumi.Tana ganina ta miƙe tsaye tare da nufo ni,“na tuna wace ce ni ” shi ne abin da ta furta mini.Cike da jin daɗi na ce “kin tuna? Kai wannan babban abin farin ciki ne amma ya na ga ba ki murna?” Idonta ya kawo ruwa tana mai cewa “na fito a yankin da aka haramta maita da kuma tsafi,ba tare da shuwagabannin sun yi la'akari cewa ba babu wani babban tarihi da magabatanmu suka shuɗe suka bari kamar Magic,ita Maitar ma ba ta fiya ƙarfi ba. Surukina kafin mutuwarsa ya yi matuƙar ƙoƙarin wurin ganin ya daƙile duk wata baƙar shirka,sai dai abin takaici Mayun ne suka haɗin gwiwa wurin kai shi barzahu.Wannan ya fusata mijina har ta kai shi da yin wani tsari shi ne kafa masarauta,yasa an gina babban wuri tare da yin shelar duk wanda ya shirya karɓar addinin gaskiya to ya shigo a cikin sabon ginin da aka yi.Ta wannan hanyar ce aka yi walƙiya aka gano mayu da matsafan cikinmu,sai ya soma yaƙarsu har ya yi nasara a kansu.Sai dai abin da bai sani ba ita maita bibiyar jini take yi,ga shi dai ya kashe tushenta amma bai cire inda ta yabanya ba.Sannu a hankali lokaci na tafiya mace-mace ya fara yawaita a daular,a bisa binciken wani mai bayar da magani ya gano cewa cutar maita ce sai kuma aka ƙara ƙarfafa tsaro.Tun ana yi wa mutum afuwa in an kama shi da cutar maita har aka zo zamanin yarona inda ya yanke ɗanyen hukuncin cewa duk wanda aka kama da laifin maita ko tsafi kisa ne kawai” tana kawowa nan ta yi shiru tare da kamo ni tana cewa “zo ki zauna hakan za ki gaji sosai,ya kamata ma Banah ya nemo miki sanda mai kyau” Kan kujerar da aka sassaka da icce ta zaunar da ni kafin ta ci gaba da bani labarin. “Mahaifin matar ƙanen mijina shi ne mutum na farko da ɗana ya fara cirewa da hannunsa saboda laifi mafi muni da ya aikata ya kashe mahaifan hadiminsa wanda ya ɗauka tamkar amininsa.Ƙarfin wannan raɗaɗin ya saka ita kuma matar ƙanen mijin nawa ta ɗauki tsanar duniya ni da ɗana ta ɗora mamu” nan ɗin ma shiru ta yi tana kallona tsakiyar ido da dukkan alamu akwai wani sirri mai nauyi da take son sanar da ni wanda baki ba zai iya furtawa ba. Ta idonta kuwa ta shaida mini cewa “ni mayya ce! Ina ɗauke da kambun Maitar prophecy” sai kuma ta yi saurin janye idonta daga cikin nawa kafin ta je da sauri ta shige ɗakinta.Na lumshe idona tare da buɗe su kafin na yunƙura dakyar ina dogara sanda na take mata baya. A zaune na tarar da kan shimfiɗarta,na ajiye sandar hannuna ni ma na zaune tare da kamo hannunta.Sai ta ɗago ta dube ni tana wani irin murmushi da ya fi kuka ciwo kafin ta ce “ban taɓa yin maita ba,ban taɓa cin ɗan wani ba kawai dai abin da na sani wani lokacin ina rikiɗa na zama kifi a irin haka ne har ita Dadda ta ganni cikin wannan siffa shi kenan ta je ta sanarwa sarki ai ni ma mayya ce.Ba tare da maganar ta fita waje ba aka titse ni sai na faɗi gaskiyar magana,in kuma na yi shiru na ƙi faɗa gobe gaban al'ummar gari za a yanke mini hukuncin kisa bayan an tabbatar shi ne kawai na yanke shawarar bin dare na gudu.Amma duk da haka bai ishi Dadda ba sai da ta jefe ni da baƙin tsafi ta haukata ni” Na ce “don me yasa kika gudo kika bar ahalinki? Me yasa ba ki zauna ba ki sanar da su babu wata baiwa a duniyar nan da ta wuce maita? In ma ba ki son a sani ai sai ki ɓoye kayarki ” Kai ta girgiza mini tana mai cewa “akwai wani garin magani da ake shaƙawa mutum a hanci muddin yana da ɗigon maita a jininsa to zai bayyana cikin ɓoyayyar siffarsa ne ya dinga tonawa kansa asiri” Na ja dogon numfashi kafin na ce “shi kuma yaronki fa,kin yi tunanin halin da zai shiga bayan tafiyarki? Me yasa ba ki taho da shi ba?” Wani murmushi ne wannan karon ya suɓuce mata bai bayyanar da tsantsar farin ciki da dukkan alamu tana mugun son ɗan nata.Ta ce “Ba fa yaro ne ƙarami ba,ko a lokacin da na bar masarauta ya haura talatin da ɗaya kawai dai a idona ne nake ganinsa ƙanƙane” “Me sunansa?” Kai ta girgiza cike da kunya tana mai cewa “a al'adarmu ba mu faɗar sunan ɗan fari, wannan yasa na yi masa laƙabi da Noor” Samun kaina na yi ni ma da yin murmushin kafin na ce “me Noor ɗin ke nufi?” “Haske!” ta bani amsa. Na ce “zan so na gansa kuwa,da na ji daɗi sosai ni ma zan yi babban yaya” ina faɗar haka sai ta ɗan ƙara matsawa ta jawo kaina ta ɗora kan cinyarta,sai ta cire luluɓin kaina ta soma warware manyan kitson kaina tana mai cewa “wata rana za ki gansa ai ” “Yaushe kenan?” “Ranar da lokacin komawa ta can ya yi,ai zan tafi da ke ne ki ga yayanki in ya so sai Banah ya tsare miki daularki ” Shiru duk muka yi,bayan ta gama warware kitson sai kuma ta ɗebo ruwa ta zuba yaɗo ta wanke mini dogon gashina sannan ta ƙara yi mini wani kitson mai kyau duk da ƙwaya biyu ne kacal amma ya yi kyau.Wunin ranar ne muka ƙara yin wata shaƙuwa ta musamman ni da Ummilo ta dinga bani labarin Yaya Noor lokacin da yana ƙarami da kuma abubuwan da yake so da waɗanda ke saurin saka shi fushi. “Wane abinci ya fi so?” na samu bakina da tambaya. “Gurasa da zuma,yana matuƙar son cin gurasa yana dangwala ta a cikin zuma” ta bani amsa tana murmushi. Na ce “ni ma ina son zuma,kullum in na je farauta sai na je na nemo ta na sha” “Wato yayanki kika ɗauko wajen son zaƙi.Bani labarinki,ina iyayenki suke?” Ummilo ta faɗa . Wani iri na ji duk babu daɗi kafin na ce “dukkansu sun mutu,shi Abbana ban san shi ba ita kuwa Maa a ranar da na karɓi prophecy ɗina ta yi gushewa.Ina sonta sosai,ina jin kewarta a kodayaushe samunki ne ya maye mini gurbinta nake jinki tamkar ke ce ita” na ƙarashe faɗa hawaye na silalo mini masu zafi.Na ƙanƙame ƙafar Ummilo ita kuwa ta shiga shafar kaina haɗi da rarrashina kafin ta ce “ina matsafiyar tarihi sai yaushe za ta zo?” “Ta ce na yi miki sannu da jiki ma tun jiya ” “Ina amsawa,ina ne gidansu?” “Ita ma ba ta da iyaye mahaifinta ya rasu,mahaifiyarta kuma an damƙe ta” “Ayya ki ce ta dawo nan wurina sai mu zauna tare” Ummilo ta faɗa ,sam ban ji zan iya yi mata muso ba hakan yasa ba tare da na shawarci Banah ba na ƙara aika saƙon wasiƙar tsafi zuwa ga Deborah ba ta kuma ɓata lokaci ba ta zo har da ƙullin kayanta.A ɗakin Ummilo na yi mata masauki ,a ɗan wunin da muka yi a tare sai kuma muka ƙara ɗinkewa ni da ita muka manta mun taɓa samun saɓani. Da dare muna zaune bayan mun gama cin abincin,Ummilo na ririga Mila da ke yin rigima ta ƙi yin bacci sai ta soma rera waƙa wacce ta saka mu duk nutsuwa.Ba da Yaren da muke magana ba ne,haka kuma ba Yaren tsafi ba ne wani yare ne can daban da ita kaɗai ta san ma'anarsa amma sosai na ji daɗin baitin.Babu jimawa Mila ta yi bacci sai ta shimfiɗe ta tana murmushi tare da cewa “a duk lokacin da Noor ya fitine ni da kuka wannan waƙar nake rera masa ko kuma in ina son saka shi bacci” "Amma Ummilo da wane yare ne wannan?” na tambaya,Deborah da ke rubutu cikin littafin tarihi ta yi karaf ta bani amsa da “Yaran serena ne,yare ne da halittun ruwa ke yi ita kuma waƙar suna yinta ne domin janyo wani ruhi zuwa gare su domin aiwatar da abin da suke buri” Ido na tsura mata ina kallonta ta hasken farin wata,kafin na ce “ ta ya aka yi kika sani?” “Ta ya ba za ta sani ba,matsafiyar tarihi ce fa” Ummilo ta faɗa . Deborah ta yi murmushi tana mai cewa “tun jiya da na yi tozali da Ummilo na cika da mamakin me ya kawo Siren a nan” Na ce “ai na lura da yanayin yadda kike kallonta,to sai da safenku zan je na kwanta” na faɗa tare da lalubo sandata na miƙe na shiga ciki. Kan gadona na kwanta tare da yin shiru ina nazari,can sai ga Banah ya ratso rufin ɗaki ya shigo.Sam hakan bai kuma bani mamaki ba,illa kawai na mujiya da na zuba masa ina kallon yadda jikinsa ya ƙara rinewa kamar wanda ya fito daga cikin rijiyar kunama. Gefen gadon ya zauna tare da miƙo mini wata ƴar kwalba ya ce “shafa mini” ba tare da na miƙe daga kwancen da nake yi ba na karɓa na soma shafa masa sannu a hankali tiririn dafin jikinsa ya soma disashe ganina. ★ Da dare bayan gama bikin baiko sai aka zauna kan teburin cin abinci.Yarima NASLAM ne da dakarunsa masu taya shi yaƙi,suna cin abinci suna raha yayin da shi kuma yayi shiru yana ta juya gurasar da aka ajiye a gabansa ya kasa ci.Jakariya Ali da ke gefensa ya ce “bari na nemo maka zuma in ba za ka iya ci da markaɗaɗen yaji ba” Ya ɗago ya dube shi tare da yin murmushi kawai, Jakariya Ali ya fita zuwa madafa bai wani sha wahala ba don ya tarar da masu aikin kula da abinci ita ta miƙo masa zumar ya karɓa kafin ya zo ya kawowa yarima. Cikin ƙarfin hali yarima Naslam ya karɓi zumar ya soma dangwala gurasar a ciki ya kai bakinsa,sai dai ko kaɗan bai ji wani ɗanɗano ba.Gudun kar ya ɓata wa kansa lokaci sai ya ture abincin, Jakariya Ali ya dube shi cike da mamaki yana shirin yin magana yariman ya miƙe ya nufi ƙofa sai a lokacin ne kuma Ali ya hango baƙin tambarin maita ya fito yau a bayan wuyan yarima Naslam.Cikin bugawar zuciya shi ma ya miƙe ya fita,bai zame ko ina ba sai gidan Barham.Kamar zai ɓalla ƙofa haka yake bugunta,Barham ya buɗe yana mai kallonsa da mamaki yake cewa “lafiya dai ko?” Sai da ya shige ciki tare da rufe ƙofar sannan ya basa amsa da “ina fa lafiya yau baƙin tabon maita ya fito a wuyan yarima sam ya kasa cin abinci” Barham ya saki kofin hannunsa yana mai kallon jakariya Ali cike da tashin hankali,kafin ya ce “tabo? Wane iri? Baƙi ko ja?” “Na faɗa maka baƙi ne” “Hakan na nufin bayan kambun baka yarima na ɗauke da ɗigon baƙar maita ?” Barham ya faɗa tare da zuwa ya ɗauko wani littafi sai dai duk bincikensa ya kasa samo gamsashiyar amsa ,tsabar firgici goshinsa har ɗigar da gumi yake.Ya ɗago ya dubi Jakariya Ali cike da rauni yana cewa “babu abin da na samu a binciken da na yi” Ali ya ce “ya zama dole mu nemo mafita tun yau kafin gari ya waye ,saboda muddin aka kwana to Maitar za ta rinjaye shi ya fara sarrafa ta ” Idon Barham suka kaɗa suka yi ja,ya rasa meke yi masa daɗi kafin can ya ce “yawwa ina matsafiyar tarihi da aka damƙe?” “Tana can a kulle” ya basa amsa. “Mu je ka kai ni can ita ce kawai za ta bamu mafita” Barham ya faɗa tare da ɗaukar wata takarda.Haka suka dugunzuma zuwa can inda ake ɓoye masu laifi,ko kaɗan babu wanda yayi gigin hana su shiga saboda duk wani dakare a ƙarƙashin ikon jakariya Ali yake shi ne shugaban dakaru gaba ɗaya. Suna zuwa suka tarar da ita a zaune tana yin rubutu a ƙasa,ba tare da ta ɗago ba ta ce “me kuka zo yi? Kun zo tafiya da ni ne a kashe ni ?” Sai suka kalli juna kafin Barham ya yi shahadar cewa “wane laƙani ne ake yin amfani da shi domin daƙile bujurowar baƙar maita tsafi wacce ke bibiyar jini?” Ta ɗago da sauri ta dube su kafin ta ce,“ba zan taɓa faɗa ba ,kamar yadda yake son tozarta al'ummar Mayu da matsafa shi ma sai na bari ya tozarta a idon duniya kowa ya san wane ne shi” Barham ya furta surkullen tsafi sai ga shi tsundum cikin ragar da take ciki,har ƙasa ya zube alamun roƙo kafin ya ce “kar ki dubi wannan ɓangaren,ki dubi matsayinki na babbar matsafiyar tarihi ki sanar da ni laƙanin” Ta kawar da kai tana mai cewa “babu wani laƙani da zai daƙile maitar yariman masarauta ,sai dai a basa magani domin ɓoye ta.Daƙile ta duka kuma dole sai sarauniyar matsafa ce da kanta za ta iya yin haka” “Bani na ɓoyewar” Barham ya faɗa ,ta juya masa baya tana mai cewa “yana can a kusa da duniyar ruwa,fure ne na floris mai matuƙar muhimmanci da zarar ka kai gare shi za ka ji ƙamshinsa na sanar da kai shi ne abin da ka zo nema“ Barham ya miƙe yana yi mata godiya,yana shirin tafiya ta ce “ban ƙare jawabi ba,masu tsaron furen nan fararen fatale ne da ba su aminta da irin tsafinka ba” Barham ya juyo cike da tsoro kafin kuma ya dubi Jakariya Ali ya ce “na gode” Yana fitowa sai kuma suka fara shawarar ta yadda za a yi su fita daga cikin masarauta ba tare da kowa ya gani ba.Jakariya Ali ne ya je inda ake ajiye dokin yarima,kamar yana magana da mutum haka yayi masa bayanin komai kafin ya jawo shi ya fito. Barham ne ya fara hawa don shi ne ya san hanya sannan shi Ali ɗin daga ƙarshe.Cikin amincin Allah suka fita daga masarautar zuwa inda aka shaida musu za su samu maganin,ana kawowa wurin kuwa ƙamshi ya buge musu hanci kafin su yi wani yunƙuri kuma fatale duk sun zagaye su shi kuwa Barham ganin mutuwa a maƙoshi tsautsayi yasa ya furta baƙin tsafi,sai kuwa aka damƙe su aka jefa ɓoyayyar duniya. A can masarauta kuwa yarima Naslam ne kwance a ɗakinsa,har aka yi sallar asuba bai farka ba sai da hasken rana ya hudo ya daki tabon maita na wuyansa,wani irin kuka yayi da ya girgiza masarautar.Daidai nan free page ya ida,duk mai son shiga paid group zai biya kuɗin karatunsa 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 *Daga yau discount yake idawa 13.April* *NB:* Da zarar book ya kammala kuɗinsa 1k ne. MRS SADAUKI [13/04 10:28] MRS SADAUKI: _____________________ MRS SADAUKI *MAITAR DARE* 1-2 #Damagaram Ƙarfe uku na dare agogon ɗakin ya nuna,a sa'ilin da mutane ke kwance suna hutawa a daidai wannan lokacin ne Hajara ta hana idonta bacci saboda yawunta da suke tsinkewa tsabar yadda suke kwaɗayin ɗanɗanon jini. Idonta ta fara rikiɗarwa tun farko kafin ta tura ƙofar ɗakin wacce ta yi sa'a ba a kulle