Murfin Jallo Dan Uwa,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,, 1 1️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Hayaniya irin na babban gida shine ya tayar da mama daga barcin data dan samu ta runtsa na safe ,bayan idar da zikirin safe data sabayi a duk safiya . Wanan dabi,an kusan ya zama mata jiki akullum idan ta idar da sallah zata zauna tayi zikiri har sai rana ya foto sosai kafin ta dan kwanta ta ba ido hakkinsa. Daga inda take kwance din tana jin yadda yaran gidan nasu da manya ke kara,kaina a tsakar gidan kusan hayaniyar babban gidan nasune ma ya tayar da ita a lokacin. Salati tayi tana dagawa a kasa inda take kwance saman sallayanta ta dan jima a zaune don gargadin likitoci dake fadin. Idan ka tashi tsaye barci kada kayi saurin mikewa tsaye a lokacin don min a daidai lokacin jinin dake kwaranya a zuciya bata gama sauka ba yana yuyuwa ka mike hakan ya ja maka matsala a rayuwanka a cewarsu. Ana son Sai ka dan bada yan mintuna a zaune kafin ka mike tsaye don kariya ga lafiyan ka a lokacin wanan dokan da mama taji illanshi. Baga yaro ba baga babba ba dokace da likitoci suka bayar don gujewa fitinan lafiyan jikin bawa daka iya haifarwa mutum ciwarwutan zamanin nan . Hakan yasa wanan boyar Allah ta rike wanan akidan ta dan bada lokaci a wajen zaune daidai lokacin da aka turo kofan dakin nata tare da daga labulen dakin aka shigo ciki da sallama muryan danta na ukkune yake sallaman tare da fadin ashema baki tashi ba mama ?. Daidai lokacin ta dago kai tana sauke mai kallo tare da fadin na tashi Habu badai har rana tayi hakaba kuna shirin fita ? Rana tayi mama yanzu kusan karfe takwas da rabi ake nema zuwa nayi muyi sallama don yau balaguro zamuyi har wani kasan ba lalai bane mu dawo a yau ko gobe saidai kun ganmu dai zance. Kallon mamaki take binsa dashi tana fadin haba Habu wai sau nawa zan maka fadan irin haka don Allah ? Mutum zaiyi tafiya mai nisa irin haka bazai fada a gida ai masa addua ba ka raina da dan adduan da muke binku dashi ko yaushe ke nan ? Zaune yakai saman kujeran dake gefe ciki da kaya yayiwa kansa wajen zama a gefe yana fadin mama muko muka san amfanin adduan ku akan mu don duk abinda muka dafa muna ganin alheri a cikinsa. Murmushi matar tayi tana fadin yanzu dai ina kuka dosa Habu ko kudun zaku kuma yau dinma ? a,a mama wajajen Camero muka dosa wajen wani taron gargajiya da za,ayi a can kinsan aikin mu ya kumshi hakan sai munje don dauko rahoto. Shine zamu dauko rahoto akai da zamu yadawa al,umma su gani ikon Allah yanzu habu har camaro zaka hankalinka kuma a kwance ? Batare daka sanar da mu ba sai yanzu ka shirya tafiya kazo kana fada min Habu ? Wai meyasa kudai maza baku mayar da tafiya a bakin komai bane wai ? Kako san nisan dake tsakanin zaria zuwa camero ? camero din nan da kake ji kawai a baki tafiyace mai nisa fa daga nan . Ya amsa da fadin kuma tafiyan mota zamuyi mama saboda kayan aikin mu dole mubi mota zuwa wajen taron wanan yasa zamu tashi tun yau ai a dai muna addua muje lafiya mu dawo lafiya. Insha Allahu lafiya zakuje ku dawo lafiya Abubakar alherin dake cikinsa ubangiji Allah ya sadaku dashi sherin dake cikin tafiyan kuma Allah ya nisantashi daku alfarman Annabi da alkur,ani ya amsa da amin cikin jin dadin adduan mahaifiyar tasu a gareshi. Sallamu Alaikum ga nakiyar baby muryan wata dattijuwa dauke da kwala a kai data shigo babban gidan Alh talle din ta tsaya daga kofane ya karade gaba daya gidan. Daga can dakin mama din inda take bankwana da danta taji muryan wanan matar cikin mamaki take sake zancen da sukeyi da dan nata. Cikin mamaki take fadin nakiya kuma da safen nan ? Har yakai a fara tallan nakiya gida gida haka me mutane ke nema da bindan kudine wai nakiya dai a sanina sai bukin aure ake nakiya don ango. Murmushi Abubakar yayi yana fadin barin inje mama kada in makara abokan tafiyana suna kirana tun dazun. Nan uwar ta dago tana fadin kaje kuyi sallama dasu hjy kafin ka tafi bana son irin korafin su na baka sallamesu ba din nan. Insha Allahu ya fada yana mikewa tsaye barin dubasu in dawo mama ya fada yana mai barin dakin cikin kuzarinshi irin ta namiji mai jin lokacinsa. Dakin hjy babba ya nufa ya gaida ita tare da fada fada mata inda suka dosa a ranan ba yabo ba fallasa tayi mai Allah ya kiyayye hanya. Ya fito yana kokarin shiga wajen hjy Nana ya hangosu gaban wanan matan dake faman kwada sallama suna leken wani abu a cikin kwalan da matar ta shigo dashi. Hakan yasa ya doshi wajen saura kiris ya karasa yaga yara da manya sun watse wasu harda faduwa kasa don tsoro ga ihun da sukeyi suna neman inda zasu shiga saboda firgici . Wanan ihun ya dakatar dashi yaja ya tsaya yana binsu da kallo fuska daure kafin ya mayar da hankalinshi wajen matar da sai murmushi take a fuskanta. Lafiya boyar Allah tace nakiyar babyce na kawo masu gashi kuma sun watse sun barni dashi . Kallon matar yayi cikin mamaki murmushin yagani a fuskanta yasa ya karasa wajen yana kokarin kallon kwallan dake gabata bude. Ido ya runtse lokaci guda don wani katon maciji kalan da sai a cikin film yake ganinsa. Ya nade a waje daya ya cika kwallan har baki sai kansa daya dora a saman jikinshi yana kiu kiu da idanuwansa dake bude. ALLAHU LAH ILLAHA ILLAH ANTA SUBBAHANAKA INNI KUNTU MINAL ZULLUMIN ya ambata a fili . Muryan matar yaji tana fadin kada kaji tsoro kai namijine kuma sadauki ba asan maza da razana ba sadauki. Daga can bayanshi yaji muryan dayan kanwarsa tana fadin yaya Habu kada kaje kusa don Allah macijene a cikin kwallan nan babba. Jin sunansa da aka ambata yasa matar fadin Garba sadauki garba gagare kai sadaukine ko a fagen fama kafiran makka sun buga sun barka sarki rikon amana mai alkawari ya cika har bayan rai,,,,,,,,,, Dubu biyu ya zaro a cikin aljihunsa ya mikawa matar takai gwiwa biyu tana zabga mashi addua da neman tsarin ubangiji gaba da bayanshi. Ya juya da niyar komawa dakin muryan hjy Nana yaji tana fadin boyar Allah aida kin fada kwai a miko maki abinda Allah ya hore ki tafi . Yayin da matar tacigaba da fadin da yardan Allah kayi gaba saudaki sara da sassaka bai taba cima a rayuwa insha Allahu sai dai makiya su buga su barka. Mama data samu ta mike don ganin abinda ke faruwa a wajen taji yadda matar kewa danta Abubakar addu,a ta fahinci kudine ya bata yasa ta dauki dari biyu ta fita ta mikawa matar nan ta dasa sabon addua kuma tanawa mama jam,i ga duk zurianta. Ta dauki kwallan ta tafi don taga sauran iyalin gidan basu da niyar fitowa balle su sallameta saida sukaji fitanta suka fito suna mayar da ba,asin zancen a tsakaninsu kowa na fadan abinda yagani a cikin kwallan hankali tashe. Mama dai bata gani ba amma ta mikawa matar sadaka don tasan wanan matar banza ba zai fito da ita gidanta haka basai neman rufin asiri da taga wanan hanyarce mai sauki a gareta. Zancen mai nakiyar ya hana su mayar da hankalinsu ga Habu da zaiyi tafiya don da tsegumin tafiyan shi za,a fara sai Allah ya fabeshi a ranan dan shigowan wanan matar mai yawo da macijin maisa a cikin kwala tana cewa ga Nakiyar baby. Idan kuma tasan sunan wani gida a gidan zata ambaci sunan maishi tace ga nakiyar wani sai wanan abin tashin hankalin da mamaki ya tsaya masu a rai har mahaifiyarshi ta fito rakiyarshi da iya kofa ta tsaya tanawa danta fatan Narsara da Allah ya tsare ya kare wamda sai lokacin hankalin hjy babba ya dawo garesu. Daga kofanta take tambayan yau Habu kuma ina za a haka tunda safe ni yazo muna gaisawa hankalina yana gun wanan bakar matar data tayar muna da hankali da safen nan. Daga kofa mama din take bata amsa da camero suka nufa lokaci guda matan da yara dake wajen suka amsa da fadin camero kuma ? Wasu na Allah ya tsare wasu kuma sunyi gun suna zancen zuci inda sabo ta saba da hakan zaman gidan yawane duk yadda kayi sai wani yaga bakai masa daidai ba irin wanan zaman. Ya fito daga cikin gidan yana kallon agogon hannunsa saboda ymshi kansa yasan da ya makara saidai dole su jirashi sai yaje wajen aiki inda zasu hadu. Kamar daga sama yayi ido biyu da wanan matar ta sauke kwallan macijinta sai faman murmushi take zabga mai a fuskanta kai ya kawar da sauri yana barin kallonta. Habu bakari don ka na tsaya nan duk da dai shigan tsugula zan ma tunda na kula sauri kakeyi ka kula da addua don kai din kana tare da tsarin Allah ga kuma tarin mahassada a tare dakai. Nagode mama ya fada yana kokarin wuce ya sake jin muryanta tana fadin ka kula sosai don alherin ka da nasara yana inda ka dosa . Kudi dai wanan matar keso gareshi ya nasa hakan a zuciyarshi ya sake cusa hannu a aljihu yana dauko dubu daya ya mika mata. Murmushi tayi tana fadin wanda kabani dakai da mahaifiyarka nagode maku Sarkin da akaiwa ya sani. Naso magana da mahaifiyar ka saidai gidan ku gidan yawane dana fada mata wani magana amma ba laifi idan tana son ji ko kai ina can gidan hjy indo mai kosai a nan na sauka. Allah ya tsare ya kare ya amsa da amin yana aje mata dubu dayan da taki karba a hannunta saman kwallan yasa kai ya tafi don ya dauka zancen shirme take masa a lokacin don kawai ta yaudareshi yasan halin mutanen yau da yaudara. [5/19, 21:37] Buhainat: Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1f MARFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,, 2️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Tafiyace ta mota da zai dauki dogon zango haka suka fara tafiya tun suna dan hira a tsakaninsu har abin yakai da anyi shiru kowa na tunane a kansan zuciyanshi. Dosan mabila da sukayine yasa su fara bayana mamakinsu a fili kowa na fadan albarkacin bakinsa ga albarkan kasan yankin mabila din. Abin sha,awane da daukan hankali ga bakon zuwa wajen harma wanda ya saba sai yabi dabbobinsu da kallon shawa yadda suke daban da wanda aka saba gani. Lokacin da suka zo wajen wanan hawan kusan kowansu hannushi a gaba yake yana ganin kamar ba zasu iya hawan nan ba don yadda sukaga wajen. Sai gashi cikin yardan ubangiji sun hau lafiya sun gangara kuma lafiya a sannu suka fara barin cikin nahiyar kasan Najeriya zuwa cikin kasan camero dake da iyaka da Nageria. Abin sha,awa don basai ka tambaya ba alakansu da addinin musulunci don har yan wani addinin shigarsu shigen na musulmaine su a kasan sukeyi. Tafiya dai tayi tafiya don shi driver yasan yankin da za ayi wanan taron wanan yasa basu damu da yada zango ba sai tsatsaya ko ina ba. Saidai idan lokacin sallah ya riskesu sai kuma shan man a hanya sukama hanya amma sam basu tsaya kwana a hanya basu kamar yadda wasu da yawa suka yada zango. Hakan yasa sukai wa wanan yankin shigar safiya duk da alokacin wurin sha dayan ranane a lokacin duk wani mai lalura ya fito a lokacin. Sai wanda ke gida baida abinyi sannu a hankali yake bin garin da kallo daga bayan motan yayin da driver ke aikin kutsawa acikin garin zuwa babban filin da za,ayi taron gwajin na gargajiyan shekara. Suna wanan al,adanne bayan ko wani shekara goma idan ya shige in rayuwa ya kewayo ake haduwa wajen wanan shagalin nuna amfanin gona da sauran al,adun gargajiya. Abaya kasan Nageria tana irin bukukuwan nan na nuna amfanin gona da sauran al,adun gargajiya wanda yake kawo dankon zumunci da habbaka sana,an mutane da cigaban kasuwanci harma da zumunci a tsakanin yan garuruwa na nisa dana kusa. Sai a yanzune da abubuwan kasan suka tabarbare wanan al,adan ya mutu mutus a arewancin Nageriaa sai dan abinda ba,a rasa ba dai kawai da akeyi yanzu. Sai dai al,adan kamun kifi da wasan ruwa da sauran al,adun har yau har gobe mutanen kasan kebbi a garin Argungu kabawan asali basu daina hakan basu a wajensu. Don suna raya garinsu basu bar al,adansu da suka gada tun kakanin farko ba da kakani baya, don manyansu sun rike da wanan abin sosai tare da kawo cigaban nahiyar tasu ta Argungu din har gobe. Wanan kadai za ace an saurayi a yanzu cikin arewancin Najeriya da har wasu kashe duniya suke zuwa kallon irin al,adunmu na hausawa tare da fasahan malam bahaushe dake tafiya da al,adanmu na Nageria. Bayan shishi din a gaskiya yana da wuya ace an saura wanan habbaka al,adan da sauran kasashen africa dake kewayen nageria irin su Niger, ghana, camero kwatano da benin da sauransu su basu yarda sun bar al,adunsu ba kamar mu. Zama ya gyara daga bayan motan yana sauraren Sahabi mai daukan photonsu dake wanan sharfin akan nahiyar ta arewacin Nageria da yanzu abubuwa suke ta kara lalacewa a kasan saboda sanyi da rashin sanin ciwon kan malam bahaushe a yanzu. Ai baka sani ba malam Sahabi zance dakai wanan abin tun lokacin da aka ragewa gidan Redio Kaduna karfi da power abubuwan da dama duk suka shiga tabarbaremuna kai in maka na mahaukaci kamar anyi wanan abin da manuface zance dakai. Don wallahi ba karamin koma baya haka ya mayar da Arewa baya akayi ba da hakan hakan ya taba kima da mutuncin arewa sosai a kasan nan. Dama sune masu haskawa suna yadawa amma tunda wanan ya faru sai sannu a hankali kaga abubuwan sun fara ci baya. Hakane kwarai malam ibrahim maganan ka dutse wallahi wanan abin ya taba arewa sosai don kashe wanan gidan redio da sauran waje irin masakan kaduna su gidan kada da wajen fata wanan abin ya kawo muna cibaya sosai a arewa yanzu don da suna raye matasa zasu samu aikin yi a kasa. Salatin Abubakar ne daga bayan motan ya dawo da hankalin driver ya maida hankalinshi sosai ga a saman dan wani tsukaken haya da suka biyo inda wasu yan mata ke gara amalanken shanu. Wanda saura kiris su gwauro da juna Allah dai ya gyara ya takaita masu wahala dole sukaja burki suka tsaya suna maida numfashi. Malam ibrahim ne ya soma fitowa daga cikin motar yana fadin kaga min almuran yarinya kawai Allah ya kawomu lafiya saida mukaga mun shigo gari muna murna zaki ja muna tsiya. Allah dai ya gyara malam ibrahim barta ta tafi kawai itama kauyancine bata sanda mota a bayanta ba sun dauka sai masu kafa kawai suke tafe a hanyar. A daidai lokacin da hakan ya faru uwa mai kulawa da yawan addu,a ga yayanta takanji wani yanayi na daban aduk lokacin da wani mumunan abu zai samu danta. Irin wanan yanayin ne ya ziyarci mama a lokacin sai ta shiga maimaita innalillahi a kasan zuciyanta da sauran addu,oin da zasu aikawa yayan ta dake cikin duniya dama wa yanda ke kusa da ita kariya. Kasa hankalinta gida biyu tayi tana tunanen Abubakar ko Jafar mai yawan tafiye tafiye don shi ko yaushe a hanya yake dan kasuwane bai tsaya ga aikin gwaunati ba ya aje ya soma kasuwanci da yake ganin yafi mai aikin gwaunati a rayuwansa. Alhamdullahi kuma an samu cigaba sosai a wanan harkan da yanzu har yakai lamarinsa ya fara tsone idon makiya. Su ukkune diyanta maza da Allah ya bata da marigayi din sai mata ukku shidda ke nan matan biyu kananane koda mahaifisu ya kwanta dama autar ta ko yayeta batayi ba a lokacin. Wanan yanayin daya bakunceta yasa ta fita da sauri ta yafa hijjab dinta dauke da kwalin sugar a hannunta wanda ta saya a cikin hijjab dinta. Kofan gida ta nufa akwai tsangaya gaba dasu kadan can takai a rabawa yara sadaka shi kuma malam ta bashi naira dubu sadaka. Tun kan tayi nisa take jin an fara raba sadakan sugar tana tafe da dan saurin don ba fita sukeyi haka ba don wai mijinsu ya rasu suna cikin gida ko yaushe zakice mijin nasu yana rayene. Don komai da akeyi gidan ba a fasa ba don ko wani daki na gidan yayansu suna rike da uwayensu da kannensu da wa yanda basuyi aure ba. Rayuwan gidan marigayi Alh Sanda rayuwace ta ba yabo ba fallasa ga iyalinsa daya bari duniya don ko yabar masu abinda zasu duba kansu ko bayanshi. Daidai wadata gwargwadon hali dai ba cancan ba kowansu ya samu kaso daga abinda marigayin fitacen dan kasuwan tsohon yabari. Wanda bayan rasuwansa duk kokarinsa da yake raye wajen ganin ya tsaya ya hada kan iyalinsa koda bayansa ba wani matsala ko barakan rashin hadin kai da zai biyo bayan hakan . Sai gashi a karshe bayan Allah ya karbi rayuwansa an samu dan matsala a tsakani iyalin nasa saidai ankai zuciya nesa da wasu bangare sukayi don kawai a zauna lafiya. Haka din ne kuwa ya biyo baya a yanzu masu zaman hakkuri sunayi yan bamu damu da gado ba ko dashi ko babu muna tsaye da kafafun mu. Irin bangaren dakin mama ke nan dake da yara kana a cikin gida don ita Allah bai bata haihuwa da wuri ba har mata biyu sukazo a bayan ta sukai ta haifo yayansu sai can kwatsam ubangiji ya azurta da samun ciki. Dama kamar camfi haka zancen yake kuma ga duk matar da bata haihuwa zakiga ubangiji ya azurta hannunta da arziki duk sana,an data dafa zaiyi albarka sosai a rayuwanta. Saidai da zaran mace ta soma haihuwane zakiga arzika ta ya soma jayewa sannu hankali ya koma ga yaya kuma wanan abin kamar wani camfi haka yake idan mutum ya duba. Haka har in Allah bai azurta ta da haihuwan ba zakiga mace komai ta dafa da sunan neman kudi abin nan zaiyi albarka sosai a rayuwanta. Anan dai kamar wani baiwane ko hikima na ubangiji daya barwa kansa sani akan hakan saidai kiga mace ba haihuwa tanata wahala da yan uwa bata gajiya da hakan. Irin wanan rayuwan mama Dubu tayi da farko a rayuwan zamanta gidan mijin nasu abaya tana da abin hannunta sosai datake juyawa wanda har yakai ta mallaki wani fili babba a lokacin . Saidai ta boye hakan ga yan uwan zamanta tabar wanan tsakaninta da dan uwanta da yai mata jagora a lokacin har ta mallaki wanan filin a wani sabon unguwa da gwaunati ke yankawa mutane filin. Wanan dan uwan nata shine ya karfafa mata ta soma gina da sunan saita bada haya inda taja daku part part har hudu a gidan saidai Allah bai nufi ta karasa ba Allah ya karbi ran mijin nasu inda ya barta da yara kanana tare da ita. Sai bayan rasuwan mijin nasu da son kai ya shigo cikin rabon gadon sune manya dake da diya masu girma da kuma yan uwa dake fada aji suka shiga suka fita aka tauyewa marasa galihu hakkinsu. Dan abinda ta samu ita da yaranta shine suka sayar ta karasa gina wanan gidan nata data soma gina sai kuma hakan ya dawo ya tsonewa abokan zamanta idanu daga baya. Wanan ya kara ja mata tsana da tsangwama daga ita har yaranta saidai duk da wanan mama Dubu bata yarda ta bargidan mijinsu wanda ba a kai ga rabashi ba har lokacin tana zaune ciki har yanzu a part dinta anan take rayuwanta da yaranta kanana da basuyi aure ba. Bayan ta dawo daga kai sadakan hayaniyan yan cikin gidan ne ya tareta tunda ta doso gidan hakan baisa ta tsaya kula mai sukewa hayaniya ba don indai da sabo ta saba da hakan ai. Wayanta dake makale a caji ne ya ta samu ya kara ta dauka muryan Habu dintane taji yana sheda masu saukansu lafiya tare da mata bayanin irin nisan tafiyan da sukasha a hanya. Murmushi tayi tana fadin a godewa Allah daya kaddara saukanku lafiya Habu tunda ankai lafiya ai Alhamdullahi. Sukai sallama don sahabi ya shiga nema masu abinda zasu dan samu suci a wajen shi kuma lokacin ya shiga masallaci ya yayi sallah ya fito shine ya nemi mahaifiyar tasu . Akwai sabo da shakuwa sosai tsakanin mama Dubu da yaranta ta koyar dasu shakuwa da ita irin ko wani hali suke din nan ko a inane kuma zasu kira mama su sheda mata halinda suke ciki din. Suna gama wayan ya sauke ajiyan zuciya tare da shafo fuskansa yana bin garin da kallo wanda yake kallonsa tankar a Nageria yake bawai kasan waje ba. Komai nasu rayuwan da komai zaka iya kirasu da yan Nageria don hatta shigan suturunsu iri dayane da mutanen Nageria . Mazan shaddane ko yadi ajikinsu da kalan dinki kuma iri daya dana yan Nageria saidai ya fahinci suma suna da yawan kabilu don yanayin shigar tasu daya sha bambam . Ya fahinci akwai masu siffan larabawa a yanayin shigarsu haka kuma a take wajen ya fahinci bambamcin dake akwai da wa yanda basa sallah a cikinsu. Mota ya bude ya zauna yana dakon abokan tafiyanshi da sukayi tattaki don duba abinda zasu dan iyaci a wajen don suna son su fara haka na,uransu da zai watsowa al,umman duniya shirin kai tsaye. Ido ya dan lumshe a cikin gajiyan dake dibansa don ba abinda yake nema a yanzu sai inda zai dan saka hakarkarinsa ya huta duk da yasan hakan yana da wuya. Inda ka dosa Habu alherin ka yana wajen muryan boyar Allah nance ta safiyan jiya da yabaro kofan gidansu da kwallan maciji yaji ya ziyarceshi a karo na biyu ke nan tun bayan barinsu gida zuwa nan . Don ko acikin mota yayi wanan tunanen inda ya zabura ya daga cikin dan firgita dajin muryanta kamar a gefenshi take zaune. Me wanan matar take nufi da zancen haka din don sai a lokacin ya tsaya yana nazari a kan wanan matar mai yawan murmushi da fara,a a fuskanta. Kana da tarin mahassada da makiya ka kula da addua da sadaka a rayuwanka inda ka dosa alherinka na wajen zancenta ya dawo mai karara a zuciyarshi. Raba kanka da irin mutanen nan masu neman abincine kawai ba wani abuba kadama ka bari zancenta ya zauna a zuciyanka. Wani sashe na zuciyarshi ya gargadeshi da hakan lokaci guda tsuki yaja yana mayar da kanshi saman kujera zubur ya mike zaune don karan gugan motar tasu da yaji anayi ya duba . Wata bakar yarinya daba zata wuce shekara takwas zuwa tara ba haka ya gani tana zoza hannunta jikin motar alaman dai abin ya bata sha,awa har takai hannunta tana wasa da kuran da motar ta kwaso a hanya. Ido ya kurawa yarinyar ya kasa magana data jaye sai binta kawai da yake da kallo gata bakace amma kuma kyakyawan gaske. Han din boniyo ke maria ki jaye wajen nan kada ki daukowa mutane magana ke kadaice yarinya a wajen kowa bai kai hannunsa ba sai ke ? Addah barin taba na koma naba da labari a ruggan mu naga motan tv har na taba da hannuna da sauri yar uwar tazo ta jaye yarinyar tana dangwarar mata kai cikin jin haushi da takaicinta. Yare ta soma cikin fada fada har lokacin tana kai hannu tana dangwaranta kan ta taba mota zata ja masu matsala suna zaune kalau. Baisan lokacin daya bude baki yace da ita barta mana ki daina dukkanta hakana jin hausanshi yasa yar matashiyar budurwan daga kai ta kalleshi kamar zatayi magana sai kuma ta fisgi hannun yarinyar sukai gaba . Binsu yayi da kallo kawai daidai lokacin daya daga cikin abokan tafiyansa ya dawo yana fadin oga akwai matsalan abinci fa a wajen nan. Son mun duba gaskiya abincin nan sai a hankali wallahi saidai fura kan da nono wanan gaskiya ko kamfani za a bude a nan albarka. Baida damuwa ibrahim akwai dan abinda na riko gudun haka ban manta da rafiyan mu zuwa calabar ba ai. Ku karya mu soma aiki kada lokaci ya kure yana fadin haka ya mike zuwa bayan dogon motan nasu da suka loda kaya ya bude ya shiga ciki. Wani jakka da kula ya jawo ya bude bread ne da cake a cikin jakkan sai wani leda dake cike da kayan cima na gwangwani ya debo ya fito daga cikin motar ya nufi dayan motan da yan uwan nasa ke ciki suna hira mikawa kowa yayi suka dauki murna da mashi godiya sai sahabine ke fadin. Kai Habu habu yaushe kayi wanan dabaran haka bamu sani ba murmushi yayi kawai ya nemi waje ya zauna ya bude kifin gwangwanin ya soma ci da bread . Daga kan da zaiyi wanan yarinyar dai ta dazun ya hango daga nesa ta zuba masu ido tana kallonsu cikin shagala tana magana da wata ta kusa da ita. A zatonshi abinda yake ci take kallo sai yaga ba haka ba motar dai tasu take kallo cikin mamaki don yadda take gwada tukin mota da hannunta cikin yanayin wasa da tukin mota. Dago kai yayi suka hada ido yayi mata alaman tazo ta karba ba bata lokaci tazo da saurinta ya mika mata bread din da kifin daya soma ci ta juya da sauri ba alaman tsayawa godiya a gareta ta nufi hanyar da sukabi dazun da yar uwarta. Goran ruwa