Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GJCgZzbBrsV8mesM7Zwyzf *RANAR NAKA...* ©️ _Fareeda Abdallah_ 1) "Duk da yadda ƙofar ta kasance ta bature mai masifar tsada, irin mai taushinnan sosai da ko an buɗe ba" "ta ƙara, daga yadda ta murɗa hannun ƙofar da ƙarfi, ta danno a haukace kuma a fusace, sai da ƙofar tayi" wata siririyar ƙara mai kama da fitar iska. Hakan yasa mazauna ɗakin waiwayowa da sauri suna kallonta da wani yanayi mai kama da maɗaukakin mamaki a fuskokinsu. Ganin irin kallon da suke mata yasa ta ƙara harhaɗe girar sama da ƙasa tayi murtuk! Kamar an sheƙawa "ƙullun kunu tafasassasshen ruwa. Kallon huɗu saura kwata ta watsa musu gaba ɗaya, sannan ta ba iska" ajiyarsu ta hanyar jan tsaki ƙasa-ƙasa. Ta taka kai tsaye ba tare da tsoro ko fargaba ba zuwa gurin "mamallakiyar ɗakin da take zaune kan kujerar gaban madubi, da kakkausar murya ta ce" """Abincin Innaye da aka manta da wanzuwarta a cikin gidannan na zo karɓa...""" """Ke dabbar ina ce ƴar ƙauyen-ƙayau da bata san abinda ya kamata ba? How dare you da za ki shigo min" "ɗaki kai tsaye da wani ƙazamin jikinki ba tare da neman izini ba ina tare da abokan aiki na?""" "Ta katse yarinyar da maganganun cikin fushi. Da miƙewarta tsaye a fusace, da ɗaga hannu ta kai ma" yarinyar wani mahaukacin mari baza'a ce ga wanda ya riga wani ba. Cikin zafin nama da ƙwarewa a zamiya yarinyar tayi saurin duƙawa ƙasa marin ya bi iska. A haukace ta "miƙe tsaye tana haki, domin an shammaceta, a zuciyarta take ayyana lallai da marinnan ya sauka a kumatunta ta rantse da girman Allah babu abinda zai hana ta ɗaukar wannan figaggiyar matar mai shegen girman kan tsiya da wulaƙanta ɗan Adam ta nuna ma Allah sannan ta maka ta da ƙasa. Sai dai" duk abinda zai faru ya faru. """Kan Uba... Ni kika mara?""" Ta faɗa cikin ɗaga murya. """Me nai miki da za ki mare ni?""" Ta sake jefa mata tambayar tun kafin ta bata amsar tambayar farko. A ranta take kitsa lallai ya kamata ta nuna ma matar nan halin dabbobi da jahilan ƴan ƙauye da take yawan zaginta da su. Bazai yiwu duk zagi da tozarcin da tayi mata a cikin kwanaki bakwai na zamansu a gidan ya tafi a banza "ba, lallai ya kamata ta nuna mata shiru-shiru fa ba tsoro bane, gudun magana ne." "Kafin matar ta amsa, ko kuma ɗaya daga cikin mazauna ɗakin ta ce wani abu ta ɗaga hannu biyu da sauri" "ta ɗora akai, ta fasa wani gigitaccen ihu da muryarta mai bala'in ƙara, cikin ƙanƙanin lokaci muryar yayi amsa kuwwa a ko wane lungu da saƙo na cikin gidan." "Tsakanin Innaye da take zaune kan dadduma a ɗakin da aka sauke ta acan BQ tana gyangyaɗi, da Hafiz" da dawowarsu kenan mai gadi ya buɗe musu ƙofar get direba yana ƙoƙarin daidaita fakin ɗin motar a tsakar gidan. Baza a ce ga wabda ya riga wani isa cikin ɗakin Bintu da ihun Zulaikha ke fitowa ba. Tana ganin Innaye da Hafiz sun shigo ba tare da jin nauyin jikinta ba kasancewarta yarinya mai garin jiki da wani irin gudu tayi gurin Innayen ta ruƙun-ƙumeta tana ƙara ƙarfin kukanta. "Taga-taga sukai za su faɗi, domin jikin Innaye irin na fulani ne ga kuma rashin ƙarfi saboda tsufa da" "rashin lafiyar da take fama da shi cikin kwanaki biyun, a dabarance Zulaikha ta riƙe Innayen tare da rage" nauyin da ta sakar mata. Cikin kuka da yanayin shagwaɓa da taɓara ta fara cewa """Innaye mari na fa tayi, wai don kawai a ladabce na ce mata Aunty Bintu ina abincin Innaye? Mai aikin" "da take kai mata kila yau ta manta ne bata kai mata ba, ga shi har yamma ta yi. Shi ne fa kawai ta ɗaga hannu ta gaura min mari... Wayyo Allah kumatuna, zafi, zafi, zafi kumatuna Innaye ki duba min ko ya" "saɓule...""" Tana zuwa nan a maganganun da take yi cikin kuka ta sake yanka ihun da yasa da sauri Hafiz ya saka "yatsarshi manuniya ya toshe kunnuwansa, saboda jin wani zazzaƙar ƙara da ya karaɗe cikin kunnuwanshi mai barazanar fasa dodon kunne." "Ita kuwa Innaye da ta yarda da maganganun da Zulaikha ta faɗa ɗari bisa ɗari, wani kallon kin kyauta ta" "aika ma Bintu a fakaice, sannan ta ƙara janyo Zulaikha jikinta tana duba ɓangaren kumatunta na hagu da hannunta ke dafe da gurin tana risgar kuka. A lokaci guda kuma tana rarrashinta da tausasan kalamai" """Yi haƙuri Auta, ƙyale ta kin ji ko? Ta yi ma kanta. Yau in sha Allah za mu tattara ina-mu ina-mu mu" "koma inda muka fito.""" Tana gama faɗin haka bata jira wani ƙarin bayani ba ta ja hannun Zulaikha suka fice daga ɗakin zuwa masaukinsu. 2) "Hankali tashe, a firgice Hafiz ya bi bayansu bayan ya aika ma da Bintu da abokan aikinta wani kakkausan" kallo da ko a wasa bai taɓa shiga tsakaninsu da shi ba. Gudu-gudu yake taka matakalar benen yana kiran sunan da suke faɗa mata cikin magiya da ban haƙuri. """Innaye, Innaye, don Allah kiyi haƙuri... Ki saurareni don girman Allah...""" Duk yadda yake bin bayanta yana magiya da maganganun ban haƙuri bata saurare shi ba sai da suka isa masaukinsu a can Bq. "Babban waje ne, kuma masauki ne mai kyau, ɗauke da gado da saitin kujeru masu kyau na matsakaitan" kuɗi. Sai dai fa Bq ɗin can bayan gida ne da yayi banbaraƙwai ace an sauki Uwar miji a gurin. Idan da sanin darajar ɗan'adam ko ƙanwar miji bata cancanta a sauketa a gurin ba ballantana uwa. Domin tun tale-tale an tsara gurin ne a matsayin masaukin ƴan aikin gidan. "Baya ga haka kuma, a can cikin muhallin da masu gidan ke zaune, akwai ɗakunan baƙi har guda uku, ko" "wane ɗaki da bayi a ciki, ɗauke da setin gado masu tsada. Sai dai duk bayan sati guda mai aiki ke buɗewa ta gyara a sake mayar da ƙofofin ɗakunan a kuk-kulle. Saboda masu gidan basa amfani da su, sai dai idan matar gidan tayi baƙi daga ɓangarenta masu matuƙar muhimmanci sosai take buɗe musu suyi masauki a" ciki. """Ina saurarenka! Ya aka yi Hafizu?""" "Innaye ta tambaye shi da murmushi a fuskarta, murmushin da duk mai hange da lura idan ya kalle ta kai" "tsaye zai fahimci murmushin yaƙe ne, irin murmushinnan da ko kusa bai kai zuci ba." "Amma da yake Hafiz a firgice yake, sam bai lura da kalar murmushin da take yi ba. Ajiyar zuciya kaɗan ya" sauke don ganin murmushin yasa shi ji a ransa lallai fa Innaye bata ɗauki abinda ya faru da zafi ba. "Daman tun tale-tale ita ɗin mai haƙuri ce, kuma har yanzu ita ɗin uwa ce mai matuƙar haƙuri da kawar" "da kai akan duk muradun ƴaƴanta, matuƙar bai saɓawa doron addininmu na musulunci ba." A marairaice ya duƙa a gabanta ya cigaba da magiya """Innaye, don girman Allah da darajar fiyayyen halitta SAW kiyi haƙuri da abinda ya faru.""" "Yayi maganar cikin ƙanƙan da kai da taushin murya, fuskarsa a takwarkwashe kamar zai saka mata kuka." "Daƙiƙu talatin ta ɓata tana kallonshi, zuciyarta cike da tunanika mabanbanta. Daga bisani ta sauke" nannauyar ajiyar zuciya. A hankali ta ce """Babu komai Hafizu. Ya wuce.""" Ta faɗa a taƙaice. Sannan ta kawar da idanunta daga kan shi ta maida kan Zulaikha. "Wacce izuwa wannan lokacin ta daina kukan da take yi, tana kwance ne akan gado ta duƙunƙune ƙafafu" "da hannaye cikin hijabin jikinta, ja juya fuskarta can ta basu baya, ita kaɗai take sakarwa kanta" "ƙayataccen murmushi, idan ta tuna diramar da ya faru yanzu-yanzu." "Abin kamar a shirin film, ko kuma a iri labaran nan na littafi." Ta sake sakarwa kanta murmushi tana maganar zuci 'Ko babu komai dai a yanzu an fara goge raini tsakaninta da matar can. Ta gwada mata kaɗan daga cikin halin dabbobi da jahilan ƴan ƙauye da take kiranta da su. Idan da ragowar hankali a jikinta gobe baza ta sake gwaɓa mata maganar banza makamantan waɗannan ba...' """Auta?""" Innaye ta katse mata tunani ta hanyar kiran sunanta a tausashe. Da saurin gaske ta ɓata yanayin fuskarta kafin ta juyo a hankali da shagwaɓaɓɓiyar murya ta ce """Na'am Innaye.""" Cikin kulawa Innaye ta sake ce mata """Ya kumatun na ki? Ya daina zafi?""" "Ƙif-ƙifta idanu tayi, nan take suka cicciko da ƙwallah, sannan ta amsa da" """Ya dai ɗan ragu, ba kamar ɗazu ba, amma fa har yanzu yana min zafin.""" "Duk maganar da take yi, ko kusa bata yarda ta saka idanunta cikin na Hafiz ba, duk da kuwa yadda shi ɗin" "yake ta ƙoƙarin su haɗa idanun, amma fau-fau ta ƙi yarda hakan ya faru." Da rarrashi Innaye ta sake cewa """To kiyi haƙuri. Zan shafa miki man zafi a gurin, zai daina gaba ɗaya in sha Allahu. Yanzu dai miƙe ki" "kwaso mana shanyar kayanmu da suke igiya, yau in sha Allahu komai dare gida muka kwana.""" "Irin yadda lokaci ɗaya ta ƙayata fuskarta da murmushi, sannan ta diro daga kan gadon da sauri ba tare" "da kasala ko jin nauyin jikinta ba, shi ya ƙara bayyana ma Hafiz lallai abinda yarinyar take jira kenan. Ya bi" "ta da wani mugun kallo, a yadda yake jin matsanancin tsanarta a ransa ji yake kamar ya janyo ta yayi ta bugu har sai ya tabbatar ta yi mugun jigata." "Na daga cikin dalilan da suka sa a kullum yake ƙara tsanar ƙanwar tasa, tun da suka zo gidan cikin" taƙaitattun kwanakin da suka yi gani yake ita ce Ummul-aba'isin da aka kasa samun gwaggwaɓar "shaƙuwa tsakanin matarsa da yake matuƙar so, da mahaifiyarsa da yake tsananin ƙauna..." """Kayi haƙuri Hafizu.""" Innaye ta katse mishi tunani da faɗin haka. Kafin ya ce wani abu ta cigaba da cewa """Yau in Allah ya yarda zan ɗauke ta mu koma inda muka fi wayau. Na san a zuciyarka ji kake kamar ka" "kamata ka yanka saboda an taɓo zinariyar matarka ko?""" "Innaye ta jefa mishi tambayar da muryar da ke bayyana ɓacin rai ƙarara, saboda akan idanunta ya bi" Zulaikha da mugun kallon da babu abinda yake bayyanawa sai matsananciyar tsana da ƙiyayya """Ba haka bane Innaye.""" Yayi maganar a sanyaye. Kafin ta amsa ya sake cewa """Da gaske ba haka bane. Ni dai roƙo na a gare ki don girman Allah kiyi haƙuri ki daina batun tafiyarki" "gida yau...""" """Yau za mu tafi Hafizu.""" Ta katse shi tun kafin ya aje numfashin maganarsa. """Ba ki haƙura ba kenan Innaye? Don darajar Allah kiyi haƙuri ki yafe min, kuma ki yafe ma Bintu. Ni na" "tabbata ko rantsuwa nayi babu kaffara da gan-gar baza ta hana ki abinci a gidannan ba. Bari in je in kawo miki abincin...""" """Da ma ka barshi Hafizu. Idan mun isa gida za mu samu abinda za mu ci.""" Ta sake katse shi da fuska mare walwala tana ninke ƴan kayayyakinsu da suke ajiye a gefen gadon. Bai sake cewa komai ba ya miƙe a hanzarce ya fice daga ɗakin. Ƙiris ya rage su gwabza karo da Zulaikha "da ta dawo hannunta ɗauke da kayayyaki, ko kallonta baiyi ba ya wuce da sauri kamar zai tashi sama." "Babbar yatsarta na hagu tasa a kunnenta, da wani irin salo na shaƙiyanci ta karkaɗa harshe da ƙarfi tana" mishi gwalo. "Karaf a idanunsa da ya juyo kamar an umarce shi da juyowa. Cije gefen baki yayi, ya ƙanƙance idanu" kamar zaiyi magana amma tuni ta faɗa cikin ɗakin a gaggauce ta barshi tsaye a gurin kamar mutum- mutumi. "Tunawa da abinda ke gabanshi yasa shi yin ƙwafa, ya karkaɗa kai sannan ya wuce da sassarfa zuwa cikin" "gidan. Yana shiga yaga Bintu ta fito daga ɗakinta ita da abokan aikinta su huɗu, da alamun rakiya za tayi musu." Da kalle shi da tattausan kallo mai bayyana matsananciyar soyayyarta a gare shi. A fuskarta babu alamun "damuwa ko misƙala zarratin, sai ma lallausan murmushin da take aika mishi." """Hi Dear... barka da dawowa.""" Ta faɗa da sanyin murya tana kallonshi fararen idanunta kar-kar masu ɗaukar hankalin duk wani lafiyayyen namiji. Duk yadda yaso ɓoye damuwar da ke zuciyarsa ya amsa mata kamar babu komai kasawa yayi. Daƙyar ya iya tausasa harshensa ya ce """Ki same ni a sama yanzunnan Bint, ina son magana da ke.""" Yana gama faɗin haka ya wuce ciki ba tare da ya saurari Aminiyar Bintu mai suna Raudha da take ƙoƙarin janshi da wasa kamar yadda suka saba a tsakaninsu ba. """Bint, ko dai in tsaya inyi ma Hafiz bayanin gaskiyar abinda ya faru ne? Kin ga fa kamar ya yarda da" "abinda wancan bulkut ɗin ƙanwar tashi ta faɗa...""" """Haba... Haba Raudha.""" Ta katse ƙawar tata da sauri tun kafin ta aje numfashi. """Kar ki wani damu kanki. Ke kanki kin san ba wancan jahilar ƙanwar tasa ba, ko ita baƙauyiyar tsohuwar" "bata isa ta shiga tsakiyar ginin kyakkyawan tubalin zaman takewa da yarda da juna da muka ɗauki tsawon shekaru biyar muna ginawa tsakanina da My Dear ba. Da kaina zan yiwa tufkar hanci... Ba sai na sake bari sun zo min gida sannan za ta zo min da wani munafurcinsu na ƴan ƙauye ba? Ni kam daman kin san ba wani zuwa can ƙauyen nasu nake yi ba, ko wani abu na dolen-dole ya faru da ya kamata in je ba" "na wuce awa biyu zuwa uku acan. Zan yi wa tufkar hanci very soon. Kar ku damu kanku.""" Ta amsa cikin fariya da ɗagawa. """To ke dai kiyi a hankali Bintu. Irin waɗannan ƙauyawan da kike gani kaska ne mashaya jini. Basu cika" "gane akwai babbar tazara tsakanin talaka da mai arziki ba sai an taka musu birki, an nuna musu iyakarsu" "da gasken-gaske. Amma... Ki iya takunki. Ko ɗan kaɗan ne kin san yana ƙaunar tsohuwarsa da ƴan'uwansa.""" Ɗaya daga cikin ƙawayen nata mai suna Aliya ta sake faɗin haka tana ƙara jinjina girman al'amarin da ya faru akan idanunsu. """Hmmm! Kar ku damu fa, kamar dai baku san hali na ba? Zan ɗauki matakin da ya dace, kun sani ba na" "barin matsala komai ƙanƙantarta ba tare da na kawar da ita ba.""" Ta sake amsawa cikin yanayin yarda da kai tana sakin murmushi. "Dariya suka yi gaba ɗayansu, sannan suka fice daga falon zuwa tsakar gidan in da motocinsu suke. Anan" ma sai da suka sake ɓata lokaci mai yawa suna jaddada ma Bintu lallai fa tasan yadda za tayi da gaggawa ta ɗauke hankalin Hafiz daga kan danginsa da iyayensa da suka kasance ƙauyawa. 3) "Duk da ce mata da yayi yana jiranta za suyi magana, bata je inda yake ba sai da ta sake ɓata fiye da" mintuna goma a gurin ƙawayenta suna ƙara tattaunawa duk akan matsalar su Innaye. "Ko da ta haura saman benen ɗakinsa ta fara shiga, a zatonta yana ciki, sai taga baya nan. Tana fitowa" "daga ɗakinsa shi kuma ya gaji da jiranta a nata ɗakin ya fito zuwa ɗakinsa a gaggauce, a rashin sani sukai gware da kawunansu." """Auuuuchhhh! My dear za ka fasa min kai... Zafi...""" Ta faɗi maganar a marairaice da shagwaɓa tana liliya goshinta inda sukai karo. """Yi haƙuri.""" Ya faɗa a taƙaice. Har lokacin fuskarsa babu walwala ko kaɗan. Tsintsiyar hannunta ya damƙa ya ja ta suka kama hanyar sauka daga saman benen """Mu je ki ba Innaye haƙuri. Abinda ya faru yayi matuƙar tunzurata ta yadda har ta sha alwashin barin" "gidannan a yau. Kuma ai kin ga hakan bai dace ba ko?""" "Ya jefa mata tambayar yana kallon cikin idanunta, fuskarsa damalmale da damuwa." "Matuƙar dauriya tayi gurin danne ɓacin ranta, har ta iya sakin taƙaitaccen murmushi." """Eh! Gaskiya kam bai kamata ta tafi yanzu ba. Ka san akwai wasu gwaje-gwaje guda biyu da aka yi mata" "wanda har yanzu sakamakonsu bai fito ba. Gobe dai in sha Allah nake sa ran fitowarsu sai in ga wasu magunguna ne zan ɗora ta akai.""" """To kin gani. Kuma saboda Allah ni da na ɗauko ta da nufin aƙallah ta samu ko wata uku tare da mu" don jikinta ya ƙara warwarewa sosai? Kawai yanzu cikin sati ɗaya ta fara zancen tafiya? Wai ma taya akai har hakan ta faru? Ina Rabi ta tafi da har aka kai irin wannan lokacin ba'a kai ma Innaye abincin rana ba "har wannan tsautsayin ya faru?""" "A daidai lokacin suka isa ƙofar ɗakin da aka sauki Innaye. Don haka Bintu bata ba shi amsa ba, ba" ƙaramin godiya tayi ga Allah ba da yasa suka isa ƙofar ɗakin a daidai wannan lokacin. Da tabbas babu abinda zai hana ta fashewa da kuka idan ta buɗe baki da nufin ba shi amsoshin tambayoyinsa. A zuciyarta take ta tufka da warwarar maganganunsa 'Wata uku? Saboda Allah a ina yake nufin wannan tsohuwar za ta zauna har na tsawon watanni uku? "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Sai a yanzu take da na sanin amince masa tun farko da ya ce mata zai ɗauko mahaifiyarsa a duba lafiyarta. Da kawai tubure masa tayi da cewar ba sai ya ɗauko ta ba, a matsayinta na likita gara ta bishi can ƙauyen ta duba ta, in yaso daga baya ta tattara duk magungunan da" ciwon tsohuwar ke buƙata ta bashi ya kai mata. "Abu ɗaya tayi tunani da yasa ta amince da ɗauko tsohuwar, shekarunsu biyu ne da aure. Kuma a cikin" "shekaru biyun ko sau ɗaya tsohuwar bata taɓa taka ƙafafunta zuwa gidan ba, hana rantsuwa dai ƴan'uwansa mata da suka kasance masu bala'in naci da takura sun je har sau uku. Su ɗin ma karon farko ne kawai ta tarbe su da fara'a, karo na biyu da na uku kuwa tarba ne tayi musu irinna lallai idan suna da hankali za su janye jikinsu daga na ta da na mijinta, irin tarbar nan ta kora da hali ya fi kora da sanda." "Kuma haƙarta ya cimma ruwa domin idan ba ta manta ba, watanni bakwai kenan babu wacce ta sake" tako ƙafarta zuwa cikin gidan. "Gare ta hakan ta fi nono fari, ba ta da niyyar raba su da ɗan'uwansu, amma tana so lallai su tsaya iya" "limit ɗin su. Su gane tsakanin shi da Allah ya tsamo shi daga rayuwar ƙauyen ƙayau zuwa cikin birni, yayi zuzzurfan karatun boko, Allah yayi mishi gyaɗar dogo ta hanyar samun babban aikin gwamnati da gaggawa, ya tara maƙudan kuɗaɗe cikin ƙanƙanin lokaci, ya tamfatsa babban gida sannan ya auro ta ƴar manyan mutane bayan shekaru biyar da suka kwashe suna buga zazzafar soyayya akwai tazara mai ƙololuwar yawa a tsakaninsu. Baya ga duk waɗancan ni'imomin da suke ciki ita ɗin babbar likita ce da take aiki a babban asibitin Abuja. Taya a matsayinta na wayayyiyar mace ƴar boko ma'aikaciyar lafiya da ta san illar yawan cuɗeɗiya tsakanin ɗan birni da na ƙauye za ta yarda waɗannan gidadawan mutanen da" suke a matsayin dangi da iyayen mijinta su dinga mata jela a gida? "Shi dai da yake nasu kuma suka zama dolenshi tana ɗaga mishi ƙafa lokaci bayan lokaci yaje gurinsu," amma fa ko kwana idan ya wuce ɗaya ba ta taɓa yarda yayi. Kuma yana dawowa tun kafin ya taɓa komai na amfanin gidan take haɗa mishi ruwan wanka da sinadarai masu kashe ƙwayoyin cuta ta sille shi da kanta. Ba ta samun nutsuwar zuciyarta har ta iya rungumarshi sai bayan ta shafe shi da turarukan jiki na maza masu mabanbantan ƙamshi...' """Heyyyyy! Tunanin me kike yi haka?""" Hafiz ya katse mata zuzzurfan tunanin da ta afka ciki ta hanyar girgiza kafaɗunta da ɗan ƙarfi. Firgigit! Ta dawo daga duniyar tunanin da take yi. """Na'am! Iye? My Dear magana kake yi?""" Ta jefa mishi tambayar a daburce. Bakinshi ya matsar kusa da kunnenta sannu a hankali ya raɗa mata maganganu masu daɗi da taushi da "za tayi amfani da su gurin ba Innaye haƙuri. Sai da ta gyaɗa mishi kai alamun ta ji, kuma ta fahimta" "sannan ya kama hannun ƙofar ɗakin ya murɗa, suka shiga ciki a tare bakunansu ɗauke da sallama." Kallo ɗaya Zulaikha tayi musu tayi saurin wawurar hijabinta da ke ajiye gefe ɗaya ta zura a jikinta. Tsabar "sauri ma a baibai ta saka, bata damu da hakan ba ta juya musu baya tana kallon bango, ciki-ciki ta fara" ƙunƙuni ƙasa-ƙasa bakinta a gaba yadda babu mai jin abinda take cewa sai ita kaɗai. Daga Bintu har Hafiz babu wanda ya kalli Zulaikha ballantana su damu da abinda take yi. Kai tsaye gaban "Innaye da take zaune a gefen gado suka ƙarasa, ba tare da wani ƙyama ko tsantseni ba Hafiz ya zube a gabanta gwuyawunshi a ƙasa. Ita kuwa Bintu ƙasa-ƙasa ta ƙarewa kan tile ɗin kallo, duk da a share yake tas kuma a goge har yana ɗaukar idanu ta kasa zama ko kuma tasa gwuiwa a ƙasa kamar yadda mijinta" yayi. "Sai da ta runtse idanu, ta cije leɓe, kafin ta iya tsaro maganganun kamar yadda ya faɗa mata." """Maganar komawarki gida ma don Allah kiyi haƙuri, ki ƙara mana lokaci kaɗan kafin ki koma. Kin ga" "har yanzu ban gama tattara sakamakon gwaje-gwajen da aka yi miki a asibiti ba. Kuma ko gobe ma idan zan tafi tare za mu fita, akwai wani gwaji da za'a sake miki na ciwon suger, kafin a karya ake yin shi. Shi yasa za mu fita da wuri, don Allah ki bar maganar komawa mu tattali lafiyarki tukunna. Kin ga babu daɗi ace kin taho da ciwo kuma ki koma da ciwon ba tare da an samu sauƙi ba. Ki yi haƙuri don Allah, in Allah" "ya yarda baza'a sake samun matsala makamanciyar wacce aka samu yau ba.""" Shiru Innaye tayi kamar baza ta amsa roƙon ba. Hafiz har ya buɗe baki zai cigaba da magiya daga inda Bintu ta tsaya sai ya ji Innaye ta ce """Zuwa yaushe za'a gama duk gwaje-gwajen a bani magunguna?""" A tare duk su biyun suka yi magana. Hafiz cewa yayi """Bazai wuce nan da wata biyu ba in Allah ya yarda.""" Ita kuma Bintu cewa tayi """Nan da kwanaki goma ma an gama komai Innaye.""" "Ba Innaye da mamaki ke neman sumar da ita a zaune ba, hatta Zulaikha sai da ta juyo da wani irin" "mamaki sosai a fuskarta tana ƙare musu kallo. Su kansu kallon junansu suke yi, irin kallon nan mai" "bayyana rashin jin daɗin yadda aka samu banbanci a maganganunsu, kuma a daidai gaɓar da ya kamata su haɗa baki gurin furta abu ɗaya." "Kallon baki kyauta min ba Hafiz ya jefa mata, sai kuma ya duƙar da kai a kunyace yana jin babu daɗi sosai" a zuciyarsa. "Ko yana so ko baya so ya san Innaye da maganar Bintu za tayi amfani, tunda dai ita ce Likita. Amma Allah" "ya sani yana matuƙar son zama da mahaifiyarsa na ɗan lokaci, shi yasa ya faɗi maganar watanni biyu, domin a daidai wannan gaɓar da zaman gidansa ya sanewa Innaye a zuci ya san zancen lafiyarta ne kawai zai sa ta danni zuciyarta ta ƙara daɗewa yadda yake so." "Ita kuwa Bintu ko a jikinta, tana sane ta ce nan da kwanaki goma duk da kafin shigowarsu Hafiz ya nuna" mata buƙatarshi na son mahaifiyarsa ta daɗe a gidan. Amma tun a yanzu cikin sati ɗaya an fara samun irin wannan gagarumin matsalar ta ya za tayi saken da "zamansu zai ƙara tsawo a gidan? Gaskiyar magana shi ne duk abinda za'a yi ma tsohuwar a asibiti bazai wuce kwanaki goman ba za'a gama komai. Don ma tun zuwansu bata yi himma akan komai na binciken lafiyar tata ba ai da yanzu wani zancen ake yi ba wannan ba. Da a gaggauce za ta haɗa mata duk magungunan da take buƙata su ƙara gaba, Umma ta gaida Assha. Ba'ayi wata halitta a duniya da za ta zo" lokaci ɗaya ta dagula zaman lafiyar da ta ɗauki lokaci tana shimfiɗawa a gidan aurenta ba. "Aka ce abinda babba ya hango, yaro ko ya hau dutsen dala bazai taɓa hangowa ba. Duk su biyun Innaye" "ta fahimci inda suka sa gaba, hakan ne ma ya saka ta sakin wani ɗan taƙaitaccen murmushi." """To shi kenan. Allah ya kaimu nan da kwanaki goman. Bayan nan ƙarin kwanaki huɗu za muyi in Allah" "ya yarda za mu koma inda muka fi wayau.""" """Nan da sati biyu kacal Innaye?""" Hafiz ya tambayeta da sanyin murya. """Eh! Nan da sati biyu idan Allah ya kaimu Hafizu. Zuwa lokacin ka ga satinmu uku kenan. To ina laifi? Ni" "da ka ɗauko ni da wayan bai fi in kwana huɗu ba ka mayar da ni gida ga shi yanzu zanyi har sati uku? Ai babu laifi ko?""" """Ƙwarai kuwa Innaye. Mun gode Allah ya ƙara lafiya.""" Bintu ta faɗa a gaggauce. Har ta miƙe za ta fice daga ɗakin ba tare da jiran komai ba karaf! Idanunta suka faɗa kan sababbin "kulolin abincin Mijinta da ke ajiye gefe guda. Da mamaki sosai ta ƙara ware idanu tana kallon kulolin, eh" tabbas su ne. Kulolin da duka-duka basu wuce sati uku da tayi Odarsu suka iso akan naira na gugan naira har dubu ɗari da ashirin ba. "Shi kan shi Hafiz da ya kasance miji mafi soyuwa a zuciyarta, wannan shi ne karo na biyu da ta zuba mishi" abinci a cikin kulolin. Amma saboda tsabar rashin adalci da rashin sanin darajar abu mai tsananin tsada ya rasa inda zai kawo mata haɗaɗɗun kulolinta sai gurin tsohuwar baƙauyiyar Mamarsa da jahila fitsararriyar mara kunyar ƙanwarsa? Lokaci ɗaya idanunta suka cicciko da hawaye. A jere ta haɗiyi wasu kauraran miyau har daki biyu masu barazanar yaga mata maƙogwaro don tsabar baƙin ciki da takaici. A haukace ta nufi gurin kulolin za ta ɗauka ta wuce da su sai jin muryar Zulaikha tayi a ladabce kamar ba ita ce ke yi mata magana a tsaitsaye ba tana cewa """Aunty Bintu bamu ci abincin ba fa. Daman Yaya ne ya kawo ma Innaye to kuma zan zuba mata kenan" "kuka shigo. Kije kawai, idan mun gama zan kai miki kulolin kicin.""" Duk yadda ta so daure ɓacin ran da ya cunkushe zuciyarta kasawa tayi. A fusace ta waiga ta aika ma da "Zulaikha wani kakkausan kallo tana zazzaro idanu kamar za ta haɗiɗiyeta. Karaf! Akan idanun Innaye da Hafiz da tun da Zulaikha ta fara magana hankalinsu ya koma kan abinda yake faruwa. Ta buɗe baki za tayi magana a bazata wani ƙaƙƙarfan kuka ya taho mata, ba shiri ta fice daga ɗakin da sassarfa" hannayenta biyu dafe da bakinta don kar ta fashe da kuka a gaban waɗanda take ma kallon maƙiya. Shiru ne ya ratsa tsakaninsu bayan ficewarta. Duk sun fahimci dalilin fusatarta tunda dai su ba yara bane. Amma tsakaninsu an rasa wanda zai fara cewa uffan! sai can bayan mintuna uku Innaye tayi ƙarfin halin cewa. """Da ganin kulolinnan sababbi ne, kuma za suyi tsada sosai. Ko kusa basu yi kama da irin kular da aka" "saba zubo mana abinci a ciki ba. Me yasa ka ɗauko mata sababbin kuloli ka kawo mana abinci a ciki Hafizu?""" """Innaye... waɗannan kulolin fa da sunan nawa ta saye su. Saboda Allah menene aibu don na ɗauko" "kular abincina na kawo ma mahaifiyata?""" Ya ƙarasa da tambayar ƙarara fuskarsa na bayyana rashin jin daɗin canjin fuskar da matarsa ta nuna kan abinda bai taka kara ya karya ba. """Uhmmmm!""" Ta ja nannauyar ajiyar zuciya ta sauke. Muryarta na fita sannu a hankali ta cigaba da cewa """Hafizu kenan. Baza ka gane abinda nake ƙoƙarin nusar da kai ba. Amma don Allah ina roƙonka daga" "yau, kar ka sake irin wannan. Tunda dai ana zubo mana abincin, duk ranar da ba'a kawo akan lokaci ba in sha Allah zan tura Auta ta ɗauko, tunda dai ta san kicin ɗin. Ta shi kaje can ɓangarenka ka huta. Kayi" "ƙoƙarin daidaitawa da matarka, kar ka kuskura wannan abin da ya faru ya janyo saɓani a tsakaninku.""" """In sha Allah zan kiyaye Innaye.""" Ya amsa shi ma tasa muryar na fita a sanyaye. "Har ya kama hanyar ficewa daga ɗakin ya waiga yana kallon Zulaikha, akayi arashi karaf suka haɗa idanu." A fakaice ya watsa mata harara. """Kina ji na? Daga yau ki tabbatar kin kiyaye duk abinda zai kai ki can ɓangaren, idan kika sake shige ma" "Matata na rantse da Allah ba abinda zai hana ni goya mata baya ta zane ki ciki da bai.""" Ko kusa bai yi kuskuren saka idanunsa a cikin na Innaye ba don ya san bazai sha da sauƙi ba. Fuuu ya fice daga ɗakin kamar zai tashi sama. Kwaɓa-kwaɓa tayi da fuska tana kallon Innaye ta ce """Innaye kina jin shi ko...?""" """Ƙyale shi Auta. Duk ranar da matarsa ta sake dukanki ba tare da kin mata komai ba ko ban gama" "karɓan maganin ba a wannan ranar za mu bar gidannan. Rabu da su, in Allah ya yarda munyi zuwan" "farko kuma na ƙarshe.""" Ta ƙarasa maganar a raunane. Irin raunin nan da ke fita tun daga ƙarƙashin zuciya. 'Ba tun yau ba Ƴan'uwan Hafiz suka sha zuwa mata da ƙananun maganganu kan yadda ƙarara Bintu "take nunawa a fili tana ƙyamarsu. Su da suka zo gidan ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba, zuwan farko ne kawai suka koma da daɗin rai. Na biyu da na uku duk labaran da suka koma mata da shi ba mai daɗi" bane. Kuma babban abin haushi da takaici shi ne duk irin abubuwan da take nunawa da wanda take yi a aikace Hafiz bai taɓa nuna ɓacin rai ko damuwarsa akan hakan ba. Ita kuma da yake Dattijuwa ce ta gaske da aka shaide ta da tsananin haƙuri bata taɓa mayar da hankalinta ko ta saka ma ranta damuwa kan irin maganganun da suke yi ba. Zulaikha ita ce mai biye "musu, tai ta ƙara ingiza su tana tuna musu irin abubuwan da Bintu ke nunawa wanda ƙarara duk mai hankali zai fahimci ƙyamarsu take yi." """Ni fa shi yasa tun ranar farko da Yaya ya kawo ta sam! bata kwanta min arai ba...""" Da Zulaikha ta fara irin waɗannan maganganun a tsawace Innaye ke korarta daga ɗakin. Su kuma Yayyin nan take za ta kwaɓe su ta nuna musu ɓacin ranta. Kamar dai abubuwan basu taɓa "damunta ba. Duk abinda ke faruwa idan Bintu taje can kawar da kai take yi tayi kamar bata gani ba kuma bata damu ba, sai dai ma tayi ta bin Bintun da murmushi a matsayinta na matar shalelenta Hafizu." Kamar misalin rashin shan ruwan ɗakinta da Bintu ke yi. Kuma duk tsaftar dadduma ko sabuntar "tabarma idan tasa aka shimfiɗa mata da umarnin ta zauna ba ta taɓa zama sai ta ɗauko wani sabon dadduma daga mota ta shimfiɗa sannan za ta zauna tana yamutsa baki a fakaice, domin sam ba ta hawa" kan kujerunta da suka fara kwana biyu. Duk da ginin gidansu da ɗakunan gidan yana daga cikin gini mafiya kyawawan gini na bulo da bulo a "ƙauyen, saboda Hafiz ya sa an gyara gidan sosai. Kuma ya gyara mata ɗakunanta ya zuba mata sabbin kayan ɗaki irin dai na tsofaffi masu gata. Bintu ta dinga kalle-kalle kenan tana ɓata fuska, alamun dai" komai bai mata yadda take so ba. "Ruwan sha, abinci, kayan ciye-ciye dangin ƙwalam da maƙulashe da Bintu za ta buƙata na ƴan awannin" da za tayi a ƙauyensu duk da abinta take tafiya a cikin mota. Wani tozarci da wulaƙanci da tayi musu da yasa ta ƙara ficewa a zuciyarsu wanda har yau sun kasa "mantawa shi ne haihuwar Aunty Balira tayi. Da rawar jiki Hafiz ya ɗauki Bintu suka je har gidan Yayar tasa barka. Aunty Balirar ita ce babbar ƴa a ɗakin Innaye. Shekarunta ashirin da aure Allah bai ba ta haihuwa ba sai a wannan lokacin. Shi yasa duk wani makusancinsu yake ɗokin haihuwar, saboda abu ne" da aka daɗe ana nema har an fidda rai sai ga rabon ya samu. "Ko da suka isa, sai suka tarar yaron yayi kashi, an cire mishi nafkin ana wanke mishi kashin a cikin baho" "nan tsakar ɗakin. Da saurin gaske Bintu ta sake gyara zaman face mask ɗin da ke hancinta. Ta sake tamke fuska tamau, ta kawar da kai tana shan ƙamshi. Daga irin zaman da tayi ɗofane a bakin kujera kamar wacce ke kan ƙaya za'a gane a takure take ƙwarai. Shi kanshi zaman, kafin tayi sai da Hafiz ya bata umarnin ta zauna mana, fuskarsa babu walwala ko misƙala zarrah. Shi yasa ta zauna tana jin babu daɗi a" "ranta, a zuciyarta take ta addu'ar Allah yasa kar ta kwashi kuɗin cizo ko ƴan matan kaduna a jikin kujerar." "Da rawar jiki Ladidi wacce Hafiz yake bi ta gama wanke ma jariri kashi, aka naɗe ɗuwawunshi da sabon" "fallen zani aka miƙa ma Bintu. Da farko kamar ba za ta karɓe shi ba, ko tunanin me tayi? Oho!" Sai ta buɗe jakarta ta zaro safar hannu ta saka sannan ta karɓi jaririn a wulaƙance. Irin wasa-reren riƙonnan da ko jikinta bata yarda jinjirin ya taɓa ba. "Kamar za ta yar da shi, daga ƙarshe dai cikin sauri Hafiz ya karɓi ɗan yana mata tsiyar a matsayinta na" "babbar likita bata iya ɗaukar jariri ba, zai ga wanda zai dinga ɗaukar mata nata idan ta haifa." """Dear! Ka san jaririn da zan haifa zai kasance dabanne da duk wasu jarirai da ka taɓa gani a rayuwarka." "Ko shugaban ƙasar Sa'udiyya ne ba zaiyi ƙyamar taɓa ɗana ba saboda tsananin kyawu da tsaftar jikinsa da na muhallin da muke ciki.""" Amsar da ta bashi kenan a gaban kowa ba tare da damuwar maganar za ta ma ƴan'uwansa daɗi ko akasin haka ba. "Kamar bai ji abinda ta ce ba, haka Hafiz ya nuna, sai ma ya ƙara mayar da hankali kan addu'o'in da yake" karantawa ƙasa-ƙasa yana tofa ma jaririn. "Aunty Rakiya da ta kasance mara haƙuri daga cikin ƴan'uwansa, har ta buɗe baki za ta ba Bintu amsa da" sauri Aunty Balira ta mintsine ta. A dole tayi shiru ba don ranta yana so ba sai don bin umarnin na gaba. "Ko da suka tashi tafiya, dubu ashirin ɗin da ta ajiye da cewa a siya ma jariri pampers babu wanda ya ce" "uffan! Balle tasa ran samun godiya kamar yadda suka saba yi mata sadda take amarya jikinsu na ɓare- ɓare idan tayi musu alkhairi, kamar ba yayyen mijinta ba." "Ko da suka ba Innaye labarin, bata nuna ɓacin ranta ba sai haƙuri da ta basu da kalamai na kwantar da" hankali. A ƙarshe ta ɓuge da nunar musu da illar miƙa ma Bintu jaririn ba tare da sun sake yi mishi nafkin ba. """Ku kalli irin suturun da take sakawa a jikinta mana? So kuke yaron yayi mata fitsari a jiki? Idan yayi" mata fitsari duk cikin kayan sakawarku kuna da kwatan-kwacin wanda za ku bata ta saka a jikinta? Haka dai ta kore maganar ba tare da ta nuna musu ta ji babu daɗi kan abinda ya faru ba. Ko da suka ce mata sun yanke zuwa gidan ɗan'uwan nasu idan ba da wani ƙwaƙƙwaran dalili na dolen- dole ba bata takura su da cewar su cigaba da zuwa ba. """Daman in banda da abinku, jelar tafiya daga nan Faƙo, zuwa Kaduna, a sake hawa mota zuwa Abuja ai" "ba nan kusa bane. Ku ɗaga ƙafan ya fi, tunda dai Allah ya sa shi Hafizun yana ƙoƙarin zuwa akai-akai ai" babu laifi. Idan kuma wata buƙata ce ta gaggawa kuke da ita sai ku tuntuɓe shi a wayar zamaninnan da ta samar ma talaka sauƙi. Da katin naira ɗari za ku isar da saƙon da idan zuwa za kuyi sai kun kashe kuɗin "mota fiye da dubu biyar.""" Da waɗannan zantukan ta sake ƙarfafa musu gwuiwar janye ma zuwa gidan Hafizu akai-akai. Da gaskiyar Bahaushe da yace gani ya kori ji. Kwanaki uku na farkon zuwanta gidan a cikinsu kawai za ta "ƙaras da marari da ɗokin ganinta a wajen matar gidan. A bayan waɗannan kwanaki uku, duk abubuwan" da suka biyo baya haƙuri kawai take yi tana kawar da kai. Zulaikha da ta kasance mara haƙuri kamar fitar zawayi kuma tun dama can ba'a shan inuwa ɗaya da matar Hafizun ita take ta cika tana batsewa kan abubuwan da suke gani na rashin kyautawa. Har zuwa "yau da tayi gaban kanta ba tare da saninta ba ganin har ƙarfe huɗu na yamma ba'a kawo musu abinci ba tun bayan karin safe, ta shiga har can cikin gidan har wannan abun ya faru.'" """Auta?""" Ta kira sunan Zulaikha bayan ta katse tunanin da take yi ta mayar da hankalinta kanta. """Na'am Innaye.""" Ta amsa tana cigaba da zuba farfesun naman kaza kan soyayyar shinkafar da ta zuba cike dam da faranti. """Kin ga matar gidannan? Ki fita daga harkar ta. Duk abinda take yi kanta take ma. Roƙo na gare ki don" Allah don Annabi ki lallaɓa ki kawar da kai kamar yadda Yayyenki suka yi a kanta har mu koma can inda muka fi wayau ba tare da mun janyo ma kanmu abin magana ba. Ko so kike a fara ya-maɗiɗi da mu a jakar magori ana cewa Uwar miji da ƙanwar miji sun zo daga ƙauye sun zama sanadiyyar mutuwar "aure?""" """To ayi mana Innaye. Wa yake tsoron a mutu? Saboda Allah irin abubuwan da matar gidannan take yi" "mana ita tana kyautawa kenan? Ki duba fa yadda take ɗaukarmu a wulaƙance. Shi Yaya haka yake ma Iyayenta da ƴan'uwanta? Innaye ko kin san har yau ban kai matsayin da matar nan za ta dinga kiran sunana kai tsaye ba sai dai ta ce min Ke jahila, ko ke baƙauyiya, ko ke dabba? Saboda Allah Innaye don Allah yasa an haife ta a cikin babban birni Abuja ni an haife ni a ƙauyen-ƙayau Faƙo sai ta dinga tozarta ni tana wulaƙanta ni? Na rantse da Allah idan su Aunty Rakiya sunyi haƙuri da ita ni kam bazanyi ba, daga" "yanzu bazan sake ɗaga mata ƙafa ba. Tunda dai ita ba ta da mutunci. Sai dai duk abinda zai faru ya faru.""" Ta ƙarasa maganar idanunta ciccike da hawaye na gaske ba na taɓara ba kamar yadda take yi a "mafiyawancin lokuta. Gefen hijabin jikinta ta kama ta fara sharar ƙwallah, da alamun tozartata da Bintu" take yawan yi ya daɗe yana ci mata tuwo a ƙwarya. "Ita kuwa Innaye shiru tayi, ta rasa ta cewa. Zuciyarta cunkushe da matsanancin damuwa, domin sai a" yanzu da ta ƙara karantar halayen Bintu duk wasu maganganu da ƴaƴanta suka sha faɗa na ƙorafi a baya ke dawo mata daki-daki a cikin zuciyarta. Kamar dai a lokacin abubuwan suke faruwa. Daƙyar ta iya yakice tunanin da take yi ta fara rarrashin Zulaikha da hawaye suka kasa tsayawa a "idanunta, tana sharce wasu suna sake gangarowa." Duk ƙamshi da kyawun abincin a idanun Zulaikha ta kasa yi mishi mugun ci kamar yadda ta ƙudurtawa zuciyarta da farko. Daga ita har Innaye tsakuran abincin suka yi. Da gangar ta ƙi mayar da kulolin ko bayan sun gama cin abincin. """Ko na mayar ma ba ci za suyi ba. Wata ƙila zubarwa za tayi saboda ƴan ƙauye sun ɗiba sun rage. Da" "tayi wannan almubazzarancin kuwa gara mu ajiye da daddare mu ci, abinda ya rage da safe mu ƙarasa" "cinyewa sai in mayar mata da kulolin da take ta sauke zafafan numfarfashi kamar za ta haɗiyi zuciya a kansu.""" """Ko da safen ma ai sai dai ke ki ci. Kin manta ta ce gobe za ta kaini asibiti da safe kafin in ci komai ayi" "min gwaji?""" Innaye ta faɗa hankalinta na kan Zulaikha da take sakacen haƙorinta da tsinken-tsinyiya. """Allah ya kaimu goben. Sai kiyi ƙoƙari ki cika cikinki dam anjima da daddare, tunda goben bamu san iya" "wane lokaci za ki ɗauka kafin ki karya ba. Ai wallahi gara dai a gama komai na asibitin nan a baki magunguna mu koma gida. Da birnin da komai na cikinsa Wallahi sun gundure ni, ƙauyen nan dai da take yiwa kallon banza da ƙyama ni shi ne abin alfaharina. A guri na ya fi Abuja sau miliyan ɗari.""" 6) Shi ba yaro bane. Ya san ya kamata ya tuhumi Bintu akan abubuwa da dama da take yi ma ƴan'uwansa "da mahaifiyarsa. Abubuwan da tun tana yi a fakaice ba ya lura, a yanzu gaba-gaɗi take aikatawa ba tare da shakkar idanunshi ba. Kawai yana yi mata uzuri ne saboda dalilai mabanbanta da shi kaɗai ya barwa" zuciyarsa. "Marin da tayi ma Zulaikha ba abinda ya shafe shi bane, saboda ya san halinta kamar yunwar cikinsa. Ba" "Bintu da take matsayin matarsa ba, ko shi Zulai ta daɗe tana shiga mishi hanci da ƙudundune, aduk sa'adda yayi yunƙurin fyatota sai Innaye ta taka mishi burki. Da wannan dalilin yasa ba ƙaramin farin ciki yayi ba da Bintu ta tsinkawa Zulaikha mari, a ganinsa, hakan zai rage kaifin rainin yarinyar a gare shi da" matarsa. "Amma duk da haka, ya san ya kamata yayi ma Bintu ƙwaƙƙwaran tuhuma akan sakaci da abincin" "mahaifiyarsa. Ya kamata ya tuhume ta akan yadda ya faɗa mata yana so mahaifiyarsa tayi watanni a gidan, amma taƙi yi ma Innaye dabarar cewa binciken lafiyarta zai ɗauki lokaci mai tsawo. Ya kamata ya tuhume ta akan yadda ta nuna ɓacin ranta don kawai ya ɗauki kulolin abincinsa da abincin ciki ya kaiwa mahaifiyarsa... Tuhume-tuhumen suna da yawa, amma a yanzu dai, waɗannan su ne abubuwan da suka faru akan gaɓa. Saboda shi ɗin ba mutum ne da ya cika riƙe abubuwan da za su janyo mishi jin babu daɗi" a zuciyarsa ba. "Ko da ya shiga cikin falonsu, zuciyarsa cike take da niyyar zai yima Bintu waɗancan tuhume-tuhumen." Amma yana yin tozali da ita zaune akan kujera tana sharar ƙwallah. Sai yaji duk abinda ya ƙullo a ransa "ya bi rariya da gudu ya wuce, babu abinda ke gaban idanunsa da zuciyarsa sai Bintu da damuwar da ya saka ta kuka. Wani abu da bai taɓa gani ba tun da suka zama mallakin juna tsawon shekaru biyu." """Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!!! Sweetheart? Subhanallahi! Me ya faru? Wa ya rasu?""" "Ya jera mata tambayoyin hankalinsa a tashe ainun. Da sassarfa ya ƙarasa kusa da ita, sannan yasa" hannuwa biyu ya tattagota zuwa jikinsa gaba ɗaya ya ruƙunƙume yana sake jera mata tambayar me yake faruwa? Waye ya rasu? Domin duk a tsammaninsa rasuwa kaɗai rasuwar ma na makusanci sosai shi zai sa Bintu zama tana risgar kuka. Sai dai wani abu da ya sake ɗaga mai hankali zuwa ƙololuwar tashi duk irin maganganu da tambayoyin "da yake mata bata amsa shi ba. Hallau kuma bata tsayar da kukan ba. A yadda yake ji, kamar ya ɗora hannu biyu aka ya fara rusa ihu. Kawai sai ya fara tattaɓa jikinta da tunanin ko ba ta da lafiya ne?" "Yanayin jikin na ta daidai ne, babu zafi ko kaɗan. Don haka ya kawar da tunanin ko rashin lafiya ke" "damunta. Can-cak ya ɗauke ta kamar jaririya ya nufi cikin ɗakinsa, ba tare da ya san taka-maimai abinda zaiyi mata ya tsayar da kukan da take yi kuma ya kore mata damuwar zuciyarta ba." "Kamar ɗanyen ƙwai sabon sakawa, haka ya ajiye ta sannu a hankali akan faffaɗan gadonsa ƙirar italiya da" "ya mamayi fiye da rabin ɗakin. Maɓallan rigar jikinsa ya fara cirewa sauri-sauri har ya zare rigar daga jikinsa. Kan gadon ya koma, jikinsa babu inda ba ya rawa ya sake tarairayota zuwa jikinsa, baiyi wata- wata ba ya haɗe bakinsu waje guda, hannayensa biyu tallabe da fuskarta, ya saka idanunsa cikin nata yana aika mata da wasu zafafan saƙonni waɗanda ita kaɗai za ta iya fassarawa." "Tun tana mutsu-mutsun ƙwacewa har ta bada kai bori ya hau. Tun hawayen suna sauka da gudu, har" "suka koma sauka sannu a hankali, daga bisani ma suka tsaya da zuba, sai ajiyar zuciya take saukewa akai- akai. Bai saki fuskarta ba sai da ya tabbatar jikinta ya mutu murus, sannan ya kwantar da kanta a ƙirjinsa yana shafa yalwataccen gashin kanta da yake fitar da daddaɗan ƙamshi." """Wa ya taɓa min zuciyata?""" """Kai ne!""" Ta amsa mishi ba zato ba tsammani da wata siririyar murya mai ɗaukar hankali. """Ni kuma? Me nayi?""" "Ya sake jefa mata tambayoyin yana ɗan ware idanunsa kaɗan, alamun amsar na ta ya bashi mamaki" ƙwarai da gaske. "A karo na barkatai ta sake jan nannauyar ajiyar zuciya ta sauke. Shiru tayi kamar baza ta amsa shi ba, a" zuciyarta take ta jujjuya maganganun da za ta karanta mishi ba tare da ya zarge ta da ƙyamar mahaifiyarsa ba. """Ina jin ki Sweetheart! Faɗa min laifin me nayi miki da har yasa kika zauna tsawon lokaci haka kina" sharɓan kuka. Abinda bai taɓa faruwa ba a tarihin zamantakewar aurenmu. Abu ɗaya dai da nake so ki "dinga tunawa ako da yaushe shi ne, Hafiz, mutum ne mai tsananin ƙaunar matarsa Bintu. Da gangar" "bazai taɓa yin abinda zai taɓa zuciyarta ba. Kina sane da haka ko?""" "A hankali ta ɗaga mishi kai alamar ta sani. Cire kanta tayi daga ƙirjinsa, ta ɗaga fuskarta tana kallon tasa." Sannu a hankali ta saka idanunta da suka canja launi saboda kuka a cikin nasa idanun. Ta riƙo "hannayensa biyu a cikin na ta, sannan ta buɗe tsukakken bakinta a tausashe ta fara magana har lokacin bata cire idanunta a cikin nasa ba." """A irin koyi da tarbiyar da Mummyna ta ba ni, ta nunar mini miji yana da ƙololuwar daraja a gurin" "matarsa fiye da komai da kowa a rayuwarta. Idan na ce komai kuwa ina nufin komai, cikin komai da kowa ɗin nan kuwa har da iyayenta. Kuma idan ba na manta ba har a addinance ma haka ne, right?""" """Haka ne Beby""" Ya amsa mata yana jin wani shauƙi da girma na ƙara lulluɓe zuciyarsa. "Ko kusa bai fahimci inda maganganunta suka dosa ba, don haka ya ƙara buɗe kunnuwansa na basira" "yana sauraren inda za ta kai shi. Abu ɗaya dai da zai ƙaras da maganganunta ba na zafi bane shi ne, yadda tun a saɗarar farko na fara maganarta zuciyarsa ya ƙara cika da tumbatsa da alfaharin samun mace ta gari kuma mai tarbiya irin Bintu. Irin matar da hadithi ingantacce ya tabbatar duk namijin da ya same ta an bashi rabin addininsa, sai kuma ya ji tsoron Allah a sauran rabin.Ta sake ɓata wasu daƙiƙu masu ɗan dama tana ƙara tsara irin maganganun da za ta faɗa masa, waɗanda take da tabbacin za suyi kwanciyar girma da muhimmanci a zuciyarsa. Kuma zai ƙara yarda da gasken gaske ita ɗin fa mai son shi da ƙaunarshi, muhimmanci da girman da yake da shi a gurinta yasa sam ba ta iya haɗa al'amarinshi da na" kowa. """Ina jin ki Sweetheart""" Ya sake faɗa a tausashe don dawo da ita daga duniyar tunanin da ya lura tana ƙoƙarin lulawa. 7) "Lumshe manyan idanunta tayi a hankali, can kuma sai ta buɗe sannan ta saki wani nannauyan numfashi." """A gidanmu, na taso na ga Mummy ba ta haɗa al'amarin Daddy da na kowa. Al'amarin Daddy da duk" wani abu da ya shafe sa ako da yaushe kuma ko wani lokaci yana kasancewa na musamman ne a gurinta. "Da irin wannan tarbiyar ta raine mu, wannan yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa duk wani al'amari na ka" "yana da matuƙar muhimmanci a gurina. Amma na lura kamar dai kai ba na maka gwaninta, ba na burge ka, kamar ma ka raina yadda nake ƙoƙarin sauke nauyin hakkinka da Allah ya ɗora min...""" "Tayi ɗan shiru tana mayar da numfashi a raunane. Ya buɗe baki zaiyi magana da sauri ta girgiza mishi kai," ta ƙara da ɗora yatsarta manuniya akan laɓɓansa. Tayi mar-mar da ƙwayoyin idanunta sai ga wasu siraran hawaye sun ziraro daga cikinsu. """Don Allah Dear ka faɗa min, ta ina ne nake kuskure maka? Zuciyata baza ta iya jurar ganin yadda nake" "tattalinka da ƙoƙarin faranta maka kai kuma kana gwasale ƙoƙarina ba. A tunanina, ɓangaren iyaye" daban na matarka daban! Duk mu biyun muna da girman haƙƙi a kanka. Me zai sa ka dinga ƙoƙarin nuna "musu ni ɗin ba kowan kowa bace a gurinka?""" "Ta ƙarasa mishi da tambayar wani raunataccen kuka na ƙwace mata. Kifa kanta tayi a ƙirjinshi, ta cigaba" da rera kukan da ya ƙarasa kassara duk wani ɗan sauran karsashi da ƙwarin gwuiwa da suka rage masa. Ya nemi kalamai a bakinsa ya rasa ɗif! Kamar ɗaukewar ruwan sama. Tsawon wasu daƙiƙu ya kasa ce "mata komai, duk kuwa da yadda yake jin zafi sosai a zuciyarsa saboda yadda take rera kuka, kuma ya tabbatar wannan hawayen suna fita a dalilin wani abu na rashin kyautawa ne da shi da kanshi yayi mata." Bayanta yake ɗan bubbugawa sannu a hankali alamun rarrashi. """Kiyi haƙuri.""" Ya iya faɗa daƙyar bayan tsawon lokacin da ya ɗauka yana kokawa da bakinsa kafin ya samu zarafin buɗewa har kalmomi biyun suka fita. "Sun ɗauki tsawon lokaci suna a haka, kafin daga bisani ya ɗauketa can-cak a jikinsa ya nufi banɗaki da ita." "Ba yau ne karo na farko da ya fara yi mata wanka ya naɗo ta kamar ƴar jaririya ba, don haka a yanzu ɗin ma bai sha wata wahala ba, haɗin kai ta bashi ɗari bisa ɗari tun tana kukan har ta koma sauke ajiyar zuciya, duk inda yayi da ita haka take bin shi da ido har ya gama komai ya sake ɗaukarta ya mayar da ita gefen gado ya shimfeɗeta. Lallausan bargo ya rufa mata a jikinta ya ɗauki remot ya daidaita mata yanayin sanyin A.c, sannan shi ma ya shige banɗaki da niyyar yin wanka, ko kafin ya fito, har wani" nannauyan barci yayi awon gaba da ita. "Gefen gadon ya zauna, ya tsura mata idanu yana kallonta a tausashe. Kamar dai yau ne ya fara ganinta." Maganganun da ta gama rattaba masa ne yake sake bitarsu yana musu karatun dalla-dallah. "A iya hange da zurfin tunaninsa, bai ga ta inda ya kuskure mata ƙarara a tsawon yininsu na yau da har ta" kasa danne ɓacin ranta ba sai akan sabbin kulolin nan da ya kwashi abincin ciki da yake mallakinsa ya kai ma mahaifiyarsa. Daga shi har ita basu yini a gida ba balle wani abu na saɓanin fahimta ya gifta a tsakaninsu. Ko da sun "yini tare ma, samun saɓani ko banbancin ra'ayi ba abu ne da ke yawan faruwa a tsakaninsu ba." Soyayya da ƙauna mai tafe da yarda tsaftatacciya suka gina a tsakaninsu tun kafin kasancewarsu "ma'aurata. Bayan sun dunƙule ta hanyar zamowa abu guda ƙarƙashin inuwar aure kuma, musamman" suka zauna suka sake sabunta sabbin tsare-tsare akan waɗancan turaku uku da suke riƙe da igiyar soyayyarsu har ta kai su ga zama ma'aurata. "Da waɗannan dalilan yasa sam ba sa faɗa, saɓanin fahimta kuwa zai iya ƙididdige sau nawa suka same ta" a iya zamantakewarsu na shekaru biyu. "Da gaske kamar yadda ta faɗa, ɓangaren mahaifiyarsa daban tata a matsayin matarsa daban. Ya zama" dole ya ƙara yin tsayuwar daka wajen ganin ya ba kowa a cikinsu haƙƙinta da Allah ya ɗora mishi. Zulaikha da yake kallonta da matsayin mai ƙara ma wuta fetur sannu a hankali zai bi da ita ya koya mata hankali cikin ruwan sanyi ba tare da Innaye ta zargi wani ba. Lallausan murmushi ya sakar ma Bintu da "take barci, yasa hannu sannu a hankali ya shafi gefen fuskarta, sannan ya miƙe tsam daga gefen gadon." "Idanuwansa ne suka faɗa kan ɗan madaidaicin agogon da ke gefen gadon, ƙarfe shida har da minti biyu" "na yamma. Gaf ake da kiran sallar magriba, banɗakinsa ya koma ya ɗauro alwala, bayan ya fito kuma sai" ya nufi gaban madubi ya fara shafa mai. Cikin ƙanƙanin lokaci ya shirya cikin jallabiya ya fice daga ɗakin zuwa falo. Sai da idanunsa suka sauka akan teburin cin abinci sannan ya tuna a yinin yau gaba ɗaya bai ci wani "ƙwaƙƙwaran abinci ba. Kuma wani abin mamaki shi ne sam ba ya jin yunwa, bayan ɗan tunani da yayi sai" ya alaƙanta hakan da rashin nutsuwar da ya samu bayan dawowarsa gidan. """Shaiɗaniya Zulai.""" Ya faɗa a fili. Sai kuma yayi ƙwafa mai ƙarfi ya ƙara da cewa """Zanyi maganinki. Ke baki isa ki zo ki hargitsa min zaman lafiya da kwanciyar hankalin da na ɗauki" "tsawon shekaru ina ginawa tsakanina da iyalina ba.""" Kaɗa kai yayi yana cije laɓɓa ya fice daga gidan zuwa masallacin cikin layinsu da yaji an fara kiran sallar magriba. ***** ***** """Innaye sai kin dawo. Allah ya ƙara lafiya yasa mu ji alkhairi.""" A karo na huɗu Zulaikha ta sake faɗin haka fuskarta a marairaice. Kamar za ta saka kuka. """Amin Auta. To shi kuma ɓata fuskar ta mece ce? Ca nake kina ji Fatima ta ce da an gama gwajin za ta" "saka a dawo da ni gida?""" Innaye tayi maganar da sigar rarrashi hannunta riƙe da na Zulaikha. """Innaye...""" """Ke dallah ki rufe mana baki anan gurin sakarya kawai. Sallama da addu'ar sun isa haka, ko an faɗa miki" "ke kaɗai ce kika damu da lafiyarta?""" Hafiz ya katse maganar da tayi niyyar yi cikin wani irin gigitaccen tsawa da yasa babu shiri ta saki hannun "Innaye, a ɗimauce ta juya zuwa ɓangaren da aka sauke su da saurin gaske kamar za ta kifa a ƙasa." "Da kallo Innaye ta bi ta, sai kuma ta dawo da idanunta kan Hafiz ƙarara take nuna mishi rashin jin daɗin" "tsawar da yayi ma Zulaikha. Ta kasa daurewa, sai da ta ce" """Haba Hafizu. Saboda Allah menene aibun bankwana da kyakkyawar addu'ar...""" """Kiyi haƙuri Innaye. Kin ga fa tun ɗazu Bintu take jiran fitowarki. Kamata yayi ace yau ƙarfe bakwai na" "safe tana asibiti amma saboda ke kinga yanzu bakwai da rabi, kuma duk ba kowa ne ya janyo ɓata lokacin ba sai Zulai. Yi haƙuri ki hau mota ku tafi, na san in Allah ya yarda zuwa ƙarfe goma an gama" "komai za ta saka a dawo da ke gida.""" Bata ce komai ba sai idanunta da ta ɗauke daga kan fuskarsa. Ta ɗan kalli Bintu da tun fara maganar "Hafiz take haske shi da murmushi, ta ɗan girgiza kai ta yunƙura da nufin kai hannunta ta buɗe ƙofar baya" na motar don ta shiga ta zauna. Da saurin gaske Hafiz ya riga ta kai hannu ya buɗe mata ƙofar. Sai da ya tabbatar ta gama daidaita zamanta sannan ya sake yi mata a dawo lafiya ya maida ƙofar ya rufe. Gurin matarshi da take zaune a mazaunin direba ya ƙarasa da murmushi a fuskarsa yake sake bata haƙurin ƙara ɓata mata lokacin da aka yi. Har wannan lokacin murmushin da take yi bai bar kan fuskarta ba. A tausashe ta amsa mishi da cewa """Kar ka damu My Dear. Komai zan iya yi don kai kaɗai. Bayan haka ma Innaye ta wuce komai a gurinmu," "zan iya jure fiye da haka saboda ita.""" "Ƙaunarta da ganin girmanta ne ya ƙara cika mishi zuciya, bai iya mayar mata da zaƙaƙan kalamai ba" saboda Innaye da ya san tana saurarensu illah cewa da yayi a taƙaice """Na gode""" Sai ya ja da baya ya ɗaga hannu yana mata bye-bye ita kuma ta tayar da motar yana tsaye yana kallonsu har ta fice daga gidan bayan mai gadi ya wangale mata get. "Daga nan tsakar gidan, kai tsaye ɓangaren da aka sauki Innaye ya wuce. Babban burinsa ya ɗan sassaɓa" ma Zulaikha kamanni kafin Innaye ta dawo gidan. Wani rashin sa'a da yayi shi ne yana murɗa hannun ƙofar sai ya ji an rufe ta ciki. """Ke! Ke!! Ke Zulai?""" Ya kira ta da sunan da shi yake faɗa mata cikin tsawa. Kafin ta amsa ya cigaba da magana cikin hargagi """Me kike yi a cikin ɗakin har da rufe ƙofa? Zo ki buɗe min ƙofar nan yanzun nan tun kafin in shigo ciki in" "same ki.""" "Ƙirjinta ne ya buga daram! Tana jin shi, amma ta sake yin luf akan gadon ko ƙwaƙƙwaran motsi ta kasa yi." "'Tun jiya ta san a masifar ƙufule yake da ita, sanin halinsa na mugunta musamman a kanta yasa sam" bata so tafiyar Innaye asibiti ita a barta a gida ba. Daga yadda ya daka mata gigitaccen tsawan da yasa ta baro Innaye a gurin mota ba tare da ta jira ta ga "tafiyarsu ba. Ta ƙara yarda ma kanta lallai akwai wani mugunta da Yayan yake kitsawa a zuciyarsa game da ita, shi yasa ko da ta koma ɗaki ta shige ciki har ta zauna tana matsar ƙwalla sai kuma ta tashi da sauri taje ta rufe ƙofar ta murza ɗan makulli." "Shi da kanshi ya nuna musu yadda ake kulle ƙofar ranar da suka je gidan, ya kuma ƙara musu da bayanin" idan suka kulle ƙofar suka bar mabuɗin a jiki to ko daga waje wani ya je da irin makullin zai buɗe ƙofar bazai taɓa buɗuwa ba. "A sadda yake musu wannan bayanin, bata ɗauki abin da wani muhimmanci ba, kawai dai ta saurare shi" "ne ba don ta wani ba bayanan nashi muhimmanci ba. A ganinta, cikin wannan ƙaton gidan, kuma a" unguwar masu kuɗi da tun a ƙofar shigowa layin sojpji ne masu gadi wani abin cutarwa ne zaiyi gigin kawo musu farmaki? Ai kura ma ta san gidan mai babbar sanda. Ko ƙananun ɓarayi ƴan kuci ku bamu irin waɗanda ta sani a ƙauyensu da waɗanda take ji a labarai sun san irin gidajen da suke shiga suyi sata ba irin na Yayanta ba. 8) "Shi yasa daga ita har Innaye basu taɓa kulle ƙofar da makulli ba, ko wani dare da sun tura ƙofar a haka" suke barin t...' Da saurin gaske ta dawo cikin hayyacinta lokacin da ta sake jin muryarsa yana mata magana cikin faɗa da ɗaga murya. """Zulai? Baza ki zo ki buɗe min ƙofar ba ko? Na san kina ji na. Na rantse da girman Allah idan kika bari" "na ɗauko safayar makulli na buɗe ƙofar Wallahi na lahira sai ya fi ki jin daɗi. Gara ma tun wuri ki buɗe in kora miki kashaidi da jan kunnen da zanyi miki a wuce gurin tun kafin in buɗe ƙofar da kaina.""" A karo na biyu ƙirjinta ya sake bugawa daram! Ta zazzaro idanu a tsorace hannayenta biyu dafe da ƙirjinta. Tsoron ta Allah tsoronta ya buɗe ƙofar da kansa yayi mata mugun bugun da tunda uwarta ta haife ta ba'a taɓa yi mata shi ba. A raunane ta yunƙura da nufin tashi taje ta buɗe mishi ƙofar sai kuma ta sake tunawa da yadda yai ta jaddada musu idan suka kulle ƙofar suka bar makulli a jiki babu wanda zai iya buɗewa daga waje. Ajiyar zuciya mai sanyi ta sauke. Ta sake komawa tayi laƙwas akan gadon tana jin kwanciyar hankali kaɗan akan fargabar da ya lulluɓe ta. Daga can waje shi kuwa bai fasa buga ƙofar yana zazzaga mata masifa da shan alwashin irin dukan da zai mata idan ta bari shi da kanshi ya buɗe ƙofar. """Ai kuma sai kayi.""" Ta faɗa ƙasa-ƙasa yadda ta tabbatar bazai taɓa ji ba. """Ta Allah ba taka ba, idan ka buɗe kar ka barni da rai.""" Ta sake faɗa a hankali tana murguɗa baki kamar yana kallonta. Ita kam ta rasa dalilin wannan ƙiyayya da Yayanta yake mata. Kamar ba ciki ɗaya suka fito ba? Ta ja tsaki ƙasa-ƙasa. """Duk abinka dai baka isa ka canja ni a matsayin ƙanwarka ba.""" Ta sake faɗa idanunta na kawo ruwa tana ƙoƙarin mayar da su ba. Da taji bugun ƙofar ya ƙi tsagaitawa "yatsunta manuniya guda biyu tasa ta toshe kunnuwanta da ƙarfi, har ya gama hargaginsa ya wuce a" gurin bata sake jin ɗuriyarsa ba. ****** """Innaye minti biyu don Allah, zan shiga gidan Raudha in karɓi wasu sakamakon gwaje-gwajen marasa" "lafiya a hannunta. Yanzu zan fito, ki jira ni a cikin mota.""" "Ko kafin Innaye ta amsa har ta buɗe ƙofar motar ta fice, da makullin hannunta tayi amfani wajen kulle" motar ta waje sannan ta shige cikin gidan da ta kira na Raihana. Fiye da mintuna arba'in ta ɓata a cikin gidan bata fito ba. Tun Innaye tana zaman daɗi har ta koma yin na "wahala, kasancewar gilashin ɓangaren da take zaune kaɗai a buɗe, kuma shi ma ɗan kaɗan ne a buɗe," shi yasa shige da ficen iska yayi ƙaranci a cikin motar. Innaye ta haɗa zufa tayi kashirɓin. Kayan cikinta sai hautsinawa suke yi kamar za tayi amai duk da babu "abinda ta karya da shi. Ta muskuta ya fi sau ashirin, tun tana iya fifita da gefen hijabin jikinta har tayi" laƙwas ta zuba ma sarautar Allah idanu tana jira taga ta inda Bintu za ta ɓillo. Can bayan wasu mintuna goma sha biyar sai ga Bintu ta fito daga cikin gidan ita da wata matashiya da "baza ta wuce sa'arta ba suna magana suna dariya. A ƙofar falon gidan suka sake tsayawa, akan idanun" Innaye suke maganar da ba ta jin me suke cewa saboda tazarar da ke tsakaninsu suna nuna motar da take ciki da yatsa manuniya suna cigaba da ƙyalƙyala dariya. "Don tsananin baƙin ciki da takaici, Innaye bata san sa'adda ta sunkuyar da kai wani zazzafan hawaye ya" silalo daga cikin idanunta ba. Da saurin gaske tasa babbar yatsa ta ɗauke hawayen tun kafin Bintu da take ƙarasowa gurin motar fuskarta a ɗaure tana daddana waya ta ga kukanta. Kamar ba ita ne ta gama ƙyalƙyala dariya da Aminiyarta ba. Ta buɗe baki a cushe ta ce """Innaye yi haƙuri fa. Na ɗan daɗe ko?""" "Innaye kasa cewa komai tayi, don a yadda take jin ɓacin rai a zuciyarta, lallai tana buɗe baki da nufin yin" magana tabbas mummunar magana za ta faɗa. Shi yasa tayi shiru don koyi da faɗin Fiyayyen halitta SAW. Bintu ma bata ƙara cewa komai ba ta tayar da motar ta ɗaga ma ƙawarta da ke tsaye can nesa hannu ta figi motar a guje suka fice daga gidan. Kasancewar gudu take da motar ba kaɗan ba cikin ƙanƙanin lokaci ta isa asibitin da take aiki. "Izuwa wannan lokacin, Innaye da take zaune a bayan mota ta kai matuƙa wajen galabaita, abu goma da" "ashirin ne ya haɗe mata, ga yunwa, kasancewarta mutumiyar ƙauye wacce tayi sabo da karin kumallo da sassafe matuƙar ba azumi take yi ba, ga gajiyar zaman da tayi a cikin mota ga zafi da ya fara taka muhimmiyar rawa gurin fara galabaitar da ita. Ga irin gudun da Bintu tai ta zugawa da motar kamar" wacce za ta kai wasiƙa. "Gaba ɗaya kayan cikinta sun takura sun dunƙule guri ɗaya, miyau bakinta sai tsinkewa yake yi, alamun" ko wane lokaci amai yana iya kawo mata ziyarar ba-zata duk da babu komai a cikinta. Ita kaɗai take sakin nishi sama-sama. "Bintu tana jin ta sarai, kuma tana kallonta ta madubin da ke gaban motar. Amma ta tafasa sauke bata ce" mata don tsananin haushin tsohuwar da jikanyarta da take ji tun bayan abinda ya faru jiya. In banda hanya mai haɗin zumuntar dole ta ina za ta haɗu da wannan baƙauyiyar balle har wani dangata ya ƙullu a tsakaninsu? Shi yasa a mafiyawancin lokuta take ƙara godiya ga Allah da ya kasance Hafiz ɗin ta bai ɗauko kamannin "tsohuwar ba. Da marigayi mahaifinsa yake kama, mahaifin nasa kuwa ya kasance kyakkyawan bafulatani" ne amma mazaunin ƙauye. Ta ɗauki tsawon mintuna biyu tana ƙara gyara kwalliyar fuskarta da kayan kwalliyar da ta ciro a cikin "jakarta, bayan ta gama ta ciro wani farin gilashi ta ƙwama a idanunta sannan ta buɗe ƙofar ta fita." Har ɓangaren da Innaye ke zaune ta zagaya ta buɗe mata ƙofa sannan ta ce """Fito muje Innaye.""" "Sau uku tana yunƙurin fitowa sai kuma ta koma ta zauna laƙwas! A galabaice, Bintu na kallonta amma sai" ta kawar da fuska kamar ba ta ga abinda ke faruwa ba. Sai a karo na huɗu Innaye tayi ƙarfin halin fitowa daƙyar ta tsaya bisa ƙafafunta da taimakon motar da ta jingina da ita. """Innaye daurewa fa za kiyi, saboda Allah kina gani dai asibiti muka shigo, kuma bamu taho da Zulai ba" balle ta dinga ɗawainiyar riƙe ki zuwa ɗakin gwaje-gwaje. Ni kam muna shiga ciki Ofis ɗina zan wuce don "marasa lafiya na can na zaman jira na, ƙoƙari ɗaya da zan iya miki dai shi ne zan haɗa ki da ma'aikaciyar jinya ɗaya ta raka ki ɗakin gwaji. Ina fatan dai baki ci komai ba tun bayan tashin ki da asubah?""" """Eh""" Ta amsa daƙyar! tana jin yadda ɓacin ranta ke ƙara hauhawa. Gefe ta kawar da fuskarta ta tofar da "miyau mai yawa kwaɓal, sannan ta sake mayar da fuskarta tana kallon Bintu da take aiko mata da kallon" ƙyama a fili. """Haba Innaye! Wani irin ƙazanta ne kike mana haka saboda Allah? Ki kiyaye pls! Nan fa asibitin birni ne" "ba irin na can ƙauye da kika saba gani a wulaƙance ba.""" Bintu tayi maganar da muryar faɗa-faɗa kamar tana yi da ƙanwarta. Sai kuma ta ja tsaki ƙasa-ƙasa ta cigaba da cewa """Ki jira ni anan, zan turo a shiga da ke ciki.""" 9) "Daman tunda za ta fito daga cikin motar ta gama tattaro duk ƴan kayayyakinta, Don haka kulle motar" "tayi da makulli ta nufi cikin asibitin ko waige ba ta yi, zuciyarta a ɗugunzume da ganin wannan ƙazantar da Innaye ta tofar a gabanta, ji take kamar za tayi amai. Har ta ƙarasa cikin asibitin tsaki take ja akai-akai" fuskarta a ɗaure. "A karo na biyu, wasu zafafan hawaye suka gangaro daga idanun Innaye, da sauri tasa hannu ta share" tana ɗan waige-waige. Ganin babu mai kallonta yasa ta sunkuyar da kanta ƙasa tana ƙara sakin nauyinta a jikin motar. Zuciyarta cike da mamakin yadda halayen mutane ke saurin sauyawa a mabanbantan lokuta. 'Duk da shedar da suka yi ma Bintu na sanin kirkinta ragagge ne. A karon farko na zuwa da ita asibiti "washe garin ranar da suka zo garin, ko kaɗan bata fuskanci irin wannan tozarci da wulaƙancin daga Bintu" ba. Ko don a wancan ranar tare suke da Hafiz shi yasa Bintu tayi musu tarbar arziki tayi ta ina aka saka ina aka aje da su? "Da ta san a wannan karon lamarin zai sauya, tabbas da ta tilastawa Hafiz su taho tare kamar wancan" "lokacin, ko kuma ta matsa mishi lallai Auta tayo mata rakiya. Ga shi garin sauri da gudun ɓatawa Bintu lokaci yasa ta manta da wayarta a gefen gado." Da a gaban Hafiz ne ta tabbata Bintu baza tayi mata haka ba. Ko a gaban Auta ne ta tabbata wulaƙancin "da Bintun za tayi bazai kai haka ba, don sam! bakin Auta ba ya mutuwa duk kuwa da yadda take yawan tsawatar mata. Ba ta taɓa yin shiru musamman kan abinda ya shafi mahaifiyarta ko ƴan'uwanta." "Da ace kuma ta taho da wayarta, wata ƙila da ko ɗaya daga cikin ƴaƴanta mata da suke can ƙauye ta kira" za su ɗebe mata kewa da wannan dunƙulallen ɓacin ran da ya tsaya mata a wuya shi bai sauka ciki ba kuma bata amayar da shi ba...' """Assalamu alaikum! Wai ke ce Innaye?""" "A bazata ta ji saukar wata zazzaƙar murya a kunnuwanta. Kafin ta amsa sallamar, sai da ta ɗago idanunta" "ta kalli matashiyar yarinyar da take tsaye a gabanta sanye da kayan ma'aikatan jinya, lokaci guda kuma" tana aika mata da wani sassauƙan kallo mai tafe da rangwame. "Sallamar ta fara amsawa, kafin ta ƙara da cewa" """Eh ni ce.""" """Yauwa! Ina kwana? Daman Dr. Bintu ce ta aiko ni in shiga da ke ciki.""" """To! Na gode.""" Ta amsa a raunane. Har ta yunƙura za ta ɗaga ƙafarta da niyyar fara tafiya sai tayi taga-taga kamar za ta faɗi ƙasa. """Subhanallahi! Sannu Innaye. Kiyi a hankali fa kar ki faɗi.""" Yarinyar ta jera maganganun cikin sauri a lokaci guda kuma tasa hannayenta duk biyu ba tare da wani ƙyama ba ta tare Innaye daga faɗuwa ƙasa. """Sannu!""" Ta sake faɗa a karo na biyu. """Idan baza ki iya tafiya ba sai in ɗauko kujerar asibiti ki zauna in tura ki zuwa ciki.""" Ta sake faɗa a tausashe. Ƙarara fuskarta ke nuna yanayin tausayi da jin ƙai da ake buƙatar gani a fuskar duk wani ko wata ma'aikaciyar lafiya. """Zan iya! Na gode Yarinya.""" "Innaye tayi maganar a hankali. Har za tayi shiru sai kuma ta ga kar ta cuci kanta, da alamun wannan" yarinyar da bata sani ba tana da kirkin da yayi ma Bintu ƙaranci. Sai ta ƙara da cewa """Kawai dai na ɗan galabaita ne da zaman mota ga kuma tsayuwar da daɗe ina yi anan. Idan baza ki" "damu ba, don Allah ko hannuna ne ki ɗan riƙa mu ƙarasa ciki in samu gurin zama...""" """Laaa... don wannan babu komai Wallahi. Mu je.""" Matashiyar ta katse Innaye da taƙaitaccen fara'a a fuskarta. Haɗuwar jini ne na farat ɗaya ya faru tsakanin Innaye da matashiyar ma'aikaciyar jinyar nan. Tallafin da Innaye ta samu a lokacin da bata taɓa tsammani ba yasa tayi wani irin sakin jiki da Matashiyar kamar dama can sun daɗe da sanin junansu. "Ita kuwa yarinyar kasancewarta mai surutu da saurin sabo, ga kuma ƙauna ta farat ɗaya da taji tana yi" "ma Innaye yasa ta saki jiki sosai da ita, suna hanya ta faɗa ma Innaye cikakken sunanta Karima Idris Madobi." "Kamar wacce ta samu Kakarta ko Yayar mahaifiyarta, haka ta tallabe Innaye suna tafe sannu a hankali da" fara'a sosai a fuskarta ta ke ba ta labarin Kakarsu da ta kasance fitinanniyar tsohuwar da ta gallabi kowa a gidansu. """Ba ma taɓa samun hutu da surutunta idan ba barci tayi ba, ko kuma mu muka fita zuwa wajen aiki ko" "wani al'amari na daban. Ba wai ni da Yayana da muka kasance jikokinta ba fa, hatta Mummy da ta kasance ɗiyarta duk mun san haƙuri take yi da al'amarin tsohuwar.""" Da murmushi sosai a fuskar Innaye ta jefa mata tambayar """In banda ke da abinki Karimatu ta yaya ƴa za ta gaji da hidimar mahaifiyarta?""" """Ba'a gajiya ko Innaye?""" Ta maida mata tambayar da wata tambaya alamun ƙuruciya ƙarara bayyane a furucinta. """Eh mana. Ai duk ɗa ko ƴa ta kirki ba ta taɓa gajiya da hidimar mahaifi ko mahaifiyarsa. Yanzu ne fa" lokacin nan da Allah ya ce kar ku taɓa ce musu uhhmmm don wata ɗawainiya ko wahala tasu da kuke yi. "Sun wahalta muku kuna ƙanana, ku kuma sai ku saka musu suna tsofaffi masu rauni kan rauni. Idan" "kuma kina tantamar abinda na faɗa miki, wata rana ki gwada aibata ita Kakar taki a gaban Mamanki...""" """Taɓ! Ki ce in janyo ma kaina gaggarumin tashin hankali tsakanina da Mummy. Duk fa wannan wahalar" da muke ganin tana yi da Hajja yanzun nan muna fara ƙorafi za ta zazzage mana kwandon masifa tana faɗin ina ruwanmu? Ita ta fi son Hajja fiye da komai da kowa na duniyar nan. Don haka mu ƙyale ta ta "hidimta ma tsohuwarta wata rana sai labari.""" Faffaɗan murmushi ne yalwace a fuskar Innaye tana jin matsananciyar ƙaunar uwar Karima da ita kanta "Karimar a zuciyarta. Suna wannan hirar ƙasa-ƙasa, har suka ƙarasa ɗakin gwajin da Bintu ta umarci Karima ta kai Innaye." Kuma da yake ita ɗin ƴar arziki ce bata bar gurin ba sai da aka gama duk abinda ya kamata ta sake riƙota "suka fito daga cikin Ofishin. Killataccen gurin zama da Nurses suke zama ta zaunar da Innaye, sannan ta bata uzurin tana zuwa." A gaggauce ta wuce Ofishin Bintu ta sanar da ita an gama komai da ta umarta. """In shigo da ita nan ne?""" """A'a!""" "Bintu ta katse ta da sauri, hankalinta na kan rubutun da take yi a cikin folder na mara lafiyar da ta gama" dubawa ko sararin ɗaga kai ta kalli Karima bata samu yi ba. Ita har ga Allah ta ma manta da wata Innaye balle abinda ya shafe ta in banda yanzu da aka zo mata da maganarta. Taja wani zazzafan numfashi ta fesar. Ɓacin ran da ya bi ruwa sanadiyyar kama aikinta gadan-gadan ya fara taso mata sannu a hankali. """Yanzu tana ina?""" "Ta tambaya a taƙaice, har lokacin bata ɗaga fuskarta ta kalli Karima ba." Faɗa mata inda ta zaunar da Innaye yasa Bintu ta ɗaga kai da sauri tana aika mata da wani kakkausan kallo. """How dare you da za ki zaunar da ita inda aka tanada don ma'aikatan asibitin nan?Me yasa baki zaunar" "da ita a reception inda ko wane mara lafiya yake zama ba?""" "A ladabce Karima ta sunkuyar da kanta ƙasa ta fara ba Bintu haƙuri, hankalinta a tashe. Domin bata daɗe" "da fara aiki a asibitin ba, tsoronta Allah tsoronta tayi abinda zai sa ta janyo ma kanta matsala daga fara aikin da take tsananin alfahari da samunsa." """Shi kenan! Amma ki kiyaye gaba. Duk wata doka na asibiti ki tabbatar kin kiyaye shi sau da ƙafa. Bayan" "haka wannan tsohuwar da kike gani ƙazama ce ta ƙarshe mai ɗauke da cututtuka mabanbanta a jikinta, gara tun wuri kiyi nesa da al'amarinta. Ki maida ita reception ta zauna ta jira ni, zan kira direba yanzu ya" "mayar da ita inda ta fi wayau. Je kiyi abinda na ce.""" Jiki a sanyaye Karima ta fice daga Ofishin tana jinjina maganganun Dr. Bintu a zuciyarta. Haka ta koma inda ta bar Innaye da yanayin da ba shi suka rabu ba. """Kiyi haƙuri Innaye. Likita ta ce in zaunar da ke a reception ki jira ta. Za ta kira direba ya mayar da ke" "gida.""" """To ba komai Karimatu. Na gode, Allah yayi miki albarka ya baki miji na gari. Idan kin koma gida ki" "gaishe min da Kakarki da mahaifiyarki.""" "Ta faɗa ba tare da ta maganar da nisa ba, ganin yanayin Karima da irin maganar da ta faɗa mata in ji" Bintu yasa ta tunanin wata ƙila Bintun ta faɗi mummunar magana ne a game da ita. "Duk da yadda take jin rashin ƙarfin jiki saboda yunwa, haka ta ƙwarara kanta ta miƙe tsaye ta fara tafiya" a hankali zuwa waje ba tare da ta san ina ne reception ɗin ba. Watsar da duk wasu maganganu da Bintu ta faɗa mata tayi ta ƙarasa da sauri ta riƙe ma Innaye hannu. "Saɓanin sadda suka shiga cikin asibitin suna hira da dariya, a yanzu babu mai cewa komai har suka" ƙarasa reception ta zaunar da ita. Sallama tayi ma Innaye da addu'ar samun sauƙi sannan ta kama hanyar komawa gurin aikinta. Innaye ta raka ta da idanu. 10) Tana daf da ɓace ma ganin Innaye sai ta dawo a gaggauce """Innaye kin karya kumallo kuwa?""" Ta tambaye ta duk da ta san gwajin da aka yi ma Innayen ana yin shi ne kaɗai ga waɗanda basu ci abinci ba. """Ban ci komai ba Karimatu. Ai an ce wannan gwajin kafin a ci abinci ake yi. Yanzu dai idan na koma gida" "zan karya, na san abincin kari na can Auta ta ajiye min.""" "Ta ƙarasa maganar idanunta na kallon ƙaton agogon da ke manne a jikin bangon gurin, wanda ya nuna" ƙarfe goma sha biyu saura minti ashirin. """To shi kenan. Allah ya ƙara sauƙi. Bari in kawo miki Maltina ki sha kafin ki koma gidan. Wannan rashin" "ƙarfin jikin naki ina ga har da yunwa ne ya galabaitar da ke.""" Bata jira amsawar Innaye ba ta wuce ciki zuwa Ofishin da suke zama inda ta ajiye jaka da sauran kayayyakinta. Maltina ta ɗauka a jakarta da samosa guda biyar a cikin robar take away ta fice a gaggauce ta kai ma Innaye. Bata tsaya amsa godiya da saka albarkar da take mata ba ta koma ciki ta kama ayyukan da suke gabanta. Da gaskiyar Mal bahaushe da yake ma yunwa take da mare hankali. Innaye bata san yunwar da take ji ya "kai ƙololuwa ba sai da taga Maltina da Samosa a hannunta. Jiya da daddare ba wani abincin kirki ta ci ba saboda tunanin rayuwar gidan Abdul-hafiz da makomarsa a can gaba, da wannan dalilin yasa take jin cikinta a rarake kamar wacce ta kwana ta yini bata ci ba. Duk yadda ta kasance dattijuwa mai tsananin kunyar idanun jama'a bata damu da mazauna gurin ba ta buɗe robar Samosa ta ɗauka ta fara ci tana" "korawa da Maltina. Kafin ace kwabo, ta cinye gaba ɗaya." Lumshe idanu tayi tana hamdala a zuciyarta saboda jin yadda a ƙanƙanin lokaci ta ƙara dawowa cikin "hayyacinta. Ashe kaso sittin na gajiya da galabaitar da tayi yunwa ce, yanzu kuwa da ta samu mahaɗi sai" ga shi ta dawo hayyacinta sosai tana jin ƙarfi a jikinta. Ƙara gyara zama tayi idanunta a lumshe tana shan A.c a zuciyarta kuma tana Istigfari da Hailala kafin ta ankara ta fara gyangaɗi. """Wai barci kike yi? Ki tashi ga direba can zai mayar da ke gida.""" Ta ji muryar Bintu bagatatan a kanta kamar a cikin mafarki. A hankali kuma a nutse ta buɗe idanunta ta zuba a cikin na Bintun. Ita ma fuskarta babu walwala ko "kaɗan kamar dai yadda fuskar Bintu yake. Sai kuma ta kawar da idanunta daga Bintu ta maida kan agogo," ƙarfe goma sha biyu da minti goma sha takwas na rana. Bata ce komai ba sai miƙewa da tayi tsam ta tsaya tana kallon Bintu. "A fakaice, Bintu ta harari gefen Innaye, ta ƙara ɓata fuska sannan ta nufi hanyar fita. Innaye ta rufa mata" baya zuciyarta na ƙara cika da tsoron halayen Bintu da sannu a hankali suke ƙara bayyana. Har suka ƙarasa gurin motarta inda direba ke zaune a mazaunin direba bata sake ce ma Innaye komai ba. Ita ma Innaye bata ce mata cikanki ba. "Kamar sadda za su zo asibitin, ƙofar baya na motar Innaye ta buɗe ta zauna sannan ta mayar da ƙofar ta" rufe da ƙarfi. 'Ta Allah ba taki ba. Duk muguntarki haka za ki ga motar nan ki ƙyale ko ƙwarzane baki isa kiyi mata ba.' "Bintu ta faɗa a zuciyarta, cike da jin haushin irin bugun ƙofar da Innaye tai ma motar ta." Dogon tsaki ta ja kafin ta mayar da idanunta kan direba. """Bala kayi tuƙi a nutse fa. Kana dawowa ka tabbatar ka wanke min motar ciki da waje saboda ƙura da" "gudun kwasar cututtukan da ban san farkonsu ba bare ƙarshensu. Ina fatan ka gane?""" """Na fahimta Ranki ya daɗe. Sai na dawo.""" Ya amsa a ladabce. "Baya ta matsa, shi kuma ya tayar da motar, tana tsaye tana kallonsu har suka fice daga cikin asibitin kafin" ta koma ciki tana sake jan tsaki sama-sama. ****** """Hmmm! Na ce ba... Au! Ina kwana Baba?""" A ɗan daburce Zulaikha ta sake gaishe da Rabi a karo na uku. Ba tare da damuwa ko nuna yanayin gundura ba ta amsa gaisuwar da murmushi fal a fuskarta. Haka "kawai, Zulaikhan burge ta take yi, basu taɓa yin wata doguwar magana ba tun da suka zo gidan, amma idan ta je can inda aka sauke su za ta kai musu abinci ta ga irin taɓara da shagwaɓar da yarinyar ke ma" mahaifiyarta abin dariya da burgewa yake ba ta. "Tun bayan shigowar yarinyar, da ajiye tsadaddun kulolin abincin mai gidan da tayi ta gaishe ta a karo na" "farko, ta lura da yadda yarinyar take saiɓi wajen fita kamar akwai wani abu da take so." "Har ta kusa fita sai ta juyo da sauri ta sake gaishe ta a karo na biyu, ko bayan da ta amsa gaisuwar, sai ta" ɗan tsaya shiru ta ƙura mata idanu. A karo na ukun kuma har ta fita sai ta sake dawowa ta gaishe ta. "Kamar baza ta amsa ba, duba da yadda Hajiya Bintu ke ta kwakkwafarta a kan baƙin tun ranar da suka zo" gidan sai kuma ta yanke shawarar yi mata magana ganin yanzu ai Hajiyar ba ta nan. """Ƴan matan Mamanta ya aka yi? Gaisuwa ɗaya biyu ai ya isa ko? Kin ga tun shigowarki na lura kamar" "akwai maganar da kike so kiyi amma kina ta nuƙu-nuƙu. Kina buƙatar wani abu ne? Kar ki damu, faɗi ko me kike so yanzu in ɗauko miki.""" Kamar damar da Zulaikha take buƙatar samu kenan. Da sauri ta ce """Ummm! Daman zan tambaye ki ne don Allah. Jiya da rana har kika tafi baki kawo mana abinci ba, kin" "manta da mu ne?""" "Ɗan shiru Rabi tayi kamar tana tunani, sai kuma ta amsa kai tsaye da cewar" """A'a! Ban manta da ku ba. Hajiyar ce ta ce ba sai nayi abincin rana ba, ko da na tuna mata da baƙi kuma" "sai ta ce ba abinda ya shafe ni bane. Ta aike ni can gidansu daga can kuma na wuce gida...""" """Da gaske haka kuka yi Baba?""" Zulaikha ta katse ta da tambayar da yanayin mamaki fal a fuskarta. """Eh da gaske, me zai sa inyi miki ƙarya? Kin san daman a ɓangaren girki abincin da nake dafawa a" "gidannan na masu aiki ne kawai, sai kuma baƙi idan akwai." Abincin maigidan ita da kanta take dafawa. To tunda ta ce ba sai nayi ba ai kin ga ba ni da hurumi ko ikon "da zan ce dole sai anyi ko?""" """Uhmmmm haka ne.""" Zulaikha ta amsa a mamakance. """Lallai ma!""" Ta ƙara faɗa tana sake jinjina girman al'amarin. Ita daman tun jiya ta san da gangar Bintu ta hana su "abinci, amma saboda tsananin ƙwarewarta a ƙarya da iya shirya zance sai ta ce bata san ba'a kai musu" abinci ba. """Ba damuwa. Ta yi ma kanta.""" Ta sake faɗa ranta a ɓace. Da sassarfa ta kama hanyar ficewa daga kicin ɗin Rabi ta bi ta da kallo. A zuciyarta take harhaɗa ɗaya bisa biyu tana hasaso abinda ya faru bayan tafiyarta. To ko dai wannan shi "ne dalilin da yasa ta ga waɗannan tsadaddun kulolin na abincin Oga a hannun Zulaikha? Kulolin da ko gurin wanke-wanke Hajiya ta jaddada mata lallai ta dinga musu wanki na musamman, sannan da an gama wankewa a kife a kwando a saka towel a goge a mayar da su ma'adanarsu, ba tare da an haɗa su" da tarkacen kaya ba... """Amma Baba Rabi ita Hajiyar ta faɗa miki matsayinmu a gurin maigidannan kuwa?""" Maganar da Zulaikha tayi ya dawo da ita cikin tunaninta ba tare da ta san sa'adda ta dawo cikin kicin ɗin ba. """A'a! Bata faɗa min ba. Abu ɗaya dai da na sani ku ɗin danginshi ne, don Hajiya Bintu ta sha faɗin shi" "ke da ƴan'uwa Ƙauyawa...""" """Ba ƴan'uwa ƙauyawa kaɗai bane. Ita wannan tsohuwar baƙauyiyar da kike ganina tare da ita," "mahaifiyarshi ce.""" Zulaikha ta faɗa idanunta ciccike da hawaye. Kafin Rabi da ta buɗe baki tayi magana ta cigaba da cewa """Ita ce ta sha wahalar naƙuda ta haifo shi zuwa wannan duniyar. Ni kuma da kike gani kamar ba kowan" "kowa ba, ƙanwarsa ce da suka fito ciki ɗaya. Saboda Allah da Annabi idan da adalci ya kyautu ace an" "hana uwar da ta sha wahalar haihuwa da rainon ɗanta abincin da shi wannan ɗan nata ne yake nemowa da guminsa?""" "Kamar an buɗe famfo, haka hawaye ke kwaranya a idanunta. Ita kuwa Rabi, tunda ta buɗe baki ta kasa" "rufewa, balle har ta iya ƙarfin halin amsa tambayar da Zulaikha tayi mata. Allah ya sani bata taɓa tsammanin Innaye mahaifiyar Oga Hafiz bane, duk ga tsammaninta ta fi tunanin ko dai wata Gwaggwansa ce daga ƙauye." "Babbar hujjarta kuwa shi ne, duba da yadda daga Hajiya Bintu har Alhaji Hafiz al'amarin tsohuwar basu" "ɗauke shi da wani gagarumin muhimmanci ba. Hujja ta biyu kuwa shi ne, babu wata kamanni ta musamman tsakaninshi da Innaye, ɗan gara-gara ma Zulaikha, suna yanayi a fisge..." """Ban ƙara sanin haka duniya take da faɗi da tarin abin mamaki ɗauke da mutane mabanbanta ba, sai" "da Bintu ta shigo cikin ahalinmu. Ko da muke ƴan ƙauye, bamu taɓa tsammanin akwai wani tazara na musamman tsakanin ɗan birni da na ƙauye ba, ko kuma banbanci tsakanin talaka da mai kuɗi. Duk a tunanina mu da ku bayin Allah ne da babu wanda ya fi wani a gurinsa sai wanda ya fi tsoronsa... Amma a yanzu na samu ƙarin ilimi, ya zama dole mu cigaba da raɓewa a ƙauyenmu don rayuwar birni da" "mutanen birni sun fi ƙarfinmu ta ko wane ɓangare.""" "Tana gama faɗin haka ta fice daga cikin kicin ɗin da sauri, lokaci bayan lokaci take kai hannu saman" fuskarta tana share hawaye. Ta fito tsakar gidan kenan da nufin zuwa can ɓangarensu aka wangale get ɗin gidan. Kamar baza ta "waiga ba, sai kuma ta juya sannu a hankali tana kallon motar da ta shigo. Ganin motar Bintu ce yasa ta ware idanu tana kallon motar da kyau domin ganin ta ina Innayenta za ta fito?" "Kallo ɗaya za'a yi mata, a fahimci jikinta a sanyaye yake sosai." Zulaikha yarinya ce mai shekaru goma sha bakwai. Amma irin yarannan ne da tun suna ƙanana suke da masifar wayau da manyancen iya magana. Ko don ta rayu a hannun Dattijuwa Innaye ce? Allah masani. Ganin fitowar Innaye daga cikin mota ita ma da nata yanayin sanyin jikin yasa tayi ƙoƙarin watsar da nata damuwar ta ƙarasa gurin Innaye da sauri. """Innaye? Me yake faruwa? Jikin naki ne?""" Ta jera mata tambayoyin da hanzari fuskarta na bayyana damuwa da tashin hankali. A lokaci ɗaya kuma tana ɗan tattaɓa jikin Innayen domin jin ko akwai zafi? "Hannayenta Innaye ta kamo ta riƙe, da murmushi a fuskarta ta amsa da cewa" """Jiki Alhamdulillah Auta. Kawai dai na gaji ne. Amma babu komai, muje ciki.""" """To Ma sha Allah! Allah ya ƙara lafiya.""" Ta amsa tana jin kwanciyar hankali kaso hamsin cikin ɗari na damuwarta. Haka suka kama hanyar zuwa ɓangarensu suna riƙe da hannun juna cikin kulawa. Babu mai cewa komai "a cikin su biyun, ko wacce da tunanin da take yi a zuciyarta." "Suna ƙarasawa ciki, ta zaunar da Innaye a gefen gado ta sa hannu ta zare mata hijabin jikinta." """Sannu Innaye. Allah ya ƙara lafiya. Ai dole ki galabaita, jiya fa duk farkin barcin da zan yi sai in ga" "idanunki biyu. Ga shi yau da sassafe baki samu komawa barci ba kuka fice zuwa asibiti. Ko kinyi barci ne acan asibitin?""" """Barci kuma Auta?""" """Eh mana. To ba naga akwai gadajen da ake kwantar da marasa lafiya ba?""" Ta amsa tana tura baki da murmushi a fuskarta. """Eh haka ne! Amma ai ana kwantar da waɗanda jikinsu yayi tsanani ne. Ni kuwa kin ga har yanzu da" "sauran ƙarfin jiki a tattare da ni...""" """Amma Innaye kin ci abinci bayan an gama gwajin da aka ce za'a miki kafin ki karya?""" Ta katse ta da sauri bayan ta tuno sun fita daga gidan Innaye bata karya ba. """Uhmmm!""" "Ta ja numfashi ta sauke a kasalance. Kamar baza ta ƙara yin magana ba daga wannan ajiyar zuciyar, sai" kuma ta ce. """Auta! Wato da gaske ne duk lalacewar al'umma ba'a rasa na kirki. Yau ba don Allah ya haɗa ni da wata" "yarinya ƴar arziki wacce ta san ya kamata ba da yanzu wani zancen ake yi ba wannan ba. Wata kila, da" "sai dai matar gidan ta dawo ta sanar da ku babu yadda nake, an kwantar da ni ranga-ranga a asibiti. Amma da yake ko cikin lalatattu ba'a rasa na kirki sai Allah ya agaje ni da taimakonsa na gaggawa a lokacin da banyi tsammani ba. Alhamdulillahi! Je ki tara min ruwan wanka inyi sai in alwala, ga shi can" "ana kiran sallah a masallaci...""" """Me ya faru da ke a asibitin Innaye?""" Zulaikha ta tambaye ta tana jin babu daɗi sosai a zuciyarta. Daman tun bayan ficewarsu take ta ji a ranta lallai a rashin kirkin Bintu za ta fa iya wulaƙanta Innaye ganin babu idanun kowa a kansu. "Ganin wayar Innaye ajiye a gefen gado yasa ranta ya ƙara jagulewa, tayi tunanin da akwai waya a" "hannun Innaye, idan ta ga abinda bai gamshe ta ba za ta iya kiran Yayansu yaje asibitin ya ɗau mataki." """Maimaita abinda ya wuce sam ba shi da wani amfani Auta. Balle kuma kin san hali na abu idan ba na" "alkhairi bane ban cika son maimaita labarinshi ba...""" """Don Allah ki faɗa min Innaye.""" Tayi maganar kamar za ta saka kuka. """Bazan faɗa miki ba Auta. Domin jin babu abinda zai ƙare ki da shi. Nasihar da zan miki a wannan gaɓar" "ɗaya ne rak! Mu mutanen ƙauye ne, can ƙauyen, can ne duniyar da muka buɗi idanu da ita. Kuma kaso casa'in da biyar cikin ɗari na mutanenmu acan suke farawa kuma su ƙare rayuwarsu." A mafiyawancin lokuta duniyar sauyawa take yi. Idan Allah yayo ki cikin masu tsawon rai yanzu kika fara "rayuwarki, ban san ko kina daga cikin ɗaiɗaiku kuma tsirarun da Allah ya ƙaddari za su tsallake" "ƙauyenmu suyi rayuwa a wani guri na daban ba. Idan Allah ya ƙaddara miki haka, ki ji tsoron Allah. Kar ki kuskura don wani ni'ima da Allah yayi miki ki wulaƙanta mutanen ƙauye, ko ki wulaƙanta na ƙasa da ke." "Je ki tara min ruwan wanka, kafin in fito ki je cikin gidan ki samu mai aikinnan ta baki abinci ki kawo min," "idan kuma babu, ki zo ki haɗa min shayi.""" Duk wasan da ke tsakaninta da Innaye a wasu lokutan kamar jika da Kaka. Ta san irin lokacin da take "tubure mata da ƴan rigingimu, ta kuma san lokacin da take ɗaukar abinda ta faɗa da muhimmanci." "Don haka a wannan gaɓar, duk yadda ta so jin abinda ya faru a asibitin sai bata ƙara cewa komai ba. Ta" "miƙe tsam, ta shige banɗaki ta tara ma Innaye ruwan wanka a bokiti." "Ko da ta fito, sai ta tarar Innaye har ta gama shirin shiga wankan, don haka bata sake ɓata lokaci ba ta" fice zuwa cikin gidan da wani irin taku na musamman. Zuciyarta cike da saƙe-saƙen yadda za ta canja tsarin zamansu a gidan kafin su bar garin Abuja. "Su ba wulaƙantattu bane, don haka bazai yiwu Bintu ta cigaba da ɗaukarsu a wulaƙance ba. Ba maula" suka je gidan ba balle ace za'a dinga ba su sadda aka so a hana su sadda aka ga dama. Idan Bintu tana da ƴanci a gidan lallai su ma suna da shi. Da wannan daliln kuwa ko da tsiya ko da tsiya- "tsiya za ta ƙwatar musu ƴancinsu, idan Yaya Hafiz yaga dama, yayi ƙuli-ƙulin kubura da ita. Amma tsakaninta da matarsa ba sauƙi ba sauƙaƙawa, shege ka fasa, ɗan halak sai yanka." "Tana waɗannan tunane-tunanen har ta ƙarasa cikin falon gidan, watsar da tunanin komai tayi ta buɗe" idanu sosai tana kallon irin ƙayatattun kayayyakin da aka yiwa falon kwalliya da su. Duk da ba sanin "kayayyaki masu tsada tayi ba, ido ba mudu bane amma ya san kima." "Kuma da ganin kura za ta ci akuya, ko da ganin kayayyakinnan maƙudan kuɗaɗe suka ja ba ƴan kaɗan ba." "Haka kawai, ba tare da sanin dalili ba sai hoton gidansu na can ƙauye tun daga soro har zuwa falo da" "uwarɗakin Innaye ya faɗo a cikin idanunta. Babu mahaɗa ko kusa, amma da ta tuna nisan tazarar da ke" tsakanin rayuwar birni da na ƙauye sai ta ajiye tunanin komai ta ƙarasa cikin kicin ɗin. """Baba Rabi an gama abincin ne?""" Ta tambaya da yanayin fuska kadaran-kadahan bayan sallama ƙasa-ƙasa da tayi a ƙofar kicin ɗin. """Ba'a gama ba Auta.""" "Ta amsa da sauri cikin girmamawa, domin maganganun da yarinyar tayi ɗazu kafin ta fice daga kicin ɗin" tana kuka sun tsaya mata a rai. Da wannan dalilin yasa ta ƙuduri aniyar in Allah ya yarda ta ɓangarenta dai baza ta sake yin wani abu da "zai nuna wulaƙantarwa ga tsohuwa da yarinyar ba, duk da daman dai tana yin komai ne don guje ma kuskurewa Uwarɗakinta. Don ta ƙara warware ma Zulaikha yadda tsarin girkin abincin ke tafiya sai ta cigaba da cewa" """Kin san yanzu ranar ta fara ɗagawa, kuma a ƙa'idar da Hajiya Bintu ta tsara zuwa uku na rana ne zan" "dinga raba abinci. Shi yasa na tsara komai yadda aikin zai dinga tafiya kan lokacin da ta tsara...""" """To madallah!""" Zulaikha ta katse ta tun kafin ta aje numfashin maganarta. """Yanzu ya za'ayi? Me za ki samar ma Innaye mai ɗan sauƙi? Daga asibiti ta dawo kuma ta bar gidannan" "ko karyawa bata yi ba.""" """Assha! Jikin ya motsa ne? Allah ya ƙara mata lafiya. To ko dai za'a haɗa mata Tea ne? Domin ya saɓa" "ma ƙa'idar Hajiya Bintu girka wani abu daban saɓanin wanda za'a dafa gaba ɗaya...""" """Wai wace ce kuma Hajiya Bintu da kike ta sako min sunanta a cikin maganganun da muke yi? Ya ina" "miki maganar mahaifiyar Maigidannan ta fita bata karya ba kina min zancen wata Hajiya Bintu da ta tsinci mai gidan a sama da haƙwaransa talatin da biyu? Dan Allah ki aje maganarta gefe kiyi abinda ya kamata. Ko Indomie ce da ƙwai ki dafa mata yanzunnan, idan kuma baza ki iya ba kina tsoron saɓa umarnin wacce kike ma aiki, ki kunna min abin girkin ki nuna min inda kayayyakin abincin suke, ni sai in" "dafa mata da kaina. Ko da nake ƴar ƙauye kin san dahuwar indomie dai ba za ta gagareni ba.""" Zulaikha tayi maganar tana ƙara harhaɗe girar sama da ƙasa. Zuciyarta cike da haushin Baba Rabi yadda take ma Bintu wata irin biyayya ta musamman kamar wacce ta girme mata a shekaru. """Anya...?""" Baba Rabi ta faɗa cike da taraddadi da tsoron abinda zai iya zuwa ya dawo. Sai kuma ta ƙara da cewa """Ko da yake, shi kenan. Bari a dafa mata, ɗan bani mintuna goma kacal. Je ki dawo, yanzu zan gama" "dafa mata.""" "Gefe guda taja ta tsaya tana bin duk inda Baba Rabi tayi da idanu, akan idanunta ta kunna Gas ɗin girki," "daman shi kaɗai ne take ga baza ta iya amfani da shi ba a kicin ɗin. Tana biye da ita har ta buɗe store, ta ɗauko duk abinda za ta buƙata sannan ta fito ta kulle. Abu na biyu da taga yadda ake kunnawa ayi amfani da shi blander ne, don haka ta kura idanu sosai taga yadda ake anfani da shi." "Tana kallon komai tana k'ara kwasar ilimin yadda ake amfani da kayan girkin 'yan birni, har zuwa lokacin" da Baba Rabi ta gama dafa lafiyayyiyar indomie da ta ji kayan had'i. Ta soya kwai guda hudu kamar "yadda Auta ta umarce ta, sannan ta kwashe komai a kula Mai kyau sabanin Wanda ake zuba musu abinci ta mika ma Auta." "Ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke lokacin da ta karbi abincin. Ta haske Baba da wani lallausan murmushi, a" tausashe ta ce """Na gode, Allah ya biya ki da alkhairi.""" """Amin ya Allah. Ki gaida Innaye, Allah ya kara sauki.""" Baba Rabi ta amsa bayan ta mayar mata da martanin murmushinta. "Ko da ta koma can bangarensu, akan darduma ta tarar da Innaye, hannunta da casbaha tana ja amma" tana gyangyad'i. Sallamar da tayi ma bata amsa ba sai da ta ce """Innaye barci kike yi?""" "Firgigit! Tayi ta farka, ta bude Baki za tayi magana wata k'atuwar hamma ta k'wace mata." """Sannu Innaye. Kiyi haƙuri, na barki kina jira na ko? Ba'a gama dafa abincin gidan bane shi ne nasa aka" "dafa miki Indomie...""" """Waɗannan siraran taliyar Auta? Kin san dai ko a gida ke ce kike ƙwazzabar a siyo miki ita gurin Isa mai" "shayi ki ci, ko ki karɓo a shagon Isiya ki dafa, ni kam bata ɗaɗarani da ƙasa ba.""" """Innaye, wannan haɗi na musamman aka yi gurin dafuwarta. Ba irin ta can ƙauyenmu bane, na tabbata" za ki ji daɗinta. Kuma kin ga fa har wata faffaɗar ƙwai aka soya miki da za ki dinga yaga kina haɗawa da "taliyar a gayance irin na ƴan birni. Bari in zuba miki ki ɗanɗana ki ji.""" "Bata jira umarnin Innaye ba ta zauna dirshan a gabanta, ta ɗauki faranti da cokali ta buɗe kular ta zuba" "mata mai ɗan dama a faranti, daga yadda take fitar da daddaɗan ƙamshi tun bayan buɗe kular, duk su biyun sai haɗiye miyau suke yi." "Da farko ƙwan gaba ɗaya ta ɗora akan abincin Innaye, sai da ta ce mata ta rage, sannan ta yanka biyu da" "cokali ta bar mata rabi. Daman tun a frige ɗin falon can cikin gidan ta ɗauko musu ruwa da lemon kwali, a kofi ta zuba mata sannan ta tura mata abincin a gabanta." "Ta tura abincin gabanta ta miƙa mata cokalin, Bismillah tayi ta fara ci a hankali ita kuma tana janta da" "hira, labarin samarinta na can ƙauye da Innaye bata taɓa sanin tana da su ba take ba ta, tana faɗa mata" yadda suke nacin bibiyarta ita kuma tana karta musu rashin kirki da kashedin kar wanda ya kuskura ya bi "ta gida, a cewarta, duk basu yi mata ba." Sai dariya suke yi kamar babu wani abu da yake damunsu. Cikin ƙanƙanin lokaci sai ga Innaye ta cinye abincin tas! Bata ankara ta cinye ba sai da Auta ta ce """Innaye in ƙara miki?""" "Ta kalli farantin, ta kalli Auta idanu buɗe, lokaci ɗaya sai suka sake kwashewa da dariya." """Lallai kam Auta kinyi gaskiya, wannan dahuwar taliyar ba irin jagwalgwalon da kike yi acan ƙauye bane." "Ta yi daɗi sosai, na daɗe rabon da in ci abinci mai yawa irin haka, lallai komai na birni ya fita daban da na" "ƙauye. Ko don ina jin yunwa ne?""" """A'a Innaye. Ta bakinki ne, tsarin dahuwar ba irin tamu bace amma duk indomin iri ɗaya ne. Kar ki" "damu, ai na zuba idanu sosai na koyi yadda ake dafa irinna ƴan gayun. Idan muka koma gida, irinta zan" "dinga dafa miki...""" """Kya dai dinga dafa ma mijinki. Domin muna komawa gida zan tura Baffanku ya tuntuɓi Idi, Hamisu, da" sauran duk masu son ki da kika gama ba ni labarinsu yanzu. Anya Auta? Ashe daman kina da masu son ki "kika bari muna ta ɗaga hankalinmu akan ko Aljani ne ya aure ki kika rasa mashinshini? Yayyinki na ta safa da marwa gurin Malam Usaini suna karɓo miki dafa'in farin jini da na kore shaiɗanu?""" Ƙirjinta ne ya buga daram! Sai a yanzu ta fahimci irin suɓul da bakan da tayi a dalilin son janye hankalin "Innaye har ta ci abinci sosai. Ƙwal-ƙwal tayi da idanunta ta sunkuyar da kanta ƙasa, domin ta san duk" abinda za ta faɗa a yanzu dai Innaye baza ta taɓa fahimtarta ba. "Kamar an buɗe famfo, haka Innaye ta cigaba da faɗa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba. Domin" "al'amarin rashin auren Zulaikha abu ne da ya daɗe yana ci musu tuwo a ƙwarya, kawai dai don ba su da" yadda za suyi ne. """Shekarunki sha bakwai fa. Saboda Allah duk faɗin ƙauyenmu ki faɗa min wace yarinya ce yanzu sa'arki" a shekaru da ba'a yi mata aure ba? Ke ko kunya bakya ji? Ganɗan-ɗan da ke ni da nake Gyatumarki ina tafe muna jera kafaɗa a cikin gida? In banda akwai zaman lafiya tsakanina da su Laraba ai da tuni sun fara yada min habaici da baƙaƙen maganganu. "Yanzu sa'anninki fa daga masu ƴaƴa uku sai biyu, Hanne ta gidan Mal Bala kuwa ita da yake kwainika" "take yi ƴaƴanta huɗu. Saboda Allah kin yi ma kanki adalci mu ma kinyi mana adalci kenan?""" "Saboda yanayin lafiya da yayi mata ƙaranci a ƴan kwanakin, nan take ta fara numfarfarshi sama-sama" saboda faɗan da take yi ba ƙaƙƙautawa. "Da sauri Zulaikha ta matsa kusa da ita ta riƙe hannayenta, a tausashe ta fara magana idanunta cike da" hawaye. """Ayya mana Innaye Allah sarki. Don Allah ki kwantar da hankalinki, kin ga ba wani wadataccen lafiya" "kike da shi ba. Kar ki manta, ke kike yawan faɗen aure lokaci ne, kamar layin markaɗe ne idan yazo kaina" "ko ina so ko ba na so sai an niƙa min...""" """Au! Da waɗannan maganganu biyun kika dogara yasa kika ƙi mayar da hankali kan abinda ya kamata" "kina gani kullum hankalinmu a tashe?""" Innaye ta jefa mata tambayar fuskarta na bayyana ɓacin rai. Sai kuma ta ɗan sassauta muryarta yayi rauni ta sake cewa """Auta ko dai so kike in koma kushewata ba tare da na ga ƴaƴanki ba?""" """A'a! A'a! Wallahi ba haka bane Innaye. Don Allah kiyi haƙuri.""" Ta ƙarasa maganar tare da gangarowar hawayen da tun ɗazu take riƙewa a cikin idanunta. """Idan ba haka bane to yaya ne? Sanin kanki ne babban burinmu a yanzu ni da Baffanki da ƴan'uwanki" "mu hannanta ki a hannun miji na gari wanda muka yarda da nagartar halayensa. Me yasa baza ki sadaukar da farin cikinki don ki cika mana burinmu ba?""" """Kiyi haƙuri Innaye.""" Ta sake faɗa cikin kuka mai tsanani. Duk da matsanancin tausayinta da ya cika zuciyar Innaye bata bari yayi tasiri a fuskarta ba. Haka ta cigaba da tsattsareta da maganganu masu karya zuciya har sai da suka kai gaɓar da Zulaikha ta ɗaukar mata alƙawarin suna komawa gida za ta ba masu sonta damar fitowa neman aurenta. Kuma duk wanda su iyayenta suka tabbatar ya fi nagarta ko da zuciyarta ba ta so za ta amince a ɗaura musu aure. """Allah yayi miki albarka Auta ta. In Allah ya yarda baza ki taɓa yin da na sani ba a auren da za muyi miki." "Allah yayi miki albarka.""" Duk yadda addu'a da saka albarkar suka yi mata daɗi a zuciya ta kasa amsawa a fili sai a zuciya. Sunkuyar "da kanta ƙasa sosai ta sake yi wasu sabbin hawayen na sake ɓalle mata, don Allah ya sani, Aure, ta bar gaban Innaye zuwa gidan wani ƙaton gardi haihata-haihata shi ne abu na ƙarshe da bata fatan ya faru a kanta." Kuma ita da kanta idan za'a ɗora mata wuƙa a maƙogwaro baza ta taɓa cewa ga dalilin da yasa take ƙin aure a rayuwarta ba. ****** ****** """Uhmmmm! In faɗa miki gaskiya Bintu? Kin ga duk irin matsananciyar soyayyar da kike ganin tana" "gudana tsakaninki da Abdul-hafiz? Wallahi baza ki taɓa samun kwanciyar hankalin mijinki da nutsuwarsa guri ɗaya ba matuƙar tsohuwar nan tana raye. Iya zallar gaskiyar magana kenan, babu wani ɓoye-ɓoye" ko kwana-kwana. "Kar fa ki manta, duk lalacewarta da ƙauyancinta mahaifiyarsa ce. Akwai wannan ƙauna da soyayyar ta" "musamman da Allah ya saka tsakanin ɗa da mahaifiya, to ke wacece da za ki ce dole ya fifita ki akan mahaifiyarsa?" Ai in faɗa miki ƙawata kin riga kin baro shiri tun rani. Yo uwar miji na birni ma ya aka ƙare da ita ballantana ta ƙauye? Waɗanda tun asali sun riga sun ginu da rayuwa akan makirci da matsanancin sa'ido "na tsiya ga bin ƙwaƙƙwafi? Ai fa ina sake jaddada miki sai dai kiyi haƙuri, shi yasa ni bana taɓa ganin laifin" ƴan matan da suke ture soyayya su ƙi auren saurayi muddin mahaifiyarsa tana raye. Uwar miji???!! Uhmm! Ciwon zuciya da hawan jini ake faɗa miki ƙawata. Ko ni abinda yasa baki san ɗan "ƙaramin biki da cikan da muka kwasa da tawa ba kafin Allah ya ɗauki rayuwarta don dai baki yi aure bane a lokacin, ko na faɗa miki irin matsalar da nake ciki ba lallai ki fahimci inda na dosa ba. Da Allah kuma ya dubi zuciyata sai ya raba mu tun kafin tafiyar tayi tsawo, shi yasa kika ganni yanzu hankalina" "kwance, kamar tsumma a randa." "Don haka idan za ki ɗauki mataki tun wuri gara ki ɗauki mataki, musamman a yanzu da wasu ƴan" "damarmaki suke a hannunki...""" """Kamar ya? Me kike nufi Raudha? Don Allah buɗa min bayanin sosai yadda zan gane.""" "Ta katse ta da tambayar a ɗokance, a zuciyarta take jin kamar wata gwaggwaɓar mafita Raudhan za ta" faɗa mata wanda zai haura da ita tudun mun tsira a cikin ƙanƙanin lokaci. "Ɗan dariya Raudha tayi tana karkaɗa ƙwayoyin idanunta, sai kuma ta gyara zama ta cigaba da cewa" """Daɗina da ke Bintu wani lokacin duk wayewarki kanki kullewa yake yi, jiya fa kika gama cika mana" "bakin mu ƙyale ki, ke kin san yadda za ki bi da komai daki-daki ki warware matsalar da ke gabanki. Yanzu kuma me ya canja miki ra'ayi kike neman mafita a waje na?""" """Uhmmm! Baza ki gane bane Raudha. Wallahi da farko duk yadda nake hango girman matsalar kamar" "bata kai haka ba. Allah ya sani ko ƙaramin kular abincina Sweetheart ban taba tsammanin zai iya dauka ya kai ma tsohuwar nan ba, sai ga shi ya goge min hadda ta hanyar kwasar abincin da na ɗauki fiye da awa biyu ina shirya mishi kuma na zuba a cikin tsadaddun kuloli ya kai ma ƙauyawan can. Allah ya gani wannan abu ya bakanta min rai ba kadan ba. Yanzu dai duk ba wannan ba, warware min maganar da" "kika yi ta karshe yadda zan gane sosai.""" "Ta ƙarasa maganar fuskarta na bayyana takaici, kamar a lokacin ne take kallon kulolinta a ɗakin Innaye." "Dariya sosai Raudha tayi kafin ta matsa da bakinta kusa da kunnen Bintu ta rad'a mata wasu maganganu," lokaci daya Bintu ta waro idanu warwaje had'e da bude baki a mamakance. Da sauri ta janye kunnenta hannunta dafe da haɓa ta ce """Ke Raudha !!! Anya kuwa zan iya? kina ganin wannan mafita ce da za ta samar da hanya mai ɓullewa?" "Ni dai gaskiya tsoro nake ji""" """Oho miki! Sai ki je kiyi ta jin tsoron. Ni dai shawara na baki, ko ki dauka ko ki cigaba da zama a cikin" "matsaloli ba ma matsala ba. Sai ma nan gaba idan ita da kanta tsohuwar da tsohonsa suka nemi dawowa gidanku da zama gaba ɗaya...""" """Haba-haba-haba-dai! Su ma baza su fara ba. Sai ka ce a garin gaɓa-gaɓa.""" Bintu ta katse ta da sauri hankalinta a tashe. """Kina ganin bazai yiwu ba? Su ai daman a garin gaɓa-gaɓan su ke. Kuma ma kanki farau zama gida ɗaya" "da iyayen miji? Kin san dai ɗansu na da wannan ƙaton gidan da duk ƙauyensu babu irinsa, kuma mai ɓangarori da yawa baza su taɓa yarda ya kama musu haya ba. Yanzu dai tashi ki tafi Ofis, daga baya ma karasa maganar...""" Ita kaɗai a cikin Ofishinta ta gama tunanin irin maganganun da suka tattauna da Raudha kafin ta ƙaraso "asibitin. Da farko, sam bata ji a zuciyarta za ta iya aiwatar da shawarar da Raudha ta bata ba, amma a yanzu da ta ƙara yi ma al'amarin karatun ta nutsu sai ta fahimci lallai fa ya kamata ta ɗauki mataki tun kafin wankin hula ya kaita dare. Kuma a yanzu dai babu wani mataki da take gani a matsayin mafita ta" gaggawa face bin hanyar da Raudha ta ɗora ta akai. "A hankali, ta mik'a hannu ta dauki takardar da ke ajiye akan teburin gabanta, sakamakon gwajin da aka" yi ma Innaye ne don ganin ko tana da ciwon suger ko babu. "Ba tare da ta buɗe ta ga me sakamakon ya ƙunsa ba ta keta shi gida biyu, hakan be ishe ta ba, sai da ta" ƙara yayyaga shi gutsi-gutsi sannan ta watsa a cikin abin zuba sharar da ke cikin ofishin. "Tattara yan karikitanta tayi ta zuba a cikin jaka, ta ɗauki wayarta da ke ajiye a gefe ta gyara zaman" mayafinta sannan ta fice daga cikin Ofishin. Bata ɓata lokaci ba tayi sallama da sauran abokan aikinta bayan ta hannanta komai ga likitan da ta karɓe ta ta shige motarta ta bar asibitin. "Kafin ta ƙarasa gida, sai da ta biya wani babban shagon sayar da magani ta sayi magunguna da alluran da" "za ta ɗora Innaye akai a matsayin na ciwukan jikinta sannan ta wuce gida. A gefe guda, tana jin wani nutsuwa na musamman yana ratsa zuciya da gaɓɓan jikinta." ******* Duk matsananciyar fara'ar da ke fuskarta lokaci ɗaya ɗaukewa tayi ɗif! Sakamakon ganin wasu setin "kuloli har guda uku da ya nuna mata da cewar a cikinsu za a cigaba da zuba ma su Innaye abinci. Saɓanin waɗanda ta ware guda biyu masu matsanancin arha da sauƙin kuɗi, ta kuma tabbatar ma Rabi duk halin" da ake ciki in dai ba ita ta canja ba kar a taɓa canja su wajen zuba ma Innaye da Autarta abinci. """My Dear? Lafiya kuwa? Me ya canja yanayinki lokaci ɗaya haka?""" "Ya tambayeta cikin kulawa da tarairaya, lokaci ɗaya shi ma yanayin fuskarsa ta ɗan canja saboda" damuwar da ta shiga duk da bai san ko ta mece ce ba. "Duk yadda ta so wayancewa kasawa tayi, sai kawai ta ɓuge da cewa" """Uhmmm!""" "Sai kuma ta sake wulƙita idanunta kan kuloli biyun da ya siyo a matsayin nata kulolin, canjin wancan da" ya kai ma Innaye abinci irinsa sak sai banbancin kala da kuma wani sabo mai zane daban da ya siyo mata don faranta zuciyarta. "A hankali ta miƙa hannu ta ɗauki ɗaya daga cikin kwalin kulolin wanda ya kasance irin nata, reciept na" "kuɗin kular da ke manne a jikin kwalin ta duba, dubu ɗari da hamsin ya siya, ita kuwa da yake Oder ne da kuɗin kawowa da komai a dubu da ashirin ya iso mata har gida." "Ajiyewa tayi ta ɗauki ɗaya kwalin kular, ita kuma dubu tamanin da biyar take. Ba kunya ba ta sake duba" "kulolin da suke matsayin na su Innaye sai taga ɗaya dubu arba'in, ɗaya dubu talatin da biyar, ɗaya dubu arba'in da takwas." "Duk da kuɗaɗen da aka siyo kuloli ukun basu taru sunyi kuɗin nata guda biyu ba, ta rasa dalilin da yasa" ranta yayi mummunan ɓaci da ganin kulolin a matsayin na su Innaye. 'Bintu ki nutsu fa... Idan kina son komai ya tafi miki dai-dai sai kin saka siyasa a ciki.' Wani sashe na zuciyarta ya ankarar da ita. Wannan tunanin da tayi yasa da sauri tayi ƙoƙarin kawar da damuwar fuskarta ta maye gurbinsa da murmushi. """Uhmmm!""" Ta sake cewa a karo na biyu. """Allah dai ya ƙara mana imani da lafiya Sweethert. Wallahi yau na ga abubuwa kala-kala masu ɗaga" "hankali a asibiti, ni da nake ta damuwar ciwon Innaye sai naga ashe tana cikin nagartattun tsoffi masu" "lafiya da ƙwarin jiki sosai a wannan zamani da muke ciki. Allah ya ƙara mata lafiya da nisan kwana.""" """Amin ya Allah.""" Ya amsa da sauri yana sauke ajiyar zuciya na samun kwanciyar hankali. """Kuloli sunyi kyau gaba ɗaya Sweethert. Allah ya ƙara buɗi da arziki mai albarka.""" """Ameen.""" Ya sake amsawa cikin jin daɗi da farin cikin da ya gaza ɓoyuwa a zuciyarsa. Ledar magani da alluran Innaye da ke ajiye kusa da ita ta janyo ta fara nuna masa tana mishi ƙarin bayani a rarrabe. "'Daman arashi akayi, bata yi tsammanin dawowarsu zai zo lokaci ɗaya ba sai ga shi tana shiga da" motarta cikin gidan shi ma direba ya shiga da tasa. Lokacin da misalin ƙarfe biyu da minti arba'in da biyar na rana. "A yadda ta saba idan tana aikin safe kuma ta tsara tun tana hanya, idan ta isa gidan ko a gurguje ne za ta" "samar mishi da lafiyayyen abincin da zai ci idan ya dawo. Tunda ƙa'idar lokacin dawowarsa a kullum huɗu da rabi ne zuwa biyar na yamma. Sai dai idan da wata ƙwaƙƙwaran dalili yakan ɗauki askis a gurin aiki kamar dai yau ɗin da ya dawo ba lokacin da ya saba ba, duk da bata san dalilin dawowar tasa a yau" ba. "Bayan ta yi masa sannu da zuwa tun a tsakar gidan, jakar hannunsa ta Ofis da wayoyinsa biyu ta karɓa ta" "wuce masa da su ciki, duk da farko so tayi su jera amma ya ce ta shiga ciki yana tafe." Da kanshi ya dinga shiga da kwalayen kulolin yana ajiyewa a gabanta bayan direba ya gama aje masa su a ƙofar falon har ya gama shiga da su gaba ɗaya. "Tun ma kafin yayi mata bayanin kulolin, har fuskarta ya cika da matsananciyar fara'a tana jin ƙarin" "matsananciyar ƙauna da soyayyarsa a zuciyarta. A tunaninta, gaba ɗaya kuloli biyar ɗin ya siyo ne don wanke zuciyarta daga laifin da yayi mata na jiya." "Tun kafin ya ce komai, ta bashi kyakkyawan runguma da sumbata biyu a kuncinsa dama da hagu, ta" "kuma ƙara da godiya da addu'ar Allah ya ƙara buɗi. Ranta bai fara ɓaci ba sai da ya ware biyu a matsayin nata uku kuma na mahaifiyarsa. Domin a idanunta, da saƙar wani ɓangare na zuciyarta, sai take ga kamar ba asalin kuɗaɗen kulolin da ya kira na Innaye aka rubuta a jikinsu ba. Kamar dai sun nin-ninka haka, kamar dai an rubuta kuɗi kaɗan ne domin a ninke ta a baibai. Idan ba haka ba taya za'a ce kuloli" masu sauƙi haka yanayin zane da ƙayatuwansu har sun fi na ta masu tsada kyau a idanun mai kallo?' Ƙoƙarin kawar da tunanin komai tayi a zuciyarta ta tsayar da hankalinta guri ɗaya ta cigaba da yi mishi bayanin magunguna da alluran. """Alhamdulillahi! Duk sakamakon gwaje-gwajen nata sun fito yau. Irin ciwukan da mukai hasashen" "samu a jikinta ma ba'a samu ba. Ba ta da ciwon suger kuma babu hawan jini, ba ta ulcer, hanta ma da ake tsammanin za'a samu a jikinta duk babu. Ka ga amfanin yin gwaje-gwaje sosai kafin a fara shan" "magunguna ko?""" Ta ƙarasa maganar idanunta cikin nashi tana sakar mishi murmushi. """Ƙwarai kuwa Dr. Bintu.""" Ya amsa bayan ya mayar mata da martanin murmushinta. Hararan wasa da soyayya ta jefe shi da shi kafin ta cigaba da cewa. """Izuwa yanzu abu biyu zuwa uku dai muka tabbatar suna damun Innaye. Ɗan typhoid ne kaɗan, sai" "maleria, sai kuma rashin hutu da bata cika samu ba. Duba da yanayin shekarunta, a yanzu ta kai matakin da ba ko wane irin aiki da ta saba yi ada can za ta cigaba da yi ba. Lallai tana buƙatar ta dinga hutawa sosai. Ka ga waɗannan su ne magunguna da alluran da zan ɗora ta akai, in sha Allahu cikin ƙanƙanin" "lokaci duk wani ciwo da yake damunta za mu neme shi mu rasa.""" """Ma sha Allah! Allah yasa haka My Dear, don dai Allah ya sani waɗannan ƙananun ciwo ce ciwo cen da" "suke addabar Innaye cikin satittikannan suna matuƙar ɗaga min hankali.""" """Kar ka damu. Za ta warke da wuri in Allah ya yarda.""" Ta amsa a fili. A zuciyarta kuwa cewa tayi 'In sha Allahu ta kusa macewa gaba ɗaya ma kai ka huta nima in huta.' Ruwan gora me madaidaicin sanyi da tun kafin shigowarsa ta ɗauko a cikin frig ta tsiyaya a kofi ta kafa "mishi a baki cike da soyayya, kallon ƙwayar idanun junansu suke yi cike da shauƙi a zukatansu, don haka" bai ma san lokacin da ya shanye ruwan ba sai da ya ji ta janye kofin daga bakinshi. Hannunshi ta kama kamar ƙaramin yaro suna tafe zuwa dakinshi tana ba shi labarin wasu dattijai biyu "mata da aka kawo asubitinsu, shekarunsu bai kai na Innaye ba amma irin ciwukan da suke jikinsu sam ita ba ta d'auke da su." """Ka ga wannan ke k'ara nuna mana ba wani gata ko rayuwa a cikin birni ke hana bawa ya kamu da" "cututtuka ba. Abin ikon Allah ne kawai da jarabawarsa, sai mu k'ara gode ma Allah da ya kawo mana na ta jarabawar da sauk'i. Allah ya k'ara mata lafiya.""" Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke na k'ara samun kwanciyar hankali da maganganunta. Kafin ya amsa da """Amin ya Allah My dear. Haka ne kam, na ji dadin maganganunki. Ina tsananin son ki matata...""" """Ni ma ina son ka Mijina.""" "Ta katse shi da amsar tun kafin ya aje numfashin maganarsa, fuskarta cike da murmushi." "Kamar ko da yaushe in dai ya dawo tana gidan, ita ta taya shi ya rage kayan jikinsa sannan ta shige" bandaki ta hada mishi ruwan wanka. A zuciyarta take dariyar yadda ta iya kirkirar zancen an kawo tsofaffin da suka fi Innaye jin jiki don kawai ta kwantar da hankalinsa. 