ba,ɗakin cike yake da duhu amma bai hana idon Hajara hango Safeenat ba wacce ke kwance ta tallabe ƙaton cikinta tana sharara bacci. Yawun Hajara suka ɗiga ga ƙasa lokacin da ta yi tozali da ɗan jinjirin da ke kwance a marar uwarsa,ta ɗaga ƙafa da niyyar isa gare ta kawai sai ga wani haske da ba ta san daga ina ya fito ba ya luluɓe Safeenat.Da wani mugun sauri ta yi baya tana zarar idonta da suke jawur kamar wuta kafin kuma ta fice daga ɗakin gaba ɗaya,ba wai don ta haƙura ba sai don ƙara yin wani sabon shirin. “Hajara lafiya kika zo kika tsaya tsakiyar falo?” muryar mijinta Dayyabu ta daki kunnenta,da mugun sauri ta lumshe idonta gudun kar asirinta ya tonu,ba tare da ta amsa masa tambayar ba ta yi gaba ta koma ɗakinta ta ja ƙofa ta rufe.Sai a lokacin ta ja wani numfashi haɗi da buɗe idon, ƙarƙashin gadonta ta je jawo wata tukunyar laka.Banda baƙin hayaƙi babu komai a ciki,wani yare ta yi sai ga shi ta rikiɗe ta koma tsakaka haka ta fito ta fara bin bango ba ta zame ko ina ba sai ɗakin Safeenat a karo na biyu.Har yanzu hasken bai ida gushe wa ba,wannan dalili yasa ta sauka kan dressing mirror ta fiddo harshenta tare da fara zuba yawunta cikin man shafawa da Safeenat ta bar shi a buɗe . Bayan ta gama ne ta ƙara bin bango ta fito mijinta ta gani ya buɗe ƙofar ɗakinta ya shiga ya kuma fito da alamu rashin ganin ta ne yasa haka. Da sauri ta koma ta je ta ɗauki siffarta ta bil'adama,gefen gado ta zauna tana jin har yanzu kwaɗayinta bai kau ba.Haka wannan dare ya kasance daren rashin sa'a gare ta,sam ba ta yi wani baccin kirki ba. Washegari Tun safe Safeenat ta yi wanka ta shafa mai da turare sannan ta shirya cikin doguwar riga kasancewar cikinta ya tsufa ba ta da wata sutura mai yi mata in ba doguwar rigar ba. Cikin sanyin jikin da ya zama tabi'arta ta fito,a falo ta tarar da ahalin gidan kan table suna cin abinci. “Daddy ina kwana?” ta gaishe da mahaifinta,ya amsa cikin sakin fuska yana cewa “ lafiya lau Feenat ya ƙarfin jikinki?” “Alhamdullah!” ta amsa tare da maida dubanta gefen Hajara ta ce “ina kwana Gwaggo?” Hajara ta haɗe rai ta ce “ da ban kwana ba za ki gan ni ? Tsabar munafurci ba ki tashi fito wa ba sai da baiwarki ta gama girki kin fito ki kwashi banza to ban girka da ke ba” Feenat ta sunne kai tana jin wani irin zafi na tasowa daga ƙasan zuciyarta,babban takaicinta kuma da ta ji Daddy yayi shiru bai ce komai ba.Yaran Hajara Munir da Munira suka shiga yi mata dariya,ba ta kula su ba ta wuce kitchen ɗin ta nema wa kanta abin da za ta ci.Ƙasan tile ta zauna dirshen ta soma tunanin bayan ta gama cin abincin,hawaye suka zubo mata ba ta shirya ba da sauri kuma ta dafe ƙaton cikinta da ke faman juyawa tana jin muguwar ƙaunarsa don a yanzu shine kawai zai rage mata raɗaɗin rashin masoyinta Bashir. “A yi dai mu gani in tusa ta hura wuta! Yo wannan kukan shi zai maido miki mijin? Ai dama duk abin da aka yi shi da cin amana ba zai je ko ina ba.Yanzu da kika yi sanadin hana Bashir auren Murjanatu ina ce ya mutu ya bar ki,kuma ita Murjanatun na can Saudi Arabia cikin gata tana auren farin ciki” Goggo Hajara ta faɗa lokacin da ta tarar da Feenat a kitchen tana kuka.Ta yi kutufo da ƙafafunta ta ce “ ja ki ban wuri na wuce ko kuma na sabanta ki muguwa mai halin uwarta” da mugun sauri ta janye ƙafafunta wani sabon kukan na ƙwace mata. Cikin masifar nan Goggo Hajara ta ci gaba da balbale ta da masifa,“ ki tashi ki fitar min daga kitchen zan ɗora girki ,ki koma can ɗaki ki ci gaba da munafurcinki” Daga bakin ƙofa Daddy ya ce “Hajara ki zo ina son ganin ki ɗakina” Idonta kamar za su faɗo ƙasa tsabar yadda take hararen Feenat,haka ta wuce ta je ɗakin Daddy a tsaye ta tarar da shi ya ba ƙofa baya. “Daddyn yara ga ni ” ta faɗa cike da ladabi. “ Haja ki kiyaye ni,bari gani na ƙyale ki ɗazu kin ci mutumcin ƴata,na yi shiru ne kawai don in nunawa Feenat ba ta kyauta da ta bar ki ke ɗaya ki ka yi aikin gida ba .Amma ba zan lamunci ki tozarta min ƴa ba,nan gidana ne don haka tana da ƴanci sake wa yadda take so.Mine ne na yi mata gori? Maimakon ki rarrashe ta akan halin da take ciki shi ne za ki tsiro mata da wata sabuwar masifar? Ta rasa mijinta wannan kaɗai abun tausayi ne,sannan ga tsohon ciki.Na san tun bayan da Feenat ta auri Bashir ki ka tsane ta,kin manta cewa matar mutum kabarinsa tun can farko Allah bai nufa Murjanatun ce zai aura ba” Cike da munafurci Goggo Hajara ta soma kuka har da jan majina kamar wata yarinya,da mugun sauri Daddy ya juyo tare da jawo ta jikinsa yana cewa “mine ne kuma na kuka? Ke fa uwa ce bai kamata sai an faɗa miki abin da ya dace ba,ɗa na kowa ne ba ka san mai taimakon ka ba” “Amma Daddyn yara ka fi kowa sanin yadda na riƙe Safeenat da zuciya ɗaya amma rana tsaka ta ruguza alaƙar nan don kawai ta ga banda burin da ya wuce Murjanatu ta yi aure” “To ai yanzu komai ya wuce,ba ga shi ta yi auren ba? Jiya ma mijinta ya min magana kan yana so ta dawo gida ta haihu ” Jin ƴarta za ta dawo sai ta manta da zancen kuka ta washe baki ta ce “au ! Madallah! Yaushe za ta zo?” Daddy ya murmusa ya ce “a'a ƴarki ta ce kar a sanar da ke za ta yi miki bazata kawai ki zamana cikin shiri” da wannan Daddy ya fice ya bar gidan zuwan can Company wurin aikinsa. Goggo Hajara kuwa kitchen ta koma sai ta tarar da Feenat ta ɗora girkin rana sai gumi take saboda zafin wutar gas,ta taɓe baki kafin ta fito. Ita kuwa Feenat baiwar Allah sam ba ta ƙaunar tashin hankali wannan ya saka ta ɗora girkin duk don a zauna lafiya.Kafin ta gama jikinta ya soma ƙaiƙayi, soshe-soshe ta fara yi ganin abun na ta yin gaba yasa ta kashe gas ɗin ta fito.Ɗakinta ta je,direct toilet ta shiga ta soma yin wanka sai dai ba ta canza zane ba sai ma wani ja da fatarta ta yi.Dakyar ta daure ta je ta ida girkin ta zuba a kuloli ta jera kan table,da ta koma ɗaki sai ta ɗauki hoton hannunta inda alamun jan ya fi yawa ta tura wa ƙawarta Sakeenatu tana tambayarta ko mene ne wannan kasancewarta likita .Babu jimawa ta kira ta bayan sun gaisa ne take cewa “ sai dai ki zo asibiti a duba ki ta waya ba a ganewa,kuma ni ba aikina ba sai dai na haɗa ki da likitan fata” Feenat ta ja ajiyar zuciya ta ce “ KEENAT kin san Daddy ba zai bari na fita ba,kuma dama bai dace mace mai takaba ta fita ba” Cike da tausaya wa KEENAT ta ce “ na sani amma ai lafiya ta fi komai ,ƙila kuma kin ci wani abu ne da ya haifar miki da hakan” “Ban ci komai ba fa,ya aikin ana ta fama ko?” “Wallahi kuwa,in sha Allah in na sauka zan biyo nan gida na duba ki” sosai suka yi hira kafin su yi sallama. Daga inda take zaune ta fara kallon hotunan Bashir inda yake sanye da Kakin soja,nan ta lalace wurin kallonsu har sai da Munira ta shigo kiranta .Ta miƙe dakyar ta fita,a falo ta tarar da Goggo Hajara tun da ta fito ta lura idonta na kan cikinta.Ta sunne kai tana mai karanta ‘ Hasbunallahu wani'imal wakil ’ a can ƙasan zuciyarta,cikin nata ne ya soma yin motsi kamar zai fito mata ta cibiya.Tsabar yadda take jin ciwon juyinsa yasa ta kai hannu ta dafe ƙasan mararta tana mai fitar da nishin wahala,ido rufe ta ci gaba da sauraren azabar da ke ratsa duk sassan jikinta. Goggo Hajara ta yi wani makirin murmushi tana mai cewa “ Safeenat lafiya kuwa?” Sai a lokacin ta ware idonta da suka yi wani mugun ja,bakinta sam ba zai buɗu ba ballantana ta iya yin magana.Bayanta da ƙugunta suka ƙage lokaci guda wanda ya haifar mata duƙawa ba ta shirya ba,tuni idonta sun fara ganin dishi-dishi duk da wannan ne cikin farko tuni ta fahimci haihuwar ce ta zo bilhaƙi. Goggo Hajara ta ce “ Haihuwa ce kam,Munira fita waje bari na ɗauko leda ” “Mama in kira mai taxi ku wuce asibiti ko?” Munira ta faɗa tana kallon Safeenat wacce tuni ta fara wani gurnani mai haɗe da nishi. “Uwar mai taxi za ki kira ,fice na ce” Goggo Hajara ta faɗa tana mai shiga ɗakin Safeenat ta ɗauko robar da aka tanadi duk wasu kayan haihuwa. Da kanta ta shimfiɗa leda ta ɗora wasu zannuwa akai kafin ta ce “ Safeenat ki cire rigar nan mai haihuwa ina ruwanta da wata sutura” tsabar azabar da take ji yasa ba ta yi yunƙurin hana Goggo cire mata kayan ba. Yawun Goggo Hajara har wani dalala suke suna tsinkewa lokacin da ta ga kan ɗa ya sawo kai.Jikinta har rawa yake wurin taimakawa yaron ya fito ,babu wani jinkiri ko ɓata lokaci ta fara juya ido tare da soma kai wa kurwar jinjirin hari sai dai ba ta ida cin galaba ba nishin Safeenat haɗi da kukan wata babyn ya dawo da ita hayyacinta. Ƙirjin Goggo Hajara ne ya kusan ɓallewa zuciyarta ta faɗo tsabar firgici,jaririyar da faɗo cibinta a yanke yake sannan kuma babu marakiya saɓanin shi namijin da har yanzu take masa reto. Sai a lokacin ne ma ta samu zarrar yanke mahaifar,ba tare da kuma ta san dalilin kawar mata da mugun nufinta ba ta soma kimtsa Safeenat wacce babu laifi ta dawo hayyacinta. Goggo Hajara ta wanke kayan da kuma gyara ɗakin ta saka turaren wuta,ita ce kuma ta zaɓo wa Safeenat riga da zane.Har da haɗo mata tea mai zafi ta sha,gefe ta koma bayan ta gama komai tana tunanin zuci ‘ mi ya shiga kaina ni Hajara? Kamar ni kamar ba ni ce ba’ kukan jariran ne ya katse mata tunani ,ta ce “ ki ɗora su ga abincinsu” sai kuma miƙe ta soma nuna mata yadda za ta yi.Namijin kawai ya sha ita kuwa macen baya ga kuka babu abin da take,Goggo Hajara na ɗaukar ta sai kuma ta yi shiru kamar ba ita ce ke kukan ba.Muƙut ta haɗiye wasu yawu hango wani baƙin kallo daga cikin ƙwayar idon jaririyar da ko minti talatin ba a yi ba da haihuwarta...... [13/04 10:28] MRS SADAUKI: _____________________ MRS SADAUKI *MAITAR DARE* 3 Sannu a hankali Gwaggo Hajara ta soma jin wani sanyi na ratsa ɓargo da tsokarta,kamar wacce aka yi wa doli kuma ta ƙi kawar da dubanta daga cikin idon Babyn.Idonta suka soma kafewa saboda wata irin shaƙa da ta ji an yi wa wuyanta,babu shiri ta buɗe bakinta na maita kurwar jaririn da ta soma cin galaba kansa ta fara fitowa daga can cikin hanjinta tana fitowa ta bakinta .Wani koren hayaƙi ne ya soma shiga cikin jaririn wanda daga bakin Gwaggo Hajarar yake fitowa,wata irin atishewa ya soma yi kafin ya tsala kuka. Da mugun sauri ta yi baya ta zauna kan kujera,idonta na kan babyn wacce tuni ta soma bacci. “Gwaggo ya ƙi yin shiru ko cikinsa ke ciwo?” Safeenat ta faɗa kamar za ta yi kuka tana ririga yaron,ran Gwaggo Hajara ne yayi mugun ɓaci sai yanzu tunaninta ya dawo a tunzure ta ce “ uban mi zan yi masa to? Lokacin da na yi haihuwata uban wa ya kama min wurin rainon ? Ki riƙe abin ki” ta faɗa tare da ajiye mata babyn kusa da ita,jikin Safeenat sai yayi sanyi dakyar ta samu yayi shiru bacci ya ɗauke shi.Ta shimfiɗe shi kusa da Baby girl ɗin kafin ta je ɗakinta don ɗauko wayarta,tana dawowa sai ta hangi maciji kan jaririyar duk ya naɗe jikinta da shi ba ta san lokacin da ta saki wata ƙara ba wacce ta yi daidai da ɓacewar macijin.Safeenat ta zo da mugun sauri ta ɗauki yaranta ta mayar da su ɗakinta,sai da aka ɗauki lokaci kafin nutsuwarta ta dawo ta soma kiran mutane tana shaida musu zancen haihuwar.Hatta Daddy sai da ta kira shi ta sanar da shi,babu jimawa kuwa sai ga ƙanwarsa Habiba ta zo gidan sosai Safeenat ta ji daɗin ganinta musamman da ta ga har da ƙullin kayanta ta zo da alamu za ta jima. Ruwan zafi ta je ta ɗora cikin ƙatuwar tukunya kafin ta dawo,“ Safeenat ya zama doli ki kula da yaran nan musamman namijin don na ga shi ne mai rauni” Habiba ta faɗa tana shafar twins ɗin. “In sha Allah Gwaggo Habibah zan yi,da alamu ma ya fi kuka dakyar na samu yayi baccin nan” cewar Feenat. “Hum! Baccin wahala ne,ah to ai doli ma yayi Allah dai ya kyauta” “Amen!" Feenat ɗin ta amsa ba tare da ta san dalilin Gwaggo Habibah na faɗar haka ba.Bayan ruwan sun tafasa ta juye su ta yi wa yaran wankan,namijin ana saka shi a ruwa ya farka tare da canyara kuka amma ita hajiya babba har aka gama wankan tana bacci tamkar wacce ba ta rai.Gwaggo Habibah kuwa sai murmushi take tana jin wani farin ciki ƙasan ranta,dama ita Allah bai taɓa bata haihuwa ba . Safeenat ma sai da ta yi wanka da ruwan zafin ta gasa kanta da kyau ta fito ɗaure da towel,sai kuma yanzu ne Gwaggo Habibah ta lura da yadda fatar Safeenat ta yi ja.Da wani mugun sauri ta tashi ta cabke hannunta da ke ƙoƙarin ɗaukar kwalbar mai,“ jira na duba na gani” ta faɗa tana mai duba man ba tare da ta ce komai ba sai kuma ta fita direct ɗakin Gwaggo Hajara ta wuce ko sallama ba ta yi mata ba kuwa ta yi tsaye kai gare ta tana mai cewa “ an gaishe da uwar mugaye ta duniya,wato baƙar zuciyarki na nan daram babu canji .To asirinki ya tonu na ga bala'in da kika zuba cikin man shafawar Safeenatu,sai dai ki sani sai dai ki ci kanki amma Twins sun fi ƙarfinki ” Da wani mugun sauri Gwaggo Hajara ta tashi zaune,dama tun bayan da ta shigo ɗaki take jin duk jikinta babu daɗi dalilin kwancin da ta yi kenan sai kuma yanzu da ƙanwar mijinta ke feso mata kalaman rashin mutumci.Wani makirin murmushi ta yi kafin ta ce “ da alamu dai kin manta wace ce ni ko Habibah? Amma za ki gani” “Babu abin da zan gani sai alkhairi...” “Eh lalle wuyanki ya isa yanka” Gwaggo ta faɗa tana