ya jawo ya soma dauraye hannayesa yana dan yarfarwa kafin ya bude mota yana fito da na,uran daukan rohoto ya soma saitawa yadda zasu samu service a wajen taron ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1f MARFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,, 3️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Baiwa da albarka yana ga yayan baiwa da Allah yasawashi yai masu arzikin duniya da lahira saidai yana da wuya mu yan adam mu gane hakan da sauri . Ko wani mahaluki yana da kalan tasa baiwan arziki da Allah yai mai sai mai natsuwa da kula zai gane hakan mama Duba ta yarda da hakan akan diyanta sun taso da baiwansu saidai rashin hayaniyansu ya boye wanan baiwan da Allah yai masu. Yana da kyau uwa tasaka hope akan yayanta ta zamo mai kawar da ido da son nuna kaunar yayaa fili irin yadda wasu uwayen na yanzu keyi. Yana da kyau nuna kaunar amma idan kun kebe da yaran don nunawan a fili yana kai idon mahassada su illanta maki yara ko da bada mugun nufi ba kuwa don wani nasa baiwa a hassada yafi aiki wani ko daya furta ba daidai ba ga mutum sai hakan ya tabbata akansa din. Ansan ko wace uwa tana kaunan danta manya sunce badon kaza bata son danta bane take takashi sai don ya kula da duniya. Wanan akidar ta mama Dubu shine ta shammaci mutane ta kawar da kanta gun yayanta tun suna kanana take turasu koyon sana,a basu zama gida ana nuna masu kauna ko so da gata da akewa yaran yanzu ana kashe masu zuciya daga boko sai boko ko islamiya sai anyi wa yaro jan ido zai tafi islamiya din. A bangaren mama Dubu wanan tsare yake yaro zai tafi boko daya dawo yaci abinci zai sauya tufafi zuwa kayan aiki ya fita wurin sana,anshi hudu nayi dole ka dawo daukan karatun Allah wanan kai,dace a wajenta don dokan data sakawa yaran nata ke nan a gidan. Yana da wuya ka kyala ido da rana kaga dan mama dubu a gida yana shawagi haka kwana bibiyu dan uwanta zai ziyarci wurin aikin yaran yagano mata halinda yayan nata suke ciki. Yayin da ita kuma takan ware lokaci da yayan nata da dare suna hira tana jin shakuwar kowansu na gyara ta gyara masu maikyau kuma ta kara dorasu a hanya madaidaiciya akai goma zasu watsa zuwa neman wajen kwanciya zata kashe kallo cikon hikima da nisa tana fada masu akwai boko da safe ga zuwa wajen aiki gara ka kwanta da wuri ka samu natsuwa yafi zaman wanan kallon . A cikin irin hakan tasan weak point din dukkan diyanta kuma tana tsaye a kansu idan suna dakin nan zaki dauka yaya da kannentane suke hira a tsakaninsu. Yar uwa mai karatu idan Allah ya halicceki gidan gadu ma,ana gidan dake da iyali fiye da daya mata biyu zuwa ukku ko hudu zaki fahinci abinda nake son maki bayani a nan. Zama a irin gidajen nan zamane mai kama da zaman haya idon kowa na akan danuwa wani bai kaunan wani da karuwa ko cigaba. Amma a zahiri zamane zakiga anayi a fili kamar ana kaunan mutum da ciganbanshi sai a badili abin ba haka yake ba yadda ake nunawa a zahirance. Mama Dubu ta fahinci haka ta dalilin tsaikon haihuwan da tayi ta fahinci yadda abubuwan suke tafiya a tsakanin abokan zaman nata ta fahinci wanan akidar sosai ga yayansu. Za anunawa dakin ana kaunarsa a gabanki amma a bayan ki kamar Allah Allah akeyi yayi wanin abin magana da kowa zai tofa albarkacin bakinsa a kai gidan yawa kenan . Irin wanda iyayyen mu ke tara mata fiye da daya zuwa hudu ko wace mace da kalan tarbiyan da zataba yayanta ko wani daki zakiga shige dabiansu gudane dama hausawa sunce Nono alkalin da. Don kowani da irin tarbiyan da uwarsa ta bashi zai taso a cikinsa kusan haka wanan abin yake idan ka bibiya mafi yawa suna tasowane bisa ga irin jajircewan uwa a garesu wanan ke nan. Mama Dubu yau ta tashi da zuman zuwa gidansu idan nace gidansu ba wai ina nufin gidan iyayyenta bane a,a gidan da suka gadane ita da yayanta data haifa . Gidan da suka saida gadonsu suka hada da na wajenta data soma gidana suka mallaki wanan din da yanzu yaya Jafar yake rayuwa a cikinsa shida mahaifiyar mama Dubu da suke kira da Iya mai mai. Iya ita ta haifi mama dubu da kawu dauda sai mama dije dake aure a kaduna unguwar sarki sune Allah ya bar mata a raye amma a baya iya ta haihu basu tsayawa sai ukun nan suka tsaya raye. Itama iya suna da dan nasu rufin asiri daidai gwargwado saidai ba can can ba auren yaya jafar da zai tare a gidansa saboda girman gidan sukai shawara da iya ta dawo nan da zama tunda akwai wadattacen waje a gidan wanan dalilin yasa ta dawo gidan don ta zauna dashi. Ance a wajen aurensu babban kawarta da tayiwa amaryanshi kawance tunda ta kyala ido taga yaya Jafar ta daga hankalinta da ita taga miji . Don bai dace ace wanan hadaden guyen dan bokon irin da take mafalkin aure shine mijin kawarta da take kamar bagidajiya da ita dai ya dace kuma shi take so . Ita din yar kadunace don a kuduna iyayyenta suke da zama yayin da ita kuma uwar gidannasa Asmau mutumiyar Gwambe ce amma mazauna garin zaria aikine ya kawo mahaifinta zaria har yai ginan kansa zama ya kamasu a garin zaria. Da farko ance shi yaya Jafar din baya son Nusaiba don yarinyar da ba tsarinsa ba saidai kamar abin sihiri kuma ya dan soma kulata har abu yai karfi a tsakanisu ta shawo kansa sai zancen aure. Wata shidene tsakanin aurensa da Asmau dashi da kuma ita a lokacin zancen aurensa da Saiba kamar yadda nickname dinta yake a wajen kawayenta shi kansa mijin haka yake kiranta da wanan sunan sai ba. Lokacin farkon komawansa Lagos da harkan business dinsa ne don ya fahinci can akwai harkokin da zai iya wanda zai hada da nan arewa. Sai sana,anshi ya karbu sosai dan kudi sun fara shigo masa sosai a lokacin don haka bai samu matsalan komai ba don bai bukatan taimako a wajen wani. Haka akasha wanan bukin amare biyu a kusan lokaci guda duk ko da tashin hankalin da uwargida Asmau tayi kan ba zata zauna da kawar nata ba. Amma abu da manya kuma tsakanin miji da mata ance sai Allah haka ya shawo kan abinsa manya suka inmata ta zauna. Don hakane babu shiri ko zaman lafiya a tsakaninsu ko kadan ita uwargida tana ganin anci amananta dashi da kawarta. Yayin da amarya take ganin abinda yai mata kome mutane zasu fada su fada mana ita dai bata damu ba tunda ta kama mijinta irin yadda take so. Nusaiba Best friend din Asmau ce sosai saidai wanan kaddaran da Allah ya kawo tsakaninsu ya hanasu kwantar da hankali su fahinci kaddaran rayuwansu ce hakan. Na hada miji daya da sunan aure a tsakaninsu zauna suba kansu lafiya a tafi tare zama yayi dadi. Tun daga wanan lokacin kawance ya watse aka koma zaman kishi kinshin ma irin na hauka din nan sukeyi a tsakaninsu. Ga miji ba mai zama baneshi iyaka yazo yayi yan kwanaki ya koma ya barsu nan da iya da itace zasu zauna har zuwa lokacin daya dawo kuma. Wani irin zama mai wuyan fasara a tsakanin su suke gudanarwa agidan zama duk da part daya suke zaune wanda ya kara fadada girmansa lokacin auren Saiba ya mayar masu dashi two two bedroom babban falo a tsakiya. Wanda haukan kishi ya saka babu mai tsayawa daga cikinsu ya gyara part din zakice wa yanda basuyi boko bane a cikin gidan. Sai in sun fito waje zaki gansu fes dasu kamar ki wanke hannu ki taba sai kinje gidansu ki raina masu ni dai zee nace har da hali a irin hakan . Don wani baiyi ba aiba zance ba zanyi ba ko don lafiyata sai idan miji yazone dole mai girki zata tsaya ta tsabtace mashi falon koshi bawai can ba don kowa na bakin ciki da dan uwansa kada ya gyara dan uwa ya huta. Haka kuma bangaren abinci akwai matsala a nan ma din don kuwa idan ba miji ke gari ba haka zasuyi ta horar da junansu da takaici har sai lokacin daya dawo. Farkon zuwan saiba taso ace miji ya tafi da ita lagos don ta fadawa yan uwa da abokai ita ba zata yarda ya barta zaria ba don ba sakarai take irin Asmau ba miji yana lagos ita ta zauna a gida. Sai bayan ta shigone taso nuna hakan amma uwar miji tace bata kai can ba yadda ta sama sun tsara abinsu haka zata bi dole shine wanan rawan kan nata ya dan fara lafawa tun lokacin. Saboda ta fahinci ashe a karkashin iyayyensa yake wanan yasa Asmau dake gabata bata motsa ba take biye dasu a zauna lafiya. A cewan mama ba zata bari ya dauki iyali yaje zaman lagos ba don kada ya shagala da dukiyan marayu dake hannunsa . Haka zalika zaman shi a can din zai iya dauke masa hankali da gida dudu nawa Jafar din yake inbada rigima yaushe ma ya isa iya aje mace daya balle yace biyu. Allah ya taimaka jafar da yan uwansa mutanene dake matukar girmama iyayyensu a yadda suka taso da tsoron mama da iya kakarsu har girmansu haka suke masu biyayya sau da kafa. Zaman iya a wani bangare na gidan yayi tasiri sosai a rayuwansu dontane suke rage wani iya shege idan su fara yanzune iya zata tsaya tayiwa wace bata da gaskiya fes hakan yasa suke dan ragewa. Rayuwan malam bahaushe akwai kalubali da yawa a cikinsa inda wani zubin ake yawan tauyewa mace incinta da sunan aure. Akwai part din da babu kowa a cikinsa instead daya ta zauna a cikinsa amma iya tace sam hakan ba zai yuyu ba wanan din dai shine kasonsa don haka shida ya dauko auren mata biyu lokaci guda dole ya zauna a cikin nasa hakana. Sani Allah sani ma,aiki aka samu kawu Dauda ya rokan masa wanan filin daya fadada girman ginansa har ya bambanta dana yan uwa saboda kara fadin wajesa da akayi. Saboda raba gado da akayi yasa yaran mama Dubu tun bayan auren yayansu Jafar da hjy Iya ta koma gidansa da zama suma kusan rayuwansu a can gidan suke da zaran sun dawo hutu zasu tare a wajen kakansu suna tayata zama wanda shi jafarne ya tilasta masu yin hakan. Haka kuma idan suna gidan wajensa yana da wuya ka samu gida kaca kaca a cikin kazanta don suna tsayawa su gyara tsakani da Allah. Tsab mama Dubu ta gama shiryawa don zuwa ta dubo mahaifiyarta da iyalan danta don tana hasashen Asmau ta samu karuwa a jikinta yadda hjy Iya ta fada mata . Idan zata zakice ba a gari daya suke zaune ba don shiri takeyi sosai sayi wanan sayi wancan taje masu dashi sai kice tazo daga kauyene ganin su. Saida ta gama shirin da komai ta fito tana fadawa mutanen gidan nasu zataje ta duba su iya ta dan kwana biyu wanan ba bakon abu bane sunsan data saba yin hakan . A zaton suma basu dauka zata zauna kamar take zaune din nan ba a cikinsu da Allah ya albarkaci yayan nata sosai fiye dakowa a gidan kusan ace dai sune sukaci moriyan gadonsu da aka raba na marigayin. Tunda wasun su har sunka ga saida kadaran da suka gada din sun koma rabe rabe duk da mahaifin nasu bai wani dade da kwantawa dama ba sosai. Dama ance mai zari a wajen rabon gado shine nasa bai faye albarka ba kusan haka dinne ya faru don kuwa su yan dakin hjy babba da aka tsaya masu suka samu kaso mai tsoka sune suka fara wullakanta dukiyan nasu. Wanan ya jawo tsaiko da iyayyen mata suka hana yayan nasu raba wanan baban gidan da suke zaune ciki a yanzu inda sukai rayuwa da mijin nasu. Tunda gidan mata hudune ras irin ginan malam bahaushe duk da ko wace bangarenta a kewaye yake sai babban falon marigayin inda turakasa yake a nan yayi rayuwa har Allah ya karbi ransa. Don haka har gobe idan ka shigo kaga yadda suke rayuwansu zakice ko maigidan nasu yana rayene amma kuma kowa a yanzu yana cin gashin kansa sai dan abinda ke shigo masu da akan kasa kamar yadda dai aka sabayi tun baya Allah yasa mu dace ya jikan iyayyen mu da rahama Allahuma Amin. Daki daki tabi tana masu sallama da sai ta dawo yadda kowansu keyi idan zai dan fita sukai mata Allah ya kiyayye zakice ba wani abu na rashin jittuwa a yadda sukeyi din. Saidai hakkurin wani ya dara na wanine a zaman don anyi ba daidai ba an nuna hadama da zalama daga bayane suka sulhunta kansu kan hakan. Yan jikokin gidan da almajirai suka dauko mata kaya suka nufi bakin titi inda zata hau keke zuwa unguwar su iya din. Fitanta soma zancen ta ukkunsu dake fadin yau kuma ta haka aka fito muna ba Habu yayi tafiya ba kada ya dawo ya sauke abinda ya dawo dashi mugani a bamu tabon mu . Sai ita amaryansu tace aiko yaya bata da haka kowa ya sani nan gaskiya ko bamu gani ba sai an bamu in rabon mu ya ratsa. Ni bance bata bamu ba ai maganace kawai nakeyi ta fada a hasale don ba a kama mata yadda taso aja zancen da nisa ba ta katseta. Yaran da suka rakata zuwa titi ta sayawa rake sai dari dari data basu suka dawo gida da murna hakan yasa data dau kaya zata fita suke taso durrrr subi bayanta da sunan rakiya don dan wanan ihisanin da take masu. Itama hakan yana mata dadi tana jin dadin rakiyan yaran wani lokaci takan daukosu suzo su wuni su koma in Jafar na gari mota tana a wadace . Daidai kofan shiga gidan mota ya ajeta da kayanta sanin da mai adaidaita din yai mata yasa ya taimaka har cikin get ya shigar mata da kayan kuma bai tsaya karban kudi ba duk da tsawan da take mashi akan ya tsaya ya karbi hakkinsa amma yaki saboda mutunci. Kauyen Zakuwande ya samu halartan baki daga sassa na duniya mu sanman a yan nahiyar africa manoma da masu kiyo da suka cika wanan gari dam ko ina bakine dake halartan taron mafi girma da akeyi bayan shekaru. Engineer Abubakar daya gama hada duk wani na,ura da zai hasko masu tauraron dan adam dinsu ya sauko daga saman motan yana kara duba saitin dayayi da kyau kafin ya nufi bayan mota ya bude yana dauko goran ruwa ya balle yana kokarin zuba don dauraye hannunsa. Hankalinsa sam bai kaiga dandazon mutanen da suka kewayesu suna kallon aikin nasu ba sai lokacin daya gama wanke hannun ya kwankwade sauran ruwan ya cillan da goran gefe . A lokaci ya kula da jama,an dake waje ashe akwai inda yafi Nageria kauyanci don goran daya cillan suka taru suna wasoson dauka . Har da manya wani dattijo daga cikin masu rige rigen daukan gora da aka tureshi tare da kekensa yasa Habu din fadin subbahanallahi yaje da sauri ya kama tsohon yana tayar dashi tare da kekensa yana mashi sannu. Tare da tambayan baba bakaji ciwo ba ko yace banji ba dana naso dai in samu wanan jallon nasaka ruwa a ciki yara kuma sun hana. Ina zuwa yace ya koma ya dago gora biyu cike da ruwa ya kawowa dattijun ya bashi cikin girmamawa godiya tsohon ya fara mashi sau ba adadi yaja kekensa ya tafi. Juyawa yayi yaje gun yan uwansa da suka zubo mai idanu saida ya karaso ibrahim ke fadin wanan yasa danasha ruwa saina jefa gora a bayan mota. Tausayi tsohon yabani yana bukatan gorance da ganin haka yafada ibrahim yace tun dazun yake tsaye ai yana kallonka . Watau wanan gari gashi dai babbane cike da jama,a kuma amma kullum basu wayewa su kasan abinda ya kawo hakan yace ina zansan hakan ni dana fari shigota yau din . Yace gargajiya donsu har yanzu gargajiyansu yana nan basu yarda sun dauki akidar nasara sunsawa kansu ba aikinsu ke nan noma da kiyo komai arzikin mutum ata wanan hanyar zai nuna halinsa. Gaga kuwa ba zasu taba cigaba ba matukar basu yarda da nasara ba a rayuwansu gargajiyace tsantsanta a garin nan ka duba ko tsarin shigarsu mafa dabanne kuma kowa da irin al,adansa wajen nan. Hakan yafi masu sauki kallo daya zakai masu kagane basuyi sakaci da addinin su ba har yanzu yawan kabilu kuma ai duk zubin fulanine garesu ko larabawa. Haka sukai ta hira tsakaninsu suna jiran lokacin da zasu fara gabatar da shirin nasu don komai a yanzu hada lokaci kadai suke jira. Kuyi hakkuri mu dauko tushen labari don fahintarku masu karatu nagode. ZAINAB IDRI MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1f MARFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,, 4️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Sallaman mama Dubu yayi daidai da jefo plate din shimkafan da Saiba tayi ya fado saman hijjab din jikinta kafin ya gangara ya sauka kasa daidai kafanta ya tsaya. A hankali mama tabi plate din da kallo haka kuma take kallon yadda sauran shimkafan dayake gangarowa daga saman jikinta zuwa kasa. Kaita girgiza ta dago ta saukewa Nusaiba kafin ta mayar kan Asmau data dafe baki cikin tsoro da firgici kai ta sada kasa tana mai tsananin jin kunyar uwar mijin nasu. Da kyat mama ta iya budan baki tace yaran nan har abin yakai haka a gareku daga haka ta juya don bari part din taga hjy Iya a tsaye itama cikin takaici take kallonsu. Gara dai da kuka gwada ga uwarku yau tunda ni kun raina min arzikina mata kamar dabbobi kullum fada dan abu kadan fada kamar karnuka. Akanku aka fara zaman kishine wai in ba auro mata ana haihuwan ku kun mayar da gidan yaro gidan yan tasha gidan dambe . Badon makwabta na tsoron jidalina ba da yanzu gidan nan ya cika da yan kallo tunda kun zama mutanen bamza. Kishi haukane wai mijin ku yana wajen nemawa kansa rufin asiri ku kuna nan kuna tona masa asiri a cinkin unguwa sai yaushe zaku bar wanan bakin kishin nakune wai ? A hankali mama da ranta yake bace ta zagaya Iya tani dake masifa ta karasa ficewa daga part din zuwa nasu wajen kokarin cire hijjab dinta da suka bata takeyi kada ya lalace ban daki ta nufa taja bucket ta jikashi tare da yayafa omo ta barshi a jiki. Fita tayi waje don bata zauna ba kayanta dake can ta waje ta shiga kwasowa zuwa cikin falon mahaifiyar ta din a daidai lokacin Iyan tani ta kara fada ta juyo zuwa wajensu rai bace. Ta samu mama na kokarin zuge zip din dan jakar kayanta data dauko wanda zatai dan kwana biyu dashi a nan zani ta dauko daga ciki tana sauyawa. Wuri ta samu ta zauna iyace ta soma magana tana fadin yau naga yaran banza a gidan nan yara kamar tashin gareji ace babu wanda zakaiwa fada yaji. Sallaman Asmauce data shigo tana sune kai hannunta dauke da cooler abinci tazo ta dire a gaban mama a daidai lokacin kuma itama Nusaiban ta shigo da ruwan data surka da postard cleak ya rine a cikin jug ta aje gaban mama din cikin girmamawa. A,a ku dauki abinku ni a koshe nake daga gidan mijina nafito yanzu koda bai raye bayansa basu barmu a cikin yunwa ba Alhamdullahi nagode. Zaune Asmau takai tana dan dukar dakai Allah ya gani tasan mama mace ce mai kawaici da kawar da kai daga abinda sukeyi bata kulawa koda ance ga abinda sukeyi a kullum nasihanta dasu shine su zauna lafiya suba mijinsu farin ciki ga nemansa. Fitansu koma bayansane ga harkokinsu tasan zaman kaunace ya hadasu da danta don haka suma dul biyun tana kaunarsu tunda dantane ya daukosu ya kawo matasu amana a cikinsu. Yau sai gashi iya shegensu yakai har plate din abincin danta suka watsa mata saman jiki ya watse a tufafinta ita yanzu me zatace da boyar Allah nan mace mai zurfin tunane da kawar da kai irin mama. Kaita kara sadawa kasa ta soma magana mama don,,,,,, Asmau jeki kawai kuci gaba kada ku bari zaman nan dai ina son ku sanin na bautan Allah kuyi akwai hakki da amana a tsakanin mu daku da mijinku dake can yana neman abin rufin asirin mu. Idan kun zauna lafiya kuji dadin hakan idan kuma kunki kome ya biyo bayan hakan kuka da kanku kada ku kuka da wanin mu nan Allah ya gani munyi iyakar yinmu akan ku kun kasa kwantar da hankalinku ku daina wanan shashancin kishin a tsakanin ku. Sauran mata da suke zaune da kishiyoyi ake ganin kamar zaman lafiyane a tsakaninsu kokari suke suna danne kishinsu a idon jama,a kowa da kuke ganin yana zaune lafiya danne abin yake kasan ransa shin ku ba zaku iya hakan ba don Allah. Mama wanan yarinyar yar rainin wayauce waini Asmau zata zubawa abinci a plate a kawo min don ta raina min wayau kome Saiba ke fadan hakan ga mama. Hannu mama din ta kara daga mata tana fadin ban tambayi ba,asiba don Allah komai mutum yayi kansa yaiwa ina dai son ku sani ba a wullakanta abinci a zauna lafiya. Wanan shine maganata dukkan ku nan ba zance bakusan abinda nake nufi ba tunda kowacen ku uwarta tana da kishiya a gida. Mama bani wullakanta abinci wullakancintane kawai ya mota innice nace ta ban abinci cewa take naje cikin tukunya in daba shin laifine ni har na zuba mata a plate mama ? Amma dai kinsan niba wullakantata bace da zaki ban abinci a cikin plate kamar nazo bara a wajen ki kema kinsan nafi karfin hakan wallahi. Yanzu dai sai kuyi ai garara ku nunawa uwar naku halinda kuke kwana kuke tashi dashi a cikin gidan nan ta gani ksllon Iya din mama Dubu tayi tana fadin mama kin hada kayan na soma wankewa ? Don dama duk aka kwana biyu mama tana zuwa gidan ta gyarawa mahaifiyarta waje tayi mata wanki da sauran gyaran waje sai idan yan matanta sun dawo hutu suna gari suke dauke mata hakan. A cikin matan Jafar din babu wace zatace bari ta dan gyarowa Iya part din ta matukar basu din bane sukazo sukayi wurin zai koma fes. Ganin mama din ta fita batunsu yasa Saiba fita cikin hasala tabar Asmau nan saida zata mike take kara fadin mama kiyi hakkuri don Allah. Jeki Asmau a kula don Allah kece dai babba a gidan nan kanninku da abinda kukeyi sukr koyi don Allah Asmau arika tausan zuciya idan rai ya baci. Fita tayi tana tunanen irin halin mama dubu na sanyi hali macece datake rike girmanta da kawar da ido akan duk abinda ke faruwa danta dasu iyakarta nasihan da zaiwa mutum amfani gaba idan yabi. Saidai ko tayi kokarin bin nasihan da ake mata hakan bai samuwa don Nusaiba taza fito da sabon fitinan da sai tabiye mata sunyi fitina. Ita wanan tana da dama sosai fiye da wacan fitsarariyar da tafita duk wani fitina daga wanan nusaiban yake fitowa a gidan nan Iyace ke wanan maganan bayan fitansu. Taron yarane kurciya shike rudinsu a wanan lokacin wanda sukeyi a kansa yana can baima san suna yiba zasu zauna su halaka kansu haka a banza kan namiji. Wata rana ko ance suyi hakan ba zasuyi ba ai don girma yazo a lokacin saidai su koma kishin mumuke wanda yafi wanan da sukeyi zafi. Mamace take fadan hakan ta mike ta dauko tsintsiya don ta fara gyaran dakin Iya din da yayi kaca kace ga kura ko ina a falon har makewayin data shiga yana bukatan gyara idan zai samu. Komai a wajen taron nan yana gudana daidai sun fara hasko wa duniya abindake wakana wanda hakan yasa hankalinsu daukuwa da aikin don abune da yake son natsuwa don kada a samu kuskure. Sallah ya tayar dashi da yunwan da yakeji ya fito daga cikin motar tasu mai na,ura zuwa lokacin wajen taron ya cika makil da jama,a tare da Sahabi suka nufi masalacin sukai ibada ya jima kafin suka fito tare da dan zaga wajen suna kallon irin baiwan ni,iman da Allah ya shimfidawa yan Africa. Malam Habu zokaga kayan nono a wajen nan Sahabi ya fada ya doshi wani hanya dashi yana biye dashi a bayansa koreni gasu nan birjit iya ganin mutum da matan fulani dake ta kaida komo a wajen. Sahabi din ya tsaya yana taya wani kwaryan nono hakan yasa Abubakar ya fara raraban ido yana bin ko ina na wajen da kallo direct ya nufi wajen wasu da suka tsabtace nasu da komai a cikin tsabta gwanin ban shawa . Malam zoka saya baida tsami ko karni lafiyanyyen nonoce tatsin yau din nan muryan wata bafulatana ke fadan hakan ya karasa gabansu cikin mamakin jin yadda take hausanta na yan Nageria sak a bakinta. Sahabine ya karaso yana fadin aina fadama sai inda kallonka ya kare a wajen nan yaji matar fulani din na fadin wanan na shanune wanan kuma na rakumi ga wananshi da akecewa wara da wani hausan nonoce sahihi ake dafawa ya hade haka. Sai wanan kuma cikwai ce mai dadi baida mixed a cikinsa zakaso ka kara idan kayi amfani da kayan don babu algus a cikinsa ko wani mixed . Kai amma ke yar Nageria ce ko sahabi ya tambaya tace meka gani tana murmushi a fuskanta. Kafin tace dashi daga dai can muke ta fada tana juyawa da alaman neman wani takeyi alokacin a cikin harshen fulatanci take kwalawa wata kira da YANDA yanda yanda tana mata hannu tazo. Sai ga wata doguwar yar matashiyar budurwa ta juyo