'Yo miye a ciki? A fakaice dai ta isar mishi da sakon ba rayuwa a birni ko kauye ke sa mutum ya kamu "da cututtuka ba. Duk da dai ita da kanta takan kiyaye tu'ammali da kayan kauyen da kuma 'yan kauyen don gudun kamuwa da cutuka. In jifa ya wuce kanta ya fada kan ko ma waye, gara su can sun saba" rayuwa a haka.' "Ko da ta gama haɗa mishi ruwan wanka, kafin ta fice a ɗakin sai da ta fitar mishi da ƙananun kayan shan" "iska da zai saka idan ya fito daga wanka, ta fesa turare, ta ajiye a gefen gadon sannan ta fita zuwa kicin a gaggauce domin samar musu abinda za su ci." "Baba Rabi ta gama rabon abinci kenan ta shiga cikin kicin ɗin, kamar ko wane lokaci in dai ta shiga a irin" "wannan lokacin, bubbuɗe kular abincin kowa tayi taga yadda aka zuba masa." Idanunta ƙur akan miyar su Innaye da aka zuba tsokokin nama masu yawa saɓanin yadda aka saba sakawa. """Rabi?""" Ta kira sunanta bayan ta janye idanunta daga kan miyar suna kallon juna cikin ido. """Na'am Hajiya""" Ta amsa a ladabce. """Yau hannunki ne ya suɓuce kika loda nama haka da uban yawa a miya har aka rasa yadda za'ayi da" "shi?""" Ta tambayeta tana ƙara tsattsare ta da idanu. """A'a Hajiya. Kawai dai ji nayi Auta ta ce Innayen ba ta da lafiya, shi yasa nayi sha'awar in ɗan ƙara musu" "naman... kuma ma fa da yanka biyu ne kawai na ƙara kam ukun da kika ce in dinga zuba musu.""" Fuska a ɗaure ta buɗe baki za ta daka ma Rabi tsawa ta tuhumi ina ruwanta da ciwon Innaye sai Zulaikha "ta sanyo kai cikin kicin ɗin, bakinta ɗauke da siririyar sallama. A hannunta riƙe da kular da aka zuba ma" Innaye indomie. """Barka da dawowa.""" "Ta faɗa a taƙaice, bayan ta yi ma Bintu kallo ɗaya ta kawar da kanta. Kai tsaye ta nufi gurin ajiye" kwanonin wanke-wanke ta ajiye kular hannunta. """Baba Rabi sannu da aiki. An gama abincin ne?""" Ta tambayi Rabi wacce tun bayan shigowar Zulaikha da kulolin ƙirjinta ke bugun tara-tara. "Ko kaɗan bata so shigowar Auta da kulolin a daidai lokacin da Bintu take cikin kicin ɗin ba. A yadda ta so," bayan ta kai musu abincinsu ne za ta ɗauko kula da farantan ta shiga da su cikin gidan ta wanke a sirrance kamar yadda ta wanke tukunyar da tayi amfani da ita ba tare da Bintu ta san an dafa ma Innaye indomie ba. Amma yanzu ganin kular ta san dole Bintu ta tambayi me aka dafa saɓanin wanda aka gama girkawa yanzu? Ganin ba ta da mafitar da ya wuce amsa tambayar Zulaikha yasa ta ce """Eh! Na gama. Je ki, yanzu zan shigo muku da shi...""" """A'a! tunda ga ni mene na wahal da kanki? Sannu da aiki. Bani kawai in wuce mana da shi.""" "Ta ƙarasa maganar idanunta na kan murfin kular miyarsu da ta gani a hannun Bintu, wacce take tsaye" "kamar mutum-mutumi, sai idanu kaɗai take iya rabawa a tsakanin su biyun, fuskarta a tamke ƙwarai" kamar bata taɓa sanin wani abu dariya ba. "Tun ranar da suka zo gidan, a cikin wannan kular ake zuba musu abinci. Don haka bata tsaya jiran Baba" "Rabi da ke harhaɗa abinda za ta ce mata ba don ta hana ta ɗaukar abincin kawai ta ƙarasa gaban Bintu ta ɗauki kular da aka zuba farar shinkafar, ta miƙa hannu za ta zare murfin kular miyar daga hannun Bintu" da sauri ta janye hannunta tare da aika ma Auta wata matsiyaciyar harara. """Waccan kular da kika shigo da ita yanzu, me aka zuba a ciki?""" Ta jefa mata tambayar cikin fushi tana aika mata da kallon tsana a fili. "Duk cikin dangin mijin nata ta fi tsanar yarinyar, ko don ta kasance a mafiyawancin lokuta tana yi mata" abubuwa na gatsali da raini ne? oho!! """Au! Wai wancan kular?""" "Ta mayar mata da tambaya cikin tambaya a raine, da kuma irin salon da ta san Bintun ta masifar tsana." Sai kuma ta ɗanyi murmushi tana kallonta cikin ido itama da yanayin kallon yadda ba kya so na ni ma ba son ki nake yi ba. """Innaye, da kika tafi da ita asibiti ko karyawa bata yi ba kika yasar da ita a wulaƙance, ita na saka aka" "dafa ma indomie da soyayyen ƙwai. Bata isa ba ne ko ni ɗin ban isa in saka a dafa mata bane?""" "Ta buɗe baki za tayi magana cikin masifa da ɗaga murya sai ta tuna Hafiz yana gidan, duk da akwai" "tazara mai yawa tsakanin ɗakunansu da kicin ɗin lallai idan ta ce za ta ɗaga murya zai iya jiyo ta. A matakin da ta ɗauki aniyar ɗauka kuwa, har su Innaye su bar gidan a fili dai baza ta taɓa nuna mishi wani" alamu na tsana da ƙiyayyarsu da ke danƙare da zuciyarta ba. Duk yadda ranta yakai ƙololuwa gurin ɓaci da tambayoyin rainin da Zulaika tayi mata sai kawai ta ɓuge "da girgiza kai, ta saki ƙarfafan ƙwafa sau biyu. A wulaƙance ta saki murfin kular da ke hannunta ya faɗi ƙasa sannan ta fice daga cikin kicin ɗin da sassarfa." "Tana da ƙaramin kicin a jikin ɗakinta da take amfani da shi ita kaɗai, don haka can ta nufa zuciyarta cike" "da saƙe-saƙen yadda za ta saka aci mata uban Zulaikha la'ada waje kafin su bar garin Abuja, wannan alƙawari ne ta ɗauka ma kanta." Fuska a dame Baba Rabi ta kalli Zulaikha ta ce """Auta Ba kiyi kalar yara masu rashin kunya ba. Saboda Allah me yasa kike son ɓata wayon ki da" "kyakkyawar tarbiyar da nake gani a tare da ke ta hanyar biye ma Hajiya.? Matar yayanki ce fa...""" """Ke baki ga yadda take mana bane Baba Rabi? Don kawai mu ƴan ƙauye ne sai mu zama ababen" "wulaƙanci da tozartawa a gurinta? In dai za ta taya na rantse da Allah ni kuma sai na sayar mata. Allahn da ya halicce mu bai wulaƙanta mu ba babu wata ƴar adam da zan zauna ta wulaƙanta mu.""" Murfin kular ta ɗauko ta rufe ta sungumi kular miyan cikin fushi bakinta a gaba ta fice daga cikin kicin ɗin. "Tana zuwa falo, suka yi kiciɓis da Hafiz shi kuma ya sauko daga sama inda ɗakunansu suke. Duk da yadda" "ƙirjinta ya buga daram saboda tunanin yadda ya gaji da buga ƙofa ta ƙi buɗe masa da safe har ya gaji ya tafi. Ko kaɗan bata bari fuskarta ya nuna tsorata ba, sai ma ƙara murtukewa da tayi ta ƙara turo baki" gaba kamar zai taɓi bango. Ja tayi ta tsaya tana kallonshi kamar yadda yake kallonta. """Sannu da dawowa.""" Ta faɗa cikin guna-gunin da ba ta da tabbacin ya ji ko bai ji ba. "A ɓangarensa kuwa, da mamaki sosai a fuskarsa yake kallonta. Bai manta yadda jiya ya kora mata" kashaidin kar ta kuskura ya sake ganinta a ɓangarensu ba. Hallau bai manta yadda ya so ya lakaɗa mata dukan tsiya kafin ya fita ofis Allah ya taimaketa ta hanyar kulle ƙofar da tayi ta bar makulli a jiki ba. "Haushin jiya da yau ne suka taso suka ƙara turnuƙe shi, don haka cikin tsawa ya ce mata" """Me ya kawo ki nan? Ban faɗa miki kar in sake ganinki a ɓangaren nan ba...?""" Da sauri ta katse shi tun kafin ya aje numfashin maganarsa """Ni ma fa ba son raina na shigo nan ɗin ba. Innaye ce ta ce lallai daga yau ni zan dinga zuwa karɓa" "mana abinci, idan mun gama kuma in kwaso kulolin in shigo da su, idan kuma baka yarda ba, sai ka je ka tambayeta.""" """Barka da dawowa Uban ɗakina.""" Muryar Baba Rabi a ladabce ya sauka a kunnuwanshi. Harara ya galla ma Zulaikha sannan yaja tsaki ƙasa-ƙasa. Ƙoƙarin sassauta murya yayi ya amsa gaisuwar "Baba a mutunce kamar yadda ya saba. Karaf! Idanunsa suka faɗa kan sabbin kulolin da ya siyo anan falon, inda ya barsu har lokacin a gurin suke." "Umarnin kwashewa zuwa kicin yayi ma Baba Rabi bayan ya nuna mata waɗanda ya siyo ma Innaye, ya" kuma gargaɗe ta kar a sake zuba ma Innaye abinci cikin tsaffin kuloli saɓanin sababbin da ya siyo. "Ko da ya waiga inda Zulaikha ke tsaye, babu ita babu dalilinta. Abinda bai sani ba tun da ya fara amsa" gaisuwar Baba Rabi saɗaf-saɗaf ta fice daga cikin falon. ******* Ɗabi'a ce da suka taso suka tarar da Innaye a cikinta jiran sallah tun kafin lokacinta ya ƙarato. Har yanzu "kuma da ta manyanta bata bar wannan kyakkyawan ɗabi'a ba, sai ma ƙara ƙaimi da tayi." Ƙarfe shida da minti goma ta shige banɗaki ta ɗauro alwala. Wuf! Zulaikha tayi ta ɗauki flask ɗin da ake "zuba musu ruwan zafi ta fice daga ɗakin, daman damar da take jira kenan." Hatta hijabin jikinta da kusan ko wane lokaci ba ta rabo da shi a jikinta sai a hanya ta sanya. Kai tsaye ta "nufi can cikin gidan ba tare da tsoro ko shakkar komai ba, tana tafe tana kalle-kallen yadda kyawawan" "shuke-shuken fulawoyi suka ƙara ƙawata tsakar gidan, kuma da yake suna samun kyakkyawan kulawa" "daga mai aiki na musamman da aka ɗaukar musu, luf-luf suke gwanin ban sha'awa kamar a lokacin damina." "Ko da ta isa ƙofar babban falon, sau ɗaya ta danna ƙararrawar neman izini kafin ta murɗa hannun ƙofar" ba tare da jiran izinin shiga daga can ciki ba. Kasancewar lokaci ne da in dai suna gida su biyun za'a same su cikin nishaɗi ne da yanayi na soyayya. Ko "a yanzu, suna zaune akan doguwar kujera, fiye da rabin jikin Bintu gaba ɗaya a jikin Hafiz take, suna sanye da kayan shan iska na turawa. Ga ɗan ƙaramin teburin glass nan a gabansu ɗauke da yankakkun" kayan marmari. A mamakance suka ɗaga idanu suna kallon Zulaikha wacce ta bayyana a gabansu tsulum kamar an jefo "ta. Ita kanta sai a lokacin ta lura da irin katoɓarar da tayi, don haka da saurin gaske kuma a daburce ta juya baya tana soshe-soshe hankalinta a tashe." """A'uzubillahi minasshaiɗanirrajim.""" "Ta janyo a'uziyyar a ruɗe, domin duk iya tsawon rayuwarta wannan shi ne karo na farko da taga mace da" namiji a cikin makamancin irin wannan halin. Tsananin ɓacin rai da baƙin ciki cakuɗe da dunƙulallen takaici yasa Bintu ta kasa magana. Sai kawai ta "mayar da kanta kan ƙirjin Hafiz ta kwantar, ta lumshe idanunta tana jan numfashi sama-sama saboda" ɓacin rai. "A ɓangaren Hafiz kuwa duk da sanin da yayi Zulaikha ba ta da hankali, bai taɓa tsammanin rashin" hankalin nata ya kai haka ba. Ko da ya buɗe baki da nufin zazzaga mata bala'i sai ya rasa ma abinda zai ce "mata, domin da ace masifa da bala'i ko duka na saka ɗan'adam ya kiyayi lamarin wani, lallai da tuntuni Zulai ta daɗe da fita daga cikin harkokinsa gaba ɗaya." "A karo na barkatai ya sake kallon yadda take ta dawurwura guri ɗaya, ita bata fita daga falon ba kuma ita" bata jiyo ta fuskance su ba balle har ta faɗi abinda ya shigo da ita a daidai irin wannan lokacin. """Me ya kawo ki?""" Yayi ƙarfin halin tambayarta da shaƙaƙƙiyar murya. """Dama... Dama... Innaye ce ... ta ce... Dama... in zo in karɓi ruwan zafi...""" Ta faɗi maganar a rarrabe tana zazzare idanu a tsorace kamar za ta kife a gurin. Ta riga ta gama yanke ma ranta lallai mai hana Yaya Hafiz cin ƙaniyarta a daidai wannan lokacin sai dai "wani ikon Allah, don haka kawai sai ta fara matsar ƙwallah, ta san ko ta gudu sai ya bi ta har gaban Innaye ya tattaka ta, shi yasa ma bata yi yunƙurin gudu ba." "Sai dai ga mamakinta, tana jiran ta ji saukar duka ta ko ina a jikinta sai ji tayi ya sake cewa da shaƙaƙƙiyar" murya. """Je ki dafa a kicin.""" A kiɗime ta juyo tana kallonsu kamar bata ji abinda ya faɗa da kyau ba. Sai kuma ta sake juya musu baya da sauri tana ƙyaƙƙyafta idanu. A hanzarce kuma sai ta kama hanyar zuwa kicin ɗin har tana haɗawa da gudu-gudu. """Ke! Ke!! Ke!!! Ina za ki?""" Bintu ta dakatar da ita ta hanyar daka mata tsawa haɗe da jefa mata tambayar. "Cak! Taja ta tsaya a inda take ƙafafunta na rawa, amma bata juyo ta kalle su ba, kuma bata amsa" tambayar da Bintu tayi mata ba. """Sweethert? Wai ko dai ka manta da wa kake magana ne? Ba fa Rabi ba ce mai aikinmu. Zulai ce da ta" zo daga ƙauye kake cewa ta shiga kicin ɗina mai ɗauke da kayan girki na zamani ta dafa ruwan zafi. Ta iya amfani da Gas ko electric cooker ne? Ko kuwa so kake ta haddasa mana gobara saboda jahilci da "ƙauyancinta?""" Maganganun Bintu masu kama da saukar tafasasshen dalma a zuciyarta suka sauka a kunnuwanta. Jikinta a sanyaye ƙwarai ta juyo tana kallon Bintu da tun da ta faɗi maganganun ta maida kanta ta "kwantar a ƙirjin Hafiz kamar ba ita ta faɗa ba. A muzance, ta kalli Hafiz da shi ma ita yake kallo, idanunta ciccike da hawaye." Shi kuwa na shi idanun ɗauke da wani irin yanayi ne da baki bazai iya fassarawa ba. Kawar da fuskarshi "yayi daga gare ta ya mayar kan matarshi, kafin ya amsa mata da cewa" """Kuma fa haka ne My dear. Wallahi shaf na manta.""" Sai kuma ya sake mayar da idanunshi kan Zulaikha ba tare da wani yanayi na tausasawa ba ya ce """Ke ajiye flask ɗin nan. Yanzu idan mun tashi Bintu za ta dafa ruwan mu taho mata da shi, daman akwai" "magunguna da alluranta duk za mu haɗa mu taho da su. Ki gaishe ta da jiki, na dawo ofis ɗazu a gajiye ne shi yasa ban shigo ba.""" "Baza ta ce ga sadda ta ajiye flask ɗin ba, balle kuma ta bada labarin yadda aka yi har ta fice daga falon." Kawai ta tsinci kanta ne a ƙofar ɓangarensu tana tafe kamar ana jaye da ita saboda tsananin tashin hankali. "Har ta sa hannu za ta murɗa hannun ƙofar ɗakin sai kuma ta fasa, can kusa da famfo taje ta tsuguna," "tasha kukanta ta gode ma Allah kafin ta ɗaura alwala ta shige cikin ɗaki. Har wannan lokacin, jin ta take a muzance. Duk da ba yau ne farau da Bintu take ci mata mutunci da tozarta ta ba, amma bata taɓa gurza" mata wanda ya tsaya mata arai kuma ya ƙona mata zuciya irin wannan ba. A yadda take ji a ranta gidan da komai na cikinsa ya gama fice mata arai. Babu abinda take so irin ta "buɗe ido ta ganta a ƙauyensu. Ko da ta shiga cikin ɗakin, sai jan gefen hijabi take yi tana rufe fuskarta, sai kuma Allah ya taimaketa ta tarar Innaye na sallah, bata ɓata lokaci ba itama ta kabbarta sallah." Tana idarwa ta haye kan gado ta duƙunƙune jikinta da bargo kamar me jin sanyi. Tana jin shigowarsu "Hafiz da Bintu ta sake ɓoye kanta, kamar bata san Allah yayi ruwansu a cikin ɗakin ba." """Zulai barci take yi ne?""" Bintu ta tambaya da karaɗin murnar da Zulaikha ta rasa ko ta mece ce. "Ba Innaye da aka tambaya ba, hatta Hafiz sai da ya kalli Bintu da irin kallon nan na mamakin yau kuma ke" ce kike tambayar Zulai? Lura da irin katoɓarar da tayi yasa tayi saurin gyara maganarta da cewa """Gani kawai na yi ta kwanta ta rufa duk da zafin da ake yi. Ka san baya ba ta da kaɗan, idan ba ta da" "lafiya ne ai gara ta faɗa a bata magani. Anyway, Innaye ya ƙarfin jiki?""" "A hankali ta ajiye casbahan hannunta a gefe ɗaya ta ƙura ma Bintu idanu. A zuciyarta, addu'a take yi" "Allah ya kare ta da zuriarta daga sharrin Bintu. Dubi dai yanzu yadda take tambayarta ƙarfin jiki da kulawa da damuwa a fuskarta da yake a gaban Hafiz ne, kamar ba ita ce ta wulaƙantata ɗazu a asibiti ba." """Auta lafiyarta ƙalau. Ni kuma jiki na da sauƙi Alhamdulillah.""" "Ta amsa da yanayi na ba yabo ba fallasa, bayan ta yi matuƙar ƙoƙari gurin kawar da tunanin da ke" danƙare a zuciyarta. "Irin kallon da Innaye ta ƙure ta da shi, shi ya ɗan sanyayar mata da jiki. Nan take ta fara addu'a a" zuciyarta kar Allah yasa Innaye ta tona mata asirin irin yadda ta banzatar da ita ɗazu a asibiti. Ko da taji amsar da Innayen ta ba ta ta kasa sakin jiki ta cigaba da kwarkwasa kamar yadda ta shiga cikin ɗakin da farko. "Ganin har lokacin idanun Innaye na kanta, sai ta fara jin ta a muzance. A dole ta saukar da ƙwayoyin" "idanunta ƙasa ƙirjinta na bugawa kaɗan-kaɗan. Ta kasa ƙara cewa komai, sai Hafiz ne ya amsa maganar" Innaye da cewa """Ma sha Allah! Allah ya ƙara sauƙi Innaye. Ga magunguna da alluranki nan Bintu ta taho da su." Kuma kin ji wani ikon Allah ashe duk irin ciwukan da aka yi tsammanin samu a jikinki ma ba'a samu ba. "Zazzaɓin cizon sauro ne kawai sai typhoid da aka samu a jininki. Kin ga a wannan karon dai ya zama dole Innaye ki haƙura da kwanciya babu gidan sauro. Kuma shan ruwan ƙauyen nan ma ya zama dole ki haƙura da shi, zan dinga aika miki da tsaftataccen ruwa duk ƙarshen wata in sha Allah, domin likitoci sun" "tabbatar da hanya ta farko ta kamuwa da typhoid daga ƙazantaccen ruwan sha ne...""" """Hafizu, wannan ruwan da kake kira da ƙazantacce tun kafin a haife ka shi muke sha, muke komai da" "shi. Kuma kai ɗin ma kafin barowarka ƙauyen ƙazantaccen ruwan nan dai kake sha, kuma ya rayar da kai" "har zuwa girmanka.""" Innaye ta katse shi da ɗan murmushi a fuskarta na jin daɗin yadda ƙarara ɗan nata ke nuna damuwa da lafiyarta. "Ƙara gyara zama yayi yana cigaba da yi mata ƙarin bayani, a fuska da muryarsa babu abinda ke fita sai" matsananciyar ƙaunar mahaifiyarsa. """Duk da haka dai Innaye. Kin san yanzu abubuwan sun canja ba kamar da ba. Yanzu cututtuka ba su" "wuyar shiga jikin ɗan Adam. Ya zama dole mu dinga ƙoƙarin kiyaye duk abubuwan da aka tabbatar suna da rawar da suke takawa wajen ɗabbaƙa samuwar cututtuka a jikinmu. Amma idan baki gamsu ba ga Bintu nan, tunda ita likita ce za ta miki cikakken bayanin da za ki fahimta na abubuwan da ya kamata ki kiyaye.""" Ya maida idanu kan Bintu yana jiran tayi ma Innaye ƙarin bayani kamar yadda ya nema. Abu ɗaya da bai "sani ba shi ne Bintu dai ba baka sai kunne, sai a yanzu ne duk irin cin kashi da tozarcin da tayi ma Innaye tun bayan fitarsu yake dawo mata arai, a tsorace take sosai kar Innaye tayi suɓul da bakan furta ɗaya daga cikin abinda ta aikata mata." """Eh! Haka ne My Dear. Uhmmm! Innaye don Allah ki kiyaye. Duk abinda zan faɗa My dear ya riga ya" "faɗa, yanzu dai bari in haɗa alluran inyi miki in baki magungunan. Ina fatan kin ci abinci?""" Ta ƙarasa da tambayar har lokacin ta kasa ɗaga idanu ta kalli Innaye cikin ido. """Eh na ci.""" Innaye ta amsa idanunta na kallon irin ruɗewar da Bintu take ciki. Duk da tayi hasashen me ya ɗaga "hankalin Bintu cikin ƙanƙanin lokaci haka, amma sam bata yi niyyar tona abinda tayi mata ba. Idan tayi" haka kamar bata gode Allah da ya dube ta ya haɗa ta da Karimatu a lokacin da Bintu ta so tozarta ta bane. Tana kallo Bintu ta haɗa allurai har guda biyu tayi mata. Sannan ta ɓallo magunguna kala huɗu ko wanne ɗai-ɗai ta miƙa mata. Hafiz ya buɗe ɗaya daga cikin gororin ruwan da ke cikin ɗakin ya zuba a kofi ya miƙa mata. Sai da tasha magungunan ta haɗiye sannan Bintu ta fice daga cikin ɗakin bayan ta basu uzurin za ta je ta amsa waya. Nan ta bar Hafiz suna cigaba da hira da Innaye ita dai ta cikawa bujenta iska tana sauke ajiyar zuciyar samun nutsuwa. Har lokacin bata daina addu'ar Allah ya kulle bakin Innaye kar ya bata ikon tona asirin tozarcin da tayi mata a asibiti. "Duk abinda ke faruwa har zuwa ficewar Bintu, da ficewar Hafiz bayan an kira sallar isha'i, Zulaikha tana" jin su. Ko ƙwaƙƙwaran motsi bata yi bane domin ba ta ƙaunar tozali da ɗaya daga cikin fuskokin su biyun. """Auta? Wai lafiya kike kuwa?""" "Innaye ta jefa mata tambayar lokacin da ta yaye rufar da tayi ma kanta, ta miƙe ta zauna akan gadon" tana mutsuttsuka idanunta kamar wacce ta farka daga barci. """Lafiya ƙalau. Kawai dai ba na jin daɗi ne.""" Ta amsa fuskarta ba walwala. """Wallahi Innaye duk na ƙosa mu koma gida.""" Ta sake faɗa fuskarta na bayyana gaskiyar maganar daga zuciyarta ne. Daƙiƙu talatin Innaye ta ɗauka tana karantar yanayinta. Irin shirun da Auta tayi tun bayan da ta idar da "sallah, ta san ba haka kawai bane. Amma tunda bata faɗa mata komai ba sai bata matsa mata da tambaya ba, don wani sashe na zuciyarta na tunanin ko don maganar auren da tayi mata ɗazu ne ya canja yanayinta? Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, kafin ta ce" """Ki kwantar da hankalinki. Kamar gobe ne za mu koma gida in sha Allahu.""" ***** "Duk da kasancewarta cikin mutane masu nauyin barci, irin numfarfashin da Innaye take ja sama-sama" tana saukewa a wahalce ya fi ƙarfin a ce ta gagara farkawa. "Bayan ƙarfin nishin kuma kusa da kusa suke kwance. Tun tana jin nishin kamar a mafarki, har dai daga" baya ta tabbatar ba mafarki take yi ba don haka ta farka a firgice. """Innaye? Inna lillahi... Me yake damunki?""" "Ta jera mata tambayoyin a ruɗe. Kafin ta amsa da saurin gaske ta miƙa hannu ta taɓa wuyan Innayen," matsanancin zafin da taji yasa tayi saurin ɗauke hannunta a gaggauce. """Subhanallahi... Jikinki zafi sosai Innaye... Zazzaɓi kike yi ne? Bari in kira Yaya.""" Ba tare da duba tsalawar da dare ya fara yi ba ta yunƙura za ta sauka akan gadon a galabaice Innaye ta riƙo hannunta. """Dare... dare ya yi... ki ƙyale.. shi zuwa safe.""" "Tayi maganar daƙyar, da yanayin da ke bayyana tana cikin mawuyacin hali." "Tafin hannun Zulaikha da ke cikin nata ta sake riƙewa sosai, ta ja hannun a hankali har zuwa kan goshinta," a jiga ce ta sake cewa """Kaina ciwo sosai kamar zai faɗi, ki kama min Auta.""" Ta sake faɗa a wahalce. Kasancewarta mai saurin kuka tuni har hawaye ya wanke mata fuska. Ta matsa sosai kusa da Innaye ta ɗauki kanta ta ɗora akan cinyarta. "Kamun kai tayi mata kamar yadda ta buƙata, bayan ta gama sai ta cigaba da tofa mata duk irin addu'ar" da ya zo bakinta. Ko da ta ɗaga idanu ta kalli agogon da ke maƙale a bango cikin ɗan madaidaicin hasken da suke bari a "kunne idan za su kwanta. Sai taga ƙarfe uku na dare saura minti takwas, sai a lokacin ita da kanta taga" rashin dacewa kiran Yaya Hafiz a wannan tsakiyar dare. "Duk irin barcin da ke idanunta tuni ta neme shi ta rasa, a taƙaice ma idanunta bushewa suka yi, idanunta" biyu tana hawaye tana tofe Innaye da addu'a har zuwa lokacin da ladanin unguwar ya kwaɗa kiran sallar farko. "A wannan dare, ta shiga cikin gagarumin tashin hankali ne irin wanda bata taɓa shiga ba a rayuwarta." Tun da tayi wayau bata taɓa ganin Innaye cikin ciwon da ya jigatar da ita ya fitar da ita a hayyacinta cikin ƙanƙanin lokaci irin haka ba. Ko wannan ciwon da take yi har ya zama sanadiyyar da yasa suka baro garinsu zuwa Abuja bai mata "tsanani haka ba. Bata taɓa tsammanin Innaye za ta kai asubahi a raye ba, ta gama fitar da rai da cewar Innaye za ta cigaba da rayuwa, saboda yadda numfashin ma a wahalce take ja tana saukewa daƙyar. Amma da yake rayuwa da mutuwa duk a hannun Allah suke sai ga shi cikin hukuncin Allah ana tayar da" iƙamar sallar asubah wani nannauyan barci yayi awon gaba da Innaye. "Minti ɗaya, biyu, sai ta kara kunnenta a hancin Innaye don ta ƙara tabbatar da barcin take yi ko dai ba" barcin bane? Sai da ta tabbatar barcin ne kafin ta iya kwantar da kan Innaye a hankali bisa filo ta sauka daga kan gadon. "Ƙafafunta duk sunyi tsami, idanuwanta sun kumbura sunyi tulu-tulu saboda kuka. Jikinta a sanyaye ta" shige banɗaki domin ɗauro alwala. "Ko da ta idar da sallah, bata tsaya yin Azkhar kamar yadda take yi duk bayan sallar asubahi ba tayi addu'a" "a gaggauce ta sake hayewa kan gadon tana ɗan tattaɓa jikin Innaye. Cikin hukuncin Allah kuma sai taji zazzafan zazzaɓin ya sauka gaba ɗaya, har ma wani zufa ne ya ɗan tsattsafo akan goshinta." Gefen hijabin da ke jikinta tasa ta goge ma Innaye gumin tana sauke nannauyan ajiyar zuciyar samun "nutsuwa. A nan kan gadon, ta cigaba da Azkhar har zuwa sadda wani daddaɗan barci ya kwasheta." Sallamar da Hafiz yake ta dokawa a ƙofar ɗakin shi ya farkar da ita a firgice daga wani mummunan "mafarki da take yi a daidai lokacin. Karaf idanunta suka faɗa kan agogo, ƙarfe bakwai da minti arba'in da" biyu na safe. "Izuwa lokacin, Hafiz ya gaji da sallamar da yake ta yi yana ƙarawa ya shiga cikin ɗakin don ganin lafiya" suke kuwa? Idanunsa cikin nata ya zabga mata harara. """Don tsabar iskanci kina ji ina ta doka sallama kin ƙi amsawa?""" """Yi haƙuri. Barci nake yi, sallamarka ce ta tashe ni. Ina kwana?""" "Ta jera mishi maganganun cikin sanyin murya, kamar dai ba Zulai ba da yasan ta bala'in raina shi." Irin yadda ta amsa mishi har sai da yasa shi ƙara kallonta sau ɗaya. Sai yaga ta sunkuyar da kanta ƙasa "tana wasa da yatsun hannayenta. Taɓe baki yayi, ya ƙarasa cikin ɗakin har kusa da gadon idanunsa akan Innaye da har lokacin take barci." """Wani irin barci Innaye take yi haka? Ina fatan dai lafiyarta ƙalau?""" Ya tambayeta ba tare da ya amsa gaisuwarta ba. Babban dalilin da yasa shi yin tambayar kuwa shi ne "barci bayan sallar asubahi ba ɗabi'ar Innaye bace, ko lokacin azumi ita ba ta komawa irin barcin nan na bayan sallar asubah." Zama take tai ta tasbihi da istigfari har gari yayi haske sosai tayi sallar walha. Ko za ta kwanta sai bayan "ta idar da sallar walha, tara da rabi zuwa karfe goma na safe." """Ba ta da lafiya. Kwana tayi da zazzaɓi mai zafi a jikinta kamar baza ta wayi gari ba...""" """Bakinki ya sari ɗanyen kashi. Sakarya kawai wacce bata iya magana ba. Kawai don ta kwana da zazzaɓi" "a jikinta sai ki ce kaman baza ta wayi gari ba?""" Nan ya cigaba da zazzaga mata faɗa ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba kawai don ta ce Innaye kamar baza ta wayi gari ba. "Ita dai Zulaikha shiru tayi mishi, a madadin ta ce wani abu ma sai ƙara sunkuyar da kanta ƙasa tayi" idanuwanta na tsiyayar da hawaye. A zuciyarta take ƙara tunanin irin rijiya da bayan da Innaye ta "tsallake jiya, duk da tana yarinya kuma ba'a taɓa yin mutuwa a gabanta ba ta san bata yi kuskuren cewa irin zazzaɓin da Innaye tayi jiya kamar baza ta wayi gari ba." "Amma tunda ba a gabanshi aka yi ba dole tayi mishi uzuri, ta san babu ma amfanin yi mishi ƙarin bayani" don bazai fahimce ta ba. Tana jin shi har ya gama zazzaga masifar da yake yi ya fice daga ɗakin a gaggauce yana jan tsaki. "Zuciyarsa cike da ɓacin ran kalmar da Zulaikha ta faɗa. Shi yasa sam ba ya shiri da yarinyar, bata iya" magana ba. Wasu lokutan haka take sakin maganganu kamar ta ci kashi. "Bai daɗe da fita ba ya dawo cikin ɗakin, Bintu na biye da shi cikin shirinta na fita aiki, sai ɓata fuska take" yi kamar anyi mata dole. "Amma ko da Hafiz ya juya yana nuna mata Innaye da yi mata ƙarin bayanin kwana da tayi da zazzaɓi, sai" tayi saurin daidaita fuskarta zuwa yanayin jimami da tausayawa. "Duk abinda take yi, ƙasa-ƙasa Zulaikha ke kallonta zuciyarta cike da mamakinta. Tana sane ko gaishe ta" "bata yi ba, don har lokacin ɓacin ran cin mutunci da tozarcin da tayi mata jiya bai bar zuciyarta ba." A tausashe Bintu ta kalli Hafiz tana mishi ƙarin bayani bayan ta ɗan tattaɓa jikin Innaye sama-sama. A "lokacin ita ma Innaye ta farka, ta buɗe idanunta a jigace tana rarraba idanu a tsakaninsu." """Sweetheart, ka kwantar da hankalinka. Daman dole za'a sami irin waɗannan ƙananun matsalolin." "Magunguna da alluran da na kawo mata masu kyau ne sosai, don haka a karon farko dole ta fuskanci irin waɗannan matsalolin, tunda a iya tsawon rayuwarta bata taɓa amfani da magunguna masu kyau da ƙarfin waɗannan ba. Cikin ƙanƙanin lokaci za ta daina fuskantar zazzaɓin, magungunan kuma za su" "fatattaki duk wani typhoid da maleria da yake jikinta.""" Da damuwa sosai a fuskarsa ya ce """Yanzu babu wani taimako da za'a iya mata ta daina fuskantar zazzaɓin? Ki dubi fa yadda idanunta suka" "yi zuru-zuru zazzaɓin dare ɗaya kawai.""" """I'm sorry to say gaskiya babu. Haka nan za muyi haƙuri ta cigaba da shan magungunan. Ka san kuma" "jiki-jiki, kowa da yadda magani da allura ke aiki a jikinshi. Ita wannan alamun shi ya bani tabbacin magani da alluran sun karɓe ta, kuma fa ba lallai yau tayi zazzaɓin ba. Ka kwantar da hankalinka pls.""" "Sai kuma ta mayar da hankalinta kan Innaye, a tausashe ta fara gaishe ta da jiki." """Sannu Innaye. Allah ya ƙara sauƙi. Yanzu dai Zulai ki kamata zuwa bayi a wanke mata baki tayi break" "fast, sai inyi mata allura kafin in fita. In sha Allah za ta samu sauki sosai.""" Ta ƙarasa maganar idanunta na kan Zulaikha da har lokacin ta ƙi yarda ta ɗaga fuska su kalli juna cikin ido. Ko kafin Zulaikha tayi yunƙurin ɗaga Innaye da ko magana bata iyawa har Hafiz ya tarairayota zuwa jikinsa a tausashe ya zaunar da ita. """Sannu Innaye. Allah ya baki lafiya.""" "Innaye dai ba baka sai kunne, ta kasa amsawa, sai raba idanu take yi tsakanin shi da Zulaikha da suke ta" jera mata sannu kamar za su ari baki. Taɓe baki Bintu tayi ta fice daga ɗakin bayan ta ba Hafiz uzurin bari taje ta ƙarasa shiryawa kafin Innaye ta gama. """Zanyi wanka... Sai inyi sallah.""" Innaye tayi maganar a hankali sosai yadda har basu ji abinda ta ce ba sai da Hafiz ya kara kunnensa daidai bakinta. "Zaunar da ita yayi a gefen gadon ya jingina mata filo, da rawar jiki ya shige banɗaki ya sirka mata ruwan" wanka. Har cikin banɗakin ya kai ta ya umarci Zulai ta taimaka mata tayi wanka da alwala kafin ya fice daga banɗakin. Can ɓangarensu ya koma a gaggauce. Ɗakinsa ya shige ya sauya kayan jikinsa saboda yamutsewar da "yayi a dalilin hidimta ma Innaye, bai ɓata lokaci ba ya fice daga cikin ɗakin ya wuce kicin. Tsaye yayi yana ɗan tunanin abinda ya kamata yayi, sai kuma ya buɗe kayan karin kumallon da Bintu ta shirya mishi a cikin basket zai wuce da shi Ofis ya ɗauko ɗaya daga cikin kulolin da ya siyo ma Innaye ya sake musu gaba ɗaya. Jikinsa sai rawa yake yi, bai ce ma Bintu da take tsaye tana kallonsa komai ba ya fice daga" kicin ɗin. "Duk abinda yake yi tana tsaye tana kallonshi ranta a ɓace, ta kasa ce mishi komai saboda ƙuncin zuciya." Bayan fitarsa a fili take ƙara Allah wadarai da zuwan Innaye gidanta. Domin a zuwansu ne ta ga abubuwa mabanbanta da bata taɓa tsammanin za ta gansu daga ɓangaren Hafiz ɗin ba. Tun bayan zuwansu kwanaki biyu kawai ta ɗauka tana yi musu abinci a mutunce kuma sau uku a rana. A "rana na uku ta sakar ma mai aikinta Rabi ragamar komai na su, aka koma basu dafaffen abinci sau ɗaya a rana." Ita da kanta ta ɗebi kayan tea da flask da kofuna ta kai musu can ɓangaren da suke. Sannan ta zauna cikin gwari-gwari tayi musu bayanin da ta ɗauki tsawon daƙiƙu tana tsarawa a zuciyarta. 'Innaye ga waɗannan kayayyakin. Kayan tea ne wadatacce da za ku dinga amfani da su gurin karyawa a "iya tsawon kwanakin da za kuyi a gidannan, idan sun ƙare kar kuji komai a faɗa min. Sannan a ɓangaren abincin rana da yamma, na faɗa ma Baba Rabi ta dinga dafa komai a wadace tana zubo muku isasshe a" kula wanda zai ishe ku cin rana da dare. "Kuyi haƙuri, kun san yanayin aikina ba na zama bane, a mafiyawancin lokuta ni da My dear abincin dare" ko na safe kawai muke iya ci tare cikin nutsuwa saboda yanayin aikinmu na da banbancin lokuta. Ko a cikin kwanaki biyunnan da kuka ga na samu lokacin kula da ku sosai hutu ne na samu a gurin aiki. "Yanzu kuma hutun ya ƙare, ina fatan za ku fahimce ni kuma kuyi min uzuri.'" "A lokacin, daga yadda Innaye tai ta saka mata albarka tana ƙara ƙarfafa mata gwuiwa akan aikinta na" ceton rayukan al'umma ya tabbatar mata Innaye ta gamsu da maganganunta ɗari bisa ɗari. Shi kuma Hafiz kasancewarsa irin mazajennan masu sakarwa matayensu ragamar komai bai taɓa tuhumar ko me za ta ko ta aikata ba. Ko da yaga an daina kai ma su Innaye abin karyawa sai dai sunƙin biredi kawai bai taɓa tambayarta dalili ba. "Ko yanzu ba ta tsammanin zai nuna mata wani ɓacin rai, amma irin wannan ɓare-ɓaren jikin da yake yi" akan tsohuwar shi ne abinda yake ƙona mata zuciya. A ganinta ba komai zai ƙara janyo mata a gurinsu ba sai ƙasƙanci da rashin godiya akan duk abinda za ta musu nan gaba. 'Saboda Allah in banda salon zubar da mutunci da niyyar janyo mata tozarci kayan karin kumallon da ta hana idanunta komawa barci ta shirya musu ita da shi shi ne zai juye nashi gaba ɗaya ya kai musu?' Dogon tsaki taja ɓacin ranta na ƙara hauhawa. "Ta daɗe a gurin tana saƙe-saƙe kafin ta wuce ta cigaba da shiryawa, duk bayan mintuna take jan tsaki" ƙasa-ƙasa idan ta tuno abinda ya faru. Haka nan ba don ranta na so ba ta sake raba nata abincin gida biyu ta zuba mishi rabi a kulolinsa. "Ko da Hafiz ya koma cikin ɗakin, a kan dadduma ya tarar da Innaye tana sallah a zaune. Ita kuma" Zulaikha tana tsaye jikin gado tana gyara shimfiɗar gadon. "Kusa da Innaye ya zauna, ya buɗe kulolin abincin ya fara zuba mata. Lafiyayyen alalen dankalin turawa" "ne da miyan ganye, a gefe guda kuma ga kunun gyaɗa da aka dama shi da madara, yayi fari kar gwanin" ban kyawun kallo a idanu. Sai ƙamshi yake fitarwa. "Ɗauri biyu ya zuba alalen dankalin a faranti, ya sa cokali ya buɗa cikinsa yadda zaiyi saurin shan iska." Kunun gyaɗar ma ɗan madaidaici ya zuba a kofi ya saka cokali yana jujjuyawa don kunun yasha iska da sauri. Ya duƙufa kan abinda yake yi har bai san Innaye ta idar da sallar ba sai da ya jiyo muryarta ƙasa-ƙasa ta kira sunanshi. """Hafizu?""" """Na'am Innaye. Kin idar? Sannu ya jikin naki?""" Ya amsa yana kallonta a tausashe. """Jiki Alhamdulillahi Hafizu.""" Ta sake amsawa da sanyin murya sosai. Sai kuma ta mayar da idanunta kan Zulaikha da itama ta tsaya da gyaran gadon da take yi tana kallonta cikin kulawa da tausayawa. """Sannu da ƙoƙari Auta. Jiya ban bari kinyi barci ba. Allah yayi miki albarka.""" """Amin Innaye. Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana.""" """Amin ya rabb!""" Hafiz yayi gaggawar amsawa tun kafin Innaye ta amsa. Ta buɗe baki za tayi magana ya riga ta da cewa """Innaye kiyi shiru haka nan. Kin ga jikinki babu ƙarfi, ki karya sai ki sha magani, Bintu za tayi miki allura" "kafin ta fita aiki.""" """To""" "Ta amsa a sanyaye. A zuciyarta take ji kamar ta ce mishi a dakata da magani da alluran, amma da ta tuno" irin bayanin da ta ji Bintu tana yi mishi ɗazu sadda ta farka barci sai bata furta abinda yake zuciyarta ba. A baki yai ta bata abincin yana ba ta kunun tana kurɓa a hankali har sai da ta kawar da kanta alamun ta ƙoshi. """Ki daure ki ƙara ko kaɗan Innaye, kin san wasu magungunan rashin isasshen abinci a ciki yana sa su" "wahalar da mutum.""" """Na ƙoshi Hafizu. In dai ba so kake in amayar da wanda ya shiga cikina ba.""" Ta faɗa tana ƙoƙarin yin murmushi amma ya gagara saboda tsananin yadda ta jigata da ciwon dare ɗaya kacal. "Kafin yayi magana Bintu tayi sallama ta shiga cikin ɗakin, idanunta kan agogon da ke ɗaure a tsintsiyar" hannunta take cewa """My dear lokaci ya tafi sosai fa, sai kira na ake yi a Ofis. Ta gama break fast ɗin?""" """Eh! Ta gama.""" Ya amsa shi ma yana sauke idanunsa kan agogon bangon da ke cikin ɗakin. Ƙarfe takwas da mintuna talatin da uku. "Bintu idanunta ta mayar kan Innaye da fuskarta yayi zuru-zuru, idanunta suka zuz-zurma ciki sosai, ciwon" "dare ɗaya kawai gaba ɗaya ya sa kamanninta ya canja, tsufanta ya bayyana ƙarara. Haushi da tsanar" Innaye da yayi kaka-gida a zuciyarta ya hana ɗan guntun tausayin da ya taso mata yin tasiri. """Innaye ina kwana? Ya ƙarfin jiki?""" """Lafiya ƙalau. Da sauƙi Alhamdulillah""" Ta amsa da yanayin maganar da take yi ƙasa-ƙasa tun da ta idar da sallah. """Allah ya ƙara sauƙi.""" Tayi addu'ar a gaggauce. Muryar Hafiz kawai ta ji ya amsa mata. Cikin rashin damuwa ta ɗauki ledar "magungunan Innaye da ke ajiye a gefe guda ta fito da su ta fara harhaɗa ruwan alluran, duk abinda take yi cikin sauri ne tana yi tana kallon agogo." Babu wani tausasawa Innaye ta juya baya ita kuwa ta zurkuɗa mata alluran biyu ba tare da tantance inda "ya kamata tayi mata ba. Ta ɓalli magungunan kamar jiya shi kuma ya miƙa ma Innaye, ya tsiyayi ruwan gora a kofi ya miƙa mata ta haɗiyi maganin." """Zulai sakko ki ga magungunan da za ki ba Innaye da rana.""" Bintu ta faɗa idanunta kan Zulaikha da take zaune a gefen gado tun bayan shigarta cikin ɗakin. "Da farko ƙin motsawa tayi, sai da Hafiz ya daka mata wani gigitaccen tsawa kafin ta taso da sauri ta" tsuguna gaban Bintu tana zumɓura baki. """Ki shiga taitayinki da ni na rantse da Allah. Idan ba haka ba kafin in fita Ofis na rantse sai na koya miki" "hankali...""" Hannun da Innaye ta ɗaga masa alamar dakatarwa yasa shi katse maganar ba tare da ya kai ƙarshen maganar ba. Kala uku a cikin magungunan ta ware ta nuna ma Zulaikha da cewar su za ta ba Innaye tasha da rana. """Ki kiyaye fa, kar ki kuskura shirme da wawancinki yasa ki dawo min da treatment baya. Domin yadda" "ta fara shan magani da allurannan kuskure kaɗan za a samu na jinkirin shan maganin aiki ya dawo baya, ba fata nake yi ba amma irin ciwukan da za su taso mata sai sun fi waɗanda tayi fama da su a baya.""" Ta yi maganganun cikin faɗa-faɗa tana aika ma Zulaikha mummunan kallo. "Bata amsa ba, a madadin tayi magana ma ɗaga idanunta tayi a fili itama ta galla ma Bintu wata" matsiyaciyar harara kafin ta miƙe ta koma gurin zamanta gefen gado. "Baki buɗe Bintu ta bi ta da kallo, fuskarta cike fal da mamaki. Ta buɗe baki za tayi magana da sauri Hafiz" "da yake ankare da komai ya ɗan taɓe ta, suna haɗa idanu ya girgiza mata kai sannan ya nuna mata" Innaye da ƙwayoyin idanunsa. "Ƙasa-ƙasa tayi ƙwafa kafin ta miƙe tsaye, fatan ƙara samun sauƙi tayi ma Innaye sannan ta kama hanyar" ficewa daga ɗakin. """My Dear ni kam na wuce. Sai munyi waya.""" Bata jira amsawarshi ba ta fice daga ɗakin. "Aka ce albarkacin kaza ƙadangare ke shan ruwan kasko. Albarkacin Innaye, yasa duk yadda Zulaikha ta" ɓata ma Hafiz rai bai ce mata komai ba har ya gama tarairayar Innaye ya fice daga ɗakin bayan yayi musu sallama zai wuce Ofis. Da harara Zulaikha ta raka shi har ya ɓace ma ganinta. "Innaye dai jingina tayi da jikin bango ta lumshe idanunta. A yanzu babu zazzaɓi a jikinta, amma fa ba ta" "jin ƙarfi ko misƙala zarratin, sakayau take jin ta kamar an kwashe duk wani ƙwarin jiki da Allah ya huwace" mata. Tana a haka har barci ya fara ɗaukarta. """Innaye ko za ki dawo kan gado ki kwanta sai in gyara tsakar ɗakin?.""" Maganar da Zulaikha tayi shi ya farkar da ita daga barcin da ya fara ɗaukarta. "Bata ce komai ba, sai yunƙurin miƙewa da ta fara yi, da sauri Zulaikha tazo ta kamata ta miƙar da ita," tana tallabe da ita har sai da ta kwantar da ita akan gadon ta rufa mata bargo a rabin jikinta. Kafin ta gyara ɗakin sai da ta zauna ta take cikinta tayi nak! Tana cin alalen dankalin turawan tana korawa da daddaɗan kunun gyaɗar a zuciyarta take zabga Allah ya isa ga Bintu da a dabarance ta daina basu dafaffen abinci lokacin karyawa sai dai su sha shayi. Ita kam da yake rainon ƙauye ne abu mai suger da safe bai cika damunta ba. Ko a gida idan akwai "ɗumamen tuwo ko sauran abincin da aka dafa da daddare sam ba ta kallon kokon da ake damawa a rarraba ma yaran gida a cikin kofuna ƙananu. Ɗumamen Tuwo take sakawa ta zambaɗa yaji ta cika cikinta tayi nak, sai ta kai ƙarfe ɗayan rana da ƙoshinta ko da an samu jinkirin gama abinci sanadiyyar" ɗanyen itace ko gawayi. "Bayan ta gama karyawa tattare kuloli da farantai da kofuna tayi gefe ɗaya ta gyara tsakar ɗakin ƙal, har" mopping ɗin kan tiles ɗin tayi ya fita fes! Sannan ta maida hijabin jikinta ta bi lafiyar gado ta kwanta gefen Innaye domin ta rama barcin da bata samu yin isasshe jiya ba. ****** Darare uku masu kama da darare dubu saboda masifar tsawonsu a gurin Zulaikha Innaye ta kwashe tana fama da balaƴaƴƴen zazzaɓi mai zafin gaske kamar baza ta wayi gari ba. Wani ikon Allah kuma da asubahi tayi sai zazzaɓin ya sauka. Haka za ta yini cikin rashin ƙarfin jiki da "kasala, ba ciwon jiki kaɗai ba, hatta tafin ƙafafun Innaye jin su take kamar an kwashe ƙasusuwan da suke taimaka mata gurin yin tafiya an bar zallar tsoka kaɗai. Dai dai da zuwa banɗaki sai Zulaikha ta riƙe ta sannan take iyawa, sallah kuwa tun ranar farko da ta fara yi a zaune har yau bata ƙara samun ƙwarin" gwuiwar yi a tsaye ba. Innaye ta rame ta zabge ta tsuke kamar ba ita ba. Tsufa da galabaita sun bayyana ƙarara a jikinta. Ba "Innaye da take fama da ciwon cikin dare ba, hatta Zulaikha da take jinya duk ƙibar nan ta fara zazzagewa." Ita kanta kallo ɗaya za'a yi mata a fahimci rashin nutsuwa da rashin kuzari a tattare da ita. Shi kuwa Hafiz duk yadda ciwon Innaye yake ɗaga mishi hankali har lokacin bai ji a jikinsa ya kamata Bintu ta canja ma Innaye magunguna da allurai ba. Maganar da ta faɗa mishi tun ranar farko ita ya riƙe daram a zuciyarsa 'Jikin Innaye bai taɓa karɓar magunguna masu kyau da ƙarfin waɗannan ba shi yasa a yanzu dole za ta galabaita na kwana biyu. A bayan waɗannan cututtukan lafiya wadatacciya ce za ta biyo baya fiye ma da wanda suke nema.' Da waɗannan kalaman yake ta dannar zuciyarsa da irin damuwa da tashin hankalin da yake ciki. Abu ɗaya dai da ya iya yi shi ne kullum bayan ya dawo sallar asubahi zai umarci Bintu ta haɗa ma Innaye "lafiyayyen abin kari, idan ta gama ya kwasa ya fice musu da shi." A rana ta uku har yayi ma Innaye sallama zai tafi Ofis bayan Bintu tayi mata allurai ta bata magunguna ta fice gurin nata aikin Innaye ta riƙo gefen rigarsa. """Innaye? Sannu. Akwai abinda kike so inyi miki kafin in tafi Ofis ne?""" Ya tambayeta a tausashe bayan ya dawo ya zauna a kusa da ita. """Hafizu, gida nake so ka mayar da ni yau. Ko da mutuwa za ta ɗauke ni na fi so ta ɗauke ni a cikin" "iyalaina.""" "Tayi maganar daƙyar, shi kanshi bai ji abinda ta ce ba sai da ya kai kunnensa daidai bakinta." Hankalinsa ne ya ƙara ɗugunzuma fiye da wanda yake ciki. A yadda ya ɗauko Innaye da ƙarfi-ƙarfinta ko kusa bazai so ya mayar da ita can ƙauyensu yadda ta fara kwararraɓewa haka ba. Saboda ba ya son ɗaga ma ƴan'uwa da mahaifinshi hankali ne yasa shi tun fara zazzaɓin daren Innaye "kullum sai ya gargaɗi Zulaikha kar ta kuskura idan ɗaya daga cikin Yayye, mahaifinsu, ƴan'uwa suka kira" Innaye don jin yanayin jikinta tayi suɓul da bakan sanar da su irin ciwon da ya taso ma Innaye gadan- gadan. Daga bisani ma karɓe wayar Innaye da ke hannun Zulaikha yayi ya kashe. Ya zama sai lambarshi kaɗai "ake kira aji ya jikinta, shi kuwa duk wanda ya kira shi ya san abinda yake faɗa musu. Ko sun nemi yin" magana da ita kai tsaye yake kawo wani ƙaƙƙarfan uzuri ya basu. Hankalinsa a tashe ya gyara zama zai fara kalallame Innaye da daɗin bakin tayi haƙuri ga mamakinsa da tsoro kawai sai ta fashe mishi da kuka. Wani abu da bai raɓa faruwa tsakaninshi da ita ba. Wannan kuka da Innaye take yi haiƙan ba ji ba gani sam ta ƙi tsayawa ta saurare shi shi ne abinda ya ƙara "ɗaga hankalinsa zuwa ƙololuwa. Afujajan ya miƙe tsaye ya fice daga cikin ɗakin, can jikin famfon da ke tsakar gurin ya hangi Zulaikha zaune ta tasa kayan wankinsu a gaba tana zaune dirshan a ƙasa tana matsar ƙwallah." "Kaman zararre, ya ƙarasa gurinta da sauri." """Kukan me kike yi?""" Ya tambayeta cikin tsawa. A tsorace ta ɗaga idanu ta kalle shi. Maimakon ta amsa tambayar da yayi mata kuma kamar haɗin baki itama sai ta fashe mishi da ƙaƙƙarfan kuka. """Gida kike son tafiya?""" Ya sake jefa mata tambayar hankalinsa a tashe. "Da saurin gaske ta dinga gyaɗa mishi kai alamar eh kamar ƙaramar yarinya, ta kasa buɗe baki ta amsa" mishi saboda kuka. """Ki haɗa kayayyakinku bari inje in dawo mu tafi yanzu.""" Ya sake faɗa hankalinsa a dagule. Yana kallonta ta kwashi kayan wankin nasu da ko jiƙawa bata yi ba ta wuce cikin ɗakin da sassarfa jikinta na rawa. Jikinsa a sanyaye yaja ƙafafunsa da yake ji kamar baza su iya ɗaukarsa ba ya wuce zuwa ɓangarensu. "A yadda ya tsara da farko, ƙarasa shiryawa zaiyi yaje gurin aiki ya ɗan rage wasu ayyukan kafin yazo su" "tafi. Amma da zaran ya tuna irin kukan da ya bar Innaye tana yi, sai hankalinsa ya ƙara ɗugunzuma." "Ya rasa abinda ke mishi dad'i, a kasalance ya k'arasa shiryawa ya fice daga falon ya nufi can tsakar gidan" ya sanar da direba ya canja motar da za su fita da ita. Ba Ofis za su ba can ƙauye za su je. """Ƙauye a yanzu Oga? Allah yasa dai lafiya?""" Direba ya jefa mishi tambayar fuskarshi na bayyana damuwa. """Lafiya ƙalau. Innaye ce ta matsa lallai a mayar da ita gida yau.""" "Ya amsa mishi yana cigaba da tafiya zuwa ɓangaren Innaye, wayarsa na hannunsa yana daddanawa don" kiran Bintu ya sanar da ita abinda yake faruwa. Kamar ta miƙe ta taka rawa take ji don tsananin farin cikin da ya sauka a zuciyarta lokaci ɗaya daga jin bayanin da yake mata. Amma da yake ta ƙware a nuna yanayin da ba haka bane a zuciyarta sai ta "kwantar da muryarta sosai, cikin yanayin damuwa da jimami ta ce mishi" """Sweetheart ƙauye kuma? To ya bayanin sauran alluranta da suka rage na kwana biyu? Kuma ka san" "halin mutanen naka dai da rashin kulawa, idan suka tafi da magungunan nan ba lallai su kiyaye ba ta akan lokaci ba. Kar ciwon ya dawo baya fa...""" """To ya zanyi mata Bintu?""" Ya katse ta da kalar tasa damuwar da yake ji kamar ya ɗora hannu aka yaita rusa ihu. """Duk irin kalaman da ya kamata in yi amfani da su gurin yi mata bayani sam ta ma ƙi saurarata. Ni" "babban damuwata ma Wallahi ba ragowar allurai da magungunan bane, ki tuna yadda na ɗauko Innaye daga gida." Ko da dai ba ta da lafiya amma ke kin san yanayin jin jikinta ko kaɗan bai kai yanzu ba. Ki duba yadda ta "rame ta lalace, raunin tsufa ya bayyana ƙarara a jikinta. Ko tafiya ba ta iya yi ita kaɗai fa sai an riƙe ta," "saboda Allah idan na mayar da ita a irin wannan halin da take ciki me mutanen gida za su ce a kaina?""" Irin yadda yake jan numfashi yana saukewa a zafafe cikin damuwa shi ne abinda ya ɗan so ɗaga mata "hankali. Alal haƙiƙa a yanzu kam shi ya bata tausayi ba halin da Innaye ke ciki ba. Don haka tayi shiru tana tunanin da zai samar mishi da mafita, duk da dai ba ta ƙaunar cigaba da zaman su Innaye a gidanta saboda damuwarsa kaɗai yasa ta cewa" """To ko dai za ka mata dabara ne kai tafiyarka Ofis ne ka ƙyale su a gida? Idan bata ganka ba ai dole ta" "haƙura da zancen tafiya gida ayau ɗin. In yaso idan zan dawo gida sai in taho mata da wasu magungunan saɓanin wanda take sha, duk da dai ba haka na so ba.""" "Da yake wayar da yake yi a ƙofar shiga ɓangaren da Innaye take ne, ya buɗe baki zai ba Bintu amsa" "kawai sai ganin Zulaikha yayi ta fito tana riƙe da Innaye, sun shirya tsaf! Da alamun gajiya sukai da jiransa" suka fito. "Ransa a ɓace ya galla ma Auta harara kafin yayi ma Bintu sallama a gaggauce, ba tare da ya bata amsa" kan shawarar da ta bashi ba. """Me yasa kika fito da ita ba tare da nayi miki umarni ba? Ko an faɗa miki na gama shirye-shiryen tafiya" "ne...?""" """Yaya ba fa laifi na bane. Tun ɗazu ita ta matsa min in fito da ita, da nace mata baka shirya ba sai cewa" tayi mu fito ko a motan haya ne mu tafi. Ta rantse ta sake rantsewa da Allah ita kam ba ta ƙara kwana a "gidannan.""" Sau uku yana buɗe baki da nufin yin magana amma ya rasa ta cewa. Sai kawai ya juya zuwa tsakar gidan "suka bi bayanshi, shi kaɗai yake ta ƙwafa yana jan tsaki saboda tsananin damuwa da ƙuncin zuciya." Direba yana kan wanke motar da za suyi tafiya a cikinta ganin fitowar su Innaye a dole ya dakata. Yadda aka tarairayota yasa da saurin gaske ya kai hannu zai buɗe ƙofar baya sai Hafiz ya riga shi buɗewa. Da sassarfa ya ƙarasa ya karɓe ta a hannun Zulaikha ya ƙarasa da ita cikin mota ya zaunar da ita. Idanunshi akan Zulaikha har lokacin bai saki fuskarsa ba ya ce """Shiga kusa da ita ki zauna, idan ta gaji da zama ki kwantar da ita a jikinki.""" """To Yaya. Amma ban fito da kayanmu ba, bari in je in kwaso...""" Da tsawa sosai a muryarsa ya katse ta tun kafin ta aje numfashin maganarta. """Dallah shiga cikin mota zan je in kwaso muku. Kuma ina fatan kin haɗa har da sauran magungunanta" "da alluran da suka rage?""" """Eh.""" Ta amsa da sanyin murya. A zuciyarta kuma cewa tayi "'Balaƴaƴƴe, ka ci kanka kasha baƙin ruwa. Gidanka ne dai ko kana so ko ba ka so yau za mu bar shi.'" Da sauri ta shige cikin mota ganin har lokacin bai daina aika mata da wani fusataccen kallo ba. Kayansu gaba ɗaya a ghana most go ɗaya ne. Don tabbatar da bata manta da magunguna da alluran Innaye ba sai da ya buɗe jakar ya gansu sannan ya maida jakar ya rufe ya ɗauka zuwa mota. "Saboda irin jan ƙafar da yai tayi za su tafi baza su tafi ba, ya shiga cikin ɓangarensu ya ƙi fitowa akan" "lokaci kuma shi ba wani takamaimai abu yake yi ba basu bar gidan ba sai ƙarfe goma da rabi na safe. Tun da Hafiz yayi aure, zuwanshi ƙauye ya kwana ɗaya bai fi sau bakwai ba." "Duk sa'adda za su tafi asubanci suke bugawa yadda za su isa da wuri, ya gama duk abinda zaiyi zuwa" "la'asar su ɗauko hanyar komawa Abuja, komai dare a gida yake kwana." Ko a yanzu direba ya zaci irin waɗancan tafiyoyin da suka saba yi ne na yini ɗaya. Don haka ya ƙure manejin mota yana ta zabga gudu kamar masu shirin barin ƙasar. "Ko da suka isa Kaduna baiyi niyyar tsayawa ba sai da Hafiz ya ce mishi ya tsaya ya sai ma su Innaye abinci," a lokacin ana ta kiraye-kirayen sallar azahar a wasu masallatai. "Da yake ko bayan an isa Kaduna tafiya ce miƙaƙƙiya zuwa ƙauyen Faƙo, ga kuma tsiya irinta ƙarfen" nasara da ba ta da tabbas. Bayan tsayawa gyara da suka yi a garin Kujama basu isa Faƙo ba sai La'asar. Sun isa ƙofar gidansu Innaye daidai lokacin da aka fito sallar la'asar a babban masallacin da yake ƙofar gidan. 'Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un' Hafiz ya faɗa a zuciyarsa hankalinsa a tashe. Ko kafin ya waiga yayi ma Zulaikha umarnin ta dakata da buɗe ƙofar sai mazan da suke fitowa daga "masallaci sun ragu har ta riga ta buɗe ƙofar ɓangarenta, ta zura ƙafafunta zuwa waje, fuskarta cike da matsanancin farin ciki na ganinta a ƙofar gidansu." Kafin ma ya kira sunanta har ta fita waje. Bai ƙara tabbatar da rashin hankali da wautar Zulai ba sai da yaji ta buɗe murya tana ƙwala ma mahaifinsu da yake tsaye suna magana da Ladan kira. """Baffah... Mun dawo.""" Hakan bai ishe ta ba sai da ta ƙara da """Zo ka ga Innaye ba ta da lafiya sosai.""" Wannan maganar da ta faɗa shi ya dawo da hankalin gaba ɗaya mazan da suke tsaye a gurin zuwa kan "motar Hafiz. Kun san mutanen ƙauye da kara, ɗuuuuu kusan gaba ɗaya suka yo gurin motar." Babu abinda ke fita a bakunansu sai """Assha! Subhanallahi! Hajiya Rahina jikin ya motsa kenan.""" Tsananin damuwa da ɓacin ran abinda Zulaikha ta aikata yasa idanun Hafiz suka cicciko da hawaye. Ba "shi da yadda ya iya, haka nan ya buɗe ƙofar ɓangarensa ya fita waje ya tarbi mahaifinsa da sauran mutanen gurin da suka rufu a kanshi suna mishi jajen ya mai jiki? Haka nan yake ta amsa musu cikin" rashin nutsuwa da kwanciyar hankali. "Bai san Yaya aka yi ba yana cikin mazan nan sai ganin matan gidansu abokan zaman Innaye yayi sun fito," "suna sanye da zumbula zumbulan hijabai, biye a bayansu Zulai ce tana musu jagora zuwa gurin motar" ɓangaren da Innaye ke kwance. "Kafin ya ce wani abu har Zulai ta buɗe musu ƙofar, su kuma suka tarairayo Innaye da gajiyar zaman mota" da rashin ƙarfin jikin da take fama da shi ya ƙara ramar da ita. Suna riƙe da ita sannu a hankali suke amsa gaisuwar mazan da suke mata ya jiki har suka shigar da ita cikin gidan. "Kamar wutar daji, haka zancen gaggarumin rashin lafiyar da Innaye ta dawo da shi ya fantsama a ƙauyen" Fako cikin kankanin lokaci. "Suna tsaye a ƙofar gida, bayan watsewar maza masu jajantawa yana yi ma mahaifinsu da yan'uwansa" biyu ƙarin bayanin ciwon Innaye bazai iya ƙididdige yawan matan da suka shiga cikin gidan duba jikin Innaye ba. Kun san ƙauye da kara da mayar da al'amarin wani nasu. Balle kuma Innaye da ta kasance mace ta "mutane, kowa nata ne. Daɗin gushi kuma macece da hannuwanta yake a buɗe, sam abin hannunta bai rufe mata idanu ba." Hatta kishiyoyinta biyu in dai batu na adalci da gaskiya za su fad'a ba ƙaramin daɗin zama da ita suke ji ba. Da gangar baza a zage ta ba sai dai son zuciya ko zalunci da ba'a raba zukatanmu na ƴaƴan Adam da shi. Duk nisan da gidajen Yayyinshi suke da shi cikin ƙanƙanin lokaci har labarin yadda ya dawo da mahaifiyarsu ya iske su a gidajensu. Ko kafin ya saɓulewa tambayoyin mahaifinsu ya shiga cikin gidan har yayyenshi sun iso. "Shi kanshi idanunshi duk sun faɗa ciki saboda fargaba, gajiya, da tashin hankali. Idan ya kalli direbanshi" "sai yaji ya bashi tausayi, saboda yau ko arzikin ruwa da furar da ake tarbarshi da shi bai samu ba." Daƙyar ya ƙwaci kanshi a hannun mahaifinshi da ƴan'uwan Innaye da suke ta tuhumarshi yadda aka "haihu a ragaya ya shige cikin gidan, lokacin ƙarfe biyar da minti goma na yamma." Ganin yadda Yayyenshi suka tasa Innaye da aka yi mata wanka tana kwance akan darduma a gaba suna "ta sharɓan kuka, ita kuma Zulaikha tana gefe cikin nata kukan take ba su labarin mafarin ciwon Innaye yasa idanunshi rufewa, bai san lokacin da ya nufe ta gadan-gadan zai rufe ta da duka yana surfa mata zagi ba." "A guje, kuma a tsorace Zulaikha ta daka tsalle ta ruƙunƙume Aunty Rakiya sannan ta ƙwallah ihu tana" karaɗin a ceceta zai kashe ta. """Hafizu me zan gani haka?""" Ta jefa mishi tambayar tana bin shi da wani irin kallo mai nuna tozarci ƙarara. Kafin ya amsa ta cigaba da cewa """Me tayi maka za ka doke ta? Kawai daga tana faɗa mana yadda aka yi mahaifiyarmu ta kamu da" wannan gagarumin ciwon shi ne za ka duke ta don zalunci da son zuciya? Ashe daman ƙarya kake faɗa mana cikin kwanakinnan idan muka kira ka muna tambayar ya jikin Innaye? To me kake nufi? Iye? Na ce "me kake nufi Hafizu? Ko so kayi sai ta mutu sannan ka sanar mana da...?""" """Kul! Kul!! Kul Rakiya... A kul!!! Kar in sake jin irin wannan mummunar maganar na fita daga bakinki.""" Mahaifinsu da shigarsa cikin ɗakin kenan ya tarar da ita tana wannan faɗan ya katse da tsawatarwa. Guri ya nema kan kujera ya zauna idanunshi akan Innaye. Har yanzu gani yake kamar idanunshi ne ke "mishi gizo, ya kasa gasgata wai Innaye ce tayi irin wannan rama da tsofewar a cikin kwanaki takwas kacal da barinta garin Faƙo. In banda yana da tabbacin duk lalacewar zamani babu ta yadda za'ayi a haɗa baki da ɗa a cutar da uwa mafi soyuwa a zuciyarsa da tabbas zai ce da haɗin bakin Hafizu aka ƙara" kwararraɓa jikin Innaye sanadiyyar magunguna da allurai. Amma kuma da ya tuna komai yana faruwa ne da ikon mahaliccin sammai da ƙassai. Sannan wasu "cutukan ba sa tashi a jikin mutum sai an sha wasu magungunan, kuma haka kawai idan Allah ya tashi gwada ikonsa ba cikin kwanaki huɗu ba, a cikin yini ɗaya ma yana iya jarabtar bawa da cutar da ta ninka wannan. Sai yayi saurin kore zargin magunguna da alluran da Bintu take ba Innaye har ma yayi istigfari." Kawar da idanunsa yayi daga kan Innaye ganin yadda tun shigarsa cikin ɗakin ƙananun hawaye ke ta tsattsafa a kwarmin idanuwanta ta kasa cewa komai. Ko tunanin me take yi a zuciyarta? Sanin gaibu sai Allah. Umarnin zama yayi ma Hafiz da tun maganganun da Yayarsa Rakiya ta caccaɓa masa yake tsaye kamar mutum-mutumi. Kallo ɗaya za'a mishi a hango gagarumin ɓacin rai da tashin hankali a tare da shi. """Hafizu ne mi guri ka zauna.""" "Ya sake umartarshi a karo na biyu cikin ɗaga murya, ganin umarnin farko da yayi mishi hankalin Hafiz" ɗin yayi nisa cikin tunani har bai san yana mishi magana. "Daga nan inda yake tsaye, kawai ya sulale zuwa ƙasa ya zauna ba tare da damuwa da inda ya zauna ko" kuma yanayin gurin da ya zauna ba. "Nasiha mai ratsa jiki sosai mahaifinsu yayi musu, ƙarara ya nusar da su muhimmancin yarda da ƙaddara" mai kyau da mara kyau. """Cuta, mutuwa, rayuwa, abubuwa ne da babu wani bawa da ya isa ya saka ma wani bawa su" "sanadiyyar magani ko wani allura face sai da yarjewar Ubangiji. Don haka daga yanzu, kar in ƙara ji ɗaya daga cikinku ta ce sanadin magani da allurar da matar Hafizu tayi ma Rahina (Asalin sunan Innaye) ne yasa ciwo suka tasar mata haka. Ina fatan kun fahimce ni?""" Ya ƙarasa maganar da ɗaga murya. """Eh! Mun ji Baffa. Za mu kiyaye in Allah ya yarda.""" Gaba ɗaya yayyen suka haɗa baki gurin faɗin haka. """Ke Zulai?""" Ya kira Auta da tsawa-tsawa. A tsorace ta amsa tana sake maƙure jikinta a na Yayarta Rakiya. """Daga yanzu, kar in sake ji kin ba wani ko wata labarin magani da alluran da aka yi ma Rahina. Kina ji" "na?""" """Kayi haƙuri Baffa. Bazan sake ba.""" Ta amsa a tsorace bakinta na rawa. """Sannan ku kuma ko da wasa kar ku kuskura ku ce za ku bari wani saɓani ya gitta tsakaninku da" "ɗan'uwanku don ɗan wannan abun da ya faru. Idan za ku yima lamarin duba da idanun basira, tsoro da fargaban irin tashin hankalin da za mu shiga idan muka ji labarin halin da take ciki shi yasa shi ɓoye mana komai. Wannan dalilin kaɗai ya isa yasa muyi mishi uzuri. Kai Hafizu a matsayinka na ƙarami ba Yayyinka" "haƙuri.""" "Cikin ƙan-ƙan da kai, da nuna nadama a fili ya ba su haƙuri kamar yadda Baffa ya umarce shi. Tare da" alƙawarin abu makamancin wannan bazai sake faruwa ya tafka irin wannan kuskuren na ɓoye musu ba. Cike da ƙauna suka karɓi tubansa. Yaya Rakiya da ta jefe shi da munanan kalamai ita ma ta bashi haƙuri. "Cikin kankanin lokaci suka fahimci junansu, bayan mahaifinsu ya kara janyo hankalinsu akan kar su" kuskura ko da wasa su bari wannan abu da ya faru yasa su canja ma Bintu fuska a matsayinta na matar kaninsu. """Na tabbata irin k'aunar da yarinyar nan take yi ma Hafizu bazai taba bari ta iya cutar da mahaifiyarsa" "da gangar ba. Kar ku bari shaid'an la'ananne yayi galaba a zukatanku kun ji ko?""" """To Baffa! Allah ya kara lafiya da nisan kwana.""" Kiran sallar magriba yasa Baffa da Hafiz ficewa daga d'akin. Su ma matan fita suka yi waje don d'auro alwala. "Kamar 'yar karamar yarinya haka aka tasa Innaye da tarairaya da kulawa ta ko wane 'bangare, ba daga" "'bangaren yaranta da mijinta ba, ba daga 'bangaren kishiyoyi, danginta da abokan arzikinta ba. Haka aka tara mata kwanonin abinci fiye da goma a gabanta." Amma saboda yanayin bakinta da babu dad'i dak'yar ta iya tsakurar tuwon dawa miyan gatsiga da aka aiko da shi daga gidan k'aninta Iro. A k'arshe dai shayi aka had'a mata mai kauri shi ma kad'an tasha ta ce ta k'oshi. Farin cikin tsintar kanta a cikin iyalanta kaɗai ya taka muhimmiyar rawa gurin dakushe rashin ƙarfin da "take ji a jikinta. Duk da bata furta ba, amma sosai yanayin fuskarta ke ƙoƙarin nunawa har Auta ta" fahimci haka. """Innaye? Ko dai gobe da safe mu bi Yaya mu sake komawa Habuja ne?""" Auta ta tambayeta cikin tsokana ganin yadda akai akai take bin ƴaƴanta da kallo tana ƙoƙarin sakin murmushi. "A yanzu ma murmushin ta ƙara yi, bata ce komai ba sai daƙuwa da ta ɗaga yatsunta tayi ma Auta. Su" kuma sauran ƴaƴan nata suka yi dariya. "A daidai lokacin Hafiz yayi sallama ya shiga ɗakin, hannunsa riƙe da jakar kayan su Innaye. A bayansa" "kuma direbansa ne ɗauke da katan ɗin ruwan gora guda uku, bayan ya gaishe da mazauna cikin ɗakin ya" "ƙara yi musu ya mai jiki, bai ɓata lokaci ba ya fice daga cikin ɗakin." """Ta ci abinci kuwa?""" "Tambayar da Hafiz ya fara yi kenan bayan ya zauna, idanunsa na kan Innaye shi ma yana karantar" cigaban da aka samu a lafiyar jikinta. """Eh! Ta ɗan ci, amma ka san bakin babu ɗanɗano, dole cin abincin kaɗan-kaɗan ne.""" Yaya Balira ta amsa mishi. """Haka ne! Allah ya ƙara sauƙi. Yanzu kafin shigowata na duba Chemis ɗin Habu ban ganshi a ciki ba, sai" "dai idan ya buɗe sai in kira shi yayi mata allura. Yanzu bari a fara ba ta magungunan...""" """Magani kuma Hafiz? Anya baza'a haƙura da magani da allurannan ba?""" Aunty Ladidi da bata cika magana ba a cikinsu ta faɗa idanunta a warwaje. Da alamun har lokacin bata manta labarin da Zulaikha ta basu ba. "Kallonta yayi, kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru yana kallonsu hannunsa riƙe da ledar maganin" Innaye. Yana jin yadda kaso hamsin cikin ɗari na ɓacin ransa da ya sauka sanadiyyar nasihar da mahaifinsu yayi musu yana ƙoƙarin dawowa sabo fil a zuciyarsa. Yaya Balira da ta kasance babba a cikinsu ne ta gyara zama ta fara yi mishi ƙarin bayani cikin tausasa kalamai. """Kayi haƙuri Hafizu, ka kwantar da hankalinka. Kar ka bari ranka ya ɓaci dalilin maganar da Ladidi tayi." Allah yana ganin zukatanmu ba wai mun raina ƙoƙarinka da na iyalinka bane. "Amma abu ɗaya da nake so ka fahimta shi ne, ko da muke mutanen ƙauye, daidai gwargwado ka san" Baban Yasin (Mijinta) a baya ya ɗauke ni munyi zirga-zirgan asibitoci da yawa na cikin Kaduna saboda matsalar haihuwa da nayi fama da shi. Ina yawan ganin idan magani yayi ma mare lafiya ƙarfi canja mishi ake yi. Idan kuwa likita ya ƙi canja ma mare lafiya magungunan da suka mishi ƙarfi shi mare lafiyan yana da ikon ya canja asibiti don ya gana da wani likitan ko warakarshi anan take. Mu kanmu haka mukai tayi "har dai daga bisani muka miƙa ma Allah al'amarin, sai daga baya kuma waraka tazo mana daga Indallah." "A lamarin ciwon Innaye ma yanzu kam shawarar da muka gama yankewa kenan, kamar yadda na faɗa" "maka da farko, ba don mun raina ƙoƙarin Bintu bane za mu ɗauki wannan matakin. A bayyane yake waɗannan magungunan sun yi ma Innaye ƙarfi, don haka gobe da sassafe idan Baban Yasin zai fita da mota zamu tafi da Innaye asibitin dutse ko Barau Dikko a cikin Kaduna a sake dubata a canja mata" "magunguna...""" "[12/27, 5:16 PM] Fareeda Abdallah: ""Na fahimce ki Yaya Balira. Babu komai, Allah ya kaimu gobe da" "safen. Ki shirya da wuri sai mu wuce da ita asibitin.""" Ya faɗa a nutse ba tare da fuskarsa ta nuna ɓacin rai ko kaɗan ba. Gaba ɗayansu sun ji daɗin yadda ya nuna sauƙin kai da fahimta cikin ƙanƙanin lokaci. """Allah yayi maka albarka Hafizu.""" "Innaye ta faɗa cikin sanyin murya, da alamun ita kanta ta ji daɗin amincewar da yayi a sauƙaƙe." """Amin Innaye. Allah ya ƙara miki lafiya.""" "Ya faɗa da bayyanannen farin ciki a fuskarsa, sosai yaji daɗin saka albarkar da tayi masa. Ko babu komai" a yanzu zuciyarsa ta ƙara gamsuwa Innaye bata ƙullace shi ba kan abinda ya faru. Dukkansu ƴaƴan Innaye mata sun so su kwana a gurinta amma mahaifinsu ya fatattake su zuwa gidajensu. """Sai ka ce a garin gaɓa-gaɓa muke? Ca nake acan Habujan ma Zulai ita kaɗai take kwana da ita babu" "abinda ya faru balle nan gida cike da mutane? Kwanan da za kuyi a gurinta ya isa yasa ko hana Allah ikonshi ne?""" "Da sauri duk suka girgiza kai fuskokinsu a dame. Domin ba haka suka so ba, amma baza su iya mishi" "musu ba saboda tarbiyar da aka ɗora su akai. Abinda suka sani ne ko sun tafi gida hankulansu ba kwanciya zai yi ba, Zulaikha ta faɗa musu ciwon Innaye cikin dare ne yake tashi gadan-gadan, ba fata" suke ba idan wani mummunan abu ya faru da ita a bayan idanunsu fa? Kamar ya san tunanin da suke yi sai ya ƙara da cewa """Don haka ku kwantar da hankalinku. Babu abinda zai faru sai alkhairi in Allah ya yarda. Ku tashi yanzu" "ku koma gidajenku, gobe idan Allah ya kaimu da safe kafin tafiya asibiti sai ku sake neman izinin mazajenku ku zo ku duba ta. Allah ya tashe mu lafiya.""" """Ameen Baffa""" Haka suka fice daga gidan jiki a sanyaye bayan sunyi ma Innaye da Abokan zamanta sallama. A hanyar raka su zuwa ƙofar gida da Zulaikha za ta yi ne suka jaddada mata lallai komai dare idan ciwon Innaye ya tashi ta kira wayoyinsu ta sanar da su. "Kamar yadda Innaye ta saba kwana cikin matsanancin zazzaɓi da kwankwatsar ƙashi ako wane dare, yau" "ma duk da bata sha magungunan dare ba haka ta kwana cikin azabar ciwo, kamar ma ya fi na kullum a ganin Zulaikha." "Baffa da yake da turakarsa yana ta safa da marwa yana duba halin da take ciki, sauran abokan zamanta" "ma ba'a barsu a baya ba gurin zirga-zirga duba halin da take ciki. To abu ne da babu yadda suka iya sai abinda Allah yayi, addu'o'i suka yi mata sosai kafin suka koma ɗakunansu." "Baffa da nauyinta yake a kanshi a ƙarshe dole ya bar turakarsa ya koma ɗakin Innaye, tsawon mintuna" "goma sha biyu ya ɗauka zaune kusa da ita yana tofe ta da duk addu'ar da tazo bakinshi, hankalinshi a tashe. Duk da faɗin Mal Bahaushe ciwo idan yaji dare ya fi tashi a iya tsawon rayuwar da yayi da Rahina" bai taɓa ganin ta yi ciwo makamancin wannan ba. Irin yadda take jan numfarfashi a wahalce tana saukewa ga gurmususu da take yi kamar mai naƙuda shi ne abinda ke ƙara ɗaga mishi hankali. "Ita kuwa Zulaikha tana rakuɓe a gefe tana ta hawaye kamar yadda ta saba, hannunta riƙe da jiƙaƙƙen" tawul da take goga ma Innaye a jiki don rage mata zazzafan zafin zazzaɓin da yake jikinta. "Daga bisani Baffa cikakken alwala ya ɗauro ya shimfiɗa dadduma a tsakar ɗakin ya fara jero nafilfili, yana" nema mata sauƙi da rangwame gurin mahaliccin sammai da ƙassai. "Kamar aikin asiri, sai gaf da asubah zazzaɓin ya sauka, nannauyan barci ya ɗauke ta kamar ko wane" lokaci. Ko da Hafiz ya shiga cikin gidan duba jikinta bayan sun fito daga masallaci irin labarin da mahaifinshi ya bashi na tashin ciwon bai ji daɗinshi ba ko kaɗan. "Ya zaci sauƙin da ya gani a yammacin jiya zai ɗore, kuma rashin shan maganin dare da bata yi ba ya ƙara" "saka shi sakankancewa yayi barci hankali kwance. Tunda ai an ce magungunan da take sha ke tayar da ciwon, tunda bata sha ba menene dalilin tashin ciwon a wannan dare?" Haka yai ta sake-sake a zuciyarsa da tulin tambayoyin da ba shi da amsarsu. Ko bayan ficewar Baffa zuwa turakarshi don ya kimtsa zuwa asibitin shi ya kasa ficewa. A falon Innaye ya zauna ya zuba tagumi da "hannu bibiyu, ƙwaƙwalwarsa a cunkushe. Ya ma rasa wani irin tunani ya kamata yayi?" A haka Yaya Balira tayi sallama a ƙofar ɗakin ta shiga ciki ta same shi zaune cikin damuwar da fuskarsa ta gaza ɓoyewa. Ƙirjinta ne ya buga daram! Da sauri ta saki jakar kayan da ke hannunta a ƙasa ta ƙarasa gurinshi hankalinta a tashe. """Hafizu me yake faruwa? Ina Innaye?""" "Bata jira ya amsa mata ba ta nufi cikin ɗakin da sauri, ganin Innaye tana barci ga Zulaikha zaune akan" "dadduma tana gyangyaɗi yasa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, ta zauna a hankali a gefen gadon tana" ƙara kallon Innaye don tabbatar da barcin take yi ko? Bata daɗe da zuwa ba Aunty Rakiya da Aunty Ladidi suka isa gidan. Duk yadda suka so suyi sammakon "tafiya asibiti bai yiwu ba saboda dole suka jira Innaye ta tashi barci don kanta, aka tarairayeta zuwa" "banɗaki aka yi mata wanka. Suka shiryata a nutse, tayi sallah a zaune, suka ba ta abin kari ta karya sama-" sama kafin suka ɗauki hanyar tafiya zuwa asibiti. "Ƴaƴan gaba ɗaya suka so tafiya asibiti, a dole suka haƙura saboda Baffa ya hana. Daga Aunty Balira sai" Hafiz sai Baffa da Innaye da direban da ke tuƙa motar suka tafi asibiti. "Kasancewar safiya ce babu go slow a hanya, kuma basu haɗu da sharrin ƙarfe irinna jiya ba. Nan da nan" suka isa asibitin Barau Dikko cikin garin Kaduna. Da yake tafe suke da gogaggen ɗan boko Hafiz sai basu "sha wata wahala ba, shi ya shige musu gaba gurin yin komai, layi na zuwa kansu aka shigar da file ɗin su suka samu ganawa da babban likitan da yake aiki a lokacin." "Bayan taƙaitaccen binciken da likita yayi akan Innaye, da kuma yanayin galabaitaccen jikinta da ya gani," nan take ya rubuta za'a basu gado. Sannan ya rubuta takardan gwaje-gwaje kala-kala ya damƙa ma Hafiz. "Ɗaki na musamman Hafiz ya buƙaci a kwantar dasu, kafin ya tafi ɓangaren biyan kuɗin da aka buƙata na" gwaje-gwajen da za'a yi mata. Da yake ya saka ma ransa son sanin takamaimai abinda ke haddasa ma Innaye waɗannan cututtukan "cikin daren shi yasa ko bayan gama ɗiban jininta don gwaji, aka ɗaura mata ƙarin ruwa bai bar asibitin ba" "sai da ya tsaya jiran fitowar sakamako. Wasu sakamakon sun fito a ranar, wasu kuma an tabbatar mishi sakamakonsu sai washe gari za su fito, sannan wani gwajin sai washe gari da safe za'a yi mata." Nan take direba ya tuƙa su zuwa cikin gari bayan ya dubo hotel mai kyau da tsada a wayarsa suna isa ya "kama musu ɗakuna, shi, mahaifinshi, direba. Kayayyakin da za su buƙata na kwana ɗaya zuwa biyu ya shiga babban shagon da ke jikin hotel ɗin ya siyo musu sannan ya koma ciki. Lafiyayyen abinci mai rai da" lafiya yayi musu Oder suka ci sannan kowa a cikinsu yayi wanka ya canja kaya. "Duk yadda yake jin gajiya a jikinshi bai zauna ba, ɗakin da Baffa yake ya shiga sai yaga har yayi barci. A" hankali yaja mishi ƙofar ya nufi ɗakin da ya kama ma direbanshi. "Ko da ya shiga sai ya tarar da shi ya gama cin abinci, yana kishingiɗe akan kujera yana sakacen haƙori." Ganinshi yasa direban miƙewa tsaye da sauri bayan ya amsa sallamarshi. """Oga barka da yamma. Allah ya ƙara arziki yaba tsohuwa lafiya. Za mu fita ne?""" Ya ƙarasa da tambayar a ladabce. Ya sani idan za su sake kwana su yini suna yawo a mota da Mal Musa ko a fuska bazai taɓa nuna mishi ya "gaji ba. Amma adalci shi ne ko da mutum yana maka hidimar da kake biyansa, yadda kake jin gajiya a jikinka shi ma yana ji, rai dangin goro ne. Haka kawai lokaci bayan lokaci yana da kyau ka dinga nuna ma hadiminka shi ma fa ɗan'adam ne mai ƴanci. Da wannan dalilin yasa shi sakin ɗan taƙaitaccen murmushi," ya ce """Ameen. A'a Mal Musa. Shigowa nayi kawai inyi maka ban gajiya. Fita zanyi yanzu amma ba tare da kai" "ba, Baffa yana ɗakinsa yana barci. Kai ma ya kamata ka huta, sai na dawo.""" Cikin fara'a yayi masa a dawo lafiya da addu'ar Allah ya tsare sannan ya miƙa mishi makullin mota. Ya "karɓa ya fice daga ɗakin shi kuma ya cigaba da kishingiɗarsa, a zuciyarsa yake jinjina kirki da karamci irinna Ubangidansa." "Ko da ya koma ɗakinsa, wayarsa ya ɗauka ya kira lambar Aunty Balira ta faɗa mishi duk abubuwan da" "suke buƙata. Bai ɓata lokaci ba ya fice daga ɗakin, kasuwa ya shiga ya lodo musu siyayya a wadace. Har" ma da abinda bata ce mishi suna buƙata ba aka loda mishi a bayan mota ya nufi asibiti. "Da yake ɗakin da aka kwantar da su kwanciyar mutane biyu ne, shi yasa basu rasa inda za su zuba" kayayyakin da ya siyo musu kamar bai san zafin kuɗi ba. """Allah yayi albarka Hafizu. In Allah ya yarda baza ka taɓe ba.""" "Minti ɗaya biyu kalaman da ke fita daga bakin Aunty Balira kenan, fuskarta yalwace da farin cikin yadda" bai taɓa nuna gajiya wajen ɗawainiya da su ko mahaifiyarsu. "Da fara'a a fuskarsa a amsa addu'ar. Gefen ɗaya gadon da babu mara lafiya akai ya zauna, yana kallon" Innaye wacce tunda aka ɗaura mata ƙarin ruwa da allurai da aka zuba a cikin ruwan barci take yi cikin kwanciyar hankali da nutsuwa. Bai daɗe sosai ba saboda magriba da ta kawo jiki yayi ma Aunty Balira sallama ya fice daga ɗakin. Yana "hanya, kiran Bintu a karo na uku ya shigo mishi amma bai samu sararin ɗauka ba, sai da ya isa ɗakin da ya kama sannan ya bi bayan kiranta." Ringing ɗin farko ana biyu ta daga wayar ba tare da jan aji ba kamar yadda ta saba. """My dear...""" Ta kira sunan da take yawan faɗa masa da wata irin raunanniyar murya. """Laifin me nayi?""" Ta sake tambayarsa tub kafin ya amsa da muryar da ke bayyana matsananciyar damuwa. "In ji Mal Bahaushe ya ce me kaza a aljihu ba ya jimirin as! A tsammaninta liƙin da ta fara yi ne ya ɓalle," shi yasa tun da ya tafi jiya da yau ko wayarta ba kasaifai yake ɗauka ba. Idan ta ci sa'a ya ɗauka kuma ko ya biyo bayan kiran da ta yi mishi kamar yanzu sam ba ya bata wani nutsuwarsa yadda ya kamata. "Tsoron ko asirinta ne ya fara tonuwa har yake ƙullace da ita yasa kawai ta sakar mishi kuka a raunane," irin kukan nan mai bayyana tana cikin matsanancin damuwa da tashin hankali. """Kiyi haƙuri Sweetheart.""" Ya faɗa a tausashe. """Don Allah kiyi shiru, ki kwantar da hankalinki. Kin san kukanki na ɗaga min hankali.""" Ya faɗa cikin rarrashi da muryar da ke bayyana damuwa. "A hankali ta fara ƙasa-ƙasa da kukan har tayi shiru gaba ɗaya, amma bata ce komai ba, sai sauke ajiyar" take yi irinna kuka. """Kin san ko da kinyi min laifi zuciyata baza ta iya jimirin fita daga al'amarinki ba. Kiyi haƙuri, al'amarin" ciwon Innaye ne yake ɗaga min hankali... Tun da muka iso jiya ba ni cikin nutsuwa ta. Jikinta har yanzu "baiyi sauƙi ba...""" """Subhanallahi. Allah sarki Innaye. Allah ya bata lafiya. Tana shan magungunanta kuma ana yi mata" "alluran safe da dare kuwa?""" Ta tambaye shi daga can ɓangaren. Har ya buɗe baki zai faɗa mata gaskiyar abinda yake faruwa sai kuma ya tuna gargaɗin da mahaifinsa yayi masa. "'Hafizu, kar ka kuskura ka faɗa ma iyalinka an daina ba mahaifiyarka maganin da ta siya mata. Ba don" komai ba kuwa sai don za ta ga kamar an raina ƙoƙarinta da kulawar da ta ba mahaifiyarka ne. Idan kunyi waya kar ka kuskura ka faɗa mata ma mun taho asibiti. Ina fatan ka fahimce ni?' Tunanin wannan maganar yasa shi amsa mata da cewa """Eh! Ana bata komai kamar yadda kika nuna min. Jikin ne dai har yanzu ba sauƙi sai na musulunci, ki" "taya ni addu'a...""" """Ka kwantar da hankalinka My dear. Za ta samu sauƙi sosai in Allah ya yarda, don Allah ka kwantar min" "da hankalinka. Ya kake so inyi idan ciwo ya kama min kai?""" Ta tambaye shi a shagwaɓe. Kafin ya amsa ta sake cewa """Ka dai san idan kana ciwo ni ce ke jigatuwa ko?""" Ta sake tambayarsa. """To yanzu ba ni kaɗai zan jigata ba My Dear. Har da Babynka ɗan wata biyu da yake kwance a" "mahaifata. Ko za ka so ka zama silar da ɗan tayinka zai bi rariya tun kafin ya fito duniya yayi tozali da fuskar kyakkyawan mahaifinsa...?""" """Mmmmme kike nufi Sweetheart?""" Ya katse ta da tambayar muryarsa na rawa. """Ban... gane ba? Me kike nufi? Kina nufin ke Bintu kina ɗauke da ɗan tayin cikina a jikinki?""" "Ta daɗe da sani, shi ɗin mutum ne mai son yara sosai. Tun kafin suyi aure ya sha faɗa mata shi fa yana" "son yara da yawa, ko da suka yi aure duk sa'adda baƙonta na wata yazo sai ya ɗanyi ƙorafin har yanzu ƙwallonsa bai shiga raga ba? Ya kamata tayi wani abu a matsayinta na likita." Shi yasa a yau da ta samu tabbacin tana ɗauke da juna biyu sanadiyyar amai da tashin zuciyar da ta tashi da shi har ya kai ta ga yin gwaje-gwaje ta a ranta bai kamata ta ɓoye mishi wannan abin farin ciki da ya daɗe yana jira ba. """Eh My dear. Da gaske nake. Yanzu haka da nake zaune takardun gwaje-gwajen da suka tabbatar min" "ina ɗauke da ciki ne riƙe a hannuna. Ka ce Alhamdulillah...""" """Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillahi ala ni'imatihi tatimmussalihat!!!""" Ya faɗa a jere muryarsa da karaɗin farin ciki tun kafin ta aje numfashin maganarta. """Na ji daɗin jin wannan kyakkyawar albishir ɗin Bintu. Lallai kin cancanci gwaggwaɓar tukwuici a" "hannuna. Ina ma ace yanzu haka ina tare da ke? Lallai da kin ga yadda ake nuna matsananciyar murna da tarairaya. Na gode, na gode. Allah yayi miki albarka. A yadda na tsara a ɗazu ko zan koma Abuja sai jibi, amma saboda wannan kyakkyawan albishir ɗin da kika yi min gobe da wuri ina nan tafe kin ji Sweetheart?" "Yanzu faɗa min, me kike yi?""" "Sai da tayi fari da idanunta kamar yana kallonta, sannan ta amsa a yangace" """Ina zaune ne a tsakiyar gadonka. Zuciyata cike da kewarka Mijina uban ƴaƴana.""" """Ni ma ina kewarki Matata. Yanzu me kike jin ci?""" Ya sake tambayarta a ɗokance. """Babu komai My dear. Tun ɗazu zuciyata tashi take yi, ba na jin cin komai.""" Ta amsa tana murmushi. Da tarairaya da kulawa haɗe da matsananciyar ƙauna a muryarsa ya fara faɗa mata tausasan kalamai. """Ayya... Yi haƙuri Sweetheart. Sanadin Babyna kike jin haka ko? With time komai zai wuce kin ji? Yanzu" "dai faɗa min, cikin ya fara motsi ne?""" "A yanzu kam ta kasa hana kanta dariya, dole ta sake shi amma a sanyaye, da salon jan hankalin wanda" aka yi dariyar dominsa. """Dariya na baki?""" Ya tambaye ta shi ma yana dariya. """Kar ki ga laifina fa, kin san abinki da sabon shiga...""" """Ban ga laifinka ba My dear. Kawai dai tambayar ce ta saka ni dariya. Ciki ba ya fara sai ya kai wata" "huɗu, ka ga ni yanzu ne nake cikin wata biyu. Amma kamar gobe ne za ka ji ya fara motsi, har ma ka taɓa da hannayenka ka dinga jin babyn yana motsawa.""" "Daga irin yadda take mishi ƙarin bayani, za'a gane cike take da farin ciki. Shi ma da yake saurarenta da" farin ciki sosai a fuskarsa ya bata dukkan hankalinsa. "Hirar sabon cikin da take ɗauke da shi, shi ya taka muhimmiyar rawa gurin rage mishi ƙarfin damuwar da" "zuciyarsa take ciki dangane da ciwon Innaye. Sun daɗe suna hira cikin farin ciki da annashuwa, kafin suka" yi sallama daƙyar bayan ya ga kiran mahaifinsa na shigo masa. Bayan gama waya da Baffa sallah kawai yayi ya sake ficewa daga ɗakin zuwa na Baffa. Daga can ɗaukarsa yayi kai tsaye suka koma asibiti. "Ko da suka shiga ɗakin, barci suka tarar da ita tana yi. Aunty Balira kuma tana zaune akan dadduma tana" "lazumi, da alamun sallah ta idar." """Ya jikin nata? Barcin take yi har yanzu? Ta farka kuwa?""" Baffa ya tambayi Aunty Balira fuskarsa da damuwa bayan sun zauna a gefen gadon da babu kowa akai. """Jiki da sauƙi Baffa. Eh ta farka, har ma ta rama sallolin da suke kanta. Kuma Alhamdulillahi babu" "galabaitannan kamar da safe, da alamun sauƙi in Allah ya yarda.""" """Ma sha Allah! Allah yasa sauƙi ya ɗore. Ni gobe da safe zanyi sammakon komawa gida, sai zuwa jibi" "kuma. Allah yasa dai yau kar ta sake kwana da wannan zazzafan zazzaɓin irin na jiya, domin da alamun kwana da zazzaɓin shi ke sa ta yini a galabaice.""" """In sha Allah baza ta kwana da shi ba. Domin wani likita ya sake shigowa ya duba ta ɗazu, a lokacin" idanunta biyu. Ya tambayeta yadda take ji tayi mishi ƙarin bayani. Ban dai san me ya ce ba don naga yayi "ma ma'aikatan jinyan da suke biye dashi bayani da turanci, kuma yayi rubutu a jikin babban katin Innaye" "da yake riƙe a hannunsu.""" Tana aje numfashin maganarta Hafiz ya karɓe da cewa """Ba matsala. Yanzu kafin in tafi zan je in samu likitan in ji halin da ake ciki. Ni ma gobe da safe zan" "koma Abuja, ana nema na a gurin aiki. Duk yadda ake ciki zan karɓi lambar likitan mu dinga magana da shi. Jibi zan biyo jirgi in sake duba jikin nata.""" """Ai ka ma yi zamanka gurin aiki kar ka samu matsala Hafizu. Tunda ga waya ai Allah ya sauƙaƙa" "al'amarin, duk yadda ake ciki ita Balira sai ta kira da dinga sanar da kai. Allah yayi albarka ya ba Rahina lafiya.""" """Ameen Baffa.""" Suka amsa gaba ɗaya. "Kamar yadda ya ce, kafin su bar asibitin sai da yaje gurin Likitan da ke kan aiki a daren ya binciki halin da" "ake ciki. Babu wata matsala mai girma, sai wasu ƙarin allurai da zai siya saboda gwajen-gwajen da suka fita a ranar." Ƙarfe goma na dare suka bar asibiti zuwa hotel ɗin da suka yi masauki. ***** ***** Yayi mamaki sosai lokacin da Likita ya tabbatar mishi Innaye tana ɗauke da ciwon Suger a jikinta. Jininta "kuma ya hau sosai fiye da yadda ake tsammani. Typhoid da Maleria da Bintu ta ce shi ke damun Innaye shi ma akwai, amma kaɗan, basu yi ƙarfin da za'a haɗa ta da manyan magungunan da za su dinga" wujijjiga jininta ba. Amma kasancewar shi mutum ne ba mai zurfafa damuwa ko bincike akan al'amura ba sai ya bar komai "akan akasin na'urar gwaji aka samu a asibitin da Bintu take aiki. Ko a fuska bai canja mata ba, kuma har" lokacin bai sanar da ita an kwantar da Innaye a asibiti ba. Tarairayarta yake yi sosai suna rainon cikin jikinta cikin nutsuwa da soyayya. "Duk da ya kwana uku rabonshi da asibitin, amma ya saki kuɗi sosai ana yi ma Innaye duk abinda ya dace." "Kuma cikin hukuncin Allah kwalliya tana biyan kuɗin sabulu, sosai Innaye ke samun sauƙi, zazzaɓi kuwa" tunda suka je asibitin bata ƙara kwana da shi ba. Jikin Innaye yayi kyau sosai fiye da yadda ake zato. Ƴaƴanta da ƴan'uwa makusanta da suka je asibitin duba ta kowa da kyakkyawan labarin sauƙin da take samu yake komawa gida. Ko da ta kwana huɗu Baffa ya koma duba ta bakinsa kasa rufuwa yayi don murna. Minti ɗaya biyu sai ya kalle ta da fara'a ya ce """Alhamdulillah! Rahina sauƙi ya samu, Allah ya ƙara lafiya.""" Tun tana amsa mishi har ya koma ba ta kunya a gaban ɗiyarsu ta fari Balira. Ita kuwa sai dariya take ma "iyayen nata, daga ƙarshe ma ficewa tayi daga ɗakin ta basu guri domin su zanta a tsakaninsu." Kwanan Innaye bakwai a asibiti aka rubuta musu sallama. Kuma a wannan ranar ne Hafiz ya bi jirgin "ƙarfe takwas na safe zuwa Kaduna, ƙarfe sha ɗaya da rabi a asibitin tayi mishi." Ba ƙaramin murna da farin ciki yayi ba da ganin yadda Innaye ta warke garas! Kamar ba ita ce mare lafiya "ba, har wani kumari tayi na musamman saboda kyakkyawan kulawan da take samu a asibitin. Domin a yanzu duk wata harka kuɗi ke magana, yana daga can Abuja yasa aka bincika mishi gidan abinci na musamman a Kaduna safe, rana, yamma suke kai ma Innaye lafiyayyen abinci da ya kamata masu ciwon" suger su dinga ci. "Ba Innaye da take mare lafiya ba, hatta Balira me zaman jinya ta yi kyau sosai, jikinta ya nuna hutu da cin" abinci mai daɗi da lafiya. Bayan murnar ganin Innaye ficewa yayi zuwa Ofishin likita shi da Aunty Balira aka ƙara musu cikakken "bayani na irin abincin da za ta kiyaye ci a matsayinta na mai ciwon suger da hawan jini. Da kalolin abincin da jikinta ya fi buƙata a yanzu. Sannan ya karɓi tulin magungunan da likita ya rubuta mata, saboda yadda ya saki kuɗi shi ne ya biyo su canji ma. Amma saboda sanin ya kamata sai bai karɓi ko sisi ba, ya ce ya bar" ma marasa lafiyan da ba su da ƙarfi. Aunty Balira tana harhaɗa kayayyakinsu ya fice zuwa kasuwa. Kayayyakin abincin da likita ya lissafa "musu na masu ciwon suger ya siya da yawa, sannan ya samu shatar lafiyayyar mota ya biya direba, suka" ƙarasa asibiti aka ɗauki Aunty Balira da Innaye suka kama hanya sai Ƙauyen Faƙo. "Ƙarfe uku dai-dai suka isa, basu daɗe ba suka juyo saboda a ranar yake son komawa Abuja. Albarka kam" "Hafiz ya sha ta daga bakin Iyaye, ƴan'uwa, da jama'ar gari. Waɗanda a baya suka dinga hum-hum-hum da zancen yadda ya dawo da Innaye cikin matsanancin ciwo daga gidanshi sai ga shi su ne kan gaba wajen saka mishi albarka." Sun bar ƙauyen bakinshi har kunne. Nutsuwa ta musamman yake ji a sassan jikinsa saboda yadda ya "zama sanadiyyar faranta ma Iyaye da ƴan'uwanshi rai, daman kullum abinda yake buri kenan." ***** ****** ***** """Wai me kike nufi Zulai?""" Ya tambayeta ransa a ɓace. Ƙara ɗaure fuska tayi tamau ta juyar da kanta can gefe guda. Uffan bata ce ba balle ma yasa ran za ta tanka mishi. Ƙwafa yayi mai ƙarfi. Ya sake jan tsaki a karo na barkatai. Cikin matsanancin fushi da fusata ya ce """Kin san Allah? A wannan karon za mu samu gagarumin matsala da ke. Wata uku kenan ina bin ki kina" "ja na a ƙasa, a yanzu da bikinmu yazo gaf idan kin isa ki cigaba da wulaƙantani Allah ya tsinen. Zan nuna" "miki gaba nake da ke ta ko wane ɓangare. In banda iskanci da rainin ajawali irin naki ke har kin isa...""" """Wai don Allah Mudan ya kake so inyi ne?""" Ta katse shi ita ma ranta a ɓace. """Auwoo!""" Ya faɗa baki buɗe yana kallonta da mamaki. """Tambayata ma kike ya nake so kiyi? To bari in sake maimaita miki. Umarni nake baki a matsayina na" "wanda za ki aura nan da sati uku. Ki shirya gobe da yamma ki je ma Yahanasu matata barkar haihuwar da tayi...""" """Uhmmm! Mudan kenan.""" Ta katse shi tun kafin ya aje numfashin maganarsa. """Ka yi ka gama. Saboda Allah in banda ƙi faɗi irin naka ta ina aka taɓa haka? Don kawai za ka aure ni" haifata kayi? Ko kuwa don za ka zama mijina sai aka ce dole idan matarka ta haihu sai na je mata barka? "Bayan haka ma duk ƙauyen nan waye bai san irin mahaukacin kishin da Yaha take yi da ni ba?""" """Yaha kai tsaye?""" Ya faɗa a mamakance. Kafin ta amsa ya cigaba da cewa """Matar tawa ce kuma Uwargidanki kike kiran sunanta kai tsaye kamar wata sa'arki?""" Sai da ta murguɗa baki dama da hauni sannan ta amsa da """To ita Yahan uwata ce da bazan kira sunanta kai tsaye ba? Matar da tun kafin in shiga gidanta" matsayin kishiya take aiko min da manya-manyan zagi da Alkaba'iran da ta tanadar min iri-iri idan na kuskura na aure ka shi ne don ta haihu kawai ni daɗi miji zan je mata barka? Na rantse da Allah babu "inda zan je. Sai dai duk abinda zai faru ya faru.""" """Au! Haka kika ce?""" """Ƙwarai kuwa!""" Ta amsa kai tsaye ba tare da wani shakka ko tsoro ba. """To shi kenan! Yayi kyau Zulai. Zaɓi yanzu ya rage gare ki, ko dai ki shirya tsakanin yau, gobe, jibi ki je" "ma Yahanasu barka ko kuma in fasa aurenki. Zan aiko ƴan'uwana sati na sama su karɓi duk kayan auren da na aika da shi gidanku. In banda ƙaddara ma da ƙuruciyana ke har kin isa in ce zan aure ki tsofai-tsofai da ke? Shekarunki sha takwas fa... Ki faɗa min duk ƙauyen nan wace ganɗaɗemiyar budurwa ce mai shekarunki zaune a gida bata yi aure ko kuma ta taɓa aure ba? Kawai don kin samu za a rufa miki asiri sai ki dinga tsammani tsoronki ake ji? Daman tun kafin in sako kai a neman aurenki mutane da yawa sun faɗa min baza kiyi min biyayya ba, saboda kin gama tsofewa a gida kina goga kafaɗa da gyatumarki gani kike dai dai kike da kowa... To ni ba tsoronki nake yi ba. Kuma ina sake tabbatar miki in banda wasu" "dalilai babu abinda zai kawo ni neman auren tsohuwar budurwa kamar ki...""" Zafafan maganganun da ya saki baki yana yaɓa mata masu kama da saukar ruwan dalma a kunnuwanta "yasa bata san sa'adda tasa hannu biyu ta toshe kunne sannan ta ƙwalla wani mahaukacin ihu hankalinta a tashe. Hakan bai ishe ta ba, sai da ta ƙara da duƙewa a ƙasa ta rushe da ƙaƙƙarfan kuka kamar wacce" aka zo wa da albishir ɗin mutuwar iyayenta. """Au! Sharri za kiyi min daga faɗan gaskiya?""" Ya tambayeta hankalinsa a tashe da irin kukan da take ruwasa kamar ƙaramar yarinya. """To ni kin ga tafiyata. Ina zaune lafiya baza ki ƙulla min jakar tsaba ba in tafi kaji su tsattsaga.""" "Kamar walƙiya, ɓat ya fice daga cikin zauren a gaggauce." Baiyi second biyar da ficewa ba Innaye da abokiyar zamanta Mama Laminde da ƙananun matasan gidan Isiyaku da Labaran suka sawo kai a guje cikin zauren. "A hannayen matasan, manyan sanduna ne suka riƙo suna ta zare idanu kamar za su ci babu, domin duk a" tsammaninsu wani mugun abun Mudan yake ƙoƙarin aikatawa ga Zulaikha ita kuma ta ƙwala wannan ihun. Ganinta ita kaɗai duƙe a ƙasa tana rusa kuka sannan babu alamar wani mummunan abu ya faru da ita yasa suka yi turus! A tsaye guri ɗaya. """Ina yake?""" Matasan suka haɗa baki gurin tambayarta. Ita kuwa Innaye cewa tayi """Me ya faru Auta?""" Ta tambayeta hankalinta a tashe. """Ina Mudan ɗin?""" Ta sake jefa mata tambayar tana jin wani faɗuwar gaba da bata san dalili ba. Ta sake jefa mata tambayar tana jin wani faɗuwar gaba da bata san dalili ba. Idanu kaca-kaca da hawaye ta ɗago kanta daƙyar tana kallon Innaye ta ce cikin kuka da ɓare-ɓaren baki. """Wai... wai... wai... cewa yayi bazai auri tsohuwar budurwa kamata ba...""" """Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!!""" "Mama Laminde, Isiya, da Labaran suka haɗa baki gurin jan salatin hankulansu a tashe." "Ita kuwa Innaye, Daɓas! ta nemi guri ta zauna a cikin zauren tana jin wani jiri-jiri na neman kayar da ita" daga zaunen da take. Kafin wani a cikinsu ya sake cewa komai daga cikin gidan Umma Laraba ce ta sake fitowa bayan ta idar da sallar isha'i da take yi a gaggauce. Ko kafin ta bud'e baki ta tambayi abinda ke faruwa ta gansu haka sunyi jugum-jugum ga Zulai tana tsugune a k'asa tana rusa kuka sai ga Baffa ya sawo kai cikin zauren. """Lafiya? Me yake faruwa anan? Waye ya mutu?""" Ya jera musu tambayoyin da saurin lokaci ɗaya fuskarsa na rikiɗewa zuwa yanayin tashin hankali. """Baffa. Wai Mudan ne ya ce ma Zulai bazai auri tsohuwar budurwa kamarta ba.""" Isiya yayi ƙarfin halin faɗa ma Baffa yana sharce gumin da ya lulluɓe goshinsa. """Zancen banza kenan. Don wannan ƴar maganar shi ne kuka tsaya anan kamar anyi mutuwa? Ke kuma" Rahina da girmanki maimakon kiyi ƙoƙarin kwantar da lamarin sai ki ɓuge da zama a ƙasa kamar wata ƙaramar yarinya? Ku tashi da Allah mu shiga cikin gida. Ai zancen aure ya wuce lokaci ɗaya ace an fasa kamar wani wasan yara. Kun binciki gaskiyar me ya faru ne? Duk ku kwantar da hankalinku. Babu abinda "zai faru sai alheri in Allah ya yarda. Ku wuce mu shiga ciki na ce.""" Ya ƙarasa maganar da faɗa-faɗa. "Da sauri Zulaikha ta miƙe ta shige ciki da gudu tana cigaba da rusa kuka, domin har lokacin zafin" maganganun da Mudan ya yayyaɓa mata bai fara sassautuwa ba a zuciyarta. Innaye kuwa saboda yadda maganar fashin auren ya buge ta baga-tatan sai da abokan zamanta suka "kamata sannan ta iya miƙewa tsaye, suka rankaya gaba ɗaya zuwa cikin gidan Baffah na biye da su a baya. Kowa a cikinsu da tunani mabanbanta a zuciyarsa." "Tun watannin baya da suka shuɗe bayan gama jinyar da Innaye ta sha daƙyar, kamar baza ta kai labari ba." "Tana gama warkewa ta ba Baffa labarin duk yadda sukai da Zulaikha a gidan Hafizu, dangane da maganar samarin da suke son ta tana dakatar da su tun ma kafin zancen ya kawo kunnuwansu." """Ikon Allah""" Ya faɗa da mamaki a fuskarsa. """To ko menene dalilinta na taka musu birki?""" Ya sake tambayar Innaye. """Ai ba ta da wani dalili Baffansu. Akwai wani dalili ne da ya wuce wauta irin nata?""" Innaye ta amsa a tausashe. Da ɓacin rai a fuskarsa ya cigaba da magana bayan ta kai aya a maganganunta. """Amma Zulai an yi shashashar yarinya. Yanzu ita daman ta san tana da samarin amma shi ne ko da" wasa bata taɓa turo ko mutum ɗaya guri na ba? Tana ganin yadda kullum hankalinmu da na jama'ar gari yake kanta saboda daɗewar da tayi bata yi aure ba? In banda Allah yasa bana sha'awar yi ma ƴaƴana "auren dole na rantse da tuni na daɗe da bayar da sadakar Zulai..""" """Ai yanzu dai duk wani jira da damuwar rashin mashinshini ya ƙare in Allah ya yarda. Kayi haƙuri, shi" "aure lokaci ne. Babu mamaki yanzu ne lokacinta yazo. Yanzu dai ya kake ganin za a ɓullo ma al'amarin?""" Shiru yayi yana jujjuya sunayen samarin da Zulai ta faɗa ma Innaye sun taɓa yi mata maganar suna son ta a zuciyarsa. Ganin duk su ukun babu wanda ba nagartacce ba yasa shi cewa """Yanzu dai ina ga zan aika a tuntuɓe su ne ɗaya bayan ɗaya. Tunda dukkansu sun fito ne daga" "nagartattun gidaje, kuma a fahimtata da ɗan gajeren sanin da nayi musu yara ne masu kyawawan halaye." "Ko ma dai yaya ne, maganar aure ta wuce wasa, duk wanda na samu tsayayyiyar maganar har yanzu" "yana son ta dole in ƙara faɗaɗa bincike domin gudun yin kitso da ƙwarƙwata.""" """Haka ne kam! To Allah ya zaɓa mana abinda yafi alkhairi.""" Innaye tayi addu'ar fuskarta da bayyanannen farin ciki. "Kamar yadda Baffa ya alƙawarta ma Innaye. Tun a daren ranar ya naɗa wakilai ya tura su gurin Khalilu," ɗaya daga cikin samarin da Zulaikha ta ambata ya taɓa furta yana son ta. Amma cikin hukuncin Allah bayan gama sauraren jawabin wakilan kai tsaye ya faɗa musu a yanzu dai kam akwai wacce yake so. Har ma an kai kuɗin na gani ina so gidansu yarinyar. """Tsahare ce ƴar gidan Mal Isiya. Ayi haƙuri, sai dai inyi ma Zulai fatan alkhairi da addu'ar Allah ya haɗa" "ta da wanda ya fi ni.""" Haka wakilan Baffa suka bar gurin jikinsu a sanyaye. Su kuwa sauran samarin biyu Yusufa da Sani da farko duk sun amince har lokacin suna son ta. Amma daga baya ba tare da sanin me ya faru ba daga gidajensu aka aikewa Baffa da wakilai ɗauke da saƙon yayi haƙuri. Zancen soyayya ma bazai yiwu ba balle har a kai ga maganar aure a tsakaninsu. Ba kuma tare da sun faɗi wani ƙwaƙƙwaran dalili da zai gamsar da Baffa dalilin fasawar tasu ba. Ranshi a ɓace ya shige cikin gida ya huce haushinshi akan Zulai ta hanyar yi mata wankin babban bargo sannan ya wuce turakarsa ya barta a tsakar gidan tana kuka. Kasancewar zancen duniya da baya ɓuya balle kuma a ƙauye irin Faƙo da ya kasance ƙaramin gari sai ga "zancen bibiyar samarin Zulai ya fasu. Shi Mudan tun kafin a aika mishi ya bayyanar da kanshi, a cewarsa ya daɗe yana son ta. Amma ganin yadda ta ƙare tsakaninta da abokinshi Khalilu yasa bai taɓa yunƙurin faɗa mata ba." "Cikin ƙanƙanin lokaci ya samu karɓuwa a cikin gidansu Zulai. Amma gare ta babu yabo babu fallasa," saboda dalilai mabanbanta. Dalili na farko shi ne Mudan yana da mata. Duk da a shekaru Mudan ɗin bai haura shekaru ashirin da biyar a duniya ba yana da mata ɗaya da ƴaƴanshi uku. Auren miji mai mata kuwa abu ne da Zulaikha bata taɓa tsammanin yin shi ba. Dalili na biyu kuwa shi ne matar Mudan mai suna Yahanasu. Tun a wancan lokacin kasancewar Zulai me "tsawon ƙafa duk da Yaha ta girme mata da shekaru biyu sun yi zamanin ƴan matanci da juna, tun a" wancan lokacin jininsu sam bai haɗu da na Yaha ba. Dukkansu ba su da haƙuri kamar zawayi. "Yahanasu akwai bala'in son girma ita kuma Zulai akwai ta da raini, musamman ga babban da ta zubar da" "girmanta. To ita kuma Yaha akwai shiga abinda babu ruwanta. Ga masifa da bala'i kamar ruwan shan ta, duk yawan taron jama'a ba ta kunyar ta kwaɓe mayafi su dambatu da wacce ta shiga hanyarta." Allah dai ya kiyaye duk wannan rashin jituwar tasu har Yaha tayi aure Zulai bata taɓa ba ta damar da za "su ba hammata iska ba. Saboda ita kura ce, ga tsoro ga ban tsoro, akwai dai baki kamar me amma da an zo batun dambe yanzu za'a neme ta a rasa. Sam ta tsani abinda zai sa ta haɗa jiki da wata in dai ba an shammaceta ba." Dalili na uku shi ne shi kanshi Mudan ɗin a halayenshi mutum ne mai tsananin iko da rashin haƙuri. Da "shi da matarsa kamar an duba halayyarsu ne aka haɗa su aure. Amma kuma wani ikon Allah suna zaman lafiya sosai, domin Yaha ta iya bi da halayenshi." Wadannan dalilai uku suka hadu suka sa duk da zancen Mudan ya shiga gidansu Auta bata dauke shi wani kayan gabas ba. Haka take ta jan shi da dadi babu dadi har zuwa sadda aka tsayar da ranar aure a tsakaninsu. A lokacin ne ta dan nutsar da hankalinta guri daya ta fara daukarshi da daraja. A lokacin kuma sai Yahanasu ta taso ta gaba da sakonnin tanadin da tayi mata na masifa da bala'i kala daban-daban matuk'ar tayi kuskuren auren mijinta. Ashe tun fara neman auren yana yi a b'oye ne bai fad'a mata ba kuma ƴan'uwa da mutanen gari ba'a sami wanda ya tsegunta mata halin da ake ciki ba har sai da aka tsayar da rana sannan ta san halin da ake ciki. Wannan tashin hankali da matsanancin kishin da Yaha ta ɗora ma ranta shi ya taso mata da naƙuda "gadan-gadan, lokacin haihuwarta baiyi ba. Ga mummunar ɗabi'ar mutanen ƙauye ta rashin wayewa da zuwa asibiti musamman idan naƙuda ta taso." "Wannan dalilin yasa ta sha baƙar wahala, kamar baza tayi ba a hannun Ungozoma na gargajiya kafin aka" kwashe ta zuwa asibiti. Kuma cikin hukuncin Allah duk da asibitin babu wasu ƙwararrun likitoci ko malaman jinya ana zuwa bata cika awa uku ba ta haifi ɗanta namiji. Wannan haihuwa ya zo ma Mudan da iyayensa da ita kanta Yaha da wani gagarumin farin ciki da basu taɓa tsammani ba. Na ɗaya saboda duk ƴaƴansa uku da Yaha ta haifa mata ne. Na biyu kuma a ranar ne ya kai amfanin gonarsa kasuwa suka yi gagarumin tsadar da basu taɓa yi ba. Kuma a ranar ne ya samu nasarar siyan mota golf wacce ya daɗe yana buri Allah bai nufa ba sai a wannan rana. Waɗannan dalilai suka tattaru suka sa yake ɗaukar haihuwar nan da wani irin girma da ƙima kamar ba'a "taɓa mishi haihuwa ba. Shukuranu shi ne sunan da yake kiran yaron tun kafin ranar raɗin suna ta zo, saboda a ganinsa duk waɗannan alkhairan sun zo ne dalilin haihuwarsa." "Tun a washe garin ranar da akayi haihuwar ya fara yi ma Zulaikha nacin taje tayi ma Yahanasu barka," wacce aka sallamota daga asibiti bayan ta kwana ta yini. Amma haka tayi ta mishi yawo da hankali har dai ranar ta biyar da aka yi haihuwar inda ta fito ƙeƙe-ƙeƙe ta faɗa mishi baza ta je ba. Shi kuma yasha alwashi sannan ya rantse da girman Allah idan bata je ma Yaha barka ba bazai aure ta ba. Zai gwada mata ya fi ta ɗanyen kai. ****** "Tun da ya fito yayi tozali da Baffa, nan take yanayin fuskarsa ya canza daga farin cikin da ya fito da shi" zuwa ba yabo ba fallasa. """Au! Baffa kai ne da safen nan?""" Ya faɗa yana ɗan ciccijewa. Duk da ganin yadda ya canja fuska farat ɗaya daga ganinshi bai hana Baffa faɗaɗa tasa fuskar da murmushi ba. """Assalamu alaikum!""" Yayi mishi cikakkiyar sallama haɗe da miƙa ma Mudan ɗin hannu. A kunyace ya ɗan kawar da fuska yana sosa ƙeya. Sai kuma ya ɗan duƙa ƙasa a ladabce ya fara gayar da "Baffa, ba tare da ya mayar mishi da hannu kamar yadda Baffa ya buƙata ba." Bayan musayar gaisuwa a tsakaninsu da tambayar lafiyar masu jego ɗan shiru ne ya ratsa tsakaninsu. Can kuma sai Baffa ne ya karya shirun da cewa """Jiya na dawo da daddare nake jin wasu zantuka na shirme daga bakin Zulai. Amma kasancewar kai ne" namiji mafi girma a kanta ban ɗauki maganganunta da muhimmanci ba. Sai ma faɗa da nayi mata na miƙa mata laifin gaba ɗaya duk da bansan cikakken bayanin abinda ya faru ba. Domin a ƙa'ida shari'a ba ta yiwuwa da jin ɓangare ɗaya. Wannan dalilin yasa nayi sammakon zuwa jin "abinda ya faru sannan in baka haƙuri. Don Allah kayi haƙuri, ka san Zulai yarinya ce har yanzu akwai ƙuruciya a kanta...""" """Shekarunta goma sha takwas ne kake kira mata yarinta Baffa?""" Ya katse shi da faɗin haka yana ƙara ɗaure fuska. Shi dai Baffa bai sake cewa komai ba. Tun da ya katse shi sai kawai ya sakar mishi ragamar maganar ya tsaya yana saurarenshi. Lura da hakan da Mudan yayi yasa shi naɗe hannaye a ƙirji idanunsa na kallon gefe ya cigaba da sakin duk irin maganganun da suka zo bakinshi. """In dai za mu faɗa ma kanmu gaskiya babu wani ƙuruciya a jikin Zulai. Yarinyar da duk sa'anninta sun" "tara ƴaƴa huɗu biyar ita ake kira ma ƙuruciya? Tsabar raini ne kawai da iskanci, kuma daman tun farko an faɗa min. Ta riga ta riƙa ta gandare a gidansu ko na aure ta baza ta taɓa jin magana ta ba. Sannan kuma tana ji da kanta don Yayanta na da kuɗi tana zuwa Habuja ita gani take ta fi ƙarfin mazajen ƙauyen nan. Kuma tana ganin duk ƴan matan ƙauyennan ita kaɗai ce ta samu nasarar gama sakandare tana" taƙama da boko shi yasa take jin ita ɗin ta kai wata shegiya. "Bayan abinda ya faru jiya ni gaskiya na riga na yanke ma kaina shawara, tunda dai ita fitsararriya ce, ni" da zan aure ta ma tun yanzu ban isa in bata umarni ta aikata cikin daɗin rai ba to ina ga mun yi aure? Kana ganin ni da hankalina zan yarda in auri macen da take min gani-gani ne? Ita fa a yadda na lura gani take kamar alfarma tayi min idan ta aure ni. "Don haka gaskiya sai dai kuyi haƙuri Baffa...""" """A'a! A'a Mudansiru!! Don Allah don Annabi kayi haƙuri. Kar ka ce ka fasa aurenta don Allah. Na ɗauki" "alƙawari zan yi mata faɗa sosai, idan ta kama da duka ma Wallahi zan haɗa mata. In Allah ya yarda baza" "ta sake ƙin bin umarninka ba, kayi haƙuri don Allah.""" "Baffa ya faɗi maganganun cikin tashin hankali, idanunsa sun kaɗa lokaci ɗaya sunyi jaa saboda tsananin" tashin hankali da damuwa. "Duk da maganganun Mudan ɗin sun ƙona masa zuciya, musamman in da ya kira Zulai da shegiya. Amma" "zai iya shanye fiye da haka akan dai ace ya fasa auren Zulai, a cikin waɗannan ƙidayayyun kwanakin da" "suka rage ya aurar da ita. Da wannan dalilin yasa bai tsaya tunkarar iyayen Mudan ba tunda dai shi ne mai aure, kuma shi Mudan ɗin ba yaro bane tunda har ya tara iyali." "Sannan bai tsaya turo ɗaya daga cikin ƴan'uwansa gurin Mudan ɗin ba ya zo da kansa, zuwa da kai ai ya" fi saƙo. Kuma yadda zai ƙasƙantar da kai yaba Mudan haƙuri ya san ba lallai ne ƴan'uwansa su iya yin haka ba. "Ɗan shiru Mudan yayi yana ciccijewa yana hura hanci, irin a dole shi fa an takura shi ɗinnan. Kamar bazai" "tanka ba, amma kuma wani tunani da yayi yasa shi cewa." """Baffa... Ni fa gaskiya na gama magana. Amma tunda ka ce za ka mata faɗa zan je inyi shawara, duk" "yadda ake ciki zuwa yamma ko gobe za ka ji ni. Na barka lafiya, a gaida iyali.""" "Yana gama faɗin haka da saurin gaske ya wuce ya ba Baffa guri, don ma kar ya sake tare shi da wasu" kalaman magiya da ban haƙurin da yake ji babu abinda za su canja matuƙar Zulai bata sauke girman kanta ta je ma Yahanasu barkan haihuwa yau ko gobe ba. "Haka Baffa ya bar ƙofar gidan Mudan jikinsa a sanyaye, jan ƙafafunsa yake tayi hankalinsa tashe har" "Allah yasa ya isa gida lafiya. Saboda tsananin damuwa duk yadda Innaye ke ta bin shi da kallon tuhuma ya kasa sanar da ita yadda suka yi, ya bari ne tukunna sai ya ji tsayayiyar magana daga bakin shi Mudan ɗin. Ita kuma Innaye saboda tsananin ladabi da biyayya irinna matan da ta kasa titsiye shi da tambayar yadda suka yi, sai kawai ta kawo ido ta zuba masa tana cigaba da addu'ar tabbatuwar auren kamar" yadda aka saka shi. "[1/1, 12:01 AM] Fareeda Abdallah: Tun safe har yamma babu wata ƙwaƙƙwaran saƙo da Baffa ya samu" daga Mudan ko wakilansa. Tsananin tashin hankali da damuwa yasa ya kasa faɗa ma ƴan'uwansa halin da ake ciki. Idan ya kalli Zulaikha da ita ma tun bayan abinda ya faru jiya sam ba ta cikin walwala sai yaji kamar zai saka kuka. Ya sani ko Zulai ta ƙi Allah a wannan gaɓar da bikinta yazo daf baza ta taɓa so ace an fasa bikin ba. "Kwanakin baya da kunnensa ya ji hirar Zulan da Yayarta Balira, tana faɗa mata ita kanta tana so ace yau ga shi tayi aure, amma tunda mijin bai zo ba ya za tayi da ranta?" "'Wallahi Aunty Balira ko da kuke ganin kamar ba na damuwa ina damuwa fa, amma ya na iya da abinda" ya gagari tuwo in ji kishiyar ƙonanniya? Mudan da kuke ganin kamar ina wulaƙanta shi don kar ya aure ni ina da dalilai da dama da nake ganin bamu dace da juna ba ni da shi. Amma ya zanyi? Tunda babu wanda ya fito neman aure na bayan shi? Haka nan zan aure shi. Ina ta addu'ar idan aurensa alkhairi a gare ni Allah ya tabbatar da shi.' "A Lokacin da ya tsinkayi waɗannan maganganun, a zauren gidan ne tayi ma Yaya Balira rakiya za ta koma" "gidanta, shi kuma ya sako kai zai shiga gidan da yaji maganar da suke yi sai ya tsaya ya saurara." Da la'asariyya liƙis yana zaune a cikin turakarsa ya ƙwalla ma Bilya ɗaya daga cikin ƙananun ƴaƴansa kira. """Salamu alekum. Ga ni Baffa.""" "Yaron ya faɗa a ladabce, bayan ya durƙusa har ƙasa a gaban Baffa." """Yi maza ɗakin Innaye ka kira min Zulai.""" """To Baffa.""" A guje yaron ya fice daga ɗakin yana haɗawa da ƴan tsalle-tsalle. Ba'ayi cikakken mintuna uku ba sai ga sallamar Zulaikha a ƙofar ɗakin. "Sai da ya amsa, yayi mata umarnin shiga sannan ta shiga cikin ɗakin. Tana sanye da wani zumbulelen" "hijabi kamar mai takaba. Idanun nan sunyi kozai-kozai sun kumbura alamun ta sha kuka, a bakin kofa ta tsuguna." """Ga ni Baffa.""" Ta fad'a da dasasshiyar murya. """Zulaikha?""" Ya kira sunanta a tausashe. """Na'am Baffa""" Shiru yayi yana sake kare mata kallo na wasu dakiku kafin ya cigaba da cewa. """Da safe na je har gida na sami Mudansiru. Irin maganganun da na ji daga bakinsa a kanki sam ban ji" "dad'insu ba. Amma na yi mishi uzuri, saboda ban san girman laifin da kika yi mishi ba har idanunshi suka rufe ya farfaɗa min waɗannan maganganun.""" Nannauyan ajiyar zuciya ya sauke kafin ya cigaba """A taƙaice dai, ya faɗa min cewa kin raina shi. Sam bakya bin umarninshi a matsayinshi na wanda yake" niyyar aurenki. Da wannan dalilin yasa na kira ki yanzu don in tambaye ki gaskiyar abinda ya faru. Kuma "ina roƙonki don Allah ba don ni ba ki ji tsoron Allah ki faɗa min gaskiyar abinda ya haɗa ku.""" A cikin ɗabi'un Zulaikha da kusan duk ƴan gidansu suka shaide ta akai shi ne ƙarya ba ya daga cikin halayenta. Za ta fito ta faɗi gaskiya ko da ita ce da laifi. Don haka a yanzu ma bata yi ƙasa a gwuiwa ba wajen sanar ma da Baffa gaskiyar abinda ya faru. Bayan ta gama sanar da shi kuma ta ƙara da faɗa masa babban dalilin da yasa ta ƙi zuwa barkan matarsa kamar yadda ya nema. """Baffa, matarsa Yahanasu tun zamanin ƴanmatacinmu da su ta tsane ni. Ban samu sauƙinta ba sai da" tayi aure. Amma jin zancen mijinta yana neman aure na babu irin baƙaƙen maganganu da munanan zagin da ba ta aiko min. Kwanaki can har aiko min tayi muddin na kuskura na auri mijinta ta rantse da "girman Allah a daren ranar za'a fitar da gawata a gidanta. Innaye shaida ce, duk irin maganganun da take" min aike Innaye ta sani. Ban taɓa faɗa maka bane don kar ku ga kamar ba na son auren ne. "Duk na faɗa ma Mudan amma ya ƙi fahimtata. Tsorona Allah tsorona in je mata barka tayi min lahani, ko" kuma ta ƙulla min sharrin da zan shiga bakin duniya. Wannan shi ne dalilin da yasa kai tsaye na ce mishi "bazan je ba.""" "Tsawon mintuna biyu Baffa ya kasa magana, babu abinda yake sai jujjuya maganganun Zulaikha a" "zuciyarshi. A karo na biyu ya sake sauke nannauyar ajiyar zuciya, sannan yayi mata umarnin komawa cikin gida." "Bayan sallar isha'i ya shiga ɓangaren Innaye da nufin yi mata sai da safe, tunda ranar ba girkinta bane." "Daga yadda idanuwanta suka zurma ciki lokaci yasa matsanancin tausayinta ya ƙara lulluɓe shi, bai shiga cikin falonta da niyyar zama ba, amma lura da halin da take ciki yasa shi zama kan kujera nesa da ita kaɗan yana yi mata nasiha kan muhimmancin yarda da ƙaddara mai kyau da mare kyau a matsayinta na" cikakkiyar musulma. """Shi ma ya fasa auren Auta ta ko?""" Ta katse shi da tambayar da raunin murya. """Eh toh! Bazan ce eh ba bazan ce A'a ba. Domin har zuwa yanzu ban samu wata gamsasshiyar amsa" "daga gare shi ba kamar yadda ya ce zai min aike. Kawai dai mu cigaba da addu'a.""" """Uhmmm! Allah ya jisshe mu alkhairi.""" Abinda ta iya cewa kenan ta sunkuyar da kanta ƙasa. Har Baffa ya fice daga falon bata iya sake ce mishi komai ba. "A wannan dare, idan Baffa ya ce ya yi cikakken barci na awa ɗaya yayi ƙarya. Duk yadda yake ganin" kamar abin bazai dame shi ba inaa... Mama Laminde da take da girki tun tana mishi nasiha da tausasan kalamai har dai ta gaji ta zuba ma sarautar Allah idanu. A ƙarshe ma juya baya tayi ta kwanta ta ƙyale shi yana ta tufka da warwara. "Babban damuwarsa ɗaya ne, idan Mudan ya ce ya fasa auren Zulai a waɗannan kwanakin wa za'a samu" "kuma yayi ƙundubalan fitowa ya ce zai aure ta? Ya sani duk maganganun da Zulai ta faɗa masa akan Yaha gaskiya ne, domin Rahina tana faɗa masa, amma duk su biyun basu ɗauki hargagin Yahan da" muhimmanci bane domin a ganinsu surutu ne kawai irinna mace me mahaukacin kishi. Sannan shi da kanshi sai yau ya ƙara yarda da halin Mudan da ake ta faɗa mishi na rashin haƙuri da "rashin iya magana. Amma duk waɗannan abubuwan bai ɗauke su da muhimmanci ba, babban burinsu shi da Rahina shi ne su aurar da Zulai." Domin anyi ittifaki a yanzu dai duk faɗin ƙauyen Faƙo babu yarinya budurwa da take da shekarun Zulai. Sa'anninta duk suna ɗakin mazajensu da ƴaƴayensu. Tun da daɗewa da ace shi mutum ne mai yarda da camfi da tuni ya daɗe da fantsama gurin masu "magunguna yana nema ma Zulai taimako. Domin da yawan mutane na ganin Aljani ne ya aure ta. Wasu kuma na ganin nauyin jini take da shi, dole sai an nemi taimako sannan za ta sami mashin-shini." Maganar ta saka ma kanta girman kai don ta yi boko ko kuma don Hafizu yana da gida a Habuja ne yasa take ɗaga ma samarin ƙauyen kai bai taɓa ji ba sai yau a bakin Mudan. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke a karo na barkatai. Ya ɗauki ƴar ƙaramar wayarsa mai tocila da take "ajiye kusa da shi ya danna ta kawo haske ya duba lokaci, ƙarfe uku da minti ashirin da bakwai na tsakiyar" dare. "Hasken tocilar wayar ya kunna, sannan ya miƙe tsaye ya buɗe ƙofa hannunsa riƙe da buta ya fita can" tsakar gidan ya ɗauro alwala. Ya sani duk wani tunani da saƙe-saƙe baza su samar mishi da mafita ba. Don haka ya ƙarasa daren yana miƙa kukanshi ga mai kowa mai komai mahaliccin sammai da ƙassai da abinda ke cikinta. Washe gari ko da ya tashi zuciyarsa babu damuwa kamar na jiya. Da asubah bayan idar da sallah ya tare "ƴan'uwansa shaƙiƙai guda uku da suke uba ɗaya ya faɗa musu duk halin da ake ciki, sun nuna alhini sosai." Sannan suka daɗe suna tausarsa da daɗaɗan kalamai. A ƙarshe suka ɓuge da addu'ar Allah ya kaɗe fitina yasa su ji alkhairi. "Ko da ya shiga gida, ya leƙa matansa gaba ɗaya yadda suka tashi turakarsa ya shiga ya kwanta. Yana" tasbihi da hailala daga kwance nannauyan barci yayi awon gaba da shi. "Ƙarfe goma da rabi na safe Innaye ta shiga ɗakinsa ta tashe shi. Idanunta sun kaɗa sunyi jaa, daƙiƙu" talatin ya ɓata yana kallonta kafin a hankali ya ce """Me yake faruwa Rahina?""" """Mudan ne ya aiko a bashi kayan auren Zulai da ya kawo. Wai ya fasa aurent...""" """Ubangiji Allah yasa hakan shi yafi alkhairi. Allah ya haɗa ta da wanda ya fi shi alkhairi nesa ba kusa" "ba.""" Ya katse ta da faɗin haka tun kafin ta ƙarasa faɗa masa abinda ke faruwa. A fuskarsa babu wata shahararriyar damuwa. "Daɓas! Ta zube a gefen katifar da yake kwance ta fara matsar ƙwallah, domin Allah ya sani ba haka ta so" ba. Da tausasan kalamai yayi ta rarrashinta har ya samu tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya. "Daga can bakin ƙofa sai ga sallamar Mama Laminde da Baba Laraba. Shi ya amsa sallamar, Innaye kam ta" kasa magana. Fuskokinsu a dame suka shiga cikin ɗakin suna ƙara jajanta ma Baffa wannan abin baƙin cikin da ya same su. """Babu komai ai. Wani baya taɓa auren matar wani. In Allah ya yarda ko da shi ko ba da shi ba ranar" "ɗaurin auren Zulai bazai canja daga yadda aka tsayar da shi ba. Ku kwashe kayansu ku kai musu.""" Da yake duk kayan da Mudan ya kai gidan hatta ihsani da yake mata na saurayi da budurwa ba amfani da "su take yi ba, Innaye take damƙa ma ita kuma sai ta kai ɗakin Baffa ta adana. Don haka cikin ƙanƙanin" "lokaci aka gama fitar ma da matan da ya aiko kayayyakinshi gaba ɗaya, hatta sadakinshi sai da Baffa ya ba Mama Laminde ta kai musu." "Kasancewar kayan ɗaki da na kicin da komai Hafizu ne ya ɗauki nauyin yin su, shi yasa ko sisi ba'a taɓa a" "cikin kuɗin na gani ina so, kuɗin gaisuwa da kuɗin sadaki da ya biya ba." "Kamar wutar daji, zuwa ƙarfe biyu labarin fasa auren Zulai da Mudan yayi har ya zaga ƙauyen Faƙo." Ƴaƴan Innaye da sauran ƴan'uwansu da suke uba ɗaya haka suka cika gidan suna jajanta ma junansu wannan abin baƙin ciki. Amma ko da iyayensu mata suka sanar da su abinda Baffa ya ce za'a ɗaura auren ko ba da Mudan ba sai kuma suka yi tsuru-tsuru. Tsoronsu Allah tsoronsu a aura ma Zulai tsoho ko kuma nakasasshe wanda baiyi mata ba ta ƙi yi masa biyayya saboda rashin haƙurinta. A sako ta kuma da ƙananun shekaru ta zama ƙaramar bazawara a gari a cigaba da mata tofin Allah ya tsine. """Innaye? Amma kina ga aurar da Zulai ga wanda bata sani ba hanya ce mai ɓullewa? Kar fa fushi yasa" "mu aikata aikin da za muzo muna da na sani...""" """Yayansu ke dai kiyi addu'a. Babu abinda zai faru sai alheri in Allah ya yarda.""" Innaye ta katse Yaya Balira da take maganar fuskarta cike da damuwa. "Kafin Balira ta sake cewa komai wayar Innaye da ke cikin hular kanta ya hau tsuwwa. Wayar ta ciro, ko" "da ta duba sai taga alamar mota, alamar da Zulai ta saka mata a lambar Hafizu." Bata ɓata lokaci ba ta ɗauka don daman ta kira shi a ɗazu domin ta faɗa mishi halin da ake ciki bai ɗauka ba. """Assalamu alaikum! Hafizu...""" """Innaye barka da yamma. Ki taya ni murna Innaye, Bintu ta haifi ɗa namiji yanzunnan, ni ma na zama" "Baba Innaye.""" Da karaɗin farin ciki da zumuɗi sosai a muryarsa yake jero maganganun. "Kamar yana gaban Innaye, haka fuskarta lokaci ɗaya ya ƙayatu da farin ciki mara misaltuwa." """Alhamdulillahi Hafizu Alhamdulillah! Barka da arziki. Allah ya raya mana yasa cikon musulunci ne?" "Yaushe ta haihu?""" Ta sake tambayarsa ta ma manta ya faɗa mata yanzu Bintun ta haihu. Da fara'a shi ma a muryarsa ya sake amsa mata yanzu aka yi haihuwar. """Ɗazu da za mu taho asibiti lokacin da take naƙuda ruɗewa da tashin hankali yasa na manta da wayar a" "gida. Sai da ta haihu na sami nutsuwar komawa gida na ɗauki wayata, yanzu wanka zanyi sai in koma asibitin.""" """Ma sha Allah! Allah ya raya mana. Hafizu na ya ƙara girma, ya zama Baba.""" Dariya ya kwashe da shi zuciyarsa cike da farin ciki. "Kafin ya katse wayar, kaf yayyinsa da suke cikin ɗakin sai da suka yi masa barka da arziki yana amsawa da" matsanancin fara'a sannan suka yi sallama. Wannan haihuwa da Bintu tayi shi ya dakushe kaifin damuwar da suke ciki na batun fasa auren Zulaikha. Hatta ita Zulan da tun zuwa karɓan kayan auren take cikin uwar ɗaki duƙunƙune akan gado tana kuka babu abinda ke fito da ita sai ɗauro alwala sai da ta daure zuciyarta ta fito falo cikin yayyenta suna murnar ƙaruwar da ɗan'uwansu ya samu. Fitar zancen haihuwar cikin gida da maƙwafta yasa ɗakin Innaye ya sake ɗinkewa da mata ana yi mata barka da arzikin samun jika. Sai da aka yi sallar Isha'i sannan Baffa ya fatattaki ƴaƴan masu aure suka wuce gidajen mazajensu. """Haba Hafizu, raɗin sunan jaririn ne har sai na taka ƙafafuna zuwa Habuja? Ai ina ga wannan duk abu ne" "mai sauƙi. Ba sai na je ba...""" """A'a Baffa!""" Ya katse shi da sauri. """Kar ka ce baza ka zo ba don girman Allah! Ka ga fa tunda aka yi haihuwar nan iyaye da ƴan'uwan Bintu" "ke ta safa da marwa a gidannan, sai ni ne daga ɓangarena babu wani shaƙiƙi nawa da zai zo takanas-ta- kano barka?""" """Kamar ya ba wanda zai zo daga ɓangarenka? Ca nake jiyan nan ka gama faɗa min irin hidimar da Alh" "Lurwanu da Iyalinsa suke yi tunda aka yi haihuwar?""" Baffa ya faɗa yana murmushi. """Baffa hidima da ɗawainiyar gidan Abba Lurwanu daban zuwan da za kayi daban. Wallahi ko shi sai da" ya tambayeni amma dai za ka zo ganin abokin na ka ko? Babban abin alfahari gare ni shi ne kai da kanka "ka taka ƙafafunka zuwa muhallina ka sa albarka, kaga jariri, sannan ka raɗa mishi suna da bakinka. Saboda Allah Baffa ni kenan don ina birni sai kuma ace mahaifana baza su dinga zuwa gida na ba? Ka ga fa Innaye ta ce baza ta sami zuwa ba, gara ma ita ta taɓa zuwa ta ga inda nake. Amma kai tunda na fara aiki shekara bakwai kenan sau ɗaya ka taɓa zuwa Abuja, dalilin zuwan ma ɗaurin aure na ne. Don Allah" "kayi haƙuri Baffa, duka tafiyar fa ta yini ɗaya ne za kuje ku dawo. Don Allah Baffa, don girman Allah.""" "Ya ƙarasa maganar da magiya sosai a muryarsa, kamar zai fasa kuka." "Tunanin gaskiyar da ke cikin maganganun Hafizu da yasa shi amincewa zuwan, amma Allah ya sani ba" "wai don zuciyarsa tana son doguwar tafiya ba. A ganinsa, tunda shi Hafizu yana yawan zuwa ƙauyen, kuma ya ɗauki duk nauyin buƙatunsu dai dai gwargwado, ba ma su kaɗai ba, hatta ƴan'uwa da jama'ar gari suna ɗanɗana daga alkhairan Hafizu. Me yake buƙata kuma bayan wannan? menene zai saka shi da" girmansa yayi ta jelar zuwa gidan yaro? "Tunda dai acan Habujan akwai Alhaji Lurwani, Baban Ibrahim abokin Hafizu, ya ɗauki Hafizun ɗa kamar" "yadda ya ɗauki ɗan shi Ibrahim, kuma ba don sun haɗa dangantaka ta jini ba, sai don kawai sun yi karatu tare da ɗan shi Ibrahim." "A taƙaice ma, hatta aikin da shi Hafizun yake yi shi ya nema mishi tare da ɗan shi Ibrahim. Duk wasu" "al'amura na Hafiz tsaye yake akai kamar ɗan shi na cikinshi, hatta hidimar auren Hafiz acan gidan Alhaji" "Lurwanu aka gudanar da komai. A ganinsa, da waɗannan dalilan me zai sa shi da ake yiwa kara ya dinga nuna rashin ta ido?" Amma tunda a wannan karon Hafiz ya nace za su shirya shi da ƴan'uwansa uku da Liman da yake "Amininsa suje su dawo. Tunda dai tafiyar ta rana ɗaya ce, in yaso daga can ma sa biya gidan Alhaji Lurwanu su ƙara yi masa godiya kan ɗawainiyar da suke yi shi da iyalansa akan Hafizu ba tare da gajiyawa ba." """Shi kenan! Zan zo. Amma ba ni kaɗai ba. Da su Babanka Abubakar za mu zo da Malam Ahmad Liman." "Yaushe ne ranar tafiyar?""" Da murna sosai a muryarsa yake jera ma Baffa kalaman godiya saboda tsananin jin daɗin amincewa zuwa gidanshi da yayi. Har sai da Baffa ya dakatar da shi da cewa godiyar ta isa haka. """Wallahi na ji daɗi sosai Baffa. Yanzu dai ka ga ƙarfe sha biyun rana. Zuwa ƙarfe biyu Mal Musa zai" "kamo hanyar zuwa, na san dai duk yadda ake ciki in Allah ya yarda magrib a Faƙo za tayi mishi, idan ya" "kwana. Gobe da asubah sai ku shirya da wuri ku kamo hanya, yadda za ku iso da wuri, idan za ku tafi sai in yanka muku tikitin jirgi zuwa Kaduna, daga can sai kuyi shatar mota zuwa gida.""" """To babu damuwa. Allah ya kawo shi lafiya.""" ***** "Kamar yadda Hafiz ya tsara, washe gari ƙarfe goma sha ɗaya na safe a gidan Hafiz tayi ma su Baffa. Sun" "isa yana gurin aiki, baiyi niyyar tafiya aiki a ranar ba. Amma kiran gaggawa da aka yi mishi a Ofis yasa shi" "fita babu shiri, da misalin ƙarfe goma saura kwata." "Da yake tun kafin ya fita ya jaddada ma Bintu su Baffa suna nan zuwa barka. A gabanshi, da murna sosai" ta karɓi maganar har tana cewa """Lallai abokin na Baffa ya zo da farin jini, daman bai taɓa zuwa gidannan ba. Allah ya kawo su lafiya.""" """Ƙwarai kuwa. Ameen ya Allah.""" Ya amsa yana dariya. A gaggauce ya sake mata sallama da cewar bari ya je ya dawo kafin su Baffa su iso. Yana fita daga ɗakin taja wani dogon tsaki ta raka bayanshi da harara. Ranta a ɓace ta fice daga ɗakinshi "zuwa na ta, ta kalli Raudha da take zaune gefen gado tana riƙe da Baby ta fara faɗa mata abinda ke shirin faruwa, bayan ta gama faɗa mata ta ƙara da cewa" """Na san shegen iyayin My dear ne yasa shi cewa su zo ganin Baby. Ai kam na rantse da Allah ba" "baƙauyen da ya isa yazo gidana ya damuƙa min baby da hannuwansu da suka saba damuƙa kayan cuta. Don haka idan suka iso, Raudha ki naɗe baby da showel da kyau sannan ki saka shi a abin ɗaukar can nasa mai kama da gado, ki kulle net ɗin kija zip ki rufe, sannan ki ɗaure belt ɗin yadda baza su taɓa iya buɗewa ba. Kin san ƙauyawa ne sosai, na san basu taɓa ganin irin abin saka jaririn nan ba balle su iya" "amfani da shi.""" Ta mayar da idanunta kan ƙanwarta Mashkura da take tare da ita tunda aka yi haihuwar ta cigaba da cewa """Mashku idan kin kai musu Babyn ki matsa su ganshi daga cikin gadon ba sai sun taɓa min ɗa ba. Atoh!" "Ni kaɗai nasan wahalar da na sha gurin haihuwarsa don haka kwanaki biyar da zuwansa duniya bazanyi sakacin da za'a goga masa cuta ba.""" """Kina da gaskiyarki Madam! Ban ga laifinki ba. Malam bahaushe ma cewa yayi taya Allah kiwo ya fi" Allah na nan. Balle ƙauyawan nan da tsubbace-tsubbace na tsiya yanzu haka sun ƙullo wani abun da za "su shafa ma yaron a matsayin tsarin jiki. Gara su kalle shi daga nesa kallon kura.""" Raudha ta faɗa da salon ingiza mai kantu ruwa. "Ita dai Mashkura bata ce komai ba, amma fuskarta kawai za'a kalla a ga yanayin rashin jin daɗi. Kamar" "dai bata ji daɗin maganganun Yayan nata da na ƙawarta ba. Amma dai bata ce komai ba, domin a" "ganinta gidan Bintu ne, iyayen mijinta ne, kuma ɗanta ne. Tana ikon tsara duk abinda take so kan iyalanta." Bayyanannen kamannin da ke tsakanin Baffa da Hafiz yasa tun kafin Mal Musa ya faɗa ma ma'aikatan "gidan wanene Baffa a gurin Oga su da kansu suka fahimci haka. Da girmamawa sosai suka dinga zubewa har ƙasa suna gaida su Baffa, bayan musayar gaisuwa a tsakaninsu Mal Musa yayi musu jagora suka shiga cikin falon gidan daƙyar, domin da sun dage su a shimfiɗa musu tabarma su zauna a harabar gidan" ba sai sun shiga ba. "Sai da Mal Musa ya kira Hafiz ya faɗa masa halin da ake ciki, shi kuma ya kira Baffa yai ta masa magiya" sannan suka amince da shigarsu cikin falon gidan. """Mahaifin Oga ne da ƴan'uwansa. Ki kawo musu abin sha da abubuwan taɓawa sannan ki shiga ciki ki" "faɗa ma Hajiya isowarsu.""" Mal Musa ya faɗi haka ga Rabi. Cikin ƙanƙanin lokaci Rabi ta cika gabansu da lemu kala daban-daban da ruwan gora. Ta haɗo musu da snacks saboda a lokacin bata gama abinci ba. "Jikinta na rawa, ta haura sama zuwa ɗakin Bintu don ta faɗa mata zuwansu Baffa." """Rawar jikin miye kike yi kamar wasu baƙi ne na musamman suka zo?""" Bintu ta daka ma Rabi tsawa da tambayar haka bayan ta saurari abinda ke tafe da ita. "Sakalau Rabi tayi da baki tana kallonta, sai kuma ta ce" """Ba komai Hajiya. Bari in koma kicin, sai kin fito.""" Jikinta a sanyaye ta fice daga ɗakin. Da kunnenta taji sadda Bintun ta raka ta da dogon tsaki. Zuciyarta cike da mamakin halayen Bintu na ƙin iyaye da dangin mijinta don kawai sun kasance ƙauyawa. Saboda Allah ta ina aka taɓa haka? Kina son ɗansu amma ba kya son iyayen da sukai sanadin zuwansa duniya? """Allah ya kyauta.""" Ta faɗa a fili sannan ta ƙarasa sauka ƙasa ta wuce kicin. Bayan ta faɗa ma su Baffa ga Bintu nan zuwa. "Kafin Bintu ta sauko Mashkura ta fara turowa da ɗan jariri, an naɗe shi a ɗan ƙaramin abin ɗaukansa mai" kama da godo kamar yadda Bintu ta tsara. Da fara'a a fuskar Mashku ta gaishe su sannan ta matsa kusa sosai tana nuna musu fuskar babyn kamar yadda Bintu ta umarceta. """Sannu yarinya, Allah ya raya. Abokin namu tsoron gamuwa da mu yake yi aka naɗe shi a cikin gado" "don kar muyi masa rubdugu?""" Liman Malam Ahmad ya tambayeta yana dariya. "Ita ma dariyar tayi, ta kasa cewa komai sai sake riƙe abin ɗaukar babyn da tayi da kyau." Baffa kuwa kai tsaye cewa yayi """Ki ciro shi daga ciki a ɗauke shi, raɗa mishi suna za'ayi da addu'o'i.""" "A ɗan daburce Mashku ta kalli Baffa bayan ta ji abinda ya faɗa, sai taga yayi mata kwarjini sosai baza ta" iya musa umarninta ba. Da ɗan rawar jiki ta aje abin ɗaukar akan kafet ta fara warware ɗaurin belt ɗin da aka ma yaron. Karaf! Akan idanun Bintu da take saukowa daga can sama. """Ke! Keh! Ke Mashkura? Me kike ƙoƙarin yi haka?""" Ta tambayeta cikin tsawa da ɗan ɗaga murya tun kafin ta ƙarasa sakkowa. "Bib-biyu ta dinga harhaɗa Step ɗin da ɗan gudu-gudu har ta ƙarasa sakkowa. Fuskarnan a ɗaure tamau," ko kallonsu Baffa bata yi ba ta sake daka ma Mashkura tsawar ta daina ƙoƙarin fito mata da Baby da take ƙoƙarin yi. Da mamaki sosai a fuskokin su Baffa duk suke bin Bintu da kallo. Da farko kamar ba wanda zaiyi magana "a cikinsu, sai kuma Baffa ya ce" """Ni ne na ce ta fito mana da shi mu ɗauke shi a raɗa mishi suna ayi mishi addu'o'i...""" """Yi haƙuri Baffa. Umarnin Likita ne ya ce kar a ringa damukarsa da hannuwa mabanbanta saboda" "jikinsa baiyi k'wari ba bazai yi wahalar d'aukar cututtuka ba...""" """Bintu?""" Hafiz da shigarsa cikin falon kenan ya tsinci maganar da take yi ya kira sunanta da mamaki sosai a fuskarsa. """A hannun iyayen nawa ne zai kwashi cuta?""" Ya sake tambayarta ranshi a bace. """Common dallah fito musu da Baby su d'auka in yaso ya kwashi cutukan duniya ba ma ciwo d'aya ba.""" Da saurin gaske Mashku ta karasa warware belt ɗin ta fito da shi ta miƙa ma Baffa. Ko fushi yayi ne Allah "masani. Bai karɓi yaron ba, sai Malam Ahmad ne ya miƙa hannu ya karɓi ɗan da murmushi a fuskarsa," duk a ƙoƙarinsa na shashantar da abinda ya faru. """Lallai wannan aboki namu manomi ne. Kai ka ganshi Abubakar har ya fi sadda aka haifi Hafizu girma?""" Yayi maganar yana dariya idanunshi akan ɗaya daga cikin Ƴan'uwan Baffa. """A lallai kuwa. Da alamun an samu Sarkin noma. Bana damuna za tayi albarka.""" Baba Abubakar ya faɗa shi ma fuskarsa cike da murmushi. Idanunsa akan jaririn yana kallonsa cike da burgewa. Bintu da take tsaye cikin matsanancin girgiza da tashin hankali don bata taɓa tsammanin bayyanar Hafiz "a daidai lokacin ba rasa tudun dafawa tayi. Bayan zafafan tambayoyin da Hafiz ya aika mata waɗanda sam ba ta da amsarsu, a ƙarshe ya ɓuge da yi ma tilon ɗan nasu fatan kwasan miyagun cututtuka tana ganin wani mahaukacin kallo da yake aika mata daga inda yake zaune a ƙasa kamar zai cinye ta ɗanye." Ita kuwa Mashkura daman tunda ta samu aka karɓi jariri daga hannunta ba wanda yasan sadda ta bar falon. "Tsakanin Mal Ahmad da Baba Abubakar, Baba Lukman, Baba Hamisu kuma raha suke tayi a tsakaninsu" suna karɓa-karɓa da jaririn suna addu'o'i da yaba girmansa. "Ɓangaren Baffa kuwa babu wanda zai ce ga yanayin da yake ciki, fuskarsa a baibai take. Kuma har" lokacin bai karɓi jaririn ba. Ya ƙura ma guri ɗaya idanu kamar yana tunanin wani abu. "Hafiz dai yana zaune a gaban iyayen nasa kan kafet, idanunsa a ƙasa kamar zai saka kuka. Idan ya ɗaga" kai ya kalli Bintu da take tsaye a gabansu kamar mutum-mutumi ransa a ɓace sai kuma ya sunkuyar da kansa. Ko da ake faɗin karin maganar nan ta ruwa na neman ƙare ma ɗan kada bata taɓa fahimtar cikakkiyar ma'anarta ba sai yanzu da nata ruwan ke neman ƙare mata. Lura da tayi lallai idan bata yi gaggawar gyara wannan shirmen da ta tafka ba kwaɓarta na gaf da yin mugun ruwa yasa ta fashe da ƙaƙƙarfan kuka sannan ta zube a ƙasa. Da rarrafe ta ƙarasa gaban Baffa ta riƙe gefen Babbar rigarshi ta fara jero mishi kalaman ban haƙuri cikin kuka da ƙanƙan da kai. """Na tuba Baffa na tuba. Don girman Allah kayi haƙuri ka yafe min. Kai mahaifi ne a gare ni idan baka" yafe min ba ina zan saka kaina? Na rantse da Allah ba da gan-gan na so hana ku ɗaukar jaririn ba. Likitan yara Dr. Kauthar da ta fita yanzu kafin shigowarku ita ce ta ce lallai a kiyaye yawan ɗaukarshi saboda gudun kwasar cutuka domin fatar shi babu ƙwari. Don Allah kuyi haƙuri ku yafe min. Baba Abubakar ku ma don Allah kuyi haƙuri. Malam ku yafe min don Allah bazan sake ba. Don Allah kuyi haƙuri. My dear "kai ma ka yafe min.""" Irin yadda take rusa kukan tana magiyar su yafe mata ba ƙaramin tausayi ta basu ba. Gaba ɗayansu basu wani ja da nisa ba suka ce sun yafe mata. Har suka sa baki Hafiz ya ce babu komai ya wuce. Bata daina kuka ba har sai da taga Baffa ya karɓi jaririn a hannunsa yayi masa addu'o'i. Sannan ya miƙa ma Malam Ahmad ya sake yi masa huɗuba ya raɗa masa suna. Kafin ya raɗa sunan ko da "ya tambayi Hafiz ko suna da wani zaɓin suna da suke so a raɗa ma yaron da sauri ta riga shi cewa, duk" dai a ƙoƙarinta na ƙara share laifinta ta ce """Malam ka raɗa masa sunan Baffa ne don Allah. Daman tun kafin in haihu na ƙuduri niyyar in dai namiji" "ne sunan Baffa za'a sa idan kuma mace ce sunan Innaye za'a saka.""" Da wannan maganar da tayi yasa Malam ya raɗa ma yaron suna Aminu (Al'ameen). Rabi da take kicin tana laɓe tana kallo kuma tana jin duk abinda yake faruwa babu abinda take yi sai dariya. """Iya duniya ya fi iya mota.""" Ta faɗa a fili tana sakin dariya ƙasa-ƙasa. Da saurin gaske ta koma gurin aikinta ganin Bintu ta taso daga gaban su Baffa ta nufo kicin ɗin da sauri. "Tun safe, ta saka Rabi tayi mata farfesun kaji a zambaɗa kayan ƙamshi da ɗan daddawa su dahu ruguf," ko za ta iya ci sosai saboda tunda ta haihu bakinta babu daɗi. Tana shiga cikin kicin ɗin ko kallon Rabi bata yi ba ta ɗauki ɗaya daga cikin kulolinta masu tsada ta juye farfesun gaba ɗaya. """Ki ɗauko farantai da cokula ki kawo min falo.""" Ta ba Rabi umarni gaf da za ta fice daga cikin kicin ɗin. Da kanta ta zuzzuba musu farfesun ta ajiye a gabansu tare da basu haƙurin su ci kafin a ƙarasa abinci. Ta miƙe za ta haura sama a fakaice ta kalli babynta da har lokacin yana hannun Mal Ahmad suna hira da Hafiz suna ta dariya. "Kamar ta ce ya kawo shi su ci abinci, amma tsoron kar ta sake ɓallo ma kanta ruwa yasa kawai ta wuce" zuwa sama duk zuciyarta a ƙuntace. Lallai da gaske idan ka ji ƙi gudu sa gudu ne bai zo ba. A irin wannan tsaka mai wuya da ta shiga cikin "ƙanƙanin lokaci, bata taɓa tsammanin za ta iya samar ma da kanta mafita cikin sauƙi haka ba. Sai ga shi tsabar tashin hankali da tsoron abinda zai biyo baya tsakaninta da Hafiz yasa ƙwaƙwalwarta buɗewa, ta" "aikata aikin basira, hikima, wayau da bata taɓa tsammanin za ta iya aikatawa ba." """Hmmmm!""" "Ta ja nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, ta huro iska mai zafi daga bakinta, sannan ta buɗe ƙofar ɗakinta" "ta shiga da siririyar sallama a bakinta. Duk jikinta a sanyaye, ga idanunta sun canja launi sun kumbura, alamun ta sha kuka." Kallo ɗaya Raudha da take kwance akan gadonta tana daddanna waya tayi mata ta miƙe zaune da sauri. Idanunta warwaje ta ce """Ƙawata lafiya? Me ya samu idanunki?""" """Uhmmm! Ke dai bari Raudha. Yau na tsallake rijiya da baya. Sai fatan Allah ya kiyaye na gaba.""" Amsar da ta iya ba ta kenan ta shige banɗaki. ***** "Ƙwan zabi ƙwarya uku, kajin hausa manyan zakaru guda goma. Garin kukar miya mai kyau da garin" busasshiyar kuɓewa su ne tsarabar da Baffa ya riƙo ma Hafiz da gidan Alh Lurwanu. Duk yadda suka so tafiya da wuri sai da suka kai ƙarfe ɗaya da minti goma a gidan Hafiz. Sun ci abinci "sunyi nak! Sannan Baffa ya ɗiba musu tsarabar ƙwan zabbi ƙwarya ɗaya, kaji guda huɗu, kuka da kuɓewa dai bai ɗiba musu ba, domin bai ga alamun cin tuwo a gidan Hafizu ba." Baya ga haka ita kanta Innaye da ta bada kuka da kuɓewar da sunan iyalan Alh Lurwanu ta bayar. """Ita kuma matar Hafizu fa?""" Ya tambayeta da mamaki a fuskarsa. Sai da tayi dariya kafin ta amsa da """Matar Hafizu ƴar gayu ce ta bugawa a jarida. Har muka gama zamanmu a gidan ko da kuskure bamu ji" "ta ambaci tuwo ba.""" "Dariya suka yi duk su biyun kafin ya sake mata sallama, ita kuma tayi mishi addu'ar Allah ya tsare hanya" sannan suka fice daga gida. Hafiz da kanshi ya tuƙa su a mota zuwa gidan Alh Lurwanu. Ya rabbi! Mal Bahaushe ya ce in da ba ƙasa nan ake gardamar kokawa. Wata irin tarba ta girma kuma ta musamman da basu taɓa tsammanin samun irinta ba suka samu a gidan Alh Lurwanu. Duk da sun daɗe da shaida shi ɗin mutumin kirki ne. Amma a wannan ranar ya ƙara tabbatar musu da halayen kirki da karamcinsa. Ya kuma ƙara tabbatar musu da fa babu wani banbanci tsakanin talaka da "mai kuɗi, ko kuma banbanci tsakanin mutumin ƙauye da na birni." Irin yadda ya sake a cikinsu suna hira da ɓaɓɓaka dariya irinta manya suna caccafkewa a tsakaninsu wanda bai sani ba sai yayi tsammanin aminai ne na ƙud da ƙud. Tun ana gobe za su zo Hafiz ya sanar da "shi zuwan su Baffa, don haka ya soke duk wasu shirye-shiryenshi na ranar da za su zo." "Kamar wasu manyan baƙi da suka taho daga wata ƙasa, ƙayatattun girke-girke na musamman yasa aka yi" musu. Bayan sun ci sun sha ya cika su da abubuwan arziki masu yawan gaske. A dole aka yi asaran tikitin jirgin ƙarfe biyu da Hafiz ya yanka musu aka sake booking ɗin jirgin ƙarfe huɗu. Wani ƙarin karamci na musamman da yayi musu shi ne tun kafin su isa Kaduna akwai direba na "musamman da Alhajin ya tura yake jiran isarsu. Suna isa, ba tare da ɓata lokaci ba ya kwashe su da" kayayyakinsu suka kama hanyar Faƙo a wata luntsumemiyar mota da idanu kaɗai zai bayyanawa mai kallonta mai masifar tsada ce. Ƙarfe bakwai da rabi na yamma suna ƙofar gidajensu. Wannan tafiya dukkansu ba ƙaramin daɗinta suka "ji ba, babu abinda ke fita daga bakunansu sai addu'ar fatan alkhairi ga Alh Lurwanu da duk zuri'arsa." "Ana sauke kayayyakinsu ba tare da ɓata lokaci ba direba ya juya zuwa Kaduna, duk yadda suka so ya" tsaya ko abinci ya ci ya ce musu a ƙoshe yake. Ya tafi suna ta bin shi da addu'ar Allah ya tsare hanya ya maida shi gida lafiya. ****** "Da mamaki a fuskarta take kallonsa. Da yake har ta fara barci ya tashe ta, sai tayi tsammanin ko" kunnuwanta ne basu ji da kyau ba. """Me ka ce Baban Yasin?""" Ta tambaye shi don ƙara tabbatar da abinda kunnuwanta suka jiye mata. """Na ce miki Hafizu ya kira ni ɗazu da rana, ina cikin Kaduna ya ce in sami mai POS a tura mishi da" Akawun namba. To a taƙaice dai bayan an tura mishi ba a daɗe ba ya saka dubu ɗari. Bayan ya tura "kuɗin ya sake kira na ya ce in samu motocin Bus guda biyu duk da tawa uku kenan musha mai, gobe idan Allah ya kaimu mu kwashe ku da sauran masu shirin zuwa suna mu kai ku Abuja...""" """Shi Hafizun ne ya faɗa maka akwai masu shirin zuwa suna gidansa har mota uku?""" Ta tambayeshi tana ɗan harhaɗe giran sama da ƙasa. Kafin ya amsa mata ta ƙara da """Ai kuwa za ku mayar masa da kuɗinsa. Domin ko ni da su Ladidi ba ma wani shirin zuwa suna balle" "sauran ƴan uwa su ce za su je. Suyi sunansu lafiya, mu dai babu inda za mu je...""" """Wani irin zancen banza ne kike yi haka Balira? Matar ɗan'uwan na ku shaƙiƙi namiji ɗaya tilo ta haihu" "kuma haihuwar farko ku ce baza ku je suna ba?""" """To miye a ciki? Mun yi murna, kuma munyi addu'a Allah ya raya. Zuwa suna Habuja ne dai baza mu je" "ba.""" Ta faɗa da dukkan gaskiyarta. "Kallonta yayi mamakinsa na ƙara girmama, sai kuma ya tuna tun bayan dawowarsu Abuja da daɗewa bai" ƙara ji tayi mishi zancen zuwa gidan Hafizun ba. Lallai akwai wani abu da ya faru a wancan lokacin amma bata faɗa mishi ba. "Guri ya nema ya zauna a kusa da ita, a tausashe ya ce" """Me yake faruwa Balira? Ko akwai matsala tsakaninku da matar Hafizu ne?""" """Babu matsalar komai.""" Ta faɗa da sauri. Domin a ganinta matsalar da ta shafi ɗan'uwanta daban! Haka zalika matsalar da mijinta zai sani daban. A ganinta babban kuskure ne ta kwaye ma ɗan'uwanta baya a gaban mijinta. Kowa da muhimmancinsa daban! """In dai kuwa babu matsala suna dole sai kun je. Domin kuɗin da ya turo har mun ciccika tankin" "motocinmu da mai. Gobe sai tafiya da misalin ƙarfe sha ɗaya na safe in Allah ya yarda. Bari ma in kira Baffa in faɗa masa halin da ake ciki...""" """Ko ka faɗa masa shi ma bazai goyi bayan zuwanmu suna ba. Kuma zan kira Hafizun yanzu in mishi" "kaca-kaca tunda ba ya jin magana, tun rannan na faɗa mishi baza mu je suna ba amma don neman zance shi ne ya tura muku kuɗin mai. To kuwa sai dai yayi asara, ni kam ba ni zuwa ko ina""" Baban Yasi dai bai saurareta ba ya fice daga ɗakin ya barta tana bambamin faɗa kamar za ta ari baki. "A fusace ta ɗaga filon da kanta yake kai ta ɗauko wayarta, ƙanƙance idanu tayi ta lalubo lambar Hafiz ta" danna mishi kira. Second ɗaya biyu sai ta ja tsaki ranta a ɓace. A can ɓangaren Hafiz da yake ya san "yadda suka rabu da ita tun sa'adda ya tambayeta masu zuwa suna yana ganin kiranta ya ki daga wayar, a karshe ma sai ya kashe wayar gaba daya don kar ta cigaba da damunsa." "[1/4, 7:40 PM] Fareeda Abdallah: Zancen d'aukar shatar motoci da Hafiz yayi ga masu niyyar zuwa suna" "gidansa yana isa kunnen Baffa ya karbi maganar da hannu bibiyu. Irin yadda ya dinga nuna farin ciki da zumudi, ba karamin mamaki ya ba Innaye ba. Domin tun a daren ya fara kiran mazajen 'ya'yansa mata da suke gidan aure yana nema musu izinin tafiya suna gidan d'an'uwansu a Habuja." "Ya kira 'yan'uwansa ya sanar da su lallai su fada ma matansu da yayansu da suke gidan aure, duk wacce" take son zuwa suna gidan Hafizu mota kyauta ne zuwa da dawowa. "Ya aika gidansu Innaye ya fada ma yan'uwanta. Tun Innaye tana shiru taga iya gudun ruwansa, sadda ta" ga ya fara aikawa gidan abokan arzikinta yasa ta kasa hakuri har sai da ta ce mishi """Anya Malam gayyar mutanen nan da kake yi zuwa gidan Hafizu zai haifar mana da d'a mai idanu kuwa?" "Matar Hafizu ba irin matan birnin nan bane da suke son mutanen kauye fa...""" """Ba don ita za su je ba. Don shi ne, tunda dai shi namu bai guje mu me ya dame mu da halinta na" "gudun mutanen kauye? Na tabbata Hafizu bazai taba bari matarsa ta wulakanta masa yan'uwa ba.""" Ya katse Innaye tun kafin ta aje numfashin maganarta. """To shi kenan! Allah ya kaimu goben Lafiya.""" Ta yi addu'ar jikinta a sanyaye. """Ameen.""" ***** Motoci ukun da Hafiz ya dauki shata sai da suka cika tam da yan'uwa da abokan arziki saboda kara irinta "mutanen kauye. Duk yadda Yaya Balira taso zille ma zuwa sunan sai da Baffa ya tilasta ta tafiya, haka nan ta shirya yan kayayyakinta kala biyu a cikin jaka suka kama hanya, duk zuciyarta a kuntace. Domin Allah" ya gani sam bata so tafiyar ba. Ita da yan'uwanta da suke daki daya fuskokinsu ba yabo ba fallasa. Su kuwa sauran yan'uwa da basu san dawan garin ba bakunansu har kunne. Sai murna suke suna "dararraku, ko wacce tana baje labarin irin nisan tafiyar da ta taba yi a rayuwarta. Dukkansu dai kololuwar" "tafiyarsu Kaduna ne, hatta yan'uwan Hafiz da suke uba daya basu taba zuwa gidanshi ba tunda yayi aure sai yanzu da za su tafi." "Karfe biyar na yamma suka isa gidan Hafiz. Da yake ya shirya ma zuwansu sosai, wadataccen abinci yasa" "aka dafa musu da ya ji nama zuk'u-zuk'u. Katan-katan na lemu masu sanyi aka tare su da shi da ruwan gora, komai dai sun same shi a wadace sai da suka ci suka sha suka bar saura." Dakunan BQ da suke manyan dakuna kuma a wadace tun kafin su isa yasa an gyara ko ina fes! Daman "akwai funitures a ciki, duk abinda babu kuma kafin su isa an tanade shi." Gidan Hafizu bai fara d'aukar harama da nuna alamun gidan da za'ayi suna bane sai da suka isa. Duk da tazarar da ke tsakanin inda suke da ainahin inda matar gidan da daidaikun yan'uwa da kawayenta ke zaune har nan ake jin hayaniyarsu. "Bintu ta cika tayi fam kamar za ta fashe. Ita kadai sai huci take yi kamar kububuwa, amma ta kasa furta" "ko uhmm! saboda Hafiz yana gidan. Kamar wata sakarya, da ya shiga dakinta ko kuma ya kira ta zuwa dakinsa sai tai ta washe mishi baki tana dariya duk don dai kar ya ji a zuciyarsa kamar ba ta maraba da zuwan 'yan'uwansa." Tun abinda ya faru ranar da su Baffah suka je a tsorace take. Don ma Allah ya taimaketa Hafiz din ba "mutum bane mai rik'o. A sadda abu ya faru, idan ya nuna bacin ransa cikin kankanin lokaci zai warware ya koma da walwalarsa. Shi yasa take iya yinta wajen kiyaye abinda zai sake janyo mata wani bacin rai da" ba ta tunanin za ta iya warwareshi cikin sauki. Abu daya da ya aikata ta ji nutsuwa kadan a ranta shi ne bai bar yan'uwansa sun shiga bangarenta ba. Umarnin shiryawa yayi mata sannan ya dauki Baby Al'ameen wanda ake yiwa inkiya da Aadil suka je bangaren da aka sauki bakin suka gaisa. "Tana ji tana gani sukai ta damukar jaririn ranta yana k'una, amma ko a fuska ta gagara nunawa har suka" "gama gaisawa da tambayar lafiyar su Innaye sannan ta fice ta barsu da d'an'uwansa. Har d'an tsayawa tayi ko za'a ce ga Aadil ta wuce da shi amma ta ji shiru, haka nan ta fice ta barsu da Hafiz tana ta jan kananun tsaki a zuciyarta." Gudummuwar naira dubu talatin 'yanuwansa suka hada mishi a matsayin gudummuwa. Sadda Aunty Balira ta kebe shi gefe ta bashi kudin ji yayi kamar zai saka kuka. Zuciyarsa ta kara cika da kaunar 'yan'uwansa. """Mun so mu siya ma Babanmu kayayyakin jarirai sai kuma muka ji tsoron siyan abinda bai dace da ku" "yan birni ba. Shi yasa kawai muka yanke shawarar taho maka da kudin, kayi hakuri. Ka san yanayin garin...""" """Haba! Ba komai Wallahi Aunty Balira, na gode. Allah ya bar zumunci. Na ji dad'i sosai Wallahi. Amma" "yanzu dai ki ajiye min kudin a gurinki, zuwa safe in sha Allah zan karba.""" "Da haka suka rabu, ya karbi jaririn da ke ta barci hankalinshi kwance ya mayar da shi gurin Mamansa. A" lokacin ana ta kiraye kirayen sallar Magriba a masallaci. Washe gari da asubah tafiyar aiki mai matukar muhimmanci ta kama Hafiz da wasu daga cikin abokan "aikinsa. Lagos za su tafi, bai so tafiyar ba ko kaɗan, amma da yake kira ne da suka daɗe suna jira daga branch ɗin su da ke Lagos yasa tafiyar ta zama dolen-dole. A gaggauce ya fara shiryawa yana rarrashin Bintu da take ta matsar ƙwalla, ta ci burin taron sunan nan ayi da shi, sai ga shi tafiyar ta bazata ta rusa musu bodjet." "Taron suna ne suka shirya shi irinna ƴan birni kuma yan gayu, domin ba ma a gidan za'a yi taro ba. Event" "center suka kama mai matuƙar kyau da tsada, acan suka shirya za'ayi taron sunan. Duk ɗinke-ɗinken da tayi sunyi ne tare da Hafiz, taron suna ne da suka shirya gudanar da shi kamar gagarumin taron bikin aure. Sai ga shi tana ji tana gani tafiyarshi ya rusa kaso arba'in cikin dari na tsarin da suka yi ma bikin" sunan. "Ranta a bace ta raka shi har gurin mota yana kara rarrashinta da tausasan kalamai, bata koma cikin gida" ba sai da taga direba ya fice da motar sun nufi Ofis inda za su haɗu da sauran abokan tafiyar tasa. "Sai da suka yi nisa da gidan sannan ya tuna da su Aunty Balira, goshinsa ya dafe kadan alamun bai ji" "dadin mantuwar ba, ya dauki wayarsa ya kira ta suka yi sallama bayan ya jaddada mata in sha Allah a ranar zai dawo." "Tun da Hafiz ya bar gidan, sai ya zama kamar an shafe su Aunty Balira da manawarsu a zuciyar Bintu. Ta" "manta gaba daya da babinsu balle ma har ta tuna da suna cikin gidan, ko kuma tayi kokarin sauke wani hakki na su da yake kanta a matsayinsu na dangin mijinta." Harkokinta kawai take yi cikin yan'uwa da kawayenta. Da kuma matasan yara mata 'ya'yan Alh Lurwanu "da suka je gidan tun da wuri, ta kuma karɓe su hannu bibiyu kamar yadda ta saba, domin su ta riƙa a" "matsayin dangin mijinta na gaske, ba waɗancan gayyar ƙauyawan da ta raina ma ajawali ba." Hatta abin karyawa sai da aka doshi ƙarfe goma da rabi na safe sannan Aunty Balira ta shiga can cikin gidan tayi ma Bintu maganar abin karinsu. """Kin san mutanenmu basu saba ɗaukar lokaci mai tsawo basu karya kumallo ba. Kuma wasu a cikinmu" "sun zo da ƙananun yara, idan manya sun jure yunwa kin ga yara baza su jure ba.""" Ba kunya ba tsoro ta kalli Aunty Balira cikin ido ta ce """Na ji ! Ki je, za'a kawo yanzu. Kin san yau ne taron ni har ga Allah na ma ma manta da ku. Kuma dai ya" "kamata ko ɗan yaya ne ku dinga yima mutum uzuri tunda kun san ranar sha'ani kai ɗaukar zafi yake yi.""" "Ta faɗa da dukkan gaskiyarta, fuskarta babu walwala ko kaɗan." "Aunty Balira ta kalle ta da ɓacin rai, kamar za tayi magana sai kuma tai shiru ta girgiza kai, ta fice daga" ɗakin ranta a ɓace. Kafin ta isa can inda sauran suke ne tayi ƙoƙarin sakin fuskarta don kar su fahimci da wata ƙasa. "Ko da taje tayi maganar abin karin, sai da aka ɗauki fiye da mintuna ashirin kafin aka kai musu abinci," "shinkafa ce dafa duka da taji busasshen kifi a cikin wata ƙatuwar kula sai alalen leda a kula daban, sai" kuma ruwan sha na gora katan-katan da aka shigar musu da shi. "Tun daga wannan abinci da aka basu, Bintu bata ƙara waiwayarsu ba. Ita ma Aunty Balira bata ƙara shiga" "cikin gidan tayi mata maganar abinci ko wani abu da suke buƙata ba. Ƙarfe biyu na rana kuma suna daga can ɓangarensu suka dinga jin tashin motoci na ficewa daga gidan, ko da suka leƙa da sauri, sai suka ga mata ne ake ta fita da su a mota sun sha kwalliya na gani a faɗa." Akan idanunsu Bintu da tasha wata ƙayatacciyar kwalliya kamar sarauniyar kyau ta saɓo jaririnta tana "tafiyar ƙasaita ƙawayenta na take mata baya, ko kallon ɓangaren da suke tsaitsaye baki buɗe suna" kallonta bata yi ba ta shige cikin mota. Ƙawayenta ma suka shiga mota aka fice da su daga gidan. ****** """Bintu? Sai naji kamar jiya Hafiz yana faɗa ma Abbansu ƴan'uwansa za su zo suna daga can gida. Ya" "banga ko mace ɗaya a cikinsu ba?""" Hajiya Balaraba uwargidan Alh Lurwanu ta tambayi Bintu da mamaki a fuskarta. Ganin tun da aka fara shagalin taron sunan ko ire-iren dangin Hafiz bata gani a gurin ba. "Dariyar yaƙe ta ɗanyi, ta ɗan sosa gefen ɗaurin ɗankwalinta da mai kwalliya ta ɓata fiye da minti talatin" tana ɗaura mata. Sai kuma tayi saurin wayancewa ta ce """Wallahi Mama kin san abinki da mutanen karkara. Babu yadda banyi da su ba su shirya a taho da su" "gurin taron nan suka ce baza su zo ba, a cewarsu sun fi so su zauna a gida. Da naji haka sai kawai na bar" "musu komai da za su buƙata a wadace mu kuma muka taho.""" """Habawa! Ko da na ji. To don Allah kafin su wuce dai a saka direba ya kawo su mu gaisa, akwai saƙon" "da nake so in basu su tafi ma da Innaye.""" """To shi kenan Mama. In sha Allah za a kawo su, gobe da wuri zan saka direba ya kawo su.""" Da haka suka rabu da Mama ta cigaba da warwasawa cikin ƙawayenta. Ɓangaren Hafiz acan Lagos duk irin hotuna da Vidion taron da Bintu take ta tura mishi kanshi ya ɗau "zafin da bai samu buɗe ko guda ɗaya ba. Meeting suke ta shiga da manyan Oganninsu, daga wannan sai wannan. Duk yadda ya so su juya Abuja a ranar ma hakan bai samu ba, saboda basu gama komai da komai ba sai bayan magrib." "Daman akwai ƙayataccen masaukin da aka kama musu na kwana ɗaya, su ne dai kawai suka yi tunanin" za su gama komai a ranar su juya Abuja cikin iyalansu. "Sai da daddare, bayan ya gama duk wasu al'adunsa na kwanciya ya bi lafiyar gado sannan ya samu" nutsuwar buɗe data ya hau online. "Ko a waya da yaga taron ya ƙayatar kamar yadda suka so, shi kaɗai yake ta sakin murmushi yana sake" "buɗe hotunan, yana kallon Yadda Bintu da jaririnsa suka yi wani fitinannen kyau kamar a sace su a gudu." "Yana daga cikin dalilin da yasa a kullum soyayyar Bintu ke ƙara sabuntuwa a zuciyarsa, kyakkyawa ce ta" "ƙarshen ƙarshe. Shi kuma a rayuwarsa haka Allah yayi shi da bala'in son mace mai kyau na ɗaukar hankali, kallon dirarriyar mace kuma kyakkyawa kamar Bintu a matsayin matarsa kaɗai yakan saka shi jin" alfahari. "Mace ce ta nunawa tsara, duk girman taro da ƙayatuwarsa babu inda zai kasa shiga da Bintu a matsayin" matarsa. Sai da ya gama kallon hotuna da vidiyin tsaf! Ya kira ta suka ɗauki fiye da awa ɗaya suna hirar yadda "taron ya kasance, a gefe guda kuma suna ƙara ba ma fulawarsu ta soyayya ruwa. Daƙyar suka yi sallama" bayan kiran Ogansu ya shigo wayarsa. Bayan ya gama waya da Oga sun tattauna kan yadda meeting ɗin da suka yi ya kasance hotunan ya sake "buɗewa, yana kallo zuciyarsa na ƙara tunbatsa da farin ciki. Nan take ya ware waɗanda suka yi kyau sosai da zai sa a wanke manyan hotunansu. Sannan ya tsara a zuciyarsa idan ya koma gida lallai dole ya sake shirya wani ɗan ƙwarya-ƙwaryan taron tsakaninshi da iyalinshi suyi hotuna, domin ya sake ware" waɗanda za a bugo manyan kati su maƙala a falonsu na tarihi. "Ƙarfe goma da rabi na dare, Aunty Balira da sauran ƴan'uwansa suka faɗo mishi a zuciya. Da saurin gaske" "ya lalubo lambarta ya danna mata kira, a zuciyarsa yake jin lallai bai kyauta ba na yadda duk yinin ranar bai samu ya tsuke lokacinsa ya kira ta yaji yadda suka yini da yadda taron sunan ya kasance a ɓangarensu ba. Sai kuma a lokacin ya sake tunawa da ai duk yawan hotuna da Vidion da Bintu ta tura" mishi ko mutum ɗaya bai gani daga cikin ƴan'uwansa ba. Haka kawai ƙirjinsa ya ɗan buga daram! A daidai lokacin kuma kiran da yayi ma Aunty Balira ya tsinke "bata ɗauka ba, bai gaji ba, ya sake danna kiranta a karo na biyu, nan ma dai har ya tsinke bata ɗaga ba. A" "taƙaice sai da ya kira ta sau huɗu bata ɗauka ba, kawai sai ya danna kiran lambar Bintu, ita ma dai har ya kira ta sau uku bata ɗauka ba." Ya kuma rasa dalilin da yasa haka kawai ƙirjinsa ke cigaba da bugawa akai-akai. """Uhmmm! Allah yasa dai lafiya.""" Ya faɗa a fili bayan ya haɗiyi wani kakkauran miyau da ya taru a bakinsa. "A can gidan Hafiz kuwa, a daidai wannan lokacin da yake kiran Aunty Balira tana can cikin gidan ita da" ƴan'uwanta biyu suna yi ma Bintu wankin babban bargo akan wulaƙancin da tayi musu a wannan rana. Kun san abinku da mai haƙuri bai iya fushi ba. Sannan Bintun ta daɗe tana shiga musu hanci da "ƙudundune, su Aunty Ladidi da Aunty Rakiya sun daɗe da burin son su fyato ta Aunty Balira da Innaye suke dannarsu." "[1/6, 10:15 PM] Fareeda Abdallah: Yau kam da suka samu dama basu tsaya sanya ba, Aunty Rakiya da" duk ta fi su zafin zuciya saboda ɓacin ran yadda Bintu take mayar musu da magana cikin tsantsar raini da gadara sau uku tana yunƙurin janyota don rufeta da duka Aunty Balira da ƴan'uwan Bintu da suka rage a gidan suna shiga tsakani. Cikin fushi da ɓacin rai sosai Aunty Ladidi ta cigaba da magana cikin faɗa tana nuna Bintu da yatsarta manuniya """Ke har kin isa ki ce za ki raba mu da ɗan'uwanmu? Na rantse da Allah baki isa ba. Kinyi kaɗan, kuma" "kinyi tsururu. Duk take-takenki mun daɗe da gano abinda kike nufi, kar muke kallonki. Hafiz ne tunda kina son shi dole ki rungumi iyaye da ƴan'uwansa da suka kasance ƙauyawa. Gidannan kuma ko kina so ko ba kya so baza mu taɓa daina zuwa ba, idan kin isa kuma kin kai isasshiya, ki saka Hafiz ya kore mu...""" """Ai kuwa ko yanzu na nuna muku na isa har nayi yawa.""" Bintu ta katse ta da sauri kuma cikin raini da gatsali. Da hannu biyu ta riƙe ƙugunta tana karkaɗawa tana fari da idanu sannan ta cigaba da cewa. """Gidannan dai gidan mijina ne, ni da nake matar gidan ni nake da girman ikon sakawa da hanawa ko" "kuna so ko bakwa so. Na riga na zame muku ɗuwawu, dole ku zauna da ni, tunda ɗan'uwanku ya ce ya ji ya gani ni yake so matsayin abokiyar rayuwa dole duk yadda na dama haka za ku sha...""" A zafafe Aunty Rakiya ta katse ta da cewa """Wallahi ƙarya kike yi Bintu. Babu dole a zama da ke, bari in tunatar da ke abu ɗaya idan haukar" "ƙwaƙwalwarki yasa kin manta... Hafizu namiji yake, ana canza mata, amma ba'a taɓa canja ƴan'uwa. Sannan ana canja mata amma ba'a taɓa canja uwa da uba. In banda ke jaka ce mare hankali wulaƙancinki har ya iya tsallake kan dangin miji ya haura kan iyayenshi? Duk mugunta da ƙulla-ƙullar da" "kikai ta yi ma Innaye sadda tazo gidannan jinya babu wanda bamu sani ba...""" "Da saurin gaske Aunty Balira tayi saurin katse Rakiya, a ganinta yanzu ba muhallin yin wancan maganar" bane. Kuma baya ga haka tun a wancan lokacin sun yi ma Baffa alƙawarin baza su taɓa canja ma Bintu kan abinda ya faru da Innaye ba. """Dakata Rakiya dakata! Idan kika sake magana anan gurin ba tare da na gama faɗin abinda zan faɗa ba" "sai na tsinka miki mari.""" "Saboda tsananin biyayya da girmama na gaba da aka hore su da shi, Rakiyar bata ƙara cewa komai ba," "sai baya da ta matsa tana sauke zafafan numfarfashi, tana huci kamar kububuwa." Ita ma Ladidi da ba'a mata umarnin yin shiru ba kusa da Rakiya ta matsa ta tsaya tana d'an karkaɗa kafafunta. Ita ma nata fuskar babu walwala ko kad'an. """Bintu na dawo gare ki.""" Aunty Balira ta fada bayan ta mayar da hankalinta kan Bintu da take tsaye har lokacin tana wani karkad'a kafaɗu babu alamun nadama ko rusunawa ko kaɗan tattare da ita. """Faɗi duk abinda za ki faɗa dai-dai nake da ku dukkanku. Kunne ke ji, baki ne zai faɗa kuma baki ne zai" "bada amsa.""" Ta faɗi hakan cikin gatsali tana wani harare-hararen gefe. "Kasancewar hasken wuta ne tar ta ko wane ɓangare a cikin falon kamar rana, shi yasa duk abinda take yi" suna kallonta rayukansu na ƙara ɓaci. Nannauyar ajiyar zuciya Aunty Balira ta sauke ta cigaba da cewa """Ki kalle ni da kyau Bintu. Shekaruna a duniya arba'in da biyu. Ina da shekara goma sha uku Baffa yayi" "min aure. Da ace Allah ya bani haihuwa tun sa'adda nayi aure da yanzu na haifi kamar ki, ko wacce ta girme miki. Sannan baya ga darajar shekaru da ya kamata ace na ci a gurinki, duk mu ukun nan yayyen mijinki ne. A lalace ko Ladidi da take ƙarama a cikinmu shekara biyar ke tsakaninta da Hafizu." "Waɗancan gayyar ƙauyawan matan da kike cewa mun kwaso su mun cika miki gida, daga Gwaggwannin" "Hafizu sai Innoninsa, sai kuma Aminan Innaye da sa'annin haihuwar Hafizu da ƙannensa da suke uba ɗaya." Yanzu duk waɗannan dalilan saboda Allah ke a gurinki basu kai matsayin da za ki girmama mu ki karrama "mu don su ba...?""" """Don Allah tsaya Aunty Balira?""" Bintu ta katse ta cikin fushi. """Wai da kuke ta wannan fuffukar tun da kuka zo gidannan menene nayi muku na wulaƙanci? in dai ba" "rashin godiyar Allah da son maƙala min laifi ba? Gurin taron suna ne tun kafin ku zo an riga an ƙayyade iya yawan mutanen da ake so su halarci gurin, kawai saboda ni ce ƴar daɗi dangin miji sai in kwashe ku" "yuuuu zuwa gurin? bayan kuma ba'a tsara gudanar da taron da ku ba?""" Ta katse Aunty Balira da tambayoyin cikin hayayyaƙa tana yi tana ɗaga hannuwa sama kamar za ta mare ta. "A bazata, idanun Aunty Balira suka kawo ruwa, da sauri tayi ƙoƙarin haɗiyewa. Ɗaya bayan ɗaya ta kalli" "ƴan'uwan Bintu su huɗu da suke tsaye a gurin suna bayar da haƙuri lokaci bayan lokaci, sai ta tsayar da" "idanunta akan wacce take ganin alamun ta ɗan fi sauran shekaru, da sanyin murya ta ce" """Baiwar Allah don Allah ki mana alƙalanci. Ni duk ɓacin raina ba akan ƙin zuwa da mu gurin taron suna" "bane. Ita kanta Bintun ta sani, tabarmar kunya ce kawai take neman naɗewa da hauka yasa take waɗannan surutan. Yanzu saboda Allah ya kyautu ace tun abincin karin safe da aka bamu a gidannan ba'a sake waiwayarmu da ƙwaran abinci ba har yanzu da ƙarfe goman dare ta wuce? Manyan mata da kananun yara mu ashirin da bakwai muka zo gidannan, duk da direbobinmu uku mu talatin. Saboda Allah idan Bintu bata ba mu abinci a gidannan ba ina take so mu sa kanmu? Ko don ta ga ɗan'uwanmu ba ya" "nan shi ne take wulaƙanta mu?""" Ta ƙarasa tambayar wasu sabbin hawaye suna sake cicciko idanunta. """Bintu?""" Babbar yayar Bintu wacce Aunty Balira ta gama yi ma ƙorafi mai suna Sadiya ta kira sunan Bintu da yanayin mamaki a fuskarta. Domin ita sai yanzu da Balira tayi bayani a nutse sannan ta fahimci inda aka dosa da inda matsalar take. Kafin Bintu ta amsa ta sake cewa """Da gaske ne abinda wannan baiwar Allahn ta faɗa?""" "Nan ma dai Bintu ta kasa amsawa, sai zumɓura baki da tayi gaba tana ƙara ƙanƙance idanu." """Daman su ɗin shaƙiƙan mijinki ne amma kika ce mana gayyar soɗin karabitin ƴan'uwan Hafiz ne daga" "ƙauye? Kuma ca nake a gabana kika faɗa ma Hajiya Balaraba kin sallame su da duk abinda za su buƙata?""" "Nan ma dai shiru tayi, sai sunkuyar da kanta ƙasa da tayi tana mui-mui da baki alamun gunguni take yi a" zuci. Da matsanancin faɗa Aunty Sadiya ta fara zazzaga mata masifa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba. """Baki kyauta ba Bintu, gaskiya baki kyauta ba. Kin ɓata wayon ki, sannan kin bani mamaki. Ban taba" "tsammanin za'a sami irin wannan halin daga gare ki ba. Wannan mummunan banzan halin na wulaƙanta ɗan'Adam don kawai sun kasance ƴan ƙauye ban san inda kika kwaso shi ba. Kuma na rantse da Allah idan baki gyara ba sai na haɗa ki da Daddy, kin dai san halinshi sarai, ba ya ɗaukar irin wannan iskancin" "da wulaƙancin, ko da kike ganin kin yi aure kin haihu ke kin san baki fi ƙarfin hukuncin Daddy ba.""" "Ta mayar da idanunta kan Aunty Balira, sannan tayi ƙoƙarin sassauta murya da yanayin da ke nuna" nadama ƙarara ta cigaba da cewa """Baiwar Allah don girman Allah kuyi haƙuri. Ba'a kyauta muku ba tabbas! Amma don Allah kuyi haƙuri," "a matsayina na Yayar Bintu na ari bakinta na ci mata albasa, kuyi haƙuri don Allah ba don mummunan halin da ta nuna muku ba. Ke Bintu maza basu haƙuri kafin in saɓa miki!""" Ta ƙarasa da yi ma Bintu umarnin cikin tsawa. Ta cika tayi dam! Amma sanin halin Aunty Sadiyar na rashin ɗaukar raini yasa ta cewa """Allah ya baku haƙuri. Bazan sake ba.""" Bakinta a zumɓure kamar zai taɓa bango. Aunty Sadiya ta cigaba da cewa """Aunty yanzu dai ku koma can gurinku, yanzunnan za mu shiga kicin mu sama muku abinda za ku ci a" "daren nan in sha Allahu. Kuyi haƙuri don girman Allah, kuma ina fatan baza ku faɗa Hafiz abinda aka yi muku ba. Don Allah ku yafe mata, ba don halinta ba.""" "Ko da ace da kissa Aunty Sadiya ta ba Bintu laifi a gabansu, abinda tayin ya taka muhimmiyar rawa gurin" rage girman ɓacin ransu. Hatta su Aunty Rakiya da suke ta cika suna batsewa abinda Aunty Sadiyar tayi ya tsaya musu arai. Ga dai maganganun da suke burin sake gargasa ma Bintu da ƙarara ya nuna ta basu "haƙuri don babu yadda za tayi ne, amma kwarjinin Aunty Sadiya yasa dole suka haɗiye komai a ransu." Godiya kawai Aunty Balira tayi ma Aunty Sadiya ba tare da ta amsa roƙonta na su yafe ma Bintu sannan kar su faɗa ma Hafiz abinda ya faru ba. Ficewa tayi daga falon ƙannenta suka rufa mata baya. Suna hanyar komawa ɓangaren da aka sauke su babu abinda Aunty Balira take yi sai sharar hawaye. "Daman tun farko abinda ta guda kenan, sanin halin Bintu na wulakanci da daukarsu da take yi a banzan- banza yasa sam bata so zuwa sunan ba balle har wasu su ce za su biyo su." "Daman ta sani, in dai Bintu ne dole sai ta aikata mummunan abinda zai haska ma sauran dangi yadda ta" ɗauke su gaba ɗaya a marasa daraja. Yanzu zuwan na su me ya haifar kenan? Duk da sauran ƴan'uwan basu yi magana ba ta sani dole sun dasa ma zukatansu ayar tambaya. Abincin karin da aka kai musu da safe ragowar ne aka ba yara zuwa ƙarfe ɗaya da rabi na rana. Zuwa "ƙarfe biyu da rabi, uku manyan gaba ɗaya idanunsu ya fara raina fata. Da kunnenta taji yadda suke" ƙananan maganganu kan yunwa suke ji. Haka ta kwashi kulolin abincin safe da aka kai musu waɗanda ana gama cinye abincin ciki aka wanke ta fita can tsakar gidan tayi shiru cikin tunani da damuwa. Kwatsam sai Allah ya dawo da Mal Musa gidan bayan ya dawo daga kai mutane can gurin taron suna. Da mamaki yake tambayarta su baza su gurin taron sunan bane? """Ai ba ma wannan ba Mal Musa. Yanzu dai ina za ka samo mana abincin sayarwa kuma mai sauƙi da" "gaggawa? Kasan da yara a cikinmu, sun cinye abincin da aka bamu tas! Yanzu yunwa muke ji kuma matar gidan ba ta nan.""" "Da farko shiru yayi, zuciyarsa cike da tunani. Duk yadda Aunty Balira tayi ma zancen kwaskwarima nan" "take ya harbo jirgin abinda yake faruwa, domin ya san halin Bintu sarai, ko su ma'aikatan gidan ba wani" daɗinta suke ji ba. Da yawansu ma in ba don kirkin Oga Hafiz da girmama na gaba ba da tuni sun ajiye aikin. """Abinci bazaiyi wuyar samuwa ba Aunty Balira." "Sai dai kin san nan Abuja ne, komai yana tsada ba kaman can gurarenku ba. Na nawa ne za'a siyo muku" "abincin?""" Ɗan shiru tayi tana sake kallon girman babban kulan da take riƙe da shi. Sai kuma ta ce """Abincin dubu goma zai cika wannan kular ba?""" Duk yadda yaso hana kanshi dariya sai da ya ɗan ƙyaƙyata kafin ya amsa da """Ai abinci garau-garau na dubu talatin ma bana jin zai cika kular nan. Abuja ne nan fa Aunty, Sai dai" "kawai aje a siyo na yadda ya samu kuyi maneji.""" Kuɗin gudummuwar da suka tara ma Hafiz da bai karɓa jiya ba ya ce ta ajiye mishi zuwa safe gaba ɗaya ta miƙa ma Mal Musa. """Ga lambar wayata, don Allah idan ka siyo ka kawo min a sirrance. Ka kira ni nan zan fito in karɓa.""" "Wannan abinci da aka siyo musu, shi ya rufa musu asirin yunwar da Bintu ta barsu da shi da rana har" zuwa dare. Da daddaren ma gajiya sukai da kukan ƙananun yara ta kira Rakiya da Ladidi suka shiga can "cikin gidan gurin Bintu, shi ne fa har aka yi wannan ɓatacciyar." ***** ***** "Kamar yadda Aunty Sadiya ta alƙawarta musu, cikin ƙanƙanin lokaci aka wadata su da lafiyayyar" "dafadukar macakaroni da taji kifin gwangwani. Bayan ruwan gora da aka kai musu har katan huɗu, katan shida aka kai musu na kalolin lemuka mabanbanta." "Duk yadda ƙamshin abincin ya gama baɗe falon da suke ciki daga buɗe kular, ko kusa su Aunty Balira" basu matsa gurin ba balle har su nuna sha'awar son ci kamar yadda sauran suke nunawa a fili. "Gwaggo Asabe, uwargidan Baba Abubakar ita ta jagoranci rabon abincin da ya ishi kowa a wadace, har" "suka bar saura a kula. Hatta waɗanda suka fara barci duk an tashe su sun wanko baki sun fara cin abinci," duk da a lokacin ƙarfe goma sha ɗaya na dare ta gota da ƴan mintuna. Gwaggo Asabe ita ta ɗauki na su Aunty Balira ta kai musu har inda suke zazzaune sun buga tagumi. Ajiye "musu tayi, sannan ta koma ta ɗauko nata abincin ta zauna a gefensu." """Rayuwar duniya haƙuri ake yi ƴaƴan nan, ko baku faɗa ba, da yawanmu a cikin nan mun san abinda" "yake damunku kuma yake ci muku tuwo a ƙwarya. To amma ya za kuyi? Su fa wasu ƴan binnin haka suke, sai dai mu cigaba da haƙuri da mayar da komai ba komai ba a matsayinmu na waɗanda Allah ya ƙaddara ma rayuwa a ƙauye. Don Allah ku ci abinci, idan kun yi haƙuri, duk gobe za mu koma inda muka fi wayau. Sannan ina mai baku shawara, kar ku kuskura ku bari matar ɗan'uwanku ta shiga tsakanin kyakkyawan" "zumuncinku, tunda dai shi ba haka yake muku ba.""" Cokali ta ciko taf da Macaroni da tunda ta fara magana ƙamshinshi yake baɗaɗe mata hanci ta cusa a baki. """Kuma...""" "Ta cigaba da magana tana shishita da baki saboda zafi da daɗin macaroni da ya haɗe mata guri ɗaya," amma tsabar yadda maganar ke cin ranta ta kasa haƙuri ta gama haɗiye abincin da ke bakinta. """Imu-imu... manya da muka zo sunan nan... munyi shawara a tsakaninmu ko mun koma gida baza mu" "taɓa bada labarin abinda matar Hafizu tayi mana ba. Domin Hafizu shi ne namu, daga gare shi kuwa bamu fuskanci wulaƙanci ko kaɗan ba. Kun ga don abinda matarsa tayi mana ai sai muyi mishi uzuri. Abinda ya rage muku dai ku kwaɓi bakunan ƙannenku, don idan mu manya munyi shiru ba lallai su suyi" "shiru da bakunansu ba. Musamman ma da ya kasance gaba ɗayanku ba ƴan ɗaki ɗaya bane.""" "Daga haka bata sake cewa komai ba ta mayar da hankali kan abincinta ta cigaba da saka loma, a" "hanzarce, kamar mai tsoron wata a cikinsu za ta cinye nata ta ce ta ƙara mata." "[1/7, 10:17 PM] Fareeda Abdallah: Wannan zazzafan abinci kuma daddaɗa, da duk loma ɗaya sai an" "haɗa da kifin gwangwani da aka dafo musu a ƙarshen dare, ga Lemu da ruwan gora a wadace, shi ya" "goge duk yinin da suka yi suna ɗame-ɗame da yunwa. Kamar dai ba su bane a ɗazu duk basa cikin walwala da karsashi, lokaci ɗaya hira ta game falon, sai shewa suke suna dararraku a tsakaninsu." Su Aunty Balira kuwa duk da maganganun da Gwaggwo Asabe tayi musu tsattsakuran abincin kawai suka "yi, duk dadinsa da d'andanon da yake fitarwa kamar mad'aci haka suke jin sa a bakunansu, ba don komai ba kuwa sai don yadda zukatansu babu dad'i. Ko da suka gama ba tare da sun tankawa kowa ba suka bar" gurin zuwa makwancinsu. "Sai da tasa haƙarƙarinta akan katifa, ta ciro wayarta a cikin ƴar pose, sannan taga kiran da aka rasa na" "Hafizu har guda biyar. Ta rasa dalilin da yasa haka kawai ta ji baza ta iya magana da shi a daren ba, a" taƙaice ma tausayinsa ne ya cika mata zuciya. Wannan fa shi ne misalin karin maganar nan ta bahaushe da yake cewa """Ga doki har doki amma ƙafar na sakaina.""" "Hafizu yaron arziki, ɗan albarka mai son zumunci da ƙaunar iyaye da ƴan'uwansa. Amma sam baiyi sa'ar" "matar aure ba. Mace ta gari kuwa ga duk namijin da ya same ta an bashi rabin addininsa ne in ji fiyayyen Halitta SAW, sai ya ji tsoron Allah a sauran rabin." 'Ko yaushe rayuwar iyalin Hafizu za ta saisaitu?' Ta tambayi kanta da kanta. Domin Bintu dai in dai ba wani iko na Allah ba bata ga alamar canji a gurinta "ba, yadda ta san halayenta tana amarya, a yanzu ma babu wani canji sai ma abinda ya karu." "Ga kuma masifaffen so da suka san Hafizu yana yi mata, balle su saka ran kila acan gaba ya dauki" "kwakkwaran matakin gyara, ko kuma yayi hobbasa ya kara aure ko zai dace da wacce za ta kaunace shi don Allah kuma ta kaunaci 'yanuwansa a yadda suke." """Uhmmm! Allah kai ka san karatun kurma.""" Ta fada a fili da murya kasa-kasa. Sai kuma tunanin Innaye ya fado mata arai. 'Baiwar Allah' Ta fada a zuciya. Ita ta san ko Innaye bata fada ba sanin mugayen halayen Bintu ne yasa tunda suka iso akai-akai take kiranta don jin ba wata damuwa ko? Ita dai bata ce mata komai ba don gudun kar ta daga mata hankali. Nannauyar ajiyar zuciya taja ta sauke. Ta danna maɓallin kashe wayar ta kashe gaba ɗaya don ma kar ya "sake kiranta, gobe idan ya dawo sa hadu. Sannan a yadda ta yanke shawara, ita dai da bakinta baza ta yi ma kannenta da suke uba daya magana a kan kar su bada labarin abinda matar Hafizu tayi musu ba." "Shi da ya gayyaci azo mishi suna, har yana daukar shatar motoci, bayan ya san halin matarsa sarai ba" kaunar 'yanuwanshi take yi ba. Shi ya kira ma kansa tonon asiri a cikin dangi. Lumshe idanunta tayi ta fara karanto addu'ar kwanciya barci. 'Yan'uwanta ma da suke kwance kowa da "irin tunanin da take yi a zuciyarta, daga karshe ko sai da safe basu iya yima juna kamar yadda suka saba ba. Barci ya dauke su a mabanbantan lokuta." ****** Washe gari duk yadda yaso su dawo Abuja da safe basu samu isowa ba sai misalin sha biyu ds kwata na "rana. Daga filin jirgi kuma kai tsaye Ma'aikatarsu aka wuce da su, hankalinsa duk ba'a kwance ba, saboda har lokacin bai samu yayi magana da Aunty Balira ba." Sauran yan'uwansa kuma da yake ta kira akai-akai yana tambayar lafiyarsu duk sun tabbatar mishi lafiya "kalau suke. Ko da ya bukaci a bashi Aunty Balira a waya ya kasa samunta sai suke ta bashi uzurirrika mabanbanta, wadanda sam basu kwanta mishi arai ba. Ya rasa dalilin da yasa, haka kawai zuciyarsa ta ki" nutsuwa guri daya. "A bangaren Bintu ma suna ta waya cikin kulawa da kaunar juna kamar yadda suka saba, ko da ya" tambayeta lafiyar yan'uwan nashi da yadda suka kwana sake tabbatar mishi tayi suna cikin koshin lafiya. """Na je da Baby Aadil mun gaisa da su da safe. Ya dade ma a goye bayan Aunty Balira.""" "Ta yanko karya ta gilla mishi duk don ta sake kankaro ma kanta girma a gurinshi, sannan ta cigaba da" cewa """Kuma tun da sassafe Aunty Sadiya ta jagoranci aikin wadataccen abin karyawa aka kai musu. Yanzu" "haka kiris ya rage a gama abincin rana da soya naman suna a mika musu, tunda sun ce baza su sake" kwana ba yau za su koma gida. Dazu da Raudha za ta shigo ma take ce min ta ga direbobin da suka kawo "su sun iso.""" Da matukar murna da jin dad'i a muryarsa yake mata godiya da saka albarka. """Shi yasa a kullum nake kara son ki Bintuna, Allah ya barmu tare. Sai na dawo. A shafa min kan" "Babana.""" Da haka suka yi sallama bayan ta mayar mishi da martanin zakakan kalaman soyayya. Dakyar ya yakice ayyukan komai ya isa gidan misalin karfe biyu saura kwata na rana. Kuma kamar yadda "Bintu ta sanar da shi, ya tarar da abinci waja-waja a gurin yan'uwansa, alamun suna cikin alkhairi dumu- damu. Sun ci, sun koshi, sunyi hani'an, ga kasusuwan naman kaji nan a cikin farantan abincin da suka gama ci, babbar alamar da ke nuna ba'a basu abinci lami ba." "Ya tarar duk sun gama shiryawa, jakunkunan kayansu da wadanda suka kullo a leda duk suna ajiye a falo." Da alamun dai shi kadai suke jiran dawowarsa. Musayar murmushi ne ya gudana tsakaninsa da Aunty Balira bayan 'yan'uwan sub gama jerangiya wajen yi mishi sannu da zuwa. Shi kuma ya bi Innoni da Gwaggwagganninsu daya bayan daya ya gaishe su. "Ficewa yayi, Aunty Balira ta rufa mishi baya suka kebe can gefe guda." """Ya hanya? Fatan an dace da abinda aka je nema?""" """Alhamdulillahi Aunty. Me ya samu wayarki? Ina ta kira ba ta shiga, kuma na kira su Aunty Ladidi su" "had'a mu a waya suna ta bani wasu kalar amso shi...""" """Wayata batir ke da matsala.""" Ta katse shi tun kafin ya gama korafin. """Sai mun koma gida in Allah ya yarda zanyi kokari in canja batirin.""" """A'a ba sai kun koma gida ba. Idan na shiga ciki akwai wata karamar waya Torching screen zan dauko" "miki sai ki saka layinki ki ci gaba da amfani da ita.""" """Menene Tochan scrub?""" Ta tambaye shi da yanayin kauyanci. Kafin ya amsa sai ta sake cewa """Ohoo! ko kana nufin waya 'yar sha-fa? Idan ban manta ba kamar ita naji Zulai na cewa tochan scrub.""" Sai kuma tayi dariya ta cigaba da cewa """Ina ni ina waya 'yar sha-fa Hafizu? Barni dai da mai maballai na. Na fi gane amfani da ita a saukake." "Waya 'yar sha-fa a k'auye hannun mata sai irin su Zulai da suka yi boko, idan kuma za ka bani in tafi mata da shi to?""" """Ko ke ma za ki iya amfani da ita Aunty Balira. Kun ki karbar canjin da zamani yazo da shi shi yasa har" "yanzu kuke a guri daya. Ni ke nayi niyyar ba wayar ba Zulai ba. A sannu za ki saba amfani da ita.""" """To shi kenan. Na gode Allah ya kara arziki.""" Da murmushi a fuskarsa ya amsa addu'ar da tayi mishi cikin jin dad'i. Har yayi mata sallama kan cewa zai shiga cikin gidan sai ya fito ya sallame su ta ce to. Ya fara tafiya sai ta kira sunanshi """Hafizu?""" """Na'am Aunty. In zo ne?""" "Ya fada a ladabce. Girmanta yake gani ba kadan ba, domin idan babu Innaye a guri tudu biyu Balira ke ci" "a gurinsa, Uwa kuma babbar Yaya." """Kayi hakuri. Kudin gudummuwar da muka kawo maka na ara, idan mun koma gida zan sayar da" "tunkiya sai in ba Innaye ta ajiye maka kudin...""" """Na bar miki halak-malak Aunty.""" Ya katse ta da murmushi a fuskarsa. "Martanin murmushinsa ta mayar masa tayi godiya, tana tsaye a gurin tana kallonsa har ya bace ma" ganinta. Nannauyar ajiyar zuciya taja ta sauke kafin ta koma cikin dakunan da aka yi musu masauki. ****** """Wai me yasa a hotunan taron suna da kika tura min jiya ko daya ban ga hoton su Aunty Balira ba?""" "Kasancewar tambayar tazo mata a bazata ne, kiris ya rage ta fad'ar da Aadil da yake rike a hannunta" "tana kokarin saka mishi nono a baki. Da saurin gaske ta rik'o shi, idanunta a kasa ta ce a daburce." """Iye! Na'am! Me ka ce Sweetheart?""" "Da yake hankalinshi na kan turaren da yake fesawa a jikinsa, sam bai ga yanayin rud'anin da ta shiga ba." A nutse ya sake maimaita mata tambayar da yayi mata. """Uhmmm!""" "Ta fara jan ajiyar zuciya ta sauke, a zuciyarta take ƙara tsara abinda za ta fada mishi ya gamsu." """Ka san halin su Aunty Balira fa, wai ganin a cikinsu da dattijai da ƙananun yara yasa ta ce kawai ba sai" "sun je can ba, za suyi taronsu a gida. Da wannan dalilin yasa aka bar musu komai a wadace muka tafi. Ga kyaututtukansu can ma a ɗaki na, ɗazunnan su Aunty Sadiya suka gama packaging.""" """Ok!""" Ya amsa a takaice. "Suna hira yana bata labarin yadda tafiyarshi ta kasance har ta gama ba Aadil nono, suka jera suna hira" "kasa-kasa har suka fice daga d'akin. Tana biye da shi har gurinsu Aunty Balira, duk da yadda kirjinta ke bugawa haka ta daure ta fuske, ko kadan bata nuna wani alamun firgicin gamuwa da su ko tsoron kar su" bi ta da wani mummunan kallo ba. "Cikin hukuncin Allah kuma sai suka bi ta a yadda ta zo musu, kadaran-kadahan suka amsa gaisuwar da" take ta bin su da shi a ladabce. Kannenta ne suka yi sallama a kofar falon suka fara shigowa hannayensu rike da jakunkunan da aka zuzzuba ma su Aunty Balira kyaututtukan suna.. "Kyaututtuka ne aka hada musu na girma, domin cikin ko wane jaka akwai turmin zani mai kyau ba roba" "ba, turaren wata a cikin kwalba madaidaiciya, Sunkin sabulun wanka, sai katon kalandar hoton jariri Aadil. Haka ta bi su daya bayan daya ta mika ma kowa a ladabce. Bayan ta ba su Aunty Balira nasu haka sake basu jakunkuna biyar a kaima Innaye, Biyar a kaima Baffa, ta bayar da uku-uku a kai ma kishiyoyin Innaye. Abu dai tubarakallah, kamar ba Bintun nan da take gwada musu wulakanci akan abinci ba, kamar" kuma ba ita ce jiya ta rufe idanu ta ci musu mutunci ba. "Su Aunty Balira bin ta kawai suke da idanu, zukatansu cike da matsanancin mamakinta, wato yanzu da" "yake a gaban d'anuwansu ne, dubi yadda take yi kamar za ta kwanta musu." "'Makira, in Allah ya yarda alkadarinki ya kusa karyewa.'" Aunty Rakiya tayi addu'ar a zuciyarta tana harararta kasa-kasa. "Kyaututtukan basu tsaya anan ba, Aunty Sadiya da kanta ta shiga falon ta bi su da kullin naman suna da" "yaji, kowa kullinsa daban. Sannan ta bayar da na Innaye da Baffa, da kishiyoyin Innaye." "Hafiz yana tsaye a gefe yana kallon duk abinda ke faruwa, da yake bai san dawan garin ba. Har ga Allah" zuciyarsa cike take taf da farin ciki ganin yadda aka karrama yan'uwansa. Musamman idan ya kalli yadda dattijan cikinsu ke ta zuba murmushi suna kalaman godiya da saka "albarka. Su kuma yaran matan suna ta dararraku suna kara yi ma Bintu addu'ar Allah ya raya Aadil ya kara daukaka, ya kuma kare ta daga sharrin makiya da mahassada." "'Yanuwansa uku ne kawai basu yi magana ba, amma labarin da fuskarsu ke bayyanawa karara shi ne" suna cikin farin ciki da wannan karamci da aka yi musu. 'Lallai Bintu ta fidda ni kunya. Alhamdulillah' Kalaman da yake ta maimaitawa kenan a zuciyarsa dad'i yana k'ara lullube shi. "Bayan duk wadannan kyaututtukan, haka ya sake bin duk yawansu da naira dubu biyar-biyar. Ya sake ba" "su Baban Yasi wadataccen kudin da za su sake cika tankunansu taf har da raran canji, sannan suka kama hanyar tafiya. Kusan kowa aka kalla a cikinsu baki har kunne, saboda matsanancin jin dadin alkhairan da" suka samo a gidan Hafizu. "A lokacin karfe uku da rabi na yamma, amma da yake komai dare suna saka ran gida za su kwana in Allah" "ya yarda. Shi yasa basa fargaban dare da zai iya musu a hanya, fatansu dai Allah ya tsare ya mayar da su gida lafiya." ******* "[1/8, 11:02 PM] Fareeda Abdallah: ""Yauwa! Gara da Allah ya shigo da ke yanzu. Na riga na gama yanke" "shawara gobe idan Allah ya kaimu, bayan sallar azahar za a daura auren Zulaikha da duk wanda Allah ya kaddari shi ne mijinta in sha Allahu.""" Tsananin yadda maganar ya duke ta yasa bata san sa'adda ta saki kwanon shan ruwan da ke rike a "hannunta ba. Wani jiri ne ya debe ta nan take tayi taga-taga za ta fad'i, da saurin gaske tayi gaggawar dukewa zuwa kasa ta dafe kujerar da ke kusa da bakin kofa." """Subhanallahi! Rahina? Lafiya kuwa? Ba ki da lafiya ne?""" "Baffa ya jero mata tambayoyin da sauri hankalinsa a tashe. A gaggauce ya mike tsaye, ya tsallake huhun" goro da dabino da suke ajiye a gabansa ya karasa kusa da ita yana jera mata sannu. Shi ya kama ta ta mike ta zauna da kyau akan kujerar da ke kusa da ita. Sai sannu yake jera mata ganin "yadda take ta hada zufa kamar mare lafiya, ta kasa magana, sai numfarfashi take yi tana kure shi da wani irin kallo da ya rasa gane inda ta dosa." """Sannu! Daman ba ki da lafiya ne?""" Ya sake tambayarta. "Dakyar ta iya girgiza mishi kai, alamar a'a lafiyarta kalau. Sau uku tana yunkurin yin magana kafin dakyar" ta iya kwato kalmomin """Wa za ka aura mata Malam?""" """Ko wani bawa dai ba ya wuce kaddararsa Rahina. Sa'annan matar mutum kabarinsa. Don Allah ki" "kwantar da hankalinki, wani ba ya taba auren matar wani. Kuma kin san da son zuciya dai bazan taba yima 'yarki auren da bai kamata ba. Ki kwantar da hankalinki don Allah.""" "Ya fad'i maganganun a tausashe, idanunsa na kanta yana ƙara karantar yanayinta." "Ta daɗe cikin shiru, babu abinda take ja a zuciyarta sai" "'Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Allahumma ajirnee fi musibati, wa aklifnee khairan minha.'" "Baffa dai yana ta aikin kallonta, bai ƙara matsa mata da maganganu ba. Har sai da ita kanta ta samu" "nutsuwa hankalinta ya dawo jikinta, sannan ta tambaye shi" """Me tayi Malam?""" Kafin ya amsa ta cigaba da cewa """Duk da ban san laifin me tayi maka ba don Allah kayi hakuri. Na san a baya ka ce ranar aurenta da aka" "sanya da Mudan bazai canja daga yadda ka saka shi ba, amma har yanzu ai da sauran kwanaki goma sha" "biyu. Me tayi? Ko kuma me ya canja wancan ƙudirin naka?"" Allah ya sani, ba na so a aurar min da Auta haka kwatsam ba tare da wata ƙwaƙƙwaran sanarwa ba.""" Ta jero maganganun da bayyanannen tashin hankali a fuskarta. """Idan ka duba har yanzu Zulaikha ba ta cikin walwala. Fasa aurenta da Mudan ya ƙara jefa rayuwarta" "cikin zulumi ne da fargaba. Maganar da ta ji ana yi kuma na ranar auren bai canja ba za'a ɗaura da ko waye ya ƙara jefa ta cikin tunani da tsoron wane irin miji za'a aura mata. Ba ta walwala. Ba ta dariya. Magana idan ba ya zama dole ba sai mu kwana mu yini bata yi min ba. Dai-dai da abinci da ya zama dole sai na zauna kusa da ita na matsa mata sannan take ɗan tsakura ta tashi. Kai baka ga yadda duk ta rame ta lalace ba? Allah ya sani ni da za ka ji ta tawa ma, ko nan da kwanaki sha biyun don Allah ka daga mata ƙafa. Kai ne fa ke ƙara tunasar da ni aure lokaci ne Malam. Ina ji a jikina mijin Auta na musamman ne in Allah ya yarda. Ko ba jima ko ba daɗe yana nan tafe, lokacin bayyanarsa a duniyarta ne kawai baiyi ba. In Allah ya yarda mijin da za ta aura zai kasance abin alfahari ne a gare ta da gare mu iyaye da ƴan'uwanta" "da sauran jama'ar ƙauyen nan baki ɗaya...""" """Kiyi haƙuri Rahina. Na riga na gama yanke shawara, tabbas in Allah ya yarda gobe iwar haka Zulai tana" "ɗakin mijinta. Kiyi haƙuri, ki kuma yi fatan Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi, ya kuma sa shi wanda za" "ta aura abokin arzikinta ne.""" "Shiru tayi, tana kallonshi yana kallonta. Banda bugawa fafafat! Babu abinda ƙirjinta yake yi, ta san halin" "Malam sarai. Tunda ya ce za'ayi tabbas za'ayi ne, babu abinda zai hana auren nan sai dai wani ikon Allah." A raunane ta sake tambayarsa. """Wa za ka aura mata?""" """Mijinta""" Ya amsa kai tsaye. """Na sani mijinta za ta aura Malam. Sunan shi da ahalinsa za ka faɗa min don Allah...""" """Wai duk wannan tambaye-tambayen na menene Rahina? Ke kin san dai idan ban fi ki son Zulai a cikin" "ƴaƴa ba sai dai muzo kan-kan-kan! Na ce miki ki kwantar da hankalinki. Banyi gaggawa a al'amarin Zulai ba, sati guda na kwashe ina Istikhara akan auren nan kuma babu abinda nake gani sai alkhairi. Ki nutsu," "ki kwantar da hankalinki don Allah.""" "Ajiyar zuciya mai nauyi taja ta sauke, duk da yadda yake mata magana a tausashe don ta samu nutsuwa," "Allah ya sani hankalinta ƙara tashi yake yi. Haka kawai ta ji ɗakin yana mata wani irin zafi, numfashinta" "ya fara fita a wahalce. Tsam ta yunƙura ta miƙe tsaye, duk da ranar ita ce da girki, ita ya kamata ta kwana" "a turaka, ta rasa dalilin da yasa bakinta ya furta ma Malam ɗin" """Allah ya bamu alkhairi. Sai da safe.""" Da idanu kawai ya raka ta har ta fice daga ɗakin bai amsa mata ba. """Uhmmm! Mata kenan""" "Ya faɗa a fili, sai kuma ya saki murmushi." "Kawar da tunanin komai daga zuciyarsa yayi ya koma inda ya zube dabino da goro da sweet, ya cigaba da" cakuɗawa yana zubawa a leda. ***** "Aka ce rana ba ta ƙarya, sai dai uwar ɗiya ta ji kunya. Washe gari, Kamar yadda Baffa ya faɗa ma Innaye," mintuna goma sha biyar da idar da sallar azahar sai ga ƴan samarin gidan da yara ƙananu sun shigo da sauri suna kwarmaton an ɗaura auren Zulai yanzunnan bayan an idar da sallar azahar. "Ɗaura auren da tunda ƙarfe goma na safe zuwa sha ɗaya tayi, Innaye ta fara tunanin ko dai Baffa da" "wasa yake mata? Duba da yadda cikin abokan zamanta biyu babu wacce tayi mata maganar auren," sannan cikin ƴaƴan Baffa mata takwas na ta da na kishiyoyinta da suke gidajen aure babu wacce ta je gidan da cewar ta je yinin biki. "Tsakanin Zulaikha da take cikin uwarɗaki ta idar da sallah, da Innaye da take zaune akan dadduma tana" "lazumi, na rasa wacce ta riga wata isa bakin ƙofar fita." Kawai ganinsu aka yi duk su biyun tsaye a bakin ƙofa sun riƙen labule. """Labaran? Me kuka ce?""" Innaye ta tambayi babba daga cikin yaran bakinta na rawa-rawa. """Wallahi da gaske Innaye. Yanzunnan aka ɗaura auren Zulai da Yaya Hafizu...""" "Wani wawan ƙaƙƙarfan mahaukacin ihu da Zulaikha ta yanka a firgice, sannan ta tafi da baya tai wani" mugun kifawa a ƙasa shi ne abinda ya katse maganar da Labaran yake yi. """Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Na shiga uku na lalace... Auta...! Ke Auta... !! Me ya same ki? Zul...""" Luuuuu itama Innaye ta tafi za ta kifa a ƙasa saboda tsananin firgici da tashin hankalin halin da Zulaikha "ta shiga, da saurin gaske Labaran da ya isa gurin tun faɗuwar Zulaikha ya riƙo Innaye ta kifa a jikinsa." "Cikin ƙasa da mintuna biyu, har labari ya kai kunnensu Baffa da ke zaune a masallacin ƙofar gida ana ta" rabon Sweet da addu'ar Allah ya bada zaman lafiya cewa ga Innaye can da Zulai sun suma. "Duk cincirindon mutanen da suke gurin fuskokinsu cike da alhini saboda jin abinda yake faruwa, Baffa ne" "ya fara shiga cikin gidan don kiyaye hakkin addini. Sai da ya shiga, can bayan wasu mintuna kuma sai ya" aika yara aka shiga da shaƙiƙan ƴan'uwansa da ƴan'uwan Innaye maza. A lokacin tuni Innaye ta farfaɗo sanadiyyar ruwa da kishiyoyinta sukai ta sheƙa mata. Tana zaune a gefe "sanye da zumbulelen hijabi tana sharɓan kuka. Ita kuwa Zulaikha har lokacin bata farfaɗo ba duk uban ruwan da aka watsa mata, sai dai an ɗauke ta daga bakin ƙofa an shimfiɗar da ita akan doguwar kujera." Shigar ƴan'uwan Baffa da na Innaye cikin gidan yasa abokan zaman Innaye da yaran gidan suka yi saurin ficewa daga cikin ɗakin. Ya zama saura Baffa ne zaune kusa da inda aka kwantar da Zulaikha yana tofa mata addu'o'i. Shigowarsu Baba Abubakar yasa Baffa ƙara gyara mata rufar hijabin da ke jikinta. "Har suka zaz-zauna, Innaye ta kasa ɗaga idanu ta kalli ko mutum ɗaya daga cikinsu, balle kuma har" gaisuwa ya shiga tsakaninsu. Kukan da take yi ƙasa-ƙasa kuma bata daina ba. """Haba Rahina? Saboda Allah menene haka kike yi kamar ƙaramar yarinya? Ni na zaci za ki fi kowa" "murna da wannan al'amarin saboda tuwon ki ne kuma man ki? Duk wannan kukan da kike yi har da su suma duk na menene?""" "Yayan Innaye Mal Kabiru yayi maganar cikin faɗa-faɗa, saboda shi mutum ne mai zafin rai." "Innaye dai ba baka sai kunne, ta kasa ko ɗaga kai ta kalle shi balle yasa ran za ta amsa mishi." """Assha! Assha! Yaya Rahina don girman Allah kiyi haƙuri. Wannan al'amarin fa duk ba wani abin" "damuwa bane kamar yadda kika ɗauke shi, tunda dai ke da kanki kin san ba haramun muka aikata ba. To menene abin tashin hankalin?""" Baba Abubakar ya faɗa a tausashe. "Shi ma dai bai samu amsa ba. Nan take kuma kowa a cikinsu ya fara tofa albarkacin bakinsa, suna sake" tunatar da Innaye babu fa haramci a cikin auren Hafiz da Zulaikha tunda dai ba iyayensu ɗaya ba. 'Hafiz shi ne ɗan da Innaye ta haifa a cikinta. Zulaikha ƴa ce ɗaya tilo ga ƙanwar Innaye da kuma ƙanin Baffa mai suna Hamisu da suka kasance uwa ɗaya uba ɗaya. Sun rasu ne sanadiyyar mummunar hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyar komawa Faƙo daga Kaduna. "Hatsarin da aka rasa rayuka da dama, Zulaikha tana cikin ɗaiɗaikun rayukan da suka tsira a wancan lokacin shekaranta ɗaya da wata biyu a duniya." "Tun daga sannan, riƙon Zulaikha ya koma hannun Innaye da Baffa. Yarinyar da ƙauna da shaƙuwar da ke" tsakanin iyayenta da su Innaye yasa suke mata wani irin so na musamman kamar ma fiye da ƴaƴan da suka haifa a cikinsu. "Duk da bata isa yaye ba a lokacin, yaye ta aka yi tunda tana tafiya. Kuma inda Allah ya sauƙaƙa lamarin" "shi ne tana cin abinci sosai. Sannan tun iyayenta na raye tana yawan yini a gurin Innaye, ta saba da su gaba ɗaya." "Ƴaƴan da Innaye ta haiha huɗu ne a duniya, Balira ita ce Babba, kuma duk cikin ƴaƴan Baffa ma ita aka" "fara haifa. Sannan Rakiya, sai Ladidi, Abdul Hafiz wanda daga bisani aka yanke sunan ya koma Hafizu shi ne Auta, kuma shi ne ɗa Namiji na farko da aka fara haifa a gidan Baffa." A lokacin da riƙon Zulaikha ya koma hannun Innaye Hafiz yana da shekaru goma sha ɗaya a duniya. "Amma kamar ɗan shekara biyu zuwa uku, haka iyayen suke lelensa suna shagwaɓa shi saboda tsananin" ƙaunar da suke masa. "Zuwan Zulaikha gidan shi ya hamɓare gwamnatinshi daga gurin Innaye da Baffa. Kulawa, tattali," "shagwaɓa, lelen da ake masa duk suka koma kan Zulaikha. Hankalinsa bai ƙara tashi ba sai da wata rana Innaye ta rufe ido tayi mishi matsiyacin duka saboda kawai ya mari Zulaikha. Bayan dawowar Baffa kuma Innaye ta faɗa masa abinda Hafiz ɗin yayi, cikin ɓacin rai ya rama ma Zulaikha marin sannan ya rufe shi" da faɗa kamar zai dake shi. Wannan shi ne mafarin ƙulluwar ƴar tsama tsakaninshi da Zulai. Wacce ita kuma tun da ta fara wayau ta "lura ba ya ƙaunarta ta masifar raina shi, a lokacin ita bata san ma ba Innaye bace ta haife ta." "[1/10, 10:29 PM] Fareeda Abdallah: Wata rana, a lokacin Zulaikha bata fi shekaru shida ba a duniya, cikin" suɓul da baka Hafiz ya goranta ma Zulaikha Baffa da Innaye ba iyayenta bane. """Duk son da suke gwada miki da iskancin da kike yi suna goya miki baya na banza ne. Watan-wata rana" "za ki gane kuranki yarinya, tunda dai iyayenki ba sa raye.""" "Karaf! Maganganunnan a kunnen Baffa, ran Baffa ta yi mummunar ɓacin da bai taɓa yi ba. Bayan mugun" "dukan da ya lakaɗa ma Hafizu kamar ba shi ya haifeshi ba, sai da ya tara iyalanshi kaf! Yara da manya ya kafa musu dokar cewa duk wanda ya sake goranta ma Zulai ba su ne iyayenta ba bai yafe mishi ba." Wannan shi ne mafarin da yasa zancen ba Innaye da Baffa bane iyayen Zulaikha ya ɓace ɓat a gidan. Ta "cigaba da zuba sangarta da shagwaɓarta yadda take so, Innaye tana kiranta Auta. Kuma saboda" ƙaƙƙarfan dangantaka da ke tsakanin su Innaye da Iyayen Zulaikha babu wanda zai ganta ya ce ba Innaye bace ta haife ta. "Hafizu kuma wannan laifin da yayi shi ne dalilin da yasa Baffa ya ɗauke shi can-cak daga ƙauyen Faƙo, ya" "kai shi wani ƙauye mai suna Kasuwar magani gurin wani abokinshi, da niyyar yayi karatun Allo. Ashe" rabon yayi zurfi a karatun boko ne. Kasancewar ƙauyen Kasuwar magani ta fi ƙauyen Faƙo wayewa nesa ba kusa ba. Akwai makarantun "boko har zuwa sakandire, saɓanin Faƙo da makarantar boko iya firamare ne, a hakan ma ba ko wasu iyaye ke saka ƴaƴansu ba. A kasuwar magani kuwa ga makarantun islamiya da makarantun hadda masu kyau babu laifi. Ko da Mal Bello ya tambayi Hafizu yana sha'awar karatun boko ya ce eh! Har ma ya ƙara da faɗa mishi ya gama firamare acan Faƙo, Sai kawai ya saka shi a Sakandire da makarantar Islamiya da" "hadda, ba tare da sanin Mal Aminu ba. Wannan shi ne mafarin samun ingantaccen karatun Hafizu." "Kasancewarsa yaro mai tsananin ƙoƙari ako wane fanni, ga nacin karatu, yana aji biyu na ƙaramar" sakandire malamai suka saka shi za na ƙaramar jarabawa ta zuwa babbar sakandire. Yana aji biyar na babbar sakandire Principal ya saka sunanshi cikin ɗalibai masu zana jarabawar WAEC da NECO saboda ƙoƙarinsa. "A wancan lokacin, karatu a ƙauyuka kusan kyauta ake yi, saboda iyaye basu gama yarda da bokon ba" balle har su saki jiki suyi tururuwar kai ƴaƴansu. "Bayan sakamako ya fita ne sunanshi ya fito cikin waɗanda suke da maki mai yawa, anan ma dai principal" ɗin shi yayi cuku-cuku ya jefa sunan Hafizu cikin ɗaliban da gwamnati ta ɗauki nauyin karatunsu zuwa jami'ar Ahmadu Bello da ke zariya. "Acan ne kuma Allah ya haɗa shi da Ibrahim ɗan gidan Alh Lurwanu, taraiya ce irinta ɗan gidan talaka" futuk mai bala'in ƙoƙari da ɗan gidan mai kuɗi mare ƙoƙari amma akwai nacin karatu. Aka samu arashi "kuma shi Ibrahim ba shi da girman kai ko kaɗan, a taƙaice ma shi ne ya maƙale ma Hafiz ɗin saboda ilimin da yake kwasa daga gare shi." "A can ƙauyen Faƙo kuwa, tafiya ta tafi, an samu cigaba kaɗan amma ba sosai ba. Sanin kowa ne ire-iren" waɗannan ƙananun ƙauyuka da suke cikin lunguna sosai ba kasafai cigaban gwamnati ya cika samunsu "ba, sai ɗan abinda Allah ya tsaga da rabonsu kawai." "Sun samu cigaba ta fannin makaranta, an gina musu sakandire, amma fa irinta je ka na yi ka. Domin ko" malaman da aka zuba musu ma ba kasafai suke zuwa aikinsu ba saboda nisan ƙauyen. An kai musu Network ɗin Glo a ƙauyen. Sannan an gina musu ƙaton asibiti amma fa babu wasu likitoci da ma'aikatan jinya sai ɗai-ɗai. "Zulaikha Aminu Faƙo, tana ɗaya daga cikin yaran da suka nace ma iyayensu bayan gama karatun" "firamare aka jefa musu a makarantar sakandire da ke ƙauyen. Tafi-tafi za tayi karatun baza tayi ba har Allah yasa ta kai aji biyar na babbar sakandire sai kuma ta watsar da karatun. Saboda a lokacin duk ajinsu babu ƴa mace mai shekarunta, ƴan matan ƙauyen da sun fara aji ɗaya, biyu, na ƙaramar sakandire suke" watsar da karatun ayi musu aure. Ita kuwa da ta kai aji biyar na makarantar sakandire har wani kallo take yiwa kanta matsayin babbar "yarinya. Duk da abinda ta tsira da shi a karatun bokon kawai hausa ne ta iya karantawa gar-gar, turanci" kam ƙananun kalmomi kawai ta sani sai kuma ƴan abinda baza'a rasa ba na yaƙi da jahilci. "A bakin mutanen gari Zulaikha ta san ba su Innaye bane iyayenta, a lokacin ta kai shekaru goma sha biyar" "a duniya. A wannan ranar tayi kuka, tayi kuka kamar ranta zai fita, daga ƙarshe zazzafan zazzaɓi ya lulluɓe ta. Kuma sam ta kasa faɗa ma Innaye dalilin kuka da zazzaɓin da take yi, a ganinta idan ta nuna musu ta san ba su ne iyayenta ba duk da irin wannan ƙoƙarin da suke yi a kanta bata yi musu halacci ba." "Daƙyar ta iya yakice maganar a ranta ta kwantar da hankalinta, ta cigaba da yima iyayenta addu'a a ɓoye," ganin yadda Innaye da Baffa ke ta jelar kai ta asibiti ana yi mata allurai da bata magunguna kala daban- daban. Ƴan'uwanta da suke gidan aure na ta zirga-zirgar zuwa gaishe ta. "A lokacin ana gaf da yin bikin Hafizu. Ya gama karatu tuni, mahaifin abokinshi Ibrahim shi ya sama mishi" "babban aiki a Abuja saboda tsananin kyawun sakamakon karatunsa. Kuma cikin ƙanƙanin lokaci Allah ya tarfawa garinsa nono ya tara dukiya mai yawa, a hakanma don yana taimaka ma iyaye da ƴan'uwansa da mutanen ƙwauyensu. Hatta iyalin marigayi Mal Bello da ya zama sanadiyyar cigaba da karatunsa yana" taimaka musu matuƙa gaya.' "Daɗaɗɗen buri ne a zuciyar Baffa tun da yaga yadda Hafizu ke samun manyan kuɗaɗe, da kuma yadda" "yaga hankalin Hafiz ɗin sam ba shi akan zama a ƙauyen ko misƙala zarratin, yaso Hafizun ya duba a cikin ƴaƴan ƴan'uwa ko na mutanen gari ya zaɓi mata a cikinsu." Ta yadda duk cigaban da zai taka a duniya shi da matarsa dai tushensu ɗaya. Kuma matarsa baza ta taɓa gudun ƴan'uwansa ko kuma ta wulaƙantasu ba tunda dai garinsu ɗaya kuma ita ma ƴan'uwanta ne. Amma kafin ya kai ga furta wannan ƙuduri nashi ga Innaye ko Hafizu kawai sai ga zancen zuwa neman auren Bintu Hafiz ya zo musu da shi. """Mahaifinta abokin Abba Lurwanu ne na kurkusa. Ya san komai a kan yarinyar da iyayenta, tare muka" "yi karatu da ita a Zaria. Amma saboda ita karatun Likita take yi shi yasa har muka gama ita bata gama ba. Amma yanzu ta gama har ta fara aiki, shi yasa iyayenta suka ce ta fitar da mijin aure. Za ka iya kiran Abba Lurwanu yayi maka cikakken ƙarin bayani Baffa.""" Sako sunan Abba Lurwanu matsayin abokin mahaifin Bintu ya katse ma Baffa duk wani hanzari. Domin Abba Lurwanu ya taka gaggarumin rawa a rayuwar Hafizu ta yadda bazai taɓa iya watsa mishi ƙasa a ido ba in dai shi ɗan halak ne. "Haka nan ya watsar da burinshi. Kafin ma shi Baffa ya kira Abba Lurwanu shi Abban ne ya kira shi, cikin" girmamawa da mutuntawa yayi masa bayanin duk halin da ake ciki game da yarinyar da Hafiz yake so. A ƙarshe ya ƙara da cewa """To amma ya ka gani Baffa? Domin na faɗa ma Hafiz duk matakin da ka yanke shi ne ƙarshe, ni da shi" "duk umarninka ne abun bi a gare mu.""" Wannan wuƙa da nama da Abba ya miƙa ma Baffa yasa a kunyace ya nuna amincewa. Sannan ya ƙara da "sallama ma Abba komai na hidimar bikin Hafizu, kama daga walittaka da komai da ake buƙatar uba mahaifi ya bar ma Abba. Godiya sosai Abba yayi da matuƙar farin ciki a muryarsa kafin suka yi sallama da Baffa." "Tun da aka yi bikin Bintu, ire-iren abubuwan da suke biyo baya na daga irin ɗabi'un da take nunawa idan" "ta je ƙauyen duk Baffa yana gani. Amma saboda dattako sai yake kawar da kai, kuma daga ɓangaren Innaye bata taɓa masa ƙorafi ba." Irin ƙorafin da Yayyen Hafizun suke yi ma idan suka je gidan acan Abuja duk yana ji. Rakiya a cikin "ƴaƴansa ta kasance ba ta da rufi, ko a waya ya kira ta cikin hikima ya tambayeta halin da gidan ɗan nasa ke ciki ba ta ɓoye masa komai." "Hankalinsa bai ƙara tashi ba sai da Innaye ta je jinya gidan Hafizu, abubuwan da suka biyo baya sun ɗaga" "masa hankali ba kaɗan ba. Amma saboda kar ya raba zumuncin da ke tsakanin ƴaƴanshi yasa yayi saurin kashe maganar, tunda ya lura ƙarara har yanzu Hafiz bai fara ganin laifin Bintu ba. Matsananciyar soyayyar da yake mata yasa a kullum alkhairanta kawai yake kallo." "Zuwan da suka yi barka gidan, yasa jikinsa ya ƙara yin sanyi. Duk irin naɗe tabarmar kunyar da Bintu tayi" "yana sane, ai wawa ba mahaukaci bane. Da wannan dalilin yasa da gangar ya tura mata da yara zuwa" suna duk don dai ya ƙara gwada hankalin Bintun. Bayan dawowarsu suna da irin labarin da ya samu daga bakin Rakiya da sauran ƴaƴansa yasa shi yanke "tsammani akan Bintu. Ƙarara ya gane manufarta na ƙoƙarin janye Hafiz daga gare su iyayensa da ƴan'uwansa, idan kuma hakan bai samu mata ba, babban burinta shi ne duk wani dangin Hafiz ya daina zuwa inda suke acan Habuja. Wannan kuma abu ne da bazai taɓa yiwuwa ba, da wannan dalilin yasa shi" yin amfani da karin maganar nan ta malam bahaushe da yake cewa """Ranar na ka sai na ka.""" Duk cikin ƴaƴan dangi ya duba kaf bai ga wacce zai aura ma Hafizu ta samu dama-dama idan ba Zulaikha ba. "Duk da kwanciyar da al'amarin yayi a zuciyarsa, baiyi gaggawar aikatawa ba sai da ya ɗauki kwanaki yana" Istikhara. Kuma cikin hukuncin Allah lamarin sai ƙara kwanciya yake yi a zuciyarsa. "Ko da ya tunkari ƴan'uwansa da maganar haɗa auren, yayi matuƙar mamaki da yaga sun goya mishi baya." Ta ɓangaren dangin Innaye kuwa su ma addu'ar fatan alkhairi kawai suke yi. "Ya riga ya sani, idan da inda zai samu tasgaro daga Innaye ne, shi yasa ko da suɓul da baka baiyi" "gangancin sanar da ita wanda zai aura ma Zulaikha ba. Ita kuwa Zulai duk haukar da za tayi za ta gama, aure ne an ɗaura kuma in Allah ya yarda mutu ka raba." Shi kuwa mai gayya mai aiki Hafizu duk da bai sanar da shi halin da ake ciki ba a wannan karon ya sha alwashin nuna mishi lallai fa da kai da kaya duk mallakar wuya ne.' "Nannauyar ajiyar zuciya Baffa yaja ya sauke, ya cigaba da kallo da sauraren ƴan'uwansa da na Innaye da" "suke ta mata maganganu na kwantar da hankali, suna ƙara nuna mata idan fa tayi haƙuri, kuma ta" "kwantar da hankalinta, lallai aure tsakanin Zulai da Hafizu alkhairi ne. Amma har lokacin ta tafasa sauke bata ce musu ba, sannan bata daina sharar hawaye ba." """Assalamu alaikum""" Sallamar da Hafiz yayi da nutsattsiyar murya yasa duk mazauna ɗakin suka mayar da hankalinsu da "idanuwansu kan ƙofar, kafin suka amsa sallamarsa." "[1/11, 6:51 AM] Fareeda Abdallah: Hafiz na shiga cikin falon, Innaye tayi gaggawar miƙewa tana tangaɗi" "ta shige cikin uwar ɗakinta. Wasu sabbin hawaye suna sake ɓalle mata, zuciyarta cike taf da tausayin Autarta." "Allah ya sani, wannan lamari ko kusa bata yi murna da shi ba. Da ace Baffa yayi shawara da ita tun farko," Wallahi baza ta taɓa goya masa ba. Kuma ko a yanzu da tana da ikon tilasta Hafizu ba tare da zuciyar Baffa ta yi baƙi ba a take za ta sa ya saki Zulaikha. "A ganinta, zaman Zulaikha a yanzu babu aure har zuwa sadda wani mijin zai bayyana ya fi gaggawar aura" mata Hafiz da aka yi. A ture ma batun Hafiz da ko kusa ba ya ƙaunar Zulaikha tun tana ƴar ƙarama. Bintu? Bintu fa? Bintun nan da ta kasance azzaluma kuma makirar da take ƙoƙarin bin duk hanyar da ta san za ta raba Hafiz da iyaye da ƴan'uwansa? Ita fa Malam ya ɗauki Zulai haihuwar ƙauye rainon ƙauye girman ƙauye ya miƙa ma Bintu ita a matsayin kishiya. "Tun daga zuwanta jinya gidan Hafizu, da irin abubuwan da suka biyo baya, ta yanke tsammanin Bintu za" ta ƙaunace su. Shi yasa ko da ta samu labarin abinda ya faru ga masu zuwa suna ta bakin Balira bata yi wani mamaki ba. Ta san in dai Bintu ce za ta aikata fiye da haka. Ita yanzu ta wace hanya za ta bi ta dakatar da wannan mummunan al'amari??? "A falo kuwa, daga kallon fuskar Hafiz za'a fahimci irin mamakin da zuciyarsa ta shiga na ganin taron dangi" "haka a falon mahaifiyarsa. Amma sai bakinsa bai furta ba, ya durƙusa a ladabce, ya bi su da gaisuwa ɗaya bayan ɗaya har zuwa kan Baffansa." """Hafizu an samu ƙarasowa? Barka da sauka. Ya hanya?""" Baffa yayi maganganun idanunsa cikin na Hafiz. Saukar da idanunsa ƙasa yayi daga kan Zulaikha da yake kallo zuciyarsa cike taf da mamakin barcin banza "da wofi haka da take yi ƙatuwarta da ita a cikin Babanninsu. Lallai da a kusa da ita ya zauna, babu abinda zai hana shi fakaitar idanun mazauna falon ya manna mata wani zazzafan tsungule da zaiyi sanadiyyar tashinta a firgice." """Eh! Na ƙaraso Baffa. Ayi haƙuri da jinkirin amsa kiran da nayi, hakan ya faru ne bisa dalilin manyan" "baƙi da muke da su a gurin aiki. Sai da muka sallame su sannan na kamo hanyar tahowa...""" """Ai babu komai. Tunda dai ka iso lafiya Alhamdulillahi. Leƙa nan Chemis ɗin Habu idan yana nan yazo ya" "duba min Zulai, sumewa tayi. Tun ɗazu ake yayyafa mata ruwa har yanzu bata farfaɗo ba...""" """Subhanallahi! Suma kuma Baffa?""" Yayi tambayar da ɗan damuwa a fuskarsa. """Me yake damunta haka? Wani mummunan abu ne ya faru da ita har ya jefa ta cikin halin suma?""" Ya ƙara jera ma Baffa tambayoyin tun kafin ya samu amsar tambayar farko. "Sai kuma ya miƙe zumbur! Ya fice daga falon, tunawa da yayi duk minti ɗaya da zai ƙara a falon fa" hankalinta na ƙara nisa ne. Gara ya taho da Habun idan aka samu nasarar farfaɗo da ita sai ya samu amsar tambayoyinsa a nutse. "Jim kaɗan bayan minti goma suka shiga cikin gidan shi da Habubakar. A lokacin, duk Babanni da" "Kawunnansa da suke cikin falon sun watse. Baffa ne shi kaɗai, zaune kan kujerar da ke kusa da wanda Zulaikha ke kwance da casbaha a hannunsa yana ja." ****** ****** """Aure kuma Baffa?""" Yayi tambayar hankalinsa a tashe. A zaune yake a ƙasa. Amma tsananin tashin hankalin yadda zancen auren ya duke shi bai san lokacin da ya miƙe tsaye ba. Da rawar murya ya sake cewa """Kuma Auren ma a rasa wacce za'a aura min sai Zulai? Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!!""" Taga-taga yayi kamar zai faɗi da saurin gaske ya zauna akan kujerar kusa da wacce Baffa ke zaune a kanta. Amma tsabar tashin hankali bai ma san abinda ya aikata ba. Hannayensa biyu na rawa ya ɗaga ya kamo hannayen Baffa ya riƙe a cikin nasa """A'a Baffa! Don girman Allah kayi haƙuri... idan ma wasa kake min ka daina. Na rantse da Allah zuciyata" gaf take da bugawa. Taɓa ka ji yadda bugunta ya ƙara matsanancin sauri saboda tashin hankalin da "wannan wasan ya jefa ni a ciki.""" "Da saurin gaske, yaja hannun Baffa ya cusa a cikin rigarsa ya taɓa dai-dai saitin zuciyarsa." """Ka ji ko Baffa? Don Allah ka daina min irin wannan wasan. Irin wasan nan ne fa ko a musulunce ma ba" "shi da kyau...""" """Ba da wasa nake yi maka ba Hafizu. Lallai da gaske yau na ɗaura aure tsakanin kai da Zulaikha. Idan" "kuma ban isa bane, sai ka ɗauki duk matakin da kake so.""" "Tsam! Baffa ya miƙe tsaye, ya karɓe hannayensa daga na Hafizu. Sannan ya fice daga cikin ɗakin." A kunnensa ya ji Hafizu yana jan """Laahaula walaa ƙuwwata illah billahil-aleeyul-azeem""" ****** "Tun da aka samu nasarar farfaɗowarta, ta kifa fuskarta a cinyar Innaye da take riƙe da ita, babu abinda" take yi sai rusa kuka kamar za ta haɗiyi zuciya ta mace. "Ita ma Innaye kukan take yi, tsakanin ita da Zulaikha an rasa wanda zai fara cewa komai." "Baffa ne ya ɗaga labulen falon da siririyar sallama a bakinsa, fuskar nan tasa a murtuke tamau, babu" sauƙi ko kaɗan. Tun da Innaye ta ɗaga kai ta kalle shi sau ɗaya bata sake marmarin kallonsa ba. """Idan kun gama kukan, ki haɗa mata duk kayayyakinta, domin gobe idan Allah ya kaimu za ta bi mijinta." In yaso daga baya idan ta kwantar da hankalinta ƴan'uwanta sa bi ta da sauran kayayyakin da aka "tanadar mata...""" A fiegice Zulaikha ta miƙe zaune tana kallon Baffa. Ta buɗe baki za ta yanka ihu ya daka mata wani gigitaccen tsawan da yasa ba shiri ta haɗiye kukanta. """Idan na sake jin ihunki a gidannan, na rantse da Allah sai na baki mamakin da baki taɓa tsammani ba.""" Da mazarin jiki kuma a tsorace ta ruƙunƙume Innaye tare da cusa fuskarta a jikinta tana sauke ajiyar zuciya sauri-sauri. Har Baffa ya fice daga ɗakin bata sani ba. """Kiyi haƙuri Auta...""" """Innaye tun da na taso Yaya ba ya so na ba ya ƙaunata. Idan na kuskura na shiga gidanshi a matsayin" "matarsa ni na san kashe ni kawai zai yi.""" "Ta katse Innaye cikin gunjin kuka, bayan ta tabbatar Baffa ya fita." """Idan ya kashe ki, ko kuma ya bari muguwar matarsa tayi miki wani mummunan abu, duk su biyun" "hukuma ba ƙyale su za ta yi ba Auta. Ki kwantar da hankalinki, ni kaina wannan auren bai min ba, kuma" "bazan taɓa yarda da tabbatuwarsa ba.""" "Jin wannan jimlar maganar ƙarshe ta Innaye, yasa sannu a hankali ta fara rage ƙarfin kukan da take yi, sai" "sauke ajiyar zuciya. Ita daman ta san Innaye ta fi Baffa son ta nesa ba kusa ba, domin ta ƙara samun" nutsuwa a zuciyarta yasa ta ce """Da gaske Innaye? Za ki sa Yaya ya sake ni?""" """Ƙwarai da gaske. Dole ma ya sake ki, domin shi da kanshi na tabbata ba son wannan al'amarin yake yi" "ba, Haɗi ne na Baffanku kawai. Amma ya zama dole a yanzu ki kwantar da hankalinki, ki bi Yayan naki ku" "tafi, ko na sati ɗaya ne. Na fi so in aikata komai a sirrance yadda Baffanku bazai ga laifi na ko naki ba. Ko ke kina so Baffanku yayi fushi da ke ne?""" "Da sauri ta girgiza kai, alamar a'a!" """Yauwa! To kin ga da wannan dalilin ya zama dole in bi komai a sannu, cikin hikima da ƙwarewa. Don" "haka mataki na farko da za mu bi yanzu shi ne ki daina koke-koken nan da kike yi, kar Baffanku ya sake" "shigowa yaga kina kuka, saboda ba na so ko kaɗan ya ɗarsa a zuciyarsa baza kiyi masa biyayya ba. Na fi so duk wani laifi ya fito ta ɓangaren Hafizu da matarsa, kin gane ko?""" "Ɗaga kai tayi, alamar eh!" "Miƙewa Innaye tayi ta shiga uwarɗakinta ta bar Zulaikha zaune akan kujera, ta buga tagumi da hannu" "bibiyu. Zuciyarta a ɗage, a yadda take ji kamar ta janyo sati ɗayannan tayi ta wuce Innaye ta saka Yaya ya sake ta. Tana waɗannan tunane tunanen sai ga sallamar yayyenta su Balira." "Da yake su ma duk sun samu labarin irin halin da Innaye da Zulaikha suke ciki, duk yadda al'amarin auren" ya daɗaɗa musu zuciya ko kaɗan basu nuna ba. Jimami da damuwa suka ara mai yawa suka yafa a fuskokinsu. Bayan gaisuwa da jaje da suka yi ma Innaye nan kusa da Zulaikha suka zauna suna ƙara tausarta da daɗaɗan kalamai. Ko da suka fahimci ƙudurin Innaye na son raba auren kuma har suka fahimci Zulaikha "ta hau kan maganganun ta zauna daram! Sai kawai suka cigaba da ɗora ta akan hakan, suna tabbatar mata ai dole ma a raba auren. Amma a zukatansu sam ba sa fatan hakan ya kasance." Da waɗannan kalaman hilatar har Balira ta samu ta tsefe mata kai. Ita kuma Rakiya ta ɗaura mata ƙunshin gargajiya da ta taho da shi daga gidanta. """Ku fa duk dama kun daina wahalar da kanku, auren da duka-duka bazai wuce sati ɗaya ba waɗannan" "gyaran ai ba su da wani amfani.""" "Ta faɗa tana zumɓura baki, kanta na kwance kan cinyar Aunty Balira ana tace mata kai a hankali. Riƙe a" hannunta wayar Balira ce da Hafiz ya bata tana shiga nan ta fita can. """Duk da haka dai Autan Innaye, ko ba don auren ba za ki bar gari ko na kwana ɗaya ne ai kya gyara" "jikinki.""" Rakiya ta amsa mata a tausashe. Ita Ladidi can cikin ɗaki ta shige tana taya Innaye harhaɗa ma Zulaikha kayan sawarta sabbi a jikin jakar "ghana most go, da duk wasu abubuwa da ta san Auta za ta iya buƙata a cikin kwanaki bakwan da za tayi" a gidan Hafizu. "[1/12, 12:03 AM] Fareeda Abdallah: Duk yadda Aunty Ladidi ta so Innaye ta ƙara yawan kayan cikin jakar" ƙiyawa tayi. Daga ƙarshe ma balbaleta da faɗa tayi ta ce idan baza ta taya aikin bakinta alekum ba ta fice ta ba ta guri. """Tafiyar da kowa ya tabbatar ba ta zama ba ce menene na girin-giɗishin zuba kaya da yawa a jaka?""" """Haka ne kuma Innaye. Allah ya baki haƙuri.""" Ta faɗa tana ƙumshe dariya. Sai da Innaye ta fita waje ɗauro alwalar sallar magriba sannan Ladidi tayi gaggawar ƙara yawan "kayayyakin, sosai ta zaune jakar yadda kayan ciki suka yi ƙasa, sannan ta ƙara wasu masu yawa ba tare" da ta tsaya shirya su a nutse ba don tsoron kar Innaye ta shigo. "Zuwa bayan Magriba, babu laifi Zulaikha ta fito a amarya sak! An wanke mata kai tas! Bayan an gama" ƙunshi kafin ya kama Aunty Rakiya ta yaryaɗa mata ƙananun kitso masu kyau sosai. Kuma da yake tana yalwar gashi mare cika sai tsawo kuma baƙi ƙirin kitson ba ƙaramin kyau yayi ba. Ɗaya daga cikin Sabbin kayanta Balira ta bata ta saka a jiki da sabon hijabi. Ko kafin ta saka kayan sai da tayi narai-narai kamar za ta fashe da kuka. Tuntuni daman ƙarfin hali kawai "take yi, kalaman Innaye ne kawai idan ta tuna yake saka ta jin ɗan ƙarfi-ƙarfi da kwanciyar hankali." """Saboda me zan saka sabon kaya? Ni bazan sa ba Aunty. Idan na saka sabon kaya ai kamar na ma nuna" "ma jama'a ina son auren nan ne.""" Tayi maganar bakinta a gaba. """Daɗina da ke Auta akwai ki da wauta. Ca nake tuni kun gama magana da Innaye kan za kiyi basaja" "baza ki ƙara nuna ɓacin ranki akan auren ba? Ta yadda idan komai ya tafi yadda ta tsara Baffa bazai ga laifinki ko na ta ba?""" """Eh!""" Ta amsa cikin ɓacin rai da waswasi. """To maza ɗauki kayannan ki sanya. Wannan duk cikin shirin ne. Idan kuma kina so shirin naku ya ɓaci" "ne kar ki saka kayan.""" Aunty Balira na gama faɗin haka ta fice daga ɗakin. Haka Zulaikha ta ɗauki kayan ta saka ba don ranta na so ba. A maimakon ta sake fita falo cikin "ƴan'uwanta, sai kawai tayi kwanciyarta akan gado, daman tana fashin sallah. Zuciyarta cike da saƙe-saƙe, ta kuma rasa dalilin da yasa tun da rana ƙirjinta ke bugawa ƙasa-ƙasa." Yinin ranar gaba ɗaya Innaye ta ƙarasa shi ne fuskarta a ɗinke tsaf! Duk matan da sukai ta shigowa yi "mata Allah ya sanya alkhairi, haka take amsawa babu walwala ko kaɗan, don ma kar mace ta ƙara cewa wani abu bayan Allah sanya alkhairin. Hatta abokan zamanta da sauran yaran gida sun rasa gane kanta, a dole suka kama kansu, suka cigaba da harkokinsu da Baffa da fuskarsa ta ƙarasa yinin cike da fara'a ta" musamman. Domin haka kawai yake jin wani nutsuwa da kwanciyar hankali na saukar masa. Duk inda Yayye da ƙannen Hafizu suke nemansa don suyi masa Allah ya sanya alkhairi sama ko ƙasa sun "neme shi sun rasa a cikin gidan da waje. Ga kuma motarsa a ƙofar gida, ga direbansa a ƙofar gida, amma" "ba shi ba labarinsa. Tun da aka kira sallar la'asar ya lallaɓa yana jiri ya fice daga ɗakin Baffa, har zuwa" bayan sallar isha'i babu wanda ya ƙara saka shi a ido. """Ku ƙyale shi, duk inda ya shiga ma zai fito ne. Shi ai ba baƙo bane, ciki da wajen ƙauyen nan babu inda" "bai sani ba. Duk inda ya shiga bazai ɓata ba.""" Kalaman da Baffa yayi musu kenan lokacin da ya ga damuwa da jajen Hafizu da suke yi ya fara yawa. Mata masu aure haka nan suka bar gidan bayan isha'i ba tare da sun ganshi ba. Amma duk sun ƙuduri "aniyar washe gari da sassafe za su dawo su gaisa da Hafizun, suyi masa Allah ya sanya alkhairi sannan su" bashi amanar ƴar'uwarsu. "Hafiz bai bayyana ba sai a masallaci wajen sallar asubah, ana idar da sallah kuma yayi wuf zai fice da" sauri ƴan'uwansa da jama'ar gari da suke son taya shi murna suka lulluɓeshi. Haka nan ya tsaya ba don "ranshi ya so ba, fuskarshi da ƴar dariyar da ana kallo an san na yaƙe ne." Bayan ya ƙwaci kansa daƙyar daga cikin mutane suna hanyar zuwa gida ƙaninsa ke tambayarsa. """Yaya ina ka shiga ne? Jiya sama da ƙasa mun neme ka mun rasa, sai direba da motarka kawai a waje." "Mun tambayi direba ya ce shi kanshi bai san inda kake ba.""" """Uhmmm! Ina nan!""" Abinda ya iya cewa kenan a taƙaice. "Ko da suka shiga gidan, ɗaya bayan ɗaya ya bi ɗakin kishiyoyin Innaye ya gaishe su. Duk ɗakin da ya shiga," "sai da ya ɓata lokaci saboda nasihar da suke masa, abu ɗaya da suka fi jaddada masa duk su biyun shi ne lallai yayi ƙoƙarin riƙe amanar Zulaikha. Tunda dai sunyi -sunyi da Baffa ya bari ko mutane uku su raka ta ɗakinta ya ƙi." """Ka ji tsoron Allah Hafizu. Ka riƙe ƴar'uwarka amana don girman Allah. Ka ga marainiya ce, Fiyayyen" halitta SAW ya ce ni da mai taimakon maraya kafaɗa da kafaɗa za mu shiga aljannah. Ka ga kai riba biyu "ma za ka ci, ga ta matarka ce, sannan kuma marainiya ce. Don Allah ka ji tsoron Allah, ka riƙe ta amana. Kar ka ga don ba idanun iyaye da ƴan'uwa ka ce za ka zalunce ta.""" """In sha Allah! Zan kiyaye""" Ya faɗa daƙyar! Kamar me ciwon baki. "Ko da ya isa ƙofar ɗakin Baffa, ya daɗe a tsaye cikin shiru, kamar kar ya shiga ciki yake ji. Amma ya sani" "ko bai shiga yanzu ba dole ya shiga ɗan anjima kaɗan, ya gaida Baffa sannan kuma yayi mishi sallama. Domin da safen yake so su juya zuwa Abuja." "Huci mai zafi ya fesar a bakinshi, idanunshi sun kaɗa sunyi jaa, ga wani fitinannen ciwon kai da yake" "damunsa. Domin Jiya kwana yayi a takure cikin mota, Ƙwaƙwalwarsa a cushe, ya ma rasa wani irin tunani" ya kamata yayi. Bai samu wani wadataccen barci ba. "Fargaba da tsoro ne cike taf da zuciyarsa, a yanzu da zai sake fuskantar Baffa, bai san kuma wasu zafafan" "maganganu zai zo mishi da su ba. Haka kawai, ya tsinci bakinsa da yin addu'o'i yana tsaye a ƙofar ɗakin, sai da ya shafa addu'ar, kafin yayi ƙarfin yin siririyar sallama, ya shiga ɗakin bayan an amsa mishi daga" "ciki, a bayyane yake jikinsa a sanyaye." "Mamaki ne ya rufe shi ganin fuskar Baffa yalwace da murmushi, abinda bai sani ba shi ne, tun" tsayuwarsa a bakin ƙofar da duk abinda yake yi Baffa yana kallonshi ta cikin labule. """Zauna mana Hafizu""" Baffa ya bashi umarni. Da saurin gaske kuma a tsorace yakai gwuiyawunsa zuwa ƙasa ya zauna. Idanunshi har lokacin na kan "Baffa, duk a tsammaninsa ko laifi yayi. Amma fara'ar da ke fuskar Baffa ita ke saka shi cikin wasi-wasi." """Fushi kake da ni ko Hafizu?""" """A'a Baffa""" Ya amsa da sauri. """Wallahi ko kaɗan ba na fushi da kai. Wane ni inyi fushi da kai Baffa? Kawai dai al'amarin ne yazo min a" "bazatan da ban taɓa tsammani ba. Ka yafe min irin yanayin da na nuna a jiya...""" """Babu komai Hafizu. Allah yayi muku albarka.""" """Ameen Baffa""" """Ka yi haƙuri. Ka rungumi ƙaddarar da ta afka maka. Ni kaɗai nasan dalilan da suka sa na yanke" "shawarar haɗa aurenka da Zulai, ba tare da ita kanta Rahina ta san zan haɗa auren ba. Idan ka riƙe Zulai da kyau, lallai nan gaba kaɗan in Allah ya yarda za ta zame maka matar rufin asiri. Amanarta na damƙa maka ! Amanar Zulai na baka Hafizu!! Ina umartarka da ka riƙe Zulai da Amana Hafizu!!! Lallai idan ka ci" amanarta za ka gamu da mummunar ɓacin rai daga gare ni. "A yanzu Zulai matarka ce, kamar yadda Bintu take matsayin matarka. Idan ka fifita Bintu a kan Zulai ka" "zalunce ta, kuma ni ma ka zalunce ni, Allah bazai taɓa barinka ba Hafizu." Lallai ina mai tunasar da kai ka kiyaye haƙƙoƙin iyalanka biyu da Allah ya ɗora a wuyanka. Kar ka kuskura "son zuciyarka ko tasirin ƙiyayyar da kake yima Zulai tun tana ƙanƙanuwa, ko kuma zugar shaiɗaniyar mace yasa idanunka su rufe ka kasa yi ma Zulai adalci. Ko kuma ka kasa sauke nauyin haƙƙinta da Allah ya ɗora a kanka, idan hakan ta faru, tabbas za ka tashi a ranar lahira da shanyayyen ɓarin jiki." "Yaushe ne tafiyar taku?""" """Da safen nan ne Baffa.""" "Ya amsa a hankali, gaba ɗaya hankalinsa a ɗugunzume, saboda nasihar da Baffa yayi mishi sun ƙarasa" kashe mishi jiki gaba ɗaya. """Tashi kaje ka gaida Rahina. Allah ya kai ku lafiya ya kiyaye hanya.""" """Ameen Baffah""" Haka ya miƙe ƙafafunsa a sake kamar wanda ya wuni yana zawayi ya fice daga ɗakin. "Ko da yayi sallama a ƙofar ɗakin Innaye ya shiga ciki, bayan amsa sallamar da gaisuwarsa da ta amsa a" "taƙaice babu wata magana da ta sake shiga tsakaninsu. Kamar surukan juna na gaske, haka suka kasance." Shi kanshi yana ƙasa yana ɗan matsa yatsun hannayensa kaɗan-kaɗan yana jiran jin abinda za ta ce masa. "Ita kuma fuskarta na kallon gefe, fuskarta babu walwala ko kaɗan, casbahan hannunta take cigaba da ja sauri-sauri." """Innaye?""" Ya katse shirun da ke tsakaninsu ta hanyar kiran sunanta a raunane. "A fakaice ta kalle shi, bata amsa ba ta sake kawar da kanta gefe ɗaya." Ajiyar zuciya yaja ya sauke kafin ya cigaba da cewa """Da safen nan za mu tafi. Kiyi haƙuri, a saka mana albarka...""" """Idan ka bari Bintu ta zalunci Auta ban yafe maka ba Hafizu.""" "Innaye ta katse shi tun kafin ya aje numfashin maganarsa, da muryar faɗa-faɗa." """Sannan kuma ban yafe maka ba idan ka ɓoye ma Bintu matsayin Auta a gare ka yanzu. Duk da dai" "wannan al'amarin ba wai ya kwanta min arai bane, har izuwa yanzu tunanin yiwuwarsa ko rashin yiwuwarsa nake yi, amma a iya ɗan zaman da Auta za tayi da ku kafin mu samu hanya mai ɓullewa, idan" "kai ko Bintu wani ya cuta mata don zalunci ban yafe masa ba. Ɓace min da gani""" Har ya miƙe zai fita yana rangaji ta sake kiran sunanshi a tsawace. "A hankali ya juya yana kallonta, idanunsa sun ƙara kaɗewa sunyi jajur!" Babu tausayinsa ko kaɗan a fuskarta ta sake cewa """Kuma ban yarda idan kuka isa can Habuja ka ajiye min Auta a wannan ƙaton ginin na bayan gida inda" "kuka saba saba yasar da mu ƙauyawa ba. Ita ma ka ajiye ta cikin aljannar duniyar da kuke kai da matarka," "tunda dai a yanzu itama matarka ce. Allah ya bamu alkhairi.""" "Ko da ya buɗe baki zai amsa addu'ar, inda kasan an saka zare da allura an ɗinke masa baki. Ga wani" "nauyi na musamman da bakin yayi mishi, a dole ya amsa addu'ar a zuciya ya kama hanyar ficewa daga" ɗakin. """A'ah! Ango Ango! Na Bintu da Zulai ba da kanka a sare kaje gida ka cewa Innaye ya faɗi.""" Aunty Rakiya da ta sanyo kai cikin ɗakin tayi maganganun da salon tsokana tana kallon cikin idanunshi. Ita kuwa Aunty Balira cewa tayi """Idanunka kenan Hafizu? Jiya ƙad da bus muka neme ka a cikin gidannan muka rasa. Ko duk murnar" "auren gatan da Baffa yayi maka ne?""" "Ya rasa dalilin da yasa, yana kallon cikin idanun Aunty Balira wasu hawaye masu ɗumi suka cicciko" idanunshi. Kawai sai ya ƙara sauri ya fice daga ɗakin don kar hawayen su zuba a gabansu. "Bai san Aunty Balira tana biye da shi ba, sai da ya shiga cikin soron gidan yaji muryarta ɗan nesa da shi" kaɗan tana kiran sunanshi. "A yadda zuciyarsa ke wani irin zafi da tuƙuƙi, gani yake idan ya buɗe baki da nufin yin magana tabbas" "babu abinda zai hana shi fashewa da ƙaƙƙarfan kuka. Don haka kawai ya zaɓi yin shiru yana kallonta, har" ta ƙarasa kusa da shi ta riƙo hannunsa na dama a cikin nata. "A tausashe, da yanayin kalami mai nuna rarrashi da damuwa da halin da yake ciki ta ce" """Kayi haƙuri Ƙanina.""" "Ɗan shiru ne ya ratsa tsakaninsu, kuma har lokacin ya kasa buɗe baki yayi magana, sai ajiyar zuciya" kawai yake saukewa akai-akai. Ita ne ta cigaba da cewa a tausashe. """Na sani ba'a kyauta maka ba Hafizu. Kayi haƙuri ka ji? A cikin biyayyar iyaye duk tsananinsa in dai ba" saɓon Allah bane in sha Allah alkhairi ne yake biyo baya. Saboda yardar Allah tana tare da yardar iyaye. Fushin Allah shi ma yana tare da fushin iyaye. Kar ka kuskura ka biye ma son zuciyarka ko kuma wata "ƙiyayya ka saɓa ma iyayenka ka ji ko?""" """Na gode Aunty. Zan kiyaye in sha Allahu""" Taƙaitacciyar nasiha ta sake mishi har Aunty Ladidi ta shigo ta tarar da su a tsaye a zauren. Ita ma ta ɗan tofa albarkacin bakinta cikin sigar rarrashi da tausasa kalami. "Godiyar ya sake musu, da alƙawarin zai yi aiki da duk shawarwarin da suka bashi. Kafin ya fice zuwa waje," su kuma suka koma cikin gida. "[1/18, 10:59 PM] Fareeda Abdallah: Duk yadda Zulaikha ta so ta cigaba da nuna dauriya kasawa tayi," "lokacin da taga gadan-gadan da gaske tafiya Abuja za a sake yi da ita. A Abuja ma ba ko ina za'a kaita ba sai gidan Bintu, Bintu da ta tabbatar duk cikin ƴan'uwansu ta fi tsanarta. Kuma za ta je gidan ne yanzu ba'a matsayin ƙanwar miji ba, a'a! Matsayin matar maigidan za ta je." "Ita ba jahila bace, daidai gwargwado tana da sani sosai a ɓangaren Islamiya. Domin wani jajirtaccen" "malami suka samu daga ƙungiyar malamai masu shiga ƙwauyuka yin da'awa. Tun da aka ajiye musu shi a ƙauyen yana koyar da ƴan mata da safe, da rana matan aure, da yamma samari, da daddare maza magidanta fiye da shekaru biyar bai taɓa barin ƙauyen da sunan tafiya gaba ɗaya ba. Sai dai ya je can birni gurin iyalinsa kwana ɗaya, biyu sai ya sake komawa ƙauyen." "Da yawan ƴanmatan da yake koyar da su karatun shashatau suke yiwa islamiyar, tana daga cikin" "ɗaiɗaikun yaran da suka nace ma karatun, domin a yanzu haka tana da haddar izu ashirin cif a kanta. Kuma ta samu karatun littattafai da dama." "Domin lokuta da yawa ita ke ƙara ma su Innaye karatun Alƙur'ani mai girma a gida da sauran littattafai," "hatta wasu hukunce-hukuncen addini ita suke fara tambaya, idan ta sani ta amsa musu, idan bata sani ba sai ta tambaya musu Ya Sayyadi a makaranta." "A yanzu, ta sani tunda aka ɗaura aurenta da Hafiz haƙƙoƙinta sun hau kansa, kamar yadda nasa suka hau" "kanta. Kuskure kaɗan za tayi mala'iku su fara tsine mata. Bata son auren ko baya son auren wannan bai isa uzuri ba a gurin Allah SWT. Idan tana son kanta da arziki ya zama dole tayi taka tsantsan wajen kiyaye haƙƙoƙinsa da suke kanta, har zuwa lokacin da Allah zai ƙaddara rabuwar auren. In dai ba kuma tana so" ta jefa kanta a halaka bane. "Kafin ta birkice musu da kuka na tashin hankali, a ɓoye Aunty Rakiya ta ja ta zuwa ɗakin Umma Laraba," "tayi mata karatun dallah-dallah na yadda za ta zauna da Bintu, har ma da shi kanshi Hafiz ɗin ba tare da ta wahala ba." Bakinta a gaba ta ce """Aunty Rakiya auren nan fa Innaye ta tabbatar min bazai wuce sati ɗaya ba, don zaman sati ɗaya da" "zanyi acan ni me ma zai sa in shiga harkarsu har su wulaƙanta ni...""" """Amma ke kam anyi sakaryar yarinya Auta. Wai halin Bintun ne kika manta ko kuwa tsoronta kike ji?" Kina sane da cewa in dai daga ƙauyen nan mutum ya je gidan Hafizu ko na yini ɗaya ne muguwar yarinyar nan sai ta san yadda tayi ta ƙuntata masa. Hatta su Baffa basu tsira da wulaƙancinta ba. Balle kuma ke da tun a farkon-fari a bayyane take nuna ma "kowa ba ta son ki ba ta ƙaunarki. Kuma kin sani sarai ba wani shiri kuke yi da Hafizu ba, balle ganin" idanunsa yasa ta jin shakkar yi miki wani muguntar. "Yarinya idan ma za ki zage damtse ki shiga gidan da shirinki gara ki zage, idan ba haka ba kuwa...""" Ta saki ƙaƙƙarfan ƙwafa kafin ta cigaba da cewa """Ba sati ɗaya ba, Ko zaman auren kwanaki biyu za kiyi a gidan irin gashin aya a tafin hannun da Bintu za" "tayi miki na rantse da Allah sai kin gane shayi ruwa ne. Don haka gara ma ki farka daga magagin da kike yi, ki shiga da shirinki da taƙamarki, ki nuna mata Zulan nan fa da ta sani a baya mare tsoro da ɗaukar iskanci har yanzu dai ke ce ba'a canja ki ba.""" Haka Aunty Rakiya ta ɓata lokaci sosai tana ƙara kitsa mata yadda za ta dinga ƙwatar kanta a hannun "Bintu da Hafiz. Kuma inda Allah ya taimake su shi ne Mama Laraba ita ke aikin abin kari, har Aunty Rakiya ta gama yi ma Zulaikha bayanin da za ta mata babu wacce ta shiga cikin ɗakin ballantana a kwaɓa mata." "Basu fito ba, sai da Aunty Rakiya ta ji muryar Ladidi tana jajen ina suka shiga." """Ki ji tsoron Allah Rakiya, me kike kitsa mata? Na fa san halinki ba ki da haƙuri kamar zawo.""" Aunty Ladidi ta faɗa tana ɗan hararar Rakiya cikin wasa. """Ba ruwana. Nasihar zaman aure kawai nayi mata irin wanda ake yiwa ko wacce amarya.""" Ta amsa tana dariya. """Ai kuma sai kiyi, dama ba'a san asalin balbela ba sai ta ce daga madina take. Kin ji Auta zo muje kiyi" "wanka, lokaci ya ƙure, tun ɗazu Hafizu ke aiken idan kin gama shiryawa za ku wuce ga shi ko wanka baki yi ba.""" Tun daga jin kalmar za su wuce ɗinnan jikinta ya ƙara wani irin sanyi ƙalau. Nan take ta fara matsar "ƙwallah, har Aunty Balira tayi mata wankan Amare da ruwan turare da lalle kuka take yi ƙasa-ƙasa." "Da yake fuskar Aunty Baliran a ɗaure yake tamau, shi yasa ko kaɗan bata samu damar kawo mata wargi" "ba har aka gama wankan, da su hayaƙin tsuguno da na jiki, da wasu mabanbantan turaruka da tayi ta mutsuka mata a sassan jiki, a dole nata kallo da shatatar hawaye har aka gama shiryata cikin wata doguwar riga ƴar saudiyya mai kyau, kuma sabuwa fil, wacce bata san daga ina Aunty Baliran ta samo ta ba. Ta saka mata sabon hijabi mai girma da ya sauka mata har ƙasa saboda ba wani tsawon azo a gani" take da shi ba. Sannan Aunty Balira da Ladidi da take ta yaba irin kyawun da tayi suka kama ta a lulluɓe jikinta babu "inda ba ya rawa suka kai ta gurin Innaye da tun ɗazu take zaune a falonta ta zuba tagumi, idanunta sun kaɗa sunyi jaa, kallo ɗaya za ayi mata a hangi gagarumin damuwa a tare da ita." Sai da aka zaunar da ita gaban Innaye da cewar tayi mata nasiha sannan Zulaikha ta samu damar sakin "ƙaƙƙarfan kukan da tuntuni take dannewa. Lokaci ɗaya ita ma Innaye ta saki na ta kukan a raunane, da alamun tun ɗazu kukan ke son ƙwace mata tana matsewa. Abin dariya abin tausayi, Zulaikha kuka Innaye kuka, haka ƴaƴan suka tasa su gaba suna kallo kamar suyi dariya ga kuma tausayin da ya lulluɓe zukatansu, saboda a bayyane yake ga kowa irin matsananciyar shaƙuwa da ƙaunar da ke tsakanin Innaye" da Autar ta. Basu taɓa tsammanin aure zai nesanta su nisa mai nisa irin haka ba. Ganin irin kukan da Innaye ke sharɓa yasa lokaci ɗaya Zulaikha ta sake birkice musu da kuka kamar wacce aka ce mata idan ta tafi ta tafi kenan har abada. "Tun ƴaƴan suna rarrashi su kaɗai, har sai da su Umma Laraba da Mama Laminde da sauran ƴaƴan gidan" mata da suka je gidan suka shiga ɗakin su ma suka fara aikin rarrashi. "Suna cikin wannan halin, Baffa ya shiga ɗakin da sallama a tsawace, amma a wannan karon duk tsawa da" "hargaginsa bayyi tasiri kan Zulaikha ba, ƙam! Ta riƙe ƙafafun Innaye tana rusa ihun kuka da kurarin ita" "babu inda za ta je, a barta a gurin Innayenta in dai ba so ake ta mutu ba. Ita ta yarda a kwance aure da" "Hafiz a ɗaura mata da ko tsoho ne, ko gurgu ko kuturu ta yarda za ta zauna tayi biyayya in dai kusa da Innaye ne." A fusace Baffa ya fice daga ɗakin zuwa ɗakinsa da nufin ɗauko zabgegiyar bulalarsa da yake ladaftar da "yaran gidan ƙananu, lura da abinda yake shirin yi yasa da saurin gaske Yayyinta suka ɓamɓareta daƙyar" daga jikin Innaye suka fice da ita zuwa mota tana gunjin kuka. "Ƴan kayayyakinta daman tun da sassafe an riga an zuba a cikin mota, fitowarta kaɗai Hafiz da direba" "suke jira, ya riga ya gama sallama da kowa. Ranshi yayi mummunar ɓaci da yadda ƴar ƙanƙanuwar yarinya kamar Zulai take ta ɓata mishi lokacin tafiya, sai dai ko kaɗan bai nuna ba. Domin babban burinsa a wannan gaɓar shi ne ya rabu lafiya da iyayensa." "Da farko yana zaune ne a ƙofar gida kan dakali, amma da yaga wasu daga cikin mutanen ƙauyen sun ƙi" "sarara mishi ya huta, kowa da irin neman taimakon da zai zo gurinshi, shi kuma ga irin ƙuncin da" "zuciyarsa ke ciki, da yayi iya taimakon da zai iya kuma Zulaikha bata fito ba kawai sai ya shige ɗakin ƙannenshi maza da ke cikin zauren gidan." Kukan da Zulaikha ke yi lokacin da za'a wuce da ita ta cikin zauren shi ne abinda ya dawo da shi hayyacinsa daga zuzzurfan tunanin da ya afka. Mamaki mai tsanani ne ya kama shi jin irin kukan da take yi. Sai kuma ya mele baki gefe ɗaya ya miƙe tare da ɗaukar wayoyinsa ya fice daga cikin ɗakin. "[1/20, 11:43 PM] Fareeda Abdallah: Akan idanunsa Aunty Balira ta buɗe tafin hannun Zulaikha ta saka" "mata wayar Android ɗin da ya bata. Kamar Aunty Baliran ta san kallonta yake yi da mamaki a fuskarsa," sai ta juya tana kallonshi da ƙayataccen murmushi a fuskarta. """Aro na ba ta ba kyauta ba. Na san a matsayinta na matar ƙanina Hafizu nan da kwanaki kaɗan za ka" "siya mata ƴar sha-far da ta ninka wannan a tsada, ka ga idan ta mallaki na ta sai ta dawo min da nawa.""" """Uhmmm!""" Abinda ya iya ce mata kenan ya mayar da hankalinsa gurin dandazon ƴan'uwansa da suke tsaye jikin motar suna ƙara rarrashin Zulaikha da har lokacin take kuka ƙasa-ƙasa da tausasan kalamai. "Ranshi ne ya ƙara ɓaci, da ma ace yana da ikon yin abinda yake so ba tare da an samu mishkila ba," tabbas da babu abinda zai hana shi lallasa Zulaikha a gurinnan. Sanin ba shi da wannan damar yasa shi "yin ƙwafa ƙasa-ƙasa, yayi ta maza gurin rage girman ɓacin ransa." """Kuyi haƙuri, lokaci na tafiya. Duk yadda ake ciki idan mun isa za muyi waya da ku.""" Yayi maganar da sanyin murya. "Ba tare da ɓata lokaci ba duk suka ja baya daga jikin motar, Aunty Rakiya ce ta rufe ƙofar baya na motar" inda suka zaunar da Zulaikha bayan ta cusa kanta cikin motar ta raɗa ma Zulaikha magana a kunne. "Fatan alkhairi da addu'ar Allah ya tsare gaba ɗaya suke mishi haɗe da ɗaga mishi hannu, har direba ya" tayar da motar suka ɓace ma idanunsu basu koma cikin gida ba. """Ubangiji Allah ya kaɗe fitina, ya bada zaman lafiya da Zuriya masu albarka.""" "Indo, babbar ƴa a ɗakin Umma Laminde tayi addu'ar." """Ameen ya Allah""" Suka amsa gaba ɗayansu. ***** ****** Da ɓacin rai sosai a muryarsa ya ɗan waiwaya baya ya kalli Zulaikha da har lokacin yake jin shessheƙar kukanta ƙasa-ƙasa ya ce """Kin san Allah? Idan bakiyi mana shiru ba a tsakiyar dajinnan da babu gida gaba babu gida baya zan" "saka a sauke ki. Kuma kin san halina sarai, tsaf zan iya aikata fiye da haka.""" Maganar na dira a kunnuwanta ɗif! ta tsayar da kukan da take yi kamar ɗaukewar ruwan sama. A tsorace ta ɗan ɗago kanta daga cikin hijabi ta saci kallon gefe da gefen hanya. "Sai taga kamar yadda ya faɗa ne, a cikin daji suke tabbas! Kuma ta san mugu ne na ƙarshe in dai a kanta" "ne, kaɗan daga cikin aikinsa ne ya yasar da ita a gurin, balle ma a yanzu da yake ganin ta zame mishi ƙarfen ƙafa. Kuma kasancewarsa gogaggen ɗan boko da ya saba da ƙarya ƙirƙirar abinda zai faɗa don wanke kansa a gurin iyayensu bayan ya ɓatar da ita ba abu ne da zai mishi wahala ba." "Tana jin shi ya ja ƙwafa mai ƙarfi, sannan yayi dogon tsaki. Ga dukkan alamu dai bai so tayi shiru ba." 