"[12/19, 10:22 AM] Sakaba: *HALIN GIRMA!*" ©®Hafsat Rano. FREE PAGES! (1) *_WAIWAYE ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_* *ZAFAFANKU BIYAR sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma "TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*" "*_SANIN HALI. yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi" "wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*" "*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu" kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi* *JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE* *_DEEN MARSHALL Mamuhghee_* *_HALIN GIRMA hafsat rano_* *_TAKUN SAƘA billyn abdul_* *_SO DA ZUCIYA miss xoxo_* *_ƊABI'AR ZUCIYA huguma_* *DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL* 2 400 3 500 4 700 5 1000 *Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA keystone bank Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 08184017082 "*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*" 09134848107 *_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_* #team zafafa biyar (1) "***Komai na rayuwa na tafiya ne bisa tsari da kudurar ubangiji, komai ya faru da bawa dama tun fil azal" "hakan na cikin kaddarar sa, Wala kaddara mai kyau ko kuma akasin ta. Yarda da Kaddara me kyau ko mara kyau na cikin Imani!" A tsaye take gaban sink din cikin toilet din tana wanke kananan kayan da ya kasance mallakin Maama "da Zeenat, lokaci zuwa lokaci tana cire hannun ta tana yarfe shi saboda sanyin da ake zugawa kasancewar karshen December ne a lokacin da ake zuga sanyi. Dauraye kayan tayi ta yi saurin fitowa ganin haske ya hudo ta window din toilet din. Karfe shida da rabi agogon falon ya nuna, tayi saurin" karasawa kitchen din domin dora abin karin kumallo kafin ahalin gidan su tashi. "Tun kafin asubah take fara ayyukan gidan wani lokacin har karfe tara na safe bata kamalla wa, duk" "kuwa da tana iyakar kokarin ganin bata wuce taran ba saboda karatun ta na islamiya da take zuwa duk weekend, tana ganin shine kadai gatan da zata yi wa rayuwar ta a halin da take ciki a gidan mahaifin ta. Bata fatan wani ya shiga irin rayuwar da take ta kunci da tsantsar makirci, babu wanda ya san halin da take ciki balle ya kawo mata dauki, bata isa ta bud'e baki ba saboda kowa ganin kirki da karamcin Maman yake, mace ce me masifar kirki, me haba haba da saka duk wani abu nata gaba da na duk sauran" "yayanta a idon ahalin gidan,a badini kuwa bata da maraba da bola." Kowa kallon mara dadin zama yake mata ko kuma mara godiyar Allah saboda rashin walwalar da take "fama da har ya shafi kaso mafi rinjaye na rayuwar ta, zaka dauka bata dariya ko doguwar magana sai dai bata da sukunin yin kamar sauran yan matan gidan nasu." "Kowa kallon wadda tayi sa'ar uwar riko yake mata, ayi ta sakawa Maman albarka da yabo a gabanta" tana amshewa amma a bayan idon mutane! Bakar wahalar da take sha ba zata misaltu ba. Da tunanin ta kammala aikin ta dauraye hannayen ta sannan ta fito ta jera musu a saman dining ta dauko nata a dan plate ta wuce zuwa dakin su. "Bude kofar da tayi ya farkar da Zeenat, a zafafe ta dago ta watsa mata kallon banza gami da jan d'an" karamin tsaki tana sake rufe kanta da katon duvet din da take kanannade a cikin sa. Cikin nutsuwarta ta karasa shigowa d'akin tana dora plate din saman d'an madaidaicin mudubin dake cike da kayan shafe- shafe ta soma gyara wajen data tashi. Katifar ta fara daukewa ta kaita chan store sannan ta dawo ta share dakin a hankali gudun magana taci abincin a tsaitsaye ganin lokaci na neman kurewa tayi saurin watsa ruwa a gaggauce ta fito. Dogon hijabin ta ash colour daya kasance a matsayin uniform din islamiyar tasu ta saka bayan ta gama shiryawa ta dau yar madaidaiciyar jakarta me dauke da Al-kurani me girma da sauran littafan addini ta fito. Habib na zaune saman dining da alamun zaman sa kenan ta gaishe shi a nutse sannan tayi masa sallama ta wuce islamiyyar dake chan kasan layin su inda take zuwa duk asabar da lahadi da safe sai sauran ranakun da yamma amma banda juma'ah. "*Babban gida ne irin wanda zaka kirashi da Family house, bangarori ne da dama a ciki wanda yake" "dauke da gidaje guda shida dake kunshe da mutane cikin su suna rayuwa irin wadda suka zaba ma kansu. Duk da kowanne bangare na da tsarin da yake tafiyar da rayuwar sa akai amma kuma suna tafiya ne da ra'ayoyin juna, daya baya taba zartar da hukunci be sanar da daya ba, sannan duk abinda suka zartar din" dole ne ya samu amincewar mahaifiyar su Hajiya Fatima wadda suke kira da Gaji. "Gidan ta ne a tsakiya in da sauran gidajen ke kewaye da ita, galibin yan matan family din suna tattare" "ne a shashen nata da ya zama tamkar matattarar su, yanayin haihuwa a family din na tafiya ne kusa da kusa, inda zaka samu yawanci sa'oin juna a kowanne gida." "Duk da basu da tarin dukiya irin me yawan nan amma suna da rufin asiri daidai gwargwado, sannan ana" damawa dasu a duk bangarorin ilimi na Islama dana bokon hakan ma bangaren kasuwanci da siyasa duk babu wanda basa tabawa. Zamu iya cewa kowanne a cikin yayan Gajin yayi sa'ar abokiyar zama ta kwarai dan babu wanda yake "kuka da abokiyar zaman sa, daidai gwargwado suna zaman su lafiya suna kuma mutunta juna suna girmana Gaji da duk wata bukatar ta." "Muguwar mace me kinibibi da kissa zai yi wuya ka gane alkiblar ta farat daya, komai su kayi daidai ne" "suna kuma da kokarin kyautatawa kowa, suna kokarin boye aibun su suyi amfani da hakan wajen muzgunawa wanda basu so, idan yayi korafi a bashi rashin gaskiya saboda kirkin su." Alhaji Muktar shine Babban dan Hajiya Gaji bayan Babbar Yayar su mace da suke kira da Hajiya Babba "dake zaune a Sheffield dake birnin London tare da family dinta , sai me bi masa Dr Ibrahim, sai Abba Usman sai Abba Musa sai dan auta Abba Kabir." Dr Ibrahim dan boko ne sosai dan har ya kai matakin associate professor in da yake lecturing a halin "yanzu. Matar sa daya ta aure Maama wanda zamu iya cewa kaf family din babu wanda baya kaunar ta saboda kirkin ta. Yaranta uku da Dr, Habib ne Babba, sai Zeenat sai karamin kanin su Marwan. Sai dai shi yana da ya daya daban wadda suke haifa da matar da ya aura a lokacin da yaje karatun sa na Masters a University of Michigan, anan suka hadu har sukayi aure suka haifi ya daya me sunan Gaji (Fatima-Iman) a lokacin ne kuma suka rabu saboda wata babbar matsala da ta taso tsakanin shi da family dinta, dan dama basa son auren, yana ji yana gani ya rabu da ita, ya dawo gida. Fatima na yin wayo suka kawo masa ita inda ya dauki rikon ta ya damka a hannun Maama wanda a lokacin take goyon Zeenat itama." Bata taba nuna masa komai ba ko a fuska kuma be taba ganin wani banbanci tsakanin Fatima da Zeenat "ba, shiyasa ya kara bata mazauni me girma a zuciyar sa." "***Daidai layin su ta hangi Zeenat tsaye da Bashir, dan dam taji a zuciyar ta kasancewar ba wannan ne" "karo na farko ba, duk wanda yace yana son ta in sha Allah ba za'a dau lokaci ba zata same shi tare da Zeenat shikenan kuma ta ta maganar ta sha ruwa. Zeenat yar uwarta ce amma duk da haka tana jin babu dadi, sai dai bata bar hakan yayi tasiri a zuciyar ta ba, ta dau hakan a matsayin wata jarrabawar rayuwar" ta. Daidai in da suke tsaye tazo zata wuce Zeenat din ta kira sunan ta """Iman!"" Tsayawa tayi chak, ta kalle su kad'an sannan tace" """Sannun ku.""" Murmushi Bashir din yayi mata sannan yace """Malamar islamiyya, sannu da zuwa.""" Bata amsa masa ba dan yadda yayi maganar taji akwai alamun rainin wayo """Ya akayi?"" Tace tana kallon Zeenat." """Babu!"" Ta dage kafadar ta." """Ok!"" Tace tana cigaba da tafiyar ta, tana jin sanda suka kwashe da dariya, ta dan ji babu dadi a ranta" "amma ta danne, ta karasa gidan duk ranta babu dadi. Da gaske ta ji zuciyar ta, ta amince da Bashir farkon magana da yayi mata har tana addu'ar Allah ya tabbatar mata dashi, sai gashi tun ba'a je ko ina ba, ya koma wajen Zeenat wadda ko da ace da wasa yaje wajen Zeenat din toh babu ita babu shi har" abadah. "A gate taci karo da Maryam, a kalla ba kamar sauran ba, Maryam ta fuskance ta, shiyasa tasu tazo daya" "sosai, duk da ba wata doguwar hiraa ce ke hada su ba amma ta kan sake da ita fiye da kowa. Bikin su za'a yi su hudu a gidan. Maryam din sai Bilkisu, Aysha da Amina. Daga su sai ita da Zeenat da yar gidan Abba Musa Rabi'ah sune a layi, duk cikin su babu wanda bashi da me son shi amma banda ita da ta gagara samun wanda ma zai tsaya din." "Bangaren Gajin suka wuce tana mata hira akan shirye shiryen bikin, rabin hankalin ta baya kan" "Maryam din har suka karasa, suna shiga ana kiran sallar magriba sai kawai suka wuce sukayi alwala." Bayan sun idar ne Gaji ta kalle su tana kan abun sallah kamar zatayi magana sai kuma ta fasa. Sai da ta gama ta tashi sannan tace """Maryama daga ina haka ke da alhuda-huda?""" """Daga islamiyya Iman take ni kuma na fito zan taho nan muka hadu.""" """Toh ku tashi ku dubo min ko an gama tuwo dan cikina ya soma kiran chiroma.""" """Wai Gaji wasa wasa fa kina da ci wallahi.""" """Saukin ta ba kowa ke siyan kayan abincin ba 'yaya na ne, ko zaku hana su bani ne?""" Rik'e baki Iman tayi tana dariya Maryam tace """Bamu isa ba ai Gaji, aci dadi lafiya lokacin ki ne.""" """ Yafi muku sauki dai, kema alhuda-huda kin fara zama su balki ko? Kika biye musu baki da bakin da zaki" "iya karawa dani atau.""" "Shiru tayi bata ce komai ba, suka zagaya kitchen din Gajin da ke baya suka hado mata abincin suka kawo" "mata sannan suka zauna suka ci tare, lokaci lokaci Maryam na tsokanar ta, ita dai Iman jin su kawai take har aka gama suka tattare kayan sannan Maryam ta tafi ta barta a nan, sai kawai ta zame tayi kwanciyar ta a saman doguwar kujerar ta fad'a kundin tunani kamar yadda ta saba." """Yaya Iman kizo inji Maama, zamu ci abinci kar ya huce baki ci ba, kiyi sauri.""" "Muryar Marwan ta iso daidai kunnenta, da sauri ta tashi zaune, sai kuma ta mike da sauri tana jin sanda" Gaji tace """Hajara ba dai kirki ba, yadda kike kula da yarinyar nan ubangiji Allah ya kula miki da naki yayan.""" "Wasu guntayen hawaye ne taji suna neman zubo mata, tayi saurin maidasu ta kara sauri zuwa shashen" nasu domin amsa kiran Maama. _*KASHI NA BIYAR*_ _*KASHI NA BIYAR*_ _*KASHI NA BIYAR*_ _*KASHI NA BIYAR*_ *_KASHI NA BIYAR_* "_*SABUWAR SHEKARA, SABUWAR TAFIYA, SABON SALO*_" . . . _*ZAFAFA BIYAR!! KASHI NA BIYAR!! SINADARIN ZAFAFA5 (BEST TOP 5)*_ "_*INA MASOYA KUMA MAKARANTA, MABIYA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR? KU MATSO DOMIN NESA" "TAZO KUSA, KU SHARE HAWAYEN KU, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE DANNOWA DA TURURUN SU, MASU ZAFAFAN FADAKARWA, NISHADANTARWA HAD’I DA ZAFAFAN KAUNA MARAR GAURAYE.*_" _*YAN BIYAR DIN NAKU KAMAR KO DA YAUSHE SUNE:*_ _*SAFIYYAH HUGUMA*_ _DABI'AR ZUCIYA_ 2-_*BILYN ABDULL*_ _TAKUN SAK’A_ _*3- MAMUH GEE*_ _DEEN MARSHALL_ _*4-HAFSAT RANO*_ _HALIN GIRMA_ _*5~NANA HAFSAT (MISS XOXO)*_ _SO DA ZUCIYA _ 1 "_DAGA TASKAR *SAFIYYAH HUGUMA* MARUBUCIYAR ZAFAFA DA TAYI; DAURIN BOYE, ALKAWARIN" "ALLAH, ALKIBLA, SIRADIN RAYUWA TA SAKE ZUWA DA WANI RANTSATTSE MAI SUNA:_ *_ƊABI'AR" ZUCIYA_* 2 "_DAGA ALKALAMIN *HAFSAT RANO* , MARUBUCIYAR ZAFAFA DA TAZO MUKE A BAYA DA, DAURIN" "GORO, ABINDA KE CIKIN ZUCIYA, SAUYIN KADDARA, MABUDIN ZUCIYA. WANNAN KARON TAZO DA WANI SABON SALON MAI SUNA:_ *_HALIN GIRMA_*" 3 "_DAGA SALON TAFIYAR *MAMUH GEE* ,WADDA A LITTATTAFAN TA NA ZAFAFA TAYI; MIN QALB, BURI" "DAYA, KAUNAR MU, UBAYD MALEEK. WANNAN TAFIYAR TAZO DA WANI DADDA’DA MAI SUNA:_" *_DEEN MARSHALL_* 4 _DAGA TAFIYAR RUBUTUN *NANA HAFSAT (MISS XOXO)* WADDA A ZAFAFAN BAYA TAYI WASU KAMAR "SU: KAI MIN HALACCI, KIBIYAR AJALI, DALAAL, IGIYAR ZATO. WANNAN NEXT LEVEL DIN TAZO DA WANI" MAI TAKEN:_ _*SO DA ZUCIYA* _ 5 _DAGA SALON RUBUTUN *BILYN ABDULL* MARUBUCIYAR ZAFAFA DA TAYI NA BAYA IRIN SU: WUTSIYAR "RAKUMI, SARAN BOYE, MAKAUNIYAR KADDARA, GUDU DA WAIWAYE. WANNAN SABUWAR TAFIYAR" TAZO DA WANI MAI SUNA:_ *_TAKUN SAKA _* "_*KADA KU BARI AYI BABU KU, KUZO A DAMA DAKU A SABUWAR TAFIYA MAI TAKEN SABON SALO," "SINADARIN ZAFAFA BEST TOP 5, MASU ZAFAFAN DARUSSA, NA RAYUWA, WANDA DUK WANI MAKARANCI BA ZAI RASA DARUSSAN DAUKA ACIKI BA.*_" _*GUDA DAYA: 300*_ _*BIYU 400*_ _*UKU 500*_ _*HUDU 700*_ *_BIYAR DUBU DAYA (1k)_* "*_YAN TALLAH SAMAN SHAFI NAIRA 300, ‘KASAN SHAFI KUMA 200 NE_*" _*YADDA ZAKU BIYA*_ *_ZAKU TURA KUDINKU ACIKIN WANNAN ASUSUN NA BANKI_* *6019473875* *MUSAA ABDULLAHI SAFIYA* *keystone bank* *Sai katura shedar biyanka ta wannan number* 08184017082 "_*IDAN KATIN MTN NE, KO VTU SAI ATURO ZUWA GA*_ " 09134848107 _#TEAM ZAFAFA BIYAR_ "[12/21, 11:37 AM] Sakaba: *HALIN GIRMA!*" ©️®️Hafsat Rano. FREE PAGE (2) ***** "Takalmin Abban su da ta gani a kofar shiga falon yasa ta sauke ajiyar zuciya, ta bud'e labulen hade da" "sallama, idonta ya sauka a cikin na Mama da take kallon kofar, tayi mata wani kallo me cike da ma'anoni da ba kowa ne zai gane ba sai ita kadai da ta san manufar sa." """Abba barka da gida."" Tace tana zamewa k'asa" """Yawwa Uwata, kina ina haka mamanki na ta neman ki kinsan bata so kici abincin da ya huce ko? Ga" "yanayi na sanyin nan ba komai ne yake rik'e zafin sa ba.""" """Ina wajen Gaji ne."" Tace tana sake yin kasa da kanta." """Toh dai a dinga kula ana abinda ya kamata kinji? Allah yayi muku albarka.""" """Amin."" Tace tana mikewa ta shige dakin su da dan sauri tana avoiding idon Maman da ta rakata dashi." "D'are-d'are ta tarar da Zeenat a saman gadon tana waya, wuceta tayi ta bud'e jakar kayan ta, ta sauya kayan jikin ta da wasu ta ninke Hijab din sannan ta dawo ta saka abun sallah a k'asa ta zauna ta ciro" littafin da akayi musu a islamiya ta soma karantawa a hankali. """Malama kina distracting dina.""" Ta zare wayar daga kunnen ta tayi maganar a chunkushe. Banza tayi mata ta cigaba da karatun ta ba tare da ta daina ba. """Mtsww!."" Ta ja dogon tsaki" """Baby bari zan kiraka ina zuwa.*" """Owk dear, ina jira.""" Katse kiran tayi ta zuro kafafunta daidai wajen da Iman din take zaune """Malama duk karatun da kikayi a islamiya be ishe ki ba, sai kinzo kin cika mana kunne mu san kina zuwa" "makaranta, bayan kowa yasan dalilin da ya saka kika nace da zuwa ko kya samu ya sayyadi ya ce yana so.""" "Bata tanka mata ba, hakan ya sake kular da Zeenat din, ta saka hannu zata warce littafin tayi saurin" "janyewa ta mike tsaye," """Wallahi sai dai ki hakura da karatun ko kije chan kiyi, naga ma aiki ne gaban ki kin sani tsabar kinibibi so" "kike sai ya jiyo ki kina karatu. """ """ Kinga duk abinda kike yi bana taba tanka miki, ba wai don ina tsoron ki bane ko wani abu, kawai bana" "son tashin hankali ne da hayaniya. """ """ Toh ki tanka min ma mana, wallahi yanzu zanje na hado ki da Mama.""" Bata sake magana ba ta fice daga dakin dan ba karamin aikin Maman bane ta hanata zuwa makarantar "na wani lokaci, sai kawai ta zarce kitchen ta tarar da kayan wanke-wanke tuli guda, ta nannade hannun ta tasoma wankewa. Abincin da ta gani a tukunya ta san nata ne, yayi mugun sanyi ita kuma a ka'idar ta bata cin abinci me sanyi, ko ruwan sanyi bata sha a rayuwarta balle yanzu da ake zuga sanyi sosai., gudun ta barshi bata ci ba gobe a hanata yasa ta samu leda ta juye a ciki ta wanke tukunyar ta goge gas da k'asan kitchen din ta gyara komai tsaf sannan ta fito da ledar ta zagaya ta kofar baya ta fita zuwa part" "din Gaji, ta samu me aikinta ta bata sannan ta dawo ta dauko katifar ta a store ta wuce dakin." "Har lokacin Zeenat bata gama wayar ba, toilet ta wuce ta dauro alwala tazo tayi shafa'i da wutri" sannan ta kwanta ta rufe kanta gaba daya da dan yalolon zanin gadon da duk ya yayyage ta gefe da gefe ta kudundune da haka bacci ya dauke ta. "Da safe ta tashi kamar kullum tayi ayyukan da suka zama wajibi akanta, kasancewar litinin ce sai ta yi" "wanka kawai ta wuce shashen Gaji bayan ta tabbatar da fitar Mama tun sassafe, a chan taci abincin ta sannan ta kwanta bacci. Sai da rana ta soma dagawa sannan ta koma ta daura girkin rana,ta gama kafin" "lokacin tafiya islamiya, ta dauki na Gaji ta kai mata ta sake zama tana jiran lokacin ya cika." """Yaki takwara ta, zo nan."" Gajin tace tana daga zaune a in da take" """Me yake damun ki?""" """Na'am?""" """Fad'a min idan kina da wata matsala ne, na dade ina lura da yanayin rashin walwalar ki, sai dai na kan" "dauki hakan a matsayin halitta, amma kuma jiya sai abun yazo kaina, na dinga tunanin ko dai kina da wata damuwa ne? Da kika kasa sanar wa wani kika barta a ranki.""" """Babu komai Gaji, yanayi na ne a haka amma ni babu abinda yake damuna.""" """Kin tabbata.""" "Daga mata kai tayi tana jin kamar ta saki kuka, ga dama ta samu amma bata da ikon furta wa, toh tace" "mene ma wai? Hakan ba shi zai hana Mama ta daina muzguna mata ba, Kai tsaye zata kare kanta da zarar Gajin ta tuhume ta karshe kuma abun ya koma kanta kowa ya cigaba da mata kallon marar kirki ko kuma wadda bata san halacci ba. Shiyasa ta zabi yin shiru kawai dan fadar ba zata sauya komai ba, su" duka sun yarda da Maman yarda irin ta ban mamaki. """Ai nasan bangaren Hajara baki da wata matsala dama, na dai zata ko damuwa ce dai irin ta rashin" "maman ki kusa dake, duk da bani da haufi akan kulawar da kika samu iyakar abinda zaki samu kenan ko da ita mahaifiyar taki ce.""" """Haka ne."" Tace a kasalance" """Yawwa ki dinga dan daurewa kina shiga cikin yan uwanki kinji? Zaman shirun da kike babu dadi.""" """In sha Allah zan gyara.""" """Yawwa... Haka nake son ji.""" """Ya batun yajin aikin nan kuwa? Kun dauko karatu tiryan tiryan yajin aiki ya tsaidaku da tuni wata" "maganar ake ba wannan ba.""" """Wallahi shiru ba labari, muna dai ta addu'a Allah ya sa a daidaita.""" """K'asar nan kenan ai, dan karatun ma yanzu nema ake a hana dan talaka yin sa.""" """Wallahi.""" """ Allah yayi mana maganin abinda yafi karfin mu.""" """ Amin ya Allah!""" """ Shiyasa nace duk ku fidda mazaje kawai da zarar wadanchan sun tafi kuma azo ayi naku zaman haka" "nan ba zai yiwu ba.""" "Shiru tayi gabanta ya fadi, bata son taji ana maganar auren su, gashi kuma taga alamar ba za'a dauki" "lokaci ba za'a ce su fidda mazaje, ya zatayi da ranta? Da ganin suna makaranta yasa maganar ta lafa amma yanzu yajin aikin da aka tafi da ba'a san ranar dawowa ba ya saka iyayen nasu yanke shawarar" suma su aurar dasu kawai sai karasa karatun a dakin su. "Tashi tayi tayi ma Gajin sallama ganin lokaci yayi, taje tayi alwala ta saka Hijab dinta ta fito, a falo ta" tarar da Mama tayi saurin tsugunnawa ta gaishe ta """ Mama barka da gida.""" """ Saura idan an tashi ki tsaya shiririta a hanya ko ki tsaya gidan Gaji karki zo kiyi abinda ya dace, jiya kam" "kinci darajar babanku yana nan.""" """In sha Allah."" Tace sannan ta mike ta fice Maman ta rakata da harara." "****Sati biyu tsakani aka fara bikin gidan nasu, duk yadda taso gujewa wasu abubuwan amma Maryam" "bata barta ba, komai idan za'a yi sai ta sakata a ciki, haka kunshi da gyaran kai tare suka je da wata kawar Maryam din." "Alhamis suka fara bikin, a compound din gidan Anty Mabruka sukayi bridal shower iya su da kawayen" "su, juma'ah akayi kamu asabar aka daura aure hade da yini, lahadi aka kai kowacce gidan ta." "Ranar litinin suka tashi gidan da sauran bakin da basu riga sun tafi ba wanda yawanci dangin Gaji ne, a" "babban kitchen din gidan suka hadu aka hada breakfast Masa da miyar taushe, har rana tayi sosai basu kammala ba hakan ya sake haifar mata da wata irin gajiya bayan wadda take fama da ita, tasan halin Mama sarai idan ta makale taki fitowa ayi aikin da ita duk da akwai masu yi din amma dolen ta ne ta fito, duk da hakan ba karamin taimaka mata yayi ba wajen gogewa da kalolin girke-girke mabanbanta." Sannan uwa uba girkin mutane da yawa wanda ba kowa bane ya iya. "Da saurin ta, ta karasa dakin su, ta kwanta a gefen gadon saboda wani irin sanyi da take ji alamun" "zazzabi ne ke neman rafke ta, rawar sanyi ta fara hakoranta suka shiga haduwa waje daya, ta saka hannu da k'yar ta jawo bargon Zeenat din ta lulluba." Shigowar ta kenan ta tsaya daga kofar """Kut! Lallai ma."" Tace tana karasawa ciki, ta fuzge bargon da karfi" """Dan Allah zee ki kyale ni bani da lafiya."" Tace muryar ta chan ciki. Shiru Zeenat din tayi tana kallon ta," "sai kuma ta sakar mata bargon ta juya ta fice daga dakin. Har dare zazzabin be sake ta ba, babu kuma wanda yazo neman ta. Tayi tunanin Zeenat din zata fad'a wa Maman ne duk da bata saka rai ba, amma jin shirun ya tabbatar mata da ta fad'a mata dan da ba haka ba da tuni Maman ta turo neman ta akan" wani aikin. "Wajajen Tara Zeenat ta dawo dakin, ta kalle ta a zaune saman abun sallah ta kudundune, juyawa tayi" "ta fita ta dawo da paracetamol a hannun ta da ruwa ta mika mata. Karba tayi da sauri tayi mata godiya," "bata amsa ba ta sake fita sai gata ta dawo da katifar Iman din, ta shinfid'a mata sannan ta dauko bargon ta, ta dora mata akai ta haye gadon ta kwanta ta rufe idon ta. Sosai Iman taji dadi a ranta, ko ba komai" "tayi mata abinda bata taba ba, tashi tayi da k'yar ta lallaba ta fita kitchen ta hado tea sannan ta dawo ta" sha da k'yar ta sake komawa ta kwanta ta kudundune. "Kwanan ta uku a haka, har ta soma samun karfin jikinta, Mama ta shigo sau daya ta bata anti-malaria" "shima dan tasan Abban zai iya tambaya ne, shima da tasan zai shigo ya duba ta ne, tana jin sanda take ce masa sun je asibiti ma kuma jikin da sauki." "***Karamin daki ne da yafi kama da shago, katifa ce karama irin ta yan boarding school sai jakar kayan" "sa a gefe, bayan haka babu komai a dakin sai wani dogon mudubi dake rataye jikin bangon dakin." Tsaye yake a gaban mudubin yana duba fuskar sa dake cike da kasumba ko ina har baka iya ganin "komai na fuskar tasa sosai, kansa rufe yake da katuwar hular sanyi, ya nannade wuyan sa da abu, kafar sa da hannun sa duk rufe suke cikin hular sanyi, idan ka cire fuskar sa da itama kasumbar bata wani bari a ganta sosai, babu wani abu na jikin sa dake a bud'e. Kayan jikin sa a wanke suke tsaf, sai dai sun tsufa sosai, har da wata yar bula a jikin hannun rigar." "A ko da yaushe yakan tsaya ne a daidai hanyar da take hucewa idan ta dawo daga islamiyya, amma" "kuma kwana biyu ya rabu da ganin ta, shiyasa ya yanke shawarar zuwa gida duk da yasan ba tsarar sa bace amma zai gwada sa'ar sa." *_WAIWAYE ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_* *ZAFAFANKU BIYAR sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma "TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*" "*_SANIN HALI. yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi" "wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*" "*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu" kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi* *JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE* *_DEEN MARSHALL Mamuhghee_* *_HALIN GIRMA hafsat rano_* *_TAKUN SAƘA billyn abdul_* *_SO DA ZUCIYA miss xoxo_* *_ƊABI'AR ZUCIYA huguma_* *DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL* 2 400 3 500 4 700 5 1000 *Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA keystone bank Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 08184017082 "*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*" 09134848107 *_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_* #team zafafa biyar "[12/26, 12:40 PM] Sakaba: *HALIN GIRMA*" Hafsat Rano 3 **** "Tsaye yayi jikin gate din gidan yana kare masa kallo, tunanin ta yadda zai fara shiga yake musamman da" "ba sanin sunan ta yayi ba, ya dai saka mata suna da zuciyar sa kuma be taba yunkurin tsaidata balle yaji sunan ta ba." "Lekowa maigadin gidan yayi, ganin mutum a tsaye yasa shi fitowa gaba daya" """Sannu."" Yace masa yana kokarin daidaita muryar sa" """Yawwa sannu, wa kake nema?"" Maigadin ya tambaye shi yana kare masa kallon cikin rashin sani." "Nan fa ake yinta, shiru yayi kamar me nazari shi kuma maigadin ya kafe shi da ido yana son jin abinda ya" kawo shi. """Am... Amm nazo wajen...""" """Malam Iliya."" Zeenat dake fitowa ta kirashi tana leko wa." """Na'am ranki ya dade!""" """Siyo min kati na 500 kayi sauri dan Allah.""" """Yanzu kuwa, ga wani bako nan bansan wajen wa yazo ba dai kin tambaye shi.""" "Yayi gaba, kallon sa tayi tun daga sama har kasa a wulakanci ta yatsine baki tace" """Wa kake nema kai kuma Malam?""" """Yar uwarki nake nema dan Allah, wata me zuwa islamiya kasan layin nan doguwa haka fara.""" """Waye kai a wajen ta?""" "Kallon cikin ido yayi mata, ta ja tsaki tana juya fuskar ta" """Ban fiye son kallo ba Malam, ka shigo ciki bari na tura maka ita dama ai sai dai ita din...""" Gaba tayi tana cigaba da sababi """A kaf gidan nan wa zai kwaso mutum irin wannman dan Allah! Ji shi kamar wani mahaukaci.""" Sai ta kwashe da dariya tana sake daga kafa. "A kwance ta tarar da Iman tana danna wayar ta da ba kasafai ta cika wani amfani da ita ba, yanzun ma" wani labari ne yaja hankalin ta a Facebook take karantawa. """ Kina da babban bako a waje da galleliyar ranar nan.""" """ Waye?""" """ Idan kika je idon ki zai gane miki shi.""" """ Owk.""" "Tace tana tashi zaune, har yanzu bata gama dawowa daidai ba amma haka ta karfafa jikinta tayi" "ayyukan ta. Hijab ta saka madaidaici akan doguwar rigar jikinta ta fito. Daga chan hanyar gate ta hange shi a tsaye ya rataye hannayen sa a bayan sa, kansa a kasa yana wasa da kafar sa." "Dogo ne na ajin farko, jikin sa ko ina a murje babu alamun rama ko kad'an, yanayin shigar sa bata dace" "da tsarin zubin halittar sa ba, kafin ta karasa ta gama ayyana shi a ranta. Da sallama ta isa, ya dago da" "sauri a lokaci daya kwayar idon sa ta sauka a cikin ta ta, gabanta ne yayi masifar faduwa, tayi saurin janye idon ta, ta russuna kad'an tace" """Ina wuni?"" Lumshe idon sa yayi ya bud'e, fuskar sa dake cike da kasumba ta dan yi fadi alamun farin ciki," ya tattaro dukkan nutsuwa da jaruntar sa yayi gyaran murya yace """Kina lafiya?""" """Alhamdulillah."" Tace a gajarce ta matsa wajen wasu kujerun roba guda biyu ta dauko daya ta kawo" masa. """Bismillah zauna kana ta tsaiwa.""" Hannun sa ya dora a saman kujerar ta kalli hannun yayi saurin janye shi ya zauna sannan yace """Kefa?""" "Wani dan tudu a wajen ta nuna masa da hannu, ta zauna akai tana jin duk ta takura ganin yadda yake" bin ta da kallo da wasu irin idanun sa da suka sake shiga ciki sosai. """Na same ki lafiya? Ya gida yasu Mama da yan uwa?""" """Lafiya lou Alhamdulillah.""" """Ban gane waye ba amma?""" """Me sonki ne, me kaunar ki da son duk wani farin cikin ki, yan kwanakin nan da na dauka banga" "wucewar ki ba, sun zame min kwanaki mafiya muni a rayuwa ta. Na kan zauna a duk yini ina dakon wucewarki, ban taba yunkurin yi miki magana ba, sai dai zuciya ta, ta gaza dauka har sai dana biyo bayanki, ina fatan ban takura miki ba?""" "Girgiza kai tayi tana jin wani bawai, wai ita ake karantawa wannan kalaman, idan har taji daidai wato ya" "dade yana bibiyar ta, bata ma sani ba." """ Kinyi shiru!"" Yace