wace aka kira da Yanda din takaraso zuwa wajen matar tana mata fulatanci. Ido ya kafe ta dashi yana kallon yadsa ta karaso tanawa matar magana acikin yanayinta. Yayi da Abubakar yake tsaye yana kallonta cikin mamaki yana fahintar me take kokarin fadawa yarinyar. Daidai lokacin kuma Sahibi ya juya harshe a cikin turanci yake fadin ko ya saye yana da wuya yakai gida bai lalace ba iyakarsa idan a nan zaiyi amfani dashi kawai. Sai sukaji muryan matashiyar na basu amsa da fadin ku saya daga nan har sati biyu baya komai koda ba a saka a cikin fridge ba. Kayan mu suna dakyau da inganci bawai ina yabo bane don kusaya ko don na cuce ku saboda nasan zakuso shi ko nan gaba. Ta kara fada a cikin turanci da alaman gajiya karara a fuskanta lokacin tana dan kakabe kuran dake taba koren nasu da wani dan gashin dake hannunta na dabba da akaiwa ado da duwatsu . Tsaye sukayi galala suna binta da kallo tare da tambayan wai dama kuna jin turanci haka ashe da zaginku mukayi shike nan kunjimu. Ta dan kai zaune tare dan murmusa tana fadin kadan kadan ba balle nasan ba kuyi kama da wayanda zasu zagemu ba ai. Dagajin hausan mamanku na gane ku mazauna Nageriane don hausanta daban da wanda kukeyi a kasan nan. Eh daga can muke koma ince a can aka haifemu rayuwace ta dawo damu gida bayan rasuwan mahaifiyar mu rikon mu ya dawo nan. Sosai ta bashi tausayi tsab ya gama kallonta yana karance yanayinta turancine neat a bakinta amma kuma gata ta saje da dabi,un mutanen wajen ba zaka taba cewa ita din tasan ko zo inkasheka ba da hausa balle turanci. Yanda din ta kawar da shirun take fadin ku saya zakace nace idan kuje dashi aka saka a fridge zaiyi rabin shekara a can bai baci ba wanan karon a cikin hausa tayi maganan tana kara bude manyan koren dake gabansu. Sahabi bai yarda da zancen ta ba don abar zancen yake fadin wai ina zamu samu abinci mai kyau a wajen nan ? Ta dan juya kafin ta fara masa kwantace ganin baigane ba yasa ta kwalawa wata yarinya kira da Maria zoki nan saiga wanan yarinyar dake firgitashi tun zuwansu garin itace aka kira da Maria din. Yarinya ce karama saidai da gani ba sai an tambaya ba don kamarsu da yar uwar nata da aka kira da yanda sukayi kama sosai ita wanan din dai ta girmewa yarinyar a shekarune kawai zace sai dan haske da karamar ta dara babban dashi. A cikin yare take fada mata ta kaisu wajen saida abincin yan maiduguri ta amsa da to tana watso masu idanuwanta masu kama da madaran tana wani irin juyasu alaman suje din tayi gaba suka bi bayanta . Zansu tafi babban matar ke fadin ya zancen sayan kayan sahabi yana kokarin fadin su barshi kawai shi kuma Abubakar din yace dasu a bari su dawo zasu saya hakan yasa yaga fara,a a fuskan yar budurwan data kashe zuciyarshi da mamakinsu. Sun kama hanya tana gaba da dan kwarya karami a hannunta bata ko tsaya wani jerawa dasu ba tasha wani kwana suna biye da ita har zuwa wanan wajen da basu san dashi ba. Oya mun gode ki tafi kada a nemeki Sahabi ya fada sai ta amsa da to tana kallonsu saidai taki gusawa daga inda take. Abubakar daya kula yace da yarinyar yaki zo nan Abubukar ya fada yana kallonta da sauri ta biyoshi a baya zuwa inda suka nufa. Tare suka shiga shagon yasa aka hada mata take away guda ukku ana mika mata ta juya a guje cikin murna bata ko tsaya godiya ba ta nufi sansaninsu kai tsaye da gudunta a cikin murna. Murmushi yayi ya juya wajen sahabi dake mamakinshi yace mutumina yaya dai nisawa yayi yana zama ya soma fadin tausayi suka bani wallahi. Haka duniya take ai dama ba ko yaushe mutum ke samun yadda yake so ba a duniya sahabi ya fada yana kallon abinci gabansa da aka aje masu. Abincine lafiyayye mai kyau irin na hausawa ga kamshin man shanu yana tashi acikinsa sukaci sukaiwa yan uwansu take away. Duk abinda yake hankalinsa na gun wa yan nan mutanen don hakane ya saci jiki ya koma sansanin nasu saidai ya samu basa nan don lokacin yamma tayi sai wata mace dake zama a kusa dasu. Yake tambaya take fada mai ai basu kai dare a wajen sun koma gida saidai gobe tunda safe zai samesu sun fito insha Allahu. Washegari kuwa rana ta biyu da taron mutane sun fara tattara kayansu don shirin komawa garuwansu daga ciki har dasu Abubakar duk daidai su sai an rufe taron suke son su kama hanya komai dare a ranan. Bai manta da zancen yaran nan ba don da zancensu ya kwana a zuciyarshi yana son ya san wani abu a game dasu din. hanya kama ya nufi runfarsu tun daga nisa ya fara hango ita babban wacce yake kyautata zaton mahaifiyarsuce ga wasu yan Nageria suna sayan kayansu. Don kayan nasu gaskiya yayi kyau sosai haka ya karasa gaban ya dan tsaya yana dakon su gama cinikaiya da wa yanda ya sama din a wajen. Karamar ya fara gani a gabansa tana binsa da kallo kafin ya tsinkayo babban dake tafe da amalanken shannunsu dake dauke da kore. Yana wajen suka sauke kayan tsab suka jera kafin ta dago ta soma gaiyar dashi a cikin dan fara,a kafin tace dashi na dauka kun muna wayaune ai kun tafi koda yake bakai kama da mayaudariba ba kai kan. Jiya kuma sai kukayi wahala haka kuka saya muna abinci mai yawa angode Allah kara arziki me za a baka daga ciki ta fada tana kallonshi tana dago kai ? Samu tayi ya zuba mata ido baya ko kiftawa sai tayi murmushi ta sake maimaita wane kake so yace yanzu ni ina na san me zance dake ?. Tace wanan zaka iya saya kakaiwa iyali mata ko mama da yan uwa zasuji dadin tsaraban shi ansan ka shigo kasan cameron . Ko data dago kai still yana kallonta sosai sai taji ta tsargu da hakan ta dan dukar da kanta kasa tana wasa da zara zaran yatsunta. Bakayi magana ba ta kara fada kallon yadda ake durawa mutane a jarka yayi yace nawa duka kayan nan da kika sauke ? Ido ta zaro waje tace dukka fa kace zasu iya kaiwa dubu hamsin da kudinku na Nageria ga mamakinta sai taga yana kokarin zaro kudin daga jikinsa. Kuyi min parking dinshi yadda ba zai samu matsala ba kudin abinda zakiyi amfani dashi ayi parking yana ciki saidai don Allah ? Saita dago ta kalloshi yayi mamakin ganin idonta da hawaye jikinshine yai sanyi ya dan matsa kusa yana fadin. Lafiya dai tayi kasa da kai tana fadin bansan irin godiya da zan maka ba a yau da an watse taron nan bamu saida kayan nan ba ba karamin fitina zamu shiga ciki ba don zamuyi hasara sosai zamu kuma shiga cikin ukuba. Saboda me ya tambaya yana kasheta da ido donson jin karin bayani shidai yanayin yarinyar yayi mashi sosai tana da natsuwa sosai dayake hangowa a gareta. Murmushi tayi tana fadin dogon labarine mundai gode da wanan taimakon da kayi muna Allah ne kadai zai sakama da alherinsa. Amma meya dawo daku kasan nan kuda kuka saba da rayuwan Nageria kuka zabi dawowa nan ku zauna ? Ya zamuyi bamu da kowa a can yanzu wanda yayi sanadin zuwanmu can Allah ya karbi abinshi dole muka dawo kasan nan tunda ba yadda zamuyi. Kina da waya in naje mu dinga gaisawa daku tace da ina dashi wanda nake amfani dashi a school saidai zuwan mu nan gaskiya mun kadar saboda yanayi saidai ka ban number wata rana zan kira insha Allah. Ai har karatu kinyi ashe kuma kika kare a nan kina tallan nono tace wanda baida gata ai duk yadda rayuwa tazo mashi haka zai rungumeta mun rasa gatanmu tunda mahaifinmu ya rasu Allah ya jikansa yace ta amsa da amin. Sai wata rana kenan zaki kira ba zaki kira kiji ko mun sauka lafiya ba ko kuma ina da bukatan wanan abin ki turo muna dashi. Dariya abin ya bata cikin dan kunya take fadin kayi hakkuri banda wayace kona karba ba zan kira ba din kaga ai gara dai kar nayima karya. Kinsan wajen motar mu ko ta amsa da ehh yace a shirya komai kusamemu can ya juya ya tafi ta bishi da kallo tana yaba irin kirkinsa da halarci. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1f MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 5️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, A tsaye ta sameshi suna hada kayansu sallama tayi daga bayanshi cikin yar siriryar muryanta ganin kalkon mamakin da Sahabi ke mata a bayanshi yasashi juyawa da sauri yagame sahabi din ke kallo a wajen ? Kasa tayi da kai tana kokarin gaidashi da aiki ta hada da fadin ga kayan ka an hada komai yadda ya dace daga nan ko lagos zaka ba zaiyi komai ba insha Allahu. Ba lagos zani dasu ba zariya zan kaiwa mahaifiyata ya bata amsa tace Allah sarki aiko yayi daidai da bakin tsofi don komai baida tsami da zai hanata bukatansu. Mungode kwarai wallahi yadda ka taimaki rayuwan mu Allah ya taimaki naka kaima ta fada cikin yar siririyar muryanta. Wai tsaya Habu wanan duk kayankane wanan haka kome nifa ban gane ba wuceshi yayi yana fadin ba zaka gane ba kuwa kai matso ku saka min a bayan mota kunji ? Lokacin ibrahim ya karaso yana fadin oga kace da shirinka dama muma bari mu debo namu ashe dama ina son saya ina jin tsoro. Kaje gunta kayansu yana da kyau sosai tace dariya sosai Sahabi ya kwashe dashi yana fadin ashe mun saura dawowa garin da alama zamu dawo wani karon kenan kuma ? Yar filo akwai saura a wajen ku tace eh za a samu bari na duba idan akwai a wajen maman mu ta juya ta soma tafiya . Kai dan iskane yacewa Sahabi dake ta kwasan dariyan shakiyanci sahabi din yace dariya nake don yadda na hasko kayi tsaye ana shadinka kasan wanan aiba karamin shadi zakasha akanta ba wallahi. Shima zancen sahabin saida ya sakashi dariya in akwai abinda ya tsana a taba lafiyan jikinshi balle shadi ta ina zai tsaya kan mace ai mai shadi ko gudane balle ba adadi. Zama yayi saman motan yana sauraren Sahabi dake bayani akan shadi da yadda akewa wanda ya gaza motsin wayarshi ce da tayi dan tsuwa daga Aljihunshi hakan yasa yaciro ya duba alert ne na lokaci har yayi niyar mayar da wayar sai kuma ya fasa hakan sim din ya debe daga cikin wayar ya mike tsaye. Wani wuri dayaga ana sayar da waya ya dosa layin waya ya saya duk da tsadansa bai tsaya neman ragi ba ya biya ya juya ya koma inda ya fito. Ya gama turo komai a dayan wayan nasa kafin ya goge na wanan wayan yana gamawa tana karasowa wajen da kayan ibrahim. Kudi ibrahim ya ciro ya bata yana fadin Allah yasa dai yadda kika yaba haka yake don kada muje gida mu samu ba gaskiya bane yana da matsala ? Irin duban mamaki din nan ta danyi masa kafin ta rausaya kai tana fadin Allah ya tsareni da cutar daku idan na cuceku ina zan ganku ku yafe min ? Daga haka tasa kai ta juya ta zoma tafiya inda kayansu yake daga bayanta muryan Abubakar ne yake tsayar da ita a bayanta ta juyo ta dakata har ya tako zuwa inda take. Baiyi wani magana ba wayan hannunshi kawai ya mika mata bata karba ba kallonshi tayi cikin mamaki ki karba mu rika gaisawa idan nakoma gida. Kaita fara girgiza mashi tana fadin ka barshi bayan wanan alherin dakai muna mai yawa zaka kuma mika min waya ? Ko haka mun gode kasan girman taimakon da kaimuna a yanzu har in mutu ba zan manta da hakan ba a rayuwata zan kuma cigaba dayima addua a kullum kan wanan alherin. Haba dai ya fada yana dan dariya kafin ya saita kansa yana fadin wai zaman me kike a wanan kasan yanzu ko wasan nan ya kawo kuma nan ? Yanayin fuskanta ta sauya lokaci guda tana fadin na fadama kaddaran zaman mu nan sanadin mahaifinmu daya rasu shine zaman mu ya dawo nan kasan don bamu da kowa can Abuja da muke zaune. Nan kuma mun dawone a cikin yan uwa saidai duk da mun dawo cikinsu da zama har yanzu suna,,,,,, Yanda warre ? Wata bakar mace ta sa mata kira daga wajen saida kayansu hakan yasa ta juya da sauri da zumar ta wuce saka mata wayan yayi a cikin kwaryan dake rike a hannunta ya juya ya koma inda ya fito ta dan tsaya ta kalleshi kafin ta nufi wajen nasu saidai kafin takai tacire wayan cikin dabara ta kada a kasan lalitan dake rataye a wuyanta. Basu dauki lokaci a wajen ba taba da umurnin su shirya su soma hanya don ganin yadda mutane keta haramar bin hanya tunda wuri kada suyi dare. Lagos Nageria. Tafe yake cikin motarsa kiran kiran benz wace bai dade da mallakanta ba a yanzu sai kira,a dake tashi a cikin sautin malam Ahmed sulaiman kano. Yake dan bin kira,an shima kafin wayanshi ya dauki kara hamnu yakai yana rage sautin dake tashi na muryan malamin addini a Nageria don ya dauki kiran Saiba amaryansa daya gani din saman layi. Ya akayi Saiba i will call you bank idan na isa yanzu ina hanya ina tukine don Allah ? Sweet J kada ka kashe don Allah ka saurareni don bansan idan ka kashe wani ya rigani kiraka a fadama abinda bashi ba. Meya faru kuma ya fada cikin kaguwa da yaji kome ke bakinta a lokacin dama akan wanan Asmaun ne wallahi idan Asmau bata kama kanta dani ba sai na illanta mata rayuwa. Tseweeee ya tsoki yana fadin akan sakarcinku kika kirani ina saman hanya haka bashi bafa Sweet J mama mukayiwa laifi muka kifa mata abinci saman jikinta. Yana kokarin kashe waya yaji karshen furicinta a dan razane yace wata maman dai kodai Iya kike son kira kikace mama ? Mama dai ta tudun wanda ita nake nufi ta fada a sanyayye innalillahi taji yana ta maimamitawa son bai taba zaton iskancin matan nasa har zai iya kai haka ba ai ? Wallahi Sweet J ba,,,,,,,,, You are very stupid idiot of you don kina yar iska kuyiwa mahaifiyana haka ki kirani kina fada min sai ya kashe wayar gabaki,daya yana jin wani tukuki a zuciyarshi. Fuskanshi ya shafo da hannunsa yana gyara zama a cikin motan don yadda yake jin zuciyarsa ya kasa samun natsuwa da zancen data fada din . Duk yadda akayi wani abu mara kyau ya faru da mama din akansu shikan wai wani aurene yayi a rayuwanshi da kullum baida natsuwa a tare dashi kan matan nasa daya tara agida ? Yanzu wazai kira yaji meke faruwane wai don baima son ji daga bakin ko dayansu a yanzu wanan karon sam ba zai kyalesu ba iskancin nasu yayi yawa har abin yakai ga mahaifiyarsa haka ? Wa,iyazu billah a ina sukaga mama din har take fadin sun mata wani abu mara dadi hakane tunawa yayi tsakiyan watane ake a lokacin don haka mama tazo gidan ke nan gyarawa iya daki . Dama daga tsakiyan wata zuwa karshen wata take zuwa wajen mahaifiyar nata taimata kwalema don samun ladan mahaifiya a gareta. Har in mama zata iya tsayawa akan nata mahaifiyar haka su da karfin su mai zai hanasu tsayawa akanta har inda karfinsu ya kare akantasu mahaifiyar. Oh shet yanzu wa zai kira yaji abindake faruwa har ya shiga haraban nasu da mota sai a lokacin Abubakar ya fado mashi a rai . Da sauri ya lalubi waya yana neman layin Abubakar din sai gashi ya samesa ya dauka yana fadin na dauka ka manta da dan kanin nakane ai gamu nan yanzun muke shigowa Nageria ai. Sam ya manta da cewa Abubakar din baya gida ya kirashi ya sheda mai zasu shiga kasan Cameroon wani shutting don haka bai gida ke nan a lokacin. Saiya waye da fadin masha Allah Allah ya kawoku gida lafiya sai zuwa gobe dai ke nan zaku iso yace insha Allahu nagode yaya J . Suka kashe wayan yace common wazan kira ke nan kafin yakai karshen tunane aka buga glass din motan nasa meiyabi ce don yana kallonta ta bangarenshi. Kallon tsab yai mata kafin ya sauke glasa din yana kako murmushin dole a fuskanshi yace hey how are you tayi murmushi tana fadin . Mr handsome ka boye da yawa kwanan nan duk bani ganin ka na dauka kayi tafiyane ai da ban ganka ba kana jin dadin kafa garin nan ? Dan murmushin yake yayi mata kafin yace in baki ganni ba aini ina ganinki sometimes tare da wanan dogo saurayin naki. Dariya ta kwashe dashi kafin tace waiko ka fara kishi akainane haka da har zaka ganni kaki min magana wani kallo ya watsa mata na takaici ya karasa fitowa cikin motan yana facing dinta. Gata bakace bata shafa mai da matan yanzu suke yawan shafawa jikinsu su canza kala ba ita tabar bakinta na natural maikyau saidai gaskiya idan ace ta girmeshi da kusan shekara bakwai zuwa takwas ko goma ba zai musa hakan ba amma kuma wai sonshi takeyi a hakan ita. Yana dai son su rabu lafiya hakan yasa yake dan tsayawa ya biyewa shirmenta wani lokacin idan mutanen arzkin na kansa ayi hai hai a watse lafiya. Handsome dama ina son ganin ka muyi wani magana naga kai mutumne mai harkan bussiness so akwai wani brother nawa dake wanan harkan acan porthercout nake son in hadaka dashi amma kaje kayi tunane idan zaka iya don harkane dake son natsuwa sosai a cikinsa. Na yaba da hankalinka da irin natsuwan ka yasa nayima sha,awan wanan harkan ya dade yana neman dan arewa dayake da amana wanda zasuyi wanan harkan dashi sai nayima sha,awan hakan. Kallon ta yayi a tsanake yana karontota a zuciyarshi ba wasa a cikin lamarinta don haka shima ya natsu ya maida hankali kanta budan bakinshi tambayanta yayi da why me ? Sai yaga tayi murmushi ta dan kara matsowa kusa dashi tana fadin you deserve ita handsome kana da natsuwa sosai wallahi beside kuma ni din ina kaunarka har cikin raina don haka tunda you are pure baka harkan banza kai nake son friendship din mu ya zamo zumunci a yanzu dakai. Ina mai baka shawara akwai alheri sosai da zaka samu a cikin harkan nan har idan ka rike gaskiya a yadda kake din nan baka sauya zuciyar ka daga baya ba. Don mutane da yawa a yanzu kudi na canza masu akida saidai idan kayi tunane tunda kana da contact dina zaka iya kirana naji shawaran daka yanke akai . Takai hannu ta kamo nasa hannun tana fadin kada ka damu Allah ne ya hadani dakai abar zancen so yanzu a tsakanin ka daukeni yar uwa a wajen ka. Zanso ace kaima ka shigo cikin system duniya tanayi dakai kamar kowa amma ta hanya mai kyau bata banza ba. Hannun nasu data rike ya kalla tayi saurin saki tana fadin sorry na manta dakai malam ne ai addinin ku bai yarda da hakan bako iam sorry for this. Ta sake ta gyara tsayuwa tana fadin ni zan tafi saina jiki nasan ba zakace a,a by god gra grace don abune maikyau da zai tamakawa rayuwanka. Nagode yace da ita zanyi tunane akai idan babu matsala zakiji itama godiya tayi mai suka rabu ta nufi tsadadden motanta dake fake a gefe fara sol mai shegen tsada da sai wa yanda suka kafu suke shiga irinsa. Juyawa yayi zuwa cikin gidanjen nasu da ake kira da one milleum quaters anan ne kuma suka hadu da Meabe din wace ta taba fada mai zamanta a nan na dan lokacine ta kusa kammala ginanta da zata koma cikinsa very son. Dutse biyu a lokaci daya zancen wanan kafiran zai tsaya nazari ko zancen da Saiba ta kirashi dashi zai tsaya duba fadawa yayi kan kujera tare da tallabo kanshi yana lumshe ido. Dolene yaje gida ba zai kira kowa ba don ba zai fahinci gaskiyan meya faru ba gara yaje da kansa ya ganowa idonsa haka kuma duk wace ya kama da laifi akan mahaifiyarsa zaiyi mumunan sabawa maishi don ya fada masu wanan duk sun sani kuma. Ba mama Dubu ba har iya da kawu dauda suna da kwakwaran kashedi ga duk iyayyen nasa daya kafa masu don bai yuyu a garesa su wullakanta mashi iyayyensa shi bai wullakanta nasu ba. Haka yake murzan goshinsa da hannuwanshi yana jin wani iri kasan zuciyarshi zancensu da Meambe na dawo mai akai sam ba zai taba yarda ya jefa kansa cikin halaka ba. Mafi yawan masu kudinnan na kabilu kudinsu kudin tsafine don haka shikan ba zaiso abinda zai tabfba martaban gidansu ba. Gara ya dogara da dan juya kudinsu da yakeyi tunda ko wanan akwai daukaka a cikinsa yana tsoro matuka da wanan shawaran da Meambe ta kawomashi. Da haka washegari ya dauki hanyar gida tunda safe yabar lagos din don baijin zai iya daukan lokaci baije gida yasan abindake faruwa ba. Karon farko ke nan daya tsani halaiyar matan nasa da irin fitinansu da suka kasa kwantar da hankalisu su zauna lafiya a tsakaninsu. Tsuki yaja yana mai ganin laifinsu duk kansu amma na Asmau yafi don me zata canza halinta daya santa dashi akanshi. Yasan Nusaiba zata iya jan fitinan da sai Asmau din takai ga tankawa amma meye a ciki idan ta shareta tayi haukanta tagama yarasa Saiba wace irin yarinyace mara jin magana haka wai ? Hanya ya tsaya ya sai doya manja jan garin kwaki domin iya dake sonshi sosai saura a can gida yake saya idan yaje wanan ne kawai yake saya a hanya don yafi sauki da kyau a nan yake tsayawa ya saya. Baiga Zaria ba duk uban sammakon daya buga sai wajajen karfe tara na dare ya shigo garin zaria kai tsaye gida ya dosa don dare yayi baijin kuma mama tana tudun wanda a lokacin yafi kyautata zaton dai tana gidansu yanzu haka . Haka shima Abubakar sunyi waya da mama take shadai mashi cewa tana unguwarsu wajen iya don haka shima kai tsaye a can motarshi ya saukeshi da kayanshi ga baki daya daya sayo Sahabi yana ta mashi sheri akan kayan bai kulashi ba. Saibace ya sama wajen part dinsu tana waya kala batace dashi ba shima kuma bai kula da ita ba haka yayi ta jidan kayashi yana kaiwa kofan iya da sukr ciki part din da yarta mama basu sanda isowarshi ba har yagama jido kayan daga waje cikin wahala ya shigo dasu lokacin ya koma ya kwankwasa kofan iya din . Mama Dubu ce ta bude kofan tana ganin danta ta dan murmusa tana fadin ikon Allah kun karaso ke nan sannuku da hanya. Daga ciki iya ke tambayan waye tace habu be Allah ya dawo dashi lafiya tasowa iya tayi tana fadin da daren nan kuke tafe haka Bukar sannunku da hanya . Karasa fitowa mama dubu tayi tana fadin a,a kaya haka ka zo dasu haka Habu kuma duk bamuji shigowanka ba sannu da zuwa ta duka ta fara tayashi kwasan kayan zuwa cikin falonsu iya din. Saida aka gama kwasan kayan kaf mama ta nufi wajen dan karamin fridge tana daukowa dan nata ruwan leda karba yayi yana fadin bari naje nayi wanka mama indawo. Ya fada tare da juyawa bai tsaya sauraren iya dake fadin ka zauna kaci abinci kafin kaje wanka mutum sai kace agwagwa da son wanka dai juyowa yayi ya dubeta ba tare daya tsaya magana ba ya fice. Yana jin yadda Saiba ta kure kida a gefen part dinta zakice wani sha,anin buki ake a wajanta alkawari yayiwa kansa zai kawar da ido daga duk wani abinda matan yayan nasa zasuyi a gidan. Don haka bai tsaya kulata ba ya bude part dinsu dashi da kaninsu dake boarding school anan suke da dakunoninsu don sunbar can cikin gidan nasu yanzu tun bayan da yayan nasu yai aure. Yafito dogon rigan jallabiyansa ya zura a jikinsa ya shimfida sallayan sa ya tada sallah saida ya idarne ya kula da gyaran dakin da akayi wanda yasan ba aikin kowa bane sai mama Allah sarki mama ya fada yana lumshe ido. Can yaji sautin buga kofa hakan yasa ya saurara da kyau ba karya kunnuwansa ke masa ba don ko nan din ake duka hakan yasa ya mike yana duban wayansa dake hannunsa. Karfe goma saura na dare a lokacin don haka ya nufi get din kai tsaye daga ciki yake tambayan waye . Aka bashi amsa da Jafar bude min get hakan yasa ya leka yana mamakin yadda akayi yayan nasa yayi tafiyan dare haka tun daga lagos. Saida ya tabbatar daya shiga da motan ya mayar da kofan ya rufo ya saka kwado dan basu da maigadi a lokacin karasawa yayi wajen motan yayan nasa yana mashi sannu da zuwa. Motar ya bude ya fito yana amsawa kafin ya daga kai ya kalli part din nasa da kida ke faman tashi yana fadin wanan kuma me suka samu haka yau ? ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1f MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,, 6️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Kai Abubakar ya kawar gefe daya alaman baima saureshi ba alokacin nufar part din yayi ya fara dukan kofan cikin hasala nocking ukku yayi masu kyau cikin hasala hakan yasa Asmau ta daure ta fito tana fadin ana zuwa kafin ta tsaya tana tambayan waye ? Ke bude min kofa nine jin muryanshi yasa ta bude kofan da sauri gami dayi masa sannu da zuwa dan kallon second ya jefa mata ya gane daga barci ta shi a lokacin ke nan har sun shiga barci. Ciki ya shiga yana fadin wanan kidan haka fa kamar gidan yan kwaya batayi magana ba don haushin da taji da dan cikinta an hanata shakat yazo kuma zai tsareta da tambaya ? Wurin fridge ta nufa ta dauko mai goran ruwa ta nufoshi dashi bai tsaya karba ba kai tsaye dakin Nusaiba ya nufa ya tsaya daga kofa yana daga labule. Kwance ya hangota tayi rub da ciki tana barci sai kanta gwigwiyye da hula ya zame suman kai yayi wani tsatsaye tsirma,tsirma dashi yaja tsuki cikin takaici. Takawa yayi zuwa wajen da kidan ke tashi yakai hannu ya kashe kidan duk da hakan bata motsa ba hakan yasa ya kai mata mugun maka a tsakiyan bayanta ta tashi firgice tana fadin wani dan ,,,,,,,, Ganinsa yasa ta soma kame kame tana fadin umm,umm sweet J dama kana hanya ashe shine baka sanar muna ba ? Fuska a murtuke yake fadin wanan kidan na meye haka ke wata irin yarinyace Nusaiba baki ganin kina daukan alhakin sauran jama,an gida ? Ke shadaniyar inace wai kina yar musulmai da daren nan zaki kwanta min da kida haka a cikin gida kamar gidan disco don rashin tauhidi a zuciyarki ? Aiko kira,a kika saka ba zaki kure volume dinsa haka ba don gudun shiga hakkin wani saidai ki kunna iyake. Daga hakan ya juya ya fita inda ya hango Asmau a tsaye inda ya barta da ruwa tana jiran fitowarsa daga dakin abokiyar zaman nata. Karba yayi kafin yayi niyar zama saman kujeran dake tab da kayan wankin Asmau data nado waje kwanan su sunkai biyar a wajen bata kwashe ba tana kuma kallon kayan a wajen. Tsuki yayi ya fasa zama yana maijin wani irin zafi a zuciyar shi ya nufi hanyar fita part din saidai yana fitane yaga alaman part din duk an kashe wuta ke nan masu part din sun kwanta haka ke nufi hakan yasa ya juya zuwa wajen motarshi daya bari bude bai dauko komai ba sai rufe ko ina da yayi har gidan ya duba yana da tabbacin Abubakar ya rufe ko ina a lokacin yasa ya koma part dinshi kai tsaye wurin iyalinshi. Kallon takaici ya tsaya yana karewa falon dake hargitse zakice ba mata biyune ke rayuwa a part din ba babu inda baida miskila don da gani falon nan bai samu shara ba na tsawon kwanaki . Dama sai ya sanar dasu ranan zuwanshi maigirki takan garje tayi dan kwaskwarima gyaran sama sama don sunsan sam baya son kazanta yanzune da ya iso zai soma fada balle wanan zuwan dayayi masu na bazata babu sanarwa. Don haka babu zancen gyara a wajensu koda ya shigo rasa mai zaiyi a falon yayi ita Asmau itace ta mike zuwa part dinta ta shiga gyara gado tana kawar da kayan data tula a ko ina dakin. Don ta dara Saiba kazanta gaskiya ita dai saiba tana da garjewa ta gyara jikinta da inda zata kwanta amma wanki da sauran aikin gida sune aiki a wajenta. Baicewa Saiba komai data hakkince saman gujera tana jiran taji me zaice dasu ko kuma taga inda zai shiga ya kwana duk da tasan in zancen gaskiya za abi wurin Asmauce zai shiga ya kwana tunda itace tayi girki a ranan sukaci. Dama ance mai mata fiye da daya kullum a cikin lissafi yake don gudun fadawa ga halaka saidai wanda baida tsoron Allah zai iya dulmuye gaskiya yayi son ransa. Donshine Jafar kai tsaye don yabi lissafi tun a hanya ya gano dakin da zai sauka kai tsaye ya nufi bangaren uwargida Asmau wace ya samu tana shimfida zanin gado don shi. Sam Saiba bata ji dadin hakan ba yana shiga ganin ko dan zama baiyi sunyi yaya hanya ba bai bata lokaci ko kadan ba sai taji ba dadi sam a ranta ta mike a cikin fushi zuwa dakin ta. Yana shiga ya tsaya a kofa ya harde kafan shi a waje daya yana bin Asmau din da take aikin gyaran gadon a gurguje da kallo a cikin mamaki. Ta jawo room freshener ta fesa ko ina har zuwa bayi kafin ta juyo gareshi tana dan sakin murmushi tace dashi bissimillah . Ajiyan zuciya ya sauke kafin ya motsa a yadda yake ya tako yana balle aninaiyar rigansa cikin daure fuska tunawa tayi da tabar towels din da yake amfani dashi a wajenta waje hakan yasa da sauri ta nufi falon da bakowa sai hasken wuta da aka a kunni ta nemo tawul din ta kashe ta dawo daki tsaye ta sameshi a bakin bayin tawul din ta mika mashi bai karba sai sunan ta daya kira. Da Asmau ta yaya zanyi amfani da bayin nan don Allah komai a kazance ke wata irice saboda Allah ace mace ba tsabta ko kadan kedai baki kaunar ki tsaya ki gyara koda muhalinkine saboda Allah ? Ai bansan zaka dawo ba shiyasa ban gyara ba ta fada a sanyayye kallon takaici yai mata kafin yace au sai zan dawo ke nan zaki gyara ashe ? Bata daiyi magana ba don tasan jafar yana da bala,in hakkuri da halayensu don da wanine yadda yake dan gayun nan dashi daya anji kansu a kullum amma haka yake shanye takaicin su a zuciyarshi. Abubakar a bangareshi haushi da takaicin yayan nasa ya juya zuwa dakinsa dashi ya rufo duban lokaci yayi a jikon wayasa shadaya bai rufe ba a lokacin haka kawai yaji yana son kiran layin Yanda ya gwada ya gani ko zai shiga. Saidai ya tsaya yana wasi wasin kasan zuciyashi ya kirane ko yabari da safe baijin zai iya hakan yasa ya danna kiran Allah da ikonsa kuwa yaji layin ya shiga kai tsaye ta soma kira. Har ya debe rai da daukanta sai gashi ta daga ta dauka da sallama muryanshi taji yana fadin baki barci ba ke nan ko kuma nina tayar dake daga barcin yanzu. Sautin murmushinta yaji tana fadin amincin Allah ya tabba bata a gareka kun sauka lafiya ko kuna hanya ban zata akwai layinka cikin waya ba ai sai yanzu daka kirani. Ke nan baki duba wayan taki ba ko gaskiya ban duba ba kasan mun wuni aikin gyaran kaya yau da kula da dabbobin baffa da suka wahala a wajen tatsansu da mukai tayi a yan kwanakin nan. Au ashe dabban kayi wahala itama sai yaji tayi murmushi tace halan ba rayuwace da ita ba yadda mu yan adam muke wahala ai itama rai gareta don haka sai mun kula dasu sosai don ba karamin alheri suka kawo muna ba a rayuwa. Sanadin kayan da kuka saye muna na samu baffan mu yau har girki yasa mukayi akaci aka koshi a gidan ko sallah albarka a yau din nan. Yadda take maganan yasa bai katseta ba don yana fahintar wasu abu daga cikin zancen datake ta zubawa din a lokacin duk shi bamai yawan son surutu bane amma sai ya biye mata. Ya fahinci rayuwan yaran a can yana cikin wahala a hannun yan uwan mahaifinsu da zaman su ya koma hannunsu. Suna a cikin matsi da tsangwama babu freedon sam a tare dasu kamar sauran yara karatunsu da sukayi ya tashi a banza yanzu wace takai matakin karatun Nurse a yanzu ta koma tana tatsan nono a rugga saboda rashin gata. Da wanan tunanen ya kwana a ransa har gari ya waye duk da ya dan samu runtsawa kadan saboda gajiyan dake jikinshi a lokacin na bin dogon hanyan da sukayi tafiyan zuwa da dawowa haka. Don shine bai fito ba da safe da wuri saboda bayan sun dawo daga sallah ya koma ya kwanta barci sai zuwa shadaya saura ya mike ya shiga bandaki ya watsa ruwa tare da brush din bakinsa ya fito. Washe gari mama Dubu tana kitchen tana hada masu breakfast sai jin sallaman Jafar din tayi a kofan kitchen din amsawa tayi tana mashi kallon mamaki da yaushe ya dawo. Ya fahinci kallon da uwar ke masa yasa yace na dawo tun jiya da dare ai mama kun kwanta a lokacin Abubakar na samu ya bude min gida na shigo. Malam meyasa baku tsoron tafiyan darene wai don haka take kiransa da malam Jafar kamar yadda uwaye da dama sanadin marigayi malam jafar suna kyautata zaton diyansu su samu irin albarkansa suke kiran yayansu da malam jafar. Ai ba da dare sosai na shigo ba mama wajajen shigowa kaduna dare yayi min na shigo nan wurin sha daya saura na darene ai. Allah ya kyauta nan ya fara gaida ita cikin ladabi kafin muryan iya ya ratso tana fadin wai Jafar ne da safen nan haka ? A nan ya kwana Iya mama ta fada ahawaraki shine baka tayar dani na karbi jakkar tsaraban taka ba ka mikawa marasa hankalin matanka ? Iya ko allura ban shiga dashi ba gida sai makullin motata kawai ko yanzu kina iya karban jakkar kafinsu ya fada yana nufar iya din itama juyawa tayi zuwa wajen kujerun falon ta zauna shima haka ya zauna yana fadin. Habu bai shigo bane ko har ya fitane zuwa wajen aiki mama ta karaso tana fadin anya yau zai shiga kaduna kuwa yadda suka kwaso gajiyan nan suma. Gama tsaraban da yayo muna nan ko kwancewa ban samuyi ba har yanzu Iyace tace badai abinda zai lalace a ciki ko ? To ina na sani iya ai kinga baiko tsaya muna bayani ba yafita da sunan zaije ya dawo har yanzu bai shigo ba kuma karna taba ya kasance ba nasa bane duka naga abinda yawa hakane ? Ba zai shigo dasu nan ba ai idan ba nasa bane kinsan halin Habu ai mama Jafar ya fada shi nake nema ya kamin mu fito da kayan danazo dasu ashe ba tashi ba har yanzu. Kuna da kokarin yaran nan saidai kai Jafar matsalan matan da Allah ya bakane sai addu,a mata ba sanin ciwon kai ace har yakai don rashin hankalin kishi irin nasu yar nan ta watsawa uwarku abinci a jikinta abinci mai yawa don wullankaci su wullakantashi haka wuein bakin kishin su na tsiya ? Abinci kuma suka watsamawa Iya kardai zancen da Nusaiba ta kirani ke nan shekaran jiya take son min ban saurara ba don dama shiya kawoni garin nan jiya tunda naji ta ambaci sunan mama a cikin zancen ta hankalina bai kwanta ba na taso. Kaiko dai akan wanan zaka taso haka zuwa nan iya shegen yaran nan ne kawai don batama san da ina tafe ba ai kodata jefowa yar uwa abincin sai saman jikina ya dira ya zube banso iya ki fada mashi ba ai tunda anyi ya wuce ko tun a wanan ranan indai zasu gyara su gyara don ba,a wasa da abinci. Mama indan iya bata fada min ba waye zai fada min bayan don haka take zaune damu gidan idan suna abu ba a tsawata masu watarana ai za a samu sun illanta kawunansu a dawo ana ganin laifin ku daga baya. Zasu aika tundai wanan mai zubin yan ruwa da take daukan kanta wata tsiya banda karyan banza da ci mutunci babu abindata koya a duniya na kwarai Iya ke fadan wanan magana a cikin hasala. Sallaman Abubakar falon yasa suka sake zancen ya shigo suka shiga gaisawa da juna kafin ya sanu wuri ya zauna mama dubu ta jefo mai tambaya tana fadin kayan can dakazo dasu fa Habu ? Juyawa tayi ya kalli wajen da mama din ke kallo kafin ya dan bata fuska yace daga can nazo dasu meye a ciki Jafar ya tambaya ? Mikewa mama tayi ta isa wajen jarkan da akaiwa nadi cikin buhun irin na da da ake amfani dashi sai wasu kwanduna da aka rufe da ganye zakice gorone a cikinsa aka rufe ta shiga budewa . Yayin da iya da su Habu din suke hiran yanayin kasan Cameron da irin mutanen dake rayuwa a cikinsa muyan mama dubu sukaji tana cewa Habu wanan ai ba karamin kaya bane ka dauko ? Meye a ciki mama Jafar ya tambaya yana mikewa mama ta juyo tana fadin wallahi nono ne da danyan madara wanan kuma kindarmo wanan wara da ake kirada (wagashi ) warar fulanice ta ainihi da aka sani da ainihin nonon kindarmo za,aita dafashi har ya cure a waje daya kana a dauko buhu ko abin tsama a matseshi yadda akeson girmansa saidai nasan akwai sauran fasahan wanan abin da ban fada ba a bayani amma dai nonoce zalla ta kindarmo sabon tatsowa ake wanan wari din dashi wanda akecinsa danyensa ko kuma a yanyankashi kamar nama a sayo da mangyada ko manja. Shi wanan abin yanzu soyashi za ayi Jafar ya tambaya mama Dubu tace kwarai kuwa sai kace a karo maka idan an soya din ai ana amfani dashine kamar nama zaka iya zubawa a cikin miya a dafa miyar dashi ko kuma ka watsa saman shimkafa kamar nama. Ban taba ganinsa ba Jafar din ya fada nima dai gaskiya bansanshi ba Yaya J , kawai dai naga ana sayane nace nima aban na sayo wasu mama mashi nazo dashi. Mama Dubu dince ta katse su da fadin wanan kuma chikwi nefa Habu sai ta mike tsaye tana fadin amma kasha kudi a wajen nan bari nazo na dibawa yan gida akai masushi a mutuncinsa tun bai tabu ba don in suka kai kwanakin da zanyi a nan suna iya lalacewa. Kallon juna diyan nata sukayi wanda ta fahinci nufinsu tace meye duniya Malam idan kaba wani ya kare idan baka bayar bama karewa zaiyi gara ka bayar din kaci moriyansa can inda bakai tsamani. Ai bamuce komai ba mama zuwa anji zan shiga na gaidasu da yamma sai a zuba na fita masu dashi don naga shi Habu kamar da sauran gajiya a tare dashi. Duk wanan nono shanune a cikinsa ya nuna sauran jarkan dake rufe mama din tace ina gani tana kallon danta habu ko zai masu bayani maimako ya bada amsa sai ya juya ya koma saman kujera a daidai lokacin mama ke fadin ikon Allah man,shanune haka cike har jarka. Kai habu wanan lissafin dariruwan kudi akeyi fa ina kasamo wanan kaya haka kamar na gara Iya ta fada tana mikewa zuwa wajen taga man shanun da aka fada din. Sai fadi take saidai wani lokacin suyan manshanun fulani kamae harace don basu irin suyan mu na mutane gari a saka albasa da gishiri don yayi kamshi haka suke soya abinsu ba komai a cikinsa. Kada kisha idan bai hadu ba Habu kai kaji iya tun bataci ba fara kushe abin murmushi yayi kafin can yace ba manshanu ba ai har mai man shanun zan dauko maki gidan idan ta girka ta baki kada kici tunda basu iya suya ba. Au to kinji abinda ya fada shidai ke nan bafulatanan kasan can da sukaje zai auro sai ki shirya Iya kishi da balatana kuma yanzu. Barni a Iyata da nake yayan hauawan ma gasu gaban mu na kasa gane kansu yara kamar kansu aka fara kishi yara kanana da bakin kishin tsiya irin ta hauka. Ai ba dukansu bane basu da hali iya habu ya fada don gara Asmau ita tasan darajan kowa batawa mutane rashin mutunci ita. Babu gara kana ina suka watsawa uwarku abinci saman jiki ga hijjabin can ta jika yaki fita har yau don iya shige irin nasu . Abinci kuma suka watsawa mama a jikin garin ya haka ya faru mama kai ya jafar wani mataki ka dauka akai yanzu ? Shine nan ka ganni zaune ina son iya tayi min bayanin abindake faruwane sai gaka ka shigo aka kawar da zancen da muka soma. Ai bada sani hakan ya faru ba nan dai mama ta kwashe yadda abin ya faru wanda ta sani ta mayar masu ran yayan nata ya baci sosai da hakan tunda Abubakar yafi daukan zafi akan zancen. Ya dago kai yace mama shine kuma kike cewa a kyalesu har su iya wanan abin kuma a saka masu ido gobe su kara wanda yafi wanan ke nan ko idan an kyalesu. Kaiya ita wanan mai shigar cikin bafa laifinta bane na fada maku yadda zancen yake ya juya wajen dan uwan nasa yace kai kaji bros ya lumshe idanunsa don baida abinda zaice kuma tunda mama ta hanashi daukan mataki akai tace rashin sanine ya jawo hakan yayi hakkuri da matanshi ya dai tsawata masu kan hakan. Gaba daya falon yai shiru saiga Asmau tashigo da sallamanta ganisu haka a zaune yasata dan tsarguwa tana kuma mamakin ganin har Habu da bai faye zama dasu ba yau duk suna tare hat dashi. Sun dai amsa mata gaisuwan saidai ta tsargu duk da wancan kaifin ita bata sashi a zuciyarta ya tsaya mata tunda ba itace tayi laifin take gani. Sai bayan ta gama gaidsune ta dubi mijin nasu tana fadin yaya J an gama breakfast don haka ta taso ana ce masa a cikin unguwa kaf manya suce dashi malam din gidan Sanda . ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1f MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,, 7️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Lokacin da Ya J ya fitar da nasa tsaraban kai tsaye part din Iya yace Abubakar ya kai mashi a can wanan yana daga cikin sallon horon da yake son yi masu a mumuke . Bai tsaya ya karya kamar yadda Asmau ta bukataba gareshi wanka yashiga har yafito duk a cikin kyankyami yake haka ya shirya a cikin wani yadi fari na maza dayasha dinki kayan sun matukar karban jikinshi sosai ga ogogonsa daka kalla kasan bana ranke ranke bane. Haka takalman kafansa baki masu dan igiya daga baya amma ya taushe igiyan da dudugenshi ma,ana bai kaunan saka belt din takalman ke nan a lokacin. Turarensa ya dauko ya fesa a jiki abinka ga farin mutum nan kyauwonsa na asali dake rudin jama,a ga kuma jin dadin da jikin nasa ya nuna tare da wayewa sai hakan ya taru ya karawa jikin nasa ma,ana sosai. Duk cikin yaran mama Dubu ya jafar yafisu haske sosai duk da kaf diyanta fararene masu matukar kyau sosai sun biyo sashen mahaifinsu da yake shima farin bufulatanine daya bar gida tunda karanta don mutumin yolane zama ya kawosu Zaria shida iyayyensa amma komai nasu yanzu a cikin zaria suke rayuwansu da komai don yan bayama basu san gida ba. Part din Iya ya nufa inda ya samu mama tana kwashe dan abincin ranan data dafa masu yayi sallama ya shigo yana gaidasu da aiki nan yake fada mata zai fita yakai wankin mota ya kuma leka kawu dauda don sun shaku sosai da kawun nasa. Kusan duk wani motsin Jafar kawu dauda yasanshi shiya rike a matsayin mahaifi tun ma mahaifinsu yana raye kafin ya rasu. Cikin jin dadi mama take fadin ashe bari a bada tsarabansu saika mika masu daga can yace yayi mama yana zama yake fadin akawo nasu umma na mika masu don har can nake son shiga in gaidasu. Ka kyauta malam abinda zance ke nan ka rigani Allah yai maku albarka ta juya don taje dauko mashi sakon kafin ta juyo tana fadin ina ai matan naka sun gama abinci wajensu ko ? Sam baiji dadin zancen ba amma haka ya daure yace cikin bata fuska mama su ai basu gaj gama abinci da wuri ba banma jin sun dora yanzu gaskiya. Ikon Allah wanan waani irin sakacine da yaran nan miji da ake murnan zuwanshi amma su sam ba hankalin gane haka ai wanan shine kishi na asali ba wanan haukan da sukeyi ba. Yanzu sai ka dawo kaci ke nan yace ko karyawa banyi ba mama saidai idan na fita zan tsaya wani shago nan gaba kadan in karya. Sam malam ba mutuncika bane kana da mata biyu ka koma cin abincin layi wanan zubar da kimar namijine da matansa bari dai inzaka iya cin namu na zubo ma ka dan hada da ruwa. Murmushi ya sake a fuskansa daidai lokacin Habu zai shigo part din don shima fita zaiyi to ga sadauki nan sai in diba maku kuci gaba dayan ku ta wuce zuwa kitchen din kai tsaye. Abunci ta zubo masu plate biyu shimkafa da miya da ganyen kabeji yaji hadi sosai sai nama yanka bibiyu a cikin ko wani plate ta direwa kowa a gabansa. Yaso ya basar amma aiya muda ya busar da iska yana fadin yaya naga plate biyu mama matansa fa basu ciyar dashi bane halan ? Yayi kamar baiji mai dan uwan nasa ke fadi ba sai wayan shi dayake faman dakila cikin basarwa kafin ya aje yana jawo plate din abincin zuwa gabanshi. Mama Dubu data dawo dauke da goran kunun ayya sai ledan pure water ta aje Habu ya dago yana fadin is not right mama yana da mata a cikin gidan nan yazo nan kuma yana ci muna abincin mu. Murmushi mama din tayi kafin takai zaune tana fadin Habu dole ya kama in bashi son da yafita yana tonawa kansa asiri yaje saye shago gara kawai in diba mashi yaci a nan din. Duk zancen da sukeyi Jafar sai aika abincinsa yake a cikinsa Abubakar din ya dan kalleshi ya jawo plate dinsa shima ya soma ci kafin can ya dago yace. Cikin gari kayi ina son nima zan fita ka saukeni saiga iya ta fito daga daki tayi wanka ta sauya tufafi yadda takeyi idan mama tana gidan tare dasu ka,idace wanka a rana gareta . Habu ai gara ka bari yaci abincinsa a nan kada yunwa ya illantashi nima tsohuwa ba iya cin abincin yaran nan nakeyi ba balleshi matashi haka da harshensa yake da kaifi a yanzu. Amma iya gaskiya ba zasuji dadi hakan ba idan sungani shiya kamata ya tsawata masu koma meye su gyara amma haka gaskiya bai dace ba karshema zasu iya dora laifinne ga mama. Kamar yadda kace din ya kara tsawata masu dai hakan yana da kyau amma wa yan nan shedanun ba kan gadone dasu ba balle su gyara din. Tsuki Abubakar da takaici ya kumshi yaja goran kunnun ayya Jafar ya mika hannunsa ya dauko ya kafa baki ya korawa cikinsa kaf ya aje yana gyara zama yace. Ita Asmau ki barta da kazanta da saurin fushi yanzu haka dakinta wallahi iya baya shakuwa don kazanta kayane ako ina watse a dakin kamar wata wace ta tara yara goma. Itako Nusaiba aikinma bata san kansa ba barta kawai da in za a fita sai kice zakizo gidanta ki samu abin kwarai duk babu mai tsaba a cikinsu ga rashin kunya kamar tashin tasha bakinta ko yaushe baya gajiya. Nayi mamakin hada kawancesu da Asmau don ita ba yawan son maganane da ita ba amma ta iya zama da ita haka da wanan rayuwan na banza. Sam ban taba zaton haka rayuwanta yake ba harna yarda na fada tarkonta dariya sosai Abubakar ya kwashe dashi jin abinda dan uwan nasa ya fada inda sabo ya saba da halin Abubukar na kyata don a haka suka taso dashi. Daga can kusurwan kitchen mama ke fadin ina aika diban ma matanka nasu tsaraban ko kada azo a kwshe a nan ? Kafin yai magana Iya tace zai shigo dashi baikai masu nasu bane ai baya kawo nan baki daya yakan fitar masu da nasu tuncan hakan yasa taci gaba da fitarwa kawu dauda da abokan zamanta indai ankai can su raba a tsakaninsu . Saida ya mike yake fadin gari iya na sawowa shi don kune masu son jan garin kwaki da manja aina gani malam saida nayi tunanen hakan Allah yayi albarka amma wanan ai yayiwa Iya yawa bari a dibawa mutane suma susa albarka. Baiyi magana ba don ko yayi tunda mama tayi niyar hakan saita diba din donshine basu tsaya bata bakinsu ba ta fitar da wanda zaikai gidansu dana gidan kawu din Abubakar ya tayashi kwasa zuwa cikon mota saida suka cika mota fam suka tafi. Gidansu ya fara tsayawa aka sauke kayan zuwa cikin gida kafin su shiga don gaida mutanen gidan shigansu Abubakar ya kalli part din mahaifiyarsu dan kwana biyun da tayi wajen yai kura an rasa wanda zai share mata shi don mugun hali irin na dan Adam. Da ace mama mutuwa tayi ashe gidan ma ba zai basu sha,awan shigowa bake nan kilama wanine zai gaje wajen ya zauna aci albarkacinsu. A gurguje aka gaisa suna masu sannu da hanya tare da godiya kan tsaraban da aka kawo din agaida mama da dai sauransu. Basu tsaya ba sukai sallama suka fice daga gidan kai tsaye suna fita inna ta kalli yar uwar zamanta tace mena fada maku yaya indai yayan Jushuce sai ta aiko muna dako kwarane a gidan nan yanzu ji wanan kaya don Allah haka. Tsuki mama taja tana fadin meye a cikin ledojin nan sabira bude muga abinda ke ciki inda kowa na gidan ya fito ya tsaya ganin abin arzikin da aka shigo dashi din don basu yarda a shiga ciki dashi don gudun rage masu kwantiti dinsa da suka san za a iya hakan don an sabayi masu hakan kuma ba daman suyi magana a kai. Mama duba wanan abin ta fada bayan ta bude ledan inna takai ido ta kalla tace nasan wanan sai yayan jushu ita kadai takai can a gidan nan. Kaico waike karima baki kishin kankine wanan katobara haka da nuna zalama a filin Allah kamar wata mayunwaciya dake ? Nidana nuna a fili za,acewa hakan ba amma kowa anan ai yana so don ban taba ganin wanda akabawa ya marya ba a cikin mu. Nidai don Allah ku bari sabira ta fada cikin dan hasala ga iyayyen nata dake son nuna halinsu fadane akulum sai anyisa kuma a shirya haka ake zaune a gidan tsakaninsu. Mama Dubuce yana da wuya kaji harshenta a cikinsu tunko mijin nasu yana a raye kafin ya kwanta dama haka halinta yake ita bata son yawan hayaniya . Sunyi mamaki kwarai da irin abinda mama Dubu ta aiko masu dashi nan gidansu su raba ke nan yana can gidansu baja baja ke nan tunda har ta iya basu haka ? Kai tsaye ya Jafar motarsa yabada wanki a nan kasan unguwarsu ya hau mashin zuwa gidan kawu Dauda da sakon tsarabanshi cikin buhu. Ya samu baba din ya fito zai fita ganinsa hakan ya dakata yana fadin malam kaine tafe yaushe garin ? Yace jiya da dare kawu yana fada yana kokarin dauko buhun da mama ta bashi ya shiga masu dashi cikin gida kai tsaye nan suka tsaya gaisawa da matarshi tana mashi yaushe gari ? Sai bayab sun gama gaisawa yake fadin mama tace a shigo da wanan au ka biya ta gidanta ke nan kawu ya tambaya yace tana