juya ido,Habibah ta tuntsire da dariya ta ce “au kin zata guntun tsafinki zai iya yin tasiri a kaina? To ki canza shawara tun wuri bai ƙure miki ba don yanzu daidai nake da ke” Ganin alamun tabbas ba Habibar da ce ke tsaye a gabanta ba yasa Gwaggo Hajara haƙura da surkullen,idonta masu cike da mugunta ta tsura mata ta ce “ mi ya kawo ki ɗakina?” “Ina so ki fita sabgar Safeenat da ƴaƴanta,in kuma ba haka ba....” sai kuma ta yi shiru tana cije baki haɗi da jinjina kai. “Ki tona min asiri? A tunaninki akwai wanda zai yarda? Hahaha! Yaro man kaza,Habibah kar ki manta hatta gyatumarki a tafin hannuna take....” ta yi saurin katse ta da “sai dai shi wanda kike tutiyar da shi mugun tsafinki bai yi tasiri kansa ba ,na san kin san haka” Ran Gwaggo Hajara ne ya ƙara yin baƙi,duk duniyar nan Habibah ce kawai ta zame mata ciwon ido duk yadda take son gudanar da lammuranta to muddin tana ga wuri sai ta roga su. Ƙarar buga ƙofa ce ta maido ta daga guntun tunanin da take,ta bi bayan Habibar da mugun kallo tana jin baƙin cikin da ba ta da MAITAR IDO (MRS SADAUKI,duk mai son complete book ɗin nan zai iya tuntuɓa ta kai tsaye ta lambar da na rubuta a can sama) da tabbas ta jefa wa Habibah ƙwayar cutar da za ta zama ajalinta. SAKEENATU Tana tashi daga aiki ta fito don samun adaidaitar da za ta kai ta can gidansu Safeenat kwatsam sai ga kiran wayar mijinta Abbas . “Mamuh ta ce yau ba ki bar mata abin da za ta ci ba ina son sanin dalili?” shi ne abin da ya fara cewa ko sallama babu,ran Sakeenatu ya ɓace amma ta haɗiye shi ta ce “ na samu ƴar aiki fa kuma kafin na fito na shaida mata kan ta girka mata abin da za ta ci” “Ƴar aiki za ta kula da uwata? Keenat mi ya shiga kan ki ne? Yanzu dai na baki minti goma ki tabbatar kin yi mata girkin abin da take so” yana gama faɗa ya yanke kiran. Tamkar za ta fashe haka take ji,mai ɗan sawu ma dakyar ta faɗa masa inda zai kaita.Tana shiga gidan ta tarar da Mamuh zaune kan kujera ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana wani yamutsa fuska,gaban Sakeenatu ya faɗi kamar kullum muddin dai za su haɗa inuwa ɗaya da surukarta ta. “Barka da yamma Mamuh” ta faɗa murya na rawa,Mamuhn ta ce “ in kin gama yawon tanbaɗar sai ki shiga kitchen ki girka min wake da shinkafa” Idonta tab ƙwalla ta shiga kitchen ɗin ta ɗora tukunya ko kayan ba ta cire ba haka ta tsaya sai da ta tabbatar ta gama sannan ta zuba a plate ta kai wa Mamuh. Da zafi da komai ta saka hannunta tana ci mai na bin hannunta sai wani lumshe ido take alamun yana yi mata daɗi, Sakeenatu wacce ta tsaya don ganin ko yau ma Mamuh za ta yi irin yanayin nan sai kuwa ta ga ta yi.Idon Mamuh sai wani haske-haske suke fitar wa kamar kullum muddin dai wake da shinkafa ta girka mata. A tsorace ta nufi ɗakinta ,kayan jikinta ta rage sannan ta shiga toilet.Shower ta sakar wa kanta,kamar abun almara haka ta soma jin yanayin jikinta na canzawa tana jin feeling wanda kuma abu ne mai wuyar faruwa da ita muddin dai ba Abbas ke a wurin ba. Abu kamar wasa amma sai yin gaba-gaba yake,kafin Sakeenatu ta farga tuni ta hankalinta ya soma gushewa ta dumulmiya duniyar son kasancewa da mijinta.Tamkar a mafarki ta soma jin kamar ana wasa da sassan jikinta,sai dai idonta sun yi nauyin da ba za ta iya buɗe su ba ballantana har ta ga shin zahiri ne ko kuwa? Sama da minti goma tana cikin wannan yanayi kafin ta dawo hayyacinta,a doli ta tsarkake jikinta ta fito tana mamakin al'amarin.Bayan ta shirya tsab cikin riga da zane sai ta fito falo,Mamuh ta gani sai sharar bacci take kamar matatta .Dining ta je ta zauna ta buɗe kulolin da ƴar aikinta ta yi girki,shinkafa ce da miyar kaji haka ta zuba ta soma ci tana mamakin yadda aka yi Mamuh ta zaɓi cin wake da shinkafa akan lafiyayen abincin nan .Bayan ta gama ta ɗauki waya ta kira Safeenat ta shaida mata za ta zo yanzu ,sai kuma ta koma ɗaki ta saka hijabinta ta ɗauko jaka ta fito.Tana fita ba ta wani wuya ba ta samu ɗan sawu ya kaita,da sallama ta shiga gidan har ta wuce can ɗakin da Safeenatu take wanda ya cika da mutane kusan dangin Bashir ne. A mutumce take gaishe da kowa amma yanayin jikinta na bata ana kallonta,tana juyawa suka haɗa ido da Habibah wacce ta kasa ɗauke idonta kan Sakeenatu har sai da ta ji ta tsargu.Ta zauna kusan Safeenat tana mai cewa “waccan wace ce sai kallona take?” “Ƙanwar Daddy ce fa ba ki gane ta ba?” Feenat ta faɗa tana mai miƙa mata boy bayan ta shafi kansa sai kuma ta ajiye shi aka miƙa mata girl ɗin.Wani irin shock ne ya ratsa Sakeenatu har sai da ta zabura,yayin da gabanta yayi mummunar faɗuwa ganin Babyn ta buɗe idonta tana kallon ta alhalin lokacin da aka miƙo mata ita tana bacci.Sakeenatu ba ta ida shiga tashin hankali ba sai da ta ga tamkar Babyn na yi mata murmushi...... [13/04 10:28] MRS SADAUKI: _____________________ MRS SADAUKI *MAITAR DARE* 4-5 Wani irin abu ne marar misaltawa ke ratsa Sakeenatu tun daga kan babban yatsan ƙafarta har zuwa kwanyarta da ta soma toshe wa .Lamarin da take ji a al'aurarta kuwa kusan girme wa hankalinta ya yi,tamkar wacce ake fitar wa da wani dafi haka take jin ana yi mata motsi gami kuma da samun sassauci a doli ta lumshe ido ba ta shirya ba.Ita kuwa Gwaggo Habibah da ke can gefe sai murmushi take tare da yin zancen zuci don duk tana ankare da abin da ke faruwa.‘ Tabbas a duk inda ke da mugunta da cutar wa Allah sai ya kawo mai ceto mai magani,na zo kenan a gidan nan mutuwa kawai za ta fitar da ni zan saka ido sosai akan jaririyar nan zan raine ta da hannuna ta yadda zan taimaka mata wurin fahimtar baiwar da Allah ya yi mata da yadda za ta sarrafa ta’ sai kuma ta miƙe tana yin wani murmushin nasara.Babyn ta ɗauke daga cinyar Sakeenatu wacce gumi ya jiƙa ta har goshinta na ɗiga,babu kuma wanda hankalinsa ke wurin hatta ita Safeenat sai hira take da dangin mijinta waɗanda suke cewa shi namijin a saka masa suna Bashir a yi madadi. Sakeenatu ta ware idonta jikinta na ɗan rawa kamar wacce ta farka daga mummunan mafarki.Idonsu ya sarƙe cikin na juna,Gwaggo Habibah ta ce “ sannu! Bari na nemo miki ruwa masu sanyi” sai kuma ta shimfiɗe babyn wacce tuni ta koma baccinta. Kitchen ta nufa don samo ruwa masu sanyi,sai suka yi kiciɓis da Gwaggo Hajara ƴar kallon-kallon suka yi kowacce na hararen ƴar uwarta. “In tusa za ta iya hura wuta a yi mu gani mana,sai shegen kinibibi da nuna isa kan an san ɓoyayyar duniya nan kuma ba asss ” Gwaggo Hajara ta faɗa don kuwa a goshin Habibah ta fahimci sun karya wata muguntar tsafi. Ita kuwa Habibar murmushi ta yi don ta fahimci mi take nufi wato in ta isa ta yi wa kanta maganin damuwarta.“ Nan gishirinki zai ƙare a dafuwar ƙaho,yadda bacci ya bar ido haka za ki gaji ki bar Habibah saboda kabewar kan kabari nake baƙin cikin masu taushe” “Aikin banza sai aukin cika baki ,a hakan kuma na yi sanadin hana ki baccin kullum cikin kukan kin ƙi haihu ba” “Haihuwa ai ta Allah ce,kuma alhamdullah yanzu na samu irina wacce tsoron samun ta yasa kika jefo min mugun nufinki ” Habibah ta faɗa tana wani murmushi,Gwaggo Hajara ta kasa cewa komai yayin da ita kuma ta ci gaba da cewa “ ko ba ki gane abin da nake nufi ba? To Safeenatu ta haifi wata Habibar sak irina ce ko na ce ma ta fi ni don ita murucin kan dutse ce ba ta fito ba sai da ta shirya” muƙut! Gwaggo Hajara ta haɗiye wasu yawun tsoro don kuwa ta fi kowa sanin babyn Safeenatu ba normal jaririya ce ba tun da ta ga zahiri. Ta ja wani irin numfashi jin saukar ruwan sanyi kan fuskarta,dakyar ta ware ido tana kallon Habibah wacce tuni ta juya ta yi tafiyarta tamkar ba ita ce ta gama zuba mata ruwan a fuska ba.Cike da baƙin ciki ta koma ɗakinta,a yadda take jin jininta ya hau in ba jini ta sha ba ƙila zuciyarta sai ta buga.Tukunyar tsafinta ta ɗauko ta yi ƴan surkullenta kafin ta ɗauki mayafi ta fita waje,yara ta gani suna wasa daga inda take a tsaye ta soma kiran kurwar wani yaro cike da ƙwarewa wurin maita tsafi.Yaron ya dafe gefen wuyansa inda ya ji kamar an tsikare shi da allura amma bai bar wasar ba haka yake ci gaba da gudun yana son kamo wani,idonsa ne suka soma rufe wa kafin bugun zuciyarsa ya tsaya cak kawai sai ya faɗi ga ƙasa.Ita kuwa Gwaggo Hajara da wani mugun sauri ta rufe ƙofa,tuni yara sun fara ihu suna faman kiran sunansa. Ɗakinta ta koma ta ci gaba da tsotse jinin yaron ko jira ba ta yi ba,don ta san sarai in ta jinkirta ajiye kurwarsa Habibah za ta iya fahimtar haka.Tsawon lokaci ta ɗauka cikin siffar mugunta kafin ta dawo normal,zuciyarta ta ji fayau babu ƙunci.Tana nan zaune sai ga Munira wacce rabon ta da gidan tun lokacin da aka ce ta fita.Kusa da mahaifiyarta ta zauna ta soma bata labarin yadda yaron maƙwabciyarsu ya faɗi suna tsaka da wasa,“ je ki nemo min Munir ya dawo gida ” shi ne kawai abin da ta ce tana jin wani daɗi a ranta ba don komai ba sai don ta yi mugunta. Habibah na shiga ta miƙa wa Sakeenatu gorar ruwa mai sanyi haka ta shanye su tasss tana sauke ajiyar zuciya.“Ki dinga kula da kan ki mana,ko barin kai a buɗe ai yana sa maƙiya su yi galaba kanka” “To in sha Allah ” Sakeenatu ta faɗa tana mai ɗan satar kallon jaririyar ƙawarta,ido ɗaya babyn ta buɗe ita ma tana kallonta babu shiri Sakeenatu ta miƙe tsaye tana cewa “ Feenat zan tafi sai kuma gobe in sha Allah zan zo da safe tun da babu aiki” “Na gode sosai Keenat wai ina Ma'idah?” “Tana wurin Mama tun wancan satin na kai ta kin san Komandan ta zo” Safeenat ta waro ido ta ce “ ki ce dai a takure kuke yanzu,kai tsohuwar nan an yi ƴar masifa mine ne na zuwa hutu ke ba ƴar makaranta ba” Sakeenatu ta tuntsire da dariya ta ce “ kar a yi babu ita mana,duk gani take wasu kuɗi ne da shi ba ta san rabin hidimar gidan ni ke yi ba a haka kuma za ta dinga tsiro da abubuwa tana saka sharaɗin abin da take so” Safeenatu ta ce “ ah lalle ta ci sunan Komandan ɗin” nan dai suka yi sallama Sakeenatu ta fito.Kafin ta isa gida sai da ta saya wa Mamuh kifi don ta san tana son shi,da sallama ta shiga amma ta ƙi amsa mata sai ma tambaya da ta jefo mata “ daga gidan uban wa kike? Wato kin matsu na koma ƙauye shi ne kika je gidan malamai da bokaye a yi min asiri na tafi ban shirya ba” Jikin Sakeenatu banda rawa babu abin da yake yi,kanta ƙasa ta soma rantse-rantse tare da sanar da ita inda ta je. “Ita ƙawar taki ce ta baki magani kika yi wanka da shi ta yadda zan ji tsoron ki? Sakeena lalacewar taki har takai ki dinga faɗawa ƙawarki ƙarya da gaskiya akan ta baki magani? In maganin za ki nema mi yasa ba ki ce a baki na haihuwa ba sai na korar maƙiyiyarki” “Wallahi Mamuh babu wani magani da aka bani,na faɗa miki barka kawai na je” Keenat ta faɗa cikin muryar kuka. Mamuh ta tsure ta da ido,sam babu tabon duk muguntar da ta ajiye a jikin Sakeenatun komai ya rushe ta koma normal.Sannan a baccinta aka nuna mata ta yi wanka da ruwan magani duk mugun nufinta ya fita daga jikinta,jin shiru yasa Sakeenatu ta ɗago ido da zumar kallon Mamuh mugun ganin da ta yi ne yasa zuciyarta kusan faso allon ƙirjinta ta faɗo. Idon Mamuh sak irin na maciji yanayin fuskarta ma ya canza duk ta yi baƙi,“ in kin gama gulmar sai ki wuce ki ɗora min wake da shinkafa” Mamuh ta faɗa tare da yin gaba,Sakeenatu ta ce “ akwai sauran na ɗazu bari na zubo miki ” Ba tare da ta juyo ba ta ce “ ban so wani nake so ki dafa min” Jakarta ta ajiye ta shiga kitchen ta ɗora girkin,wannan karon ko waken ba ta wanke ba kamar yadda tsarin dafa shi ya zo mata daga Mamuh ɗin ,dama ita shinkafar ba irin wacce ake wankewa ce ba.Cikin plate ta zuba bayan ta tsalala mai dayawa,sai ta fito ta nufi ɗakin Mamuh da sallama ta shiga duk da ta san ba za ta amsa ba. Cike da ladabi ta duƙa har ƙasa ta miƙawa Mamuh plate ɗin wake da shinkafar amma ta ƙi karɓa sai ido da tsura mata.Tuni gaban Sakeenatu ya fara dukan uku-uku,“ ba zan ci ba!” “Amma ke kika ce na girka miki ” ta faɗa murya na rawa. “Tun zuwana gidan nan na faɗa miki sai an dirje wake an waken shi da hannu sannan ake girka min mi yasa yanzu ba ki yi ba?” “ Na zata kina jin yunwa ne sosai shi yasa na yi haka don na yi sauri” “To sai ki je ki sake dafa wani” Mamuh ta faɗa tana mai miƙe wa tsaye,cikin dakiyar zuciya Sakeenatu ta ajiye plate ɗin ta ce “ ki yi haƙuri Mamuh akwai aikin da nake son yi yanzu,ki ci wannan ɗin gobe in Allah ya kai mu sai na yi miki irin wanda kike so ɗin” Sam ko kaɗan Mamuh ba ta yi mamakin furucinta ba ,don dama da tsafi ne ta ci galaba har Sakeenatun ke mugun tsoronta yanzu kuma komai ya karye.Ita kuma tana gama faɗar haka ta fice,da ta fito har sai da ta ja ajiyar zuciya tana mamakin yadda yau ta cire tsoron Mamuh. Tana shiga wanka sai ta ga period ɗinta ya zo,wanda kuma ba komai ya haifar da haka ba sai gwagwarmayar fitar da sihirin jikinta.Cikin ƙananan kaya ta shirya sannan ta haye bed tare da kiran Abbas,cike da nishaɗi suka yi hirar soyayya nan ne kuma ya shaida mata gobe zai zo sannan a karɓo Ma'idah don ita yake son fara cin karo.Har ƙasan ranta ta ji daɗin furucinsa , wannan yasa suna gamawa ta kira can gidansu ta ce a kawo mata Ma'idar. Washegari Kuwa tun safe Sakeenatu