yana gyara zaman sa" Shirun ta sake yi dan bata san me zata ce masa ba. """ Nasan dama karambani ne irin nawa, ban kai ajin ko da me wanke miki takalmi bane, kiyi hakuri idan" "nayi miki shishigi a rayuwar ki.""" """ A ah wallahi, ba haka bane ba, a kalla mutumin da yace yana son ka ai yafi makiyinka, nagode sosai da" "soyayyar ka gareni."" Tace da sauri sannan tayi murmushi, ji yayi kamar zuciyar sa zata fito daga kirjin sa, ya danne sosai ya maida mata murnushin" """Nagode Nuryyy... Nagode sosai.""" "Shiru ya biyo baya, ta dinga wasa da gefen Hijab dinta shi kuma yana satar kallon ta. Nutsuwarta tafi" komai tafiya dashi. """Bari na wuce.""" "Da sauri ta mike kamar me jiran kad'an," """Ka gaida gida."" Tace tana saurin yin gaba" """Ko zan samu number waya dan Allah?""" "Tsayawa tayi ta mika masa hannu, ya shafa aljihun sa dukka" """Kinga garin sauri na manta wayar a daki, amma zan rik'e fad'a min.""" """Ok ."" Tace ta karanto masa," """ Nagode sunana Muhammad.""" """ Fatima, ka gaida gida.""" "Ta juya ta barshi a tsaye a wajen. Sake maimaita sunan Fatiman yayi, ya saki murmushi a hankali sannan" ya juya ya fice daga gidan. "***A zaune a falo ta tarar da Mama na waya, zata wuce ta tsaida ta da hannu ta cigaba da wayar ta" """ Ba za dai ka bar maganar nan ba ko Khalil? Toh shikenan sai kazo din dai ma sake tattaunata, idan yaso" "ko a dangi ne sai ka duba sosai ba za'a rasa ba ai.""" "Amsa ya bata daga bangaren sa, ta ja tsaki tace" """ Matsalata da kai kafiya wallahi toh sai anjima, sai kazo din.""" Ta kashe wayar ta dangwarar da ita a gefen ta """ Na rasa shegen taurin kai irin na Khalil wallahi, sam baya kaunar ya ganni cikin farin ciki, mtsw.""" Ta sake jan tsaki a karo na ba adadi. """ Daga ina kike?""ta jeho mata tambayar bayan ta riga ta san inda take." """ Wani ne yazo dama.""" """ Waye shi?""" """ Bansan shi ba nima, wai a bayan layi yake.""" """ Toh kina jina? Idan zaki yiwa kanki kiyamullaili ki rik'e shi hannu bibiyu toh, idan kuma kika yi" "wasarairai da shi shima ya gudu kamar sauran, sai ki zauna muyi ta jerawa a gidan nan,tunda dai bakin hali ya hana samarin zama kowa yazo sai ya tafi.""" "Bata dago ba, bata kuma ce kala ba, tana jin Maman tana kuma ajiye kowacce magana a mazaunin da ya" "dace, sai da ta gama yi mata cin fuskar sanann tace" """ Khalil zai zo gobe, babu ruwanki dashi da shiga harkar sa, ko falo bana so naga kina kaiwa da komowa" "har ya tafi, zan fi so ki tattara ki koma wajen Gaji da zama aikin ma na yafe miki, idan ya gama kwanakin ya tafi shikenan, bana son daukar magana dan shi ba kunya magana yake ji ba, kinji dai na gaya miki.""" """ In sha Allah.""" """ Jeki.""" "Tashi tayi ta bita da kallo ranta na tafasa, da gaske take kishi da ita dukda bata zauna da mahaifiyar ta ba," amma duk sanda ta kalle ta sai ta tuno abinda ya faru. "****A guje suka taso ganin ya fito, ya nufi wajen da jerin motocin ke fake suna jiran sa, ransa a bace" "yake da kiran amma bashi da ikon kin amsawa, dole ya ajiye shirin sa a gefe ya kirawo su domin ba zai taba yarda da shigar masa shirin sa ba. Shiyasa su kansu basu da yakini ko masaniyar komai, dan ya" tabbatar da zasu taimaka wajen lalata masa shirin sa. Dan su din basu da ikon kansu sai abinda aka gindaya musu. "Bud'e masa bayan motar daya daga ciki yayi, ya russuna kad'an sannan yace" """We are very sorry sir!""" "Be tanka masa ba, ya shige cikin motar ya jingina bayan sa da kujerar ya lumshe idon sa." """Oga Main house zamu?"" Yayi tambayar yana tada motar" """Lamido Crescent!"" Yace yana sake rufe idon sa." "Chan suka wuce direct, suna isa ya fito ya shige ciki, tun daga falo ya fara wurgi da kayan jikin sa, ya rage" "daga shi sai boxer da farar singlet, kallon kansa yayi a jikin tangamemen mudubin dake tsaye kikam a falon, ya juya ya sake juyawa sannan ya wuce zuwa cikin bedroom din sa." Wanka ya fara yi a gurguje sannan ya fito ya shirya cikin shigar babbar riga da jamfa da wando farare "kal, sau cikin sa ya jawo ya ajiye a gefe ya fara saka farar socks a ciki sannan ya saka ya fito rik'e da babbar rigar a hannu." "Zama yayi sannan ya danna remote din kofar, da sauri suka shigo su biyu, ya mik'a wa daya babbar" "rigar, karba yayi ya taimaka masa ya saka sannan ya dauki abubuwan da yasan zai bukata ya fita dasu." """Ka zauna anan zan kiraka da zarar na sauka.""" Yace da dayan sannan ya tashi ya fice cikin takun da yafi kama dana jinin sarauta. "Motoci biyu ne suka fita daga gidan, shi yana cikin daya su kuma suna bin sa a daya har zuwa airport." *Muhammad Ahmad Santuraki* *(*Captain Moh*)* *_WAIWAYE ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_* *ZAFAFANKU BIYAR sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma "TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*" "*_SANIN HALI. yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi" "wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*" "*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu" kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi* *JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE* *_DEEN MARSHALL Mamuhghee_* *_HALIN GIRMA hafsat rano_* *_TAKUN SAƘA billyn abdul_* *_SO DA ZUCIYA miss xoxo_* *_ƊABI'AR ZUCIYA huguma_* *DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL* 2 400 3 500 4 700 5 1000 *Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA keystone bank Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 08184017082 "*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*" 09134848107 *_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_* #team zafafa biyar*HALIN GIRMA* *_Hafsat Rano_* 4 **** *Adamawa-Yola* "Tun daga yanayin manyan motocin da suka cika harabar ya tabbatar da bakin dake cike da fadar, yana" "da yakini dalilin kiran Bubun kenan a kalla zasu ganshi sannan ayi masa maganar da tafi komai kona masa rai, maganar mulki da yake dukkan kokarin sa wajen guje mata." "Be jira an bud'e masa ba, ya balle murfin motar ya fito bayan hango Aji da yayi yana nufar ciki tare da" "tawagar sa, da saurin sa ya cimmusu,domin ya samu su shiga a tare, ko ya gujewa idanun Bubun daga zuwan nasa. Yasan a cike yake taf dashi" """Aji!"" Ya kira shi da sunan da yake kiran sa" """Hoo d'an nema, na dauka ba zaka zo ba ai.""" """ Na isa naki amsa kiran ka ko na Bubu? Ai ban isa ba.""" """ Dadin baki, idan har da gaske ne ai sai ka amsa kiran da muka jima munayi maka ko?""" "Sosa keya yayi ba tare da yace komai ba, suka karasa ciki. Da ido Bubu ya kafe shi tun shigowar sa," "tabbas ya rame fiye da ganin da yayi masa kwanaki da suka wuce, sannan akwai wani yanayi a tattare dashi da be gamsu ba, a gabansa ya tare, ya kwashi gaisuwa ya cigaba da bin sa da idon ba tare da shi ya yarda sun hada ido ba, gefen Ajin ya samu ya rabe yana sake hade fuskar sa tamau, murmushi kawai Bubu yayi ganin da gaske Muhammad yake har yau yana nan akan bakan sa, ya rasa dalilin da ya saka shi baya son mulki ko kad'an, tamkar ba dan naga da ba, kamar wanda aka juyawa tunani kwata kwata akai, gashi da gaske yake jin ya kamata ace ya huta, yakamata ya karbe shi kamar yadda ya karbi Aji a lokutan baya. Sai dai d'an nasa sam be shirya hakan ba, abinda yasa yake dada jan lokacin sosai, burin sa kawai yasa a gaba tun bayan shigar sa jami'ah, in da ya kwallafa rai akan aikin tsaro, ya kuma samu cikar burin" sa duk da ba hakan ne ya kasanci burin sa ba shi. "Kamal ne ya shigo wajen, ya gaida kowa cike da girmawawa sannan ya samu gefe ya zauna yana" "fuskantar Muhammad din, kallon juna suka yi ba tare da wata magana ba, murmushi kawai Kamal din ya sakar masa wanda ya kasa maida masa domin ya san ma'anar sa, be damu ba ko kad'an, da ace Bubu zai ji shawarar sa da ya jima da yiwa Kamal din abinda yake muradi, amma shima kemaimai yaki, ya kwallafa" "rai akan Muhammad din, ko me yasa? Oho. Ya dage kafadarsa alamun baya da bukatar ya sani ma dai." "Duk batutuwan da aka tattauna a wajen be tsinci komai ba, zuciyar sa ta lula chan zuwa in da ya baro," "tunanin halin da take ciki ko abinda take aikatawa kawai yake har kusan kowa ya gama ficewa ya zama na daga shi sai Aji, da Bubu." """Muhammadu."" Yayi firgigit sai kuma ya hau sosai kai yana murmushi" """Barka da rana Bubu.""" """Kalli shigar ka fa Muhammad, kalle ka? Hakan ya dace a matsayin ka da gidan nan? Haka kaga dan" "uwanka Kamal yayi shiga irin ta masarauta?""" """Wallahi Bubu garin sauri ne, kuma gashi ba wani iya nada rawanin nan nayi ba wallahi, infact ciwon kai" "wallahi yake sani, amma za'a gyara ba za'a sake ba.""" "Murmushi Aji yayi me dan sauti, ya kalle shi yana sake fadada fara'ar fuskar sa." """Ayi hakuri ranka ya dade munyi kuskure ba zamu sake ba."" A duk sanda irin hakan ta faru Ajin ne ke yin" "uwa yayi makarbiya ya hana ayi masa fad'a, hakan yasa ba kasafai Bubun ke korafi gaban Ajin ba, sai ya tsuke bakin sa kawai be sake cewa komai ba." "Tashi yayi, ya dan russuna a gaban mahaifin nasa" """Zan shiga ciki Bubu!""" """Ka same ni a shashe na bayan sallar magriba.""" """ In sha Allah. A tashi lafiya.""" """ Aji sai na shigo wajen yar tsohuwa ta.""" """ Tana nan tana jiran ka da manshanun ta da yajin daddawa.""" "Murmushi yayi, ya fice suka raka shi da ido. Yana fita Bubu yaja tsaki" """ Na rasa me yake damun yaron nan wallahi, ace yaro ya taso a cikin abu amma sam ya tsane shi?" "Wannan wanne irin abu ne?""" """ Mu cigaba da hakuri kawai Ahmadu, komai zai wuce ne.""" """ Allah yasa, kowa jira na yake, mutanen gari da manyan mutane kowa ya zuba ido yaga me zanyi akai," "ga Kamal da gaske yake son mulkin nan, gashi sam be chanchanta ba, na rasa yadda zan.""" """Shima ka barni dashi kawai, ayi masa abinda yake so din, yanzu dai a zaman da zakuyi sai kayi masa" "maganar auren muji, a kalla auren zai taimaka masa ya zauna a cikin mu, kaga dole ya koyi komai.""" """ In sha Allah, idan ma bashi da yarinyar da tayi masa ni zan nemo masa.""" """ Kul, Muhammad ba irin yaran da za'a yi musu haka bane, mu da muke son amfani da soyayyar shi ga" "yarinyar, abi dai komai a sannu.""" """ Shikenan in sha Allah, Allah yasa mu dace.""" """ Amin ya Allah.""" "***Bangaren Ammin sa ya wuce, yana tafe yana amsa gaisuwar da ya tsana, ayi ta gaida mutum kamar" "wata tsiya, hakan na daya daga cikin abinda yake hada shi da gidan su, ya gwammace yayi guduwar sa waje daya kawai ba tare da hayaniyar mutane ba." "Tana zaune ta dora kafarta a saman dan tumtum din dake falon, kafar na damun ta sosai shiyasa ko" "yaushe zaka ganta a mike ana dan mammatsa ta. Yana tura kofar duk suka mike, har rige rigen gaishe shi suke kowa yasan yadda Ammin ke masifar ji da tilon dan nata, mace me kirki da sanin yakamata, shiyasa ta karbe kowa a gidan daga ma'aikata har dangi kowa nata ne, wajen Bubu ma Itace star,itace kuma" uwar gidan sa dan dai Allah be bata yawan haihuwa bane. """Barka da zuwa yarima, sarki me jiran gado, uban mara uba me uban ma kaine gatan sa, shalelen" "Gimbiya da maimartaba, ka tsare gaba ka tsare baya, Allah ya kara maka daukaka da girma, Allah ya ida nufi.. sai...""" "Da sauri ya dakatar da ita, sai ta juya sum-sum-sum ta fice, ya kalli Ammi yayi mata murmushi kafin ya" zauna a daidai saitun kafafun nata ya tankwashe kafafun sa """Ashe zaka zo."" Tace masa tana murmushi itama" """ Na isa naki zuwa Ammi? Barka da gida mun same ku lafiya?""" """ Lafiya lau Alhamdulillah , shiru daga cewa zaka je wani aiki Kano shikenan kamar an aiki bawa garin su," "su ba labarin su da suka bika kaima ba labari, gidanka da kake sauka ma an ce min ba chan ka sauka ba.""" """ Wani babban aiki ne ai Ammi, ki tayani da addu'a kawai in sha Allah zakuji labari me dadi.""" """ Allah yasa toh, ya aikin naku?""" """ Alhamdulillah wallahi, muna ta fama, ba dadi amma haka dai za'a cigaba da lallabawa.""" """ Tunda kana so ba."" Tace." Dariya ya saka kawai be ce komai ba. Ya dan jima a tare da Ammin tasa kafin ya tashi ya yi mata sallama "zuwa shashen shi, da yake kusa da na Bubu." "Yana shiga ya tarar da kayan abinci a jere a falon nasa, sai kamshin turaren wuta dake fita ta cikin yar" karamar burner din dake makale a jikin wani dan karfe. "Wuce komai yayi zuwa bedroom dinsa, ya kwanta rigingine a saman gadon ya jawo woyoyin sa, ya" "shiga cikin contact dinsa, number farko da yayi saving dinta da emoji din heart da padlock ya danna kira ya kwanta sosai yana lumshe idanun sa lokacin da ta soma ringing..." "****Da safe ta tashi kamar kullum tayi duk abinda tasan wajibin ta ne, har zuwa sanda rana ta fito sosai," "kayan ta na wanki dana Marwan ta hada ta zagaya baya ta hau wanke su, daga gefe ta ajiye wayarta" "tana jin karatun alkur'ani me girma, tana wankin tana bi har ta gama tsaf, ta tattare su ta shanya sannan" "ta dawo ciki ta chanja kayan ta, ta fice zuwa shashen Gaji." "Fitar ta kenan Khalil ya shigo, maigadi na bin sa janye da katotuwar trolly din sa a baya. Da Habib suka" "ci karo yana kokarin fita, ya bashi hannu suka chapke cike da murnar ganin juna" """Welcome welcome."" Yace masa yana juyawa suka shiga ciki. Da sauri Mama ta fito jin hayaniyar su.." """Wa nake ji kamar Khalil, inyee lallai yaron nan Ashe dai da gaske kake.""" """Gani dai, ai dama na gama shirin zuwa kawai ban sanar dake bane sai jiyan.""" """Maraba lalle da manyan yan jarida.""" "Zama yayi a cikin kujerun falon, itama maman ta zauna tana gyara dan kwalin kanta." """Wai dama kinsan zaizo Mah?""" """Nima sai jiya na sani, na zata kuma halin nasa ne Ashe da gaske yake shiyasa ma ban fad'a ma kowa" "ba.""" """Ina wuni Anty?""" """ Lafiya lou Khalil, yaso Hajiya da kowa da kowa?""" """ Duk suna nan lafiya, itama tayi mamaki da nace zanzo, gashi kuma zan dade sosai dan aiki ne ya kawo" "ni.""" """ Ahaap ko da naji, Ashe zuwan dai da dalili, jairi dama nasan akwai abinda ya kawo ka.""" """ Abubuwa dai Anty, karki manta da wannan maganar tamu hadda ita ma.""" Tsaki taja ta harare shi """ Zaka fara ko?""" """ Nayi shiru."" Yace yana dora hannun sa baki" """ Yafi maka dai.""" """ Ina su Zeenat ne? Banji duriyar su ba.""" """ Zaka ji su ne ai ba dai kananan ba, ka tashi ku shiga ciki ka huta kaci abinci, sannu da zuwa.""" "Tashi yayi, yabi bayan Habeeb suka wuce dakin sa suna hirar yaushe gamo, idanun sa da kunnuwan sa na" "jiran yaji ta inda zasu bullo, he can't wait to see her beautiful face, ko me Anty zatayi masa kuwa ba zai fasa bawa zuciyar sa abinda ta dade tana so ba. Kishin ta daban soyayyar sa daban. Period!" "****Zaman ta a bangaren Gajin yafi komai yi mata dadi, abu daya ne kawai yake dan takura ta yawan" "maganar Gajin, duk da haka take daurewa tana amsa mata, gashi ta manta wayar ta a kitchen bayan ta gama wankin nan, gashi taji alamar Khalil din yazo ta tabbata idan taje dauka zasu iya haduwa, ta kuma san me hakan ke nufi a wajen Mama." "Zaman ta ta cigaba kawai har sanda taji ana kiran sallar, alwala tayi ta zauna ta jira a tayar, tana jin" "sanda za'a tada sallar ta fita zuwa bangaren nasu, lokacin tasan sun tafi sallah Maman ma kuma ta shiga ciki tayi sallar itama, ta baya ta bi, ta shiga kitchen din a daidai lokacin da ya saka wayar a kunnen sa" """Waye?""" "Yace yana gyara rikon da yayi wa kofin hannun sa, tashi zaune Moha yayi da sauri, ya kalli screen din" wayar ko be kira number daidai ba? Kai Anya? Daidai yadda ta fad'a masa ne """Fatima nake nema, ko tana kusa?"" Yace jin me maganar ya sake tambayar waye a karo na biyu." """Fatima? Malam Waye kai din da kake neman ta?""" """Sanin waye ni ba zai taba maka dadi ba, idan tana kusa ka bata zanyi magana da ita.""" """ Ba zan bata ba, abun yar karfi ne kazo ka karba idan kana dashi, mtsw.""." "Yaja dogon tsaki hade da kashe wayar, kafar ta ta sako a kitchen din zata shigo domin ta karbi wayar ta" "da ya daga mata ba tare da izinin ta ba, muryar Mama ta dakatar da ita, ta juya da sauri ta bar kitchen din." """ Kai kuma me kake anan kana jin an tada sallah?""" """Ruwa nazo sha.""" "Yace yana juyawa ya bar kitchen din, kofar bayan ta leka ta tabbatar babu komai a wajen, tayi kwafa ta" juya bayan ta jawo kofar ta ciki. "Wani irin tashin hankali ne ya ziyarce shi, ya tashi da sauri yana jawo dayar wayar tasa, cikin kankanin" "lokaci ya birkice ya koma Captain Moh din sa na ainihi, a yau ba sai gobe ba zai juya, dan ba zai taba daukar rainin hankali ba, ba dan ganin da zai wa Bubu ba, da babu abinda zai hanashi daukar hanya a" "yanzu, amma dole ya hakura zuwa lokacin da ya dauka masa duk da yana ganin yayi masa masifar nisa." "Kaiwa da komowa ya dinga yi a tsakanin dakin, zuciyar sa tamkar zata hudo daga kirjin sa saboda tsabar" kishi. _WAIWAYE. ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_* *ZAFAFANKU BIYAR sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma "TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*" "*_SANIN HALI. yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi" "wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*" "*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu" kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi* *JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE* *_DEEN MARSHALL Mamuhghee_* *_HALIN GIRMA hafsat rano_* *_TAKUN SAƘA billyn abdul_* *_SO DA ZUCIYA miss xoxo_* *_ƊABI'AR ZUCIYA huguma_* *DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL* 2 400 3 500 4 700 5 1000 *Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA keystone bank Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 08184017082 "*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*" 09134848107 *_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_* #team zafafa biyar *****HALIN GIRMA* *_Hafsat Rano_* *5* *_Last free page!_* **** "Tana zaune ta idar da sallah, bata tashi daga kan abun sallar ba taji shigowar sa shashen Gajin, gabanta" "taji ya fadi, tayi kamar bata ji sallamar da yayi ba, tayi tsam a kan sallayar tana kallon gabanta. Da kallo ya bi bayan ta ya samu waje ya zauna a cikin kujerun falon yana kokarin daidaita yanayin da yake ciki. Gajin ce ta fito," """Wa nake gani kamar Ibrahim?""" """Nine nan wallahi Hajiya.""" """Lale marhabin, barka da zuwa. Saukar yaushe?""" """Dazu na shigo, mun same ku lafiya?""" """Lafiya lou wallahi, yasu Hajiyan da yan uwanka?""" """Kowa lafiya suna gaida ku.""" """Muna amsawa, sannu da zuwa.""" """ Yawwa."" Yace yana yawo da idon sa akan ta," """ Iman ba magana?"" Yace yana son Gajin ta tanka" """Kaji sokonci, wai bata gaishe ka ba?"" Tayi maganar da sauri" """Ina wuni?"" Tace a gajarce" """ Lafiya lou, kina lafiya?""" "Shiru tayi bata amsa ba, Gaji ta hau sababi tana mata fad'a, tashi yayi hannun sa cikin aljihu ya zaro" wayar ta """Gashi na tsince ta a kitchen.""" "Ya mik'a mata sannan yayi wa Gajin sallama ya fice yana raya ta yadda zai bulowa Iman din, ya gama" "gane yanayin ta ba irin nasa bane, shirun ta yayi yawa amma duk da haka shi ba damuwar sa bace, yadda ya shiga zuciyar kowa a gidan nan da hakan zaiyi amfani ya kafa kansa, ba zai wani ja lokaci ba zai gabatarwa Gaji da kansa, baya jin ma zai wuce gobe, zai sai fara tuntubar Yaya Hajara idan yaga ba ta goyi bayansa ba zai yi gaban kansa, iya ka tayi masa fad'a shikenan ya wuce. Be koma shashen ba, sai ya fice daga gidan a kafa yana adana number da ya dauka a wayar ta ta, so yake ya saka number a" truecaller yaga ko zai samu wani information akai. "Cikin call log dinta ta shiga ta duba amma bata ga number da aka kirata ba, taji babu dadi dan bata so" "yaga kamar tana sane ta bayar aka daga wayar tasa. Ko da tafiyar su ba zatayi daya ba, ba zata so yaji a ransa dan yana lacking wani abu bane shiyasa hakan ta faru. Kwantar da kanta tayi a saman hannun kujerar ta rufe idon ta tana tariyo zuwan da yayi wajenta, akwai wani abu me girma a muryar sa sai kuma abu daya da ya tsaya mata shine kamshin turaren da taji yana yi, wanda yayi kama da me tsada ne irin ajin farko, domin Allah ya hore mata kaunar kamshi, shiyasa ta kan yi saurin ganewa. Sai dai akwai irin tuurare yan durin nan da suke da kamshi me dadi har ka kasa tantance su, kila irin su ne, abunda ya kara burgeta dashi kenan, duk da yana cikin yanayin da zaka ce kai tsaye babu, amma be bar kansa a" wulakance ba. Juya kanta tayi daya gefen ta dora wayar a saman cinyarta ta cigaba da tunani. "***Kiran sallar magriba ya sashi fita daga sashen nasa zuwa masallaci, achan yayi alwala ya shiga sahun" "farko sukayi sallar. Bubu na ganin shi yaji dadi sosai. Bayan an idar ya wuce bangaren nasa domin ya jira shi, yana zaune sai gashi ko ya shigo, ya tashi tsaye har sai da ya zauna sannan ya zauna shima a k'asa cikin girmamawa ya sake gaishe shi, ya amsa masa sake yana nazarin sa." """Muhammadu!"" Ya kira sunan sa, gyara zaman sa yayi ya tattara hankalin sa waje daya cikin son ganin" be yi wani abu a gaban Bubun ba """Kana ji na Muhammad?""" """Inaji Bubu.""" """Madallah, Muhammad ka san dai a tsarin gidan nan kana cikin lokacin da ya kamata ace ka ajiye iyalin" "ka kaima, ka nutsu waje daya a kalla hakan zai taimaka maka wajen cikar kamalarka.""" "Kansa a kasa yana jin Bubun yayi ta bayani yana gida kansa cike da gamsuwa," "**A kofar ta tsaya tana kallon takalmin Muhammad din dake zube a wajen, ta samu labarin zuwan sa a" "wajen Kamal amma bata tsammaci irin wannan ganawar da Maimartaba ba, shiyasa ta kasa hakuri tazo ta nemi iso wajen Maimartaba din wajen sarkin kofa amma sai ya nuna mata ba zai yiwu ba, domin an gargade shi akan barin kowa ya shiga shashen maimartaba din har sai ya kammala ganawar sa da Muhammad din, ranta a matukar bace ta koma sashen ta tana jin wani irin tashin hankali, tana tsoron" kar Muhammad din ya amsa tayin mahaifin nasa a wannan zaman da zasuyi. "Safa da Marwa tayi tayi, har wajen sallar isha basu fito ba, tana hangen bangaren ta cikin nata shashen," ta kasa zama tana da yakinin ko menene suke tattaunawa haka me muhimmanci ne sosai. "Tana tsaye jikin window taga fitowar su, fuskar Muhammad din a sake yana takewa mahaifin nasa" "baya. Tsaki taja ta saki labulen tana juyawa zuwa gefen gadon ta, ta zauna tana sake jan wani tsakin, tsakin haushin Muhammad din da ya zame mata ciwon ido shi da mahaifiyar sa." """Ranki ya dade, Maimartaba ya aiko yana da bukatar ganin ki bayan ya dawo sallar isha'i.""" "Bata amsa ba, sai ma juya fuskar ta da tayi wani sashen tana sake sakin siririn tsaki." "***Bangaren sa ya koma, ya tattaro abunda ya san zai bukata ya fito, sai kuma ya tuna da maganar" "Maimartaba ta karshe da suka tattauna, yana son ganin sa da safe kafin ya fito fad'a, komawa yayi ba" "dan yaso ba, ya ajiye komai ya zauna yana kirga lokacin zuwa wayewar gari. Nisan yayi yawan da yake jin kamar yayi loosing idan har ya kyale shi tsawon wannan lokacin." "Wayar sa dake ajiye a gefen sa ta dauki sowwa, ya daga ganin kiran da yake ta jira ne tun dazu," """Oga na duba maka number din, akwai bayanan sa da komai har da wajen aikin sa, hoton sa da kuma" "location dinsa a yanxu, na tura maka ta mail sai ka duba.""" """Ok! Thank you, zan neme ka. """ "Ya katse kiran ya shiga mail dinsa, ya hau kan message din ya bud'e. Hoton sa ya bud'e yayi zooming" "sosai, sai kuma ya fita ya karanta information din. Karamin tsaki yaja ya ajiye wayar yana jin a ransa wannan din karamin kwaro ne be kamata ya hana shi walwalar sa ba, abu daya zai masa ya kama shi a" "hannun sa, sai dai ba zai hakan ba har sai ya je ya tabbatar da zargin sa." "***Anan sashen Gajin ta shirya, ta wuce islamiyya tana tafe tana satar kallon hanyar ko zata ganshi" "tunda yace mata yana zama ne domin yaga wucewar ta, har ta isa makarantar bata ga ko me kama dashi ba, sai kawai ta share tayi abinda ya kaita. A dawowa ma haka ta sake yi shima bata ga kowa ba, ta dawo gida ta chanja kayan ta kenan aka shigo aka ce tazo inji Muhammad, Hijab ta dora a saman kayan jikinta ta fito. A tsaye yau ma ta hange shi wajen kujerar, ya rataye hannayen sa a bayan sa yana tsaye kyam" akan kafafun sa. """Assalamu alaikum."" Tayi masa sallama tana jan kujerar." """Sannu da zuwa, nan akwai rana bari na saka maka a chan."" Taja kujerar zuwa k'asan wata yar bishiya ta" "ajiye," """ Bismillah."" Tace masa tana nuna masa kujerar, be zauna ba, ya zaro hannun sa daga bayan sa, ya dawo" "dasu gaba ya rungume su a kirjin sa," """ Bismillah."" Ya nuna mata kujerar da baki" """ Zauna babu matsala."" Yace mata" """ A ah dan Allah ka zauna, be kamata na zauna kana tsaye ba, ance bakon ka...""" """ Kyale fadar hausawan nan, zauna dan Allah.""" "Allah da taji ya ambata yasa ta zauna a kunyace, ya zura mata ido har sai da ta dan ji wani iri." """ Na cika kallo ko? Kiyi hakuri."" Yace mata yana murmushi,kallon ta kadai yayi jin sa yake kamar yafi" kowa sa'a a duniya """ Ba komai."" Tace tana gyara wayar hannun ta" """ Ina wuni?"" Ta gaishe shi yana dan zamowa" """ Lafiya lou, sai kika jini shiru, tafiya nayi zuwa kauye Baba ya kira ni, naso ma na zo kafin na wuce toh" "tafiyar ce tazo a gaggauce, sauka ta kenan ma.""" """ Allah sarki... Allah yasa lafiya.""" """ Lafiya lou, sai godiya. """ """ Ka baro su lafiya?""" """ Alhamdulillah. Nagode da kulawa.""" """ Ba komai."" Tace tana wasa da hannun ta." "Turo gate din akayi, Habeeb na gaba yana bin sa a baya, wani irin daukewa yaji ganin sa na neman yi." "Iman zaune tare da wani suna hira, a cikin gidan kuma? Be san sanda ya isa wajen ba, sai ganin mutum sukayi a gaban su." "Wani kallo Moh yayi masa, yayi murmushi yana taune gefen lips dinsa na kasa" """Yaya sannu da zuwa."" Yace yana mika masa hannu, kin bashi hannu Khalil yayi, sai Habeeb ne suka gaisa," ya daki kafadar Khalil din """ Muje ko?""" """ Yi gaba ina zuwa."" Yace masa," """Ok."" Ya wuce ya bar Khalil din a tsaye" """ Iman shiga gida."" Yace a gadarance, ta dago ta kalle shi da sauri, ya hade girar sama data k'asa tamau" irin ba wasa din nan. """My heart, ki shiga gida ki huta dama naji ba zan iya zuwa gida ban zo na ganki ba, shiyasa na taho nan" "kai tsaye, zan kira ki anjima ki ajiye waya a kusa dake kinji?""" "Kunya ce ta kamata ta noke, ta mike da k'yar tace" """Ka gaida gida."" Sannan ta wuce ciki, tana barin wajen ya hade fuskar sa sosai." """ Da tsakar ranar nan ka taso yarinya, kazo zaka ishe ta da uban surutu, ku dama talakawa haka kuke, da" "kunga yar hanya sai kuzo kuce kuna so, kai kanka kasan ba sa'ar ka bace, ba sa'ar auren ka bace shishigi" "dai, toh ita din matata ce, ni zan aureta an gama magana, sai kaja tsumman kafafunka a koma in da aka fito, ka samu daidai da kai.""" """ Zaka ga tasirin talaka da talauci kuwa, baka da ikon tsarawa kowa rayuwa, haka arziki ba wani abu" "bane face fitina, wadatar zuciya itace mutum..."" Ya dan matso gaban sa" """ Mark my word, a gaban idon ka, right under your noses, talaka zai baka mamaki, mamakiin da har ka" "kare rayuwar ka zaka fita daga cikin sa ba, count down dinka ya fara daga yanzu.""" """ 1,2,3!"" Sai na jika." "Ya juya ya fice daga gidan cikin takun da ya tsayawa Khalil a rai, cikin wani