'Mugu! Aniyarka ta bi ka. In Allah ya yarda har mu raba gari muguntarka ko na matarka bazai taɓa tasiri a kaina ba. Allah nake roƙo ya cigaba da bani kariya daga dukkan sharrinku.' Tayi maganganun a zuciyarta. "Kasancewar ta daɗe tana kuka, kuma daren jiya gaba ɗaya barcinta raba da rabi ne. Don haka bata ɓata" lokaci cikin tunani ba nannauyan barci yayi awon gaba da ita. "Kamar a mafarki, ta ji saukar wani zazzafan duka a gefen kafaɗarta. A firgice ta ɗago fuskarta idanu a" warwaje ta ce """Wayyo Allah Innaye...""" "Cike da jin haushi ya kai hannu zai make mata baki, Allah ya taimake ta taga tahowar hannunsa, da" saurin gaske tayi gaggawar kawar da fuskarta can gefe ɗaya. """Idiot! Kina barcin ma baki san idan an tashe ki kiyi salati ba sai ihu.""" Ya faɗa da ɓacin rai yana harararta. "Ƙasa-ƙasa ta mayar mishi da martanin hararar da yayi mata, duk da bata san cikakken fassarar kalmar" "'Idiot' ba ta san zagi ne, domin malamansu na boko suna yawan faɗa ma ɗaliban da basa jin magana. Bakinta a gaba a zuciyarta ta ce" 'Ni dai ba Idiot bace.' A fili kuma cewa tayi cikin guna-guni """Yaya duka na fa kayi ba tashi na ba... Kuma da zafi sosai. Bayan Innaye ta ce amana maci amana" "maye...""" """Idan kika sake min maganar Innaye anan sai na ɓata miki rai. Za ki fito ko sai na sa an kulle ki cikin" "mota?""" "Kafin ta fito, sai da ta waiga ta tabbatar ba'a tsakiyar daji suke ba. Mamaki ne ya kamata da taga ashe" "har sun isa gidanshi a Abuja, bata ce komai ba sai girgiza kai da tayi. A maimakon ta fito ta ɓangaren ƙofar da yake tsaye yana jiran fitowarta, muskutawa tayi zuwa can ɗaya ƙofar ta buɗe da sauri ta fita tun" ma kafin ya sake cewa komai. "Miƙa tayi haɗe da salati a hankali, a zuciyarta take ayyana ƙarshen tika tiki tik! Ga ta dai a cikin gidan," kuma a matsayin matar mai gidan. Sanin irin wainar da za'a toya kuma a cikin gidan Allah kaɗai ya bar ma kansa sani. Da saurin gaske ta ɗaga ƙafa ta bi bayansa ganin har ya kusa isa bakin ƙofar shiga ɓangarensu ba tare da "ya ƙara ce mata kanzil ba. Har ta kusa cimma inda yake, sai ta tuna da jakar kayanta da yake cikin boot ɗin mota. Ba tare da kunya ko jin nauyin jikinta da ta kasance irin yarannan masu ƙiba ba ta juya da gudu" zuwa gurin motar. """Mal Musa jakar kayana da wayata a cikin mota.""" Ta faɗa da ƙarfi kuma cikin karaɗin da yasa hatta Hafiz sai da ya tsaya a inda yake ya waiga yana kallonta. """Wawuya kawai.""" Ya faɗa a fili haɗe da jan tsaki ganin irin gudun da take yi. """Afuwan ranki ya daɗe. Ai da ma kin shiga daga ciki sai in ɗauko miki jakar kayan naki.""" "Mal Musa ya faɗa cikin girmamawa, domin tun a ƙauye yasan matsayinta a gurin maigidansa yanzu tudu" biyu ne. "Dariya ne ya kamata ganin yadda yayi mata magana, har da wani ɗan durƙusa mata irin bayar da girman" "nan. Duk yadda ta so fuskewa ta ci magani kasawa tayi, sai da ta ɗanyi dariya kafin ta ce" """Ka ga Mal Musa, ni fa ba wata baƙuwar zafi ba ce. Kar ka wani ɗaura min girman da ko kusa bazan iya" "ɗauka ba. Buɗe min mota kawai in ɗauki wayata da jakar kayana.""" "Yana buɗe boot ɗin motar, bata tsaya jiranshi ya ciro jakar kayan ba da sauri ta ciro abarta, ta buɗe" "gidan baya na motar ta ɗauki wayar da Aunty Balira ta bata sannan ta nufi ɓangaren masu gidan. Idan tayi taku ɗaya, biyu, sai ta waiga ta kalli hanyar ɓangaren BQ inda aka sauke su ita da Innaye." Haka kawai tsoro ya mamaye zuciyarta """Allah yasa dai ba a can ɓangaren za su ce in zauna ni kaɗai ba.""" "Tayi addu'ar a fili, zuciyarta cike da tsoro." """Taɓ! Ai Wallahi idan Yaya ya ce in koma can ni kaɗai bazan je ba, sai dai yasa a maidani Faƙo, haka" "kawai ni kaɗai ƙwal kamar mayya za su tura can gurin? Taɓ! Bazai yiwu ba.""" Ta sake faɗa a fili tana ɗan murguɗa baki kamar Yayan yana gabanta. "A daidai lokacin ta isa ƙofar shiga ɓangaren masu gidan, bata tsaya wani ƙwanƙwasawa ba kawai ta" "murɗa hannun ƙofar tare da cusa kanta cikin falon, bakinta ɗauke da siririyar sallama." "Cak! Taja ta tsaya tana ƙare ma tanƙamemen falon kallo, babu kowa a ciki. Matsanancin mamaki ne ya" "kamata ganin gaba ɗaya falon an canza kayan ciki da ta sani, wasu tsadaddun setin kujerun aka canja da kayayyakin more rayuwa kala daban-daban. Duk da daman can falon mai bala'in kyau ne, amma yanzu" sai taga ya ƙara ninka kyau fiye da yadda ta san shi a baya. Ga kuma wasu tanƙama-tanƙaman hotunan Yayanta da Anty Bintu da jaririnsu da aka kafa a kusurwoyin "falon. Saboda tsabar ƙauyanci bata san sa'adda ta saki jakar kayanta a tsakiyar falon ba, ta fara zagayawa" a hankali tana ɗan tattaɓa abubuwan kwalliyan da tunda aka haife ta bata taɓa ganin irinsu ba. "Baza ta ce ga iya adadin mintunan da ta ɓata tana kallon ƙauyancin ba, kafin daga bisani ta tsaya gurin" wani ƙaton hoton Jariri Aadil da yayi kyau sosai kuma ya fito fes a cikin hoton kamar ɗan turawa. A "hankali ta miƙa hannunta ta taɓa fuskarsa a cikin hoton, ita kaɗai sai sakin murmushi take yi tana shafa fuskarsa kamar a gaske shi take shafawa." "Allah ya sani tana son yara, musamman yara masu kyawu tun suna jarirai, shiyasa ko a maƙwafta in dai" aka haifi yaro ko yarinya kyakkyawa ta dinga jelar ɗauko yaron yana yini a gurinta kenan. """Keh! Wace ce ke?""" Saukar gigitaccen tsawa da tambayar Bintu a kunnuwanta yasa ta ɗauke hannunta a jikin hoton da sauri "tare da waigawa baya a tsorace. Da yake ta ba hanyar saukowa daga matattakalar baya ne, shi yasa tun" daga saman benen bayanta kawai Bintu take hange ba tare da sanin ko wacece ba sai yanzu da ta juyo suka yi ido biyu. "Da maɗaukakin mamaki sosai a fuskar Bintu take kallonta, domin ko da suɓutar baki Hafiz bai faɗa mata" tare da Zulaikha yake ba. Farin cikin ganin kyakkyawar zinariyar matarsa da ɗansa mafi soyuwa a zuciyarsa ya mantar da shi duk irin ɗunbin damuwar da ya kwana ya yini da shi. Tunda suka haura sama wanka kawai yayi suka yi musayar sumbata da rungumemeniya tsakaninsa da matarsa ya ɗauki ɗansa yana ta mishi wasa kamar wani babba. Saukowar nan da Bintu tayi ma ta sauko ne da nufin ta ɗauko mishi abubuwan motsa baki kafin ta ƙarasa mishi abinci ashe rabon tayi tozali da ɓacin rai ne. "Yo ɓacin rai mana, idan ba ɓacin rai da takaici ba me zai kawo Zulai gidanta a irin wannan lokacin bayan" ko sati gayyar na'ayyen danginsa basu yi da komawa can ƙauye daga taron sunan da suka zo ba. """Ke ce?""" Ta tambayi Zulai da murya mai bayyana fushi ƙarara tana harhaɗe girar sama da ƙasa. """Me ya kawo ki gidana?""" Ta sake tambayarta a tsawace ba tare da ta jira amsar tambayar farko ba. "Ƙasa-ƙasa Zulaikha ta galla mata harara, zuciyarta cike da tunanin irin cin kashin da Bintun tayi musu" wancan karon zuwansu gidan ita da Innaye. Tana kuma ayyana lallai wannan karon baza ta taɓa ɗaukar wulaƙanci daga Bintu ko Yayanta ba sai dai duk abinda zai faru ya faru. "Sai da ta kawar da fuskarta gefe ɗaya, da taƙama-taƙama a muryarta ta amsa ma Bintu da cewa" """Gidan Yayana dai. Kuma tare da shi muke tafe, abinda baki gane ba shi za ki je ki tambaya ba ni ba.""" "[1/21, 8:22 PM] Fareeda Abdallah: Har ta buɗe baki za ta yi magana, sai kuma ta katse maganar ta" "hanyar jan ƙaƙƙarfan tsaki. Da sassarfa ta juya ta fara haura matakalar benen bibiyu ranta yana ƙara ɓaci, har ta isa ɗakin Hafiz. Tsabar yadda ganin Zulaikha ya tunzurata ta ma kasa tsayawa ta rage girman ɓacin ran da ke bayyane ƙarara a fuskarta, ko kuma tayi ƙoƙarin saisaita yanayin kalaman bakinta." """Hafiz? Zulai na gani a falo? Me ya kawo ta gidana?""" "Ta tambayeshi cikin ɗaga murya ba tare da damuwa da barcin da taga ya fara yi ba, Aadil na kife a" ƙirjinshi shi ma yana barci. "Kamar a mafarki, haka muryarta ya sauka a kunnuwanshi da wani irin tsawa-tsawa. A hankali ya buɗe" idanunsa da suka fara canja launi saboda gajiya da kuma barcin da ya fara ɗaukarsa. """Me kika ce Sweetheart?""" "Ya tambayeta a nutse, a ƙoƙarinsa na ƙaryata zuciyarsa da take ta raya mishi kamar fa ɓacin rai yake gani" a fuskar Bintu kuma tsawa tayi mishi yayin magana don kawai ta ga Zulai ƙanwarsa a cikin gidan. Wai a hakan ma don bata san matsayin Zulai a gare shi ya ƙara sama daga ƙanwa zuwa mata ba. """Zulai na gani a falo. Na tambayeta me ya kawo ta tace min in tambaye ka. Shi ne nake neman sanin" "abinda ya kawo ta da ƙaton jakar kaya bayan ko sati ɗaya ba'ayi da su Aunty Balira suka koma ba...""" """Don su Aunty Balira sun zo suna sun koma wata a cikin dangina ba ta da ikon zuwa bayansu?""" "Ya katse ta da tambayar tun kafin ta aje numfashin maganarta, mamaki mai girma bayyane akan" fuskarsa. "Suuu tayi a tsaye guri ɗaya, sai da yayi mata wannan tambayar ne yasa ta jin kamar fa ta kwafsa a" "yanayin yadda ta zo mishi da ƙorafin. Narai-narai tayi da idanunta kamar za ta saka kuka, muryarta a raunane ta amsa da" """A'a ba haka bane. Kawai dai na yi mamaki ne.""" Har ta yi shiru sai ta ƙara da """Kuma dai My dear sanin kanka ne Zulai ba ta wani ƙaunata, ba shiri muke yi ba. Saboda Allah sai ka" "rasa wacce za ka ɗauko ta kwana biyu a gidannan sai ita? Ka sani sarai ni raini ne ba na so... Amma idan maganganuna sun ɓata rai Allah ya baka haƙuri.""" "Shar... hawaye suka sauko daga idanunta, a sanyaye ta juya za ta fice daga ɗakin." Bata san sa'adda ya kwantar da Aadil akan gado ba sai ji kawai tayi ya riƙo hannunta na dama. Ko kafin "tayi wani yunƙuri har ya kwantar da ita a ƙirjinsa, a tausashe, ya fara shafa bayanta alaman rarrashi." "Ita kuwa hawaye ne suka ɓalle mata kamar an buɗe famfo, sai tsiyayar da su take yi a ƙirjinsa zuciyarta" "na ƙara zafi. A yadda take ji, kamar ta buɗe baki tayi ta kwarma ihu ko za ta samu sauƙin damuwarta" amma babu hali. "Allah ya sani, ta tsani mu'amala ta kusa ko ta nesa ya dinga haɗa ta da dangi da iyayen Hafiz. Wai me" "yasa baza su sakar mata mara tayi walwalarta bane tunda dai shi da ya kasance dolen-dole a gare su yana zuwa can ƙauyen? Da gangar tun bayan komawar Innaye ƙauyen ta ƙi zuwa, duk sa'adda ta ji ya fara zancen zai je duba iyayensa za ta fake da laulayin ciki, ko kuma ta ce cikinta baiyi ƙwari ba a matsayinta na likita baza ta iya jure doguwar tafiya a cikin mota ba don gudun abinda zai je yazo wanda" ba'a fata. Shi kuma da yake Allah ya jarabce shi da masifaffen son cikin haka yai ta mata uzuri bai taɓa matsa mata "ba har Allah ya sauke ta lafiya. Kullum idan yaje, da irin uzurin da zai ƙirƙira ya faɗa ma iyayen a matsayin abinda ya hana Bintu zuwa duba Innaye. Su kuwa da yake dattawan arziki ne ko a fuska basu taɓa nuna" "mishi ɓacin ran rashin zuwan nata ba, tunda dai shi da yake nasu yana zuwa akai-akai, to Alhamdulillahi." """Beb kukan kuma na menene?""" Ya tambayeta da mamaki bayan ya ɗago fuskarta yaga hawaye kaca-kaca har ta jiƙa mishi gaban lallausar rigar shan iskar da take jikinsa. Sai da ta ja shessheƙa kafin ta iya danne zuciyarta ta amsa da """Damuwar yadda na ɓata maka rai daga dawowarka ne My Dear... Kayi haƙuri don Allah ka ji?""" Ta bashi haƙurin a shagwaɓe. Kafin ya amsa ta ƙara da cewa """Kuma zuciyata cike take da tsoron irin zaman da za muyi da Zulai, Allah yasa bata zo da nufin sauke" "min kwando-kwando na rashin kunyarta ba, domin ko yanzu daga tambayarta a mutunce baka ga wata uwar harara da ta aiko min ba...""" """Zan ja mata kunne sosai, ko kusa bata isa ta ce za ta maimaita iskancin da tayi mana lokacin zuwansu" "da Innaye ba. A gabanki zan gargaɗeta.""" "Ya faɗa a tausashe, zuciyarsa na ta canki-cankar ya faɗa mata matsayin Zulai a gare shi yanzu ko kuma ya" bari sai can gaba? Duk da dai maganar da Innaye tayi mishi na bata yarda ya ɓoye ma Bintu matsayin Zulaikha a gare shi ba yana ta bugun can ƙasan zuciyarsa. """Shi kenan My dear. Ina mata barka da zuwa. Bari in je in kawo maka abin motsa baki.""" Ta faɗa da sanyin murya bayan ta goge hawayen fuskarta tsaf! Har ta kama hannun ƙofar za ta buɗe ta fita maganarsa yasa ta tsayawa cak! """Baffa ne yace in taho da ita zuwa nan da ki gama wanka, ko wasu ƙananun ayyukan ne sai ta taya ki da" "su, ko kuma rainon Aadil, don ita ɗin gwana ce gurin rainon ƙananun yara.""" "Da shi da yayi ƙaryar don samun maslahar kai da kai, da ita da take saurarensa hankalinta a ɗugunzume," a tare ƙirajensu ya buga daram! "Lumshe idanu tayi tana jan Lahaula walaƙuwwata illah billah a zuciyarta. Ko da ta buɗe ido, bata yarda ta" kalli fuskarsa ba balle yaga yadda wasu sabbin hawaye suka sake cicciko idanunta. Da shaƙaƙƙiyar murya ta ce """Allah sarki Baffa... Ai kuwa na gode sosai... Amma da an barta tunda ga Mashkura (Ƙanwarta) har" "yanzu bata koma gida ba. Amma tunda an zo da ita ma bai ɓaci ba. My dear bari in je in dawo, na bar Zulai a falo ko ruwa ban bata ba.""" Bata jira amsawarsa ba ta wuce da sauri don ma kar ya sake tsayar da ita. Sai da ta tsaya a tsakiyar bene na sharɓi hawaye na cikakkun mintuna uku kafin ta iya ƙarasawa cikin "falon fuskarta a ɗaure tamau. Turus! Ta ja ta tsaya ganin Zulaikha zaune akan kujera ta yi ɗaiɗai," "hannunta riƙe da babbar kwalin madarar hollandia tana ɗaɗɗaka, ko kofi bata samu zarafin ɗaukowa a kicin ba, haka take gwaɓa bakinta a jikin kwalin tana sha babu abinda ya dame ta." """Wani shegen ne yasa ki buɗe min frig ki ɗauki abu ba tare da umarnina ba?""" "Ta tambayi Zulaikha ranta a ɓace. Duk da zamanta akan kujera ya ɓata ma Bintu rai ba kaɗan ba, amma" ganinta tana shan madara hankalinta kwance kamar a ɗakin uwarta ya danne ɓacin ran zamanta akan kujerar. "Kafin Zulaikha ta amsa mata, sai da ta lumshe idanu ta ƙara zuƙar madarar sosai da irin salon cusa" haushin nan sannan ta kalle ta tana murmushi. """Yaya ne fa ya siyo, saboda Allah Aunty Bintu a gidannan da irin matsayin da nake da shi har sai na" "nemi izininki kafin in ɗauki wani abu da nake da tabbacin ɗan'uwana ne ya siyo?""" "Karaf! Maganganun suka sauka a kunnen Hafiz da yake saukowa daga bene. Ranshi a ɓace, ya daka ma" "Zulaikha wani gigitaccen tsawan da yasa ta yarda kwalin madarar ba shiri, a tsorace ta ɗaga idanu tana" kallonsa ƙirjinta na bugawa akai akai har ya ƙarasa saukowa daga benen. Kai tsaye gurinta ya nufo kamar zai rufe ta da duka ya tsaya a kanta yana huci """Sa'arki ce ita da za ki dinga faɗa mata maganar banza? Yi maza ki ba ta haƙuri kafin in tattaka ki anan" "gurin""" "A tsorace, ta ɗaga idanu ta sake kallonsa. Ganin yadda yake zazzare mata idanu kamar zai haɗiye ta yasa" da saurin gaske ta kawar da idanunta ta mayar kan Bintu da take tsaye a bayansa hannayenta harɗe a "ƙirji, da alamun al'amarin ba ƙaramin daɗi yayi mata ba. Domin idan ba idanun Zulaikha ke mata gizo ba sai taga kamar murmushi Bintu take yi." A tsorace da salon kare kai ta fara magana bakinta na rawa """Yaya ita ce fa...""" """Na tambaye ki ƙarin bayani?""" Ya katse ta cikin tsawa. """Za kiyi abinda na umarce ki ko sai na tattaka ki a tsakiyar falon nan?""" "Lokaci ɗaya itama ranta ya ɓaci, a ganinta wannan ai rashin adalci ne ƙarara. Taya zai yanke hukunci kai" "tsaye ba tare da jin dalilin da yasa ta mayar ma da Bintu baƙar magana ba? Har ta tsuke baki alamun baza ta ba Bintu haƙurin ba, sai dai duk abinda zayyi yayi, idan yaso ya kashe ta." Sai kuma wani sashe na zuciyarta ya tunasar da ita matsayin Yayan yanzu a gurinta. Ƙin aikata abinda ya umarceta matuƙar ba saɓon Allah bane kamar ta gayyato ma kanta tsinuwar mala'ikun rahama ne. """Kiyi haƙuri.""" Ta faɗa cikin fushi bakinta a zumɓure. Guri ya nema ya zauna kan ɗaya daga cikin kujerun falon ya fara zazzaga mata faɗa ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Da alamun haushin abinda ya faru da shi a ƙauye yake son saukewa a kanta bayan ba ita ta kar zomon ba. """Bazai yiwu ba. Bazan taɓa yarda da irin wannan rainin da iskancin da kika saba yi mana ba. Idan ma za" "ki saka ma kanki nutsuwa da karatun ta nutsu gara ki saka, tun wuri gara ki sauke duk wani rawar kai da wani gigi da yake damunki, idan ba haka ba na rantse da Allah ba ƙaramin wahala za ki sha da ni a gidannan ba." "Ko ban faɗa ba ke kanki kin sani, ta ko wane ɓangare na rayuwa matata gaba take da ke. Ta sha gabanki" "fiye da yadda kike tsammani, in dai kika ce raini da tsaurin idanu za ki nuna mata, lallai kuwa zan kawar da duk wata sanayya da dangantaka in koya miki hankali fiye da yadda kike tsammani...""" "Bai san Zulaikha kuka take yi ba, sai da ya ji shessheƙarta ya cika falon. Duk da haka bai sassauta faɗan" "da yake yi ba, sai ma ƙara caccaɓa mata baƙaƙen maganganu yake yi kamar bai san daga inda ta fito ba, duk da sunan ƙwaƙƙwaran kashaidi da jan kunnen ta kiyaye irin zaman da za tayi a gidansa da kuma" iyalinsa. "Bintu da matsanancin farin ciki ya gama ƙume ta, kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha take ji. Sai da ya daɗe" "yana cin zarafin Zulaikha ita kuma tana ta rusa kuka kafin a yangace ta ƙarasa inda yake zaune, akan cinyarsa ta zauna, ta ɓalle maɓallai biyu na gaban rigarsa ta fara shafa ƙirjinsa ba tare da kunyar idanun Zulaikha ba." """Ayya mana My dear... don ɗan wannan abin da ya faru ne kake ɓata ranka haka? Ka san fa halin Zulai" "ciki da waje, ni kawai ina mata uzuri ne saboda har yanzu yarinya ce, da ƙuruciya a kanta. Kayi shiru haka" "pls, ka ga da gajiya a jikinka har yanzu, kar ka bari abinda bai kai ya kawo ba ya taɓa min zuciyata.""" "Shiru yayi yana mayar da numfashi, da alamun maganganunta ba ƙaramin taɓa shi suka yi ba." Bintu kuwa mayar da hankalinta kan Zulai da har lokacin take kuka tayi da wadataccen murmushi a fuskarta. """Kin ga Zulai yi shiru, share hawayenki. Daga waɗannan maganganun na Yayanki dai ya isa yasa ki" "hankalta, ki san yanzu fa ba da bane. Idan wancan karon ganin idanun Innaye yasa kin tsula tsiyarki yadda kike so wannan karon baza kiyi ki ci riba ba. Ɗauki jakarki ki tafi can ɓangaren da kuke sauka ki yi wanka ki huta, gurin a share yake a goge, tun bayan tafiyar su Aunty Balira da aka gyara ba na jin yanzu" "ya sake yin ƙurar da zai sa ki sabon shara.""" "[1/23, 10:25 PM] Fareeda Abdallah: Duk baƙaƙen maganganun da take yaɓa ma Zulaikha a fakaice tana" "jin ta, kuma tsaf ta fahimci saƙon da take aika mata. Amma a madadin ta miƙe ta aikata umarnin da Bintu tayi mata, sai kawai ta ƙara gyara zama ta cigaba da kukan da take yi." """Au! Faɗan Yayan naki bai ishe ki ba kenan ko? Ki tashi ki tafi masaukinku na ce tun kafin ranshi ya ƙara" "ɓaci...""" Cikin ɓacin rai da muryar kuka Zulaikha ta katse Bintu da cewa """Ni fa bazan zauna acan ɓangaren ni kaɗai ba. Tun a gida ma ai Innaye cewa tayi a matsayina na...""" """Wa ya tambaye ki wani matsayi da kike da shi a gidannan? Za ki rufe mana baki a gurin nan ko sai na" "ɗora hannu a jikinki?""" Hafiz ya katse ta da saurin gaske tun kafin ta ƙarasa ɓaram-ɓaramar da take niyyar yi. Sunkuyar da kai ƙasa tayi ta cigaba da jan shessheƙar kuka. Ba ta ma da niyyar tashi ta ɗauki jakarta balle "har Bintu ta saka ran za ta aikata abinda ta umarce ta. A mamakance, Bintu take kallon Hafiz, sai kuma ta kalli Zulaikha. Duk ga zatonta cikin tsawa da faɗa zai sake balbale Zulai da umarnin ta tashi ta tafi can ɓangaren da suke sauka." "Amma a madadin ta ji ya faɗi abinda take tsammani, sai kunnuwanta suka jiyo mata kalamansa kamar" saukar aradu yana ce mata """Sweetheart! Ki ƙyale ta anan. Kin ga ita kaɗai ce, can ɓangaren baƙi yayi mata girma, baza ta iya zama" "ita kaɗai acan ba. Tunda ga Mashku anan sai su zauna a ɗaki ɗaya...""" """Bazai yiwu ba gaskiya My Dear. Mashku ko a gida ba ta yarda ta haɗa ɗaki da su Amina ƙannenta" "ballantana ta haɗa da wacce bata sani ba. Tunda akwai wadatar ɗakuna anan ɗin, ita ma sai ta ɗauki ɗaki ɗaya tayi amfani da shi. Excuse me pls! Bari in duba girki.""" Ta miƙe daga jikinshi da sauri ba tare da jiran abinda zai sake cewa ba. "Da haka aka bar maganar saukar Zulaikha a can ɗakunan BQ. Shi da kanshi ya tashi, yaje ya buɗe mata" "ɗaya daga cikin ƙayatattun ɗakunan da suke nan ƙasa, sannan ya koma gurinta fuskarsa a ɗaure ya umarci ta ɗauki jakarta zuwa cikin ɗakin." "Tana shiga, ya mayar da ƙofar ya rufe, kusa da inda take tsaye ya ƙarasa a bazata ya damƙo kunnenta na" "dama da yake cikin hijabi ya murɗa, a gigice ta buɗe baki za ta ƙwallah ihu da saurin gaske ya toshe mata" baki bayan ya saki kunnen da sauri. """Kin san Allah? Muddin kika yi gangancin faɗa ma matata an ɗaura mana aure da ke acan gida na" "rantse sai na ɓatar da ke a cikin garin nan, sai dai duk abinda zai faru ya faru.""" "Cizon da ta gantsara mishi a tafin hannu yasa shi sakin bakinta da sauri ya matsa baya yana yarfe hannu," ga dukkan alamu ya ji zafi sosai. """Cizo na kika yi?""" Ya tambayeta fuskarsa a ɗaure. """Eh ɗin""" "Ta amsa a tsiwace, zuciyarta cike fam da takaicinsa." """Kuma na rantse da Allah idan ka sake min irin wannan cin mutuncin a gaban matarka sai na kira Baffa" "da Innaye na faɗa musu duk irin wulaƙancin da kake min tunda kazo da ni garinnan.""" "A fusace ya miƙa hannu zai damƙo ta. Da mugun sauri ta zille masa, sannan ta ƙwalla wani gigitaccen" ihun da yasa ba shiri ya fice daga ɗakin da saurin gaske jin da yayi karaɗin ihun na barazanar toshe mishi dodon kunne. A guje Bintu ta fito daga ƙaramin kicin ɗinta suka yi kiciɓis da shi a tsakiyar falon. """Lafiya ? Ihun me nake ji? Kar dai ace dukanta kayi?""" Bintu ta tambaye shi da damuwa a fuskarta. A zuciyarta kuma addu'a take yi Allah yasa dukan Zulaikha yayi. """Yarinyar ba ta da kunya Sweetheart. Idan ba taɓa lafiyarta nayi ba baza ta shiga taitayinta ba. Bari in" "je ɗaki, ki kawo min abincina sama.""" Yana gama faɗin haka ya fara hawa matakalar sauri-sauri. Zuciyarsa cike da damuwa da ƙuncin aura mishi Zulaikha da aka yi. "Gaba ɗaya kanshi ya kulle, ya ma rasa ta ina ya kamata ya ɓullo ma al'amarin? Ga shi ya rasa hanyar da" zai bi wajen sanar ma da Bintu yanzu matsayin mata Zulaikha take a gurinsa. Domin bai manta irin alƙawurran da suka ɗauka ma junansu kafin aure da kuma bayan aure ba. "A alƙawuran da ya ɗauka mata akwai, ita kaɗai ƙwallin ƙwal ta ishe shi rayuwar duniya. Ita kuma kaɗan" "daga cikin alƙawuran da ta ɗauka mishi shi ne ako wane hali wuya ko daɗi za ta kasance tare da shi, za ta bashi ƙololuwar farin ciki fiye da wanda yake tsammanin samu daga gare ta. Za kuma tayi duk iya mai yiwuwa wajen bashi dukkan tarairaya da soyayyar da zai kawar da hankalinshi daga kan ko wace mace" sai ita ƙwallin ƙwal. "To ga shi tun ba'a je ko ina ba an fara samun karya alƙawari daga gare shi, shi kam ya zayyi ne? Ina zai sa" kansa? Kuma ta wace hanya zai ɓullo ma wannan ƙaddararren aure da su Baffa suka ƙulla masa? ****** ****** "Zulaikha mai bala'in son girma sama da ƙasa ta kalle ta, sai kuma ta ɗanyi dariya. Tana jin wani girma na" "ƙara mamayeta, daga yadda ta ga yanayin jikin Mashkura ɗan daidai kamar na Bintu, duk ga tsammaninta bata wuce shekaru goma sha biyar ko sha shida ba." """Uhmmm! Ta ina kika taɓa ganin anyi ƙawance tsakanin ƴar birni da ƴar ƙauye? Sannan kuma ni ba" "yarinya bace fa, na girme ki nesa ba kusa ba, shekaruna sha takwas cif...""" Sassanyar dariyar da Mashkura ta ƙyalƙyale da shi yasa Zulaikha tayi sakalau da baki tana kallonta. Sai da tayi dariyarta ma'ishi kafin ta ce ma Zulaikha """Shekaru sha takwas ne kike faɗin kin girme ni nesa ba kusa ba? To ni shekaruna ashirin da ɗaya," "Wallahi da gaske nake miki. Kawai don kin ganni da ɗan ƙaramin jiki ke kina da ƙiba shi ne kike min kallon ƙaramar yarinya? Sannan in banda ke da abin ki, da ni da nake birni da ke da kike ƙauye ai duk Allah ne ya halicce mu. Babu wacce ta fi wani a gurin Allah sai wacce ta fi tsoronsa. Sannan kuma" "ƙawance ba'a shekaru bane, shekaru lambobi ne kawai. Ni dai don Allah ki karɓi tayin ƙawance na, kin ga," "yanzu ma dai bani lambar wayarki.""" Duk yadda Zulaikha ke zillewa a dole ta saki jiki da Mashku har suka yi musayar lambobin waya. Da yake "Mashku irin yarannan ne da in suna son ka suna so ne da dukkan zuciyarsu, tana da miskilanci amma" idan ta so hira sosai take sakin jikinta tayi har da ƙyaƙyata dariya. Balle kuma ta haɗu da Zulaikha ga "barkwanci ga wauta, cikin ƙanƙanin lokaci shaƙuwa ta shiga tsakaninsu." "Yadda suka bararraje a tsakiyar gadon suna hira da dariya, kamar sun daɗe da sanin juna. Har Mashkura" "ta fice zuwa kicin ta haɗo musu tea mai kauri a kofuna biyu, suna sha suna hira." "A daren, Mashkura ta tura ma Zulaikha fina-finai masu yawa a cikin wayarta. Sannan ta ƙara da wayar" "mata da kai kan yadda ake amfani da wayar Android, ta kuma koya mata games ɗin da ta tura mata masu daɗi da za su taimaka gurin ɗebe mata kewa da zaman kaɗaita." "Tunda ita Mashkura ba zaman gidan sosai ta cika yi ba, kullum da safe takwas zuwa tara na safe take" ficewa zuwa makaranta. Ba tare da kunya ko wani kwana-kwana ba Zulaikha ta faɗa ma Mashkura ita fa ba ta jin turanci. """Kin san karatunmu na ƙauye, ba ɗaya ne da naku na birni ba. Sai dai na iya karatun hausa fiye da" "yadda kike tsammani, turancin ne dai ƴan ƙananun kalmomi kawai nake iya ji in fahimci abinda ake nufi.""" """Kar ki damu. Don wannan ai ba wata matsala bace. Sannu a hankali zan tsara mana jadawalin da za mu" "dinga bi ina koyar da ke abubuwa masu yawa, idan kika mayar da hankali kuma kika nace cikin wata uku bakinki zai goge da turanci kamar ƙanwar mangwafak! Kin san shi karatu naci yake so, sannan kuma hausa ya fi turanci wahalar koyo, tunda kika iya karatun hausa, turanci bazai wahalar da ke ba in Allah ya" "yarda.""" Maganganun Mashkura ba ƙaramin daɗaɗa ma Zulaikha rai suka yi ba. Sai godiya take zuba mata kamar "ma har ta iya turancin. Allah ya sani a yanzu ba ƙaramin son ta koyi turanci take yi ba. Ta iya a baki, idan" "an faɗa ta san me aka ce, kuma ta iya mayar da martani da yaren turanci, sannan idan ta gani a rubuce ta karanta ta kuma fahimci me ake nufi." "Idan ta iya waɗannan, ɗaya daga cikin manyan burikanta sun cika. A da can baya bata taɓa damuwa da" "koyon turancin ba, bata ma ɗauke shi a wani kayan gabas ba. Sai bayan shigowar Bintu cikin ahalinsu ne" ta gane lallai fa ta tafka kuskure rashin mayar da hankalinta a karatun boko. Ba ma kamar yadda minti "ɗaya biyu Bintu take goranta mata da munanan kalmomi kamar jahila, daƙiƙiya, baƙauyiya, wawuya, a" "ganinta, rashin iya turancin shi ke sa Bintu goranta mata da waɗannan munanan kalmomin." Mashkura bata bar ɗakin ba sai misalin ƙarfe ɗaya da minti arba'in na dare. Sun rabu duk su biyun zukatansu cike da farin cikin hirar da ta gudana a tsakaninsu. "Har Zulaikha ta kwanta, ta ɗaga hannu za ta fara karanto addu'ar barci kenan sai ga Mashkura ta sake" shiga cikin ɗakin bakinta ɗauke da siririyar sallama. """Kiyi haƙuri da ni Ƙawata. Yau dai na hana ki barci.""" "Ta faɗa tana murmushi. Kayayyaki masu ɗan dama da suke riƙe a hannunta ne ta zube su a gefen gadon," "ta fara ɗaɗɗaga su ɗaya bayan ɗaya. Kayan barci ne masu kyau da laushi sosai a ido har kala uku, riga da" "wando biyu, sai kuma riga ƴar ciki da ta samanta guda ɗaya. Sai kuma Abaya sababbi masu kyau sosai kala uku." """Ban san ko nayi miki karambani ba. Allah yasa dai kina saka kwance, duk da dai kamar sabbi suke a" "gurina. Domin bayan sau ɗai-ɗai ban ƙara saka su ba. Na kawo miki ne ko kina so, na ga manya ne, za" "suyi daidai da jikinki.""" "Tsananin murna da farin ciki, yasa Zulaikha ta kasa cewa komai. Lokaci ɗaya tayi ƙwal-ƙwal da idanunta," can kuma sai ga hawaye shar... sun zubo daga kwarmin idanuwanta. Lallai sai a yanzu ta ƙara yarda da maganar Mashku da ta ce ba halinsu ɗaya da Bintu ba. Ashe haka Allah ke ikonsa dare ɗaya ya haɗa ƙauna a zukatan bayinsa? """Na gode Mashku. Na gode, Allah yabar ƙauna da zumunci.""" "Kalaman da take ta maimaitawa kenan cikin kuka da dariya, sai ɗaɗɗaga kayan take yi tana jinjina" kyawunsu a idanunta. "Ko Mashku bata faɗa ba, daga yanayin kyawun kayan sun isa su bayyana maka masu tsada ne sosai. In" dai ba ta manta ba za ta iya rantsewa da Allah ba'a taɓa yi mata kyautar kaya irin haka kuma daga bare wacce basu haɗa komai da ita ba. """Don Allah ki daina hawayen nan da kike yi. Miye don na baki ɗan waƴannan kayan? Ba komai bane fa," "kuma don ma yanayin jikinmu ba ɗaya bane ai Wallahi da sai na haɗa miki akwati guda. Ni kin ga ma tafiyata tunda baza ki daina kuka ba. Allah ya tashe mu lafiya.""" "Da sauri ta fice daga ɗakin taja mata ƙofa, fuskarta yalwace da farin ciki." "Ko bayan fitar Mashku, ta daɗe bata yi barci ba. Bayan ta gama matsar ƙwallar da take yi murza key tayi" a ƙofar ɗakin ta kulle. Ta canja ƙwan lantarki zuwa mai haske ta fara gwada kayan ɗaya bayan ɗaya. "Wani ikon Allah kamar da man can kayan domin ita aka siya. Sunyi mata dai-dai, kuma sunyi mata a" "wadace, basu yi kaɗan ba sannan basu yi mata yawa yadda take saka manyan riguna ba. Ba ma kamar Abayoyin nan, sai ta fito shar a ciki kamar wata balarabiya, kasancewar tana da hasken fata." Saboda murnar ganin yadda tayi kyau sai juyi take yi a gaban madubi tana ƙyalƙyala dariya ita kaɗai a "cikin ɗaki. Gaba ɗaya ta manta da damuwar Bintu, Hafiz da wani ƙaddararren aurensa da aka ɗaura mata." """Ashe daman haka nake da kyau?""" Ta tambayi kanta a fili tana dariya. """Gaskiya daga yanzu zan zo nima in koyi gayu ko gurin Mashkura. Kuma bazan sake yarda Innar Hadiza" (Telarta acan Faƙo) tayi min burguza-burguzan ɗinkunan nan da take min ba. Ƴan cas-cas za ta dinga min "irinna ƴan gayu, musamman ma dai yanzu da zan koyi turanci. Ta sake ƙyalƙyalewa da dariya tana shafa ƴan yiri-yirin kitson da suke kanta." "Ko da ta cire kayan naɗe su tayi tsaf ta shirya su can ƙasan jakar kayanta, sannan ta mayar da sauran" "kayan ta rufe zip ɗin jakar. Kafin ta kwanta, ƙarfe uku saura minti goma sha biyar. Da yake tana cikin" farin ciki ga bashin barcin da yake kanta bata daɗe ba nannauyan barci yayi awon gaba da ita. "Sabo da yin sallar asubah akan lokacinta shi ya tasar da ita, daƙyar ta iya miƙewa bayan ta yi salati da" addu'o'i tana tangaɗi ta faɗa banɗaki. Alwala da ruwa mai ɗumi da tayi shi ya taimaka mata gurin dawowa hayyacinta. Ko da ta koma cikin "ɗakin, kafin ta kwanta sai da ta murza makullin ƙofar ɗakin ta buɗe, sannan ta saka babban hijabi ta" tayar da sallah. Bayan ta idar tana cikin yin azkhar kamar yadda ta saba nannauyan barci ya sake yin awon gaba da ita nan kan daddumar da tayi sallah. ***** ***** "Ƙirjinta ne ya buga daram!! Ganin kiran Innaye na shigowa cikin wayarta, abinda bai taɓa faruwa ba tun" bayan musayar lambar waya tsakaninta da Innaye matsayinta na Uwar mijinta. "Matsanancin tsoro ne ya lulluɓeta, ƙirjinta ya cigaba da bugawa akai-akai. Kamar baza ta ɗaga kiran ba," domin duk a tsammaninta Zulaikha ce ta kira Innaye ta kai mata ƙararta. Har kiran farko ya tsinke na biyu ya sake shigowa tana canki-cankar ta ɗaga ko kar ta ɗaga kiran? Tunanin idan bata ɗauka ba Innaye za ta iya kiran Hafizu ta kora mishi kashaidi zuwa gare ta yasa tayi "shahadar ƙuda ta ɗaga kiran, a zuciyarta take tunanin yaushe rabonta da magana da Innaye ko da ta waya ne balle har suyi ido biyu?" """Barka da safiya Innaye, ina kwana? Da fatan duk kun tashi lafiya?""" Tayi saurin miƙa gaisuwa bayan ta yi sallama da ƴar karkarwa a muryarta kamar tana gaban Innaye. """Lafiya ƙalau Fatima. Ya wanka?""" Innaye ta tambayeta a nutse. Bayan ta amsa da lafiya lau daga can ɓangaren Innaye sake gyara zama tayi akan daddumar da ta idar da sallar walha. Cikin nutsuwa ta sake jefa ma Bintu tambayar da shi ne ƙwaƙƙwaran dalilin da yasa ita da kanta ta ɗaga waya ta kira Bintu ba saƙo ba. """Am nace ba? Ina fatan dai Hafizu ya faɗa miki matsayin da Zulai take da shi yanzu a gurinsa?""" """Eh ya faɗa min. Ya ce za ta taya ni ƴan aikace-aikace har zuwa sadda zan gama wanka.""" "Bintu ta amsa kai tsaye, ba tare da tunanin komai a tambayar da Innaye tayi mata ba." """Uhmmm!""" "Innaye ta faɗa daga can ɓangarenta, fuskarta bayyane da ɗan mamaki kaɗan, domin daman ta yi tunanin" "hakan zai iya faruwa. Ta daɗe da fahimtar idan al'amari ya biyo ta ɓangaren Bintu kamar dai Hafiz tsoronta yake ji. Shi yasa ta kira da kanta don ta faɗa ma Bintu yanzu Zulai matsayin matar Hafiz take, kuma tayi mata ƙwaƙƙaran jan kunne kan kar ta kuskura ta ce za tayi gigin ci mata amanar Zulai, idan" hakan ya faru da ita da Hafizu za su gamu da mummunar ɓacin ran da basu taɓa tsammani ba. """Shi Hafizun ne yace miki an kai Zulai ne don ta taya ki aiki?""" Kafin ta amsa da zafi-zafi a muryar Innaye ta cigaba da cewa """Ƙarya yake yi, bai faɗa miki gaskiya ba. Yanzu Zulai matsayin matarsa take ta sunnah kamar yadda kike" "matarsa. Shekaran jiya Baffansu ya ɗaura musu aure... Domin ita Zulaikha ba ni na haife ta ba, ɗiyar ƙanwata ce...""" Ɗif! Wayar ta ɗauke daga can ɓangaren Bintu bayan wani ƙaƙƙarfan ihu da ta yanka da yayi barazanar kashe ma Innaye dodon kunne. """Subhanallahi! Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Fatima lafiya kuwa? Me yake faruwa?""" Innaye ta tambaya hankalinta a tashe bayan ta kawar da wayar daga kunnenta saboda amsa kuwwar da "ihun yayi mata a kunne, daga bisani kuma ta mayar da wayar bayan taratsin ihun ya ragu a kunnuwanta. Shi ne har take jera ma Bintu waɗannan tambayoyin, duk a tsammaninta, wani abun ne can na daban ya" ɗaga hankalin Bintu ba maganar da taji daga bakinta ba. "Jin shirun yayi yawa babu amsa daga can ɓangaren yasa ta ciro wayar ta duba, sai a lokacin ta fahimci" "kiran ya tsinke. Hankalinta a tashe ta sake danna kiran lambar Bintu, nan take na'ura ta sanar da ita wayar a kashe take. Amma da yake ba jin abinda ake cewa take yi ba sai da ta kira kamar sau biyar ana" maimaita mata amsa ɗaya sannan ta haƙura da kiran lambar. Da damuwa a fuskarta ta ajiye wayar ta cigaba da lazumin da take yi. 'Idan kuma ya kasance matsanancin kishi ne yasa Bintu ƙwallah ihun da kika ji ta waya fa?' Kwatsam! Wani sashe na zuciyar Innaye ta jefa mata wannan tambayar. """Autata.""" Ta faɗa a fili hankalinta a tashe. """Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un! Auta tana cikin gidan kuma tun ɗazu da Hafizu ya kira ni mu gaisa ko" "da na nemi ya bani Auta ya faɗa min tun safe yana Ofishin shi.""" "Ta sake faɗa a fili, tashin hankalinta na ƙara hauhawa." Sai a lokacin ta tuna ai Balira ta faɗa mata ta ba Auta wayarta ƴar sha-fa ta tafi da shi Habuja. Kenan idan "ta kira lambar Baliran za ta ji a wane hali Autarta take ciki... Ba tare da wani ɓata lokaci ba ta rarumo wayarta ta fara bin lambobi tana neman lambar wayar Balira, wanda aka yi mata saving da alamar ƙwallo a jikin lambar." "Saboda tsananin ruɗewa daƙyar ta iya gano lambar, jikinta na ɗan karkarwa ta danna ma lambar kira. Sai" dai kuma cikin hukuncin Allah kira tayi har sau bakwai bai shiga ba. """Hasbunallahu wa ni'imal wakeel. Ya Allah ka tsare min Zulai aduk inda yake.""" Tayi addu'ar a fili hankalinta a tashe. Zuciyarta cike da fargaba da tsoron irin kishin matan birni da take "jin labari a radio. Matan birni da idan kishinsu ya motsa don su yanke ma namiji mazakuta ba komai bane a gurinsu, tsoronta Allah tsoronta kishi yasa Bintu ƙona mata Auta da tafasasshen ruwan zafi. Domin a irin labaran kishin matan birni da take ji a shirin In da Ranka... wannan ba komai bane." "Da saurin gaske ta lalubo lambar Hafizu mai alamar mota ta danna mishi kira. Yana ɗauka, bata tsaya jan" wani dogon zance ba ta fara kora mishi ƙwaƙƙwaran kashaidi """Hafizu, kabar duk abinda kake yi yanzunnan ka tafi gidanka ka duba min halin da Auta take ciki. Domin" "na kira Bintu na faɗa mata Zulai matarka ce, na ji ta ƙwallah ihu, to ina rantse maka da Allah idan" "mahaukacin kishi yasa Bintu illata min Auta bazan taɓa yafe muku ba har duniya ta naɗe...""" Ɗif! Cajin wayarta ta ɗauke ba tare da ta gama kora ma Hafizu kashaidi ba. "Duk yadda take ta kunna wayar a ƙoƙarinta na sake kiransa, wayar da ta kawo sai ta ɗauke. A zuciye tayi" "cilli da wayar akan gado ta miƙe tsaye tana safa da marwa, bakinta ɗauke da duk wata addu'a da ta zo zuciyarta." A ɓangaren Hafiz ma ko da ya gwada kiran lambar Innaye ya ji swich off! Ya kira lambar Bintu ita ma a "kashe, ya kira lambar Aunty Balira da yake hannun Zulai ita ma ya ji a kashe. Hankalinsa a tashe ya tsallake tarin ayyukan da ke gabansa ya fito daga cikin Ofishinsa ya nufi gida." ***** ***** "Ba ita ta farka ba sai ƙarfe tara da minti biyu na safiya, ganin yadda garin ya waye sosai yasa ta yin" mamakin irin barcin da tayi akan dadduma. Da sauri ta faɗa banɗaki ta yi wanka ko jikinta ya ƙara warwarewa daga gajiyan da yake tare da ita. Bayan ta fito ne ta lura da wata baƙuwar fallen takarda da aka nannaɗe ajiye a gaban madubi. A hankali ta ƙarasa ta ɗauka. """Mashkura""" Shi ne sunan da ta gani rubuce da manyan baƙi a farkon saƙon. Ɗan murmushi ne ya suɓuce mata kafin ta fara karanta taƙaitaccen rubutacciyar saƙon da ya kasance da hausa ne. "_""Ƙawata, Na shigo mu gaisa sai na ga kina barci. Sanin jiya baki wani samu isasshen barci ba shi yasa" "na kasa samun ƙwarin gwuiwar tashinki. Ki huta lafiya Ƙawata, ni na wuce makaranta. Idan na dawo in" "sha Allah yau za mu fara ɗaukar darussanmu kamar yadda muka tsara. Bye._""" A hankali ta nannaɗe takardar har lokacin murmushin da take yi bai bar kan fuskarta ba. """Allah sarki Mashku. Ubangiji Allah ya dawo min da ke lafiya. Na gode ƙwarai da karamcinki a gare ni.""" "Tayi maganganun a fili. Gefen gado ta ƙarasa ta ɗauki wayarta, sai a lokacin taga wayar a kashe. Ko da ta" "kunna sai taga ashe cajin wayar ce ta ƙare, kuma Aunty Balira bata ba ta cajar wayar ba." "Ɗan ɓata fuska tayi alamun bata ji daɗin haka, wayar da wasiƙar da Mashkura tayi mata ta cusa a aljihun" jakar kayanta sannan ta ciro manshafawarta ta zauna a gaban madubi ta fara shafawa. Zuciyarta cike da tunanin Innaye. Ta so ƙwarai ta kira Innaye yau da safennan su daɗe suna hira. Abinda yasa ta kasa kiran Innaye jiya shi "ne ba ta so ta ƙara ɗaga mata hankali, shi yasa duk yadda take son jin muryarta ta danni zuciyarta har zuwa safiyar yau. Sai kuma ga shi wayar nasara ta yi mata tsiya." Ta gama shiryawa kenan a fisge ta ji kamar an yanka ihu daga can waje. Tsam! Ta tsaida hankalinta guri "ɗaya ta ƙara saurarawa, sai kuma bata sake jin ihun ba. Nannauyan ajiyar zuciya ta sauke, ta ɗauki hijabinta ta zura ta kama hanyar ficewa daga ɗakin a niyyarta na zuwa kicin don sama ma kanta abinda za ta karya da shi." "Hankalinta yayi nisa sosai a tunanin da take yi, kuma baza ta ce ga takamaimai abinda take tunani ba." Sam bata lura da tahowar Bintu a haukace ba sai ji tayi anyi mata wani wawan angiza da yasa lokaci ɗaya tayi taga-taga ta zube a ƙasa. A tsorace ta ɗaga idanu tana kallon Bintu da tayi amfani da wannan damar na faɗin da Zulaikha tayi ta "haye ruwan cikinta tayi mata wani mugun shaƙa, ko da ta kalli cikin idanun Bintu, matsanancin tsoro da firgici ne suka ƙara lulluɓeta ganin yadda idanunta suka kaɗa suka yi jajur." """Munafuka, algunguma, matsiyaciya, tauraruwa mai wutsiya ganinki ba alkhairi ba. Da gaske ne an" "ɗaura miki aure da Mijina Hafiz ko kuwa wancan tsohuwar banzan ƙarya take min?""" Ta ƙarasa da tambayar tana zazzaro ma Zulaikha idanu kamar wacce ta hau aljanu. "[1/28, 7:23 PM] Fareeda Abdallah: Sai a lokacin Zulaikha ta fahimci dalilin haukar Bintu, idanu ta ɗan" runtse jin yadda Bintu take ta ƙara tattare hijabinta da wuyanta tana ƙara shaƙo ta da hannayenta duk biyu. Lokaci ɗaya kuma tana ƙara maimaita mata tambayar cikin tsawa da ɗaga murya """Za ki amsa min tambayar da nake miki ko sai na illata ki? Da gaske ne ƙiyayyar da matsiyata kuma" ƙauyawan iyayenku suke min ya kai matsayin da yasa suka aura ma mijina ke ko ƙarya tsohuwar banzan "nan take min?""" Da ɓacin ran yadda Bintu take ta furta kalaman tozarci ga iyayensu saboda mahaukacin kishi da ya rufe mata idanu yasa ta amsa mata tambayar ita ma cikin tsawa da ɗaga murya. """Eh! Da gaske ne. Shekaran jiya an ɗaura aure na da Yaya Hafiz. Idan kina da abinda za kiyi ko kuma kin" "isa kiyi wani abu sai kiyi.""" "Tana gama faɗin haka da ƙarfi tasa hannuwanta biyu ta ɓamɓare hannayen Bintu daga wuyanta, tayi" kukan kura ta wancakalar da Bintu daga ruwan cikinta ta miƙe tsaye a zafafe. """Ke jaka kuma dabbar ina ce da za ki dinga zagin tsofaffin da suka zama silar zuwan mijin da kike" "taƙama da shi duniya? Ko kina tunanin tsoronki suke ji da za su zuba ido kiyi ta wulaƙanta su a gidan ɗan da suka haifa da cikinsu? Wannan auren ba kowa ne ya janyo shi ba face ke da kanki, baƙin halinki da mugun halinki na dabbobi yasa suka nema ma kansu mafita ta hanyar ɗaura ma ɗansu aure da ni. Domin sun san duk tsiya ni bazan taɓa wulaƙanta su ba, ranar naka sai naka... ko sun fi haka ƙauyanci da jahilcin" "da kike kira bazan taɓa tozarta su ko in banbanta su da nawa iyayen ba...""" "A haukace, Bintu ta sake ƙwallah wani gigitaccen ihu a karo na biyu. Kalaman Zulaikha kamar zuban" tafasasshiyar dalma haka suke sauka a kunnuwanta zuwa ƙwaƙwalwarta. """Ni za ku ciwa amana??? Ni kike faɗa ma irin waɗannan banzayen maganganun? To na rantse da Allah" "yau ko ni ko ke a gidannan. Zan kashe ki har lahira, in ga uban da ya isa ya tsaya miki duk faɗin tsinannen" "ƙauyen naku da jahilan iyayen naku da kike taƙama da su.""" "Bintu tana gama faɗin haka, da mugun gudu ta nufi cikin babban kicin ɗin ta da yake falon. Ɗaya daga" "cikin sababbin wuƙaƙenta manya masu masifaffen kaifi waɗanda bata taɓa amfani da su ba ta ɗauka, ta sake ficewa da gudun gaske." "Zulaikha da take tsaye hannuwa riƙe da ƙuƙumi tana huci duk ga tsammaninta Bintu taɓarya za ta ɗauko," shi yasa ta tsaya domin ta gwada mata idan hauka da ɗanyen kai take ji ta dame ta ta shanye. "Hango wuƙar da ke ƙyalli a hannun Bintu yasa ta zare ido, bata tsaya raba ɗayan biyu ba ta juya da gudu" "zuwa ɗakin da aka yi mata masauki, tana shiga ta danno ƙofar Bintu ta isa gurin. Daƙyar ta samu nasarar murza makullin ƙofar daga can ciki ta kulle tana numfarfarshi." "Bintu a haukace ta kai ma ƙofar wani wawan suka da wuƙar hannunta, amma da yake dakakkiyar ƙofa ce" mai tsada ɗan karcewa kaɗan jikin ƙofar tayi. """Ashe ke ƙaramar mara kunya ce? Jaka, kucakar ƙauye dabba, na rantse da Allah yau sai na ga bayanki" "a gidannan. Zan nuna miki mijina nawa ne ni kaɗai, ko da macen birni ƴar gayu bata isa inyi sharing ɗin shi da ita balle ke da nake miki kallon ƙazantacciya a cikin dabbobi. Na rantse da Allah yau sai na bar ma waɗancan munafukan tsofaffin mummunar tabon da bazai taɓa gogewa a zukatansu ba. Zan kashe ki, in" "kashe banza a banza, duk faɗin ƙauyenku sai in ga idan da shegen da ya isa yayi shari'a da ni...""" "A haukace ta sake kaima ƙofar wani wawan tokari da ƙafafunta, ihu ta ƙwallah saboda azaban zafi da" "raɗaɗin da ya ratsa ƙafar nata lokaci ɗaya, sai kuma ta zube ƙasa ta fashe da wani ƙaƙƙarfan kuka gwanin ban tausayi, hannayenta duk biyu ɗore a kanta. Ga kuma wuƙar da take riƙe da shi tsirara har lokacin bata yar da wuƙar ba." A haka Hafiz ya shiga cikin falon a sukwane Raudha na biye a bayanshi. Ya matsa zai ƙarasa kusa da ita da saurin gaske ta nuno shi tsinin wuƙar hannunta. """Munafuki! algungumi!! maci Amana!! Wanda bai san darajar Alƙawari ba!!!""" Ta jefa mishi munanan kalaman cikin matsanancin kuka na tashin hankali. """Na rantse da Allah idan ka ƙaraso kusa da ni sai na caka maka wuƙar nan sannan in cakawa kaina." "Gara duk muyi mutuwar kasko in san babu wata tsinanniya da za ta sake rayuwa da kai a matsayin mijin aurenta.""" Ta cigaba da magana cikin kuka. "Hankalinsa a tashe, ya fara mata magana da taushin murya don ya kwantar mata da hankali." """Bintu, Bintu, kin ga, don girman Allah kiyi haƙuri ki ajiye wuƙar, ki saurare ni...""" """Me zan saurara?""" Ta katse shi cikin tsawa tana wani zaro mishi idanu kamar ba ita ba. """Ƙarya? Ko kuwa kalamanka na yaudara da daɗin baki da ka saba cika kunnuwana da su? Ayau na" "tabbatar babu soyayya tsakanina da kai Hafiz, kuma na rantse da Allah sai dai idan Munafukar Allah ta'alan nan baza ta fito daga ɗakinnan ba, sai na kashe ta har lahira, sai dai duk abinda zai faru ya faru.""" Bai san muhimmancin tahowa da Raudha da yay ya kai ƙololuwa ba sai da yaga cikin hikima ta ƙarasa "kusa da Bintu ta rungumota jikinta, sannan a dabarance ta zare wuƙar da ke riƙe a hannunta tayi hurgi" da shi gefe ɗaya. Cikin kuka da magagin kishi take yi ma Raudha bayanin abinda Hafiz yayi mata. """Ki ƙyale ni Raudha... Hafiz ya ci amanata... ku kuke faɗa min namiji ba ɗan goyo bane ni kuma ina" muku tutiyar nawa ɗan goyo ne har da majanyi... Ashe duk mazan mamugunta ne halayensu ɗaya? Ashe da gaske ne da Hajiya Binta take yawan faɗin Namiji ƙanin ajali? Wai Raudha kamar ni Hafiz zai yaudara? Ni zai ciwa amana ya karya min alƙawari? Ƙauyensu ya tafi aka ɗaura masa aure da tsinanniyar ƙanwarsa amma saboda ya raina ni shi ne yake faɗa min ya taho da ita ne don ta taya ni aikin gida? To na rantse da "Allah sai na kash...""" "Da saurin gaske Raudha tasa hannu ta rufe mata baki. A tausashe ta fara ma Bintu magana, fuskarta na" "bayyana yanayin ɓacin rai da jimami, alamun itama tana jin ciwon abinda Hafiz ɗin yayi ma Aminiyarta." """Tabbas! Hafiz bai kyauta ba Bintu. Amma kar ki manta, idan hankali ya ɓata hankali ke nemo shi." "Yanzu abinda nake so da ke kiyi haƙuri, ki kwantar da hankalinki. Ki sama ma kanki nutsuwa ko ɗan kaɗan ne don mu samu mafita cikin ƙanƙanin lokaci. Tashi mu tafi zuwa ɗakin ki, Hafiz ɗin me? Ina ƙudan yake balle romonsa? Ai shi ma ya san yayi kaɗan, ba irinmu ake yiwa wannan cin amanar a zauna lafiya" "ba.""" "Da ire-iren waɗannan kalaman tayi amfani har ta samu nasarar miƙar da Bintu tsaye, tana riƙe da ita a" jikinta suka taka a hankali tana sake faɗa kalaman kwantar da hankali har suka haura sama zuwa ɗakinta. "Suna ɓace ma ganinsa, hankalinsa a ɗugunzume ya ƙarasa zuwa ƙofar ɗakin. Ya daɗe da sanin Bintu tana" "da masifaffen kishi, amma bai taɓa tsammanin kishi zai iya rufe mata idanu har tayi yunƙurin kisan kai ba. Yau in da ace kafin dawowarsa gidan ta samu nasarar caka ma Zulai wuƙar nan fa?" """A'uzu billahi minasshaiɗanirrajim""" Yayi ta'awizi da sauri yana ƙoƙarin kawar da mummunan tunanin daga zuciyarsa. "Wuƙar da Raudha ta cillar zuwa gefe ɗaya ya fara ɗauka ya kai kicin ya ɓoye, ba ma ita wannan wuƙar ba," "duk wasu wuƙaƙe manya da ƙananu da suke kicin ɗin kwashe su yayi gaba ɗaya zuwa cikin wata durowa ya kulle, ya zare makullin ya jefa a aljihu." "Ƙofar ɗakin da Bintu take ciki ya koma ya fara ƙwanƙwasawa. Bintu da take ciki hankalinta a tashe, izuwa" wannan lokacin ta shiga bayi sau biyar don tsananin firgita da tashin hankali. Cikin ƙanƙanin lokaci ta zabge gaba ɗaya kamar wacce ta kwana ta yini tana amai da gudawa. Duk irin maganganun da Bintu take yi tana jin ta. Ta kunna wayarta ya fi sau talatin don kiran can ƙauye "ta bada wasiyyar halin da take ciki, amma da yake matsiyaciyar waya ce da ta kawo sai ta ɗauke. A ƙarshe ma wayar sai ta daina kawowa. Tsananin tashin hankali yasa ta zube a ƙofar bayi tana sharɓan hawaye, hannayenta duk biyu dafe da bakinta, don kar sautin kukanta ya fita balle har ta ƙara janyo ma" kanta wani tashin hankalin daga Bintu. "Tana cikin wannan halin ne taji an fara ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin da ɗan ƙarfi. Idanu ta zazzaro a tsorace," "ta cire hannuwanta daga baki ta ɗora a kai hankalinta a tashe. Ko da ta ji ƙwanƙwasar ya ƙi tsagaitawa sai ta yanke ma kanta shawarar gara ta fara ƙwallah ihu, wataƙila idan aka ji ihunta ya karaɗe gidan wasu" daga cikin ma'aikata suyi ƙoƙarin kawo mata ɗauki. Ta buɗe baki za ta yanka ihu kenan sai ta ji muryar Hafiz a fusace yana cewa """Zulai don ubanki baza ki zo ki buɗe ƙofa in fitar da ke daga gidannan ba? Na rantse da Allah idan kika" "yi wasa zan ficewata in ƙyale ki da Bintu, in yaso ba caka miki wuƙa ba, idan taga dama ma ta ƙona ki ƙurmus! Ko babu komai an rage mugun iri a doron ƙasa...""" Tsulum! Ya ganta a gabansa ba tare da ya ji sadda ta buɗe ƙofar ba. Kallo ɗaya yayi mata ya gane a "bala'in firgice kuma a tsorace take, Zulai da ba ta ƙaunar zama ba hijabi sai ga ta tsaye a gabansa ƙiƙam" "babu hijabi babu ɗankwali. Rigar ma duk ta tattare, har yana hangen wani sashe daga farin fatar cikinta. Ko da ya kalli idanunta duk sun zurma ciki sun canja kala." Da bala'in haushi da takaicinta da ke cike da zuciyarsa ya galla mata harara. """Ina hijabinki?""" "Da saurin gaske ta koma cikin ɗakin jikinta na rawa ta fito riƙe da hijabin a hannunta, ta ma kasa" "sanyawa, sai da ya daka mata tsawa da umarnin ta saka hijabin mana, sannan ta saka a baibai tana ta zare idanu tana waige-waige don kar Bintu ta shammaceta ta caka mata wuƙa." "Lura da yayi Zulaikha fa ba ta a cikin nutsuwarta, harara ya sake galla mata sannan yasa hannu ya finciki" "hannunta ɗaya ya matsar da ita daga ƙofar ɗakin ya shige ciki. Ɗankwalinta da ya gani yashe a ƙasa," wayarta da ke ajiye a ƙofar bayi da takalmanta da suke ajiye a bakin ƙofa ya ɗauka ya cusa mata a cikin jakar kayanta. Duk abinda yake yi shi ma a gurguje yake yi da tsoron kar Bintu ta fito ta tarar da Zulai a falon. Bai tsaya ba ta umarnin su je ba kawai ya finciki hannunta da sauri tana biye da shi tana harharɗewa har suka fice daga cikin falon. "Bai saki hannunta ba, sai da ya buɗe ƙofar baya na motar ya zaunar da ita a ciki, ya aje jakar kayanta a" kusa da ita sannan ya mayar da ƙofar ya rufe. Mal Musa har ya taso a zatonshi tare za su fita amma sai Hafiz ya dakatar da shi. """Yanzu zan je in dawo Mal Musa, ba nisa zanyi ba. Idan na dawo sai mu koma Ofis.""" Makullin motar ya amsa ya shiga mazaunin direba ya figeta a guje suka bar gidan. "Hankalin Zulaikha bai fara kwanciya ba sai da taga sun bar unguwar gaba ɗaya, sun harba kan babban titi" suna ta ɓanana gudu. A fili taja wani nannauyan ajiyar zuciya da yasa Hafiz ɗan kallonta ta cikin madubi. "Harara ya sake gallah mata, ya ƙara da jan wata doguwar tsaki, ya saki wata ƙaƙƙarfan ƙwafa." "Duk abinda yake yi tana jin shi, amma ko kallo bai ishe ta ba. Sai ƙara gyara zamanta tayi akan kujera a" "fili ta fara godiya ga Allah, addu'a lokaci ɗaya tana haɗawa da sambatu." """Allah na gode maka da ka kuɓutar da ni. Allah kasa ko mutuwata ce tazo bazan mutu a wulaƙance" "hannun wacce ba ta so na, ba ta ƙaunata, kuma bata san darajar rayuwata ba. Na yi dambe iri-iri zamanin yarintata, na ga dambe-dambe kala-kala a rayuwata. Amma irin wannan ta'addancin damben da ake amfani da wuƙa mai shegen tsini da kaifi ban taɓa yi ba, kuma ban taɓa gani ba. Sai yau a gurin matar birni da take tutiya da wayewa amma ta bari linzamin kishi ya ja ta zuwa hauka, har take yunƙurin" "aikata abinda ni ƴar ƙauye bazan taɓa aikatawa ba...""" """Ƙiiiiiii...""" Ya taka wani wawan burki da yasa ta katse surutan da take yi a tsorace. Ta ɗaga kanta a firgice tana "kallonsa. Sai taga ashe har ya gangara gefen titi bata sani ba, hankalinta a tashe take kallon yadda ya buɗe ƙofarsa a fusace ya fita daga cikin motar." "Tana kallonshi, har ya gangara gurin wani mai kanti da yake can gefen hanya. Baza ta iya cewa ga" "takamaimai abinda ya aikata a gurin ba, tunda hangen bayansa kaɗai take yi daga cikin mota. Yana hanyar dawowa dai ta hango shi yana saka wani abu a cikin aljihun rigarsa." ": Duk da bata taɓa yin doguwar tafiya a motar haya ba, amma ta gama sakankancewa tashar mota zai kai" ta ya saka ta a motar zuwa Faƙo. Bata ankara duk doguwar tafiyar da suke yi ba tasha suka nufa ba sai da taga ya faka motarsa a ƙofar wani gida madaidaici amma kuma mai kyau tun daga waje. """Fito muje.""" "Ya umarceta bayan ya fita waje, fuskarsa a ɗaure tamau. Babu walwala ko misƙala zarrah." "A tsorace ta kalle shi, ta sake kallon ƙofar gidan da suke tsaye a gabansa. A marairaice ta ce" """Yaya ina ne nan ɗin ka kawo ni? Dan girman Allah kayi haƙuri ka saka ni a motar zuwa gida. Wallahi" "gaba ɗaya a firgice nake da Habujan nan, ka taimaka ka mayar da ni gurin Innaye inda na fi wayau.""" Sai ga hawaye sun zubo mata shar... Da rawar murya ta cigaba da cewa """Ni Wallahi daman auren nan yadda kake jin tsanarsa a ranka na ma fi ka jin tsananin tsanarsa a" "zuciyata. Ka kwantar da hankalinka, idan ka mayar da ni gida salin-alin na yi alƙawarin zan bi duk hanyar" "da ya kamata gurin wanke ka a gaban Baffa da Innaye. Bazan taɓa bari su ga laifinka ba, Wallahi da gaske nake yi...""" """Za ki koma gida, amma ba yanzu ba. Don haka gara ma ki rufe min tsattsamar bakinki tun kafin in" "canza shawarar da na yanke. Fito muje.""" Ya sake ba ta umarnin da tsawa a muryarsa. "Tana hawaye, ta fito daga cikin motar ta tsaya ɗan nesa da shi. Shi ya buɗe motar ya fito mata da jakar" "kayanta, ya zage zip ɗin ya fito mata da takalminta ya bata umarnin ta sa a ƙafafunta. Bayan ta saka ya" "sake umartarta da ta gyara hijabinta da yake a baibai, har ta gama gyara hijabin hawayen idanunta basu" daina sauka a guje kamar an buɗe famfo ba. Hannu yasa a aljihunsa ya zaro kuɗi masu ɗan dama za su kai dubu ashirin ƴan ɗari biyar-biyar ya damƙa mata a hannunta. """Ki riƙe wannan, ko za ki buƙaci wani abun ba ni a kusa. Nan ɗin gida ne na mutanen kirki da karamci" "ba na so ki ishe su da bani-bani. Kina ji na?""" A raunane ta ɗaga mishi kai alamar ta ji. "Hannunsa ya sake cusawa a aljihu ya zaro wata farar takarda da take a nannaɗe, ɗan shiru yayi yana" kallon takardar. Sai kuma ya sake naɗe takardar sosai ya miƙa mata """Ki ɓoye wannan a cikin kayanki, idan kin samu nutsuwa kin dawo cikin hankalinki sai ki karanta...""" """Takardar mece ce Yaya?""" Ta tambaye shi tana ɗan jujjuya takardar a hannunta. """Muhimman bayanai ne waɗanda ba ni da lokacin da zan iya ɓatawa wajen karanto miki su da bakina." "Allah yasa dai su Baffa basu yi asarar kuɗin tara ba, domin da turanci na rubuta. Wuce muje.""" "Jikinta a sanyaye ta bi bayansa, ranta a ɓace da baƙar maganar da ya gwaɓa mata da ya ce anyi asarar" "kuɗin tara. Ta sani tabbas asarar kuɗin taran aka yi, domin baza ta iya karanta dogon rubutu da turanci" ba. Sai a wannan lokacin Mashkura da alƙawarin da tayi mata na koya mata karatun turanci ya faɗo mata a zuciya. "'Ba komai. In da rai, da rabo.'" "Ta ayyana hakan a zuciyarta, sannan ta fara ƙoƙarin tsayar da hawayen da take yi ganin har sun isa ƙofar" gidan ya fara ƙwanƙwasawa. """Waye?""" Muryar namiji dattijo ya tambaya daga cikin gidan. """Baba ni ne. Hafiz ne.""" Ya amsa da girmamawa. Cikin sauri aka buɗe ƙofar daga ciki. Daga yadda dattijon yake gaisar da Hafiz da girmamawa sosai har yana ɗan duƙawa ƙasa yasa ta fahimci Mai gadin gidan ne. """Ina kwana.""" Ta gaisar da tsohon a mutunce da shaƙaƙƙiyar murya bayan sun gama gaisawa da Hafiz. A daraje ya "amsa mata, sannan ta bi bayan Hafiz da taga ya nufi cikin gidan kai tsaye." Daga yadda yake kutsawa lungu da saƙo na gidan har suka isa ɗan madaidaicin falon matar gidan yasa ta "gane Yayanta ba baƙo bane a cikin gidan. Ita dai tana biye da shi a baya, da alamun gajiya ƙarara a" fuskarta. "Ko da ya zauna akan kujera ita a ƙasa ta zauna, ta nannaɗe ƙafafunta a cikin hijabi, hankalinta a tashe. Ta" "rasa dalilin da yasa sam hankalinta ya kasa kwanciya da wannan baƙon muhallin da ya kawo ta, don dai" kawai ba ta da yadda za tayi ne. Sallamar da matar gidan tayi ta shigo cikin falon yasa ta ɗaga kai a hankali ta saci kallonta. Kyakkyawar "dattijuwa, wacce gayu, gyara, cin abinci masu gina jiki suka taka muhimmiyar rawa gurin ɓoye" "shekarunta. A haka idan aka bar Zulaikha za ta iya rantsewa da Allah Aunty Balira ta girmi matar, amma kuma a zahirin gaskiya ba haka bane." "Tana waɗannan tunane-tunanen har matar ta zauna, suka gaisa da Hafiz. Sai da Hafizu ya katse mata" tunani ta hanyar kiran sunanta sannan ta iya gaisar da matar. """Lafiya ƙalau. Ya kike?""" "Matar ta amsa mata a mutunce, sannan ta ƙara da tambayarta lafiyarta, da fara'a sosai a fuskarta take" "kallon Zulaikha, kamar dama can daɗe da saninta." """Lafiya ƙalau nake.""" "Ta amsa cikin sanyin murya, tana jin ɗan nutsuwa kaɗan a zuciyarta da ganin fara'ar da ke fuskar matar." Bata yi kama da mugaye ba sam! """Kar dai ka ce min kaima yau baka je Ofis ba?""" Matar da Hafiz ke kira Mummy ta tambaye shi bayan ta mayar da hankalinta kan shi. "Ɗan sosa ƙeya yayi, kafin ya amsa da" """A'a! Na je Mummy. Wani ɗan rikici ne ya mayar da ni gida. Don Allah alfarma nazo nema idan bazan" "takura miki b...""" """Dalla rufe min baki. Ashe ɗa yana neman alfarma a gurin wacce take kamar mahaifiyarsa? Me kake" "buƙata Hafiz? Feel free and ask me anything, in sha Allah bazai gagara ba.""" "Duk da ya san babu abinda zai nema gurin Hajiya Balkisu ta gagara yi mishi, ƙara tabbatar mishi da hakan" da tayi a yanzu ba ƙaramin daɗi da nutsuwa ya ƙara samu a zuciyarsa ba. """Na gode Mummy.""" A nutse ya cigaba da yi mata bayanin abinda ya kawo shi gidanta a daidai wannan lokacin """Wannan yarinyar da kike gani, ƙanwata ce, Sunanta Zulaikha. Jiya da na tafi gida nazo da ita, aurenta" nan da sati uku ne sai aka samu matsala daga can ɓangaren mijin ya ce ya fasa. "To kin san lamarin ƙauye da ƙananun maganganu, wannan dalilin ne yasa Baffana ya ce in taho da ita" "nan ko za ta samu nutsuwa. To kasancewar tun asali babu shiri tsakaninsu da Bintu, kwananta ɗaya" "kawai har sun fara samun saɓani, rikicin ne yasa har sai da na tsallake ayyukan Ofis na koma gida... Kawai don dai a samu maslaha, shi yasa na ɗaukota na kawo ta nan ta ɗan kwana miki biyu." "Baza ki samu matsala da ita ba in sha Allahu, duk wasu aikace-aikace za ta taya ki. Da farko na yi tunanin" "in kai ta gidan Abba Lurwanu sai kuma naga kamar an gudu ne ba'a tsira ba, daga cikin gidan baza'a rasa wanda zai kira Baffa ya faɗa mishi halin da ake ciki ba.""" "Zulaikha dai kanta a ƙasa, zuciyarta cike da baƙin ciki da takaicin yadda saboda tsananin ƙiyayyar da Yaya" "yake mata ba ya iya jingina mata matsayin matarsa. Daɗin abin ba shi kaɗai yae ƙin auren ba, ita kanta ta tsani auren, kila ma fiye da yadda ya tsana. A yadda take ji gara ta ƙare rayuwarta babu aure da dai ace ta tabbata matsayin matarsa ba ya son ta ba ya ƙaunarta. Saurin kawar da tunanin tayi, lokacin da ta ji" Mummy na cewa """Allah sarki. Babu komai in sha Allah Hafiz, ka san lamarinmu na mata sai haƙuri. Kuma na ji daɗi sosai" "da baka bari ka samu saɓani da matarka akan ƙanwarka ba, tunda dai ko wacce tana da ɓangaren muhimmancinta da haƙƙinta da yake wuyanka. Ka barta anan ɗin, kuma ba kwana biyu ba, iya tsawon satittika ko watannin da su Baffa suke so tayi ka barta tayi anan ɗin. Ba mu da damuwar hakan in sha" "Allah.""" Da murmushi a fuskarta ta mayar da kallonta kan Zulaikha ta ce """Zulaikha? Za ki zauna nan tare da ni ko?""" """Eh Mummy.""" Ta amsa a hankali. """Yauwa! Kin ga nima ba ni kaɗai bace a gidan, akwai mahaifiyata Hajja, da Yayanku Fadil, da ƙanwarsa" "Kareema, sai yaron Fadil mai suna Imam. Ko da na tafi Ofis i'm very sure zaman kaɗaita bazai dame ki ba. Kin ji ko? Ki saki jikinki kamar kina gidanku. Kuma ina fatan daga ɓangarenki baza ki kira su Baffa ki faɗa" "musu Yayanki ya canja miki muhalli ba?""" """Eh! In sha Allah bazan faɗa musu ba.""" """Yauwa! Madallah! Hafiz za ka iya tafiya.""" "Godiya mai yawa ya sake yi ma Mummy har sai da ta nuna mishi ɓacin ranta kafin ya daina godiyar," sallama yayi mata. Ko kallon Zulaikha baiyi ba ya fice daga gidan. "Mummy da kanta ta shiga kicin ta kawo ma Zulaikha lafiyayyiyar sakwara miyar agushi, wacce ta ji" naman rago zuƙu-zuƙu a cikin miyar. Sannan ta kawo mata ruwa da lemu ta ajiye mata a gabanta. """Baby ki ci abinci, idan kin gama ga kicin can ki shiga da farantan ciki. Ga kuma ɗaki can na tsakiya daga" "ɓangaren dama, ki shiga ciki ki ajiye jakar kayanki, akwai banɗaki a ciki sai kiyi alwala, daga yau nan ne" "ɗakinki, kin ji ko?""" """To Mummy, na gode! Allah ya saka da alkhairi. Ubangiji ya ƙara girma.""" """Ameen. To ni bari in shiga ciki inyi sallah.""" """To Mummy! A fito lafiya.""" "Idanunta na kan matar da a zuciyarta take jin nutsuwa da ita har ta ɓace ma ganinta. Kafin ta ci abincin," "sai da ta shiga ɗakin da aka nuna mata a matsayin nata ta ajiye jakar kayanta, ta shiga banɗaki ta wanko hannuwanta duk biyu ta fito zuwa falo ta zauna a gaban abincin." """Uhmmm! In ba gayu irinna ƴan birni ba ta ina sakwara zai ciwu da cokali?""" "Ta tambayi kanta a fili tana ɗan murmushi, bismillah tayi, ta gutsuri sakwarar ta ɗebi miya ta kai bakinta." """Uhmmm!""" Ta faɗa tana jin wani masifaffen daɗi mai barazanar tsinke mata kunnuwa. """Allah na gode maka da ka rabo ni daga gidan Bintu. Ko babu komai daga irin tarbar da aka min anan" "na san in Allah ya yarda bazan rasa abinda zan ci ba.""" "Ta faɗa tana sake yanko ƙaton lomar sakwarar da ya daku luƙwui kamar ba da hannu aka daka ta ba, ta" haɗa da miya mai yawa ta kai bakinta. Bata san tana jin yunwa sosai ba sai da taga cikin ƙanƙanin lokaci ta cinye manyan ƙullin sakwara guda "biyu, duk yawan namomin da ke cikin miyan haka ta cinye tas, ta shanye ragowar miyan ta suɗe kwanon tas kafin ta kwashe su zuwa kicin." "Wanke-wanke kaɗan ta gani a cikin sink, tattare hijabinta tayi ta haɗa da nata farantan ta wanke su tas" ta kife a cikin kwandon da ta gani a gurin. Goge ruwan da ya ɗan zuba tayi da mopper kafin ta fice daga cikin kicin ɗin ta nufi ɗakinta don sauke farali. "[1/30, 5:32 PM] Fareeda Abdallah: ***** *****" """Haba don Allah! Ta ina aka taɓa irin wannan rayuwa? Ace mace gandamemiyar budurwa baza ta iya" "tuƙe tuwon dawa luƙwui ta haɗa shi da lafiyayyiyar miyar kuka wacce ta ji daudawa ba? Ni kam ba haka nake ba, sunana Karimatu aka saka miki amma sam ba haka halina yake ba. Yanzu saboda Allah da" "Annabi idan Allah ya haɗa ki aure da dattijo maciyin tuwo fa? Ya za kiyi...?""" Wacce ake yiwa sababin ƙara zumɓuro baki gaba tayi ranta a ɓace ta ce """Allah ma baya sa haka ba Hajja. Ni kam in Allah ya yarda bazan taɓa auren tsoho ba balle kuma ya" "kasance mai masifar son tuwo, tuwon ma ya wuce na shinkafa, ya tsallake tuwon semo, ya shallake tuwon garin surfaffen masara har sai an gangara tuwon dawa. Kuma da kike ta wannan mitar kina min sababi ca nake sadda za ki fita na tambayeki abinda kike son ci zaɓi biyu kika bani? Ke fa kika ce ko inyi miki sakwara ko tuwon dawa, da naga bazan iya tuwon dawan ba shi ne na miki sakwara. Kuma ki tambayi Mummy ki ji tun bayan fitarki da safe ban zauna ba sai da na gama haɗa miki lafiyayyiyar sakwara miyan agushi, amma da yake ke ba'a miki gwaninta duk gidannan ba wanda bai ci abincin ya jinjina min ba sai ke, kuma saboda tsabar sabo da yi tun kafin ki ɗanɗana za ki sauke min kwandon" "sababin da kika taho da shi daga gidan Aminiyarki Hajiya Talatuwa mai tuwo-tuwo?""" "A fusace Hajja ta buɗe baki za ta mayar mata da martani, sai ga Zulaikha ta shigo cikin falon bakinta" "ɗauke da siririyar sallama. Ta yi wankanta tsaf! Ta yi kwalliya cikin ɗaya daga dogayen rigunan da Mashkura ta bata. Duk da fuskarta fayau yake babu wani ɗige-ɗige ko jagira sai powder kaɗai, ba ƙaramin kyau tayi a cikin doguwar rigar ba, kasancewarta farar fata, rigar kuma baƙa ce. Abu ɗaya da ya ɗan ɓata kwalliyar tata shi ne, bayan ɗankwalin rigar da ta yafa a kanta, sai ta kawo wani hijabi kuma ta" yafo ta bayanta don ya rufe tudun mazaunanta. """Sannunku da hutawa! Ina yininku?""" "Ta gaishe su da sanyin murya, da ɗan murmushi a fuskarta. Amma kallo ɗaya za ayi mata a fahimci tsoro" "a fuskarta, domin hayaniyarsu ne ya fito da ita. Da kamar ma baza ta fito ba, sai kuma ta tuna tana wanka ta ji motsin an buɗe ƙofar ɗakinta an shiga, daga bisani kuma aka fita. Wannan shi ne dalilin da" "yasa ta fito falon, a tunaninta ko Mummy ke son ganinta." "Tun kafin ta fito, duk su biyun Mummy ta riga ta yi musu bayanin wacece ita. Ƙosawa da ɗokin yin tozali" da abokiyar hira da Karima take tunanin ta samu yasa ta gaza haƙuri har sai da ta leƙa ɗakin da aka sauki Zulaikha. Da ta fahimci tana wanka ne yasa ta fita ta shige ɗakinta. "Dama ɗakuna uku da suke jere a ɓangaren ɗaya na Imam ne, ɗaya na Karima, ɗayan kuma shi ne aka" sauki Zulaikha a ciki. Ita ma sababin Hajja ne bayan ta buɗe kular abincinta ta ga sakwara saɓanin Tuwon dawa da tayi tsammani shi yasa ta fitowa. "Duk su biyun, a tare suka mayar ma da Zulaikha martanin murmushinta. Karima ta buɗe baki za tayi" magana Hajja ta riga ta cewa """Zulaihatu ko? Amma fa sai dai kiyi haƙuri, ni kam gaskiya Zulai zan dinga ce miki. Zulaihatu yayi min" "tsawo da yawa...""" """Hajja ba fa sunanta Zulaihatu ba, Zulaikha, haka Mummy ta ce. Don Allah kar ki wani ɓata mata suna" "da wani Zulai kamar wata tsohuwa.""" Ƙanƙance idanu Hajja tayi cikin sababi ta ce """To ina ruwanki ƴar'iya? Sunanki ko na ta? Ƴanmata akwai wani damuwa ne idan na kira ki da Zulai?""" """A'a! Babu wata damuwa Hajja. A gidanmu ma haka wasu suke kira na.""" "Ta amsa tana ɗan dariya, don izuwa yanzu diramar jika da kakar ya fara daina ba ta tsoro sai dariya." """To kin dai ji, aka ce miki kowa irinki ne, ga cikakken sunanki na musulunci Karimatu amma kika yanke" "shi wai ke nan gayu kika mayar da shi Karima. Ita Zulai ba haka take ba, da ganinta ƴar duma-duma yarinyar kirki ce. Zo nan ki zauna kusa da ni kin ji Zulai? Ina miki maraba da shigowa cikin ahalin Marigayi Modibo, alkhairin da ke tare da junanmu Allah ya sada mu da shi, sharrin da ke tattare da junanmu Allah" "ya kare mu ya yaye mana.""" """Ameen ya Allah""" Zulaikha da Karima suka amsa addu'ar gaba ɗaya. """Na gode Hajja.""" "Zulaikha ta ƙara da faɗin haka, fuskarta cike taf da murmushi. Kusa da ƙafafun Hajja ta ƙarasa ta zauna" "akan kafet kamar yadda ta umarce ta, lokaci guda kuma tana satar kallon Karima, wacce take zaune can gefe ɗaya tana murmushi." """Ke fa Zulaikha da alamun kin samu shiga a gurin Hajja. Ai kam ina tausaya miki, domin samun shiga a" "gurin Hajja daidai yake da tsayuwar...""" """Uwar tawa kike yiwa sharri Mamana?""" Mummy da take fitowa daga cikin ɗaki ta katse maganar da Karima take yi. """A'a toh! Ai gara ki ji da kunnuwanki kuma ki gani da idanuwanki Saudatu. Yau fa tunda na kushe" "wannan gantalallen sakwarar da take ta tutiyar ta daɗe tana aikinsa ai ni kam na shiga uku. Gaskiya ce kuma sai na faɗa, sakwara ce dai ba ita na so ayi min ba, tuwon dawa na so miyar kuka ke kuma baki iya" "ba.""" "Zulaikha da karambani, kamar an saka ta, a hankali ta buɗe kulolin abincin Hajja da suke ajiye akan ɗan" "ƙaramin teburin cin abinci a gabanta. Ɗaurin sakwarar guda ɗaya ta saka mata, ta zuba miya da namomin a gefe ɗaya, ta miƙa mata farantin, har lokacin murmushin fuskarta bai ɓace ba." """Ki daure ki ci sakwarar Hajja. Ta yi daɗi sosai Wlh, kuma ta daku luƙwui, miyar ma ta yi daɗi kamar za" "ta tsinke kunne. Anjima da yamma idan akwai garin dawar ni sai inyi miki tuwon, in dai za ki iya cin girkin" "ƴan ƙauye ni kuwa zan tuƙa miki tuwon da duk kalar miyar yauƙin da kike so.""" "Da idanuwan burgewa suke kallonta gaba ɗaya su ukun. Hajja bata tankwaɓe ƙoƙarinta ba, farantin da ta" "zuba mata sakwarar ta karɓa, bayan ta yi bismillah ta yanki loma guda ta kai bakinta. A lokaci guda kuma tana tauna sakwarar tana cewa" """Na gode Zulai. Ni ko me zai hana ni cin girkin ƴan ƙauye? Nima fa daga can nake. Ba ma haka ba, duk" wani ɗan birni da za kiga yana boƙara idan kika binciki tarihinshi tun tale-tale kakanninshi ƙauyawa ne na "asali.""" Ita kuwa Mummy cewa tayi """Da gaske kike yi Zulaikha? Kin iya tuƙa tuwon dawa da ko wace kalar miya ta yauƙi?""" Sunkuyar da kanta tayi tana wasa da yatsun hannayenta. """Eh Mummy. Kin san mu mutanen ƙauye ba kasafai muka cika yin kalolin abinci na ƴan birni ba, ko da" "yaushe an fi gane ma tuwo, sai kuma shinkafa ita ma jefi-jefi. Duk ranar girkin Innaye kashi tamanin cikin" "ɗari na aikin ni nake yi, in dai ɓangaren abincin gargajiya ne na iya su gwargwadon hali...""" """Tubarakallahu ma sha Allah! Ke kuwa Zulai kin huta, Allah ya saka ma Innaye da alkhairi. Babu" "ruwanta da fargaban aurar da ke ga ko wane irin miji. Takwara don Allah a sauke gwalli da iyayi a koyi kalolin girke-girken gargajiya don gudun gorin miji a gaba.""" Hajja ta ƙarasa maganar idanunta na kan Karima. """Ni dai kam yau na bani da ke Hajja. Tunda dai na ƙi miki tuwo kushe ni kawai kike yi, kiyi haƙuri mana" "tunda ga ƙanwata Zulaikha za tayi miki anjima. To ya kika ji sakwarar? Ta yi daɗi sosai ko?""" Sai da ta gyatsine fuska kamar wata ƙaramar yarinya kafin ta amsa da """Ba laifi dai. Ta ɗan yi. Zulai ƙaro min rabin malmala in ƙarasa da miyar nan kar ta min fatalwa na ƙi cin" "sakwara da yawa.""" "A tare Karima da Zulaikha suka tuntsure da dariya. Ita kuwa Mummy ɗan murmushi kawai tayi, zuciyarta" cike da farin cikin ganin yadda aɗan ƙanƙanin lokaci sabo ya shiga tsakanin Zulaikha da iyalanta. Tabbas "kamar yadda Hafiz ya ce, da alamun baza'a samu matsala da yarinyar ba." "Ƙanƙance idanu Hajja tayi tana harararsu duk su biyun, a ɗan fusace ta ce" """To miye kuma abin dariya? Ko don kawai an ga na daure tashin zuciya ina cuccusawa? To tunda haka" "ne ma ke Zulai bar shi kawai na fasa ƙarin...""" """Allah ya baki haƙuri Hajja. Ba da ke muke dariya ba fa.""" "Zulaikha ta faɗa tana danne dariyar da ke sake tuƙo ta. Ta rasa dalilin da yasa, bayan dariyar diramar" Hajja haka kawai take jin zuciyarta yalwace da farin ciki. Duk wani ƙunci da damuwar Hafiz da mahaukaciyar matarsa ta aje su gefe ɗaya can ƙarshen zuciyarta. "Bayan farkawarta aɗan gajeren barcin da ya kwashe ta ɗazu, ita da kanta tayi ma kanta karatun ta nutsu," "addu'a mai tsawo tayi kan Allah ya tabbatar mata da duk abinda yafi zama mafificin alkhairi a rayuwarta. Damuwa, ƙunci, tunani da baƙin cikin Hafiz ta sama musu matsuguni can ƙarshen saƙon zuciyarta tayi musu mummunan ɓoyo. Ta sa a ranta lallai za ta fuskanci gaba, ga gaban kuma da alamun za ta zo mata" da alkhairai masu yawa da farin ciki. "Nan falo suka bararraje suna hira da dariya, Zulaikha da ba ta da baƙunta sai labarin ƙauye take basu" "suna dariya. Ita ma Hajja da yake ƙuruciyar ƙauye ce kafin aurenta da marigayi Modibo ya tsallako da su cikin birni har suka hayayyafa sai labarin ƙauye take ba su, irinna zamaninsu da can." "Ko da lokacin ɗora tuwon da za ta yima Hajja yayi, ita da Karima suka shige kicin ɗin, sai dariyar maganar" Hajja suke yi da take ta jaddada ma Zulaikha kar ta kuskura ta bar ma Karima tuƙa tuwonta. """Bata iya komai ba, duk sadda tayi tuwo haka za ki ji shi duk gudaji. Sai ki rasa shin ido rufe take tuƙa" "tuwon ko kuwa ya take yi, kamar dai ba mace ba.""" "Mamaki ne ya kama Karima ganin yadda Zulaikha ke aikin tuwon cike da ƙwarewa da gwanancewa," "kamar wacce tayi zaman birni, kayan miya da daddawa da kayan ƙamshi sai da ta soya su sama-sama" "sannan ta tsayar da sanwan ruwan miyan. Ta kasa haƙuri, har sai da ta tambayeta shekarunta nawa?" Duk da Zulan tana da girman jiki fuskarta kawai za'a kalla a ga zallar ƙuruciya. """Shekaruna goma sha takwas Aunty Karima.""" Ta amsa tana dariya. """Ikon Allah! Amma gaskiya kin burge ni, yanzu kina nufin duk su dambu, fate, burabusko, ɗanwake, da" "sauran girke-girken gargajiya masu wahalar nan duk kin iya?""" """Eh! Kin ga duk da Yaya Hafiz yana ƙoƙarin kai mana kayan abincin birni Innaye da Baffa sun fi sabawa" "da kalolin abincin gargajiya. Shi yasa na fi ƙwarewa a dafe-dafen irin su.""" Ta sake amsawa har lokacin murmushi bai bar kan fuskarta ba. """To gaskiya dole za mu koyar da juna, amfanin zaman tare cuɗe ni ne in cuɗe ka. Kar ki wani ji kunya ko" "nauyi na kin ji? Duk abinda kike son koya daga tsarin rayuwar birni ki faɗa min, ni kuma zan koyar da ke daidai gwargwado. Duk da dai lokacina na zaman gida ragagge ne, domin ni ma'aikaciyar jinya ce a asibiti. Amma ya zama dole in mayar da hankali in koyi girki a gurinki. Kema kuma in sha Allah zan koyar da ke" "ire-iren girkin birni da na iya, da sauran duk abubuwan da kike buƙata, in sha Allah""" """Allahu yasha Aunty Karima, ai kam na gode. Na ji daɗi ƙwarai.""" "Cikin ƙanƙanin lokaci sabo mai girma ya shiga tsakaninsu, kamar dama can sun daɗe da sanin juna. Ko da" "aka gama tuwon, duk yadda Karima ta tsani tuwo musamman na dawa wannan kam sai da ta ci mai ɗan dama. Saboda yadda miyan take ta ƙamshi, ga kuma kyawu da tayi sosai a idanunta. Ta sha mamaki" "ƙwarai yadda ta ji tuwon ya tuƙu sumul babu gudaji, kamar ba a gabanta aka tuƙa ba." Albarka kam Zulaikha ta sha shi a bakin Hajja da Mummy babu iyaka. Tun tana amsawa da baki har sai da ta koma sakin murmushi kawai. "A gurin Karima ta samu aron cajar da ta jona wayarta, jikinta na rawa, wayar tana yin 10% ta cire ta" lalubo lambar Innaye ta danna mata kira. """Auta? Auta ke ce? Auta kina ji na? Ina fatan dai kina nan lafiya babu abinda ya same ki? Duk da Hafizu" ya rantse haɗe da tabbatar min lafiyarki ƙalau rashin jin ki ta wayar tarho ya saka ni cikin wasu-wasi. Ina "fatan babu abinda Fatima tayi miki ko kuma tayi yunƙurin aikata miki?""" Tambayoyin da Innaye ta dinga jera mata kenan da bayyanannen tashin hankali a muryarta. "Idanunta ciccike da hawaye ta nemi guri ta zauna a gefen gadon ɗakin da aka sauke ta, sannan ta amsa" "Innaye da lafiyarta ƙalau. Kamar za ta ba Innaye labarin abinda ya faru, sai kuma ta tuna alƙawarin da ta ɗaukar ma Mummy cewa baza ta sanar ma su Baffa Yaya Hafiz ya ɗauke ta daga gidanshi ba." Kuma ko ba haka ba ma a yadda ta fara jin daɗin zaman gidan Mummy baza ta so a raba ta da shi cikin "ɗan lokaci haka ba. Ta sani ko da ta koma ƙauye tabbas tsugune ne bata ƙare ba, to da wannan dalilin" gara kawai ta bi tsarin Hafiz har zuwa sadda za ta ga iya gudun ruwansa. "Hira sosai suka sha da Innaye, duk yadda Innayen take ta bugun ruwan cikinta don ta ji ko da wata" damuwa daga ɓangaren Hafiz ko Bintu sam Zulaikha ta ƙi faɗa mata komai. """Kin san halina fa Innaye. Idan mutum ba shiga harkata yayi ba nima bana shiga tasa. Kuma batun" "abinci Yaya shi da kanshi ya jaddada ma Baba Rabi lallai kar ta barni da yunwa, to har yanzu dai gaskiya ban ga wata matsala da za ta takurani ba. Kin san idan da matsala ma da kaina zan kira in faɗa miki.""" Ire-iren kalaman da tayi amfani da su kenan ta kwantar ma da Innaye hankali. "Har sai da kuɗin cikin wayar ya ƙare, Innaye ta kira ita ma nata kuɗin suka ƙare, sannan suka haƙura da" "magana, ta mayar da wayar a caji tana jin yadda zuciyarta ya ƙara cika da matsanancin farin ciki." "[1/31, 5:39 PM] Fareeda Abdallah: Washe gari, da yake Karima aikin dare take da shi. Haka kawai ta" "ƙirƙiri fita ita da Zulaikha, ba don komai ba sai don kawai ta zagaya da ita taga cikin garin Abuja." "Imam, yaro ɗan shekara shida da tun jiya ya dawo daga makaranta daf da magriba ya tarar da Zulaikha a" "gidan ya maƙale mata. Duk da ba wata shahararriyar hira ke gudana a tsakaninsu ba, saboda shi turanci" "ya fi kama bakinsa fiye da hausa, ita kuwa Zulaikha ba turanci. Kasancewarta wacce bata iya ɓoye-ɓoye" "ba, idan ya takura mata da dogon turanci ba wani kunya a tare da ita ko a gaban su Mummy ne ba ta jin" kunyar ce mishi """Hey Boy! No English.""" "Da yake su Mummy wayayyu ne sai suyi kamar basu ji me ta ce ba, shi kuma da yake yana da son baƙi" "haka zai kwaɓo hausar a jagwalgwale, ita kuma ta daddage ta bashi amsa yadda ta fahimta ba tare da nuna gundurarwa ba, domin Allah ya yi ta da son yara." "A haka dai duk inda Zulaikha ta saka ƙafa nan yake mayar da tasa, duk inda ta zauna a jikinta zai raɓu ya" "zauna. Aikin gida da aka bashi daga makaranta ma takardun ya kwaso gaba ɗaya ya zube a gabanta, yana yi tana kallo duk da ba ta fahimtar abinda yake rubutawa. Ba ita ta samu hutu ba, sai da yayi barci aka" kai shi ɗakinsa. "Da sassafen ranar ya ma ƙi yarda Karima tayi mishi shirin makaranta, sai tarewa sukai su biyun a ɗakinshi," "Zulaikha tana shirya shi Karima tana harhaɗa mishi abubuwan da yake tafiya da su makaranta. Ƙarfe takwas saura minti ashirin motar makarantarsu tazo har ƙofar gida ta ɗauke shi, kamar zaiyi kuka haka" "yake ta jaddada ma Zulaikha lallai ta jira shi ya dawo, kar ta tafi, ya yi alƙawarin zai kawo mata tsaraba." "Da dariya a fuskarta take jaddada mishi baza ta tafi ba, za ta jira shi ya dawo. Kuma za tayi ta zama a" gidansu har sai ya gaji da ganinta. Ya shige cikin mota yana ɗaga mata hannu tana ɗaga masa har sai da motar ya ɓace ma ganinta sannan ta shiga gida. "Ƙarfe goma sha ɗaya da rabi na safe suka gama shiryawa ita da Karima, ta kwashe su a mota suka fice" kasuwa yin siyayyan abubuwan gida da basu da shi. "Gurin shirin Zulaikha ne dai haka aka sha dirama da ita gwanin ban dariya, daƙyar ta iya ajiye babban" hijabinta ta karɓi ɗan madaidaicin gyalen da Karima take miƙa mata ta saka. Shi ma kafin ta saka sai da Hajja ta ishe ta da gorin ko ita da take tsohuwa baza ta zumbula wannan ƙaton hijabin ba idan za ta fita. """Kin ga Zulai ki kwantar da hankalinki, nan fa binni ne ba ƙauye ba. Idan kika ji inda ake rayuwa babu" ruwan wani da wani to binni kenan. A ƙauye ne suke da masifaffen sa'ido da abu kaɗan ko ba na saɓon Allah bane sun dinga yamaɗiɗi da ke kenan. Bayan wannan zumbuleliyar riga da kika sa saboda Allah menene amfanin sake zumbula hijabi kuma? Ai wannan mayafin da takwara ta baki shi ne daidai da "kwalliyarki Zulai. Ko ba kya so Allah yayi miki gyaɗar dogo ki samo mana wani sabon miji ne ɗan binni?""" "Ta tambayeta da dukkan gaskiyarta, saboda yadda Hafiz ya faɗa ma Mummy saura sati uku auren" Zulaikha mijin ya ce ya fasa haka ta faɗa ma Hajja. "Bata iya cewa komai ba, sai ɗan dariya kawai tayi, ta karɓi mayafin ta yafa tana ta jero istigfari a" zuciyarta. Domin ba ta jin za ta iya kware ma ɗan'uwanta baya ta hanyar tona asirin auren da yake tsakaninta da shi. A idanun su Mummy da ta lura sun yarda da shi ɗari bisa ɗari. Ko da ganin yadda take ta jan gyalen tana ƙara tale shi don ya ƙara sauka mata za'a san bata saba sakawa ba. Ita kuwa Karima me za tayi mata in ba dariya ba """Kin san Allah? Za ma ki ware ne, sai yanzu na ƙara tabbatar da ina da babban aiki a gaba na. Har na ji" "na fara addu'ar Allah yasa ko wata biyu ne kacal kiyi a gidanmu, in sha Allah zan mayar da ke ƴar gayu fiye da yadda ba'a zato. Shi fa tsoron Allah a zuciya yake, in dai ba tsiraici mace za ta bayyana ba, babu wani laifi ki saka yalwataccen suturarki sannan ki yafa ɗan siririn gyale. Don Allah ki saki jikinki kin ji" "ƙanwata?""" """Toh Aunty.""" "Ta faɗa cikin sanyin murya, sai dai har suka isa kasuwar ta kasa sakin jikinta yadda ya kamata." "Abu ɗaya da yayi ma Zulaikha daɗi shi ne ganin kasuwar ma a birnance ne, ba irin kasuwarsu bane na" "ƙauye da za aga mutane cunkus ana yamutsi tsakanin maza da mata. A taƙaice ma, duk siyayyar da suka yi a cikin manyan kantuna ne, nan taga yadda aka san daraja da kimar kayan miya. A babban kanti anyi packaging ɗin tumaturi irin manyan nan a leda anyi sealing ɗin shi, su tattasai ma da tarugu da albasa ma" "duk sun samu muƙami na musamman, ba kamar yadda take ganinsu a wulaƙance a ƙauyensu ba." "Basu bar cikin kasuwa ba sai ƙarfe ɗaya da rabi na rana. Kuma maimakon su nufi gida, juya akalar motar" Karima tayi suka nufi gidan Aminiyarta. Sunanta Hibbah uwar gayu. Bayan sun gaisa da mahaifiyar "Hibbah wacce ƴaƴanta ke kira da Mama, kai tsaye ɗakin Hibbah suka shige, kan gadonta suka bararraje" suna hira irinta aminan da akwai shaƙuwa mai girma a tsakaninsu. "Ita kuwa Zulaikha banɗaki ta tambaya aka nuna mata, ta ajiye mayafin jikinta ta shige da sauri saboda" fitsarin da ya matse ta. Hibbah ta bi ta da kallo ƙasa-ƙasa. Sai da ta shige ta rufe ƙofa sannan Hibba ta "mayar da idanunta kan Karima, da salon tsegumi ta ce" """Ina kika samo kyakkyawar yarinya haka mai ƙira irinta Hadiza gabon? Ke kin ga wasu manyan kaya da" "take ɗauke da su a bayanta kuwa?""" "A tare duk su biyun suka kwashe da dariya. Kafin Karima tayi magana aka yi sallama a ƙofar ɗakin, bayan" sun amsa mai aikin gidan ta shigo da babban faranti a hannunta ɗauke da kulolin abinci da abin sha. Gefe ɗaya ta ajiye tayi musu sallama ta fice daga ɗakin. "Ƙofar banɗakin da Zulaikha ke ciki Karima ta kalla, sannan ta mayar da hankalinta kan Hibbah ta ce" """Kin shiga uku da sa'ido Ƙawata. Ƴar danginmu ce tazo daga ƙauye, kuma za ta ɗan kwana biyu a" "gidanmu. Kin san me yasa na zo da ita gurinki?""" "Girgiza kai Hibba tayi, a zuciyarta take mamakin yadda kyakkyawar yarinya haka mai sanyin kyau za'a ce" daga ƙauye take. Irin wannan da a birni take kuma ta san kanta ai ba ƙaramin gwarama za ta haɗa na "samari ba. Shi yasa fa wasu mazan ke cewa tsantsar kyawun mace na gurin ƴar ƙauye, matan birni mafiyawancinsu gayu ne kawai da ƙyale-ƙyale." "Ƙara rage murya Karima tayi, sannan ta cigaba da cewa" """So nake ki wayar min da ita a cikin kwanaki ƙalilan, ki koya mata salo-salo na gayu don Allah. Kin ga" "waɗannan mazaunan da kika hango a bayanta? Baki ga komai ba Wlh, sai yau da na shiga ɗakinta da sassafe, na ganta sanye da doguwar rigar barci da ya ɗan kama ta. Uhmmm! Ke dai abin ba'a cewa komai, ƙiran jiki ne da ita mai kyau Wlh! Ga wani shape da take ɗauke da shi abun sha'awa, ta bakinki" "dai kamar Hadiza gabon. Duk wannan ƙibar na ta sam ba ta da tumbi...""" Fitowar Zulaikha daga banɗaki yasa suka bar maganarta da suke yi suka shiga wata hirar. Tana ɗan goge ruwan da ke kwance a fuskarta da gefen ɗankwali tace ma Karima """Aunty ni fa nayi alwala ne, a taimaka min da Hijabi inyi sallah.""" """Ba kya jin yunwa Zulaikha? Ai da kin bar sallar mu fara cin abinci, idan mun gama sai muyi sallah a" "tsanake.""" "Sai da Karima tayi maganar, sannan Zulaikha ta lura da kulolin abinci da aka ajiye a tsakar ɗakin. Ga" "kuma Jug ɗin tangaran nan shaƙe da zoɓo, jikin jug ɗin sai raɓa yake fitarwa alamun sanyi ƙarara." """Ku fara ci Aunty, tunda na yi alwalar bari in fara yin sallar, idan na idar sai in ci abincin in huta gaba" "ɗaya.""" """To shi kenan! Yi sallar, ni kam dai sai na ci abinci zan sauke farali.""" "Hijabi da sallayar da Hibba take miƙa mata ta karɓa, ta tambayi gabas aka nuna mata, ta shimfiɗa ta" tayar da sallah. "Ko da ta idar da sallah tayi ƴan addu'o'inta, bata ɓata lokaci ba ta cire hijabin ta ninke, sannan ta ƙarasa" kusa da abincin ta ɗiba a ɗaya daga cikin farantai uku da aka ajiye musu. Duk yadda Hibba take ta mata "nacin ta tashi ta zauna a gefen gado kamar yadda suke zaune ƙiyawa tayi, nan ƙasa ta zauna ta fara cin abincin, lokaci bayan lokaci take amsa musu hirar da ƙarfi da yaji suke ta tsoma ta a ciki." """Fuskarki za tayi kyau da sassauƙar kwalliya Zulaikha, gama cin abincin in gwada kwalliya a fuskarki mu" "gani ko za ta zauna miki yadda nake hasashe. Kin san ni fa sana'ata kenan, kwalliya, ɗaurin ɗankwali, lalle, da duk wata harka ta gyaran jiki ba wanda ba na taɓawa. Mamana da kika ganta a waje ƴar maiduguri ce, kin san kuwa mu ne sirrin ƙamshi da gyaran jiki. Da wannan dalilin yasa wasu daga cikin" "ƙawayena ke ce min Uwar gayu.""" Ta ƙarasa maganar tana kaɗa idanu tana wani yarfe hannaye don tsabar yanga da firirita. "Zulaikha dai sai kallonta take yi, kamar tayi dariyar irin yadda take ta fari da idanu tana wani watsa" "hannaye kamar za ta tada aljanu, amma sai ta matse dariyar bata yi ba. Ko da ta gama cin abincin, bata" ƙi tayin kwalliya da Hibbah tayi mata ba. Haka take ta bin komai da kallon mamaki ganin wani ƙaton akwati da Hibba ta ɗauko wai duk kayan "kwalliya ne a ciki. Kamar da wasa, ta zauna a kujerar gaban madubi Hibba ta fara yi mata kwalliya kala daban-daban a fuskarta." "Kuma da yake Hibbar ta san aikinta, kwalliya kala huɗu da aka gwada ma Zulaikha ba ƙaramin hawa da" kyakkyawar fuskarta suka yi ba. Su kaɗai a ɗaki sai tuntsura dariya suke yi suna shewa kamar ƴan matan "Amarya. Duk kalar kwalliyar da aka yi sai an yi mata ɗaurin ɗankwalin da zai hau da ita, Karima kuwa sai aukin ɗaukarta hotuna take yi tana ɗora ta a status ɗin whatsapp." """My luvly Ƙanwa Zuly. Allura cikin ruwa... mai tsananin rabo ka ɗauka.""" Ire-iren kirarin da tayi ta bin hotunan da shi kenan. """Gaskiya ni dai wannan kwalliya da ɗaurin ɗankwali sun burgeni matuƙa Wallahi. Ashe lokacin auren" ɗiyan mai garinmu da aka ɗauko mai mata kwalliya tun daga Kasuwan magani zuwa ƙauyenmu ta "cancaɗa mata mukai ta yabo muna zuzutawa ashe ɓata mata fuska kawai ta yi?""" "Zulaikha tayi maganar fuskarta cike da farin ciki, tana sake ƙure kanta da kallo a gaban madubi ganin" "yadda ta canja gaba ɗaya. Kamar ba Zulai ƴar Innaye da Baffah ba, ta yi wani irin kyau na musamman da" bata ma san zai iya kwatanta shi ba. "Kamar wacce ta tuna da wani abu, da sauri ta matsa kusa da Hibba ta riƙe hannayenta, fuskarta a" marairaice ta ce """Aunty Hibbah, don girman Allah ki koya min kwalliya da ɗaurin ɗankwalin. Ba kuma wai don in dinga" "sana'ar da kike yi in kashe miki kasuwa ba, don fuskata kaɗai, na rantse da Allah fuskata kawai zan dinga yiwa kwalliya ina ma matan ƙauyenmu burga. Daman kullum idan suka tashi gwaɓa min magana suna cewa don na ga ina da Yaya a Habuja shi yasa nake musu ɗagawa, haka ma Mudan ya ce min kafin ya ce" "bazai aure ni ba, kuma fa Wallahi ba haka bane.""" Ta ƙarasa maganar idanunta ciccike da ƴan ƙananun ƙwallah. """Kar ki damu Zuly, ai tunda Karima ta kawo ki gurina babu abinda bazan iya miki ba.""" Ta mayar da idanunta kan Karima ta ce """Besty kiyi adding ɗin ta a group ɗin da nake koyar da kwalliya da ɗaurin ɗankwali na whatsapp...""" Da murna sosai a fuskar Karima ta katse Hibbah tun kafin ta aje numfashin maganarta. """Lallai ke kam Zulaikha kina da sa'a. Besty Allah ya saka da alkhairi, kin gama mana komai. Na san ko iya" "haka aka tsaya cikin ƙanƙanin lokaci Zuly za ta faso gari, ta zama babbar yarinya.""" A tare duk su ukun suka sake kwashewa da dariya. "A haka suka ƙara cinye fiye da awoyi uku a gidan, har sai da Mummy ta kira Karima a waya tana faɗan" "daɗewar da suka yi, ga shi a lokacin Hibbah ta kwaɓa lallen zamani ta fara yi ma Zulaikha a bayan" hannunta da saman ƙafafunta. Tunda dai tafin ƙafa da tafin hannu akwai lallen aure da Aunty Rakiya tayi mata a gida. Haƙuri Karima tayi ta ba Mummy tana ba ta uzurin lalle ake yi ma Zulaikha har dai aka zirara mata lallen "ba mai yawa sosai ba, haka suka fice daga gidan da ɗanyen lalle ko bushewa baiyi ba. Mama sai dariya" "take musu, bayan ta ba su ƴan ƙananun ledoji ɗauke da turarukan jiki na shafawa irin nasu na ƴan mata." "[2/1, 5:15 PM] Fareeda Abdallah: ******" "A marairaice ta kalli fuskar Karima da take miƙa mata wayarta, bayan ta gama hidimar buɗe mata" "Facebook, whatsapp, Instagram. Kuma tayi adding ɗin ta a group ɗin Hibbah, da duk wasu groups da take ciki, waɗanda ta san lallai ana gabatar da abubuwa na ƙaruwar ilimi a ciki." """Ni dai Aunty Allah yasa ba wahalar banza kika yi min ba. Allah dai yasa in iya amfani da waɗannan" "kafafen sada zumuntar. Musamman ajujuwan da kika saka ni da wanda kika sa shugabannin group ɗin suka saka ni. Ni kin san babbar matsalata shi ne ba na jin turanci, sannan rubutu in dai da turanci ne gaskiya ba lallai ne in iya karanta kalmomin a yadda suke ba, ko na karanta ma gaskiya kashi casa'in da" "tara cikin ɗari na kalmomin ban san me suke nufi ba...""" """Yauwa! Dakata Zuly.""" "Karima tayi saurin katse ta, doguwar hamma tayi, saboda ta kwana a asibiti ba wani wadataccen barci." Tana dawowa da safe kuma maimakon ta kwanta kamar yadda ta saba ita da kanta ta ce Zulaikha ta kawo wayarta ta buɗe mata whatsapp da sauran kafafen sada zumunta. Gyara zama tayi kafin ta cigaba da cewa """Daman tun jiya nake ta so in tambaye ki. Acan ƙauyenku baki yi makarantar boko bane?""" """Na yi makaranta mana.""" Zulaikha ta amsa da sauri. Kafin Karima ta ce wani abu ta cigaba da cewa """Kin ganni nan Wallahi har aji shida na sakandire na gama, kuɗi tsugugu Baffa ya biya min na zana" "jarabawar WAEC dA NECO a Kasuwar magani, amma gaskiya ban ci ba. A hausa da Islamic ne kawai na samu Credit, sai lissafi na samu Pass. To kin san dai yanayin karatun namu na ƙauye, babu wasu tsayayyun malamai, sannan shi kanshi zuwa makarantar da ɗaukar karatun da muhimmanci duk asha ruwan tsuntsaye muke masa. Don a ƙauyenmu yara mata sa'annina waɗanda muka fara makarantar boko da su ni kaɗai ce ma na jajirce har na gama aji shidda ban tsaya kula samari ba balle ayi min aure. Mu a ƙauyenmu ko a maza ɗaiɗaiku ne suke ɗaukar karatun boko da muhimmanci. Na dai iya karatun hausa da rubuta shi lafiya ƙalau. Amma na turanci kam gaskiya sifili ne, gara in faɗa miki tun wuri kar in" "dinga kunyataki a cikin ƙawaye da abokan arzikinki.""" """Don wannan matsalar, kar ki wani damu kanki. Ba ke kaɗai ke fama da matsalar rashin jin turanci ba," "har anan cikin birane akwai mutane da yawa sun yi karatu amma ba sa jin turanci. Kin san in banda yanzu da ake ta ƙara gane muhimmanci iya yare mabanbanta, da yawa daga cikin mutanenmu basu fahimci muhimmancin iya magana da turanci da kuma gogewa a karanta turancin ba. Duba da yadda kusan komai an cigaba, Hausa ta game kusan ko ina a Nigeria, kusan babu inda za ki je ki rasa wanda zai" miki tafinta da Hausa. A yanzu da aka fahimci rashin iya turancin na janyo matsaloli a wasu ɓangarorin na rayuwa sai mutane "suka zaburo suna so su koya, amma kuma da yawa ana jin kunyar komawa makaranta, wasu kuma ba su da lokacin da za su koma makaranta don kawai su koyi turanci." "Duba da waɗannan dalilan, yasa da yawan makarantu da kuma wasu manyan malaman turanci suka" buɗe fagen koyar da turanci ta kafafen sada zumunta ka'in da Na'in. Akwai pajika da groups da suke yi a "kyauta, akwai kuma waɗanda sai an biya kuɗi. Yanzu dai duk ba ma wannan ba, Almuhim shi ne, shin ke" "da gaske kin shirya dagewa da nacewa wajen koyon magana da karatun turancin ko baki shirya ba...?""" """Na shirya! Wallahi Aunty na shirya!! Na rantse da Allah na shirya Aunty.""" "Ta amsa da sauri, bakinta har yana mazari. Da saurin gaske ta ƙara matsawa kusa da Karima kamar za ta" hau jikinta. """Aunty? Kin kuwa san yadda rashin iya turancinnan yake ja min tozarci, wulaƙanci, cin mutunci daga" "gurin Aunty Bintu kuwa?""" "Tayi ƙwal-ƙwal, idanunta suka cicciko da hawaye." Tsabar damuwa yasa bata san sadda ta buɗe baki ta dinga ba Karima labarin ire-iren cin mutunci da "tozarcin da Bintu take musu ba. Domin ita Zulaikha a yadda ta ɗauka shi ne, kawai Bintu tana yi musu" "haka ne saboda ta gansu ƴan ƙauye, kuma jahilai, waɗanda basu yi ilimin boko ba." """Dakata Zuly. Tun shekaran jiya da na ji kin kira sunan Innaye sunan yake ta min yawo a ƙwaƙwalwa," "kamar na taɓa jin sunan, amma sam na manta a ina ne, shi yasa na share zancen a raina. Sai yanzu da kika ɗan bani wannan labarin na tuna inda na taɓa jin sunan, kina nufin Innaye mahaifiyarki ce?""" "Karima ta tambayeta da mamaki fal fuskarta, a zuciyarta take tuna wancan lokacin da ta taɓa taimaka" "ma Innaye a asibitinsu, tana kuma sake tuna yadda Dr. Bintu ta wulaƙanta Innaye kamar ba uwar mijinta" ba. """Eh! Mahaifiyata ce.""" Zulaikha ta amsa mata da sanyin murya. """Kin santa ne?""" Ta sake jefa ma Karima tambayar. """Ƙwarai kuwa na santa.""" A taƙaice ta ba Zulaikha labarin haɗuwarta da Innaye a asibitinsu a wancan lokacin. """Allah sarki Innaye. Mutuniyar kirki, ya jikinta kuwa? Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci sabo ya shiga tsakanina" "da ita daga haɗuwa a asibiti kawai, na daɗe ban manta da al'amarinta a zuciyata ba.""" """Ta ji sauƙi sosai.""" "Zulaikha ta amsa da ɗan murmushi a fuskarta, don jin daɗin an yabi Innayenta." """Ai tun daga wancan lokacin, ni da ita bamu sake zuwa Habuja...""" """Abuja ne fa asalin sunan. Haba ƴan mata, ki fara nuna kin waye mana? Kamar baki karanta State and" "Capitals ba?.""" "Dariya suka yi duk su biyun, sannan Zulaikha ta cigaba da cewa" """Bamu sake zuwa Abuja ba tun wancan lokacin, sai yanzu da na dawo. Kuma kin san Innaye ma ta bani" "labarinki tun wancan lokacin? Ta ce min taimakon da kika yi mata shi ya hana ta wahala da yunwa, tunda sun fita bata karya ba.""" """Allah sarki... Allah ya ƙara mata lafiya da nisan kwana.""" """Amin ya Allah.""" "Nan suka cigaba da hira sama-sama, Karima tana danna wayarta. Ta ɗauki fiye da mintuna sha biyar tana" danne-danne kafin ta ɗago fuskar wayar ta nuna ma Zulaikha. """Kin gani, an gama komai. Na yi miki register, na biya miki 15k na register. Za ki koyi magana da turanci," "karatun turanci, da sanin fassarar kalmomin turancin a cikin watanni uku kacal in Allah ya yarda. Amma fa idan kin dage, kin nace, kin mayar da hankali sosai. Ki duba Whatsapp ɗin ki, za ki ga sunyi adding ɗin ki yanzu, don na basu lambarki.""" Tsananin farin ciki yasa bata san sa'adda ta rungume Karima tana zabga mata godiya. """Na gode, na gode Aunty Karima. Kin gama min komai, bazan taɓa mantawa da alkhairanki a gare ni ba." "Allah ya saka miki da alkhairi ninkin ba ninkin abinda kika yi min.""" """Ameen ya rabb""" Karima ta amsa bayan ta sake jan wata doguwar hamma. Zamewa tayi daga zaune ta kwanta. """Kin ga tun ɗazu ina ta hamma, idan ba runtsawa nayi ba bazan samu nutsuwa ba. Kin san barci, ba'a" "cin bashinsa. Yanzu dai tunda na saka miki data, kuma na gama saita miki komai, ki karɓi wayarki ki duba" "kina bin komai sannu a hankali. Duk abinda baki gane ba, idan na tashi barci sai inyi miki ƙarin bayani.""" """To Aunty. A huta gajiya. Na gode. Bari in tafi ɗakin Hajja muna hira ina daddana wayar...""" """A'a ki ce ba danna waya za kiyi ba. Hajja ce za ta barki ki danna wata waya ita tana zaune? Je ki dai ta" "cika miki kunne da mita da karaɗi, can anjima kya danna wayar.""" "Bata ce komai ba, illah dariya da tayi ta ɗauki wayarta da cajar da Karima ta bata kyauta ta fice daga" "ɗakin. Kamar yadda ta ce, ɗakin Hajja ta nufa kai tsaye. Don Allah ya sani ba ƙaramin kewar Innaye" "tsohuwar ke ɗebe mata ba, barkwanci da mitar tsohuwar ita bata taɓa ɗaukarshi abin damuwa ba, ko don bata daɗe bane a gidan? Oho!!!" ***** ***** "Ya juyar da fuskarsa ɓangaren gabas, ta bishi. Ya sake juyar da fuskarsa ɓangaren yamma, ta sake bin shi" idanunta ciccike da hawaye. Yana yunƙurin sake juyar da fuskarsa ɓangaren kudu tayi saurin sa hannayenta biyu ta riƙe fuskarsa tana ɗan girgiza mishi kai. "Suka kalli juna cikin ido na tsawon wasu daƙiƙu. Tasa fuskar a ɗaure tamau, idanunsa babu wani shauƙi" "ko kewa. Ita kuma tata fuskar a marairaice, idanuwanta ciccike da hawaye, da wani irin sassanyar yanayi" "mai bayyana So, Ƙauna, Kewa, damuwa da nadama ƙarara." "Hawayen da take ta riƙewa tun ɗazu a hankali ta sake su, suka zubo kan kumatunta shar!!! Ya yunƙura" "zai karɓe fuskarsa daga hannunta da gaggawa tayi saurin matsawa da tata fuskar izuwa tasa, kafin ya ankara ta haɗe bakinsu guri guda. A lokaci guda kuma tana cigaba da aika mishi saƙon tuba da neman" yafiya da idanunta. "Da fari, datse laɓɓansa yayi ƙam! Ya ƙi bata wani dama da harshenta zai samu isa cikin bakinsa balle ta" "tsotsa, amma da yake ta san lagonsa, da duk wani salo da take amfani da shi wajen samun kansa ba'a daɗe ba ya saki bakinsa ta fara juya shi yadda take so." "Tun yana turjewa yana basarwa har dai ya bada kai bori ya hau, domin babu ƙarya shi kanshi ba ƙaramin" kewarta yayi ba a cikin kwanaki biyun. 