ta soma gyaran gida ita da ƴar aikinta wacce ba za ta wuce shekara ashirin ba mai suna Fa'iza.Mamuh dai na ta kallonsu ba ta ce komai ba don fushi take da Sakeenatu,da kanta ta yi girki Fa'iza na kama mata. “Shi kuma waken nawa sai yaushe za a girka?” Mamuh ta leƙo kitchen ɗin tana mai faɗar haka. Sakeenatu ta ce “ yanzu zan yi” ba ta ƙara cewa komai ba ta tafi. “Fa'iza wanke min waken nan da kyau sai ki girka wa Komandan ban son ta kawo min cikas ina cikin farin ciki” Ƴar dariya Fa'iza ta yi kafin ta soma wanke waken kamar mai wankin kaya,ita ce ta girka shi kuma.Sakeenatu ta zuba a plate da kanta ta kai wa Mamuh jikinta har rawa yake ta soma ci tana lumshe idonta waɗanda tuni suka soma yin hasken nan.Ita dai Sakeenatu Allah na gani tsoron yanayin nan take ,da sauri ta wuce ɗakinta ta yi wanka ta shirya cikin wani rantsatsen less tana tsaka da fesa turare Ma'idah ta shigo da gudunta ta na kiran Ammyna.Ita ma sosai ta yi kewar yarinyar sai ta rungume abarta tana cewa “ ke da wa ne?” “Anty” ta bata amsa. A ɗan firgice Nafisa ta shigo tana cewa “ anty Sakeena wace ce waccan a kitchen? Zo ki ga abin da take” “Ƴar aikina ce lafiya?” “Zo dai ki gani” cewar Nafisar tana mai yin gaba Sakeenatu na take mata baya har suka shiga kitchen ɗin. Fa'iza suka tarar duk ta cire suturar jikinta tana fitar da wani nishi idonta a rufe suna tsiyayar da hawaye....... [13/04 10:28] MRS SADAUKI: _____________________ MRS SADAUKI *MAITAR DARE* 6-7 Tamkar wacce ke wata mu'amala da namiji haka Fa'iza ke yi ,hankalin Sakeenatu in yayi dubu to ya watse.Ta kalli ƙanwarta ta ce “ Nafisa ko iskokai ne? Dubi abin da take yi” Nafisa ta ce “ anty Sakeena tun da nake ban taɓa ganin mai kalar iskokan nan ba,hatta masu aljanin soyayya ai sai in suna bacci ne suke zuwar musu dubi ita wannan fa tamkar idonta biyu fa” “Yanzu dai don Allah ki taimaka mata tun da ke Malama ce kin ga Ma'idah har ta soma kuka” cewar Sakeenatu tana mai jan ƴarta zuwa waje.Nafisa ta cika kofi da ruwa ta tofa ayatul ƙursiyu da amanar rasulu sannan ta shiga watsa ma Fa'iza ruwan,a sannu a hankali ta soma barin abin da take daga ƙarshe ta buɗe idonta waɗanda suka kaɗa suka yi ja.Nafisa ta shiga yi mata sannu kafin ta taimaka mata ta mayar da kayan jikinta,“ dama kina da aljanu?” Sakeenatu ta tambaya wacce ta dawo. Fa'iza ta girgiza kai,“ to tashi ki yi wanka sai ki zo ki zuba abinci ki ci” Da “ toh” ta amsa kafin ta fita zuwa Toilet ɗin tsakar gida kamar yadda Sakeenatu ta shaida mata da ita za ta dinga amfani. Wanka ta soma sai da ta saɓa jikinta har sau biyu sannan ta fito,wasu kayan Sakeenatu ta bata ta saka abincin ma da ta zuba gidansu ta wuce da shi. Su kuwa a falo suka zauna suna hira Nafisa na bai wa Ma'idah abinci a baki,Abbas yayi sallama da gudu ta nufe shi tana “ Daddyyy” ya caɓe ta tare da cira ta sama yana yi mata wasa haɗi da kai mata sumba. Cike da farin ciki ya ƙarasa ya zauna,Nafisa ta gaishe shi yayin da suke aikawa juna wani kallon so shi da Sakeenatu mai cike da kewa. “ Mu je ka fara yin wanka ko?” “A bani abinci tukuna don Allah ” ya faɗa yana wani murmushi,Ma'idah ta ce “ Daddy ni ma ina ci” sai aka zuba musu ya dinga bata a baki ita kuma sai surutu take yi masa.Suna tsaka da nishaɗinsu sai ga Mamuh ta fito,fuskar nan kicin-kicin,“ ita kuma wannan farar tinkiyar?” ta yi tambayar tana zunɗen Ma'idah wacce ta tsorata da ganin Mamuhn. “Ina wuni Mamuh? Fatan na same ku lafiya?” Abbas ya faɗa cike da ladabi. “Ka bani amsa ta” “Ma'idah ce fa ƴar wurin Keenat” ya bata amsa a sanyayye. “Shegiya za ka ce wacce ba a san taƙamaimai wane ne ubanta ba,kai da ka iya kwashe-kwashe ka rasa wacce za ka auro sai wadda ta gama yawon duniya ta tsiyayar da duk ƙwayaƙwayin haihuwarta a titi.To ban yarda ban lamunce wannan tinkiyar ta zauna a gidan nan ba” Mamuh ke faɗa cikin masifa ita kuwa Ma'idah tuni ta soma kuka musamman irin abin ban tsoron da take hangowa a fuskar Mamuh. Abbas ya sunne kai ya ce “ a dai yi haƙuri Mamuh dukkan bawa bai wuce jarabawa,Ma'idah ita yarinya ce ba ta san komai ba” “Wallahi sai ta bar gidan nan” Mamuh ta faɗa cikin ƙaraji, Sakeenatu kuwa banda kuka babu abin da take yi . Hannun Ma'idah ta kama da niyyar jawo ta,ita kuwa baiwar Allah cike da tsoro ta ɗauki cokali mai yatsu ta caka ma Mamuh ita a ido da zumar ceton kanta ga dodo. Wani uban ihu Mamuh ta yi tana cewa “wayyo idona! Ƴar daba ta kashe ni” jikin Abbas na rawa ya je ya kamo Mamuh wacce tuni idon ya soma fitar da jini,hankali tashe ya soma goge jinin wani na zubowa a doli ya kama ta zuwa asibiti. Bayan tafiyarsu ne Nafisa ta soma tofa ma Ma'idah addu'o'i saboda yadda take wani irin kuka tana firgita,cikin kuka Sakeenatu ta ce “ Nafisa ki ɗauke ta ku wuce gida don Allah” “Ke kuma a nan za ki zauna? ” “To ina zan je Nafisa? Haƙuri zan yi dama aure ya gaji haka sanin kan ki ne a can gidan ba wani jituwa muke ba ni da Mama ta ɗauki ƙiyayyar ɗan farin ta ɗora min” “To amma dai ki kula da kan ki,in kin ga abin ya yi yawa kawai ki tawo gida” Kuɗi ta basu sannan suka bar gidan,ita kuma ta ɗauki waya ta kira Abbas don jin asibitin da suke shi da Mamuh yana shaida mata ita ma ta fita ta je.Tuni Mamuhn ma ta yi bacci an naɗe idon nata da bandeji ga kuma ƙarin ruwa an saka mata. Jikinta a sanyayye ta ce “ ka yi haƙuri” Abbas ya kamo hannunta ya ce “ dama haka Allah ya tsara,ina Ma'idah?” “Nafisa ta koma da ita can gida” “Don me? Zan rarrashi Mamuh na san za ta amince ta zauna da mu” Ta sakar masa murmushi ta ce “ na gode sosai da kawaicinka gare ni” wani kallo yake aika mata yana mirza tafin hannunta,da ido ɗayan mai lafiya Mamuh ke kallonsu tana jin wani irin haushi da takaici. “Mine ne haka? A asibiti fa muke ka bari har mu koma gida” Sakeenatu ta faɗa tana janye jikinta daga nasa ganin abin zai wuce gona da iri. “Mu je gidan to tun da kin ga Mamuh ta samu bacci ,sai mu dawo daga baya” Abbas ya faɗa yana langwaɓar da kai saboda ba ƙaramar kewar ta yayi ba. “To ai na farka” cewar Mamuh tana mai tashi zaune haɗi da hararen Sakeenatu,da ɗan sauri ya miƙe yana tabayarta jiki.“ Ka kira likita ya cire min ƙarin ruwan nan sai mu wuce gidan tun da uwarka ba za ta barin ka cikin salama ba” cewar Mamuh a zafafe,Abbas ya fita don kiran likita. “Duk tsiyarki dai ba za ki iya canza ma tuwo suna ba,Abbasi ɗana ne ba naki ba don haka ni ke da iko da shi ba ke ba.Kuma wannan shegiyar taki sai ta san ni ta caka da cokali sai na shayar da ke mamaki” Da wani mugun sauri Sakeenatu ta je gaban Mamuh ta tsuguna ta ce “ don girman Allah Mamuh ki yi haƙuri , Ma'idah yarinya ce ba ta da wayo ko me za ki yi to ki yi min amma kar ki taɓa ƴata” ta ƙarashe maganar hawaye na zubo mata saboda zuwa yanzu ta yarda Mamuh muguwa ce. Kafin ta kai ga bata amsa Abbas ya shigo shi da likita,ya ce “ sai kin yi kwana uku sannan za mu sallamar ki” “To ka sanar da uwarmu wacce ta matsa mu je gida” Mamuh ta faɗa a zuciye tana hararen Sakeenatu. Likitan yayi murmushi ya ce “ yanzu yadda za a yi sai ka nemo wacce za ta zauna da Mama,amma gaskiya ba za mu sallame ta ba yau” sai yayi wa Mamuh allurar bacci,duk yadda masifa ke cin ta haka ta haƙura saboda ƙarfin allurar. Shi kuwa Abbas Gwaggonsa ya kira wacce ke nan Damagaram ita ke bi ma Mamuh,babu jimawa kuwa ta zo .Ya ja matarsa zuwa gida,cike da zallar soyayya suka gamsar da junansu. SAFEENATU Tun bayan da kowa ya watse aka bar su ita da Gwaggo Habibah sai ta nutsu sosai kafin ta ce “ Gwoggo ni kam ɗazu wani abin ban mamaki ya faru,maciji na gani ya naɗe Baby girl ɗin nan ina yin ihu ya ɓace kamar aljani ” Gwaggo Habibah ta yi murmushi ta ce “ kar ki wani ji tsoro,sannan ina so ki kwantar da hankalinki duk wani abu da za ki gani ki yi shiru da bakinki.Duk kusan ƴan biyu suna da wannan baiwar,to ke macen ce ke da shi don haka ki shirya ganin abubuwa iri-iri wasu na tsoro wasu kuma na almara” Safeenat ta ja wani numfashi kafin ta ce “ to Allah cire min tsoron” ba ta ida rufe bakinta ba hasken ɗakin ya ɗauke duhu ya turnuƙe shi kai ka ce dare ya tsala.Duk tsit suka yi babu wanda ya ce wani abu,sai kukan jaririyar da ya soma tashi sannu a hankali tsawon minti biyu kafin ta yi shiru.Hasken ɗakin na dawowa Safeenatu da Gwoggo Habibah suka yi ƴar rige-rigen ɗaukar babyn duk suka yi tsaye suna kallon yadda goshinta ke fitar da wani haske yana ƙyalli a gaban idonsu ya ɗauke sai ga shatun haƙoran maciji ya bayyana raɗau .Safeenat ta kai hannu ta shafi wurin sai kuma ya ɓace,ta ja ajiyar zuciya tana mai ɗaukar jaririyar ta soma shayar da ita. Daddy ya yi sallama ya shigo,duk suka gaishe shi kafin a basa babys ɗin ya gani.Sosai yayi musu addu'a sannan ya fita,haka suka ci gaba da yin hirarsu har dare ya tsala.Duk sun yi shirin bacci za su kwanta amma ita Baby kamar ɗiyar aljanu ta ƙi baccin sai ma wani kuka-kuka da take yi. “Safeenat ki bata abincinta mana” Gwaggo Habibah ta faɗa tana shirin tashi ta kunna wuta. “Ina ta ƙoƙarin bata ta ƙi karɓa” cewar Safeenar. Kusa da ita ta zauna tana shirin ɗaukar babyn sai ta lura da yadda hannunta na hagu ke fitar da wani zane mai hasken wuta kamar ta murhu.Wani irin murmushi ne ya suɓuce wa Gwaggo Habibah ba tare da ta shirya ba cike da murna ta jawo hannun jaririyar ta riƙe sannu a hankali har zanen ya fito raɗam letter M ta fito sai a lokacin kuma jaririyar ta yi shiru sai ajiyar zuciya da take saukewa. A ɗan ruɗe Safeenatu ta ce “Gwaggo mine ne kuma wannan?” Sam Gwoggo Habibah ba ta bata amsa ba sai safar hannu da ta je ta binciko cikin kayansu ta saka wa hannun mai zane.“Daga yau kar ki ƙara barin hannunta a buɗe ki dinga saka mata safar hannu ” “Gwaggo ina tambayar ki mine ne ba ki bani amsa ba” “Alama ce ta prophétie/prophecy,da yawan ƴan baiwa tana soma aiki ne in sun kai shekara sha takwas amma ke yarinyarki tun farkon dirowar ta duniya tata baiwar ta fara aiki.Ta ceci ɗan uwan tawaicinta sannan kuma ta ceci ƙawarki Sakeenatu ” Ba don ta fahimci zancen da kyau ba ta ce” mi ya samu Keenat ɗin?” “An yi mata ajiya cikin ruhinta ta yadda esprit zai samu damar yin yanda ya so da gangar jikinta har ya cutar da ita” “Ya aka yi kika sani to?” “Safeenatu yi bacci in lokacin fahimtarki yayi babu buƙatar ki yi tambaya” Da wannan duk suka yi bacci, Safeenatu na tsaka da yin mafarki akan goben ƴarta Gwaggo Habibah ta tashe ta daga bacci.“Ruwan wankan ki na can toilet ta tsakar gida,ki je yi wankan sabulu kafin na zo na gasa miki jikinki da towel” Ta yi miƙa ta tashi a gajiye saboda kwana dare ta yi tana shayarwa,sai da ta ɗauki wani zane da hijabi sannan ta fita ta bar Gwaggo Habibah za ta yi wa Twins wanka. Sakeenatu na fitowa suka yi kiciɓis da Gwoggo Hajara ta gaishe ta sannan ta wuce toilet.Ita kuwa tsabar mugunta yasa ta koma ɗakinta ta yo shirin mugunta yau ma siffar tsakaka ta ɗauka ta yi tsinke can toilet inda Safeenatu ke wanka tun tuni.Da ga can saman katanga Gwaggo Hajara ke ƙarewa surar Safeenat kallo,cikin salon mugunta ta mayar da harshenta dogo sannan ta zuro shi tun daga can sama har ƙasa yana taɓa tile. Safeenatu ta yi wani ihu wanda bai sauka ko ina ba sai cikin kunnen ƴarta jaririya,kwacaaaa Gwaggo Hajara ta faɗo cikin ƙatuwar robar tafasasshin ruwan zafi....... Ga masu son complete na book ɗin nan akwai shi 800 ne via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank . DM +22795045822 [13/04 10:28] MRS SADAUKI: _____________________ MRS SADAUKI *MAITAR DARE* 8 Da wani mugun sauri Safeenatu ta yi tsalle ta koma jikin ƙofa tana kyarma ,idonta ƙur cikin robar wacce tsakakar ke ta ƙoƙarin fitowa daga ruwan .Ganin ta soma yin girma sosai yasa Safeenatu ta buɗe sakatar toilet ɗin zane a hannu ta fito Allah yayi sa'a babu kowa a tsakar gidan,dakyar ta yi ɗaurin ƙirji kafin ta nufi can ciki da gudu. “Ke lafiyar ki?” Gwaggo Habibah ta yi tambayar . Feenat ta dafe gefen zuciyarta da yake mugun bugawa ta ce “ tsaka...ka ce ta faɗa cikin ruwan da nake wanka” “Shi ne kike wannan haƙin? Kai Allah ya shirya min ke ban san lokacin da za ki girma ba” “Gwaggo ba normal tsakaka da kika sani ba ce, wannan ƙatuwa ce inda kin ga yadda halshenta ke da tsayi ya fi pampo fa” Shiru Gwaggo Habibah ta yi tana kallon Baby girl don kuwa a gaban idonta da tana yi mata wanka wani mugun haske ya fita goshinta tamkar an jefa kibiya. “Allah ni dai ba zan sake shiga toilet ɗin waje ba ƙila ma aljani ne” muryar Safeenatu ta katse mata ɗan guntun tunaninta. “Bari na je na gani ” cewar Gwoggo Habibah kafin ta miƙe ta fita zuwa Toilet ɗin tsakar gida,tun kafin ta ƙarasa ciki take jin nishin wahala . Ido huɗu suka yi da Gwaggo Hajara wacce zuwa yanzu tuni ta galabaita ta yi wani tsamo-tsamo cikin ruwan zafin ta kasa fita . Gwaggo Habibah ta yi wani murmushi tana kallon yadda ruwan suka yi baƙi tsabar yadda muguntar da ta shiryo ma Safeenatu ba ƙarama ba ce. “Ƙarshen alawa ƙasa! Yanzu wa gari ya waya? Shi dama ramen mugunta an ce ka gina gajere in kuma ka gina dogo kai za ka faɗa .Ai wallahi ba zan taimaka miki ba sai dai ki dawwama a ruwan zafin