irin yanayi yayi cikin gidan" "yana jin yanzu ba sai anjima ba, zai yi abinda ya dace, gida be koshi ba, babu yadda za'a yi a bawa dawa." **A tsaye ya tarar da Habib yana ganin shi yace """Kaiko me ka tsaya yi ina ta jiran ka.""" """Abinda ka kasa yi, kana ganin kanwar ka da mutum a tsaye, kana ganin sa kaga mara gaskiya, wa ya sani" "ma ko dan boko haram ne da wannan uban kasumbar, amma baka damu ba kayi tafiyar ka, hakan ba daidai bane.""" "Kallon sa Habib yayi, mamaki na kamashi," """ Yaushe hakan ya zama ba daidai ba khalil?""" """ Habib, maganar gaskiya ina son Iman, son da ni kaina bansan adadin sa ba, zan iya komai akan na" "sameta, dan haka ba zan iya jure ganin ta da kowa ba, musamman mutum irin wannan da ya nuna alamun rashin gaskiya, gashi fakiri jibi shigar jikin sa, no ba zan iya ba, rakani wajen Gaji ayita ta kare.""" """ Idan har kai din jinina ne, idan har na isa da kai babu kai babu Iman Khalil, na rasa kafiya irin taka, na" "rasa dagiya irin taka, bayan maganar nan mun dade da gama ta, na gaya maka ba zai taba yiwuwa ba.""" """ Akan me? Dan Allah Anty ki gaya min hujja me karfi a musulunci da ya haramta min auren ta, na daya" "ni ba muharraminta bane tunda ita din ba ke kika haife ta ba, toh sai menene? Akan dalili mara tushe?""" """ Akan duk abinda zaka kira shi Khalil ka kirashi, amma idan har ina numfashi ba zamu hada jini ba" "wallahi, ga mata nan bila adadin, me yasa sai ita, wannan da yazo shi ya dace da ita, shine daidai da matsayin ta, inaso auren da zatayi ya zama sakayyar aure min miji da uwarta tayi, ta saka yayana samun" "yan Uba!.""" """ Ohh shit! Kin kasa fuskanta ta Anty, kiyi hakuri wannan karon zabin raina zan bi, zanje na samu Gaji na" "sanar da ita, gwara kowa ya sani a san me yakamata ayi.""" """ Khalil!""" "Ta k'wala masa kira, ya juya da sauri yayi hanyar fita, wayar sa tayi kara, ya tsaya chak jin layin da yake" "ajiye numbers din manyan mutanen sa ne, ciro wayar yayi sunan Sir ya bayyana a wayar, ya daga da sauri yana daidaita numfashin sa" """ Kana ji Ibrahim? Sako ne daga sama ba daga ni bane, an dakatar da kai aiki zuwa wani lokaci, za'a neme" "ka idan bukatar hakan ta taso."" Be jira yace komai ba , ya katse kiran. Da sauri ya dafe bangon da yake kusa dan ji yayi jiri na neman kadashi, gaba daya rayuwar sa akan aikin ta dogara, yana da passion sosai a Kai sannan yana iyakar kokarin sa wajen aikin sa, maganar promotion dinsa ma ake idan har ya" "kammala wannan assignment din da ya kawo shi Kano, shikenan sai dakatarwa haka nan ba wani dalili?" """ Ya akayi?! Habib ya matso ya taba shi ganin kamar ya shiga coma" *HALIN GIRMA* 6 "*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107*" _ASSALAMU ALAIKUM BEAUTIFUL PEOPLE!! ZAFAFA BIYAR FAMILY _ _MUNGODE DA ZABIN LITTAFAN ZAFAFA BIYAR. ALLAH YA KARA BUDI YA KUMA BAR ZUMUNCI_ "_KAMAR KO DA YAUSHE, WANNAN KARON MA MUNZO DA KOKON BARAR YOUTUBE CHANNEL DIN" "YARON MU, SUDEIS MASOYI KUMA MAKARANCI, MAHADDACIN ALKUR’ANI MA GIRMA_" _WANNAN KARON MA DAN ALLAH A TEMAKA ADANNA WA CHANNEL DINSA KARARRWA DOMIN "KASANCEWA DA MU A DUK SANDA MUKA DORA FEFAN BIDIYON SA, A TALLAFA A KALLA A KUMA DANNA MASA SUBSCRIPTION. HAKAN NA KARAWA SUDEIS KWARIN GWIWAR SAKE DAGEWA YA KUMA" KARA KAIMI WAJEN YIN KARATUN SOSAI. MUNGODE KWARAI _ _GA CHANNEL DIN DAKE YOUTUBE NAN _ https://youtube.com/c/sudaiskura _Sudais is a young boy who has passion in recitation of the Holy Qur'an at a very young age._ _Please help him grow his YouTube channel by subscribing and liking his videos to encourage the little boy. Jazakumullahu khairan _ *** Girgiza kai ya hau yi da sauri da sauri. """Habib aiki na, innalillah wa inna ilaihi rajiun.""" """Me ya samu aikin naka?"" Mama ta matso da sauri tana rik'e shi" """Wai sun dakatar dani, babu wani kwakkwaran bayani kawai wai daga sama ne.""" """Innalillah wa inna ilaihi rajiun, zo ka zauna, rik'e shi Habib ya zauna.""" "Zaunar dashi Habib yayi, yayi saurin dauko masa ruwa ya mik'a masa" """Sha ko zaka ji sauki a zuciyar ka, ba wani abu bane babba in sha Allah, wata yar matsala ce zasu gyara" "da yardar Allah.""" "Jujjuya kansa yake ya kasa magana, shi kadai yasan hakan me yake nufi, shi kadai yasan yadda yake ji a" "halin yanzu, tabbas idan suka hana mishi aikin nan sun yi masifar cutar sa, akan me? Me yayi haka da ya chanchanci wannan hukuncin? Bayan irin kokarin da yake ganin ya rik'e aikin sa, tsawon lokacin da ya dauka kafin ya samu aikin, da irin wahalar da yasha kafin ya kawo matsayin da yake, sai yanzu? Daga sama ta ka kawai ace an dakatar dashi? Innalillah wa inna ilaihi rajiun. Ya sake maimaitawa." """Kalle ni nan Khalil, karka ce zaka daga hankalin ka akan abinda kasan baka da iko dashi, kayi hakuri ka" "kwantar da hankalin ka, in sha Allah ba wata matsala bace, kaji?""" "Gid'a mata kai yayi kamar karamin yaro, ya kwantar da kansa yana jin kamar ya zubar da hawaye saboda" "bacin rai. Shiru sukayi kowa yana jimamin abinda ya faru, ya ma manta da abinda yake shirin aikatawa. Shigowa Zeenat tayi dauke da wasu manyan ledoji,uwar ta bita da kallo bata ce komai ba." """Daga ina kike?"" Habib yace yana bin hannun ta da kallo" """Bashir ne yazo.""" "Kallon Mama yayi, yaga ta dauke kanta" """Mama fa Bashir din nan naji wasu maganganu akan sa marasa dadi, ya kamata a duba sosai kafin a" "barta tana fita wajen sa.""" """Bana son maganar nan yanzu, dame zamu ji? Da abinda ya faru da Khalil din ko da naka zancen?""" "Tsuke bakin sa yayi be sake cewa komai ba, ya tashi ya bar falon ma," """Me ya samu Uncle Khaly din Mama?""" """Babu komai, ki wuce ki bani waje uwar yan magana.""" "Da sauri tayi gaba da ledojin ta, ta shige dakin uwar ta rakata da kallo kafin ta sauke ajiyar zuciya tana" tuna abinda ya faru daren jiya ita da Abban su. *** """Ya ake ciki da yaran nan?""" """Name fa?""" """Akan maganar yaran da suke zuwa wajen su, Yaya yayi min magana akai yace ya kamata asan abinda" "ake ciki, kindai san tsarin gidan nan ba'a wani daukar dogon lokaci ana zance.""" """Eh toh, ita Iman akwai wani wanda yazo.""" """Zuwan sa biyu kamar ko?""" """Ashe ka sani?""" """Eh ina sane da komai ai, kinga alamun zasu dai-dai ta ne? Naga zuwan nasa biyu dududu.""" """Toh idan bashi ba waye? Babu kowa ai.""" """Khalil din fa?"" Yace yana mata kallon mamaki" """Wai Dr bar maganar Khalil din nan, ba da gaske yake ba wallahi.""" """Ana wasa a maganar aure ne Hajara?""" """Shi dai yayi, gwara a tsayar da magana akan wanda yazo din dan da alama ba da wasa yazo ba.""" """Toh shikenan, Zeenatu fa?""" """Eh ita ai Bashir ne dama.""" Tashi yayi tsaye yana girgiza kansa """Ban yarda ba sam, ban amince da yaron ba, binciken da nayi akansa be min dadi ba, kamar ance min" "ma kuma yana da mata duk da hakan ba zai hana a bashi aure ba, sai dai na samu labarin bashi da hali" "me kyau gaskiya, a wani labarin ma ance min har zaman prison yayi, sai ki fad'a mata nace banda Bashir ta kawo wani.""" Hankalin ta a tashe tace """ Amma baka ganin sharri akayi masa? Don a hana a bashi?""" """ Akan me za'a masa sharri? Akan wanne dalili kenan?""" "Ya tsare ta da idanun sa, sunkuyar da kanta tayi bata ce komai ba, tsoron yadda za'a kwashe da Zeenat" "din take domin ta san yadda ta saka Bashir din a ranta, gashi babu laifi yana mata hidima sosai, hakan ya saka Maman sake yarda dashi da yar ta ta." """Bari na shiga ciki Anty."" Khalil yace yana mikewa, ta daga masa kai kawai ya wuce ya barta tana cigaba" da tunanin yadda zata bullowa al'amuran. "***Tana zaune a falon Gajin tana tunanin abinda ya faru tsakanin shi da Uncle Khalil, wayarta dake" "saman cinyarta tayi kara, ta kalli wayar ganin bakuwar number ya saka ta tashi, ta wuce zuwa bedroom din Gajin ta daga tana zama a gefen gadon ta" """Assalamu alaikum."" Tayi sallama cikin muryarta da tafi komai tafiya dashi, lumshe idon sa yayi ya bud'e" a hankali ya amsa sallamar ta ta """Wa alaikisalam...""" """Ina wuni?"" Ta gaishe shi jin muryar sa" """Lafiya lou Mi Love, na barki lafiya?""" """Alhamdulillah."" Tace a kunyace ganin shi kai tsaye yake maganar sa." """ Kina jina Zahraaah na? """ """ Na'am?"" Tace tana mike kafafunta" """ A zahirin gaskiya ba da wasa nazo ba, da gaske nazo neman auren ki ba kuma naso a dauki wani dogon" "lokaci in sha Allah, ni din dai ba wani bane kin dai ganni, bawan Allah ne me neman amincewar Fatima Zahra, ina fatan zaki bani dama dan Allah!""" """ Hmm..."" Ta sauke ajiyar zuciya maganganun sa na taba ta, me zata ce toh? Da gaske take jin ya kwanta" "mata duk da taga alamun ba wani shi nne dashi ba, amma sai taji yadda yake abu kai tsaye ya birgeta" "sosai, babu karya straight kawai yake maganar sa, bayan haka da gaske take son matsawa daga wajen Mama, ko ba komai ta samu yanci itama." """Baki ce komai ba?""" """Allah ya shige mana gaba, Allah ya zaba mana abinda zai zamar mana alkhairi gaba daya.""" "Wani irin dadi yaji ya shige shi, ya rufe idon sa, ya dau yan sakanni yana jin sonta na sake ruruwa a" "zuciyar ta, yana tuna tsawon lokacin da ya dauka yana dakon soyayyar ta, a lokacin da shi kansa be san me ake nufi da so din ba." "Mahaifiyar sa 'ya ce ga sarkin Kano kuma shi jika ne a gidan, hakan ya saka yake da alaka me karfi da" "garin na Kano duk da mahaifin sa da mahaifar sa Adamawa-Yola ne, rayuwar sa bayan ya tasa yayi ta ne tsakanin Kano da Adamawa, shiyasa babu in da be sanin a Kanon ba, yake kuma jin kamar yafi zama comfortably a Kanon, musamman da bashi da son hayaniya sosai sai nan din yafi zamar masa peaceful" wajen hutawar sa. "Akwai ranar da ya fito shi da abokin sa Musaddik, suna tafe a mota hanya ta biyo dasu ta area din su" "Fatima, a lokacin ya ganta duk da lokacin ba ta kai yanzu ba, be kuma taba jin abinda yaji akanta, shiyasa ya nace a lokacin suka yi ta bin ta har suka ga gidansu, suka kuma yi tambaya akan ta da komai. A lokacin yaso ya shigo da karfin sa, sai dai wani labari da ya samu ya sauya masa tunani da shawara, ya kuma" "yanke ma kansa shawarar da yake ganin itace zata daga masa darajar ta, a ranar da gaskiya ta bayyana." "Musaddik be aminta da shawarar ba duba da gidajen da Muhammad din ya fito, amma haka ya kafe" "akan bakansa, shiyasa ma kawai Musaddik din ya kyale shi amma fa kullum cikin masa korafi yake." "Bangaren aikin sa zai iya cewa yana cikin yan gata da sai abinda suka zaba da inda suka zaba zasu zauna," "kasancewar gaba daya k'asar babu in da kakan shi mahaifin Ammi zai nemi alfarma ba'a masa ba, sannan gefe guda mahaifin sa yayi sunan da zaka yi mamaki sosai." "Duk da hakan be daina aikin sa ba, sai dai babu wani matsi ko takura tun ma be kai matakin captain ba," balle yanzu da yake da rank me girma. """Kinsan me?""" "Yace yana gyara kwanciyar sa sosai, sanda Musaddik ya murda handle din dakin ya shigo bayan yayi" knocking ya bashi izinin shigowa. """Ya Iman Abba na kira."" Marwan ya fad'a mata yana tsaye a gefen ta, hannun sa ta riko shi kuma yace" """Yaya Iman ki gaida min da Abba, idan kin dawo ki kira ni please, zan fad'a miki wani abu."" Murmushi" tayi me sauti yana jiyo ta """Ok bye."" Ta ajiye wayar ta rik'e hannun Marwan din suka fito a tare.." """Yaushe Abban ya dawo?""" """Be dade ba, yana falo yana cin abinci.""" """Owk."" Tace suna karasawa." """ Abba barka da gida.""" """ Barka da Uwata, na dawo ban ganki ba, da zan fita ma ban ganki ba, shiyasa nace ya kira min ke.""" """ Ina wajen Gaji Abba.""" """ Eh haka maman ku tace, amma ai na ganki dai ko?""" K'asa tayi da kanta Mama ta karbe """ Tafi son zaman chan yanzu ai.""" """ Kuna shan hira da Gaji kenan ko?"" Yace yana murmushi" """ Ko kuma tafi jin dadin tayi wayarta a chan ba, ko 'yata?""" "Maman tace cikin son a sako zancen Moh, shiru kawai Iman tayi Abba ma ya girgiza kansa kawai" """Allah ya kyauta, kinci abinci dai ko? Nasan ki da wasa da cikin ki.""" """ Naci Abba.""" """ Toh karbi nawa ki kara, nasan ba da wani yawa kika ci ba."" Ya tura mata plate din gabanta" """Maza kirawo min zeenatu Marwan.""" "Gaban Mama ne ya fadi, ta zamo daga kujerar tana sakin salati a ranta. Tana gyara daurin dankwalin" "kanta ta shigo falon, ta zauna a kusa da Iman ta gaida Abban." """Abinda yasa na kiraku ke da yar uwarki, akan maganar yaran da suke zuwa wajen ku ne, duk da shi" "wanda yake zuwa wajen Uwata bansan shi ba, inaso ki sanar dashi yazo yaga Yaya kafin ya cigaba da zuwa.""" Abincin da ta diba ta hadiye da k'yar gabanta na dukan uku uku. """Ke kuma..."" Ya nuna Zeenat" """Ki kawo wani daban ba yaron nan Bashir ba, ki sake dubawa a cikin sauran ki nemo wanda ya dace da" "nasabar gidan nan, me Halin Girma mutumin kirki, kinji na fad'a miki.""" Waro ido tayi cikin tashin hankali ta kalli Abban """ Hakan shine abunda ya kamata muyi a matsayin mu na iyaye, dan haka kiyi hakuri.""" "Tashi yayi, ya kalli Iman da tayi tsam a wajen, ya juya ya kalli Mama yayi mata alama da ido sannan yace" """ Na fita!""" Da k'yar Mama ta bud'e baki tace """ Adawo lafiya.""" """ Allah ya kiyaye Abba."" Iman tace yana kokarin fita" """ Amin."" Ya amsa kafin ya fice gaba daya." "Wani kallo Mama tayi mata, tayi kwafa ta mike sannan ta kalli Zeenat da ta soma kuka wiwi tace" """ Ki same ni a daki.""" "Kamar wadda zata fadi saboda kuka haka ta tashi, ta kusan fadowa Iman din aka, a ranta tana jin babu" "abinda zai hana ta auren Bashir, duk tashin hankalin da za'a yi sai dai ayi shi, amma babu wanda zai hanata abinda zuciyar ta take so." "***Cikin wani yanayi bayan ya gama jin komai ya gaida Abban da ya fito, yayi masa adawo lafiya sannan" "ya juya zuwa wata hanyar ya fasa shiga dakin. Idan har abinda yaji gaskiya ne, wannan me zubin yan boko haram din aka bawa damar turowa kenan, ba zai taba yarda yayi biyu babu ba, ba aiki ba Iman, shi zai fara isa wajen Yayan idan yaso ayi wacce za'a yi, yasan ba zasu taba hanashi ba, domin shi ya" "chanchanta ba wani bare ba, da ba'a san daga ina yazo ba." *** "Tashi zaune yayi zaune bayan ya ajiye wayar, ya kalli Musaddik da ya zauna a gefen sa" """Ya akayi ne?""" """Na shigo kana ta waya""" """Eh wallahi, ni da Wifey ne.""" """Wifey kuma? Yaushe kayi aure ba labari?""" """Bana son iskanci, kasan wa nake nufi ai.""" """Toh ai sai kace aljanar ka da ka nacewa, amma kace wifey bayan bamu shafa fatiha ba.""" Jefa masa dan pillow din da yake kusa dashi yayi """Dan iska, ka jira ka gani ai.""" """Wai karo maka yaran ka akayi ne? Naga gate din naka ya sake cika ga wani uban iyayi kamar basu san" "mutum ba?""" """Sai hakuri kawai, ya ake ciki ne?""" """Normal, shiru ne ko ina, ya ka baro su Ammi?""" """Lafiya lou wallahi, Bubu yayi min maganar aure ai, nace zan zo musu da magana in less than a month," "kafin nan mun gama daidaitawa da Wifey.""" """ Ya zakayi toh idan aka ce ka turo?""" """ Shine matsalar wallahi, amma zan san yadda zan dai.""" """ Toh Allah ya sa muji alkhairi angon Fatima.""" """ In Sha Allah."" Yace yana dafe saitin heart dinsa, dai-dai lokacin kiran ta ya shigo wayar, yayi saurin dora" "hannun sa akan baki alamun Musaddik yayi masa shiru, wurga masa pillow da ya jefe shi dashi yayi ya fice yana cewa" """ Ka same ni a kasa idan ka gama zan kalli laliga.""" Da kai ya amsa masa yana kara kiran a kunnen sa """ Nagode sosai da kika kirani, na zata ba zaki kira ba.""" """ Haba! Zan kira ai.""" """ Nagode sosai, bari na kira ki toh.""" """ A ah ba komai, muyi magana akwai kati kar a cinye maka naka kai kadai.""" Murmushi yayi me sauti """ Kinga kuma 200 nasa dazu har ta kusa karewa, bari na fita sai na sake siyo ko na 100 ne sai na kiraki.""" """ Allah ba sai ka fita ba, ga sanyin nan da ake yi ma.""" """ Shikenan Nagode.""" """ Me kikayi a wajen Abba.""" """ Abinci naci.""" """ Iyeeeee, yar gata! Har abinci abba ke baki? Allah sarki ni.""" """ Kaima ai dan gata ne.""" """ Ni din? Tab ni ba dan gata bane, gashi ke har abinci Abba yake baki, niko kin ganni a dan shago na" "sanyin nan duk a kaina zai kare, babu me tausayi na ya bani abinci.""" """ Allah sarki.""" "Tace cikin tausayawa, da ace sun saba sosai da tace yazo ya karbi abinci, ta hada masa har da abin rufar" "ta idan yaso ita sai ta samu wani wajen Gaji, amma ba zata iya ba, sai kawai tayi shiru tana tunanin ta yadda zata fad'a masa Abba yace yazo ya samu yayansa." """Dama... Dama...Abba ne yace.""" """Me?"" Yace cikin zakuwa" """Wai ka fara zuwa ka samu Abba (Baban yayansu) ka nemi izinin zuwa kafin ka cigaba da zuwa.""" """In Sha Allah zanzo, yaushe ake samun sa a gida?""" """Kamar da yamma haka zuwa bayan Magriba.""" """ Ok in sha Allah zanzo, nagode sosai da wannan karamcin na Abba, duk da ni din ba kowa bane, amma" "har aka bani wannan damar, nagode Sosai.""" """ Ni dai dan Allah ka daina cewa kai ba kowa bane, a islamiyya an fad'a mana, babu wanda yafi wani sai" "wanda yafi tsoron Allah.""" """ Haka ne, wai kinga ina nufin ni din ba kudi ne dani ba, amma...""" """ Kudi ba sune farin ciki ba ai, wadatar zuciya itace mutum, dan Allah ka daina wannan maganar kana" "sani jin wani iri.""" """An daina ta daga yau, ba zaki sake ji ba, kiyi hakuri idan na bata miki rai.""" """ Babu komai.""" """ Yawwa, kiyi min murmushi naji toh.""" Shiru tayi """ Kinji mana, pleaseee.""" Yace sai kuma yayi saurin daidaita kansa ganin zai zarme da yi mata shagwaba har ta ranfo wani abu """Nayi fa, ai baka gani na.""" """Tam shikenan, idan naje na nemi izini wajen Abban mu, zanzo na gani a zahiri.""" """Uhum."" Tace tana jin zuciyar ta na sake nutsuwa dashi, ko ba komai ta samu wani da yake dauke mata" damuwar ta da kadaici """Bari na barki haka kar na cinye miki kudi...""" """Goodnight, sweet dreams of meeeee.""" """Allah ya tashe mu lafiya."" Tace tana yin dariya k'asa k'asa" """Amin ya Allah, bye inji turawa.""" """Bye."" Tace mishi ta ajiye wayar." """Yess!"" Yayi tsalle ya dire kafin ya fice yana saka hannun sa cikin aljihun dogon wandon sa. A falon ya" "tarar da Musaddik da tea yana sha, ya zauna ya diba shima yana murmushi." "_""You don make me fall in love, you don make me fall in lov, Baby I love you.""_ " Dariya sosai Musaddik ya saka """ JJC kawai, zaka cika mana kunne da wata wakar ka.""" """Idan fitsari abin banza ne, kaza ma tayi mana?""" """Okh haka ne, shikenan ai.Wait and see. Ni yanzu ba wannan ya kawo ni ba, me yasa ka saka aka dakatar" "da gayen nan ne?""" Tashi yayi rik'e da cup din yana bata fuska """Kaga dacewar ya nemi irin abinda nake nema?""" """Kamar ya?""" """Ba'a takara da Sarki, be chanchanci karawa dani ba, bashi da qualities din da zai iya neman auren ta," "cika bakin sa ya saka na nuna masa iyakar sa, anyways warning ne kawai, zan sake gwada hankalin sa , idan yayi hankali fine, idan be ba kuma sai muje a haka, sai a karbi application din wasu.""" "Gid'a Kai Musaddik yayi be sake cewa komai ba, yasan waye Moh, yasan bashi da matsala ta kowanne" "bangare, amma bashi da dadi idan har kayi crossing din sa, zai nuna maka shi din babba ne a cikin manya!" """Ka fahimta dai ko?""" """Yes Captain!"" Ya mike sannan ya sara masa." """Aje waya!"" Yace masa suka kwashe da dariya a tare." HALIN GIRMA Hafsat Rano WAIWAYE. ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_* *ZAFAFANKU BIYAR sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma "TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*" "*_SANIN HALI. yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi" "wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*" "*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu" kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi* *JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE* *_DEEN MARSHALL Mamuhghee_* *_HALIN GIRMA hafsat rano_* *_TAKUN SAƘA billyn abdul_* *_SO DA ZUCIYA miss xoxo_* *_ƊABI'AR ZUCIYA huguma_* *DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL* 2 400 3 500 4 700 5 1000 *Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA keystone bank Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 08184017082 "*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*" 09134848107 _*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_* #team zafafa biyar . *_LAST BONANZA_**HALIN GIRMA* 7 "*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107*" I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb *** "Kukan ta ne yake karuwa Mama na tsaye a kanta, ta ja tsaki tace" """Bana son shirman banza kina ji na? Akan namiji zaki zauna kina rafka wannan kukan kamar uwarki ce ta" "mutu ko ubanki?""" """Mafita nake so mu samawa kanmu, saboda anga zaki huta shine aka shiga aka fita ake so ayi mana" "bakin ciki, idan ba haka ba, me ya kawo wadannan zantukan?""" Cikin kuka tace """Wallahi Mama nasan Iman ce taje ta samu Gaji da maganar tunda dama ita yace yana so ai, shine dan" "taga wanda yazo wajen nata talaka ne shine zata min bakin ciki, toh wallahi babu wanda ya isa ya hanani auren Bashir, naji na gani kowanne hali ne dashi.""" "Shiru Maman tayi tana kallon yar ta ta, idan har ta bari maganar ta sha ruwa akwai matsala, sanin cewa" "Zeenat din ba wani farin jini bane da ita, dama dai jamaar Iman din ne tun farko take sanin yadda zatayi, dole ta san abinda ya kamata amma duk da haka ba zata nunawa Zeenat din komai ba" """ Kina jina? Ki tashi ki tafi dakin ku, ki daina wannan kukan tunda ba ubanki bane ya mutu, zan san yadda" "zanyi komai ya daidaita.""" "Da bayan hannun ta ta goge kukan, ta fice tana rangaji, tana sake kudurewa a ranta babu gudu babu ja" da baya a auren ta da Bashir din. "Tana isa daki ta tarar da missed calls din sa, ta bi kiran da sauri tana sake daidai ta kanta." """ Gani a waje."" Yace tana dagawa." """ Mu hadu a bayan layi akwai matsala karka zo gida.""" """ Me ya faru?"" Yace a kidime." """ Babu komai gani nan zuwa.""" "Kashe wayar ta, tasan zai ta tambayar ta menene gwara kawai taje suyi magana su sama wa kansu" mafita dan ba zata iya hakura dashi ba. "Ficewa tayi ta kofar kitchen bayan ta gyara fuskar ta, ta bar gidan cikin sauri tana tsoron haduwa da Ya" Habib ko wani. "A chan bayan layin ta hange shi jikin motar sa, a tsaye yake yana ta jijjiga jikin sa daga gani baya cikin" "nutsuwar sa, tana isa ya juyo da sauri." """ Lafiya baby?"" Yace yana riko hannun ta. Kuka ta saka da sauri yace" """ Na shiga uku, me ya faru?""" """ Abba ne yace wai na rabu da kai, wai yayi bin...""" """ Shisshsh..."" Yace da sauri yana dora hannun sa a saman bakin ta" """ Kinsan dai hakan ba gaskiya bane ko? Sharri akayi min ko menene akace domin a hana mu aure, duk" "wanda ya yi min wannan sharrin na bar shi da Allah kawai."" Yace yana girgiza kansa" """ Shikenan yanzu rabuwa zaki dani? Nasan rayuwata shikenan ta kare, idan har zaki iya yarda mahassada" "su shiga tsakanin mu, bakya so na baby, rayuwata shikenan ni.""" """ Ni ban yarda da duk abinda akace ba ai, kawai sharri ne na sani, amma ya zanyi da Abba? Bayan shi din" "kaifi daya ne akan maganar sa.""" """ Dan Allah Zeenat karki yarda a raba mu, wallahi Ina sonki , bansan ya zanyi da rayuwa ta ba idan har" "baki aure ni ba.""" Hawaye ya fara yi tayi saurin sa hannu ta goge masa """Zanyi duk yadda zanyi, ba zan bari a raba mu ba...""" """ Da gaske? Kinyi alkawari?""" """ Nayi maka alkawari.""" """ Dan Allah karki saba alkawari dan Allah, ki taimaka wa rayuwa ta, kinji?""" """ Karka damu."" Tace tana jin wani karfin zuciya," """ Ba zan taba yarda su yi min abinda bana so ba, Kai nake so kuma duk yadda kake ina son ka a haka.