'Kawai dai ya janye jikinsa daga nata ne don ya nuna mata kuskurenta. "Ya sani asalin laifin nashi ne, amma a tsammaninsa akwai fahimtar juna da soyayyar da ko da wasa baza" "ta taɓa yunƙurin aikata mishi irin abubuwan da ta aikata ba. Wuƙa ta ɗauka za ta caka mishi fa? Wai shi ne Bintu take rantsewa da girman Allah idan ya kuskura ya ƙarasa kusa da ita za ta caka mishi wuƙa, sannan ta jefe shi da iyayensa da baƙaƙe kuma munanan kalaman da ko tana cikin hauka tuburan ne bai" taɓa tsammanin za ta iya kallon cikin idanunsa ta furta mishi su ba...' """Kayi haƙuri My dear... Don girman Allah SWT da Darajar Fiyayyen halitta SAW ka yafe min.""" "Ta faɗa cikin kuka bayan ta raba bakinta da nashi, kamar ta san tunanin da yake yi." "Da saurin gaske ta zame zuwa ƙasa ta riƙe ƙafafunshi tana cigaba da rusa kuka wurjanjan, kamar wacce" aka aikowa da saƙon mutuwar iyayenta duk biyu a lokaci ɗaya. Cikin kukan ta cigaba da magana """Na sani ko kusa banyi amfani da hankali da tunani ba gurin aikata irin abubuwan da nayi... Na sani" "banyi maka uzuri ba, kamar yadda na sha alƙarwarta maka a baya cewa duk juyin juya hali na rayuwa bazan taɓa fahimtarka a bai-bai ba... Na sani ban saurareka ba balle har in baka dama kayi min bayanin gaskiyar abinda yake faruwa... Amma ya kamata ka fahimce ni My dear, ko ɗan yaya ne kayi min uzuri, duk da ni na kasa yi maka uzuri sa'adda idanuna suka rufe ruf da tsananin kishi da matsanancin" soyayyarka. Wallahi ban taɓa sanin haka kishi yake da azababben zafi da raɗaɗi ba sai a wannan ranar... Komai na "duniyar baƙi-ƙirin yayi min Sweetheart! A wancan lokacin, Wallahi Tallahi ban ƙi duniyar ta kife ayi" "mutuwar kasko ba duk a wuce gurin.""" "Taja shessheƙar numfashi cikin kuka, kafin ta cigaba da cewa" """Babu ma amfanin maimaita abinda ya wuce. Kuskure ne nasan na riga na aikata, bazan gaji da baka" "haƙuri ba har sai ka furta ka yafe min da bakinka. Wannan shiru-shirun naka neman hallakani yake yi," "gara ka ɗauki duk matakin da za ka ɗauka a kaina a wuce gurin. Idan yi min duka zai sa ka huce, ka daina fushi da ni...""" "Da sauri ta miƙe ta isa gurin cajojinsu ta ɗauko cajar kwamfuta da ta kasance mai kauri, ta dawo tasa" gwuiyawunta a ƙasa sannan ta miƙa masa. """Ka zane ni My dear... Don Allah kayi min mugun duka har zuwa sadda za ka ji a ranka ka huce kuma" "ka yafe min.""" "Duk da bai karɓi bulalar ba sunkuyar da kanta ƙasa tayi, hannayenta ɗage a sama tana miƙa mishi cajar," a lokaci guda kuma ta cigaba da rera mishi kuka sannu a hankali. "Jikinsa a sanyaye, yasa hannu ya karɓi cajar. Duk da haka bata ɗaga idanu ta kalle shi ba, sai runtse idanu" tayi tana jira ta ji saukar duka ta ko ina a jikinta. "A hankali, da wani irin salo na slow motion ya zame gwuiyawunsa zuwa ƙasa bayan yayi hurgi da cajar" gefe ɗaya. Rungumeta yayi tsam-tsam a ƙirjinsa. A tare ita da shi suka saki nannauyar ajiyar zuciya. A kunnenta ya raɗa mata da wata irin tattausar murya """Na yafe miki Bintuna. Allah ya yafe mana gaba ɗaya. Ni ma ina roƙonki ki yafe min, tun farko...""" Da sauri tasa tafin hannunta ta rufe mishi baki. A shagwaɓe ta ce """Abinda ya wuce mu barshi a wanda ya wuce Abban Aadil. Mu fuskanci gaba kawai da sabuwar rayuwa" "mai cike da soyayya da ƙauna.""" "A lokaci ɗaya suka sake ruƙunƙume juna suna ƙyalƙyala dariya, nan da nan kuma dariyar ta sauya salo," daman kwana biyu sunyi kewar juna. Don haka duk ƙoƙari suke kowa ya nuna ma ɗan'uwansa lallai fa ya fi ɗayan wahaltuwa a wannan yajin da suka ma juna na kwana biyu. "Tun daga wannan rana, suka dawo da gudanar da kyakkyawar rayuwarsu har ma fiye da da. Suka cigaba" da rainon ɗansu Aadil da yake ta kakkaɓa girma tubarakallah cikin ƙauna da soyayya. Basu ƙara tayar da "zancen wata Zulaikha ba, balle kuma igiyoyin auren da aka ƙaƙaba ma Hafizu waɗanda yake ɗaukarsu a matsayin wasan yara." "Kuma yana waya da Iyaye da ƴan'uwansa. Duk bayan sati biyu yana zuwa ƙauye kamar yadda ya saba," amma ko da wasa bai taɓa ba da wata kafa da zai sa ayi zargin lallai shi da Zulaikha ba sa rayuwa a muhalli ɗaya ba. "Domin kamar yadda yake waya da iyayensu da ƴan'uwansu, itama tana waya da su, duk da bai je da ita" "ƙauyen ba, ko da wasa bata taɓa alamta musu lallai fa akwai gagarumar matsala tsakaninta da Yayan nata ba." """Hafizu ya Zulai take? Don Allah don Annabi kar ka ɓoye min komai. Ka ga dai ni ƴar'uwarka ce," "shaƙiƙiyarka wacce za ku kashe ku rufe tare ba tare da wani ya ji abinda muke ciki ba. Na rasa dalilin da yasa duk irin amsar da kake bamu na tana nan lafiya ƙalau, da irin amsar da itama take bamu na kuna zaune lafiya ƙalau ni dai hankalina ya gaza kwanciya. Kuma nayi-nayi da Baffa ya barni ko ni ɗaya in je Habuja in gano halin da kuke ciki ya ƙi, a taƙaice ma doka ya kafa mana gaba ɗayanmu kar wacce ta kuskura ta ce za ta kai ma Zulai ziyara sai ta haihu, idan kuma Allah bai kawo haihuwar da wuri ba sai ta" "shekara cif kafin muje mu gano halin da take ciki.""" "A lokacin da Aunty Balira take mishi wannan maganar ruwa yake sha, amma tsabar yadda maganganun" suka doke shi musamman maganar haihuwar Zulai bai san sa'adda ya shaƙe da ruwan da yake sha ba. Nan take ya fara tari ba ƙaƙƙautawa. """Sannu! Sannu Allah ya sauwake. Ka sha a hankali, ya bi ta ƙaramin maƙogwaro. Sannu Hafizu.""" "Aunty Balira ta faɗa da damuwa a fuskarta, tana zaune kusa da shi tana mishi fifita." """Haihuwa kuma Aunty Balira? Saboda Allah wani irin haihuwa kuma ana zaune ƙalau? Daga yin aure" "kuma a shekara ɗaya sai haihuwa?""" Ya jera mata tambayoyin da dariyar yaƙe a fuskarsa bayan ya samu tarin ya lafa mishi daƙyar. """Ji wani sakarci daga gurin Hafizu. Yo idan rabo na kusa me zai hana Zulai samun ciki ta haihu a cikin" "watanni tara zuwa goma ?""" "Sai kuma ta ƙanƙance idanu ta ƙara ƙure shi da kallo, ta sake jefa mishi tambayar" """Ko dai akwai wata matsala da kake ɓoye mana tsakaninku ne...?""" """Wani irin matsala kuma? Ke dai Wallahi duk kin damu kanki. Babu komai, ina sake maimaita miki babu" "komai. Lafiya ƙalau muke zaune. Idan ma akwai matsala ko ni ban faɗa ba a yadda Zulai take komai na ta a barbaje ai kin san za ta faɗa muku. Ki kwantar da hankalinki pls! Ki cigaba da taya mu addu'a. Ko yanzu abinda yasa ban zo da ita kun ganta ido da ido ba don kar Baffa yayi faɗa ne, amma lafiya ƙalau muke zaune.""" """Madallah! To Allah ya ƙara zaunar da ku lafiya ya kawo rabo mai albarka.""" Tayi addu'ar bayan ta sauke nannauyar ajiyar zuciya. Da waɗannan maganganun da ya shirya mata ya samu ya kashe bakinta. Suka rabu lafiya tana saka mishi albarka. Baiwar Allah Innaye kuwa hankalinta a kwance yake luf kamar tsumma a randa. Daman dai babbar "damuwa da tashin hankalinta akan auren Zulai ce, to tunda wacce za tayi yaƙin dominta ta bada kai bori ya hau ita mene nata da za ta ja ta ƙume kan cewa sai an raba auren? Sai kawai itama ta kwantar da" hankalinta ta cigaba da bin su da fatan alkhairi. Duk ɗaure fuskar da take ma Hafizu yanzu ta daina. Abu ɗaya da ba ta gajiya da shi shi ne a waya suke magana ko kuma ziyara ya kai musu ba ta gajiya da jaddada mishi lallai ya ji tsoron Allah ya riƙe Zulai "amana, idan ya kuskura ya ci amanarta tabbas amana za ta ci shi." """To Innaye! Zan kiyaye in Allah ya yarda. A cigaba da taya mu addu'a.""" Amsar da yake ba ta kenan ako wane lokaci ba don maganganun na ta na shiga kunnensa su zauna a ƙwaƙwalwarsa ba. "[2/1, 11:21 PM] Fareeda Abdallah: Duk zuwa ƙauye idan yayi, Innaye ba ta gajiya da harhaɗa mishi" "tsaraba irinna mutanen ƙauye, musamman waɗanda ta tabbatar Zulaikha tana masifar so. Kuka, kuɓewa, daddawa, garin citta da sauran kayan ƙamshi, garin ƙuli, busasshiyar rama, shuwaka, zogale, magarya, aduwa, goruba, kurna, haka za ta harhaɗa mishi leda-leda gaba ɗaya ta ce ya kai ma Zulai." Sannan ta kawo wasu kayayyakin masu yawa ta ce ya kai ma Matan Abba Lurwanu. Don fita hakki duk sadda ta bashi waɗannan saƙonnin sai tace mishi """Ko za ka kira Fatima ka tambayi idan akwai abinda take so anan sai in baka ka tafi mata da shi? Na san" "su mutanen birni ba kasafai suka cika cimakar ƴan ƙauye ba. Ita kuwa Zulai rainon ƙauye ce, ta saba da" "waɗannan ciye-ciyen.""" """Ai ba ma sai na kira ta ba Innaye. Idan ma akwai abinda take so sai Zulai ta ɗiba mata. Waɗannan" "kayayyakin da kika haɗa ma sun isa, Allah ya saka da alkhairi ya ƙara lafiya.""" "Haka zai ɗauki kayan a boot ɗin mota girma-girma har Abuja, amma tun kafin su isa gidanshi zai yi ma" "Mal Musa umarnin su fara wucewa gidan Mummy Saudah. Can yake damƙa ma Mummy tsarabar da cewa ga tsarabar ƙauye nan, haka Mummy da Hajja za suyi ta godiya suna saka albarka." "Tun kafin ya bar gidan, Mummy za ta kira Zulaikha tayi mata umarnin shiga da kayayyakin kicin." """Tsarabar gida ne Yayanku ya kawo mana, ki rarraba komai ki adana inda baza su samu matsala ba kin" "ji ƴan matana?""" """To Mummy.""" "Daƙyar take iya buɗe baki ta gaisar da Hafiz sannan ta kwashi ledojin zuwa kicin, da yake an ce ba'a raba" hanta da jini. Da ganin irin kayayyakin da ke cikin ledojin Zulaikha take gane takanas-ta kano wannan "saƙon nata ne daga hannun Innaye. Daɗi ne yake cika mata zuciya, sai tayi murmushi kawai ta cigaba da rarraba kayan zuwa inda suka fi dacewa." Abubuwan ciye-ciye kuma tun kafin ta fice daga kicin ɗin za ta ɗiba ta wanke na wankewa ta kai ma Mummy da Hajja falo. "A kwanakinta na farko-farko a gidan, idan Hafiz yaje har ya gama zamansa ya tafi bayan gaisuwa ba ta" ƙara yarda wata magana ta shiga tsakaninsu. Sai wata rana da Hajja tayi mata tatas ta umarci taje ta raka "ɗan'uwanta gurin mota, haka ta fice ta bi bayanshi tana zumɓura baki." """Hmmm! Komai akai da jaki ai sai ya ci kara. Sai yanzu na ƙara yarda da aka ce baƙauye sai ya shekara" "arba'in a birni kafin ɗabi'a da al'adun mutanen ƙauye ya bar jikinshi...""" """Jaka mai faɗa irinna ƴan daba tana can yanzu za'a tadda ta a gida, da tsinin bakinta irinna jaɓa." "Ƙauyanci kuwa naga duk za ni ce ta tadda muje mu, wanda yake gorin shi ma har yanzu ɗabi'a da al'adun" "ƙauyawan bai sake shi ba tunda ko shekara ashirin baiyi a cikin birnin ba.""" "Tana gama faɗin haka ta wuce fuuuu, ta koma cikin gida ta barshi tsaye a gurin, baki da hanci buɗe don" tsabar mamakin irin ƙwarin gwuiwar da Zulai ta samu har ta iya mayar mishi da mummunan baƙar magana irin wannan. "Bai ma san ta shige ba, sai da ya dawo hayyacinsa yaga ba ta a gurin. A fusace ya ɗaga ƙafa zai bi ta ya ci" "ubanta sai kuma ya tuna a gidan Mummy take fa, idan yayi wani mummunan action lallai zai zunguro sama da kara, ƙarshenta Zulaikha ta tona mishi asiri, mutuncinsa na shekara da shekaru ya zube ƙasa war-was a idanun Mummy." "Mota ya shige a fusace, ya ɗauki wayarsa ya lalubo tsohon lambar Aunty Balira da a yanzu ya zama" "mallakin Zulaikha ya danna mata kira, yana fara ringing kuwa cikin sa'a ta ɗaga da siririyar sallama a bakinta." """Ke don ubanki ni kike faɗa ma baƙar magana? Ni sa'an ki ne...?""" """Wrong number""" "Ta katse shi da faɗin haka tun kafin ya aje numfashin maganarsa, kafin ya sake cewa komai ƙit! ta katse" wayar. Ko da ya sake kira fiye da sau bakwai na'ura na faɗa masa wayar a kashe take. "A fusace ya buɗe motar ya fita ya ƙwalawa direbansa kira, wanda yake zaune acan gurin Maigadin gidan" "suna hirar rayuwa. A wannan ranar, haka ya isa gida ranshi na ƙuna da raɗaɗi, duk yadda Bintu tayi" "ƙoƙarin shawo kanshi ta kasa, kuma ya ƙi faɗa mata takamaimai abinda ya ɓata masa rai." "A ƙarshe sai kawai yayi mata ƙaryar kanshi ke ciwo, da rawar jiki ta ɗauko mishi paracetamol yasha," "sannan ta lallaɓashi ya kwanta, ta daidaita mishi yanayin sanyin A.C ta bashi guri da cewar yayi barci." """Idan ka huta, in sha Allah ciwon kan zai tafi. Allah ya baka lafiya Sweetheart.""" """Ameen.""" "Ya amsa daƙyar yana cije laɓɓa, kamar da gaske ciwon kan yake yi. Nan kuwa tsabar ɓacin ran kalaman" Zulaikha ne da suke ta amsa kuwwa a ƙwaƙwalwarshi kamar bitar karatu. Wannan shi ake cewa baki "idan ya san abinda zai faɗa, bai san amsar da za'a mayar mishi ba." "Tun daga wannan ranar, bai ƙara gangancin taƙalarta da mummunar magana ba. Sai dai ya ƙara kamewa" "daga gare ta, idan ya je gidan, ta gaishe shi a gaban mutane yana iyakar ƙoƙarinsa wajen amsawa da" "sakin fuska. Amma idan zai tafi ta bi bayanshi da niyyar yi mishi rakiya ko kallonta ba ya yi, balle har ta saka ran zai amsa Allah ya tsare hanyar da take mishi." ***** ***** "Da gaske ne da ake cewa babu wani al'amari da ya gagari bawa ya koya, sai dai idan tun asali shi wannan" "bawan bai saka a ranshi yana so ya koya ba. Zulaikha da ta saka ma ranta kuma ta ƙwallafa zuciyarta tana so lallai ta koyi turanci, sai ga shi a cikin watanni biyu an shiga na uku sosai bakinta ya faɗa da turanci." Bayan ƙoƙarin koyarwa kuma a sauƙaƙe da makarantar online ɗin da Karima tayi mata register suke da "shi. Mummy, Karima, Imam sun taimaka mata ƙwarai gurin faɗawar bakinta a iya magana da turanci, domin gaba ɗaya suka daina yi mata magana da Hausa, sai turanci." "Tun tana fahimta kaɗan-kaɗan, suna fassara mata manyan kalmomin da suke amfani da su a jimlolin" maganganunsu. Wata kalmar kuma idan ta gani ko a kafar sadarwa a google take searching ta ga ma'anarta da Hausa. Daga nan fa ta kafa ma kalmar ƙahon zuƙa kenan har sai ta haddace a ƙwaƙwalwarta. Yanzu dai a gidan idan aka ji tana hira da hausa tana ƙyalƙyala dariya da Hajja ne kaɗai. Sauran mazauna "gidan idan tana so suyi dogon hira dole sai da turanci, tun tana kwaɓo jagwalgwalo suna dariya, a haka har bakinta ya goge da iya turancin." "Da gaske ne fa da aka ce da babu makoyi gwani ma da ya ji kunya. Zulaikha dai ta dage da koya, kuma" Alhamdulillahi ta ɗauko hanyar zama gwana. "Ta inda rayuwarta yake burge mazauna gidan shi ne, ba ma turanci kaɗai ba, abubuwa da yawa waɗanda" "bata iya ba a baya, yanzu ka'in da na'in ta dage da koyonsu. Rayuwarta ya ɗauko hanyar canjawa gaba ɗaya, ta fara zama wata ƴar gayu kuma ƙasaitacciyar mace ta musamman. Komai na ta ya canja, hatta yanayin yadda take magana yanzu a ƙasaice kuma cike da yanga da nutsuwa take yi. Saboda kuskure" "ƙalilan za tayi Karima ko Mummy su gyara mata, ita kuma da hanzari take karɓar gyaran tayi godiya." Yawan zuwan Hibbah gidan akai-akai. Da kuma yadda take ɗaukarta a mafiyawancin lokuta tana raka ta "guraren sana'arta, ko babu Karima a gidan Mummy bata cika hana fitar ba, saboda ta yarda da nutsuwar Hibba da kamun kanta. Wannan yawan fitar, tana haɗuwa da wayayyun ƴanmata iri-daban-daban, shi" ma ya ƙara taimakawa ƙwarai da gaske gurin gogewarta. Abun daɗin shi ne har yanzu bata yarda ta zubar da kyawawan halayenta na koyi da addininmu ba. Duk "wani abu da za tayi addini shi ne gaba, kafin aikata komai." ***** ****** """Daddy pls kar ka yanke wayar, ga Aunty Zulai ta shigo ku gaisa.""" Imam bai jira amincewar uban ba ya ruga a guje ya kamo hannun Zulaikha da shigowarta cikin falon "kenan da waya maƙale a kunnenta, tana magana tana sakin wani lallausan murmushi." "Ita da Mashkura ce a wayar, wacce da farko kamar zumuncin nasu zai yanke bayan barin Zulaikha gidan," saboda tsoron abinda zai je ya zo kasancewarta ƙanwar Bintu. "Shi yasa Zulaikha ta so yanke duk wata alaƙa ta kusa ko ta nesa da ita. Amma saboda naci irinna Mashku," "duk yadda Zulaikha take ƙin ɗaga wayarta ita kuma ba ta taɓa gajiya da kira ko nuna ɓacin ranta ba har dai ta gaji ta sakar mata. Suna gaisawa da zumunci ta waya sosai da sosai, tunda har yanzu da take cikin" wata na uku a Abuja ta ƙi yarda Mashkura ta san gidan da take zaune. """Oyoyo Aunty Zulai.""" Imam ya faɗa cikin karaɗin murna sannan ya rungumeta kamar sun daɗe basu haɗu ba. Riƙe shi tayi ita ma tana dariya fuskarta na nuna jin daɗin ganinshi ƙarara. Da harshen turanci take tambayarsa yaushe ya dawo gidan? Ina tsarabar makaranta da ya kawo mata? """Tsarabarki na nan ta musamman Aunty Zulai. Ga Daddyna can ya kira Vidio call a wayar Granny, zo" "muje ku gaisa. Pls yau ma kar ki ce a'a! Pls... pls... pls Aunty Zulai... ba don shi ba don ni kaɗai.""" "Ya ƙarasa mata magiyar a marairaice, lokaci guda kuma yana ɗan jan hannunta zuwa inda wayar take" ajiye akan kujera. "Kamaluddeen, babban ɗan Mummy Saudah kuma baban Imam, wanda ziyarar aiki na tsawon watanni" "shida ya kai shi ƙasar Gambia. Watanninshi biyu acan ƙasar Zulaikha ta zo gidan, har izuwa yanzu da yake wata na biyar acan ƙasar ko sau ɗaya bai taɓa gaisawa da Zulaikha a waya ba." Sai dai yana ganin hotunanta jefi-jefi a status ɗin ƙanwarsa Karima. Sannan labarin Aunty Zulai a bakin "Imam ɗan shi sai dai idan bai kira a waya an haɗa shi da yaron ba. Tun yana kore hirarta daga bakin ɗan har ya haƙura, domin matuƙar yana so hirar shi da yaron yayi tsawo to kashi biyu cikin uku na hirar" labarin Aunty Zulai da irin yadda take kula da yaron ne. "Idan ya zauna shi kaɗai har mamaki yake yi, na yadda a cikin ƙanƙanin lokaci shaƙuwa mai girma ya shiga" tsakanin Imam da Aunty Zulai amma bai shiga tsakanin yaron da Safina da ta kasance ƙanwa a gurin marigayiya Aisha mahaifiyar Imam ba. "Yau dai haka kawai, shi da kanshi ya ji a ransa lallai ya kamata ya ga Aunty Zulan nan ya gaisa da ita." "Sannan yayi mata godiyar irin kulawar da take ba yaronsa, ko a ɓangaren Haddar karatun Alƙur'ani mai girma na yaron da a baya yake tafiyar wahainiya, amma a yanzu ba ƙaramin nisa yayi ba, abin mamaki" har ya kusa haɗa izufi goma cif a kansa. Ko da uban ya tambayeshi ya akai haddarshi take sauri yanzu? Kai tsaye yaron ya faɗa mishi Aunty Zulai "ce take ƙara mishi, kuma tayi ta maimaita mishi cikin nutsuwa da lalama har sai ya haddace." Duk diramar da yake gudana tsakaninta da Imam na yadda yake ƙoƙarin janyo ta zuwa gurin wayar ita "kuma tana tirjewa, tana ba shi wasu ƙananun uzurirrika marasa muhimmanci yana jin su. Amma ba ya" "hangen fuskarta sosai sai gefen kafaɗunta. Shi kaɗai ta cikin wayar, babu abinda yake yi sai murmushi." """Haba Aunty Zulan Imamu. Kiyi haƙuri mana don Allah, yau dai ɗaya ki gaisa da Baban Imamu shi ma" "yaga wacece Auntyn Imam.""" Mummy da take zaune acan kan dining ta saka baki don kawo ƙarshen taƙaddamar da ke tsakanin Imam da Zulaikha. """To Mummy.""" "Zulaikha ta amsa a kunyace, don bata san Mummy na zaune a falon ba. A kunyacen dai ta bi bayan Imam" da har lokacin ya ƙi sakin hannunta har suka ƙarasa kusa da wayar. "Daƙyar ta iya ɗaga kai ta saci kallon fuskarsa, wani kwarjini da haiba sosai da yayi mata a idanunta yasa" babu shiri ta zube a ƙasa ta fara gaishe shi a daburce. """Ina yini...? Au! Ina kwana...? Lah! Yi haƙuri... Good evening.""" Ta ƙarasa maganar a tsorace da tunanin kila ma ba ya jin hausa. "Da wani irin tattausan murya mai tafe da zallar kwarjini da mazantaka ya fara magana, har lokacin" murmushin da yake yi bai bar kan fuskarsa ba. """Aunty Zulan Imam! Barka da yamma. Ai ni ya kamata in gaishe ki, saboda ƙoƙarin da kike yi wajen jure" "surutun Imam. Na gode. Allah ya saka miki da alkhairi.""" """Amin. Nima na gode.""" Ta amsa a kunyace sannan ta tashi da ɗan gudu-gudu har tana harɗewa ta wuce ɗakinta. Mummy da Kamal suka bi ta da kallo fuskokinsu cike da murmushi. Shi kuwa Imam me zaiyi in ba ƙyalƙyala dariya ba. "Tun daga wannan ranar, bata sake yarda gaisuwa ta waya ko ta Vid call ya shiga tsakaninta da Baban" "Imam ba. Don a yadda take ji a zuciyarta kamar ma tsoronshi take ji, shi yasa sawunta a likkafa da ta ga an fara gaisawa da shi za ta zame ta gudu zuwa ɗakinta." ***** ****** "[2/3, 12:04 AM] Fareeda Abdallah: ""Sweetheart?""" Ya kira ta a tausashe. "Siririyar hamma ta sake, cikin saiɓi da mutuwar jiki ta sake gyara kwanciyar kanta a ƙirjinshi." """Na'am...My Dear.""" Ta amsa aɗan shagwaɓe. "Lallausan gashin kanta ya cigaba da shafawa, yana mata waiwayi sannu a hankali. Kamar bazai yi magana" "ba, can kuma sai ya ce" """Jibi idan Allah ya kaimu, ki shirya da wuri. Tare za mu tafi Faƙo...""" "Da saurin gaske ta ɗago kanta tana kallonshi cikin ido, sai kuma tayi laƙwas! Ganin shi ma kallonta yake" "yi, yana karantar yanayinta. Saukar da ƙwayoyin idanunta ƙasa tayi a hankali, sai kuma ta mayar da kanta ƙirjinsa ta kwantar, duk a ƙoƙarinta na danne maɗaukakin tashin hankalin da yake taso mata." """Aadil just 4 month yake da a duniya. Ba ka tsoron muyi doguwar tafiya da shi ya kwashi iskar hanya?" "Ka san mura a jikin jarirai fa, yanzunnan sai ta zame musu Nemonia...""" """Babu abinda zai faru in sha Allah! Za mu tafi tare da shi, kuma mu dawo lafiya. Ki tuna fa yaushe" "rabonki da Faƙo? Tun bayan haihuwar Aunty Balira, to ga Babyn nata nan har yayi 2years. Duk irin jinyar" da Innaye baki samu kin je gaisheta ba saboda laulayin ciki. An haifi Aadil har yau Innaye bata taɓa "ɗaukar gudan jinina ba balle ta saka mishi albarka. Jibi tare za mu tafi tabbas, ku shirya da wuri.""" """To shi kenan! Allah ya kaimu.""" "Ta amsa da sanyin jiki, duk zuciyarta a ƙuntace. Amma ba ta da yadda za tayi ta nuna mishi, saboda ko" kaɗan ba ta ƙaunar abinda zai sake janyo wani saɓani ko misƙala zarratin a tsakaninsu. "Shiru suka yi duk su biyun, kowa da irin mabanbantan tunanin da yake yi a zuciyarsa. A haka barci ya" kwashe su. "Washe gari da yamma, bayan sun dawo guraren aikinsu, suna zaune a falo suna hira. Tana zaune a" "gefensa, Aadil na riƙe a hannunsa yana mishi wasa, yaron kuma sai dariya yake yi, da alamun ya fara" gane fuskar Babansa. A tausashe ya kalleta ya ce """Gobe idan muka je gida, duk irin magana ko tambayar da za'a yi miki game da Zulai ki amsa musu da" "to kawai, ki kuma tabbatar musu muna zaune lafiya ƙalau. Kin gane?""" """Eh!""" "Ta amsa, ba don ta gane ɗin ba." """Good. Duk da tun bayan faruwar al'amarin har yau bamu zauna ni da ke na warware miki yadda" "al'amuran suka faru ba, domin a ganina sam hakan ba shi da wani amfani, tunda dai matsalar na riga na maganceta. Amma na san a wancan lokacin Raudha ta yi miki bayani kamar yadda nayi mata, ko ba haka" "ba?""" """Haka ne.""" "Ta amsa, a zuciyarta take sake tunano cikakken bayanin da Raudha tayi mata wancan lokacin, wanda har" "yayi sanadiyyar zubda makaman kishinta, hankalinta ya kwanta luf kamar tsumma a randa." """Madallah! To ko bayan da na magance matsalar har yanzu su Innaye basu san takamaimai halin da" "ake ciki ba. Akwai lokacin da na tsara zan musu cikakken bayanin komai, yadda ransu bazai ɓaci da ni ko ke ba, amma ba yanzu ba. Don haka gobe idan mun je ki kama bakinki, kar ki kuskura ki bada wata kafar da zai sa su gane akwai matsala tsakaninmu da Zulai. Kin gane ko?""" """Eh""" Ta amsa a sanyaye. Shiru yayi yana cigaba da yi ma ɗanshi wasa. Can bayan wasu daƙiƙu ta matsa kusa da shi ta rungume shi ta gefen kafaɗarsa. """Na gode My dear... Na gode. Ina roƙon Allah yabar ƙauna da tabbatacciyar soyayya a tsakaninmu. Da" "ace a wancan lokacin baka ɗauki matakin da ya dace ba, na tabbata da yanzu na daɗe a kushewata...""" """Shshshshhhhhhh! Kar ki sake faɗan irin wannan maganar.""" "Ya katse ta da sauri, jin tana zancen mutuwa." """Na daina Daddyn Aadil. Allah ya huci zuciyarka.""" "Bai amsa ba, sai lallausan murmushi da ya sakar mata, kafin ya mayar da hankali kan Aadil yana cigaba" da yi mishi wasa. ***** Washe gari da sassafe suka kama hanyar tafiya Faƙo kamar yadda suka tsara. Saboda a ranar yake so "suje su dawo. Bayan motarshi shaƙe yake dam da tsaraba, saboda a wannan karon ba tsarabarsa bace" "kaɗai, har da zannuwan da Bintu ta lodo da sunan za tayi tsaraba wa su Innaye." Wani irin shirin jibga-jibgan kayan sanyi da Bintu tayi ma Aadil shi kaɗai ya isa abin dariya. Amma a "zahirin gaskiya kayan ta saka mishi ba don iskar hanya bane, ta saka mishi ne duk a ƙoƙarinta na kiyaye" yaron daga kwasar cututtuka saboda ɗaukar da take tunanin zai sha a hannun mutanen gidansu Hafiz. "Da yake gudu sukai ba na wasa ba, ƙarfe goma sha ɗaya da rabi ta yi musu ne a ƙofar gidansu Hafiz na" "ƙauyen Faƙo. Wani sauƙi da Hafiz yake ganin sun samu shi ne taron sunan Balki, ƴar ɗakin Umma laraba da ake yi anan gidan Baffan." "Haihuwar fari ce, kuma ta zo mata da gardama. Shi yasa tun daga can asibiti kai tsaye gidan iyayenta aka" "dawo da ita domin ta samu ingantaccen kulawa. Yau ta kama suna, don haka sun tarar da gidan Baffan ne damƙam da ƴan'uwa da abokan arziki, wanda hakan ko kusa baiyi ma Bintu daɗi ba, domin ta san jagwalgwalon da Aadil zai sha a hannun mata ƴan ƙauye sai ya ninka wanda tayi tsammanin zai sha da" farko. "Motar na fakawa, kafin ma tayi yunƙurin saka yaron a ɗan abin ɗaukarsa mai kama da kwandon ɗaukar" jarirai ta kulle shi har Hafiz ya ɗauki yaron daga cinyarta. Ya buɗe mota ya fice waje sannan ya saɓa ɗan a kafaɗarsa """Fito muje. Kin ga na manta yau ake sunan Balkin Umma Laraba. Kin ga shi kenan ma mun samu sauƙi," "ba sai munyi ta jelar zuwa gidajen ƴan'uwa a gaisa ba. Na san duk za mu tarar da su a nan gida.""" """Haka ne.""" Ta amsa daƙyar! Tana jin yadda bakinta ke wani irin ɗaci kamar ta tauna flagyl. "Tun kafin su shiga cikin gidan, har labarin isowarsu ya riga isa cikin gidan. Ko kafin Bintu ta fito daga cikin" mota har wasu daga cikin ƴan'uwansu sun lulluɓe jikin motar suna yi musu barka da zuwa. """Yauwa... Sannunku. Labaran, Inusa, ina su Kadiri? Ku zo a buɗe muku boot ku kwashi kaya ku shiga da" "su cikin gida.""" "Ya faɗa da fara'a sosai a fuskarsa, idanunsa na kan ƙannensa maza da yayi ma umarnin kwasar kaya." """Hafizu? Ina Zulai? Baku taho da ita ba?""" "Indo ta tambaye shi bayan ta ga Bintu ce kaɗai ta fito daga cikin motar, kuma ta rufe ƙofar ba tare da ta" ga fitowar Zulai ba. "Kafin ya amsa ma Indo ƙanwarsa Halima ta miƙa hannu da nufin karɓan Aadil, nan take kuwa ya sakar" mata shi ba tare da wani damuwa ba. """Oyoyo Babanmu! Tubarkallah ma sha Allah! Kai ne haka kayi kukkuɓeɓe barakallah? Hajiya Bintu" "sannunku da zuwa.""" Bata jira amsawar Bintu ta take ta ƙoƙarin haɗiye wani gululun takaici da ya tsaya mata a wuya ba ta wuce da yaron cikin gida. """Zulai tana gida Indo, ban zo da ita ba. Ai ita da zuwa gida sai ta yi wata shidda cif a ɗakin aurenta. Idan" "ba na manta ba haka Baffa ya saka doka ga duk ƴaƴansa mata da suka yi aure, kin ga bai kamata a karya" "dokar daga kanta ba.""" Kafin ma Indo ta amsa nan take sauran ƴan'uwa da suke gurin suka fara yi mishi surutun wannan ai wayau ne. Tunda ita Zulai ɗan gida ta aura ai ko bayan sati biyu ne da yin aure za ta iya zuwa gida. "Shi dai bai sake cewa komai ba sai dariya da yake ta bin su da shi, har suka shiga cikin gidan. Bintu na" "biye da su a baya ranta na ƙara ɓaci, ganin yadda da yawansu suka nuna kamar basu santa ba, babu irin wannan ɓare-ɓaren da rawar jikin da suka saba yi mata acan baya idan tazo garin. Yanzu ta ɗan'uwansu" "da ƴar'uwarsu kawai suke yi, ga ɗan laɓuɓun ɗanta kuma an ɗauke shi an shige da shi cikin ƙauyawa," "salon ya shaƙi numfashi mai cike da cututtuka irin wanda bai saba shaƙa ba. Ƙasa-ƙasa taja tsaki, tana ƙara haɗe fuskarta, a haka har suka shiga gidan suna gaisawa da mata ba ta da wani walwala har suka" ƙarasa ɗakin Innaye. "Bayan mitar da ƴan'uwa suka yi ta mishi na rashin zuwa da Zulaikha, har a fuskar Innaye sai da ya fahimci" rashin jin daɗinta da bata ga Zulai a tare da su ba. """Auta ita kaɗai kuka baro min a gida kenan Fatima?""" """Ba ita kaɗai bace Innaye. Akwai ƙanwata Mashkura. Kuma Daddyn Aadil shi ya ce baza ta biyo mu ba" "sai ta cike wata shida, saboda kar Baffa yayi faɗan zuwanta gida.""" "Bintu ta faɗi maganganun a ɗarare, kanta a ƙasa, tana jin yadda kaifafan idanun Innaye masu cike da" kwarjini suke yawo a sassan jikinta. Aunty Rakiya da Aunty Ladidi kuwa ƙarara suka ce mishi ai dama bai zo da Bintu ba. """Saboda Allah Hafizu kana sane da yadda duk muke ɗokin ganin Zulai, amma kawai sai ka wani zo da" "Bintu ita kaɗai?""" Cewar Aunty Ladidi tana kyaɓe baki. Aunty Rakiya ce ta karɓe zancen da cewa """Ita ma Bintun da tayi zamanta. Yaushe rabonta da garin? Ni Wallahi na zaci ma ta yanke da zuwa" kenan. Zulai da take ƴar nan dai na san baza ta taɓa ƙin zuwa ba ko da za su zo kullum! Amfanin auren "na gida...""" """Ke dallah rufe mana baki. Bana son shirme, kuje ku kawo musu kunun zaƙi mai sanyi kafin a ƙarasa" "abinci.""" Aunty Balira ta katse su fuskarta a ɗaure. "Sum-sum suka fice suna guna-guni, Hafiz ya bisu da kallo ƙasa-ƙasa, zuciyarsa duk ba daɗi da yadda aka" "karɓi Bintu. Bayan kuma a ganinshi rashin zuwanta laifinshi ne, tunda da ya matsa mata tazo, tabbas za ta zo ko da zuciyarta ba ya so. Balle ma ya san Bintu baza ta taɓa ƙin asalinshi ba." Bintu da take ta rarraba idanun ta ina za'a miƙo mata ɗanta fiye da awa ɗaya sai ga shi an kawo shi yana "ta tsala ihu. Hankalinta a tashe, ko ta manta a inda take ne? Ta miƙe zumbur tana zare idanu, da saurin gaske ta miƙa hannu ta karɓe shi tana ɗan dudduba jikinshi" """Me aka mishi ne haka yake kuka? Sam bai taɓa irin wannan kukan ba tunda na haife shi...""" """Wannan ɗan yalolon jinjirin me kuwa za'a mishi a gidan Kakanninshi?""" "Aunty Balira ta katse ta da sauri, daman tana cike da ita ganin yadda tun ɗazu ita kaɗai take ta wani" ciccin magani kamar wacce aka tilastawa zuwa. Da Hafizu kaɗai suke hira da Innaye. "Jin irin tambayar da Aunty Balira ta gwaɓa mata yasa ta dawo hayyacinta, lokaci ɗaya tayi laƙwas, ta" koma gurin zamanta tana jijjiga yaron. """Bai wuce zafi ne ya dame shi ba saboda uban kayan sanyin da kika jibga mishi bayan ba wani sanyi ake" "yi ba. Ki rage mishi kaya, ki bashi ruwa da nono zaiyi shiru.""" "Hafizu dai kanshi na ƙasa, a kunyace da irin rashin karar da Bintu ta nuna a gaban Innaye. Duk da bai" "wani ga laifinta ba, ko shi hankalinshi ba ƙaramin tashi yayi ba da jin irin ihun da ɗan ke callarawa tun kafin su iso ɗakin. Baiken Bintu ɗaya da ya gani shi ne rashin nuna kara a gaban Innaye da Aunty Balira." "Wannan ziyara dai ba Bintu kaɗai ba, hatta Hafizu ba wani daɗinta yaji ba. Saboda yadda ya zaci Innaye" "za ta nuna ɗoki sosai irinna ƙaunar abin cikin ƙwai da yafi ƙwan daɗi bata wani nuna ba. A taƙaice ma yaron ko cikakken mintuna uku baiyi a hannunta ba ta miƙa shi ga Aunty Balira, ita kuma tana karɓa ta" miƙa shi ga Bintu. "Haka suka zagaya ɗakunan sauran matan gidan suka gaishe su, ko ina suka je tambayar ina Zulai? Ya take?" Me yasa ba'a zo da ita ba? Gaba ɗaya ya ƙarasa dusashe ɗan hasken Bintu da ya rage a gidan. "Ko tsarabar da aka raba na zannuwa da kuɗi da sunanta a wulaƙai sukai ta yi mata godiya, babu wani" rawan jikin da suka saba yi idan ta musu kyauta a baya. Duk tsawon awoyin da suka yi a ƙauyen Bintu ta kasa cin komai. Sai ɗan ruwan goran swan da ta ciro a "cikin jakarta kawai take iya kurɓa saboda yadda bakinta ke ta bushewa kamar mai azumi. Daman ba abincinsu take ci ba, ba ta shan ruwan ƙauyen, amma a cikin babbar jakar hannunta akwai robar takeaway shaƙe da snacks, don tsananin takaici da baƙin cikin da suka shaƙa mata ta kasa buɗe jakar ta" ciro balle har ta samu ƙwarin gwuiwar ci a gaban mutane. "Shi kuwa Hafizu ba ruwanshi, kunun zaƙi mai sanyi da Aunty Balira ce tayi aikatau ɗinsa ya sha sosai," "shinkafa da miya da Umma laraba ta aiko musu da shi a kwanon samira sabo ya ɗiba ya take cikinsa, ko tayi bai ɓata lokacinsa wajen yi ma Bintu ba. Domin ya san ba ci za tayi ba, ya sani tun da daɗewa tsarinta ne ba ta iya cin abincin gidan sha'ani." "Har suka gama zamansu Baffa bai dawo ba. Amininsa ne ya rasu acan ƙauyen Guraji, nesa da su kaɗan." "Tun safe Baffan yayi sammakon tafiya can gurin jana'iza, har yanzu uku da rabi bai dawo ba." "Sai saƙon kuɗi masu kauri Hafizu ya bar masa a hannun Innaye, ita kuma Bintu ta bada shaddoji kala uku" da turaruka kala biyu a ajiye masa. """Sannu da ɗawainiya Fatima. Mun gode, Allah ya saka da alkhairi ya raya zuri'a.""" "Innaye tayi ma Bintu addu'a da murmushi a fuskarta, a zuciyarta take jinjina atamfofi kala uku da Bintun" ta bata abokan zamanta kuma kala bibiyu. "Ƙarfe uku da rabi Hafizu suka sallaci la'asar, suka yi sallama da mutanen gidan gaba ɗaya, ƴan'uwa suka" rako su har gurin mota ana musu addu'ar Allah ya kiyaye hanya ya mayar da su gida lafiya. "Da Amin suke ta amsawa har suka shige cikin mota, direba yaja suka kama hanyar komawa gida." "Nannauyan ajiyar zuciya Bintu ta sauke idanunta a lumshe, hannunta ɗaya a kan Aadil da yake kwance a" "jikinta yana barci cikin nutsuwa, a hankali take ɗan shafa kanannaɗaɗɗen gashin kansa irinna jarirai." 'Uhmmm! Allah na gode maka. Idan kun sake ganina a wannan tsinannen ƙauyen naku ku yanka ni.' "Tayi maganganun a zuciyarta. Ranta a ɓace da irin wulaƙancin da su Rakiya suka yi mata a fili, kuma" Innaye na gani bata ce komai ba. "[2/3, 10:17 PM] Fareeda Abdallah: ****** ******" "Ƙwarya-ƙwaryan liyafar cin abinci Mummy ta haɗa ma ƴaƴanta, da dangi na kurkusa sosai, saboda" "murnar dawowar Kamal, Baban Imam. Kuma wani abin burgewa da ƙarin farin ciki shi ne yadda tafiyar tasa tayi nasara, gurin aikinsa da suka tura shi sun samu fiye ma da sakamakon da suka tsammata daga gare shi. Da wannan dalilin yasa tun kafin isarsa gida, ya samu ƙarin matsayi mai girma a gurin aiki, da" kyaututtuka masu yawa daga gurin shugabanninshi. Farin ciki ne ya haɗe musu kan farin ciki. Da wannan dalilin yasa Mummy da ƴan matanta Karima da "Zulaikha, da Mai aikinta Rahina suka shafe fiye da awanni biyar a kicin suna dafa ƙayatattun girke-girke mabanbanta." Da yake kicin ɗin mai faɗi ne sosai sai suka rarraba ayyukan yadda zai musu sauri. Suna aikin Hajja na "zaune gefe guda akan kujera ƴar tsugune tana ba su nishaɗi da maganganunta na ban dariya. Sam ba ta gajiya, ta tsokani wannan ta taɓi wancan, hatta Mummy da ta kasance ƴarta bata raga mata ba." "Haka suka gama aikin ba tare da gajiya liƙis a jikinsu ba, suka lulluɓe komai a gayance. Sannan suka fice" "daga kicin ɗin zuwa ɗakunansu don yin wanka su shirya, kafin mutane su fara hallara. Tunda lokacin da" "aka saka na fara liyafar ƙarfe huɗu ne da rabi na yamma, yanzu kuma ƙarfe huɗu saura kwata." "Kamal ma ya iso daga Lagos tun ɗazu, yana ɗakinsa shi da manyan aminansa guda biyu, Auwal da Isma'il." "Sai Imam da ya ƙi barin mahaifinsa ya huta, duk inda yasa ƙafa yana biye da shi, a ƙarshe nannauyan" barci ne ya ɗauke shi acan ɓangaren Daddynsa. "Tsadaddiyar shadda Mummy ta ware zunzurutun kuɗi tayi musu anko gaba ɗaya iyalanta, kuma wani" "abin burgewa da armashi shi ne, hatta Zulaikha da ta kasance bare a cikinsu bata ware ba, a taƙaice ma, ɗinki da aiki duk iri ɗaya aka yi musu. Ta ƙara da siya musu mayafai masu kyau da za su shiga da kayan, da jaka, da takalma masu sauƙin tsawon dunduniya. Hatta ƴan kunne, sarƙa, zobba, awarwaro da za su saka a wannan rana duk sabbi Mummy ta siya musu. Ƙananun kaya na ciki kuwa abinda yasa bata siya musu da su ba, sati biyu da suka wuce ta kwashe su ita da kanta a mota suka shiga kasuwa, ko wacce ta" "ɗibi abinda take so, Mummy ta biya kuɗin ba tare da jin zafi ko ganin ƙyashi ba." "A farko-farkon zuwan Zulaikha gidan idan suka yi irin wannan fitar, aka ce ta ɗebi duk abinda take so, ba" "ƙaramin kunya take ji ba. Sai Karima ce ke warewa ta ɗiba mata kayayyaki masu yawa kamar yadda ta ɗebi na ta, to kuma sai ya kasance idan sun koma gida ta gwada kayayyakin wasu duk sai suyi mata kaɗan. Da taga dai asara take ja ma Mummy a hankali itama ta ware, duk abinda take buƙata na fannin inner wears ko sutura ba ta kunyar ɗauka, da wannan dalilin yasa a yanzu haka manyan akwatunan suturunta uku. Ita da taje gidan daga ita sai ghana must go. Shi yasa ako wane lokaci cikin addu'o'inta ba ta gajiya da yima Mummy da iyalanta fatan alkhairi, tabbas zamanta da su alkhairi ne, sun taka" muhimmiyar rawa gurin canja mata rayuwarta gaba ɗaya. "Ƙarfe huɗu da kwata Zulaikha ta shiga ɗakin Karima bakinta a gaba, ta saka doguwar rigar shaddarta," amma ko Zip ɗin bata zage ba saboda yadda rigar ta ɗame ta daga saman ƙirjinta. """Aunty Karima kin gani ko? Zip ɗin ya ƙi zaguwa. Sai da nace miki a ɗan ƙara kika ce ayi min wani fitted," "ai yanzu sai ki san yadda za kiyi da ni...""" """Daɗina da ke ƙorafi ba ya miki wahala Zuly. To ai fitted ɗin kenan, dama wa ya faɗa miki idan aka yi" "riga fitted zip yana zaguwa a sauƙaƙe? Juyo bayanki mu gani in zage miki.""" Karima ta ƙarasa maganar tana dariya. "Ko da ta juya, a sauƙaƙe aka zage Zip ɗin, sai dai har lokacin matseta da rigar tayi musamman ta wajen" "ƙirjinta bai saki yadda take so ba, sai ma ƙara fito da shape ɗin su da yayi." "Gaban madubi ta ƙarasa ta kalli yadda rigar tayi mata, ta juyo tana kallon Karima, idanunta sun yi" ƙwalƙwal da hawaye. """Yanzu saboda Allah ta ina mutum zai fara fita cikin jama'a da wannan ɗamammiyar rigar?""" """To miye a ciki? Ba akwai mayafi ba? Kina warware mayafin ta baya kika ɗan yafo shi zuwa gaba tsab" "zai rufe ɗan matsewarnan da bai taka kara ya karya ba, ke kuma sai wani ƙorafi kike yi. Kin ga ni don Allah yi min sassauƙar kwalliya ki ɗaura min ɗankwali, lokaci ya fara tafiya, tun ɗazu naji muryar su Mummy Balaraba da su Aunty Safina. Yanzu za kiji Mummy ta fara ƙwalla kiran mu fito. Ke ina naki" "ɗankwali da mayafin?""" """Suna ɗaki.""" """Je ki ɗauko da akwatin kayan kwalliyarki mu ƙarasa shiryawa anan. Bari in saka ƴan kunne da sarƙa" "tunda ke naga har kin saka.""" "Duk da yadda suke cikin sauri, Zulaikha bata tafi bagazan-bagazan ko kuma ta sa gudu irin yadda take yi" "da ba. A nutse ta fara tafiya, manyan mazaunanta suna wani irin juyawa a slow motion." "Karima ta bi ta da kallo, fuskarta cike fal da murmushi." """Ya Allah! Ina tawassali da kyawawan sunayenka da siffofinka maɗaukaka, ka haɗa wannan baiwa taka" "mai kyawawan halaye da nagartaccen miji ɗaya tamkar dubu. Amin ya rabb!""" "Karima tayi ma Zulaikha addu'ar a fili, Allah ya sani tana ma Zuly wani irin ƙauna mai yawa, jin ta take" "kamar ƴar'uwarta ta jini. A yadda ta saba da ita yanzu, Har ba ta fatan ace ga ranar da Zulaikha za ta bar" gidan. "Yana tsaye a gefen babban dining table ɗin da aka ƙayata kanshi da shimfuɗa mai kyau da ɗaukar idanu," "kafin aka kawo manyan kulolin abinci aka shirya akan table ɗin. Wayarsa ce a hannunsa yana ɗan dannawa, gurin Karima ya nufa don karɓo kayan Imam. Amma ko da ya tunkari ɗakin nata sai yaji suna magana da Aunty Zulai, don haka ya koma da baya saɗaf-saɗaf ya tsaya can gurin dining table yana" ƙoƙarin kiran Karima a waya. "Kamar ance ya ɗago kanshi, karaf idanunsa suka faɗa kan bayan Aunty Zulai da take tafe kamar wata" "wahainiya, baki da hanci buɗe ya bi ta da kallo da waya riƙe a hannunsa, har ta shige ɗakinta." "Yana nan tsaye ya sake ganin ta fito, matsewar rigar da yaji tana yi ma Karima ƙorafi ya gani a fili. Da" sauri ya kawar da idanunsa yana ta'awizi a zuciyarsa saboda yadda abubuwan suka ɗauki hankalinsa cikin ƙanƙanin lokaci. "Ita kuwa da yake hankalinta ba shi akan kalle-kalle, bata ma san yana yi ba har ta sake shigewa ɗakin" Karima. "Ya ɗauki fiye da mintuna uku tsaye a gurin, ba tare da ya san takamaimai tunanin me yake yi ba. Muryar" "Safina da ya ji tana fitowa daga ɓangaren Mummy, yasa shi barin inda yake tsaye da sauri, tun kafin tazo" ta ishe shi da balaƴaƴƴen surutunta. "Sai da ya isa ɓangarensa, sannan ya kira Karima a waya yana mata ƙorafin barin masa hidimar Imam da" tayi yau don kawai ta ga ya dawo. """Yaya nima fa tuntuni Imam ya yaye ni, yanzu Zuly ce" ". Komai nasa ita take mishi, ba ya yarda inyi masa wata hidima. Ka turo shi ta shirya shi, daman yanzu ta" "gama ƙorafin ka riƙe shi a gurinka ko shiryawa baiyi ba...""" """Lah! Kai Aunty Karima... Ni de ba ruwana...""" Daga can cikin wayar yaji muryar Aunty Zulai tana faɗin haka a shagwaɓe. "Haka kawai, wani ƙayataccen murmushi ya suɓuce masa a fuskarsa. Jikinsa a saiɓance ya katse wayar," har lokacin murmushin da yake yi bar kan fuskarsa ba. """Dude. Ya aka yi ne?""" Isma'il ya tambaye shi. """Nothing.""" Ya amsa a taƙaice. Sannan ya mayar da hankalinshi kan Imam da yake zaune akan kujera yana daddana sabuwar Tab ɗin da ya kawo masa a cikin tsarabarsa. Da harshen nasara yace """Imam, oya ɗauki Tab ɗin maza ka tafi cikin gida a shiryaka. Lokaci ya tafi, Aunty Zulai tun ɗazu take" "jajen inda ka shige...""" """Ok Dad!""" Ya amsa tun kafin uban ya rufe bakinsa. Da saurin gaske ya fice daga falon ya nufi cikin gida. Alhamdulillah! Anyi liyafar cin abinci lafiya an gama lafiya. Zulaikha da ta kasance baƙuwar fuska a "cikinsu ita ce ta dinga shan kallo, da tambayar Mummy wacece ita? Abu ɗaya da yayi ma Zulaikha daɗi shi ne yadda tun ma kafin Mummy ta amsa Hajja tayi karaf ta ce" """Ƴar ƙanwata ce tazo daga can gida.""" Da haka ta kashe bakunan ƙannen mahaifin Karima biyu mata da suka fi takura mata da kallo duk inda ta "motsa. Daga yanayin fuskokinsu, za a gane sam basu ji daɗin amsar da Hajja ta basu ba. Musamman duba da yadda Imamu ya maƙale ya mata, alamun shaƙuwa ƙarara tsakaninsu har ma fiye da ƴaƴayensu. Domin duk sun je gidan ne da ƴaƴansu mata budarai, zukatansu cike da burin Imamu ya zaɓi ɗaya daga" cikin ƴaƴan a sake ƙulla zumunta mai ƙarfi. "Ita Aunty Balaraba, da ta kasance mai bi ma mahaifinsu Karima, ƴarta ta farko Aisha ita Kamal ya fara" "aura, cikin hukuncin Allah sai zaman baiyi tsawo ba, gurin haihuwar Imam Allah ya karɓi rayuwarta." "Daga baya ƙarara Aunty Balaraba ta sake ɓullo mishi da tayin auren Safina, wacce a wancan lokacin" "yarinya ce sosai. Ba tare da wani ɓoye-ɓoye ko kwana-kwana ba ya ce ayi haƙuri, shi kam dai ba ya buƙata a lokacin." "Rasuwar matarsa Aisha ba ƙaramin bugunsa yayi ba, shi yasa ya tattare zancen auren gaba ɗaya ya" "jingine gefe ɗaya. To tun a wancan lokacin dai basu haƙura ba, shekaru shidda kenan. Safina ta zama cikakkiyar budurwa, kuma ƙarara ita ma take nuna mishi tana ra'ayinshi." Ita kuwa Aunty Lubabatu da take bin Aunty Balaraba a haihuwa irin abinnan ne na bahaushe da yake "cewa a rashin tayi ake barin arha. Tun a wancan lokacin, duk sun san Kamal ya ce baya ra'ayin auren Safina, don haka a yanzu da nata ƴar mai suna Salma ta taso ta zama budurwa sai take cusa ta, da addu'ar Allah yasa rabon a gidanta yake. Domin Kamal miji ne na kerewa sa'a, na bugawa a jarida. Tun" Salma tana nuna ba ta ra'ayinshi har dai uwar ta fara cin galaba a kan ta. Amma dukansu da yake sun san Kamal ɗin ba'a zuwa mishi da wargi. Hatta ƙannan uban nashi a hankali "suke bin shi, saboda girmamawa ce tsakaninshi da su gaba ɗaya. Ga alkhairin da yake musu ako wane lokaci kamar bai san zafin kuɗi ba. Shi yasa duk suke abin nasu cikin iya taku da gogewa don kar su ƙona" sunkurun kashinsu. "Ita kanta Mummy, duk da ɗan'uwan nasu ya bar duniya. Har yanzu tana ɗaukarsu da girma sosai, kamar" ƴan'uwanta ne su ɗin ba na mijinta ba. Sannan duk wani sha'ani nasu idan ya taso da jikinta da aljihunta ba ta jin ƙyashin yi musu hidima. Sosai girmamawa da mutuntawa ke tsakaninsu. "[2/4, 10:46 PM] Fareeda Abdallah: Ko a yanzu, bayan gama liyafar cin abincin ya miƙe tsaye yayi musu" "godiya sosai. Da yake tun farko Mummy ta tsara abin a ƙayyade ne, ta lissafa mishi duk waɗanda za su halarta." Ya riga ya gama shirya duk abinda zai raba musu na tsaraba ya damƙa ma Mummy. Yana gama yi musu godiya yaja abokansa zuwa ɓangarensa. Bayan gama tattare duk abubuwan da aka yi amfani da su Karima da Zulaikha Mummy ta umarta kan "cewa suje ɗakin Hajja su kwaso mata jakunkunan tsarabar da suke ajiye a cikin ɗakin. Abinku da ƴan boko wayayyu, masu yin komai cikin tsari, ko wace jaka maƙale take da sunan mamallakiyarta, kuma saman jakar a rufe yake da wani irin abin maƙalewa, babu wacce za ta ce ga abinda ke cikin jakar" ƴar'uwarta in dai ba buɗe jakar aka yi ba. "Cikin nutsuwa Mummy ta gama rarraba musu tsarabarsu. Ta ƙara da yi musu godiya sosai, zuwa ƙarfe" "takwas na dare, gidan ya zama saura su kaɗai, baƙin da suka halarci liyafar duk sun koma gidajensu," zukatansu cike da farin cikin tsarabar da Kamal yayi musu. "Misalin ƙarfe goma da rabi na dare. Kamal ne kwance a gefen katifar Mummy can cikin Bedroom ɗin ta," "hira suke yi a nutse. Yana sake bata labarin yadda yanayin tafiyarsa ta kasance, da irin yadda komai yazo" "masa a sauƙaƙe acan ɗin, da irin nasarorin da ya samu a tafiyar tasa." Bayan ta gama jera mishi fatan alkhairi da addu'ar Allah ya ƙara ɗaukaka sai ta kira sunanshi a nutse. Da irin salon da ke nuna lallai ko me za ta faɗa muhimmiyar magana ce za ta yi mishi. """Na'am! Mummyna.""" Ya amsa a tausashe. Yana ƙara ba ta dukkan hankali da nutsuwarsa. """An daɗe idan nayi maka maganar aure kana cewa ka damƙa min wuƙa da nama wajen zaɓin matar" "aure. Tambayarka zanyi, ka samu matar auren ko har yanzu lalube kake a cikin duhu ko kuwa jiran tsammani kake yi?""" """Mummy, babu ko ɗaya gaskiya. Zancen auren ne fa gaba ɗaya na jingine shi gefe ɗaya. Ko kin sama" "min matar auren ne?""" "Ya tambayeta, da murmushi a fuskarsa." """Eh! Na sama maka.""" Ta amsa da dukkan gaskiyarta. "A nutse ya miƙe zaune daga kishingiɗar da yayi, saboda yadda maganar ta bugi zuciyarsa. Bai taɓa ɗauka" "za ta ce ta zaɓa masa mata ba, shi yasa a yanzu da ta faɗi ta zaɓa masa maganar ya bashi mamaki." """Wace ce? Mummy wa kika zaɓa min? Kin sani ni mai biyayya ga umarninki ne ko da zuciyata ba ta" "so...""" """Babu ma zancen dole a ciki. Shawara ce ba umarni ba. Kaje kayi addu'a, ka nutsu, ka kalli rayuwar" "ɗanka da Allah ya baka a yanzu da can gaba. Zulaikha, ita ce yarinyar da na zaɓa maka saboda dalilai masu yawa. In dai kaji zuciyarka ta nutsu da ita, ni kam ina maraba da ita a matsayin sarkuwa, domin na" "yaba da ita ɗari bisa ɗari...""" """Aunty Zulan Imam kike nufi Mummy? Kina ganin banyi mata tsufa ba? Shekaruna talatin da takwas fa," "ni ina mata kallon kamar yarinya ce ƙarama.""" """Ba wani tsufa da kayi mata, sai dai idan bata yi maka ba, bazan tilastaka ba. Kaje ka huta, kayi addu'a," "kayi tunani a nutse. Zuwa nan da sati mai zuwa kazo min da cikakken amsar da ka yanke.""" """To Mummy. Allah ya tabbatar mana da alkhairi.""" """Amin ya rabbi.""" "Da haka suka yi sallama ya fice zuwa ɗakinsa, zuciyarsa cike da tunanin maganganun da suka yi da" Mummy. "A wannan dare, duk irin gajiyar da ke jikinsa bai samu wani wadataccen barci ba. Da ya fara sai ya farka a" "nutse, zuciyarsa sai hasko masa Zulaikha take yi a sadda ya ganta ɗazu babu mayafi, da kuma irin ganin da yayi mata lokacin liyafar nan." "Babu laifi, ta yi daidai gwargwado. Sai dai abin dubawar shi ne ita za ta iya amincewa da shi a matsayin" "mijin aurenta kamar yadda Mummy take so? Domin shi fa bai wani iya soyayya ba, ko Aisha a haka suka yi rayuwar babu wani romansiyya ta musamman." "Wayarshi ya ɗauko, ya buɗe hotunan status da ƙanwarsa take sakawa na Zulaikha ya fara kallo ɗaya" bayan ɗaya. """Uhmmmm!""" "Yaja nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, sannan ya ajiye wayar gefe ɗaya." "Zuzzurfan tunani ya afka a ciki na tunanin makomar rayuwar ɗanshi Imam, kamar yadda Mummy ta" umarce shi. Ya sani ko ya ƙi ko ya so duk tsawon zamani dole ya nema ma Imam wacce za ta zame mishi makwafin uwa. "Ada can baya har ya fara tunanin zai iya haƙuri ya auri Safina ko don saboda Imam, amma sai yaga sam" babu wata shaƙuwa ko shiri tsakanin Imam da Safina. Idan Imam yaje can gidan yi musu hutu a "matsayinsu na kakanninshi, duk dawowa idan Imam ɗin yayi ya dinga mishi ƙorafin Aunty Safina kenan, ya dai fahimci kamar ba ta da haƙuri da yara. Da wannan dalilin yasa lamarinta ya sane mishi a zuciya." Ita kuwa Aunty Zulai... shi da kanshi idan ya zauna yana mamakin yadda matsananciyar shaƙuwa ta shiga "tsakaninta da Imam. Kuma a cikin ƙanƙanin lokaci haka, Imam bai taɓa kai mishi ƙarar Aunty Zulai ba. A" kullum alkhairinta yake faɗa mishi. "Daga ƙarshe dai, Kamal tattare tunanin komai yayi ya aje gefe ɗaya. Ya shige banɗaki ya ɗauro" "kyakkyawar alwalarsa, ya shimfiɗa dadduma ya fuskanci gabas, ya kabbarta sallah don neman zaɓin Allah." "Kwanaki bakwai da Mummy ta bashi yayi tunani, ya shafe su ne cikin yin sallar istikhara ako wane dare." Kuma cikin hukuncin Allah a kullum al'amarin ƙara kwanciya yake male-male a cikin ransa. Ƙara samun nutsuwa yake yi ta musamman. "Da yake an bashi hutun sati biyu a gurin aikinsa, shi yasa yake ƙara samun lokacin zaman gida sosai," kuma ya mayar da zaman nasa ya fi ƙarfi a ɓangaren su Mummy da ɗakin Hajjah. "Ba domin komai ba, sai don ya ƙara fahimtar wai wacece ma Zulaikha? Don haka a fakaice kuma a" hankali yake karantar duk yanayinta da ɗabi'unta. Zulaikha kuwa tun tana ɗari-ɗari da sakin jiki har dai sannu a hankali ta fara sakin jikinta. Saboda ko ta "janye jikinta shi da kanshi ko Mummy ko Karima ko Hajja sai sun janyo ta, a dole ma ta fara sakin jikinta." Matsakaitan akwatuna ya kawo musu shaƙe fal da tsaraba ita da Karima. Sai dai kusan gaba ɗaya kayan "na turawa ne, ita kuma bata saba saka su ba. Don haka ta nemi guri ta adana akwatin, ba tare da tunanin ranar da za ta iya saka ɗaya daga cikin kayayyakin ba." Kwanaki bakwai na cika cif! Da kanshi ya samu Mummy a ɗakinta ya sanar da ita ya amince. """To Madallah! Allah ya tabbatar mana da alkhairi. Sai ka dage kayi ƙoƙarin neman soyayyarta...""" """Soyayya kuma Mummy? Sai kace wani ƙaramin yaro?""" Ya tambayeta da mamaki a fuskarsa. Daƙuwa tayi mishi da ƴan yatsunta kafin ta amsa mishi da """A'a kai ka yanke ma ƙasa cibiya saboda tsufa Baban Imam! To ina tabbatar maka idan baka nemi" "soyayyarta ba baza ta taɓa aurenka ba, kana zaune garin kallon ruwa kwaɗo zaiyi maka ƙafa. An faɗa" "maka irin waɗannan kyawawan yaran masu nutsuwa ana sake da su ne? Uhmmm! Ka zauna nan dai, sai dai kaji wufff! Wani ya yi awon gaba da ita...""" """Haba Mummy... wannan fa kamar kina min baki ne. Bayan kuma ke da kanki kika kwaɗaita min" "aurenta a raina.""" """Eh! Duk da haka kuma ai ban ce zan tilastata ta so ka ba. Idan kana son ta ka zubar da duk wani girma" "ka nemi soyayyarta, na faɗa maka.""" "Da haka suka rabu da Mummy, ya fice daga ɗakin yana tunanin shi ta ina ma zai fara?" Bayan ɓata hankalin dare da yayi yana tunanin hanyoyin da zai bi gurin kwarkwanta notikan Autar Innaye cikin kwanaki ƙalilan. Mataki na farko da ya fara bi shi ne karɓan lambar wayarta ta hannun Karima. """Yaya?""" """Lafiya kuwa?" """Allah yasa dai ƙanwar tawa ba laifi tayi ba?""" Ta jera mishi tambayoyin a firgice. """Kin shiga uku da sa'ido Karima. To tambaya zanyi mata akan Imam.""" "Har za ta sake jefa masa wata tambayar, wani ɗan tunani da tayi kuma yasa ta sakin murmushi. Katse" "kiran tayi, cikin ƙasa da minti ɗaya ta tura mishi lambar Zulaikha, a ƙasan lambar ta ƙara da" """Allah yasa mu ji alkhairi Yayana.""" "Dariya kawai yayi, ya amsa addu'ar a fili amma bai mayar mata da martani ba." ****** Sannu a hankali cikin kwanaki ƙalilan shaƙuwa mai ƙarfi ya shiga tsakanin Abban Imam da Umman Imam. "Kamar yadda Zulaikha take kiranshi shi ma yake kiranta, amma ƙarfin shaƙuwar tasu ta fi a waya, gurin" "chatting da kuma kiran da yake yawan takura mata da shi da cewar ya kira ne suyi hira, yana gidan ko ba ya gidan." "A cikin kwanakin ya hana ta da zuciyarta sakat! Duk inda ta bi da tunaninsa maƙale da ita, saboda yadda" "yake yawan sakota cikin al'amuransa. A cikin hirarrakin da suke yi, cikin hikima ya bata labarin kaso saba'in cikin ɗari na rayuwarsa." Yanzu har an kai matakin da idan ya tafi gurin aiki kafin ya dawo zai kira ta ya faɗi abincin da yake so ta "dafa mishi. Ita kuma bata taɓa ce mishi a'a ba, yana dawowa zai tarar da abinda yake so an jera mishi a" "dining ɗin ɓangarensa. Sai dai ba ta taɓa yarda ta ƙetara iyakar addininta wajen mu'amala da shi, a" "taƙaice ma, ta fi sakewa da shi suyi hira sosai ta waya, a fili ba ƙaramin kunyarsa take ji ba." "Tana zama a inda yake suyi hira ne kaɗai idan su Mummy suna gurin, duk yadda yaso su dinga keɓewa ta" "ƙi bashi damar hakan. Shi kuwa bai takura ta ba, ko a hakan ma ya gode, kuma kan tafe kan isa watarana jariri ango ne." ****** Duk yadda ya so ya yakice tunaninta a zuciyarsa ya kasa. Ga wani matsanancin ciwon kai da yake ta "addabarsa tun da asubah. Har ya ɗauki jakarsa ta zuwa wurin aiki ya ajiye, ko takalmin ƙafarsa bai samu" "sararin cirewa ba ya faɗa rub da ciki a kan gado, ƙafafuwansa na lilo a ƙasa." "Hannunsa ya laluba ya janyo filo guda ɗaya ya ɗora kansa, sannan ya sake ɗauko wani filon ya kifa a" "kansa. Lumshe idanu yayi, a zuciyarsa yake ta addu'ar Allah ya kawo barci ya ɗauke shi ko na awa ɗaya ne." "Cikin hukuncin Allah kuma sai addu'arsa ta karɓu. Barcin ya ɗauke shi, amma irin rikitaccen barcinnan" "mai tafe da wasu irin birkitattun mafarkai. Kamar dai yadda ya faru da shi cikin dare, wani al'amari da tun bayan rasuwar marigayiya da ya tattara batun aure ya ajiye gefe ɗaya bai sake faruwa da shi ba sai" yanzu. "Yanzu ɗin ma kuma akan Zulaikha, Aunty Zulan da duka-duka tsawon lokacin da ya san da wanzuwarta a" "duniya basu taka kara sun karya ba. Haka ya farka a firgice, ko da ya fahimci abinda ya sake faruwa a karo na biyu tsakanin daren jiya zuwa yanzu wani matsanancin kunya ne ya lulluɓe shi." "Filon da ya ɗora a kanshi ya janye ya rungume tsam-tsam a ƙirjinsa, ya janyo lallausan bargon da ke ajiye" "a gefen gadon ya lulluɓa har kansa. Ƙara matse filon yayi, zuciya da gangar jikinsa cike da wani irin matsanancin shauƙi da son aure ƙarara." "Shi kaɗai, ya kwaɓe fuska kamar zai saka kuka. A hankali ya ce" """Na shiga uku, Allah na tuba ka yafe ni. Wannan yarinyar za ta lalata ma Mummy ɗa.""" "Shi kaɗai, yayi ta juyi akan gadon yana ƙara jin yadda sabon al'amarin ke ƙara amsuwa a dukka sassan" jikinsa. Ga kansa da yake matsanancin ciwo har lokacin bai sassauta masa ba. A jejjere yake ta sauke "ajiyar zuciya. Daƙyar ya yunƙura ya miƙe ya nufi banɗaki, ko da ya tsaya a gaban madubi, sai yaga idanunsa sun yi ja sosai." Kaɗa kai kawai yayi hannunsa ɗaya dafe da mararsa yana tafe a hankali har ya shige banɗaki. Ruwan "sanyi ya sakar ma kansa da tsammanin zai samu sassauci a yanayin da yake ciki, ashe bayan tiya akwai wata cacar, yana gama yin wankan kuma ya fara rawar ɗari. Alamun zazzaɓi na shirin kawo masa farmaki." "Daƙyar, ya iya janyo ɗaya daga cikin rigunan wanka masu kauri da suke ajiye a banɗakin ya saka a jikinsa," ya lallaɓa a hankali ya fice daga bayin. Kan gadon ya sake komawa ya ƙudundune jikinsa gaba ɗaya da "bargo, haƙoransa sai haɗuwa suke gaf-gaf." Ya ɗauki tsawon lokaci a cikin wannan hali yana ta jan duk addu'o'in da suka zo zuciyarsa. Hankalinsa a "tashe, ga shi ya kasa miƙewa tsaye balle ko waya ce ya ɗauka ya kira cikin gida a kawo mishi ɗauki." "Sannu a hankali kuma sai barci ya fara fisgarsa, haka yayi barcin a jigace, da yake akwai bashin barci a" "idanunsa fiye da awa ɗaya yana barci sannan ya farka. A lokacin kuma zazzaɓin ya sauka, zufa ya lulluɓe gaba ɗaya jikinsa." "Hamdala yayi sannan ya janye bargon daga jikinsa ya miƙe tsaye, gurin kayansa ya nufa ya ɗauki wasu" "kayan marasa nauyi ya canja. Ko da ya kalli agogo, ƙarfe goma sha ɗaya da kwata ne na safe." "Mai ya shafa sama-sama ya fesa turare. Ya yaye zanin gadon da ke shimfiɗe akan gadonsa ya canja wani," sannan ya sake hayewa kan gadon ya kwanta bayan ya ɗauki wayarsa. Har ya lalubo lambarta zai kira sai kuma ya yanke shawarar bari ya fara dubawa ko tana Online. "Ƙwaƙƙwarar magana yake so suyi guda ɗaya, tsakanin jiya zuwa yau irin abubuwan da suka faru da shi sun bashi tsoro, bai san idan ya cigaba da jan lokaci yana lallaɓata me zai iya faruwa a gaba ba." Gara kawai ya fito fili ya faɗa mata halin da zuciyarsa take ciki game da ita. Yana da kyakkyawar yaƙinin "in sha Allahu za ta fahimce shi, za kuma ta bashi damar da yake buƙata, ayi komai a gaggauce a wuce" gurin kafin shaiɗan ya jefa shi a halaka. """Hi Beb!""" "Ya fara tura mata, zuciyarsa cike da fatan tana kusa da wayar, ya sani in dai taga saƙonsa za ta amsa" mishi a gaggauce. "Minti biyu tsakani ya tsura ma suna da lambarta idanu kafin yaga ta buɗe saƙon, nannauyar ajiyar zuciya" ya sauke lokacin da yaga alamun tana typing daga can ɓangaren. """Abban Imam! Ya aiki? Fatan ka isa Ofis lafiya?""" """Ban fita ba fa, ba ni da lafiya Wallahi. Har na ɗauki jaka kawai na ajiye na koma na kwanta.""" "A ƙarshen saƙon, ya ƙara da hoton kan gwaigwai (Emoji) mai nuna alamar shagwaɓa, da mai nuna zama" "abin tausayi, da mai kuka ya tura mata." "Mamaki ne ya ɗan kamata, domin tun sassafe suka yi waya, bayan gaisuwa da tambayar yadda ta wayi" "gari ya tabbatar mata a ranar bazai karya a gida ba. Zaiyi sammakon tafiya Ofis ne, akwai wasu" "muhimman ayyuka da bai ƙarasa jiya ba, yau zai ƙarasa ya tura su Lagos." Da damuwa a fuskarta kamar yana gabanta ta ce """Subhanallahi! Me yake damunka Abban Imam?""" """Ke ce!""" "Ya amsa mata kai tsaye, ba tare da wata kwana-kwana ko ɓoye-ɓoye ba." Da mamaki sosai ta tura mishi da kan gwaigwai na zare idanu. Sannan ta ƙara da rubuta mishi """Ni kuma?""" """Eh""" "Ya sake amsawa, sannan ya tura mata da alamar zuciya mai motsi." """Allah sarki ni... Me nayi kuma?""" "Ta aika mishi da tambayar. Acan ɓangarenta, sake gyara kwanciya tayi akan katifar Hajja tana ƙara riƙe" wayar ƙam-ƙam a hannunta. Ta rasa dalilin da yasa duk cikin mutanen da take mu'amala da su lamarin Abban Imam na musamman ne a zuciyarta. "Ko a waya idan suna magana, ko kuma idan suna chatting, irin yadda yake riritata, yana nuna mata ita" "ɗin ta musamman ce. Yana mata raki da shagwaɓa-shagwaɓa kamar wani Imam, ita kaɗai ta san irin yanayin da take ji a jikinta. Bakinta bazai taɓa iya fasalta irin yadda take ji ba, shi yasa ako wane lokaci cikin jin kunyarsa take. In dai ba akwai su Mummy a gurin ba gaskiya ba ta jin kunya zai barta ta iya" sakewa da shi suyi magana ko da na minti biyar ne kacal. "Amma a waya, ko kuma ta kafar sadarwa, tunda ba ganin idanun juna suke yi ba shi yasa har take iya" sakewa da shi suyi hira haka. "[2/6, 12:04 AM] Fareeda Abdallah: ""Kin hana ni nutsuwa Beb! Kin hana zuciyata samun nutsuwa tun" "sa'adda na fara yin tozali da kyakkyawar fuskarki. A yanzu kuma ɗan barcin da nake samun yi raba da rabi ma kina neman hana ni. Don Allah ki barni in huta mana Beb.""" "Ɓurum! Doguwar saƙonsa ya faɗo cikin wayarta. Jikinta na ɗan rawa ta buɗe, domin ko da ta ji shi shiru," kusan mintuna biyar bai ba ta amsa ba. Tayi tunanin ko ya sauka ne. A yanzu da saƙonsa ya shigo da sauri ta buɗe don jin laifin me tayi masa? Ko da ta gama karanta dogon "saƙon, jikinta ne gaba ɗaya ya ɗauka ɗummm! Sannu a hankali ta ɗora lumshe idanunta." Sai a yanzu ta ƙara zurfafa tunaninta akan irin yanayin da take ji akan Abban Imamu. Duk da a iya tsawon rayuwarta bata taɓa faɗawa cikin kogin son wani mahaluki a faɗin duniya ba. A yanzu kam ko rantsuwa tayi babu kaffara wannan yanayin da take ji a jiki da zuciyarta ba komai bane face alamomin So. """So dai?""" Tayi ma kanta tambayar a fili tana mamaki. """So kuma? Wa ake so ko kuma wa yake so?""" Hajja da fitowarta kenan daga banɗaki zancen da Zulaikha tayi ya dira a kunnenta tsulum ta saka bakinta. """Hajja ba fa magana nayi ba... zancen zuci ne kawai ya fito fili. Wani labari nake karantawa a facebook" "ya ɗauki hankalina.""" Ta amsa ma Hajja da sauri tana ƙoƙarin buɗe wayarta da taji ƙarar saƙo ya sake shigowa. """Beb! Baki ce komai ba... Ki agaza ma Ɗan Mummy kar kiyi kisan kai... Da gaske nake yi fa...""" Saƙon da Abban Imam ya ƙara turo mata. "Lura da tayi shauƙin da take ji na Soyayyar Abban Imamu zai iya saka ta yanka ihu a ɗakin Hajja, sawunta" a likkafa ta sauka akan gadon. """Hajja ina zuwa, ki gama shiryawan zan dawo yanzu in lallaɓe miki kan.""" Ta fice da sauri tun kafin Hajja ta amsa. "Sai da ta shige ɗakinta, ta mayar da ƙofar ta rufe, ta jingina da jikin ƙofar sannan ta iya ba shi amsa" """To ni me zan ce? Ni dai babu ruwana... Kar ma ka bari wani ya ji wannan wasar da kake min.""" """Wallahi, Summa tallahi ina son ki Zulaikha.""" Ya tura mata da sauri saƙonta na isa gare shi. """Da gaske nake yi, ina bala'in son ki.""" Ya sake tura mata. """Don Allah, don girman Allah kar ki ce min bakya so na.""" A karo na uku ya sake tura mata. """Na sani akwai tazarar shekaru masu ɗan yawa a tsakaninmu, amma na miki alƙawarin zan so ki, in" "riritaki, in shagwaɓa ki, in ji da ke, har ma fiye da saurayin da kike tunanin aura.""" Saƙon shi ya sake sauka a karo na huɗu. """Ki taimakeni Beby ki so ni, ko da rabin son da nake miki ne. Ke ni ko bakya jin so na a yanzu, ki bani" "dama don girman Allah in koya miki so na. In Allah ya yarda baza kiyi da na sani ba.""" "Tsananin yadda maganganunsa suka kassara mata sassan jiki, yasa bata san sa'adda ta zame zuwa ƙasa" "ba. Saboda jin ƙafafunta tayi kamar an zare mata duk wasu ƙasusuwa da suke cikinsu. Ta karanta saƙon, ta ƙara maimaitawa, a karo na uku ta sake bitar manya-manyan maganganunshi. Da ta rasa abinda za" "tayi, kawai sai ta fashe da kuka." "Da saurin gaske ta kashe wayar a daidai lokacin da kiranshi ya fara shigo mata. Daƙyar, da jan mazaunai," "da muskutawa, da rarrafe, taja jiki zuwa gefen gadonta. Da tayi iya ƙoƙarinta ta kasa miƙewa ta hau kan gadon kawai sai tayi kwanciyarta a gurin, har lokacin hawayen idanunta basu daina tsere kamar an buɗe famfo ba." ****** Mamaki mai girma ne ya bayyana a fuskarsa lokacin da yaga kiranta na shigowa cikin wayarsa. Abu ne da bai taɓa faruwa ba tun da ya ɗauko ta daga Faƙo zuwa Abuja. A yau da ya faru kuwa kun ga dole yayi mamaki. "Da fari, ya tsammaci kiran daga Aunty Balira ne kamar yadda ya ga sunan, Sai da ya lura babu New a" "ƙarshen sunan Aunty Baliran, sannan ya gane tsohon layinta ne da ta bar ma Zulai. Kenan a yanzu, Zulai ke kiransa." "Ɓici-ɓici yayi da fuska saboda tsananin takaicin kiran da tayi masa, kamar tana gabansa, a fusace ya ce" """Ko uwar me take nema da take kira na ina tsaka da aiki oho!!""" "Ya faɗa a fili. Kiran na gaf da tsinkewa ya ɗaga wayar, ya kara a kunnensa, har lokacin fuskarsa a ɗaure" tamau babu walwala ya ce. """Menene kike kira na a irin wannan lokacin da kika san ina tare da iyalin...""" """Madallah Yaya mai iyali. Kana tare da iyali ko bakwa tare ba abinda na kira in ji ba kenan.""" "Ta katse shi da shaƙaƙƙiyar muryar da ke bayyana alamu biyu, ko dai tana fama da matsanancin mura," ko kuma ta yi kuka sosai don tana cikin matsanancin damuwa. Kafin ya sake kwaɓo mata wata baƙar maganar don ba abinda ta kira shi taji kenan ba tayi saurin sake cewa """Daman tambayarka zanyi, gobe asabar za ka je Faƙo ne...?""" """Bazan je ba. Ko zan je ma ba abinda ya dame ki bane.""" Ya katse ta a fusace. """To ni kam zan tafi gobe in sha Allah. Zanyi sammakon zuwa pack in hau motar haya. A gobe, babu" "abinda zai hana ni zuwa ga Innaye da Baffa sai dai wani ikon Allah. Daman na zaci za ka tafi ne, in shirya ka biyo ka ɗauke ni mu tafi tare don cigaba da rufuwar asirinka. Amma tunda baza ka je ba ni kam zan tafi...""" """Zzzzzaaaa ki tafi Faƙo kike cewa? Da izinin wa za ki tafi?""" "Ya tambayeta bakinsa na rawa, da wani irin bayyanannen tashin hankali a muryarsa duk da yana ƙoƙarin" ɓoyewa. "Izuwa lokacin, acan ɓangarenta ranta ya fara ɓaci. Amma tana ta ƙoƙarin dannewa don ba ta so su raba" "hali kamar yadda suka saba, duk da haka, bata san sa'adda taja mishi wani dogon tsaki ba kafin ta ce a fusace" """Har wani izinin waye zan nema don zan je ganin iyayena? Look Yaya Hafiz, kana iya fitowa gobe ƙarfe" "bakwai da rabi na safe ka ɗaukeni mu tafi Faƙo a mutunce, kana kuma iya shantakewa kayi zamanka ni" "kuma in tafi a motar haya. Sai dai kyakkyawan albishir a gare ka shi ne duk abinda ya biyo baya kar kayi kuka da kowa face kanka da son zuciyarka...""" """Zulai??? Umarni kike ba ni?""" Ya jefa mata tambayar a tsawace. """Ba umarni nake baka ba Hafiz.""" Ta kira sunanshi gatsatsau abinda bata taɓa yi ba. """Ina faɗa maka abinda zai faru ne tabbas! Ko da son zuciyarka, ko babu son zuciyarka. Domin kai baka" "isa kasa ko ka hana ni yin abinda zuciyata ke so ba.""" "Ƙit! Ta katse wayar ta barshi sake da baki, ƙirjinsa na wani irin bugawa sauri-sauri saboda tsananin" kaɗuwa da firgita da irin kalaman da ke fita a bakin Zulai. Kamar ba ita ba? Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!!! Me yake shirin faruwa ne? ****** ****** "Neman aurensa da Aisha mahaifiyar Imam, nema ne da iyaye suka fara nuna sha'awar ƙulluwar" "dangantakar. Kafin daga bisani da zancen ya isa kunnuwansu suka riƙa da hannu bibiyu, kasancewar duk" su biyun masu biyayya ne da bin umarnin iyaye. "Don haka a wancan lokacin bazai ce ya ɗanɗani zaƙi da guban da ke cikin soyayya ba, duk da dai jagoran" "aurensa da Aisha babu ƙiyayya ko kaɗan, zallar ƙauna ce da biyayya suka haɗu wajen samar da sassanyar" soyayya da shaƙuwa mai tsayawa a zuciya. "Amma a yau, da ya gama fallasawa Zulaikha sirrin zuciyarsa ta bar shi a maƙale, ba tare da ta amsa mishi" da eh ko a'a ba duk da yana matuƙar tsoro da fargabar jin kalmar a'a daga bakinta. Ya daɗe bai shiga cikin mummunar yanayi na gagarumin tashin hankali da fargaba irin wannan ba. "Ko da ya kira wayar Zulaikha ya ji kiran ya shiga, daga bisani kuma aka katse sannan aka kashe wayar" "gaba ɗaya. Wani wawan bugawa ƙirjinsa yayi, lokaci ɗaya kuma kamar aikin asiri zazzaɓin jikinsa ya dawo ɗanye jagab." "Cikin ƙanƙanin lokaci sai ga shi akan gado yana rawar ɗari. Wani abin dariya da tausayi shi ne, duk da" "wannan hali da yake ciki ba kansa yake tunani ba, tunaninsa wane irin hali Zulaikha take ciki a wannan" lokacin? Me yake damunta? Me yasa ta kashe mishi waya? Har ya ɗaga waya zai kira Mummy ko Karima don a duba mishi halin da take ciki sai ya tuna ai duk sun fice gurin ayyukansu. "Lambarta ya sake gwada kira, a kashe. Ya ƙara gwadawa ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba, amma duk amsa" ɗaya na'uwa take maimaita mishi. Wannan lambar da yake kira a kashe take. "Jikinsa a sanyaye ya ajiye wayar gefe ɗaya, hankalinsa a tashe, ga wasu ƴan ƙananun ƙwallah na" matsanancin damuwa da zazaaɓi da suka taru a kwarmin idanunsa. "Ya ɗauki fiye da awa ɗaya yana cikin wannan hali, kafin ya yunƙura ya miƙe tsaye a wahalce ya fice daga" "ɗakin, sannu a hankali ya fice daga ɓangaren nasa gaba ɗaya ya nufi cikin gida ɓangaren su Mummy." "Yana shiga, ya hangi mai aiki Rahina tana jera abinci kan teburi. Da rawar jiki ta zube ƙasa, za ta fara" gaishe shi ya katse ta da tambayar """Ina Zulaikha?""" """Tana ɗakin Hajja za ta yi mata kitso...""" "Kafin ta gama faɗa har ya bar gurin, kai tsaye ɗakin Hajja ya nufa ba tare da wani tunani ba. Siririyar" "sallama ɗaya kacal yayi, bai jira an amsa ba ya buɗe ƙofar ɗakin yasa kai ciki, Hajja ya gani, kwance akan kujera. Da alamun tsifa take yi barcin ya kwashe ta, domin ga kan nan a buɗe ta kwance rabi saura rabi." "A hankali ya koma da baya da baya ya fice daga ɗakin sannan yaja mata ƙofa. Daga nan, ɗakin Zulaikha" "ya nufa kai tsaye, yana tafiya, amma ji yake kamar ba ya sauri don tsananin ɗokin son tozali da kyakkyawar fuskarta da gane ma idanunsa wane hali take ciki?" "Ko da ya isa ƙofar ɗakin, ita ko arzikin sallama ɗayan ma bata samu ba. Hannun ƙofar kawai ya kama ya" buɗe ya cusa kansa cikin ɗakin. A firgice Zulaikha da take zaune a gefen gado ta buga tagumi da hannu bibiyu ta miƙe tsaye. Hankalinta a "tashe, tsawon daƙiƙu sittin suka ɓata suna kallon ƙuda a tsakaninsu ko wanne ƙirjinshi na bugawa fat-fat." "Kamar wacce aka tsikara, aka ankarar kuma sai tayi saurin komawa ta zauna da sauri bayan ta tuna da" "irin rigar da ke jikinta. Duk da ba mai bayyana tsiraici bace, amma ta kamata ƙwarai. Sannan babu hijabi ko mayafi a jikinta, ga kanta babu ɗankwali, lallausan gashin kanta da yasha gyaran saloon a barbaje, amma tana ga gara shi da ɗan sauƙi sauƙi a bisa ace ta cigaba da tsayuwa a gabansa da matsattsiyar riga. Miƙewa domin zuwa ɗaukar ɗankwali ko mayafi kuma kamar ta ba shi damar ƙare mata kallo gaba da" baya ne. """Allah ya baki haƙuri Beby. Ki yafe min don Allah... kalamaina ne suka jefa ki a cikin damuwa har ya" "saka ki kuka ko?""" Yayi maganganun da rauni sosai a cikin muryarsa. "[2/8, 9:20 PM] Fareeda Abdallah: Duk da yadda maganganunsa suka daki zuciyarta, ta kasa ɗagowa ta" ƙara kallonsa a karo na biyu. Balle kuma har ta iya buɗe baki ta amsa masa. A madadin ɗaya daga cikin "biyun ma, sai idanunta ne suka ƙara ciccikowa da hawaye. Lokaci ɗaya suka fara sauka ɗis, ɗis, a jikinta." "Kasancewar idanunsa ƙur yake a kanta, hakan ya bashi daman ganin hawayen da take yi. Hankalinsa a" "tashe, da wani maɗaukakin sauri yaja jikinsa zuwa gare ta. Ba tare da damuwa ko fargabar komai ba yasa" "gwuiyawunsa a ƙasa, hannayensa biyu na rawa, yasa hannu ya ɗago fuskarta suka kalli juna a karo na biyu." """Kuka kike ƙara yi Zulaikha?""" "Ya jefa mata tambayar, da wata irin shaƙaƙƙiyar murya kamar wanda zazzafar mura ta riƙe mishi" maƙoshi. """Kiyi haƙuri. Ki yafe min. Ni ma ba yin kaina bane, Allah ne ya jarabce ni. Kiyi haƙuri don Allah... Amma" "na rantse da Allah ban fara son ki don zan iya dainawa ba. Ki daure ki bani dama Zulaikha...""" """Gobe, zan... tafi gida... can ƙauyenmu...""" Ta katse shi da faɗin haka cikin kuka da karkarwar murya. """Dummmm!""" "Haka ƙirjinsa yayi wani mummunar bugawa, kansa ya sara duk a lokaci ɗaya. Tsananin mutuwar jiki da" mummunan tashin hankalin da ya ƙara lulluɓe shi yasa bai san sa'adda ya saki fuskarta yayi zaman ƴan bori a gabanta ba. "Ya haɗiyi wasu kauraran miyau daki biyu daƙyar, masu masifar ɗaci da kaurin da ke barazanar yaga mishi" maƙogwaro. """Saboda... Saboda... Saboda na ce ina son ki ina son aurenki shi yasa za ki tafi???""" "Ya tambayeta daƙyar, bayan yayi ta ƙoƙarin harhaɗa kalmomin da zaiyi amfani da su gurin tambayarta" suna suɓucewa a harshensa. "Tunawa da tayi da inda suke ita da shi, da kuma tunanin ako wane lokaci daga yanzu Aunty Karima za ta" "iya dawowa cikin gidan. Kuma da ta dawo, wacce za ta fara nema a gidan bayan Mummy ita ce." Ba ma a gansu a yanayin da suke zaune ita da shi yayi zaman dirshan a gabanta kaman mai roƙon gafara "ba, a ganshi a cikin ɗakinta ma babban ƙalubale ne a gare ta, kuma abin a saka musu ayar tambaya ne da" zargi. "Don haka ta daure, ta ƙwarara zuciyarta. Abinda ta lura da shi shi ne tabbas Abban Imam da gasken-" "gaske yake yi, tunda har ya iya ajiye kunya da kamun kansa ya biyo ta har cikin ɗakinta, abinda bai taɓa ko kwatanta yi ba. Ko ɗakin Karima da taƙe ƙanwarsa ba shiga yake yi ba, balle ita da ta kasance ba" muharramansa ba. "Abinda ta lura da shi shi ne, a yadda yake ɗinnan zaune dirshan a gabanta, idan ba wata ƙwaƙƙwaran" magana ɗaya ya ji daga bakinta ba bazai fita mata a ɗaki salin-Alin cikin sauƙi da kwanciyar hankali ba. """A'a!""" Ta faɗa a hankali. """Wallahi ba saboda ka ce kana so na bane zan tafi gida. Kawai dai na yi ma Innaye wani alƙawari ne" "kafin tahowata...""" "Tayi ɗan shiru, kafin ta cigaba da magana a kunyace." """Na mata alƙawarin duk sadda na samu wani Namijin da ya nuna sha'awar aure na a yadda nake, zan" "koma can ƙauye, domin aje can a nemi aure na... Ko baza ka bi ni ƙauye ba Abban Imam?""" """Zan bi ki. Na rantse da Allah zan bi ki.""" Ya amsa mata da sauri. """Ai ko cikin ramin macizai kika shige da sunan asalinki, Zulaikha ni mai iya jure duk wani cizo da sara ne" "in shiga cikin ramin don zuwa neman aurenki. Daman dai babban buri na shi ne in ji shin kin amince da soyayyar da nake miki? Za ki bani damar mallakar zuciyarki ta hanyar buɗa min filin guri inyi dashen kyawawan furanni? Ina so ki fahimci ni da gaske nake son ki, ki amince min don Allah... In Allah ya yarda" "baza ki taɓa yin da na sani a tarayyarmu ba.""" """Na amince!!!""" "Ta amsa a kunyace, sannan ta sa tafukan hannayenta biyu ta rufe fuskarta tana murmushin jin kunya." Wani matsanancin daɗi da farin ciki na ratsa duk wani lungu da saƙo na zuciya da sassan jikinta. """Alhamdulillah!""" Ya faɗa da yanayin da ke bayyana matsanancin farin ciki. Da ya rasa abinda zai ƙara bayan kalmar "hamdalar kawai sai ya juya zamansa ya fuskanci gabas, yayi sujudus-shukur." Ya daɗe yana jera kalaman godiya ga mahalicci kafin ya miƙe zaune ya fuskanci Zulaikha itama ya fara "mata godiya, da alƙawurra kala-kala na irin yadda zai kula da ita ya riritata idan har Allah ya tabbatar da aurensu." "Ita dai ta kasa cewa komai, sai murmushi kawai take ta jifanshi da shi, zuciyarta cike da matsanancin" farin cikin da ta daɗe bata tsinci kanta a cikin makamancinsa ba. """Abban Imam, ya kamata ka tafi ɓangarenka pls! Kar a shigo a ganka a cikin ɗakina.""" "Ta tunatar da shi cikin sanyin murya, ganin kamar ya ma manta a inda yake." """A'a ni dai, ban gaji da ganin kyakkyawar fuskarki ba gaskiya Beby.""" "Ya faɗa da dukkan gaskiyarsa, har yana ƙara gyara zaman dirshan a gabanta." "Zazzaro idanu tayi da farko, sai kuma ta ɗan ɓata fuska. A shagwaɓe ta ce" """Ni dai don Allah ka tafi, ba ga waya ba za mu cigaba da magana? Don Allah ka fita. Ka ga fa tun ɗazu" "kitso zan je inyi ma Hajja, na san yanzu ta gama tsifa. Kuma ma Aunty Karima ta kusa dawowa, bazan ji daɗi ba gaskiya idan aka tarar da kai anan, don Allah ka tafi.""" """Zan tafi. Amma bisa sharaɗi ɗaya...""" """Menene sharaɗin?""" Ta katse shi da tambayar tun kafin ya rufe baki. """Ki ɗaukar min alƙawarin za ki kunna wayarki, kuma idan na kira za ki ɗauka, sannan baza ki sake kashe" "wayar saboda ni ba.""" """Na yi alƙawari. In sha Allah zan kiyaye, bazan sake kashewa ba.""" "Ta amsa mishi da murmushi a fuskarta. Domin ta zaci wasu sharuɗɗa ne masu wahala, da taji sauƙaƙan" sharuɗɗa ne yasa ta amsa har da murmushinta. "A maimakon ya miƙe ya fice, sai yayi tagumi ya ƙura mata idanu." """Menene kuma?""" Ta tambayeshi tana ɗan tura baki gaba. """Ina son ki ne...""" """Ni ma haka. Abban Imam don Allah ka tafi...""" "Da saurin gaske ya fice daga ɗakin tun kafin ta gama maganar da take yi, fuskarsa cike fal da murmushi." ****** "Duk da zancen tafiyar Zulaikha ya zo ma Mummy, Karima, Hajja a ƙurarren lokaci, bayan ƙorafi da nuna" "mata ɓacin ran rashin sanar da su batun tafiyar akan lokaci, ita kuma ta ɗauki laifin ɗungurugum ta ɗora akan Hafiz cewa shi ne bai sanar da ita za su tafi tare ba sai a ranar. Haka suka haɗa mata tsaraba mai yawa da za ta tafi ma da iyaye da ƴan'uwanta." Karima dai hankalinta sam ya ƙi kwanciya da tafiyar Zulaikha. Gani take kamar idan Zulan ta tafi baza ta dawo ba kamar yadda ta ce. Minti ɗaya biyu sai ta kalle ta ta ce """Zuly ina fatan dai ba tafiyar gaba ɗaya za kiyi ba? Don Allah kar kiyi mana haka, bamu shirya rabuwa" "da ke a yanzu ba.""" """Ki kwantar da hankalinki Aunty Karima. Zan dawo in sha Allah, ai kin ga ko kayayyakin sawa ta ma ba" "duka na ɗiba ba. Zan dawo, don Allah ki daina damuwa.""" "Tun da yammacin ranar, bayan Abban Imam ya gama ramakon barcin da ke kanshi, ya fitineta a waya da" tambayar me take so a matsayin tsaraba? Ita kuma tana ta sake maimaita mishi ba ta son komai. "Duk da haka dai be yarda ba, ana idar da sallar magriba ya ɗauki Karima da Imam suka shiga kasuwa siya" mata tsaraba. Tunda yayi-yayi da ita tazo su je ta ce baza ta je ba. Ba tare da jin zafin kuɗin da zai kashe ba haka Karima ta zage ta zaɓo mata turamen zannuwa masu kyau "da tsada, ta ɗauki shaddoji kala uku da turaruka, sannan ta ɗibi ƙananun abubuwa wanda Zulaikha za ta" "raba ma sauran mutanen gidansu. Domin labarin ahalinsu Zulaikha ba wanda bata faɗa mata ba, sai dai kawai ace bata san su a idanu ba." A ƙarshe bayan sun gama siyayya gaba suka ƙara zuwa wajen sayar da wayoyi. Wayar samsung ya siya mata mai kyau da tsada ya biya kuɗin komai suka fice daga gurin. "Ita dai Karima sai murmushin farin ciki take saki lokaci bayan lokaci, domin tun kwanaki ta fara fahimtar" "take-taken Yayan nata akan Zuly, amma da yake duk su biyun suna ta nuƙu-nuƙu, sai ta kawo idanu ta" "zuba musu. A yau kam ta tabbatar da gaskiyar komai, duk da Yayan nata mutumin kirki ne mai hannun" "kyauta, wannan uban siyayyar ba kowa za'a iya yima ba sai wacce zuciya ke tsananin So da ƙauna." "Daga Zulaikha har mutanen gidan babu wanda ya faɗa ma Imam washe gari za ta tafi, saboda gudun irin" rikicin da zaiyi. Kawai sun bari ne idan ya dawo makaranta washe gari sai yaga ba ta nan. "Tsoro ne sosai ya kama Zulaikha da ganin irin tsarabar da Abban Imam ya kawo mata, a gabansu" "Mummy. Jikinta na rawa ta miƙe tsaye, idanunta a warwaje ta ce" """Mummy... Don Allah ku rufa min asiri. Na rantse da Allah idan na tafi da kayayyakinnan gida daga" "Innaye har Baffa sai sun kusa karairaya ni. Don Allah ku bar su, waɗanda kuka haɗa min ke da su Hajja ma na rantse da Allah sunyi yawa, kawai dai zan tafi da su ne in faɗa a gaban Yaya cewa ke kika bani," "idan basu yarda ba sai in kira a waya kiyi musu ƙarin bayani...""" """Kin san Allah baki isa ba. Kin karɓi tsarabar kowa sai nawa da nake shirin aurenki za ki ce baza ki karɓa" "ba?""" "Abban Imam ya faɗa ransa a ɓace, ba tare da kunyar idanun Hajja da Karima da suke gurin ba, kuma sam" basu taɓa sanin da zancen soyayyar ba sai yanzu da bakinsa ya suɓuce ya faɗa. """Ayyyuririririiiiiiii""" Hajja ta kama hanci ta rangaɗa ƙaƙƙarfan guɗa. Fuskarta na bayyana matsanancin farin ciki da jin wannan daddaɗan labari. Mummy da Karima kuwa me za suyi ba dariya ba. Ita kuwa Zulaikha ina ma ƙasa zai tsage ta shige don kunya? Daƙyar ta iya juyawa da sassarfa ta gudu zuwa ɗakinta. "Sai a lokacin, shi kanshi ya tuna da ɓaram-ɓaramar da yayi. Amma da yake shi namiji ne sai kawai ya" fuske ya daka ma Karima tsawa da tambayar wa take ma dariya? """A'ah Yaya! Yanzu fa lallaɓani ya kamata kayi gaskiya... Domin a ɓangaren Zuly ka san dai ina da ƙarfin" "sakawa da hanawa, don haka gara ka bi ni a sannu kar in ɓata maka budget.""" Waige-waigen neman abinda zai jefe ta da shi yasa ta miƙe da saurin gaske ta wuce zuwa ɗakin Zuly tana "ƙyalƙyala dariya. Ko da ta shiga, haka ta tasa Zulaikha da tsiya da tsokana har sai da taga za tayi mata" kuka sannan ta rabu da ita. "A gefenta ta zauna, ta cigaba da bata shawarwari, a fakaice kuma tana ƙara yi ma ɗan'uwanta kamfen." Domin al'amarin ba ƙaramin daɗaɗa mata zuciya yayi ba. "[2/9, 10:20 PM] Fareeda Abdallah: Saboda yadda Abban Imam ya kafa ya tsare a dole aka yi raba dai-dai" "tsakanin tsarabarsa da ta su Mummy. Aka rage yawan na su, aka zuba wasu daga cikin nashi. Sauran kuma aka haɗa a cikin babban jaka aka ajiye a ɗakin Mummy da cewa bayan sati ɗaya da tafiyarta ahalin gidan gaba ɗaya za su kai mata ziyara can ƙauye, a lokacin sai a tafi da sauran kayan a matsayin tsarabar" da suka yi mata. Wayar da ya siya mata kuwa ba don ranta na so ba tana ji tana gani Aunty Karima ta kwashe komai nata "da ke cikin tsohuwar wayar, ta mayar mata a sabuwar wayar, tana kwashe kayayyakin tana mata mitar yadda komai aka ce ta tafi da shi sai ta ce a'a, ita tana tsoron Baffa da Innaye." """Wannan wayar dai ko kin je gida da ita na tabbata basu san kuɗinta ba balle ayi miki faɗa. Kina zuwa" "ki mayar ma da Aunty Balira tsohuwar tata, tunda daman aro ta baki. Ki ce musu Mummy ce ta siya miki wannan, na tabbata baza suyi miki wani faɗa ko ƙorafi ba.""" Yarda da Aminci mai yawa ne ke tsakanin Zulaikha da Karima. Ta yadda a tarihin Zulaikha ɗai ɗai ne "abinda Karima bata sani ba, daga cikin abubuwan da har yau Zulaikha ta kasa buɗe baki ta ba Karima labari aurenta da Hafiz yana ciki." "Auren da tunaninsa kaɗai ke tsittsinka mata zuciya. Amma dai tana addu'a, kuma tana fata da yaƙinin" "wannan tafiya gidan da za tayi ya kawo ƙarshen komai, kuma ƙarshen komai ɗin ya taho a sauƙaƙe." ****** "Tafiya Faƙo a wannan satin sam-sam ba ya cikin lissafinsa, saboda satin da ya wuce ya je. A yadda ya" "tsara, sai sati na sama zai tafi." Amma maganganun Zulaikha da suka tsaya mishi a zuciya yasa ya katse komai da ya tsara gudanarwa a asabar ɗin ya shirya tafiya Faƙo. "Da damuwa sosai a fuskar Bintu take mishi ƙorafin tafiyar, saboda sun riga sun gama tsara ziyarar" muhimman guraren shaƙatawa za suyi a wannan weekend ɗin. """Kiyi haƙuri Sweetheart. Wallahi tafiyar ce tazo min bazata. Amma duk yadda ake ciki zanyi ƙoƙarin" "dawowa da wuri, idan lokaci bai ƙure ba sai mu fita, idan kuma lokaci ya ƙure sai mu bari lahadi.""" "Da haka suka rabu, ba don ranta ya so ba tayi mishi rakiya har bakin ƙofa, sannan ta karɓi Aadil daga" "hannunshi, ya sumbaceta a kunci kafin ya fice daga falon tana mishi addu'ar Allah ya kiyaye hanya." "Da yake shirin tafiyar a fusace yayi ta, ana idar da sallar asubah babu daɗewa suka fita shi da direba," ƙarfe shida rabi na safe yana ƙofar gidan Mummy. A lokacin Zulaikha ko wanka bata yi ba. A taƙaice ma tana kicin tana yi ma Imam gashin Meat pie da yace zai tafi da shi makarantar Tahfeez. "Wayarta kuma na ɗaki, shi yasa yayi ta kira bata san yana yi ba." "A ƙarshe sai Mummy ya kira, ya faɗa mata ga shi a ƙofar gida. Don Allah ta faɗa ma Zulai ta fito su wuce," idan ya dawo da yamma zai shigo. Da ɓacin rai a muryar Mummy ta fara mishi faɗan ƙin faɗa mata tafiyarsu da yayi. """Hafiz? Wani irin tafiya ne ka shirya haka tun da wuri baka sanar da ni za ka tafi da Zulaikha ba? Sai jiya" take sanar da ni a ƙurarren lokaci wai ka ce tare za ku tafi gida. Akwai wani abu da ya faru acan gidan ne? "Ko kuwa sun shirya komawarta can gida ne gaba ɗaya?""" "Da farko shiru yayi, ya rasa amsar da zai bata, domin dai asalin wannan tafiya ba shi ya tsara ba, kuma" shi kanshi bai san takamaimai abinda zai kai Zulai Faƙo ba. Amma saboda kar ya kware mata baya a gurin Mummy ita ma ta kware masa nasa bayan a gurin Innaye yasa shi cewa """A'a Mummy, ba abinda ya faru. Kiyi haƙuri, za ta dawo in sha Allah. Innaye ce hankalinta ya ƙi" "kwanciya ganin tunda Zulai ta taho bata taɓa zuwa can ba sai dai su gaisa ta waya, shi yasa zan tafi da ita don hankalinta ya kwanta. Amma ba na jin za ta wuce sati ɗaya ko biyu, idan na je sati na sama zan" "dawo miki da ita. Kiyi haƙuri don Allah.""" """Shi kenan. Allah ya tsare ya dawo da ku lafiya.""" """Amin Mummy. A faɗa mata ta fito da sauri don Allah.""" Duk yadda yake sauri sai da Zulaikha ta sake ɓata mintuna arba'in kafin ta fito cikin rakiyar mutanen "gidan, Abban Imam da Imam ne kawai basu biyo ta ba." Manyan sabbin jakunkuna biyu da yaga Karima na jaye da su har zuwa gurin boot ɗin motarsa ne yasa shi buɗe baki da mamaki a fuskarsa. """Waɗannan kayayyakin fa?""" Ya tambaye ta. """Na Zuly ne.""" Ta amsa mishi a taƙaice. A zuciyarsa ya ce "'Uhmm! Su Zuly manya.' Sai kuma a fakaice ya juya ya kalli Zulai da aka kira da Zuly, a bazata, ƙirjinsa" "yayi wani wawan bugawa, ganin wasu canje-canje ƙarara da yake gani tattare da Zulai." "Kamar dai ba ita ba. Ta zama wata babbar yarinya mai aji da kwarjini, doguwar rigar abaya da yake" jikinta ya zauna mata cas! Kamar wata Hadiza gabon sadda take da ƙiba kafin tayi sleeming. Ta yi "kwalliyarta sama-sama, wanda ya ƙara bayyana cika, ƙasaitarta, da wayewarta." "A ɗan firgice, ya mayar da hankalinsa kan Hajja ta take masa tsiyar irin wannan sammako da ya bugo" musu kamar wanda zai bar ƙasar? "Har suka bar ƙofar gidan, da dariyar yaƙe yayi ta bin su Mummy. Zuciyarsa cike da ɗumbin mamakin" "gagarumin canjin da ya gani tare da Zulai, wanda bai taɓa mayar da hankali ya lura ba sai a yau da suka" kama hanyar zuwa Faƙo shi da ita bayan watanni shida da wasu ƴan kwanaki da tayi rabonta da ƙauyen. "Duk da yadda baƙaƙen maganganu ke cike da bakinshi kafin su haɗu, ya kuma yi niyyar yi mata wankin" "babban bargo tas! Domin ta san har gobe fa ruwa na maganin dauɗa. A yanzu da suka haɗu, kuma suna" "tare a cikin mota ɗaya sai ya zama kamar wanda aka ɗaure masa baki, ya kasa ce mata komai. Lokaci bayan lokaci dai yana ɗago fuskarsa ya kalleta ta cikin madubi." "Ita kuwa bata ma san yana yi ba, kanta yana ƙasa, tana danna sabuwa kuma tsadaddiyar wayarta," fuskarta cike fal da wani lallausan murmushi. "Mamaki da tsoro mai girma ne ya kama shi ganin wayar da ke riƙe a hannunta," 'Na shiga uku! Kar dai a ce Zulai ta fara bin maza?' "Wani sashe na zuciyarsa ya jefa masa tambayar, sai kuma yayi saurin kore maganar ta hanyar yin ta'awizi." "Kamar bazai tambayeta game da wayar ba, sai kuma ya tuna idan bai tambayeta ba tabbas ya ci" "amanarsu Baffa. Fuskarsa a ɗaure, ya daka mata tsawa ya ce" """Keh! Wannan wayar fa? Ta waye kike amfani da ita kamar ta ki?""" "A taƙaice, ta ɗan ɗago kai ta kalle shi da gefen idanunta." """Tawa ce, Mummy ta siya min jiya.""" "Ta amsa mishi a taƙaice, sannan ta sake mayar da hankali kan chatting ɗin da take yi da Abban Imam." "Har zai bar maganar a yadda ta faɗa, amma sai zuciyarsa ta kasa nutsuwa guri ɗaya. Wayarsa ya ɗauka" "ya kira Mummy, bai ji kunya ba yake tambayarta wai ita ta siya ma Zulai waya?" """Eh! Ni ce. Akwai wata matsala ce tattare da hakan?""" Ta tambaye shi. A daburce ya amsa da """A'a! Babu komai Mummy. Daman kawai na yi mamaki ne, Allah ya saka da alkhairi ya ƙara arziki.""" ****** Ƙarfe goma sha ɗaya da rabi a ƙofar gidan Baffa tayi musu. Tun kafin direba ya gama daidaita fakin ɗin "motar a ƙofar gidan, Zulaikha da ganinta a ƙauyen nasu ya taso mata da matsananciyar kewar Innaye da ƴan'uwanta ta buɗe motar da sauri ta fice da sassarfa ta nufi cikin gidan." "Hafiz yana ƙwalla mata kira amma ko saurarenshi bata yi ba, kafin ƙiftawa da bismillah har ta ɓace ma" ganinshi. """Assalamu alaikum! Mutanen gidannan barkanku da safiya... Oyoyo Innaye na...""" Tayi maganganun da karaɗinta da mutanen gidan suka daɗe suna kewa. "Kai tsaye ɗakin Innaye ta nufa a guje saboda rashin ganinta a tsakar gida, sauran mutanen gidan suka" rufa mata baya bakunansu har kunne don murnar ganinta. """Maraba lale marhaban da Amarya Zulai... Lale lale, barkanku da zuwa... Sannunku sannunku, kun sha" hanya. Sannunku da zuwa. "Ire-iren kalaman da ke fita daga bakin mutanen gidan kenan yara da manya, cikin ƙanƙanin lokaci aka" cika ɗakin Innaye taf da jama'a. "Ita dai Zulaikha har lokacin tana maƙale da Innaye tana bin masu iyaye da ƴan'uwanta da dariya, ta hana" "Innaye tashi gaba ɗaya, don gani take kamar mafarki take yi, Innaye tana tashi daga kusa da ita za ta farka daga nannauyan barcin da take yi." Mama Laminde da Mama Laraba su ne sukai ta ɗawainiyar kawo ma Zulaikha da Hafizu da ya shigo daga baya ruwa da sauran kayayyakin motsa baki. Tunda a lokacin ba'a gama abincin rana ba. Ko kafin su fice daga ɗakin har labarin zuwa da Zulai da Hafizu yayi ya iske Baffa da ke can bakin kasuwa. "Ai kuwa sai ga shi bagazan-bagazan yana saɓa babbar riga, bakinshi har kunne. Da gaske yayi kewar ƴar" "marainiyar ɗiyar tashi, matsayinsa na namiji ne kawai ba ya magana kamar yadda Innaye take yi." Kuma sanin da yayi a yanzu Hafizu ya fi shi ƙarfin iko da Zulai shi yasa bai taɓa mishi ƙorafin me yasa "baya zuwa da Zulai ba? Yau da shi Hafiz ɗin da kanshi ya yanke shawarar tahowa da ita, ba ƙaramin" faranta mishi rai hakan yayi ba. "Ba ma kamar yadda yaga Zulai ta ƙara kyau da cika na musamman, alamun da ke nuna lallai fa ba ta cikin" "matsala ko kaɗan. Idan ya kalle ta yayi murmushi, sai ya kalli Hafiz yayi murmushi. Alamun da ke nuna zuciyarsa cike take da matsanancin farin ciki." Minti ɗaya biyu kuma sai ya kalli Hafiz ya ce """Hafizu na gode. Lallai ka cika ɗan halak! Allah yayi maka albarka.""" """Amin Baffa.""" "Ya amsa addu'ar da farin ciki sosai a fuskarsa, domin ya manta rabon da yaga irin wannan farin cikin a" fuskar mahaifinsa. "Ita kanta Innaye bakinta ya ƙi rufuwa, kamar gonar auduga haka take ta yaƙe haƙora tana shafa kumatun" Zulaikha da ta ji sun ƙara laushi sosai. """Zulai? Auta ke ce kika koma haka? Tubarakallah ma sha Allah! Lallai Hafizu baka watsar da amanar da" "na baka ba. Me kuke ba Autar tawa ne tayi irin wannan cikar ɗakin Hafizu?""" "Ya rasa amsar da zai ba Innaye, sai kawai yayi murmushi yana ɗan sosa ƙeya." Ita kuwa Zulaikha da ake ta caftar a kanta ganin irin matsanancin farin cikin da tsofaffin suke ciki yasa "jikinta yin sanyi. Ƙuduri na daban ke a cikin zuciyarta, a yanzu kam ta shiga tsaka mai wuya, anya idan ta" zama sanadiyyar yanke wannan farin cikin a cikin taƙaitaccen lokaci ta yi ma tsofaffin da suke matsayin "mahaifa a gare ta adalci kenan? Ko kuwa haƙuri za tayi ta cigaba da zama a sagale, cikin wata iriyar rayuwa ita ba mai ƴanci ba ita ba mare ƴanci ba har zuwa lokacin da bata san iyakarsa ba?" "Tana wannan saƙe-saƙen da canki-cankar, har aka kira sallar azahar. Baffa da Hafiz suka fita zuwa" "masallaci, ita da Innaye suka yi alwala suka yi sallah a cikin ɗaki. Ta daɗe sosai tana addu'o'i kala-kala" "bayan ta idar da sallah, har Innaye ta tashi ta fice ta shigo ma da Zulaikha abinci bata tashi daga kan dadduma ba." "[2/10, 10:39 PM] Fareeda Abdallah: ""Auta addu'o'in sun isa haka. Ki katse haka nan ki tashi ki ci abinci.""" "Innaye ta faɗa da murmushi cike fal da fuskarta, domin kallon Zulaikha da yadda ta koma kaɗai ba" ƙaramin farin ciki yake saka ta ba. """Innaye sannu da aiki. Ni fa bana ma jin yunwa, ki zauna mu ci tare don Allah. Na yi kewar hakan" "Wallahi.""" Ta ƙarasa maganar a shagwaɓe. "Suna zaune gaban farantin abincin, suna ci suna hira Hafizu da Baffa suka sake shiga cikin ɗakin." """Kin ji Hafizu wai wucewa zaiyi yanzu, nayi-nayi ya tsaya su ci abinci ya ce a'a!""" """Ba dai tare da Auta zai koma ba ko?""" "Innaye ta tambaya da sauri, idanunta a warwaje." Yanayin yadda tayi tambayar yasa Hafiz da Baffa murmusawa. """A'a Innaye. Ita kam tana nan, idan na dawo nan da sati biyu zan tafi da ita.""" "Hafizu ya amsa, har lokacin murmushin bai bar kan fuskarsa ba." "Nannauyar ajiyar zuciya Innaye ta sauke, kafin ta fara jera mishi addu'ar Allah ya tsare ya mayar da su" gida lafiya. """Amin Innaye. Na gode. Sai munyi magana ta waya.""" """Yaya? Minti biyu don Allah""" "Zulaikha ta kira shi da sanyin murya, a lokacin har sun juya za su fita shi da Baffa." A tare suka sake juyowa suna kallonta. """Ya aka yi?""" "Ya tambayeta da ɗan murmushi a fuskarsa, ganin idanun iyayen na kanshi." """Ko za ki bi ni mu koma ne?""" "Ya sake tambayarta, tsabar iya duniya irin nashi har yana wani ɗan kashe mata ido ɗaya." "Martanin murmushinsa ta mayar masa, ƙirjinta na bugawa sauri-sauri, amma ko kusa bata bari tsoro ya" bayyana akan fuskarta ba. Nannaɗaɗɗiyar takardar da tun ɗazu take ta yuƙwu-yuƙwu da shi a cikin hijabi ta fito da shi ta nuna masa """Ka tuna wannan takardar?""" "Kallon takardar da ke hannunta yayi, ya kalleta, duk da bai gane ko takardar mecece take nuna masa ba" ya rasa dalilin da yasa ƙirjinsa bugawa daram! """Ban tuna ba. Takardar mecece?""" "Ya tambayeta, sannan ya taka da sassarfa da nufin ƙarasawa kusa da ita don karɓar takardar ya karanta" abinda ke cikinta. "Yana miƙa hannunsa da nufin karɓa, ita kuma ta janye nata ta mayar cikin hijabi." """Takardar da ka bani ranar da ka kaini gidan Mummy ne, har ka gwaɓa min maganar cewa in dai su" "Baffa ba asarar kuɗin tara suka yi ba idan na nutsu in zauna in karanta abinda takardar ta ƙunsa. A wancan lokacin, Wallahi tallahi ko cikakkun sati biyu ba'a yi ba na karanta muhimmin saƙon da ka rubuta" "min a cikin takardar.""" "Tana zuwa nan a maganganunta ta sauke nannauyan ajiyar zuciya, ga mamakin iyayen biyu sai ga" hawaye sun silalo daga kwarmin idanuwanta. "Shi kuwa Hafiz ƙamewa yayi a tsaye kamar mutum-mutumi, jijiyoyin sadar da saƙonni daga zuciya zuwa" ƙwaƙwalwarsa suka tsaya da kai saƙonni na wasu daƙiƙu. Da rawar murya Zulaikha ta cigaba da magana """Yaya... Zaman ƙaryan nan da yaudarar iyaye baza ta ɓulle da mu ba. Na gaji da tunanin inda ƙarshen" "tafiyar za ta ajiye ni, domin ta ko ina aka ɓullo ni ce zan kwana a ciki. Don Allah, don darajar fiyayyen" "Halitta SAW, ina roƙonka kaji tsoron Allah, ka warware ma iyayenmu halin da muke ciki...""" """Mmmmmme yake faruwa?""" "Baffa ya katse ta da tambayar da sauri, bakinsa na rawa. Kafin ta amsa ya ƙara tambayarta" """Me kike ƙoƙarin cewa Zulai? Hafizu me kuke ɓoye mana?""" Ya ƙarasa maganar yana rarraba idanu tsakanin Zulai da Hafizu. "Ita kuwa Innaye, tuni ta fara jan duk wata addu'a da ta zo cikin zuciyarta, domin ta gama haƙiƙancewa" "duk abinda za su ji a yanzu, ba mai daɗi bane a gare su." "Kafin Hafizu ko Zulai ta buɗe baki tayi magana, sai ga sallamar Aunty Balira a bakin ƙofar ɗakin, tun kafin" a amsa mata ta yaye labulen ɗakin ta shigo fuskarta cike fal da fara'a take cewa """Wai ina Amaryar Hafizun take ne? Duk na ƙosa in ƙarasa aikin alalen da na tsira da ranar nan in zo" "inga irin ƙiba da kyawun da yara suka kururuta min cewa kin yi.""" "Ganin yanayin da su Baffa suke ciki kuma sai tayi suuu a tsaye, lokaci ɗaya fara'ar fuskarta ta ɗauke ɗif" """Baffa me yake faruw...""" """Ne mi guri ki zauna.""" Baffa ya katse ta tun kafin ta ƙarasa tambayar da take niyyar yi mishi. Jikinta a sanyaye ta zauna a ƙasa kusa da Zulai da take ta aikin tsiyayar hawaye kamar an buɗe famfo. "Umarnin zama Baffa yayi ma Hafizu, sannan shi ma da sanyin jiki ya lalubi hannun kujera ya zauna," "saboda wani jiri da ya ji yana barazanar kayar da shi, tun ma kafin yasan takamaimai abinda yake faruwa tsakanin Zulai da Hafizu." "Idanunsa ya mayar kan Zulai, domin a ganinsa ta fi ɗan dama-dama cikin yanayin da za ta iya musu" gamsasshen bayani na abinda yake faruwa. """Zulaikha?""" Ya kira cikakken sunanta a tausashe. """Na'am! Baffa""" Ta amsa bakinta na karkarwa. """Na sani tun kina ƙanƙanuwar yarinya ƙirƙirar ƙarya ki faɗa don cikar wani buri ko son zuciyarki ba ya" "daga cikin halayenki. Kuma ina da kyakkyawar zaton har na aurar da ke baki canja daga wannan halin da na sanki ba. A bar ki dai da rashin haƙuri ga wanda ya shiga gonarki, da kuma ɗan taurin kai ga wanda kika raina ajawalinsa. Amma na tabbata ko wanda kike ƙi ne baza ki ƙirƙiri ƙarya ki jingina mishi don kawai ki cimma wani muradi na zuciyarki ba. Ina roƙonki kiji tsoron Allah, ki faɗa mana gaskiyar abinda" "yake faruwa tsakaninki da ɗan'uwanki kuma miji a gare ki...""" """Baffa... Tun da muka bar ƙauyen nan, kwana ɗaya kacal nayi a gidan Yaya Hafiz... Duk sauran" "watannin nan na yi su ne a gidan Hajiya Saudah wacce yake kira da Mummy, ita ɗin Shugabansa ce a can gurin aikinsa...""" """Ban... gane ba...""" "Innaye ta katse ta bakinta na rawa, zuciyarta na bugawa sauri-sauri don jin wani sabon labari da ko kusa" hankalinta ya gaza ɗauka. """Rahina, kiyi shiru don Allah. Mu saurara tayi mana cikakken bayani yadda za mu fahimci abinda ke" "faruwa.""" Baffa ya faɗa ma Innaye da sanyin murya. Hafizu dai har lokacin yana tsaye ƙi ƙam! Kamar wanda aka sassaƙa shi. Duk da Baffa ya yi mishi umarnin "zama, sam ya kasa motsa ƙafafunsa balle har ya ja su zuwa gurin kujera, ko kuma ya zauna a ƙasa kamar" yadda sauran suke zaune. Baffa ne kawai a sama kan hannun kujera. "Ya riga da ya sani ko ba jima ko ba daɗe fallasuwar abinda ke tsakaninshi da Zulai dole ne, amma bai" "taɓa tsammani ko hasashe ko tunanin faruwarsa a irin wannan tsukun lokacin ba. Wani abin mamaki shi ne duk maganganun da ake yi yana ji tsaf, amma kamar wanda aka saka mishi dabaibayi a baki, sam ya kasa buɗe baki ya ce uffan! Balle har yayi yunƙurin kare kansa, ko kuma yayi ƙarin bayani yadda baza'a ga laifinsa ba. A taƙaice ma, kansa ya kulle tamau, ya rasa ta ina ya kamata ya kamo bakin zaren kurar da" Zulai take neman ta kwanto mishi. "Yana ji, Zulaikha ta gama bayar da labarin rikicin da ya shiga tsakaninta da Bintu, da har yayi sanadiyyar" "ɗauke ta daga gidan da yayi zuwa gidan Mummy. A hankali, kuma cikin nutsuwa ta cigaba da bayanin zamanta a gidan Mummy, da irin kyakkyawar kulawar da ta samu a hannun zuri'ar gidan. Wanda shi ya hana rayuwarta tagayyara ko kuma taji ta ƙosa ta dawo gabansu iyayenta." "Abu ɗaya da ta ɓoye musu a labarin shi ne soyayyarta da Kamal (Abban Imam), tafi-tafi har zuwa jiya da" "ta buƙaci lallai Hafiz ya kawo ta Faƙo ayau, ko kuma ita da kanta ta taho a motar haya." "Tana zuwa nan a labarin da take ba su tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya, irinna wacce ta jima tana kuka." Muryarta a shaƙe ta cigaba da cewa """Rashin zama na a gidan Yaya ba shi ne abinda ya fi damuna ba Baffa. Wannan takardar da kuka ji ina" "tambayarsa ya tuna ta?""" Ta fito da takardar da har ta fara jiƙewa da gumi saboda cukwuikwuiyeta da tayi a tafin hannunta tana "nuna musu, da karkarwar murya ta cigaba da cewa" """Duk da ya rubuta bayanin cikin takardar da yaren nasara ne, ba saƙon komai takardar take ɗauke da" shi ba illah na yanke igiya ɗaya daga cikin igiyoyi uku da suka ƙulla aure tsakanina da shi... Sannan ya "rubuta takardar ne tun ranar da ya rabo ni daga gidansa, saboda rashin iya karatun turanci yasa ban san" "me takardar ta ƙunsa ba sai bayan sati biyu da ba ni takardar. A yanzu haka kuma fiye da watanni shidda kenan da faruwar wannan al'amari, kuma duk da yana zuwa gidan Mummy ga shi nan ku tambaye shi na rantse da Allah bai taɓa furta cewa ya mayar da ni ɗakina ba har na gama iddah... A taƙaice dai Baffa, Innaye, Aunty Balira don Allah kuyi haƙuri ku yafe mana irin wasa da hankalinku da muka yi ni da Yaya," "amma zance na gaskiya shi ne babu wani aure ko zamantakewar aure tsakanina da shi.""" Lallai wannan shi ne asalin karin maganar nan da Malam bahaushe ke cewa Tashin hankali wanda ba'a saka masa rana. Izuwa yanzu da Zulaikha ta gama koro musu wannan cukurkuɗaɗɗen labarin da basu taɓa tsammanin "faruwarsa a nesa da ƙauyensu bama balle har ya faru a cikin ahalinsu. Ba Hafizu ne kaɗai bakinsa da tunaninsa ya tsaya na wucin gadi ba, Innaye da Aunty Balira ma sun bi sahunsa." "Shi kuwa Baffa tsananin mamaki, takaici, baƙin ciki, haushi ne suka taru suka zame mishi wani" "dunƙulallen abu a maƙoshi. Sau uku yana ƙoƙarin kalato miyau don ya haɗiye ko zai samu dunƙulallen abun ya sauka a cikinshi amma bakinshi ya bushe ƙayau, kamar mai azumi a lokacin da ake tsananin ƙwallara rana." "Shi da ba mura yake yi ba, ba kuma kuka ya ɗauki lokaci yana yi ba balle ace su suka zama sanadiyyar" shaƙewar muryarsa. Ko da ya buɗe baki da niyyar tambayar Hafizu daƙyar maganar ta fito a dusashe ya ce """Da gaske ne duk abinda ƴar'uwarka ta faɗa? Ka sake ta tun washe garin ranar da kuka bar ƙauyen" "nan?""" "Sai a wannan lokacin da Baffa ya jefa mishi waɗannan kausasan tambayoyin guda biyu, sannan ya ji" "kamar an kwance duk wani dabaibayi da aka yi ma bakinsa, ƙwaƙwalwarsa, da jikinsa. Cikin sauri ya motsa ƙafafunsa da suka yi masa tsami sosai saboda doguwar tsayuwar da yayi ya zube a ƙasa." "Ya sani, laifi ne ya riga da ya aikata shi. Yunƙurin yin ƙarya don kariyar kai ko kuma musanta abinda ta" "faɗa duk ba shi zai hana tonuwar asirinsa komai daren daɗewa ba. Don haka yaga gara kawai ya faɗi gaskiya, tare da yi musu gagarumin sadaukarwar da a wancan lokacin da aka ɗaura aurensa da Zulai a" karo na farko ya kasa yi musu. """Da gaske ne Baffa. Na sani ni mai laifi ne sosai, domin na yi wasa da hankalinku. Amma don Allah kuyi" haƙuri ku yafe mana kamar yadda Zulai ta roƙa mana. Sannan tunda yanzu lokacin da nake da damar "mayar da ita ya wuce, na rantse da Allah yanzu a shirye nake in karɓi aurenta da hannu bibiyu don in faranta muku rai...""" Saukar wasu tagwayen maruka a kuncinsa dama da hagu shi yasa shi rufe baki ba tare da ya shiryawa hakan ba. Duuummm! Shi ne ƙarar sautin da yake ji a kunnuwansa na tsawon wasu daƙiƙu. A idanunsa kuwa babu abinda yake kallo sai gilmawar wasu ƙananun taurari masu tsananin haske da sheƙi. Da saurin gaske ya rufe idanunsa don tsoron kar hasken taurarin su illata mishi ƙwayoyin idanu. Da "farko, ya zaci ya kurmance saboda ƙarar duuummm ɗin da yake ji a kunnuwansa ya daɗe bai daina ji ba. Sama-sama kuma sai ya fara jiyo muryar Innaye tana mishi magana kamar daga can nesa kafin maganar ya matso kusa da kunnensa sosai." "A tsorace, ya buɗe idanunsa yayi arba da Innaye da Baffa suna tsaye a gabansa suna huci. Da ganin irin" tsayuwar da suka yi ba shi buƙatar a faɗa mishi daga hannun su wa tagwayen marukan da ya amsa suka fito. "[2/11, 10:54 PM] Fareeda Abdallah: ""Hafizu su wa ka mayar sa'anninka?""" Innaye ta sake jefa mishi tambayar da matsanancin ɓacin rai a muryarta. """Mu za ka wulaƙanta Hafizu? Mu? Mu za ka wulaƙanta?""" "Izuwa wannan lokacin, muryarta rawa yake sosai, zafafan hawaye na sauka daga idanunta. Cikin fushi da" gushewar hankali ta sake buɗe baki ta ce """Hafizu Allah...""" Da wani mahaukacin tsawa Baffa ya katse ta """Keh Rahina kin yi hauka ne? Ɗan naki za kiyi ma baki saboda abinda bai taka kara ya karya ba?""" Ba Baffa kaɗai ba ya shiga firgici da jin kalaman da Innaye ke ƙoƙarin furta ma Hafiz ba. Aunty Balira da "Zulai ma sai da suka miƙe tsaye, hannayensu biyu ɗore akai hankulansu a tashe." "Kamar ƙaramar yarinya, haka ta fashe da kuka zuciyarta na ƙuna da raɗaɗi" """Ya zanyi Malam? Shin akwai inda na ragi Hafizu a tarbiyya ne da zai min wannan mummunar sakayyar?" "Ya zanyi?""" Hannayenta biyu ya riƙe ya ja ta ya zaunar akan kujera. A tausashe ya fara mata magana """Kiyi haƙuri. Hannunka ba ya taɓa ruɓewa ka yanke ka yar. Ki yafe masa, ita kuma Zulai mu cigaba da yi" "mata addu'ar dacewa da wanda ya fi shi alkhairi.""" Hannayenta ya saki ya koma gurin Hafizu da kallo ɗaya za a mishi a fahimci ba ya cikin hankalinsa. """Ka je, je ka Hafizu. Babu komai ai, wani zamani ne Allah ya kawo mu da kuyanga take haifar" "uwargijiyarta. Je ka, mun sallama, mun kuma yafe maka. Allah ya haɗa fuskokinmu da alkhairi.""" "Yana gama faɗin haka ya koma kusa da Innaye ya zauna, tafukan hannayensa biyu yasa ya rufe fuskarsa." "Kamar yana kuka, amma a zahiri ba kukan yake yi ba, nauyayan ajiyar zuciya yake ta sassaukewa akai-" "akai. Ba ya ko son ganin fuskar Hafizu, shi kanshi in banda ƙarfin zuciya da mazantaka babu abinda zai" hana shi furta mummunan kalami ga Hafizu kamar yadda Innaye tayi niyya. "Hankalinshi a tashe, maɗaukakin tashin hankali irin wanda tunda ya zo duniya bai taɓa shiga kwatan-" "kwacinsa ba. Da rarrafe, ya fara muskutawa da nufin ƙarasa gurinsu Baffa a fusace Aunty Balira ta" dakatar da shi. "Hannunsa ta kamo, ta miƙar da shi tsaye a fusace, yana waigen su Baffa yana cijewa a haka ta ja shi har" sai da ta fice da shi daga cikin ɗakin. Bata ƙyale shi ba sai da ta kai shi har gurin motarsa. "Direba da tun ɗazu yake jiran fitowarsa yana ganinsu ya buɗe ƙofar, tura shi ciki Aunty Balira tayi sannan" ta cusa kanta cikin motar suna kallon juna """Kayi haƙuri. Mu kam su kaɗai muke da, ba mu da makwafinsu a wannan duniyar. Gara kai, ko da sun" "mace kana da Tauraruwa Bintu da gudan jininka Aadilu. Kaje kawai, domin cigaba da ganinka kaɗai ya isa yasa zuciyar Innaye da Baffa bugawa. Mun sallama ka ga Bintu Hafizu.""" Fuuuuu ta wuce zuwa cikin gidan ba tare da ta saurari ko zai ce mata wani abu kamar yadda taga bakinshi na motsi ba. "A ɓangarensa har ya yunƙura zai bi bayanta, sai kuma ya tuna wasu daga cikin maganganunta gaskiya ta" faɗa. A yadda ya ɓata ma Baffa da Innaye rai lallai ya kamata ya basu iskar da za su huce ko na kwana ɗaya ne. """Mu je.""" "Ya faɗi haka ga direba daƙyar! Sannan ya janyo ƙofar motar ya rufe, ya lumshe idanunsa ya jingina da" "jikin kujera, yana jin yadda kanshi ke wani irin matsanancin sarawa kamar zai faɗo." ****** ****** Kwanaki bakwai da suka biyo baya wasu irin zafafan kwanaki ne suka kasance ga Baffa da Innaye da "Aunty Balira. Duk da labarin mutuwar auren ya bazu ga sauran dangi, amma waɗannan mutane uku su ne waɗanda al'amarin yafi yi wa mugun dukan da in banda Allah ya kiyaye tabbas da sun samu matsala a" lafiyarsu. "Innaye da Baffa jininsu ne yayi mummunan hawa, gara ma Innaye daman an san tana da hawan jini, shi" kuwa Baffa da ba'a taɓa sanin yana da shi ba sai yanzu Allah ne ya tsare shi amma da ya kamu da cutar mutuwar ɓarin jiki. "Kasancewar yanzu an samu gagarumin cigaba a asibitin ƙauyen, duk ranar litini da talata da laraba," "akwai babban likita da yake zuwa daga kaduna ya duba marasa lafiya. Kuma an zuba ma'aikatan jinya ƙwararru a asibitin, cikin hukuncin Allah da taimakon wannab likitan na kyawawan magunguna da ya rubuta musu, da kuma nasiha da tunatarwa kan muhimmancin yarda da ƙaddara daga bakin babban malaminsu Zulaikha Baffa da Innaye har ma da Aunty Balira suka cigaba da rayuwa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Kaso sittin da biyar na damuwarsu ya ƙaura, musamman ganin yadda Zulai ita da" kanta take iya ƙoƙarinta wajen rarrasarsu da kalaman kwantar da hankali. "A cikin waɗannan kwanaki bakwai, zuwan Hafizu sau uku ƙauyen, amma sam ko kusa ya kasa samun" yadda yake so. Lallai wannan shi ne BAYAN TIYA AKWAI WATA CACA. Sa'adda ya yanke ma kanshi shawarar rabuwa da Zulaikha salin-alin don samun kwanciyar hankalinsa da na iyalinsa ko kusa bai hango ma kansa faruwar wannan ƙalubalen ba. Shi dai kam Allah ya sani ko na daƙiƙa ɗaya bai taɓa jin soyayyar Zulai a zuciyarsa ba. Kuma tun da aka ɗaura aurensa da ita ya shafe kwanaki biyu ne cif cikin zazzafan tunanin ta yadda zai iya fara gudanar da rayuwar aure tare da Zulai. "Bai hango ma kanshi zai iya ko da kwatantawa ba. A ganinsa, zaman aure da Zulai zaluntarta kawai zaiyi" "ƙarara, ba ya son ta, Bintu ita ce zaɓin zuciyarsa. Ta yaya zai iya kwatanta adalci a tsakaninsu? Ya gama" haƙƙaƙe ma kansa zama da Zulai tamkar jefa kansa a halaka ne. Sake tunawa da babu ɗa'a ga abokin halitta wajen saɓa ma mahalicci yasa shi rubuta ma Zulai takardar "saki bakinshi ƙanin ƙafarshi. Kuma ko a yanzu, baiyi da na sanin sakin Zulai ba, domin har yanzu shi ba ya" jin sonta a zuciyarsa. "Amma kuma irin gagarumin farin cikin da ya gani a fuskar iyayensa, lokacin da suka je Faƙo shi da Zulai," yasa shi ji a ransa lallai zai iya yarda a sake ɗaura mishi aure da ita su zauna a wani gida daban ba tare da sanin Bintu ba ko don ɗorewar faffaɗan farin cikin da ya gani a fuskar iyayensa. "Ko da Zulai bata tona asirin abinda ke faruwa ba, shi da kanshi zai bayyana abinda ke faruwa idan lokacin" "da ya tsara yayi, cikin hikima da iya magana ta yadda al'amuran baza su taɓarɓare haka ba." Shi yanzu ta ina zai ɓullo ma wannan al'amari? Sai da yayi kwanaki huɗu a Kaduna kafin ya koma Abuja "saboda tsananin tashin hankalin da yake ciki, ya san ko ya koma Abuja Bintu, ɗansa, da gurin aikinsa da sauran abokan arziki baza su taɓa samun nutsuwarsa ba. A cikin kwanaki huɗun da yayi a Kaduna zuwanshi Faƙo sau biyu, ya koma Abuja a daddafe cike da damuwa yayi kwana uku sannan ya sake tafiya" "Faƙo, nan ma dai babu wani cigaba." "Gaba ɗaya iyayen sun ƙi sauraransa, duk yadda yake tunanin girman al'amarin ya wuce haka. Ko da yayi" tunanin bi ta hannun Ƙannen Baffa su Baba Abubakar su ma gaba ɗaya sun ƙi masa hannu. Haka ma ƴan'uwan Innaye sun ƙi sauraransa. A zuwansa na huɗu ne ya tara Aminan Baffa da waɗanda yasan Baffa yana jin maganarsu har da ƙwallarsa ya roƙi don Allah su shige mishi gaba wajen sasanta shi da iyayenshi. "Sun yi mishi faɗa sosai kamar za su ari baki. Shi dai kanshi yana ƙasa, sai haƙuri yake cigaba da bayarwa" "yana sharar ƙwallah, tunda matar na tuba ba ta rasa mijin aure." "A ƙarshe Mal Liman ya kira Baffa a waya ya roƙe shi alfarman ga su nan zuwa gidan, yana so zaiyi" "magana da su shi da Innaye. Baffa zai musa Mal Liman ya haɗa shi da Baba Lurwanu a wayar, a dole ya amince da ziyarar tasu." "Ko da ya gansu tafe da Hafizu baiyi wani mamaki ba, gaba ɗayansu suna zaune ne a falon Innaye saboda" "ya fi girma. Hankalin Hafiz bai ƙara tashi ba sai da yaga yadda Baffa da Innaye suka ƙara ramewa sosai a cikin kwanakin, kuma wani abu da ya lura shi ne sam ba sa ko ƙaunar kallonsa, a ɗazu, matso ƙwallar" "dole yai tayi a gaban su Mal Liman, a yanzu kuwa kukan na gaske yake yi." Hankalinshi ba ƙaramin sake tashi yayi ba ganin duk irin nasiha da kyawawan kalaman da aka yi ta faɗa "ma su Baffa sun ƙi cewa komai. Har dattijan suka gama duk maganganu da nasihar da za suyi, suna" "ƙoƙarin rufe taron da addu'a. Baffa bai ce komai ba, balle Innaye da tun ɗazu fuskarta ke lulluɓe cikin hijabi." """Baffa, Innaye, don girman Allah ku yafe min. Na san na aikata kuskure mai girma a gare ku, bazan sake" "ba in Allah ya yarda. Kuma a shirye nake a sake ɗaura min aure da Zulai in riƙe ta...""" Da sauri Baffa ya katse shi da cewa """Hafizu, a madadin Rahina zan ari bakinta in ci mata albasa. Mun yafe maka. Amma daga yanzu," "zancen aure tsakaninka da Zulai ya haramta har abada, kar in sake jin ta daga bakinka. Ina fatan ka fahimce ni?""" """Na fahimta Baffa.""" Ya amsa jikinsa a sanyaye. Godiya Baffa yayi ma dattijan da Aminansa sannan Mal Liman ya rufe taron da addu'a. Bayan shafa "fatiha suka fice daga ɗakin Hafiz ya bi su a baya yana ƙara yi musu godiya. Ko da ya koma cikin gidan, ya" "zaci ko ɗan kaɗan ne zai ga canji a fuskar Baffa da Innaye, sai yaga ba wani canji." Bayan kashaidi mai girma da Baffa ya kora mishi cikin ɓacin rai akan kar ya kuskura ya sake tattaro mishi mutane kan matsalar da shi kaɗai ya jaza ma kanshi ficewa yayi daga falon Innaye yana jan ƙaramin tsaki. "Ita kuwa Innaye ko kallo bai isheta ba, miƙewa tayi daga falon ta fice tsakar gida, don ma kar ta shiga" ɗaki ya ce zai bi ta da wani magiyarsa na banza da wofi. Ba komai yake ƙara ɓata mata rai da lamarin ba "face idan ta tuna yadda Hafiz ɗin yayi wasa da hankalinta, tsawon watanni tana harhaɗa mishi tsaraba da abubuwa da yawa kan cewa ya kai ma Zulaikha ashe sam ba sa tare da juna." Don tsabar ya raina ta har yana zuwa da matarsa tana ƙara jaddada mata lallai suna zaune lafiya da Zulai. In dai ɗan da ta haifa a cikinta zai iya yi mata irin wannan rainin wayau wanene ma a duniya bazai raina ta ba? Babu! "Tabbas ta yafe ma Hafizu kamar yadda Baffa ya nema, amma ba ta ji a ranta ko can gaba za ta iya" sakewa da Hafizu ta yarda da shi kamar yadda suke a baya. Abu ne da bazai taɓa yiwuwa ba. Haka Hafiz ya ƙaraci zamansa a ɗakin ya fito yayi musu sallama ita da sauran matan