nan,in kuma kin ga na taɓa robar nan to wallahi cikin masai ne zan zubar da ku ke da ruwan” Gwaggo Habibah ta faɗa tana wani murmushin jin daɗi. Kamar daga sama tsakaka ta soma magana wacce ta kasance Gwaggo Hajara ,“ ki taimaka min Habibah na yi miki alƙawarin daga yau na zubar da makaman yaƙi” “Kar ma ki zubar ki yi ta riƙon su har sai Mahadi ya bayyana,ba dai maita ita ce jarinki ba? Ki ci gaba da yi wata rana mutuwarki za ki ci” tana gama faɗar haka ta fito daga toilet ɗin,sai kuma ta tuna duk wanda ya mutu a ruwa yayi shahada da sauri ta koma ba tare da ta ce komai ba ta ɗauko robar ta fito da ita tsakar gida tare da juye ruwan ga ƙasa. Tamkar acid haka turɓayar ta soma yin bori tana fitar da kumfa tsabar bala'in da ke tattare da ruwan,a kunyace Gwoggo Hajara tsakaka ta soma jan ciki ta nufi hanyar ɗaki. Ita kuwa Gwaggo Habibah ji ta yi kamar ta sa ƙafa ta laɓe shegiya kowa ya huta.Tana komawa ciki ta cewa Safeenatu “Ki shiga toilet to kafin na juye ruwan yi miki wankan” sai kuma ta fita ta ciko ƙaton bokiti da ruwan zafi,da ɗan ƙaramin towel ta soma yi wa Safeenatu wankan jego ita kuma tana ihu kamar wata ƙaramar yarinya. Macijin jiya ne ya sake bayyana a jikin macen yana wani naɗe jikinta,ita kuma ta buɗe ido taram tana kallonsa kamar mai wayo.Tsawon lokaci ya ɗauka tare da ita yana yi mata wasa kafin ɓace jin motsin su Safeenatu za su fito.Gefen gado ta zauna ta soma shayar da yaran kafin ta kimtsa cikin riga da zane,sai da Gwaggo Habibah ta gama wanka ita ma ta fito ta shirya sannan ta je ta kawo masu abinci suka ci daga nan suka wuce asibiti bayan sun karɓi kuɗi wurin Daddy.Lafiyarta da ta babys aka duba kafin su dawo gida,tuni kuma ƴan Barka suka fara zuwa in waɗannan sun fita wasu sai su shigo. SAKEENATU Tana rungume jikin Abbas ta ce “ Yau tana ɗaya daga cikin ranakun ovulation ɗina,yau na gama period ” cikin tsokana ya ce “ period ɗin ɗaya rana ” ta ja hancinsa ta ce “ eh na dai ji,inda ina jimawa kafin ta ɗauke ai da yanzu ba ka kasance da ni ba don jiya ne na gan ta” Ya gyara mata kwanciya kan ƙirjin nasa yana mai cewa “ Keent don Allah ki dinga bin Mamuh a hankali kin san ta tsufa,ban so kina yin abin da zai ɓata ranta ki guji ɓata mata don farincikina.Ina yi miki wani mugun so ne wanda na san ke ko rabin shi ba ki yi min” “To in sha Allah na yi ma alƙawari zan kiyaye,ai Ma'idar ma an tafi da ita” “A'a za ta dawo,sanin kan ki ne yadda nake mugun sonta ba zan iya yin nesa da ita ba” Wani daɗi ne ya luluɓe zuciyar Sakeenatu,ita ce shaida kan son da yake yi wa ƴarta duk da ta fito ba ta hanyar aure ba.Za ta iya cewa halarcin bai nuna mata ƙyama ba ne ya ɗunguza ta ga aurensa,soyayyarsa ma ba ta jima da samun gurbi a zuciyarta ba. “Ina son ki Keenat!” furucinsa ya katse mata tunani,ta yi murmushi mai ɗan sauti ta ce “ na gode” “Ke ba za ki faɗa kina sona ba? Keenat sai yaushe zan ji furicin so daga bakinki?” Ta laƙace masa hanci ta ce “ sai ranar da na haifo ma kyakkyawan Prince mai kama da kai” sai kuma ta miƙe ta je ta shiga toilet,shower ta sakarwa kanta tana tunanin saurayinta mahaifin Ma'idah.Ruwan hawayenta haɗi da na pampo suka haɗu wuri ɗaya suna zuba.Daga bayanta ta ji an rungume ta,da sauri ta juyo suna fuskantar juna kallo guda yayi mata ya hango damuwa a shimfiɗe a ƙwayar idonta.Zuciyarsa kuma ta basa ta yi kuka,bai tsaya tambayar ta ba ya ɗora bakinsa kan nata a wannan rana a kuma daidai lokacin nan Abbas ya shayar da ita zumar ƙauna mai haɗe da yayafin kalaman soyayya masu nuni da sadaukarwa.Ba tare da ta shirya ba ta ce “ I love You Abbas!” numfashinsa ne ya kusan tsaya wa tsabar murna da farin ciki,kamar wani ƙaramin yaro ya soma yi mata kuka saboda kawai ta ce tana sonsa. Shi yayi musu wanka ya shirya su,a ranar a gida ya ja su sallah har ta isha'i .Bayan sun salamce sun yi dogayen addu'o'i ya dube ta da kyau ya ce “ Keenat fatan bayan tafiyata duk salloli kin yi su kan lokaci kuma kin tsare su?” Da sauri ta sunne kai ba tare da ta basa amsa ba,yatsun ƙafarta ya soma ja mata tare da soma yi mata nasihar da ya saba game da mai wasa da sallah a ƙarshe yake cewa “ in kuma na ga kin ƙi yi zan kawo miki ƙanwa ustaziya” a shagwaɓe ta faɗa jikinsa ta ce “ to ai ina yi ko” “Kina yi ko za ki dinga yi?” “Duka biyun! Ba za ka koma asibiti ba?” “Tare za mu koma tashi ki shirya” da “ to” ta amsa kafin ta canza kaya suka fito,sai da ya tsaya ya saya musu fruits sannan suka isa asibitin.Da sallama suka shiga ɗakin Gwaggo Rahamu ce ta amsa yayin da Mamuh ta juya musu baya tana jin wani irin baƙin ciki ya turnuƙe ta saboda a yadda ta gansu cikin farin ciki suna nishaɗi ta san sun keɓe da junansu.Abbas ya ƙarasa yana mai cewa “ Mamuh ya jikin naki?” “Ka damu da ni ne ka sa ƙafa ka yi tafiyar ka? Wato Abbasi matarka ta fi ni ko?” ta faɗa cike da masifa tana juyowa. “Ki yi haƙuri Mamuh Allah dai ya baki lafiya ” ya faɗa kansa ƙasa. Tsabar fitina ta Mamuh sai cewa ta yi “ ina wakena?” Abbas ya ɗago da sauri yana kallon ta yana mai cewa “ wane irin wake kuma Mamuh yanzu da daren nan? Ga ayaba nan da lemu da apple na sayo ” “Na yi da kai na ce ka sayo? Ita waccar abar ai ta san wake nake ci mi yasa ba ta dafo ba?” “Yi haƙuri Mamuh gobe sai a daf....” bai rufe baki ba Mamuh ta saka kuka yana cewa “ shinenan tun da mata ta fi uwa” Da mugun sauri Sakeenatu ta ce “ bari na koma gida sai na dafo mata” Abbas ya ce “ to ki yi sauri” ta yi tunanin shi zai kai ta amma sai kuɗin ɗan sawu ya bata,tana zaune tana hawaye har suka iso gida ta biya shi kuɗin kafin ta wuce ciki. A gaggauce ta soma aikin tana mita “ an yi tsohuwa kamar mayya kullum wake yanzu nan in ban wanke shi ba sai ta sani mtsww ” ta ja tsuki tana dirje waken amma jin ita ma an ja mata tsuki yasa ta zabura tana dube-dube sai dai babu kowa.Watsar da tunanin ta yi ta ci gaba da aikinta wani tsukin ta kuma ji sannan ana magana ƙus-ƙus,gabanta ya faɗi jin tamkar ana tafiya cikin falo.Tana shirin fitowa aka ɗauke wuta,lalubo ta soma yi cikin duhu ko Allah yasa ta ɗauko wayarta ta kuwa yi sa'a ta samu jakarta hannunta har rawa yake ta zuge zip ta ciro wayar sai ta ga saura ƙiris batirin ya mutu alhalin a cike ta bar ta.Tana ƙoƙarin ganin ta kunna fitilar ta ji tamkar saukar huci kusa da ita,ta wani juyo da sauri ta inda take jin abin tare da haska hasken screen babu kowa sai ƙafafuwan ƙofato da ta yi arba da su babu kuma gangar jiki....... Domin samun complet book ɗin nan 800 ne via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 [13/04 10:28] MRS SADAUKI: _____________________ MRS SADAUKI *MAITAR DARE* 9 Babu shiri Sakeenatu ta saki wayar ta arta a guje,sai dai ta nemi ƙofar fita ta rasa saboda mugun duhun da ya mamaye gidan baki ɗaya.Cikin ƙanƙanan lokaci duk ta firgice,dakyar ta iya samu ta fito tsakar gida da lalabe zuciyarta sai ƙara tsananta gudu Waige-waige ta fara sai ta ga ashe kaf unguwar ne babu wuta,ba ta gama daidaita numfashinta ba wata baƙar mage baƙa ƙirin ta soma yin kuka miyau!miyau! Kukanta duk ya cika gidan. Ta ɗaga kai dakyar ta dubi inda sautin kukan ke fitowa,ido huɗu suka yi da magen wacce hasken idonta yake kamar na lantarki sai canza kaza suke.A hankali ta sauko daga katangar ta soma nufo inda Sakeenatu ke tsaye da gajiyayun ƙafafunta,Allah ya gani ba ta wani ba wai karatun addini muhimmanci ba dukkan lokacinta da hazaƙarta ta zuba su ne a harakar boko wannan ya sa ba ta iya wasu addu'o'i ba .A halin yanzu da take tsaye ta yarda kuma ta aminta rayuwarta na cikin haɗari,tabbas ta san wannan magen ba normal ba ce muguwa ce cutar da ita za ta yi. Ta na dab da ta kawo kusa da ita ta samu bakinta na furta “ la haula wala ƙuwata illa billah!!!” ƙiiii magen ta wani ci burki tana mai canza salon kuka zuwa na jarirai amma sam Sakeenatu ba ta yi gigin yin shiru da bakinta ba sai ma ƙaimi da ta fara wurin maimaita addu'ar.A gaban idonta magen ta soma mayar da idonta kamar na mutane kafin ta ruga a guje ta yi tsalle ɗaya ta haye katanga,daidai nan kuma aka maido wuta yaran unguwa suka hau ihun murna.Sakeenatu ta ja ajiyar zuciya tana mai yin hamdala ga Ubangiji,bakinta bai gushe ba yana ta furta lahaula wala ƙuwata illa billah a haka ta koma can ciki.Gas ɗin ta kashe saboda muguwar gajiya da ta saukar mata wacce ba ta san dalili ba,wayarta ta ɗauka Allah yayi sa'a babu abin da ya same ta abun mamaki kuma yanzu cajin wayar a cike yake saɓnin ɗazu da aka nuna mata ta kusa mutuwa. Lambar Nafisa ta kira,tana ɗauka babu wani tsaya wa gaisuwa ta ce “ Nafi ki turo min karatun nan da kike saurare don Allah duk dare” “Anty Sakeena lafiyar ki kuwa?” “Ki turo min karatun dai don Allah ina son saurare ” “Ok to bari na hauda data yanzu zan turo miki” “Yawwa ina jira” ta faɗa tare da kashe kiran,ita ma datar ta kunna babu jimawa kuwa karatun ya shigo suratul Baƙara ce ta turo mata sai Yasin .Tamkar abun tsiya network ɗin ya ɗauke ɗif ko ɗaya babu wanda ya buɗe,juyin duniya ta yi amma sun ƙi buɗewa har wayar ta kashe ta kunna amma network ɗin ya ƙi yi.Cike da damuwa ta sake kiran wayar ƙanwarta,tana ɗauka sai ta rasa abin da za ta ce mata kawai ta fashe da kuka.Daga can ɓangaren Nafisa ta ce “ subahanallah! Anty Sakeena don Allah mike faruwa? Mike damun ki?” Cikin muryar kuka take cewa “ Nafisa tsoro nake ji! A tsorace nake ji nake kamar ba ni ɗaya ba ce cikin gidan nan tamkar ina ....inaaa” ta kasa ida maganar saboda motsin da ta gani ana yi can cikin labule wanda ta tabbata kuma ba ɓera ne ba saboda girman halittar.Ihu ta fasa ganin ƙatuwar gafiya ta faɗo timmm da ƙasa,yayin da kuma wata ta biyu ita ma ta sake fitowa a guje ya kama waccan wacce ta faɗo a gaban idonta suka soma faɗa suna cizon junansu.Babu shiri Sakeenatu ta haye ɗaram kan bed ta na kuka,Nafisa na jin haka ta ziri hijabi ta fito ko Mamarsu ba ta sanar ma ba ta fito ta samu ɗan sahu.Allah yayi sa'a ba wani nisa ne sosai a tsakaninsu ba,da gudu ta shigo gidan tana ambaton sunan Allah daidai nan gafiyoyin suka yi ɓatan dabo hatta. Nafisa ta je ta rungume ƴar uwarta wacce da ace tana da cutar asuma da tuni numfashinta ya fita,“ yi shiru don Allah ya isa yi min bayanin mike faruwa? Ina shi Abbas ɗin?” “Yana asibiti wurin Mamuh,na dawo na dafa mata wake da shinkafa ne shi ne ake ta firgita ni” nan ta kwashe duk abin da ya faru ta shaida wa ƙanwarta. Nafisa ta ja dogon numfashi bayan ta saurare ta,sannan ta ce “ wannan duk sharrin miyagu ne shi yasa a kullum ake son bawa ya keɓe wani lokaci don nemawa kansa kariyar ruhi da gangar jiki ba wai gyaran duniyarka ba kawai.Ni wallahi na fara zargin Mamuh ɗin nan,kina dai ganin yadda Ma'idah ta caka mata cokali da dukkan alamu ta hango abin da idanunmu basu gani.In ba masifa ba cikin daren nan za ki dafa mata wake kamar mayya,ke ƙila ma ita ce.Tashi mu je ki yi alwala ai zama bai gan ki ba tun da kin ji kin gani aure a inda ba a ƙaunar ki” Da taimakon Nafisa ta yo alwala dama ita Nafisar kusan kowanne lokaci tana da alwala mace ce mai riƙo da addini ba ta da sake,hasali ma malamar makaranta ce a wata islamiyya. Karatun Alkur'ani ta soma koya wa Sakeenatu kamar wata ƴar yarinya haka take biyawa inda ta yi kuskure kuma ta gyara mata. “ Ki kasance kullum cikin tsarki bima'ana alwala saboda tana da muhimmanci sosai wurin bada kariya,ko sheɗanu suna shakkar mutum mai zama da alwala a koyaushe,ke ko period kike to ki yi abarki sannan ki riƙe azkhar na safe da maraice” “Amma ai kin san ban iya su ba ko?” “Ki koya mana anty Sakeena ,shi ilimi ai bai da ƙa'ida shekaru ko tsoho ɗan shekara ɗari zai iya shiga makaranta ballantana ke da ko talatin ba ki kai ba” “ Ni rubutun larabcin ne ke bani wuya ” “Zan nemo miki littafi mai fassarar Hausa ,sai na dinga koya miki yanzu bari na tura miki app ɗin Alkur'ani sai ki dinga saurare ” Ta karɓi wayarta ta tura mata tare da saita mata komai ta kunna sautin ya soma tashi,ta ce “ to ni zan tafi gida ko Mama ban sanar ma ba” “ Don Allah Nafisa kar ki tafi ki bar ni ki jira har Abbas ya dawo,bari na kira Mamar na shaida mata” haka suka yi kuwa,tun suna jiran Abbas har ƙarfe sha biyun dare bai zo ba a tare suka fito suka rufe gida da ko ina sannan suka je suka kwanta. A can asibiti kuwa bayan fitar Sakeenatu,Gwaggo Rahamu ta yi wani kishingiɗa ga kujera kamar mai bacci nan kuwa ruhinta ne ta soma fitar wa daga gangar jikinta.Sawun Sakeenatu ta bi,hasali ma ta rige ta zuwa gidan duk abin da take yi akan idonta hanyar farko da ta soma bi shi ne tafiya ta shiga tunanin mai kula da nepa na unguwar ya ɗauke wuta ba tare da shi kansa ya san dalili ba a cikin wannan duhun ne ta yi ta yi wa Sakeenatu mugunta.Da ta koro ta da addu'a shine ta biya wurin wasu miyagun ƙawayenta ta basu address suka je a siffar gafiya,su ma ba su bar gidan ba sai zuwan Nafisa. Abbas na daga can gefe Mamuh na yi masa hira tana murmushi saboda duk abin da ke faruwa ita tana gani saɓanin shi Abbas ɗin.Bayyanar esprits biyun yasa yanayin shaƙar iskan ɗakin ta sauya saboda tsabar muguntar su, wannan karon hatta Abbas sai