*" """Nagode nagode baby, in sha Allah ba zakiyi dana sanin amincewa dani ba.""" Zatayi magana wayar sa tayi kara """ Sorry."" Yace mata kafin ya daga yana rage volume din wayar sosai" """ Malam tun dazu nake jiran ka, ka dawo min da mota zan fita, wai ina ka tsaya ne?""" """ Gani nan yanzu in sha Allah.""" Ya kashe kiran ya ce """ Baby bari naje, urgent call daga Baba, zamuyi waya kinji?""" """ Tam shikenan."" Tace a sanyaye" """ Yawwa ga sakon ki..."" Ya bud'e murfin motar ya fiddo da ledoji, hannu tasa ta karba tayi godiya, ta juya" "ta soma tafiya shi kuma ya shiga motar ya tada ita da sauri ya bar wajen, yasan ba zasu kare kalou ba da ita, amma kuma hakan shine kadai zai kankaro masa mutuncin sa." "***Daki ta koma ta ajiye ledar bayan ta bud'e taga ice cream ne da Pizza, sai charger waya da yake ta" "lalace ta ta, sai wasu tarkachen alawoyi. Bata taba komai ba sai charger din ta jona wayarta a jiki sannan ta fice zuwa bangaren Gaji dan ta samu Iman a yi wacce za'a yi." "Iman din ce kuwa kadai a falon tana karanta hisnul muslim. Sai ganin mutum tayi a kanta, bata tanka" mata ba ta sauke kanta ta cigaba da karatun ta kawai. """Saboda kina bakin ciki kin samu fakiri talaka shine zaki kai munafurci kice Bashir bashi da hali ko?""" """Wacce irin magana ce wannan Zeenat?""" """ Malama karki pretending kaman baki sani ba, idan bake kika fad'a ma Gaji wata magana akan Bashir ba" "waye ya samu Abba ya fad'a masa Bashir bashi da hali me kyau?""" "Tashi tayi zaune tana kallon ta, ta girgiza kanta kawai kafin tace" """ Kinsan bani da lokacin batawa akan irin wadannan maganganun, dan haka please bana son maganar.""" """ Zaki ce bakya so mana kina min bakin ciki, toh wallahi sai dai ki mutu da bakin ciki amma aure na dashi" "babu fashi, kije chan kiji da wanda zaki aura, mutum kamar shi ya kawo talauci duniya.""" "Tashi kawai tayi ta bar falon zuwa bedroom din Gaji dan ba zata iya irin wannan shirmen na Zeenat ba," "sai dai da gaske maganar ta taba ta, har taji ta rasa gaba daya walwala da farin cikin ta, kwanciya kawai tayi ta rufe idon ta tana hasaso rayuwar ta nan gaba!" "***Cikin shigar Khaki pants da wata jibgegiyar rigar sanyi da ya saka a saman armless rigar sa ya fito," "kansa da yake a kwance yasha gyara ya tsaya yana sake dubawa a katon mudubin da yake ajiye a falon, yasan Takawa zai saurare shi ya kuma bi abinda yake so sai dai baya son ko kad'an karya ko wasa ya shigo a cikin maganar auren sa. Kallon kafar sa yayi, sai ya koma ya sauya takalmin zuwa wani daban" sannan ya fice yana tura hannun sa cikin aljihun dogon wandon nasa. "Suna tsaye k'yam suna jiran fitowar sa, kowanne su cikin shigar da take nuna shi din waye, bud'e masa" "motar akayi da sauri ya fad'a yana makala bakin glass din sa yasan yau zai same shi a wajen hutawar sa, in da ya dace da maganar da zasu tattauna, shiyasa ma yayi shigar sa da yasan Takawan bazai masa surutu ba, dan ya riga ya san shi, ko yace kowa ya san shi da tsanar manyan kaya musamman a lokacin" zafi sai yace wai takura masa suke. "Da yake sun san in da zasu, kai tsaye suka wuce dashi Family house din, in da Takawan ke hutawa a duk" ranaku irin wannan ba tare da shigowar wani shaani na mulki ba. Iyakar abinda ya shafi kansa da iyalin sa kawai yake tattaunawa a rana cikin saukakakkiyat shiga da ba zaka taba cewa sarki bane duba da ko yaushe yana nannade cikin rawani da manyan kaya. "A kofar wajen motocin nasa suka tsaya, ya balle murfin tare da me bud'e masa ya fito yana kallon ko" ina na harabar gidan. Kansa sanye da hular sanyi ya cire glass din idon sa ya shiga takawa zuwa ciki. Gaisuwar da ya tsana ya dinga kokarin kaucewa har ya dangana da inda takawan yake ya hange shi a zaune a cikin wajen yayi matashi da pillow yana kallon yadda yan yaran da suka kasance jikokin sa ke wasa a wajen. "Sarkin dogarai ne ya fara ganin shi,ya washe cikin farin cikin ganin shi yace" """Maraba da Yarima!""" """Sarkin dogarai...""" "Muryar sa ta saka takawa d'agowa, ya gyara daga gishingid'ar da yayi, ya fad'ad'a fara'ar fuskar sa da tayi" "ma Moh iso har gaban kakan nasa. Russunawa yayi cikin girmamawa ya kai gaisuwa, hannu ya mik'a masa ya matso kusa dashi sosai, ya shafi saman kansa" """ Sai yau kaga damar leko ni ko Muhammadu?""" """ Tuba nake Takawa, ayyukan ne suka yi min yawa.""" """ Toh madallah, naji kace kana son gani na, toh gani ya akayi?""" """ Dama magana ce akan abinda Bubu yayi maka magana.""" """ Auren ka? Jairi toh sai akayi yaya?""" Dariya ya saka sosai """ Toh kunce sai nayi aure yanzu kuma nazo da maganar kuma, sai na fasa auren ma gaba daya.""" """ Fasa mana, waya yayi asara? Kaji dan nema.""" "Dariya suka saka a tare, kafin Takawa yace" """ Toh sai ka fadi a inda yarinyar take ko? Idan yaso sai a nemi iyayenta.""" """ A ah ni dai Takawa, ayi min aikin gafara a bari a samu wasu suje su nema min auren ta.""" """ Wasu?"" Yace yana kallon sa" """ Eh a dangi haka ba, ba manya sosai ba, Ina nufin ba cikin manyan masarauta ba, yan chan kasa kasan" "dai.""" """ A wanne dalili?""" """ Kawai ni bana so suji tsoro su ga kamar mun fi karfin su.""" Girgiza kai Takawa yayi """ A neman aure babu boye boye Muhammadu, a sak dinka zaka je, kai ne fa jika na farko a gidan nan," "sannan a wajen mahaifin ka, wanne irin tunani ne haka ya shiga kanka?""" Sosa kai Moh yayi yana marairaice fuska """Ni dai dan Allah takawa, a bar wasu suje.""" """Sam sam kaima kasan hakan ba mai yiwuwa bane, dole ne su san kai din daga gidan da ka fito.""" "Shiru yayi yana jin kamar ya daure kansa da ya budewa Takawa zuciyar sa, yasan shi sarai da tsayawa" "akan ra'ayin farko, amma yayi tunani zai fuskance shi duba da irin son da yake masa, dama Musaddik ya gaya masa, babu me yarda da shirmen sa kamar yadda yake jaddada masa a kullum, babu me biye masa ko bashi goyon baya. Tun daga lokacin yasan sarai babu me tsayawa ya saurare shi, balle ya yarda da tsarin sa. Ammin sa ce kadai itama bata ja da maganar Takawa, ballantana Bubu da baya iya aiwatar da" komai sai abinda Takawa din yace. """Kana jina Muhammadu, maganar da kazo da ita bata kamawa bace. A tsari na gidan nan ma zamu iya" "aika musu suzo nan din domin muna da damar bada diyar tasu, sai dai ba zamuyi haka ba, zamu basu" "girman su da darajar su in Sha Allah, za kuma musu duk abinda Muhammad yake so amma banda shiririta.""" "Ya karashe yana murmushi, murnushin shima yayi kawai ba tare da yace komai ba. Suka cigaba da hira" "irin wadda suka saba har be san iya adadin awoyin da ya bata ba, sai da suka ci abinci da Takawar sannan ya lallaba ya shiga gidan ya gaida matan gidan ya kare a dakin kakarsa ya tarar da yan matan family din sunzo suna da wani get-together da suka shirya sannan suyi maganar tsari bikin Abidah guda" daga cikin jikokin gidan. "A kaidar sa baya sakar musu fuska ko kad'an domin suna da rainin hankali sosai, duk da shi basa yi" "masa neman ma ya kula su suke amma shi sam baya tsayawa shirmen su, da gaske suka shakkar shiga shirgin sa hakan yasa yana shigowa shashen suka dinga yayewa da d'aya d'aya." Dan tsiririn tsaki yaja sanda suka gama ficewa ya zauna yana muzurai a dole baya son raini shi. Mutane da yawa na fad'a masa yadda yake abubuwan sa kadai ya tabbatar da shi din jini ne na sarauta amma shi sam be san ma yana yi ba ma. Ya dan jima a wajen nata kafin ya tafi yana jin zai dan dade kafin ya sake waiwayo su duba da tafiyar dake gaban sa akan aikin sa. "***Yana zaune a gate din gidan yana dakon shigowar Abba Babban, a kan idon sa ya dawo ya tashi da" sauri ya tare shi ya bud'e masa kofar mota. """Sannu da zuwa Abba.""" """Yawwa Ibrahim, kaine yau a gate din kenan.""" """ Wallahi kuwa Abba, sannu da dawowa, ya aiki?""" """ Alhamdulillah mun gode Allah, ya naka aikin?""" """ Alhamdulillah."" Yace yana tuna abinda ya faru dashi." """ Allah ya taimaka ya bada sa'a.""" """ Amin Abba."" Yace yana bin sa rik'e da jakar sa a baya." """ Mika jakar ciki bari na fara gano Gaji.""" "Yace yana bin hanyar da zata kaishi bangaren Gajin, da sauri Khalil din ya kai masa jakar ya dawo ya" "zauna yana jiran ya fito. Ya dan jima a wajen Gajin kafin ya fito sai dai ganin Khalil ya saka shi mamaki, abunka da Babba nan da nan ya gane akwai wani abu." """ Ya akayi Khalil? Kana son gani na ne?""" """ Eh Abba."" Yace yana sosa kansa" """ Haba ko da naji, toh zan turo a kiraka kaji?""" """ Toh Abba Nagode."" Girgiza kai Abban yayi ya wuce bangaren sa. Maimakon ya koma gida sai yayi" zaman sa anan yana jiran kiran Abban. Yana zaune kuwa yaga fitowar Sadik ya tashi da sauri ya tare shi """Yawwa wai kazo in ji Abba.""" "Rik'e hannun sa yayi suka koma yana jin wani iri a ransa, bakin sa dauke da addu'a ya shiga falon ya tarar" Abban ya chanja kaya yana zaune da alama abinci ya gama ci. A chan gefe ya zauna yana jin kunya. """Yawwa ina jin ka Ibrahim, ya akayi?""" "Shiru yayi yana tsara yadda ya kamata ya ce, sai da ya dau sakanni yana hado maganar kafin yace" """Dama Abba akan maganar Fatima ne.""" """Uhum ina jinka. Ya akayi?""" """Dama... Dama so nake dama a bani dama kamar yadda tsarin gidan nan yake.""" Murmushi Abba yayi cikin jin dadi yace """Masha ALLAH naji dadin wannan abu matuka, Allah ya tabbatar mana da alkhairi kaji? Allah yayi muku" "albarka.""" """ Amin Abba."" Yace a ciki-ciki farin ciki na kamashi," """ Kaje ku daidaita idan Allah yayi mu haka muke so, an riga an zama daya ai in sha Allah babu wata" "matsala.""" """ Nagode Sosai Abba, Allah ya kara girma.""" """ Amin."" Yace yana chanja tasha a tv, shiru Khalil din yayi kafin ya mike" """ A huta lafiya Abba.""" """ Yawwa Ibrahim.""" Yana fita ya daka tsalle a wajen yace """Yes!!""" "Da sauri ya bar wajen yana jin kamar ya same ta ya gama ne, zai nuna wa fakirin saurayin ta cewa dan" gida yafi bare. "***Sabon yadi ne me saukin kudi sosai, dinkin ma irin dan 1500 din nan ne, a rayuwar sa be taba" "hasashen saka ire-iren kayan da yake sakawa a yanzu ba, wani kallo Musaddik yake masa yana jin kamar ya kamashi yayi ta bugu." """Yanzu Moh irin kayan da zaka saka kenan zaka ganin sirikin ka?""" """Wait and see."" Yace yana kawo wata leda a kusa dashi, ya wurga masa yana cigaba da kallon kansa a" mudubi """Ka chanja mu tafi idan yaso muyi sallar magriba a hanya sai mu karasa.""" """Na saka me?"" Musaddik yace da sauri yana bud'e ledar." """Wait what! Kana nufin ni zan saka wannan kayan.""" """Mu nawa ne a dakin nan?""" """You must be kidding me, haba haba an fad'a ma kowa ma irin ka ne.""" """Allah su zaka saka mu tafi, kayi sauri karka batan lokaci I'm dying to see my love.""" """Aiko sai dai ka tafi kai kadai wannan karyar ba dani ba.""" """Da wa toh? Wa nake dashi bayan kai? Kasan da ace ban samu kanta ba dole kaima ka tattaro ka dawo" "sabon shagon nan dana zauna mu zauna tare. Allah dai ya taimake ka wallahi.""" """ Ai wallahi babu yarinyar da ta isa nayi mata irin wannan son, the whole you, Captain Muhammad" "Ahmad Santuraki, dan ga sarki jikin sarki sannan kuma babban soja, ko da yake fa dama ance ku sojoji baku iya soyayya ba, musamman idan allurar ku ta motsa.""" Daina abinda yake yayi ya matso kusa dashi """ Idan bansa an saka min kai frog jump ba, kace ba suna na Muhammad ba.""" "Dariya maganar ta bawa Musaddik," """ Ni zaka saka frog jump?""" """ Sosai, ka cigaba da batan lokaci kaga.""" "Tashi Musaddik yayi ya sake daga kayan, kafin ya fara sawa yana cigaba da mita." """ Kanka akeji wallahi."" Moh yace yana cire agogon hannun sa." """ Ka cire watch dinka please, anything da zai sa ta zama suspicious, I don't care idan kowa na gidan su" "yasan ni waye, amma ita? Da marikiyarta will be the last da zasu sani, surprise ne me kyau nake son basu dukka, sai dai kowanne da yadda surprise din zai zo masa.""" """ Wicked soul."" Musaddik yace yana jefar ta watch dinsa akan mirrow" """ What ever!"" Yace yana yin gaba yabi bayan sa yana jin dadin kayan jikin sa, babu nauyi shawai shawai" amma kuma ba zai yarda Moh din yasan ya ji dadin kayan ba. "A daidai shagon aka daajiye su, yace su je chan in da suka saba jiran sa su jirashi zai kirasu. Duk da basu" "so ba amma haka suka tafi suka barsu, Musaddik ya dinga jan tsaki suna tafiya a k'asa har suka isa kofar gidan. Wayar sa ya ciro ya kira ta, tayi ta ringing bata daga ba," """ Bata daga ba.""" """ Da ka kirata tun kafin muzo ai.""" """ Wannan ba matsala bace, bari kaga.""" "Ya kwankwasa gate din kafin ya dan tura shi suka shiga, dai-dai lokacin Khalil ya taho zai fita sukayi" "kichibis, wani kallo ya bisu dashi irin na sama da k'asan nan, kafin ya tuntsure da dariya sosai, hakan yayi bala'in bata ran Musaddik da dama chan baya daukar nonsense." """ Malam lafiya zaka kalle mu kayi dariya?""" """ Lafiyar kenan, sai dai kun makara, dan gida ya shiga ya fita ya gama tabbatar da komai akansa, sai abi" "wani sarkin dan an riga an gama magana kuma su din ba kananan mutane bane da zasu sauya maganar su.""" """ Kana nufin?"" Musaddik yace a zafafe" """ Ina nufin kamar yadda na fada mishi ne a baya, Iman matata ce an riga an gama magana rana kawai" "ake jira a saka mana.""" "Wani kallo Moh yayi masa da ya saka Khalil shan jinin jikin sa, amma sai ya dake ya cigaba da gaggayawa" "musu magana. Muhammad be ce komai ba har ya gama, ya juya ya fice ya barsu a tsaye kamar mutum mutumi." """ I have no option than to show him my real identify, idan yaso duk abinda ya biyo baya yayi kuka da" "kansa ba da kowa ba, karfe nawa ne appointment dinsa?""" """ Da safe ne, goma kamar.""" """ Owk Allah ya kaimu.""" """ Amin."" Musaddik ya amsa ransa na sake baci akan abinda Khalil din yayi musu" HALIN GIRMA Hafsat Rano WAIWAYE. ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_* *ZAFAFANKU BIYAR sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma "TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*" "*_SANIN HALI. yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi" "wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*" "*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu" kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi* *JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE* *_DEEN MARSHALL Mamuhghee_* *_HALIN GIRMA hafsat rano_* *_TAKUN SAƘA billyn abdul_* *_SO DA ZUCIYA miss xoxo_* *_ƊABI'AR ZUCIYA huguma_* *DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL* 2 400 3 500 4 700 5 1000 *Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA keystone bank Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 08184017082 "*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*" 09134848107 _*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_* #team zafafa biyar . "*_farincinku shine namu,ZAFAFAN DAI,sun sake amsa kokenku,sun sake rage muku kaso 20 cikin 100_*" "*_Daga yau 29 ga wata,har zuwa 31 ga watan nan,xaku iya biyan 800 a amadadin 1000 na kudin" litattafai biyar_* *_za'a fara posting in sha Allah 1st January da yardar Allah_* *HANZARTA KI BIYA NAKI KAFIN RANAKUN SU QARE* *XAKI BIYA TA WANNAN ACCOUNT NUMBER DIN* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA "SAIKU TURA SHAIDAR BIYA[1/5, 10:07 PM] Sakaba: *HALIN GIRMA*" 8 "*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107*" *** "Sake kiranta yayi a karo na biyu, ta daga tana goge ruwan da yake hannun ta, tana ciki tana wankewa" "Gaji toilet shi yasa bataji kiran farko ba, sai da ta fito wanda yayi daidai da sake kiran." """Assalamu alaikum."" Tayi sallama cikin muryar da ta saka Moh sallama duk bacin ran Khalil da ya kwasa" yanzu. """Wa alaikisalam, kina lafiya?""" """Lafiya lou wallahi, ya aiki?""" """Alhamdulillah, ina waje nazo ganin Abba.""" """Owk tam gani nan.""" "Tace sannan ta ajiye wayar, ta fito tana tunanin yadda zata sanar wa Abban, a harabar gidan ta hangi" "motar sa, alamun ya dawo kenan, karasawa tayi wajen su tun kan ta isa Moh yake sake admiring kyawun ta, koman ta very simple hatta da tafiyar ta kamar ba zata taka k'asa ba, a matukar nutse take komai hakan yake sake dulmiyashi a kogin soyayyar ta." "Taba shi Musaddik yayi, ya dan yi firgigit sannan ya saki murmushi" """Allah zaka bada maza, kamar ba soja ba?"" Yayi whispering maganar yadda Moh din ne kawai zaiji, banza" yayi masa ya rigata karasowa wajen suka hadu a hanya. Kamshin turaren sa me dadi ya rigashi karasawa """Sannu da zuwa."" Tace tana shakar kamshin da ta kasa tantance shi" """Yawwa Dear, kina lafiya?""" """Alhamdulillah, lafiya lou.""" """Masha ALLAH, gani nazo neman izini wajen Abban mu, ina fatan ban makara ba.""" Girgiza masa kai tayi """ Masha ALLAH, yanzu ya za'a yi, shige mana gaba zakiyi muje ko?""" "Da sauri ta kalle shi, idanun ta suka haska cikin nasa sai a lokacin taga ya rage kasumbar fuskar sa sosai" "kamar ya aske, fuskar sa ta fito sosai idanun sa da suka fi kama da a lumshe suke sun fito sosai, saurin dauke kanta tayi tana jin wani irin faduwar gaba" """ Tunda ba zaka yi introducing dina ba, bari nayi da kaina."" Musaddik da ya karaso wajen ya harare shi" yana murmushi """ Sannu malama Fatima, sunana Musaddik kuma ni ogan sa ne a komai, ina fatan zaki karbi aboki na" "hannu bibbiyu dan da gaske yake ba da wasa ba.""" """ Sannu da zuwa, Ina wuni?"" Ta gaishe shi tana sauke kanta kasa har yanzu bata daina jin faduwar gaban" ba """ Lafiya lou, ya komai da komai?""" """ Alhamdulillah."" Tace" """ Bari na duba Marwan sai yazo ya yi wa Abban magana.""" """ Owk.""" "Ta juya zuwa part din su tana addu'ar kar su hadu da khalil, a falo ta tarar da su dukka Zeenat na danna" "wayarta, Maama na zaune Marwan yayi filo da kafarta yana kallon Disney World, shigowar ta ya saka suka maido hankalin su kanta" """ Sannu da gida Mama.""" "Kin amsawa tayi, ta gimtse fuskar ta ta muskuta tana cigaba da kallon TV." """ Mama dama Muhammad ne yazo wajen Abban.""" "Da sauri Zeenat ta mike, ta hau kyalkyala dariya kamar wata sabuwar tababbiya, kawai sai Maman ma ta" "hau tayata, suka sakata a gaba da dariya abinda ya bata mata rai har taji kuka na neman xuwar mata" """ Su Malam ne anzo za'a Abba kenan, ya kyauta miki ai ya taimaka da yazo, dan Khalil yafi karfin ki, shi" "din dai shine daidai da me bakin hali irin naki, me kike so nayi yanzu.""" "Daidaita muryar ta tayi, tace" """Dama so nake Marwan yayi musu iso wajen ..."" Da sauri ta katse numfashin ta" """Tashi maza maza Marwan, je kace wa Abban gidan su Aliyu yana da baki, yi masa kar ya gaji da jira yace" "ya fasa.""" Sai ta sake tuntsurewa da dariya Zeenat na tayata. Hawayen da take ta rikewa ne suka shiga sakkowa a "fuskar ta," """Kadan kenan kika gani in dai junan mutum bakin ciki toh wallahi shine a ciki."" Zeenat tace tana jan tsaki." Juyawa tayi zata fita Maman ta tsaida ta """Zo ki wuce ki wanke kanukan da aka bata.""" "Bata ce komai ba, tayi hanyar kitchen din zuciyar ta na kunci sosai. Wanke wanken take tana kuka sosai," "irin wand a ta jima batayi ba, tana da masifar dauriya akan duk abinda za'a yi mata, amma kuma a" "wannan bangaren ta rasa me yasa ta kasa jurewa, wulakanci bashi da dadi kuma yanaa da ciwo musamman a tasaka gaba ana dariyar shakiyan ci da wulakanci." Adadin lokacin da ta saba dauka tana wanke wanken sai data ninka shi saboda damuwar da take ciki. "Ta baya ta fice ta koma bangaren Gaji tana jin kamar ta tattara komai ta bar musu gidan. Sau daya a cikin ranaku masu yawa yau ta tuna mahaifiyar ta, shiyasa bahaushe yace wanda ya rasa uwa yayi kuka." ***Da kallo Abba ya bisu har suka zauna suna masu nuna jin nauyi da kunyar sa. Bayan sun gaisa yace """Gashi kuma ban shaida ku ba.""" """Dama Fatima ce ta sanar mishi da Abban yace yazo ya nemi izini a wajenka, toh shine dama dalilin" "zuwan namu."" Musaddik yayi maganar yana addu'ar Allah yasa be kwafsa ba." """Toh toh..."" Abban yace yana tunanin yadda al'amarin yake, musamman maganar Khalil da ya riga ya" karbe ta """Ita Ummin ce tace kuzo ko?"" Yayi tambayar yana kallon su" """ Ummi?"" Suka Hada baki" """ Auw Fatima toh, sunan Uwata ne ni ummi nake kiran ta.""" """Masha ALLAH, Eh Itace ta turo mu.""" """Toh shikenan, ina zuwa.""" "Tashi yayi ya shiga ciki, ya kira wayan Abban su Fatiman dan yasan be kai ga dawowa gidan ba" """Yaya barka da warhaka.""" """Barka dai, ya aiki?""" """Alhamdulillah mun gode Allah.""" """Allah ya bada sa'a, kana ji, dama akan maganar Ummi ne, yaron nan Ibrahim yazo da maganar sa jiya" "har ma na bashi izinin daidaitawa da ita ganin shi din na gida ne, yau kuma kwatsam sai ga wani yazo shi kuma wai Ummin ce ta turo shi.""" """ Ibrahim Kuma?" """Eh shifa.""" """Amma da kaina na tuntubi Hajara da maganar sa, amma ta nuna min sam ba da gaske yake ba, hakan" "ya saka na ce Ummin ta sanar wa wannan din yazo ya ganka.""" """Ibrahim kam yazo jiya ya same ni, ga wannan kuma shima.""" """Allah ya kyauta.""" """Zamu duba muyi bincike, idan yaso sai a bashi dama shima, wanda suka daidaita shikenan, bamu san" "me Allah ya boye ba, kar muyi gagagwa.""" """Shikenan Yaya, duk yadda akayi yayi.""" """Madallah.""" "Fitowa yayi ya tarar dasu a zaune, ya zauna yana fuskantar su" """Kace sunan ka?""" """Muhammad.""" """Toh Muhammad daga ina?""" """Adamawa-Yola, amma mahaifiya ta yar Kano ce, nima kuma kaso me yawa na rayuwa ta nayi shi ne a" "Kanon.""" """Toh toh Masha ALLAH, Anyi karatu Muhammad?""" """Eh Abba, nayi karatu.""" """ Aiki fa?""" """ Soja ne ni.""" """ Ah Masha ALLAH, soja ga wuta ga yaki, soja marmari daga nesa. Hakan yayi kyau a cigaba da samar" "mana da tsaro a k'asar mu, Allah ya yaye mana abubuwan da suke damun mu suka hanamu zaman lafiya a k'asar, Allah kuma ya cigaba da dafa muku.""" """ Amin."" Suka amsa cikin jin dadin yadda Abban ya sake dasu" """ Shikenan Muhammad, ka bani number wayar ka da address din ka, zan neme ka in sha Allah.""" Hannu Musaddik yasa a aljihun sa zai ciro wallet dinsa ya dauko complimentary card din Moh din yayi "sauri fara karantowa Abba number, yace kuma zai masa text message na address din in sha Allah. Godiya sukayi masa suka fito yana jin tsoro na shigar sa, tsoron kar Abban yayi rejecting dinsa, tsoron yadda zai yi komai ya tafi yadda yake so." "Kiranta ya sake yi ta fito bayan ta wanke fuskar ta sosai dan kar ya gane, duk da haka sai da ya gane" "kuwa,ya kafe ta da ido yana jin babu dadi." """Me ya samu idon ki?"" Ya tambaye ta dan ba zai iya hakuri ba," """Ba komai.""" """Ban yarda ba, kalli idon ki, Dan Allah ki fad'a min me ya faru?""" """Abu ne ya fad'a mina idon dazu, amma ya fita ma.""" """Ban yarda ba, ki fad'a min waya bata miki rai? Waye ya saka ki zubar da hawayenki masu tsada?""" "Ji tayi kukan na sake taso mata, dan dama idan kana cikin halin kuka aka matsa maka da tambaya ko ana" "so ka maida zance sai kaji sabon kuka ya taho maka," """Ba komai da gaske ba komai.""" """Dan Allah ki fad'a min menene?""" """Mamana na tuna."" Ta fad'a masa saboda kawai ya kyale ta da tambayar" """Kiyi hakuri, akwai abubuwa da yawa da nake son sani, I ll call you idan na koma, ki daina kuka kinji?" "Komai zai wuce in sha Allah.""" """In Sha Allah."" Tace tana daidaita kanta." """Kinyi alkawari kin daina kukan ko?""" """Nayi.""" """Nagode, zan kiraki.""" """Shkenan ka gaida gida."". Juyawa tayi ta koma ciki shi kuma ya fita ya tarar da Musaddik ya cika yayi fam" kamar zai fashe. """Muje ko?""" """Allah iyakata wajen bishiyar chan, ka kirasu suzo su dauke mu wahalar tayi yawa ai.""" """Naji muji toh.""" "Ya ciro wayar sa ya kirasu cikin kankanin lokaci suka karaso, har suka isa babu wata magana tsakani" Musaddik ya sauka su kuma suka wuce. "A gaggauce ya gama komai ya shirya cikin kayan sa masu kauri, ya zauna yana jawo wayar sa, kafin ya" "kirata ya samu kiran DG, yayi saurin dagawa yana karawa a kunne. Gaisuwa sukayi ya bukaci ganin sa a Abuja idan an shiga working days, da toh ya amsa masa sukayi sallama ya juya akalar kiran zuwa number Ammin sa." """Ammi na barka da dare.""" Yace sanda ta daga wayar """Barka dai yarona, kana lafiya?""" """Lafiya lou Ammi, ya gida da kowa da kowa.""" """Kowa lafiya, ya aikin naka?""" """Alhamdulillah Ammi, babu dadi gashi ina missing dinki sosai.""" """Ban yarda da wannan zancen naka ba, idan da gaske ne ai kasan in da nake.""" """ Ina na zuwa ai, ranar ma wani aikin ne ya taso urgent shiyasa na tafi.""" """ Ku kenan aiki, Allah ya taimaka ya bada sa'a.""" """ Amin Ammi, naje naga Takawa ai, har munyi magana ma akan maganar da Bubu yayi min.""" """ Eh naji kuwa suna waya jiya, sai dai bamu zauna munyi maganar ba, me yace maka?""" """ Akan yarinyar ne dama Ammi, mahaifin ta yace nazo na ga wanshi ya bani izinin zuwa wajenta.""" """ Ina jinka.""" """ Toh nayi magana da Takawa akan idan har zuwa gidan su ya taso ba sai kowa yaje daga royal family ba," "a samu wasu cikin mutanen Takawa din da ya aminta dasu suje neman auren.""" """ A wanne dalilin kenan? Ina ka taba jin anyi irin wannan shirmen Muhammad? Idan ma anyi hakan an" "fad'a maka ba zasuyi bincike akanka ba kafin su baka izinin ganin yarsu ba? Ai dole ne iyaye na kwarai su yi bincike sosai su san wa zasu bawa yarsu.""" """ Nafi son duk wannan yazo daga baya Ammi, dama dole su sani amma ba yanzu ba, marikiyar yarinyar" "ce matsala, idan har taji da wuri zata iya bata abun dan ta jima tana bata wa.""" """ Idan hakan ne matsala, toh ka bar komai a waje na, karka manta wanne gida kake magana Muhammad," "wargi ma ance waje yake samu, bata isa tayi komai ba idan har taji kai din waye, gaba da gabanta fa, ka daina tunanin komai kayi addu'a, har naji inason yarinyar da dukkan zuciya ta, Allah ya sa ta zama" "abokiyar arzikin ka.""" """ Amin Ammi, in sha Allah ma ba zata sani ba har sai ranar, zanyi duk yadda zanyi bata sani din ba, yadda" "abin zai dake ta, kuma nayi alkawarin hukunta ta daidai da abinda tayi.""" """ Ya sunan diyar tawa?""" """Fatima sunan ta, Iman.""" """ Masha ALLAH, Allah ya tabbatar mana da alkhairi.""" """ Amin.""" """ Inyeee, lallai babu kunya Babana? Hadda saurin amsawa ko?""" "Dariya ya saka sosai,yayi saurin kashe wayar jin Ammin zata yi masa dan biki." "Rik'e wayar ya cigaba da yi a hannu yana juyata,maimakon ya kirata sai wata dabara ta fado masa, take" yaji wani dadi ya kamashi ganin ya samu hanyar da zai hana Maman sanin komai har sai lokaci ya kure mata. "Kwanciya yayi ya ja blanket har saman kansa, sannan ya kirata yana jin ringing din na tafiya daidai" bugun zuciyar sa. "***Da safe ya so ya makara bayan ya koma bacci da asubah, kiran Musaddik ya tuna masa abinda suka" "shirya, a gaggauce ya tashi ya shirya, ya kimtsa kansa cikin shigar Khakin sa, ya fito a sojan sa, kayan sun yi masifar karbar sa, yanayi da tsarin zubin halittar sa sunyi daidai da kayan, shi kansa yana jin sa ontop a" duk lokacin da ya samu kansa cikin irin shigar kayan. "A hannu ya rik'e wular ya fito suna ganin shi suka taso da sauri, duk suka k'ame su biyun kafin daya ya" bud'e masa motar daya kuma ya zagaya mazaunin driver ya tada motar suka fice daga gidan. "A chan permanent site din sukayi zasu hadu da Musaddik, yana isa yaga motar sa a waje, be shiga ba" "ya kirashi a waya ya fito ya same shi. Tare suka fito da Ja'afar, Musaddik ya zura kansa cikin motar yana kallon sa." """Ya riga yazo, yana reception yana jiran MD ya hada shi da oga at the top""" """Ga kuma Oga kwata-kwata anan ba."" Ya kalli Ja'afar suka kwashe da dariya" """ Me ka shirya masa Oga?" """ Ni na isa Captain? Ai ban isa ba Wallahi. Duk abinda ka shirya min dai, ni ai bani da say.""" """ Ya akayi be gane ka Musaddik bane wai?""" """ Ba zai gane ba ai, I'm not in charge of staff din wajen, wannan aikin admin human resources ne, plus" "kaga chan sabon branch ne nan kuma main site.""" """ Haka ne kuma, yanzu zan jira anan.""" """ Yes Sir!"" Ya Sara masa suka kwashe da dariya" "Khalil na zaune cikin zulumi yana fatan haduwar da zasuyi da shugaban wajen ya zama alkhairi, yana so" "ya dawo da aikinsa as soon as possible yadda zaifi jin dadin kwace Iman da karfin ikon sa, da yan kudaden sa a aljihu. Fitowar MD ya saka shi tashi da sauri" """ Yawwa Ibrahim, yazo yana parking lot, sai kaje ka same shi, best of luck.""" """ Nagode sir, Allah ya kara girma.""" """ Amin.""" "Saurin fita yayi, ya tarar da motoci biyu a wajen, duk da bakin glass, tunanin wacce a ciki ya bi numbers" "din motar da kallo. _Royalty_ aka rubuta a jikin plate din babbar da tafi kyau da sheki, wajen ya nufa kirjin sa na dukan tara tara, kafin ya karasa yaga murfin bayan motar ya bud'e, anyi masa fitala. Kofar ya nufa ya zura jikin sa bakin sa dauke da sallama, sai da ya zauna ya daidaita a ciki, kofar ta rufe ruf ya shaki kamshin motar me dadin gaske, ya juyo sukayi ido hudu da wanda ko a mafarki be taba hasashe ko" tunanin gani ba. """Hello Ibrahim.""" Moh yace yana sakar masa wani irin murmushi me dauke da ma'anoni masu yawan gaske """Me... Me ban gane ba?"" Ya hau k'inkina ya ma kasa daidaita maganar sa." """Sunana Muhammad Ahmad Santuraki, Also known as Captain Moh, shugaban wajen nan gaba daya," "nice to meet you.""" """ Nooo! Impossible! This most be a joke, Kai din? Kai din? Kai... Kai Kai din?""" """ Calm down and take a deep breath, karka hargitsa kanka dan akwai sauran surprises, na farko karka" "taba wulakanta mutum baka san shi din waye ba.""" """ Innalillah wa inna ilaihi rajiun.""" "Ya shiga maimaitawa ba kakkautawa, gaban motar ya kalla yaga sojoji ne su biyu majiya karfin gaske," "kowannen su fuskar sa murtuke take babu alamun dariya, jiran umarni kawai suke kamar mayunwatan" "zakuna, hadiye wani mugun yawo yayi yana jin sanda Muhammad din ya bada umarnin tada motar ,be" "iya bud'e baki ya hanashi ba, yana jin sanda motar ta soma tafiya a hankali har ta daidaita akan babban titi, kafin me tuka motar ya kara taka motar da gudun gaske" """Shikenan na gama yawo."" Ya furta a zuciyar sa be san maganar ta fito fili ba." Murmushi Muhammad yayi ya taune gefen lips dinsa yana ayyana kalar rashin m din da zai masa. "[1/7, 9:40 AM] Sakaba: Halin Girma" 9 "*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107*" I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ft46u5twk6r3&utm_content=nj79azb *** "Yana jin sanda motar ta tsaya, ya juyo da sauri ya kalle shi, hankalin sa na kan wayar sa yana dannawa," "fuskar sa a hade tsaf babu alamun wasa ko kadan, tsoro ne ya sake shigar Khalil din sosai, yaji kamar yayi" "ta kurma ihu yana neman taimako, amma kuma ya san babu wanda zai taimaka masa musamman idan aka zo aka ga wanda yake tare dasu." "Ji yayi an murda handle din bangaren sa, yayi saurin matsowa sai gashi a