wajen iya ai. Kace tayi tataki zuwa kwasan lada nimafa yau nake zancen naje nagonasu na kwana biyu ban lakasu ba kawu ya fada ya kara da yaya wajen iyalin naka suna lafiya Jafar ya bashi amsa. Fita sukayi tare da kawu din dake tambayanshi baizo da mota bane wanan karon yace nazo da ita kawu tana wajen waki nakaita can tudun wanda. Ai hakanma na dakyau wuri suka samu suka tsaya daga kofa kawu din ke fadin naga kamar kazo da magana a bakinka ? Yadan kara rankwafawa kafin ya fuskaci kawu yana fadin nazo dashi kawu shawara nazo nema akan wani harka da nake son fadawa shine nace barin nemi shawaranka muji indan hakan zai yuyu ? Nan ya kwashe yadda sukayi da Meiambe ya fadawa kawu din shiru kawu yayi inda Jafar din yaga yana kokarin tsugunawa kasa shima yabi sahunsa suka kai kasa din. Can yanisa yace tau malam Jafar bakin wanan abin ba son hanyar karuwace saidai ina tsoron harkan kudi a yanzu . Don rikon amana haka abune dake son taka tsantsan duk da banda shamakin hakan a kan Jafar saboda kai ko ince har yan uwanka kuna da natsuwan zuciya sosai kan duniya don gwargwado kuna da kamun kai har yau Allah ya tsare ya kara karewa babu dan daya taba dauko muna magana a cikin ku. Don haka Jafar ba zanki shawaranka ba tunda hanyace ta samu amma shawaran da zan baka shine kafin muyi komai ya kama mu binciki idan ba wani matsala ka bari zanje gidan yaya sale na kusfa na fada mai a roka muna Allah a cikin lamarin . Saida Jafar din ya sauke ajiyan zuciya kafin ya karawa Kawu haske akan yadda abin zai gudana da kuma irin yadda yake so shima a ta bangarenshi abin ya kasance kawu yace ya fahinta insha Allahu zaiyiwa yayansa magana zaiji komai da yardan Allah kafin ya tafi da haka suka rabu da kawu din kowa ya kama gabansa. Suna fita daga cikin gidan nasu ya kama fabanshi yafi ganewa wanan unguwan daya taso a cikinsa don ana kowa nasu yake wancen wajen a yanzu ya zama kamar sabon wajene garesu. Abubakar din shagon sanusi ya nufa sukai daidai da sanusi din yana shagon nasa ta sayar da waya a kofa ya tsaya bai shiga daga ciki ba duk da ya saba shiga din amma a yau daga kofa ya tsaye. Sanusi yaji dadin ganinsa sosai sai faman washe baki yake yana fadin kai mutumina kace min har kun dawo ashe tafiyan bamai jimawa bace dama ? Tafawa sukayi suka soma hiran bayan rabo inda shi sanusi din ke bashi labarin abinda ya faru cikin unguwa sai yaga hankalin Abubakar din baya tare dashi lokacin sai waya hannunsa dayake faman dannawa hankalinsa ya dauke dashi. Yasan halin abokin nasa don haka ya bashi lokaci tun safe yake faman kiran layin ta amma baya shiga sai kuma hakan ya daga mai hankali a zatonsa an karbe wayan ne don yadda yake tunanen suna cikin matsi akan hakan. Dafashi sanusi yayi yana fadin lafiya kake kuwa abokina naga kamar kana cikin damuwa niko naso na gama baka labari in fada ma riban da aka samu bayan tafiyan ka. Barshi kawai zuwa gobe idan nashigo ya fada ya juya ya soma tafiya hankali tashe har lokacin yana gwada sa,anshi ga kira ko zai shiga. Garba sadauki garba gagare Abubakar mazan fama irin ku biyu ke gyara gari kwana biyu ashe ka dawo daga tafiyan ? Kai ya daga a hankali ya kurawa matar ido yana son tuno ta kwalan kanta yasa yayi saurin ganeta ita matar ranan da sukai tafiya data shiga da maciji gidansu. Fuska ya tsuke a waje daya sai dai duk da hakan saida yaji kawai ya gaida ita don baisan wacece ita din ba da take faman bibiyan shi tambayan daya fara yiwa kansa kenan a zuciyarsa. Baabba ina wuni ya fada sai tayi murmushi tace dashi kada kaga na kulama yarona akwai abinda nake son ka sani game da rayuwanku na fadama ka fada wa mahaifiyarku inda nake ko baka fada bane yasa bata zo ba ? Yanzu haka naga hankalin ka a tashe yake don baka samu mutumiyar ka bako kada ka damu zuwa yamma insha Allahu ka gwada zaka sameta. Saidai ka kula da amana taraiyanku akwai nasara don kusan ince ka tsira daga sherin magautanka habu. Saidai yan uwanka amma a gaskiya in mahaifiyar ku batayi da gaske ba za,a dukar daku gaba dayan ku . Ka maida hankali akwai alheri da nasara daga wanan yarinyar daka hadu da ita acan saidai iyayyenta mutanen banzane shine kadai matsalan da zaka dan fuskanta. Habu yau fiye da sati fa ina cigiyan ka garin nan muryan Sabi,une abokin shi yake fadan hakan ya juya yana cewa sabi,u yaya nima ai naso ganin ka sai na danyi tafiya ina zuwa ya fada ya juya girin wanan matar don yace yagode. Saidai wayau baiga kowa a wajen ba cikon mamaki ya juyo ga abokin nasa sabi,u yana fadin ina wanan matar tabine sabi,u ? Wace mata ke nan fa sabi,un ya tambaya matar daka samemu mana magana a nan mana naga kamar nan tabi ya fada suka juya gaba dayansu har sabi,un suna kallon hanyar cike da mamakin ta. Ikon Allah kasantane ya girgiza kai alaman a,a amma dai ranan tashiga gidan mu anan taji sunana ta rike sai ya canza topic din don ba zaiso ya matsa mai da tambayan daya fara ba yasan halinsa bakinsa baida sirin rike magana. Yanzune ma zai iya juya zaicen zuwa wani tsiga ta daban ya dauko mashi zancen magana da soka soma dashi a ranan zasu hada kudi su sayi wani shago anan cikin unguwa suba da haya. Ire iren hakan yanayi sosai da abokansa na kut da kut dama yan zaria basu da wasa wajen sana,a rigima da naci kawai kanawa suka fisu 😍. Har suka rabu da Sabi,u a wajen sallah yana tunanen zancensu da wanan matar dake yawo da kwalla tana tallan maciji a cewarshi. Saidai abinda ya daure masa kai shine zancen data soma ta katse ta yaya tasan cewa yana gwada kiran layin Yanda tun safe bai samu ba. Gabanshine ya fadi lokaci guda wanan wata irin matace take kokarin bibiyan rayuwatane wai meyasa ta lake min hakane ? A iya tunanesa baiga alaman tana nemam wani abu a wajensa ba tunda bata tsaya karban komai garesa ba yauma amma kuma me take son fadawa mamane wai ? Data matsa tana son yin magana da mama me zata fadawa mama din akan shi shirme ya dauki zancen da sallon yaudara irin na mutane. Wata zuciyace ta bashi shawara ya gwada abinda tace mana ya gani idan hakan gaskiya har yakira yanda ya sameta da yamma to akwai kamshin gaskiya a cikin zancen ta ke nan yake fadawa kansa. Zama ya gyara yana fadin abu sai kace almara meye hadina da wanan matar da take son shiga min rayuwa ya akayi tasan dana hadu da Yanda ? Gaskiya dole ya sanarwa mama barazsn matar nan a kanshi kada sai abu yazo ya faru dashi ba yadda za ayi a lokacin yace zai sanar da ita daga baya. Anan cikin unguwar yai sallah magariba da isha,i yana fitowa kuma suka dauki hanya da sanusi daketa kokarin masa bayani kan shagon nasu na saida waya da kayan wayoyi din wanda ba kowane yasan da kudin habu a cikon shagon nan ba sai iyayyensu kadai suka sanda wanan. Kusan lokaci guda suka iso gida da yayansa do zakice tafiyarsu gudane yadda suka shigo din shi jafar part dinsa ya nufa shi kuma habu ya tsaya nan jikin motar yayansa yana gwada kiran layin Yanda da son ya kure karyan wanan matar don ya samu madugaran yi mata kashedi akansa. Ga mamakinsa yana kira kiran ya shiga mamakine karara a fuskanshi yaji ta dauka tana sallama da muryantan nan mai nuna sanyi hali irin nata. Kamar kullan yadda take fadan amincin Allah ya tabbata a gareka hakane ko lokacin ta fada gareshi a cikin sanyin murya daya sakashi cikin wani irin yanayi shauki. Tare dake sahibata ya fada ba tare da yashirya furta hakan agareta ba sai yaji sautin murmushinta na jin dadin abinda ya fada a gareta da Sahibata. Tun safe nake gwada kiranki baya shiga da fatan dai lafiya hakan ko take bashi amsa da fadin lafiya kalau kasan da zaran bakwai yayi muna daji muna kiyon dabbobin baffan mu nida sister . Duk da kuwa a kwai maza da yakamata suje kiyo amma mu baffa ya zaba da mu dinga fita mashi da shanunsa wajen kiyo acewarsa don mu koyi wahalan ruga da bamu taso a cikinsa ba a baya. Shi wani irin mutum ne da zai yanke hukuncin hakan yasan abinda gobe zatayi a kanku hira dai sukayi sosai dashi wanda a cikin irin hiran yake tsuntan wani abu daya shafi rayuwansu na baya ita da yan uwanta. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1f MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,, 8️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Yanda wace akafi sani da maria kamar yadda aka rada mata zanen sunnanta tun haihuwanta inda sunan nata ya samo asaline ga sunan kakarsu kasancewar hakan da uwar bata iya kira saboda sunan sarakuwartace sai ta juya sunan a cikin harshen yarensu da yan mata. Dama sunan da mahaifiya ke kiran da dashi shine mafi karbuwa a bakin mutanen dake kewaye dasu don suma da wanan sunan zasu dinga kiran yaro saboda agane. Yanda yariyace natsatsiya ga ilimi da Allah ya bata na addini dana boko wanda sanadin samun hakan zaman da mahaifisu yayi a Abujan Nageria ne dasu. Inda yake sana,anshi na sayar da kayan masarufi wanda daga baya ya dan samu kariyan arziki saiya koma gadin gidan wani dan majalisan taraiya mutumin maiduguri. Zamane na amna a tsakaninsu don matarshi mutumiyar arzikice dama ance silan gyaran gida yada a wajen mata don ko hjy itace tasa Yaro ya dauko iyalinsa ya dawo dasu gidansu a inda suke wani unguwa a cikin masaka. Zuwan yairo birni da kuma kariyan arzikinshi kuwa ya samo asaline daga kiyayya irin na yan uwa daya taso a cikinsa kusan bafulatani da riko haka kuma duk bafalatin asali suna da wani hanya irin ta kaucewa da suka rike dimun dimun a zuciyarsu wanda ba kowane zaisan wanan ba sai su yasu yasun su yan wajen. Zaki gansu adaji suna rayuwa kiyi ta tunanen ko basujin tsorone wai idan kika zauna kikai nazarin fulani da kyau koda a birni suke kuwa zaki fahinci asalin fulani yana da wani boyayyen siri nai kama da surkin jinnu a cikin halaiyansu. Wanan zancen ba karya bane haka zancen yake duk da fulanin yanzu ba damuwa da irin abubuwan haka sukayi ba suma don wayenwa kai a yanzu. Zakiga tsofin fulani ba kasafai zasu iya barin daji ba saboda anan Allah ya halicci rayuwansu tare da dabbobinsu da tsuntsaye da sauran namun daji dake kewaye dasu da kuma sauran abin boye. Kiyiwa kanki tambaya ke mai karatu su basu tsoron dajine wai ko basu tsoron dare da abinda ke cikin darenne wai wanan amsan yana ga balafulatanin asali daya san kansa wanda bai iya ruwa ko a cikin mutane sai gefen daji zai zauna shi kadai. Irin hakane da Allah ya tsamo Yairo daga ruga don yawan tsagwaman yan uwa ya dawo birnin ya fara sana,a sai suke ganin ai yaro ya lalace a yanzu ya zama dan duniya. Abu ga Allah haka sukai ta jefo masa asiri tun bayan da sukaga da gaske yaro keyi da zaman birni tunda har yazo ya dauki matanshi da tsohon ciki zuwa birno to tabbas zaman Yairo birni ya tabbata tunda har ya iya daukan matarshi dele suka koma birni da zama. To tanbada ya hau kan yairo ke nan a yanzu ka,ida wanda suke ciki daya zai tattara dan sauran abinda ya bari ya hade da nasa na tsawon wasu shekaru idan bai dawo ba sun zamo nasa ke nan ladan kiyo. Haka baffa sa,idu ya tattara sauran dabbobin mahaifisu ya hade da nasa ga bakar asirin dayai ta jefawa Yairo din wanda gida ya fita ransa baki daya har yakai yayi haihu hudu duk bai tako gida ba. Allah ya rufa mashi asiri rikon amanansa yaja mashi farin jini sosai ga Alh da iyalinsa da suka rikesu amana a tare dasu da farko zuwa yake shi kadai sai bayan wata yace zai tafi dubo iyalansa. Ranan Alh da hjy ya samu a tsaye yazo sallamansu akan yana son ya dan leka iyalinshi don bashi dayane maigadi ba sukan shirya a tsakaninsu sai mutum daya ya tsaya ya fake gida har dayan ya dawo irin hakane yazowa Yairo din . Kudin mota Alh ya bashi yana godiya har ya dan daga hjy Falmata ke fadin wai kai Yairo har ina iyalinka suke zaune kai din mutumin wani garine wai ? Ya dawo ya gurfana ya soma fadin hjy ni mutumin nan Gembo ne nan wajajen tasanwa kasan Camero saidai yan uwana da kowa nawa sun ketara yanzu suna kasam ccamero din da zama. Iyalina kuma suna nan masakane zaune inda na kama haya a nan na barsu suke zaune nan masaka na Abuja ko ince nan Nasarawa yace kwarai hjy nan na kama masu haya suke zaune don yafi min kusa da zuwa can gida. Matarka dayace yara nawa yace dayace hjy da yarinya daya da take goyo kallon mijinta tayi don a gaskiya suna jin dadin zama sosai da yaro mutum ne mai mutunci da kamun kai sosai mutumin. Ai ina ganin Alh basai na dako wata yar aiki ba indai matarsa zata iya min komai ai gara ya daukota nan tunda ga wuri zaifi sauki. Yafi muyi tafiya mu bar yaran nan a cikin zullumi ko yaushe ina ganin haka yafi ai ko meka gani kai yaro ? Hjy nikan in anyi min haka ai banda bakin godiya a hakan Allah ya kara daukaka da nisan kwana nagode kwarai Allah kara rufa asiri amin hjy din ta fada. Ta dora da fadin yanzu kaje duk shawaran da kuka yanke sai muji ko mu ganku tare ya kara mata godiya donshi mijin yana ta faman amsa waya a lokacin. Wanan ne sanadiyan zuwansu zama gidan Alh inda hjy taji dadin zama da Ashatu mata mai kirki bata da kiuya ga tsabta da mutunta kowa har yara . Jin dadin zaman nasu yasa hjy batayi kyashin sakasu boko ba tasa aka hada Yanda da yaranta suna zuwa makaranta haka kuma ta islamiya da suke zuwa a tare da ita. Wanan yasa yaran suka taso cikin jin dadi da natsuwa ba zaki taba sanin su din yayan tugga bane don basu taba sanin wani abu rayuwan ruga ba. Sun dauka Alh dan uwan mahaifisune don su kadai suka sani a danginsu lokacin kwatsan ranan mahaifisu ya samu labarin rasuwan tsohonsu hakan yasa ya roka da zasuje gida har yaran. Ba jin komai hjy tasa aka kaisu har garinsu cikin motan gida wanan zuwan shine yayi silan komai garesu. Don kuwa mahaifisu bai dawo gida ba saida dafi da aka jefashi dashi inda ya dawo yayi ta jinya daya zamo ajalinsa akarshe. Anan babban asibitin Abuja Allah ya dauki rayuwansa ganin halin da iyalin yaro suka shiga yasa Alh da hjy suka kaisu gida da kansa da niyar suje suyiwa yan uwansa ta,aziya su dawo dasu daga baya. Saidai tun zuwansu budan bakin baffa fara tambaya yayi ina dukiyan dan uwansa daya tara abuja din ? Mamakine ya kama Alh yace shidai a saninsa baisan Yairo yana da wani dukiya ba yasan dai duk wata yana bashi hakkinsa kuma yaransa kaf sun dauke masu laluran karatunsu suke biya shida matarshi. Karshe dai ba a rabu da dadi ba tsakaninsu da Alh saima sukace zasu bar iyalansa a nan don za a dinga zuwa gaisuwa ana tambayansu daga baya in komai ya lafa zasu nemesu. Sukan tunda suka roko ko yanda dake shirin zana jerabawa a bari suje da ita sukaki suka fahinci ba su son yaran su koma hannunsu ne. Haka suka tafi suka barsu a wajen yan uwan mahaifinsu karshe da suka gano ashe dukiyan da suke zaton na yairone ba nasa bane ashe sai haushin hakan ya koma wajen yaransa. Nan wanan baffan nasu ya rufe ido yana fada yana fadin indai hakane dole su biyasu hakkin kiyon da Yairo ya gudu bai karasa ba ya koma birni da zama don iyalinshi suji dadi . Wanan dalilin yasa suke zaune a hannunsu cikin ukuba da tsagwama ga yunwa da wahala daya juye masu kamaninsu a lokaci guda. Dan wayan dataje dashima garin baffan ya karbe ya sayaryan suturunsu duk sun koda a karshe dole suka koma amfani da irin wanda mutanen wajen suke amfani dashi suka saje dasu baka gane sun taba rayuwan Abuja a baya. Irin wanan labarin da Yanda takan ba Abubakar a cikin waya shine suke tsuma zuciyarshi yana jin yana son ya taimaka masu duk da yasan karfin sa baikai ba amma zai gwada sa,anshi ya gani ko Allah zaisa a dace. Da haka kuma ta kara shiga ransa sosai yake matukar jin ko ta halin kaka saiya taimaki rayuwan Yanda din inma da son samu gaba dayansu zaiyi sanadin dasai sun dawo cikin gari da zama amma kuma ya kan tambayi kansa da taya haka zai faru ? ( IKKO Ikon Allah ) Tafiyan jirgine yayi don haka bai huta ba washegari ya fita wajen business dinsa yabar zancen da sai Meimbe ta nemasa da kansa don har yanzu bai kai ga yanke hukunci ba duk da malam na kusfa ya gaya masu akwai alheri tattare da wanan abin saidai zai dan fuskanci baraza amma kuma ya bashi addu,a tare da ruwan rubutu dayasha tun a wajensa. Haka kuma baiyi sanyi a gwiwaba tun dawowan nasa yana duk abubuwan da kawunan nasa suka bashi shawaran yayi don rigakafi a rayuwansa. Har wani annashuwa yakeji don abubuwa yanzu sai budewa sukeyi tun dawowanshi daga gida kofofin samunsa kamar an bude mai yake gani duk abinda ya taba cikin yardan Allah zaiga nasara akan abin. Haka saida ya tabbatar da matansa sun horu sosai kafin ya fara daukan wayansu koshi saida iya ta kirashi tana sheda mai zuwansu Asibiti da Saiba da aka tabbatar da tana da matashin ciki a jikinta na wata biyu da kwanaki. Kamar yadda iya ke fadamai tun bayan barinshi gida bata da lafiya wanan yasa ya kira Asmau ya fara jin lafiyanta kafin ya kira saiba din a gurguje suka gaisa yayi mata ya jiki ? Zata fara kawo mashi kissa yace aiki yakeyi zai kirata idan ya gama shine farkon da har yake saurarensu idan sun kira wayanshi din koshi ya kira yaji lafiyan jikinsu. Tunda ya tara guzame a gidansa don ko,wacesu tana dauke da cikinsa a yanzu ya zama dole ya kulasu haka kuma duk sati yana turowa ko wacensu kudi a account dinta don bukatun yau da kullum irin haka na mata. Yau ya kasance saura kwana biyu ya cika sati biyu da dawowa gidane suka hade miss meimbe a wani shago itace ta fara hangoshi ta nufi wajenshi cikin sakin fuska tana fadin kai kayi wuyan gani fa ? Shima murmushi yayi cikin dan basarwa yana fadin mun daiyi wuyan gani koda yake naje gidane kinsan mutum mai iyali sole inayi ina leka gida. Dariya ta kwashe dashi tana fadin kajika sai kace wanda ya aje mata masu mata a gida sune bini bini suke zuwa gida lokaci lokaci ba irin ka yaro karami ba. Dariya zancenta ya bashi yake fadin nine yaro karami nida keda mata biyu a gida zaki kalleni kice min yaro. Dariya sosai ta kwashe dashi tana fadin abinda kakewa kanka fata kenan ka fada ka aje mata biyu kamar yadda ku musulmai kukeyi ? Sam kai baka dace da tara mata ba lover boy kada ka tauye kanka sa yawa mana mace daya is ok for you ku more rayuwanku da lokacin ku. Wani kallo yake mata kafin ta tsaigaita da maganan tana kallonshi itama tace iam tell you gaskiyata ke nan har zuciyana na fadama saboda kai din mai tsadane zanso naga wanan mace mai sa,an da zata aurenka ? Me kika daukenine mrs na fada maki matana biyu wallahi kuma ko wace a yanzu tana da ciki da zata haifa min baby. Kallon serious tayi mai tana fadin kacire wasa abinda naga ya dace dakaine na fada sai yayi murmushi don yasan ba zata yarda da yana da mata ko bama mata ba a lokacin. Can ta dan tsagaita dariyan ta saita kanta ta soma fadin ina ta nemanka naji shawaran daka yake don broda ya kirani yace ina guy din don kaya sun fara yawa yana son a fara plan din turawa arewa din. Shima Jafar din gyara tsayinsa yayi ya soma fadin eh to gaskiya ban tsayar da maganan zanyi ko ba zanyi ba a yanzu saina gana dashi yayan naki na fahinci wasu abubuwa daga bakinsa. Wanan baida matsala don yana Nageria yanzu haka kaga bari na nemesa sai muji time din da zamu samesa don gaskiya mr handsome ina sonka da wanan business din don ba karamin samu zakayi a cikinsa ba yafi wanan buga buga din da kukeyi a yanzu. Tana magana tana dauko wayanta a cikin handbag dinta a lokacin ta soma dialing din number dan uwan nata kira kusan zai katse ya daga yana fadin sorry sister ina meetinga ne a yanzu. Dama broda guy din nan danayi ma zancenshi shine yake son ka bamu time da zai gana dakai yake fada mata zai shigo lagos next tomorrow idan ya shigo by 4 pm zasu iya ganawa dashi a ranan. Suka danyi yaresu inda take kara rokawa mr handsome dinta alfarma a wajen yayan nata tana yabawa har yayan ke fadin tabari din yazo din da alama guy din yasan kansa tunda har ya nemi su fara ganawa dashi. Abinda baiso shine cuta da cin amana idan haka ya faru ba zai dubi alakansu ba zai dauki mataki mai muni akan ko waye. Tace by god grace hakan ba zai faru ba son ta yaba da halinsa sosai sun dade suna business dashi ta fada mai hakan don ya yarda. Kai ta dag ta saukewa Jafar kallo tana fadin munyi sa,a basai muje can ba zai shigo lagos banda gobe kaga zamu sameshi 4 o,clock ku gana dashi don forget with d time ta kara fada suka taka zuwa bakin motarta tashiga ta wuce. Shima motanshi dayazo da ita wajen ya nufa ya shiga ya nufi inda zai tafi tare da tunanen yadda abin nasu zai kaya saboda zuciyarshi ta shiga wasi, wasin don imani da tauhidi dake yawo ajinsa na adduan iyayye. Kamar yadda suka aje time karfe biyu yana fitowa sallah ya kirata karo na farko yana tambayanta ko brother din nata ya samu shigowa lagos din tace zata kira ta tambaya taji. Ba a dauki wani lokaci ba ta turo mai sakon wajen da zasu hadu zuwa wajen yayan nata yaci gaba da harkokinsa na yau da kulum a lokacin. Sai bayan ya fito sallah a masallaci mafi kusa ya shiga mota ya sameta tana jiran sa hakkuri ya bata daya tsaya sallah ne a masallaci tace ba matsala tana gaba motanshi nabin nata a baya har gidan dan uwan nata dake wani unguwar masu kudi anan kusa da ruwa. Kai tsaye ganinta security suka barsu suka shiga gidan don tayi masu bayanin tare suke yaji mamakin girman wanan gidan haka yasashi nasa wanan yayan nata ba karamin mai kudi bane ashe. Sun samu waje sun faka motocinsu wajen suka fito zuwa cikin gidan shidai yana dauke da addu,a a bakinshi don zuwa yanzu sai tsoron zuwa shi kadai ya darsu mashi a zuciya yana tuna addua shine mafita koda yazo da wani din ba zai iya mai abinda Allah zai yi mai ba ya fara jero duk abinda ya sani a bakinsa. Wasu kulka kulkan mutanene ta gani suna gadin gidan bai damu ba saboda addua yasa ya daina jin tsoro a yanzu. Sun samu yana meeting da wasu yan kabilansu kana ganinsu kaga manyan matasan arnakun kasan nan ya fake da waya da wani abokinshi a lokacin. Ya fahinci duk wanda ya fito yaga Meiarbe sai yayi mata kirari da bata girma irin tasu na iyamurai da sukeyi bayan sun fitone akai masu iso zuwa ciki don yayan nata ya hangota daga waje yasan sun iso ke nan. Addu,an da Jafar ya doshi wajen dashi yasa suna shiga yaga mutumin aiba wani babba bane can yanda ya zata don irin matasan daya ganine a waje yanzu. Hannu ya mikawa Jafar din su gaisa baiki ba ya mika masa yaga zalla nagartan jafar daya hango a yaron lokaci guda. Bayan sun gaisa yake tambayanshi daga ina yake ya fada mai kai tsaye daga zaria yake yana zaune nan lagos. Ya dan kara kallon Jafar din dake zaune a cikin ladabi kafin ya soma magana yana fadin quity sure kayi min haka nake son dama matashi mai lokacinsa wanda zai iya bada karfinsa ga aikin mu ba ya zauna ya tura ai masa ba. Saidai kota fadama harkan mai zamu soma a yanzu mutane da dama daga arewanku suna son wanan harkan ban basu daman hakan ba don ina jin tsoron hurda hausawan ku saboda basu da amana. Kai jafar ya dago ya kalleshi yacewa Jafar din gaskiya na fada nagwada aiki da mutanen ku a baya banji dadin hakan bane. Allah sarki malam bahaushe da abaya iyamuri ko bayerabe suke tsoron koyi masa kallon banza balle fada a yanzu zamani yazo da iyamuri zai fito fili ya fadi magana akan bahaushe sune ke fadin basu yarda da bahaushe ba suda muke kyama sosai. Saida wasu marasa zuciyan bahaushe da suka batamu a wajensu sun ari rigan bahaushe sun yafawa kansu suna yaudara suna batawa hausa asali suna da akidarsu ta yaudara a yanzu. Kada ka damu you are lucky tunda autace ta kawo ka nasan idan bata yarda dakai ba zata kawoka har wajena ba zan barka hakan don nasan tunda kace kana son ganina kaima kana da abinda kake son fada a kaina. Zama Jafar din ya gyara ya soma fadin najo duk abinda ka fada saidai ina son jin ainihin yadda kake son sana,an naka ya kasance a arewa idan zan iya zan karba da hannu biyu inma godiya idan kuma naga ba zan iya ba zan fada tun a wajen nan ka neme wani don addini mu bai yadda da wasu tsare,tsare ba a cikin sana,an mutum. Kallon guy din chibuza yayi yaro karami yasan kansa akan addininsa abinda bai taba jin manyasu sun fada ba Allah Allah ma suke ai signing din contract dinsu su farawa mutum yaudara shi gashi yazo masa da nasa tsarin akan addininsa yanzu. Ehh to ba wani abu bane ya soma mai bayani akan yana bukatan gina gidajen mai a arewacin Nageria din shi Jafar duk zai kula da wanan bayan haka akwai motoci da zasu shigo wa yanda zasu dinga sintiri kai mai kuma duk zasu tsayane akarkashin kulawan jafar din da komai illa iyaka shi nasa balancen zasuyi yana turo mai kudi a wajensa eather shekara ko bayan duk wasu watanni haka yadda dai abin ya samu karbuwa a wajensa. Ajiyan zuciya Jafar ya sauke don jin ba wani abinda zai soki addininsa ko rayuwansa nan gaba donshine ya amince suka tsara yadda abin zai kasance tare da musayan secret number da zasu dinga magana a tsakaninsu. Ya gargadi Jafar sosai da bai son yawan magana inda yace koda ba,a aka sunan yadda za a fahinci nasa bane shi wanan ba matsalan shi bane kada dai a samu kuskure a cikin harkan . Budan bakin Jafar yace wanan kada muyi fatan haka mu nemi sa,a a wurin ubangiji ya dafa muna kan lamarin da muka dosa . Iyawan mutum ko kwazon mutum baiyi kamar na Allah ba da komai yake a hannunsa kai chibuza ya daga yana yaba nagartan Jafar a zuciyarsa. Dafa Jafar din yayi yana fadin idan ka rike gaskiya zamuji dadin juna sosai dani dakai don a wanam harkan kadai zamu tsaya ba a sannu zanyima hanyar international business . Sun rabu cikin jin dadi da fatan nasara a tsakaninsu sukai sallama akan in Jafar yagama nazari zai nemesa yaji inda za a fara. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1f MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,, 9️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Kamar yadda yake dan adam bai gani bai tofa nasa ruwan a cikin lamarin da bai shafeshi ba shike faruwa yanzu akan Jafar . Wanda yasan jafar yasan mutumne daya taso da kwazon nema saidai ganin rufin asirin da ubangiji yai masa lokaci guda yasa mutane nata tofa albarkacin bakinsu akan cigaban daya samu inda a yanzu ya gyara gidansu da suke zaune a cikinsa don haihuwan matansa yaiwa kowa part dinta amma falo na tsakiya babba haka bangaren Abubakar da zancen Aurenshi yanzu kowa ya san da yana neman aure a Cameroon . Don har manya su kawu sun shiga zancen zuwan farko baffa yake amincewa da zancen saida suka biyu ta Alh can abuja ya fito masu ta bayan gida a dan Nageria ya hadasu da hakimin garinsu shiya aika masu da sammaci aka nemosu har can inda suke zama akan human right tayi karan baffa din. Tsoro da gudun wahala yasa baffa cewa ya yafe yaran su koma nan kauyen su gidan hardonsu don zaman kaka yake ga yaran. Yace su zauna anan tunda shi baida iko dasu dama taimakonsu yakeyi ai tunda naggen da ubansu yabari a yanzu sun zama nasa tunda shekaru ya kora shike kula dasu. Hardo yaso yayi magana amma sai su Abubakar sukace ya kyaleshi daha baya za,ayi wanan zancen yanzu zancen yarane da uwarsu su samu freedom ayanzu akeyi. Abubakar bai tsaya dogon nema ba irin na barna lokaci a dade da budurwa ana shan soyayya daga shiga rayuwansa ya fito da zancen aure. Inda mama Dubu ta kama mashi tana kuma tayashi da addua da shawara wanda a yanzu kowa yasan da zancen bafulatanan ruggace yake son ya aura. Inda wasu ke ganin ya rago kamarshi dan boko dan gaye mai jin lokacinsa zai buge ga auren yar daji jahila mara boko wace bata waye ba ? Sun manta kida Jahilace haka Allah ya tsara idan itace matar da zai aure din ba (makawa ) inkiyan kauyen zee makawa) sai ya aureta. Allah yayi za ai abin a gabar da dan uwansa ke cikin tashen Naira Allah da yardansa yadda aka saka watan auren lokaci yayi akasha buki. Bukina mai kama da dunkula irun ta fulani ba wani shagali aure kawai aka daura aka dunkulo amarya sai yan rakiya da hardo yabayar mutum biyu sai kanwata da zatazo zama da ita don ta samu wani a kusa da ita cikin garin da bata san kowa ba . Hardo ya roka kuma anyarda mai da hakan gidan su Abubakar din mama tace dama tana da niyar hakan a zuciyarta don ta samu na gida a kusa da ita. A bangaren matan yaya jafar kuma sai dariya sukewa Abubakar a fakaice tunda Saiba dake fadin duk bakin ransa da jiji dakai a bafulatan daji ya kare ashe. Ga mata birjit a gari amma ruwan ido ya kaishi daji auro bafulatana saidai basu fadi a gabanshi saidai a bayanshi basu kadai ke wanan zancen ba harda matan gidansu gidan mahaifinshi. Suma sunata sakin irin zancen nan da fadin magana akan fulani abindai kamar yadda aka saba tsegumi akan ko wani irin aure wanan ma a tofa iya tofawa da za a iya. Mutum dai bai isa ya hana abunda Allah ya nufa ga bawa ba saidai gajin hakkuri namu na yan adam yakansa mu daukanwa kanmu zunubi a cikin rashin sani. Ita kanta maria bata taba zato ko tsamani haka zata samu gidan Abubakar din ba don ya nuna mata shi baida komai a lokacin nemasa da ita. Sai gashi hadaden gidan dataga an kawota ciki ya tsinka mata zuciya ta kara godewa Allah daya duba mairaicinsu ya fitar da ita daga kuncin bautan da sukeyiwa baffa. Sai addiua take wanan auren ya zamo mai dorewa a gareta don baffa yai mata baki da cewa indai auren kado ne taje ya bata shekara tasan baffa mugune na bugawa a jarida. Don ko yan uwansu kaf fulani tsoronsa sukeyi abu dayane ke razana baffa shine hukuma baison abinda ya dangantashi da hukuma. Don bai kaunan ya cire nagge daya balle fiye da dayan a cikin garkenshi ko yaushe a cikin lissafin garensa yake a tsakar dare bai barci nan zaita sintiri yana kidayan shanun dake garken sa. Yana kuma surukullensa a ciki yanawa mutane aiken shirin daya saba wanan tunane data shigane yasa har bataji sallaman su saiba ba da suka shigo ganin amarya da safe. Sai da yar uwarta ke fada mata a cikin hausa anty Yanda ana maki sallama fa ta zabura tana fadin wa ,alaikis sallam. Kallon juna sukayi suna fadin tubarkallah amaryan ke nan ta fito tana masu sannu da zuwa sai yar budurwan dake tare dasune da ba zata gime mata sosai ba take fadin. Anty maria wanan matan Yaya J ne ana suke gidan suma ina kin gane yaya J babban yayan mu na dakin mu sune matansa. Cikin fara,a da yar kunya ta sake dago kai tana masu sannu da zuwa tare da gaidasu tana dan kare fuskanta don kallon kurullah da suke mata. Ba zakace ita din bafulatan daji bane yadda suke fada don dinkin da anty fadila tayo mata daga Abuja sune jikinta a lokacin dinkin dakosu basu saka irinsa ba dogon rigace da yaji duwatsu kamar sarka ya danne a jikinta sai dogon gashin kanta daya sha gyara an daureshi a waje daya yana kyalli a jikinta. Mikewa tayi tana fadin bari tazo taji saiba ta juya harshe a cikin turanci tana fadin muje mana me zamu tsaya yi kuma ta juya tana fadin excuse me please a cikin sallon turancin dake bakinta. Kallon juna sukayi tun lokacin suka fara mamakin anya bafulatan dajice wanan kuwa suke tambayan kansu cikin zuciyarsu. Bana fada maku ba babu inda tai kama da yar daji yadda kuke fada yaya Habu fa duniyane dama nasan za a rina kallon kowa yakeyi kar a gidan nan. Leda ta kawo masu shake da kayan buki ta mikawa Sare data santa tun jiya tasan kanwarsu Abubakar dintane ita. Ke wanan kuwa anya yar dajice wayewanta yayi yawa ko fuskanta kagani kasan wanan ba yar kauye bace. Ai ba wayewa ko kauyanci akajawa a aure ba hali ya kasance tana da halin kwarai shine zaman lafiya ga ko Asmau ta fada. A harzuke ta juyo tana fadin to me kike nufi da zancen ki da bani wanan amsan a yanzu Asmau nifa irin zancen nan naki na gugar zana kin san shike hadani dake Asmau. Nan fada yaso ya fara a tsakaninsu Sare ce ta dakatar dasu da take fadin wanan ai saiku nuna mata irin zaman da kukeyi a nan itama ta fara. Jin hakan yasa Asmau tayi gaba ta barsu a baya son ita dai bataga abin laifi a cikin zancenta ba kawai dai Saiban ce kamar a jirace take da ita lokacin. Fitowan Ramah daga wajensu mama dubu yasa su duk binta da kallo suna mamakin yaran don wanan koba a fada ba kanwar wanan amaryam Abubakar dince da suka fito wajenta. Ya Allah wa yan nan diya akwai halitta dole yaya Habu ya rude a kansu ji wanan karamar don Allah zakice itace ta halicci kanta wajen kyau. A can wajensu mama dubu baki yan kawo amarya suka sauka don iya tace ba mai zama a wajensu a bata masu part din don akwai dakuna a wajenta shine aka gyara masu daki guda suka sauka a ciki. Babu wani laifi a nan din don ina aka saka ake faman yi dasu tun jiya da suka iso garin abincine iri iri kafin su bude wanan wanan ya iso sun rasa wani zasu taba a ciki. Karasawa rama tayi cikin dakin tana fadin a cikin fulanci anty Yanda baffa yace ki fito kiyo hakan ne ya basu dariya ita da kanwar nata lokaci guda suka zauna suna hiran baffa Buga da shu,umancin daya nuna masu a baya. Allah ne ya kwatomu Ramah don babu da amanan baffa Abban mu baici amananshi ba a rayuwansa amma ya azabantar damu haka a gidansa. Kinga matan gidan nan da suka fita yanzu matan yayan Abubakar ne sune abokan zamana a gidan nan saidai na fahinci kamar akwai zaman lafiya a tsakaninsu don suna fita nan suka soma fada. Tsoro nake ji Ramaah zama da irin matan nan akwai fitina da barazana irinsu ba zasu barka ka huta a rayuwanka ba da ace ba gida daya muke a zaune dasu ba hakan yana da sauki. Babu ruwanki dasu tunda ba a bangare daya kuke zaune ba suyi harkansu a can muyi namu a nan dani dake. Murmushi tayi tana bin kanwar nata da kallo tasan Ramaah da iya fadin zance kalma daya zata fada ya wadatar da abokin zancen ta. Kwana biyu yan rakiya sukayi suka juya bayan nasiha da kuma jan kunne da sukaiwa yaran nasu da sanadin aure ya rabosu dasu zuwa nan yanzu. A dan zaman da sukayine suka har sun fahinci wasu abubuwan dake faruwa a gidan wanda suke son natsuwa da gyara a kansu donshi suka tsawatawa ita Yanda din. Sun tafi a ranan kuma Yanda ta fara girki a gidan bisa umurnin mama data bata baki data dora abincin darewa mijinta. Hakan ya bata daman zagewa ta dora girki tare da amfani da sanadaran da sukasa gidan gaba daya ya dauki kamshin dake tashi a girkin. Tuwon shimkafane da ya tuku yayi laushi kamar ba shimkafa aka sarrafa ba ga danko ga leda fara data kwashe a ciki daga nan suka kara mayar da hankali ga miyan da suka dora wanda kowa ke son ya dandana yaji dadinsa. Miyan bindin saniyace ta dora sai miyan yauki na agwano da dan karkashi kadan yaji daddawa da kayan kamshi a gargajiye. Tayi hakanne don hiran da sukaji iya nayi cewa mama ta huta da tambayan tuwo yau maciyi tuwo yakai ga matar da zata tuka masa tuwo yadda yake so yaci sai ya koshi. Sun kammala an zuba waje uku suka shige yin wanka don itace kusan karshen shiga wanka a lokacin. A falon ya J Saiba ce ta fito rugume da yarta tana fadin yau kamshin meke tashi hakane a gidan nan ? Asmau dake zaune ta dago tana fadin nima tun dazun nake jin kamshin nan yana shigo min wata kila a part din iyace kamshin ke tashi. Baki saiba ta tabe ta gyara zama tana fadin kamshi kamar wani girkin kwarai ina bafulatana ta iya girki banda tatsan nonon shanu. Badai gyaran gyaran ba tayi mai wanan da gani daban take a cikin fulani don tayi kama da wace ta zauna a birni ba a cikin daji ba. Bayan magariba Ramaah tayi sallama part din Iya ta sauke kayan abincin data dauko niki niki tana gaidasu inda suke zaune. Abincine Yanda tace na kawo cikin murmushi mama tace a,a abincin hardamu aka sakawa angode aida tayi iya bakinku sai mijinta. Sare ce ta mike ta karba suna fadin sun gode har Ramah din ta juya taji muryan mama na fadin. Nace ba idan kun karasa aikin a can anan wajen Iya zaki dawo da kwana idan kin karasa saiki dawo nan din ki kwanta kinji. Ta amsa a ladabce ta fita na part din ya J ta dauka ta mika masu inda ta samesu zaune a falo duk da hiran nasu ba wani hiran arziki bane mai tsawo. Amma ya zama dole garesu don dokan da maigida ya kafa a kansu yanzu kuma kowa na tsoron yayi abinda zai bantale masa auren a lokacin da suke jin dadinsa. Gaidasu ta fara a falon ta dire abincin acikin wani kula mai kyau tana fadin abincine daga wajen amarya a gyatsine Saiba ke fadin ta aje a saman table din. Babu wace tace angode a cikinsu ko a gaidasu da mai girki ba wace ta iya fadan hakan a cikinsu haka yarinyar ta fita tana mamakin hali irin nasu. Part din yar uwan ta koma taci abinci saida ta gama ta mike take fada mata abinda mama dubu tace dan shiru yar uwar tayi indai son samune taso a barta da yar uwanta da take amana a wajenta yanzu ta zauna a wajenta din. Saidai ba yadda zatayine don umurnin mama dubu ne hakan tayi mata saida safe ta fita zuwa part din tsofin don ta fahinci ana son ta bar ango da amaryansane lokacin. A bangaren yaya Jafar kuma Ramaah ta fita bada dadewa ba saiga maigidan ya shigo suna mai sannu da zuwa ya amsa tare da bin kulolin da kallo ya kai zaune yana fadin wanan abincin fa ? Daga bangaren amaryan Habu aka kawosa Saiba ta fada tana mikewa donta dauko mashi abincinshi da suka girka a part din. Saidai taja ta tsaya tana bin maigidan da kallo wanda ta sama ya bude abincin yana zubawa tare da yaba yadda aka tsara komai cikin nuna wayewa da zallah gwaninta tare da iya tsabta da kuma sanin darajan dan adam. Bai jira wani cewa ba ya mika hannu ya fara serving din kanshi saiga Saiba ta fito da only warmer din data zuba mai ja,loop din taliyan da tayi na manja. Tunkan ta karaso ta soma magana tana fadin wanan abincin yarincan ne fa ga abincin ka nan na dauko maka ? Bai kullata ba yacigaba da zuba abincin a cikin plate iya yadda zai iya tare da fara zuba miyar yana jin wani irin tukuki a da zafin matan nasa na yadda basu iya tsayawa suyi girki haka irin da malam bahaushe ya sani saidai shiririta irin na shirmey din nan da matan yanzu keyi saboda sakaci. Mikewa yayi ya wanko hannunsa ya dawo ya zauna yana shirin zamane ta kara fadin J fa bafa nina girka ba wacan yarinyar ce matar Habu ta aiko muna dashi. Bissimillah taji yayi yana yankan tuwon ya fara kaiwa a bakinshi tare da lumshe ido don jin yadda tuwon ya hadu tsab rabo da yaji tuwo haka tun suna gida mahaifinsu yana raye mama na girki ta saka masu. Komai yaji acan acan kayan yaji na gargajiya sai dandanon daddawa ga kuma kamshin man shanu dake tashi gwanin ban sha,awa. Daidai Asmau data gama shirya danta ta fito dashi rugume a hannunta itama tabishi da kallo tare da mamaki ta zauna a saman kujera. Wai ikon Allah yanzu girkin nata zakaci J ya dago yana kai loma a bakinsa ya hade yake fadin wai wanan din sunansa me kin isheni da wanan abin da kike dafa da sunan abinci. Wanan din shine muka sani da abinci a gidan nan ba wanan shirmen da kukeyi ba ku diba yarinya karama tasan ta girka wanan abincin hakawa mutane ? Ku me yaci karfinku da ba zaku iya ba ya dauko gutsuren nama ya kai abakinsa ya lumshe ido kallon Asmau saiba tayi cikin mamaki itama ta lumshe idanunta. Tana fadin wai bari dai nima naci naji hannun ta da akewa yabo haka ta fara serving din kanta itama saida ta loda taja plate din gefenta ta fara ci. Loma biyu taci ta dago tana fadin kici kiji abincin ya hadu gaskiya ba laifi kici don Allah murmushi tayi cikin takaici tana kallon kulan dake hannunta ta dangware tana fadin wanan ai baiyi ba. Ta fara jan plate din ta bude ta zuba kadan don ta gano matsalan abincin ta fada ta soki wanan girkin da taga suna santinsa. Saidai ta cinye wanda ta zuba din ba tare da tasan tayi hakan ba shiko maigidan ya tashi da duk abincin ya koma cin naman da bai jin zai gaji da cin wanan naman da kamshin sanadarin girki ke tashi a cikinsa. Da sallama ya shigo tana zaune tana addu,a saman sallaya ta juyo tana amsa mashi sallaman babban rigan sa daya ishe,shi a jikinsa ya debe ya sagalo a hannunsa ya dora saman kujera yana zama. Shafa addu,an tayi ta mike tana fadin sannu da dawowa yaya Habu kai ya dago ya kalleta jin yadda ta kirashi a ranan sabanin yadda ta saba kiransa da dan zaria. Murmushi yayi yasan wanan sunan a bakin su Sare tajishi kallamane da kannesa ke kiranshi dashi dole a wajensu taji wanan sunan. A cikin muryanshi mai natsuwa yake fadin amaryata ya zaman kadaici ina Ramaah ya dan fara dube dube yana neman yarinyar a zatonshi tana daki zaunene. Rigan daya aje ta dauka tana fadin tana wajen su mama tun dazun au ke kadai ta bari nan ke nan ya fada yana kallonta cikin so da kauna tare da godiya ga ubangiji Allah daya nufeshi da samun wanan tsatsiyar yarinyar a matsayin mata a gareshi. Wanka zakayi ko sai kaci abinci muryanta ya katse mashi tunanensa ya dago ya sauke mata kallo yana fadin bari muci abincin sai na shiga gaba daya. Ta juya ta shige ciki ta aje rigan ta fito ta sameshi ya lumshe ido yana godewa Allah indai Yanda tacigaba da hakan a rayuwanta zaifi kowa murna da aure a rayuwanshi. Ga abincin can na jera a dinning ta fada ya kalli daning din ya hango kuloli a jere gwanin ban sha,awa ya lumshe ido yana mikewa tare da kamo hannunta . Idonta tayi saurin lumshewa lokaci guda tana maijin wani iri a zuciyarta basu nufi dining din ba sai ji tayi yakai mata runguma yana sauke ajiyan zuciya da itama shita sauke lokaci guda tana hawaye. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K44JhTApwmM4gU33AbpqHC MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,, 11️⃣00️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Rayuwan aure mai tsabta suka shimfida a tsakaninsu a ranan inda yakwana yana lalashin amaryan nasa wace ya sameta da mutuncinta da kimarta na ya mace. Zamanta a daji ko rayuwan birni baisa ta zubar da kimarta na ya mace ba a waje daga shi har ita sun shiga wani hali bayan zazzabin daya rufeta zuwa safe hakan yasa ya fara tsaguwan kansa tare da tuhuman kansa dabai rangwanta mata ba. Wanan yasa daga masallaci part din iya ya nufo ya samesu a falo suka gaisa nan yake fada mata cewa Maria ce ba lafiya. Wallahi tun asuba jikinta yai mugun zafi tana kuma rufe da bargo tana rawan sanyi ko asibiti zasu tafine da ita ? Haba dai kaje iya na tafe mama ta bashi amsa lokacin na fito da tsinya a hannu na tsuguna ina gaidasu da kwana na wucesu ban tsaya ba. Tsakar gidan kamar yadda muka saba share gidansu hjy a abuja hakan na duka na fara shara. Don gidan yana bukatan gyara saboda gidan tunda akai buki ba a samu wanda ya tsaya ya gyara wajen ba ganin hakan yasa na kwana da niyar gyara wajen na fito tunda safe . Daga bangaren Anty yanda na fara na gangaro dayan part din da babu kowa a cikinsa har zuwa part din wa yan nan matan dana shiga jiya nakai masu abinci. Duke nake na shagala naji mutum a kaina yana gaidani na amsa kafin na duka ina gaidashi farine dogo yana saye da jallabiya a jikinshi suna da kama sosai da yaya Abubakar. Saidai yaya Abubakar bai kai wanan fari da tsayi ba shi wanan jin dadi ya huda jikinshi kallo daya zakiyi mai ki gane yana jin lokacinsa. Duk a kallo daya da nayi mai na zayyano wanan kamanin nasa dana hango lokaci guda tas nayiwa gidan kafin na samu komawa part din iya inda na fara gyara tare da tsabtaceshi na fito falon daga kitchen dinsu dan soma sharo falon na iya a lokacin ya kara sallama ya shigo wanan karon ya sauya tufafin jikinshi zuwa wasu kananan kaya zakice shidin ba dan hauwa bane . Kayan sun matukar karban jikinshi sun fitar mai da kurciyansa a fili saiki rantse bai taba auren farko ba suna fadin Abubakar yayi rigima wanan mai mata biyu din ashe shine mai rigima din. Mama dake zaune tana jan tasbaha a hannunta ya kalla yace wai ina kuka samo wanan yar mama tun dazun naga tana aikace akaice gidan nan ? Kai dai bari yar albarka yar uwar amaryan Habuce da suka bar mata ita a nan shine ta tashi da wanan aikin ina su Sare ya tambayi kannensa mata . Wa yan nan mashiriritane ai suna daki kwance ko gyaran kwanciya basuyi ba balle susa niyar tashi iya fa ya tambaya ? Ta shiga gun Habu ta duba amaryansa ina ganin yarinyar yar albarkace yazo wai zai kaita asibiti nace iya ta fara duba mashi ita a gani. Fuska ya daure a cikin wani yanayi ya kai zaune yana fadin da anbari sun tafi asibitin kada wani matsala ya biyu baya kuma. Inba zamani ba ba komaine ake zuwa asibiti ba rashin sabone ga dai iya din can taje ta dubata ai tun dazun wayansa aka kira ya dauka ya cigaba da wayan karshe ya mike ya fita. Saida nagama aiyukan gyaran ko ina na nufi part din antyna inda nayi mamakin ganin tsohuwar a wajen ban tsaya ba na gaidasu na shiga dakin da kayana suke ciki wanka nayi na gyara jikina fes kafin na fito na samu tsohuwar ta fita daga wajen. A hankali nakai zaune ina duban kofan antyna din duk da ake cewa mu fulani bamu da hankali kankantana a lokacin baisa na fada dakin nata ba kai tsaye don muna da tarbiya zaman muna birni bai barmu da duhun kai ba. Bayan hakan kuma gwargwado muma fulani muna da namu addinin munsa abinda yake daidai da wanda bai dace muyi ba balle bamu taso cikin duhun kai ba ai. God so kind na iya kunna gas tun a abuja wanan yasa jin yayata shiru na fada kitchen tare damu mahaifiyar da yayata sukewa hjy Yaghana girki da mijinta . Haka diyansu su anty salma idan suna kasan nan mune suke sakawa muyi masu duk wani girki da zasuci har su bar kasan nan. Zaman na shekara biyu da rabi ko ukku a wajen baffa baisa komai ya fita kanmu ba tunda a cikin hakan muka tashi. Haka yasa na dora ruwan zafi na debo dankali na fara ferewa ruwa yayi zafi na juye a flask na dora suyan dankali duk a zatona suna dakinsu kwancene basu tashi ba kafin wani lokaci nagama hada breakfast na zuba a kula na fito daidai lokacin ya Habu ya shigo gidan da ledan magani a hannunsa. Zaka gane anyi girki don kamshin da gidan nasu keyi gaidashi nayi da dawowa na juya zan fita ya tsaya yana fadin kinyi breakfast ne Ramaah ? Ehh na hada yaya gashi can a dining na fada a dan ladabce yadda mukewa su anty salma a Abuja sai naga ya dan kalleni na second sai kuma ya juya zuwa ciki . Komawa nayi kitchen ban fita ba na wanke kayan da nayi aiki dasu na tsabtace kitchen din yadda ummah na koya muna tun muna kananun mu. Dama kuma idan kinsan bafulatana badai kazanta ba don tsabta kan akwaishi wajen fulani ko cup aka fara darazanshi wajen wankewa sai yayi fari sol za a barshi haka kore da sauran kayan aikin mata. Muryansu naji yasa na fito daga kitchen din dauke da kayan abincin part din tsofin dana wa yancan mutanen kamar yadda naga anty Yanda ta zuba masu a jiyan. Nasu na fara kaiwa suna falo dukkansu biyun nayi sallama na shigo bread ne ko ina baja baja a falin yaransu suna wasa dashi . Kyan kyami naji haka na ratsa ina gaidasu na aje masu abincin na juya da zumar fita daga wajen naji muryan wata na fadin. Ke meye wanan din kika kawo muna jin hakan yasa na juyo ina fadin abin karyawane sai akace daku bamuyi ba anan sai an kawo muna ? Ita kuma Asmau cewa tayi kice a daina kawowa hakana mun gode basai ta wahal da kanta ba kinji zoki dauka ki tafi dashi ta kara fadan hakan. Kallonsu na danyi kafin na yunkura zan dauki kulan abuncin naji muryanshi yana fitowa wani daki yana fadin ke ajeshi nan kice an gode ni