da ya ji wani iri.Har yanzu Gwoggo Rahamu ba ta farka daga baccin ƙaryar da take ba,cikin hirarsu ta ƴan duniyar ɓoye suke bata labarin yadda suka firgita Sakeenatu tana ta yin kuka. “Na gode sosai ƙawayena,kar ku manta in kun gama yawon Maitar dare ku biyo ta nan mu sake komawa mu uku mu haɗa ƙarfi mu shayar da ita mamaki” baƙin ruhin Gwaggo Rahamu ya faɗa ,suka yi dariyar mugunta tare da ɗaukar mata alƙawari kafin su bar wurin.Cikin ƙwarewa ta dawo da ruhinta a gangar jikinta,ta dubi Abbas tana mai cewa “ bacci ya ɗauke ni duk yau ban rintsa ba,ina sauran waken ni ma na ci yunwa nake ji” Shi Abbas sam ya manta da wani zancen wake saboda yadda Mamuh ke masa hira,sai yanzu ya tuna Sakeenatu ta je gida dafawa.Da ya duba agogon hannunsa ransa ne yayi mugun ɓaci,“ uwar tamu ai ba ta dafo ba tana can tana gantalin da ta saba,ah to dama su likitoci ba su da kamun kai tsakaninsu da abokan aikinsu suke neman juna in aka ce miki tana can asibiti wani ƙato ya taushe kar ki yi gardama” Mamuh ta faɗa ,yayin da Gwaggo ta karɓe “ i sosai ita ma wannan shegiyarta ta ai shugabansu ne ya ɗirka mata cikin ya bar yaronmu da wahala,wai Abbasi wai ya ƙaƙaba maka aurenta?” Kasa cewa komai yayi,haushi goma da gomiya tara ya rasa da wane zai ji abin ka kuma da zuciyar namiji sai ya ji zargi ya ɗarsu a ransa.Da ya nuna zai je gida Mamuh ta hana shi tafiya ta hanyar amfani da tsafinta,haka suka dinga kwaso sharri iri-iri suna yaɓa ma Sakeenatu sosai kuma suke samun gurbi a zuciyarsa.Can waje ya koma ya kwanta kan wani banci yana ta tunanin rayuwa baya yadda neman aurensa ya kasance yadda sam Sakeenatu ba ta samu shaidar ƙwarai ba ga mutanen unguwa amma ya rumtse ido ya ce sai ita . Ƙarfe biyu da rabi na dare ƙawayen Gwaggo Rahamu suka biyo mata,kafin su yi tsinke gidan Sakeenatu.Sai da suka shiga kitchen suka cinye kaf abincin da ta dafa sannan suka dawo falo suka fara shawarar abin da za su yi mata,suna dariyar mugunta suka tura ƙofar falon sai dai da zarar sun yi niyyar ɗora ƙafarsu a tile ɗin bedroom sai su ji tamkar cikin garwashin wuta ne suke ɗora su.Gwaggo Rahamu ta ƙanƙance ido tana kallon gefen Nafisa inda kusan kanta ta ɗora wayarta ne sautin karatun Alqur'ani na tashi a hankali wanda ba ma a jinsa sosai,kamar ta san suna nan kuwa sai ta kai hannu ta ƙara volume a tare suka saki wani ihu wanda sai da gidan ya girgiza a firgice Sakeenatu ta farka tana zarar ido... Mai son complete 800 ne via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 [13/04 10:28] MRS SADAUKI: _____________________ MRS SADAUKI *MAITAR DARE* 10 A wahalce Gwaggo Hajara ke bin bango don isa ɗakinta,fatar nan tata ta tsakaka duk ta yi wani taushi ta fara fitar da wani fanko.A yadda bango ke zuzar fatar cikinta ji take kamar ta yi ta ƙurma ihu sai dai ba dama sata lahira! Tana isa ɗakinta ta ɗauki siffa ta mutum nan ne fa ta yi tozali da yadda duk jikinta ya kumbura yayi ja kamar wacce aka soya,mai ta ɗauko ta shafe jikinta da shi tana matsar ƙwalla tare da jin tsanar Safeenatu na sake feso mata daga can ƙasan zuciyarta. A fili ta furta “ sai na wulaƙanta rayuwarki,sai na saka kin tozarta a duniya,sai na shayar da ke gubar azaba wacce sai kin gwammaci mutuwa akan rayuwarki. Ke kan ki Habibah ba zan bar ki ba zan ɗora miki karatu da alamu har yanzu ba ki ji jiki ba shi yasa kike taimaka wa wata wurin ruguje plan ɗina” shiru ta yi jin an turo ƙofa.Daddy ne ya shigo da sallama a bakinsa,ba ta amsa ba sai ma saurin jawo hijabi da ta yi ta saka duk ta luluɓe jikinta. “Ni kam Hajara lafiya kike? Kin ga yadda fuskarki ta yi suntum sai huci take kamar ƙullun wainar da ya ji yis?” Daddy ya faɗa yana ƙare mata kallo.Wani ƙululun baƙin ciki ne ya ƙara turnuƙe Hajara ta ce “ uwar waina ce....” ba ta ida kai aya ba ta ji yatsun Daddy biyar kan kuncinta,shaye da mamaki take kallonsa nan ta hango wani baƙin tauraro tsakiyar goshinsa wanda ko shakka babu aikin Habiba ne ta tura masa shi. Ba ta gama dawowa daga duniyar mamakin da ta je ba Daddy ya soma magana cikin masifa,“ wato abun naki ya fara zama iskanci,daga tambaya shine za ki zagin uwata saboda kin san yau za ta zo.To tsaya ki ji Hajara duk wata tijararki ki tattara ta ki ajiye wuri guda muddin Hajiya ta koma da baƙin cikinki gida to wallahi akan aurenki.Ki tashi ki ɗora girki tsabar lalaci muna da mai jego a gida amma kin zo kin shige ɗaki kin haye gado tare da saka hijabi kamar matar liman kowacce za ta yi aikin ƙwarai” yana gama faɗa ya nufi ƙofa,sai kuma ya juyo ya ce “ Murjanatu na kan hanya sai ki fara shirin tarben ta” kawai ya fice. Gwaggo Habibah da ke zaune kan kujera a falo ta saki wani irin murmushin nasara,tun da uwarta ta haife ta yau ce ranar farko da ta juya taurarinta na baiwa ta yi aiki da su.Tun bayan da ta yi wa Twins wanka ta shirya su sannan ta bai wa uwarsu abin da za ta ci kawai ta fito falo ta zauna,Daddy na fitowa ta soma yi masa transfer ɗin tauraron ta hanyar kallonsa tsakiyar ido da farko har ya tambaye ta lafiya sai kuma yayi shiru jin sabon abu a tattare da shi. Duk abin da yake faɗa wa Gwaggo Hajara sarai ta ji alamun aikinta yayi kyau,ta saki murmushin nasara tana mai cewa ‘ mijinki zai zame miki kumurci,da haka zan raunata muguwar zuciyarki’ “Habibah karɓi wannan ko kuna da buƙatar wani abu sai a ɗauka ciki” Daddy ya faɗa yana mai katse mata tunanin zuci.Ta karɓa tana mai cewa “ Yaya Ɗayyabu na ce bayan biki sai Safeenatu ta koma can gida wurin Hajiya ko?” “Saboda me? Ba a nan za ki zauna ba?” “Eh to ni ma da haka na ce ɗin amma sai na ga kamar anty Hajara ba ta son zamana tun da na zo idonta kamar za su faɗo tsabar yadda take jifana da mugun kallo” Ran daɗi ya ɓace, yanayin fuskarsa ya canza tuni tauraron goshinsa ya ƙara yin baƙi ba tare da ya ce komai ba ya ƙara komawa ɗakin Gwaggo Hajara ita kuwa Habibah har da wata dariyar mugunta ta yi tare da tashi tana taka rawar murna. Daddy na shiga ɗaki ya yi wa Hajara wankin babban bargo,ko ina ana jin muryarsa yadda yake yi mata masifa in ta je yin magana kuma sai ya gwaɓe bakin.Da wannan baƙin cikin ya fita ya bar ta,sai da ta sha kuka wiwi sannan ta fito ta ɗora girki babu jimawa kuwa sai ga Hajiya ta zo .A ladabce Gwoggo Hajara ta gaishe ta wanda sosai ita hajiyar ta yi mamaki don rabon da ta yi mata irin wannan ladabin tun ranar da Ɗayyabu ya kawo mata ita a matsayin matar da zai aura.Cikin sakin fuska ta amsa tare da cewa “ to barkarmu Safeena an sauka Allah raya kan sunnah,kin samu mai taya ki aiki da kuma miji” Hajiya ta faɗa tana murmushi a doli ita ma ta yi murmushin yaƙen a can ƙasar zuciyarta tana cewa ‘ an haifo mana masifa dai aljanar jaririya muguwa wacce ta yi gadon jaraba ’ “Zan shiga daga ciki” hajiyar ta faɗa tare da nufar ɗakin Safeenatu,cike da murna ta zauna tana kallon jariran Gwaggo Habibah ta ɗauki namijin ta bai wa Hajiya ta karɓa tana mai kai masa sumba haɗi da yi masa addu'a sannan ta miƙa shi.Ana ɗora mata macen jikin Hajiya ya ɗau kyarma kamar mazari,murya na ɗan rawa ta ce “ wane suna za a saka musu?” “Basheer da Baseerat ” Habibah ta bata amsa tana murmushi tana kallon mahaifiyarta wacce kambun muguntar Gwaggo Hajara duk ya dabaibaye ta yanzu kuma ya fara barazanar tarwatsewa. Hajiya ta ce “ karɓar ta” tana mai miƙo Baseerat don ruhinta ya soma yin rauni, Habibah ta ce “ Hajiya don Allah ki riƙe t...” ba ta kai ƙarshe ba Hajiya ta miƙe ta je ta shimfiɗe Baseerat a shimfiɗa,sai aka yi rashin sa'a safar da aka saka ma hannunta na hagu ta fita wani mugun haske ya fito ya shiga ƙirjin Hajiya saura ƙiris ta faɗi saboda yadda fitilun idonta suka rufe jiri kuma ya ɗebe ta. Safeenatu dai na daga gefe tana kallon abubuwan ban al'ajabi , Gwaggo Habibah ce ta kamo Hajiya ta taimaka mata ta zauna.Kamar mai cutar huka haka numfashinta ke fita,ruwan sanyi ta nema da sauri aka bata ta shanye ƙatuwar gora. “Habibah bani pilow bacci nake ji” cewar Hajiya ,da sauri ta ɗauko ta miƙa mata ita kuma ta kwanta babu jimawa bacci mai nauyi ya ɗauke ta . Safeenatu ta ce “ Gwaggo Habibah ni fa na fara jin tsoron lamarin Baseerat kina dai ganin abin da ya faru, wannan ai ba zan fita da ita unguwa ba gudun ta jawo min masifa ace mayya ce ma” Da mugun sauri Habibah ta katse ta “ kar na sake jin kin faɗi haka,saboda ƴarki ba mayya ce ba ƴar baiwa ce” “To amma ai wasu ba za su ganin haka ba ko? Tun yanzu tana jaririya tana haka ina ga ta girma?” Gwaggo Habibah ta yi murmushi ta ce “ Safeenatu bari dai na soma ɗan guntsira miki labaran duniyar ɓoye, kowane mutum da kike gani a duniyar nan yana da matriculation na sama.Ko kuma lambar sirri ta samaniya,da wannan ne in aka sayar da ruhin mutum daga lokacin matriculation ɗinsa ta saminiya sai ta canza.Duk wani ɗan Adam kasance yana da taurari iri-iri waɗanda suke taimakawa wurin gudanar da al'ammuran duniyarsa.Ya zama doli kowa ya kare taurarinsa ya basu tsaro,muddin ka yi sakaci da su kuma to wannan mutumin zai iya zama cikkaken maƙasudi wurin tallafawa masu sayar da taurari su ƙwace masa su.” Safeenatu ta katse ta da cewa “ ta ya za a ƙwacewa mutum taurarinsa alhalin mallakinsa ne?” Gwaggo Habibah ta bata amsa da “ ba ki taɓa jin labarin wata ma'aikaciyar saloon ba mai gyaran gashi? Ki nemi littafin Mrs Sadauki na MAITAR IDO a nan duk za ki samu cikakken labarin.Ki sani cewa matsafa don su kama ruhinka ma abu ne mai sauƙi,abin da suke buƙata shi ne kawai keɓaɓen abu na gaskiya ta atomatik da ke fitowa daga mutumin da ake son cutarwar,kamar gashinsa,sunansa,date ɗin ranar haihuwarsa,zufar jikinsa wato tufafin da ya saka ba a wanke ba,ko kuma jinin jikinsa.Daga lokacin da matsafi ya riƙe ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan zai iya buɗe katinka na samaniya kuma ya karɓe ƙarfin ikonka wato power daga nan sai yayi abin da yake so” A sanyayye Safeenatu ta ce “ duk Baseerat za ta iya yin wannan? Gaskiya ni dai ban so in kin san hanyar da za a toshe wannan baiwar tata ni dai ki taimaka min don ina ji a jikina muddin aka bar ta da ita a gaba za ta zame mana masifa” Gwaggo Habibah ta yi mata wani irin kallo irin na ba ki da hankali kafin ta je ta ɗauki safar hannun ta saka ma jaririyar wacce ta buɗe ido sai kalle-kalle take kamar mai wayo,kafin kuma ta kafe idonta ga madubi Gwaggo Habibah ta yi kasaƙe tana kallon Baseerat a sannu a hankali ta ga idon yarinyar na sauya kala har suka zama farare tasss babu ɗigon baƙi,wani abu kuma ya soma fita daga bakinta yana bin direction ɗin madubi.Habibah ta ja wani dogon numfashi don kuwa ta fahimci Baseerat za ta yi tafiya ne ko kuma yawon buɗa ido wanda dayawan mutane na yinsa ba tare da sun san mine ne ba.Sai ka ji tamkar jikinka ya zama gawa kana son tashi daga bacci amma ka kasa tamkar an danne ka da dutse,har kwatanta buɗe ido ake amma baka iyawa saboda ruhinka da yayi balaguro ya bar gangar jikinka a kwance. #SAKEENATU Gefen da Nafisa ke ta sharar bacci ta duba kafin ta ɗaga kanta sama tana kallon yadda rufin ɗakinta ke wani lomaƙawa tsabar yadda ake tafiya a guje.Kukan jaki da na kare ga kuma na mage duk a lokaci guda,gefe guda kuma wata siririyar murya take ji tana kiran sunanta.Idonta ya ciko da hawaye,fitsari take ji amma tsoro ya hana ta tashi.Nafisa ta soma tayar wa,ita kuwa dakyar ta buɗe ido ta ce “ mine ne ?” “Fitsari nake ji” ta bata amsa kamar wata ƙaramar yarinya,cikin magagin bacci Nafisa ta ce “ ki je ki yi mana” sai ta koma baccinta.A hankali Sakeenatu ta zuro ƙafafunta ƙasa a tsorace ta shiga toilet ko Bismillah ba ta yi ba ballantana karanto addu'a,a tsorace ta je ta haye WC ɗin ta soma fitsari sai kuma jikin ya soma kyarma ganin ruwa na ta ɓulɓulowa ta ƙasan tile suna cika toilet ɗin ko kafin ta ƙyafta ido sun kawo mata a wuya ta yunƙura za ta tashi amma sai ta ji tamkar an saka super glue an manna ta a jikin WC ɗin ta ƙurma wani uban ihu wanda dama su mugayen shine suke jira ai kuwa suka tsaga rufin ɗakin ji kake ƙiiiiii kamar suna yaga zane.Idon Sakeenatu duk a waje take kallon yadda bindi mage,na kare da kuma idon wata baƙar mujiya a daidai wurin da suka tsaka.Cike da mugunta suka diro toilet ɗin wanda yayi daidai da tsinkewar numfashin Sakeenatu..... [13/04 10:28] MRS SADAUKI: MRS SADAUKI *MAITAR DARE* 11 Duk da Sakeenatu ta suma hakan bai sa mugayen nan sun ƙyale ta ba,haka suka ajiye mata cutar a jikinta kafin su bar ta nan yashe a toilet.Cike da murna suka koma asibiti suka dinga bai wa Mamuh labarin abin da ya faru,cike da mugunta ta ce “ gobe da safe da hannunta za ta dafo wake ta kawo min ,daga nan kuma zan datse alaƙar farin cikinsu ita da Abbas zan maye mata gurbinsa ” duk suka sa dariya suna ƙara tsara mata wani salon muguntar. Washegari Kiran sallar asuba ya tashe da Nafisa,ta sauka daga bed ta shiga toilet nan ta ci karo da Sakeenatu a yashe babu numfashi.Hankalinta a tashe ta cika bokiti da ruwa ta zuba mata,ta ja ajiyar zuciya kafin kuma ta soma kuka cikin firgici.Nafisa ta kamo ta tare da fiddo ta haɗi da tambayar ta,duk a tsorace take wannan yasa ta kasa yi wa ƙanwarta