tsakiyar motar, daf da Moh," wani banzan kallo ya watsa masa da ya sakashi saurin komawa inda yake zaune. """Come ou!"" Wani murdadden soja yace matsa bayan kofar ta gama budewa, idanu ya soma rabawa" tsakanin Moh da sojan fuskar sa ta nuna matukar tashin hankalin da ya shiga """I said come out!"" Ya daka masa tsawa da ta saka shi saurin fitowa" """Dan Allah Oga kayi hakuri, wallahi sharrin shaidan ne da rashin hankali, duk abinda na farfada ba wai" "har zuciya ta bane wallahi.""" "Ya hau magiya yana kallon Moh da yayi kamar baya wajen, damtsen hannun sa sojan ya kama ya shiga" jan sa har zuwa wata kofa in da ya hangi sojoji sun fi su ashirin suna tsalle tsalle a wajen. """Oga dan Allah ka bawa oganku hakuri Dan Allah!""" """Kasan waye oga kuwa?""" Da sauri ya girgiza kansa """Ban sani ba wallahi, rashin sani ya jawo nayi masa abinda nayi amsa amma dan Allah na tuba yayi" "hakuri.""" Dariya sojan ya saka sosai """ Baka da hankali amma, ka zo har nan wajen kayi tunanin zamu kyale ka, ka tafi free? Nah sai mun dan" "sassamaka yadda gobe ba zaka kara ba. """ """ Dan Allah nace fa? Ka tayani bawa ogan hakuri. """ """ Naka wasa ne. """ "Yayi gaba yana rik'e dashi, yanayin rikon da yayi masa da yanayin jikin Khalil din zai baka dariya sosai," "dama bashi da wani jiki sosai gashi kuma a hannun manyan maza, wani daki ya kaishi sannan ya sake shi yana masa dariyar mugunta" """Zaka kwashi kashin ka hannu yau, wallahi Oga zai iya sawa a batar da kai a k'asar nan, kasan waye kuwa?" "Tab.""" Jawo masa kofar yayi ya rufe ta har da key yana kwasar dariya. "Chan karshen dakin yaje ya tsugunna yana jin dana sanin barin zancen da yayi, dama a maida baya da" "ya goge duk abun da yace ma Muhammad din cikin rashin sani. Ji yayi cikin sa na kara alamar ya lalace, ya tabbatar bala'in tsoro da firgicin da ya shiga ne ya saka cikin nasa lalacewa. Mikewa yayi da sauri ya" hau zagaye a dakin yana maimaita """Innalillah wa inna ilaihi rajiun.""" "Ji yayi ana murda key din dakin, ya tsaya yana kallon kofar cikin tsoro. Captain Moh ne ya shigo sojoji" "biyu na biye dashi a bayan sa, daya rik'e da kujera yazo ya ajiye masa ya zauna yana wa Khalil murmush" """Alhaji Khalil barka da warhaka.""" """Dan Allah dan Allah kayi hakuri, wallahi sharrin shaidan ne da yarinta wallahi amma ba zan sake ba.""" """Haba Khalil, so soon haka? Ka sani ko sojan gona ne ni, kasan fa talaka da samun wuri.""" """Wallahi ni dai ba zan sake ba, kayi min rai, mahaifiyta da ni ta dogara, dan Allah.""" """Calm down magana zamuyi, ka nutsu ka saurare ni, warning ne me hade da dokoki, ina fatan zaka bud'e" "kunnuwan ka kaji ni sosai.""" """Ina ji wallahi.""" """Babu kai babu abinda ya zama mallaki na, Ina nufin Fatima, ko a hanya ka hadu karka taba nuna ka" "santa balle har magana ta hada ku, a da nayi niyyar barka ka gwada sa'ar ka akanta, amma kuma a yanzu na gama yanke wa, baka kai na nemi abu tare da kai ba, dan haka ko son ta zai kashe ka sai dai ka" "hakura... """ """ Na biyu, a yau ba sai gobe ba zaka wuce in da ka fito, ba tare da ka bud'e bakin ka kace wa kowa komai" "ba, ina nufin, bakin ka ya zama kanin kafar ka, kar naji zancen a wajen kowa ciki har da ita yayarta ka da bata tsoron Allah. """ """ Last but not the list ka koma bakin aikin ka, ka rik'e mutuncin ka sannan bakai ba wulakanta kowa. """ """ Duk abinda ka fad'a wallahi zanyi, nayi alkawari, ni dai kar ka raba ni da mahaifiyata wallahi bata da" "kowa sai ni. """ """ I'm done with you, gashi nan take him back, ku tabbatar ya bar Kano kafin karfe shida na yamma. """ "Juyawa yayi cikin wani irin taku ya fice daga wajen, yana fita sukayi kansa" """ Ai wallahi ba zaka shigo nan a banza ka fita bamu ci ladan ka ba. """ Wani soja yace yana kai masa rankwashi. """ Tashi kayi frog jump. "" Dayan ya daka masa tsawa yana zaro belt dinsa. Da sauri ya hau yi yana hada" "zufa su kuma suna tuntsura dariya, sai da suka gajiyar dashi sosai sannan suka fito dashi suka sashi a mota suka maidashi har kofar gidan suka ajiye sannan suka tafi." "***Abba na zaune yaji text message ya shigo wayar sa, tunanin sa ma ko alert ne ya bud'e sai yaga sako" "daga bakuwar number da be sani ba, bud'e message din yayi ya soma karantawa" "_"" Dr. barka da warhaka, ya aiki? Allah ya taimaka. Dama wata magana nake son yi akan fatima, ina" "rokon alfarmar daka saka ido sosai akan abinda yake faruwa a cikin gidan, in sha Allah zaka gano wani abu da ya dade yana faruwa ba tare da sanin ka ba. Sai anjima a huta lafiya. ""_" "maimaita karanta sakon ya dinga yi yana kokarin daidaita tunanin sa waje guda, waye ko wace wannan?" Me sakon yake nufi? Me ya faru da Fatima din? Duk wadannan tambayoyin ne suka shiga yi masa yawo "aka, be san me yasa ba, kawai sai yaji hankalin sa ya kasa kwanciya da abinda ya karanta. Tashi yayi ya fito zuwa falon gidan, ya k'wala kiran Iman din. Zeenat ce ta fito" """ Ina Ummi? """ """ Ina ga tana wajen Gaji. """ """ Je ki kira min ita. """ Fita tayi shi kuma ya cigaba da tsaiwa awajen har suka shigo a tare. """ Ki same ni a daki na. "" Yace yana juyawa tabi bayanshi, dariyar mugunta Zeenat tayi a tunanin ta wani" laifin Iman din tayi dan sosai yanayin Abban ya nuna bacin rai. "A gefen gadon sa ya zauna, ta samu chan gefe daga kasa ta rakube tana tunanin dalilin kiran." """ Kina jina Uwata? Kina da wata matsala wacce ban sani ba? """ Girgiza kanta tayi """ A ah Abba babu. """ """ Kalle ni nan, ni ne mahaifin ki, baki da wanda yafi ni bayan mahaifiyar ki, ki fad'a min gaskiya idan" "akwai wani abu da yake damunki.""" "Zuciyar ta ce tayi rauni, taji kuka na taho mata, ta k'asa rike shi kawai ta fashe da kuka. Dafe kansa" "Abban yayi, ya shiga tunanin me yake faruwa? Wanne irin abu ne haka da har shi ya kasa ganewa?" """Fatima..."" Ya kira ainihin sunan ta a karo na farko a rayuwar ta" """Na'am."" Ta amsa cikin muryar kuka" """Kowanne bawa da irin yadda rayuwa take zuwar masa, kiyi hakuri zanyi bincike, sannan akwai shiri da" "nake yi na kaiki wajen mahaifiyar ki da zarar maganar bikin ku ta tabbata, nayi mata alkawarin kai mata ke da zarar lokacin auren ki yayi, mahaifiyar ki na son ki fiye da yadda take son kanta, ki rik'e wannan.""" """ Tashi kije kinji, ki daina kukan haka.""" Tashi tayi bayan tace """ Nagode Abba."" Ta fice ya bita da kallo yana jin kamar be kyauta mata ba." "Dakin su ta wuce ta tarar da Zeenat na waya har da shewa, juyawa tayi zuwa store ta zauna a gefen" "katifar ta, tayi kuka sosai har sai da taji babu abinda yayi saura a zuciyar ta. Tsawon lokaci ta sauka a ciki har sai da taji maganar Mama tana fad'a a waya anan ta gane ta dawo dan dazu bata gidan. Tashi tayi ta" fice ta kofar baya bayan ta gyara fuskar ta a sink din kitchen. "***Zama Mama tayi tana sababi akan tafiyar Khalil din babu sanarwa, sai dai a k'asan zuciyar ta taji" "dadin hakan domin a kalla hankalin sa zai dauke daga kan Iman din har a gama magana da shi dayan da yazo. Abba ne ya shigo ya sameta tana zaune , ya zauna a gefenta sai tasha jinin jikin ta musamman da" ta gama sanin halin sa tsaf. """Me yasa kika ce min Ibrahim ba da gaske yake akan maganar Ummi ba, sannan shi kuma yaje ya samu" "Yaya da maganar.""" Yadda ta zabura yaso bawa Abban mamaki. """Khalil din ne yaje wajen Yaya? Yaushe akayi haka? Me yayan yace masa?""" """Duk ba wannan na tambaye ki ba, baki bani amsa ta ba.""" """Toh toh ai gani nayi shi Khalil ba yanzu zai yi aure ba, su kuma yaran nan yanzu ne muke so mu aurar" "dasu, bana so Zeenat ta tafi da bar Iman tunda kaga tare suke komai, shiyasa nace gwara wanda ya shirya.""" """Haka ne kuma."" Yace yana mata wani irin kallo da ya sakata tunani sosai" """Toh hakan yayi ai, Ina fatan dai zeenatu ta sallami yaron nan Bashir ko? Dan ina nan akan bakana ba zan" "bashi ba.""" """Dan Allah Dr ka bar wannan maganar, tunda tana son shi kayi hakuri kawai ayi tunda an wuce zamanin" "da za'a yi wa yara auren dole.""" Girgiza mata kai yayi yana dakatar da ita """Wannan maganar taki shirme ce, musulunci mu ya bawa damar zaba wa yayanmu mazaje na gari, dan" "haka ban yarda da Bashir ba, idan akwai wani ta kawo shi.""" "Ya tashi ya fice ransa na baci da yadda maganar Bashir din taki karewa, sam Hajara bata shirya gane" "abunda yake hango musu ba, eh hango musu tunda duk in da aka je aka jawo ita uwa sai tafi cutuwa da abinda zai samu yarta." "***Text message biyu ya tura a lokaci daya, address din sa da Abba yace ya tura masa ta message sai" "kuma message din da yayi wa Abban Iman din, wanda yake ganin shine kadai hanyar da zai bi wajen hana Maman sanin duk wani abu akan Iman din, ya tabbata daga lokacin Abban zai saka ido sosai, ba kuma za'a dau lokaci ba zai gano komai, shi kuma sai yayi amfani da wannan damar ya nemi alfarmar barin komai ya zama sirri a tsakanin su iyaye maza, domin dama su iyaye maza baa sansu da ratatin zance ba, ba kasafai ma suke zama suyi ta magana anyhow ba, ya tabbata idan har hakan ta yiwu toh zai samu abinda yake so, zai kuma tabbatar da Fatiman sa ta samu gatan da bata taba tunani ko hasashen" samun sa ba. "***Tunani Abba ya fad'a ganin address din da Muhammad ya turo masa a matsayin in da yake,Emir" "Palace Kano, Emir Palace Adamawa-Yola, me hakan ke nufi? Kiran Abban su Fatiman yayi yazo ya same shi a part din sa, ya nuna masa message din sannan ya kira sauran yan uwan su Abba Musa suka hau tattaunawa akan abinda ya kamata su yi. Dama chan Abba Musan yana siyasa sosai, sai sukayi shawara akan shi ne zai wuce gaba wajen binciken waye Muhammad din a cikin kwana uku kachal. Haka kuwa akayi, washegari ya same su da maganar da ta yi matukar basu mamaki. A yadda suka sani idan wani daga cikin irin wannan yaga yarinya yana so, kawai aikawa ake iyayenta suzo ayi magana a fadar sarkin, a matsayin shi sarki dama uban kowa ne, sai suga ga banbanci inda Muhammad din yazo kai tsaye ba tare da ya nuna shi din waye ba, ba kuma tare da ya nuna karfin iko na mulki ba, hanyar da ta dace da kowa" yake bi wajen neman aure shima ita yabi. "A cikin su babu wanda be yi amanna da maganar ba, musamman binciken da Abba Musan yayi da irin" yabon da Muhammad din ya samu daga wajen mutane da dama musamman mazauna masarautar. "Shiru Abba yayi bayan kowa ya gama tofa albarkacin bakin sa, aka bashi dama a matsayin sa na" "mahaifin Iman din," """Bakwa ganin idan iyayen yaron nan suka san in da yazo neman aure zasu kyale shi, duba da mu din ba" "wasu bane akan irin girma da nasabar gidan da ya fito.""" """Idan har a yadda bincike na ya nuna min ne, iyayen sa basu da matsala masu son talakawan su ne, dan" "haka muyi addua kawai in sha Allah alkhairi ne.""" """Shikenan, Allah ya tabbatar mana da alkhairi,.""" """Yanzu kayi magana, Amin ya Allah.""" """ Ina neman alfarma daya, da mu bar maganar nan a tsakanin mu zuwa muga abinda Allah yayi.""" """ Hakan yayi, Allah ya shige mana gaba.""" "Suka hada baki a tare, sai kuma suka shiga wata hirar tunda daman su dan dade basu yi irin wannan" "zaman ba, anan duk suka ci abinci a tare sannan kowa ya tafi zuwa sabgar sa. Aka bar Yaya a zuwan zai kira Muhammad din da daddare ya sanar dashi ya bashi izinin yazo yaga Fatiman su daidaita, da daddaren bayan ya gama komai ya turawa Muhammad din text message akan ya cigaba da zuwa." Muhammad na zaune shi da Musaddik suna kallon video da ya saka akayi wa Khalil suna kwasar dariya "text din ya shigo, tashi yayi ya daka tsalle kafin yace" """Yess!!!" """ Ya akayi?""" """ Karfe nawa yanzu?""" Yace yana kallon agogon falon """ Opss Ashe dare ya fara, ba dan ba dan ba da yanzu zanje na ganta, amma ba komai kafin na wuce" "Abuja zan tsaya na fara ganin ta.""" """ Me faru wai.""" """ Karanta!"" Ya mik'a masa wayar" """ Ah congratulations angon fatiti, Allah ya tabbatar mana da alkhairi.""" Rik'e k'ugu yayi yana hararar sa """ Allah ka sake bata mana suna sai na saka frog jump, kaji ma na ratse.""" """ Kut! Allah fa ka raina ni Moh, komai sai kace zaka sani frog jump an fad'a ma nima kamar wadanchan" "dogs din naka ne na bakin gate.""" """ Ka dai kula, kana magana ne da Captain Muhammad Ahmad Santuraki, Captain Moh!""" """ Whatever, ni dai muhammadu na sani, ba wani bragging da zaka min.""" """ Zaka gane ne idan na dauke ka na je na jefa wa mayunwatan zakunan nan na barack, ba zaka sake kiran" "sunana gatsal ba.""" """ An gaya ma kowa irin khalil ne? Lusari!""" "Dariya suka saka Muhammad ya shiga gwada yadda Khalil din yake, suka sake tuntsurewa da dariya suka" tafa """ Ashe farar kura ce a wajen, sai uban cika baki dan iskan yaro, gobe ma ya sake, naso ka dan saka su sun" "sassama masa jiki wallahi,.""" """ A hakan ma nasan sai sunci zalinsa ai.""" """ Wicked soul!"" Yace yana dariya" """ Naji, bari naje na kira Baby na, naji voice dinta me dadi kafin gobe naje na ganta, dan yanzu ina da" "license, na matsu na ganmu tare, muna yawo a garin nan cikin mota my hands in to her's, ga cool music na tashi Malam, wow love in the air.""" """ Toh Mr Romeo, Allah ya kaimu dai zamuyi kallo, yadda kake son ta Allah yasa tana maka ko rabin sa" "ne.""" """ I don't care, as long as munyi aure, zan koya mata yadda zata so ni.""" """ We shall see.""" "***Ruwan zafi ne a katon bawo, Khalil na zaune a gaban ruwan hajiyar su na danna masa bayansa, gaba" "daya jikin sa ciwo yake kafarsa kamar zata cire yake ji, babu irin tambayar da batayi masa akan me ya same shi ba amma yaki fad'a mata, haka Mama ta bugu tana fad'an tafiyar Khalil din hajiyar ta fad'a mata a yadda ya dawo, kuma yaki cewa komai. Yana jin su har suka gama ya tashi ya koma dakin sa ya kwanta yana tariyo abinda ya faru cikin tausayin kansa. Shi ya jawo yana takama da shegen bakin sa ya je ya kaishi ya baro, dama an fad'a mutum ya kiyayi harshen sa, akwai hadisi guda da akayi magana akan harshe da kiyayar sa, yaga izina a kansa, gashi bashi da damar fadawa wani abinda ya faru domin yasan shi za'a yi wa dariya, ko da muhammadu a iya soja ya tsaya matsayin da yake kai ya isa ya taka shi son ransa ba kuma wanda ya isa yace dan me? Balle ganowar da yayi waye Muhammad din, anan ya gane bakin rijiya ba wajen wasan yaro bane, shi din ma ganganci ne da kuruciya. Eh toh kuruciya mana tunda dai yasan a girme Muhammad din zai girma shi dole ya fishi hankali da komai. Abu daya ne zai hana shi walwala, yadda zai yi da tarin soyayyar ta, gashi yayi masa kashedin ko a hanya babu shi babu ita, ya kuma tabbatar idan har ya kuskura yayi wani abu, za'a iya neman shi ma baki daya a rasa, dan masu" "kudin nan yasan ba wani abu bane a wajen su su batar da mutum bat, har abada a daina jin labarin sa." Tagumi ya rafka yana jin kamar yayi ta kurma ihu ko yaji sassaucin radadin da zuciyar sa ke masa. Allah sarki Khalil 08184017082 "GA MASU TURA KATIN WAYA KO KUMA VTU,SAIKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYANKU" "09134848107[1/9, 8:38 AM] +234 803 765 3189: Halin Girma" 10 "*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107*" I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ft46u5twk6r3&utm_content=nj79azb "***Be ji sallamar ta ba, sai ganin ta yayi kawai a dakin bayan a zahiri tayi sallamar amma saboda baki" daya hankalin sa na ga tunani shiyasa be ji ba sam. """Ya Khalil wai a kawo maka abinci...""" Ai kafin ta karasa ya daka mata uwar tsawa """Uban abincin, dallah Malama karki dame ni.""" """Toh... Me yayi zafi? Hajiya ce ta aiko ni ai.""" """Fitar min daga daki!"" Yace yana tasowa, da gudu ta juya tana dariya, sai da ta ga ta fice sannan ta daga" murya tace """Bani na kar zomon ba...""" "Ransa ne ya sake baci, ya bigi kofa yana komawa ya fad'a saman katifar sa yana jin kamar yayi ta cizon" kansa. A falo ta samu Hajiya ta zauna tana haki """Allah ya taimake ni na kusa cin duka, daga tambaya kawai ya hayayyako min Hajiya.""" """Toh wai ko dai Khalil tsokana yayo ne aka tattaka shi, kinsan fa Khalil ba dai tsokana da cika baki ba.""" """Alamu dai sun nuna Hajiya, fad'a ya takalo da yafi karfin sa wallahi, gashi nan yaki fad'an abinda ya" "faru.""" """Toh Allah ya kyauta "" Hajiyan tace tana tashi ta fita zuwa dakin nasa." "***Tana tsaye a bayan kitchen dinsu, wanki ta gama tana ta sauri saboda kwana biyu bata maida hankali" "zuwa islamiyya saboda abubuwan da suka sako kai, tana wankin tana tunanin maganar da sukayi da Abba da ta zama tamkar bitar karatu haka take yin sa, takun tafiya taji, ta juyo sai taga Abban a tsaye yana duban ta, da sauri ta dan russuna," """Abba sannu da zuwa.""" """Wanki ake ne?""" """Na'am.?"" Tace tana zaro ido sanin cewa ba da sanin sa take wankin ba, musamman ya samu almajiri" "yake wanke musu kaya ita da Zeenat da Marwan yake biyan shi ta hannun Mama, duk da yasan dole zasuyi wanki irin kayan ciki da abubuwan da ba za'a iya bawa me wanki ba, amma kuma tarin kayan da ya gani a wajen da ya gane na Marwan ne sai wasu na Maman ya saka ransa mummunan baci, har a jiya" sai da Maman ta karbi kudin wanki a wajen sa da zumar yau me wankin zaizo karbar kudin sa ya kuma "bata babu musu. Yanayin sanyin garin zai yi wuya wajen wanki musamman da tun da dadewa yasan fatar Iman din bata son wahala idan tayi wanki hannun ta kanyi ja sosai, shi kuma Allah ya hore masa son yaya Kuma gasu ba wai yawa ne dasu ba shiyasa duk wani aikin wahala baya son siyi duk da ba wai kwata kwata ba zasuyi komai ba, amma kamar wanki yana ganin be kamata shima a saka shi a cikin aikin mata ba, mata na wahala da aikin gida kula da yara da girki wankin aka dauke musu zasu samu sassauci." Matsowa yayi ya sake leka kayan kafin ya girgiza kansa ya juya bayan yace """Ki bar wankin nan kizo ki wuce ciki.""" Sakalo tayi a tsaye tsoro na kamata """Bakya ji ne?"" Ya daka mata tsawa, da sauri ta bi bayansa har cikin gidan, dakin su taga ya wuce ya" kwankwasa sannan ya tsaya """Waye?"" Zeenat tace tana daga kwance cikin rufa, a yadda tayi maganar zaka gane knocking din ya" "takura ta, sake kwankwasa wa yayi sannan ya tura kofar da sallama, be shiga ba, ya tsaya a kofar yana karewa dakin kallo, gadon zuwa katifar dake shinfid'e a kasa da ta tabbatar masa da ta Iman din ce. Tuna lokacin da ya bada kudin gadajen nasu yace a siyawa kowa nasa amma sai Mama tace daya ya ishesu me dan girma saboda hakan zai sake shakuwa tsakanin su,da wannan yayi amfani a ganin sa hakan ne ya kuma dauki hakan a matsayin soyayyar da Maman ke wa yar tasa. A yadda yake jin zuciyar sa a lokacin" "zai iya yin komai, sai kawai ya fice daga gidan gaba daya ba tare da ya koma daki ba." "Tsoro ne ya kama Iman musamman da bata san me zata ce wa Maman ba akan wankin, shiryawa tayi" "cike da fargaba ta tafi makarantar tana fatan koma menene ya taso ya zama daidia kafin ta dawo dan a rayuwar ta, ta tsani tashin hankali ko kad'an." "Rabi da kwata bata gane kan karatun ba, haka dai ta taho gidan tana ta zulumi, tana shigowa ta ganshi" a tsaye ya harde hannayen sa a gadon bayan sa yana kallon kofar shigowar. Shigar jikin sa ta bi da kallo "zuwa gyaran da yayiwa fuskar sa, murmushin da ta gani kwance a fuskar tasa, ya saka ta samun nutsuwa har ta karaso wajen da yake a tsaye." """Ashe kina kusa da shigowa, naji a jikina.""" Murmushi tayi kafin tace """Sannu da zuwa.""" """Yawwa, ya hanya?""" """Alhamdulillah wallahi.*" """ Akwai wanda ya kalleki da kina tahowa? Idan akwai fad'a min naje na same shi.""" "Sosai ya bata dariya," """ Kai... Babu kowa fa, ya gida yasu Mama?""" """ Mama? Ammi muke ce mata, tana nan lafiya tace ma na gaishe ki, na gaida wacce ta kwace mata" "yaronta kafin tazo haka tace.""" Rufe fuskar ta tayi tayi yar dariya """ Allah sarki, ina amsawa nagode.""" """ Itama ta gode, tace ta matsu ta ganki.""" """Watarana zata ganni in Sha Allah.""" """In Sha Allah, very soon.""" """Abba Babba yace idan kazo ka shiga ciki.""" """ Da gaske? Kice na zama dan gatan Abba.""" Dariya tayi """ Naga alama kam, Abba ya yarda da kai sosai.""" """ Allah sarki, ai yana da kirki sosai.""" """ Sosai."" Tace" """ Bari na bud'e maka, chan ne seat room din sa.""" """ Owk."" Yace ya harde a jikin ginin yana kallonta, har ta bud'e ta dawo sannan ya bita a baya yana" admiring steps dinta zuwa ciki. "A kofar dake farkon kofar ya zauna ita kuma ta shiga ciki, yana zama Aliyu ya shigo da ruwa a tray, ya" "ajiye ya gaishe shi sannan ya fita, ruwan ya dauka ya sha sosai sannan ya kalle ta, gefe take kallo tana wasa da jikin kujerar da take kai." """ Zahraah, tafiya ce ta kamani, ba zan iya wucewa ban sanar miki ba, ba wani dadewa zan ba in sha Allah," "inaso kafin lokacin da zan dawo mu sake fahimtar juna sosai, idan na dawo sai a shigo da magana me karfi, bana so a ja lokacin.""" """ Allah ya kiyaye ya tsare, ya dawo da kai lafiya.""" """ Amin ya Allah, Amin Amin Zahraah Nagode""" "Shiru ne ya dan shiga tsakani, shi yana kallon ta yana sake ganin ainihin kyawun ta, ita kuma ta tafi" "tunanin Allah yasa ya dawo din kar taji shiru idan ya tafi, har zuciyar ta bata son tafiyar tasa, amma kuma ya zatayi? Ba zata hanashi ba ai." """Ina wannan yayan naki da muka hadu ranar nan? Har ya korar min ke?""" """ Uncle Khalil?"" Tayi dariya" """ Auw sunan shi kenan.""" """ Eh kanin Mama ne, a nan gidan ya taso kafin ya koma gida.""" Gid'a kansa yayi kamar be sani ba """ Shiyasa ya nuna min iko kenan.""" """ Uhum."" Tace kawai bata ce komai ba." """Yana ina kuwa?""" """Kamar dai ya koma, naji dai mama na fad'an ya tafi be sanar ba.""" """Ai be isa ya sanar.""" """Na'am?"" Tace tana kallon sa" """Sorry ba komai."" Ya maze kamar be ce komai ba, be san maganar zata fito ba shima." """ Bari na gudu, kar nayi rana.""" Mikewa tayi """ Daga nan zaka wuce?""" """ Eh gaskiya, idan na koma gida na koma baya.""" """ Ok ina zuwa.""" "Ta fita ya tashi ya dan zagaye falon yana observing komai na ciki, yana tsaye jikin wani frame ta shigo" dauke da leda ta mika masa tana dan russunawa """ Gashi ka kaiwa Ammi, ina gaishe ta.""" "Rik'e ledar yayi yana kallon ta, tayi saurin dauke kanta k'asa ta sakar masa ledar gabanta na faduwa." """ I love you.""" "Ya samu kansa da whispering cikin muryar da tayi masifar shigewa ciki, wani irin feeling taji, sarai ta jishi" "sai tayi kamar bata ji ba, ta ja baya sosai tana diriricewa, shi kansa wani iri yake ji, be taba tunanin haka daga gareta ba, da tasan yadda Ammi take a wajen sa, da kuma yadda sakon nan yayi nasarar kara masa son ta ninkin ba ninkin, da tun ranar da ya fara zuwa tayi, kasa matsawa daga in da yake yayi, sai" murmushi yake shi kadai. """Nagode sosai, Ammi ta gode.""" """Ba komai."" Tace tana jin nauyi da kunyar yadda yayi" """Zan tafi, ki kula da kanki kinji? Karki yarda wani ya bata miki rai, kin fi karfin haka, ke din ta daban ce, ta" "musamman ce.""" """In Sha Allah."" Tace tana jin dadi , a kalla idan tana tare dashi tana jin cewa itama tana da yanci, sannan" takai matsayin a so ta. "Ta cikin idon sa yake ta kokarin aika mata da sakon sa, sakon da yake so ya tafi ya bar mata, irin me" "zafin nan da zatayi wuyar dauke shi daga tunanin ta, sau daya ya samu nasarar aika mata da sakon, ya kuma je a yadda yake so, sai ya marairaice mata fuska yana jijjiga kansa." """Allah ya kiyaye Allah ya kaimu lafiya."" Tace da sauri ta bud'e kofar kuusa da ita ta fice ta bar shi a ciki," "dariya sosai ya saka, ya sake rik'e ledar hannun sa gam gam, ya fice yana jin sa tamkar yana yawo a cikin gajimare." "A kafa yake tafiya rik'e da ledar, iska na kada shi, sam baya jin komai baya ganin kowa sai tsadadden" "murmushin sa, shi kadai yasan yadda yake ji a lokacin, shi ya saka shi tafiya kawai ba tare da ya neme su" "ba. A chan bayan layin da suka saba haduwa suna tsaye tana masa mitar kwana biyu be zo ba, hakuri yake bata akan wata tafiya ce ta taso masa Muhammad din yazo wucewa" """Kaga saurayin Iman.""" "Tace da sauri tana nuna masa shi. Wani kallo Bashir yayi masa daga nesan kafin yayi saurin juya bayan sa," "yayi saurin bud'e motar ya shiga ciki, yayi kamar yana neman wani abu a ciki" """Baby me kake nema? Fito ku gaisa da Malam mana.""" "Kin fitowa yayi ya cigaba da bud'e dashboard yana rufewa," """Assalamu alaikum."" Moh yayi musu sallama yana karewa motar kallo." "A wani yanayi Bashir ya fito bayan nacin da Zeenat din tayi masa, ya diririce ganin Moh din" """Sannu ko?"" Moh yace masa yana mika masa hannu" """Sunana Muhammad, kaifa?""" "Yace masa, a sakale Bashir ya miko nasan hannun kamar me tsoro cikin rada rada yace" """Bashir.""" """Yayi Bashir, sai anjima."" Ya wuce ba tare da yace komai ba. Dariya Zeenat ta saka" """Shi wannan din kika ce shine zai auri Iman?"" Yace da sauri" """ In Sha Allah, baka ga sun dace ba? Ko baka ga yanayin su daya bane?""" """ A haka yake tun zuwan sa gidan kuma?" """Babe me ta faru?""" """Noo noo babu komai.""" """Naga duk ka damu ne, me ya faru?""" """ Ah babu komai, kawai na ganshi haka haka ne.""" """Dan ma baka ganshi sanda ya fara zuwa bane, tab!"" Ta sake kwanshewa da dariya" """Abun mamaki."" Ya furta ba tare da ya sani ba." """Abun mamakin gaske , mutum kamar wani mahau.""" """Keee."" Yace mata yana zaro ido, sai kuma ya waske da sauri" """Bari naje, ya kamata mama tayi tayi ya shawo kan Abba ina so na turo manya.""" """Ka turo kawai, ka bar komai a hannu na, bbu me min auren dole, wanda nake so zan aura babu me" "hanawa.""" """Toh shikenan.""" "Sallama sukayi ya tafi itama kuma ta koma gida, tana shiga ta tarar da Abba a compound, ya tasa ta a" gaba ransa a bace. "***Wani kallo da Maman tayi wa Iman lokacin da ta shigo ya saka ta shan jinin jikin ta, ta wuce bayan ta" "gaishe ta bata amsa ba, ta ajiye jakar ta sannan ta fito ta shiga kitchen ta sha ruwa ta dora ruwan abinci sannan ta fito falon, tana tsaye ya hade ran ta sosai, ta tsaida ita" """Uban waye ya baki izinin ajiye min wankin da na sakaki? Ka tafi?""" """Ubanta ne!"" Abba da suka shigo tare da Zeenat yace, da sauri Mama ta juyo sukayi ido biyu dashi" "***Ba karamin matse kaina nayi ba saboda na cika alkawari, kuyi hakuri babu yawa" "[1/10, 8:03 PM] +234 803 765 3189: Halin Girma" 11 "*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107*" I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ft46u5twk6r3&utm_content=nj79azb _*Mierah's dukkan_* _*Mierah’s dukkan_* _*Mierah’s dukkan_* _(Palace of exotic scent and more) _ "_MD: is ur plug! Muna siyarda kaya kala2 kamar jaka da takalmi kamfanin lamis,Dior,vellabela da dkny" "da sneakers 'yan yyi dominku da yaranku,Muna order kaya dga kasashe daban-daban,Muna siyarda da" "kayan decors,plated gold,da turaruka kala-kala Hadi dna tasa (oil perfume) dga kamfanin naseem hr" "suratti,Muna da room fresh da turarukan wuta Dan gangaria. Muna adashe na yargata(kaya) Dana kudi ku tuntube mu awannan nmbr kamar haka wa.me/07039773001 Muna turawa ko Ina afadin Nigeria da" wasu kasashen ketare ngd_ *** "A wani yanayi Maman ta dago, gabanta ya fadi ganin Abba a tsaye a kofar Zeenat na rakube a gefe" kamar munafuka """Dr, Sannu da zuwa.""" """Kinsan daga ina yarinyar nan take?""" Ya nuna Zeenat