gidan duk zuciyarsa a jagule. Fatan Allah ya kiyaye hanya suka yi masa ba wani walwala da ƙauna irin ta da a muryoyinsu ya fice yana jan ƙafafu. "Ko da yaja motarsa kamar zai kai ma Aunty Balira ziyara, amma sai ya tuna yadda suka rabu baram-" "baram a wancan zuwan nasa, da kukanta har tana mishi Allah ya isa kan ɗaukar haƙƙinta da yai tayi yana ce mata lafiya ƙalau suke zaune da Zulai." Anty Ladidi da Anty Rakiya kuwa tun da suka haɗu a gidan Baffa ya gaishe su babu wacce ta amsa mishi "ko kusa baiyi gigin zuwa gidajensu ba, ya san idan ya je duk munin abinda suka yi mishi shi ya siya da kuɗinsa." Haka yabar garin Faƙo zuciyarsa cike da saƙe-saƙen sabbin hanyoyin da ya kamata ya bi don daidaitawa da iyaye da ƴan'uwansa. """To Alhaji ina ga me zai hana tunda duk an fahimci juna a ɗaura auren kawai a wuce gurin?""" "Da fara'a sosai a fuskar Abba Lurwanu, Kamal, Alhaji Musa suka ɗaga fuskokinsu suna kallon Baffah." """Da gaske kake yi Malam Aminu?""" Abba Lurwanu ya jefa ma Baffa tambayar don kore tantama. "Ɗan muskutawa Baffa yayi, kafin ya kalli ƴan'uwansa uku da Yayyen Innaye biyu da Malam Liman da su" ma fuskokinsu ke bayyana farin ciki da nutsuwa da jin kalaman bakinsa. Sai kuma ya sake mayar da hankalinsa kan su Abba Lurwanu. """Ƙwarai kuwa. Da gaske nake yi. Tunda dai duk na faɗa maka muhimman abinda ya kamata ku sani" "dangane da Zulai, kuma kuka ce duk waɗannan ba matsala bane. Wanda ke da alhakin aurenta ya rantse min da girman Allah shi ko a matsayin bazawara take yana son ta a haka, kuma zai riƙe min ita tsakani da Allah. To me za'a jira?" Kuma don yin kitso da ƙwarƙwata a gabanku na kira yarinya na tambaye ta ta amince da auren Kamalu? Ta nuna kunya da murmushi wanda a gurinmu babbar alama ce ta amincewa. Muhimmin abu kuma da fiyayyen halitta SAW ya umarcemu da yi kafin mu bada auren ƴaƴanmu shi ne "bincike, kai da na yarda da kai ɗari bisa ɗari ka tabbatar min da nagarta da ingancin halayen wannan" "yaro. To me za'a jira bayan haka kuma? Ai ina ga kawai a ɗaura auren kafin ku tafi, ko zuwa nan da sati biyu ko uku sai ta tare a ɗakinta in sha Allah." "Saboda mu kanmu abun ya zo mana bagatatan ne, bamu shirya komai na aurenta ba...""" """Alhamdulillah! Ma sha Allah! Baffah na gode, na gode, Allah ya saka da alkhairi. Ubangiji ya ƙara lafiya" "da nisan kwana. Ni Wallahi auren Zulai ma da za'a bani a sauƙaƙe haka ya fiye min komai, ita ɗin kawai" "nake buƙata. Ba sai kun wahalar da kanku wajen siya mata komai ba.""" Abban Imamu yayi maganganun da matsananciyar farin cikin da ya gaza ɓoyuwa a fuskarsa. Ganin komai yake yi tamkar a mafarki. Sai ga shi cikin lokaci ƙanƙani Alhaji Musa ƙanin mahaifinsa ya "zaro bandir na dubu ɗari daga Aljihunsa, Abba Lurwanu ya ƙara wata dubu ɗarin akai suka zama dubu ɗari biyu. Nan take aka miƙa ma Baba Abubakar a matsayin sadakin Zulaikha. Suka tashi daga zaman da cewa idan aka idar da sallar azahar sai a ɗaura auren, tunda a lokacin ƙarfe goma sha biyu da rabi ne na" rana. Ko da labarin halin da ake ciki ya iske Mummy Saudah da Hajja a cikin gida ɗakin Innaye zubewa kawai sukai goshinsu a ƙasa suna godiya ga Allah. Bayan sun miƙe tsaye kuma Hajja ta karkace kai ta riƙe hanci ta fara rangaɗa wata ƙaƙƙarfan guda kamar yarinyar mace. Daga bisani kuma ta fara rera waƙa irin tasu ta mutanen da tana ƴan raye-raye. Innaye dai tun tana "kawaici tana ɗan murmushi har ta sake ta fara dariya sosai. Cikin ƙanƙanin lokaci, ɗakin Innaye ya cika da" "abokan zamanta da yaran gida, matan maƙwafta suna yi mata Allah ya sanya alkhairi." Mummy Saudah kuwa uwar ɗakin Innaye ta shige ta ciro wayarta a cikin jaka ta fara latso lambar ƴan'uwa da abokan arzikinta tana faɗa musu za'a ɗaura auren Baban Imam yanzu da bayan sallar azahar. """Haba Hajiya Saudah? Wani irin aure ne haka na bazata babu ko gayyata? Ko sadaka aka bashi?""" Kaɗan kenan daga cikin ire-iren tambayoyin da mutanenta suke mata suna mamakin al'amarin. """Tsaleliyar yarinya ce ɗaya tamkar da miliyan. Ba sadakarta aka bashi ba, shi da kanshi ya gano ta ya" "nace yana so, da yake dai iyayenta dattijan ƙwarai ne shi yasa daga zuwa tambaya suka ce za'a ɗaura aure nan da sati biyu sai ayi biki.""" "Amsar da take basu kenan, da matsananciyar murna a muryarta." "Ko a wannan lokacin, sai da ta sake gwada kiran lambobin Hafiz amma gaba ɗaya basu shiga ba. Mamaki" "ne ya kamata, don ya saɓa daga cikin ɗabi'unsa haka kawai ya kashe waya tun daren jiya har wayewar garin yau ga shi ana neman a sake yini bata same shi ba." Ko da yake ta wani ɓangaren rashin samunsa a wayar ma ya zame musu alkhairi. Domin rashin samun nasa don ya kwatanta musu hanyar da za su bi don su zo Faƙo su kawo ma Zulai ziyara bayan sati biyu da "tafiyarta yasa ta nemi Alhaji Lurwanu a waya, tunda ta san irin zumuncin da ke tsakanin Alhajin da iyayen Hafiz ɗin." Ita kuma Alhaji Lurwanu ya kasance Amini ne ga marigayi mijinta Babansu Kamal. Da yake ita ɗin ba "mace ba ce mai ɓoye-ɓoye, kai tsaye ta faɗa ma Alhaji Lurwanu halin da ake ciki, da kuma a taƙaice abinda zai kai su ƙauyen shi ne gaisuwa da roƙon iri." """Ai kuwa Hajiya Saudatu ina ga faɗuwa ce tazo daidai da zama. Dama akwai abinda zai kai ni Kaduna" "gobe, to kuma ina tunanin ƙarasawa har can ƙauyen in kai ma shi Malam Aminu ziyarar bazata, shi yasa ma ban faɗa mishi ba. Don haka ina ga goben kawai sai mu tafi gaba ɗaya. Amma kuma ba kya ganin ya dace mu tafi da Alhaji Musa? Ko don acan ɗin su ƙara sanin lallai fa da gaske Kamal yake ƙaunar" "yarinyar.""" Abba Lurwanu ya ƙara mata da wannan shawarar. Hangen nasarar da za'a ƙara cimmawa idan aka tafi da Alhaji Musan yasa bata ɓata lokaci ba wajen saka "Kamal ya kira shi ya faɗa mishi halin da ake ciki. Daga bisani itama ta ƙara kiranshi a waya ta sanar da shi halin da ake ciki, ta kuma roƙi alfarmarsa na idan goben ba shi da muhimmin uzuri ya shirya su tafi tare." Da yake tsakaninta da dangin mijin nata akwai kyakkyawar fahimta. Duk da yana da uzurin haka ya katse komai nashi ya shirya aka yi tafiyar da shi. "Ko da suka iso, irin kyakkyawar tarbar da suka samu daga su Baffa duk da ba'a san da zuwansu yasa ta" ƙara ji a ranta lallai Kamalu yayi sa'ar mata da surukai. Ita ma bata mishi zaɓen tumun dare ba. Duk da mamakin da tayi na jin labarin an taɓa ɗaura aure tsakanin Hafiz da Zulai abin bai ɓata ranta ba. "Musamman da taji cewa duk zaman da Zulai tayi a gidanta a lokacin babu auren, ko kaɗan bata ƙullaci" Hafiz ba balle Zulai. Abinda ta ɗauka ma rabon ɗanta Kamal ne ya rantse shi yasa da Hafiz yake neman inda zai aje Zulai na "ɗan lokaci gidanta ne kawai ya faɗo mishi arai. Yo menene a ciki don Hafiz ya saki Zulai ɗanta Kamal ya aura? Ai daman haka rayuwa take. Sai wani ya aje wani zai ɗauka, kuma sai wani ya rasa wani zai samu." "Ko yanzu da take sake kiranshi a waya ba komai take son yi mishi ba face godiya, sannan kuma ta bashi" labarin duk irin halin da ake ciki. Kuma tayi mishi alƙawarin in Allah ya yarda kafin su bar ƙauyen ita da Abba Lurwanu za suyi iya ƙoƙarinsu wajen daidaita shi da iyayensa da suka lura ba ƙaramin fushi sukai da shi ba. "Sai a wannan lokacin, tunanin kiran Bintu don tambayar halin da Hafiz yake ciki ya faɗo mata arai. Ba" tare da ɓata lokaci ba kuwa ta lalubo lambarta ta danna mata kira. """Wallahi Mummy ba shi da lafiya ne tun jiya. Kin ganshi nan kwance a gida na ɗaura mishi drip, barci" "yake yi.""" Bintu ta faɗa ma Mummy bayan gaisuwar da ya shiga tsakaninsu. """Subhanallahi! Me yake damunshi haka? Har da ƙarin ruwa?""" Mummy ta tambayeta da damuwa sosai a muryarta. """To ga shi nan dai Mummy, ya kwana biyu yana yawo da ciwon a tsaitsaye jiya zuwa yau ne dai ya" "kwanta. Kuma ya ƙi yarda mu tafi asibiti, na ɗibi jininshi dai na tura asibiti yanzu ina jiran sakamako ne, amma na san bai wuce typhoid.""" Bintu ta amsa itama da tata kalar damuwar. """Allah ya sauwaƙe ya bashi lafiya. Yanzu dai ba na Abuja, idan mun dawo da wuri zan leƙo gidan, idan" "kuma munyi dare gobe sunday zan shigo in sha Allah. Idan ya tashi ki gaishe min da shi.""" Da haka suka rabu. "A can ƙofar gidan Baffah, Abban Imamu ne zaune a cikin ƙatuwar jeep ɗin sa yana waya da abokinsa" "Isma'il, bakinsa har kunne kamar gonar auduga." "Tsananin farin cikin da yake ciki yasa tun ɗazu ya kasa rufe baki, a yadda yake jin zuciya da ƙirjinsa a" "yanzu, kamar bai shiga cikin ƙunci da matsananciyar damuwa a iya tsawon sati biyunnan da Zulai tayi ba" ta amsa wayarsa kuma ba ta chatting da shi sai lokaci bayan lokaci ba. "Shi da kanshi tun ranar da ta tafi da ya kira ta a waya ya fahimci tana cikin damuwa, amma duk yadda ya" "buga ya kaɗa ya raya ta ƙi faɗa masa abinda yake damunta. Idan ya matsa mata da tambaya ma, sai dai ta saka mishi kuka ta katse wayar." Wannan dalilin yasa a daddafe cikin rashin nutsuwa da kwanciyar hankali yayi sati biyu bai biyo ta ba. In "banda ya kasance yaro mai tsananin biyayya lallai da tuni ya ƙetare umarnin Mummy ya bi bayan Zulai a ɓoye duk da bai san hanya ba, matambayi ai ba ya ɓata." Da gaskiyar Mal bahaushe da ya ce abinda babba ya hango yaro ko ya hau dutsen dala bazai hango ba. "Yanzu da ya danni zuciyarsa, ya cigaba da haɗiɗiyar ƙunci da damuwa duk da damuwar Zulai na damunsa." Sai ga shi jinkirin ya zame mishi gagarumin alkhairin da bai taɓa zata ba. Daga zuwa neman aure sai ace a ɗaura auren kawai a wuce gurin? """Wai da gaske kake yi Dude?""" Isma'il ya sake tambayarsa daga can ɓangaren da murya mai bayyana matsananciyar mamaki. Ƙaƙƙarfan dariya ya kwashe da ita yana ɗan dukan sikiyarin mota kamar ba shi ba. """Kana mamaki ko Dude? Nima har yanzu mamakin nake yi Wlh. Yanzu fa ana idar da sallar azahar" "ɗinnan za'a ɗaura aurena... Gaskiya... ina cikin alkhairi dumu-dumu... Alhamdulillahi rabbil-Aalamin.""" """Ma sha Allahu laaƙuwwata illah billah! Na taya ka murna Aboki. Allah ya sanya alkhairi. Yanzu dai bari" "in kira Auwal mu tsara yadda za mu biyo jirgin yamma zuwa Kaduna, wannan gagarumin abin farin cikin bai kamata ace bamu a kusa da kai ba...""" """Kar ku damu, ba sai kun zo ba. Mu ma bayan Asr prayer za mu kamo hanyar komawa gida. Ka san" "yanzu ɗaura auren kawai za'ayi, bikin sai daga baya. Iyayenta sun nemi in basu sati uku ni kuma gaskiya bazan iya ba, na ma faɗa ma Mummy gaskiya bikin kar ya wuce nan da sati biyu. So kaga duk wasu" "shirye-shirye muna da isassun lokacin da za muyi a Abuja, duk da dai ni bidi'o'innan ba burgeni suke yi ba." "Bari in je inyi alwala kar in rasa jam'i, za mu yi magana bayan ɗaura auren.""" """To Aboki, once again Allah yasa albarka yasa mahaɗin arzikinka ce.""" """Amin ya Allah Dude. Na gode.""" ***** ***** "[2/15, 9:35 PM] Fareeda Abdallah: Zulaikha da tun ɗazu taja Karima da Imam suka tafi gidan Aunty Balira" sam ba su da labarin halin da ake ciki. Suna zaune suna hira da dararraku sun tasa lafiyayyiyar gurasar da "Aunty Balira ta gasa musu a gaba suna ci, kawai sai jin sallamar abokan zaman Innaye tayi wai sun zo tafiya da ita in ji Baffah." "A tsorace, duk suke kallon su Umma Laraba, ita ta ma kasa cewa komai don tsoro da faɗuwar gaba. Sai" Aunty Balira ce tayi ƙarfin halin tambaya bakinta na rawa """Umma lafiya kuwa? Me Autar Innayen tayi kuma?""" """A'a lafiya ƙalau Balira. Bata yi laifin komai ba, abin alkhairi ne ya faru da ita. Auranta aka ɗaura yanzu" "da ɗan'uwan wannan yarinyar da take zaune kusa da ke. Duk da tarewar ba yanzu ba sai nan da sati biyu, kinga matsayinta na matar aure ai bai kamata ace an barta tana yawace-yawace ba, shi yasa Baffanku ya" "ce muzo mu tafi da ita.""" Tsananin murna da farin ciki yasa Karima bata san sa'adda ta ture kwanon man ƙuli da yake gabanta ba ta miƙe tsaye ta fara kwaso shoki tana watsa ma Zulaikha. Lokaci ɗaya tana haɗa da waƙar gwanja ta "Ahayye sama cibiyar nisa, tsakaninki da yaro sai kallo." "Aunty Balira babu abinda bakinta ke furtawa sai kalaman godiya ga Allah, da jinjina girman hikima irinta" "Ubangijin sammai da ƙassai, da ya ƙaddara faruwar komai cikin ƙanƙanin lokacin da basu taɓa tsammani ba." "Zulaikha kuwa, da farko daskarewa tayi a zaune, bakinta a ɗan buɗe, ta ƙura ma Umma Laraba idanu" "don ji take kamar dai kunnuwanta basu ji abinda aka faɗa daidai ba. Sai da karaɗin Karima ya isheta sannan tayi firgigit, sai kuma matsananciyar kunya, da wani irin matsanancin daɗi da farin ciki suka lulluɓe sassan jikinta." Cusa kanta tayi a tsakanin cinyoyinta tana murmushi ƙasa-ƙasa. Ita kaɗai take jin ta kamar wacce take yawo a kan gajimare. """Ashe haka ake ji a jiki da zuciya idan aka auri wadda ake so?""" "Ta tambayi kanta da kanta. Da gaske tana son Abban Imam, irin matsanancin son nan da ita kanta baza" "ta ce ga iyakarsa ba, domin a wasu lokutan soyayyarta har zillo da tsungulin zuciyarta take yi." "Kawai dai a matsayinta na mace, wacce aka fi sani da kunya da kawaici, da iya danne abu a zuciya yasa" take matuƙar ƙoƙari wajen yi ma soyayyar tasa waigi a zuciyarta. Amma in da ba don haka ba... Wata-kila da tuni ta ƙwace da sambatun sunansa da labarin irin son da take masa duk bayan minti ɗaya biyu... A ƙarshe dai gurasar da basu samu ƙarasa ci ba kenan. Ita ma Aunty Balira miƙewa tayi ta bi bayansu "bakinta har kunne bayan ta haɗa sauran gurasar a cikin ƙaton kwanon samira, ta yayyanka kabeji ta tafi" da shi da nufin kai ma mahaifiyar Karima da Kakarta Hajja. "Ko da ta isa gidan Baffa, irin yadda ta ga Mummy da Hajja na tarairayar Zulaikha da ina za'a saka ina aka" aje da ita cikin matuƙar ƙauna da tarairaya yasa ta ƙara ji a ranta lallai fa yanzu ne Autar Innaye ta daje da miji ɗaya tamkar da dubu. Irin wannan ƙauna da tarairaya haka? Gaba ɗaya sun babbake komai sun hana kowa kusantar Zulaikha. "Hajja da ta kasance haifaffiyar ƙauye ita ta dinga lissafa irin kayayyakin da take buƙata a kawo mata," "wanda za ta fara yi ma Zulaikha amfani da su wajen gyaran jiki. Cikin ƙanƙanin lokaci aka haɗa mata komai, sai ga Hajja a gaban murhu tayi bake-bake kamar ƴar gida, Balira, Indo, Rakiya, Ladidi da sauran manyan ƴaƴan Baffa suna kusa da ita tana basu umarnin daka wannan, miƙo wancan, ɗauraye wannan," "kuma ta riƙe sunayensu ram a bakinta, kamar dai daman can ta san su." "Cikin awanni biyu da suka biyo baya, Hajja ta haɗa lafiyayyen ruwan lalle da yaji magunguna da turaruka" irin nasu na mutanen da tayi ma Zulaikha wanka da shi. Ana wankan tana zazzaga ma Zulai masifa saboda yadda take ta noƙewa cikin kunya. """Kin san Allah Zulai zan ci ƙaniyarki. Kalle ni dakyau! Jikata na ɗauke ki ba matar jika ba. Yadda zan bugi" ƙirji in shirya Kareema ranar aurenta haka zan shirya ki Zulai. Don haka duk wannan nuƙu-nuƙun da kike "yi gara ma ki bari, bai sha min kai ba in saka tsumagiya a cikin banɗakinnan in zane ki ciki da bai idan kika ce za ki min taurin kai. Atoh! Ni ba ruwana. Haka nake free falo, kin sanni sarai.""" "Ko bayan gama wankan, haka ta tasa ta gaba da hayaƙi kala daban-daban. Daga ƙarshe aka yi mata" "wankan turare, a cikin sabbin kayayyakin da suka tafi mata da shi aka zaɓi doguwar riga ɗaya aka ba ta ta saka." "Bayan dogon naci da roƙo da Abban Imam yai tayi ma Mummy, a ƙarshe ya bi ta hannun Anty Balira da" sabo na surukuta ya shiga tsakaninsu cikin ƙanƙanin lokaci ya samu damar ganawa da ita a falon Baffa. "Tunda ta shiga cikin ɗakin, ta kasa ɗaga idanu ta kalle shi, wata matsananciyar kunyarsa ce ta lulluɓeta." "Ko gaisuwa daƙyar ta iya buɗe baki ta gaishe shi, ƙirjinta banda bugawa babu abinda yake yi, har yanzu," ganin komai take yi kamar ba da gaske ba. Shi kuwa babu kunya yayi zaman dirshan a gabanta kan dadduma yana leƙen fuskarta. Bakinsa har "kunne, da farko ya kasa cewa komai bayan gaisuwarta da ya iya amsawa." """Beb kin ga ikon Allah ko?""" "Ya tambayeta bayan ya ga kiran Mummy na shigowa cikin wayarsa, yasan ba kiran komai bane face na" "tunasar da shi ƙurewar da lokaci ya fara yi, ƙarfe huɗu na yamma har ta gota." """Alhamdulillah!" Alhamdulillah!! "Alhamdulillah!!! Daga yau, har zuwa ƙarshen rayuwata, bazan taɓa gajiya da cigaba da godewa" "Ubangiji da ya nufe ni da samun aurenki a sauƙaƙe ba Zulaikha. Wallahi ina son ki, irin matsananciyar" "soyayyar da ni kaina ban san iyakarta ba. Ubangiji Allah ya bamu zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba.""" """Ameen.""" "Ta amsa daƙyar, a ciki-ciki." """Baffa yace bikin sai nan da sati biyu, amma ni dai ina jin gaskiya bazan iya bari har sai nan da sati biyu" "ba... zan je in roƙe shi ya bari mu tafi da ke yau kawai...""" """A'a don Allah kayi haƙuri.""" "Tayi maganar a shagwaɓe, tare da buɗe fuskarta da sauri tana kallonshi da dara-daran idanunta." Da sanyin murya ya ce """To bayan ma tunda kika taho ja min aji kike tayi don kin ga ba na kusa da ke, na san yanzu ma idan" "nayi gangancin tafiya na barki haka za ki cigaba da ja na a ƙasa tunda ba wani so na kike yi ba...""" """Ayya Ayya mana Abban Imam.""" Ta sake faɗa a shagwaɓe. Kafin yayi magana ta sake cewa """Allah kuwa ba haka bane. Kawai dai tunda nazo ba na cikin nutsuwa ne saboda abubuwan da suka" "faru. Kayi haƙuri, bazan sake ba, ka ji?""" "Ƙuriii yayi mata da idanu yana kallonta, yadda hatta muryarta yake fita da wani irin sanyi da ƙamshin da" "yake ɗan bugun fuskarsa. Wani daddaɗan shaukin ƙauna na ƙara ratsa duk sassan jikinsa. Tun da ya fara ganinta, ya rasa dalilin da yasa, komai tayi burge shi take yi, kuma kyau na musamman take ƙarawa a idanunsa ko wane lokaci." Domin kawai ya ƙara ganin shagwaɓa da taɓarar da take masa yasa ya maƙale kafaɗa kamar ƙaramin yaro ya cigaba da tsokanarta. """Na ƙi ɗin! Ba wani nan. Na san wayau kawai za ki min. Ni dai gara kawai mu tafi yau gaba ɗaya.""" """Allah ba wayau zan maka ba. Don Allah ka bar maganar tafiyarmu yau.""" Tayi ƙwalƙwal da idanunta kafin ta ci gaba da cewa """Ka ga fa yanzu an ce an ɗaura mana aure, idan na ƙi bin umarninka ai sai mala'ikun rahama suyi ta" "tsine min. Haka ne ko? To don Allah ka yi haƙuri, ka ji Abban Imamuna?""" "Tayi masa far da idanunta, ƙasa-ƙasa ta cigaba da cewa" """Kuma maimakon sati biyu ma ina laifin wata biyu? Kamar gobe ne za kaga sati biyun ta zo ta wuce, a" "cikin sati biyu bazai isa inyi shirye-shiryen komai ba...""" """Lallai ma Yarinyar nan. Baki isa ba Wallahi.""" Ya katse ta da sauri yana ɗan buɗa mata idanu. """Sati biyun ma Wallahi don Baffa ya yanke ne, amma Wlh da bazan bari ba ki ƙara sati biyu ba tunda" "kin zama matata. Ni fa ba na son komai, na faɗa ma Baffa tun ɗazu amma ya ƙi cewa komai. Ke nake so," don haka ke ɗin kawai nake buƙata. Alfarmar da aka yi min ma wajen mallaka min wannan zuƙeƙiyar "yarinyar ba tare da na wahala ba ya ishe ni abin alfahari...""" """Yaya? Wai Mummy ta ce anan za mu kwana ne? Ƙarfe biyar na yamma ta wuce fa""" Ya tsinkayi muryar Karima daga can bakin ƙofa tana faɗin haka. "Da sauri Zulaikha ta miƙe tsaye tana zazzare idanu tana kallon ƙofa, a tsorace take sosai kar Karima ta" shigo taga irin zaman da Abban Imam yayi a gabanta. """Je ki ce mata ga ni nan zuwa.""" "Ya amsa yana ɗan ɓata fuska, kamar Kariman tana gabansa." "Hannu yasa ya janyo Zulaikha da ta nufi hanyar fita daga ɗakin da sauri, da yake janyowar na bazata ne," "taga-taga kamar za ta faɗi yayi saurin tareta ta faɗa jikinsa. Ko kafin tayi wani yunƙuri na ƙwacewa, yayi" "mata wata kyakkyawar runguma, kansa ya ɗan kwantar a saman ƙirjinta yana sauke ajiyar zuciya sauri- sauri." "Lokaci ɗaya jikinta ya mutu murus, bata yi wani yunƙurin ƙwacewa ba don riƙo yayi mata ba na wasa ba." "Runtse idanu tayi da ƙarfi, tana jin yadda ƙirjinta ke bugawa sauri-sauri, a tsorace take gaba ɗaya." """Ina son ki. Don Allah ba don ni ba ki kula min da kanki sosai. Kuma ko da yaushe ki zama kusa da" "wayarki. Kin ji?""" "Sosai bakinta yayi mata wani irin nauyi, sai da ƙyar ta iya ɗaga masa kai, alamar ta ji." "Wasu daƙiƙun ya sake ɓatawa yana riƙe da ita a jikinsa kafin ya sake ta a hankali, hannunta na dama ya" "kamo, ya laluba aljihun wandonsa ya ɗebo kuɗaɗen ciki gaba ɗaya ya damƙa mata." """Ko da za ki buƙaci wani abu don Allah kar ki tambayi su Baffa. Ki faɗa min a waya, zan saka a kawo" "miki duk abinda kike buƙata.""" """Tam!""" Ta faɗa a hankali. """Don Allah ka bar kuɗinka, babu abinda zan nema. Allah ya mayar da ku gida lafiya.""" """Amin Maman Imam.""" "Ya amsa da sanyin jiki, bai karɓi kuɗin ba kamar yadda ta nema, sannan kuma bai saki hannunta ba. Allah" "ya sani shi fa gaba ɗaya ji yake kamar kar ya tafi ya barta a garin, gara kawai ya tafi da matarsa, ko kuma ya zauna har zuwa sadda za a bashi matarsa." "Kamar ta san tunanin da yake yi, sai ta kalli hannayensu da ke maƙale da juna. Kafin ta mayar da kallon" "kan fuskarsa, a kunyace ta sakar masa murmushi." """Kayi haƙuri, sati biyu ne fa kacal. Kuma na maka alƙawarin in sha Allah duk sadda ka kira za ka same ni" "a waya. Ka kwantar da hankalinka, ka je, Su Mummy na jiranka.""" "Ya kasa cewa komai don tsananin sanyin da jikinsa yayi, hankalinsa a tashe. Hannunta da yake cikin nasa" "ya ɗaga yakai bakinsa, ya sumbata a hankali sannan ya fice daga cikin ɗakin da sassarfa." "Ko da ya fita, ta kasa bin bayansa don tsananin kunyar su Mummy da mutanen gida, yau dai hatta" "Karima da Yayyenta kunyar haɗa idanu da su take yi. Don haka ta cigaba da zamanta a ɗakin Baffa," "zuciyarta cike taf da tunanin mijinta. Lokaci bayan lokaci ita kaɗai sai ta saki lallausan murmushi, tana shafa bayan hannunta inda ya sumbata da tausasan laɓɓansa." """Allah na gode maka.""" "Ta faɗa a fili, zuciyarta cike da matsanancin farin cikin da baki bazai iya furta adadinshi ba." "[2/17, 10:59 PM] Fareeda Abdallah: Kamar yadda Mummy ta alƙawarta ma zuciyarta, sai da ta sake" roƙar ma Hafiz gafara a gurin Innaye da Baffa. Ta ƙara tunasar da su komai fa na duniya yana faruwa ne bisa doron ƙaddarar da aka shirya faruwarsa tun kafin muzo duniya. """Kuma idan kun duba, a yanzu komai da ya faru za mu iya cewa mafificin alkhairin da muke ta roƙa ne" "ako wane lokaci Allah ya tabbatar da faruwarsa a sauƙaƙe.""" """Haka ne Hajiya. Daman mun yafe mishi, Allah ya yafe mana gaba ɗaya.""" Baffa ya faɗa da yanayin da ke nuna tun daga ƙarƙashin zuciyarsa yayi maganar. Ita kuma Innaye cewa tayi """Daman babbar damuwa da ɓacin ran na yadda ya mayar min da ƴa ƙaramar bazawara ce, amma" "yanzu tunda Allah ya canja mata da wanda ya fi shi alkhairi komai ya wuce. Allah ya shirya mana zuri'a.""" """Amin ya rabbi.""" "Kamar haɗin baki, shi ma Alhaji Lurwanu gaf da za su bar ƙauyen ya nemi ganawa da Baffa da Innaye a" keɓance ya sake roƙar ma Hafiz gafara. """Babu komai Alhaji. Wallahi har ga Allah mun yafe masa. Allah ya yafe mana gaba ɗaya.""" Baffa da Innaye suka haɗa baki gurin amsawa. Kafin tafiyarsu sai da Hajja ta damƙa komai na gyaran jikin Zulaikha a hannun Umma Laraba da Aunty Balira. """Amana! Ga amana nan na damƙa muku. Kuma kun san dai amana maci amana maye ɗan'wuta ne inji" "yara. Ban yarda ko dai dai da rana ɗaya a tsallake yi mata gyaran nan ba, duk abinda ya ƙare kafin kwanaki sha huɗunnan ke Balira ki ranta kuɗi a siyo. Duk abinda aka kashe idan kun zo zan biya ki, ƙwandalarki baza tayi ciwon kai ba ƴar nan. Alƙawari na ɗauka.""" Maganganun da tayi ta jaddada musu kenan har suka fice daga cikin gidan zuwa gurin motocinsu. "Duk sun riga sun sani kunya ce ta hana Zulaikha fitowa suyi sallama, shi yasa babu wacce ta matsa da son" ganinta tsakanin Mummy da Hajja. Ita kuwa Karima a ɓoye ta shige ɗakin Baffa tayi ma Zulaikha tsiya son ranta kafin ta fito daga ɗakin tana ƙyalƙyala dariya. Basu bar Ƙauyen Faƙo ba sai ƙarfe shidda saura kwata na yamma. Sun rabu ne ko wane ɓangare "zukatansu cike da matsanancin farin ciki. Su Mummy basu wani tayar da hankulansu kan yamman da suka yi ba, saboda sun sani komawarsu Abuja bazai yiwu a ranar ba, in dai ba so suke suyi tafiyar dare ba, wanda sam Hajja baza ta bari ba. Sun tsara za su kwana a Kaduna, washe gari suyi sammakon wucewa" Abuja. "Shi kuwa Alhaji Lurwanu da yake yana da harkokin da zai gabatar a Kaduna, ba ma a washe garin zai" koma Abuja ba. Labarin da Hafiz ya samu na aurar da Zulaikha ga Ya Kamal ɗan gidan Mummy ba ƙaramin farin ciki ya "jefa zuciyarshi a ciki ba. Ko kaɗan ranshi bai ɓaci, domin shi daman babu soyayyar Zulaikha irinta aure ko kaɗan a zuciyarsa." Ba ma kamar da ya samu labarin yafe masa da iyayensa suka yi daga bakin Abba Lurwanu da Mummy. "Bayan uban faɗan da yasha, ƙiris ya rage ya karɓi tukwuicin mari daga gurin Abban, saboda ɓacin ran yadda irin wannan muhimmin al'amarin zai faru amma ya ɓoye masa." "Shi dai haƙuri yayi ta basu cikin ƙanƙan da kai, har zuwa sadda suka tabbatar mishi da su Baffa sun yafe" "masa, komai ya wuce, da fatan zai kiyaye gaba." Samun waɗannan daɗaɗan labarai guda biyu da bai taɓa tsammanin jin su a irin wannan lokacin ba yasa "ɗan sauran zazzaɓin da ya rage a jikinsa ƙarasa fecewa. Sai ga shi ya miƙe garas, da ƙwarin jiki yayi ma su" Mummy rakiya zuwa gurin motocinsu yana ta zabga musu godiya kamar zai ari baki. "Da yake a lokacin da suka je gidan Bintu tana asibiti, shi yasa duk bata san abinda ke faruwa ba sai da ta" koma gida ya labarta mata. "Ƙarara ɓacin rai, hassada, ƙyashi, baƙin ciki suka bayyana a fuskarta jin irin cigaba da ɗaukakar da Allah" "yayi ma Zulai a lokacin da bata taɓa tsammani ba. Ta san Mummy Saudah tun da daɗewa, Ogar Hafiz ce" "a gurin aiki, babbar macece hakima da ta tara ɗumbin abin duniya, don ma dai ba ta da girman kai ko kaɗan." "Ta kuma san Kamal, babban ɗan Mummy da ya auri Zulai, haɗaɗɗen gaye ne da ya tara dukiya mai yawa" "sanadiyyar aikinsa, kuma an mutu an bar musu gadon dukiya mai yawa." A taƙaice saboda irin alfarmomin da suke ci ta sanadiyyar Mummyn ita da Hafiz yasa sadda Karima ta gama Karatunta na aikin jinya ta shiga ta fita har sai da ta samar ma Karima gurbin aiki a asibitinsu. Yanzu shi kenan Zulai ta samu ɗaukaka? Ta faso gari kenan za ta goge duk wani ƙauyanci da jakanci haɗe da dabbanci su bar jikinta? """Taɓɗijan! Shi kam a ina ya haɗu da ita ne haka har aka haihu a ragaya?""" Ta tambayi Hafiz ɗin fuskarta babu walwala ko kaɗan. "A taƙaice, ya bata labarin irin zaman da Zulaikha tayi a gidan Mummy na tsawon watanni." A fili ta taɓe baki """Amma kuwa dai ya ji kunya, ya kuma yi faɗuwar baƙar tasa. Ace duk wayewa da gayu haɗe da aji irin" tasa ya rasa yarinyar da zai aura sai ƴar ƙauyen ƙayau kuma jahila daƙiƙiya irin Zulai. Gaskiya ya ci "baya...""" """Me kike nufi kenan Bintu?""" Hafiz ya tambayeta da ɓacin ran da ya bayyana a fuskarsa tun da ta fara maganganun da ke nuna baƙin cikinta ƙarara. """Me nake nufi kuwa Dear? Kawai dai abinda ke raina na faɗa, kai ma kuma kasan ai gaskiya ne.""" Fuuu ta miƙe tsaye ta ɗauki jakarta za ta wuce sama. Da saurin gaske ya janyo ta ya dawo da ita baya sannan ya danƙwafar da ita akan kujera. """Kar ki manta, abinda yayi Zulan da kike kira baƙauyiya, jahila kuma daƙiƙiya shi yayi ni Hafiz da kike" "aure. Domin ita ɗin Ƙanwata ce, jininmu ɗaya, ƙauyenmu ɗaya, ashe ke ma baya kika ci da kike aure na?""" """A'a da banbanci fa My dear... banbanci mai nisan gaske ma. Kai ai ka daɗe da shigowa birni, ka waye," kuma ka yi zuzzurfan ilimin boko. Idan ma ba ka faɗa ba babu wanda zai kalleka yace kana da jiɓi da "wasu ƙauyawa can... Amma dai duk inda ka nufa ni ba haka nake nufi ba, idan ka ji haushi Allah ya baka haƙuri.""" "A karo na biyu ta sake ɗaukar jakarta da nufin wucewa sama, ba tare da ta yarda ko fuskarsa ta kalla ba." Domin Allah ya sani labarin irin cigaban da ya sami Zulaikha ba ƙaramin baƙanta mata rai yayi ba. Ta zaci "zai sake dakatar da ita a karo na biyu, sai taji bai janyo ta ba har ta fara haurawa matattakala." Shi kuwa Hafiz tsananin mamaki da girgizar da kalamanta suka jefa shi a ciki ne yasa ya kasa sake ce "mata komai, har ta ɓace ma ganinsa. Duk da farin sanin da yayi ma halayen Bintu na son harkar wayewa" "da birnanci da nuna ilimi, abu ne da bai taɓa tsammani ba ta iya tsayawa a gabansa ƙeƙe da ƙeƙe ta faɗi" munanan kalamai irin haka akan ɗaya daga cikin ƴan ƙauyensu ma ba Zulai da ta kasance jininsa ba. "Ya daɗe zaune a gurin maganganunta suna wujijjiga shi, zuciya da mugun saƙe-saƙe sai ga shi cikin" "ƙanƙanin lokaci ta fara shigo mishi da wasu irin tunanika mabanbanta da juna. Duk yadda yaso yayi watsi da tunanikan da yake yi, ya kasa, a dole suka samu matsuguni a zuciyarsa suka yi darshe-darshe, ya cigaba da ɓata lokaci a gurin yana sake raba ɗaya biyu a kalaman Bintu." "Daga ƙarshe dai, tattara tunanin komai yayi ya aje gefe ɗaya. Ya miƙe tsaye, har ya nufi hanyar da zai" "sada shi da ɗakunan barcinsu sai kuma ya canja shawara, yana ji a ransa in dai ya haura sama suka yi ido biyu da Bintu tabbas zai cigaba da tuhumarta kan kalaman da ta faɗa masa ne. Shi kuma a halayensa ba mutum bane mai yawan mita da son maimaita magana ɗaya. makullin motarsa da yake ajiye nan kusa da shi ya ɗauka ya fice daga falon." ***** ***** "A cikin kwanaki goma sha biyu da suka biyo baya, Baffa ya sa an gama shirya ma Zulaikha ɗakunanta da" "ke ɓangaren Kamal da kayayyaki na gani a faɗa cikin rufin asiri. Duk kuwa da yadda Abban Imam ɗin yace baya buƙatar komai, sam-sam Baffa ya ƙi yarda da haka. Kuma wani abin sha'awa da burgewa shi ne kayayyaki kalar ƴan birni aka zuba mata, dai-dai ruwa dai-dai tsaki." "Wani kyawun hange da Baffa yayi shi ne, bai tura ƴaƴansa Kaduna suyi siyayya ba don gudun kar a sayi" "abinda bazai dace da ɗakunan Zulai a Abuja ba. Alfarmar Abba Lurwanu ya nema, ya tura mishi da kuɗi naira na gugan naira har miliyan ɗaya da cewa matar Abba ta shiga kasuwa ta sayi duk abinda ya dace, Duk da Abban yayi-yayi Baffa yabar kuɗinsa shi zai ma Zulai komai na kayan ɗaki matsayinsa shi ma na" "uba, amma Baffa ya ce yayi haƙuri, ɗawainiyar da yake da ɓangaren Hafizu da su iyayensa ma ya isa haka." Ko da Hafiz ya samu labarin halin da ake ciki hankalinsa a tashe ya kira Baffa. Domin a saninsa tun da ya "fara aiki shi ke da alhakin yima ko wacce daga cikin ƙannenshi kayan ɗaki, kuma ko Zulai in banda Allah baiyi aurenta da Mudan ba a wancan lokacin har kuɗin kayan ɗakinta ya biya, fasa auren da aka yi ne yasa shi karɓan kuɗinsa." Ko da ya gama roƙon Baffa cikin ƙanƙan da kai da taushin murya kan a barshi ya ɗauki ragamar shirya mata ɗaki kamar sauran ƴan'uwansa ƙarara Baffa ya faɗa mishi ya fi so yayi ma Zulai komai da guminsa. """Ba kuma don wai na raina ƙoƙarinka bane Hafizu, ko kuma wai don har yanzu ina jin haushin abinda" "kayi, a'a! Ko ɗaya ba haka bane.""" Baffa ya ƙara da faɗa mishi haka don kwantar masa da hankali. Ɗan shiru yayi yana jin babu daɗi a zuciyarsa. Sai kuma ya ce """To Baffa don Allah a barni in ɗauki ragamar yi mata gara, tunda dai hidindimun da yawa. Don Allah" "Baffa.""" Kamar Baffa zai ce a'a! Sai kuma ya ce ba damuwa. Yana iya yin ɗan daidai misali ba na ƙarya ba. "Sai dai abinda Baffa bai sani ba shi ne, kuɗin da ya bayar na kayan ɗakin da za'a siya mata kaso ɗaya ne" "bisa uku na abinda aka kashe. Abba Lurwanu ne ya cika kuɗin, matansa suka shiga kasuwa aka yi mata siyayyar kaya masu kyau." Bayan an kai kayan gidanta kuma washe gari suka je da manyan ƴaƴansu mata aka ƙarasa shirya mata gidanta. Yayi kyau sosai. "Duk da Baffa ya gargaɗi Hafizu kan kayan gara bai ji ba, kuɗi ya kashe sosai duk don dai ya fanshe" takaicin kayan ɗakin da bai mata ba. "Ana jibi biki, su Aunty Balira suka yi shatar mota aka loda musu cincin, dubulan, alkaki, nakiya, manshanu," da sauran ƙananun tarkace daga Innaye suka tafi da shi gidan Zulai. "Tarba ta mutunci da girmamawa suka samu daga Mummy da mutanenta. Zukatansu cike da farin ciki," "sun ci, sun sha, sun yi nak da ƙayataccen abinci na girma. Haka suka dinga santin ɓangaren Zulai da kayan da aka zuba mata." Kayan ciye-ciyen da suka je da su daman tun daga Faƙo Innaye ta sa an raba komai kashi huɗu ne. Biyu "na Mummy, ɗaya na Zulai, ɗaya na Hajja. Haka su Mummy suka karɓi kayan suna murna, zuciyarsu da" "fuskarsu ɗauke da bayyanannen farin ciki, kamar anyi musu kyautar duniya. Sha tara ta arziki aka haɗa sake haɗa ma su Aunty Balira a matsayin tukeuici suka juya da shi." "Washe gari kuma ana gobe tarewa Mummy ta haɗa manyan mata guda shida, danginta biyu, dangin" "Abban Imamu biyu, ƙawayenta biyu, suka hau jirgi zuwa Kaduna, daga can suka ɗauki mota da haɗaɗɗun" "akwatunan lefe guda shida zuwa Faƙo, shaƙe da haɗaɗɗun kayayyaki." "A ɓangaren su Innaye ma sunyi musu tarba daidai ƙarfinsu, haka aka rabu zukatan ko wane ɓangare da" "farin ciki, babu raini ko wulaƙanci balle kallon banza daga mutanen Mummy har suka bar Faƙo. Farin" cikin wannan kaɗai ya ishi Innaye da sauran dangi. """Wani hanin ga Allah baiwa ne. Ke kam Zulai kin dace da miji da iyayensa, Allah ya bada zaman lafiya" "da zuri'a ɗayyiba.""" Ire-iren maganganun da ke fita daga bakunan ƴan'uwa da abokan arziki kenan. "Tun ana gobe biki, gidan Baffa yake danƙam da mata, sai sauke girke-girke ake yi ana ɗora wasu" tukwanen. Washe gari kuwa tun ƙarfe goma na safe manyan motocin ɗaukar amarya da danginta har motoci takwas suka faka a ƙofar gidan Baffa. "Kuma basu takura kowa ba, domin umarni ne daga Abban Imam, har zuwa ƙarfe uku na rana kafin aka" gama shirya amarya da ƴan rakiyarta suka kama hanyar tafiya Abuja. "[4/2, 6:12 AM] Fareeda Abdallah: ******" "Cikin ƙanƙanin lokaci nan da nan sai gasu a cikin Abuja, wajen karfe shida da rabi na yamma. Tafiyar da" ko kaɗan Amarya da tagawarta basu ga nisan ta ba. "Fuskar Amarya wasai, sai ƴan ƙananun ƙwallan da tayi na sake rabuwa da su Innaye a karo na biyu." "Amma babu irin kururuwar nan ko ƙuncin zuciya mai bayyana ƙarara auren dole aka mata, tana cikin farin cikin albarkar da su Baffa sukai ta sa mata. A gefe da gefenta kuma ga Yayyunta da za su raka ta har ɗakin mijinta. Bayan sun iso kai tsaye gidan Mummy Sauda aka wuce da ita, kamar yadda aka tsara sai" an gama duk bukukuwan a gidan sannan za a wuce da ita gidan mijinta. A wannan sha'anin ne su Aunty Rakiya suka ƙara tabbatar da lallai fa ƴan birni masu kuɗin ma suna suka "tara, ba ko wasu masu arziki ne masu wulaƙanta ƴan ƙauye irin Bintu ba." "A bikin Zulai, kwanaki biyun da suka yi a Abuja gidan Mummy komai za'ayi ana saka su gaba-gaba" matsayinsu na dangin Amarya. Duk wani shagali da aka yi sai da aka kai su gurin kuma a masauki na musamman. "A taiƙaice dai, an girmama su iya girmamawa. Wani abin mamaki shi ne har aka gama bikinnan na kwana" "biyu Bintu ko leƙe bata yi ba, tana can gida ta ɗora ma kanta ciwon ƙarya har da su ƙarin ruwa don kawai kar Hafiz ya ƙullace ta." "Shi kaɗai yayi ta zirga-zirgan zuwa gurin ƴan'uwansa. Ko da ya faɗa musu Bintu ba lafiya, fatan samun" sauƙi kaɗai suka yi mata suka shashantar da maganar. "Wani abu da ya sosa zuciyar Hafiz amma ya danne bai musu ƙorafi ba shi ne, yadda ganin yawan" waɗanda suka zo bikin daga can ƙauye yasa shi suɓutar bakin yi musu tayin ya rage wasu suje gidanshi su kwana. """Wa? Mu? Allah suturi buƙwui... Ai gidan Bintu shi ne ramin kura sai ƴaƴanta... Idan ka ganmu lahira" "kaimu aka yi Hafizu. Ai ko sha'ani ake yi a gidanka mun daina zuwa mu kwana Hafizu.""" Ire-iren maganganun da ƴan'uwansa sukai ta yaɓa mishi kenan. """Uhmmm! Hafizu kenan. Ai kai da kanka ka ture wannan damar da aka miƙa maka na zuwan ƴan'uwa" "gidanka su sake. Ban san dai ko can gaba ba, amma a yanzu ko sha'ani ake a gidanka sai dai muyi maka" "fatan alheri ta waya, babu wacce za tayi gigin zuwa balle har ta ƙunshi takaici da baƙincikin da ba shi" "kenan ba.""" Cewar Aunty Balira. """Yo wai ko da ka ganmu da yawa aka ce maka muna takure ne anan ɗin? Ai surukan Zulai sai dai muyi" "musu fatan alkhairi, wadataccen gurin kwanciya suka samar mana da wadataccen abinci, kai baka ga har wani kumari muka ƙara a cikin kwana guda da zuwanmu ba? Mun gode Allah a yanzu ba kai kaɗai bane a binni, ga gidan Zulai nan, na san ko za mu zo muzo gobe jibi mu sake zuwa baza ta taɓa gajiya da mu ba." "Ai ranar naka sai naka.""" Aunty Rakiya ta yaɓa mishi maganganun. Haka ya fice daga gidan zuciya cike da ƙunci amma ba shi da halin tofawa balle har cibi ya zama ƙari. Sai kuma a wannan lokacin ne ya fara tunanin to ko dai Bintu tayi ma ƴan'uwanshi wani wulaƙanci ne lokacin sunan Aadil? Idan ba haka ba waɗannan baƙaƙen maganganun duk na menene? A ganinsa guje ma auren Zulai kaɗai bazai sa su dinga nuna tsangwamar zuwa gidanshi ƙarara haka ba. "Su dai ko a jikinsu, bayan fitarsa ma walwala da warwasawarsu suka cigaba da yi." Washe gari da wuri Mummy tasa Hibba ta sake tsantsara ma Amarya rantsattsiyar kwalliya aka ɗauketa da danginta sai gidan mijinta da ke unguwar Aso rock. Ƴan'uwanta sai hangame baki suke yi cikin tsananin ƙauyanci da mamaki suna ƙarewa gidan kallo. Tun daga farkon unguwar za'a gane ba ta ƙananun masu kuɗi bane. Tsarin gidan na musamman ne. Madaidaici ne zaman mace ɗaya da iyalanta da tarkacen da ba za a rasa ba. "Ya so ƙwarai ya sake zama acan ɓangarenshi da ke gidan Mummy, kamar yadda suka zauna da" marigayiya matarsa. Amma shi kanshi ya rasa dalilin da yasa Mummy ta ce su zauna a sabon gidan nashi "da ba'a daɗe da kammala komai ba. Sai dai can ɗin ma yana nan a matsayin nashi, an ƙara gyarawa an" "zuba sabbin kayayyaki, da yake shi ɗin mai yawan tafiye-tafiye ne sai Mummy ta ce idan zaiyi tafiya Zulai" za ta dinga komawa can gidan tana zama kafin ya dawo ƙasar. "Tsarin gidan Amarya Zulai idan aka shiga falo babba za a fara tararwa, wanda aka tsara shi da tsadaddun" "funitures, daga can jikin bango kuma wata ƙatuwar TV stand ce wadda ita ginata ma aka yi kuma aka kafe wata ƙatuwar TV plasma dake barazanar cinye bangon saboda girma. A gefe da gefe kuma ga wasu" tsadaddun show glass waɗanda aka ƙawata cikinsu da kayan ado da hasken wuta mai sheƙi. "Acan wani ɓangare na falon kicin yake, inda aka ɓata basira wajen zuba duk wani abu da ƴa mace za ta" "buƙata a cikin madafin gidanta, na gargajiya da na zamani. Abin sha'awar kuma shi ne komai an killaceshi" wajen da ya dace. Store ɗin ta shaƙe yake da kayan gara wanda "Hafiz ya siya kamar bai san zafin kuɗi ba, nan ma dai babu ce kawai babu a cikin kayan abincin." Daga can wani ɓangare na falon kuma ɗakunan baƙi ne guda biyu da bayi a cikin ko wane ɗaki. Can gefe guda kuma matakala ce da za'a haura sama inda ƙaramin falo da ɗakunan mazauna gidan suke. "Dakin Zulai daban, shi ma ya sha jerenshi, na Abban Imam yana kallon nata, duk da a rufe yake amma" shima a gyare yake tsaf. Idan ka matsa gaba kaɗan kuma zaka tarar da ɗakunan yara na maza daban na mata daban. "Gida kam ya haɗu iya haɗuwa, sai dai fatan Allah Ya ba mazauna cikinshi zaman lafiya da zuriya masu" albarka. "Bayan tawagar amarya sun gam kallon gida sun huta, suka yi watanda da soyayiyar shinkafa da ta ji" "soyayyen nama da ganyayyaki, ga soyayyar agada da coleslaw, suka kuma ɗora da kalolin lemuka mabanbanta." "Sai da aka yi la'asar sannan Mummy ta kira Aunty Balira ta sanar da ita su yi ma Amarya sallama, za a" "mayar da su gidanta su kwana, washe gari kuma da sassafe za'a mayar da su Faƙo." "Da jin wannan maganar nan da nan sai idanun Zulaikha suka fara kawo ruwa, tsakaninta da Allah ita duk" tunaninta anan ƴan'uwanta za su kwana. Ta kalli Karima cikin marairaicewar fuska ta ce """Ayya mana Aunty Karima don Allah ki sa baki su zauna anan mana su kwana? Kin ga fa har yanzu" "bamu gama sallama da su Aunty Balira ba.""" Karimah ta kama baki tana dariya ƙasa-ƙasa tace """Lallai ma yarinyar nan, daman wa ya faɗa miki ana gama sallama da dangi? Ai auren kenan. Ko so kike" Yaya ya ci ƙaniyata da yammacinnan? To wallahi ba dani ba aikata wannan ɗanyen aiki. Ke baki lura da yadda tun ɗazu mijinki yake ta auno min kira yana tambayar baƙi sun tafi? Kina tunanin idan ya zo ya samu gidannan da mutane zai saurara min ne? Bayan haka kuma dai umarnin Mummy ne a dole za kiyi "haƙuri.""" "Shigar Aunty Balira cikin ɗakin yasa dole suka bar maganar, Karima ta fice daga cikin ɗakin tana yima" Zuly dariya ganin yadda ta kwaɓe fuska ta cigaba da matsar ƙwallah. "Kusa da ita Aunty Balira ta zauna, itama da fara'a sosai a fuskarta ta fara raira ma Amarya waƙar ke kika" "ce kina so, da baki ce kina so ba da ba'a baki shi ba. Duk yadda Zulai ta kai ga ɓata fuska bata san sa'adda" ta fara ƙyalƙyala dariya ba. Ganin ta saki fuskar yasa Aunty Balira amfani da wannan damar ta ƙara yi mata nasiha mai Nasiha mai shiga jiki. "Daga bisani ta ɓuge da bata sirruka da kissosin kama miji a tafin hannu irin nasu na mutanen ƙauye," "amma fa kamu wanda zai ƙara kwantar da mace a cikin zuciyar mijinta, babu boka balle Malam. Zulai har" mamakinta ta dinga ji. Anty Balira ta kalleta da dariya ta cigaba da cewa """Haba yarinya! Don kina ganinmu a ƙauye kuma sai aka ce miki kan duk dusa ne? Mun fa san yadda" "zamu bi da mazajenmu, dai-dai gwargwado ba na tunanin ko wata ƴar birnin za ta iya kamoni ta wannan fannin. Ke dai ki riƙe abinda na faɗa miki za kiga aiki da cikawa.""" "Ana haka su Aunty Rakiya da Ladidi suka shigo, a gurguje suka yi nasu nasihar sannan sauran waɗanda" suka rakota duk suka shigo suka mata sallama. Har bakin ƙofa ta raka su sannan ta rungume Yayunta cike da kewa tana kuka su kuma suna aikin lallashi. A haka dai har suka lallabata ta koma cikin gida ita da Karima su kuma suka shige motoci suka tafi. Duk yadda su Aunty Balira suka gyara gidan saboda ɓata shi da abinci da ƴan'uwansu suka yi. Suna tafiya "Mummy ta tura masu aiki suka sake ƙalƙale gidan, aka kunna turaren wuta a lungu da saƙo na gidan." "Hibbah da isarta gidan kenan ta sa Zuly ta sake yin wanka, sannan ta suka taimaka mata ta shirya cikin" "tsadaddiyar lafaya mare nauyi, tayi mata sassauƙar kwalliya." Daga cewa za su zagaya cikin gidan su ga yanayin kwalliyar fulawoyin tsakar gidan sai jin tashin motar Hibba tayi. Ko kafin Zulai ta sauka ƙasa ta leƙa har mai gadi ya buɗe musu get sun fita. "Haka ta tsaya a tsakiyar falon ƙasa jikinta a sanyaye. Ko da ta ɗaga wayarta ta kira Aunty Karima, wayar" har ta ƙaraci ringing ɗin ta bata ɗaga ba daga can ɓangaren. "Sai bayan kiran ya tsinke ta turo mata da gajeren saƙo cewa tayi haƙuri ta bi Hibbah sun wuce gida," amma gobe da safe tana nan tafe. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tana jinjina kai bayan ta gama karanta saƙon. Duk da fargaba da tsoron "da ke danƙare da zuciyarta bai hana ta ƙare ma falon da yake matsayin mallakinta kallo ba. Duk da falon bai kamo na gidan Hafiz tarkace da kayan ƙawa ba, amma fa daga kallon farko ta san ya kere na Hafiz aji" da kashe naira kamar ba'a san zafinsu ba. "Ta lallaɓa cikin sanyin jiki ta koma ɗakinta, ta lalubi bakin gado ta zauna tana ta aikin sauke ajiyar zuciya" "jefi-jefi, zuciyarta cike fal da tunanin yadda ranar zai kasance tsakaninta da Angonta." "Babu jimawa kuma taji dirin mota a waje, kafin ta ji an shigo cikin falon gidan. Kafin ta ankare ta yi wani" "abu, an turo ƙofar ɗakinta an shigo, bakinshi ɗauke da siririyar sallama cikin nutsuwa da tausasa murya." "Kamar wacce aka kullewa baki, ta kasa amsa sallamarsa. Sai ɗaga kai da tayi a hankali tana kallonsa," bugun zuciyarta yana ƙaruwa sannu a hankali kamar ana luguden daka. Farar shadda ce a jikinshi kar da "ita, ta sha ɗinkin hannu irin na gidan sarauta da zare kalar brown mai cizawa, hular kanshi sai ya sanya brown wadda ta hau da takalmin kafarshi sau ciki." "Wani kwantaccen murmushi mai matukar daukar hankali ne akan fuskarshi, da ba don yadda cikinta" "yake cunkushewa da fargaba ba, a gefe guda ga wata irin matsananciyar kunya da ta rufe ta, da baki za ta buɗe tayi ta yabon kyawun da yayi a idanunta. Don kuwa yayi kyau sosai da sosai, ya fito a Ango ɗanye sharaf!" Ya ƙarasa shiga cikin ɗakin tare da maida ƙofar ya rufe. Rufewar da yayi daidai da ƙara saurin bugun zuciyarta. Tsoronta ya sake ninkuwa. "Shi kuwa ko a jikinshi, duk da ya kula da yadda take ta wani mutsu-mutsutu akan gadon kamar mai jin" fitsari. "A hankali da wani irin taku na ƙasaita ya ƙarasa jikin gefen gadon, inda aka ajiye ɗan ƙaramin teburi," ledar dake hannunshi ya ajiye akai. Sai kuma ya hau kici-kicin cire babbar rigarshi yana kallonta murmushin fuskarshi yana ƙara faɗaɗa. """Manya-manya maganin ƙananan ƙwari. Hajiya Zulaikha amarya a gidan bawan Allah Kamaluddeen!" "Iye!! Irin wannan kyawu Ummu Imam anya ba zaki sa ɗan Mommy ya ƙarasa haukacewa a kanki ba?""" "Kalamanshi suka bata kunya matuƙa, har ta kai ga sanya hannu tana kare fuskarta, a ɓoye take sakin" wani lallausar murmushi tsigar jikinta na tashi. "A gefenta ya ajiye rigar, ya zauna a kusa da ita har jikinshi yana gogar nata, kamshin turaren da" "jikkunansu ya cakuɗe ya haɗe waje ɗaya, ya bayar da wani irin daɗi mai matuƙar sanyaya zuciya. Ba ma" kamar daddaɗan ƙamshin da Zulai din take yi na haɗaɗɗiyar humra ta amare da Anty Hibba tayi mata amfani da shi. Cikin ƙanƙanin lokaci Kamal ya ji kamshin yana neman ya sanyashi fita a hayyacinshi. Ƙoƙarin zamewa Zulaikha take yi saboda kusancin da suka yi da juna yayi yawa. "Fahimtar abinda take ƙoƙarin yi yasa shi yin caraf ya kamo ruwan cikinta, sannu a hankali da wani irin" salo ya ja ta cikin jikinshi yana sauke numfashi sannu a hankali. Lokaci ɗaya Zulaikha ta hau kifkifta idanu kamar wacce tayi ma sarki ƙarya. Jin baƙon lamari a tattare da "ita yasa ta faɗawa cikin matukar kidime, tsoro da fargaba ya sake lulluɓeta." "Lura da halin da ta shiga yasa shi kama hannuwanta ya rike ƙam a cikin nashi, cikin taushin murya mai" "nuna kulawa da son amintar da ita yake mata magana, ƙamshin Listerine yana fita daga bakinshi yana" "bugun fuskarta, lokaci ɗaya yana aikawa sassan jikinta wasu irin saƙonni da suka sanya taji jikinta ya fara" rawa sannu a hankali. """A'a fa! Kar muyi haka dake ba Babyna. Kina sane da alƙawarin da muka yiwa juna ko? Ko in tuna miki?" "Da bakinki kika yi ta jaddada min za mu gudanar da rayuwar gidanmu babu kunya, babu tsoro, kuma shakka sai girmamawa da so da kaunar juna. Ya aka yi kuma tun a yanzu zaki sage min gwiwa Ammata?""" "Tayi shiru ta kasa magana. Ya kai hannu ya daga fuskarta yadda zata kalleshi da kyau, amma ta kasa haɗa" idanu da shi sam. A maimakon ta kalleshi ma sai ta lumshe idanunta. """Uhmmm! Ko dai don ban sayi bakin amaryar tawa bane take sha min ƙamshi? Kiyi hakuri to! zakwaɗi" da zumuɗin zuwa inyi tozali da kyakkyawar fuskarki ni kaɗai ƙwal ya sanyani hana masu sayen bakin "zuwa, don nasan lokaci za su ɓata min. Amma a min uzuri, in Sha Allah gobe za a sayi bakinnan da abu mafi daraja! Kin ji?""" "Ɗan murmushi tayi kawai, har lokacin idanunta na lumshe. Sai ta hau girgiza mishi kai alamun ba haka" bane fa. """To menene?""" Ya jefa mata tambayar bayan ya fahimci manufarta. Kafin ta amsa ya sake cewa """Ko rowar daddaɗan muryar ake min ni marayan Allah?""" Yadda yayi maganar yana lanƙwasa kai gefe guda sai ya bata dariya. Ta sake yin murmushi tana kara girgiza mishi kai a nutse. """Talk to me pls Baby! Tun dazu babu abinda nake ta son gani da ji kamar ke da kuma muryarki. Me" "yasa zaki hanani jin muryarki a yanzu?""" Ya ƙarasa maganar a marairaice kamar zai saka ihu. "Ganin yadda ya matsa yasa dole ta buɗe baki kamar mai tsoron magana, don taga alamun bashi da niyar" barinta ta sarara matuƙar bata buɗe baki ya ji muryarta ba. """Yi haƙuri Abban Imamuna. Ina yini?""" Yayi murmushi sosai har hakoranshi suka bayyana """Yauwa! Good girl. To ko ke fa amaryata? To ya amarcin? Ya hanya? Ya kuma kika baro su Innaye?""" "A hankali da dabaru ya fara janta da hirarraki, tun tana amsawa a ɗarare har ta saki jiki da shi. Daga" "ƙarshe ya miƙar da ita, suka fara takawa sannu a hankali gwanin ban sha'awa har zuwa ƙaton bayin dake" manne a dakin. "Alwala suka ɗauro, ya ja su suka yi sallar nafila raka'a biyu. Bayan yayi sallama ya dafa kanta yayi addu'a" "sosai da sosai, yayi mata tambayoyi kan addininta tana amsa mishi da gwargwadon sanin da take da shi." Ya sha mamaki ƙwarai jin irin sanin da take da shi a addinance duba da inda ta rayu. A fili ya dinga shi mata albarka yana godewa Allah da ya mallaka mishi ita matsayin matarsa. Shi da kanshi ya zare mata hijabin jikinta sannan ya ce """Kiyi shirin kwanciya Beb, ina zuwa.""" Ledar da ya shiga da ita cikin ɗakin ya ɗauka ya fice da ita. "Zaman minti biyu ta ƙara a gurin bayan fitarsa, babu abinda ƙirjinta ke yi face dakan lugude. Amma" tunawa da karin maganar da take cewa duk wayon amarya sai an sha manta yasa ta miƙe a hankali ta nufi wardrobe din ta ta buɗe. "Kafin tafiyar Karimah duk ta nuna mata yanayin yadda tsarin shirin kayayyakinta suke, shi yasa bata sha" wahalar gano ɓangaren kayan barci ba. "Dai-dai gwargwado tana da iliminta na addini, na fannin rayuwa ma da zamantakewa tana da su" "gwargwado. Ta san tana son mijinta kamar yadda shi ma yake sonta, don haka tayi ɗamarar kula da shi" da sauke duk wani nauyi na shi da ke kanta in dai ba tana son ta wayi gari taga wata mai zafin naman ta yi wuff da shi bane. A hankali take ɗaɗɗaga tarin kayan barcin da aka zube mata tana dubawa har Allah Ya hadata da wata "doguwar riga mai gajeren hannu ruwan madara. Ta dauka ta sanya, ta ƙara feshe jikinta da turare." "Da ta tsaya gaban mirror taga yadda rigar tayi mata kyau ta kuma kamata, sai taji ba zata iya tsayawa" gabanshi a haka ba musamman a daren yau. Don haka ta ɗauki madaidaiciyar hijabi ta dora akai wadda ta tsaya mata a ruwan ciki. Tana cikin saka hijabin sai gashi ya shiga dakin saye da pyjamas na barci masu budadden kirji. Hannunshi rike da babban tray. "Tayi duru-duru tana kokarin hana idanunta kallonshi, kafin kuma ta yunkura da nufin karbar farantin" "hannun nashi, yayi gaggawar dakatar da ita. Ya ajiye farantin a tsakiyar daki, ya zauna yana linke kafafunshi tare da kama hannunta ya kara zaunar da ita kusa dashi kugu da kugu." """Yau ke amarya kike fil! Oya, zo in ciyar da ke in kuma shayar da ke madara.""" "Haka nan tana noƙewa da sussunne kai, ya dinga yankar wani lafiyayyen gashin nama yana bata a baki," gefe guda kuma ga tatacciyar madarar yoghurt mai masifar daɗi yana bata. Sai da ya tabbatar ta koshi sannan shi ma ya ci yayi nak! "Ko da ya tashi da niyar dauke kayan wannan karon hana shi tayi, ta daukesu ta kai kicin. Sauran naman" "ta nade a foil paper ta sanya a cikin firjin, kayan da suka ɓata kuma ta daurayesu ta jingine a jikin rag." "Ta tunkari hanyar dakinta zuciyarta na bugu, jiki na mazari. Da ta je jikin kofar ta jima tana kokonton" "budewa, har sai da ta jiyo muryarshi daga cikin dakin yana cewa" """Wai dodo ne a cikin dakin da ba zaki shigo ba Umman Imam? Ko dai so kike in bar miki ɗakinki in" "koma nawa?""" Kamar kazar da ƙwai ya fashe ma a ciki ta buɗe ɗakin ta shiga. Sai ta gan shi har ya kwanta yana danna waya. "Shigowarta cikin ɗakin ne yasa shi ajiye wayar, ya juya yana kallonta yana mata wani murmushi kasa-" kasa. """Zo kiji wani labari mai daɗin gaske.""" Tayi duru-duru tana kallonshi duk a daburce. Bakinta na rawa ta ce """Uhmmm... dama... bari in wanke bakina""" Ya gyaɗa kai """Ok! je ki wanke ki dawo. Ina nan ina jiranki""" Ta fada banɗakin a sukwane ta rufe kamar wacce wani abin tsoro ya biy. Shi kuwa me zayyi in ba dariya ba. "Yana kallonta ta dinga shige da fice tsakanin bandakin da dakin, babu wani takamaimai abinda take yi" kuma sai zirga-zirgar. "Da dai yaga abin nata ba na karewa ba ne, sai ya tashi da kanshi yayi caraf da ita tana fitowa daga bayin" sai ganin mutum tayi a gabanta ya riƙo ƙugunta da sauri. Ya cakumo wuyan hijabinta da hannu ɗaya lokaci guda ya ƙarasa haɗe ta da jikinshi. "Wata irin ajiyar zuciya mai nauyi ya saki sannan ya fara kokarin zame mata hijabin, suka hau kici-kici," yana ƙoƙarin cire mata ita kuma tana hana shi. Murya can ƙasa ta yadda take jin shi ƙasa-ƙasa ya ce """Don Allah don Annabi kada kiyi min iyaka da abinda Allah Ya halatta min. Nasan kin fini sanin" "hukuncin hakan, kiyi haƙuri. Nayi tunanin mun gama magana akan kunyar nan? Don gaskiya wahalar da" "ke kawai zata yi, ni dai babu ruwana. Ba zan taɓa yarda kunyar nan ta dinga shiga hakkina ba!""" Yana maganganun a lokaci ɗaya kuma yana cusa hannunsa ɗaya a cikin rigarta. Bayan nasarar cire mata hijabin da yayi har ya fara ɓalle maɓallan gaban rigarta. "Zulaikha dai kunya ta gama rufe ta, ji take ina ma kasa za ta tsage ta shige ciki don kunya. Kamal dai ko a" "jikinsa, a ƙarshe ma cusa kanshi yayi tsakankanin kirjinta yana sakin wani irin numfashi mai nauyi. Duk" yadda taso ta hana wata nannauyar ajiyar zuciya da ta taso mata kasawa tayi. Ya saki murmushi a tausashe jin ajiyar zuciyar da ta saki. Lokaci ɗaya kuma ya cigaba da kokarin cakuda mata lissafi a matsayinta na sabon shiga a wannan harkar. Tsananin kamshin da ko'ina na jikinta yake yi da taushin fatarta da wani irin yanayi da ya ziyarceshi irin "wanda zai iya rantsewa bai taɓa shiga cikin makamancinshi ba, ya taimaka kwarai wajen fitar da shi daga dan sauran hayyacin da ya rage mishi a jiki." Ya manta yaushe ne karshe da ya jingina jikinshi da wata mace da sunan romanciyya. Labaran da ya fara bata sun fi karfin tunani da jikinta baki daya. "Musamman da yayi nasarar danganata da gado. Sai idanunta suka raina fata, ta fara kokarin yakiceshi da" ƙarfin tsiya jiki na rawa hawaye na kwarara a idanunta. "A rikice yake, gani yake kamar kokarin raba shi da ruhinshi take yi. Da dukkan ƙarfinsa ya kara mannata" da jikinshi har yana wasu ƴan ƙananun shessheƙar kuka. Tsakanin su biyun ya rasa jikin wanne yafi na wani kaɗawa. Murya cike da ƙauna da matsananciyar soyayya yake rallashinta da daɗaɗan kalamai """Ki taimake ni Zuly ta, taimakeni don Allah kiyi hakuri.... It has been so long...!""" "Duk yadda ta daure kamar yadda ya ce ba ƙaramar wahala ta sha ba, a jigace ta cigaba da sauraren" "labaran da yake bata daki-daki, cikin rawar jiki da fitar hayyaci." "Sai dai zuwa lokacin da ya samu nutsuwa, tuni ta gama yin wujiga-wujiga ta fita haiyacinta." Ya haɗeta da jikinshi yana jin kamar ya tsaga kirjinshi ya sanyata a ciki don tsananin so da ƙaunar da yake "mata. Sai kuma ya ɗago fuskarta ya fara share mata hawaye da tarin zufan da tayi, duk da sanyin AC da ya wadaci ɗakin." ****** "Tunda suka yi sallar asubahi, ya haɗa mata tea mai kauri ta sha, sannan ya bata paracetamol da" "ibuprofen ta sha saboda zazzabi da ta kwana da shi, suka koma barci." Janta yayi cikin jikinshi ya rungumeta tsam! Duk da tabbacin cewa babu abinda zai mata da ya dinga faɗa "mata, bata natsu ba sai da taji yayi barci da gaske. Sannan itama ta saki jikinta sosai ta yi barci." "Wajen karfe tara na safe ta farka, ta ji dama sosai akan azaban raɗaɗin da take ji a jikinta da kuma" zazzaɓin da yake damunta. A hankali ta fara ƙoƙarin zare kafafunta daga na Kamal da ya haɗe su da nashi ya makalkaleta. Kafin ta gama zame jikin ta daga nashi ta ji ya sake janta ya rike ƙam! Murya cike da barci yake tambayarta """Ina zuwa da wannan farar safiyar?""" "Agogon da ke jikin gadon ta sake kalla, da shaƙaƙƙiyar murya ta ce" """Karfe tara ta gota fa. Ya kamata mu tashi haka nan. Kuma ina son ɗora mana abinda zamu yi karin" "kumallo da shi ne.""" A hankali ya girgiza mata kai. """Kar ki damu. Na san daga gidan Mommy za ta bada a kawo mana abinci. Don haka zo mu koma barci" "ni bai ishe ni ba.""" Murmushi ta saki tana kallon fuskarsa da har lokacin bai buɗe idanunsa ba. A tausashe ta ce """Ai kuwa sai dai kai ka cigaba da barcin, amma ni dai na gama. Na gaji da kwanciya. Wanka nake son" "yi.""" Ta gangara ta zame daga jikinshi ta dira daga kan gadon tana mishi dariyar yadda yaso ya sake damkota ta zulle. Sai a lokacin ya buɗe idanunsa gaba ɗaya yana kallonta da murmushi kaɗan a fuskarsa. """Ke ko? Za mu haɗe ne yarinya""" "Ta kuwa sake kyalkyalewa da dariya sannan ta faɗa banɗaki. Don ma kada ya biyo ta, sai ta murza" makulli ta kulle ƙofar. "Aikuwa tana cikin haɗa ruwan wanka ta ji ana kokarin turo kofar, tayi murmushi kawai tana mamakin" rashin kunya irinta Abban Imam. Ko da asubahi duk yadda ta kai ga zullewa shi yayi mata wanka tsaf ya "gargasa mata jiki, daƙyar ya barta tayi wankan tsarki bayan ta bashi tabbacin za ta iya yi da kanta." "Daga can waje ya fara mata magiya yana roƙon ta buɗe mishi kofar, tayi mirsisi kamar ba ta jin shi. Don" ta san idan ya shiga ba lallai ya barta ta shirya akan lokaci ba. Kuma yadda ta ji su Anty Balira suna fadin sammako za suyi gurin tafiya gida tasan lallai babu jimawa za su dira a gidan don yi mata sallama. Don haka ta kyale shi. Ya gaji da magiyarsa ya tafi dakinshi yana maimaita mata za ta sani ne idan suka haɗu. Ta sake shiga ruwan zafi sosai ta zauna a ciki kamar yadda Anty Balira tayi ta jaddada mata. Bayan ta gama wankan kuma ta samu man zaitun mai kyau ta shafe yammatancinta da shi. Kwalliya sosai tayi cikin ɗinkin shadda surfani ƴar kasar Mali. Zama a group ɗin Aunty Hibbah yasa ta iya "ɗaurin ɗankwali iri-iri, ko da ta kalmasa, ta lanƙwasa, ta cokara ɗaurin sai ta fito a amaryar sak! Da angon ya ganta kasa ɗauke idanunshi daga kanta yayi." "Banda direba da ya kai musu abinci ya katse shi a lokacin, da lallai sai Ango Kamal ya saka ta sake" "sabuwar kwalliya, wataƙila ma har da sabon wanka." Haɗaɗɗen dahuwar naman kan rago da yaji kayan ƙamshi kuma yayi romo sosai aka kai musu da wainar farar shinkafa. sai ruwan tea mai kayan ƙamshi a cikin flask da biredi da sultan chips. Zulaikha dai tunda ta zuba naman kai da uban romo shi taci tayi ƙat! Sai da ya tilastata da rarrashi da ban baki sannan ta ci wainar kaɗan. "Bayan sun gama duk yadda tai ta hana shi ƙiyawa yayi, shi ya taya ta suka gyara wajen tsaf, ta jona" "burner ta zuba turaren wuta, nan da nan falon ya ƙara gamewa da ƙamshin turare mai daɗin ƙamshi." Bayan sun ɗauraye farantai da kofunan da suka ɓata jan ta yayi suka zauna akan ɗaya daga cikin kujerun "falon suna hira mai daɗi, ga kuma TV a kunne suna suke kallo jefi-jefi." Cikin ɗan kankanin lokacin Zulaikha ta fahimci Kamal mutum mai son haɗa jiki da iyalinshi. Shi dai duk "wani abu da zasu yi, to sai ya ji ta a cikin jikinshi. Idan cin abinci ne, hannunshi cikin nata, idan zama ne, sai ya jata cikin jikinshi, idan kwanciya ce, sai ya dangana jikinshi da nata. Tun tana dari-dari tana jin" "kunya, har ta sadakar ta hakura. Don kuwa bata ga alamun zai daina hakan ba." "Su Anty Balira basu je gidan ba sai bayan sallar azahar, nan din ma a tsaitsaye suka musu sallama suka" "tafi, saboda direbobin da za su mayar da su suna jiransu a waje." "Bayan abin arzikin da Mummy ta haɗa su da shi, har da wanda za su kaima Innaye, Baffa, da kishiyoyin" Innaye haka Kamal ya musu sha tara ta arziki. "Sun bar garin Abuja bakunansu har kunne, babu abinda suke faɗa sai son barka da fatan alkairi. Sun" gama tabbatar da cewa Zulaikha dai ta yi dacen abokin zama da surukai na gari. "Bayan tafiyarsu duk yadda yaso ya zauna a gidan hakan ya gagara, saboda baƙi da suka cigaba da zuwa" "ta ɓangaren danginshi, da iyalan gidan Abba Lukman waɗanda suka je ƙwansu da ƙwarƙwatansu don" ganin gidan Amarya. A dole ya yi sallama da amarya ba don ranshi ya so ba ya tafi wajen abokanshi dake ta aikin kiranshi a waya tun safe. Yanayin baƙin da suka dinga yi akai-akai yasa bata samu kanta ba sai can bayan La'asar sosai. Gidan ya "rage daga ita sai Mashku da Karima, suna ta mata shakiyanci. Su din ma ana yin magriba da direba ya kai abinci, suka mata sallama suka tafi." "Sai lokacin ta samu ta zauna ta kira Innaye suka gaisa, taji cewa yan tafiya sun isa tuni. Bakin Innaye har" kunne saboda murna da jin farincikin yadda kowa yake yabon halin da suka bar diyartata a ciki. Ita ma Zulaikha da murnarta take ƙara jaddada ma Innaye tana lafiya kuma tana cikin farin ciki. "Sun daɗe suna hira, Innaye tana ta jaddada mata tayi haƙuri dai, don zaman aure sai da haƙuri kafin suka" yi sallama. "Tana katse kiran ta shiga cikin messages ta fara maidawa angon nata amsar sakonnin da ya tura mata," "bayan kiranta da ya dinga yi a waya akai-akai duk bayan awa guda sai ya tura mata saƙon yadda yake son ta da yadda yayi kewarta, tun tana tsayawa mayar mishi da martani har dai ta fahimci abin ba na ƙare bane ta ajiye wayar ta cigaba da hidimar baƙinta." Tana gama mayar masa da martanin zaƙaƙan kalamai ta faɗa wanka. Kafin tafiyar su Karima sai da suka "gyara mata gidan ƙal suka kunna turaren wuta, shi yasa bayan tafiyarsu wanka kawai tayi tai sallah ta" "tsantsara kwalliya ta zauna zaman jiran dawowar angonta. A gefe guda kuma tana cikin matsananciyar fargaba na yadda darensu na yau zai kasance, domin bata manta azabar da ta sha daren jiya ba." Wajajen karfe takwas na dare ya shiga gidan tare da zugar abokanshi. Nan suka zauna suka sha "shakiyancinsu, suka ɗora da nasiha da addu'a da fatan zaman lafiya, kafin suka yi ma Amarya kyautar manyan kuɗaɗe da cewar na bakin da basu siya ba sannan suka musu sallama suka tafi." Yana kallon yadda take tafiya tana wani dingishi da kanainayewa wai ita ala dole bata da lafiya. Har wani "magana take yi kasa-kasa, motsi kadan sai ta taba gefen wuyanta ta ce" """Wash!""" "Ba tare da gajiyawa ba yake ta jera mata sannu cike da tarairaya, ko abinci a baki ya ciyar da ita yana" "haɗa mata da rarrashi, a zuciyarshi ko dariya yake mata, don shi kaɗai yasan irin alwashin da ya ciwa dare na biyun nan." "Ƙarfe goma na dare, ya samu kiran Oganshi yana tambayarshi wasu documents da shi Kamal ɗin ya haɗa" "tun sati biyu da suka wuce. Umarni yai mishi cewar ya tura mishi documents ɗin a daren, zai yi wani aiki a kansu." Da ƙwarin gwuiwarshi ya amsa da Ok Sir! Amma wani abin haushi da takaici a gare shi shi ne ko da suka "gama wayar, ya duba cikin ɗakinshi da nufin ɗaukar Kwamfutarshi sai bai gani ba. Nan ya gane ya barta a can ɓangarenshi na gidan Mummy." "Agogo ya sake kallah a karo na biyu, goma da kusan rabi na dare. Wayarshi ya ɗauka da nufin kiran" "Karima ya umarci ta ɗauko Kwamfutar a ɗakinshi ta ba direba ya kawo mishi amma sai yaji wayarta a kashe. Ko da ya kira Mummy kuma wayar tai ta ringing bata ɗaga ba, haka ma lambar Hajja." Da damuwa a fuskarsa ya kalli Zulaikha yana faɗa mata ƙila fa dole sai ya tafi can gida a daren nan. """Ayya mana Abban Kamal... Ni kaɗai za ka bari a darennan? Don Allah ka tafi da ni mana...""" """Keh! So kike Mummy tayi min faɗa ta ce na fara yawo da ke tun yanzu...""" """Don Allah!""" Ta fara mishi magiya a shagwaɓe. """Ai baza ta san tare da ni kaje ba. Ni da kawai muna shiga zan wuce ɓangarenmu na can gidan in ɓuya," "idan ka gama abinda za kayi sai mu dawo.""" "Shi kanshi ba ya son barinta ita kaɗai, don haka bai ƙara ja da nisa ba yace ta sako hijabinta su tafi." ******* ******* """Laaa'ilaha illallahu muhammadurrasulillahi sallallahu alaihi wa-sallam! Na shiga uku ni Ta rasulu!!" "Waye anan??""" "Hajja ta jero salati da maganganun cikin ɗaga murya da firgici, hannunta dafe da ƙirji, idanunta a" warwaje alamar tsorata ƙarara. "Da yake barcin nata raba da rabi ne, baiyi nisa ba, ga kuma firgici da tsoron da zuciyarta ke ciki. Hajja na" fara salatin ta buɗe idanu a firgice tana kallonta. """Hajja... Nnnnni ce fa... ni ce.. Zulaikha ce.""" Tayi maganar cikin rawar murya. "Duk da muryarta da Hajja ta shaida, bata gasgata da gaske ita ce ba sai da ta kunna ƙwan lantarki mai" haske ta ganta ra'ayil aini. Domin ƙara share tantamar ita ce ko ba ita ba sai da Hajjan ta sake cewa """Zulai? Da gaske ke ce nake gani anan ko gizo idona ke min?""" Tayi mata tambayar zuciyarta cike da mamakin abinda zai kawo Zulai da take Amarya ɗanya shakaf cikin "gidan kuma cikin falonta a irin wannan lokacin da dare ya fara tsalawa, Zulai dai da jiya ne aka kai ta gidan Kamal matsayin matarsa." """Ni ce Hajja.""" Zulaikha ta amsa a marairaice. Idanunta ciccike da ƙwallah. """Ikon Allah!""" Hajja ta faɗa hannunta ɗaya riƙe da haɓa. Kafin Zulaikha ta ce wani abu ta sake jefa mata tambayar """To me ya kawo ki gidannan? Kuma har kika shigo falo na a irin wannan lokacin na talatainin dare? Ca" "nake jiya ne yayyinki suka kai ki ɗakin miji?""" "Mar-mar tayi da ƙwayoyin idanunta, wasu ƴan ƙananun ƙwallah suka gangaro, da rawar murya ta ce" """Hajja don Allah ki barni in kwana anan. Wallahi ni tsoron can nake ji. Mun zo ne fa tare da Abban" "Imam zai ɗauki kwamfurarshi da ya manta, shi ne ni kuma na gudo gurinki.""" Cikin ƙasa da mintuna biyu Hajja ta gano abinda ke faruwa. A zuciyarta ƙara gamsuwa da irin tarbiyar da "su Innaye suka ba Zulai tayi, lallai ita ɗin rainon ƙauye ce, da aka hore ta da kunya da rashin rawar kai ba irin wasu ƴan matan na yanzu ba." "Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, kafin ta taka sannu a hankali ta ƙarasa inda Zulaikha ke kwance bisa" kujera mazaunin mutum uku ta zauna kusa da ita. A tausashe ta fara mata magana da sigar rarrashi. """Haba Zulai, a ina kika taɓa ji an ɗaura ma yarinya aure a darenta na biyu ta gudo ta bar angonta shi" "kaɗai ? Kiyi haƙuri, ki kwantar da hankalinki. Ko wace mace da haka take sabawa kin ji ko?""" "A raunane kuma a tsorace ta ɗaga kai, alamar ta ji." """Kuma ma Abban Imam ɗin ki ne fa, ko kin manta halayensa ne na haƙuri da kawar da kai? Kin manta" irin matsananciyar soyayyar da yake miki ne? Na tabbata a irin kyawawan halayen Kamalu da na sani bazai taɓa yin wani abu don ya cutar da ke ba. Ko so kike tun a daren nan ki fara dasa mishi tunanin wata "ƴa mace a zuciyarsa?""" "Da sauri ta girgiza kai, tana jin yadda ƙirjinta ya buga daram saboda kishi daga jin saɗarar maganar Hajja" ta ƙarshe. """To in dai bakya so hakan ta kasance ya zame miki dole ki jure, ki daure, ki kwantar da hankalinki ki" "faranta ma mijinki rai a wannan dare da sauran dararen da za su biyo baya. Yanzu ina shi Kamalun?""" """Yana can""" Ta amsa daƙyar! Kamar wacce aka shaƙewa maƙogwaro. """Tashi maza muje in raka ki gurin mijinki. Kuma kar ki kuskura ko da wasa ki ba Karimatu ko wata" "labarin abinda ya faru. Kin ji?""" A karo na uku kai ta sake ɗagawa. Sannan ta miƙe tsaye jikinta a sanyaye ta bi bayan Hajja suka fice daga "ɗakin. Wani abin mamaki shi ne suna fita daga ɓangaren Mummy suka hangi Kamal tsaye a ƙofar ɓangarensu yana ta safa da marwa, bisa ga dukkan alamu ba shi cikin nutsuwarsa." """Kin ga irin damuwar da kika jefa mijinki a ciki ko? Ki tabbatar kin bashi haƙuri bayan tafiyata. Kar ki" "sake aikata irin wannan shirmen ko ba yanzu ba, domin mazajenku na yanzu ba irin namu na da bane." Tun yana lallaɓa ki yana bin ki a hankali kina botsarewa sannu a hankali zaiyi watsi da lamarinki ya fara "nema ma kansa mafita...""" "Maganganun Hajja sun ɗauke ne bayan Abban Imam ya ƙaraso gurinsu da sauri. Sai da ya isa, sai kuma" "kunya ta kama shi, ja yayi ya tsaya yana ɗan sosa ƙeya cikin kunya." """Hajja Afuwan! Ta taso ki ko?""" "Duk yadda Hajjan taso cijewa sai da dariya ta ƙwace mata ganin yadda yake ta sussunne kai, kamar ba" Kamal ɗan bokon nan da bai cika jin kunyarta ba. """Kai dai ɗauki matarka ku tafi. Na yi mai wuyar tunda na dawo maka da ita. Amma dai kar ka manta," matarka ba irin ƴanmatannan bane masu buɗaɗɗen idanu da suka san me ke cikin rayuwar aure tun "kafin su shiga cikinta. Bayan haka kuma girman jikin ne kawai, amma yarinya ce ƙarama. Ka bi ta sannu a hankali, kayi haƙuri da duk shirmen da za tayi maka. Allah ya bada zaman lafiya.""" Bata jira amsawar ɗaya daga cikinsu ba ta juya za ta shige cikin falon Mummy. """Amma dai ina fatan ba a cikin talatainin darennan za ku koma can gidanku ba?""" Ta tambayi Kamal tana daf da shigewa cikin falon. """A'a Hajjah. Dare ya riga yayi. Gobe dai da asubah in sha Allah za mu tafi don kar Mummy tayi faɗa.""" Kamal ya amsa a nutse. """Ba laifi. Allah ya tashe mu lafiya.""" """Amin.""" Kamal ya amsa da ɗan ƙarfi yadda za ta ji shi. "Bayan shigewar Hajja, tsayuwar daƙiƙu sittin suka ƙara a gurin, shi yana kallonta da karantar yanayinta," "ita kuma tana kallon ƙasa, gaba ɗaya jikinta a tsarmame, kamar kazar da aka tsoma a ruwan zafi aka tsamo." """Kayi haƙuri Abban Imam""" "Ta karya shirun da faɗin haka, muryarta na ɗan rawa, a kunyace." Bai ce komai ba. A madadin yayi magana ma sai hannunsa ya miƙa a hankali ya kamo hannunta. A fili "take jin yadda yake sauke ajiyar zuciya sauri-sauri, ya daɗe a haka, kafin ya ɗaga hannunsa da ke riƙe da" nata ya ɗora a ƙirjinsa daidai saitin zuciyarsa. """Allah ya sani ina tsananin son ki Zulaikha. Ina son kasancewa tare da ke a wannan dare. Amma idan" kin fi son kwana a gurin Hajja zan ɗaga miki ƙafa... Har zuwa sadda ke da kanki za ki ji a ranki kina son "kasancewa tare da ni. Kin amince? In mayar da ke gurin Hajja?""" """A'a!""" Ta amsa da sauri. Kafin yayi magana ta sake cewa. """Kayi haƙuri.""" Cikin sanyin murya. "A hankali kuma ta ɗaga kanta ta saci kallonsa, karaf! Idanunta suka faɗa cikin nashi. Ya sakar mata" lallausan murmushi. """Kin amince da ni? Mu tafi ɓangarenki mu kwana da asuba mu koma can gidanmu?""" Ya tambayeta a tausashe. """Eh! Na amince.""" "Ta amsa a hankali, a zuciyarta take ta ƙoƙarin ƙara ƙarfafa ma kanta gwuiwa tana yaƙar tsoron da ke" danƙare da ranta. "Ɗan shiru yayi, sai kuma ya sake cewa" """Baza ki sake guduwa gurin Hajja ki barni daga shiga cikin ɗaki ba ko?""" "Kunya ne ya kamata. Hannunta ɗaya da bai riƙe ba ta ɗaga ta rufe fuskarta tana dariya ƙasa-ƙasa, a" zuciyarta take tuna abinda ya faru har ta gudu ɗakin Hajja. 'Sai da suka gama shan madarar holandiya mai sanyi sosai da ya ɗauko a cikin frig. Bayan ya gama "kwashe kofunan da suka ɓata yakai kicin. Ya dawo ya ce mata bari yaje ɗakinsa ya ɗauko abu sai su tafi, har yana bata tukwuicin sumbata saboda duk yadda yayi da ita su shiga cikin ɗakinshi ko nata ta ƙiya." "Yana shiga ɗaki, ita kuma ta gudu cikin gidan ta shige ɗakin Hajja...'" Maganarsa ne ya katse mata tunanin da take yi. """Kin san fa ɗazu ba ƙaramin tashin hankali na shiga ba bayan fitowata cikin falo ban ganki ba.""" "Hannunta yaja suka fara takawa a hankali zuwa ɓangarensu, lokaci ɗaya kuma yana cigaba da yi mata" bayanin irin damuwar da ya shiga bayan nemanta da yayi ya rasa a cikin falon. """Bayan duba ki da nayi tayi lungu da saƙo har ƙarƙashin gado da cikin durowa da cabinet na kicin ban" "ganki ba. Afujajan na fito ina duba ki a harabar gida, binciken inda kika shige bayan dube-dube lungu da" saƙon fulawoyi ni ne har gurin mai gadi ina tambayarshi ko ya ga fitar ki? Da mamaki sosai a fuskar Baba maigadi ya tabbatar min babu wacce ta fita a darennan. "Na yi yunƙurin zuwa ɓangaren Mummy ya fi sau hamsin amma sai in kasa, tunda bata san mun zo gidan" "ba. Kuma bayan haka Kin san miye tunani da fargabata?""" Girgiza kai tayi. Kafin ya cigaba da cewa """Idan na shiga duba ki me zan ce musu? Kin fita ba da sanina ba? ko kuma wani abu nayi miki kika gudu" "don ceton kanki? Kin dai san halin Mummy da tambayar ƙwaƙwaf. Da waɗannan dalilan yasa nayi fakare a ƙofar ɓangarenmu kamar maraya, daga bisani kuma na fara safa da marwa tsakanin ɓangarenmu da na Mummy, zuciyata cike da addu'ar duk inda kika shige Allahu yayi gaggawar bayyana min ke. Sai kuma ga shi da yake Allah maji roƙon bawa ne, ya tausashi zuciyar Hajja ta fito min da ke a lokacin da ban taɓa" "tsammani ba.""" "A daidai lokacin suka isa ƙofar ɓangarensu, da hannu ɗaya ya tura ƙofar, kasancewar har lokacin" hannunsa na dama na sarƙafe da hannunta na hagu. """Kar dai ki manta, ki yi Bismillah! Don kore shaiɗanin da ya fara zuga ki ki gudu ki bar mijinki.""" Ya faɗa idanunsa na cikin nata. "A tare duk su biyun suka yi murmushi. Suka ɗaga ƙafafuwansu na dama lokaci ɗaya za su shigar, kamar" haɗin baki kuma a fili suka ambaci Bismillahirrahmanir raheem. A karo na biyu lallausan murmushi suka sake haske junansu da shi kafin suka shigar da ƙafafuwansu na "hagu. Har lokacin yana riƙe da hannunta ya mayar da ƙofar ya rufe, ya murza ɗan makulli, yaja hannunta suka nufi cikin ɗakinsa." """Kiyi haƙuri. Ɗazu na tsorata sosai, kar in barki a falo ko in shigar da ke ɗakinki ki sake tafiya ki barni...""" """Bazan sake ba. Kayi haƙuri.""" Ta katse shi a marairaice tun kafin ya aje numfashin maganarsa. """Na yi! Amma duk da haka bazan kai ki ɗakinki ba. Ɗaki na za mu je, domin can ɗin ma kamar naki ne," "akwai komai da za ki buƙata a ciki. Na san kina jin barci ko?""" """Eh! Ina ji.""" Ta amsa a hankali. Zuciyarta cike fal da fargabar da take ta ƙoƙarin dannewa kar ya bayyana a fili. "Ko da suka shiga cikin ɗakin a gefen faffaɗan gadonsa ya zaunar da ita, cikin lallaɓawa da tarairaya" "kamar wata sarauniya. Jikinsa na rawa-rawa ya shige gurin ma'ajiyar kayan sawansa, ya buɗe ɓangaren da kayayyakin sakawarta ne sababbi shaƙe da gurin. Kama daga laces, atamfa, shadda, har zuwa kayan barci da Inner wears." Kayan barci masu kyau sosai ya ɗauka mata ya fice daga gurin ya nufi inda take zaune. Daga irin yadda ta "takure kanta ta naɗe hannaye cikin ƙirjinta kamar mai jin sanyi ya kusa saka shi dariya, amma sai ya" daure baiyi dariyar ba. """Babe sanyi kike ji?""" Ya tambayeta a tausashe. """A'a! Barci kawai nake ji.""" Ta amsa a kasalance. """Sorry. Ga kayan barci na ɗauko miki. Yanzu dai ki shiga bayi kiyi wanka sai ki canja kayan jikinki zuwa" "na barci ki kwanta.""" "Har ta buɗe baki za ta ce mishi ta yi wanka tun a gida, sai kuma tayi shiru bayan ta tuna yadda Aunty" "Balira ke ta jaddada mata banda yi ma miji musu. Kayan barcin hannunsa ta karɓa, ta miƙe tsaye a hankali tana kallonshi ƙasa-ƙasa." """Ina ne banɗakin?""" "Da yatsarsa manuniya ya nuna mata inda banɗakin yake, ita kuma bata ɓata lokaci ba ta nufi hanyar" zuwa banɗaki tana tafiya kalalau-kalalau kamar kazar da ƙwai ya fashe ma a ciki. "Duk yadda yake ta ɗoki da zakwaɗin wannan dare don maimaita wainar da suka soya jiya, tsoro da" fargabar da yake gani ƙarara a cikin idanuwanta ya hana shi taɓuka komai. "Ta bakin Hajja ce, matarsa sabuwar shiga ce a komai, lallai ya kamata ya bita sannu a hankali, idan ba" haka ba kuwa da sannu zai haifar da gagarumin tsoron gamuwa da shi a zuciyarta. "Bayan ta yi wankan shi ma yayi, rungumeta da yayi tsantsan a ƙirjinsa, bayan haka bai mata komai ba" suka yi barci har ladanin masallacin unguwar ya kwaɗa kiran sallar asubah. ******** "A kwanakin da suka biyo baya amarci suke zubawa tsantsa abinsu, soyayya zallah ake shimfidawa a" "gidan, mai tsafta da burgewa, wanda ko kaɗan babu algus a cikinta." "Karima da ta je gidan a cikin satin, kasa rufe bakinta tayi. Cikin ɗan kankanin lokaci har sun kara yin wani" "fresh su biyun, fata ta kwanta luwai-luwai, saboda hutu da kwanciyar hankali, ga kuma lafiyayyun abinci da ake dafawa daga gidan Mommy ana kai musu." "Ga Zulaikha gwana ce da ta kware wajen tarairaya da kulawa da Kamal, a ɓangaren auratayya ne dai sai" "a hankali take sabawa. Ta gama karantar mijinta ciki da bai, tasan duk wani abu da ke faranta mishi rai kuma ta kware akan shi." "Karima Tana zaune tana kallonsu akan kujera 2 seater, kankana da abarba suke sha wanda Zulaikha ta" "yanka musu bayan zuwanta. Yadda Kamal yake wani zuba ma Zuy shagwaba son ranshi kamar wani karamin yaro shi ne abin ke bata mamaki, ita kuwa ta dage tana ta tarairayarshi, sun hade kawuna suna ta kus-kus suna dariya ba tare da kunyar idanunta ba, sai ta kama ma suke sanyata cikin hirarsu." "Ana nan kuma sai ya tashi wai zai shirya yaje ya gaida su Mommy, Zulai kuma ta tashi ta bi bayanshi" bayan ta ba Karima uzurin za ta raka shi sama ya shirya. Karima tana nan zaune shiru-shiru tana jira har aka fi minti ashirin babu duriyarsu. Abin ma ya kasa bata "haushi ko dariya, sai kawai ta yayimi jakarta ta fita. A ranta tana fadin idan sun kara ganinta a gidan su mata abinda suka ga dama." "Gaf da za ta fita sai ga Zuly ta biyo bayanta a sukwane, ta hau sunne kai tana bata hakuri cikin dadin" "murya, da kyar ta samu ta lallasheta suka koma cikin gida. Shi kuma ya musu sallama ya tafi." "Sai lokacin suka samu lokacin zama su yi hira sosai. Kwarai Karima ta yabawa yanayin da ta gansu a ciki," har cikin ranta tayi murna da fatan Allah Ya dorar da su akan wannan rayuwa da soyayya har abada. Itama kuma tana yiwa kanta fata da dacewa da samun rayuwar aure irin wannan. Sai can bayan isha'i sannan ta bar gidan lokacin da Kamal din ya koma. Sai da Zulaikha ta cinye sati uku cif ana kai musu abinci daga gidan su Mommy kafin ta fara cancada musu kalolin girke-girken da ta kware akai na gargajiya da na bature. "Rigima kuma sai ta koma akan a dawo mata da Imamu gidan. Shi kuwa gogan tsoron akai shi can yake," "kulawar da ake bashi tayi kasa, a raba musu ita biyu. Shi ne yake ta mata kauce-kauce da bada excuses iri-iri." "Ita kuwa da ta ga haka sai ta dangana shi ga Mommy, ita ta dage tsakaninta da Allah a bar mata Imamu," shi kuma yace ai Imamu ya riga ya zama dan gidan Mommy. Ta hakura kawai ta lalubi junior Imamu. Sai gata tana kuka riri har abin ya so basu dariya. Har cikin ranta tana kaunar zama da yaron. Ga zaman kadaici da take tunanin shiga ciki idan Baban Imam din ya koma bakin aikinshi ka'in da na'in. "Daga karshe dai Mommy ta kashe rigimar ta hanyar raba musu gardama, tace Imam zai dinga zuwa yana" "yi musu weekend duk karshen sati, sannan a ranakun karatu watarana zai dinga zuwa da yamma yana kai dare daga can makaranta. Duk da ba haka taso ba, a haka dai aka tashi." Suna komawa gida ya hau kalallameta da dadin baki da ban hakuri don ya kula dai hukuncin da Mommy "ta yanke ba haka taso ba. Daga karshe dai ya samu ya shawo kanta da kyar. Don kuwa shi yasan yar kayanshi, ya kuma san ta yadda yake shawo kan abinshi." ****** "Watansu biyu da aure, rayuwarsu na tafiya cikin tsari da ban sha'awa. Rayuwace suke shimfidawa mai" kyau da tsafta wacce babu boye-boye da cutarwa a cikinta. "Kamal yana girmama matarshi da ɗaukaka duk wani sha'ani nata, haka itama tana kaffa-kaffa da" "al'amuranshi, kuma tana iyaka kokarinta wajen ganin ta kyautata mishi yadda yakamata." A cikin satin ne kuma kwatsam ba zato ba tsammani Bintu da Hafizu suka kai musu ziyara. Bayan sun buga rikici mai yawa har Hafiz yayi mata rantsuwar idan bata shirya sun tafi gidan tilon ƙanwarsa ƙwallin ƙwal da take aure a garin Abuja ba za ta haɗu da mummunan ɓacin rai daga gare shi. "Haka ta shirya ranta a ɓace, bakinta a gaba, ta ja tsaki ƙasa-ƙasa ya fi sau hamsin kafin su isa gidan. Tun" "daga bakin gate ta fara buɗe idanu tana kalle-kalle. Lokaci ɗaya zuciyarta ta ƙara jagulewa, komai ya ƙara" kwance mata. "Tun sadda aka yi bikin, taji labarin irin gidan da aka kai Zulai a bakin Mashku, amma ko da wasa bata yi" tsammanin irin wannan tsararre kuma haɗaɗɗen gidan aka kai Zulai ƴar ƙauyen ƙayau ba. Da gaskiyar bahaushe da yace gani ya kori ji. Ashe haka gidan yake da masifar kyau tun daga bakin gate sai kace a kasar turawa? Aka ce ido wa ka raina? Ya ce wanda ya saba gani kullum! Duk ƙayatuwar gidansu da irin kwalliyar da ke ciki sai taji ta raina kyawunshi saboda gani yau da gobe. "Kai tsaye falon gidan aka yi musu masauki, ta zauna akan kujera tana yatsine-yatsine na rainin ajawali." "Ita da kanta ta sani ko hasidin Iza hasadin idan ya gani sai ya yaba, amma don tsananin tsanar da take ma" Zulai yasa taƙi ba zuciyarta damar bayyana irin kyawun da gidan yayi mata akan fuskarta. "Falon a gyare yake ƙal, ga wani daddaɗan ƙamshi kuma tattausa na turaren wuta da yake fitarwa." "Kasancewar ranar Assabar ce, Kamal yana gida, bayan zaman mintuna biyar da suka yi suna jiran masu gidan suka fito shi da ita a lokaci guda." "Daga ganin yadda Zulai ta ƙara yin ɓul-ɓul, farar fatarta da ya dusashe saboda zaman ƙauye ya goge ya" "tsatso kamar a taɓa ta jini ya ɓullo, daga kallon fatar za a fahimci jikinta sumul-sumul yake sai shekin hutu da jindadi yake fitarwa." Daga cikin matsakaicin hijabin da ke jikinta suke hangen kananun kayan da take sanye da shi. Shi kuwa gogan nata gaba-daya ya kasa dauke idanunshi a kanta sa'ilin da take zirga-zirgar ɗauko musu ɗan abin taɓawa da jiƙa maƙoshi. "Ta tare su da fara'arta, sosai fuskarta ya bayyana jin daɗin ganinsu. Har kasa tasa gwiwoyinta ta gaishe" da Hafiz. Shi kanshi Hafiz ɗin bakinshi ya ki rufuwa ganin irin kyau da tayi da girma da nutsuwar da ya bayyana a tattare da ita. Babu wannan yarinta da gigin da ya saba gani a jikin Zulan Innaye. "Bintu kuwa baƙin ciki kamar zai kashe ta, ita kaɗai take ƙara kumbura tana hanƙoro kamar za ta fashe." Jindadi da farincikin da ta gani a tattare da Zulai ya bala'in ƙona mata rai. Wani rashin wayau da ta yi kuma shi ne kasa boye hakan da tayi. Hassada da bakinciki da kishi suka bayyana a fuskarta ƙarara. Ita duk a tunaninta wai me wannan banzar "Zulai ɗin take da shi ne da zata kasance a cikin irin wannan daular? Yarinyar da ko karatun sakandare bata fita da sakamako mai kyau ba? Yarinyar da tayi rayuwar kauyen kayau? Wacce ta rayu a cikin duhun jahilci da rashin wayewa? Amma ace yau ita ce a cikin babban birnin tarayya, a cikin unguwar da sai" wane da wance suke zama a cikinta? Shi daman Kamal irin matasan nan ne masu kwarjini da nutsuwar da in ba sabo kukayi sosai a tsakaninku "ba basa iya sakin fuska da jiki suyi hira. Ita kuwa Zulai ko da taga take-taken Bintun sai tayi banza da ita, ta share ta, ta mayar da hankali kan ɗan'uwanta suna hirar yaushe gamo. Aadeel da ke hannun Bintu ma da taga tana ta wani kara rirrike shi da kankameshi don kar ma ta amshe shi sai tayi kamar ma bata" ganshi ba. Tana zaune kusa da mijinta tana sunne kai cikin kunya sa'adda Hafiz ya fara tsokanarta kan irin ƙiban da "ta ƙara, a nutse Kamal ɗin ke tare mata suna dariya su ukun, kamar sun ma manta da Bintu a cikin falon." "Izuwa sa'adda suka yi mintuna talatin a cikin gidan, Bintu ta kai maƙura wajen takura, so take yi su tafi," amma ko kallonta Hafiz baya yi balle tayi mishi alamar su tafi. "Daga ƙarshe dai da taga hirar tasu ta ƙi ƙarewa sai ta fara saka hannu tana tsikarinsa. Ta yi na ɗaya, ta yi" "na biyu bai kalleta ko ya tanka ta ba, tana tsikarinsa na ukun kuwa ya daka mata wani gigitaccen tsawa ranshi a ɓace." """Wai ke miye matsalarki ne?""" "A tsorace kuma a kunyace ta saukar da ƙwayoyin idanunta ƙasa, ta kasa ce mishi komai saboda kunyar" wannan tsawar mai cike da tozarci da yayi mata a gaban Zulai da take gani babban maƙiyiyarta. "Ƙasa-ƙasa yaja tsaki, sai da ƙyar ya iya mayar da hankalinshi kan Kamal suka cigaba da tattaunawa kan" halin da ƙasarmu ta tsinci kanta a ciki. Zuciyarsa cike da tunanin murɗaɗɗen hali irin na Bintu. "'Tun a mota ya faɗa mata zai barta a gidan Zulai ita da Aadil su ƙarasa yini, idan aka yi sallar magriba sai" "ya koma ya ɗauko ta. A cikin mota bata ce masa za ta zauna ko baza ta zauna ba, shi kuma ganin ta yi shiru sai ya ɗauka ta amince ne. Tunda suka shiga gidan, ganin take-takenta yasa shi tunanin baza ta zauna ba. Shi da kanshi a zuciyarsa ya rushe shawarar da ya yanke na barinta a gidan, amma yadda take ciccin magani tana ɓata rai abu ne da bai taɓa tsammani daga gare ta ba. Sai a yau ya ƙara tabbatarwa da gaske ne Bintu ba ta ƙaunar ƴan'uwansa, abinda Innaye da ƴan'uwansa suka daɗe suna yi mishi" hannunka mai sanda yayi kamar ba ya gani.' "Ana kiran sallar Azahar, Hafiz da Kamal suka tashi don su je suyi alwala. Zumbur! Itama Bintu ta miƙe a" "tsammaninta tafiya za suyi, don hankalinta ba shi akan hirar da suke yi bata san sun miƙe da nufin yin" "sallah bane, ita dama ko gyalenta bata cire ba balle ayi tunanin ta ji daɗin zama." A mamakance Hafiz ya juya yana kallonta """Wai ina kike shirin zuwa Bintu? Ki zauna muje muyi sallah mana!""" "Ganin da ɗan sassauci a fuskarsa ba kamar ɗazu ba yasa ta yi kwaba-kwaba da fuska, a hankali ta ce" """Wallahi ba na jin daɗi ne My dear, don Allah muje ka sauke ni a gida sai kayi sallar a can. Aadeel ma" "na ji jikinshi kamar da zazzaɓi.""" "Tsananin haushi da takaici yasa Hafiz kasa magana, ƙarin baƙin cikinsa ga Kamal da Zulai duk suna tsaye" "suna jinsu, ya sani tun ɗazu sun fahimci hassada da ƙyashi ke ɗawainiya da Bintu, a yanzu kuwa daga" yadda tayi magana ko ƙaramin yaro zai fahimci karya ce kawai take shirgawa ba kunya ba tsoron Allah. "Ya sani idan basu tafi ba, Bintu baza ta taɓa nutsuwa tayi yadda yake so a gidan Zulai ba, ta dinga" "kunyata shi kenan tana zubar mishi da mutunci. Karo na biyu da ya sake ƙarewa Bintu kallo, zuciyarsa cike da tunanin irin maganganun su Anty Balira a kan Bintu, da irin abubuwan da take nunawa akan idanunshi tun shigarsu gidan Zulai ayau. Ayar tambayar da ya daɗe da ɗiga mata a take ta koma alamar" motsin rai!! "Ya kasa daina mamaki, ashe da gasken-gaske Bintu ba ƙaunar ƴan uwanshi take yi ba? Da gaske ne" abinda ake mishi shaguɓe a kanta? A wannan karon lallai idanunshi sun washe. """Uhmmm!""" Yayi ƙwafa a fili. Ya ƙara tamke fuska idanunshi a kanta da salon bayar da umarni ya ce """Bintu ki zauna inje inyi sallah in dawo.""" Har yayi shiru sai kuma ya ƙara da cewa """Na zaci idan da ƙauna da soyayya gidan Zulai kamar gidan Mashku yake a gurinki?""" Ya jefa mata tambayar yana ƙara tsattsareta idanu. "Da saurin gaske ta taɓe baki, ta ƙara da wani zazzare idanu kamar wacce ta ji yayi wani babban saɓo a" maganarsa. """Gidan Mashku dai?""" Ta tambayeshi da mamaki sosai a muryarta. Kafin ya amsa ta ƙara da cewa da cewa """Mashkura ƙanwata fa? A'ah wallahi! Wannan misalin sam bai ko kusa hawa ba. Kada ma ka ƙara jona" "min wannan ka-re-ren! In banda ma ƙaddara me haɗo gabas da yamma me zai haɗa kifi da kaska?""" "Tsananin mamaki da takaicin maganganunta yasa shi kasa ce mata komai, sai baki da ya ai hangame" "yana kallonta, Kafafunshi suka daskare guri ɗaya kamar an zare mishi laka." "Ita kuwa Zulai, dariya maganganun Bintu suka bata, a ƙasaice, ta saki wata siririyar dariya kafin ta kalli" "Kamal, da taushin murya sosai ta ce" """Abban Imam kar ka makara sallah fa, lokacin yana ƙoƙarin wucewa""" Ta sake mayar da idanunta kan Hafiz da murmushi a fuskarta ta ce """Yaya mun gode da ziyara, ku gaida gida. In Allah Ya yarda idan na fara fita ni zan zo in muku yini.""" "Daga shi har ita sun san ta fada ne kawai, ba zuwan za tayi ba. Ita kuwa a ranta tuni ta gama kudurtawa" nan da shekara biyar masu zuwa idan muna raye ba lallai su ga keyarta a cikin gidansu ba. "Ya kasa amsa ma Zulaikha, sai ɗan murmushi da ya sakar mata. Ya ɗaga hannunshu daƙyar ya cusa a" "aljihu, ya ƙirgo dubu ashirin ya aje mata a gefen hannun kujera. Bai saurari godiyar da take masa ba yaja kafa jiki a sanyaye ya fice daga falon, Bintu ta bi shi a baya tana saɓe da Aadil a kafaɗa, ko arzikin sallama su Zulai basu samu daga bakinta ba." "Sai da suka isa gurin mota sannan Hafiz ya lura da Kamal na biye da su a baya, sallama yayi mishi a" "mutunce kafin ya wuce masallaci. Kunya duk ta cika Hafiz, saboda irin rashin kirkin da matarsa ta zuba a gidan ƙanwarsa kuma a gaban mijinta. Shi kuwa Kamal da yake wayayyen mutum ne, ko a fuska bai nuna ma Hafiz rashin jin daɗin abinda ya faru ba ba." "Hafiz ya tayar da mota kenan sai ga wata motor tana ƙoƙarin shigowa, a dole ya dakata har sai da" "wancan motar ta shigo, ta samu gurin perking kafin ya fara ƙoƙarin fita da motarsa." "Kamar an ce ya kalli wancan motar da ta shigo, karaf! Idanunsa suka faɗa cikin na Karima da take zaune" "a mazaunin direba, da waya maƙale a kunnenta tana magana tana sakin murmushi akai-akai. A gefenta Imam ne gishingiɗe akan kujera yana barci." Akan idanunshi Zulai ta fito daga cikin gidan da saurinta da bayyananniyar murna a fuskarta ta ƙarasa "gurin motar Karima, buɗe ƙofar mai zaman banza tayi, ta rungumo yaron cikin tsananin kauna da kulawa" "ta ɗauko shi cak ta fito da shi daga cikin motar, a lokacin ita ma Karima ta fito, suka wani kashe hannu da" Karima alamar da ke nuna amincin da ke tsakaninsu. Bai san cewa ya saki baki da hanci yana kallonsu ba sai da Bintu ta taɓa shi tana tambayar lafiya? mai yake kallo? """Karima ce fa ƴar gidan Mummy Saudah, baka santa bane ko akwai wani abu ne a tsakaninku?""" Ta ƙarasa tambayar ƙarshen da salon da ke bayyana zargi ƙarara a muryarta. "Bai ce mata komi ba, ya cigaba da jan motar a sanyaye suka fice daga gidan." "A cikin mota haka ta cigaba da mita kamar cin ƙwan makauniya, duk dai akan kallon da ya ƙure Karima" "da shi kamar bai taɓa ganinta ba. Shi kuwa ta tafasa sauke bai ce mata ba sai da suka ƙarasa gida, sannan ya fara sauke mata kwandon bala'i da tashin hankali irin wanda bai taɓa mata ba, duk dai akan irin wulaƙanci da tozarcin da tayi masa a gidan Zulai. Da irin yadda take wulaƙanta danginsa a ɓoye amma a" gaban idanunsa sai ta dinga nuna mishi tana ƙaunarsu. "Itama da yake a wuya take haka ta biye mishi yana faɗa tana faɗa, kamar za su ba hammata iska. Daga" karshe ma da abin ya kai ta maƙura haka ta nannaɗo wani murgujejen zagi ta laulayawa ƙauyensu da kafatanin mutanen da ke rayuwa a ƙauyen. "Ɗif! Ya ɗauke wuta na wasu ƴan daƙiƙu, kafin ya farfaɗo ya nuna kanshi da yatsarsa manuniya, fuskarsa" ɗauke da matsanancin mamakinta ya ce """Bintu! Ni kike kallon tsakiyar idanuna ki zagi ƙauyen da na fito da duk mutanen cikinta? Har da ni da" iyaye da dangina fa kenan? Kika cewa iyayena da dangina kucakan ƙauye? Masu datti dangin ƙazanta da "dauɗa? Ashe dangina ba danginki bane?""" Dogon tsaki ta ja babu alamun nadama ko kaɗan a fuska da kalamanta ta amsa da """Allah suturi buƙwui in ji kishiyar mai mageɗuwa. Can ga su gada wallahi, wannan tarkacen ba da ni ba." "Kaje dai can ka ji da danginka kai da suka zame maka dolen dole ba ni ba. Kuma zancen gaskiya ka ma nisantani da su da tarkacen da ya kwasosu, don tuni na daɗe da fahimtar yadda ba sa ƙaunata ko kaɗan. Daga yau kar in ƙara ganin ƙafar wani ya tako min gida. Tunda nayi kawaicin da kawar da kan ka ƙi gani," gwara in fito ɓaro-ɓaro in fada maka kawai tunda ka ƙi fahimta! Itama wannan mai gwala-gwalan idanun "da jiki kamar na yan dambe, ka fada mata hawainiyarta ta kiyayi ramata, kada ta kuskura ta zo min gida wallahi!""" Ta juya fuu ta wuce ɗakinta tana maganganu """Auren banza da na wofi! Daga gani wannan auren babu inda zai je, don kuwa ba sa'an aurenta ta aura" "ba. Wannan jikin da ta saki wai ita ta ganta a cikin daula ta jindaɗi tana ganin ta tsinci dami akala, to tasan cewa ba mai ɗorewa bane...!""" Ta shige ɗaki ta tura ƙofar bam! Bugun da ya ji shi kamar akan fuskarsa. Ya kama baki hannunsa ɗaya dafe da kai ya haɗiye wani kakkauran miyau. Zancen mamaki ma ba a "magana, don kuwa yau dai Bintu ta shayar da shi ruwan mamaki kala-kala. Ya gama fahimtarta sarai," bakin ciki da hassada ne danƙare a cikin ranta ba wani abu ba. Waɗannan abubuwa biyu kuma su suka ja mata gora gurin fallasa wacece ainahin Bintun da bai taɓa sani ba. "Da kyar ya iya ɗaga kafa ya bar gidan. Ya shiga masallaci yayi sallah. Ya jima a masallacin yana lazumi," gaba daya ranshi kamar an cire mishi komai ya ma kasa tunanin komai. Daga karshe ya tashi ya shiga motarshi yayi ta zagaye a cikin garin Abuja ba tare da takamaiman wajen zuwa ba. Bai koma gidan ba sai can gab da magriba. Wani tunanine yake ta yawo a kanshi tun da ya idar da sallar "la'asar, abin ya kasa fita a cikin ranshi duk kuwa da yadda yaso ya yakice tunanin." Zai iya cewa wannan tunanin ma shi ya mantar da shi ɓacin ran da Bintu ta ƙunsa mishi. Don bai tuna da "saɓanin da suka yi ba sai da ya shiga falon gidan. Ya same ta ta ci kwalliya, shima Aadeel ta shirya shi tsaf." "Da yake ita ɗin ƙwararriya ce a iya kissa da kisisina sai ta tare shi da matsananciyar farin ciki, soyayya," "ƙauna, da tarairaya, kafin ya ce komai ta rushe da kuka tasa gwuiwa a ƙasa tana bashi haƙuri." "Hankalinta bai kwanta ba sai da taga ya saki fuskarshi, ya kuma tabbatar mata da komai ya wuce. Sannan" cikin rawar jiki ta gabatar mishi da kalolin girke-girke irin waɗanda ta tabbatar yana so. "Shi ya ma manta rabonshi da ƙwaƙƙwaran abinci tun karin safe, sai lemo da snacks da ya ci kaɗan a" gidan Zulai. "Duk yawon da yayi a cikin gari ruwa kawai ya dinga ɗaɗɗakawa cikinshi, ba ya jin yunwa, balle ya tsaya" ko gidan abinci ne ya shiga ya cika ciki. Duk ƙamshi da haɗuwar da abincin yayi ranar dai kasa ko kallonshi yayi balle yayi tunanin ci. Haka ta bishi har cikin dakinshi tana ta kwarkwasa. So tayi ta hillaceshi kamar yadda ta saba don maganar ta "ƙarasa wucewa, amma ya ki damar hakan." Haka tana ji tana gani ya sake yin wanka ya sanya wani yadi mai kyau ya fita. Ta bishi da kallo jiki a sanyaye. Ranta ya gama bata cewa lallai yau ta tsokanowa kanta faɗan da yafi karfinta. ***** "Da misalin karfe takwas da yan mintuna na dare Hafiz yayi sallama a kofar falon gidan Mommy Saudah," "sai da ya jira aka amsa daga ciki, aka yi mishi izinin shiga kafin ya danna kai cikin falon." Karima da Hajja kaɗai ya samu a zaune a falon suna kallo TV. Ya samu kujera ya zauna bayan ya gaishe da Hajja ta amsa a mutunce. "Da sanyin murya Karima ta gaishe shi, bayan ya amsa ta miƙe a nutse ta nufi kicin don kawo mishi ruwa" "da abin taɓawa. A fakaice yabi bayanta da kallo, a zuciyarsa yake jin ƙarin nutsuwa ta musamman." "Gorar ruwan faro da madarar hollandia ta fara ajiye mishi, sannan ta koma cikin kicin ta kawo mishi" "Meat pie shaƙe da faranti, da alamun ba'a daɗe da gama soyawa ba, don sai ƙamshi yake yi." """Yaya Bismillah! Ya su Aunty Bintu da Aadil?""" Ta tambaye shi. "Bayan ya amsa mata da lafiyarsu ƙalau ta sanar da shi Mommy tana amsa waya ne, idan ta gama za ta" fito. "Don haka ya zauna anan yana sauraren hirar da suke yi da Hajja, lokaci bayan lokaci yana ɗan tsoma" "musu baki idan Hajja ta sako shi cikin hirar. A kaikaice yake ƙare ma Karima kallo, wani iko na Ubangiji kuma sai yaji tunanin da yake ta taunawa a cikin ranshi yana ƙara kwanta mishi sosai da sosai." "A da kam, ya riga ya gama ƙudurtawa ranshi cewa shi fa Mijin mace ɗaya ne. Sam! ba shi da wani ƙudiri" "na karin aure. Amma a yanzu, sai yake jin cewa zai iya, kuma zai yi. Ba wai kuma don kawai munanan halayen Bintu da suka bayyana ƙarara a idanunshi ba, ba kuma wai don ba ta kaunar danginshi da iyayenshi ba, sai don kawai samun damar cin moriyar karin maganar nan ta bahaushe da ya ce gida biyu" maganin gobara. Duk da dai rashin kaunarta ga danginshi shi ya fara ɗarsa masa tunanin lallai ya kamata ya nemi mafita. "Aka ce ranar naka sai naka, daɗin zama sai bare. A matsayinsa na namiji kuma yana da gida nasa na" kansa bai kamata ace ƴan'uwansa idan suka shigo garin Abuja basu da gurin zama a gidanshi ba. "Karima ƴa a gurin Mummy Saudah, ita kaɗai ce ƴa mace tilo da yake jin zuciyarsa ta nutsu da ita kuma ta" yarda da tarbiyar da ta samu. Kuma a yadda yaga shaƙuwa da ƙauna tsakaninta da Zuly yasan baza ta taɓa ƙin iyayenshi da ƴan'uwanshi ba ko da sun fi haka ƙauyanci. Yini yayi a ranar yana tunanin al'amarin. Wani abun ikon Allah kuma sai yake jin har wani ɓurɓushin "soyayyar Karimar ke taso mishi a zuciyarsa. Da wannan dalilin yasa yayi ta addu'a sosai, ko a hanyarsa ta zuwa gidan yana tuƙa mota yana addu'ar idan babu alkhairi a al'amarin kar Allah ya bashi ikon ƙarasawa gidan balle har ya samu sararin furta abinda ke ranshi. Ya tabbatar da alkhairi a lamarin ne jin yadda" yake ta ƙara samun nutsuwa da kwanciyar hankali a tunanin Karima da son aurenta cikin gaggawa. "Ko da Mommy ta fito falon, bayan sun gaisa Hajja da Karima shigewa ɗakunansu suka yi bayan sun bayar" da uzurin za su je su gabatar da sallar isha'i. A karo na uku ya sake kallon Mommy ya sunkuyar da kai yana ɗan sosa ƙeya. "Mamaki ne ya kamata, sai kuma ta ɗan saki dariya tana cewa" """Hafiz? Wai ni ɗin na zama sarkuwarka ce? A sanina dai girmamawa ce a tsakaninmu amma babu ƴar" "kunya ko ɓoye-ɓoye. Yaushe muka fara ƴar haka da kai?""" "A kunyace ya saki dariya, kafin yayi ƙarfin halin cewa" """Mommy yau dai zuwa nayi da ƙoƙon bara wajenki, ban san yadda za ki ɗauki al'amarin ba shi yasa" "nake jin wani iri. Amma tunda kin buƙaci in faɗa zan faɗa.""" "Ɗan shiru yayi, sai kuma ya cigaba da cewa" """Ki dubi girman Allah ki bani auren Karima. Na miki alkawarin zan rike miki ita da amana da mutunci!""" "A bazata, zancensa ya sauka a kunnen Mommy. Shi yasa tayi ɗan shiru tana jinjina girman maganar a" "zuciyarta. Sai kuma ta koma ta jingina da kujera tana kallonshi a nutse, kafin murmushi ya ɓalle a fuskarta." """Hafiz, da gaske kake yi ko da wasa?""" """Da gaske nake yi Mummy. Wallahi tallahi da gaske nake yi.""" Ya rantse mata don ma ta tabbatar shi fa ba da wasa yake yi ba. """Madallah! Allah ya tabbatar mana da alkhairi. Amma ina so ka sani a wannan gaɓar babu abinda zan" "iya maka, iyaka in ce ka zage dantse ka nemi amincewa a wajenta, idan ta yarda, tabbas babu wanda zai" kaini farinciki da jindadin wannan al'amari. Zuriyar Innaye da Baffa ai abin farin ciki da alfahari ne ƙara "haɗuwa da su a karo na biyu.""" Lallausan murmushi ya saki da jin kalamanta yana jinjina kai sannu a hankali. ****** ****** ****** """My dear...""" Ta kira sunanshi da taushin murya """Na'am!""" Ya amsa da yanayin muryar da ke bayyana gaf yake da fara barci. "Duk da fahimtar hakan da tayi, bai sa ta fasa faɗin maganar da ke bakinta ba. Saboda gobe tun da wuri" take so ta kira Mashkura ta wuce da Aadil gurin Ummansu ko za ta huta da masifar tsotson da ya tsiro mata da shi a kwanakinnan. """Daman ina so in faɗa maka ne, gobe asabar in sha Allah zan yaye Aadil...""" """Yaye dai Bint?""" Ya tambayeta a mamakance. Kafin ta amsa ya yunƙura ya ɗaga kansa daga cinyarta ya zauna suna fuskantar juna. """Na zaci shekararsa ɗaya ne? Har ya isa yaye?""" """Ya isa mana My dear... Yana tafiyarsa ko ina, kuma yana cin abinci sosai. To me ya rage?""" Tayi maganar bayan ta kwaɓe fuska don ma kar yace zai hana ta. "Jinjina kai yayi, sannan ya ce" """Kin ga mu kuwa iyayenmu ba tafiya ko cin abinci ne ma'aunin yaye yaro ba. Sai yaro ya kai shekara" "ɗaya da rabi, idan yakai ɗin ma sai yayi haƙora fiƙa, idan baiyi har watanni ashirin yaro yana yi ana bashi" "nono, daman ko a addinance watanni talatin ne ciki da shayarwa...""" """Watanni talatin dai My dear..?""" Ta katse shi da sauri bakinta na rawa. """Ƙwarai kuwa! Watanni talatin.""" "Ya amsa mata, don ƙara tabbatarwa har yana jinjina mata kanshi." """Bazan iya ba. Allah ya sani bazan taɓa iyawa ba. Ka tausaya min don girman Allah... Kai baka ga yanzu" "yanda yake neman fin ƙarfina da tsotso ba?""" Ta jefa mishi tambayar idanunta ciccike da ƴan ƙananun ƙwallah. """Ki kwantar da hankalinki. Ni daman tunda kin yi niyyar yaye shi bazan hana ki ba Bintu. Allah ya raya" "mana shi.""" Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke na samun kwanciyar hankali. A hankali ta amsa da """Amin ya rabb!""" Shiru ne ya ratsa tsakaninsu na ƴan wasu daƙiƙu. Can kuma sai ta ce """Gobe tun da safe Mashkura za ta zo ta wuce da shi can gida gurin Umma...""" """Wani gidan?""" Ya sake tambayarta a mamakance. Kafin ta amsa ya sake cewa """Ba wani gida da za ki kai shi fa. Ki haɗa kayanshi idan zan tafi Faƙo gobe zan wuce da shi gurin" "Innaye...""" """Amma dai wasa kake yi ko?""" Ta tambaye shi da murmushi a fuskarta. Don ita har ga Allah da dukkan gaskiyarta ta ɗauka da wasa yake mata. Bata tabbatar da gaske yake mata ba sai da cikin ƙanƙanin lokaci ya haɗe girar sama da ƙasa yayi murtuk sannan ya ce """Wasa? Zancen raha muke yi da zan miki wasa ko kuwa na zama abokin wasanki ne? Look Bintu, na" gama yanke wannan zancen tun ba yau ba. Tun da kika haifi Aadil daga ke har shi sau ɗaya kuka taɓa taka ƙafa zuwa Faƙo. Idan a matsayinki na matata kin yanke mu'amala da iyaye da ƴan'uwana na zuba miki idanu shi baki isa ki yanke alaƙarsa da su ba. Su ɗin wajib ɗin sa ne. Don haka gobe zan tafi da Aadil "gurin Innaye ta yaye shi acan, faƙat!!""" Sau uku tana buɗe bakinta tana rufewa amma ta kasa furta komai saboda tsananin yadda "maganganunsa suka yi mata mugun dukan da yasa jikinta mutuwa murus!! Kalaman bakinta suka ƙafe ƙaf! Miyaun bakinta ya bushe ƙamas! Ta rasa abinda za ta ce masa kamar yadda ta rasa abinda ya kamata ta fara aiwatarwa da gaɓɓan jikinta. Abu ɗaya dai da yake ta amsa kuwwa a zuciyarta amma bakinta ya kasa furtawa shi ne ko sama da ƙasa za su haɗe a gobe, babu yadda za'ayi ta bari Hafiz ya" ɗauki ɗanta ƙwara ɗaya ƙwallin ƙwal ya tafi mata da shi ƙauyen Faƙo. "Wani ɗan tunani da ya tsirga mata a zuciya yasa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya. Sannu a hankali, ta" "ɗan tsuguna kaɗan, kamar makauniya sai ta fara lalubar bakin gado da hannunta ɗaya sannan ta ɗosana mazaunanta. Idanunta tsaye ƙyam a kanshi kamar wacce ta warke makanta." "Ta sani, idan ta ce za ta biyo mishi da sigar tashin hankali babu abinda hakan zai haifar sai ƙara samar da" ƙatoton giɓi a zamantakewarsu. Dama yaya lafiyar giwa balle ta yi hauka? Tun watanni biyu baya da suka kai ziyara gidan matsiyaciya Zulai har ta kasa mallakar zuciyarta tayi ta aikata abubuwan da ƙarara suka fallasa ma Hafiz ba ta ƙaunar ƴan'uwansa har yau basu koma kamar tif da taya irin yadda suke a baya ba. "Ba faɗa suke yi ba, suna gudanar da komai lafiya ƙalau, musamman daga gare ta da ya kasance kullum" "tana ƙirƙirar sabbin abubuwa don ƙara janyo hankalin mijinta gare ta. Amma ita da kanta ta sani Hafiz ya canja mata, irin canjin nan da baza a kira shi ɗari bisa ɗari ba, amma fa lallai canjin ya wawuke hamsin bisa ɗari. Kaso hamsin ɗin ne take ta lallaɓawa tana ta-ka-tsan-tsan don kar a sake samun matsala daga" gare ta. "A karo na biyu, ta sake sauke nannauyar ajiyar zuciya. Tayi narai-narai da idanunta tayi ƙasa da su sosai." Da sanyin murya mai bayyana tsananin ladabi da biyayya ta ce """Allah ya huci zuciyarka Abban Aadil. Ubangiji Allah ya huci zuciyarka. Wa ce ni in ce zan raba Aadil da" kakanninsa? Ni a su wa? kuma ko ni da kake ganin kamar na yanke alaƙata da su wallahi ba haka bane... "Kawai dai na ɗan ja baya ne har zuwa sadda za su huce sosai saboda abinda ya faru na lamarin Zulai... Don Allah kayi min kyakkyawar fahimta masoyi...""" Ajiye maganar yayi daidai da silalowar wasu siraran hawaye daga kwarmin idanunta. "Kuma karaf a idon Hafiz. Amma wani abin mamaki shi ne, duk waɗannan tausasan kalaman, da" "waɗannan hawayen da suka cigaba da sauka a idanunta kamar an buɗe famfo, ko gezau baiyi ba balle har ya ruɗe ya fara ɓare-ɓaren jiki yana rarrashinta kamar yadda yake yi a baya. Sai ma wani siririn tsaki da yaja ƙasa-ƙasa ya nemi bakin gado ya zauna, wayarsa da take ajiye gefe ɗaya ya janyo ya fara latsawa" sannu a hankali. Wani matsanancin tsoro ne ya tumbatsa a zuciyar Bintu. Abu ne da bata taɓa tsammani daga Hafiz ba shakulatun ɓangaro da zubar hawaye a idanunta. Abu kamar aikin asiri? Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Daga zubar hawaye na kissa sai na gaske suka koma zuba a idanunta. "Kamar za ta share shi, amma niyyarta na yaye Aadil gobe kuma Ummanta take so ta yaye mata shi" domin har sun gama magana da ita Umman tun kwanaki yasa ta ja sanyayan ƙafafunta kusa da shi ta jingina kanta da kafaɗarsa tana cigaba da shessheƙar kuka. Da rawar murya irinta wacce kuka ke neman cin ƙarfinta ta ce """My dear yaye yaro ɗan shekara ɗaya abu ne da ake buƙatar ya kasance kusa da mahaifiyarsa." "Musamman da ya kasance Aadil yaro ne mai masifar ƙulafuci ga ƙwuiya, ka ga kuma ko babu komai ya saba da su Umma, sannan ga Mashku wacce duk tashen ƙwuiyar da yake yi sam ba ya mata. Ba ka ganin idan aka kai shi can Faƙo gurin mutanen da bai san su ba, bai taɓa ganinsu ba, bai saba da su ba, zai iya" "shiga wani mummunan hali da ba'a fata?""" "Bai amsa mata ba, bai kalle ta ba, sannan bai fasa danna wayar da yake yi ba." "Ita kuma bata gaji ba ta cigaba da magana cikin ƙanƙan da kai da magiya, daga jingina kai a kafaɗunsa sai" ta zame zuwa ƙasa ta haɗa hannayenta biyu alamar roƙo ta cigaba da cewa """Ina roƙonka don Allah ka yi haƙuri My dear, Umma ta yaye a yanzu, nan gaba kaɗan ko shekaru biyu" "idan ya cika a duniya ni da kaina zan haɗa kayanshi ka kaishi gurin Innaye ya kwana musu biyu...""" Wani mahaukacin kallo da ya watsa mata kamar zai rufe ta da duka yasa ta ajiye numfashin maganarta "ba tare da ta shirya ma hakan ba. Ajiye wayarsa yayi, ganin haka yasa taja da baya da sauri, don a tsammaninta zai kai mata hannu ne karo na farko a tarihin rayuwar aurensu." """Uhmmmm! Bintu kenan! Na rasa abinda ya rufe min idanu tun a baya na kasa gano munana kuma" "baƙaƙen halayenki!! Yanzu saboda ba ki da kirki ni kike kallo tsakiyar idanuna kina kiran iyaye da ƴan'uwana wasu mutane can??? To bari in faɗa miki, ko Aadil zai mutu saboda ƙwuiya da rashin sabo" "Innaye ita za ta yaye shi...""" "Izuwa wannan lokacin, duk yadda ta kai ga ƙoƙarin danne ɓacin ranta kasawa tayi. Ranta a ɓace ta miƙe" "tsaye ta tsaya a gabansa suna musayar kallo, da ɓacin rai mai bayyana maɗaukakin tashin hankali ta ce" """Amma gaskiya tsakani da Allah idan kayi min haka baka min adalci ba Hafiz. Saboda Allah ya kake so" "yaron da ya taso cikin gata, tsafta, tarairaya, shagwaɓa irin Aadil ya gudanar da ƙazantacciyar rayuwa" "irinta su Innaye...?""" "Tahowar tafin hannunsa kawai ta gani a cikin idanunta, a zafafe ta yunƙura za ta ja da baya ankara da" hakan da yayi yasa shi saka hannunsa na hagu ya finciko wuyar hijabinta. Cikin sauri da sadaƙarwa haɗe da faɗuwar gaba tayi gaggawar runtse idanunta tana jira taji saukar mari "a kumatunta, sai kuma taji shiru. Sakan ɗaya, biyu, uku, a hankali ta ɗan buɗe idanu ta saci kallonsa sai" taga hannunsa maƙale a iska daf da kumatunta. Ko da ta kalli fuskar Hafiz da sauri ta sauke idanunta ƙasa saboda irin fusata da hucin da taga yana yi kamar zai ci babu. """Kin ci sa'a! Kin ci sa'a Bintu tun da na tashi a rayuwata ban taɓa ganin Baffa ya daki Innaye ko ɗaya" "daga cikin matansa ba. Don haka ba na fatan ni ɗansa ace na fara dukar matata. Amma idan giyar wake kike sha ki ci gaba da aibata Iyaye, ƴan'uwa, ƙauyen Faƙo a gabana. Na rantse da Allah sai na koya miki hankali ta inda baki taɓa tsammani ba. Kuma ina sake faɗa miki, Wallahi Tallahi Aadil ko mutuwa zaiyi" "Innaye ce za ta yaye shi ba Ummanki ba.""" "Wuyan hijabinta da ya shaƙe ya wancakalar da ita, tayi taga-taga za ta faɗi, daƙyar ta iya tsayawa guri" "ɗaya. Bai sake kallonta ba ya ɗauki wayarsa, wallet ɗinsa da makullin motarsa ya fice daga ɗakin bayan ya ja mata wani dogon tsaki." "Ko bayan fitarsa ta daɗe cikin shiru, bayyanan tashin hankali da maɗaukakin tsoro ƙarara a fuskarta. Duk" "da wannan taratsin da ya mata ko kaɗan ba ta ji a ranta za ta iya saduda ya ɗauki Aadil ya kaishi gurin Innaye ba. Abu ne da sam-sam bazai taɓa yiwuwa ba ko da za suyi tashin hankalin da ya ninka wannan ya ƙara ninkawa. Don haka ta watsar da zancen ta fara tunanin yadda gobe da sassafe za tayi sammakon ɗauke Aadil daga gidan tun ma kafin ya farka daga barci, za ta gani, ko idan ta kai ma Ummanta Aadil" yana da ƙwarin gwuiwar da zai iya zuwa ya ɗauko shi? "Can kuma sai idanunta ya faɗa kan agogo bayan ta ji ƙarar ficewar motarsa daga gidan, ƙarfe tara da" minti goma sha bakwai na dare. """Ina my dear yake haramar zuwa a darennan?""" Ta tambayi kanta a fili. Lokaci ɗaya kuma sai tunanin yadda yake yawan yawace-yawace a cikin kwanakin ya faɗo mata a rai. Ƙirjinta ne yayi kwance-kwance ya buga daram! """Na shiga uku ni Bintu? Kar dai ace yawon zuwa club My dear ya tsira abinda ba halinsa ba?""" Ta sake tambayar kanta hankalinta a tashe. Domin tunanin yi mata kishiya a soyayya balle har ya fara neman aure abu ne da ko a mugun mafarki bata taɓa hasashen zai iya faruwa ba. ****** "A hankali yake tuƙa motar, jefi-jefi idanunsa na sauka akan fuskar wayar yana kallon lambar Karima da" "yayi saving sunanta da Ƙurratul-ayni. Kamar bazai kira ba, sai kuma ya danna mata kira, domin a yadda zuciyarsa ke tafarfasa ita ce kawai zaiyi tozali da kyakkyawar fuskarta ya nemi ɓacin ran da ke danƙare a zuciyarsa ya rasa." "Har ya cire ran za ta ɗauka sai kuma ta ɗaga a lokacin da kiran ke daf da tsinkewa. Bayan sallama, shiru" tayi daga can ɓangaren tana jan fasali irinna macen da ake bibiya ana neman soyayyarta. Domin har "yanzu ba wai ta sake mishi bane, jan zarenta take yi yadda take so shi kuma yana bibiye da ita sawu da" "ƙafa, abinda ke ƙara fasa mata kai kenan tana ci gaba da murza kambunta yadda take so." """Ƙurratul Ayn...""" Ya kira ta a tausashe. """Na'am Nurul-ƙalb""" Ta amsa shi da wani irin salo da ko a fili ko a waya bata taɓa gwada mishi irinsa ba. Wani zirrrr da ya ji tun daga tsakiyar kansa zuwa babbar yatsarsa yasa shi saurin gangarawa gefen titi tun "kafin ya buga ma motar gabansa. Ƙara ƙanƙame wayar yayi a kunnensa kamar me tsoron kar a ƙwace masa. Ya sake yin ƙasa ƙasa da muryarsa yana jin yadda zuciyarsa ke bugu sauri-sauri da matsanancin soyayyar Kariman. Allah ya sani yana son Karima, irin soyayyar nan mai saiɓi da shiga cikin zuciya sannu sannu kafin malallakiyar zuciyar ya ankara ta yi masa mugun kamu." Idan za a ritsa shi da wuƙa shi da kanshi bazai ce ga abinda ke ƙara jansa a afka ma soyayyarta ka'in da "na'in ba. Lallai sai yanzu ya ƙara yarda so tsuntsu ne, yana tashi haihata-haihata daga wannan bishiyar ya koma wancan. Bazai ce ya daina son Bintu ba, amma fa shi baya jin ta a ransa kamar yadda yake jin Karima." Da gaske yanzu idan za a bashi Alƙur'ani zai rantse da Allah Karima yake so! Karima yake ƙauna!! Da Karima yake burin yin rayuwar aure na har abada!!! """Ina so in ganki Ƙurratul-ayn! Yanzu...!""" Ya sake faɗa da murya ƙasa-ƙasa. Shiru tayi na ƴan wasu daƙiƙu! Ta buɗe baki za tayi magana sai yayi saurin katse ta da cewa """Kar ki ce min a'a dare yayi don Allah sanyin idaniyata. Ina cikin matsananciyar damuwa, tabbas idan" "banyi tozali da kyakkyawar fuskarki ba zanyi kwanan baƙin ciki ne a wannan dare.""" """Me yake damunka Nurul ƙalb? Wa ya taɓa min kai ?""" Ta tambaye shi da murya mai bayyana damuwa da damuwarsa. """Ke kaɗai nake son gani kawai... I'm very sure hankalina zai kwanta idan na ganki. Pls ƙurratul-ayn""" "Ya sake faɗa cikin magiya, ba tare da ya amsa ɗaya daga cikin tambayoyinta ba." """Shi kenan! Allah ya kawo ka lafiya. Amma yanzu ina asibiti...""" """Ga ni nan zuwa.""" Bai jira ta sake cewa komai ba ya katse wayar. Tayar da motar yayi ya harba kan titi a guje yana jin yadda zuciyarsa ke tsallen baɗaken murnar za tayi tozali da muradinta. "A can ɓangaren Karima, narai-narai tayi da idanu tana kallon Hibba haɗe da cewa" """Na shiga uku Hibbah! Mijin Aunty Bintu ne fa...!""" """And so what?""" Hibba ta katse ta haɗe da gallah mata harara. """Wani lokacin ke dai banza ce Wallahi Karima. Na rantse da Allah da tuntuni na san da wannan labarin" "da tuni kun daɗe da wuce wannan matakin. Sai me don mijin Bintu ne? Haramun ne? Uban me kuka haɗa da Bintun da har kike shakkar auren mijinta?""" Taja dogon tsaki ta sake gallah ma Karima harara a karo na biyu sannan ta cigaba da cewa """Dama ace Bintun wata mutuniyar arziki ce shi ne har za ki ɗan ji wani ɗar don mijinta na son ki. Na" zaci ke kika bani labarin irin yadda Bintun take wulaƙanta iyaye da danginsa don sun kasance ƙauyawa? Kuma baya ga haka ma ko asibitin nan nazo gurinki ai ina ganin yadda take wulaƙanta ku Nurses tana daka muku tsawa don kawai taƙamar ita likita ce. Don haka ki aje wata Bintu a gefe ɗaya ki rungumi masoyinki da gasken-gaske. "In dai har za ki ji shawarata, ki bashi dukkan goyon baya ɗari bisa ɗari. Tunda kika ga Mummy ita da" "kanta ta zaunar da ke tana faɗa miki kyawawan halayen Hafiz ɗin, alamun da ke nuna ta yi na'am da al'amarin ɗari bisa ɗari kawai dai ba ta son yi miki tilas ne." "Yanzu dai duk ba ma wannan ba, tashi ki shiga bayi ki wanke fuskarki kizo in miki kwalliya sama-sama" "don kar ya ganki garau-garau duk kin jigata da aiki...""" """Don Allah ki bari Hibbah, ni ba wani kwalliya da zanyi...""" Ai ko kafin ta rufe baki har Hibba ta finciki hannunta taja ta da ƙarfi suka fara tafiya zuwa banɗaki. """Wallahi baki isa ba. An faɗa miki namiji irin Hafiz da sanyin jiki ake samun hankalinsu? Ko don kina" ganin Allah ya kashe ya baki? To in faɗa miki ko kina da kyau sai kin ƙara da wanka kamar yadda ba'a "bori da sanyin jiki.""" A ƙasa da mintuna goma sha biyu Hibba ta yi ma Karima sassauƙar kwalliyar da ya ƙara fito da ita fes! Ta tsiyayi humrah ta shafa mata. Don saboda tsabar sabo da gayu da gwalli duk inda Hibba za ta saka ƙafa a cikin jakarta akwai komai da za ta buƙata na kwalliya. Ko don ya kasance sa'na'arta ne oho!!! "Kamar yanzu dai, ƙanwar Hibban aka kwantar a asibitinsu Karima, mahaifiyarta ita ta yini da mare lafiyar" ita kuma Hibba za ta kwana da ita. Duk da sanin jinya za ta je asibiti hakan bai hana ta zuwa da kayan kwalliya da ɗaya daga cikin kalolin humrar da mahaifiyarsu take sayarwa ba. Ashe rabon tayi ma Karima amfani da kayan kwalliyar ne. "Karima aikin yamma tayi, tun tuni ya kamata ta tafi, amma ganin Hibba ya saka ta zama tana rage mata" "dare, bayan ta kira Mummy ta faɗa mata ba sai an turo mata direba ba, direban gidansu Hibba zai dawo da ita gida." Hira ne yayi hira har Allah ya matsi bakinta take ba Hibbah labarin irin naci da matsanancin son da Hafiz ke mata. Bayan ta gama zage ta tas kan irin wasa da dama ɗaya da Allah ya jefo mata sannan ta ɓuge da bata shawarwarin yadda za ta sauke duk wani izzah da aji ta ƙara ruƙo wuyan Hafiz ɗin ƙam! Ta yadda "bazai taɓa gigin barinta ba. Suna cikin wannan tattaunawar ne Hafiz ya kira ta a waya, shi ne fa har ta" fara gwada masa kulawa da soyayya wanda da can ba ta wani nuna masa saboda tsoron abinda zai je yazo idan zancen soyayyarsu ya koma kunnen Bintu. Isowar Hafiz harabar asibitin ya yi daidai da isar Dr. Raudha aminiyar Bintu na ƙud-ƙud cikin asibitin. Ita a "ranar aikin dare take da shi. Mamaki ne ya kamata don ta san Bintu aikin safe tayi, tunanin ko wani abu yazo karɓa ma Bintu a cikin asibitin yasa tayi watsi da mamakin ta cigaba da latsa waya tana ƙoƙarin danna kiran lambar Mamanta har Hafiz ya shige cikin asibitin akan idanunta." Tsayawar da tayi amsa waya a cikin mota yasa tayi kyakkyawan ganin da yasa wayarta ya suɓuce daga "hannunta ya faɗa kan cinyarta. Bata ko bi ta kan wayar ba ta cigaba da kallon Hafiz da Karima da suka jero suna takun da ke bayyana ƙarara masoya ne su biyun. Kamar ita ce Bintu, saboda wani baƙin ciki da kishi da ya rufe mata idanu, a haukace ta yunƙura za ta buɗe motar ta fita sai kuma tayi gaggawar saka ma kanta linzami." "Wayarta ta rarumo da sauri, bata bi ta kan muryar mahaifiyarta da take ji yana fita a cikin wayar ba ta" "katse kiran a gaggauce, hannunta har rawa yake yi gurin lalubo lambar Bintu ta danna mata kira, amma" wani abin baƙin ciki da takaici shi ne wayar Bintun a kashe take. Cikin ƙasa da sakan hamsin sau huɗu tana gwada kiran Bintu na'ura na faɗa mata wayar a kashe take. Baki da hanci buɗe zuciyarta tumbatse da maɗaukakin mamaki ta cigaba da bin su Hafiz da kallo har suka shige cikin motarsa shi da Karima. Tsoro ne sosai ya ƙara kamata ganin yadda Hafiz ya buɗe ma Karima ƙofar da za ta shiga yana kashe ta da lallausan murmushi. Idan ma ba idanunta ne ke mata gizo "ba, sai taga kamar har wani ɗan duƙawa Hafiz ɗin yayi ma Karima alamun girmamawa." Ita kuwa Karima sai wani rausaya take yi tana rangwaɗa haɗe da fari da idanu. Ko rantsuwa tayi babu kaffara akan idan ba matsananciyar soyayya ba ce a tsakaninsu babu yadda za ayi ta gansu a cikin wannan yanayin. """Taɓɗijan! Namiji! Namiji!! Mugu ɗan masara ana goyonka kana gemu... Don ubanki Bintu ki buɗe" "waya in baki labarin kaɗan daga cikin sakayyar da Hafiz zai miki kan irin alwashin da kika daɗe kina sha akan shi ya fita daban a cikin maza.""" "Ta yi maganganun cikin masifa kamar za ta ci babu, a lokaci guda kuma tana cigaba da gwada kiran" lambar Bintu. Wanda har lokacin na'ura ke sake tabbatar mata wayar a kashe take. Ita kaɗai a cikin motar take masifa tana zage-zage kamar za ta ci babu. A Lokaci guda kuma tana shan alwashin kaloli mabanbanta na cin uban Karima da za suyi ita da Bintu gobe a ofis idan an wayi gari. """Kuga min shegiyar yarinya sumumu-kasau ashe ƙasungurmar munafuka ce? Ko da yake ai maganin" "Bintun ma da ta sakarwa uwarta Hajiya Sauda fuska, ai ga sakayyar sakin fuska nan ta fara gani. Tana" "niyyar wanke zuƙeƙiyar ɗiyarta ta bashi ya aura.""" Tana wannan masifar har bata san lokacin da motar Hafiz ya bar harabar asibitin ba. Waigawa kawai tayi taga inda motarsa take ba shi sai filin gurin. "Ta ja tsaki ya fi sau hamsin, duk yadda mahaifiyarta take ta biyo bayan kiran wayarta ta kasa ɗauka. Duk" da magana ce mai muhimmanci suke yi. Ta sani a yadda take fusacen nan ko ta ɗauka baza ta iya mayar da hankali su cigaba da magana ta nutsuwa ba. "A ƙarshe sai kashe wayar tayi, ta figi jakarta da wayar ta fice daga cikin motar ta nufi cikin asibitin. A" zuciyarta take ƙudurta yadda za ta ci uban duk wata nurse budurwa da ta tarar da ita a bakin aiki a wannan daren. "'Munafukai, Algungumai, duk bakinsu ɗaya matsiyata. Ashe bayan kwarkwasa da gwalli da suke yi ma" Likitoci maza har mazajen likitoci mata basu bari ba. Duk za su ci ubansu ɗaya bayan ɗaya.' Da wannan ƙudurin ta ƙarasa cikin asibitin zuciyarta cike da addu'ar Allah ya haɗa da ƴanmatan nurses "ɗin asibitin, musamman waɗanda ta san sun fi shiri da Karima." ****** Wannan gwaggwaɓar canjin bazata da aka samu bagatatan a cikin tafiyar soyayyar da a farko shi kaɗai "yake kiɗansa kuma yake rawarsa ba ƙaramin faranta masa zuciya yai ba. Tuni ya manta da Bintu, ɓacin ran da ta cusa mishi da duk wani abu da ya shafe ta." "Ba ma kamar yadda minti ɗaya biyu a hirar da suka gabatar da Karima sai ta ambaci Innaye, ko kuma ta" "ambaci kirkin ƴan'uwansa. A cikin hirarsu har ta bashi labarin haɗuwarta na farko da Innaye, da yadda jininsu ya haɗu farat ɗaya. Amma ko da wasa bata bashi labarin yadda Bintu ta wulaƙanta Innaye a" wancan lokacin ba saboda gudun tayar da husuma tsakanin ma'aurata. "Sun yi hira na awa ɗaya cif bayan isarsu gidan Momy Sauda. Kamar bazai tafi ba, sai da Momyn ta kira" shi a waya tayi mishi tatas kan cewa baza ta yarda da irin wannan rashin adalcin tun yanzu ba. """Allah ya huci zuciyarki Mummy. Zan tafi yanzu, sai da safe. Gobe idan Allah ya kaimu da yamma zan" "zo...""" """Kar ma ka fara Hafiz, hira sau biyu a sati ya isa. Ga waya nan ku dinga magana, shi ɗin ma ban yarda ya" "wuce sau uku a rana ba. Ina fatan ka fahimce ni?""" """Na fahimta Mummy.""" Ya amsa a ladabce. Har ya kama hanya zai fita ta kira shi. """Da alama dai kun daidaita da ƙanwartaka. Zan tuntuɓeta yau da dare saboda gudun yin kitso da" "ƙwarƙwata. Idan ta tabbatar min da amincewarta kayi ƙoƙarin zuwa Faƙo cikin satinnan ka sanar da iyayenka halin da ake ciki, idan sun shirya ko zuwa watan gobe sai ka turo kawai ayi mai gaba ɗaya a wuce gurin. Nima nan zan sanar da iyayenta maza, tunda an fahimci juna kuma da sanayya ta ko wane" "ɓangare to gaskiya babu wani amfanin ɓata lokaci. Ko kana da wani shiri ne da kake buƙatar jinkiri...?""" """Ba ni da wani shiri Mummy.""" Ya katse ta da matsanancin farin ciki bayyane a fuskarsa. """Ai ni Wallahi ko gobe ne a shirye nake a ɗaura auren kawai a wuce gurin. Na gode Mummy. Allah ya" "ƙara girma.""" """Amin ya rabb! To ina fatan Bintu dai ta sani?""" "Ta sake jefa mishi tambayar, tare da ƙure shi da kallo tana ƙoƙarin karantar yanayinsa." "Ɗan shiru yayi yana sosa ƙeya, amma har lokacin fara'ar da ke fuskarsa bata ɓace ba. Can kuma sai ya ce" """Gaskiya bata sani ba Mummy... Amma zan faɗa mata. A daren nan ma in sha Allah zan sanar da ita." "Gobe idan naje Faƙo sai in sanar da su Baffa.""" """To madallah! Allah ya tabbatar mana da abinda yafi zama mafificin alkhairi. Ni dai don Allah ina" "roƙonka alfarma... A matsayinka na miji, kasan irin kalaman da za kayi amfani da su gurin faɗa ma Bintu al'amarin. Tsakani da Allah kishiya babu daɗi, amma tunda umarnin Allah S.W.T ne ba mu da yadda za muyi. Ka bi ta sannu a hankali, cikin tausasan lafuzza da ƙanƙan da kai. Sannan ka nusar da ita auro" "Karima ba shi ke nufin soyayyarta ya ragu a zuciyarka ba...""" "A matsayinta na Babba, haka ta sake ɓata wasu lokutan tana nusar da shi irin tausasan hanyoyin da zai bi" wajen sanar ma Bintu zai auri Karima. Bai bar gidan Mummy ba sai ƙarfe sha ɗaya na dare. Zuciyarsa cike taf da farin ciki. Yana tuƙi a hanyarsa ta komawa gida sai waƙe-waƙe yake saboda murna da yayi masa yawa. Ya ma rasa "wa ya kamata ya kira ya fara yi ma wannan daddaɗan albishir ɗin? Har ya ɗaga waya zai kira Zulai, sai ya ga dare yayi sosai. Sai kawai ya buge da kiran Ibrahim abokinsa ɗan gidan Abba Lurwanu yayi mishi" albishir. "Kamar yadda ya zata, Ibrahim ɗin yayi murna sosai da sosai. Don yana ɗaya daga cikin ƴan adawar Bintu," "masu nusar da shi tun a baya ire-iren kura-kuran da Bintun ke aikatawa amma sam idonsa ya rufe, ba ya ji ba ya gani saboda soyayya da ya rufe masa idanu." """Shi kenan! Ka ga yanzu za'ayi balancing, idan su Aunty Balira sun zo za su samu gurin da za a tarbe su" "da haba-haba babu wulaƙanci, tozarci, ko kyara.""" """Ƙwarai kuwa Ibbu""" Suna magana a waya Ibrahim ɗin yana ƙara bashi shawara kan kar ya kuskura ya haɗa Bintu da Karima gida ɗaya har ya isa cikin gidanshi. A lokacin sha biyu saura ƴan mintuna. Sallama yayi ma Ibrahim da cewar za su haɗu bayan ya dawo Faƙo su ƙarasa maganar ya katse wayarsa. "Yana shiga cikin falo ya tarar da Bintu zaune a kan kujera, idanunta ƙyam akan ƙofar shiga cikin falon" "tana jiran ganin ta inda zai ɓullo. Saɓanin ɗazu da ya barta sanye da kayan barci, yanzu ta ci kwalliya ne" cikin wata ƴar ɓingilar rigar mama da wata yaloluwar ɗan kamfai. Fuskarta da kwalliya raɗau kamar wacce take shirin zuwa gurin perty. "Ko kusa baiyi mamakin ganinta ido biyu ba, don yana daga cikin ɗabi'arta da ke faranta mishi rai duk inda" ya je in dai yana garin Abuja to Bintu ba ta taɓa kwanciya tayi barci sai ta jira ganin dawowarsa gidan lafiya. Abu ɗaya da ya ɗan bashi mamaki shi ne tattausan murmushin da ta fara watso mishi tun daga inda take "zaune, sannan ta miƙe tsaye cikin yauƙi da lanƙwasa, ta fara tafiyar mage tana wani yayyarfe yatsu tana" "karkaɗa mishi ƙirji, lokaci guda tana haɗawa da fari da idanu har ta ƙarasa inda yake tsaye ƙyam yana" kallonta. "Iya duniya aka ce ya fi iya mota, kamar dai ba Bintu ne suka rabu tana kuka shi kuma ya fita da ɓacin rai" "mai tsanani ba. Hannu ya buɗe mata yana mayar mata da martanin murmushi, ita kuma a slow motion" ta shige cikin ƙirjinsa. A tare duk su biyun suka sauke nannauyar ajiyar zuciya. "Basu tsaya a nan ba, kamar mayunwata haka suka kamo bakin juna suka fara tsotsa tamkar sun samu" "alawa. Tun daga nan bakin ƙofa, al'amura suka fara kankama, duk su biyun suka watsar da fushi da ɓacin ran juna suka cigaba da ƙoƙarin faranta rayukansu." Daga bisani dai can-cak Hafiz ya ɗauki Bintu suka haura sama. ******* "Hafiz ya riga ya karanci Bintu kamar yunwar cikinsa, ya sani tunda tayi alƙawarin yaye Aadil a washe" "garin ranar asabar, babu abinda zai sa ta fasa aniyarta." "Ya kuma sani tun da ta ambaci Ummanta ne za ta yaye shi, to tabbas gurin Ummanta za ta kai shi sai dai" duk abinda zaiyi ya daɗe baiyi ba. Da wannan dalilin yasa shi gwada mata babba babba ne. Kuma wanda ya riga ta kwana dole ya riga ta "tashi, duk sammakonta, shi a tafe ya kwana." "Suna idar da sallar asubah a masallaci, ko da ya koma gida ya tarar da ita har ta idar da sallah ta koma" "barci. Da wannan damar yayi amfani gurin aiwatar da shirinsa a gurguje, ko da ya shiga ɗakin Aadil, ga manyan jakunkuna nan har guda uku ta shaƙe da kayan sakawarshi da duk wasu abubuwan buƙatarsa. Don haka ɗauka kawai yayi ya fice da su ya zuba a boot ɗin motarsa. Ɗakinsu ya koma inda Aadil ɗin ke kwance can gefe guda a gadonsa yana barci cikin nutsuwa. Bismillah yayi sannan yasa hannu a nutse ya" ɗago yaron ya rungume a ƙirjinsa yana ɗan jijjiga shi don kar ya farka. Saɗaf-saɗaf ya fice daga ɗakin don kar ya tashi Bintu. Kuma wani ikon Allah shi ne duk yadda ta kasance ba ta da nauyin barci har Hafiz ya samu nasarar ficewa daga gidan Bintu ko ƙarar motarsa bata ji ba. "Sai da ya fara miƙar hanya sosai sannan ya ɗaga wayarsa ya kira Innaye, bayan sun gaisa, ya sanar da ita" "ga shi nan ya kamo hanyar zuwa Faƙo, kuma tafe yake da Aadil za ta yaye shi a can." """Ita Fatiman da hankalinta da nutsuwarta ta damƙa maka yaron da cewa ka kawo shi in yaye muku shi" "a nan?""" Tambayar farko da Innaye ta fara yi mishi kenan. "Har ya yi niyyar yanko ƙarya ya faɗa mata, sai kuma ya yanke shawarar gara ya faɗa mata gaskiya kawai," saboda gudun abinda zai je ya zo. """A'a Innaye! A matsayina na ubansa ni ne kawai nayi ra'ayin in kawo shi gurinki mahaifiyata ki yaye min" "shi...""" """Bazan karɓe shi ba.""" Ta katse shi cikin faɗa tun kafin ya aje numfashin maganarsa. Ta cigaba da magana muryarta na rawa kamar za ta saka kuka. """Yi sauri ka mayar mata da ɗanta. Idan ba haka ba Wallahi ko ka zo da shi wahalar banza kawai za ka yi" "don sai ka koma mata da shi.""" Ta ja numfashi sannan ta cigaba da cewa """So kake in karɓi ɗan ta ta zo ta tozarta ni a cikin jama'a sannan ta ɗauki ɗanta? Ita da kanta Bintun da" "take babba yaushe har ta iya sakin jiki tayi rayuwa a cikinmu ƙauyawa balle har tayi kuskuren bari ɗanta ƙwallin ƙwal ya rayu da mu? Dama yaya lafiyar giwa balle ta yi hauka? Mayar mata da ɗanta, in da rabon mu rayu da ƴaƴan binni zan rayu da na Zulai, na san Kamalu ko kyauta na ce ina so ya bani ɗansa bazai" "hana ni ba...""" Tsananin zafi da raɗaɗin da maganganun Innaye suka yi masa yasa bai san sa'adda ya katse wayarsa ba. "Gangarawa gefen titi yayi ya faka motar. Ya daɗe cikin shiru, zuciyarsa ba abinda take yi sai tafarfasa." Idanuwannsa ciccike da hawaye saboda irin baƙaƙen maganganun da Innaye ta yayyaɓa masa. Lokaci bayan lokaci yana waigawa kujerar baya ya kalli Aadil da yake kwance a ɗan gadonsa na cikin "mota, har wannan lokacin barcinsa yake yi hankalinshi kwance." 'Yanzu shi kenan Bintu ta gama cin galaba a kanshi? A matsayinshi na miji bai da iko da gida da iyalinshi "sai yadda Bintu ta tsara ko ba ya so haka za ayi? Yanzu yadda ya ɗauko Aadil haka zai mayar mata da shi yana ji yana gani sai dai ta kai shi gurin Ummanta?""" Bai taɓa shiga matsananciyar da-na sanin biye ma Bintu da yai ta yi irinna yau ba. Ba ma da na sanin biye "mata ba, a yau har da na sanin aurenta ya yi. Wane irin zamantakewa ne ace ƴan'uwa da iyayen miji ba" su da ikon zuwa gidanshi su sakata su wala yadda suke so? """Ya hayyu ya ƙayyum! Bi rahmatika astageethu, aslihlee sha'anee kullah, wala takilnee ɗarfata ayn""" "Ya faɗa a fili idanunsa a lumshe, zuciyarsa cike da sakankancewa da neman agaji." "Ya daɗe sosai yana maimaita addu'ar, har zuwa wani lokaci sannan ya buɗe idanunsa da suka canja launi" "zuwa jajaye. Amma a maimakon ya cigaba da tafiya da motar hanyar da zai fice daga Abuja, revers yayi," "ya miƙe hanyar komawa zuwa cikin gari, zuciyarsa babu daɗi ko kaɗan." ****** ****** "A karo na saba'in da biyu ta ɗaga waya ta danna kiran lambar Hafiz, amma wani abin takaici shi ne da" "kiran ya fara alamun zaiyi ringing, sai ya katse, sai su rubuta mata User busy. Bisa ga dukkan alamu Hafiz dai kulle lambarta yayi don kar ta same shi a waya." "Haushi da baƙin ciki yasa tayi cilli da wayar jikin bangon gado, a karo na biyar ta sake ɗora hannu bibiyu" akai ta fashe da wani ƙaƙƙarfan kuka kamar wacce aka isarwa da mummunan labarin mutuwar iyayenta biyu ta hanyar hatsarin mota. "Da madungure ta sauka daga kan gadon tana rusa kuka, takai gwauro ta kai mari a tsakiyar ɗakin. Duk" tunaninta shi ne ya ƙuƙe ne akan ina Hafiz yake haramar kai mata ɗanta Aadil? Tun bayan da ta farka daga nannauyan barcin da ya kwasheta da misalin ƙarfe takwas da minti ashirin na "safe, ta shige bayi tayi brush. Ko da wasa hankalinta bai kai kan gadon Aadil ba balle har ta fahimci ba ya" "kwance a ciki sai bayan da ta fita zuwa ƙaramin kicin ɗinta na sama, ta haɗo tea ta koma ɗakin tana kurɓa a hankali saboda wani masifaffen yunwa da take ji kamar anyi mata yasa a cikinta." Tunda ta leƙa harabar tsakar gidan taga babu motar Hafiz ta san ya wuce Faƙo kamar yadda ya saba duk ranar asabar. In dai ba ita ta ɗaga Aadil daga kwance ba tayi mishi wanka yana kai misalin ƙarfe goma zuwa goma da rabi na safe yana barci. Shi yasa hankalinta bai kai kan ba ya cikin gadonsa ba. "Sai da ta gama shan tea, ta mayar da kofin kicin, ta koma cikin ɗakin ta shige banɗaki ta haɗa ma yaron" "ruwan wanka. Tana yaye net ɗin saman gadonshi da niyyar ɗaukan yaron sai taga wayam. Da farko ta zaci idanunta ne ke mata gizo, don haka sai ta ɗan mutsittsika idanunta don su ƙara washewa. A lokacin ne fa ta tabbatar ba ya nan. Ai a sittin ta fice zuwa ɗakinta inda ta haɗa kayayyakin Aadil. Suma suka ce" ɗauke mu inda kika ajiye. "Da yake ta san yadda suka rabu da Hafiz ɗin a daren jiya, bata tsaya wani raba ɗaya biyu ba ta san Hafiz" ne ya shammaceta ya ɗauke mata yaro. """Kan ubancan kayyasa. Ni Hafiz zai shammata? Na rantse da girman Allah yadda ka ɗauke shi ka tafi da" "shi kai da ƙafafunka za ka dawo da shi, zan ga ƴar iskar tsohuwar da take da ƙwarin gwuiwar riƙe min ɗa a ƙauyen ƙayau idan ita ce tayi min naƙuda ta haifo min shi.""" "Tayi maganganun cikin masifa da bala'i, bakinta har tartsatsin miyau yake yi don tashin hankali." "Da farko har za ta bari ya isa sannan ya dawo mata da ɗanta, domin tana da tabbacin in dai Innaye da" ƴaƴanta ba giyar wake suke sha ba baza su riƙe mata ɗa a ƙauye ba. Can kuma sai taga ai idan ta bari Hafiz ya tafi da Aadil ya wuni mata da ɗa a ƙauye ba tare da amincewar ita uwar ɗan ba ai ya gama cutar "da ita, cutarwa ta ƙarshen-ƙarshe." Don haka afujajan ta koma ɗakinsa inda tayi barci ta ɗauki wayarta akan durowar bedside ta lalubo lambarsa ta fara danna mishi kira. Zuciyarta cike da alwashi iri-iri da barazana da rantse-rantsen da za "tayi mishi kan idan bai dawo mata da yaronta yanzu-yanzu ba za su samu mummunar saɓani, irin saɓani da balbalin bala'in da bai taɓa tunanin za su samu ba a tarihin rayuwar aurensu." "Sau uku kacal ta samu nasarar kiran ya shiga bai ɗauka ba, tun daga waɗannan ukun, duk sadda kiran" yayi kamar zai shiga sai a saka mata user busy. "A cikin daƙiƙu sittin da suka biyo baya, ta yi kuka, ta yi kuka, irin matsanancin kukannan da tunda uwarta" ta haifeta bata taɓa yin irinshi ba. Domin a wannan lokacin zuciyarta ta fara tunanin idan su Baffa suka riƙe Aadil a can Faƙo kamar yadda Hafiz yake so ya za ta yi? Cikin kuka da majina ta fara rantse-rantse tana shan alwashi... """Na rantse da girman Allah... ko sun riƙe shi gobennan zan yi sammakon tafiya in karɓo ɗana, in sama" da ƙasa za su haɗe Wallahi Tallahi sai sun ba ni yarona. Idan kuwa sun ƙi ko da ƴan sanda da sojoji ne sai "na je na amso yaro na, duk abinda zai faru ya daɗe bai faru ba...""" "Kamar a mafarki sai taji Mai gadi yana buɗe get ɗin gidan, da saurin gaske ta matsa jikin window," "zuciyarta cike da fatan Hafiz ne ya canja ƙudurinsa ya dawo mata da ɗanta, duk da wani sashe na zuciyarta na faɗa mata abu ne mare yiwuwa Hafiz ya fasa ƙudurinsa a sauƙaƙe." Ƙuri tayi da idanunta jikin motar da take shigowa sannu a hankali har ta ƙarasa shigowa tsakar gidan. "Nannauyar ajiyar zuciya taja ta sauke, motar Aminiyarta Raudha ce." Tana nan tsaye a jikin window har Raudha ta gama daidaita fakin ɗin motar ta kashe ta fita. Hakan yasa "ta saki labulen windon ta fice daga ɗakin da sassarfa, zuciyarta na ƙara ɗugunzuma." "Kamar an buɗe famfo sabbin hawaye suka sake ɓalle mata, haka ta sauka ƙasa ta tari Raudha a falo" "fuskarta kaca-kaca da hawaye, ga idanunta da suka kumbura suka canja launi saboda tsabar daɗewa tana rusa kuka." """Raudha... Hafiz ya kashe ni...""" "Kalaman da ta fara faɗa ma Raudha kenan cikin matsanancin kuka da rawar baki, bayan ta ruƙunƙumeta" a tsakiyar falon. Ita kuwa Raudha ga tsammaninta Bintu ta gano Hafiz yana soyayya da Karima ne. Daman kuma takanas- ta kano abinda ya kawo ta gidan kenan ta faɗa mata. Ashe kaya ne ya tsinke a gindin kaba. Don haka sai cewa tayi """Uhmmm! Kaɗan daga cikin halin maza kenan! Ai da can da muke faɗa miki ba cewa kika yi Hafiz ya" "sha ban-ban da sauran maza ba? Yanzu wa gari ya waya Bintu?""" "Bintu dai ba baka sai kunne, illa iyaka ma sai ƙara ƙarfin kukanta take yi tana rerawa kamar tashin jiniyar" motar ƴan sanda. Da fuska mai cike da tausayi Raudha ta riƙe kafaɗar Bintu taja ta suka zauna a kujera mazaunin mutum "uku, a tausashe ta ce" """Kiyi haƙuri Bintu! Na san abin da ciwo to amma ya kika iya da abinda ya gagari wuta? Kukan nan da" "kike ta rusawa sam ba mafita ba ce. Idan ma za kiyi shiru mu nemi mafita gara kiyi shiru. Yanzu ina shi Hafiz ɗin?""" """Ya tafi da shi fa Raudha... Ya tafi da shi... Ni babban damuwata idan Aadil ya farka bai ganni ba kuma" "bai ga Umma ko Mashku ba wane irin firgita da tashin hankali zai shiga? Na rantse da girman Allah akan ɗaukar min ɗa da Hafiz yayi ya tafi da shi wannan tsinannen ƙauyen ba tare da izinina ba sai munyi gagarumin tashin hankali da shi.""" Galala Raudha tayi da baki tana kallon Bintu ba tare da ta gane maganganun da take yi ba. Ganin dai ta kasa raba ɗayan biyu yasa ta cewa """A'a! Wai tsaya Bintu, akan me kike magana ne?""" Ba tare da damuwa ko tuhumar irin maganganun da ita Raudha ta fara yi ba Bintu ta kora mata bayanin duk halin da ake ciki na tafiya da Aadil yaye gurin Innaye. """Kam bala'i!! Amma gaskiya Hafiz ya gama raina ki Bintu. Ko da yake ni banga laifin Hafiz ba sai na ki," tun farko ke ce kika ba shi yarda ɗari bisa ɗari shi yasa har yaga wallenki ya fara gara ki yana wulaƙanta "ki yadda yake so.""" Raudha ta faɗa cikin tsantsar takaici da baƙin ciki. Kafin Bintu ta ce wani abu ta cigaba da cewa """Saboda in dai ba burin ya wulaƙantaki ya tozarta ki ba ta ya za'ayi ya ɗauki kyakkyawan yaro ajebo irin" "Aadil kuma ɗan shekara ɗaya kacal ya kaishi wannan ƙazantaccen ƙauyen na su? Wannan burin kashe miki ɗa kawai yake da shi. Idan kuwa kika bari kuka cigaba da tafiya a haka! Na rantse da Allah sunanki sorry...!""" Maganganun Raudha babu abinda suke ma Bintu illa ƙara tunzurata. Shi yasa hawaye ya ƙi tsayawa a "idanunta, ga wani fitinannen ciwon kai da ya addabeta amma don tsananin baƙin ciki da takaici ta kasa" daina kuka. "Sai da Raudha ta gama ziga Bintu iya ziga, sannan ta fara rarrashinta da cewar ta adana kukanta ya isa" "haka. Kawai ta jira dawowar Hafiz suyi duk wacce za suyi, amma tana ƙara jaddada mata ko sama da ƙasa za su haɗe kar ta kuskura ta bar Aadil ya kwana biyu a ƙauyen Faƙo." "Wannan tashin hankali da Raudha ta tarar da Bintu a ciki, shi ya hana ta faɗa mata maganar Karima da" Hafiz. Tsoronta ɗaya kar Bintu ta sume mata idan ta ji labarin tashin hankalin da ya ninka maganar kai Aadil Faƙo. Ko a yanzu ba ƙaramin tsorata tayi ba da wani irin numfarfashi da Bintun take ja akai-akai kamar mai "cutar athma. Shi yasa ta ƙara ɓata lokaci tana rarrashinta da tausasan kalamai, ta gyara mata ɗakunan sama kafin isowar Baba Rabi." "Bata bar gidan ba sai da ta tabbatar Bintu ta ɗan samu nutsuwa kaɗan, ta sha paracetamol ta kwanta" "barci. Sannan ta samu ƙwarin gwuiwar barin gidan jikinta a sanyaye, zuciyarta cike da tausayin ƙawartata" da sai a yanzu ne namiji ya fara buɗa mata shafi-shafi na munanan halayensa. "Babban fatanta ɗaya shi ne, Allah ya ba Bintu ikon fige wannan kazar wahalar a sauƙaƙe. Domin ita" "shaida ne, duk abinda zai biyo ta kan soyayyar da Bintu take ma Hafiz ba ta ɗaukar shi da sauƙi balle har tayi gangancin ɗaukarshi a wasa. Yarda take da shi mai girma akan irin son da Hafiz yake mata, da wanda ita take mishi, babu kunya babu tsoron Allah take bugun ƙirji a cikin ƙawayensu tana tutiyar mijinta ya" fita daban da sauran gama-garin mazaje. Tsakani da Allah ta fara tausayin Bintu. Har ta isa gidanta zuciyarta cike take fal da tunanin mabanbantan hanyoyin da za ta bi wajen taimaka ma "Bintu da dukkan ƙarfinta da dabararta. Domin Bintu ta yi mata halarci mai yawa a rayuwa, baza ta taɓa mantawa da taimakon Bintu gare ta ba har zuwa wannan matsayi da take kai a yanzu, sakamakon kyautatawa kuwa kyautatawa ce." ******* "Saboda tafiyar da baiyi da wuri ba, kuma ko da ya isa can Faƙo ma bai fito da wuri ba. Ya isa gida ne da" misalin ƙarfe goma sha ɗaya da minti biyar na dare. Kallo ɗaya za'ayi mishi a fahimci tabbas a jigace yake. "Ga wahalar hanya, ga wahalar tuƙa mota kuma tafiya mai nisan gaske, abinda ya daɗe baiyi baiyi ba." "Ko a yanzu don direbansa ba ya nan ne, ƴarsa ta cikinsa Allah yayi ma rasuwa bagatatan a garin Suleja." "Dole suka tafi da Hafiz yayi ma iyalanshi gaisuwa, yayi musu sha tara ta arziki sannan ya tuƙa motar da" kansa ya koma Abuja. "Duk da dare ne, tsakar gidan ko ina haske ne tar kamar rana, saboda wadatattun ƙwayayen lantarki" masu haske sosai da aka maƙala guri-guri a tsakar gidan. Duk da tsarabobin da su Innaye suka haɗa mishi a cikin mota ya kasa ɗaukar komai. Wayarsa kaɗai ya iya "ɗauka sai makullin motarsa da ya zare ya nufi babban falonsu. Sannu a hankali yake tafiya saboda gajiya, yana isa bai tsaya wani ɓata lokaci ba ya murza hannun ƙofar ya cusa kanshi cikin falon." "Kiciɓus suka yi da Bintu, wacce duk wannan dare da ya fara tsalawa idanunta biyu. Tsayuwar motarsa a" "tsakar gidan yasa ta ɗauki hijabi ta saka ta sauko ƙasa zuwa falon a gaggauce, ba don komai ba sai don" zakwaɗin ganin shin Hafiz ya dawo mata da Aadil? Ko kuwa su Innaye sun shirya tarbar bala'i da masifarta ne yasa suka yi gangancin riƙe mata ɗa? "Abu na farko da ta fara yi shi ne kallon hannayensa, ganin wayam! yasa ta jefa mishi tambaya da murya" mai cike da tartsatsin tashin hankali ba tare da ko sannu da zuwa ta samu sararin furta mishi ba. """Hafiz ina ka kai min yaro na?""" "Da yake Hafiz ɗin namijin duniya ne, ko kallonta baiyi ba. Sai ma hannunsa da yasa a hankali ya matsar" "da ita gefe ɗaya, saboda bake-bake tayi a gabansa ta tare masa hanyar shiga cikin falon." "Da yake a cikin bala'i take, sam bata lura da yanayin da yake ciki ba. Don haka da saurin gaske ta sake" shan gabansa ta ƙara bake-bake har da riƙe ƙugu. Bakinta har yana tartsatsin miyau saboda masifa ta cigaba da cewa """Babu inda zan matsa, na rantse da Allah babu inda zan matsa sai ka faɗa min in da ka kai min ɗan" "jaririn yaro na...""" """Bintu...!!!""" Ya ƙwalla kiran sunanta da wani irin tsawa mai taratsi da barazanar fasa mata dodon kunne. Duk turjewa da daurin zuciyarta bata san sa'adda ta ɗan ja da baya ba saboda firgitan da tayi. A ɗan "tsorace ta ɗaga ido tana kallonsa, sai a lokacin ta lura da yadda ƙwayoyin idanunsa suka kaɗa suka yi jajur, kamar ba nashi ba." Da wata irin gwarjejiyar murya mai cike da fitina ya ce """A yau! Ke Bintu kin ci albarkacin rayuwar mutane uku mafiya muhimmanci a gare ni. Na rantse da" "Wallahi! Tallahi!! Billahi!!! Ba don waɗannan mutane uku ba da yanzu tsakanina da ke wani mummunan zance ake yi ba wannan ba. Don haka, ki matsa ki bani hanya in shiga ciki salin-alin ba tare da wani tashin-tashina ba. Idan kuma kin shirya taron Aradu da ka, don Allah ki sake yunƙurin tare min hanya" "Bintu.""" Duk yadda ta shafe tsawon yinin tana shan alwashi kan irin balbalin bala'in da za ta sauke mishi idan ya "dawo gidan ba tare da Aadil ba, ta rasa dalilin da yasa maganganunsa suka yi ma sassan jikinta wani irin dukan da yasa lokaci ɗaya tayi laƙwas! Ba ma kamar waɗannan manyan rantsuwa uku da ya jero mata a lokaci ɗaya. Duk da bata gama fahimtar inda maganganunsa suka dosa ba lallai jikinta yayi mutuwar da" yasa lokaci ɗaya ta nemi duk wani bala'i da masifa da ta yini tana ji da su ta rasa. Ita da kanta ta ƙara janye jikinta daga kan hanya. Shi kuma ya shiga cikin falon da wani irin taku na cikakken namiji ya nufi hanyar da zai hau sama ba tare da yayi mata kallo na biyu ba. Saboda wani irin baƙin Bintu da yake gani. "Bayan shigarsa cikin ɗaki, wayar hannunsa da makulli kawai ya ajiye ya faɗa banɗaki. Cikakkun mintuna" "ashirin da biyar ya ɓata yana gasa jikinsa da ruwan zafi kafin ya fito, jikinsa sanye da rigar wanka." "Wasu mintuna goma sha biyar ya sake ɓatawa gurin shafa mai, shirin barci, ya fesa daɗaɗan turarukansa" masu sanyin ƙamshi sannan ya ɗauki wayarsa ya bi lafiyar gado. "Ba tare da duba tsalawar da dare ya fara yi ba ya lalubo lambar Zulai, ya tura mata ɗan gajeren saƙo mai" ɗauke da kalaman godiya da addu'ar Allah ya ƙara danƙon zumunci a tsakaninsu. "Bayan saƙon ya tafi ajiye wayar yayi, ya janyo lallausan bargon ya lulluɓa har zuwa saman ƙirjinshi. Luf" yayi akan filo ya lumshe idanu yana tunanin abinda ya faru bayan Innaye ta tabbatar mishi baza ta karɓi Aadil ta yaye shi ba. "Har ya kama hanyar komowa gida, zuciyarsa cike da shan alwashin yadda Innaye bata karɓi Aadil yaye ba" "itama Bintu bata isa ta kai shi gidan Ummanta ba. Sai dai ta yaye shi ita da kanta a gidansu, idan kuma ba haka ba to saidai ta cigaba da bashi nono har zuwa sadda shi da kanshi Aadil ɗin zai yaye kansa." "Har ya kusa isa gida sai ga kiran Zulai ya shigo cikin wayarsa, karo na farko tun bayan da tayi aure." """Yaya... Yanzu muka waya da Innaye ta ke cemin za ka je Faƙo yau. Don Allah idan baka yi nisa ba ga" "saƙo ka tafi mata da shi. Nima da yau za mu je, sai kuma bagatatan tafiya ta kama Abban Imam. Allah" "yasa dai baka yi nisa ba.""" """Ban yi nisa ba Zulai. Na juyo ne, yanzu haka ma gani na kusa isa gidana...""" Ya amsa mata da cusasshiyar murya mai bayyana damuwa ƙarara. """Toh fa!! Lafiya? Me yake faruwa?? Ko ka fasa tafiyar ne???""" "Ta tambaye shi cikin sanyin murya, zuciyarsa cike da tunanin me ke damunsa haka? Duk lalacewar" "ɗan'uwa ɗan'uwa ne, lokaci ɗaya ita ma Zulaikha ta ji ta shiga cikin damuwa. Duk da bai faɗa mata abinda ke damunsa ba." """A'a! Ba fasa tafiyar nayi ba...""" """To ko baka da lafiya ne?""" Ta sake katse shi da tambayar tun kafin ya aje numfashin maganarsa. Da yake zuciyarsa cunkushe take da damuwar da shi kanshi ya san tabbas yana buƙatar abokin tauna "wannan damuwa. Kuma ƙarin shawara daga wani ɓangare na zuciyarsa da ta tunasar da shi mai shawara fa aikinsa ba ya ɓaci, sai dai ace yana da ƙarancin sirri. Waɗannan dalilan guda biyu suka ja mishi gora" wajen zaiyane ma Zulai duk halin da yake ciki. Da takaicin munanan halayen Bintu a muryar Zulaikha ta ce """Lallai ma Innaye. Ita Bintun wacece da har za'a ji tsoron riƙe ɗan da ake da tabbacin ba nata ne ita" "kaɗai ba? Allah yasa dai baka yi gaggawar mayar mata da Aadil ɗin ba?""" """Ban mayar mata da shi ba. Amma ga ni a hanya zan mayar mata da shi. Ya zanyi Zulai? Dole in mayar" mata da shi tunda dai ba ni da mai riƙe min shi... Ke dai kin san tunda Innaye ta ce baza ta riƙe shi ba cikin su Aunty Balira ma babu wacce za tayi gangancin riƙe shi. Balle ma yadda baƙin halin Bintu bai "tsallake kowa ba...""" """Duk da haka dai Yaya... Ai hannun mutum bai taɓa ruɓewa ya yanke ya yar! Ni idan baza ka damu ba" "ka kawo min shi in yaye.""" Saboda tsabar yadda maganarta ya dake shi bai san sa'adda ya taka burki da ƙarfi ba. In da Allah ya "taimake shi shi ne a lokacin ya shiga cikin layinsu, da a kan babban titi yake irin wannan burki da ya taka na ba zato babu abinda zai hana motar bayanshi ta buga mishi." "Da saurin gaske ya gangara gefen hanya sannan ya kashe motar, bakinshi na rawa ya jefa mata tambayar" """Me kika ce Zulai?""" Dariya tayi sannan ta sake maimaita mishi abinda ta ce. """Amma don Allah da gaske kike yi Zulai?""" "Ya sake tambayarta da wani irin yanayi ɓoyayye, shi ba farin ciki ba shi kuma ba baƙin ciki ko fargaba ba." """Wallahi da gaske nake yi. Amma idan baka amince ba sai in haƙura...""" """Na amince. Wallahi yanzu zan kawo miki shi Zulai. Na gode. Na gode. Allah ya saka miki da alkhairi" "yayi miki albarka. Ga ni nan zuwa.""" Bai jira cewarta ba ya tayar da motar da sauri yayi revers ya miƙe hanya. Fuskarsa bayyane da matsanancin fara'a zuciyarsa tumbatse da nutsuwa. "Har ya yi nisa sosai a hanyarsa ta zuwa gidan Zulaikha, sai kuma ya tuna ai duk wannan budurin da suke" yi shi da Zulai basu sako mijinta Kamal a ciki ba. Kuma tsakani da Allah in dai shi matsayinsa na babba yana da lafiyayyen hankali ya kamata ya tuna yanzu fa ba kamar da bane. Hatta Innaye da take kamar mahaifiya ga Zulai Kamal ya fi ta iko da Zulai. "Jikinsa a sanyaye ya ɗauki wayarsa ya buɗo lambar Zulai ya danna mata kira. Yana shiga ta ɗauka, abinda" ta fara tambayarsa shi ne """Yaya ka ƙaraso ne?""" """A'a!""" Ya amsa mata. Sai kuma ya ɗanyi shiru kafin ya cigaba da cewa """Zulai kar inyi aikin marasa hankali. Kina ga Kamal zai amince a haɗa Amaryarsa da raino alhalin ba" "haihuwa tayi ba?""" "Dariyar da Zulai ta ƙyalƙyale da shi yasa shi ma ya ɗan saki dariyar, amma jikinsa a sanyaye." """Allah da gaske nake yi. Kin san fa Aadil har yanzu jariri ne. Shekararsa ɗaya ne kacal saboda tsabar" "fitina irinta Bintu ta tsiro da zancen yaye shi.""" Ajiyar zuciya Zulaikha ta sauke bayan ta tsagaita da dariyar da take yi. """Kar ka damu Yaya! Ko ba ya tafiya za ta iya yaye shi a shekara ɗayan balle kuma yana tafiyarsa ko ina." "Batun Abban Imam kuma ka kwantar da hankalinka, sam ba shi da matsala. Ko rantsuwa nayi babu kaffara bazai taɓa yunƙurin hana ni duk wani abu da ya shafi ƴan'uwana ba, saboda ya san muhimmancinsu a gare ni. Ta gwaɓa mishi magana da gan-gar. Kuma yau ɗinnan yayi tafiya, zai ɗauki tsawon sati shida acan. Anjima nima zan tattara ƴan abubuwan buƙata ne in koma gidan Mummy... ka" "san ta kuma ba ta da damuwa.""" """Haka ne! To ga ni nan zuwa.""" Ya amsa da sanyin jiki yana jinjina maganar da ta gwaɓa mishi a zuciyarsa. "Yana isa gidan Zulaikha, Aadil ya farka da wani irin gigitaccen kuka kamar wanda aka sa mishi wuƙa a" wuya. Da wannan dalilin yasa Hafiz yana shiga da motarsa harabar gidan ko gama daidaita fakin baiyi ba ya sungumi ɗan hankalinsa a tashe ya nufi babban falon gidan. Sau biyu ya ƙwanƙwasa bai jira an buɗe masa daga ciki ba ya fara murza hannun ƙofar yana ƙwalla kiran Zulai hankalinsa a tashe da irin kukan da yaron yake yi. Shi daman ba irin mutanen nan bane masu "masifaffen son yara, duk yadda suke dariya da Aadil da zarar ya fara kuka zai miƙa ma Bintu shi." "Daga can cikin falon, a gigice Zulai ta ƙarasa sako hijabinta tazo ta buɗe mishi ƙofa. Bai saurari kalaman" barka da zuwa da take furta mishi ba ya fara miƙa mata Aadil da har wannan lokacin yake tsula kuka. """Ɗan tsaya mana Yaya.""" Tayi maganar a nutse. A hankali tasa hannunta na dama ta ɗaga fuskar Aadil tasa idanunta a cikin na shi. Daƙiƙu goma bayan "nan sai ta haske yaron da lallausan murmushi, sannan ta ɗaga hannuwanta biyu ta miƙa mishi alamar ya" zo. "Tun Zulai tana ƙarama, ba sau ɗaya ba sau biyu ba Hafiz ya sha ji Innaye tana yi ma Zulai kirari da mai" "baiwar iya sarrafa ƙananun yara. Duk irin ƙwuiyar yaro da fitinarsa sai dai idan Zulai bata so ƙulla harƙalla da shi ba. In dai zuciyarta na son ɗa, to fa ko ke uwar ɗan sai dai kiyi haƙuri, domin idan za ta jera wata guda tana zuwa ɗaukar ɗa ko ƴa zuwa gidansu ana hana ta baza ta taɓa gajiyawa ba. Idan kuwa har yaro" ya saba da ita to fa uwa da kanta za ki ji tana aika ma da Zulai yaron ko bata je ɗaukarsa ba. "A wancan lokacin, bai ɗauka baiwar na ta ya kai yadda Innaye take kururutawa ba sai yanzu da yaga ikon" "Allah. Aadil da kanshi ya miƙa ma Zulaikha hannu ta ɗauke shi. Ƙarin mamakin kuma yana zuwa jikinta ya kwantar da kanshi a kafaɗarta, sannu a hankali yake rage ƙarfin kukansa har zuwa sadda yayi ɗif! Kamar anyi ruwa an ɗauke." Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke na samun kwanciyar hankali. Godiya ya fara yi mata haɗe da kyawawan addu'o'i. """Na gode Ƙanwata. Ubangiji ya baki duk abinda kike nema duniya da lahira. Allah ya jiƙan mahaifanki" "da gafara.""" """Amin thumma Amin.""" Ta amsa addu'ar da murmushi a fuskarta. """Ya yi break fast ne a gida?""" Ta tambayeshi kafin ya ƙara cewa komai. """A'a! Tun misalin ƙarfe uku na dare dai Mamanshi ta bashi nono, daga nan barci yake ta yi sai yanzu ya" "farka.""" """To ba damuwa. Yanzu dai shigo min da kayayyakinshi, ina zuwa.""" "Ko kafin ya gama shigo da kayayyakin, Zulai ta haɗa tea mai kauri da zallar madarar peak ta 1,2,3 wanda" "take ma Imam amfani da shi idan ya je gidan ta zuba milo ba tare da ta sa suger ko ɗigo ba ta fara ba Aadil da ɗan ƙaramin cokali, yana sha tana mishi ƴan waƙe-waƙe da wasanni." Cikin ƙanƙanin lokaci sai ga yaron yana ƙyalƙyala dariya. Sai da ya ƙoshi taf sannan ta surka ruwa tayi "mishi wanka fes! Kafin Hafiz ya bar gidan, har Aadil yayi barci goye a bayan Zulai, abinda sam bai samu ba a gurin Mamanshi wai don tsoron kar tsayayyun nonuwanta su faɗi." "Ganin ƙarfe goma sha ɗaya saura mintuna kaɗan yasa Hafiz miƙewa tsaye, sai da ya gama kai saƙonnin" Zulaikha da zai tafi ma da Innaye cikin mota sannan ya koma a tsaitsaye ya bata abinda ke tsakaninshi da Kareema. "Tsananin murna da mamakin lamarin yasa bakin Zulaikha ya ƙi rufuwa, ta kasa cewa komai, har ya gama" yi mata ƙarin bayanin cewa """Wannan dalilin ne yasa komai rana in sha Allah zan tafi Faƙo ayau ɗinnan. Domin gobe da wuri nake" "so su Baba Abubakar su shigo su samu Abba Lurwanu aje wajen iyayenta maza. Tunda dai Mummy ta bani dama gaskiya ba na son a ɗauki wani lokaci mai tsawo ba tare da anyi komai an wuce gurin ba.""" """Uhmmm! Ai ni na ma kasa magana Yaya. Allah ya tabbatar da alkhairi. Lallai ma Aunty Kareema, wato" "shi ne ana ta kwasar love da Yayana ko a gista min...""" """A'a kar ki ga wani laifin Ƙurratul-Ayni.. Ni ne nan na umarceta tayi shiru da bakinta har sai lamarin ya" "fara nuna. Yanzu da ya kamata ki ji ba ga shi na faɗa miki ba?""" Ya ɗauki laifin komai ya jibga ma kansa don kawai ba ya so a ƙullaci rabin ransa. Ita dai Zuly ta kasa daina dariya... Abubuwa da yawa ne suka haɗe a zuciyarta. """Amma kuwa Bintu ta sani Yaya?""" Ta tambaye shi tana hasashen irin tashin hankali da haukar da Bintu za tayi idan ta ji irin gagarumin tashin hankalin da ke tunkaro ta. """Bata sani ba. Amma zan faɗa mata idan na dawo.""" Ya amsa a lokacin da ya kama hanyar fita daga falon. "Sallama suka sake yi, tayi mishi addu'ar Allah ya tsare ya kiyaye hanya sannan ya fice daga cikin falon." Tana tsaye jikin window tana hangenshi har maigadi ya buɗe mishi ƙofa ya fice daga gidan. "Labulen windon ta saki, ta koma tsakiyar falon sannan ta saki wata ƙaƙƙarfar dariya da yasa Aadil da ke" "bayanta motsawa kamar zai tashi, da sauri ta toshe bakinta don rage ƙarfin dariyar tana haɗawa da ɗan jijjiga shi." """Bintu ruwa ya ƙare ma ɗan kada bai gama wanka ba, daɗina da gobe saurin zuwa...""" Ta sake ƙyalƙyalewa da dariya a hankali don kar ta tashi Aadil. Zuciyarta cike da wani irin farin ciki mara misaltuwa. ****** "Ƙarfe biyu da ƴan mintuna na tsakar rana ya isa Faƙo. Kamar ko wane lokaci, haka ƴan'uwa da abokan" arziki suka tarbe shi da matsananciyar murna. Shi kuma ya buɗe bakin aljihu kamar yadda ya saba yayi musu yayyafin alkhairi. "Daƙyar ya samu ya ƙwaci kansa suka keɓe da mahaifansa, bayan sun sabunta gaisuwa ne yake sanar da" su muhimmin abinda yake tafe da shi a wannan rana. Wani abu da ya lura da shi shi ne daga Innaye har "Baffa farin ciki ya gaza ɓoyuwa a fuskokinsu daga jin wannan labarin, wannan shi ya ƙara tabbatar mishi lallai baƙin ciki da takaicin munanan halayen Bintu ya daɗe yana damun iyayensa." Tambaya ɗaya da Baffa yayi mishi shi ne """Ka faɗa ma Alhaji Lurwanu?""" """Ban riga da na faɗa mishi ba Baffa. Amma ina komawa gida in sha Allah ayau zanyi ƙoƙarin sanar da" "shi.""" Ya amsa kanshi yana ƙasa. """Lallai ya kamata ka sanar da shi da gaggawa, saboda kar su Abubakar su je ya zama ya ji labari daga" "bakinsu, ka ga idan aka yi hakan ba'a kyauta ba.""" """In sha Allah zan faɗa masa ayau Baffa.""" Bayan sun gama magana da su Innaye ya fita da nufin zuwa gidan Anty Balira ya gaishe ta. Wani arashi da ya tarar shi ne acan ya tarar da Aunty Rakiya da Aunty Ladidi sun je gaishe da Aunty Balira da tayi zazzaɓi kwanaki biyu da suka wuce. "Farin ciki sosai ya bayyana a fuskokinsu, sa'ilin da suka gama gaisawa yake faɗa musu zai auri Kareema" "ƙanwar mijin Zulai. Addu'o'i kyawawa da fatan alkhairi suka yi mishi, sannan Aunty Balira ta tashi ta zagaya banɗaki." "Kuma kun san irin banɗakunan da ake yi a ƙauye, can nesa da ɗakunan gida ake yi saboda masai ne ake" yi na gargajiya. """Haba! Ko kai fa Hafizu? Amma me ake da mace mai mugun baƙin hali da kafirin munafunci da kissa" "irin Bintu?""" Kalaman da suka fara fita daga bakin Aunty Rakiya kenan bayan ta tabbatar Aunty Balira ba ta jin me take cewa. Nan fa kamar an matsi bakunansu su biyun suka buɗe baki suka dinga kora ma Hafiz labarin irin cin kashin da Bintu tayi ta musu ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba. Amma saboda tsabar munafunci idan yana gurin sai ta dinga musu haba-haba kamar za ta haɗiye. Suman zaune kawai Hafiz yayi yana jin waɗannan baƙaƙen labarai masu barazanar fasa mishi zuciya. "Tabbas idanunshi sun buɗe, kuma ya fahimci kissa da munafuncin Bintu, amma bai taɓa tsammanin ta daɗe tana wasan kwaikwayo da fahimtarshi har na tsawon lokaci haka ba." Bai ƙara shiga cikin tashin hankali ba sai da Aunty Ladidi ta ce """Ni fa duk waɗannan munanan halayen nata abu ɗaya da idan na tuna har yanzu yake min ciwo a" "zuciya shi ne yadda da gangar ta so kashe Innaye... Yo ta so kashe ta mana. Tunda ai likitan nan na asibitin Nasin Ham (Nursing home) Ya faɗa ma Aunty Balira cutar da ke damun Innaye daban magunguna da alluran da aka yi ta zurkuɗa mata daban, har ya ƙara da cewa lallai duk likitan da ta ba" "Innaye waɗannan magungunan ta so kawai ta illata ta ne...""" """Waɗanne irin zantukan banza ne kuke faɗa ma Hafizu haka Rahina?""" Aunty Balira ta katse ta cikin tsawa da ɓacin rai. "Firgigit suka yi duk su biyun, sai a lokacin suka dawo hayyacinsu suka lura da wasu zafafan hawaye da ke" "kwaranya a idanun Hafiz. Duk da sun san gaskiya suke faɗa, sai kuma jikinsu yayi sanyi ƙalau da ganin irin" hawayen da ke gudu akan fuskarsa. "Faɗa Aunty Balira ta rufe su da shi ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, a ƙarshe ta ce su ɓace mata" da gani tunda su ba su da hankali suna so su shiga tsakanin mata da miji. "Sum-sum suka saka hijabansu suka fice daga ɗakin, jikinsu sanyi ƙalau, kamar an sheƙa musu ruwan" sanyi. Kusa da Hafiz Aunty Balira ta zauna ta fara rarrashinshi da tausasan kalamai. Duk da ta nuna ɓacin ran abinda su Rakiya suka yi amma ko kaɗan bai ji ta ƙaryata maganganun da suka faɗa mishi ba. Sai da ta daɗe tana rarrashinshi sannan daƙyar ya tsagaita sharɓen hawayen da yake yi. Ya ɗaga kanshi yana kallonta da idanunsa jajaye ya ce cikin rawar murya """Amma... Amma... me yasa baku taɓa ankarar da ni ko ku fito ƙarara ku faɗa min irin abubuwan da ke" "faruwa ba...?""" """Ta ina za mu samu ƙwarin gwuiwar faɗa maka Hafizu bayan duk mun fahimci irin son da kake mata," "sannan mun ga yadda idanunka suka rufe ruf a kanta. Ca nake don a sama maka sauƙi ne Baffa ya ɗauki Zulai sukutun da guda ya aura maka amma ka watsa masa ƙasa a ido?""" "A karo na biyu duƙar da kanshi yayi ya cigaba da sharɓen hawaye, a zuciyarsa yake tuna yadda ya" ƙeƙashe ƙasa ya biye ma Bintu ya kasa yi ma iyayensa biyayya. Ya daɗe a haka kafin ya iya tsayar da "hawayen daƙyar! Ya laluba aljihunsa ya ɗauko damin kuɗi yayi mata alkhairi kamar yadda ya saba, ya" "bata na Ladidi da Rakiya, sannan ya bata wanda za ta raba ma ƴan'uwansa mata da suke uba ɗaya." "Jikinsa a sanyaye ya miƙe yayi mata sallama zai wuce, har zaure ta raka shi tana sake haɗa shi da girman" Allah kar ya kuskura ya ce zai hukunta Bintu da laifukan da suka gabata. """Ka gode ma Allah da yasa idanunka suka washe akan halinta. Ka ga yanzu sai ka sake sabon lale akan" "zamantakewar da za kayi da ita. Mu dai Allah ya sani bamu riƙe ta arai ba.""" Da haka suka rabu. "Ko da ya koma gida gurin Innaye, duk yadda ya so su sake tauna zancen ta ƙi bashi damar haka. Da" "murmushi a fuskarta take ƙara tabbatar mishi ita bata riƙe Bintu arai ba, kuma bata yafe mishi ba idan ya" hukunta Bintu da laifukan da suka gabata. "A karo na barkatai ya duƙa har ƙasa ya sake neman yafiyarta, ta ƙara jaddada mishi ta yafe sannan ya fita" gurin Baffa. "A can ɗin ma dai zancen suka sake taunawa, a matsayin Baffa namiji, ya sake bashi shawarwari masu" "kyau na yadda zai zauna da Bintu, a yanzu, da kuma bayan ya ƙara aure. Kamar haɗin baki shi ma dai sake jaddada mishi yayi kar ya kuskura ya ce zai ɗauki wani mataki akan Bintu. Abinda ya wuce a barshi a wanda ya wuce." "Yamma liƙis ya bar Faƙo, bakunan iyaye da ƴan'uwanshi cike da addu'ar Allah ya maida shi Abuja lafiya." Da yake tun yana hanya ya kira Abba Lurwanu ya sanar da shi akwai muhimmiyar maganar da yake so "suyi, amma yanzu yana hanyar komawa Abuja, idan Allah ya sa ya koma lafiya kuma dare baiyi sosai ba zai tsaya a gidanshi suyi maganar." Wannan dalilin yasa ko da ya shiga Abuja ƙarfe goma na dare ya wuce gidan Abba Lurwanu. Acan ya ci "abincin dare, bayan sun gama tauna maganar neman aurenshi da Kareema sannan ya kama hanyar komawa gida." Da wannan gajiya da ɓacin ran ne bayan isarsa Bintu ta so ta kunno ma kanta bala'i shi kuma ya karta "mata kashaidi, haɗe da rantsuwar ba don rayukan mutane uku mafiya muhimmanci a gare shi ba (Baffa, Innaye, Aunty Balira) Da yanzu wani zancen ake yi tsakaninsu ba wannan ba." ************ "Ta ɗauki tsawon mintuna ashirin a tsaye inda ya barta, jikinta sanyi ƙalau. Zuciyarta a cunkushe, ta ma" rasa wani irin takamaimai tunani ya kamata tayi. A ƙarshe dai da taga tsayuwar bazai fissheta ba sai taja ƙafafunta a sanyaye ta koma cikin falon. Har ta "ɗofana mazaunanta akan kujera, sai kuma ta miƙe tsaye tsulum kamar an tsunguleta." "Wayarta da ke ajiye can gefe ɗaya ta ɗauka ta fara tafiya zuwa ɗakinta. A hannunta tana lallatsa wayarta," lambar Raudha ta lalubo ta danna mata kira ba tare da duba tsalawar da dare yayi ba. Wayar tana daf da tsinkewa Raudha ta ɗauka da magagin barci sosai a muryarta. """Bintu? Lafiya kike kuwa? Me ya faru?""" Ta jera mata tambayoyin a rarrabe. """Yi haƙuri Raudha na tashe ki kina barci... Daman zan faɗa miki abinda ya faru bayan dawowar Hafiz" "ne...""" """Toh! Toh!! Ina jinki!!! Amma Ina fatan dai ya dawo miki da Aadil?""" Ta tambayeta da murya mai cike da ɗoki da sakankancewa. """A'a! Bai dawo da shi ba.""" Ta amsa da rawar murya. """Alfarmarki nake nema don Allah Raudha.""" Ta sake faɗa muryarta na ƙarasa karyewa sosai. Don tsabar fitina da bala'in da ta saka ma ranta duk yadda nonuwanta ke ciwo suna tsikarinta saboda yaye ko jin su ba ta yi. Ba komai ke ƙara karya ma Bintu "zuciya ba sai idan ta tuno ita tana nan a birni irin Abuja Aadil ɗanta yana wulaƙantaccen ƙauye irin na su Innaye, ƙauyen da ko ita da girmanta bata taɓa gigin yin kwana ɗaya a ciki ba." Ta sani aminci ne mai ƙarfi tsakaninta da Raudha. Babu wani alfarma da za ta nema gurin Raudha ta ƙi yi mata kamar yadda ita ma a ɓangarenta za ta iya yin komai don kare martabar Raudha. """Kin sani kin wuce komai a gurina Bintu. Faɗi duk abinda kike so kawai inyi miki ki ga aiki da cikawa.""" Cewar Raudha daga can ɓangaren da muryar da ke nuna da dukkan gaskiyarta take magana. "Nannauyar ajiyar zuciya Bintu ta sauke, ta lalubi gefen gadonta ta zauna sannan ta cigaba da magana." """Ina wannan mutumin naki na filin jirgin ƙasa wanda ke samar mana da ticket ɗin zuwa Kaduna a" "sauƙaƙe?""" """Lurwanu? Yana nan. Me kike so yayi miki?""" """Ki tura masa saƙo a darennan ya tanadar mana da ticket biyu na jirgin gobe da safe. Bazan iya ba" "Raudha, Wallahi tallahi bazan taɓa iya barin Aadil ya kwana biyu a ƙauyennan ba. Goben nan zan je in ɗauko shi, duk abinda Hafiz zaiyi ya daɗe baiyi ba...""" """To me ma ya isa ya yi? Ai shi kansa ya san ba shi da gaskiya... Duk inda za aje a dawo kin fi shi gaskiya" "Bintu, kamar yadda kika fi shi girman haƙƙi akan Aadil har a gurin Allah... Don haka kar ma ki wani ɗaga hankalinki. In banda ma tun safennan bamu yi tunanin zai iya barin Aadil acan ba ai da tun ayau za muje" "mu ɗauko shi. Ki kwantar da hankali ƙawata...""" "Waɗannan maganganun na Raudha, su suka zaftare kaso arba'in cikin ɗari na damuwar da ke danƙare a" zuciyar Bintu. Da wannan dalilin yasa bayan sun gama waya da Raudha har ta iya samun ƙwarin gwuiwar "zuwa kicin ta haɗa tea mai kauri ta sha. Ta ɓalli paracetamol guda biyu ta haɗiya, ta sake yin wanka sannan ta bi lafiyar gado." Ko tunanin Hafiz bata yi ba balle tayi gigin zuwa ɗakinshi su kwanta. Abinda bai taɓa faruwa ba tsakanin "su biyun raba makwanci tunda suka yi aure, in dai ba tafiya Hafiz yayi ba." ********* "Washe gari tunda sassafe Hafiz ya ji ƙarar tada motar Bintu, yana kwance a kan gadonshi. Tunda ya tashi" "yayi sallar asubahi a makare saboda rashin barci da bai samu yi da wuri ba, ya kasa fita ya duba ta tashi ko bata tashi ba?" Azkhar ma sama-sama ya yi ya sake bin lafiyar gado da nufin yin ramuwar barci. Ya kwanta kenan ya ji "tashin motar Bintu, mamaki ne ya kama shi har ya tambayi kanshi." 'Ina Bintu take niyyar zuwa ba tare da ta faɗa mishi ba?' Sanin ko daga can asibitinsu ne aka yi mata kiran gaggawa tana faɗa mishi kafin ta fita yasa shi yin "mamakin fitar tata a yanzu. A hankali ya ya ye bargon da yake lulluɓe da shi ya sauka daga kan gadon, ko kafin ya fita daga ɗakin ma har mai gadi ya buɗe mata get ta fice daga gidan." "Don haka bai ɓata lokacin duba ɗakinta ba ya san ita ce ta fita, tunda direbansu ba ya nan. Idan ba ita ba" wa zai ɗauki motarta ya fita da ita da sassafen nan. "Ko da ya koma cikin ɗakinsa, har ya kwanta, sai kuma yayi tunanin bai kamata ya riƙe Bintu har ya" banzatar da al'amarinta haka ba. Tunda su kansu iyayenshi sun roƙe shi alfarmar kar ya kuskura ya hukunta Bintu da laifukan da suka gabata. "Wayarsa ya ɗauko, ya lalubo lambarta ya danna mata kira, sannan ya kara wayar a kunnensa yana jiran" ta ɗauka ya ji me yasa ta fitan sassafe haka? Don a saninsa yau ba ta da aiki in dai ba wani muhimmin abu bane ya taso mata. "A can ɓangaren Bintu, tana ganin kiran ta jaa wani dogon tsaki ranta a ɓace." """Aikin ɓur in ji tusa! Ai kuma sai ka yi. Na rantse da Allah idan za ka kira sau dubu bazan ɗauka ba. Kai" ma ka ɗanɗana ka ji idan a kira mutum ya ƙi ɗauka da daɗi. Don ma dai ni da hannuna bazan iya blocking "ɗin ka bane kamar yadda ka yi min.""" Ita kaɗai a cikin mota tana tuƙi tana masifa har ta isa gidan Raudha. Ko da ta shiga ciki basu wani ɓata "lokaci ba suka fito, domin a shirye ta tarar da Raudha. Motar ta suka sake shiga mai gadi ya buɗe musu" ƙofa ta figi motar a guje suka bar gidan. "Kamar yadda suka tsara, komai ya tafi musu daidai yadda Bintu ta so. Ƙarfe goma sha ɗaya da minti" hamsin na safiya mai taxi ɗin da suka ɗauki shata tun daga Kaduna yayi fakin a ƙofar gidansu Innaye. Tana gyara zaman ƙwamemen baƙin gilashi no respect da ta siya a Kaduna ta saka a idanunta take cewa da direba. """Malam ka ɗan jira mu kaɗan, kamar yadda na ce maka ba daɗewa za muyi a ciki ba. Yaro kawai zan" "ɗauko ka juya da mu inda ka ɗauko mu.""" """Babu damuwa Hajiya. A fito lafiya.""" Ya amsa a ladabce. "Har sun nufi zauren gidan Raudha ta dakatar da ita, zip ɗin jakarta ta zage, ta cusa hannu a ciki ta ɗebo" cingam guda huɗu ta miƙa ma Bintu biyu itama ta ɓare biyu ta watsa a baki ba tare da kunyar idanun mutane da ke kallonsu ba. """Saka wannan a baki ki tauna cikin ƙwarewa ƙawata. Kin san sheggun ƙauyen nan in bi ki nuna musu ke" "ma ƴar iskar kanki bane baza su baki Aadil a sauƙaƙe ba. Kuma ko da wasa idan muka shiga kar ki kuskura kunyar ƴar iskar tsohuwar nan ya hana ki yayyaɓa mata baƙaƙen maganganu...""" """Kin san wannan ai dole ne Raudha. Yadda raina ya ɓaci Wallahi dole nata ya ninka nawa ɓaci. Mu je." "Shegu yaran ƙauye dubi yadda suke kallonmu kamar mayu... kurwanmu kur!!!""" Ta ƙarasa maganar da ɗan ƙarfi tana kallon wani yaro ɗan tsamurarre da tulelen ciki wanda tun ɗazu yake tsaye gefe ya ƙura musu idanu. Bayan ta ɓare cingam ɗin ta watsa a baki sai ta nufi cikin gidan tana sake tamke fuska. Raudha na biye da ita a baya itama da nata fuskar a haɗe babu sassauci ko kaɗan. ****** "A cikin gidansu Innaye, misalin ƙarfe goma sha ɗaya da kwata na safiyar ranar, Aunty Balira, Rakiya," Ladidi suka yi ma gidan dirar mikiya. "Bayan barinsu gidan Aunty Balira jiya, da daddare ta kira su kan cewa su tambayi mazajensu su haɗu su" "ukun su je suyi ma Innaye Allah sanya alkhairin aure da Hafiz zaiyi. Wannan shi ne abinda ya kawo su, ashe rabon suyi kiciɓus da Hajiya Bintu ne." "Suna zaune a tsakar ɗakin Innaye kan tabarma suna shan Fate da Mama Laraba tayi, hira suke da" "dararraku a tsakaninsu ukun, Innaye tana zaune a kan kujera tana saka musu baki jefi-jefi." "Suna cikin wannan halin ne suka ga an yaye labulen ɗakin, kwatsam! Sai ga Bintu ta bayyana da Raudha" "tsaye a bayanta, sai taunar cingam suke yi ƙaras-ƙaras cike da tsantsar raini da fitsara." Da farko duk ƙamewa suka yi ana kallon-kallo a tsakaninsu. Sai Aunty Rakiya ta karya shirun da cewa """A'uzubillahi minasshaiɗanirrajeem.""" Da matsanancin ɓacin rai a muryar Bintu ta ce """Kan'uba!! Amma lallai Rakiya kin ci uwar rainin wayau. Ni za ki kalla kiyi wa a'uziyya? To Me kike" "nufi?""" """Me kuwa nake nufi in banda korar shaiɗan da nayi? Idan banyi a'uziyya ba me kike so inyi? In ba" "shaiɗaniya a cikin siffar mutane ba wacece za ta shigo ɗaki mai daraja irinna sarkuwarta babu sallama...?""" """Rakiya!""" Innaye ta kira sunanta da ɗan tsawa-tsawa a muryarta. """Ya isa haka nan.""" Ta sake faɗa tana ƙoƙarin sassauta muryarta. A karo na biyu ta mayar da idanunta kan Bintu ƙirjinta na bugawa kaɗan-kaɗan. Ta daɗe da sanin Bintu "ba ta da mutunci, amma tsantsagwaron rashin mutunci irin wanda take ƙoƙarin shimfiɗa musu yau bata taɓa ganin ta yi ba. Tunaninta ɗaya ne, Bintu ta ji Hafiz zai auri ƙanwar mijin Zulai shi ne ta zo ta sauke" musu rashin mutunci don a tsammaninta da haɗin bakinsu ake shirin ƙulla auren. """Fatima lafiya? Me yake tafe da ke?""" Ta tambayeta bayan ta tuna zato zunubi ne ko da ya kasance gaskiya. "Yatsarta manuniya tasa ta ja gilashinta ƙasa kaɗan, ya zama tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya ta saman" "gilashi. Cingam ɗin da ke bakinta ta tauna yayi ƙas, ta huro shi yayi ƙaton balo-balo ta fasa sannan ta fara" magana tana yamutsa fuska kamar tana shaƙar warin kashi. """Innaye... Kin ga ina ganin mutuncinki, kuma da gaske ina ganin girmanki. Bana tunanin tunda na auri" "Hafiz wani sa'insa ya taɓa shiga tsakanina da ke, don haka kar ki bari mu fara ayau. Salin-alin ki bani ɗana in tafi da shi...""" """Saurara Bintu! Wani ɗan kike magana akai?""" Aunty Balira ta katse mata numfashi da wannan tambayar. """Ɗana Aadil, jinina. Wanda na haifa a cikina...""" """Uhmmm! A sanina dai ƙarfe ɗaya ba ya amo... idan kuma ɗan naki ne ke kaɗai ai sai mu ji. In dai har" "Babanmu ɗan da Hafizu yayi miki cikinshi kika haifa ne, a tunanina yana da ikon yin yanda yaga dama da" "ɗanshi?""" Aunty Ladidi ta katse ta da faɗin haka ranta a ɓace da maganganun da Bintu ta faɗa. Habawa!!! Waɗannan maganganu da Ladidi ta faɗa ina wuta Bintu da Raudha su jefata a ciki wai tana "neman sheganta Aadil. Haka suka shigo har tsakiyar ɗakin Innaye suna zuba rashin daraja ko takalmansu basu samu sararin cirewa ba. Suna yi, Rakiya da Ladidi suna basu amsa, nan da nan guri ya fara rikicewa kamar za'a ba hammata iska. Kishiyoyin Innaye da tashin muryarsu Bintu ne ya shigo da su babu abinda" "suke yi sai aukin bada haƙuri, tunda sun taki babbar sa'a Baffa ba ya nan." "Su Baba Abubakar da kusan yini suke yi a ƙofar gidan kuma su ma basa nan, tun sassafe suka hau motar" da Hafiz ya ɗauka musu shata suka kama hanyar Abuja don a tsayar da maganar aure tsakanin Hafiz da Kareema. Wannan shi ne dalilin da yasa su Bintu suke cin karensu babu babbaka cikin rufewar idanu. "Innaye dai tana zaune ƙiƙam kamar mutum-mutumi. Kanta a ƙasa, a idanunta kuwa babu abinda ke fita" sai zazzaafan hawaye. Zuciyarta cike da tunanin yadda Ɗan kuka ke ja ma uwarsa jifa. Wai yanzu fa "wannan matsayin matar ɗanta take. Saboda tsabar rashin kirki ta shiga har tsakiyar ɗakinta da takalmi, kuma take zuba musu rashin mutunci yadda take so." A ɓangaren Aunty Balira da take zaune itama baƙin ciki da takaicin Bintu na neman kai ta kushewa "wayarta ta zura hannu a lalita ta ciro. Lambar Hafiz ta lalubo ta danna mishi kira, a niyyarta na tambayarsa wai shin shi ne ya turo Bintu tazo ta zubar musu da mutunci ta ɗaga hankalin mahaifiyarsu? Ko kuwa zuwan na gaban kanta tayi?" "Acan ɓangaren Hafiz, yana ganin kiran ya ɗaga, da ɗan taƙaitaccen murmushi a fuskarsa. Ya buɗe baki" zaiyi sallama kenan sai ya jiyo hayaniya na tashi sosai ta cikin wayar kamar ana faɗa. Ƙirjinshi ne ya buga daram! Don haka ya saurara sosai don jin hayaniyar me ake yi haka a gidan Aunty Balira.? Muryar Baba Laraba da ya fara jiyowa tana magana yasa shi fahimtar hayaniyar a gidansu Innaye ne ba gidan Aunty Balira ba. Raɗau ya cigaba da saurarar muryar Baba Laraba tana magana cikin magiya da roƙo """Hajiya Bintu... kinga Hajiya Bintu ina gama ki da girman Allah da ma'aiki kiyi haƙuri... Tunda dai baki ga" "alamar wani ɗa naki anan ba ki koma...""" Muryar Bintu da ya ji cikin masifa tana mayar da martani yasa shi wuntsilawa daga kan gadon hankalinsa "a tashe. Bai ƙara shiga tashin hankali ba sai da ya ji irin munanan maganganun da ke fita a bakinta. Tana mayar ma da Baba Laraba martani, amma kamar tana yi da ƙanwarta." Lokaci ɗaya jikinsa ya fara rawa kamar yayi tsuntsuwa ya ganshi a tsakiyar ɗakin Innaye bayan ya ji kalaman Bintu. """Ke tsohuwa saurara. Na rantse da Allah tunda na sa ƙafa na shigo wannan tsinannen ƙauyen babu" "inda zan je sai wannan tsohuwar da munafukan ƴaƴanta sun fito min da ɗana...""" "Daga wannan maganar, bai sake jin wata ba sai ƙarar saukar marin da daga ji ba ɗaya bane, marin da ya" rasa wa aka yiwa? Bintu aka mara ko ita ce ta mari ɗaya daga cikin yayyinsa? Ko kuma haƙurin Innaye ne yakai ƙarshe ta mari Bintu? Kuma sanadiyyar marin ne yasa duk hayaniyar da ake yi ya ɗauke ɗif! Kamar ɗaukewar ruwan sama. "Sai da aka ɗauki mintuna biyu kafin ya ji muryar Aunty Balira tana magana cikin kuka, saboda hawayen" da sai a lokacin ta lura Innaye tana yi ya ɗaga mata hankali. """Tir da mace irinki Bintu!!! Tir da ke da munanan halayenki Bintu!! Sai yau na ƙara tabbatarda lallai" "Hafizu yayi asara baiyi sa'ar mata ba. To saurara ki ji, ke kinyi kaɗan ki ce za ki zo ki saka mahaifiyarmu kuka sannan mu zuba miki ido. Idan shi wanda ya auro ki ba ya kishin mahaifiyarsa mu muna yi. Ki je can ki nemi inda Hafizu ya kai miki ɗa, mu kam saboda sanin mugun halinki da baƙin halinki babu wacce tayi gigin karɓar mummunan tsatso irin naki. Zo ki fice mana daga ɗakin uwa, za ki fice ne salin alin ko sai na" "nakaɗa miki tsinannen duka in barki kwance?""" "Ta ƙarasa maganar cikin tsawa da hargagi, jikinta sai rawa yake yi saboda yadda kukan Innaye ya ke" bugun zuciyarta. "Bintu da tunda Aunty Balira ta sauke mata tagwayen maruka ita da Raudha suka ƙame ƙam kamar statue," sai a lokacin ta iya buɗe baki da rawar murya idanunta ciccike da hawaye ta ce """Nnnnnn ni kika mara Balira...?""" "Ai ko kafin ta rufe baki, Aunty Rakiya da Aunty Ladidi da tun ɗazu hannuwansu ke ƙaiƙayi suka sake" gaura mata wasu ƙarfafan maruka a kuncinta na dama da hagu. """An mare ki ɗin! Don abu kaza-kazanki idan kin isa ki sake cewa uffan anan gurin idan bamu yi ƙasa-" "ƙasa da ke ba.""" Suka haɗa baki gurin faɗin haka a zafafe. Aunty Rakiya da ta daɗe tana jiran irin wannan ranar da za ta jibgi Bintu a haukace ta cire ɗankwalin "kanta ta ci ɗamara da shi. Ta tsaya gaban Bintu tana jijjiga, babu abinda take jira sai Bintu ta ce kule ta rufe ta da mahaukacin duka." "Raudha da tun da aka yi marukan farko hankalinta yakai ƙololuwa gurin tashi, a ɗan tsorace ta ƙare ma" "Rakiya kallo, ta ganta irin sangama-sangaman matannan ne ga tsawo ga ƙiba. Ko dambe aka ce suyi su" biyu ita da Bintu su taru ma Rakiya ko rantsuwa tayi babu kaffara tun a mintuna biyun farko Rakiya za tayi ƙasa-ƙasa da su. "Domin daga ita har Bintu ba su da ƙiba ko kaɗan, kuma Mal bahaushe ya ce alamun ƙarfi yana ga mai" ƙiba. Da sauri ta riƙo hannun Bintu ta fara janta da nufin su fice daga ɗakin. """Zo mu je ƙawata. Idan muka tsaya taron dangi za suyi mana. Idan sun ƙi ba mu Aadil ta lalama ai" "akwai hukuma. Kuma na rantse da Allah waɗannan marukan da suka yi miki basu ci bulus ba, tabbas za su biya bashi amma a gaduron ɗin sojoji. Zo mu je mu sake sabon shiri.""" "Tana jan hannun Bintu, Bintun tana turjewa hawayen baƙin cikin mari huɗu da aka mata na zuba a" "idanunta amma bata iya rama ko ɗaya ba, kuma ta kasa cewa uhummm ɗin saboda tsoron kar su dake ta" "abinda ta san za su aikata tunda shegun ƙauye ne, a haka har suka fice daga gidan gaba ɗaya tana sharɓen hawaye." ****** ****** "Misalin ƙarfe bakwai na daren ranar, Bintu tana kwance akan gadon ɗakin Raudha. Ta ci kuka har ta" "gode Allah, hawayen da tunda suka ɓalle mata a can Faƙo har yanzu sun gagara tsayawa. Duk kuwa da" yadda Raudha ta yini tana rarrashinta sam ta kasa daina kuka. "A yanzu abubuwa ne suka haɗe mata goma da ashirin. Ga damuwar rashin sanin inda Hafiz ya kai Aadil," ga damuwar irin wannan mummunan cin mutunci da tozarci da dangin Hafiz suka yi mata. """Yanzu shi kenan? An sha ta misilla-banza? Hafiz da ƙauyawan ƴan'uwansa sun ci galaba a kanta? Sun" "raba ta da ɗanta lokacin da bata yi tsammani ba sannan sunyi sukuwar sallah akan kima da martabarta?""" Tunanin hakan kaɗai tayi sababbin hawaye ne ke sake ɓalle mata. "Ko bayan da suka koma Abuja a yammacin, kafin su isa gidan Raudha sai da ta kira Hajiya Maama matar" Abba Lurwanu ta tambayeta cikin hikima ko Hafiz ya kai mata Aadil? """Bai kawo shi ba Bintu. Hafiz ɗin bai dawo bane ko kin kasa samun shi a waya ne? Kin san Aadil da" "ƙwuiya na tabbata duk inda yake yana tare da mahaifinsa. Kiyi haƙuri, zai dawo miki da ɗanki.""" Amsar da Hajiya Mama ta ba ta kenan. "Gidan Zulai shi ne guri na ƙarshe da tayi tunanin Hafiz zai iya kai Aadil. Har sun kusa isa gidan Raudha," haka ta sake neman alfarmar Raudha ta juya da kan motar da a yanzu Raudha ke tuƙawa suka nufi gidan Zulai. Suna hanya kamar mahaukaciya haka take ta kuka tana rantse-rantse da shan alwashin duk waɗannan marukan da su Balira suka yi mata akan Zulai za ta rama. Sai dai wani rashin sa'a da suka buga shi ne suna isa mai gadi ya tabbatar musu Zulaikha ba ta nan. Ta tafi can babban gida saboda Oga yayi tafiya. "Da fari ta so suje gidan Mummy Saudha tun a daren, amma sai Raudha ta taushi zuciyarta da shawarar" "tayi haƙuri su bari zuwa gobe da safe. Lokacin Mummy ta tafi aiki sai su je, yadda za su samu damar cin ƙaniyar Zulai ba tare da anyi yunƙurin hana su ba." "Amincewa da shawarar tayi, don haka ta jingina da kujerar mota ta lumshe idanu ta cigaba da hawaye" zuciyarta na ƙuna da tafarfasa. Har suka isa gidan Raudha bata sani ba sai da ta taɓa ta cewa ta tashi su shiga ciki. Tunda ta shiga kuwa tayi kwance-kwance tana kuka akan gadon Raudha. Ko ramakon sallolin da suke "kanta ta kasa yi, tun Raudha tana rarrashinta har dai ta gaji ta zura ma sarautar Allah ido. Daga ƙarshe ma ficewa tayi zuwa kicin, ta samu abinci ta ci tayi nak, sannan ta koma ɗakin bayan ta yi nakwa-nakwa da fuska, sak yanayin taya Bintu baƙin ciki da jimami." Agogo yana buga ƙarfe tara daidai ta ɗaga jajayen idanunta da suka kumbura suntum saboda yawan kuka ta kalli Raudha. Da ɗasasshiyar murya ta ce """Ina Abdallah? (Ƙanin Raudha da yake zama a gurinta.) Don Allah ki kira shi ya mayar da ni gida... kaina" "ciwo yake sosai, bazan iya tuƙa mota ba.""" """Tom! Na dai ji dawowarsa ɗazu ban san ko yana nan ba. Bari in taɓo shi ta waya.""" "Raudha ta amsa, a lokaci guda tana daddanna wayarta." Suna hanyar zuwa harabar tsakar gidan take ƙara tausar Bintu da daɗaɗan kalamai. """Na san izuwa yanzu ƴan'uwan Hafiz sun kira shi sun kitsa mishi ƙarya da gaskiya kan abinda ya faru." Don haka ko kin koma gida don Allah don Annabi SAW duk yadda zaiyi ƙoƙarin tararki da rigima kar ki "kuskura ki kula shi. Ki cigaba da tara shi har zuwa sadda za mu gano inda ya kai Aadil mu ɗauko shi, a lokacin kina da damar warware mishi balbalin bala'in da bai taɓa tsammanin kin iya ba.""" """Hmmm! Ba damuwa. Na gode ƙwarai Raudha.""" Ta amsa a taƙaice. "Ko da ta shiga gidan baya na motar ta jingina da kujera, a jikinta jakarta ne rungume da kuɗi da wayarta" da sauran ƙananun tarkace. Lumshe idanu tayi bata ce Uffan ba har suka isa gidanta. "Har ciki ya shiga mata da motar, ya daidaita fakin a tsakar gidan sannan ya kashe motar ya miƙa mata" makullin. Cike da kasala ta miƙa hannu ta karɓa tayi mishi godiya. Hannu ta cusa cikin jakarta ta ƙirgo naira dubu "goma ta bashi, ta sake yi mishi godiya sosai. Ya fice daga harabar gidan, ita kuma ta nufi cikin gidan tana" rangaji kamar wacce ta sha ƙwaya. ****** "Washe gari da misalin ƙarfe goma na safe, Bintu ta gama shiryawa da wani sabon ƙwarin gwuiwa na" musamman wanda a jiya sam bata kwana da shi ba. Cikin hukuncin Allah jiya da dare har ta gama duk abinda za tayi ta kulle ƙofar ɗakinta Hafiz bai koma gidan ba. Kamar magani haka ta dinga kurɓar furar Rufaida har ta ji cikinta ya ɗauka. "Tayi wanka, ta rama sallolin da suke kanta cikin rashin nutsuwa. Sannan ta harhaɗa Magunguna ciki har" da na barci ta ɗaɗɗaka. Da yake da gajiya a jikinta ga rashin wadataccen barci tsakanin jiya da yau Mintuna goma da gama shan maganin wani nannauyan barci yayi awon gaba da ita. "Ta kai ƙarfe takwas kafin ta farka, a gurguje tayi sallar asubah. Tana zaune akan dadduma take tsara" muhimman abubuwa biyu da ta ƙuduri aniyar aiwatar da su a ranar. "Wayarta da tun jiya bata bi ta kanta ba ta ɗauko, bata bi ta kan tarin misscalls da saƙonnin da suke" fuskar wayarta ba ta shiga cikin ma'adanar lambobi. "A hankali take wucewa har zuwa sadda ta ci karo da lambar da take nema, ba na kowa bane face na" Kwamishinan ƴan sanda da ya kasance abokin mahaifinta. "Kiranshi tayi, bayan gaisuwa da gabatar mishi da kanta tambayarshi tayi yau zai samu zuwa Ofis kuwa?" """Yau ɗin Monday ce fa, tushen aiki ko nasara na tsoron monday. Ina Ofis tun 8.""" Ya amsa mata. """Na gode Abba. Zuwa 11am in sha Allah zan ƙaraso...""" """Lafiya kuwa Fatima?""" Ya tambayeta da mamaki a muryarsa. """Lafiya amma ba lau ba Abba. Maganar ba ta waya bace. Sai na zo dai.""" """Ok!""" "Ya amsa a taƙaice, sannan ya kashe wayar." "Tana riƙe da wayar, ita kaɗai take sakin murmushi akai-akai. Zuciyarta cike da tunanika mabanbanta." Sannu a hankali kamar allurar soja aka zurkuɗa mata haka take jin ƙwarin gwuiwa yana zagaye duk sassan jikinta. "Ɗan ƙaramin frige ɗin da ke ɗakinta ta buɗe, kamar ba safiya ba, coke mai sanyi ta ɗauka ta buɗe, ta" "lumshe idanu ta kafa a bakinta ta fara sha, tana jin yadda sanyin ke sauka har cikin-cikinta." "Bata shirya haɗuwa da Hafiz ba, shi yasa bata buɗe ƙofar ɗakinta ba har ta gama duk shirinta. A yadda ta" "tsara, gidan Mummy Sauda za ta fara zuwa, tayi ma Zulai tsinannen duka sannan ta ƙwace ɗanta. Daga" can kuma ta wuce hedikwatar ƴan sanda Ofishin kwamishina ta kai mishi ƙarar su Aunty Balira. A yau ba sai gobe ba take so a kamo su Aunty Balira a wulaƙance cikin motar ƴan sanda a watsa su a "firzin. Za ta kashe ko nawa ne don ganin anyi musu mafi munin wulaƙanci da tozarci, za su san lallai sun" taɓo tsuliyar dodo. "Tana sauka daga kan step ta ji motsin buɗe ƙofar Hafiz, ko waige bata yi ba, don ma kar ya nemi dakatar" da ita ƙara sauri tayi har ta sauka ƙasa ta fice daga falon. "Tana cikin mota ta ɗaga waya ta kira Raudha, da dariya a muryarta bayan sun gaisa take cewa" """Ƙawata yau fa Wallahi akwai show, za ki samu zuwa ko inyi wucewa ta...""" """Haba... ai amana bai ce haka ba Ƙawata. Tuntuni na daɗe da shiryawa, ke kawai nake jira.""" Raudha ta amsa cike da zakwaɗi. "Ko da ta isa gidan Raudha bata shiga da mota gidan ba, hon kawai tayi mata ta fito cikin kwalliya sosai ta" shiga ɓangaren mai zaman banza suka kama hanyar wucewa. A hanya take ba Raudha labarin irin tsarin da take da shi na ɗaukar fansa akan su Aunty Balira. """Good! Very good ƙawata!! Kamar kin san dama ƴan ƙauye da bala'in tsoron ƴan sanda. Ki sa aci" "ubansu dakyau!!! Ta yadda nan gaba ko ɗaga ido baza su iya yi gurin yi miki magana ba, balle har suyi" "gigin kai ƙazantaccen hannayensu zuwa jikinki.""" """Ki bari kawai Raudha. Zan koya musu babban darasi a rayuwarsu.""" Ta faɗa tana sakin ƙayataccen murmushi. """Sannan kuma ga ƙarin wata shawarar. Why not yanzu kafin mu isa gurin ita wancan ƙanwar tasu mu" "fara biyawa butique mu sayi belt da za mu ɗumama mata jiki da shi? Don dai ina ga kai kyawawan hannayenmu zuwa jikin wancan local yarinyar zubar da aji ne. Amma idan muka samu belt, cikin" "ƙanƙanin lokaci za mu farfasa mata jiki da fuska, don da gurin ƙarfen za mu ci ubanta...""" """Muguwa Ƙawata.""" "Bintu ta katse ta da faɗin haka, sannan suka kwashe da dariya haɗe da tafawa." Bayan sun sayi belt ɗin a hanya suka cigaba da tattauna yadda za su ci uban Zulai la'ada waje har suka isa gidan Momy Sauda. Saboda tsabar ƙarfin hali irinna Bintu har cikin gidan ta shiga da motarta. "Bayan sun fito suka nufi cikin gidan tinƙis-tinƙis, da belt tsirara riƙe a hannayensu. Ko da suka danna" "madannin da ke isar da na ciki akwai baƙo a waje, bakunansu cike yake da addu'ar Allah yasa Zulai ce za" ta buɗe ƙofar. "'Lallai da tun daga nan za su fara tafka mata belt, sai sun ruɗa ta da duka sun farfasa mata jiki. Sannan a" "wulaƙance Bintu za tayi mata wani shaƙa da sai ta fara jiyo ƙamshin mutuwa, za ta wancakalar da ita a ƙasa ta mutsuke mata ƙazantattun yatsun hannayenta da har suka yi kuskuren riƙe mata ɗa na kwana" biyu. Ita da kanta za ta shige ɗakunan gidan ta zaƙulo duk inda ɗanta yake ta tafi da shi.' Wannan duk tunani ne da yake danƙare a zuciyar Bintu. "Cikin rashin sa'a Imam ne ya buɗe musu ƙofar Falon, kuma yana buɗewa ta ciki, bai tsaya ba a guje ya" koma cikin falon ya cigaba da wasanshi. "Haɗa idanu suka yi, sannan suka gyaɗa kai kamar wasu ƙadangaru, Bintu ta ƙara da ƙwafa a hankali" sannan suka bi bayan Imam zuwa cikin falon. Kiciɓus aka ce mugun gamo! Kamar haka ne ya same su bayan sun shiga falon suka yi arba da Zulaikha "zaune akan kujera, ta pose kamar wacce za a ɗauka hoto, cikin wani ƙayataccen kwalliya da kayan" "turawa, wandon jeans ne a jikinta ya matse ta sosai." Ta miƙar da ƙafafunta ta ɗora ɗaya kan ɗaya tana ɗan girgizawa sannu a hankali cikin ƙasaita da aji. Daga "inda take zaune, suna hango tudun mazaunanta yadda suka wani botso ta cikin wandon jikinta sannan suka ɗan baje akan kujera. Rigar da ta saka irin mai wawakeken wuyan nan ne, ta saman na shanunta da suke farare tas sun bayyana a fili. Babu hula ko ɗan kwali a kanta, sai sumanta da yasha gyara tun daga" nesa yake ɗaukar ido ta sake shi ya sauka har kan kafaɗunta. Wata iriyar siririyar dariya take saki sannu-sannu gwanin ban sha'awa. Sai da suka sake ƙure ta da kallo sai suka ga ashe Laptop ne ajiye akan wani ɗan teburi da ke gabanta. Bisaga dukkan alamu Vidio call take yi da mijinta. "Duk da ta ji ƙarar buɗe ƙofa alamun an shigo bata tsaya da dariyar da take yi ba, kuma bata ɗaga kai ta" kalli su Bintu da suka yi suman tsaye suna kallonta ba. Sai da ta gama dariyar sannan a tausashe da wata iriyar siririyar murya ta ce ma Abban Imam ya bata minti biyar anyi baƙi. "Daga can cikin laptop ɗin sumbatar hannayensa yayi ya hura mata, ba tare da kunyar idanun su Bintu ba" ta mayar mishi da martani sannan ta katse kiran. "Mayar da hankalinta kan su Bintu tayi, kallon sakan goma tayi musu sannan ta buɗe baki a hankali ta ce" """Au! Ashe ma ku ne.""" Ta faɗa tana ɗan yamutsa fuska da salon wulaƙanci da tozarci. Bintu da takaici da baƙin cikin irin canjin da ta sake gani na sosai a jikin Zulai yake neman kaita kushewa bata san sadda ta buɗe baki cikin ɗaga murya ta lailayo wata bamagujiyar ashar ta maka mata ba. "Da ɗan sauri Zulaikha ta saka yatsarta manuniya ta toshe kunnenta ɗaya, sannan da yanayin muryar da" ta goge da furta kalaman turanci cikin ƙasaita ta ce "“Keep it low, you are so loud”" Bintu da bata taɓa tsammanin bayan wayewar da Zulai tayi har turanci ta iya ba taga-taga tayi za ta kifa saboda tsananin yadda maganar ya dake ta. "Da saurin gaske Raudha ta yar da belt ɗin hannunta ta riƙo Bintu kafin ta kai ƙasa. Fincikewa Bintu tayi," "hankalinta tashe da irin tozarcin da Zulai tayi mata ta yi zaman ƴan bori a ƙasa, sannan ta ɗora hannu biyu akai ta saka kuka wi-wi kamar ƙaramar yarinya." Hankalin Raudha a tashe ta ce """Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Miye haka kike yi Bintu? Kuka a gaban wannan yarinyar ai sai ki ja ma" "kanki raini da tozarci...""" """Raini? tozarci? wulaƙanci na nawa kuma Raudha? Baki ji irin kalaman da ta furta min bane?""" Tayi maganar cikin kuka wasu sababbin hawaye na sake ɓalle mata. """Ki ce mata ta bani ɗana. Kuma Allah ya isa tsakanina da ita da duk danginsu. Kuma na rantse da Allah" "basu ci bulus ba duk sai na saka ƴan sanda sun ci kutumar ubansu...""" "Zulaikha tana hakimce akan kujera, babu abinda take yi sai ƙyalƙyala dariya amma a hankali. Gogewar da" tayi yasa hatta dariya idan za tayi yanzu a ƙasaice take yi. Kukan da Bintu take rusawa ba ƙaramin faranta mata rai yayi ba. Jin irin maganganun da take furtawa yasa ta ɗaga waya ta kira Hafiz yana ɗauka ta saka a hands free. Su Bintu basu san ta kira shi ba sai jin muryar Hafiz suka yi ya karaɗe kunnuwansu yana ce ma Zulai """Hello Sis! How far?""" """Normal Luvly Bro.""" "Ta faɗa da salon ƙara cusa ma Bintu haushi, kafin yayi magana ta sake cewa" """Yaya kai ne ka turo Bintu ta zane ni da belt sannan ta ɗauki Aadil...?""" """Zana kuma Zulaikha?""" Ya katse ta cikin tashin hankali. """Eh! Ga su nan rirriƙe da belt ita da wannan figaggiyar ƙawar tata wai za su min duka.""" Ta ƙarasa maganar a shagwaɓe. """Ke kuma sai ki tsaya su zane ki? Ke ce fa Zulai shago ta Innaye. Ko rayuwar birni yasa kin zama saiwar-" "sala ne?"" Yayi mata kirarin da Baffa yake mata tana ƙarama, saboda tsabar ƙarfinta, duk yarinyar da ta" kuskura suka haɗa ƙashi da Zulai duk girmanta sai ta kai ta ƙasa. Shi ne Baffa ke kiranta Shago ta Innaye. """Ni ɗin ce dai. Har gobe ruwa na maganin dauɗa Yaya.""" Ta amsa tana dariya. """Yauwa Ƙanwata. Kina ji na? Bintu da ƙawarta mahaukata ne a cikin riguna. Cikin su biyun duk wacce" "tayi gigin taɓa ki nayi miki izini ki ɗaga ta sama ki nuna ma Allah sannan ki damfarata da ƙasa... Allah yasa ma su kakkarya ƙasusuwan baya... kin ga ko babu komai an rage miyagun iri da basu san darajar mutane ba. Kuma a hukumance ba ki da laifi, biyo ki suka yi har muhallinki, kuma ƙwararren lauya za mu" "ɗauka ya kare ki a kotu da cewar garin kare kanki ne tsautsayi ya afka musu...""" Dariyar da yayi ma Zulaikha yawa yasa ta katse kiran tana cigaba da ƙyalƙyala dariya. Tsawon wasu daƙiƙu ta ɗauka sannan ta tsaida dariyar ɗif kamar ɗaukewar ruwan sama. Da ɗaurarriyar fuska take kallon Bintu da jiniyar kukanta ya tsaya sai tsiyayar hawaye. """Kin dai ji ko? Ko a gurin mijinki farashinki ya riga ya daɗe da faɗuwa ƙasa war-was! Sakarya kawai!!!""" Daga Bintu har ƴar kanzagi Raudha an rasa wanda zai tanka ma Zulai da miyagun kalaman da take yaɓa ma Bintu. Har sai da ita da kanta Zulaikha ta gama jan aji ta cigaba da gargasa mata maganganu masu ɗaci. """Tabbas! Ɗanki Aadil yana hannuna. Don haka ki daina wahalar da kanki kina yawo daga wannan gida" "zuwa wancan gida kina nemanshi. Yana gurina, kuma idan sama da ƙasa za su haɗe na rantse da Allah bazan taɓa baki shi ba, matuƙar ba Yaya da kanshi bane yazo ya karɓe shi kamar yadda ya kawo min shi. Ku tashi ku ɓace min da gani kafin inyi rehazal ɗin irin dukan da na sha yima su Ladiyo a dandali akan ku.""" Ta ƙarasa maganar haɗe da miƙewa tsaye. "A ƙauyen Faƙo, Raudha ce take jan Bintu ita kuma tana turjewa. Ayau kuma Bintu ce ta miƙe tsaye ta" "riƙe hannun Raudha ta ja ta a fusace suka fice daga falon, ba tare da sun ɗauki belt ɗin da suka kashe dubu goma sha biyar gurin siyansu ba." "Suna fita daga cikin falon, Zulaikha ta ƙyalƙyale da dariya har tana tafa hannuwa. Al'amarin ya yi mata" "daɗi ba kaɗan ba, zuciyarta cike da godiya ga Allah da ya kasance babu kowa a gidan daga ita sai Imam." Mummy da Karima tun safe suka yi sammakon tafiya gurin aiki. Ita kuma Hajja ƙarfe tara da rabi ta shirya ta tafi rabon dabino da sweet na auren Karima da Hafiz da aka tsayar nan da sati huɗu masu zuwa. Tun jiya da daddare Aunty Rakiya ta kira ta a waya ta bata labarin duk irin ba ta kashin da suka yi da "Bintu. Kuma ta jaddada mata lallai ta zama cikin shiri, domin bisa ga dukkan alamu baza ta rusina ba sai ta gano inda ɗanta yake kuma ta karɓe shi." """Kar ki kuskura ki ɗaga mata ƙafa Zulai. Dukan da naso inyi mata anan ban samu dama ba don Allah ki" "cika min wannan burin.""" "Cewar Aunty Rakiya, muryarta cike da takaicin yadda har yau bata samu damar ɗunɗuma ma Bintu jiki" ba. """Kar ki damu Aunty. Ai ita Bintu ta san karonmu da ita babu daɗi. Za ta kwashi kashinta a hannu.""" Ta amsa tana dariya. "Tun daga lokacin take ta addu'ar Allah yasa idan Bintu ta tashi zuwa su Mummy basa nan, sai kuwa ga" shi addu'arta ta karɓu. Tana wannan dariyar ta ɗauki wayarta da Laptop ta wuce cikin ɗaki inda Aadil ke kwance yana barci cikin "kwanciyar hankali. Yaron da a kwana ɗaya da tayi da shi ta fahimci sam ba shi da damuwa, idan anji kukanshi yunwa yake ji. Da an bashi abinci zai cigaba da wasa da Imam, wanda zazzaɓin dare da yayi ya hana shi tafiya makaranta a ranar." ******* "Tun da ta figi motar suka fice a guje daga gidan Mummy Sauda, tsakanin ita da Raudha an rasa wanda zai" "fara kore zaman ƙuda da yake tsakaninsu. Sai dai daga yanayin yadda Bintu take sauke zazzafan huci akai-akai, take murza sitiyarin da uban ƙarfi kamar shi ya kar zomon, take ƙara taka giyar motar tana ƙara gudu kamar wacce za ta kai wasiƙa, za a fahimci matsanancin ɓacin ran da yake danƙare sunƙi-sunƙi" a zuciyarta. "Da farko ta yi tunanin ita da kanta za ta ladabtar da Zulai, amma a yanzu ta yanke shawarar gara ta haɗa" ta da su Aunty Balira hukumar ƴan sanda su koya musu hankali. Gudun da take zurawa yanzu ba ko ina ta nufa ba sai ofishin kwamishinan ƴan sanda. "Kiran da Babbar Yayarsu Aunty Sadiya tayi mata, shi ya katse duk wani hanzari da take tafe da shi. Kamar" "baza ta ɗauka ba, sai kuma ta ɗaga bayan ta yi tunanin haka kawai Aunty Sadiya ba ta kiran mutum a" waya sai da ƙwaƙƙwaran dalili. """Helloo Aunty...""" """Bintu kina ina ne?""" Ta katse ta da tambayar da muryar da ke bayyana rashin wasa. "Har Bintu ta buɗe baki za ta faɗa mata gaskiya, sai kuma tayi tunanin gara kawai tayi mata ƙarya. Domin" za ta iya dakatar da ita daga ƙudurinta. """Ga ni a hanya zan koma gidana...""" """Gidanki ko gidan Hafiz?""" Ta sake jefa mata tambayar a tsawace. Kafin Bintu ta amsa ta cigaba da cewa """Anya Bintu ko dai kin fara shaye-shaye ne bamu sani ba? To duk inda kika nufa ina umartarki da" gaggawa ki juyo kizo ki sameni a gidan Daddy... Tunda hauka da rashin hankali da rashin kunyar ɗan fari "yasa ki iya rufe ido ki zazzagi uwar mijinki da yayyensa sai ki dawo gida ki cigaba da zama a ɗakin Mashku... Ga takardarki Hafiz ya kawo min ni kuma na kawo ma waɗanda suka haife ki...""" "Ƙit! Wayar ta katse, daga can ɓangaren Aunty Sadiya." "Bintu da ta kasance cikakkiyar bahaushiya gaba da baya, kalaman Aunty Sadiya duk da da hausa tayi su" sai suka sauka a kunnenta kamar da wani irin yare ne da bata taɓa sani ba. Sam! bata fahimci me "maganganun suke nufi ba, infact bata ma fahimci inda suka nufa ba. Da wani yanayi mai wuyar fassaruwa ta kalli Raudha, kasancewar a handsfree ta saka wayar bayan ta ɗaga" """Ko kin fahimci inda maganganun Aunty Sadiya suka nufa?""" Tsaf! Raudha ta fahimta. Amma tsoron aji mutuwar sarki a bakinta ga shi suna tsakiyar babban titi yasa tayi saurin gyara yanayin tashin hankalin da maganganun Aunty Sadiya suka jefa ta tace """Nima dai ba wani fahimta nayi ba. Amma na san bai wuce ace Hafiz ya kai ƙararki gidanta ita kuma" "taje ta faɗa ma su Mummy. Don haka ina ga ki bar batun zuwa gurin kwamishina yanzu, kije ki ji kiran da take miki.""" """To shi kenan. Bari in fara sauke ki a gida...""" """Ai ba ma sai kin kaini gida ba Bintu. Sauke ni anan in samu taxi ya ƙarasa da ni. Gara kiyi gaggawar" "zuwa kiji dalilin kiran, idanma wasu ƙarerayin Hafiz ya shirya miki kiyi gaggawar warwarewa da bayanin" "gaskiyar abinda ya faru. Idan basu yarda ba kina iya kira na in bada shaida.""" """Na gode Raudha. Allah yabar ƙauna da zumunci. Shi yasa a kullum ba na gajiya da godiya ga Allah da" "ya bani ke matsayin babbar ƙawa.""" """Kar ki damu Bintu. Kin cancanci fiye da haka a gurina.""" "Da haka suka rabu, zuciyar Bintu cike da karsashi da ƙwarin gwuiwa, ita kuwa Raudha zuciyarta cike da" "fargaba, da addu'ar Allah yasa Hafiz ba sakin Bintu yayi ba. Tunda da kunnenta ta ji maganar takarda, to wace takarda ce kuwa za ayi maganarta idan ba ta saki ba?" "Bintu tana shiga layin gidansu da mota, ta hangi motar Hafiz na fitowa daga cikin layin. Lokaci ɗaya" zuciyarta ta ƙara ƙuntata da ɓacin rai. 'Kenan zancen Raudha ya tabbata?' """Uhmmm! Namiji kenan! Ƙudan zuma ga zaƙi ga harbi. Na rantse da Allah ko me za kayi Hafiz kai da su" "Umma baku isa ku hana ni ƙwatar ƴancina ba a matsayina na uwa.""" "Tayi maganar a fili cikin masifa, ko da suka zo gitta juna daƙyar ta iya dannar zuciyarta bata buɗe gilashi" ta watsa mishi daƙuwa ba. "Ta ja motarta a guje ta wuce shi ma ya cigaba da tafiya, ko ɗan horn ɗinnan babu wanda ya latsawa juna," kamar dai ba su ne masoyannan da suke bala'in ƙaunar junansu ba. "Ko da ta isa gida, da farko ta shiga ne da wani irin fitinannen izza da jiji da kai. Sai da taga ba a cikin falon" "mahaifiyarta bane Aunty Sadiya da sauran yayyenta maza uku suke zaune. Suna cikin falon mahaifinta ne, kuma ƙarin ɗaga hankali a gareta shi ne idanun magahaifiyarsu da Aunty Sadiya ya yi jajur, alamu ƙarara da ke nuna sun ci kuka sun gode Allah." "Tun daga nan jikinta ya fara sanyi. A ɗarare ta nemi kan kafet ta tsuguna, bayan ta yi sallama babu" wanda ya amsa mata a cikinsu. """Daddy...""" Wani gigitaccen tsawa da mahaifinta ya daka mata yasa bata san sadda ta zame daga tsuguno tayi "zaman ƴan bori a ƙasa ba. Lokaci ɗaya idanunta suka kawo ruwa, lallai wannan shi ne a dake ka a hana ka kuka." "Bata daddara ba da tsawan da yayi mata ba, don ta sha alwashin baza ta taɓa bari shirunta ya ja Hafiz ya" "ci galaba a kanta ba, cikin rawar murya da saurin baki ta sake cewa" """Daddy don girman Allah ka bari inyi muku bayanin gaskiya...""" """Ba ma buƙatar wani bayani na gaskiya daga bakinki Bintu.""" "Ya sake katse ta a karo na biyu, da yanayin magana mai bayyana ɓacin rai a fili." Kafin ta amsa ko ƙoƙarin kare kanta ya cigaba da cewa """Mun ji gaskiyar zance daga bakin yayyen mijinki biyu da aka kira a waya aka saka su a handsfree." Sannan Mun ji rekodin ɗin muryarki jiya da kika je tsakiyar ɗakin sarkuwarki a can ƙauyensu kika yi mata cin mutunci na ƙarshe ita da ƴaƴanta. Sannan mun ji bayanin yadda kika je gidan ƙanwar mijinki yau za kiyi mata duka. Daga nan ɓangarenki kuma Yayarku ga ta nan ta kora mana bayanin duk irin rashin mutuncin da taga kin yi ma dangin mijinki lokacin haihuwar ɗanki. Wannan shi ya ƙara tabbatar mana da "gaskiyar maganganun mijinki da ƴan'uwansa. Don haka ki riƙe bayanin gaskiyarki, wata ƙila za tayi miki" "amfani a gaba. A ƙarshe dai ungo wannan.""" Ya ƙarƙare maganar haɗe da ɗaukar wata farar nannaɗaɗɗiyar fallen takardar da tun shigarta cikin falon "bata lura da ita ajiye kusa da shi ba, sai yanzu da ya ɗauka ya miƙa mata." "Da farko ƙin karɓa tayi, sai da Yayanta Faruƙ da yafi sauran zafi ya ƙunduma mata ashariya haɗe da" "yunƙurawa zai mare ta sannan ta karɓi takardar a tsorace. Lokaci ɗaya Jikinta ya ɗauki rawa, kamar wacce aka watsawa ruwan sanyi lokacin hunturu." Duk da bata buɗe takardar ta ga ko ta mece ce ba haka kawai jikinta ke bata babu alkhairi ko kaɗan tattare da wannan takarda. Yayanta Abubakar ne ya fara magana shi ma da nashi salon ɓacin ran. """Kin bani kunya Bintu. Na rantse da Allah ban taɓa tsammanin irin wannan munanan halayen daga" "gareki ba. Haba!! Sai kace wacce bata yi ilimin boko da Arabi ba? Ta ina kika taɓa ji mata ta fi uwa da ƴan'uwa? To bari in sake tuna miki, ana canja mata, amma ba a taɓa canja uwa da ƴan'uwa. Don haka kin ga yanzu ga sakamakon ƙoƙarin raba miji da danginsa nan kin karɓa, zai canja ki, amma bazai taɓa" "canja ƴan'uwansa ba. Dubi nan""" Wayarsa ya buɗe ya lalubo hoton Invitation card ɗin Auren Hafiz da Karima ya matsa har kusa da inda take zaune tana rawar ɗari ya aje mata a cinyarta. "Duk yadda ta so ta runtse idanu don kar ta karanta hoton I.V ɗin kasawa tayi, raɗau idanunta suka sauka" "akan hoton, cikin ƙanƙanin lokaci ta haɗa baƙaƙen ta karanta sunayen da ke manne a jikin hoton." "Wata wawuyar bugawa zuciyarta ya yi, cikin ƙanƙanin lokaci ta fara jan numfarfashi daƙyar, kuma sama-" sama kamar mai cutar athma. Hannunta shi ya jagoranci umarnin zuciyarta gurin warware fallen takardar da ke damƙe a hannunta don ganin me ta ƙunsa. "_"".... Hafiz Aminu Faƙo na saki matata Fatima Bintu saki ɗaya...""_" "Kalaman da suka manne a cikin idanun zuciyarta kenan, kuma kalaman da suka ƙara assasa hauhawar" bugawar zuciyarta fiye da misali. "A haukace, cikin ɗimuwa, gigita, ficewar hayyaci Bintu ta miƙe tsaye a zabure. Tayi taku ɗaya, biyu, uku," sai kuma ta zauna daɓas! Ta ɗaga idanu a gwalale ta kalli Ummansu da Aunty Sadiya. Sai kuma kamar tsikarin basir ta ƙwalla wani gigitaccen ihu! Sai kuma ta ɗauke Ɗif! Kamar an saka seletef an ɗaure mata baki. "Da saurin gaske ta sake miƙewa tsaye, ta tattare siket ɗin jikinta za ta yanka da gudu Yayanta Aliyu da" "yake mata kallon wacce gigita yasa ta haukace yayi gaugawar damƙo kafaɗunta, da ƙarfin gaske ya" girgiza kafaɗunta haɗe da ƙwalla kiran sunanta da ƙarfi. """Yaya... Hafiz... Ya sake ni... Na mutu...""" Daga faɗin haka sai ta tafi luuuu ta kife a kafaɗunsa a sume. ******** Tabbas da gaske ne... A yayinda saki ya shiga tsakanin ma'aurata biyu wanda ya kasance bai da gaskiya shi zai fi jigatuwa. Irin haka ne ya kasance a ɓangaren Bintu. Shi kuwa Hafiz kwanakin da suka biyo baya harkokinsa yake yi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. "Shirin aurensa yake yi a nutse, rashin Bintu a gidanma sai ya bashi damar cin karensa babu babbaka." "Soyayya mai lasisi kuma irin ta bugawa a jarida suke sha shi da Karima, a gefe guda kuma Zulaikha tana" ƙara ƙarfafa masa gwuiwa akan duk wasu shirye-shirye nasa. Sai a yanzu ne ya fahimci ma'anar karin maganar da Aunty Balira take yawan faɗa masa na *RANAR "NAKA SAI NAKA...*, In banda Zulai ta kasance nasa ta ina ƙaramar yarinya kamar Zulai da ko haihuwa" bata yi ba za ta karɓi yayen Aadil? Sai ga Hafiz duk yadda yake yawan faɗi a baya cewa Zulai ba ta da hankali yanzu ba shi da abokiyar "shawarar da ya wuce Zulai. Tsarin yadda za'a fasalta gidansa a canja masa tsari, da yadda za'a fitar da" gurin saukar baƙi ƴan'uwansa duk da ita yayi shawara. "Haka ɓangaren haɗa kayan akwati, ba tare da jin zafin kuɗi ba haka ya dinga antaya mata manyan" kuɗaɗe tana shiga kasuwa ita da Hibba da Karima suna haɗo kayan akwati. Ba tare da ƙyashi ba kuwa "Zulai ta dinga zaɓo komai mai bala'in tsada, cikin ƙanƙanin lokaci ta haɗa mishi akwatuna guda goma sha biyu cif!" Sai daga baya ne ma da Mummy ta ga kayan tayi faɗa kamar za ta ari baki. Ta rage kaya masu yawa har akwati biyu ta damƙa ma Zulaikha da cewar lallai ta aika ma Innaye da su Aunty Balira su samu na cin buki. "Ko da Hafiz yaje gidan, Zulaikha ta faɗa mishi yadda aka yi kuma ta nuna mishi kayan ba ƙaramin kimar" Mummy ne ya ƙaru a idanu da zuciyarsa ba. A ransa yake ji lallai yanzu ne fa zaiyi aure. Idan ya kalli Aadil kuwa farin ciki da nishaɗinsa ƙara ninkuwa yake yi. Duk yadda Bintu take ji tana "gatanta yaron sai dai kawai ace ita ta haife shi, amma ko rantsuwa yayi babu kaffara an fi gatanta shi a gidan Mummy fiye da gurinta." "Kuma wani abun burgewa shi ne yaron sam yanzu ba ya ƙwuiya, ga wani wayau da ƙiba, kyau na" "musamman da yaron ya ƙara. Ba shi gurin Mummy, ba shi gurin Karima, ba shi gurin Hajja, balle kuma" Zulaikha da take riritasu shi da Imam kamar su kaɗai ne ƴaƴaye a duniya. ******** Tsawon sati biyu kenan da faruwar al'amarin amma Bintu ta kasa komawa dai-dai. Tun iyayenta suna "hantarar ta, suna share al'amarinta, suna watsi da damuwarta, har sun zo sun fara tausaya mata. Amma a ɓoye, saboda dukkansu sun san irin matsanancin soyayyar da take ma Hafiz." "Duk wanda yasan Bintu a baya, idan ya ganta yanzu abu na farko da za'a fara tambaya shi ne" """Ta yi rashin lafiya ne?""" "Ƙara auren Hafiz, da sakin da yayi mata na bagatatan, wasu abubuwa ne da ko ana yaƙin duniya na uku a" zamantakewar aurensu bata taɓa tsammanin za su gitta a tsakaninsu ba. Ta daɗe da gama sakankancewa Hafiz na ta ne ita kaɗai. Don ita kaɗai aka halicce shi kamar yadda aka halittota don shi kaɗai. Duk da tun kafin faruwar wannan al'amarin zamantakewar na su ya ɗan fara tangal-tangal sanadiyyar sakaci da kasa danne zuciyarta ita bata taɓa tsammanin zai iya kallon wata ƴa mace da idanun so balle har ya nemi sama mata sarari a filin zuciyarshi ba. Saki kuwa... Idan ta tuno wannan kalmar wasu sababbin hawaye ne ke sake ɓalle mata kamar an buɗe famfo. 