bayani.Ganin haka yasa ita kuma ta je ta yo alwala ta yi sallah,bayan haka ne ta matsa wa Sakeenatu ta je ita ma ta yi sallar.Ko wanka ba su yi ba ta ce “ Nafisa tashi mu je gida wallahi tsoro nake ji” haka suka runguɗa suka je can gidan Mama wacce ke ta ƙoƙarin hura wuta domin ta ɗora ɗumame,tana ganinsu ta san ba ƙalau ba.Kamar wata ƴar yarinya haka ta je ta rungume mahaifiyarta tana wani sabon kukan,“ Subahanallahi! Nafisa mike faruwa?” “Wallahi Mama ban sani ba ni ma na yi ta tambayar ta amma ta ƙi faɗa min,alamu dai sun nuna tsorata ta ake yi a can gidan nata” Nafisa ta bata amsa. Mama ta ce “ to Allah ya sawwaƙa,ku wuce ciki bari na kira malam na shaida masa ” Can cikin mitsitsin ɗakinsu suka shiga,Ma'idah na kwance sai bacci take ba ta farka ba.Sakeenatu ta ɗauki abarta ta rungume ƙam kamar an ce za a raba su,mugun mafarkin da ta yi kan Ma'idar ya dawo mata a kai.Ta lumshe ido ruwan hawaye na kwaranya a kumatunta,ta yi tunanin kakarta ta yanke saƙa,ba ta taɓa tunanin za ta sake yin ƙunci a rayuwa bayan wanda ta yi a baya ba tun lokacin da Abbas ya shigo rayuwarta komai ya dawo mata normal ashe da sauran kallo a sama.Tsohuwar shuɗaɗiyar rayuwarta ce kwanyarta ta soma yi mata tariya,cikakken sunanta shi ne Sakeenatu Abubakar,ƴar gwagwarmayar rayuwa mai zuciya cike da burin zama wata aba a duniya.Karatun boko shi ne abokin da ta riƙa sannan kuma tubali don gina rayuwa mai inganci,sai dai ƴan magana na cewa rashin sanin ya fi dare duhu.Sakeenatu ba ta taɓa sanin cewa ba sanadin boko ne za ta zubar da mutuncinta ba,zuwanta jami'a shi ya ƙara buɗe mata ido sosai ta waye ta zama ƴar gayu,ƙwazonta a wurin karatu shi yasa ta ciri tuta a wurin malaman makaranta kusan duk maganarta suke suna yabon baiwar da Allah yayi mata banda malam Agali wanda tun ranar da ya ɗora idonsa kanta yake jin mugun sha'awarta saboda ta haɗu ta kowanne fanni.A wata rana Laraba ce wacce ta kasance ranar farko da ya fara ɗana mata tarko da kuɗi,“ki hau taxi” ya faɗa cikin taushin murya a gaban ɗalibai ba tare da ya ɓoye ba kuma ya sakar mata murmushin nan nasa wanda yake haukata ƴan matan makaranta da na wajensu .Ba za ta cewa tana sonsa ba,amma ita ma tana cikin waɗanda yake burge su saboda yadda yake da kyau kamar Balarabe ga baƙar sumar kansa ko wata macen ya fi sannan ɗan gayu ne kullum cikin shiri mai kyau yake.Ƴan matan ajin suka hau yin shewa suna taɓi tare da cewa yau dai an samu wacce ta sace zuciyar Dr Agali,da ido ta bisa kawai lokacin da yake fita daga ajin yayin da ɗalibai duk suka dawo kusa da ita kowacce na tofa albarkacin bakinta.Sakeenatu ta ji wani irin girman kai ya zo mata tare da alfaharin ita ce ta ciri tuta,cours ɗin da aka yi musu na gaba sam ba ta fahimci komai ba saboda tunanin malam Dr Agali.Ba ta buɗe ƴar enveloppe ɗin kuɗin ba sai da ta je gida, kuɗi ne ƴan jika-jika sabbi da su har guda goma.Ta kai su kusan hancinta ta shaƙi ƙamshin turarensa,tuni jikinta ya mutu murus ta na shirin saka kuɗin a jaka ne ta lura ɗaya daga cikin takardun kuɗin an rubuta lamba a jiki.Kamar wacce ake tsikara ta ɗauki wayarta ta loda lambar sannan cike da waswasi ta tura masa saƙo babu jimawa ya kira ta,kamar wani mutumin ƙwarai har da yi mata sallama ta amsa tare da ce masa “ fatan ka je gida lafiya?” Cikin muryar nan tasa ta buzaye waɗanda ba su ida iya Hausa ba ya amsa mata da “ a'a ina wata asibiti an kira ni in tiyata” Ta saki murmushi mai sauti ta ce “ ina son ganin ranar da za a ce Sakeenatu na yin tiyata” “Lokacin zai zo ke dai ki ci gaba da dagewa wurin yin karatu,na ji malamai sai yabon ki suke ashe ba a cours ɗina ne ba kawai kika ƙware” nan ma murmushi mai sautin ta yi kafin ta ce “ burina shine zama babbar likita wacce duk duniya za ta yi alfahari da ita,ana dinga nuno ni a TV” “Kina iya barin Nijar Keenat?” Dr Agali ya tambaye ta,kai tsaye ta basa amsa da “ eh sosai sai in gwamnati bai ɗauki nauyin karatun nawa ba” “To ki fara shiri in sha Allah ni nan zan sa burinki ya cika” “Keee Sakeenatu keee!” Mama ta faɗa tana mai kamata dundu wanda shi ya katse mata tunanin shuɗaɗiyar rayuwarta,da sauri ta dawo hayyacinta tana mai kallon Mama wacce ta janye Ma'idah da sauri tana mai ci gaba da cewa “ kawai ki kama yarinya ki riƙe gam tana kuka da ranta amma kin ƙi sakin ta” Sam ita ba ta san riƙon da ta yi wa Ma'idar ya cutar da ita ba,cike da takaici da zugin da zuciyarta take yi ta tashi ta fita ta cika bokiti da ruwan ta shiga banɗaki.Wanka take son yi amma tunanin Dr Agali sai ƙara kawowa kwanyarta farmaki yake,abin da ya faɗo mata a rai a yanzu kuma shi ne ranar da ya kira ta ya shaida mata Visa ɗinta ta fito ta zo ta karɓa bai jin daɗin jikinsa.Ba tare da wani tunani ba ta je gidan nasa kamar yadda yayi mata kwatance,duk a tunaninta yana da mata amma sai da suka shiga ciki ne ta ga shi ya bata ruwa sannan ya kawo mata lemu wanda ya zubar da shi a jikinta da gayya har tufafinta suka ɓace.Ta wani rumtse ido don takaicin ganin video yadda Dr Agali ya ɓalle maɓallan rigarta ya cire ta ya bar ta daga ita sai bra ya je wanke mata ita duk ta yi tunanin ƙauna ce ta kawo haka sai bayan ya dawo ne ya soma yi mata wasu zafafan romance.“ Ni fa dama ba zan yi miki komai ba, wannan ɗin ma ban san ya aka yi ya faru ba ki yi haƙuri ba zan sake ba sai bayan aure” Dr Agali ya faɗa lokacin da ta sakar masa kuka. “Anty Sakeena don Allah ki aje tunanin nan gefe ki yi wanka ki fito ga malam nan ya zo” Nafisa ta faɗa daga bakin ƙofa.Sai a lokacin Sakeenatu ta fara wankan ,bayan ta fito ta je ta gaishe da malam wanda ya kasance ƙanen Mama ne.Cikin garwashin wuta ya zuba ƴaƴan habbatu sauda hayaƙi ya turniƙe ɗakin,idon Sakeenatu duk suka fito waje ta soma tari kamar ranta zai fita shi kuwa karatu ya soma nan lamarin ya ƙara yin gaba don tuni ta soma yin kuka .Tsawon lokaci kafin ya bar ta haka nan,magani ya bada wanda za ta dinga shafawa da hayaƙe jikinta da kuma gidan.Bayan tafiyarsa ne ta samu ta ci abinci,wunin ranar dai Mama haka ta ƙare shi wurin yi mata nasiha dab da magrib Nafisa ta yi mata rakiya zuwa gidanta.A tare suka yi gyaran gidan da girki kafin ta yi wanka ta shafa man da malam ya bata ta kuma yi turare. A can asibiti kuwa tun safe da Abbas ya bar su bai koma ba,kuɗi kawai ya bar musu hakan bai yi wa Mamuh daɗi ba.Ana yin sallar magrib ba tare da likita ya sallame ta ba Gwaggo Rahamu ta haɗa tarkacensu suka fito a ɓoye.A bakin hanya suka samu adaidaita wacce za ta kawo su gida ,suna tafe suna hira “ ai tun da kika ga bai dawo ba to tabbas babu makawa da ya koma gida karuwanci ta yi masa kin san halin namiji kan mace sakarai yake zama” Gwaggo Rahamu ta faɗa . Mamuh ta tsuke bakin nan nata ta kasa cewa komai saboda baƙin cikin da ke addabar baƙin ruhinta,gani take yi ma tamkar adaidaitar ba ta gudu. Suna isa gida tun a bakin ƙofa suka canza kalar idonsu daga na mutum zuwa na mugunta,sai aka yi rashin sa'a Nafisa na tsakiyar falo tana hayaƙa hantiti da tazargade .A tare suka shigo,a tare kuma suka saki ihun azaba suna masu faɗuwa ƙasa suna yin wani irin huci a gaban idon Nafisa suka rikiɗe suka zama jibga-jibgan macizai kowa yace shi ba ma matsoraci ne ba to bai ga abin tsoron ba .Da wani mugun sauri Nafisa ta mangal ɗin hannunta mai cike da garwashi,da azama ta nufi hanyar ɗakin Sakeenatu sai dai kafin ta isa Gwaggo Rahamu ta yi wani uban tsalle ta naɗe handle ɗin ƙofar da bindinta tana mai buɗe ƙaton bakin,Nafisa na shirin komawa baya ta ji ana bin ƙafafunta wanda kuma tunaninta da ruhinta tuni sun shaida macijiya Mamuh ce...... [13/04 10:28] MRS SADAUKI: _____________________ MRS SADAUKI *MAITAR DARE* 12 Ido ta lumshe jikinta na ci gaba da kyarma,tuni Mamuh macijiya kuma ta ɓullo kanta tsakanin ƙirjin Nafisa ta fiddo halshe ta lashi fuskarta,yawunta masu mugun ɗohi suka daki hancin Nafisa.Ba tare da ta buɗe ido ba ta buɗe bakinta murya na rawa can ƙasan maƙoshi kamar mai yin raɗa ta soma karanto wasu ayoyin Alkur'ani da ke cikin suratul Yusuf daga aya ta 79 har zuwa 82 .Jikin Mamuh macijiya ne ya soma yin sanyi tsabar yadda ayayoyin ke dagargaza ruhinta musamman da ya zamana Nafisa ta soma ɗan ɗaga murya.Sululuuuu Mamuh macijiya ta faɗo daga jikin Nafisa ,a mugun tsiyace Gwaggo Rahamu ta bi ta ƙarƙashin ƙofa ta shiga ɗakin Mamuh don kuwa ƴan magana na cewa in ka ga gemun ɗan uwanka ya kama da wuta to kai ka shafa wa naka ruwa. Nafisa na jin saukar macijin ta buɗe idonta a hankali tare da sauke su ƙasa inda Mamuh ke kwance har yanzu cikin siffar maciji sai wani irin numfashi take fatar cikinta na lotsawa kana gani ka san ta wahala. Nafisa ba bakinta bai gushe da ci gaba da yin duk addu'ar da ta zo bakinta ba,a yadda take tsayen suka ƙure juna ita da Mamuh wacce duk wanda ya san ta to tabbas in ya ga macijin zai shaida wannan idon na Mamuh ne.Nafisa ta saki wani murmushin nasara lokacin da ta ga hawaye sun fara fita daga idon macijiyar,ta sani sarai har da kunya da gajiya suka hana Mamuh ƙoƙarin guduwa don babu abin da Mayu suka fi tsana kamar asirinsu ya tonu wannan yasa Nafisa ta nufi ɗakin Sakeenatu.Tana shiga daidai ita kuma ta fito daga Toilet ta yi wanka ƙugunta ɗaure da towel,“wani wankan kika sake yi?” Nafisar ta tambaye ta ba tare da ta nuna mata alamar wata damuwar ba. “Eh wallahi,maganin nan da na yi hayaƙi da shi sam babu daɗi shi yasa na yi wanka” Sakeenatu ta bata amsa tana mai kallon Nafisa,“Me? Wannan kallon fa?” “Fuskarki ce nake ganin kamar tana min wani iri” “Wani iri kamar ya fa?” Nafisar ta tambaya tana mai shafar fuskarta a daidai wurin da Mamuh ta lasa. “Babu komai! Bari na shirya na san yanzu Abbas zai shigo” “Ni zan yi sallah” cewar Nafisa tare da shiga Toilet,har ta gama alwala tana tunanin abin da ya faru da ta zo ta yi sallah sosai ta yi addu'ar neman tsari. Sakeenatu ma ta yi sallah tare da fara bitar karatun jiya da aka koya mata,in ta yi kuskure sai Nafisa ta gyara mata suna nan zaune har aka kira isha'i suka miƙe suka gabatar sai bayan sun ida ne suka fita falo. Nafisa ta dubi daidai wurin da ta bar Mamuh a ɗazu,tuni capet ɗin yayi alamun datti. “Anty Sakeena ni kam ina mai aikinki?” “Wa Fa'iza ? Wallahi kin ga shaf na manta da zancen ta.Ga shi kuma ba waya ce da ita ba ballantana na kira ta amma gobe in ba ta zo ba zan je gidan nasu na gani tun da babu nisa nan baya ne gidan Fulanin nan” “Oh! Can take ashe,tun da babu nisa bari na je na dubo” Kafin Sakeenatu ta bata amsa Abbas yayi sallama tare da shigowa,duk fushinsa ne ya ɓata nan take ganin uban adon da matarsa ta yi. “Ina wuni Ya Abbas ?” Nafisa ta gaishe shi tana mai yin murmushi don tana mugun sha'awar soyayyar antynta da mijinta,ba ƙaramin so yake yi mata. “ Lafiya lau Nafi ya gida?” ya amsa. “Alhamdullah” ta faɗa tana mai fita,ita kuwa Sakeenatu kamar wata yarinya haka ta wani rugo da gudu ta faɗa a jikinsa tana kuka.Abbas ya lumshe ido ya na mai cewa “ mene ne kuma na yin kuka uhum?” ba ta basa amsa ba ta dai lafe a jikinsa,tsawon lokaci suna a haka kafin ta hauƙura ta ja shi zuwa cikin bedrom ɗinsu.Da taimakonta yayi wanka ya shirya cikin ƙananan kaya sannan suka fito suka ci abinci,cikin hira ne take faɗa masa ba ta da lafiya har sai da ta je gida. Ya ja dogon numfashi kafin ya ce “ni kina Keenat ban san abin da ke damuna ba yau gani nan dai” “Allah kawo mana sauƙi” “Amen!” FA'IZA Tun da lamarin nan ya faru da ita duk jikinta ya zama wani iri,tun da take ba taɓa jin makamancin abin da ta ji ba a ranar nan.Tana da saurayi don har manya sun shiga zancen amma duk tsawon lokacin da suka ɗauka ita tun can ba ta taɓa jin sha'awarsa ba don a tunaninta ma ba ta da lafiya ne tun da ta ji ana faɗar akwai matan da basu jin feeling.Sai ga shi babban al'amari ya faru da ita mai kamar mafarki kamar zahiri an yi wasa da sassan jikinta,a ranar da ta isa gida kasa cin abinci ta yi.A washegari kuma ta tashi da zazzaɓi dalilin da yasa ba ta je aiki ba,yanzu ma tana kwance kan tabarma ta shafe jikinta da wani maganin zazzaɓi sai ga sallamar Nafisa.Duk da gidansu bai da ƙwan lantarki zamani amma suna kunna uban sanjo wannan yasa ta gane Nafisa duk da ƙarancin haskensa.Ta tashi da sauri tana mai cewa “sannu da zuwa” Ita kuwa Nafisa gaisa wa take da Mamar Fa'iza wacce ba ma sosai take jin Hausa ba,ta zauna kan tabarmar tana mai cewa “fatan dai lafiya? Anty na ta jira shiru ba ki zo aiki ba” “Zazzaɓi ne ya rufe ni amma da sauƙi gobe zan je in sha Allah ” Fa'iza ta bata amsa. “Allah ƙara lafiya,ni zan koma” cewar Nafisa tare da miƙewa,har ƙofa Fa'iza ta rako ta sai a lokacin kuma ta yi mata tambayar “ni kam Fa'iza abin da ya faru da ke gidan anty Sakeenatu dama kina yin haka?” “A'a wallahi ban taɓa yi ba” “To ki dage da addu'a kin ji ko,saboda yanzu duniyar sai a hankali” “To na gode” da wannan suka rabu maimakon Nafisa ta koma gidan Sakeenatu sai ta yi tsinke gidansu tun da dai ga mijinta nan ya zo. #GIDANSU SAFEENATU Wuni guda currr jaririya Baseerat ta ɗauka tana bacci wanda gangar jikinta ta koma kamar gawa ko motsi ba ta