yana jin kamar ya rufe ta da duka. """Aiken ta ne nan baya gidan Amarya me koko."" Tace bayan tasan ba hakan bane. Kwafa yayi cikin kada" Kai yace """Yaron da nace babu ita babu shi take zuwa suna haduwa a bayan layi, na fad'a miki na kuma bana son" "yaron domin ba yaron kirki bane, amma a bayan kunnenku.""" """Idan har ta dage ba zata ji magana ta ba, zata dinga fita suna haduwa a wani wajen ba da izini na ba ko" "na yan uwana, zan sallama masa sai tace ya turo,amma...""" Ya nuna ta da yatsa """Idan har wani abu ya je ya dawo, kar ku kuka da kowa, ta kuka da kanku!""" "Shiru Maman tayi taki cewa komai, haka Zeenat din da ya zaci zata bashi hakuri sai yaji tayi shiru" """ Kin amince da Bashir din, kin yarda zaki aure shi?""" "Daga kanta tayi da sauri babu kunya ba tsoron Allah, wani irin faduwa gaban Abban yayi, yaji tamkar zai" "fadi saboda wani jiri da ya nemi zubar dashi, be zaci haka daga gareta ba, sam ba tarbiyyar da yayi wa yaransa bace, sake maimaitawa yayi cikin danne abinda yake ji yace" """ Kinji kin gani, kin Amince?""" """ Dr ka bar maganar nan idan muka shiga ciki sai mu..."" Dakatar da ita yayi da hannu, ya dakawa Zeenat" din tsawa """ Ki bani amsa!""" """ Eh Abba."" Tace tana nokewa idon ta fes tamkar an soye gyada" """ Shikenan, shikenan."" Ya maimaita" """ Kice dashi ya turo magabatansa, suzo wajen Yaya.""" Sai ya juya wajen Iman da tayi kamar ta bud'e kasa ta shige saboda kunyar abinda Zeenat din tayi yace """ Kema ki ce masa ya turo dan ba zan bata lokaci ba.""" "Daga kanta tayi da sauri, ya wuce su yana jin wani irin tashin hankalin abinda Zeenat din tayi, tabbas" "laifin Hajara ne, ita ce bata tankwarata ba, bata nuna mata daidai da akasin haka ba, abinda ma ya lura" "Itace take son abin, ba zai yarda wani abu ya faru ba a dalilin hana ta auren Bashir din, dan yaran yanzu" "zasu iya komai akan soyayya, shiyasa kawai ya yanke shawarar aura mata shi din idan har ta kafe, da azo ana wallahi tallahi." "Abban na barin wajen itama Iman tayi saurin ficewa dan tasan sarai Mama zata huce akanta, tana juyo" "fad'an da take wa Zeenat din sama-sama, ta kara sauri ta zagaya ta baya ta shiga ta kitchen ta wuce dakin su kawai." "Tsawon kwanakin Abba bashi da walwala sam, ita kanta Mama ta kasa gane kansa, da ya shigo zai" "wuce dakin sa kawai sai kuma gobe, a da tayi tunanin fushin ba zai nisa ba, sai taga abin yana neman zarcewa, takanas ta same shi da maganar da ban hakuri amma sai ya share ta yama yi ficewar sa ya barta, haushin hakan ya sakata share shi itama ta san dole zai gama fushin sa ya dawo ko da Anyi auren yaji su kalou zai ajiye komai ya dawo, tasan ta fishi gaskiya shiyasa taki goyon bayan sa, dan tasan" zugashi akayi dan an ga Zeenat din zata huta. "***Bayan tafiyar Muhammad basu yi magana da ita ba, sau biyu tana kiran number sa bata samun sa," "hakan ya saka ta damu sosai, gashi tasan Abba zai sake mata magana akan abinda yace ta fad'a masan, gashi bata sameshi ba, tsoron ta daya Allah yasa ba guduwa yayi ba, dan har ga Allah zuciyar ta, ta yarda dashi. Har tana jin son sa na shigar ta, koman sa daban ne hatta maganar sa, ta kasa gane komai akansa musamman a fagen da zata ajiye shi, yanayin sa da koman sa yasha banban da shigar sa, tana bukatar sanin sa sosai kila ko bayan sunzo da iyayen sa an daidaita, a lokacin zata bijiro masa da tambaya akan sa," "ko da ba komai ba, a kalla ya bata labarin wani abu da ya shafe shi." "Fitowa tayi falo ta zauna bayan ta gyarawa Gaji daki, maman su Maryam ce ta shigo, ta gaishe ta tana" "tashi ta kira mata Gaji, tare suka dawo da Gajin ta gaishe ta sannan suka soma hira akan abubuwa da" dama. Ita dai Iman na zaune tana jin su tana duba wayar ta. Maganar Maryam suka shiga ya sakata d'agowa tace """Umma Ya Maryam din ce bata da lafiya?""" """Wallahi Iman, wai har kwananta uku a asibiti amma basu fadawa kowa ba, bari tayi an sallameta dazu" "amma, shine nake tunanin wanda zai je mata ya dan taimaka mata ko na sati daya ne.""" """Allah sarki, Allah ya kara sauki.""" """ Ko ke zaki je ne takwara?""" """Toh..."" Tace har cikin ranta bata so ba" """ Iman bata son mutane ai, zata iya zuwa kuwa? Maman su Maryam din tace tana murmushi" """Idan ta kamata ya zatayi?"" Gaji tace" """Wai kar a takura ta dama.""" """Haba kinji wani zance, yar uwarta ce fa? Idan batayi mata ba wa zatayi wa?""" """Haka ne.""" """Zance Umma, ba komai ai.""" """Toh shikenan, anjima sai wani cikin samarin ya mik'a ki.""" """Ai ba sai anjima ba, yanzu zata shirya sai su wuce, ki shiga sai ki sanar da Maman tasu, idan yaso sai ta" "fadawa Ibrahim din duk da nasan babu abinda zaice.""" """Toh shikenan bari na shiga wajen nasu."" Ta tashi ta fita,ita kuma Iman ta wuce ciki ta dauko charger ta" tazo ta fita. "A zaune ta tarar da Umman suna maganar da Mama, tana shiga tace" """Ki shirya zaki je gidan Maryam kiyi kwana biyu, Allah ya kara sauki.""" """Toh."" Tace ta wuce ciki, ta dauki wata karamar Jakarta, ta saka kayanta kala biyu sai undies da hisnul" "muslim, da dan abinda tasan zata bukata ta fito, bata ga su Maman a falo ba, sai ta nufi dakin ta rataye da jakar a kafadarta, ta kwankwasa kafin ta shiga" """Mama na fito."" Tace daga kofa, jakar ta dake kan gado ta dauko ta ciro dubu daya ta mik'a mata" """Sai kin dawo.""" "Hannu biyu tasa ta karba mamaki na kamata, tayi godiya ta fito still tana jin kamar mafarki, magana me" "dadi daga Mama har da bata kudi? Akan me? Sam sai taji hankalin ta be kwanta ba, taji kamar ta koma ta tambaye ta dalilin action dinta amma babu hali." "Ita kadai ta dinga juya dubun har suka isa gidan Maryam din, ta fito rik'e da jakar ta shiga gidan. A falo" "ta tarar da ita da mijinta sai sister dinshi wata babba haka. Wani farin ciki ne ta gani a fuskar maryam din, ta tashi zaune tana mata sannu da zuwa." "Gaishe su ta fara yi suka amsa dukka sannan ta nufi wajen Maryam din tana mata ya jiki," """D-D bari naje na kai Yaya gida tunda ga Maryam tazo.""" """Ok tam."" Tace" """Nagode sosai Anty Saliha, ku gaida gida.""" """Gida zaiji Maryam, Allah ya kara sauki ki kula da kanki sosai kinji? Ki dinga cin abinci sosai saboda kiyi" "saurin dawowa dai, Allah ya kawo wani rabo me albarka.""" """ In Sha Allah zanci, nagode."" Tace a kunyace, sukayi sallama suka fita" """ Sa mana key din a kofar.""" Tace wa Maryam din tana gyara zaman ta. Key din Maryam ta saka musu ta dawo ta zauna kusa da ita """Ashe ke zaki zo, naji dadi da ba'a turo wata cikin yaran chan ba wallahi.""" """Wallahi, ya jikin naki? Naga kinyi fari sosai.""" """ Toh ba dole ba, kin ga uban wahalar da nasha kuwa? Kai Iman aure- aure akwai wahala wallahi.""" """ Sannu, Allah ya kara sauki.""" """ Amin ya Allah.""" """ Ya gida yasu Mama, Gaji da kowa da kowa?""" """ Kowa lafiya lou, duk suna gaishe shi.""" """ Ina amsawa, amma zasu zo su dubani ai ko?""" """ Eh toh nasan zasu zo, dan baki ga ma fad'an da Umman tayi ba, kwana uku a asibiti baku fad'a ba.""" """ Ina na sane, hankali na baya jikina, laifin D-D ne, shi ne be fad'a ba wallah. Anty Saliha ma baki ga" "fad'an da tayi ba.""" """ Ai dole, wani abun kana bukatar Babba kusa da kai.""" """Aikuwa.""" """ Allah ya kara sauki ya kiyaye gaba.""" """ Amin addu'ar kenan.""" """ Sai naji labari kuma, Ashe su Abba sun fara maganar ku, Umma tace min ma ke kamar su abba sun" "gama bincike akan shi har ma sun tabbatar da shi din zasu bawa, Umma tace bata taba ganin Abba ya damu da wani a cikin masu zuwa neman yayan gidan ba kamar yadda ya damu da wannan din, ko dai" "wani Babban kika samo mana ko wani basarake?""" Tace cikin zolaya """ Kai Ya Maryam, bafa kowa bane hasalima dai ba wani me kudi bane kawai dai inaga ko Abba ya gamsu" "da halayen sa ne.""" """ Eh toh haka ma Umma tace, nima tsokanar ki nake, ke yanzu ka samu miji na gari me son ka me son" "farin cikin ka shine, ba yalwar arziki ba, da wani arzikin gwara rufin asiri.""" """ Haka ne.""" """ Allah ya kaimu lokavin, musha biki.""" "Dariya tayi kawai dan ita jikinta a sanyaye yake da rashin jin sa har tsawon kwanaki hudu, ta damu sosai" "sosai har ta kan zauna tayi ta tuna moments din da sukayi tare, wani lokacin tayi murmushi ita kadai wani lokacin kuma ta ji kunya ta kamata." "_""I love you.""_ Kalmar da yadda ya fade ta take ta tunawa, har yadda lips dinsa suka hade waje daya" "yayin da yake furtawa, cikin muryar da take yawan yi mata amsa kuwwa a cikin kunnenta" """Dan Allah dafa min danwake, shi kawai nake sha'awa baki na babu dadi wallahi.""" "Maryam ta katse mata tunanin da take, ajiye wayar ta tayi a gefen Maryam din, ta tashi zuwa kitchen din," minti kad'an ta leko """Toh ai bansan Ina kayan naki suke ba.""" "Tasowa Maryam din tayi, tazo ta dauko nata komai ta nuna mata sauran sannan ta dawo falon ta jona" "wa Iman din wayar ta a charge kusa da ita ta kunna tv ta koma ta zauna tana kalla, jefi jefi tana yiwa Iman din hira daga nan." "Wayar Iman din ce tai kara, alamar shigowar kira, tana daga kitchen din amma sai da ta ji gabanta ya" "fadi, saboda tsabar jiran kiransa har ringing tone ta chanja masa nashi shi kadai saboda da ya kira yadda zata fi saurin ganewa," """Ana kiran ki Iman."" Maryam tace tana jawo wayar ta kalli screen din" """M ne yake kira, M M M waye Ma? Sirikin nawa?""" "Tace tana murmushi, maimakon Iman din ta fito ta karba sai kawai ta cigaba da aikinta tana jin Maryam" "din na mata sababin zata katse, kamar ba kiran da take jira bane, amma kuma a kalla yanzu hankalin ta ya kwanta, tasan cewa da gaske be manta da ita ba. Sake kira akayi karo na biyu," """Bana son wulakanci Iman, bari na daga kizo ki karba.""" Dagawa tayi ta saka a kunne """Sweetheart.""" "Ya furta cikin rada yana sauke ajiyar zuciya, da sauri Maryam tayi gyara murya tana cire wayar kafin ta" mayar tace """Yayarta ce maryam, tana kitchen ne.""" """Anty Maryam, Ina wuni?""" """Lafiya lou wallahi, ya aiki?""" """Alhamdulillah.""" """Dama tana kitchen ne, amma yanzu zata zo zata kira.""" """Owk nagode sosai.""" """Nima Nagode."" Ta katse kiran tana tashi, zuwa tayi kitchen din da daddage da d'aka mata duka a baya" """Dan wulakanci kina ji yana kira ko? Wannan irin hot guy din ba'a musu jan aji wallahi, kinji kuwa? Haka" "yake kashe ki da soyayya? Hmmm lallai yau ga wanda yafi D-D na.""" "Banza Maryam din tayi mata tana murmushi, ta karbi wayar ta ajiye a gefe ta karasa kwashe danwaken" "ta zuba a flask ta zuba ruwan zafi akai ta rufe, ta soya man ta hada komai a babban tray ta dora Maryam din na tsaya a akanta tana mata hirar Moh din ita a dole sai taji wani abu daga iman din amma tayi mata fumfurus" """Mara lafiya ba'a cika son shi da yawan magana ba, muje na kai miki abincin falo.""" "Dukan ta kara kai mata ta goce tana dariya, suka jero Maryam din na rik'e da bottle water ta ajiye mata" komai a falon ta zuba mata sannan ta dauki jakarta tace """Ina ne dakin?""" Da baki Maryam din ta nuna mata lokacin ta cika bakin ta da dan wake. Dakin ta nufa ta shige ta rufo "kofa sannan ta cire hijab dinta ta ajiye a agefen gadon ta zauna tana kallon wayar, kunya da nauyin kiran sa take amma kuma tana bukatar kiran nasa, tayi missing dinsa da muryar sa gaba daya. Kiran nasa tayi tana tashi tsaye lokacin da ta soma ringing, be daga ba, amma kuma tana katsewa ya biyo kiran a take." """Assalamu alaikum."" Tayi sallama wayar a hannun ta bata saka a kunne ba" """Wa alaykisalam.""" "Ya amsa sai yayi shiru, itama shirun tayi tana saka abinda zata ce" """Shine baka kirani ba?"" Ta samu kanta da fad'a ba tare da tayi tunani ba. Abinda dama yake son ji kenan," "tayi missing dinsa in dai har tayi korafi akan rashin kiran, murmushi yayi wanda taji sautin sa ta cikin wayar" """Kinyi kewa ta kenan ko?""" """Um um."" Tace da sauri" """Kawai dai na kikkiraka bata shiga, kuma Abba ya bani sako shine kawai dama.""" """Ohh, sakon Abba ne yasa kika kira ni ba don kinyi kewa ta ba?""" "Shiru tayi dan a zahirin gaskiya ba hakan bane, tana bukatar ji daga gareshi, tana bukatar comforting" "words dinsa, tana bukatar shi kawai ma in short." """Ni kuma kinga nayi kewar ki, sosai sosai komai ma da nake anan din yinsa kawai nake ba don naso ba," "kiyi hakuri kin kirani, ina wajen da dole na kashe waya, shiyasa har kika jini shiru haka.""" """Ok."" Tace a ba tare da tasan me zata ce ba" """Ya gida ya kowa da kowa?""" """Alhamdulillah, yasu Ammi? Ka samesu lafiya?""" """Lafiya lou, banje gida ba, yau nake shirin zuwa in sha Allah.""" """Ok tam, karka manta ka gaishe ta.""" """Ba zan manta ba, zance mata sirikarta na gaishe ta, zan kira sai na bata kuyi magana.""" """ Um um ba zan iya ba.""" """ Kunyar ta kike ji? Irin kunyar surkutan nan ko?"" Ya kyalkyale da dariya" """ Ni dai bance ba.""" """ Ni kuma nace.""" """ Uhum.""" """ Wacece Maryam?""" """ Yayata ce da akayi bikin su, nazo gidan ta bata da lafiya zan kwana biyu na dan taimaka mata.""" """ Owk ayya, ki duba ta, Allah ya bata lafiya.""" """ Amin zataji.""" """ Baki fad'a min ba, me Abbanmu yace?""" """ Na zata ba zaka tambaya ba ai?""" """ Na isa? Ina sane kawai dai.""" """ Dama cewa yayi, a turo.""" """ Me!!! Alhamdulillah, Alhamdulillah Alhamdulillah! Kina nufin Abba yace na turo magabatana ayi" "magana? Kenan Abba ya yarda ya bani ke? Kai mAsha Allah, Alhamdulillah.""" """ Wannan murnar haka."" Tace cikin mamaki" """ Ba zaki gane ba, ba zaki gane ba Zahraah, Nagode sosai, Allah ya sakawa da Abba da alkhairi. Nagode" "nagode, wannan ranar ta shiga cikin ranaku masu matukar muhimmanci a tare dani, Alhamdulillah.""" """ Allah ya tabbatar mana da alkhairi.""" """ Amin Zahra nah, Amin Amin. Bari kiga na tashi, banga ta zama ba a yau zanje na same su da maganar," "in sha Allah a kwana daya zuwa biyu magabatana zasu zo, ayi komai a gama, Allah yasa Abba ya saka mana lokacin kankani, bansan irin farin cikin da zan ba, Alhamdulillah.""" """ Uhum."" Tace dadi na kamata, a kalla ta samu wani da yake son ta sosai, irin soyayyar da ta rasa tun" tana yar kankanuwar ta. """ Zan kiraki anjima, ki kula da kanki.""" """ In Sha Allah. Ba-bye.""" Fadawa tayi saman gadon tana jin farin ciki matsananci """ Ya Allah ka sa ya zama alkhairi a rayuwa ta, Allah ka tabbatar mana da alkhairi.""" Ta furta tana jin kamar bata da saurin bakin ciki. "***Da karfin sa da kwarin guiwar sa ya isa masarautar su, wannan karon shigar da yasan Bubu yafi so" "yayi, shigar Manyan kaya da rawani, yayi masifar kyau ya fito a basaraken sa na ainihi, duk wanda yaci karo dasu sai sun kalle shi sun sake kallon sa, kai tsaye bangaren Aji ya nufa, domin wanchan karon be samu ganin Hajjan sa ba, shiyasa ya fara tachan dan tasan sai tayi korafi. Tana ganin shi kuwa ta hau murna, ta rasa in da zata sakashi, mace ce me jin mulki sosai domin mulkin a jinin ta yake dan har tafi Aji, amma kuma a duk abinda ya hada da muhammad bata hada shi da komai da kowa, da kanta take masa" komai duk abinda yake so kuma shi take so ko da kuwa kowa ba zai goyi bayan sa ba. Sai da ya gama mata shagwabar sa son ransa sannan ya gabatar mata maganar auren da yake so aje a "nemar masa, murna a wajen ta kamar ta dauke shi ta goye haka taji, karshe ta dinga tsokanar sa da sauran idan amaryar tazo ya manta da ita, da tsohuwar zuma dai ake magani. Da haka ya wuce fada in da yasan zai samu Bubu wanda tuni labari ya riga ya kai masa, ya shirya yana dakon karasowar Muhammad din. Ganin sa ya saka Bubun farin ciki, musamman da ya ganshi cikin shiga irin ta gidan" sarauta! "***Abba na zaune ya gama karatun alkur'ani me girma Maman ta shigo, ta zauna a gefen sa yayi kamar" be ganta ba """Dr wai fushin ne har yanzu? Be kamata ace abu irin wannan ya bata maka rai ba, yara hakuri ake dasu.""" Daga mata hannu yayi """Bana son maganar nan, idan har ba zaki iya tankwara yarki ba, kuma ba zaki nuna mata dai-dai ba," "shikenan, abinda kuke so kuka zaba zanyi muku.""" """Allah ya huci zuciyar ka, da anyi auren ma.in sha Allah zaka sauko, musamman idan kaga zaman nasu" "lafiya lou.""" """Allah ya taimaka."" Yace yana kokarin mikewa" """Dama magana nazo muyi, gida zanje.""" """Allah ya tsare hanya, ya kiyaya"" yace kawai cikjn halin ko in kula" """Kwana uku zuwa sati nake son yi.""" """Duk yadda kika ga yayi miki."" Ya karasa ficewa. Kwafa tayi ta mike tana jin haushin sa. Ko me zaiyi ba" "zata hana Zeenat abinda take so ba, an wuce zamanin auren dole. Zai gaji dan kansa ya sakko.[1/11, 9:34 PM] +234 803 765 3189: Halin Girma" 12 "*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107*" I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ft46u5twk6r3&utm_content=nj79azb "***Kai tsaye ya wuce zuwa chan gaban Bubun, fadawa na aika masa da kikari, kirarin da yake jin sa har" "cikin kansa, sai dai baya taba bari yayi tasiri a gareshi, hasalima yi yake tamkar be san me suke cewa ba. Dukawa yayi kamar yadda yake a al'adah ya gaida Bubun, ya amsa masa da ka ba tare da yace komai ba, a irin wannan zaman Bubun baya magana sai ta kama, sanin haka ne yasa Muhammad din ya koma daga bangaren dama ya zauna kafin sauran yan fadar su shiga kawo masa gaisuwa. Amsawa yayi duk a jimlace, ya hakimce a gefe yana sauraron zaman yake wakana. Kasancewar zaman na gab da tashi ne yazo, shiyasa yayi tunanin ba za'a wani ja lokaci ba, sai yaga an dauki lokaci ana maimaita abinda aka fad'a a baya, ya sani sarai hakan tsarin bubu ne, kila kafin ya iso ya shirya hakan saboda shi, murmushi yayi yana satar kallon Bubun da shi din ma shi yake kallo. A karon farko yaji tausayin mahaifin nasa ya kamashi, yadda yake kokarin ganin ya damka mulkin a hannun sa bayan shi kuma bashi da ra'ayin hakan, amma" "kuma be tursasa masa ba, ya cigaba da bin sa a hankali zuwa lokacin da yake ganin ya dace." "Be san ta yaya zai fahimtar dashi ba, amma yana da dalilin sa babba da ya saka shi tsayawa akan bakan" "sa, akwai babban kalubale a gabansa idan har ya amince da muradin Bubun , amma ta yaya zai iya gujewa hakan? Bayan babu wanda yasan dalilin sa?" "Yana jin sanda zaman ya kare, ya sauke ajiyar zuciya me nauyi ya daga idon sa sama yana kallon" "tsaruwar fad'ar, komai na ciki me tsada ne da kawa, haka duk wani abu da yake ciki me muhimmanci ne ga masarautar." "Tunanin Bashir ne ya fado masa, da ganin da yayi masa da fitsararriyar yarinyar nan, Bashir yana" "direbobin Masarautar Kano wanda ya sanshi sosai saboda kaudin sa da hayaniyar sa, kafin ya auri wata mata wadda ake kyautata zaton auren jari yayi, tun daga lokacin kuma ya bar masarautar sai jefi jefi yakan je ya gaida Fulani idan ta kama. Yayi mamakin ganin sa da zabgegiyar mota amma da ya bincika ya gane komai, sai yaji hakan yayi matukar yi masa dadi, yayi Kuma daidai da tsarin da yake son dora su" akai. "Dawowa yayi daga tunanin jin kamar an taba shi, ya kalli wanda ya taba shin sai ya fad'ad'a fara'ar" "fuskar sa," """Aji!""" """Tunanin me kake haka Muhammad?""" """ Babu komai, mun same ku lafiya?""" """ Lafiya lou, ya aikin? Amma kazo kenan ko? Zaka dade?""" """ In Sha Allah!""" """ Sannu da zuwa."" Yace yana mikewa" """ Zuwan ka dana ji ne ya sakani zuwa , Ina fatan idan ka huta zaka shigo, akwai batutuwan da nake so mu" "tattauna.""" """ Muje na taka maka, dama nima akwai maganar da nake so muyi.""" """ Toh toh madallah.""" """ Muhammad.""" Bubu ya kira sunan sa yana daga zaune """ Na'am Bubu!""" """ Naji dadin ganin ka da shiga irin wacce ta dace da kai, Ina fatan dorewar hakan.""" """ In Sha Allah Bubu, zan kokarta.""" """ Madallah da kai.""" """ Allah ya kara girma.""" "Tashi yayi suka fice tare da Aji, hannun su cikin na juna, Maimartaba ya jinjina kansa yana mamakin tarin" "kaunar da suke wa juna, har suka bacewa ganin sa sannan ya sauke ajiyar zuciya yana tafiya tunanin abubuwan da aka tattauna don cigaban al'umma. Sai dai yana fara tunanin, tunanin ta ya shigo ya katse masa duk hanzarin sa, ya rasa dalilin da ya saka a duk sanda ya tuna da maganar yake jin duk wata walwalar sa da farin cikin sa ya ragu, musamman a dan tsaikon nan, sai yake jin tamkar ana dakatar dashi da yin wani yunkuri. Shi din mutum ne me riko da addini matukar gaske, baya taba bawa maganganun da za'a zo a fad'a masa muhimmanci ko kad'an, sai dai a duk abinda ya shafi Muhammad baya wasa, yana ji a ransa kar fa abinda tsohuwar matar ta sanar masa ya zama gaskiya, tsoron hakan ya hanashi gabatar da komai cikin sauri yake bin komai a hankali, ba kuma wai dan ya gasgata maganar ta dari bisa dari ba, sai dan yana ji da tsoron sharrin masu sharri, be san me suke shirya wa dan nasa ba, sai dai be gaza ba, babu dare babu rana kullum cikin nema masa kariya yake a wajen ALLAH, ko ma menene" tabbas zai zo masa da sauki. "***A falon Ajin ya same shi yana zaune fuskar sa kamar gonar auduga, da kansa zai je amma sai Bubun" yace ya bari yazo kawai ya huta. Bayan ya zauna ne fadawan suka fice suka jawo musu kofar. """Na matsu na sanar da kai wannan albishir din, abinda muka dade muna jira ne, Muhammad dai yazo da" "magana, har yana neman aje ayi masa tambaya!""" "Fuskar Bubu ta fad'ad'a,farin ciki ya mamaye shi" """ Masha ALLAH! A kanon ne kamar yadda Takawa yace?""" """ Eh har binciken da mukayi, nan din ne in Sha Allah.""" """ Sai a sanar wa Takawa babu jira, in Sha Allah gobe duk abinda ya kamata ayi sai ayi, jibi sai aje musu da" "magana, da tsayayyiyar rana domin Takawa ya bukaci ayi komai a cikin kankanin lokaci.""" """ Madallah...Hakan yayi.""" "Tattaunawa suka shiga yi har dare yayi sosai,kafin ya koma bangaren sa cikin jin dadin labarin auren" Muhammad din. "***Jifa tayi da kofin hannun ta, ya fashe a wajen gaba daya kwalbar ta wawwatsu a dakin, wani irin" "bakin ciki take a duk lokacin da taji wani abu da ya danganci Muhammad din. Yau Itace a turakar Bubu amma tasan ba zata taba samun kansa ba, idan ma ta zafafa zai iya cewa ta bar masa dakin shiyasa ta yanke wa kanta hukuncin ko da yadawo daga wajen Aji ba zata je ba zatayi zaman ta tayi tunanin" menene mafita a gareta. """Ranki ya dade, Yarima Muhammad yana waje yana neman iso.""" """ Uban me zai min!!""" "Ta daka mata tsawa tana huci, sai kuma ta hau kokarin daidaita kanta" """ A shigo dashi babban falo gani nan.""" Da sauri baiwar ta fice tana mamakin uwar dakin nata. "Zaman sa yayi yana karewa falon kallo, an sabunta komai ba kamar zuwan sa na karshe ba. Murmushi ne" "a fuskar sa, yana da yakinin bata da bukatar ganin shi, ko da gilmawar sa ne balle har ya kai ga zama a falon nata, yana sane yazo domin ya kara tabbatar da abinda ya sani tun tuni." "A yadda ta fito, da yadda ta zauna kadai ya isheshi amsar abinda yazo nema, yana kallon yadda take" satar kallon sa cikin kallon da yasan na tsantsar tsana ne tun da ya riga da ya dade da sanin bata kaunar sa ko daidai da minti daya ne """ Barka da gida, mun sameku lafiya?""" Ya fad'a da yanayin da yasan zai sake tunzura ta. """ lafiya, ya aikin naku?""" """Babu dadi, na gudo ma na dawo gida cikin yan uwa!""" """Ka kyautawa kanka."" Tace a gajarce" "Mikewa yayi yana zuba hannayen sa cikin aljihun sa, ya yi mata kallon cikin ido tace" """Bari na koma.""" """Baka Sha ko ruwa ba."" Tace tana daga zaune" """Na yafe, bani da bukata.""" "Ya dage gira yana juyawa, da kallon bakin ciki tabi bayansa har ya fice daga falon, ta yarfe hannunta" tana jin kamar ta kamo shi ta tayi ta jibgar shi har sai taga ya daina motsi. """Ciwon Ido, zanyi maganin ka!"" Ta furta tana tashi ta koma ciki" "***Daga nan bangaren Ammin sa ya wuce, yana jin kansa kamar sabon ango, farin ciki yake ciki shiyasa" "ma be wani damu da abinda ya faru ba. Dama yasan kafin ya isa ta samu labarin ko ta wajne Hajja ko Bubu, aikuwa yana shiga ta tare shi da murnar ta, ya zauna ya tankwashe kafarsa a gabanta tana jin yadda take lissafo masa abubuwan da za'a bukata na zuwa gidan su Fatiman. A farkon farko be so wani abu na sarauta ya shigo ba, amma kuma da ya tabbatar hakan ba zai yiwu ba, shiyasa yayi amfani da damar nan wajen hadawa Mama gadar zare, dalilin tafiyar ta da shine ya assasa bayan ya kira Khalil a waya ya karanta masa yadda duk yake so ayi, babu musu ya amsa kuma ya tabbatar masa da zai yi komai daidai. Dazu Kuma ya kira shi ya tabbatar masa da Maman ta iso tun wayewar gari. Da wannan ya yi" gaba wajen aiwatar da saura shirin sa da ya tabbata zasu yi matukar girgiza kowa ba Maman kawai ba. "Har dare sosaii yana shashen Ammin, ta hada komai abubuwan da ya tabbata zasu dace da tsarin" "fatimar sa, shi din ma akwai tanadin da yayi mata amma ba yanzu ba, sai ranar da dubban mutane suka shaida, ya zama ita ta zama shi, a ranar zai nunawa duniya kalar gatan da take dashi a wajen sa." "Da sassarfa ya karasa part dinsa, Kai kace wani uban aiki yayi saboda yadda yake jin sa a gajiya." "Kwanciya kawai yayi bayan ya aika mata da cool night text message ya kashe wayar sai bacci, baccin da yake yi a duk lokacin da ya samu kansa a dakin sa na cikin gidan." "Zai iya cewa ya jima beyi bacci me dadin na ranar ba, ko dan abinda ya faru a ranar ne? Ko Kuma dai" "dan ance gida daban yake, dama bahaushe na cewa kowa ya bar gida... wanka ya soma yi, ya fito domin ya karya dan yasan komai na kammale a ajiye yana jiran sa. Zaman karyawa yayi, yayi dialing number dinta yana kallon plate din da ake zuba masa abinci, da hannu yayi masa alamar ya isa, ya karba ya soma ci jin bata daga ba, a yar mu'amular da yayi da ita, ya lura tana da bawa kowanne abu muhimmanci idan har shi ta saka a gaba, misali idan tana aiki takan ajiye wayar ta waje daban ta kammala aikin, haka idan tana wani muhimmi abun bata hada shi da komai har sai ta gama. Tunanin sa ne ya katse lokacin da kiranta ta ya shigo nasa. Murmushi yayi yana jan tissue ya goge bakin sa, yayi rejecting kiran sannan ya" bi bayan yana kishingid'a a jikin lallausan tumtum din dake kusa dashi. "Da sallamar ta, ta daga kamar ko wanne lokaci, ya amsa mata shima kafin ta dora da gaisuwa" """Ina kwana?""" """Lafiya lou, kin tashi lafiya?""" """Lafiya lou, yasu Ammi? Ka same su lafiya?""" """Kalou kowa, ya sister Maryam da jiki?""" """Gata ta samu sauki, inaga ma na tafi gida tunda naga ta warke sosai. """ """ A ah kiyi zaman ki! "" Yace da sauri" """ Me yasa? """ """ Amm kin gane, kinga tana bukatar ki, ki dan kara mata ko da kwana biyu ko uku ne, zata ji dadi. """ """ Owk tam. """ """ Yawwa. """ """ Ina kika shiga dazu na kira no answer, kitchen? Ko shara? """ """ Ya ka sani? Ina kitchen. """ """ Na sanki ai, nasan bakya wuce wuraren nan biyu. """ """ Lallai, kasan abubuwa da yawa akaina, amma ni bansan komai ba. """ """ Zaki sani, karki damu zaki sani fiye da sanin da kowa ma yayi min. ""." "Ya karashe maganar cikin sigar tsokana, bata ce komai ba, yasan kuma ba zata ce din ba, shima ba dan" tace wani abu yayi maganar ba """Zan zauna takanas, kiyi min duk tambayoyin da zaki yi min, zan amsa, amma kafin lokacin ina so ki san," "nifa soja ne!""" """Soja!"" Tace gabanta na faduwa sosai, bata son aikin soja ko miskala zarratin, bata kuma taba tunanin" "auren soja ba, dan tasan yadda