'Ita Bintu Hafiz ya saka? Ita? Ita Bintu fa?' Zuciyarta na cika da tantamar anya kuwa Hafiz ne da kanshi ya iya sakinta? Ko dai wani mai baƙin ciki da aurensu ne ya shiga rigar Hafiz ya tafka wannan ƙatoton kuskuren? Sai ta yi kamar baza ta yarda da sakin ba kuma sai ta tuna ai ranar da abin ya faru ta ga ficewar Hafiz daga layinsu. Kuma wanda ya bata takardar sakin wani mai mutum ne mai muhimmanci a rayuwarta da bazai taɓa yi mata ƙarya don ya kassara ta ba. "A cikin waɗannan kwanakin ƙunci da raɗaɗin, ta yi Allah ya isa ga Innaye da ƴaƴanta mata ya fi baki" dubu!! Domin ita a ganinta duk su ne ummul-aba'isin faruwar waɗannan munanan al'amura a gareta. "A karo na barkatai, ta yi juyi akan gadon, zuciyarta cike da ƙunci da matsanancin damuwa. Sannu a" "hankali ta fara jan shessheƙar kuka kamar yadda ta saba, tana yi tana taushe bakinta don kar Mashku ta" ji kukan da take yi. "A karo na farko, tun bayan faruwar al'amarin da tsawon dararen da ta kwashe tana raba biyu bisa uku da" kuka Mashkura ƙanwarta da suke kwana ɗaki ɗaya tayi mata magana a tausashe. """Aunty Bintu a ganina kukan nan da kike kwashe tsawon lokaci kina yi ko wane dare, ke baki yi barci ba," ni baki barni na yi nutsattsen barci ba bazai taɓa miki magani ba. Why not baza ki ɓata lokacin kukan "akan dadduma kina kaima mahaliccin sammai da ƙassai kukanki ba...?""" """Mashku... Don Allah ki faɗa min. Aduk cikin wannan al'amarin ina abin saki? Me nayi ma Hafiz da zai" "sake ni? Me nayi masa?""" Ta katse Mashkura da jerin tambayoyin muryarta na fita da matsanancin kuka. Abu ɗaya da Mashkura ta fahimta a maganganun Bintu shi ne har yanzu ita bata yi da na sanin abinda "tayi ba. Kamar ma laifin ɗungurungum ta kwashe ta ɗora kan Hafiz ne da danginsa, bayan kuma ita ke da laifi kaso casa'in da biyar bisa ɗari." "Kafin ta amsa ɗaya daga cikin tambayoyin Bintu, lalubawa tayi a kusa da filonta ta ɗauko wayarta ta" "duba lokaci, ƙarfe uku da minti arba'in na dare. Barci ne sosai a idanunta, don haka ta katse dogon" maganar da Bintu ke neman jan ta da shi ta hanyar cewa """Uhmmm! Ba ni da amsar ɗaya daga cikin tambayoyinki Aunty Bintu. Ni dai shawara kawai na ba ki, da" "ki dinga ɓata tsawon lokaci kina rusa kukan da bazai miki magani ba, gara ki dinga ɗaukan lokacin kacokan kina kai ma Allah kukanki. Ko babu komai za ki samu sanyin zuciya da nutsuwa. Allah ya tashe" "mu lafiya.""" Daga haka bata sake ce mata komai ba ta juya mata baya. "Da yake Bintu ba ta daga cikin irin matannan da ibada ya dame su, duk da wannan shawarar da ƙanwarta" "ta ba ta bata yi amfani da shi ba. Sharɓen Kukanta ta cigaba da yi, tana haɗa da jan ajiyar zuciya tana saukewa, ta ɗauki tsawon lokaci a haka har zuwa sadda gwanin iya sata da taimakon shaiɗan yayi awon" "gaba da ita, lokacin ana ta kiraye-kirayen sallah a wasu masallatai." "Washe gari, kamar yadda Raudha ta saba zuwa gidan duba jikin Bintu duk bayan kwana biyu, misalin" ƙarfe huɗu na yamma tayi ma gidan dirar mikiya. "A waɗancan kwanakin, duk zuwan da take yi bata taɓa samun damar yin nutsattsen hira da Bintu ba." "Cikin kuka ta faɗa mata Hafiz ya sake ta, sannan kuma zai ƙara aure. Daga haka har ta bar gidan ba ta" "ƙara samun kan Bintu balle har suyi wata doguwar magana, sai dai ta gama zamanta da maɗaukakin" damuwa a fuskarta daga bisani tayi ma Umma sallama ta tafi. "A yau, ko da ta isa gidan ta yi mamakin samun Bintu cikin ƴar nutsuwa kaɗan. Ta yi wankanta tsaf, duk" "da dai babu ko ɗigon kwalliya a fuskarta. Wayarta ne ma a hannunta tana dannawa, fuskar nan a ɗaure tamau." """Raudha... Ashe don tsabar wulaƙanci tun ranar da muka je Faƙo misalin ƙarfe biyar da rabi na yamma" "Hafiz ya turo min saƙon saki ta text message...""" """Da gaske kike yi?""" Raudha ta jefa mata tambayar da mamaki a murya da fuskarta. "Bata iya amsawa ba, sai wayar ta miƙa mata tana nuna mata saƙon." """Uhmmm! Allah ya kyauta... Sai haƙuri kawai.""" "Raudha ta faɗa jikinta a sanyaye, bayan ta gama karanta saƙon." """Ni yanzu kin san menene damuwata?""" """A'a! Sai kin faɗa!""" Raudha ta amsa mata. """Wace ƴar iskar matsiyaciya tsinanniya annamimiyar yarinyar ce za tayi gangancin aura min miji uban" "ƴaƴana? Duk tunanina ya ƙuƙe, na rasa gane wace Karimatu ce? Ko dai wata baƙauyiyar ce matsiyatan danginsa da basa ƙaunar Allah da Ma'aiki SAW suka sake haɗa shi da ita...""" """Uhmmm! Za kiyi mamaki idan na ce miki Nurse Karima ce, ƴar gidan Hajiya Saudah da kike kira" "Mummy sama Mummy ƙasa...""" """Mmmmm me kika ce Raudha? Dddddddda gaske kikkkkkkkeeee yi?""" Bintu ta tambayeta da wata fitinanniyar in'ina a muryarta saboda tsananin tashin hankali. """Wallahi da gaske nake yi. Lamarin maza ba sai dai a barsu ba Bintu? Abinda ya kawo ni gidanki kenan" "ranar sai na tarar da ke cikin tashin hankalin ɗauke Aadil da Hafiz yayi.""" "Gyara zama Raudha tayi, ta kora ma Bintu labarin duk abinda ya faru wancan ranar a asibitinsu gaban" idanunta. """Karima dai Raudha? Karima? Yanzu sakayyar da Mummy za tayi min kenan? Ni ce fa na shiga na fita" "har na sama mata aiki a asibitinmu, ashe sakayyar da za suyi min kenan?""" Ta jera ma Raudha tambayoyin cikin rawar murya da tashin hankali. Kafin Raudha ta amsa ta cigaba da cewa """Saboda Allah me Karima take da shi wanda ni bani da shi da har za ta ɗauki hankalin Hafiz...""" """Uhmmm! Bintu kenan! Sau nawa ina faɗa miki Namiji ɗan kunama ne ga zaƙi ga harbi kina saka" "auduga ki toshe kunnenki? Ko da yake yanzu da layi ya biyo ta kanki ai za ki ƙaras a gaba.""" Raudha ta katse mata sambatun da take yi hankalinta a tashe kamar wacce ƙwaƙwalwarta ya fara taɓuwa. """Bar tuna min Raudha! Don girman Allah ki bar tuna min.""" "Bintu ta katse ta da sauri, da murya mai bayyana matsanancin takaicin da zuciyarta ke ciki. Babbar" "yatsarta ta sanya ta ɗauke wasu zafafan hawaye da suka sake taruwa a kwarmin idanunta. Da asubahin ranar tasha alwashin in Allah ya yarda za ta danne zuciyarta baza ta sake yi ma wannan mummunan al'amarin kuka ba, amma duk yadda ta so tsayar da fitar hawayen ta kasa, shi yasa take saurin share" hawayen tun kafin su gangaro zuwa kumatunta su saka ta azumin kaffara. "Nannauyar ajiyar zuciya ta ja ta sauke, a hankali ta cigaba da cewa" """Abinda ya wuce mu barshi a matsayin wanda ya wuce Raudha. Ilimi ɗaya da na ƙaru da shi a cikin" "kwanakinnan shi ne, duk mazajen duniya halayensu ɗaya, kuma a kullum sauyawa suke yi kamar wahainiya. Lallai da gaske ne duk matar da ta ɗauki namiji uba za ta mutu marainiya... Yanzu dai mafita nake nema da gaggawa... Ya zanyi Raudha? Ya zanyi? Wallahi zuciyata zafi da tafarfasa take min kamar" "za ta babbake... Don Allah ki taimaka min""" """Kul! Kul!! Kul Bintu!! Kar ki kuskura ki bari zuciyarki ta buga akan namijin da idan kika mutu yau, ya yi" "tsananin daɗewa ne yayi wata shida zai manta da shafinki ya buɗo na wata kamar yadda yake shirin faruwa da ke a yanzu.""" "Ta yi shiru tana mayar da numfashi, sannan ta cigaba da magana a hankali, tana yi tana waige-waige," alamun duk abinda za ta faɗa ba ta so kowa ya ji """Akwai mafita... Amma sai kin nutsu sosai kin saurare ni da kunnen basira...""" Jikinta a sanyaye ta tari numfashin Raudha da cewa """Allah yasa dai mafitar ba na bin hanyar da Hajiya Rabi ta faɗa min rannan bane.""" Sai da Raudha tayi dariya sannan ta amsa da """Wannan old version kenan ai. Ita ma don tsohuwar yayi ce shi yasa har yanzu take ganin idan ba ta" hanyar malamai da bokaye da ƴan tsibbu ba babu hanyar da za ta bi wajen ladabtar da ƊA NAMIJI har "yayi laushin da zai rusuna mata...""" "Fitowar Mashkura daga banɗaki, wacce shaf Bintu ta manta da shigarta daf da Raudha za ta shigo cikin" "ɗakin, shi ya katse Raudha daga maganganun da take yi masu ɗauke da zallar cika baki." "A tsorace suka kalli Mashkura, itama ta ɗaga idanu tayi musu wani kallo mai bayyana ƙasƙanci ƙarara." Sannan ta ɗauki hijabin sallarta ta zura a jikinta ta fice daga ɗakin. Da damuwa sosai a fuskar Raudha ta ce """Na shiga uku ! Amma dai Bintu baki kyauta min ba. Me yasa tun ɗazu baki faɗa min Mashkura tana" "bayi ba kika barni ina ta zuba zance? Allah dai yasa bata ji maganganun da nake yi ba...""" """In Allah ya yarda ma bata ji ba. Wallahi sam na manta ta shiga wanka sadda kika shigo, kuma kin santa" "da bala'in daɗewa gurin wanka kamar wacce za ta canja halitta. Yanzu dai ina ga ki tashi kawai ki tafi, ma" "ƙarasa zancen da muka fara yi a waya...""" Numfashin maganarta ne ya ɗauke ɗif lokacin da Ummansu ta shiga cikin ɗakin da wata iriyar "murtukakkiyar fuska, kamar bata taɓa dariya ba." A ɗarare duk su biyun suka kallete da yanayin rashin gaskiya. Da saurin gaske Raudha ta yayimi jakarta da mayafi ta miƙe tsaye. """Bintu bari in wuce, sai na sake leƙowa...""" """Ki leƙo ina Raudha?""" Ummansu ta tambayeta cikin tsawa. """Munafuka algunguma, dama ke ce kike hure mata kunne har kika hana ta zama gidan mijinta bayan" "ke kina naki gidan?""" Cikin rawar murya da in-ina Raudha ta fara yunƙurin kare kanta. """Babbbbbbaaaa haka bane Wallahi Umma...""" """Idan ba haka bane to yaya ne? Saurareni ki ji da kyau!! Daga yau, na raba ki da Bintu tunda dai ke ba" "ƙawar arziki bace. Idan kuma kika bari na sake samun labarin kin zo gurinta, ko kuma ita taje gurinki har a ganku tare, ko kuma ki kirata a waya ko ita ta kira ki na rantse da Allah da Aliyu zan haɗa ki. Kuma kin san halinshi sarai, don ya bi ki har gidan mijinki ya hukunta ki ba abinda ya dame shi bane. Ɓace min da" "gani munafuka kawai.""" "Sum-sum Raudha ta fice daga ɗakin kanta a ƙasa, hankalinta a ɗugunzume, ko ƙwaƙƙwaran kallo ta kasa" ɗaga idanu tayi ma Bintu balle mahaifiyarta. "Har ta fita daga ɗakin, Bintu ko ƙwaƙƙwaran motsi ta kasa yi, tsumu tayi a zaune inda take kamar kazar" "da aka tsamo a cikin ruwan zafi. Hankalinta a tashe ainun, miyaun bakinta ya ƙafe ƙaf! Ta rasa wasu irin kalamai ne ya kamata tayi amfani dasu gurin ba Ummansu haƙuri." """Ke kuma na dawo gare ki! Sakarya! Wawuya!! Shashasha!!! Wacce duk irin shekarun da tayi a duniya" "bata san inda yake mata ciwo ba.""" Mahaifiyarta ta katse mata tunani da faɗin waɗannan maganganun cikin matsanancin fushi da ɓacin rai. Kafin ta buɗe baki tayi magana Umma ta cigaba da cewa """Ba ni da lokacin ɓatawa wajen baki shawara Bintu, saboda kin daɗe da goge min hadda, kin yi abinda" "ban taɓa tsammanin ko rabi-rabinshi za ki aikata ba. Abinda ya faru yasa na daɗe da yanke tsammani a kanki Bintu. Magana ɗaya zuwa biyu zan faɗa miki a yanzu, idan kin so ki bi, idan baki so ba za ki iya aikata duk abinda ya kwanta miki a rai. Ni kuma za ki ga abinda zan aikata a matsayina ta wacce tayi" naƙudarki zuwa duniya. "A matsayina na mahaifiyarki, daga yanzu har zuwa nan gaba ko da wasa kika yi yunƙurin aikata wani abu," "ko sakawa a aikata wani abu da zai cutar da Amaryar Hafiz, ko shi kanshi Hafiz ɗin, ko auren da yake" "yunƙurin yi ban yafe miki ba.!""" "A haukace Bintu ta ɗago kai, jikinta babu inda ba ya rawa, daƙyar ta iya buɗe baki ta ce" """Umma...""" Da saurin gaske Umma ta ɗaga mata hannu alamar dakatarwa. """Magana ta biyu shi ne idan kika sake zuwa gurin Raudha, ko kiranta a waya, ko ita ta kira ki a waya" kika ɗauka har kika yi amfani da ɗaya daga cikin munanan shawarwarin da take baku ban yafe miki ba. "Na ga kamar dusa ne a ƙwaƙwalwarki, dole sai ana yi ana taka miki burki ƙarfi da yaji. Sakarya kawai.""" "Da gama faɗin haka bata tsaya saurararta ba ta fice daga ɗakin, bayan ta ja wani dogon tsaki kamar" bakinta zai taɓa ƙasa. Ta fita ta bar Bintu cikin wani mawuyacin hali na tashin hankali. Zuciya da ƙwaƙwalwarta a tsaye cak! Ta ma rasa wani irin tunani ya kamata tayi? ******* "Labarin sakin da Hafiz yayi ma Bintu, abu ne da ya zama a sirrance ta ɓangaren Hafiz ɗin. Ko da wasa" "baiyi gigin faɗa ma wani daga ɓangarensa ba, hatta Zulai da a yanzu suke very close da ita." Bayan sati biyar da faruwar al'amarin ne Mahaifin Bintu ne ya kira Alhaji Lurwanu yake mishi ƙorafi kan yadda bai kira shi a waya ya jajanta mishi kan abinda ya faru ba. "Mamaki mai girma ne ya kama Alhaji Lurwanu, da takaici sosai a muryarsa yake nuna damuwar yadda" Hafiz ɗin ya iya sakin Bintu ba tare da ya kai mishi ƙorafinta ba. """Uhmmm! Shi fa Hafizu ba shi da laifi Alh Lurwanu. Gaba ɗaya laifin na Bintu, kuma ko ni ne a matakin" "da yake kai iya hukuncin da zan iya ɗauka kenan zuciyata tayi sanyi-sanyi.""" Ba tare da ɓata lokaci ba ya kora ma Alh Lurwanu bayanin duk abinda ya faru. """Ikon Allah! Amma kuwa in dai haka ne Bintu bata kyauta ba. Sai dai kuma shi Hafizu kamar ya yi" "gaggawa gurin sakinta. A sanina akwai hanyoyi da dama na ladabtar da mace, saki shi ne mataki na" ƙarshe-ƙarshe bayan duk an bi waɗancan hanyoyin an kasa cimma matsaya. "Amma Alh Aminu (Baffa) ya sani kuwa?""" """To gaskiya ba na jin shi ma ya sani, don dai bai kira ni ba. Ko kai ɗinma dalilin da yasa na kira ka ganin" "yadda Bintun ta kasa haƙura ta rungumi ƙaddara ne. To ya zanyi? Hannunka ba ya ruɓewa ka yanke ka yar Lurwanu. Duk da dai ita ce ba ta da gaskiya, kuma har yau na kasa nuna mata a fili ina tausaya mata. A can ƙarƙashin zuciyata ina jin zafin yadda ta lalace, ta ƙare, ta shiga cikin halin ƙaƙa-ni-kayi. Ko gurin" "aiki fa ba ta iya zuwa, a yanzu idan ka ga Bintu na rantse ba lallai ka gane ta ba." "Don Allah idan da hali kayi wani abu akan lamarin...""" """Yin wani abu ya zama dole Alh! Amma ina roƙonka alfarma ɗaya. Alfarmar kuwa ita ce don Allah" "yanzu muyi ma Hafiz uzuri, ka ga jibi idan Allah ya kaimu za'a ɗaura aurenshi... Muyi haƙuri, zuwa sati na sama idan mai duka ya kaimu da kaina zanyi takakkiya zuwa Ofis ɗin shi in ji ya za mu ɓullo ma al'amarin. Ka kwantar da hankalinka, in sha Allah komai zai zo ya wuce...""" """Ba damuwa Alh! Na gode.""" ****** Ta ɗauki tsawon mintuna goma sha biyu hawaye masu zafi na sauka daga kwarmin idanuwanta. "Duk da hawayen da ke jerangiyar sauka daga idanunta, kallon fili da na idanun zuciyarta bai ɗauke daga" kyakkyawan hoton free wedding pic na Hafiz da Amaryarsa Kareema ba. "Zuciyarta ƙuna, raɗaɗi, zafi, azaba take yi mata, kamar za ta faso ƙirjinta ta fito don tsananin baƙin ciki da" takaici. """Yanzu shi kenan? Tana ji tana gani za ta sadaukar da mijin da ta gama shan wahalar ɗawainiyarsa ga" "wata banza can da bata san darajarsa ba?""" "Ƙarin baƙin cikinta shi ne, Hafiz ɗin ne da kanshi ya saka kyawawan hotunan a status ɗin shi na whatsapp." """Yanzu shi kenan har Hafiz ya manta da babinta a rayuwarsa?""" "Yatsa ta saka, ta ƙara zumin ɗin hoton fuskarsa tana ƙara kallon wani masifaffen kyau da yayi. Dama can" "Hafiz mai kyau ne, kyawunsa na ɗaya daga cikin abinda yasa take mutuwar son Hafiz. Domin idan ba faɗa aka yi ba, irin kyawun Hafiz da gayunsa ko rantsuwa aka yi babu kaffara za a ce bai haɗa jini na kusa" ko na nesa da mutanen ƙauye ba. *Assalamu alaikum* Ina yininku? Akwai set ɗaya na maganin mata wanda wani malami ya haɗa bisa amana. Amma don "girman Allah ƴar'uwa ki ji tsoron Allah idan kin san ba kya fama da matsala tsakaninki da mijinki kar ki siya. Saboda maganin ya taɓo wani ɓangare na mallaka, wata ƴar'uwa ce da mijinta ke neman mata aka haɗa ma maganin. To kuma cikin hukuncin Allah sai auren ya mutu kafin isowar maganin, kun ji dalilin da" yasa na tallata maganin. Kuɗin maganin 10k ne. Idan baki shirya ba don Allah kar ki taɓo ni ta pc. Maganin rashin haihuwa. Cutar sanyi na infection ko wani iri. Maganin cancer ko wane iri. Maganin wankin nono ga masu jego. Maganin sanyi na masu jego. Da sauran cututtuka in sha Allah muna da ingantattun magunguna na gargajiya akan farashi mai sauƙi "07039080978, 09077591726" """Yanzu haka za ta zauna ta naɗe hannu a ƙirji ta zura ido tana ji tana gani wata mace can da ba ita ba ta" "mallaki Hafiz bayan ita ta gama shan wahala da shi?""" Ta sake tambayar kanta a fili. Lokaci ɗaya jikinta ya ɗauki rawa kamar ana kaɗa mata ganga. "Umarnin zuciyarta jikinta ya bi, ba don ranta yana so ba ta talubo lambar Hafiz ta danna mishi kira. Cikin" "ƙanƙanin lokaci wayar ta fara ringing daga can ɓangaren, ƙarar da yake bugawa kamar da sautin bugun" zuciyarta. "Daga can ɓangaren Hafiz, barci yake yi hankalinsa kwance. Sun shafe fiye da mintuna talatin suna hira da" "Kareema a waya tana ta zuba mishi shagwaɓa da ƙananun koke-koke. wacce rashin ganinta da baya yi kwanaki biyar kenan wai an ɓoye ta ana mata gyaran jiki, ko ya je sai dai ya gama hira da Zulai da Hajja yasa shi rage zuwa gidan, sai dai bini-bini kaɗan zai kira ta, ko kuma ita ta kira shi tayi ta ƙara rikita shi da" zafafan kalamai na soyayya. "Yana cikin nutsuwa ƙwarai, irin nutsuwar nan da shi da kanshi idan aka titsiye shi bazai iya tuna lokacin" "da yake cikin makamanciyar wannan nutsuwar ba. Bintu, da duk wani abu da ya shafeta ya tattara shi ya ajiye gefe ɗaya." Daman a gyaran gidan da yayi duk wasu abubuwa nata da suke cikin ɗakinsa ya tattara ya mayar mata "da su ɗakinta. Idan ya kwanta, barcinsa yake kwasa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, ko mafarki zaiyi na Karima yake yi, saboda ita ce a cikin zuciyarsa." "Gaf da kiran zai tsinke, ya jiyo vibration ɗin wayar kamar a mafarki. Daƙyar ya iya miƙa hannunsa ya" "lalubo wayar, ba tare da ya duba mai kiran ba kawai ya ɗauka ya kara a kunne." Hafiz yana ɗaya daga cikin mutanen da suke da ɗabi'ar idan suka farka daga barci mai nauyi suna ɗaukar "wasu sakanni kafin suyi magana. Don haka ko da ya ɗauki wayar, shiru yayi yana ɗan mayar da numfashi a hankali." Shessheƙar kuka da ya fara jiyowa yana tashi ƙasa-ƙasa ta cikin wayar yasa shi ƙarasa wartsakewa. Ya "ɗan buɗe idanu kaɗan, sai kuma ya ciro wayar daga kunnensa ya kalli fuskarta. Ganin Bintu ce akan layi" "yasa fuskarsa faɗaɗa da yanayin mamaki, mamaki na sosai, ba kaɗan ba fa. Abu ne da anan kurkursa bai" taɓa tsammanin ganinsa akan wayarsa ba. Da wannan dalilin yasa dole yayi mamaki. "Har ya ɗaga wayar zai katse, sai kuma wata zuciyar ta bashi shawarar ya ɗauka. Bai san me ke tafe da ita" "ba, kuma duk da sun rabu, ko don darajar ɗa da yake tsakaninsu ai an rabu ba'a rabu bane." "Da wannan dalilin yasa shi mayar da wayar a kunnensa, haɗe da yin ɗan gyaran murya ƙasa-ƙasa. Gyaran" muryar da ya tabbatar ma da Bintu yana saurarenta. """Hafiz... Yanzu shi kenan Hafiz?""" Tayi maganar cikin rawar murya. Bata jira ya amsa ba ta cigaba da cewa """Saboda Allah ka yi min adalci kenan? Bayan duk rashin adalcin da kayi min ka rasa sakayyar da za kayi" "min sai na auren Kareema? Haba Hafeez! Kareema fa? Ƴar gidan Mummy Saudah, wannan local ɗin yarinyar... Bayan tozarcin auren kuma ka rasa sakayyar da za kayi min sai ta saki... Ina duk alƙawurran da" "kai min Hafeez?""" Ta ƙarasa maganar haɗe da fashewa da wani ƙaƙƙarfan kuka da yake tahowa tun daga ƙarƙashin zuciyarta. "A ɓangaren Hafeez kuwa da sauri ya cire wayar a kunnensa, saboda yadda sautin kukan ya dira a" kunnensa da ƙarfi... Kamar tana barazanar fasa masa dodon kunne. "Wani abin mamaki shi ne duk irin yadda ta jero maganganun da salon a tausaya mata, take kuma rusa" "kuka kamar ƙaramar yarinya, irin kukan da ya daɗe a fili ko a waya bai ji Bintu ta yi irinsa ba. Ko kaɗan maganganunta basu taɓa mishi zuciya ba, sai ma wani ɗan ƙaramin murmushi da ya suɓuce a fuskarsa, ya daɗe yana sakin lallausan murmushi kamar tana kallonsa, yana jin saukar kukanta a kunnensa kamar" busar sarewa. """Bintu...""" "Ya kira sunanta a hankali, bayan ya ji ba ta da niyyar tsagaitawa a kukan da take yi." """Ki saurara da kukan nan muyi magana, idan ba haka ba Wallahi zan kashe wayata.""" Yayi maganar cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara. "Ta sani tsaf zai aikata abinda ya faɗa, musamman a yanzu da ƙarfi da yaji maƙiyanta suka ci galabar cusa" mishi tsanarta a zuciya. Don haka a sannu-sannu ta fara rage kukan har ta daina gaba ɗaya. "Nannauyar ajiyar zuciya ya ja ya sauke a hankali, sannan ya cigaba da magana da wata irin murya mai" bayyana rashin damuwa ko misƙala zarratin da halin da take ciki. """Kin ga barci nake yi fa... kiran wayarki ne ya tashe ni. Don Allah idan ba ki da abin cewa mai" "muhimmanci ki ƙyale ni in huta Bintu.""" Daƙyar ta iya riƙe wayar saboda tsananin kaɗuwar da tayi sakamakon jin irin kalaman da ke fita a bakinsa. Har ga Allah ta yi tsammanin kalaman rarrashi da ban hakuri ne za ta ji suna fita daga bakinsa. Wannan wane irin mummunan al'amari ne haka ya dabaibaye kyakkyawar zamantakewarsu? Gaskiya duk wanda yayi wani ƙulli don wulaƙanta tubalin zamantakewarsu baza ta taɓa yafe mishi ba... """Kina ji na?""" Hafeez ya sake faɗa. """Ina tunanin sauƙaƙa miki nayi ta hanyar yi miki abinda kike so Bintu. Bazai taɓa yiwuwa mu cigaba da" "tafiya a haka ba, ke ma kin sani." Iyaye da ƴan'uwana sun fiye min kowa da komai a wannan duniya. Ke kuma babu wanda kika tsana "sama da su, don haka na sama miki sauƙi ta hanyar yanke alaƙarki da mutanen da kika fi tsana a" rayuwarki. "Don Allah Bintu ki manta da ni, kamar yadda nima na daɗe da mantawa da ke. Na kama hanyar nemo" wacce rayuwarta za tayi daidai da rayuwata ta baƙauye da rayuwar ƴan'uwana ƙauyawa. Don haka ina "miki fatan alkhairi, da addu'ar dacewa da miji muradin rayuwarki, wanda ba shi da wata alaƙa ta kusa ko ta nesa da ƙauyawa." "Idan da abinda ya rage tsakanina da ke a yanzu, bai wuce ɗa ɗaya da Allah ya bamu ba. Albishir ɗaya da" "zanyi miki shi ne ni bazan raba ki da ɗanki ba, lokaci bayan lokaci zan dinga kawo shi gurinki kina ganin" "lafiyarshi. Amma fa ki sani, rayuwar ƙauyennan da kika tsana tabbas sai Aadil ya ratso ta wannan hanyar" kamar yadda ni mahaifinsa na ratsa har nazo kan wannan matakin da nake ciki. Sannan ina sake gargaɗinki ki daina kira na a waya idan ba da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba. Kayanki na "gidannan tuni an tattara miki su an kulle a ɗakinki, da wasu daga cikin ɗakunan BQ, duk sadda kika shirya" ko ta text message ki sanar da ni za ki turo ƴan'uwanki su kwashe miki kaya. "Amaryata tana da matsanancin kishi, ko kaɗan bazan bari ki zama sanadiyyar da baƙin ciki zai ratso ta" "tsakiyar farin cikin matata abin son zuciyata ba...""" "Ƙit! Bintu ta katse wayar daga ɓangarenta, saboda yadda kalamansa suke babbakata kamar ana zuba" "mata tafasasshen ruwan dalma, tun daga tsakiyar kanta har zuwa diga-diginta. Wasu irin zafafan numfarfashi take ja, kamar mai cutar numfashi. Da farko a zaune take a tsakiyar gado, ba tare da sanin" yadda aka yi ba sai gata a tsakiyar ɗakin tana safa da marwa. Ashe wani tashin hankalin ya fi gaban ayi mishi kuka? Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Gaba ɗaya kukan "ɗaukewa yayi daga idanunta, sau uku tana ɗaga hannu ta ɗora akai da nufin ta ƙwalla wani matsiyacin ihu, sai kuma ta ji muryarta ya ƙi fitowa sam! kamar wacce aka shaƙewa maƙogwaro." "Daga yadda take jan numfashi da ƙyar, tana haɗawa da shishitu da baki, sai take jin kamar iskar ɗakin ne" yake neman yi mata kaɗan. Kamar ma dai idan ta cigaba da zama a cikin ɗakin lallai ajali zai risketa a "gaggauce. Ga shi yau ita kaɗai ce a ɗakin, Mashkura tana can gidan Yaya Abubakar, balle idan ta yanke jiki ta faɗi Mashkura ta kawo mata ɗauki." Ba tare da duba kayan barcin da ke jikinta ba ta kama hanyar fita daga ɗakin. Tana tafe tana tangaɗi "kamar wacce ta sha kayan maye. Ba tare da duba tsalawar dare ba, kai tsaye ɓangaren mahaifinta ta nufa." "Cikin hukuncin Allah tana shiga falon Daddynta ta tarar da shi zaune a kan dadduma can gefe guda, da" "alamun sallah ya idar, domin ga Alƙur'ani nan ajiye a gefensa, hannunsa kuma riƙe da casbaha yana ja." "Ƙarar buɗe ƙofar da ya ji ne yasa shi waigawa a mamakance, domin ya san babu mai shigowa ɗakinsa" "falonsa a irin wannan lokaci sai Hajiya. Ita kuma tun ɗazu ta shigo, ya ma barta a cikin ɗaki tana barci." "Ganin Bintu ce yasa motsin tasbihi da bakinsa ke yi tsagaitawa, ya ƙura mata idanu yana kallon yadda ta ƙara yin zuru-zuru a cikin kwanakin, kamar wacce ta ɗauki wasu watanni masu yawa tana jinya." Bai gushe yana kallonta ba har zuwa sadda ta ƙarasa inda yake ta zube a gabansa. """Na tuba... Na bi Allah na bi ka Daddy... Ka taimaka min... Wallahi ina matsanancin son Hafeez... Bazan" "iya rayuwa babu shi ba...""" Tana zuwa nan a maganganunta ta fashe da wani ƙaƙƙarfan kuka... ******* ******* "Tuwon girma aka ce miyarsa nama. Tun ana gobe ɗaurin auren Hafiz da Kareema, su Baffa da sauran" tawagar maza ƴan ɗaurin aure da ɗaiɗaikun mata ƴan biko suka dira a babban birnin tarayya Abuja. Biki ne da duk da an saka kwanakin a ƙurarren lokaci amma fa an shirya ta ko wane ɓangare. Kuma ƙarin abin ban sha'awar shi ne ta ko wane ɓangare suna murna da haba-haba da al'amarin. Ga wanda bai sani ba ma sai yayi tsammanin wannan auren shi ne na farko da Hafiz zaiyi a rayuwarsa ta duniya. "Taron biki ne na gani a faɗa aka shirya a gidan Abba Lurwanu, gidan Mummy Saudah, sai dai babban" "gangamin kuma yana can Faƙo gidan Innaye. saboda Hafiz ya sha alwashin bayan an gama ɗaura aure, anyi dinner a ranar za'a kai Amarya gidan Abba Lurwanu ta kwana, washe gari da sassafe za'a wuce da ita Faƙo. A taƙaice dai, baza'a kai Amarya gidanta ba sai ta kwana ta hantse a ɗakin Innaye, saɓanin Bintu" da iyakarta gidan Abba Lurwanu aka wuce da ita gidan Hafiz. "Kamar wancen auren na Bintu, wannan karon ma Abba Lurwanu ne ya zama waliyyin Ango, kuma shi ya" "biya mishi sadaki. Yana zaune a tsakiyar su Baffa, da mahaifin Bintu, wanda ya ke ta dariyar yaƙe, daga" can ciki kuwa yana jin zafin yadda Bintu tayi wasa-rere da damarta har tayi saken da waɗannan nagartattun mutane masu halin girma da kawaici suke neman kuɓuce mata a matsayin surukai. Kamar Baffa bai samu labarin rashin mutuncin da Bintu taje har tsakiyar ɗakin Innaye ta shimfiɗa ba. "Haka ya saki fuska sosai suka gaisa da mahaifin Bintu, kuma wani ƙarin halin girman shi ne duk inda Alh Lurwanu ya ja shi, in dai mahaifin Bintu na gurin kai tsaye yake damƙo hannunsa su gabatar da al'amarin" su uku. Wanda bai sani ba sai yayi tsammanin ƴan'uwanta ne mai ƙarfi "Misalin ƙarfe uku na rana, Baffa da ƴan'uwansa maza da suka halarci ɗaurin aure sun gama shirin" "komawa Faƙo. Daga ɓangaren Abba Lurwanu, mahaifin Bintu, Hafeez an haɗa ma su Baffa sha tara ta arziki. Domin har wannan lokacin mahaifin Bintu na tare da su, yana ta dama-dama da Baffa yana ƙara" karantar kirkinsa. "Har sun yi sallama, suna tsaye a jikin motar da Baffa zai shiga, Daddyn Bintu yayi suɓul da baka wajen" furta maganar da tun ɗazu take mishi ƙaiƙayi a maƙoshi. """Mal Aminu, ina dai sake baka haƙuri game da kuskuren da Bintu tayi, don Allah idan ka je gida aba" "Innaye da sauran Yayyen Hafizu da duk waɗanda Bintu ta ɓata ma haƙuri. Ba goyon bayanta nake yi ba, amma ina tabbatar maka a zaman gidan da Bintu take yi ta shiga taitayinta, ayi haƙuri... Don Allah a" "taushi Hafizu, bayan kwana biyu yayi haƙuri ya maida ita ɗakinta kafin ta gama iddah!""" "Da saurin gaske Baffa ya saki hannun ƙofar da yake riƙe da shi, jin kalaman da ke fita daga bakin Daddyn" "Bintu. Domin ko da wasa Hafizu bai faɗa mishi ya saki Bintu ba, duk da a wancan ranar bayan ya koma gida Rahina da kanta ta faɗa mishi duk irin tijarar da Bintu taje tayi musu." """Maganar me kake yi Alhaji? Ban... fahimta ba. Kar dai ka ce min Hafizu ya saki matarsa ba tare da sani" "na ko na mahaifiyarshi ba?""" Lokaci ɗaya aka fara kallon-kallo tsakanin Daddyn Bintu da Abba Lurwanu. Daƙyar Daddy ya iya buɗe baki ya ce """Tun wancan ranar da taje Faƙo tayi ma iyalinka rashin kyautawa, da kuma washe gari da taje nan" "gidan ƙanwarsa tayi mata rashin mutunci. Hafizu yaje har gida ya faɗa min duk abinda ya faru, sannan ya bani takardarta na saki ɗaya...""" """Assha! Assha!! Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!!! Amma kuwa Hafizu baiyi aiki da hankali ba... Wa ya" "faɗa mishi cikin sauƙi ake sakin matar da aka fara tara zuri'a da ita? Ya sani, da ya faɗa mana zai aikata ni ko mahaifiyarshi babu wanda zai lamunci haka. Ina zuwa, bari in kira shi.""" Yana wannan maganar ne yana latsa wayarsa da nufin lalubo lambar Hafiz. """Abu dai duk baiyi daɗi ba Baffa. Ni kaina bai faɗa min ba sai bayan da komai ya gama faruwa. Kuma" tunanin kun sani tunda ance rashin kyautawar ku tayi ma shi yasa na bari sai bayan an kwaranye hidimar "bikinnan sai in kira in baku haƙuri in roƙi alfarmar a mayar da ita ɗakinta. Muje daga ciki sai ka kira shi Baffa.""" "Ko da suka koma cikin falon Abba Lurwanu, kira na farko da aka yi ma Hafiz bai ɗaga ba, sai a kira na biyu" "ya ɗauka, da alamun yana cikin abokansa ne, don ga muryarsa nan ana ji suna dararraku." """Assalamu alaikum! Baffa ya hany...""" """Hafizu ka keɓe yanzunnan daga cikin mutanennan. Ina son yin magana da kai me muhimmanci.""" Abba ya bashi umarni. """To Baffa!""" "Ya amsa a ladabce, sannan ya katse kiran. Mintuna biyu tsakani ya sake kiran lambar Baffan, yana ɗauka" ya faɗa mishi ya keɓe. Da faɗa sosai a muryar Baffa yake magana. """Hafizu? Ina ganin ka yi hankali tunda ka fara aje yara ashe har yanzu da sauran rina a kaba? Me yasa" "ka saki matarka uwar ƴaƴanka?""" """Baffa...""" """Ka ga ni ban nemi jin wani ƙarin bayani daga gare ka ba. Tabbas na sani Fatima bata kyauta ba, amma" "hukuncin saki ya yi girma sosai akan ɗan wannan laifin. Matar da aka fara tara iyali da ita, an riga an zama ɗaya, da daɗi babu daɗi haƙuri ake yi a cigaba da gungurawa in ba wata muguwar ƙaddara ba da ba'a fata har zuwa sadda za ta birne ka ko kai ka birne ta. Akwai hanyoyin ladabtar da mace masu yawa ba tare da an kai ga saki ba. Don haka ina roƙo tare da umartarka ka mayar da ita ɗakinka, bayan haka na" "yarje maka ka ɗauki duk irin matakin da ka so a kanta matuƙar bai saɓa ma addininmu ba.""" "Shiru Hafiz ya yi na tsawon daƙiƙu sittin, a cikin waɗannan daƙiƙun, babu abinda zuciyar Daddy da Abba" "Lurwanu ke yi sai luguden daka. Aminci ne mai ƙarfi tsakanin su biyun, don haka damuwar da ke damun" ɗaya ta shafi ɗayan. Amma saboda adalci da dattako irinna Abba Lurwanu baiyi niyyar tauye Hafiz don faranta ran Amininsa ba. """Shi kenan Baffa. Ka zama shaida, na mayar da matata Fatima-Bintu ɗakinta.""" Hafizu ya faɗa da cusasshiyar murya. """Na gode. Allah yayi maka albarka. Ubangiji ya haɗa maka kan matanka.""" Baffa ya jero addu'o'in da farin ciki a muryarsa. """Amin ya Allah. Na gode Baffa, Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana. Ubangiji ya mayar da ku gida" "lafiya.""" """Amin ya rabb""" Su Baffa suka amsa gaba ɗaya. Fuskokinsu cike da matsanancin farin ciki. Mayar da Bintu ɗakinta da Hafiz yayi ba ƙaramin farin ciki ya jefa zuciyar Abba da Daddy ba. Shi yasa har "Baffa ya shige cikin mota basu daina jera mishi kalaman godiya ba, abin ma sai ya koma ba Baffa kunya," a ganinsa ai ba wani abun azo a gani bane yayi idan aka haɗa da irin gwaggwaɓan karamci da girmamawar da suke mishi da iyali da duk wani da ya shafe shi. ******* "Bayan gama waya da Baffa, jikin Hafiz sanyi ƙalau ya zube a gefen gadon ɗakin hotel ɗin da suke ciki da" abokansa. "Allah yana gani bai so mayar da Bintu ba, shi yasa yake ta ɓoye maganar sakin don kar su Baffa su ji. Ko" "Zulai baiyi gigin faɗa mata ya saki Bintu ba, ya sani idan ta ji, kamar Innaye ne ta ji." Yana cikin wannan halin na damuwar abokinsa Ibrahim ɗan gidan Abba Lurwanu da suke zaune a falo da sauran abokansu suna shirye-shiryen zuwa dinner ya shiga cikin ɗakin ya tarar da Hafiz a wannan halin. """Ya aka yi ne Ango? Me yake faruwa..?""" Da ɓacin rai sosai ya amsa mishi """Uhmmm! Wallahi yanzu Baffa ya umarceni in mayar da Bintu ɗakinta.""" """Shi ne kake ta wani ciccin magani kamar ka kurɓi maɗaci? Common guy, kar ka kuskura ka bari" "wannan zancen ya ɓata mood ɗin ka na farin ciki. Yau kake sabon ango fa, ka aje duk wani ɓacin rai gefe" ɗaya ka rungumi farin cikin da ke tattare da kai. "Kawai shawarar da zan baka ɗaya ne, kar ka kuskura ka bari kayi saken da za'a sake samun matsalolin da" "aka samu a baya tsakaninka da Bintu. Kuma tun yanzu idan kana da wasu tsare-tsare da dokoki ka kira ka faɗa mata tun yanzu, idan ta shirya sake zama da kai a karo na biyu za ta amince, idan bata shirya ba da kanta za ta sake neman ka sauwaƙe mata. Ka ga shi kenan, ka yada ƙwallon mangwaro ka huta da ƙuda.""" Yana gama wannan maganar bai jira cewar Hafiz ba ya fice zuwa falo gurin sauran abokansu. "Maganganun da Ibrahim yayi mishi, su suka dawo ma da Hafiz farin ciki da walwalar da yake neman" "rasawa sanadiyyar mayar da Bintu ɗakinta. Wayarsa ya ɗauka da yake ajiye gefensa, ya lalubo lambar Bintu ya buɗe gurin tura saƙo ya tura mata saƙon cewa" "_*""Kamar yadda albarkacin kaza ƙadangare ke shan ruwa a kasko. Haka Albarkacin Baffa na amince ma" "sake zama da ke ayau. Na mayar da ke ɗakinki Bintu, amma bisa sharuɗɗa guda biyu. Na ɗaya shi ne, nan da kwanaki uku masu zuwa ki shirya ki tafi har gida ki ba Innaye da sauran ƴan'uwana da sauran matan Baffa haƙuri kan irin cin mutuncin da kika yi musu. Sharaɗi na biyu kuma shi ne ki shirya komawa zaman Faƙo, a gidan Baffa zan sama miki ɗakin zama, sannan za ki dinga cin abinci da abinsha ƙarƙashin kulawar Innaye ne har zuwa lokacin da ni da kaina zan gamsu za ki iya zama da ni baƙauye da ƴan'uwana ƙauyawa. Idan kin amince da waɗannan sharuɗɗan, ina miki maraba da sake zama matar Hafiz a karo na biyu. Idan kuwa baki amince ba ki faɗa min don Allah, ni kuwa yanzun nan zan faranta miki ta hanyar" "datse sauran igiyoyin da suka rage tsakanina da ke. Hafiz Aminu Faƙo.""*_" "Yana aika mata da saƙon, ya miƙe tsaye ya fice zuwa falo gurin sauran abokansa suka cigaba da" harkokinsu cikin walwala da farin ciki. "Zuciyarsa cike da tabbacin ƙarshen zamansa da Binto ya zo a sauƙaƙe, domin ko rantsuwa yayi babu" "kaffara, ya sani a girman kai irinna Bintu, ba ta yadda za ayi ta amince da waɗannan sharuɗɗan da ya gindaya mata. Shi kuwa bazai ɓata lokaci ba gurin cike mata sauran saki biyun da ya rage a tsakaninsu," "yana da tabbacin Kareema ita kaɗai, ta ishe shi rayuwar duniya da lahira." ********* "Ana idar da sallar magriba, manyan motoci masu numfashi suka cika ƙofar gidan Mummy don ɗiban" Amarya da manawarta zuwa wajen dinner. Daman tun da yamma Zulaikha ta faɗa ma Hafiz kar ya wahalar da kansa wajen zuwa ɗaukar amarya. """Ni zan wakilce ka Yaya, sabuwar motar da Abban Imam yayi min oder ta iso last week. Tunda aka" "kawo ta ban hau ba, na tsaya jiran wannan ranar mu fara hawa tare da Aunty Kareema...""" """Zzzzzulai...?""" Ya katse ta da kiran sunanta cikin rawar murya. """Kin yi hauka ne?""" Ya sake faɗa hankalinsa a tashe. """Yaushe kika koyi tuƙin mota da har zanyi gangancin bari ki ɗaukar min amarya zuwa wajen dinner?" "Don Allah ki bari, kar ki fara yi min wannan gangancin, in za ki tuƙa kanki bismillah tunda mijinki da yake can wata ƙasa ya amince. Amma ni dai ban yarda ba, tunda dai ba karen hauka ne ya cijeni ba...""" "Da sauri ta katse wayar tana tuntsira dariyar ƙeta, a zuciyarta ta ayyana za kuwa ta bashi mamaki. Wato" "ita rayuwarta a banza ko? Ai kuwa zai gani, da ɗanshi da Amaryarshi ita za ta kai su wajen dinner, duk abinda zai faru ya daɗe bai faru ba." Ƙarfe shidda da rabi dai-dai ta shiga ɗakin da Amarya da ƙawayenta suke ta ce Hibba da Amarya su fito su tafi. """A'a! Na zaci Ango da kansa shi zai zo ɗaukar amarya?""" Wata daga cikin ƙawayen Amarya mai kafiɗirin tsiya ta faɗi haka tana wani fari da idanu. Yatsa manuniya Zulaikha tasa tayi ƙasa-ƙasa da gilashin da ya mamayi kusan rabin fuskarta ta aika ma da "yarinyar kallon uku saura kwata, ta yatsuna fuska kamar ta ga kashi sannan ta amsa da" """Idan na ɗauki Amarya kamar Angonta ne ya ɗauke ta, dmin ni ɗin ƙanwar Ango ce. Ko akwai wani" "banbanci tsakanin ƙanwar Ango da Ango?""" """A'a! Mayar da wuƙar ƙanwar Ango. Ni ban ɗauka da zafi ba.""" Ta faɗa cikin waskiya tana dariya. "Ko kafin motocin da za su kwashi jama'a su iso, tuni Zulaikha ta kwashi Kareema, Hibba, Aadil, Imam" "sunyi gaba, babu abinda take yi sai dariya cikin ranta." """Yaya, kar kayi wahalar zuwa gidan Mummy ɗaukar Amarya, mu munyi gaba. Amma kana iya tarar da" "mu a ƙofar event center ɗin don ku shiga tare, Amma fa idan tuƙin rashin ƙwarewa ta bai sa na kashe" "maka amarya ba.""" Saƙon da ta tura ma Hafiz kenan bayan sun isa gurin ******* "Kamar yadda aka tsara, a daren ranar aka wuce da Amarya gidan Abba Lurwanu. Sun sami tarbar girma," tun a daren aka ringa ina aka saka ina aka aje da su har zuwa washe gari. Bayan sun karya kumallo misalin ƙarfe tara na safiya suka kama hanyar tafiya Faƙo. A cikin tsadaddun motoci guda huɗu da Abba Lurwanu ya bada ayi tafiyar da su. "Sun yi tafiyar ne a wadace, babu takura ko kaɗan. Mota ɗaya aka saka Amarya, Zulaikha, Hibba, sai ɗaya" "daga cikin ƙawayen Amarya mai suna Maryam. Mota ɗaya aka Matan Abba Lurwanu biyu, matar Ibrahim," babbar ƴar Abba Lurwanu mai suna Aunty Zainab. "Mota ɗaya kuma ƙannen Momy guda biyu, sai ƙannen mahaifin Kareema biyu. Mota ɗaya kuma aka" ɗauki ƴan biko da suka zo daga Faƙo. Sai babbar motar Hillux da aka cike bayanta aka shaƙe da kayan garar surukai wanda za a kaiwa su Innaye. "Da yake direbobin an faɗa musu tafiya ce mai nisa a gabansu, shiyasa basu yi tuƙi na wasa ba. Wajen" "karfe ɗaya na rana suka isa Faƙo. Kun dai san mutanen ƙauye da karamci, balle ma su Innaye da suka" "samu shaidar kirki da sanin ya kamata. Sun samu tarba ta girma sosai a wajen su Anty Balira da Innaye, abokan zamanta." "Dama tunda bikin ya matso, kasancewar gidan Baffa akwai fili sosai daga can ɓangaren ɗakin Innaye, nan" "Hafiz yasa aka yanka mishi fili, duk a ƙoƙarinsa na gyara kuren da yayi a zamansa da Bintu, ya ɗauko ƙwararrun magina daga Kaduna, cikin sati biyu aka gama gina uwar ɗaka da falo da bayi, a cikin sati uku kuwa, hatta funitures an zuba a cikin ɗakunan. A ganinsa har da rashin kwana biyu da basa yi a cikin ƙauyen shi yasa sam Bintu bata saba da ƴan'uwansa ba, ya gyara nan ɗin ne a matsayin gurin saukarsa" "da iyalinsa. Kwana ɗaya, biyu, uku, idan ta kama har sati ɗaya ko biyu za su dinga yi a ƙauyen." "Sannan yasa aka ƙara gyara duk inda ke buƙatar gyara a gidan, aka yi fenti mai masifar kyau, sannan ya" canja ma su Innaye da abokan zamanta da Baffa kayan ɗakunansu gaba ɗaya. "Ginin da Hafiz yayi nan aka sauki Amarya da manawarta, kafin ƙiftawa da Bismillah aka dabaibayesu da" "kayan abinci cima iri-iri da katan-katan na lemuka. Wani abun burgewar kuma shi ne a kayayyakin abincin da su Innaye suka tarbi Amarya da manawarta da shi har da kalolin cima ta marmari, irin wanda ba'a cika samu a birni ba sai a ƙauyuka. Sun ci, sun sha, sun yi hani'an! A nutse su ka yi sallah, fuskokinsu gaba ɗaya cike da farin ciki. Bayan sun huta, suka dauki Kareema zuwa gurin su Innaye domin yin buɗar" kai. Dangin Hafizu ƙwansu da ƙwarƙwata kowa ya fito. Cikin gidan Innaye cike yake da bil'adama dan-ƙam babu masaka tsinke. Kuma abinda ya ƙara ƙayata bikin shi ne masu kiɗan ƙwarya da aka tafi har garin "Kaduna aka ɗauko hayarsu, Sune suka je tun da misalin sha biyun rana, aka ware musu gurin zama ta" cikin gidan Baffa suna ta waƙe-waƙensu na gargajiya matan ƙauye suna juya mazaunai. Fitowar Amarya da danginta da niyyar zuwa ɗakin Innaye yasa masu kiɗa canja salon kiɗansu da yanayi "mafi daɗaɗawa, nan take filin rawa ya ƙara tumbatsa da mata, masu girgiza na yi, masu guɗa nayi, masu kirari na yi, abin dai gwanin ban sha'awa." "Wani harkar girma da Matan Abba Lurwanu da Auntys ɗin Kareema suka yi shi ne, kafin su wuce zuwa" "ɗakin Innaye, sai da suka ɗan tsaya da Amarya a filin rawar, suka yi ma masu kiɗi da mai waƙa da masu rawa yayyafin kuɗi masu yawa, sannan suka ja hannun Amarya zuwa ɗakin Innaye aka bar Hibba da Maryam a fili da Zulaikha, wacce jin guɗar da ke alamta an fito da Amarya yasa ta fitowa daga uwarɗakin" Innaye. "Innaye tana zaune cikin ƴan'uwa da abokan arzikinta, ta yi kwalliyarta gwargwado ta mutanen da," "saboda kyawun jikinta babu wanda zai ce ita ta haifi su Aunty Balira. Ta sha atamfarta super Holland, ɗaya daga cikin ɗinke-ɗinke masu tsada har kala goma sha biyu da Zulaikha ta aika mata da su, shida Hafiz ne ya siya, shida Zulai ta siya, sannan ta haɗa duka sha biyun ta ba tela da na su Aunty Balira" hurhuɗu ya ɗinka musu. "Matan Baffa kuma kala uku-uku, sauran yaran gidan kuma mazansu da mata yara da manya kowa kala" bibiyu. Baffa kalolin shadda da yaduka har bakwai ta ɗinka mishi. Su Baba Abubakar da matansu duk sun shiga "cikin kasafi, har Liman da Ladan da suka kasance abokan Baffa sun karɓi rabonsu. Maƙudan kuɗaɗe Abban Imamu ya sakar mata, sannan ya ƙara da jaddada mata lallai ta tabbatar ta yi ma kowa tsaraba, idan kuɗaɗen basu isa ba ma ta faɗa mishi ya ƙara mata." Wani aikin hankali da Zulaikha tayi shi ne mota guda ta aike musu da shi na kayayyakin ana saura "kwanaki uku bikin Hafiz. Shi yasa tun da Zulai ta isa gidan, kamar tauraruwa haka ta zama, kusan kowa so yake ya gaisa da ita yayi mata godiya. Daƙyar ta yakice kanta ta gudu uwarɗakin Innaye bayan ta basu uzurin kanta na ciwo, duk da haka sai da yayyinta uku suka bi ta, bata fito ba sai yanzu da ta ji an fito da Amarya." "Innaye babu abinda take aikin yi sai sakin murmushi a kunyace, lokacin da aka damƙa mata amanar" "Amarya ita da abokan zamanta. A taƙaice tayi addu'a, bayan haka ta kasa ƙara cewa komai, har zuwa sadda aka fara shigo da manyan randuna na kayan gara da buhuna na kayan abinci, tun matan ƙauye suna ƙirga buhu da kwalaye har bakunansu ya mutu-murus." Tsakiyar falon Innaye da ƙofar ɗakinta sai da aka shaƙe taf da kayayyaki. Abin dai ba'a cewa komai sai "hamdala. Bayan waɗannan kayan abincin kuma, Zannuwa da shaddodi guda goma sha biyar Mummy Saudah ta bayar na su Innaye, abokan zamanta da yayyen ango." Tuwon girma aka ce miyarsa nama. Nan take iyaye da ƴan'uwan Hafizu suka fara kwance haɓar zani suna "fito da kuɗin da za su haɗa ma Amarya na tarba. Zulaikha ta shigo da fara'a ta haɗa zufa tai sharkaf saboda rawar da tayi, ta ɗan tsallaka ta shige cikin ɗaki, bandir ɗin dubu ɗari ta ɗauko a jakarta ta miƙa" ma Aunty Balira cewa a haɗa a cikin kuɗin sallamar Amarya. Abu dai anyi shi cikin mutunci da arziki. An mayar da Amarya ɓangaren da aka sauketa da kuɗi naira dubu ɗari biyu da hamsin da biyu. Domin matan Abba Lurwanu da Aunty Zainab su ma dubu ɗari suka "bada, Innaye da abokan zamanta da ƴaƴansu suka haɗa dubu hamsin da biyu." "Washe gari da safe haka aka yi hidima da Amarya da danginta, hidima ba ƴar kaɗan ba, da yake duk" abinda za'a nema Baffa da Hafiz sunyi matuƙar ƙoƙari gurin tanadarsa. Ƙarfe goma da rabi Amarya da danginta da Zulai suka bar garin Faƙo. "Alƙawari Zulaikha ta ɗauka ma Kareema sai ta kaita har ɗakinta na gidan Hafiz, shi yasa ba tare da ta" "gama gaisawa da Iyaye da ƴan'uwanta ba ta sake bin Amarya suka koma Abuja, bayan ta faɗa ma Innaye" "kwanaki goma masu zuwa za ta koma Faƙon, a lokacin za tayi sati ɗaya. Kuma lokacin ne za ta tafi da Aadil su Innaye su ganshi." ******** "Duk tarin abokansu da suka rufa mishi baya gurin hidimar bikin sun koma gurin ayyukansu, saboda" "jinkirin da aka samu wajen kai Amarya Faƙo. Yau da ya kasance Amarya ta isa gidanta bayan sallar Isha'i," Ibrahim ne kaɗai yayi mishi rakiya. Lokacin da suka shiga gidan babu kowa sai Zulaikha. Iyaye da sukai rakiyar Amarya duk sun koma "gidajensu. Ƙawayen amarya da suna jin labarin Kareema ta koma gidan Mummy suka dawo, duk ta kore" "su bayan ta basu kuɗin sallamar da suke yiwa ƙwa-ƙwa. A cewarta, ba za su bata wa yayanta lokaci da" "zancen kuɗin sayen baki ba, balle har su shiga lokacinshi da na amarya." "Ita da aka bari cire mayafinta tayi ta ƙara gyara wajen ɓangaren Amarya da yayi kyau sosai, saboda an" narka dukiya wajen tsara gurin ba kaɗan ba. Ta dauko burner da humidifier duk ta jonasu da zuba abin kamshi a ciki. Gidan ya kaure da kamshi kashi-kashi. Idan ka shiga har ka rasa wanne za ka shaka. "Wajen karfe tara da rabi suka ratsa ta cikin main parlour suka shiga ɓangaren Kareema, Hafiz da Ibrahim" "sun sha Angon babbar shadda wagambari, fara, ta sha surfani iri ɗaya. Fuskar Hafiz sai sheƙi take yi da" annuri irin na angwaye. "Lokacin da suka shiga, Zulai da Kareema na zaune a falonta da ya sha saitin wasu hadaddun leather seats" ruwan madara. Hafiz ya kalli Zulai ya watsa mata harara """Kin shiga uku da masifar sa'ido Zulai. Ke kuma zaman uban me kike yi anan bayan tun ɗazu an ce kin" "sallami ƙawayen Amarya?""" "Ta kyalkyale da dariya, sai kuma ta ɗan kumbura fuska ta ce" """Yaya ai ni tudu uku nake ci. Ƙanwar Ango, Yayar Amarya, kuma ƙawar Amarya. Don haka kuɗin" "sallamar da baka biya ba ni za ka ba, idan ba haka ba daga nan har gobe Amarya baza ta buɗe maka baki da fuska ba.""" "Duk da ya san tsokanarsa take yi, da saurin gaske ya ɗan narke fuska, a marairaice ya fara roƙonta" """Haba-haba An Zulai ta Innaye da Baffa. Ai na san baza kiyi ma Yayanki haka ba? Ko kin manta ni da ke" "mun shirya tsakaninmu yanzu ba ta ɓaci?""" """Ban manta ba Yaya.""" Ta amsa da dariya. """To tunda haka ne zo ki wuce gidanki. Na gode da ƙoƙarinki ƙanwata, Allah ya bar zumunci. Za muyi" "waya da safe, kina iya tuƙi da daddare ko in haɗa ki da direba...?""" """Direban Mummy na waje yana jira na Yaya, sai da safe...""" "Tana gama faɗin haka ta rataya jaka, ta gyara zaman mayafi a kafaɗarta. Sai da ta kai bakin ƙofar fita" daga falon sannan ta waiga ta ce """Yaya?""" """Na'am Zulai.""" "Ya amsa da sauri, bayan ya mayar da hankalinshi kanta." """Ka ji tsoron Allah don Allah Yaya, ka bi min ƙawa a hankali...""" Ta ƙarasa maganar haɗe da ficewa a guje tana dariya. """Uhmmm! Zulai ƙuruciya dangin hauka. Allah ya shirya. Kamar ba ƴar lukuta ba sam ba ta jin nauyin" "jikinta.""" "Ba tare da kunyar idanun Ibrahim ba ya maye gurbin da Zulai ta tashi kusa da Kareema, kan kujera" mazaunin mutum biyu. Ibrahim na tsokanarshi """Ko kunyar idona ba ka ji Hafizu?""" Ya jefa mishi harara ba tare da ya amsa ba. "A gefe guda Ibrahim ya zauna, ya fara da sallama sannan ya buɗe taron da addu'a. Nasiha sosai ya yi" "musu game da zaman aure da zamantakewa, kafin daga baya yayi musu addu'a sosai da fatan Allah Ya" ɗaurar da auransu har a gidan Aljanna. Daga ƙarshe ya yi musu sai da safe ya fice daga falon "Daƙyar Hafiz ya iya tashi ya raka shi bakin ƙofar babban falo, daga nan ya coge ya ce mishi" """Na gode Aboki, a gaida Madam da yara""" A Nan ma sai da Ibrahim ya ƙara mishi shakiyanci kafin ya mishi sai da safe ya tafi. Shi kuma ya tsaya ya rufe kofa da tagogin falon. "Ya samu Amarya a yadda ya barta, da alamun ko ƙwaƙƙwaran motsi bata yi ba. A hankali ya ƙarasa ya" tsuguna a gabanta yana leka fuskarta ta cikin lullubin jikinta. "A sanyaye ta zuba mishi idanunta da suka yi ciki sosai, alamun kukan da ta daɗe tana sharɓa." "Cikin marairaice fuska, ya ce" """Ƙurratul-ainiy? Kuka kika yi? Sai kace dai wadda aka kawo ki gidan makiyinki ba masoyi ba? Idan ma" "kina zaton wai ba zan iya kulawa da ke kamar yadda Mommy take yi to ki canza shawara. Domin yadda zan kula da ke ma sai ya ninka nata uku sau uku! In sha Allah!""" "Sai ta samu kanta da sakin ƴar dariya, a hankali ta ce" """Sau tara fa kenan?""" """Eh! Ai tara ma kamar ya yi kaɗan. Ko ita ma taran a ninka ta sau tara?""" Sosai ta sake dariya ba tare da ta shirya ba. Ganin yadda ta sake tana dariya sai hakan ya sanyaya mishi rai. "Ya mike tsaye tare da mika mata hannu, babu musu ta sanya zara-zaran yatsunta a cikin nashi, yatsunta" "sun sha zanen lalle baki da ja, sun yi kyau sosai. Ya ɗan ɓata daƙiƙu yana kallon yatsun sannan ya janyo" ta ta tashi tsaye. Kai tsaye ya ja ta zuwa dakinshi. "Ya umarceta da ta shiga bayi ta dauro alwala. Daƙyar, ta shiga bayin tayi alwala cikin dar-dar. Ganin" "yadda duk ta bi ta tsorata da shi a fili yasa yayi kokarin kin kai hannu ya tabata duk da yadda zuciyarshi take azalzalarshi da yayi hakan. Ya jira ta tayi alwalar ta fito, kafin shima ya shiga bayin don ɗauro alwala." "Bayan fitowarsa daga bayin, kai tsaye inda take rakuɓe a gefen gado ya fara kallah. Bai san sa'adda" "murmushi ya suɓuce masa ba, ganin yadda ta wani takure, kamar ace kyat! Ta zura a guje." "Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, a hankali ya ƙarasa kusa da ita, ya ɗauki babbar rigarsa da ya ajiye a" gefen gadon sadda zai shiga banɗakin. """Pls ɗan bani mintuna biyu Ƙurratul-ayn, ina zuwa.""" Kai kawai ta iya ɗaga masa alamar to. Shi ma bai takura sai ya ji maganarta ba ya fice daga ɗakin. "Mintuna uku tsakani ya sake komawa cikin ɗakin, jikinsa sanye da jallabiya mai laushi sosai, kalar ruwan madara." "Hannunsa riƙe da darduma. Kai tsaye, wadataccen ɓangaren da aka ware don yin a cikin ɗakin ya nufa ya" shimfiɗa sallayar hannunsa. """Amarya zo muyi sallah, mu gode ma rabbil-izzati da ya mallaka mana junanmu cikin ƙanƙanin lokaci." "Sannan muyi addu'ar dacewa da dawwamammen zaman lafiya, kwanciyar hankali, zuri'a masu albarka.""" "Da yake idanunsa a cikin nata yake maganar, ya ga saukar lallausan murmushi a fuskarta. Sai kuma ta" "miƙe tsaye ta warware babban mayafin jikinta, ta rufa shi da kyau. Kamar kazar da ƙwai ya fashe ma a ciki haka ta tafi laƙaƙai-laƙaƙai har zuwa bayansa, inda ya shimfiɗa mata ƙaramar sallayar da ya gani an ninke an ajiye da Alƙur'ani mai girma kan wani ƙaramin stool da yake gurin." "Ya ja su suka yi sallar nafila raka'a biyu masu tsayin surori. Bayan sun idar, ya jima a zaune yana kwararo" "musu addu'ar samun daidaito da fahimtar juna a tsakaninsu, da kuma zuriya ɗayyiba, a hankali ita kuma take amsawa da Amin, har zuwa sadda suka shafa Fatiha." "Duk da tabbacin da yake da shi kan ilimin addininta, hakan bai hana shi yi mata tambayoyi kan" addininmu ba. Kuma ya samu gamsassun amsoshi kamar yadda yayi hasashe. "Abinda ya gabatar na ƙarshe shi ne matsawa kusa da ita, ya dafa goshinta yayi addu'ar da fiyayyen" "halitta SAW ya koyar don dacewa da alkhairinta, da kuma neman tsari daga dukkan sharrin da yake tattare da ita." "Bayan sun gama komai, a hankali ya kama hannunta ya miƙar da ita tsaye, sannan ya saka idanunta cikin" "nasa ya fara kashe ta da lallausan murmushi, lokaci guda kuma yasa hannunsa yana aikin warware naɗin gyalen da yake jikinta." Ƙugunta ya riƙe da hannayensa biyu yana tafe da baya da baya suna tafe a slow motion cikin rausaya har "zuwa tsakiyar ɗakin, inda aka shimfiɗa lallausan kafet, da wani irin salo na soyayya da kulawa ya zaunar da ita kan kafet ɗin. A kunne ya raɗa mata" """Ɗan ba ni minti ɗaya Sarauniyata, yanzu zan dawo.""" "Bai jira amsawarta ba ya fice daga ɗakin da sauri. Falo ya koma, ya ɗauko ledar da suka shigo da ita shi" da Ibrahim. "Kai tsaye kicin ɗin Kareema ya wuce, ya samu babban faranti ya ɗauraye, sannan ya warware ledar" "jikinshi na rawa, zuciyarsa cike fal da tunanin Kareema, da irin shape ɗin jikinta na coca-cola da ya gani yanzu da ya cire mayafin jikinta." "Yana gama warware ledar, daddaɗan ƙamshi ya cika hancinsa. Gashin naman talo-talo ne aka yi da" "albasa da tumatiri da yaji haɗi da kayan ƙamshi. Gaba ɗaya ya sake a cikin farantin, sannan ya ɗauki wani farantin ya rufe ya kai ɗakin Kareema da sauri." "Yana ajiyewa a gabanta bai ɓata lokaci ba ya koma cikin kicin ɗin. Fridge ya buɗe, ya ɗauko kwalin lemun" "five alive, ya haɗa da kofuna guda biyu, ya sake ɗaukar faranti guda ɗaya, cokula masu yatsu guda biyu," da ƴar ƙaramar wuƙa da cokula na cin abinci guda biyu ya koma cikin ɗakin. """Yau zan ƙara tabbatar miki ke Sarauniya ce a zuciyata Ƙurratul-ayni. Da kaina zan ciyar da ke har sai" "kin ce kin ƙoshi.""" "Yayi maganar a tausashe, da ƴar ƙaramar dariya a muryarsa." "Dirshan ya zauna a gabanta bayan ya tattare jallabiyarsa. Farantin naman ya janyo, ya fara yankawa" sannu a hankali cikin ƙwarewa yana zubawa a empty plate da yake ajiye a gurin. "Lokaci ɗaya kuma a tausashe, bakinsa na raira mata waƙar Ke ce Aljannata, na Auta waziri." "Duk da tana jin yunwa sosai, saboda rabonta da ƙwaƙƙwaran abinci tun karin da tayi a Faƙo, sai ɗazu da" "Zulaikha ta takurata ta sha ruwan tea mai kauri. A yanzu, ta kasa sakin jikinta sosai ta ci naman yadda ya" "kamata saboda kunya da fargaba, idan ta tuno irin shaƙiyancin da Zulai tayi mata kan wannan dare, sai" ta ji tsoro ya sake cika cikinta. Ya dube ta kasa-kasa yana ɗan murmushi """Bari in ajiye miki sauran da safe sai ki ɗumama ki ci kayanki. Kin san dai dole ne sai amarya ta ci naman" "amarci ko? Amma tunda naga kunya ta hana ki ci, ba zan takura ki ba. Sai dai assignment ɗina na farko" yanzu shi ne inyi ƙoƙarin cire miki wannan kunyar da take neman hana mu walawa yadda ya kamata. "Don tsakani da Allah ni ba zan bari in cutu ba.""" "Bata amsa ba, sai ɗan murmushi da tayi kanta a sunkuye. Sannu a hankali ya cigaba da yagar naman" yana korawa da lemu. "Shi ma kaɗan ya ci, don daman a ƙoshe yake. Maƙasudin siyo naman ita ce, kuma ta kasa ci sosai. Yana" gamawa ya ɗauke komai ya kai kicin. "Yana dawowa ya fice zuwa ɗaya ɗakin bayan ya faɗa mata tayi shirin barci, yana dawowa." "Tunanin ya daren zai kasance a gare ta ne ya lulluɓe zuciyarta, bata ankara ba kawai sai sallamarsa ta ji a" "bakin ƙofa, ko kafin ta amsa har ya shigo ciki, ya maida kofar ya rufe, tare da kashe wutar dakin." Ganin duhu ya mamaye ɗakin lokaci ɗaya yasa ta yi zumbur ta tashi tsaye tana laluben hanyar banɗaki. "Bata san sadda ya tako zuwa gare ta ba, sai ji tayi caraf ya riƙota, lokaci ɗaya ya rungumota zuwa jikinsa." """Haba Sanyin idaniyata, ni ne fa hasken Zuciyarki. Ko kin daina so na ne?""" Kanta yana jikinsa ta girgiza mishi kai a hankali. """To tunda haka ne ki daina ƙoƙarin guduna. Ni fa ba dodo bane. Ba kuma zan taɓa cutar da ke ina sane" ba. Na san profession ɗin ki da ilimin da kike da shi sun sanar dake duk wani abu na rayuwar aure. To menene kuma na wani shure-shure bayan ba ya hana mutuwa? Sannan kuma idan baki sani ba ina so "yanzu ki sani, babban burina shi ne nan da wata tara ki bani takwarar Innaye ko abokin zuwa Masallaci.""" Cusa kanta ta ƙara yi a ƙirjinsa a kunyace tana yar dariya. """Au! Dariya na baki? Ko ya yi kusa ne?""" Kafin ta bashi amsa sai ta ji ya fara zuge zip ɗin rigarta. Sai kuma ya duƙar da kansa saitin wuyanta ya "fara manna mata sumba, irin sassanyar sumbar nan da ke saka tashin tsigar jiki lokaci ɗaya." "Can kuma sai ya ɗago fuskarta ya haɗe leɓenta da na shi, ya cigaba da sumbatarta a hankali yana ɗan" "kallonta ta cikin hasken da ke shiga ta windojin ɗakin, idanunsu ya hade waje ɗaya, zallar soyayya da kauna haɗe da shauƙi da suke yiwa juna manne akan fuskokinsu ɓaro-ɓaro." Ya ƙara rirriketa a jikinshi yana jin kamar ya tsaga kirjinshi ya sanyata a ciki ko ya samu ya huta da abinda yake ji a game da ita. """I love you baby girl, so much. Bakina da kalmomina har sun fara gazawa wajen bayyana miki hakan." Kin shigo cikin rayuwata kin haskata a lokacin da na gama cire rai da samun wani haske. Ina ƙaunarki "sosai, fiye da tunaninki.""" "Gaba-daya sai tsoron da take ji ya bar jikinta, ta daga ido ta kalleshi, zuciyarta na gaya mata wannan shi" "ne mutumin da ta amincewa ta mallakawa zuciya da ruhinta, wanda take yiwa so irin wanda bata taba yiwa kowa irinshi ba." "Bata san wa yayi motsi na gaba ba, ita ce ko shi? Kawai dai tasan cewa ta sake tsintar bakinta ne dumu-" "dumu cikin nashi, yana kwance duk wasu notikan kanta da suke kara maidata putty a hannunshi, ta kasa yin kataɓus." "Haka ya cigaba da lulluɓeta da soyayyarshi mai sanyaya rai, har bata san lokacin da ya kai ta kan gado ba," "ya zare mata duk wata sutura ta jikinta. Ya hilaceta ta biye mishi suka keta hazon kauna, sai can da azaba tayi azaba ta fara shirin kwatar kwanta. Lokacin shi ai tuni ya gama yin nisa a duniyar da ta kaishi, baya jin kira balle ayi maganar dakatawa. Sai gashi tana bashi hakuri da kukan ya mata rai, shi ma yana bata" hakurin. "Wannan dare dai bai saurara mata ba sai da ya maidata mace cikakkiya, sannan ya sarara mata, ya" "rungumeta cikin kirjinshi yana jin yadda zuciyoyinsu ke bugawa a lokaci guda. Kalamai yake amayar mata na godiya da zallar kauna, wadanda ita a karan kanta tasan cewa ba a cikin hayyacinshi yake fadarsu ba." Da yana sane kam da ya rage wani abun. "Dare ya tsala sosai lokacin da ya samu ya rabata da jikinshi da kyar, tana ta kuka da shessheka na azaba" "da zallan shagwaba. Shi da kanshi ya hada mata ruwan wanka bayan ya tsarkake jikinshi. Ya taimaka mata itama tayi wankan, yana bayin haka tayi a gabanshi duk da yadda taso ya fita." "Da ta gama kuma ya naɗe ta da showel dauketa cak kamar jaririya, bai dire ta ba sai da ya je kan kujerar" "gaban mirror, ya jona hand dryer ya mika mata don ta busar da kanta, shi kuma ya tafi dauko mata kayan barci da zata sanya." Bayan gama ɗaɗɗaga kalolin rigunan barcin a ƙarshe ya zaɓa mata wata doguwar riga tsayinta iya "gwuiwa, kalar ruwan hoda. Rigar ta yi kyau sosai a idanunsa. Ganin duk motsin da zata yi sai tace 'wash!' yasa shi sake ɗaukarta cak zuwa kan gadon da ya gyara da kansa.." "Gabadaya ta bi ta gama rikitashi da salon kissarta, sai nan-nan yake yi da ita. A ƙarshe dai a ƙirjinsa yayi" "mata makwanci bayan ya kunna musu ƙwan lantarki mai duhu na barci, ko da ya duba fuskar wayarsa a lokacin, ƙarfe uku da kwata na tsakiyar dare." "Lumshe idanunsa yayi da zummar barci, zuciyarsa cike da matsanancin farin ciki da ƙaunar Kareema." "Hannunsa na hagu dafe da tsakiyar bayanta, na dama kuma yana kanta yana aukin shafa lallausan gashin" kanta da yake ta ƙamshi. "A hankali yake jin saukar numfashinta a saitin wuyarsa, alamun ta fara barci." ******** Da saurin gaske ya riƙo wayar da take ƙoƙarin suɓucewa daga hannunsa saboda tsananin mamakin da ya ji na maganganun da ke fita daga bakin Innaye. "Domin share ma kansa tantama, don tunanin ko kunnensa ne bai ji daidai ba ya saka shi cewa" """Innaye wai kika ce me?""" """Na ce ƙaniyarka Hafizu""" "Ta faɗa daga can ɓangaren, muryarta na ɗan bayyana ɓacin rai, saboda karo na uku kenan yana sake" tambayarta tana maimaita mishi magana ɗaya. "Ɗan dariya ya yi, idanunsa cikin na Ibrahim da yake tuƙa motar za su je gaisuwar surukai gidan Mummy." """Allah ya baki haƙuri Innaye. Ɗazu ina cikin mota ne, kuma kin san iskar hanya na saka network yin" "rawa ba'a ji sosai. Don Allah kika ce Bintu mene?""" """Na ce maka ƙarfe goma sha ɗaya da rabi na safiyar yau a ƙauyen nan ya yi ma Bintu. Da fari, duk mun" "zaci wani cin mutuncin ta zo yi mana, shi yasa bata samu wani tarba daga gare mu ba. Amma a yanzu tunaninmu ya canja Hafizu... Ina fatan dai ba tilastawa ko barazana kayi ma Bintu kan lallai dole ta zo ta" "bamu haƙuri cikin ƙanƙan da kai ba?""" """A'a! Wallahi ba ruwana Innaye. Ni ban san ma za ta zo ba.""" Ya amsa da mamaki sosai a fuska da muryarsa. """Madallah! To Bintu dai ta zo, ta bamu haƙuri sosai, har da kukanta Hafizu. Ta bi duk ɗakunan su" "Laraba da na Baffanku ta zauna dirshan a ƙasa ta nemi gafararsu. Wani abu da bata taɓa yi ba shi ne shan ruwan ɗakina, yau, ruwan randata Bintu ta sha Hafizu, na san ba ta shan komai ko cin wani abu na ƙauyen nan, shi yasa ko tayi banyi mata ba. Amma da ta ji ƙishi da kanta ta ƙarasa gurin randar ta buɗe ta ɗebo ruwa da kofina ba tare da wani ƙyanƙyami ba ta kafa kai ta shanye Hafizu. Kuma ka san wani" "abun ban al'ajabi?""" Innaye ta jefa mishi tambayar da muryar da ke bayyana jin daɗinta ƙarara kan irin yadda Bintu ta girmamata a yau. """A'a ban sani ba. Sai kin faɗa Innaye!""" "Ya amsa yana mamakin irin sauƙin halin Innaye da sam ba ta da riƙo, ka shekara dubu kana ɓata mata" "rana ɗaya idan ka tuba a gurinta an wuce gurin har abada. Lallai a gaida Innaye, a ɓangarenshi kam ko kaɗan bai ɗauki al'amarin a wani abu da Bintu take yi har zuciyarta ba. Ya daɗe da sanin ita ƙwararriya ce a pretending, don haka duk wani salo-salo na makircinta baza ta taɓa layance mishi ba." Tunaninshi ya katse lokacin da Innaye ta cigaba da cewa """Uhmmm! Da yake ban san za ta ci abincina ba, cikin ɗaki na barta na fita waje nayi aikin haɗa dambun" zogale da Baffanku ya ce yana sha'awa. Wallahi ina gama haɗawa tun kafin inyi mata tayi ta ce """Innaye a sammin dambun zan ci. Da mamaki na zuba mata, haka ta cire hijabin jikinta tana cin" "dambun nan tana shan ruwan randa, bata daina ci ba sai da ta cinye tas!" "Ka ga abinda nake faɗa maka ko Hafizu? Shi ɗan Adam, ba'a taɓa yanke masa tsammani da shiryuwa" zuwa hanya madaidaiciya... Na san a yanzu haka tunani kake kila wani ƙaryar ne yasa Bintu zuwa da "wannan salon ko?""" Da mamakin yadda ta san tunanin da yake yi ya ce """Ƙwarai kuwa Innaye. Kamar kin shiga zuciyata.""" "Ta yi dariya, sannan ta cigaba da cewa" """Hafizu kenan. To bari ka ji, da ace ana yanke ma bawa tsammani daga rahamar Ubangiji da ba'a ba" "bayi damar yin istigfari ba. Me yasa aka ce duk laifin da bawa ya aikata matuƙar ya tuba Allah zai yafe masa? Mu ma fa ƴaƴan Adam ne, muna kura-kurai da dama, kuma Allah yana yafe mana. Idan kuwa haka ne to me yasa mu a junanmu idan muka yi laifi baza mu yawaita yafiya ga kawunanmu ba? Daɗin gushi akan haka Kar dai ace ka manta da Hadithi na huɗu da ke cikin arba'una? Ko wane bawa kafin mutuwarsa sai littafi ya tabbata a kansa shaƙiyyun au sa'idun. Ina yi ma Bintu kyakkyawan zaton ta samu" "tuba ne tun kafin ajali ya riske ta.""" Ta ƙarasa maganar tana jinjinawa. Kafin ya ce komai ta cigaba da jaddada masa maganar da take yi """Tabbas! Na hango tuba da shiriya na gaske a idanu da halayen Fatima a yau ɗinnan. Sai dai dalilin tuba" da shiryuwar cikin ƙanƙanin lokaci ne dai Allah kaɗai ya bar ma kansa sani. "Ni yanzu babban dalilin da yasa na kira ka shi ne, ko da ta zo bata tarar da su Rakiya ba. Rashida ta haihu" "a can Ƙauyen Wusar, sun tafi tun sassafe, ayi suna yau, gobe idan sun soya hakika su dawo gida. Na yi na yi Bintu ta komo Habuja yau ta ce baza ta bar ƙauyen nan ba ko da kwana za tayi sai su Rakiya sun dawo ta roƙe su gafarar irin abubuwan da ta aikata musu tun daga farkon aurenku har zuwa yanzu...""" """Innaye ita Bintun ce da kanta ta ce za ta kwana a Faƙo?""" Ya sake tambaya da maɗaukakin mamaki. """Ƙwarai kuwa. Baffanku ma ya ce ta tafi, idan sun dawo shi da kanshi zai isar musu da roƙon gafararta" "ta ce ya yi haƙuri. Duk abinda ta ɓata ita da kanta take so ta gyara, ashe wai ko zuwa ta bamu" "haƙurinnan iyayenta da Yayarta sun so su biyo ta tace su bari ta taho ita kaɗai. Hafizu ko dai za ka kira ta a waya ka ce ta tafi kawai ba sai ta kwana ba...?""" """A'a Innaye!""" Ya katse ta da sauri. """Ku ƙyale ta kawai.. Tunda dai ita da kanta ta ce za ta kwana ba wani ne ya takura mata ba ai shi kenan." "Kar a matsa mata da cewa ta tafi kuma taga kamar baku yafe mata irin munanan laifukan da ta daɗe tana aikata muku bane...""" """Kuma fa haka ne.""" Ta amsa da alamun gamsuwa da maganarsa. """Yauwa to kin gani. Ku ƙyaleta kawai, ita tace ta ji ta gani ai. Duk yadda ta yiwu dai zan kira ki anjima." "Yanzu muna hanya ne za mu je gaishe da iyayen Kareema.""" """To Hafizu, Allah ya kaimu jimawar. Ina fata dai Kareematun tana nan lafiya?""" """Lafiyarta ƙalau Innaye.""" Ya amsa fuskarsa cike fal da murmushin jin daɗi don an tambayi lafiyar abar ƙaunarsa. """Madallah! Ka gaishe ta, yarinyar arziki. Tun da aka yi bikin nan yau kwanaki bakwai kullum da safe da" "yamma sai ta kira ni ta gaishe ni. Don Allah Hafizu ka riƙe matayenka da amana ka ji ko?""" """To Innaye. Na gode. In sha Allah zan ƙara kiyayewa.""" """Madallah""" Ta amsa sannan ta aje wayar. "A ɓangaren Hafizu inda suka gama magana da Innaye nan ya watsar da zancen Bintu, ko Ibrahim bai ba" "labarin abinda yake faruwa ba, shi ma Ibrahim ɗin bai tambaye shi abinda yake faruwa ba." ****** Mintuna biyar Innaye ta ƙara a ɗakin Umma Laraba suna ƙara jajanta irin canjin da suka gani a gurin "Bintu, sannan ta fice daga ɗakin zuwa na ta." "Da siririyar sallama ta shiga cikin ɗakin, tausayin Bintu ne ya kamata, ganin yadda take kishingiɗe akan" "daddumar Innaye da tayi sallah tana barci, kuma da alamun barcinta ya fara nisa, domin numfashi take saukewa cikin kwanciyar hankali." Ƙara tabbatar da gaskiyar canjin da ta gani a tattare da Bintu tayi. Wannan ya wuce a ce duk tana yi ne "don kissa ko makirci. Kamar dai ba Bintun nan mace ƴar gayu mai cike da ƙwalisa da gwalli ba. Bintun nan da ko akan kujerar ɗakinta ba ta iya zama sai ta shimfiɗa sabon daddumar da ko wane lokaci ba sa rabo da shi a mota. Yau ita ce kwance akan daddumar Innaye, ƙafafunta na taɓa dandaryar tile, lallai da" gaske ne ba'a yanke ma bawa ƙauna daga rahamar Ubangiji. "Innaye ta sake ƙura ma Bintu idanu, sai a lokacin ta lura ba ƙaramin rama tayi ba, fuskarta ya ƙara tsawo," "sai karan hancinta ya fito sosai. Nannauyar ajiyar zuciya Innaye ta sauke, sannan ta shige uwar ɗakinta da tafiyar sanɗa don kar ta tashi Bintu. Zuciyar Innaye cike da saƙe-saƙen ko auren da Hafizu yayi ne yasa Bintu yin laushi? Allahu aa'lamu. (Da yake ko da Baffa ya koma gida ranar ɗaurin aure bai faɗa ma Innaye" Hafizu ya saki Bintu amma ya saka shi ya mayar da ita ba.) "Kusan ko wane ƙauye suna da ɗabi'ar shimfiɗa tabarmi a tsakar gida daf da sallar magriba, idan aka idar" "da sallah a fita tsakar gida yara da manya a zazzauna akan tabarmi. Wacce take da girki ta zuzzuba abinci," "ana cin abinci ana hira. Wannan al'adar har yanzu ana yinta a ƙauyaku, musamman lokacin zafi." "Su Innaye suna zaune a tsakar gida, Umma laraba ce tayi tuwon dare, tuwon dawa miyar busasshiyar" kuɓewa. Da an doshi gurin abincin babu abinda ke tashi sai ƙamshin daudawa. "Su Innaye suna zaune akan tabarma suna cin abinci a kwano ɗaya su uku, yara na zaune a gefe ɗaya. Ita" "kuma Bintu tana cikin ɗaki Innaye ta dafa mata ruwan zafi ta kai mata kayan tea, duk da ta ce a ƙoshe" "take ba ta jin yunwa, domin da rana dambu ta ci da yawa, har lokacin cikinta dam yake." "Ga mamakinsu kwatsam sai ga Bintu ta fito tsakar gidan, da murmushi a fusjarta ta zauna a gefen" tabarmar da ta gani Innaye ta shimfiɗa a ƙofar ɗakinta. """Sannunku da hutawa Innaye. Tun ina cikin ɗaki ƙamshin daudawa ke bugun hancina. Ko za a ɗan saka" "min tuwon kaɗan in ci...""" """Kin gani fa Hajiya Bintu.""" "Inna Ladiyo ta ɗaga kwanon tuwon da suke ci ta nuno ma Bintu da sauri, kafin Bintu ta amsa ta cigaba da" cewa """Tuwon dawa ne fa, kin gansa baƙiƙirin babu ko kyawun gani a ido sai laushi a baka. Wannan tuwon na" "tabbata ko an zubo miki a mugun ƙyanƙyamin da muka sanki da shi baza ki iya ci ba, kila ma ya saka ki" "amai...""" """Zan iya ci.""" Bintu ta katse ta da faɗin haka. Fuskarta na ƙoƙarin ɓoye rashin jin daɗin kalaman da Inna Ladiyo ta "jingina mata, amma da ta tuno abinda aka faɗa ɗin halayenta ne ada, sai kuma cikin sauri tayi watsi da" ɓacin ran da ya fara damunta. """Ummanmu tana yi ma Daddy tuwon dawa lokaci bayan lokaci, a zubo min kaɗan, in sha Allahu zan iya" "ci.""" Ta ƙara da faɗin haka tana ƙoƙarin maye gurbin damuwarta da murmushi. "Umma Laraba da kanta ta miƙe zuwa kicin, ta yanki tuwon kaɗan ta saka ma Bintu. Wani ƙarin kulawa da" "tayi ga Bintun shi ne ɗaukar dunƙulen maggi mai star da tayi ta ɗan barbaɗa a miyan Bintu, ta ɗebi yajinta na tafarnuwa da ya ji maggi da kayan ƙamshi ta zuba kaɗan a gefe, sannan ta kai mata tuwon." """Na dai yi karambanin barbaɗa miki yaji, ban san ko kina so ba...""" """Na gode Umma, Allah ya saka da alkhairi.""" Bintu ta faɗa a ladabce sannan ta karɓi tuwon. "Mamakin da Bintu ta sake shayar da yara da manya na gidan shi ne cinye tuwon da tayi tas, ta ɗauki" kwanon ta kai gurin wanke-wanke. Kuma ta cigaba da zama a tsakar gidan tana jan yaransu da hira ta hanyar tambayar sunayensu da na sauran ƴan ɗakunansu har aka kira sallar isha'i. Sannan ta sake alwala ta shiga ɗakin Innaye tayi sallah. "Tun misalin ƙarfe biyar na yamma Innaye ta shiga ɗakin da Hafizu ya gina matsayin masaukin iyalansa, ta" ƙara gyarawa tas! Magriba na yi ta kunna maganin sauro ta kai ɗakin sannan ta rufo ƙofar. "Sai dai ko da ƙarfe tara na dare tayi, Innaye ta gabatar ma da Bintu ɗakin a matsayin inda za ta kwana," shiru tayi cikin tunani na wasu daƙiƙu. "Can kuma sai ta ɗaga kanta tana kallon gefen Innaye, idanunta ƙasa-ƙasa, da sanyin murya ta ce" """Innaye in dai bazan takura miki ba ni na fi so in kwana anan, ko kan dpguwar kujera ma ya ishe ni." "Amma idan zan takura miki sai in je can ɗin in kwanta...""" """Babu komai, ki shiga ciki ki kwanta kawai. Allah ya tashe mu lafiya.""" Innaye ta faɗi haka tun kafin ta aje numfashin maganarta. """Na gode. Allah ya tashe mu lafiya.""" Ta faɗa sannan ta shige cikin ɗakin. "Tsohon fallen zanen Innaye da yake maƙale jikin bango ta ɗauka ta ɗaura, bayan ta cire sket ɗin leshin" "da yake jikinta. Da bismillah a bakinta ta haye gadon Innaye da yasha gyaran zanin gado sabo fil, an lafe shi tas!kamar gadon ɗakin matashiyar mace." "Da yake bata yi tunanin kwana zai kamata ba, shi yasa bata zo da shirin komai na kwanciya barci ba." "Ƙuriii tayi da idanu tana kallon saman POP ɗin ɗakin Innaye, zuciyarta cike da tunanika mabanbanta." "'Lokacin da saƙon text message ɗin Hafiz ya riske ta, daman tana cikin tension, domin ko a lokacin" "kwananta biyu a kwance bata da lafiya. Kuma ta ƙi yarda sam a kaita asibiti, sai likita ne yake zuwa gida" yana kula da ita. "A lokacin da saƙon ya shiga cikin wayarta, suna zaune ne ita, Ummansu, da Aunty Sadiya da ta je gidan" "ƙara duba lafiyarta. Kamar baza ta ɗaga wayar ba, sai kuma ta ɗauka ta buɗe, duk da wani sashe na zuciyarta na faɗa mata ƙarar shigowar saƙon da ta ji bazai wuce na kamfanin MTN ba." Tun kafin ta gama karanta mummunan saƙon da ta ɗauke shi a mafi munin wulaƙantaccen saƙo da Hafiz "ya taɓa aika mata a iya tsawon rayuwarsu, jikinta ya ɗauki kyarma kamar ana kaɗa mata ganga. Tana gama karantawa ta saki wayar a ƙasa, tayi diri-diri tana zazzare idanu kamar sabuwar kamun hauka, sai kuma ta ƙwalla wani gigitaccen ihu da yasa Ummansu da Aunty Sadiya toshe kunnayensu a tsorace." "Bayan gama ihun, ƙaƙƙarfan kuka ta fashe da shi a lokacin Umma da Sadiya suka taho kusa da ita a gigice" suna tambayarta Lafiya? Me yake faruwa? """Yayarsu ɗauki wayar ki duba mu ji saƙon me aka aiko mata da har ya jefa ta cikin wannan halin?""" Umma ta faɗi haka ga Sadiya bayan ta lura Bintu baza ta nutsu ta faɗa musu abinda ke faruwa ba. "Da saurin gaske Sadiya ta rarumi wayar Bintu da ke yashe a ƙasa, tana gama karanta saƙon, saboda" "tsananin baƙin ciki da takaicin da Bintu ta ba ta riƙo kafaɗar Bintun ta yi da hannu ɗaya, ɗaya hannun" kuma ta yi amfani da shi wajen gaurama Bintu wani ƙaƙƙarfan marin da yasa lokaci ɗaya ta ɗauke wuta ɗif! Kawai ƙarar da take ji a kunnuwanta shi ne dummmm!!! Ta dawo cikin nutsuwarta ne ta ji muryar Aunty Sadiya tana ta zazzaga faɗa kamar za ta ari baki. Ɗaiɗaikun kalmomin da suka shiga kunnenta su ne """Idan kin raina ma su Ummanmu hankali ni baki isa ki raina min hankali ba, mintuna ashirin na baki, ki" "harhaɗo kayanki mu wuce can gidana, idan dai ba dussa bane a cikin ƙwaƙwalwar kanki kwanaki bakwai" ya ishe ki koyon yadda ake mu'amala da mutane. "Kasancewar Aunty Sadiya babbar ƴa a gidan, kuma ta mori hankali da nutsuwar da iyaye da sauran" "ƙannenta gaba ɗaya suke alfahari da ita. Da wannan dalilin yasa a mafiyawancin hukunci idan ta yanke ba'a mata musu a gidan. Kafin Daddy ya dawo, har ta ɗauki Bintu da take sharɓen hawaye da kumburarren kumatu sun wuce gidanta, sai a waya ta kira mahaifinsu ta faɗa mishi duk abinda ke" faruwa. """To babu damuwa. Amma duk yadda ake ciki dai kar ta daɗe, tunda mijinta ya mayar da ita ɗakinta" "gara ayi duk mai yiwuwa ta koma ɗakinta cikin ƙanƙanin lokaci.""" """To shi kenan Daddy. In sha Allah.""" "Zaman gidan Aunty Sadiya da tayi na kwanaki bakwai, wata sabuwar rayuwa ce ta samu Bintu da" taimakon Allah da taimakon Aunty Sadiya. Aka yi sa'a kuma a lokacin da taje gidan Yar mijin Aunty Sadiya tana gidan tana jinya bayan sun gama jerangiyar asibitoci babu sauƙi sai na Allah. Da farko dai Mummunar hawan jini ne ya haifar ma da mare "lafiyar mutuwar ɓarin jiki, daga bisani kuma sai ciwon ya juye kamar asiri aka yi mata, tana kwance sharɓan kamar matacciya, Kashi a kwance fitsari a kwance haka take yi." "Akwai yaran mare lafiyar guda biyu da suke gidan suna jinyarta, sannan ga mai aikin Aunty Sadiya, amma" duk da haka ta ga yadda Yayarta ke cin uban aikin kashi kamar Ummansu ke kwance tana jinya. Ganin hakan shi ya fara sanyayar mata da jiki. Wani abu da ta ƙara lura da shi shi ne wani extra ordinary kulawa ta musamman da mijin Aunty Sadiya mai suna Alh Buba yake mata. Ba tare da jin kunyar idanun Bintu ko ƴaƴansu ba a gaban kowa yake yawan faɗin """Allah ya miki albarka Sadiyata. Allah ya sani Ina alfahari da ke, amma kulawa da Yaya Asabe da kike yi" "yasa na ƙara alfahari da ke. In dai Aljannarki a ƙarƙashin ƙafata take, na ɗaga miki ki shiga a sauƙaƙe" "Sadiyata.""" "Idan ya jero ma Yayar tata waɗannan kalaman, daga irin murmushi da wani ɗan mirgina kai da take yi, ta" san daɗi da matsanancin farin ciki ne ke kai mata karo. "Kafin ta amsa sai ta ɗanyi fari da ido, sannan ta mayar mishi da martani a tausashe" """Na gode Alhajina. Nima ina alfahari da kai. Kuma in banda kai da abinka... Yaya Asabe ai ko ba Ƴar'uwa" bace ta cancanci kulawa da kyautatawa saboda jarabtar da Allah yayi mata. Fatanmu dai Allah ya bata "lafiya. Ina kuma ƙara roƙon Allah ya barmu tare har a Aljannatul-Firdaus.""" """Ameen.""" "Suke amsawa gaba ɗaya. Bayan haka kuma Kamar ba tsofaffi ba, sai suyi musayar tattausan murmushi a" tsakaninsu. Bayan zama na fuska da fuska da suka sha yi a mabanbantan lokuta ita da Yayar tata tana mata rihazal "ɗin munanan halayenta, da irin matakan da za ta bi a sauƙaƙe gurin gyara rayuwarta sannan ta gyara" "rayuwar aurenta. Ta kuma ƙaru da sake kusanta kanta sosai da Ubangiji, duk inda ƙarfe uku da rabi na" "dare tayi, Yayarta za ta fito turakar mai gida ta tashe ta, ta saka ta yin ibada, ba ta sake kwanciya sai" misalin ƙarfe takwas da rabi idan ta yi sallar Duha. "Daman dai sakaci ne irin namu na ƴaƴan Adam, amma duk inda damuwa da ƙunci haɗe da baƙin ciki" "suka yi yawa, to babbar mafita da hanyar da za'a kama mai ɓullewa shi ne a kusanta kai da Ubangiji, sannan ayi ta istigfari da hailala." "Waɗannan abubuwa da Aunty Sadiya ta koyar da Bintu cikin kwanaki bakwai, yasa ta samun wani" "nutsuwa da kwanciyar hankali na musamman, wanda ita da kanta baza ta iya tuna lokacin da ta shiga cikin makamancin wannan nutsuwar ba." "Har yanzu Hafiz da ɗanta Aadil suna cikin sahu na farko a rayuwarta, amma fa kaso saba'in cikin ɗari na" "yadda al'amarinsu ya dame ta a baya, yanzu ba ya damunta." "Sun tattauna muhimman batutuwa da ƴar uwarta, ta kuma gane kura-kuran da ta daɗe tana tafkawa." Wani abun burgewa kuma shi ne da gaske ta ɗauki aniyar gyara kura-kuranta. Da wannan dalilin yasa bata yi ƙasa a gwuiwa ba wajen zuwa ƙauyen Faƙo neman gafarar su Innaye. Ba kuma don barazanar da Hafiz yayi mata ba.' "Nannauyan ajiyar zuciya ta ja ta sauke sadda ta zo nan a tunaninta, ta ɗaga hannu biyu sama ta karanto" "addu'ar barci ta shafa a fuska da sassan jikinta. Sannan ta lumshe idanu tana sauke numfashi cikin nutsuwa, har zuwa sadda nannauyan barci yayi awon gaba da ita." "Kamar yadda ta fara sabawa da ɗabi'ar da Auntynta Sadiya ta ɗora ta akai na tashi cikin dare yin ibada," ƙarfe huɗu saura minti goma na asubahi ta farka da salati a bakinta. "Ɗankwalin kanta da ya zame saboda barci ta ɗauka ta ɗaura a kanta, sannan ta sauka daga kan gadon ta" fito da nufin zuwa waje don ɗauro alwala. "Tana fitowa Falo, ta ga Innaye tana sallar nafilfili, kamar yadda itama ta saba gabatarwa ko wane dare." "Ajiyar zuciya ta ja na ƙara samun nutsuwa, ta ɗauki buta nan lungun kujerar da take kusa da ƙofar ɗakin Innaye, ta buɗe ƙofa ba tare da tsoron komai ba ta fita tsakar gida ta ɗauro alwala." ******** "Ƙarfe biyu na rana tayi ma su Aunty Balira a gidan Baffa. Da yake duk basu da labarin zuwan Bintu, turus" suka yi da ɗaurarriyar fuska suna aika mata da kallon banza lokacin da suka ganta zaune dirshan a tsakiyar ɗakin Innaye tana cin ɗanwake. Da farko jikin Bintu ne ya ɗanyi sanyi bayan ta tuna irin tozarcin da tayi musu a haɗuwarsu ta ƙarshe. Sai "kuma ta yi ƙoƙarin yalwata fuskarta da murmushi, a zuciyarta take godiya ga Allah da yasa bata bi dokin" zuciya da zugar shaiɗan ta miƙa su gurin ƴansanda ba. Yau da ina za ta saka kanta da kunya? """Oyoyo... Sannunku da dawowa Auntys ɗina. Ku shigo mana?""" "Tayi maganar da sanyin murya, har lokacin murmushin fuskarta bai ɓace ba." """Uhmmm! Bintu kenan! Wani salon munafurci da kisisinar ce kuma ta saka ki yi mana murmushi? Kar" "dai ki manta, mu ɗin ne dai warki daidai da ƙugun kowa, la'ada waje za mu ci...""" Idanunta ciccike da hawaye ta katse Rakiya da cewa """Wallahi Tallahi alkhairi ne ya kawo ni gare ku ba sharri ba Aunty Rakiya. Na zo neman gafararku ne," "don Allah ku yafe min.""" Dariyar da Rakiya da Ladidi suka saka mata yasa ta ƙara jin duk ta tsani kanta. """Uhmmm! Bintu kar dai ace a cikin kwanaki bakwai da auren Hafizu da ƴar mutunci da arziki" "Kareematu har kin nuna kinyi luguf ɗin da za ki gane Borno gabas take...""" """Miye haka Ladidi? Me kike faɗa haka? Wani irin maganganun banza ne haka kuke min a cikin ɗaki?""" Innaye da ta idar da sallah ta faɗi haka ranta a ɓace. Kafin ta sake cewa komai Baffa yayi sallama a ƙofar ɗakin. Da saurin gaske duk su ukun suka amsa masa sannan suka nemi gurin zama suka zazzauna a ƙasa. "Baffa yana shigowa ya nemi gurin zama kan kujera ya zauna. Bayan sun gaishe shi, barka da dawowa ya" "fara yi musu, sannan ya tambayesu yadda aka yi taron suna. Bayan sun amsa da lafiya ƙalau ne ya buɗe taron da addu'a. Nasiha mai shiga jiki yayi musu akan falalar da ke tattare da yafiya, sannan ya ƙarƙare maganganunsa da faɗin abinda ke tafe da Bintu." "Ba don sun yarda ɗari bisa ɗari Bintu ta shiryu ba, duk suka yafe mata don ganin idon Baffa da Innaye." Da yanayin jin daɗi a fuska da muryar Bintu tayi musu godiya. Baffa ya ƙara musu taƙaitaccen nasiha "sannan ya fice daga ɗakin, bayan ya jaddada ma Bintu lallai tayi gaggawar gama cin abinci, ga direban da zai tafi Kaduna can ɗan maƙwafcinsu sai ya wuce da ita." "Duk yadda Bintu ta so ganin sakin fuskarsu Aunty Balira abun ya gagara, ko da tayi nakwa-nakwa da" "fuska za ta saka musu kuka ƙasa-ƙasa Aunty Rakiya ta galla mata harara, ta haɗa da jan siririn tsaki ta kawar da kai." "Ita kuwa Aunty Ladidi don haushi ma buta ta ɗauka ta fice daga ɗakin, a cewarta, bayi za ta je." """Kin ga Bintu, tunda dai duk mun furta mun yafe miki don Allah kar ki nemi ki takura mana. In banda" "ma zuciyar musulunci mai cike da imani ta ya lokaci ɗaya bawa zai yafe tozarcin da aka yi mishi shi ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba ba sau uku ba? Ki tafi kawai Bintu. Don yafewa mun yafe miki, amma ɗorewar kyakkyawar mu'amala a tsakaninmu da ke zai biyo bayan yadda kika cigaba da" "mu'amalantarmu ne. Allah ya mayar da ke gida lafiya..""" "Aunty Balira ta faɗi haka, da fuska mara walwala." "Innaye bata nemi matsanta musu ba, saboda ta san suna da gaskiya. Bayan haka ma zuciya kowa da irin" "tasa, wata zuciyar ko ta yafe sai a hankali za ta manta abinda ya faru. Nasiha ta ɗora musu daga inda Baffa ya tsaya har zuwa lokacin da aka aiko yaro wai idan Hajiya Bintu ta gama ta fito su tafi." "Bintu da taje garin daga ita sai ƙaramar jaka rataye a kafaɗarta, sai ga shi ta tafi da buhu guda na" "tsarabar da iyalan Baffa suka haɗa mata. Tana zaune a cikin mota, tayi shiru tana tunanin halayen Innaye, Baffa, da ahalinsu. Zuciyarta cike da da na sani a karo na barkatai." "Duk da bata taso a gidansu ta ga suna da dangi irinna ƙauyen-ƙayau haka kamar su Innaye ba, ko daga" "mu'amalar da Ummansu take yi da ƴan'uwan mijinta, maƙwafta da basu da shi da almajirai, ya kamata" ace ta koya daga halin arzikin iyayenta. Ta rasa ta yadda aka yi tayi sakacin da har ta bari shaiɗan yaci galaba a kanta ta dinga tsula irin wannan "tsiyar, kamar bata san inda yake mata ciwo ba. Sai ga shi mutanen da ta daɗe tana cuta musu, sun samu" "damar ramuwa a kanta basu rama ba, a madadin haka ma suka yafe mata, sannan suka bi ta da karamci mai tsayawa a zuciya." Lallai ta gode ma Allah da yasa ta gane kuskurenta tun lokaci bai ƙure mata ba. Alhamdulillah! ********* Washe gari da misalin ƙarfe huɗu na yamma direba ya aje Bintu a ƙofar gidan Zulai. Domin can gidan "Mummy ta fara zuwa, bata tarar da kowa ba sai Hajja, bayan gaisuwar mutunci da girmamawa da ya shiga tsakaninsu Hajja ta sanar da ita Zulai ba ta nan, ta tafi can gidanta ta ɗebo wasu kayayyaki, saboda" gobe za ta tafi Faƙo. "Bata ɓata lokaci ba tasa direba ya juya da ita bayan ta yi mishi kwatancen gidan, zuciyarta cike da" addu'ar Allah yasa kar sake samun saɓani. "Cikin sa'a kuwa ko da ta isa ta tarar da ita a gidan, tana tsaye a bakin ƙofar Falonta da jakunkunan kaya a" gabanta maigadi yana kwasa yana lodawa a boot ɗin motarta. """Ke kuma Lafiya haka wata ƙozai-ƙozai da ke?""" Tambayar da Zulaikha ta fara jefa mata kenan tana mata wani kallo mai cike da wulaƙanci da ƙasƙanci. "Ko kaɗan Bintu bata bari ɓacin rai ya bayyana a fuskarta ba. Ta sani duk cikin ƴan'uwan Hafiz daga Rakiya," "sai Zulai, sai Ladidi a rashin haƙuri. Don haka tun kafin ta shigo ta sa ran za ta fuskanci fiye da haka." """Allah ya huci zuciyarki Hajiya Zulai. Don Allah ki kwantar da hankalinki, kin ga, na rantse da girman" "Allah ba tsiya ne ya kawo ni ba. Na zo ne kawai don in nemi gafarar irin abubuwan da na aikata miki a baya, shi kenan ba wani abu ba.""" """Bintu?""" Zulai ta kira sunanta da mamaki. """Ke ce kuwa?""" "Ta sake tambayarta mamakinta na daɗa ninkuwa. Domin ita sam ba ta da labarin zuwan Bintu Faƙo," abinda ya wakana da kwanan da tayi. """Ko dai wani wulaƙancin ne kika sake zuwa kiyi min? Idan ma wulaƙancin ne kin san na dama ki na" "shanye ki.""" """Wallahi ba haka bane Zulai, yafiyar dai da kika ji na ce ita nazo nema. Idan kuma baki yarda ba, kina" "iya kiran Innaye a waya ki tambayeta, don shekaran jiya na je can, acan ma na kwana, ban bar Faƙo ba" "sai da na tabbatar sun yafe min ita da su Aunty Balira.""" """Shi kenan! Shigo, Bismillah.""" "Zulai ta faɗa sannan ta matsa mata daga hanyar shiga cikin falon, har lokacin mamakin da take yi bai bar" kan fuskarta ba. Kafin ta zauna sai da ta shiga kicin ta ɗauko ma Bintu ruwa da lemu. """Gidanki ya yi kyau sosai Zulai, Allah ya sanya albarka ya ƙara zaunar da ku lafiya.""" "Bintu ta faɗa fuskarta na bayyana gaskiyar asirin zuciyarta ta tona, kamar ba gidan bane a wancan karon" hassada da kishi da baƙin ciki suka rufe mata idanu ta kasa yaba kyawunshi a wancan lokacin. """Uhmmm! Amin.""" Zulai ta amsa a taƙaice. "Ruwan ta tsiyaya a kofi ta sha kaɗan, sannan ta buɗe baki ta sake roƙar yafiyar Zulai cikin ƙanƙan da kai," har tana ƴan ƙananun hawaye. Ba tare da wani ja'inja ba a mamakance Zulai ta ce ta yafe mata. Don ita ganin al'amarin take yi kamar a "shirin film ko kuma tatsuniya, jira kawai take yi taga ƙarshen shi ta samu sararin furta ƙurungus!" Sai kuma ta ga har Bintu ta tashi tafiya bata yi wani yanayi da zai bayyana yafiyar da ta nema ba har zuciyarta bane. "A mutunce suka yi sallama, Bintu tana ta godiya ma Zulai kan yafiyar da tayi mata cikin ƙanƙanin lokaci," "har ta fita waje ta koma cikin falon, ga tsammanin Zulai za ta tambayi ina Aadil yake ne, sai ta ji ta ce" """Taimaka min da lambarki mu dinga gaisawa mana Zulaikha? Kin san bahaushe ya ce yawan gaisuwa ya" "fi yawan faɗa.""" """Haka ne.""" "Ta amsa a ɗarare, da alamun har lokacin mamaki da kaɗuwa bai sake ta ba, ta karanto mata lambar" "wayar ita kuma Bintu tana shigarwa cikin wayarta. Sai da ta gama tsaf sannan ta sake yi mata godiya ta fita a falon, fuskarta cike da murmushi." Zulaikha tana jin ƙarar rufe get alamun Bintu sun wuce ta rarumo wayarta da sauri ta danna kiran lambar "Innaye, tana ɗauka daga can ɓangaren, ko gaisuwa bata tsaya sunyi ba ta fara kakabin al'amarin" """In da ranka ka sha kallo Innaye... Wai fa Bintu ce tazo har gidana neman gafara kan irin wulaƙanci da" "cin mutuncin da tayi min a baya...""" """To menene a ciki Zulai? Ai ta yi kyan kai da bata tsaya girman kai ya hanata aikata abinda ya kamata" "ba. Mu ma ta zo nan har da kwana. Ina fatan dai kin yafe mata ba tare da tashin-tashina ba?""" """To ya zanyi Innaye? Na dai yafe ba don halinta ba...""" """To madallah! Zan kira ki anjima. Barin sallami Baffanku, kwaɗon rama nake masa...""" "Jin sunan kwaɗon rama yasa miyaun bakinta tsinkewa, A shagwaɓe ta ce." """Innaye ni ma zan ci, a tsinko da yawa gobe da wuri a kwaɗanta min kafin mu ƙaraso.""" """Allah ya tsare, Ubangiji ya kawo ku lafiya.""" Innaye bata jira ta amsa ba ta katse wayar. ******** "Yau kwananta huɗu da dawowa daga Faƙo. Sosai hankalinta ya ƙara kwanciya, kwana biyu ta ƙara a" gidan Aunty Sadiya sannan ta tattara kayanta ta koma gidan Daddy. "Yau ne ta yanke shawarar za ta kai ma Hafiz ziyara har Ofishinsa. Saboda idan ba can ɗin ta je ba, babu in" "da za ta samu ganinsa suyi magana ta nutsuwa fuska da fuska. Ta daɗe da sani ko ta kira shi bazai zo ba, baya ma ɗaukar wayarta, balle har ta sararin faɗa mishi abinda take so." "Bata sha wahalar samun iso zuwa Ofishinsa ba, saboda duk an santa a ma'aikatarsu Hafiz ɗin. Tana sanye" "ne da sutura ta mutunci, hijabin jikinta ya sauka har ƙasan gwuiwoyinta, sai daga can ƙasa ake ganin sket ɗin jikinta na atamfar Super Holland. Duk da fuskarta ta yi fayau saboda rama, amma ta yi kyau abinda, kuma da yake jikinta mai kyau ne babu ma wanda zai kalle ta ya ce ta kai shekaru talatin da huɗu, balle har ayi tunanin ta yi aure ko kuma ace ta haifi Aadil, in dai za'a faɗi gaskiya, Bintu tana cikin kyawawan mata ajin farko. Kuma kyawunta na ɗaya daga cikin dalilin da yasa ta daɗe tana taka rawa a rayuwar" Hafiz. Tsawon daƙiƙu talatin suka ɓata suna musayar kallo a tsakaninsu. Hafiz da idanu cike da mamaki da "yanayin rashin murna da ganinta, ita kuwa Bintu da fuska mai cike da kewa... wata matsananciyar ƙauna" da ta gaza ɓoyuwa ta bayyana a fuskarta. """Ayya mana Daddyn Aadil, baka yi murna da ganina bane?""" Ta faɗa da sassanyar murya. """Uhmmm! Bintu kenan.""" Ya yi maganar da yanayin takaici. """Me ya kawo ki nan?""" Ya sake faɗa tun kafin tayi magana. """Zan iya zama?""" Ta kore tambayarshi da na ta tambayar. """Uhmmm! Idan kin so""" Ya amsa a taƙaice. Da sanyin jiki sosai ta taka a hankali zuwa inda aka tanadi kujerun zaman baƙin da suka zo Ofis ɗin. Zuciyarta cike da baƙin cikin yadda son zuciyarta ya janyo rugujewar matsananciyar soyayyar da Hafiz yake mata. 'Ya rabbb!' "Ta faɗa a hankali, sannan ta sausauta murya ta fara gaishe shi da tambayar bayan rabuwa." """Lafiya ƙalau Alhamdulillah!""" "Amsar da ya bata kenan a taƙaice, da yanayin gundura ƙarara." """Me ya kawo ki nan?""" Ya sake tambayarta a taƙaice. """Kayi haƙuri Daddyn Aadil. Na sani duk ni na jawo abubuwa suka taɓarɓare har haka a tsakaninmu. Ina" "mai sake baka haƙuri a karo na uku...""" """Bintu!! Me ya kawo ki nan??""" Ya jefa mata tambayar da murya mai bayyana ɓacin rai ƙarara. "Jikinta ne ya ƙara sanyi, gwuiyawunta suka ƙara saki, kamar wacce ta kwana ta yini tana zawo." "Daƙiƙu talatin ta ɓata tana kallon cikin idanunshi tana karantarsu, ƙirjinta ne ya buga daram!!! Domin" babu abinda take gani sai matsananciyar tsanarta. """Na zo ne in ji makomar zamantakewar aurenmu daga bakinka...""" """Makoma?""" Ya tambaye ta. """Wace makoma kike magana kuma Bintu?""" Ya sake tambayarta da tsawa-tsawa. """Na zaci duk makomar da kike magana akai na riga da na bayyana miki ta saƙon text message tun ranar" "da aka tilasta min ba da son raina ba na mayar da ƙaddararren aurenki...?""" """Ƙaddararre Hafiz?""" Ta tambaye shi muryarta na rawa. """Auren nawa ne kake kira ƙaddararre Hafiz?""" "Ta sake faɗa hankalinta a tashe, bayan ta miƙe tsaye, idanunta a warwaje. Hannayenta duk biyu dafe da" ƙirji. """Kina mamaki ne Bintu?""" "Ya tambayeta yana ƴar dariya, amma irin dariyar nan ta zallar takaici." """Ai idan na kira aurenki da ƙaddararre na yi miki da sauƙi Bintu. Ko dai kin manta irin makirce-makirce" "da kissa da tuggun da kika yi ta haɗawa a zamantakewarmu ne? Kai... Ni kam me za'ayi da mace irinki Bintu? Iyaye da ƴan'uwana na jini kika so raba ni da su fa... Shi yasa a kullum ba na gajiya da godewa Allah da yasa idanuna suka buɗe tun lokaci bai ƙure min ba... Allah na gode maka...""" """Ha...fiz...""" "Ta katse shi da rawar murya, jin da tayi zuciyarta na neman bugawa saboda zafin baƙaƙen maganganun" "da yake yayyaɓa mata. Maganganun da ita da kanta ta san gaskiya yake faɗa, gaskiya mai masifar ɗaci da" maƙaƙi a zuciya. """Na sani, ni da kaina na aikata kura-kurai masu yawa a baya... Kura-kurai masu girma da gyaruwarsu" "sai a hankali, domin ba a taɓa ɓari a kwashe duka. Me yasa a yanzu da nake neman tuba baza ka bani dama ta biyu ba? Sannan abu ɗaya da nake so ka sani shi ne, sam ban zo Ofishinka don ƙara fama gyambon da tun asali ni ce sanadiyyar samuwarshi ba. Alfarmarka nake nema Hafiz, dama ta biyu kawai nake buƙata a gurinka... Kwanaki uku da suka wuce na je Faƙo na nemi yafiyarsu Innaye, kuma duk sun yafe min ba tare da wani tashin tashina ba. Shekaran jiya na je gidan Zulai, ita ma na roƙe ta gafara, kuma ta tabbatar min ta yafe min har ma munyi musayar lambar waya a tsakaninmu. Me yasa baza ka" "kwaikwaya daga halin Iyaye da ƴan'uwanka ba...?""" """Saboda ni ɗin ba su bane da kika saba raina ma hankali kina buga su kamar Tamaula. Look Bintu, salo-" "salo na munafurcinki kin daɗe kina buɗa min shafi bayan shafi, ko wannan neman yafiyar da kika yi na tabbata wani salon munafurcin ne. Bari in sake maimaita miki, idanuna ya daɗe da washewa a kanki Bintu, yanzu kar nake kallonki. Ki tattara kayanki ki koma Faƙo idan har kina mu cigaba da zama... idan" "ba haka ba kuwa sai in ce Allah raka taki gona...""" """Me kake nufi Hafiz?""" Ta tambaye shi da maɗaukakin tashin hankali a fuskarta. Sai da yayi taku biyu zuwa gabanta sannan ya ce """Ina nufin in dai baza ki koma Faƙo ki zauna da su Innaye ba, ni kuma bazan cigaba da riƙe igiyar auren" "ki ba. Zan sake baki takardarki ki je can ki sami wani mijin da bashi da iyaye ƙauyawa...""" """Anya kana so na kuwa Hafiz?""" "Ta jefa mishi tambayar ƙirjinta na bugawa, domin bata san irin amsar da zai fito daga bakinsa ba." """A da kenan Bintu. A yanzu kuwa ko rantsuwa nayi miki babu kaffara Kareema ta daɗe da mamaye filin" "da a baya mallakinki ne... Idan akwai wata ƴar kimarki da ta rage a idanuna bai wuce ta kasancewarki uwar Aadil ba, a bayan haka kuwa na rantse da Allah kallonki ma ba ƙaramin baƙin ciki da takaici yake saka ni ba.""" "Da saurin gaske Bintu ta lalubi kujerar da ke bayanta ta zauna, jin da tayi lokaci ɗaya wani hajijiya mai" ƙarfi yana neman kifar da ita a ƙasa. """Na gode Hafiz. Na gode ƙwarai.""" "Tayi maganar da muryarta da lokaci ɗaya ya shaƙe, ya shige can ciki kamar wacce aka maƙurewa" maƙogwaro. "Dafe kanta da taji yana bugawa da ƙarfi kamar ana sara mata guduma tayi, idanunta a lumshe. A" "zuciyarta take ta janyo duk irin addu'ar da ya zo mata. Ta daɗe a cikin wannan halin sannan daƙyar ta ɗan dawo cikin nutsuwarta, ta sake buɗe baki daƙyar ta ce" """Allah ya sani ni har yanzu ina son ka Hafiz... Sannan in da ace ina da tabbacin kana so na, zama a Faƙo" "tare da su Innaye ba komai bane, ko babu komai zan ƙara gogewa da wani sabon ilimi na zamantakewar" "rayuwar duniya wanda da can ban san shi ba.""" "Ta ɗanyi shiru tana mayar da numfashi a wahalarce, daƙiƙu sittin ta ɗauka sannan ta cigaba da magana" """A fahimtata da zaman aure yarjejeniya ta amincewar zamantakewa tsakanin mutane biyu, ba nau'i ne" "na cutarwa ko bautarwa ba. Kuma ko wane aure akwai wasu muhimman turaku da suke riƙe da wannan aure, So, Ƙauna, Yarda, amincewa haɗe da yima juna uzuri su suke taka muhimmiyar rawa gurin jan" ragamar ko wane zamantakewar aure zuwa tudun mun tsira. Daga abinda na fahimta a kalamanka na "yanzu Hafiz ba ka so na, sannan kuma ka daɗe da yanke min tsammanin zan shiryu, don haka da" "waɗannan dalilan ina ga babu amfanin cigaba da zaman aure a tsakaninmu...""" "Tana zuwa nan a maganganunta ta fara shessheƙar kuka da ƙarfi, amma duk da haka bata tsagaita ba sai" da ta kai aya """Allah ya sani ina daga cikin matan da matsananciyar soyayya ta yi kaɗan ta rufe min idanu inyi zaman" "kwantai da wulaƙanci a gurin ɗa namiji... Bazan yi zaman cutuwa sannan inyi haƙurin da babu lada in hallaka ba, sannan kai ma in halakar da kai, saboda rashin ƙauna zai sa baza ka iya sauke nauyin haƙƙina da ya rataya a wuyarka ba. Don haka, ina roƙon mu kawo ƙarshen wannan tafiyar Hafiz... Allah ya sada" "mu da alkhairinsa.""" "Da saurin gaske ta duƙunƙune gogaggen hijabinta ta cusa a baki saboda kukanta da ya ƙara ƙarfi, sannan" ta fice daga Ofis ɗin da sassarfa tana sharɓen hawaye. "In da Allah ya taimaketa shi ne da direba ta je Ofis ɗin, ba don haka ba lallai da sai dai ta ɗauki shatar" "Taxi ya mayar da ita gida, domin a irin wannan halin da take ciki sam baza ta iya tuƙa mota ba." """Baba Mamuda gidan Aunty Halima za ka kaini.""" Ta faɗi haka ga direba bayan sunyi nisa a kan hanyarsu ta komawa gida. """To Hajiya Likita. An gama, Allah ya huci zuciyarki ya yaye miki abinda yake damunki.""" Direban ya faɗa da murya mai bayyana damuwa da halin da Bintu ke ciki. ****** """Anya Bintu kin yi tunani mai zurfi kuwa? Kina ganin rabuwarki da Hafiz shi ne zai zama maslaha a" "rayuwarki?""" "Aunty Sadiya ta faɗi haka da murya mai bayyana damuwa sosai, bayan ta gama sauraren duk irin" bayanin da Bintu tayi mata cikin kuka da tashin hankali. Ita kanta ta shiga cikin ɗimuwa. Kuma ta sani duk irin abubuwan da suka faru a zamantakewar auren Bintu laifin Bintun ne. Amma bata yi tsammanin bayan sakkowa da Bintu tayi ta gane kuskurenta har tayi aniyar gyarawa Hafiz zai cigaba da riƙe laifukanta a zuciyarsa ba. """Kiyi haƙuri Aunty... In sha Allah hakan shi ne mafi alkhairi.""" "Bintu ta amsa da shaƙaƙƙiyar murya, gwanin ban tausayi. Idanunta sun kumbura sun yi tulu-tulu saboda" kukan da ta ɗauki tsawon lokaci tana yi. """Shi kenan Bintu. Za mu cigaba da taya ki addu'a Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi. Amma dai na so" "ace kin ƙara zurfafa tunani. Mata da yawa Bintu suna rayuwa ne a gidan mazajensu ba tare da wata aba wai ita soyayya ba. Idan za ki tara mata ɗari, ko wacce za ki ji dalili ne mabanbanta ke zaune da ita a gidan mijinta ba don tana jin wani mashahurin daɗi ba...""" """Bazan iya ba Aunty.""" Bintu ta katse ta da sauri. """Allah yana gani bazan iya irin wannan zaman ba. Da dai ace in ƙare rayuwata a irin wannan zaman da" "ƙarara miji ya nuna min kuma ya faɗa min ba ya so na, na rantse da Allah gara in haƙura da auren gaba ɗaya. Ban ce bazan iya haƙuri a cikin rayuwar aure ba, haƙurin da na san ina cutuwa ne gaskiya bazan taɓa iyawa ba...""" """To Aadil fa? Yanzu ko rayuwar ɗaya-ɗayan ɗan da Allah ya baki bai isa yasa ki haƙuri da Ubansa ba" "Bintu? Malam bahaushe fa cewa ya yi duk bakin da ya furta so a farko, ko daga baya ya zo ya furta ƙi ɓacin rai ne yasa shi faɗin haka. Ki tausaya ma rayuwar yaron ki.""" """Uhmmm! Aunty kenan! Ni fa duk wata shaci-faɗi ta Malam bahaushe ba da ni za'ayi ta ba. Ina duba" "maslahar rayuwata ne, idan da rabon mu sake zama can gaba wata ƙila mu haɗu, amma a yanzu kam na rantse da Allah ko son Hafiz zai kashe ni bazan koma gidansa ba." "Batun Aadil kuma yara da yawa suna rayuwa ba tare da mahaifiyarsu ba, kuma Allah yana raya su cikin" "aminci. In da ace mutuwa nayi kuma fa?""" """Shi kenan. Tunda har kin rantse. Yanzu sai ki tashi mu tafi can gida gurin Daddy, tunda dai ta inda aka" "hau ta nan ake sauka.""" ******* "Ko da suka je ma Daddy bayanin halin da ake ciki, Tambaya ɗaya da yayi ma Bintu shi ne" """Tausayin halin da kika shiga sanadiyyar rabuwarki da Hafiz, da irin mawuyacin halin da kika sake" faɗawa ranar da kika ga hoton auren Hafiz yasa na karya gwuiwata na roƙi mahaifinshi ya kira Hafiz ya "tilasta mishi mayar da ke ɗakinki. A yanzu da ke da kanki ki ke ganin rabuwar ta fi alkhairi a tsakaninku, ina fatan baza ki sake ɗaga mana hankali da koke-koken baza ki iya rayuwa ba tare da mijinki ba?""" """In sha Allahu hakan baza ta sake faruwa ba Daddy.""" "Ta amsa idanunta a ƙasa, wasu sabbin hawayen suna tsattsafo mata amma tayi ƙoƙarin haɗiyewa." """Shi kenan. Allah hakan shi ne mafi alkhairi a tsakaninku.""" """Amin thumma Amin.""" Umma da Aunty Sadiya suka amsa cikin haɗin baki. "Sallamarsu Daddy yayi suka koma falon Ummansu. Yayi shiru cikin tunani, zuciyarsa cike taf da rashin jin" daɗin al'amarin. Can kuma sai ya ɗaga waya ya kira Abba Lurwanu ya kora mishi bayanin duk halin da ake ciki. "Shi ma sosai ya nuna alhini akan lamarin, daga bisani kuma ya ƙarke da addu'ar Allah yasa haka shi ne" "mafi alkhairi. Bayan gama waya da Abba Lurwanu kai tsaye lambar Baffa ya lalubo ya danna mishi kira, bayan sun gaisa, a nutse ya faɗa mishi duk abubuwan da ke faruwa." "Da farko sosai Baffa ya ɗaga hankalinshi, saboda a tunaninshi duk laifin na Hafizu ne, sai da Daddy yayi" "mishi bayani gwari-gwari, da irin hujjojin da Bintu ta bashi sannan yayi sanyi, da rashin jin daɗi da alhini sosai a muryarsa shi ma yayi ta jera addu'ar tabbatuwar abinda ya fi zama mafi alkhairi tsakanin ma'auratan biyu." ****** """Yaya? Wai kuna duba lokaci kuwa? Yanzu fa ƙarfe goma sha ɗaya saura kwata na dare, daga yini ɗaya" "har yanzu baku dawo min da ɗana ba. Gaskiya in dai haka ne yinin bazan sake baku aron shi ba.""" "Zulai tayi maganar tana kumbura baki, kamar Hafiz ɗin yana gabanta." Dariyar Kareema da Hafiz da take jiyowa ƙasa-ƙasa ta cikin wayar yasa ta sakin baki galala. """Kinga Zuly, gara ma ki kwanta kiyi barcinki. Aadil ya dawo gida kenan. Tun ɗazu ma ya yi barci, haba!!" "Yaye fin wata ɗaya ai kinyi na Allah da Annabi. Ke ma ki huta ki ji da lafiyarki.""" Kareema tayi maganar daga can ɓangaren har lokacin da dariya a muryarta. """Kar ku min haka Aunty Kareema, kina sane dai na faɗa ma su Innaye gobe da Aadil zan je Faƙo...""" """Jibi idan Allah ya kaimu mu ma muna tafe. Don haka ki kwanta kiyi barci, gobe kafin ku wuce ki barma" "Mummy duk kayanshi zan aiko a karɓa.""" Hafiz bai jira ƙorafin da za ta sake yi ba ya katse wayarsa. Tsananin haushi yasa bata duba tazarar lokaci da ke tsakanin inda take da ƙasar da Abban Imam ya je ba "ta lalubo lambarsa ta danna mishi kira. Kiran farko da na biyu bai ɗauka ba, sai a kira na uku ya ɗauka, da magagin barci a muryarsa ya ce" """Beb...!""" Kukan da ta sakar mishi yasa shi wartsakewa ba shiri. Hankalinshi a tashe ya fara tambayarta lafiya? Me yake faruwa? """Ba Yaya bane da Aunty Karima...""" Ta amsa mishi a shagwaɓe. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke na samun nutsuwa sannan ya sassauta murya ya ce """Su basu san da a taɓa min ke gara aje a rungumi transformer bane? Amma dai faɗa min, me suka yi" "miki don in san irin matakin da zan ɗauka a kansu.""" Tana ƙananun kuka ta bashi labarin duk abinda ya faru. "Ɗan murmushi ya saki, amma ko da wasa bai bari murmushi ya bayyana a muryarshi ba ya fara" rarrashinta yana kakabin rashin kyautawar da suka yi mata. """Amma ba komai, sun yi ma kansu. Kiyi zuciya kin ji ki ƙyale musu ɗan su. Abinda ma nan da sati uku" "zan dawo mu duƙa da noma mu ma mu samo namu ɗan. Kila ma a karon farko ƴan'uku za ki haifa min, ai" "na san Matata jaruma ce ko?""" Dariya ta fara ƙyalƙyalawa sannan ta katse wayar bayan ta ce """Ni dai sai da safe. I love you wujiga-wujiga Hubbyna.""" ******** ******* *_BAYAN SHEKARU BIYU_* """Ina ga kamar duk mun gama siyayyar da ya kamata muyi ko Ƙurratul-ayn?""" "Hafiz ya tambayi Kareema cikin kulawa, kyakkyawar babynsu ƴar watanni Shida mai sunan Innaye ana" "kiranta da Najma saɓe a kafaɗarsa. Ita kuma Kareema tana riƙe da hannun Aadil wanda ya girma sosai ya ƙara wayau, idan ma sani mutum yayi ba, sai ayi tsammanin ya shekara biyar a duniya. Ya yi kyau sosai cikin kayan turawa da aka saka masa, kallo ɗaya za ayi mishi a fahimci yaro ɗan gatan iyayensa gaba da" baya. """Eh kamar dai mun gama Nurul-ƙalb! Mu je mu biya Bill ɗin kawai, idan da wani abu da muka manta" "ma ai gobe rana ce. Mu je kawai, tun ɗazu Zuly take kira na wai mai lallen ta kusa gama mata.""" """Ok!""" "Ya amsa a taƙaice, sannan suka nufi gurin biyan kuɗi." Kusan duk inda suka gitta sai sun zama abin kallo a idanun jama'a saboda tsananin haɗuwar da suka yi. "Da ganinsu an ga masoya da suke bala'in son juna, ga ƴaƴayensu guda biyu gwanin ban sha'awa." Cikin ƙanƙanin lokaci Hafiz ya biya duk bill ɗin yaran shagon suka kwasa musu manyan ledojin kayan zuwa gurin motarsa. "'Zulaikha ce ta haihu, tun farkon auren da tayi ɓari sau ɗaya bayan watanni biyar da aurensu, a lokacin" "ita kanta bata san da cikin ba. Allah bai sake ba ta wani rabon ba sai da ta shafe watanni takwas, a hakan ma sai da Innaye tasa aka karɓo mata maganin sanyi da na haihuwa a wani ƙauye can nesa da su. (Masu buƙatar ingantaccen maganin sanyi da na haihuwa ko na cancer su tuntuɓeni ta wannan lambar" 07039080978) "A watan da ta sha maganin cikin hukuncin Allah ta samu ciki, haka ta raini cikin a wahalce cikin kulawa" "da tarairaya daga mijinta Abban Imam, Sarkuwarta Mummy, kakarsu Hajja, Kareema da Hafiz, Innaye, Baffa, yayyenta har Allah yasa ta haihu lafiya. Ta haifi ɗanta namiji ƙato da shi." "Tun da aka yi haihuwar Hafiz ba ya nan, yana can Lagos ma'aikatarsu ta tura shi sai jiya ya dawo," sayayyan kayan barka ne suka zo yi shi da Kareema.' Suna daf da ficewa daga gurin Bintu ta sawo kai cikin Store ɗin. Kallon-kallo aka tsaya yi na wasu daƙiƙu "tsakanin Hafiz da Bintu, saboda shekara ɗaya kenan cif ba ta Nigeria." "'Bayan riƙo da kalmar nan ta Mal bahaushe da ya ce idan so cuta ne, haƙuri magani ne. Ta sha wahala" "ba kaɗan ba duk a ƙoƙarinta na yakice Hafiz daga zuciyarta. Haka ta dinga murgina rayuwar da daɗi babu daɗi cikin godiya ga hukuncin Ubangiji ta cigaba da aikinta, amma da taimakon MD ɗinsu ta samu canjin gurin aiki, saboda ba ta son tana ganin Kareema balle har ta dinga jin ɗacin rabuwa da Hafiz." Sai da aka yi watanni huɗu cif da rabuwarsu wata rana kwatsam ta koma gida daga gurin aiki ta tarar "Hafiz ya kai Aadil hutu gidansu. A wannan ranar ta yi kuka a ɓoye kamar babu gobe, zuciyarta cike da tunanin baya da abubuwan da suka faru a cikinta." Sai daga bisani ta wartsake ta rungume ɗanta tsam tana shaƙar daddaɗan ƙamshin da ke fita a jikinsa. "Daga bisani ta fara ina aka saka ina aka aje da shi zuciyarta cike da jin daɗi, ko kaɗan bata ga alamun wani wahala a jikin ɗanta ba. Sati biyu cif yayi a gidan sannan Hafiz ya aika direba da saƙon jibi zai aika a ɗauko shi. Zuwa jibin kuwa biyu bisa uku na tattalin arzikinta haka ta ƙarar da shi akan sayi banza sayi" "wofi na siyayyar yaron, boot ɗin motar Hafiz cike taf da kayayyakin tsarabar yaron aka mayar da shi gida." "Tun daga sannan, duk sadda yaron suka samu dogon hutu yana aike mata da shi har zuwa sadda suka" "shafe shekara guda cif a cikin wannan rayuwar mai rangwamen daɗi ga Bintu, mai cike da daɗin daɗi ga" "Hafiz, saboda bayan kulawa, tarairaya, nutsuwa, kwanciyar hankali, soyayya, ƙauna da yake samu daga" Kareema ya samu ɗaukaka sosai ako wane fanni na rayuwarsa. Kwatsam! Sunan Bintu ya fito a cikin wasu gungun likitoci guda talatin da gwamnati ta ɗauki nauyinsu "don zuwa yin couse na shekara guda a ƙasar India. Wannan dama da Bintu ta samu shi ya zama sanadiyyar manta baya a gare ta, ta cicciɓa rayuwarta zuwa tudun mun tsira ta fuskanci gaba, a yanzu haka bayan kammala couse ɗin ta dawo ne da mijinta a hannu. Likita ne ɗan'uwanta Dr. Hashim, ya taɓa aure sau ɗaya amma matarsa ta rasu, masifar ƙaunar Bintu yake yi yayinda a ɓangarenta za'a ce babu" yabo babu fallasa. "Tun kafin su dawo Nigeria, iyayen Hashim sun miƙa komai na kayan aure gidansu Bintu, yanzu haka bikin" saura sati biyar da kwanaki biyu. "Lokaci ɗaya Hafiz da Bintu suka yi saurin wayancewa daga kallon da suke ma juna, saboda idanuwan" "Kareema da take tsaye kamar mutum-mutumi tana kallonsu, da wani irin yanayi mai wahalar fassara a fuskarta." """A'a! Mummyn Aadil ku nake gani haka? Ya kuke? Ya bayan rabuwa kuma?""" "Bintu tayi saurin jero maganganun ga Kareema, fuskarta cike taf da dariyar yaƙe. A zuciyarta kuwa yaƙi" take da shaiɗanin da ke neman ɗarso mata wani banzan tunani akan Hafiz daga ganinsa sau ɗaya bayan shekaru biyu da suka shafe basu ƙara haɗuwa ba. """Aunty Bintu ashe kin dawo? Shi ne babu ko labari ai da mun zo miki sannu da zuwa ni da Yaro na.""" Kareema ta faɗa tana dariya. Kafin Bintu ta ce komai Kareema ta sake cewa ga Aadil cikin harshen turanci. """Aadil ka ga Ummee ta dawo? Je ka gaishe ta kayi mata oyoyo.""" Da gudu Aadil ya tafi ya rungume ƙafafun Bintu yana murnar ganinta. Cike da ƙauna ita ma Bintu ta tsuguna daidai tsawon yaron tana biye ma surutunsa. Aadil ɗin ne ma yake faɗa mata ai Auntynshi Zulai ta haifi baby boy ƙatoto. Tsakanin Hafiz da Bintu an rasa wanda zai fara cewa da kowa komai har sai da Kareema ta karɓi makullin motar da ke riƙe a hannunsa bayan ta bashi uzurin za ta buɗe boot a zuba kayayyakin da suka siya. """Dr. Bintu! Hope kin dawo lafiya.""" Hafiz ya karya gwuiwa matsayinsa na namiji ya tambayeta da muryarsa mai cike da kwarjini. Ba ƙaramin namijin ƙoƙari tayi ba gurin danne tsohon mikin da ke taso mata a zuciyarta ta amsa mishi a "mutunce. Sannan ta gaishe shi, ta ƙara da tambayarsa bayan rabuwa." """Lafiya ƙalau. Congratulation.""" "Ya amsa gaisuwar a taƙaice, ya ƙara da yi mata murna." "Amsawa tayi cikin sanyin murya, sannan ta miƙa hannu ta karɓi Najma da ke riƙe a hannunsa tana yi" mata wasa lokaci guda kuma tana tambayar sunanta. "Karima da take zaune a cikin mota tana kallon duk abinda yake faruwa, shiru tayi ƙirjinta na bugawa," zuciyarta na suya saboda kishi. Shaiɗan da iya ƙayata abu kuma sai take ga kamar har wani murmushi na musamman Hafiz da Bintu suke sakar ma juna. Ta samu sauƙin damuwarta ne sanadiyyar addu'o'i da tayi ta ja cikin zuciyarta. Kamar Hafiz ya san halin da Kareema ke ciki sai cewa ya yi """Bari mu wuce, Ƙurratul Ayni na jiranmu a cikin mota. Duk da de waccan weekend ɗin a gida gurinsu" "Umma Aadil ya yi gobe da safe direba zai kawo miki shi ku gaisa, zuwa yamma sai a dawo da shi. Saboda jibi sunan Zulai, za su tafi da wuri.""" """Na gode ƙwarai Daddyn Najma. In sha Allah nima zan leƙa gidan sunan don mu gaisa da su Aunty" "Balira. Allah ya raya.""" """Amin.""" "Ya amsa sannan ya karɓe ƴaƴanshi ya nufi mota, ita kuma ta tsaya tana kallon bayanshi, zuciyarta na" "ƙuna da tafarfasa. Dama ta sani, za'a daɗe bata daina da na sanin kura-kuran da ta aikata har suka janyo rabuwarta da Hafiz ba." Da ƙyar ta iya haɗiye ƙwallar da ya taho mata kafin ta juya da sauri ta shige cikin Mall ɗin. ******** Bubbuga ƙafa ta fara yi a shagwaɓe sannan ta ce """Ni dai gaskiya Aunty Ruwan wankannan ya yi zafi da yawa. Don girman Allah ki surka. Wallahi ni kaɗai" "na san azabar da nake sha idan kika ɗebo tafasasshen ruwan zafin nan a tawul kika danna min a baya.""" "Daƙuwa Aunty Balira tayi mata, ta ƙara da cewa" """Ƙaniyarki Zulai, Wankan jego idan ba'a yi da tafasasshen ruwa ba da me kike so ayi? Ba kya so jikinki" "ya yi ƙarfi ki samu lafiya a gaggauce da juriya fiye da da ne?""" "Shiru tayi, sai kuma ta amsa a hankali" """Ina so mana Aunty. Amma azabar ruwan zafin ne ba sauƙi...""" """Kin san Allah Aunty ki daina biye ma Zuly. Ki gargashe ta da kyau yadda ya kamata, idan ruwan ma ya" "fara sanyi ki ƙwalla min kira in ƙaro tafasasshe. Gaba ɗaya Yaya Kamal ya sangartata kamar ba mace ba.""" "Kareema da take zaune a cikin ɗakin ana yi mata lalle ta tsoma bakinta a cikin zancen da suke yi, tana" maganar tana dariya. Da fuskar tausayi Zulaikha ta ce """Ba komai! Ba komai Aunty Kareema. Na gode. Na san zama na da ke. Kuma wannan maganar da kika" "faɗa kamar a kunnen Abban Imam...""" Da sauri Kareema ta ce """Aaaa ni kar ki ƙulla min jakar tsaba in tafi kaji su tsattsaga.. Ba ruwana. A kanki Abban Imam idanunshi" "rufewa yake yi...""" """Kamar yadda na Yaya Hafiz suke rufewa a kanki ba.""" A tare duk su biyun suka yi dariya. Haka suka ci gaba da hira da raha a tsakaninsu har ruwan ya ɗan sha iska kaɗan sannan aka yi wankan. "Tana fitowa daga bayin ta ji shigowar motar Abban Imam cikin gidan, da saurin gaske ta cire tawul ɗin da" "yake kanta, ta ɗauki babban hijabinta ta saka ta kama hanyar fita daga ɗakin da sauri, bata saurari" Kareema da ke ƙwalla kiran sunanta ba. Cikin mita da mamakin rashin ta idon Zulaikha a fuskar Aunty Balira ta ce """Uhmmm! Ai in dai Zulai ce za kiyi ki gama, ba ta haɗa lokacin mijinta da komai duk da jego take yi. Ni" "da nake gidannan ai ina shan kallo. Shi yasa sati biyu kacal zanyi in tattara komatsaina in koma inda na fito. Ga Hajja nan, da taimakon Mummy sai su ɗora daga inda na tsaya.""" """Ki ƙyale su kin ji Aunty, idan kika yi sati biyun anan, kawai mu wuce gidanmu ki ƙarashe sauran" "kwanakin a can...""" """Taɓɗijan! Ashe kuwa da na yi gudun gara na faɗa zago. Bazan iya da rashin kunyar Hafizu ba, ke dai da" "kunya a idanunki, Hafizu kuwa kunya ta bi can! Shi ya bi nan.""" A kunyace Kareema ta sunkuyar da kanta ƙasa tana dariya. Ita ma Aunty Balira dariya ta yi. "Can kuma sai ta fara jajen mutanen Faƙo masu zuwa suna, har yanzu basu iso ba saboda basu fito gida" da wuri ba. Su Aunty Rakiya sun iso ne daf da kiran sallar magriba. Nan take gidan ya ƙara kaurewa da hayaniya. "Dom ma dai tunda cikin ya tsufa suka koma ɓangarensu na can gidan Mummy, a can ta haihu. Don haka" ba su da matsalar gurin saukar baƙi. ****** "Washe garin suna, yaro ya ci suna Abdulfatah. Taron sunan da ya haɗa gagga-gaggan ƴan gayu abokan" "aikin Abban Imamu da na Mummy. Suna ne aka yi na ƴan gayu, an dafa kalolin abinci sun yi kala goma." "Sannan duk wani abu da za'a ci, a sha, ba daga gidan aka dafa shi ba." Tun da wuri waɗanda aka ba kwangilar dafa abincin suka taho da yaran da za su raba abincin. Duk yawan "mutanen da suka taru a gidannan sunan sun ci, sun sha, sun ture, saboda komai a wadace ake zubowa." Mutanen Faƙo kuwa sai da suka yi ta cizon yatsa saboda yadda suke ganin kiɓi-kiɓi na abinci an ci kaɗan "an barshi, ga guri nesa, balle su ce za suyi guzuri su tafi da shi gida." "Misalin ƙarfe uku na rana Bintu da Aunty Sadiya, Mashkura, da Ummansu suka isa gidan sunan. Nan take" "kallo ya koma sama, saboda yadda Bintu ta haɗu ta haɗe, ta fito a Dr. Bintu sak! Dama in dai gurin gwalli," "kwalliya, ƙwalisa ne in dai aka haɗu da Bintu to a shafa lafiya, ita ɗin ƙarshe ce." "Abinku da ƴan ƙauye da basa rabo da tsegumi, nan take suka fara hum-hum-hum ana ai tsohuwar matar" "Hafizu ce. Sai dai tambarin rashin kirki da aka yi mata a baya yasa bata yi wani kwarjini ba a idanunsu, duk da yadda ta dinga bin su tana gaisar da su cikin girma da mutuntawa." Turamen zannuwa uku masu tsadan gaske da rigunan Baby guda huɗu Bintu ta kaima Zulaikha. Sannan ta kawo wani babban akwati shaƙe da kayan arziki ta damƙa a hannun Aunty Balira cewa ta kai ma Innaye. Duk waɗanda za a ba da sunayensu manne a jikin kayayyakin. Rakiya da Ladidi iyayen riƙo da rashin mantuwa. Ko kaɗan bata wani burge su ba. Sai dai duk yadda suke "ta cin magani suna share Bintu a dole suka saki fuskarsu, saboda yadda take ta musu shisshigi tana jan su da hira da dariyarta, kamar ma bata san suna ɗaure mata fuska ba." "Bintu shigewa cikinsu tayi sosai, kamar ita ɗin ƴar'uwar Zulai ce ta jini. A Canjin kaya kala na bakwai da" Zuly tayi ita Bintun ce tayi mata sassauƙar kwalliya ba Hibba ba. """Bari in ɗan tsara miki fuska mana ƙanwata. Ni ma fa na iya kwalliyar nan, amma abubuwa da yawa a" "yanzu sun sha min kai ba ma na ko samun lokacin yin kwalliya sosai.""" Bintu ta faɗa lokacin da taga Hibba ta shigo da akwatin kayan makeup ɗinta za tayi kwalliya ma Mai jego. "Maganar da tayi yasa Hibba bar mata fagen kwalliyar, kuma cikin hukuncin Allah sai Zuly tayi kyau sosai, kamar duk sauran lokutan da aka mata kwalliyan." "Tun da Bintu ta shiga gidan sunan, Kareema ta zama a ɗarare, sai take jinta kamar ma a muzance." "Saboda irin kyawu da ajin da ya bayyana ƙarara tattare da Bintu, duk da ita ma tana da nata kyawun dai-" "dai ita, amma ita da kanta ta sani wutsiyar raƙumi ta riga ta yi nesa da ƙasa. Haɗin ma ai ba na haɗi bane, baba ma da babansa." Bata san Zuly tana lura da halin da take ciki ba sai da ta damƙi hannunta taja suka shige ɗakin Abban "Imam. Lokaci ɗaya Zulai ta ɗaure fuska, kamar ita ce Yayar Kareema. Da ɓacin rai a muryarta ta ce" """Mene ne kike ta wani ɗari-ɗari kin kasa sakin jiki tun da Bintu ta shigo cikin taron nan? Miye" "matsalarki da ita?""" "Jikin Kareema a sanyaye ta ɗaga idanu ta kalli Zulai, sai ga hawaye shar, zuciyarta cike da wani irin" "raɗaɗin kishi, a gefe guda kuma ga wani tsoro na daban da ta rasa gane ta inda yake ɓuɓɓugowa. Bakinta na rawa ta ce" """Zuly... Tsoro nake ji Wallahi. Ki ga yadda Aunty Bintu ta ƙara komawa wata mace mai aji ta" "musamman fa... Dama ya ya lafiyar giwa bare ta yi hauka? Na shiga uku! Shi yasa auren mijin wata bai ba. Idan Nurul-ƙalb ya ce zai mayar da ita ban san inda...""" Make bakinta da Zulai tayi yasa ta yi shiru tana hawaye. """Wani lokacin dai ke banza ce Aunty Karima. Ni Wallahi kin ma ba ni haushi. Yanzu ke har akwai wata" "mace mai ɗaura ɗankwali da kike fargabar za ta iya ƙwace mijinki a hannunki? Ba'a aure ita aka aure ta? Kar ki sake faɗa min zancen banza wai wani mijin wata. Bayan haka ma, ke kina ganin a irin matsanancin Son da yaya yake miki har akwai wata ƴa mace da za ta sha gabanki a zuciyarsa? Bintun da dai ita ce a yanzu, babu wani abu na musamman da ta canja. Sannan kuma Miji naki ne, a hannunki yake, ki daina ma wani banzan tunanin wai Yaya zai mayar da Bintu ɗakinta, da zai mayar da ita da tuni an wuce gurin." "Ki saki zuciyarki kiyi walwala a cikin mutane...""" Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin da aka fara yi ta waje yasa Zulai ta katse maganar da take yi. Da muryarta ƙasa-ƙasa ta cigaba da cewa. """Saura kuma ki fito in ga kin cigaba da tsangwamar kan ki, ki shiga bayin Abban Imam ki wanke fuska." "Zan turo Hibba ta sake miki kwalliya.""" Tana gama maganar ta fice daga ɗakin ba tare da ta saurari cewar Kareema ba. "Wasu ƙawayen Mummy ne suka shiga gurin mai jego duba ta da baby, ashe shi ne kiran da aka yi mata." "Da ladabi sosai Zulaikha da gaishe su, suka ƙara yi mata barka suka bata kayan barka, sannan suka fice" daga ɗakin. Ba a ɗauki tsawon lokaci ba Kareema ta dawo cikin ƙawayensu da su Mashkura suka cigaba da "warwasawa. Bintu na can cikinsu Aunty Balira suna hira, tun da tazo ko idanun Aadil bata gani ba, yana can tare da Imam da sauran yara suna wasa." "Kareema ta zo fita daga falon Zuly zuwa cikin gida karaf maganar Aunty Balira ya sauka a kunnenta," "maganar da yasa ta rage saurin tafiyar da take yi, don kawai ta ji amsar da zai fito daga bakin wacce aka jefa ma tambayar." """Bintu? Na ce wai ya maganar aure ne? Kar dai ki ce na yi miki shisshigi, amma tsakani da Allah zaman" "hutun dai isa haka. Aure shi ne daraja da cikar mutuntakar ko wace ƴa mace, in dai Allah ya kawo miki" "miji, ki daure kiyi aurenki. Idan kuma kun daidaita da Hafiz ne...""" """Babu maganar daidaitawa Aunty Balira. Zama ya ƙare tsakanina da Daddyn Aadil. Domin a yanzu haka" "saura wata ɗaya ne da ƴan kwanaki a ɗaura min aure.""" "A hankali Kareema ta sauke ajiyar zuciya na samun nutsuwa, sai kuma ta ƙara sauri har ta fice daga falon." Wani kwanciyar hankali na musamman na sauka a duk sassan jikinta. """Too ma sha Allah! Allah ya sanya alkhairi, yasa ayi da mu.""" Rakiya da Ladidi suka faɗi haka da fara'a a fuskarsu. Dama can su ba sa wani ƙaunar dawowar Bintu "cikinsu, duk da dai ta shiryu, taje can ta ƙarata da shiryuwarta." Ita kuwa Aunty Balira a sanyaye tayi fatan alkhairi. Allah ya sani duk da Kareema bata rage su da komai "ba, ta so ace Hafiz ya yi haƙuri sun daidaita da Bintu. Ko don Aadil, amma inaa... Sam-sam Hafiz ya tsani ma a dinga tayar mishi da maganar wata tsohuwar matarshi wai ita Bintu." Sai gaf da Magriba Bintu da Tawagarta suka bar gidan sunan. Sun rabu suna raha a tsakaninsu. Daɗai wani abu na muni ko rashin fahimta bai taɓa shiga tsakaninsu ba. "Anyi taron suna lafiya, an tashi lafiya. Mai jego da Jaririnta sun tashi da rikitiɓar arziki mai yawan gaske." Sai fatan ayi wanka lafiya a gama lafiya Zulaikha ta Abban Imam. *_Alhamdulillah. Komai yayi farko zai yi ƙarshe. Anan na kawo ƙarshen labarin RANAR NAKA SAI NAKA "DAƊIN ZAMA SAI BARE. Kuskuren da ke ciki ina roƙon Allah ya yafe min. Alkhairan da ke ciki Allah yasa mu amfana gaba ɗaya ya haɗa mu a cikin ladan. Ina godiya gare ku ƴan'uwana masu karatun wannan littafi tun daga farko har ƙarshe. Sunayenku da yawa, bazan iya ambatanku ɗaya bayan ɗaya" "ba Na gode, na gode. Allah ya bar ƙauna da zumunci. Sai mun haɗu a Cigaban labarin" "ƘASAITACCIYAR MACE... In sha Allah Fareeda Abdallah ce, domin magana da ni kai tsaye a tuntuɓeni ta wannan lambar 07039080978_*"