yi. Idon Safeenatu taf da hawaye ta ce “ Gwaggo Habibah jaririyar nan fa ba ta motsi,ina ga ta mutu ne” “Da ranta Safeena,don Allah ki fitar lamarin yarinyar nan tun da dai ba ki da ƙarfin zuciya.Tun farko na faɗa miki Baseerat ba normal ba ce,kenan sai ki shirya ganin abubuwan ban mamaki.Wannan kwancin da kika gani ruhinta yayi tafiyar dogon zango ne amma da ranta,ƙila sai goshin magarib su maido ta” Hawayen da take ƙoƙarin mayar wa ne suka yi nasarar sauko wa akan kumatunta,ta girgiza kafin ta ce “ ni kam ba zan iya rainon ta ba,don muddin na ce zan zauna da ita zuciyata na iya bugawa.Su wane ne za su maido ta? Yarinya kamar ɗiyar jinnu ace tun safe tana bacci ko nono ba ta sha ba alhalin ɗan uwanta ya sha fiye da goma.Haba kuma ace ba zan yi magana ba?” Safeenatu ta faɗa zuciyarta na yi mata ciwo kafin ta miƙe ta fita, frigine ta buɗe ta ɗauko ruwa masu mugun sanyi ta juyo a roba sannan ta koma ɗakinta.Babu wani tunani ta ɗauki Baseerat ta tsoma cikin ruwan ƙanƙarar nan ,ko daƙiƙa biyu ba yi ba ta buɗe idonta farare tasss babu ɗigo baƙi kafin su rine su koma ja kamar nunnanen tumatur.Safeenatu ta yi baya da sauri cike da tsoro,tana jin wani azababen sanyi na game duk illahirin jikinta tamkar wacce aka jefa a frigini.Haƙoranta ne suka fara dantsewa suna fitar da wani ƙasƙas,sai a wannan lokacin Gwaggo Habibah ta miƙe ta cire Babyn tare da lumshe ido tana mai bata haƙuri “ku yi haƙuri uwa-uwza ce ta yi kuskure ba za ta sake ba” tana maganar ne tana jimƙe da hannun hagun Baseerat wanda ke fitar da haske,Gwaggo Habibah ba ta buɗe idonta ba sai da ta ji Sakeenatu na sauke numfashin wahala ta yi mata wani kallo ta ce “yanzu kin fahimci abin da nake son yi miki nuni?” kai ta gyaɗa,Baseerat ta soma yin kuka. “Zo ki bata ta sha” Safeenatu ta maƙe kafaɗata ta ce “wallahi tsoronta nake” “Sun tafi yanzu ita kaɗai ce ,zo ki bata yunwa take ji” tana ji tana gani haka ta shayar da jaririyar. Ana kiran sallar magrib Murjanatu ta dira a gidan da ɗirkeken cikinta,cike da murna suka rungume juna ita da Gwaggo Hajara.“Na yi kewarki sosai Mama ” cewar Murjanatu tana matsar ƙwalla,shiru Gwaggo Hajara ta yi jin ƙaton cikin ƴarta na tokare ta yayin da kuma yawunta suka soma tsinkewa tsabar maita...... [13/04 10:28] MRS SADAUKI: _____________________ MRS SADAUKI *MAITAR DARE* *Last free page 13-14* Wani irin mugun ƙishi ne ya wanzu a maƙoshin Gwaggo Hajara saboda Maitar shan jini ta motsa.Dakyar ta iya sakin Murjanatu ta koma gefe tana kallon ta,sai kuma ta kasa haƙuri sai da ta shafi ƙaton cikin da mugun sauri Murjanatu ta kai hannunta ita ma kan cikin saboda mugun juyawa da yayi. “Washhh! ” ta furta a wahalce kafin kuma ta dafe ƙugu jin kamar ta soma naƙuda ne,“ sannu Murjanatu ki zauna mana” Gwaggo Hajara ta faɗa tana haɗiyar yawu don tsaf take kallon jaririn wanda sai juyi yake a ciki. Kan gwiwanta ta zube tana mai ci gaba da yin gumurzu,tuni ita Hajara ta san da yau in ba wani iko na Allah ba sai ƴarta ta haihu.Da sauri ta shiga cikin ɗaki ta fito kafin ta ce “tashi mu je asibiti” a wahalce ta ɗago ta dubi mahaifiyarta ta ce “ wallahi Mama ban iya tashi” “To haka za ki zauna? Sai nake ganin kamar haihuwar ce” Ba ta rufe bakinta ba Murjanatu ta fasa wani uban ihu wanda ya jawo hankalin Gwaggo Habibah da saurinta kuwa ta fito tana tambayar lafiya sai kuma ta yi tozali da Murjanatu a cikin mawuyacin hali.Da taimakonta suka samu suka Murjanatu ta miƙe tsaye,Munir ne ya je ya nemo musu mai ɗan sahu.Kayan robar Safeenatu aka yi aro aka kai ta asibiti,sai uban ihu take tana kururuwa tana faɗin za ta mutu. Daga nan waje kuma inda mutane ke zauna wa,ran Gwoggo Habibah ya ɓace sosai tun tana ɓoyen abin har ta kasa ta ce “ yanzu ke hatta ƴarki ba ki bari ba? Wannan mugun hali naki bai yi ba.Wato babu babban makunyaci a duniya irin maye,tun da har jininsa bai bari ba” Gwaggo Hajara ta ƙanƙance idonta da suka kaɗa suka yi ja kafin ta ce “ ina ruwanki da ni ? Ke kika haifa min Murjanatun? Ƙanwar uwa ko ta uba?” Gwaggo Habibah ta miƙe ta ce “ kina fa da gaskiya,amma ki yi haƙuri farar zuciyata ta taimakon jama'a tasa na zo na tsoma hannnuna inda ba a gayyace ni ba.Tabbas Murjanatu ƴarki ce in kina so ki haɗa har da ita duk ki cinye” tana gama faɗa ta yi tafiyarta ta bar Hajara a zaune babu jimawa kuwa Murjanatu ta haifo ɗanta namiji. Ɗakin hutu aka kai ta,murya na ɗan rawa Gwaggo Hajara ta ce “ yo ina jaririn?” “Nurse na duba shi ne don tabbatar da lafiyarsa” ta bata amsa. Tsawon lokaci kafin a kawo shi jikinta har rawa yake ta karɓe shi,nurse ta ce “ a basa abincinsa ya sha da alamu yunwa yake ji” “Toh! Toh” cewar Hajara tana wani kafe yaron da idon mugunta,ya soma kuka Murjanatu ta tashi zaune babu kunya ta ce “ Mama kawo shi” ba don ta so ba ta miƙa mata shi ta koma gefe cike da ƙwarewa ta damƙe kurwar yaron .Da ta fita wankin kayan da suka ɓace ta samu wuri ta haƙa rame ta binne ,duk da zuciyarta babu daɗi amma ji take ya zama doli ta cinye jikanta na farko ko yawunta sun koma. Daren nan dai ba su yi bacci ba jariri nata yin kuka hatta likitocin sai da suka shigo suka duba shi,sai asubahi ya rumtsa wuraren ƙarfe tara na safe aka basu takardar sallama bayan sun biya.Hajara ce ta je ta taro ɗan sahu,bayan ta saka kayansu Murjanatu ta shiga sannan ita ma ta shige tana kallon wurin da ta binne kurwar jariri can ƙasan zuciyarta ta furta ‘ zuwa dare zan zo na tone’ haka suka isa gida. Ta kuwa ci sa'a Daddy bai fita ba,Murjanatu ta gaishe shi ya amsa tare da yi mata barka kafin ya maida dubansa ga Hajara wacce sai raba ido take kana gani ka san ba ta da gaskiya. “ Hakan da kika yi daidai ne? Don dai ba ni ne na haifi Murjanatu ba shine kika koro Habibah daga asibiti? ” “Ka yi haƙuri ba koro ta na yi ba,na dai ce ta dawo gida tun da ba za a barin mai jego ita ɗaya ba a gida” “Mi yasa ba ki kira ni kin shaida min zancen haihuwar ba? Ban cancanta ba ne ko me?” “Ka yi haƙuri Daddyn yara,yanzu dai ka kira shi mijin nata ka shaida masa zancen haihuwar ” Bai amsa mata ba ya fice,sai a lokacin Habibah ta fito idonta kan jaririn wanda ke baccin wahala.Cike da tausayinsa ta ƙarasa ta ce “ barka Murjanatu Allah raya shi kan sunnah” “Amen na gode” ta amsa tare da miƙa mata jaririn,Habibah ta karɓe shi tana mai zaunawa kan kujera ta shafi sumar gashinsa tana kallonsa da kyau ta tabbata kurwarsa na gidan yari ba a cinye ba sai dai ba ta san a ina aka binne ta ba.Haka ta gaji da binciken ta miƙa shi ga uwarsa ta miƙe suna ƴar kallon-kallon ita da Hajara wacce idon nan nata suke wiƙi-wiƙi na maras gaskiya. A sanyayye Habibah ta koma ɗakin Safeenatu,“ ya dai Gwaggo Habibah lafiya na gan ki duk kin yi wani iri?” Feenat ta tambaya. “ Babu komai Safeena,bacci Baseerat take?” “Eh ba ta jima da rufe idon ba” “Mu gan ta” Habibah ta faɗa tare da yin zama, Safeenatu ta ɗora mata jaririyar kan cinya.Hannunta mai safa ta kamo ta cire sannan ta soma shafa shi ,zuciya cike da rauni ta soma yin magana “ ki tausaya ki ceto jaririn da bai san komai ba,ki sani shi ma tamkar Basheer yake mai rauni ne.In kuma har yanzu kuna cikin fushi ne shi yasa kuka hana ta ɗauki mataki ku yi haƙuri,amma dai a duba lamarin” tana gama faɗa Baseerat ta buɗe idonta taram cikin na Habibah,ita kuwa ta shiga kallon abubuwan da suka faru bayan ta bar asibitin a cikin ƙwayar idon jaririyar ta ga komai har inda Hajara ta binne kurwar.Tana gama gani Baseerat ta maida idonta ta rufe, Safeenatu dai na gefe a yanzu ma kallonsu take ba tare da ta ce komai ba. Habibah ta ja ajiyar zuciya ta sakar mata murmushi ita kuwa kai ta ɗauke,tana mai jawo wayarta ta kunna data so take ta yi bincike don gano shin abubuwan da suke faruwa zai iya kasancewa ko kuwa ƴarta ce kawai ke da shi. Tunanin ta watsar ta shiga WhatsApp ta fara duba saƙonnin mutane masu yi mata barka kafin kwatsam ta ganta cikin wani group.A hankali ta soma biyayar abubuwan da ke faruwa sai ta ga amsoshin tambayoyinta kan wani posting. ```“M” CIKIN TAFIN HANNU,MAUME HAND/PAUME DE MAIN Chiromancy wata daɗaɗiyar hanya ce ta hango makomar mutum da kuma fassarar halayyar mutum daga dalilin layukan hannu. Wani lokaci waɗannan layuka na iya samar da lambobi da haruffa. Ɗaya daga cikin waɗannan wasiƙun na iya zama wasiƙar M, ma'anar wacce mystics da dama suka yi nazari a kanta. Kamar yadda mutane da yawa suka yi imani, layukan da ke kan tafin hannunmu suna bayyana halinmu da ƙaddararmu. La lettre M est attribuée à des personnes vraiment spéciales(The letter M is assigned to truly special people). An ba su kyakkyawar fahimta kuma suna wakiltar abokan haɗin gwiwa akan dukkan wasu kasuwanci. Idan mutanen da kake so suna da wasiƙa ta musamman M a cikin tafin hannu ya kamata ka sani cewa ba za ka iya raina masa hankali ba kuma ta wata hanyar ba za ka iya yin ƙarya ko yaudarar wannan mutumin ba. Kasancewar shi mai dubara da hankali da tsantsar lura sosai, mutamin da ke da harafin M a tafin hannu cikin sauƙi zai fahimci cewa ana yi masa ƙarya ne ko yaudara. ``Matan da suke da harafin M a tafin hannunsu suna da zurfin tunani fiye da maza, har ma da waɗanda suke da wannan wasiƙar. Ana yi musu baiwa da ikon sarrafawa da shawo kan duk wani cikas a rayuwa, kuma sun san yadda ake amfani da albarkatu da damar da ake da su. Harafin "M" a kan tafin hannu ma na iya nufin: • Ƙwarewar shugabanci • Iko wato power/pouvoir``` Zuciyar Safeenatu banda bugawa babu abin da take yi har sai da ta ajiye wayar ta je ta ɗauki ruwa masu sanyi ta sha .Ta dawo ta zauna don ƙara duba saƙon sai dai hatta shi kansa group ɗin ya ɓata a wayarta babu shi sam .Kamar mahaukaciya haka ta miƙe ta je ta yi wani gurwanau a gaban net ɗin da aka saka Baseerat,ta zuge zip ɗin ta kalli ƙofar toilet inda motsin ruwa ke ta zuba da alamu Habibah wanka ta shiga ba tare da ita ta san yaushe ta shiga ba . Murya a ɗan kasalance ta ce “ Baseerat ni ce mahaifiyarki,ni na haife ki.Duk wani wanda bai son ganin kin cutu to tabbas sai dai ya biyo bayana,don haka kar ki ga kamar ban son ki a'a wallahi zuciyata raunk ne da ita.Magana nake son yi miki game da abin da na gani cikin wayata,shin kina da masaniya? In dai tabbas ke ƴar baiwa ce kamar yadda saƙon nan ya bayyana to ki buɗe idonki ki kalle ni” ko rufe baki ba ta yi ba kuwa Baseerat ta buɗe idon sai da Safeenatu ta dafe ƙirji saboda tsoro. “Mine ne wai?” daga bayanta Habibah ta tambaya ,zip ɗin net ɗin ta mayar tana mai cewa “ babu komai Gwaggo Habibah,na yarda na aminta da lamarin nan gaske ne ana samun ƴan baiwa to Allah bata ikon yin amfani da ita ta hanyar ƙwarai” ruwan sama ne suka fara sauka a daidai lokacin da Safeenatu ta rufe bakinta. Gwaggo Habibah ta yi wani ɗan ihun murna tare da rungume Safeenatu ta ce “ kin ga ko? Ƴarki ta musamman ce ancestor/ ancêtre suna tare da ita” A wannan daren cike da zullumi da tunani Safeenatu ta yi shi,da ta samu bacci ya ɗauke ta mafarkai ta yi barkatai akan goben Baseerat. Washegari tun da safe kukan jaririn Murjanatu ya cika gidan kamar wanda ake cirewa rai. “Jaririn can ba dai kuka ba” Safeenatu ta faɗa . Habibah ta ja baki ta yi shiru tana tuna jiya irin gumurzun da suka yi ita da Hajara akan kurwar yaron.Dakyar ta yi nasara ta tone ta tare da saka Hajara don doli ta mayar masa abarsa wacce tuni ita kanta kurwar ta yi rauni,kukan da yake yi kuma saboda ciwon jiki ne. ★A kwana a tashi babu wuya wurin Allah yau ne sunan Twins ɗin Safeenatu waɗanda dangin Bashir suka yi bajinta sosai wurin yankan manyan raguna uku biyu na BASHEER ɗaya kuma na BASEERAT .A wannan rana ta farin ciki Safeenatu ta rakuɓe wuri guda tana ta yin kuka,ga shi dai ta sha ƙunshi da kitso ga kuma gizner ta gani ta faɗa amma rashin masoyinta ya dawo mata daram musamman yadda ake ta faɗar an yi masa madadi da kuma addu'o'in da mutane ke yi. Da wannan damar Gwaggo Hajara ta shirya mugunta wacce take kambacin fansar da ta yi niyyar ɗauka akan Habibah da hana ta rawar gaban hantsi.Sai da ta bari duk hankalin mutane ya ɗauku,sannan jarirai duk an fitar da su can tsakar gida saboda zafin da ɗakin ya ɗauka sannan ta nufi ɗakin Safeenatu.Duk da akwai mutane hakan bai hana ta gwada sa'arta ba,“ ungo Safeena Gwaggonki Habibah ta ce ki ci abincin nan kafin ta zo ta yi miki ta ƙarfi tun da dai ke ba ki jin magana kina jego amma kin ƙi cin abinci ” Hajara ta faɗa tare da miƙa mata plate mai cike da nama ya sha jar miya,ta karɓa tana turo baki tare da soma ci don ita duk a tunaninta gaske dai Habibar ta bata.Cike da murna Hajara ta bar ɗakin ta je ta kasa kunne tana jiran sakamako. Da rana mutanen arziki sun cika gida, Safeenatu ta shiga Toilet ta yi wanka da canza kaya daga shadda zuwa less.Kamar wacce aka yi wa wankin ido haka take ganin ƴan biki tsirara tamkar babu kaya jikinsu,zuciyarta ta yi wani mugun bugawa ganin ta soma ganin hanjin cikin mutane yayin da kuma take jin wani abu a bakinta da ba ta san mine ne ba.A daidai nan free page ya ida mai son complete zai tura 800 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822