suke very busy da aikin su" """Eh ni soja ne, amma fa irin kurtun nan.""" """Soja dai ai duk soja ne, sunan daya ne.""" """Amma rank din daban daban ba.""" """Uhummm. "" Ta ja ajiyar zuciya, ya sammace ta, kenan dai zaman kadaici be rabu da ita ba, dan sojoji" "basu da lokacin kansu balle na matan su, yanzu ita kenan..." """ Karki damu, ba zan dinga nisa ba kinji? Zan zama ko yaushe kika bukace ni Ina kusa, nayi miki alkawari.""" """Allah yasa, dan da gaske bana son aikin soja wallahi.""" """Saboda me? Aikin taimakawa kasa ne fa, aikin lada ne idan har ka yi yadda ya dace.""" """Na sani, ni kawai bana so ne, basu da time din kansu ballanta na ...""" """Na matan su? Haka ko yaushe aka cewa dama, toh ni dai Ina da time dina Ina kuma da na matata, har" "sai kin gaji kin koreni daga gidan ma wataran.""" """Shikenan.""" """Zaki gani ai, ki zuba ido.""" Shigowar Ya Maryam ya sakata yin shiru """Ki fito falo ya tafi wallahi, ni kadai kamar mayya."" Tace mata tana rik'e kofar, tun dazu tace tazo falo" "taki sboda maigidan yana nan, shiyasa Maryam din tazo kiranta da ya tafi, ko yar hira sa yi" """Kice ina gaishe ta, ya jikin nata.""" """Da sauki."" Tace tana janye wayar daga kunnenta." """Ashe waya kike shine kika yi luf, toh ki gaishe shi, in kin gama Ina jiran ki.""" Ta fita ta ja mata kofar """Bari na barki kuyi hirar ku, zan sake kira anjima.""" "Kamar ta tambaye shi maganar zuwa gidan amma ba zata taba iyawa ba, sallama tayi masa ta ajiye" wayar ta fita wajen Maryam. "Yana sane sarai yake ce mata komai, baya so tasan komai sai anyi komai ya kammala, ba zai ma gaya" "mata zuwan nasu ba, Abba kawai zai wa text ya sanar masa, idan yaso sai ya turo Musaddik ya sameshi ya sake fad'a masa Incase ko be ga message din ba. Haka kuwa akayi, yana masa text din ya gani, yayi saurin kiran kowa ya sanar dasu zuwan bakin, anan suka fara tunanin abinda ya kamata suyi, baki daga irin wannan babban gidan dole ne ayi abinda za'a fita kunya. Sun dade suna shawarwarin su kafin su" "tsaida matsaya, nan da nan suka shiga shirin tarbar su cikin tsarin da suka san ba zai zama wani iri ba." "Abba na zaune kiran Mama ya shigo wayar sa, shi kadai ne a gidan sai Habib ta tafi da Zeenat da Marwan," "shiru gidan babu kowa kallon tv yake a zahiri amma a badini tunanin masu zuwa neman auren Iman yake a gobe, yaso ya sanar wa mahaifiyar ta zuwan nasu da komai akan maganar sai dai baya samun ta a waya wajen kwana uku kenan, yasan tana business sosai kamar ma tana fita kasashe saro kayayyaki" shiyasa yayi tunanin ko kila bata k'asar ne. "Kallon wayar tasa yayi, har lokacin haushin Maman yake ji musamman abubuwan da ya gano akan irin" "rikon da tayiwa Fatiman tsawon lokaci be gane komai ba, har Marwan ya titse ya tambaya ya kuma gaya masa komai abinda ya sake daga masa hankali sosai kenan. Kiran ne ya sake shigowa ya daga ba dan yaso ba, dan dai kawai be san ko wani abu bane emergency ya taso, sallama tayi ya amsa ciki ciki. Dama" tasan za'a rina shiyasa kawai ta tafi kai tsaye akan dalilin kiran """Dama Zeenat ce ta ce na sanar da kai iyayen Bashir zasu zo gobe idan Allah ya kaimu.""" """Su bari jibi gobe Yaya yana da abinda zai yi.""" Yace mata kai tsaye """Amma da ka barsu sunzo goben ba dole sai wajen Yayan ba ai.""" """Haka tsarin mu yake tun farko, babu Kuma dalilin da zai saka na chanja yanzu dan anzo auren nawa" "yayan, idan har ba zasu iya bari sai jibin ba sai ki nema musu wanda zasu gani a goben.""" """Abin be kai haka ba ai, Allah ya kaimu jibin.""" """Amin.""" "Yace ya katse kiran yana Jan tsaki, wato duk dadewar ka da mace ba zaka taba sanin wasu daga cikin" "halayen ta ba har sai abu ya faru, lallai. Shi kadai yake ta wannan tunanin har lokacin da zai kwanta yayi, ya kwanta da addu'ar Allah yasa komai ya tafi dai-dai goben." "***Duk cikin su babu wanda ya makara, suka tashi aka hau gaggayara gidan harabar da lungu da sako su" "Habib suka taimaka aka tsaftace ko ina, dama dai a gyara yake saboda takanas aka dauki me aikin kula da wajen amma duk da haka idan suka tuna bakin da zasu zo sai suga ya kamata a sake gyara ko ina." "Wajajen sha biyu cikin jagorancin Musaddik suka iso, cikin manya manyan motocin alfarma da aka" rubuta Emir Kano 1 guda biyu sai guda biyu dauke da tambarin Adamawa Palace. "Cikin kankanin lokaci unguwa ta dauka, mutane suka dinga lekowa daga gidajen su dan tabbatar da" "abinda yaran su suka je suka fad'a musu, kowa ya leko sai ya rik'e baki cikin tunanin abinda ya kawo irin mutanen gidan." "Cikin matuakr girmamawa Abba suka karbe su, sai dai sunyi tunanin zasu gansu a matsayin mutanne" "da basu kai ba ko kuma level dinsu ba daya ba, amma sai suka ga akasin haka, cikin girmamawa, karamcin da dattako suka zo musu, suka nuna Halin Girma, halin babban gida babu fariya ko nuna su din wasu ne, cikin tattautasa harshe da girmamawa suka nemarwa dan su kuma jikansu Muhammad auren Fatima. A take Abba yace an bashi. Su kuma nan take suka gabatar da ranar da suke so a saka, babu musu nan ma Abba ya amince suka tsaida wata daya kachal, shi din ma saboda Muhammad din ne ya" "bukaci haka, amma idan sune toh sati biyu zasu saka." "Babu wani bata lokaci abinka da manyan mutane, masu Halin Girma, suka yi komai cikin sauki sannan" "da zasu tafi suka gabatar da kyaututtuka daga iyaye da kakannin Muhammad din da yake cikin al'adarsu idan za'a zo neman auren. Tarin kayan da suka kasance mota guda sai da suka bawa su Abba mamaki, a gefen Abba aka ajiye mukullin motar nufin su har da motar da duk abinda yake ciki kyauta ce ga sirikar" "Sarki Ahmad Santuraki, da iyalan gidan sa kafin zuwan ta, sannan suka yi musu sallama suka tafi." #HafsatRano #ZafafaBiyar2021 Not edited Ignore typos "Masu sharing sannun ku da kokari kunji? Allah ya shirye ku idan masu shiryuwa ne, idan kuma ba masu" shiryuwa bane toh... Kun san sauran dai "[1/13, 4:25 AM] +234 803 765 3189: Halin Girma" 13 "*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107*" I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ft46u5twk6r3&utm_content=nj79azb "***Sai da suka ga tafiyar su sannan suka dawo ciki, kowa da abinda yake cin sa a zuciya. Tabbas sun" "amsa sunan babban gida, haka sun nuna Halin Girma da dattako na irin manyan mutane da suka san mutunci da yakana." "Fadar irin tarin kayan da suka zo dashi ba abu bane me sauki, hakan ya dan tarsa tsoro a zuciyar Abba," "yake jin tamkar siyar da Iman din zai yi, wannan uban dukiya a matsayin tambaya, ina ga idan aka zo auren? Basu da talaucin da arziki zai tsorata su, sai dai dole ne suyi mamaki ganin uban dukiyar da aka lafto da sunan na Iman din ne, tun daga kan sutura zuwa kayan kawa na mata, da kyautata gwala-gwalai" tamkar ba'a san darajar su ba. Haduwa suka yi suka tattauna yadda zasu adana komai saboda yadda rayuwar yanzu ta zama ta rashin "tssro, shawarar farko shine su bar maganar tsakanin su domin mata akwai sakin baki musamamn idan abun da ya sha musu tunani ne, yanzu zasu yi ta kwazozotan sa har wasu dake waje su samu damar" aiwatar da mummunan kuduri akan su. Tabbas shawarar tayi dan da gaske komai na iya faruwa idan maganar ta fantsama shiyasa kawai a take aka fita da motar da duk abinda yake ciki daga gidan zuwa in da zai fi zama safe kafin bikin yazo kusa "sosai sai ayi abinda ya dace dasu, ko bata kayanta ta tafi dasu tunda dama su chan babu wani tsoron" "rashin tsaro ta ko ina zagaye suke da Jami'an tsaro. Karshen magana kuma ma shi Muhammad din kansa, su ne tsaron ma baki daya. Da wannan shawarar suka tashi bayan Abba ya sanar musu da zuwan iyayen" Bashir a gobe kamar yadda Mama ta shaida masa. "Sake gwada kiran Maman Iman din yayi bayan ya koma gida, cikin sa'a kuwa kiran ya shiga, bata wani" "jima tana ringing ba ta dauka a nutse cikin sallamar ta da muryar da yake jin ta kullum a bakin Iman din, maganar da sak ta mahaifiyar ta, hatta nutsuwar ta irin ta uwarta ce shiyasa yake jin ba zai iya mantawa da ita ba ko da shekaru sun ja, duk da yanzu babu batun soyayya a tsakanin su tun da be riga yasan matsayar da take a yanzun ba ko da aure ko babu, a dai kwanakin baya ya samu labarin tayi aure har da" albarka Yaya a tsakanin su. """Ina wuni Abban Iman?"" Ta gaishe shi jin yayi shiru bayan amsa sallamar ta" """Lafiya Lou Maimunatu, ya gida ya kowa da kowa?""" """Kowa lafiya Alhamdulillah, Iman fa?""" """Tana nan lafiya.""" "Shiru sukayi baki daya, kowa da kalar tunanin sa a ransa, shine ya katse shirun ta hanyar cewa" """ Inaso zan kawo miki ita kamar yadda nayi miki alkawari idan auren ta ya tashi, ta samu miji har an" "tsaida rana wata daya, in sha Allah a tsawon wata dayan nan zata zauna a wajenki, a matsayin ki na mahaifiyar ta sai kiyi duk abinda ya dace, kiyi hakuri da Kaddara, kiyi hakuri!""" "Wani irin yar taji har cikin kanta, Iman dinta har ta girman da zata yi aure, rayuwa na gudu sosai, tana" "tuna lokacin da ta dawo masa da ita, da irin tashin hankalin da ta shiga a rashin ta wanda bata taba tunanin zata dawo daidai ta cigaba da rayuwa ba, a lokacin tunani take rayuwarta ta kare gaba daya, amma kuma sai gashi ta cigaba da rayuwa duk da babu ranar da zata fito ta fadi bata tuna yar tata ba," amma ya zatayi? Mutane na fifita al'ada akan addini. Ta sani sarai uwa ce taka da ikon rik'e yarta har "zuwa aurenta, tare da sharadin kula da duk wata bukatar ta daga mahaifin ta, sai dai idan anji tsoron" "tarbiyyar da zata samu a wajen uwar, toh amma a lokacin wa take dashi da zai tsaya mata? Bayan iyayenta da take ganin su a matsayin gatan ta sun kekashe kasa sun ki amincewar da rikon nata a wajenta? A lokacin da akwai karancin shekaru a tare da ita, amma da ace yanzu ne, babu me raba ta da yarta kuwa, duk yadda zatayi zatayi ta tabbatar da ta rik'e ta a wajen ta. Ta bata kulawa da dukkan gatan" da take bukata. """Allah ya sanya alkhairi, ya nuna mana lokacin.""" "Kawai tace dan bata kuma san me zata ce masa ba, taji dadi da ma ya cika alkawarin sa, zatayi kokari a" "dan zaman nan ta koya wa yarta kaunar ta da sabawa da ita da yan uwanta, sannan ta nusar da ita rayuwa da yadda zata kula da auren ta. Sallama sukayi da alkawarin ana gobe zai kawo ta, zai kira ya sanar mata. Godiya tayi masa dan har gobe tana ganin kima da mutuncin sa, mutum ne shi na gari, me" kirki da son iyalin sa. "Bayan gama wayar da sukayi ne zuciyar sa ta gwada masa kiran Zeenat ya sake gwada tankwarata, idan" "Allah ya taimake shi ta hakura sai yafi kowa murna, dan yanzu bashi da babban tashin hankali kamar auren zeenatun da yake da yakinin zai iya zamar mata wani Babban tashin hankali a gaba." "Kiran nata yayi, tana dagawa yace ta matsa daga wajen kowa zai yi magana da ita, da ido ta kalli Mama" dake zaune ana maida maganar auren Zeenat din da Hajiya ta fice zuwa tsakar gidan. """Abba na fito.""" """Yawwa zeenatu, magana nake so muyi a matsayi na, na mahaifin ki, kin san dai ba zan taba zabar miki" "abinda zai cutar dake ba, ba kuma zan ga cigaba a gareki na dakushe ki ba, ina neman alfarma, kiyi hakuri da Bashir ki kawo wani ba shi ba,nayi miki alkawarin tsaya miki kinji?""" "Gabanta ne ya fadi, a tunanin ta an gama wannan babin, sai gashi Abban ya dawo da shi yana kuma" kokarin daure ta da jijiyoyin jikinta. """ Kina jina zeenatu?"" Ya sake fad'a cikin yanayi me wahalar fassarawa" "Shashekar kuka yaji, ta fashe da kuka cikin muryar kukan tace" """ Dan Allah Abba kayi hakuri?""" """Ai ba laifi kikayi min ba Zeenatu, alfarma kawai nake nema a matsayi na, na mahaifin ki.""" """Abba dan Allah kayi hakuri, wallahi ba zan iya hakura da Bashir ba.""" "Kamar saukar aradu haka Abba yaji, ya dafe kansa ya shiga karanto innalillah wa inna ilaihi rajiun, babu" "babbar jarrabawa irin yayanka suyi rashin sa'ar miji, duk abinda yaje ya dawo dole kana ciki, kamar ka saida akuyar ka ne tazo tana ci maka danga, baya fatan hakan ta faru ga ita, shiyasa tun farko ya hakurkurtar da zuciyar sa be ga laifin ta ba sai na Mama, amma yanzu ya tabbata abinda Zeenat din take" "so shi Maman take goyan ba, dama mafiya yawan lokuta uwa na tafiya ne da ra'ayin yarta." """Shikenan zeenatu, duk abinda yaje ya dawo karki kuka da kowa, ki kuka da kanki.""" """Abba dan..."" Kafin ta kai karshe ya katse kiran, Jan kafarta tayi ta koma ciki tana jin a ranta tayi abinda" "ya dace, a kalla ta yi kokarin kare soyayyar ta ko ba komai idan akayi auren Abban zai hakura ya sakko." """Lafiya?"" Mama tace tana kallon ta." """Ya kukayi da Baban naki? Maganar dai ce ko?""" "Da kai ta amsa mata da eh, tsaki Maman taja" """Shine kike kuka ko me? Ni wai Zeenat asiri Bashir yayi miki ne? Da bakya ganin kowa da komai sai shi?""" Kanwar Maman Atika ta fad'a cikin bacin rai """ Ni banga wani abun naci a Bashir din nan ba, tunda mahaifin yarinyar nan baya so toh a hakura mana?" "Iyaye maza sun fi mu tunani da hangen nesa.""" """Toh Atika ya za'a yi? Shi ma fa duk zuga ce wallahi, ai da be san da hakan ba sai bayan yaga mijin da yar" "lelen tasa ta samu, shikenan kuma sai kananan maganganu bansan daga ina ba, amma ina kyautata zaton daga wajen Gaji ne, dan ita kadai ce take sauya musu tunani da raayi dukkan su, ita kuma na" "tabbata munafurcin Iman ne dan ko yaushe tana wajen ta.""" """Duk wannan ta tunani ne Yaya Hajara, bamu da tabbas din hakan, kinga dai yadda Dr ya dage ya kamata" "ace kin bashi dama kinji ta bakin sa akai.""" """Kyale shi kawai, zai sakko ne.""" """Me yace miki?"" Ta tambayi Zeenat din tamkar abin be dameta ba." """Cewa yayi nayi masa alfarma na hakura da Bashir.""" """Ehen kinji? Har ya saukar da kansa a matsayin sa na mahaifi yace yana neman alfarma kema Yaya" "Hajara kinsan da matsala.""" """ Me kika ce masa ke kuma?"" Taki amsa atikar ta tambayi Zeenat din." """ Hakuri na bashi."" Tace tana rakubewa a gefen Hajiya da tunda aka fara maganar bata saka musu baki" ba sai lokacin """ Gaskiya da kun hakura kun bi zabin Ibrahim, a kalla shi namiji ne yafi mu dukka tunani da hangen" "nesa.""" """ Hajiya toh ya za'a yi? Lokaci ya riga ya wuce bata kula kowa sai shi, yaushe zata fara daga farko kafin" "ma ta samu saurayin su fuskanci juna a zo maganar aure.""" """ Duk wannan me sauki ne akan ka dauki dan ka, ka kaishi inda zai Sha wahala.""" """ It's better to marry late than to marry wrong."" Atika tace tana girgiza kafarta" """ Khair in sha Allah, babu abinda zai faru.""" "Maman tace a kasan zuciyar ta tana jin tsoron abinda zai je ya dawo, ita kanta ta fara tsoron yadda" "Abban ya kafe ta tabbata akwai babban dalili, amma kuma ta Ina Zeenat din zata fara? Hasalima bata da farin jinin samarin duk asalin su Iman suke so sai ita maman tayi amfani da wannan a juya mata kansu zuwa Zeenat din dan ba zata iya gani Iman din tayi aure musamman auren babban gida ita kuma Zeenat" din na zaune a gida. "***Da sauri ya karasa part dinsa yana jin kayan na masa nauyi sosai, yau tun safe Bubu ya Aiko masa da" "kaya sannan ya bukaci ganin sa a kofar part dinsa dan shiga tawagar sa zuwa Fada, haka ya tashi ya shirya ba dan yaso ba ya fita. Tun lokacin sai yanzu ya samu dawowa part din sa, yana shiga ya hau cire kayan yayi wurgi da rawanin yana jin shi sakayau. Allah Allah yake ya samu feedbacks din aikin da ya saka Musaddik sai gashi kuwa ya kirashi adaidai lokacin, dagawa yayi yana rage daga shi sai singlet da" boxer kasancewar zafi ya fara hurawa kadan kadan ba kamar kwanakin baya da ake sanyi sosai ba. """Gani fa ga mutumin ka."" Musaddik yace yana dagawa" """Da gaske? Sharp sharp haka? Ok bari na kiraka Video Call.""" "Ya katse sannan ya kira video call, a daidai saitin fuskar Bashir Musaddik ya saka wayar yadda yana" "dagawa Moh zai fara ganin sa. Yana durkushe tamkar me neman gafara, wata dariya ce ta zowa Moh, yayi murmushi kawai yace" """Oga Bashir barka da warhaka.""" """Dan girman Allah ranka ya dade kayi hakuri, wallahi bansan gidan da kaje Neman aure bane nima naje," "wallahi kuskure ne kawai amma kayi hakuri.""" """Ai ba laifi kayi ba Bash, ni hakan yayi min dadi sosai, kuma ina tayaka murna, kaga ni da kai mun zama" "yan uwa tunda zamu auri yan uwa.""" """Tuba nake ranka ya dade!"" Yace yana kasa da kansa" """Dago kanka bash, bafa wani laifi kayi ba, aiki nake so na baka, bana son kuskure ko kadan a ciki, idan" "har kayi min yadda ya dace akwai babban tukuiwaci.""" """Hakan shi yafi komai sauki a wajena ranka ya dade, fadi ko menene .""" """Yaushe za'a je tambyar maka auren?""" """Gobe ne ranka ya dade, amma idan kace a fasa na fasa wallahi.""" Girgiza kai yayi """ Ba za'a fasa ba, Ina so idan sun je su nemi a saka musu wata daya!""" """ Wata daya!"" Ya zaro ido" """ Wata biyar nace ko shekara, ban shirya ba wallahi,dan dai bana son na rasata ne.""" """ Ba zaka taba rasata ba, ni zan maka komai na auren tun daga lefe har gidan zama zan baka, ni dai" "kawai kayi duk abinda nace kayi.""" Dukawa yayi jiki na rawa """ Nagode nagode Allah ya kara girma, zanyi duk abinda kace, ba zan yi komai ba sai da sanin ka.""" """ Good, yanzu aikin me kake?""" """ Buga buga kawai, sai kuma aiken Hajjaju idan ya tashi.""" "Dariya sosai Moh yayi, ya hangi tsantsar mutuwar zuciya da son zuciyar a tattare da Bashir din, mikar da" "yan yatsun sa yayi baya, ya dawo dasu gaba suka bada sauti kafin ya katse dariyar yana zama so serious." """ Abinda nake so kayi min, zaka ji daga bakin Musaddik, bana son kuskure ko kadan, komai Ina so ya tafi" "cikin tsari , Ina so gobe ka dauki hanyar Katsina, zan aiko maka da sako ka kaiwa Gimbiya Zeenatu, hakan zai sake goge shakku ko wani tunani akanka.""" """ Nagode ranka ya dade, nagode nagode.""" """ Karka damu, kai dai kayi abinda nace, bana son kuskure ko kadan!""" """ Da yardar Allah zaka same ni da bin duk umarnin ka. """ Daga masa kai Moh yayi sannan yace """ Guy!""" """ Yeah Captain!"" Musaddik yace yana matsawa daga wajen da Bashir din yake" """Ka kula dashi sosai dan dan iskan kansa ne, duk da be isa ba, amma dai bana so a samu matsala har" "zuwa ranar daurin auren, watch him and report anything da be maka ba.""" """Karka damu, babu ma abinda zai faru. """ """ Yau nayi zaman fad'a, kamar nayi kuka wallahi, wannan yazo ya fadi yayi gaisuwa, wanna yazo ya ce" "makwafcin sa kaza, wannan suzo maganar aure, wannan ta kawo karar mijinta wannan ya kawo karar matar sa, maganar gado, kai abubuwan da mugun yawa, kamar na gudo nake ji, nasan iya zaman da zan" "Bubu ba zai raga min ba wallahi, har na fara ramewa. """ """ Haka zaka hakura kayi abinda yake so, iyaye dole a bisu ayi musu yadda suke so. """ """ Haka ne dama, shiyasa na matsu nayi auren nan nima na zama me yancin kaina, kasan aure fa yanci" "yake siyo ma da martaba ba komai Bubu zai dinga matsa min ba da zarar yaga nima na zama dan gari a harkar. """ """ A harkar me? """ """ Harkar auren mana, ina fita daga novice zai yanta ni, kwana kad'an kaji nima ana Daddy, Daddy! Wayyo" "I can't wait. """ """ Kaifa yanzu baka da magana sai ta aure ko? Wannan sanyin ne ba komai ba. """ """ Sanyi ai ya wuce kuma, ba zan kara yarda na sake wani sanyin a gauro ba wallahi, haba Malam ai an ji" "jiki kawai. """ """ Dan air. "" Musaddik yace yana dariya" """ Yan air dai, Wa ma ya kaika ne? Gwara ni wallahi kowa yasan uztaz. """ """ Nima haka ai. """ """ Fadawa wanda be sani ba toh. """ """ Toh ai idan har Moh uztaz ne toh tabbas ni sai da shehin malami, kai din? Ina dai tausayin yar mutane" "da zata shigo hannun tuzuru irin ka wallahi. """ """ Naji karka bata min tunani, jeka zan neme ka anjima bacci zan.""" """ Hahaha, shikenan sai na jiki, angon Fatiti. """ """ Musaddik.!!! "" Ya furta da karfi" """ Sorry sir, angon Fatima. """ """ Zaka shigo hannu ne wallahi, sai na saka an samin kai frog jump. """ """ Idan wannan ne ai na gaji da yi, a chanja wani punishment din dai Captain. """ "Kashe kiran Moh yayi, yasan ya biye Musaddik sai su cinye lokacin suna abu daya, wurgi yayi da wayar" gefe ya kwanta dan rama baccin da Bubu ya katse masa Halin Girma 15 _*Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._* *_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK * https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share *_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK * https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb *_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK _* https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content =share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1D xoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2F xLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS *_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK _* https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw •••••••••• "Kasa fitowa tayi, tana taraddadin yadda zasu karbe ta, ji tayi an bud'e kofar bangarenta, taji muryoyinsu" a lokaci daya suna mata sannu da zuwa """Yau ga Fatima,sannu da zuwa dota, sannu da zuwa.""" Wata farar mata da a kalla zatayi sa'ar Mama ta fad'a tana riko hannun ta. Da wani irin yanayi take "kallonsu su dukka, kowannen su kokari yake ya nuna mata kansa, mutum daya dage gefe tsaye ta harde hannayen ta a kirjin ta ta daga kai ta kalla, tun isowar su wajen ita kadai ce bata yi magana ba. Wani irin shock taji ta furta Mommy a tsakanin lips dinta, gyada mata kai matar tayi da sauri ta isa gareta ta rungume ta tana sakin kuka, bata chanja ba ko kad'an daga yadda take a hoton ta da take dashi tun na zamanin yan matantaka, duk da ganin ta da ita a zahiri kadan ne amma ko yaushe zuciyar ta na manne" da hoton mahaifiyar ta. "Tafi sukaji an saka daga bayan su, duk Kuma sai suka saka dariya har Iman din da kunya ta kamata ta" sake shigewa jikin mahaifiyar ta tana jin wani irin son ta da kaunar ta. """Muje ciki ko?"" Babban namijin ya fad'a yana nuna musu hanya da hannun sa. Sakin Mom din tayi, matar" farkon nan ta kama hannun ta zuwa ciki hanyar da ta ga sun fito dazun. "A falo suka yada zango, kowa a cikin su kokari yake yaga ya nuna mata soyyayyar sa, da kallo kawai" "take binsu cikin mamakin dalilin da ya saka basa neman ta tsawon lokaci haka duk kuwa da soyayyar ta da ta hanga a tattare da family din. Tana da bukatar amsa saboda tasan yadda kowacce uwa take kulafucin danta musamman ita da aka dauke ta da karancin shekarun ta, tabbas a farko farko ta kan zo ta ganta tare da wani babban namiji duk kuwa da karancin shekaru basa barin ta tuna komai amma" tabbas ta san anyi haka kuma Abba da kansa ya kara sanar da ita a wani lokaci da ta tambaye shi. "Kamar an jeho su suka shigo su biyu, suka yo kanta da gudu macen ta rungume ta tana sakin ihu," namijin kuma ya durkusa a kusa da su yana dariyar farin ciki """Welcome sister!"" Yace bayan macen ta saketa ta zauna tana maida numfashi" """Welcome sis!""" Tayi saurin fad'a itama tana hararar sa """Sannun ku.""" "Tace tana murmushi tana mamakin su," """na riga shi ganin ki, na rigashi yi miki magana dan Allah ni kadai zaki so kinji? Dama kullum ina jin" "haushin bani da big sister sai wannan coconut head din , sai gashi na samu yanzu, I'm so happy wallahi, da k'yar na bari aka gama islamiyya yau wallahi.""" """Amaani kin cika surutu wallahi, ai sai ki barta ta huta ko?""" """ Tell her Mamma, wallahi kamar na bugeta yau din nan ta bani haushi.""" """ Kaifa ya sunan ka?"" Ta tambaye shi" """ Amaan."" Amani tayi charaf ta rigashi fad'a sannan ta dora" """Nice hassana, shine husaini, na girme shi so nice babba.""" "Murmushi Iman tayi, so adorable yaran," """Oya ku wuce kowa ya cire uniform dinsa kuzo muyi dinner, nasan Iman ta gama gajiya tana so ta huta""" Mamma tace tana mikewa """ Zayd, Ya Mubarak dinner na table.""" """ Ni sai nace gida gaskiya, I'm full.""" "Ya Mubarak yace yana gyara zama sosai. Kama hannun Iman Mamma tayi, suka wuce dining din tare da" "Zayd yana mata tambayoyi. Mommy na jinsu bata saka baki ba, dama kuma ita haka take da kara sosai, komai nasu Itace akai amma bata taba nuna musu iyaka akan nata, shiyasa suma duk wani abu da ya shafe ta toh sune a gaba gaba, sai ta koma gefe ta zama yar kallo. Bata da hayaniya kamar dai Iman koman ta a nutse takeyi musamman kuma abun da ya hadu da arziki sannan ga ilimi both boko da islamiyya. Kujera taja gefen Iman din da suka bar mata ta zauna daidai lokacin Amaan da Amaani suka dawo kowa ya sauya kayan sa zuwa na zaman gida. Amaani na kokarin fara surutun ta suka hada ido da" "Mommy, kallon da tayi mata kadai yasa taja bakin ta tayi shiru har suka gama babu wanda yayi magana." "Falon suka dawo, a lokacin Ya Mubarak da Zayd suka yi musu sallama akan zasu dawo gobe kowa da" "family dinsa, har bakin mota Mommy ta rakasu ta dawo sai kawai ta wuce dakin ta, ta bar Mamma da yaran suna hira, ta lura da yadda Iman din ke jin kunya da rashin sabo amma kuma tasan wace Mamma ba zata taba barin ta ba har sai ta tabbata ta sake dasu, balle uwa uba iyayen magana su Amaani su" kadai ma sun isheta. "Kwanciya Mommy tayi farin cikin zuwan yarta na ratsa ta, wayar ta ta dauka ta kira number Abba," "lokacin ya gama cin abinci kenan yana kokarin duba wasu papers dinsa a computer yaga kiran nata, tsaywa yayi da abinda yake yi ya daga." """Nagode sosai IB, naga Iman fiye da yadda nayi tunanin ganin ta, hankali na ya kwanta dan na tabbatar" "da tarbiyyar ta, kayi ma maman tasu godiya dan Allah. """ """ 'yaya amana ce a garemu da dole mu kula dasu da tarbiyyar su, domin dole ne Allah ya tambaye mu a" "ranar gobe kiyama, banyi komai ba face abinda ya zama wajibi na.""" Ya fad'a yana jin chan kasa zuciyar sa da zata samu labarin abinda ya faru a zaman Iman din da Maman "daku tabbas za'a iya samun matsala, abu daya ya hanata yin wani katabus akan maganar Iman din, tabbatar mata da yayi akan bata da matsalar komai, kuma tana hannu na gari." "Sallama sukayi ta runtse idon ta, hasashen irin shirye shiryen bikin da zatayi kawai take, ba zata bari ta" koma ba har sai tayi mata nata kalar gatan da zata tabbatar da ita din yar gata ce. "Turo kofar akayi, ta daga kai ta kalli Iman din cikin rakiyar Mamma." """ Sai ki gudo ki bar mu? Gamu toh mun biyo ki.""" """ Na zata wajen Hajiya kuka yi ai.""" """ Munje chan din ma.""" """ Ok."" Tace tana mikewa zaune." """ Bari na duba yaran chan, ina ga daga haka zan kwanta, sai da safe Iman.""" Murmushi Iman tayi ta amsa sannan mummy tace """Sai da safe Yaya.""" Fita tayi ta ja musu kofa cike da farin cikin kwanan da ya da uwar zasuyi yau. """Dawo kusa dani.""" "Dawowa tayi ta zauna daf da Mummy din, ta jawota ta dora kanta a saman cinyar ta, cikin tattausan" lafazi tace """Kin girma sosai Iman, nayi mamakin yadda kika kara chanjawa akan last da Dr. Ya tura min hoton ki," "amma kuma naga baki da walwala sosai, ko rashin sabo ne? Ko kuma hakan halitta ne?""" "Murmushi tayi me sauti, nutsuwa ta saukar mata, taji da gaske she's safe fiye da yadda ta taba ji a" "rayuwa ta, a hankali ta furta" """Babu komai Mummy.""" """Shikenan, ki kwanta idan kika huta duk maganar da zamuyi sai muyi kinji?""" Ta shafa kanta tana murmushin. Daga kan ta tayi ta ajiye a saman gadon ta fita daga dakin. Wajen kayan "ta, ta nufa ta ciro wayar ta, tasan ya mata magana a WhatsApp bata samu sukunin dubawa ba. Misscalls ta gani ta whatspp call sai messages dinsa da ya turo mata. Sakon ta fara dubawa ta,tabi kowanne tayi reply ta bar daya da yake tambayar ta size din undies dinta kunya na kamata. Godiyar kudin da ya bata tayi masa hade da addu'a tana turawa sai gashi yazo online, maimakon ya amsa sai taga yana kiranta," kasa dagawa tayi kunyar tambayar da yayi mata na dawo mata "_"" Baby menene size din B da P?""_" "Haka ya rubuto mata fa, kin dagawa tayi har ta katse ya sake kira ta kara bari ta katse," "_"" Please dan Allah ki daga, kwana nawa banji muryarki ba? Sam na manta zan iya kiran ki ta whatspp" "call sai daxu, please ki taimaka ki daga inaso naji muryar ki wallahi.""_" "_"" Ni dai muyi chatting.""_" "_"" Ni dai ki daga, zan sake kira. ""_" "Kafin tayi reply sai ga kiran sa, ta daga da k'yar tanayin nesa da wayar. Ajiyar zuciya ya sauke da karfi" """ Kin iya rigima wallahi, haka kawai sai anyi punishing dina ko? """ """ Um um. """ """Toh naji, ya hanya? Ya me ya faru?""" Cikin zumudi tace """ Ina cikin farin ciki yau, komai ya tafi yadda ya kamata, kowa so na yake kamar zai goya ni. """ """Mum fa? """ """ She's just like me, kamar ni take har I don't care attitude dinta, amma deep down she's super happy," "na gani a idon ta. """ Dariya ya saka """ Alhamdulillah, nayi miki murna sosai sosai, Alhamdulillah. """ """ Nagode sosai. """ """ Yau kwana zakuyi nasan da Mum kuna magana. """ """ Anya? Kila ko sai an kwana biyu. """ """ Bari ki gani dai. """ """ Uhum tohm shikenan. """ """ Baki min replying dayan chat din ba, abinda na tambaye ki. """ "Dauke wuta tayi gaba daya kamar bata ji ba, ya sake maimaitawa yana rik'e dariyar sa, ya gano kunya taji" "tunda taki daga wayar sa, bata san halin sa ba lallai, rage murya yayi sosai yace" """ Dan Allah ki fad'a min Aunty zata yi min fad'a gobe idan nace ban tambaye ki ba, dan Allah. "" Shiru tayi" masa """ Please ki fad'a min, ko da yake ma zan iya chanka ai, bari muga... zasu kai size...""" """ Innalillahi. "" Tace tana zare wayar gaba daya ta kashe ta. Tuntsurewa yayi da dariya kamar zai fado" "daga gado, yayi saurin komawa chat din ya hau rubuta mata" """Sorry matar Muhammad, daga wasa sai ki yanke min waya? Toh ai ban gama jin muryar ki ba wallahi.""" "Tick daya ya gani alamar ta ma kashe datan gaba daya, gwada kiran ta yayi aikuwa yaji switch off." "Tsaki taja ta wurgar da wayar , ta rasa me yasa me maxa sam basu da ta ido, zata dade kuwa bata yi" waya dashi ba. Samun kanta tayi da yin murmushi sai kuma ta hade fuska ta sake jan tsaki. Ya ma bata haushi gaba daya. "Har ta gama shiryawa ta jona wayar a charge amma bata kunna ba har lokacin Mum din bata shigo ba," "gefen gadon ta kwanta cikin lallausan zanin gadon da yake kamshi sak irin kamshin da mummy din take, tana rufe idon ta, ta shigo rik'e da cup a hannun ta." """ Iman, kinyi bacci?""" """ A ah."" Tace tana mikewa zaune" """ Yawwa ungo karbi kisha, fresh milk ce nayi miki warming dinta.""" "Karba tayi, tayi godiya ta kafa kai ta shanye tas, ta tashi da cup din rik'e a hannun ta" """ Ajiye shi anan zan kira azo a fita dashi.""" A saman fridge din jikin kofar ta ajiye ta dawo ta zauna tana so abinda tasha ya dan yi settling a cikin ta. """Zo ki tayani duba wannan kayan.""" "Tayi maganar tana bud'e profile dinsu a cikin system din, gefenta Iman ta zauna suka hau duba wasu" "jewelries, duk wanda Iman din tace yayi kyau sai tayi starring dinsu, sai da suka gama tsaf sannan suka dawo kan wanda akayi starring din suka sake fidda guda biyar masu kyau sosai, biyu gold biyu azurfa sai daya fashion ne daga wani babban company, a take mummy tayi payment din da komai sannan tace" Iman din taje ta kwanta zata karasa wani aiki. Tana kwanciya bacci ya dauke ta dama ta gama kurewa sosai tana lura da Mummy din bata so ta "matsa daga kusa da ita ne. Cikin bacci tayi juyi ta jita a bayan ta, daga nan bata sake farkawa ba sai da aka kira sallah." "***Gaba yayo ya bar su a chan su karasa siyayyar abinda zasu siya dan yaga abin nasu bana kare bane, a" "Kano ya dira domin su karasa abinda zasu karasa da Bashir saboda yadda lokacin yazo sosai. A gidan sa ya same shi, suka jira Musaddik ya karaso suka fita zuwa wata unguwa da tafi kama da a kirata da unguwar talakawa kai tsaye, tunda suka shigo layin Moh ya tabbatar da zai samu yadda yake so, lallai Musaddik mugu ne na gaske, idan ba haka ba ya rasa unguwar da zai samo ya siya gida sai irin wannan unguwar. A daidai wani kofar gida karamin gaske suka tsaya, suka fito a tare wanda zasu gani yana tsaye yana jiran su, yana ganin su ya karaso bakin sa cike da murna ya gaishe su, sannan ya bud'e musu gidan" yace su shigo. "Siminti ne gaba daya tsakar gidan sabo yana ta kamshi, bashi da girma tsakar gidan sosai dan be fi yaci" "tabarma days da rabi ba, a gefe yar karamar rijiya ce saboda rashin ruwan unguwar." Dakunan guda biyu da suka kasance falle-falle ya bud'e musu suka shiga nan ma ko ina an masa fenti "yana ta kamshi, babu abinda ba'a saka ba hatta karamin gado da kujeru an saka,da yar karamar tv babu batun fridge ko cooker gas balle azo maganar su AC da sauran kayan more rayuwa, kitchen din babu komai dama sunyi da nufin daga gida sai a kawo mata kayan kitchen suyi amfani dashi. Kitchen din karamin gaske ne dan mutum biyu ba zasu iya aiki a ciki ba saboda kankantar sa, balle a samu sukunin" cika shi da kaya. Fitowa sukayi ya rufe gidan yana sake washe baki """Ranka ya dade gidan yayi ko?""" """Yayi sosai yadda nake so, sai ka sanar musu ba sai an kawo kayan gida ba ,iya kitchen ya isa shima karsu" "matsawa kansu duk abinda babu zaka saka musu.""" """An gama ranka ya dade, sai maganar lefe.""" """Ana gobe daurin aure za'a kai, an gama hada komai ina tunani.""" """ Nagode Allah ya kara arziki.""" "Be amsa ba, yayi gaba ya fad'a motar yana kallon tsarin gidan, murmushi ne ya kwace masa, ya girgiza" "kansa yana ayyana yadda zuciyar Mama zata buga ko kuma ta kusan bugawa,yayi alkawarin shayar da ita mamaki irin wanda bata taba tunani ko hasashe ba." "Kai tsaye wajen gym suka wuce, ya kwana biyu be motsa jikin sa ba, yana bukatar hakan saboda tafiyar" "da sukayi be samu lokaci ba. Dariyar shakiyanci Musaddik ya dinga yi masa, ya tsaya daga abinda yake yana hararar sa" """wai dariyar menene haka? Uhum?""" """ Naga yadda ka dage kake ta faman daga karafu nan nan ne wallahi, kar dai ka illata musu yarinya" "wallahi, kasan dai kai din tsohon tuzuru ne da yaki auruwa. """ "Robar ruwan da ya gama sha ya jefe shi dashi, ya goce ta fadi kasa yana sake tuntsurewa" """ Ka kiyaye ni wallahi. """ """ Anki din, daga fadar gaskiya?""" """ Zan kamaka ne, naga kafarka a gida na wallahi. """ """ Gidanmu dai. """ "Towel ya ja ya goge gumin fuskar sa, ya biye wa Musaddik zai dauke hankalin sa ne ga abinda yake shirin" "yi. Wayar sa ya dauka akan dan table din wajen yayi dialing number ta, sai da ta kusan katsewa sannan ta daga." """Huh!"" Ya furzar da iska yana jan numfashin" """Ranki ya dade an gama jamin ajin ne?""" """Ina wuni?"" Ta kautar da maganar ta hanyar gaishe shi" """Lafiya lou, ya gida ya kowa da kowa?""" """Alhamdulillah.""" """Masha ALLAH, yaushe Abba yace zaki dawo?""" """Be fad'a ba, amma naji Mummy tace ba zan dawo ba sai ranar.""" """Ranar? Yaushe kenan?""" """ Ka cika tsokana wallahi, nima ban sani ba.""" """Ke kuma kin cika kunya ba, sai kici sai ranar auren mu kawai.""" """ Allah zan kashe wayar."" Ta fad'a tana turo baki, dariya yayi yace da sauri" """ Allah ya baki hakuri Matata.""" Shiru tayi tana wasa da album din hotunan da Mamma ta bata bayan ta mata bayanin kowa da yake jiki. """In sha Allah ana gobe za'a kai lefe, kinsan sha'anin rayuwar, Allah yasa be makara ba.""" """ Be makara ba, Allah ya saka musu albarka.""" """Amin Matata, nagode sosai da bani dama da kikayi, in sha Allah ba zaki yi Dana sani ba.""" """Kullum godiya? Ni me nayi?""" """Ai wai kinga dai yanayin yadda abubuwan suke.""" """Babu komai Allah ya tabbatar mana da alkhairi.""" """Amin Amin amarya ta.""" "Yar karamar dariya tayi, shima ya tayata kafin suyi sallama. Mamma ce ta shigo dakin rik'e da jaka babba," "sai me aikin gidan dake biye da ita da wasu kayan suma da yawa, ajiye su sukayi a gefe me aikin ta fita kafin ta sake dawowa ciki dauke da tray da aka doro chicken pepper soup da wani cup shima cike da abu kamar kunu, sai wani da akayi ma hadin fruits aka saka madara. Dora shi tayi a saman drawer ta fita ta" barsu. "Da hannu Mamma tayi mata alamar ta taso, ta taso ta zauna a k'asa in da Mamma din ta nuna mata," "tray din ta sakko mata dashi tace maza ta cinye naman tas, idan ta gama akwai bakuwar da zata shigo wajenta, Itace me jakar chan. Tun zuwan ta gidan take faman shan abubuwa, a dan lokacin tayi masifar chanjawa, tayi kara fari da kiba jikinta ya sake murjewa sosai. Ita kanta tana jin da gaske ta kai mace," "tana jin zata iya karawa da ko ma wace amma a dah, bata da wannan confidence din." Bata kyuwar cin duk abinda aka bata dan da bata samu wanda zai dubeta ba balle har ya bata abinda yasan zai amfane ta. Shiyasa ta bada himma take yin duk abinda za'a sata. "***A bangaren gidan su Iman kuwa, bayan dawowar Abba sai da suka sake wani rikicin da Mama, wanda" "ya saka kowa ji har aka dinga ganin baiken Maman, amma kishi ya rufe mata ido matar Abba Musa na" "zugata tayi masa tijara son ranta, be kula ta ba don a yanzu baya sakata cikin jerin masu hankali, yana mata uzurin kishi ne ya sakata yin wasu abubuwan. Bayan kamar kwana biyu da dawowar sa ta same shi" "har daki ta bashi hakuri abinda ya bashi mamaki sosai, hakura yayi ya sakko amma ba wai don ya hakura" "da maganar Iman ba, yana nan sai ya yi mata hukunci daida abinda ta aikatawa yar sa." "Shirye shirye ya kankama sosai, mama babu zama kullum tana hanyar kasuwa tun da ta samu labarin" "cewa Bashir yace iya kitchen kawai zasuyi, hakan yayi mata dadi shine ta maida hankalinta sosai wajen kawata kitchen din dan ta tabbata gidan ba karamin gida bane, dole ne su fita kunya ta hanyar hada mata kitchen din yayi sosai." "Duk abinda ta tambaya Abba bata yake dan baya son wata doguwar magana, hankalin sa gaba daya" "yana kan maganar auren Iman, da yadda daurin auren zai kasance domin yasan za'a yi taro ne irin wanda ba'a taba yi ba, manyan mutane zasu halarta da yan siyasa da manyan sarakunan k'asar nan da ma na ketare. Duk abin nan Mama bata san komai akai ba, bata taba tambayar shi game da Iman din ba ko" "yadda nata tsarin yake, shiyasa kawai shima ya rufe ta ruf ya barta da abinda take yi." "A yadda tsarin bikin yake, alhamis za'a yi kamu, juma'a a daura aure sai asabar dinner kamar yadda" Zeenat din suka zauna suka tsara ita da Bashir bayan ya sanarwa Moh da tsarin ya kuma bashi go ahead. "Tsarin bikin da su kuma chan masarauta suke shirya wa biki ne gagarumi za'a yi a Kano da Adamawa," "kowanne kuma kwanaki za'a dauka anayi tun daga asabar din washegarin bikin, na Kano za'a fara kafin a koma adamawa in da za'a kai amarya." "Kamar yadda yake a tsari, ranar alhamis za'a karbi lefe, lefen Zeenat da Iman, wanda Mama tayi gayya," "gayya irin ta ban mamaki, tana Kuma sanarwa mutane suzo suga lfen Zeenat dan ta tabbatar za'a ga kayan da baa taba gani ba." "Yan uwa da abokkan arzikin Mama su suka cika gidan, aka shirya kaya na mamaki, aka gyara gidan." "Wata sister Mama ce tazo ta sameta tana zaune cikin kawayenta ana shewa, ta jata gefe hankali a tashe tace" """Yaya, wani labari naji fa, dangin mijinki na hirar basu san Ina wajen ba, naji suna cewa Iman tayi goshi ta" "samo jinin sarauta, ana ma tunanin dan sarki ne duk da Basu tabbatar ba ana boye zancen ne amma kamar hakan ne.""" "Wata irin dariya Maman ta saka, har da hawaye" """ Kinji ki Fatima da wani zance, su fa basu san kan zancen ba, maganar Zeenat ake ba Iman ba, na ji" "wannan zancen tun bayan zu ba ai, kawai na kyale mutane ne yadda abun zai kada su, ba dai anjima kadan zasu iso ba? Zamu gani ai.""" """ Allah yaya? Kin Kuma tabbatar da hakan ne?""" """ Zaki gani ai.""" "Tayi gaba tana murmushin mugunta, ba karamar kunya tasan za'a sha ba a lefen Iman din ba." Hmmm ***Assalamu alaikum sisters fatan alkhairi ga kowa da kowa. In Sha Allah hutun mu zai kama asabar da "lahadi, domin kowa ya samu damar aiwatar da wani abu me muhimmanci a rayuwar sa, sannan mu kula da gidajen mu da iyalan mu dukka, mu bawa yaranmu da mazajenmu lokacin da suke bukata daga garemu. In Sha Allah Monday to Friday za'a samu posting in sha Allah, sai dai wani uzurin ya gifta." "Sannan masu korafin ba'a basu page biyu ko uku a rana, wani page dayan yayi wasu pages din guda biyu," so idan hakan ne gwara dayan me tsawo mu tafi a hankali har Allah ya bamu ikon kammalawa. "Zafafa biyar na godiya da zabin su da kuke a kowanne lokaci, dan Allah mu cigaba da yi ma juna uzuri" kuma mu kyautata lafazi a tsakanin mu domin magana me kyau ma sadaka ce. "Masu sharing novels group group una weldone kunji? Dan Allah ku daina babu kyau, ka sowa dan uwan" ka abinda kake sowa kanka hakan na cikin cikar imanin mumini. Rano "[1/19, 6:15 PM] Sakaba: Halin Girma" 16 *_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK _* https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share *_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK _* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb *_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK _* https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content =share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1D xoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2F xLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS *_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK _* https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw ***************** "Yana zaune a daki kiran Aunty Faty ya riske shi, dagawa yayi yana tashi dan yasan dalilin kiran" """Mun shirya tafiya kawai zamuyi kana ina ne?""" """ Ina cikin gidan bari nazo.""" "Yace yana cire wayr, takalmin sa ya zura ya fito falon, fadawan dake wajn part din suka yunkuro jin" "motsin sa, da hannu yayi musu alamar kar su bi shi ya shiga takawa zuwa shashen Fulani da ya san a chan zai same su." "Babban falon ta ya nufa in da ya tarar da su da yawan su, daga gefe akwatuna ne masu yawan gaske," "da ido ya bi kayan kafin ya zauna suka hau tsokanar sa da ango ango, yawancin su yan uwan Ammin sa ne,sai dangin Bubu da matan abokan sa da badu da yawa sosai, komai Takawa yace sai Bubu yace masa ba sai an zo ba, ayi komai a nan din kawai. Yanzu ma dan dai abun kamar al'ada ne, shiyasa kawai" Takawa yace ya kyale su idan yaso sai ya zama ba kowa da kowa ba. Anty Faty ce ta tashi ta hau nuna masa yadda kayan suke """Wannan saitin na Takawa ne, gasu nan 12 ne cip, kaya ne na alfarma komai da kasan ya kamata a saka" "an saka ciki, sai wannan masu pink din su kuma saitin Ammi ne, suma Sha biyun ne kamar na Takawa, wadannan kuma masu purple din na Hajja ne da dan tsohon mijin ta Aji, guda shida ne gasu nan ko? Sai masu maroon din nan na karshe, namu ne dan muma ba za'a bar mu a baya ba, suma guda 6 ne idan ka" "hada set nawa kenan? """ """ 36!"" Yace yana sake bin kayan da ido." """ Wadannan kwandunan kuma, gasu nan guda 24 kowanne da ka gani, abokin Bubu Maimartaba sarkin" "Ghana ne ya aiko dasu.""" """ Allah sarki."" Yace yana murmushi" """ Kilishi fa?""" """ Auw kaga na manta ko? Gasu chan fito dasu Harira.""" "Tayi wa daya daga cikin bayin dage tsaye daga gefen kayan magana," """ No a barsu bana bukatar su, a barsu anan zan duba su daga baya, akwai kayan da za'a kai na rabon da" "zasuyi a dangi, suna cikin Ford 2 nasa an saka su, zaku duba kafin ku wuce, komai yayi in sha Allah.""" """ Owk shikenan, kaga wadannan boxes din da kasa aka yi musu design a dubai da hoton ku?""" """ Na gani aunty sunyi kyau sosai, su nake so a fara fitowa dasu, dan Allah aunty ayi duk yadda nace.""" """ An gama karka damu.""" """ Shikenan, Musaddik zai shige muku gaba, ya za'a yi tafiyar?""" """ Eh da wai kamar motoci goma haka, sai wanda za'a zuba kayan Hilux din Takawa masu rufin bayan nan," "idan yaso sai su biyo baya ko?""" "Murmushi yayi me aji, ya girgiza kansa yana ayyana kalar tsiyar da ya shuka yana kuma jinjina abinda zai" "faru nan da wasu yan awoyi. Bed room din Fulani ya shige, ya sameta da yan uwata da suka zo, ya zaune tsakanin wasu tsofaffi biyu ya dinga tsokanar su ya hanasu sakat, kowa ya ganshi yasan yana cikin farin ciki mara misaltuwa, yanayin sa kadai zaka san ba karamin murna yake da auren ba, su kuwa basu san harda murnar hawan jinin da ya tabbatar zai kama Mama, dama ita hassada ga mai rabo taki ce, idan" kuma zaka gina ramin mugunta toh ka gina shi gajere baka san ko kai ne zaka fad'a ciki ba. "****Mama babu zama tun da taga yamma tayi ta tabbata suna hanya ko sun kusa zuwa, tayi nan tayi" "nan duk farin ciki ya hana mata sakat, karar tsayawar manyan motoci a kofar gidan ya saka kowa nutsuwa aka hau sake gyara wajen, kowa ya zauna ana dakon shigowar su." "Gate din gidan me gadi ya bud'e da sauri, aka shigo da motocin da akwatunan suke ciki, sauran aka bar" su a waje saboda babu wajen da zasu shiga dukka. "Sauke akwatunan aka fara yi a harabar wajen, kafin su gama sauke su dukka guda talatin da shida, sai" "baskets din suma. Boxes din da Anty Faty tayi masa magana akai suka riko kowacce mace ta rik'e daya a hannu dama yan kanana ne, matan da Mama ta wakilta da idan sun zo su tare su ne suka karaso" "kowanne fuskar sa dauke da fara'ar suka tare su sannan suka yi musu jagoranci zuwa ciki, Mama na" "zaune an sha lullubi da kayan alfarma suka shigo, ta bisu da kallo ta kasan Ido, mata ne hamshakai" "wanda suka amsa sunan su mata, hutu da jin dadi ya kama jikin kowacce kai ba sai an fad'a maka ba. Rawar jiki jamaar Mama suka fara su a lallai an zo wajen su, dangin su Abba na gefe sun zama yan kallo, akwatunan aka dinga shigowa dasu Mama ta hadiye wani yawu me karfi, cikin al'ajabin uban kayan da ake ta shigo dasu, gaba daya ma sai ta bata lissafi suka dinga yi mata gizo, kamar ta tashi ta hau bubbudasu taji, wani farin ciki na ziyartar ta. Duk gaishe gaishen da ake tsakani bata wani fahimta saboda yadda ta tafi tunanin kalar hutu da gatan da Zeenat zata shiga, gashi alamu sun nuna dangin" "mijin nata masu karamci ne, basu da nuna kyama ko wulakanci ko kadan." """Baki ne daga gidan sarki, mun kawo lefen dan mu, jikan Maimartaba sarki, sannan d'a ga sarkin" "Adamawa Alhaji Ahmad Santuraki,Ina mahaifiyar amaryar tamu take?""" "Mama tayi firgigit sanda taji wata cikin matan na tambaya, murmushi ta yi tana sake kama kanta ita a" "dole akwai surkutar nan. Aunty Faty ce ta tashi tsam, ta isa gaban Maman ta mika mata akwatin hannun ta, dake dauke da hoton Moh da Iman da ita kanta Iman din idan ta gani zatayi mamakin yadda ya same shi, hoton yayi masifar kyau zaka rantse tare suka dauka, yana sanye cikin shigar babbar riga da rawani, yayi wani murmushi da zaka kalla ka sake kalla. Wani irin shock Mama taji lokacin da ta karbi akwatin a" hannun ta hoton da yake jiki ya shiga cikin idon ta ya aikawa da kwakwalwarta sako a take. """Wannan itace kyauta ta farko ga yar mu Fatima, akwai sauran kyaututukan da bazasu kirgu ba, amma" "dai ita wannan din ita ce zamu iya cewa ja gaba ga sauran.""" Kamar mutum mutumi haka Mama ta dinga kallon matar da take mata wani yare da sam kwakwalwarta ta gaza dauka balle ta fassara mata abinda matar take cewa. """Wadannan kayan kad'an ne daga cikin abubuwan da muka tanadawar Fatima, in sha Allah ba zata taba" dana sanin amincewa da dan mu Muhammad ba. """ Dan sarki jikan sarki kuma sarkin gobe idan me dukka ya kaimu.""" "Wata mata tace daga gefe, duk suka amsa da in sha Allah." "Guda aka saka a wajen, gudar da Mama taji kamar an saka allura ne ana chacchaka mata a tsakiyar" "kanta, kokarin sakin box din hannun nata take, wata kanwar su Abba da take lura da ita tuntuni ta taso da sauri ta karbe tana ma yan uwan Maman kallon banza." """Masha ALLAH, lallai mun ga Halin Girma da karamci na wannan babban gida, mun kuma tabbatar da yar" "mu ta shiga hannu na gari""" "Ta fad'a bayan ta koma wajen zaman ta, ta kuma mikawa wata babba a dangin box din. Murmushi" "matan sukayi dukka, sannan aunty Faty tace" """ Sai a bude kayan ko?""" "Da karfin guiwar su dangin Abba suka tashi, aka fara bud'e box din farkon nan, kowa ya shiga mamaki," "mukullaye ne wajen guda uku na mota, sai mukullin gida da takardun su, sai kuma wani babban set of gold masu girman gaske. Wata irin guda da tafi ta dazu aka sake saki, jira ya soma dibar Mama, ta kasa gane komai sai hajijiya da take ji kamar zata kayar da ita daga zaunen da take, me yake faruwa? Me yake" shirin faruwa. "Daya bayan daya aka dinga bud'e kayan, tun mutane na irgawa har kowa ma ya gaji aka zuba ido ana" "kallon tarin dukiya, dukiya me sunan dukiya, dangin Abba da Mama ta dinga dagawa kai sai suka zama kamar sune kawai a wajen, farin ciki suke dama kowa yaji haushin abinda Maman tayi a dan tsakanin gabatowar bikin, sai kuma yadda ta dinga yada habaici a ranar da za'a kawo kayan wanda suka tabbatar dasu take shiyasa suka ji haushin ta sosai, amma yanzu da haka ta faru sai suka hau murna suka dinga" yin abu da gayya dan su kara haukata Maman. "Tashi sukayi bayan an gama ganin kayan, aka damka duk wasu abubuwan da suke da muhimmanci" "sosai kamar golds da takardun gida da keys a hannun kannen su Abba sannan suka yi musu sallama, abubuwn da aka shirya da sunan Zeenat suka je suka dauko aka saka musu a mota, basu ma so karba ba" amma yadda suka dinga insisting yasaka suka karba dan kar suga kamar sun raina musu ne. "Suna gama fita daga gidan masu kawo kayan Zeenat ta shigowa, mata ne kwantsam masu mugun yawa," "masu goyo ne, gasu nan harda wanda suka ciko bus suka zo. Ana kokarin daga Mama a maida ta cikin daki sanarwar zuwan su ya katse su, a sanyaye suka dawo suka zauna, suka shigo bayan an matsar da" kayan Iman an tura wasu dakin Abba da dakin Maman. "Da kallon bakin ciki Mama take bin su, kamar ta tashi ta hau bugun su haka taji, yaran da suka zo dasu" "suka dinga ihu na goyen sai da aka sakko su, na hannu kuwa suka hau wasa a falon. Gaisawa akayi suka gabatar da kansu, kafin ma su dire sunan Zeenat din Mama ta ja numfashi da take jin kamar zai fice daga" jikin ta. """Kuyi hakuri asthma ce da ita nema take Kuma ta tashi tun dazu, tashi Yaya mu shiga ciki ki huta.""" "Aunty Maimuna kanwar Maman tayi saurin rufawa ta janye Maman dan ta hango matsala babba, kamar" "ma kokawa take da numfashiin ta. Suna shiga dakin ta kurma ihu, ihun da kowa ya ji shi, da tayi sauri ta saka hannu ta rufe mata baki" """Haba Yaya Hajara, ai sai aji kunya, dan Allah kiyi hakuri.""" """Kutmar uban hakuri, kike ce min nayi hakuri? Bayan kinga abinda ya faru? Kinga yadda Ibrahim ya" "munafurce ni da yan uwansa? Bayan duk halaccin da nayi musu ? Amma kike cewa nayi hakuri, ke kinsan me nake ji? Innalillah, wayyo Allah na.""" """ Ni dai kiyi hakuri, ko ma menene ki bari a gama taron nan, kinga mutane zasu tafi dake a baki.""" """ Taro? Ke kina ganin za'a cigaba da taron nan?""" """ Toh me za'a yi Yaya?""" """ Ba zai yiwu ba, wallahi sai dai a fasa auren, amma ba zan bari bakin ciki ya kashe ni ba a banza."" Sai ta" "sake fashewa da kuka, kuka irin wiwi din nan da kana gani zaka tabbatar da ba karamin kuka mutum yake ba. Duk yadda Aunty Maimuna taso ta bata baki tayi hakuri ta kasa, sai kawai ta fito ta rufo mata kofar ta dawo wajen bakin, lokacin har an soma bud'e kayan, akwatu na guda hudu sai kit daya, da kayan ta masu kyau daidai da tsarin akwatunan, amma ganin da mutane sukayi wa kayan Iman ya saka zasu ga na Zeenat din kamar bola, a daddage kowa ya kalla, suka dauko dubu ashirin suka ce gashi nan ta kai" dinki ba'a samu an dinka ba saboda kurewa lokaci. Daga haka sukayi musu sallama aka je dakin Mama a "dauko ragowar kayan da suka rage ta ce idan an basu ko ruwa ba'a za'a basu ba, da k'yar Aunty" Maimuna ta bata hakuri aka saka musu ruwa da lemo a bayan mota suka tafi. Daya bayan daya yan uwan Abba suka zo suka kwashe kayan iman suka maida su bangaren Gaji a cewar su kar bakin ciki da kishi ya saka Mama ta saka wuta ta kona su. "Hauka hauka Maman ta soma da suka shigo, kowa yayi mata banza suka dinga dariya suna yada mata" "da magana, suka kwashe komai suka yi tafiyar su. Jiki a sanyaye kawayen Mama suka dinga sulalewa suna guduwa kowa burin sa ya isa gida ya bada labarin abinda ya faru." "Zeenat na wajen saloon suna ta waya da Bashir kiran Maman yake ta shigowa tana kin dagawa, da dai" "taga kiran ya ishe ta sai tace ya bari ta daga wayar Maman, katse nasa kiran tayi ta daga na Maman." """Kina gidan uban wa wai?""" """Mama kinsan fa ina saloon.""" """Toh ki bar komai kike ki taho gida, kizo yanzu ki same ni.""" """Mama ban gama ba, kuma kinga zamu je mu siyo head din da zan saka da dinner da Bashir daga nan...""" """Bashir din yaci abu ta kaza uban sa, na rantse da Allah kika bari man da awa guda baki dawo gida ba, sai" "kinga yadda zan miki"" tana kaiwa nan ta katse kiran, saroro Zeenat din tayi rik'e da wayar cike da mamakin Maman." """Me ya faru kuma?"" Ta Tambayi kanta cike da mamaki." "Safa da Marwa Mama ta dinga yi a daki tana jiran Zeenat, ko sama da kasa zata hade ba zata yarda ayi" "auren nan ba, tasan idan ita kanta Zeenat din tazo taga abinda ya faru zata ce ta fasa ne, shege matsiyaci dama munafurtar su yayi kenan." """ Yaya Hajara da kin zauna kin nutsu, tashin hankali ba zai gyara komai ba.""" """ Ba zaki gane halin da nake ciki ba, ba zaki gane ba, ina cikin tashin hankali, bayan kunyar da nake ciki.""" "Ta fad'a tana cigaba da zagayen, idanun ta ya kada yayi jajur taci kuka ta godewa Allah. Jugum sukayi" "kowa da abinda yake rayawa a ransa. A haka Zeenat ta shigo ta same su, Mama tayi kanta da sauri ta fizgo hannun ta da sauri." """ Kika ce min talaka ne, kayan jikin sa ma a yayyage, daga gani bashi da komai.""" """Waye? Wai Mama menene ya faru?""" """ Ubanki, bake ce kika ce min wanda yazo neman auren Iman talaka bane?""" """ Eh Mama, dan baki ganshi ba.""" Dundu Mama ta kai mata ta goce cikin bacin rai tace """ Toh dan ubanki dan sarki ne.""" """ Sarki!!!"" Zeenat ta fad'a da karfi tana zaro ido" *_ZAFAFA BIYAR 2022 _* *_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_* _SO DA ZUCIYA_ *_SAFIYYA HUGUMA_* _DABI'AR ZUCIYA_ *_MAMUH GEE_* _DEEN MARSHALL_ *_HAFSAT RANO_* _1aHALIN GIRMA_ *_BILLYN ABDULL_* _TAKUN SAKA_ *_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_* D’aya 300 Biyu 400 Uku 500 Hudu 700 Biyar 1k *_Zaku tura kudin a_* 6019473875 *MUSAA ABDULLAHI SAFIYA* *keystone bank* *Sai shedar payment dinki a* 08184017082 *Kokuma katin waya na MTN anan* 09134848107