aka kawowa baku ba da zaku yanke hukunci kuba da dokan kada a kara sako min abinci. Lah illah amma wanan kan gaskiya baiyi ba dan abin karyawan ma sai ankawo muna saboda me za ace a zubo muna. Nikan tunda yace in tafi na fito part din da saurina na barsu sunayi bansan ya suka karasa ba a wajen. Na koma na dauki na tsohuwar na kai mata suna daki suna hira na shigo ina gaidasu suka amsa na aje abin karyawan nasu a gefe daya. Wuri na samu na zauna gefe daya tunda ba sabawa nayi dasu ba lokacin sai ga mama dubu ta fito daga daki alaman wanka tayi tana fadin . Badai wanan yar girki tayi ba yanzu nake cewa idan na fito akai mata abin karyawa can wajen ku ai sai ga kuma wanan abin ta nuna kulan dana shigo dashi da hannu. Nice nayi mama anty Yanda tana daki kwance ina gani na fada yar albarka irin yaran nan ai bakuntanku baida wahala a waje. Meyene kuka dafane Sare data mike zuwa bude kulan abincin take fada tana bude kulan don taga abinda ke ciki Arish ne sai kwai da suyanshi yayi kyau sosai bai kuma yamutse ba zakice wata mace ce tayi aikin. Ke baki da kunya ku diba kuna daki yarinyar nan duk fadin gidan nan itace ta shareshi tas ta gyara nan ta gyara wajen yar uwata yanzu kuma ta hada masu abin karyawa. Kai amma kuwa dai tayi kokari Sare din ta fada nikan hankalina yana ga tv dake aiki ina tuna wani rayuwa a baya idan an saka waka muka kama rawa muna nishadi a falon yara gidan daddy na Abuja. Anty Salma yar daddy din itace ke koya muna rawa da waka sai mu dinga rawa ina yawan cin gasa idan ana competition a tsakanin mu yara. Sweet zata sayo da cake da yought a dinga rabawa a wanda ya iya rawa wai tana da saurayi mai rawa da waka shine take koyon waka itama. Yadda ta fado muna dakin zaisa kaji tsoro tana haki yasa gaba daya muka mayarda hankalin mu a kanta muna kallonta. Mijin ne yashigo a hasale ya nufota ta boye bayan mama Jafar meya hau kanka hakane kanka daya kuwa duk iskaci ai ba zata zo gurina kace zaka biyota ba ? Nikan tsorone ya kamani sosai da har yasa na mike tsaye juyawa yayi ya fita sai bayan fitanshi ta soma magana tana fadin. Kawai don nace ba zaici abincin wacan yarinyar ba shine wai zai dakeni mama din tace wace yarinya ke nan matar Habu dake sako muna girki idan tayi . Shine yake ci tun jiya yau nace ba zaici ba na zubar shine ya biyoni zai dukeni kafin takai aya mama tace kika zubar da abinci Nusaiba har kike fadi kin zubda ? Mama akan me zai zauna yana yaba girkin yarinyan nan daga zuwanta yana fadin haka aka san mace da iya,,,,,,,, Shiru tayi don ganin Habu dake tsaye kofa ya harde hannayesa a waje daya yana saurarensu don tunda suke rikicin har fitowanta yana tsaye kofan part dinshi. Ganin mijinta ya fita hasale ya shigo ya gaida mama ya samu tana kokarin aibanta matarshi da kwananta biyu kawai a gidan . Zama yayi su Sare suka fara gaidashi ya amsa a dakile yace mama kiyi masu kashedi akan maria idan suna rikicinsu da mijin su ya tsaya iyasu amma kada su kara hadawa da matana balle mace tace zata aibanta min mata. Sam ba zan dauki wanan ba ban shiga zancen yarinya ba mama kada wata mace ta kawo min zancen banza za a jini da mace a cikin gidan nan. Nasan za a rina da wanan yau alheri da kyautatawa abokin zama kuma laifine Nusaiba ? Shi dan arziki a duk inda yake yakan nuna halinsane da irin tarbiyan da akai masa ai alheri kuma a cikin jinin bawa yake. Nayi mamakin yadda yaran nan har zasi iya saka muna abinci bama mu kadai ba harku a gidan amma ku din nan kuna bakin ciki ace yau abinku ya shigo a hannun ko tsohuwar nan balle ni ? Har yaushe yarinyar nan tashigo gidan nan da wani zance can zai biyu baya binsu mukayi da kallo mijin da dayan matanne suka shigo part din zama sukayi nan mijin nasu shima ya dora da fadin yazo dasu gaban tsofin ne ya kafa hujja akan abinda yake son fada game da matan nasa. Ga kaninsa nan ya soma fadin tare da iyalinsa ina son kuji ku sani kada ku dauka ban san plan din ku bane saboda kun daukeni bansan me nakeyi ba. To ina son ku sani duk ranan da wata daga cikinku naji kona gani tayi fada ko tsangwama akan yarinyar nan da aka kawo gidan nan zan ba mace mamaki sosai ga matakin da zan dauka. Babu macen da zata hadani fada da dan uwana ko wani nawa a gidan nan mama ki duba matan nan basuji kunya ba don Allah idan zanyi magana mama kice na barsu zasu canza. Yau ace matar Habu ce datazo jiya jiyan don nan tasan tayi girki ta sako maku abinci har nima a saka min don girmamawa da halarci wai kuma don suna dolaye sun kasa fahintar ma,anan hakan da yarinyar nan tayi. Aiko ita bayin kanta bane mijinta ko wani ya bata dabaran ta dinga hakan Saiba ta fada daga gefen mama wajen da take zaune din. Ban fada maki idan kina zancen ki kibar sakani a ciki ba habu ya fada a harzuke yana mikewa tsaye zai dosheta don abinda ta fada. Kai Habu koma ka zauna kada ka tako wajen nan mama ta fada mama ki bari in koya mata wayau don Allah wanan yarinyar bata da kunya wallahi. Kinfa ji abinda ta fada waini na koyawa Maria wanan hikimar idan kuma bani bane wani ya saka tayi hakan tana nufin ke kenan ko iya ? Ballema nice ta tambaya jiya da zata zuba ta kirani tace mutum nawane manyan yaya Habu a gidan nan na fada mata amma wallahi ba wanda yasa tayi hakan a gidan nan . Na fada mata basai ta saka ba tunda muna girki a nan muma tace a,a idan tayi hakan rashin kunyane tayi girki iya bakinsu bata ba manyan shi ba da wani ido zata kallesu . Don ya habu yana mijinta ai bashi kadai zata bawa abinci ba su a wajensu hakan rashin tarbiyane kuma bayan hakan ina zata da alhakin kamshin da mutane sukaji a kanta. Sare ce dake rike da labule tana kallon draman da yaninta keyi da matan nasu take fadan hakan amma wallahi ba wanda ya saka anty maria zuba abincin nan. Ita tasan darajan mutane tarbiyan data taso a gidansu cikine ta fara nuna muna nan koyin da gidansu sukai matane take wanzarwa yanzu a nan. Ai dama ko wani tsuntsu kukan gidansu yakeyi a duk inda yaje haka kuma Allah ke nan ya nuna maku bakin cikin da kuke shukawa sarakuwarku gata zaune. Yau ubangijo ya kawo mata yar da zata share mata hawayenta kuna kallo ban taba gani ko ji inba gareku ba yau ace matar data haifi mijinka baka san darajanta a idanunka ba. Uwar mijinka tazo ko ruwa baka iya daukowa ka bata balle abincin alhalin kuma dantane ya ya sayi wanan abincin kika zauna kikaci har kina bawa yan uwanki amma ba zaki iya ba yan uwan mijin ki ba ? A,a iya mu munga cewa abincin nan duk abinda ya kawo sai an kawoshi nan wajen ki shiyasa aka daina zuba maku komai idan mun dafa. Fau ya dauketa mari yana harzuka yace idan duk na kawowa iya ina ruwanku sai in zauna ku kashe muna tsohuwa da yunwa kome ? Jafarne ya dauke Asmau dake kusa dashi zaune mari ya mike yana fadin wallahi iya ban taba sanin cewa basu dafa abinci da kuba a gidan nan sai yau din nan amma babu komai ke kuma zaki dawo ki sameni ai bari ganin kin boye a bayan mama ya fada a hasale ya juya zai fice daga falon. Kada ka daki yarinyar nan bai tsaya sauraro ba ya fice fada sosai iya da mama sukai masu Abubakar ya mike yana fadin indai abincin part din kune na soke dama bansan ta saka maku ba da ban bari takai maku ba don ku ba mutanen arziki bane kowa kuma ya sani. Matan dake bakin ciki da yan uwan mijinsu kada wani yazo gidan nan ya ci wani abu daga jikin J basu kaunar ganin J yaiwa wani alheri a rayuwansa . Ina son ku sani ba J kadai yake da ikon gidan nan ba gaba dayan mune muke da iko a cikin gidan nan har Ahmed da yake yaro yana da hakki a cikin gidan don naji abinda kuka fada ranan game da zaman mu a cikin gidan nan. Mama gata nan itace mukewa biyayya dagamu har mijinku din don ra,ayin mamane tagan mu a waje daya haka zaune. Ra,ayin uwarkune hadin kanku dana matan ku amma wa yan nan shedanun da Jafaru ya tara da alaman zasu durkusar da wanan mafalkin na Dubu nason taga kun samu hadin kai tsintsiya daya madaurinta ku daya. Iya ta fadi hakan ga shi Habu da ya saura a falon yace basu isa ba iya kuma sunyi kadan mu zuba da mace a gidan nan a yanzu zasu gane waye Habu ? Duk abinda akayi ina zaune a gaban idona akayi shi har fitan matan yayan nasa da sukaji fitan mijinsu suka koma part dinsu bayan sun gama koke kokensu don ranan mama ta nuna masu bacin ranta sosai a gabansu. Tunawa nayi da yar uwata da naji ana fadan wai bata da lafiya hakan yasa na mike na nufi part dinta da sauri na sameta zaune a falo saidai yanayin ta kawai zai sanarwa mutum bata da lafiya. Sam ban fada mata tashin hankalin da akayi ba balle in kara mata damuwan da na ganta a cikinsa abinci na dora muna bayan tayi min bayanin abinda zan dafa saidai har lokacin zuciyata tana min sake,sake. Na wani irin rayuwa akeyi a gidan nan haka kuma yaya yar uwar tawa zata kasance cikin matan nan dana hango rashin da,a a tare dasu dolene nima in zage a yanzu in kare yar uwata tako wani hanya . Can wajensu kuma sai waya kowa keyi nan aka fara fadin mena fada maki saiba tunda kikace bafulatana kanin mijinku ya dauko ? Fulani da kika gansu mutane da akewa kallon basu san komai ba amma sunfi mutum sanin duniya kar suke kallon mutum sun iya sace zuciyar duk wanda suke so su kuma nunawa wanda basu kauna boni a cikin ruwan sanyi kin fara gani ke nan wanan ma ai kadan kuka gani indai bafalatanin mutum ne. Wallahi mama saina nuna mata ba kowa take ba a gidan nan ba zan yarda da sherin daduk zatazo muna dashi ba yar daji da ita kawai. A dakin Asmau kuma yar ta ke fadi a cikin waya bance kada ki yarda da hadin kan Nusaiba ba Asmau nusaiba munafukace yar iskace ta karshe irin na bugawa a jarida din nan amma kinki ki gane me nake nufi ? Ki zauna tayi amfani dake ta cika burinta a kanki ta fitar dake gidan kila lokacin zaki gane me nake nufi da kalmana inba kina shasha ba. Ta yaya zaki zauna yarinyar data hanaki farin ciki a rayuwanki kin sani wai ki dinga bin kaidin ta kuna musgunawa uwar mijinku da kakanshi ? ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K44JhTApwmM4gU33AbpqHC MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,, 1️⃣1️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Wanan case don da akayi shine mafarin komai a gidan har zuwa wani lokaci muna rayuwa dasune kawai da sunan muna gida daya. Amma hassada da kyashin duniya sun dauka sun dorawa anty Yanda dani kanwarta a gidan bamu da da matsala da surukan anty Yanda ko kadan . Don mutanene su masu mutunci daba zan iya fadan irin halarcinsu ba a garemu don sun rikemu kamar mu din jininsune . Haka muma bamu yarda wani rashin hankali ko sabani muyi kuskure a garesu idan mama ta koma can tudun wada nice zanta hidima da Iya . Wanda ban daukeshi wani hidima a wajena kafin na wuce makaranta zan tashi kiran sallah farko in gyara part din tsohowar ko ince part din mu in dora ruwan zafi na wanka dana flask idan akwai dumame in gyara muna don tafi son dumame ita. Sai infito in share haraban gidan nan kaf ba zakiga wani datti ba a wajen gidan ko kadan saidai kafin in dawo zaki matan part din yaya J sun jefo abubuwa sun bata wajen hakan bai damuna. Don wanan kadanne daga aikin da muka baro a gidan baffa ba yabon kai ba nafi anty na kuzari nakan gama nawa na hada da nata sai mun gyara garken shanu munyi ma matansa tatsin nono da surfe da acan muka koya wata rana harda fura mu wuce kiwo. Sai yamma lis zamu dawo gida mu sakawa shanaye hayaki muna kula dasu wanan yasa ban dauki aikin gidan nan wani aiki ba a wajena. Idan na gama inyi shirin school in wuce kuma ban makara tunda karfe hudu nake tashi zuwa makarantar idan na dawo nayiwa iya dan miya ko abincin da take so taci a ranan kullum cikin saka min albarka take. Duk da haka kuma zan shiga wajen anty na na gyara part dinta don shigan cikin data samu mai bata wahala hakan yasa yanzu da mijinta shima dan uwansa ya kadashi cikin business dinsa bai zama sosai a gari idan bai gari abincin da nayi wajen iya mekeci tare da ita. Duk ciwon da anty maria takeyi bai sa matan yaya J tausaya mata ba ba ruwansu da ita wai bata da lafiya balle su tausaya mata. Haka itama lamarinsu bai dameta ba idan bani gida ina school zata shigo wajen iya su zauna tare har lokacin dana dawo. Wani lokaci a nan zamu zauna sai dare zata koma wajenta wanan ya jawo tsegumi saidai ba suyi a gabanta don ba ruwanta dasu ko abinda sukeyi bata kallon hakan don ita bata da yawan magana kamata. Don ni a cikin dan lokaci nasan mutanensu sosai har iya kan aikeni irin gidan Kawu dauda ko can tundun wanda wajen mama . Ko acan wajen mama da mukanje mata wuni wani lokacin nayi sabo sai da mutanen gidan don akwai yan mata sa,anina da wa yanda suka girmemin a gidan. Hakan ya jawo sabo sosai a tsakanin mu cikin dan kankanen lokaci wata rana na dawo daga school da rana ina zaune muna hira da iya da antyna. Anty Asmau ta shigo part din kallo guda zakai mata kasan bata da lafiya gaida ita mukayi na cigaba da kankare kumbana da nakeyi . Naji tana fadin iya don Allah nazo aron budurwan nan nakine taje ta taimaka min tun shekaran jiya banda lafiya . Girki nakeso dan Allah ta taimaka min har yanzu saiba taki dora girki kuma tasan banda lafiya amma bata do,,,,,,,, Jeki ki girka mata din saidai ki sani ba zan yarda da hakan kullum ba haba iya iya yau din nan ne ko zuwa gobe dai haka har Allah ya ban lafiya. Koma dai meye banson abinda zai jawo kace nace akan hakan son Allah iya ta fada tana kara kallona tace min jekiki ki taimaka mata din kinji yar albarka. Kallon yayata nayi tayi min alama da intafi mana tunda iya tace inje din tare muka shiga part din nasu ga dai gida kan amma babu mata a cikinsa saboda kazanta. Wani plate don yakai kwana bakwai a wajen wani cup har yayi huhuna da abinda akaci cikinsa aka barshi nan kaya saman lafiyayyen kujeran dake falon kayan yayansu da nasu abin ba tsarin fada wallahi. A kitchen din naga tashin hankali don tukwane abincin ne a girke da ruwa da ruwa duk sun yi babu kyau gani a wajen hakan na tsaya saidana wanke tukunyan da zanyi amfani dashi lokacin na dora girkin . Ban iya sakewa kitchen da kazanta haka dole na shiga wanke kayan dake tare a kitchen din ina mamakin yadda mace zata samu daula haka kazanta ya hanata gyaranshi. Lafiyayyen shimkafa da miyar kaza na hada masu fridgen din nan nasu dankare yake da nama haka store dinsu kayan abinci a dankare kamar sun lalace a wajen gyara sosai na tsaya nayi masu tsakani da Allah ga yarta dake ta kuka na dauketa na goya ta a bayana yarinyar tayi barci haka kuma nake wanan uban aikin da ita a goye a bayana. Banji kyashi ko kiuya yi masu aiki tsakani da Allah ba inayi ina gyaran falon ina duba girkin daya gauraye gidan ba wani abu bane girki kamar mace ta tsaya ta soya kayan miya yadda ya dace . Haka tayi amfani da sanadarin girki na zamani ko na gargajiya da muka sani wanda nagani a kitchen din shi nayi masu amfani dashi a lokacin. Na bude miyar naga ko ya isa daukewa saiga dayan matar ta shigo kitchen din ksllon mamaki take min kafin ta karaso gabana tana fadin . Banyi mamakin ganinki a nan ba tunda har ga yar gida a bayanki yau nagani nidai ki gama ki fito muna dashi in diba na amsa da fadin. Ba aiki ya kawo ni nan ba zuwa nayi in taimaka mata idan wace ta sani na girka ta fito sai ta baki daga haka ban kara tankawa ba kuma. Huumm,ummm kama kanki yarinya bakin rijiya ba wurin wasan yaro bane nan ba wurin raininki bane ko yarki bata isa ta kawo min rashin mutunci ba balle ke ? Muryan Asmaun mukaji a bayan mu tana fadin sannu da aiki Ramaah yauwa sannu anty na kammala na fada ina kokarin fita daga kitchen din. Ai da kice min munyi sabuwar yar aiki a gidan nan Saiba ta fada sai naji Asmau na fadin . Yar aiki kuma ina take kafin ta gano me take nufi sai tace haba dai kanwar tamuce kuma yar aiki daga taimako ? Ninaje gun yar uwarta na rokota tazo ta kama min kaina yana damuna da ciwo ga zazzabi kada mu zauna da yunwa. Ki duba irin aikin da yarinyar nan tayi muna kamar ba mutum yayisa ba cikin dan kankanin lokaci haka ga kuma gitki . Yarinyar tayi kokari gaskiya wanan matsalankice Asmau banga abinda zaisa na ja wa yanda sabodasu akaci min mutunci a gidan nan. Kitchen din na dawo ina fadin karbeta zanje nayi sallah ta mika hannu ta karbi yarta daga bayana zan fice take fadin zoki dibi abincin mana ? A,a akwai abinci wajen ,,,,, Dakata don Allah Asmau nifa ban son kaskanci ki bari in diba inyaso idan na diba sai ta diba din wani kallo nayi mata na wuce zuwa part din iya din. Koda na koma suna zaune da anty da Yanda a falon suna hira na shigo na fada saman kujera sai iya ke fadin har kin hada nace nagama iya. Ai yanzu dai sunga ranan dan mutum ke nan yaro dama ba a haifeshi don mutum daya ba yau da babu zaman mutunci ai ba zata zo neman alfarma haka ba. Ina jin tsohuwar saidai na kasa magana saboda maganganun da Saiba din ta fada min duk da ban kyaleta ba nima amma sai nake ganin ta shammaceni ai a lokacin data fada min magana irin wanan . Asmau ta shigo da abincin a cikin kula tana fadin ga abincin Ramaah kinki tsayawa ki dauko a,a ba zanci ba na fada ina gyara zama . Tace saboda me ko akan maganan da saiba tayi zakiki karban abincin aiba ita ta sakaki ba nuce na roka kiyi min kuma nagode da abinda kakai min. Ita haka halinta yake bata da tunane sai ta dauka kowa bai isa ba ita kadaice ta isa a gidan nan shiyasa ko yaushe kuke jin fadan mu da ita a gidan nan ai. Ba ita ta sakani ba ai balle ta dameni na fada ta dan juyo tana kallona sai kuma tayi murmushi a fuskanta tace. Yadda kikayi ai naji dadin hakan Ramaah tayine don kada gobe ki kara taimaka min kiyi fushin zuciya akaina haka take min wallahi. Duk wanda taga ina abin arziki dashi duniyan nan Saiba na bakin ciki da maishi ko gaisuwa batayi da kai indai ina hurdan arziki ki da mutum. Aiko zata wahala wallahi indai Ramaah ce dama bata nuna hakan ba da dukkanku kunji dadinta antyna ta fada tana dariya. Daga wanan ranan da haka ya faru muka dan fara shiri da Asmau a gidan har antyna suna dan biye juna sama sama . A cikin wasa Asmau zata jani zuwa wajenta muyi gyaran daki haka yarta a yanzu yarinyar tayi mugun sabo dani sosai idan ta ganni ta fara washe baki ke nan tana miko min hannu tana son in dauketa. Idan na bushi iska zan shiga wajen anty Asmau din mu dan taba hira sama sama da ita wanda hakan tun yana ba Saiba haushi har tazo takan dan saka muna baki a cikin maganan mu din wani lokaci. Wani lokaci kuma kamar bata san da Allah ya ajeni ba takeyi ranan da yan iskan nata suke kai saidai tayi ta jan tsoki tana jin haushi ta nuna cewa bata son zaman mu a lokacin. Wanan yasa ban faye damuwa da ita ba ban kuma fasa shiga ba idan na bushi iska ranan da ba karatu sai hakan yasa shakuwa sosai yashiga tsakanin mu. Saidai matsalan ta shine kazanta da kuma rowa tana iya hanawa mutane abu koda ba zatayi amfani dashi ba zata bar abin ya lalace saidai ta zubar dashi a karshe. Amma yana da wuya tace maka gashi a cikin dadin rai saidai in rabon mutum ne ya ratsa a gareta sai dai kuma anan saiba gaskiya a dan shigan da nakeyi ita saiba tasha bamban da Asmau din. Don saiba ko bakaga abu ba zata iya cewa dake idan zakici abu kaza akwaishi a kitchen ko kuma idan kun zauna kuna hira ta dauka abin ta mikama shi a gadarance ta juya bambamcin su ke nan. Sakin fuska sai Asmau kyauta kuma Nusaiba amma wajen kazanta gaskiya a ganina kamar suna kwatawa duk da ance wai Nusaiba tafita dama a wanan fammanin. Nasan matan hausa sun camfa mu matan fulani da iya yi da kisisina da makirci wanan kirarine da akewa matan fulani dake auren kado wani lokaci. Wanda a wurin mu abin ba hakana bane na dauka iya kamun kaine da sanin darajan aure wanda ake ganin hakan kamar wani kisisinane nasu sukeyin hakan. Ko a yanzu gidan nan haka suka fara radawa yar uwata don tsananin bin dokan mijinta da kiyayyewa da takeyi. Don duk umurnin da mijinta ya bata bata taba ketareshi tana kuma kafa,kafa da duk abinda ya gargadeta dayi wanan yasa suka saka mata suna zundenta. Don yana da wuyane ka shigo ka sameta a waje ko kaga gilmawanta a haraban gidan idan har ba wajen iya zata shiga ba. Duk shigan da nakeyi wajen su anty Asmau bata hanani saidai ita ta kama kanta kamar yadda mijinta yace kada yaga tana shiga wani rikici yazo ya faru sunanta ya fito a cikon case dinsu. Hakan yasa nima takan ja min kunne a duk lokacin da taga kamar nayi zurfi a cikin sha,aninsi zata taka min burki da jan kunne kada in yarda wani abu ya fito ace nice na fada. Hakan kesa in kara kama kaina dasu saidai a danyi hiran yaransu ko hiran film iyakata dasu ke nan suma din kuma sun fahinci haka a gareni. Hutu muka samu na dogon zango haka yasa muka samu wanan irin zaman da ko yaushe kana gida da sunan hutu saidai a wajena abin ba haka yake ba. Ranan tunda na tashi nayi irin aiyukan dana saba yi a gidan gyaro ko ina na cikin gidan da waje bangaren yayata da kuma bamgaren iya kamar yadda na saba a kullum. Duk da su Anty Sare suna gida a lokacin ban damu da sai sun tashi sunyi ba Allah baisa min kallon irin hakan ba a rayuwata kace baka abu don wani baiyi ba . Wajen yayata na koma don yanzu dasu anty Sare suka dawo hutu tare da ita nake kwana idan mijinta baya gari. Don cikin jikinta dake bata matsala tana yawan zazzabi da amai da sauran laluran masu shigan cikin . Haka kayana har wanan lokacin a wajenta suke sai na amfanina na yau da kullum ne a wajan iya. Kwance na sameta falonta na zauna a wajenta gaidani tayi da aikin yasa na zauna ina dariya nake fadin ina aikin a yanzu Yanda ? Ramaah kinsan abinda ke damuna yanzu ta fada hakan yasa na sake kallonta ina girgiza kaina alaman a,a a gareta. Nisawa tayi tana fadin wallahi baffan mu nake yawan mafalkinshi sosai Ramaah a kwanakin nan yana yawan zo min a cikin mafalkina kamar yana kokarin aikata min wani mugun abune nake gani kinsan baffa mugun mutum ne Ramaah. Baki addu,ane idan zaki kwanta anty tace inayi kuwa sosai Ramaah ai duk dare ya habu sai ya tunana min da addua idan zan kwanta kina jinsa ai wani lokaci. Tunane na shiga yi don sanin da nayiwa baffa mutum ne mai kyashi da hassada kashe mutum a wajensa ba wani abu bane shi da bakinsa zaki yana ikirarin sai yaga bayan mutum idan dan wani abu ya hadashi da wani. Balle mu da akai rabuwan tashin hankali dashi zai iya cewa zai dauki fansa yanzu akan yar uwata din dan abinda ya faru kafin aurenta. Hakan yasa na dago ina fadin anty yanda mu kira hardo mu fada mai yafi abar zancen nan don kinsan hardone kawai maganinsa shi kadai naga baffa yana tsoro a cikin yan uwa. Dan murmushi ta sauke a fuskanta tana fadin Ramaah ban son saka kowa a cikin lamarin nan ni nasan baffa yana wani shiri a kanmu Ramaah ko ince a kaina don ni kadai nasan yadda nake ji tun zuwana gidan nan a wahalce nake kai safe idan na kwanta. Dan dama idan habu yana garin nan nakanji saukin lamarin amma duk da hakan wani lokaci kuma sai nayi wanan mugun mafalkin nasa. Nasan ba zata taba fadawa wani halinda take ciki ba koni din a yanzu data fadawa Allah ne ya matsi bakinta har ta sanar dani din tunda duk dadewan nan bata taba sanar dani komai ba. Saidai na fahinci tana cikin damuwane sosai a lokacin danafi saka ran akan zaman gidan nan ne ko kuma rashin sabo ke damunta tunda nasan bata da matsala acikin lamarin aurenta. Don haka nasan ba zata fadaba ba kuma zatayi komai ba saboda alkunya irin na fulani data gado. Shiru nayi ina nazari kafin na mike na shiga wanka ba tare dana kara mata maganan komai ba abin mamaki kodana fito daga bayin na samu ta dawo cikin dakin ta kwanta da alaman tsoro ko wani abu yana damunta. Bandai yi mata magana ba balle ta fahinci hankalina yayi mugun tashi a lokacin da abinda take ciki din tana kwance har na gama shirina kafin ta mike ta shiga ban daki don kewayawa. Hakan ya bani daman samun abinda nake so na dauki wayanta na dannawa mijinta kira na fice daga dakin yana ganin kiran ya daga wayan yana fadin . Maria ya akayine na amsa daba ita bace yaya nice Ramaah sai naji yace Ramaah lafiya ina yayan taki kuma meya sameta ? Ba komai yaya saidai yana gab da faruwa amma zurfin ciki irin nata ba zata fada ba balle a dauki mataki nan na kora masa abinda ta fada min bai ko bari nakai karshe ba naji yace ina zuwa zan koma kira . Ashe hjynsu mama Dubu ya kira hankali tashe ya fada mata abinda ke faruwa nan itama mahaifiyar nasa hankalinta ya tashi sosai dajin hakan. Bansan ya sukayi ba dai sai ganin hjy din mukayi gidan lokacin da na gama wayan na mayar mata bina tayi da kallo na mika mata wayan take tambaya wana kira nace kawata bata damu ba ta karba kawai ta koma ta kwanta. Nima ganin hakan sai ban fita ba zauna da ita ina janta da hira inda naga ta dan sake muna zaune mukaji sallaman mama tare da iya a part din. Hakan yasa muka fito muna masu sannu da zuwa idon mama dubu yana kan sarakuwar nata cikin tausayi take tambaya da fadin . Maria meke damun kine yaya kike ganin shi a mafalkin naki ido takai gareni na dukar dakaina kasa hakan yasa mama dubu fadin . Aimu ta kyauta muna data kira Habu ta sanar dashi yau wa take dashi garin nan daya kaiki maria yar uwarki kar kiga laifinta irin wanan abin ba a wasa dashi tunda kunsan halin mutumin nan . Bari kawun ku ya karaso yanzu ki shirya kuje da Iya kafin ya iso ki tashi ki shiga ki shirya idan ya karaso sai ku tafi ba magana takeyi ba ita. Saidai ta mike don bin umurnin sarakuwar nata nan iya ta soma magana tana fadin yanzu yar nan duk sabon dake tsakanin mu irin haka ya faru dake gamu a gida daya ki kasa fada min ? Wancan cikin na farko ya zube kin samu wani kuma lalura ya shigeki irin hakan ba zaki fada ba yar nan asan abin yi akai ? Kawu yai sallama suka shigo da anty Sare data rakoshi ina jin suna gaisawa nima na gaidashi na shiga daki wajenta na sameta ta saka hijab saidai ta kasa fitowa falon ta samesu. Juyowa tayi ta kalleni tana fadin yanzu abin nan da kikayi Ramaah kin kyauta ke nan don Allah zaki tayarwa mutanen nan da hankali haka Ramaah wanan yasa ban fadawa kowa halin da nake ciki nake bari a zuciyana. Hawayene ya zubo min lokaci guda na soma fadin Yanda idan ban fada ba ki halaka ina kallo kuma na sani baffa mugune komai zai iya aikatawa akan kuma don ya fadi hakan kuma mun sani. Muryan mamace dake fadin idan kun shirya ku fito mana kuje maria hakan yasamu fitowa falom muka samesu take fadin sai sun dawo iya zancen nan kada ya fita a cikin gidan nan don Allah. Bana son azo a wuya zancen ta wani tsiga kin dai san halin yaran nan matan shiyancan yanzu ne da sunji zancen zai juye zuwa wani daban. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K44JhTApwmM4gU33AbpqHC MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,, 1️⃣2️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, (Ikon Allah )abinda malamin ya fada ke nan ya dago kai ya kalli kawu dauda da iya da suke zaune gabanshi cikin damuwa tare da son sanin ainihin abinda ya kawosu. Ga mamakin kawu dauda dake sauraren malamin zancen Yanda ce ya kawosu saiga malam ya fara wasu zantutuka na daban da bai shafi ita Yanda din ba sai yayan mama dubu. Yana faman fadin umm,umm subbahanallahi Allah ya kyauta ya dago kai yana ajiyan zuciya yace wanene fari dogo haka matashi a gida ? Su biyune guda yafi guda haske a cikinsu dan tsayi kawu dauda ya kallo iya kafin ya mayar da kallonshi kan malamin yana fadin mun ganesu yayan mune saidai don Allah malam idan akwai wani matsalane a game dasu abari mu gama na wanan yariyar a yanzu kafin a furta nata take mutumin ya fahinci me kawu yake nufi. Sai malam yayi murmushi yana fadin gaskiyane ita wanan da tana tabuwa malam dauda aida tuni an gama da ita ko saidai labari to saukin abin dai yaran nada tsarin ubangiji a jikinsu. Saidai ayi ta raunana cikin da take samu amma ba ita ba wanan hayaki zan bata da rubutu yanzun nan ta shaye insha Allahu ba abinda zai faru da cikin jikinta data sauka lafiya kai malam dauda kazo nan ka sheda min daga wanan karon za a daina bibiyanta amma turene da akai mata na iska da suke son lalata cikin jikinta din . Zata dage kuma sosai da addu,a shi kansa wanda keyi yasan yaran suna da wani baiwa da Allah yai masu wana da wuya a iya cin masu da sauri barma yar uwarta da tafita karfin tsari a tare da ita. Ya dai bata abinda zai bata sun aje zance kawu zai dawo karban abu yake fadin ai matsala da sakaci yakai ga hakan amma yaran nan da nake zance uwarsu ce da laidin komai don akwai wata mace dataso taimaka mata amma ya kasance uwar bata mayar da hankalinta ba. Sam kawu baison zancen a gaban yar uwata hakan yasa ya kau da maganan akan zaije ya dawo sukai mashi godiya tare da dan bashi abinda zai bashi na goron sadakan taimaka masu din suka bar wajenshi suna godiya. Hankali iya yai matukar tashi amma kawu ya kwantar mata da hankalin hakan ba komai bane ai suka bar zancen. Kawu bai kaunar komai za a fada kada wata mace daga cikin sarakansu taji zai kasance abin sirine da iyasune zasu iya jin matsalan a tsakaninsu yasa ya hana zancen gaban yar uwata. Shima a tsorace yake da abinda malamin ya nuna don baisan abinda ke shirin faruwa da diyan yar uwar tashi ba lokacin da sunanansu ya fito a zancen malamin . Don shine bai tsaya yayi bin kwakwafi ba a lokacin kan zancen don Yanda dake kusa ga yanda din bata cikin kwanciyan hankali kan matsalanta. A gida kuma bin kwakwafin tambaya suke min don saiba taga fitan su iya gidan da yayata saidai bata san inda suka dosa ba da ita hakan yasa tazo tana fadawa kishiryarta . Wace yau ayi fari gobe zama duk da shirin bai wuce na yan mintuna ayi fada a shirya don dokan da mijin nasu ya saka akan duk wace ke ja mashi matsala zai rabu da ita a cikinsu. Asmau ce take bugun cikina taji inda suka tafi na nuna mata bansan fitansu ba ai ina daki suka fita hakan yasa ta kyaleni da zancen. Sun kai wani lokaci kafinsu dawo gidan ina part din antyna na kara gyara ko ina dan shigowan da akayi din yasa na kara tsabtace wajen tas. Har cikin falon iya ta rakota tana mata sannu kafin iya din dan matsa kusa ds ita tana fadin ki kula kada kowa a gidan nan yasan halin da kike ciki ki kumayi yadda aka ce kiyi din . Ta amsa a galabaice ta samu waje ta kwanta abincima sai da kyat na samu taci saboda damuwa da take ciki a lokacin hakan dana ganta cikine ya dan daga min hankali sosai ban dai nuna a fili ba. A cikin dare mijinta ya shigo gari daga misalin karfe tara saura muna falo zaune ya shigo horn din motarshi taji take fadin yaya Habu. Na dago na dan kalleta a inda take zaune naci gaba da kallo tunda batayi magana ba nayi mamaki sosai daya tabbata shi dine ya dawo a lokacin. Banyi shishigin tashi ba na dai gaidashi da dawowa na nufi kitchen na dauko mai goran ruwa kodana kawo na sameshi ya rankwafo saman kanta yana magana da ita na aje ruwan da sauri tare da nufar daki. Don kada insha hakkinsu a yadda na gansu din ba don niba a lokacin tugimar matarshi zaiyi a jikinshi kayana duba na dauki abinda zan dauka zuwa part din iya. Na fito na barsu nan a falon bayan fitana kuwa abinda danake zargi ya faru don rugumeta yayi a jikinshi yana fadin Maria hope ba abinda ya taba lafiyan ki dai yanzu ? Tayi na rai narai da idanu tana fadin ba komai ya Habu saidai yawan mafalkin da nakeyi shine ke daga min hankali sosai. Kara jawota yayi zuwa jikinsa yana shafan kanta yake fadin ba abinda zai faru dake wanan karon da yardan ubangiji Allah ya fishi yafi mugun nufinsa akanmu insha Allah. Nan ya zauna tana masa bayanin irin yadda take wahala sosai a cikin mafalkin haka kuma yayi ta kwantar mata da hankali yana karfafa mata zuciya akan ta yarda ba wani mahaluki da ya isa yaiwa dan uwansa mutum wani abu sai Allah. Su anty Sare na samu a falon suna kallo na shigo sai lokacin suka sanda dan uwansu ya dawo gari ban tsaya falo kallo ba na nufi daki don in gyara inda zan kwanta a lokacin. Nasan ba lalai bane in samu dakin yadda nake so Allah yayimu fulani da tsanda da tsabta don akwaimu da tsabta sosai nima din haka na kasance a cikinsu lokacin. Banji motsin mama ba har na kammala gyaran dakin na sake fitowa falo na zauna ina tambayan mama nan suke fada min aita koma gida tunda akai magariba. Mun dan taba kallo muna hira jefi jefi dasu a wajen nakoma daki na kwanta tare da tunanen halinda yar uwata take ciki a lokacin. Don nasan baffa mugun mutumne baida imani ko kadan a rayuwansa tunda kuma tace tana ganinsa ko wani lokaci a mafalkinta dole akwai wani mugun abinda yake aiwatarwa akan mu lokacin. Amma yar uwata mai tayi mashi da mahaifinmu yake fadanshi tsakaninsu don me zai taba min yar uwa kuma a yanzu wani irin tsanar baffa naji kasan zuciyana irin da ban taba masa ba sai a ranan duk ko da wahalan da mugasha a hannunsa ? Haka barci ya daukeni washegari dana falka banyi sanyin jiki ba wajen gyara ko ina dana saba gyara kafin na shiga nayi wanka na gyara jikina. A yanzu ban damu da yin abin karyawa ba a part din iya kamar yadda nakan yiwa iya idan muna mu kadai daga sai ita don ganin masu part din sun dawo hutu a lokacin. Don haka yasa na koma na kwanta bayan nayi wanka na gyara jikina tsab sai barci ya dan daukeni ban sani ba. A cikin dan barcin dana dan samu nayi wani irin mugun mafalki daya firgitani na tashi ina zufa ina bin dakin da kallo. Muryan iya na tsinkayo a falon naji tana fada da yan matanta kan basu fito sunyi mata abin karyawa ba har rana wanan lokacin haka ? Mikewa nayi a cikin sanyi jiki na fito falon na samesu fada tsohuwar keyi sosai dasu suna zaune suna kallo an rasa mai motsawa a cikinsu ta shiga kitchen din a lokacin. Nima ban shiga ba na samu waje na zauna ina gaida ita da kwana ta amsa take fadin . Ke dai yar nan kedai sannu da kokari kinfi min mutanen banzan nan da basu san ciwon kansu ba gidan nan suna koyi da halin wa yan can shashashun matan dan uwan nasu. Inda mace zatayi kwance cikin lalaci da kiuya ba zata zage ta tsinanawa kanta komai a rayuwanta wai a haka kuma mace zatace aure takeyi don lalaci ? Da kece iyanzu nakai ga abin karyawa a gidan nan amma su wai yanzune zasu dora min abin kari da rana tsaka kiri kiri haka ? Sallaman ya Habu ya katseta take fadin kai kuma yaushe kadawo garin tana mashi kallon mamaki ? Saida ya karasa shigowa falon yace tun jiya da dare mana nasan kinyi barci a lokacin yasa ban shigo nan ba ai. Antyna ce tashigo a bayanshi tana dauke da kayan karya kumallo data hada a hannunta tana gaida iya da kwana sai binta takeyi da kallo cikin mamaki. Yar nan har kinyi karfin halin tashi shiga madafi yin giki a yadda kike din nan hankalina ya daga matuka da zancen yarinyar nan jiya . Abin tausayi wai ace kuma yar nan mai hankali har akwai wanda ta tarewa wani abu a duniyan nan yake binta da sheri. Wai, nakane yau yake kokarin illanta ka haka don bakin ciki an daiyi mutum banza a wajen nan wallahi wanan mutumin da zan gashi saina tsine masa albarka. Kina zaginsa mugune fa iya kada yazo ya waiwaiyeki habu ya fada yana zama a saman kujera sai naji iyan tace meye hadinshi dani kuma da zai dawo kaina ? Wayace ki zageshi yanzu yana iya jinki ai koba haka aka fada maku ba a can inda kuka je jiyan ba zaginsa nayi ba habu halinsa na fada ai yanzu . Muryan Yanda cetace Iya ki kyaleshi ga abin karyawa na kawo maki ta fada tana aje bowl din data riko a hannunta ta samu waje itama ta zauna a kusa dashi ta fara gaida iya dake fadin Allah yai maki albarka yar nan kinji. Yanzu nake sababi da yaran nan suna daki sun mimike kafa wai sai yanzu zasu dora muna girki ta fada tana kiciniyar budan kwanan gabanta din. Nan Sare ta taso tana dariya ta karbe kwanon tana budewa iya ta soma fadin kingani ba, ki duba ba kunyane dasu ba ai, ace mace na kwance wai tana barcin safe a daidai lokacin daya dace mace ta mike ta dorawa mijinta da yara girki safe. Idan baku koya a yanzu ba sai yaushe zaku iya hakan don Allah, irin wanan lalacin shike wahal da matan shiyan can da yayanku yatara. Idan baka koya a gida sai bayan kayi aure kace zaka koyi abu yanzu don basu koya a lokacin daya dace ace sun koyi hakan ba yaushe zasu iyashi yanzu. Dankalin turawane da kwai shake a cikin kulan da Sare ta bude din take fadin nasan dai wanan har damune aka zuboshi. Nasan baza a rasa ruwan zafin da za a hada shayi a nan ba ai shiyasa ban dauko ba maria din ta fada tana kallon Sare. Hakan yasa na fahinci ta zubawa kowane harni mu karya a nan din mikewa nayi na dauko plates s kitchen na fito dashi na zama nayi na fara dibarwa iya dana fahinci tsohuwar tana jin yunwa a lokacin don fadan da takeyi. Na zuzuba masu a cikin plate na mikawa kowa nasa lokacin naji ya Habu ya soma magana yana fadin Iya zankai Maria asibiti a dubata ? Wani abin kuma ya samu maria din iya ta fada tana duban yar uwar tawa yace a,a iya zandai kaita a dubatane ko da abinda zasu iya bata asibitin ? Wani kallo tayi mai tana hade dankalin data tura bakinta dakyat tace Habu kana haukane da zaka dauki matarka dake fama da laluran jinnu zuwa asibiti ? Jinnu kuma iya ya fada yana kallon tsohuwar yayinda yar,uwata ta dukar da kanta kasa cikin sanyi jiki nabita da kallo cikin mamaki jin abinda tsohuwar ta fada. Kaga mubar zancen nan yanzu ka bari uwarku nasan tana nan tafe gidan nan taje ta shirya wajentane ta dawo yau din nan don ta fito jiya bada shiri ba yasa ta koma gidan. Sun dan jima a part din kafin su fita nabi yar uwata da kallon tausayi don na fahinci me iya ke nufi da zancen ta saboda matar baffa dake fama da matsalan jinnu idan tafara lalura saita ba mutum tausayi. A yadda naji yan rugga suna fadi lokacin wai saboda matsalanta baffa ya aurota don ta rasa manemi baffa yace shi zai iya yanzu har ta haifi yaya uku da baffa lokacin da muke rugga din tare dasu. Tuna hakan yasa hankalina ya daga sosai a lokacin gashi mijinta yana gari bamu samu kebewa da ita ba tun safe saboda mijinta dake gari. Misalin shabiyu saura mama ta iso da alama zata kwana biyu a gidan don bata saba zuwa da kaya haka masu yawa ba idan zatazo. Balle a yanzu din da taga inawa mahaifiyarta komai mama din ta rage zuwa sosai kamar yadda takeyi a baya zatazo tayi sati biyu ko wata kafin ta kwasa ta koma gida kuma a yanzu saidai tayi kwana biyu ko ukku ta koma. Munyi mata sannu da zuwa nice na dauko ruwa na kawo mata tana zaune iya tana bata labarin yayan matan mama din yadda suka kwasa dasu da safe. Daki na koma tunda na fahinci kamar suna boye muna halinda ake ciki yasa na nuna ban damu da insani ba nima saidai a zuciyana zancen jinnun da iya ta ambata yana daga min hankali. Yar uwata da take kamar uwa a wajena tun tasowan mu da ita na bude ido yau naga tana son shiga halin rayuwa duk da ta girme min nisa ba kusa ba amma tare muke komai da ita ko yaushe muna tare muna gudanar da rayuwan mu. A bakin iya nake jin cewa wai ashe sun fita asibiti a ranan duk data gargadesu da zuwa asibitin fadan da takeyi da yaya Habu din a lokacin ya tayar dani daga dan barcin dana samu a lokacin. Kiran sunana da ya habu din yayi yasani fitowa ina amsawa yake fadin naje Yanda din tana nemana a part dinsu. A kwance na sameta falo da alama sosai tana jin jiki don yanayinta daya nuna hakan sosai a lokacin gaida ita nayi take fadin in gyara part din in dora masu abinci . Cikin dan lokaci kankani nayi duk wani abinda ta umurceni da yi a lokacin na jera masu abincin dana samu taci sosai saida mijin ya shigo wanda kallo daya zakai mashi kasan yana cikin wani yanayi na bacin rai. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K44JhTApwmM4gU33AbpqHC MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 1️⃣3️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Sosai mama Dubu ta bada lokacinta tana kula da yayata haka kuma taja min kunne nasa ido kan yar uwata sosai ga duk abinda zataci ko zatayi a gidan. Hakan kuma nake wanan kokarin duk da a lokacin akwai sauran kurciya sosai a kaina amma ban fita saina tabbatar da nayi komai daya dace a gidan. Dana dawo kuma zan shiga in mata abinci da gyaran waje saidai indan mijinta yana gari dan yanzu bai faye dogon tafiya ba sosai. Koya tafi baifi yai yan kwanaki ba ya dawo saboda laluran matashi a yanzu duk da abin baikai daga hankalin da kowa zai fahinci akwai matsala ba gareta. Bayan kamar wasu yan satutuka ya Jafar daya je kasan waje kamar yadda nakeji a bakin matanshi da yan uwansa ya dawo kasan. Ranan Anty Saiba ta sauke jin kanta ta samemu a part din Iya zaune muna kallo take fadin Sare zuwa nayi don Allah muje wajen mu ku tayamu aiki. Anty Sare na mata ba,a da cewa lalaima ba dole ba maigida zai dawo ana mashi soye suka dan taba ba,a zata tafi har ta juya sai kuma ta tsaya tana fadin . Ramaah har kefa zamuje don aikin yayi muna yawa sosai gashi rana yayi komai bamu hada ba yasa nake son don Allah kuzo ku tayamu. Mama dubu ta kalli inda nake zaune tana fadin Ramaah ai bata da matsala ga dai mashiririta nan su da kika fara gaiyata ba komai zasuyi ba banda surutu. Saida naje wajen antyna na gyara don mijinta yana iya fadowa ko wani lokaci gidan yasa koda yaushe cikin tsabtace mata wajenta nake zakice ba wani mahalukin dake rayuwa a part din don yadda yake kal ko dayaushe. Nayi mamakin yadda na samu wajen nasu don na kwana biyu banshiga ba saboda exam din da mukeyi banda lokacin laka part dinsu a yanzu . Haka kuma iya ta hana wanan aikin da Asmau ke fakewa tana sakani a baya yanzu iya tayi mata gatse da hakan yasa na samu ta shafa min lafiya. Don wai ashe shigan cikine da ita lokacin yasa take narkewa haka bata iya yiwa kanta komai a rayuwanta nayi mamakin yadda mata biyu zasu kasa gyaran wanan katafaren ginan nasu . Su biyu sai yan yaran su amma part din har wani bashi yakeyi da tsamin dauda tunda daminane a lokacin aka shiga. Kitchen na samesu tsaye suna shawaran abinda zasuyi din ga dai kaya abincin nan amma da yawa sun lalace saboda rashin amfani dasu da ba ayi sun lalace. Wanan bashin kuma wai daga fridge dinsune wari ke fita haka da ace nice zan kwashe kayan nan kaf in kyautar dashine in wanke fridge din insaka kamshi ko wani yaro ba zanso yaji wanan warin da fridge din nan keyi ba balle babba. Saidai kashh duk sherin da Sare ke zuba masu kwando kwando bai sa sun duba maike wanan warin haka su fitar dashi ba karshe falo muka koma muka kara aikin ko a nan ma warin bai barmu mun zauna da dadin rai ba. A dakin Nusaiba maigidan zai sauka shine dalilin wanan shirin da mukeyi din inda Asmau take dakinta tana shakar barcinta hankali kwance saida muka dawo falone hayaniyar mu ya tayat da ita ta kuma dan jima bata leko falon ba a lokacin. Saida ta bushi iskanta ta fito sabe da yarta a kafada da dan cikinta daya tasa kadan tana fadin duk aiki ake sha hakane ? Banza kowa yayi da ita ta samu waje ta zaune don sun fahinci kishine ya hanata fitowa a yadda na kula su anty Sare sunfi kula Saiba bisa ga Asmau wata kila don kyautantane data dara Asmau din dashi ko kuma wani abu can dai na tunanensu. Dukko da cin mutunci irin na Saiba da nuna ita watace kuma matan wani saidai zasuyi fadan kiga sun dawo sun shirya kuma dasu nidai wanan abin yana daure min kai dasu sosai wallahi. Munyi cake dunut milk pop wanda a karshe aikin ya dawo nawa suka koma tayani don da ban wajen shirme zasu tabka da hasara don basu iya kwabin bama balle . Wasa wasa saida muka kai yamma don suyan kajin da muka tsaya yi wanda yayi ja gwanin sha,awa dashi sai bayan magariba muka samu kan mu da aikin muka kammala . Ni dai ina mamaki rashin ganin sun gyara falon gidan tsab da sauran part din gidan kosu Sare banji suna masu tunin hakan ba a lokacin a kasan raina nake mamakin hakan sosai a lokacin. Wanka na shiga antyna tana falo zaune tana azzakar Saiban ta shigo part dinta tana fadin ina Ramaah ga dan abin da mukayi na debo mata. Tana wanka Anty maria ta fada ta aje saman table suka danyi gaisuwa sama sama da yar uwar tawa da sai bin wajenta takeyi da kallon mamaki don ko kai waye shiyan yar uwata dole ya baka sha,awa kome tsab yake ga kamshi. Ita Saiba zance baifi sau nawa ba duk dan zaman mu gidan data shigo part din sai wanan dalilin daya kawota yanzu din. Kodana fito wanka ta fice antyna ke nuna min nake fadin kici donni ya hau min kai tun a wajen suyan da mukayi din na koma nayi sallah. Saida na fito take fadin ina ganin Habu yana hanya Ramaah kallon ta nayi ina fadin ya bugo ke nan tayi dan luuuu da ido tana fadin haka dai naji a jikina kawai kamar shima zai zo dai yau. Hira muke jefi jefi da ita wanda hiran zaman mu na Abujane wanan abin da mukayi ya tuna muna idan wani zai dawo gidan yadda akan wuni ana gyaran waje da aiyuka saidai su banga hakan garesu ba ko kadan. Karan wagale get din gidan da akayi ya katse muna hiran mu wanda mazan gidan ne suka iso lokacin ashe zancen antyna gaskiyane ya Habu shine yaje ya dauko dan uwansa da yai wajen wata uku bai kasan . Ta window part din anty na muka leka mukaga tare suke ashe dukka su ukku har da wasu mutum biyu a lokacin. Ya Abubakar ya jima bai shigo part dinsa ba don sun tsaya a na sauke kayan yayan nasu zuwa part dinshi na tsaya jiransa mu gaisa sai gashi ya shigo mukai mai sannu da zuwa. Shi mutum ne wanda baida sakewa da kowa haka yake dunkunkun dashi ni ina mamaki ma yadda suka hadu da yar uwar tawa haka. In har kinji muryan yaya Habu yana tare da iya ne ko mahaifiyarsu saiko idan ransa ya baci zai tsaya yayi fada akan abin ko kuma ya barka a cikin zullumin abin. Bayan na gaidashine na shige na dauko abinda zan dauko nafice na koma wajensu iya a zaune na samesu ga kayan tsaraban da aka shigo dashi part din tsofin a gefe daya an tara. Ban zauna falo hira ba saboda gajiyan dake jikina na shige dakin kwanan mu nan ma ba kwanciya nayi ba saida na dan tsabatace dakin har ban dakin kafin na kwanta. Can cikin barci nake jin maganan su Saare dake fadin dama nasan wanan abin sai yaya yayi fada wallahi idan ya iso ya samu waje haka. Warin ne yayi yawa Salima ta fada tana hawowa saman gadon da muke kwana tare da ita tace na bude fridge din aina duba naman kaine yake wanan wari haka. Makin su zubar amma wai sun aje basu fitar dashi ba duk part din ya dume da warinsa ga kuma kazantan dake falon koshi ai takaicine. Banfa sa sunda yau zai shigo garin nan ba Saare ta fada nan nasa masu baki nace kuma gashi munyi aiki ba a gyara falon ba saukin abin ita Saiba ta dan gyaro wajenta dazun din don kodana shiga na samu tana gyaran dakinta ai. To ai a banza Ramaah duk fa cikinsu babu mai tsabta a raina nace kamu na zagin koko ke nan kuma ai halin kuka dauka na fada kasan zuciyana. Sai gashi Salima na bata amsa da fadin abinda iya ke fada muna ke nan kullum wallahi nima dai zagewa zanyi da koyon irin na Ramaah ina dan aiyuka a gidan nan don in saba. Tabe baki Saare tayi tana fadin ko ita dake hakan ai halittance hakan bawai yin kanta bane muryan ya J ya dakatar damu don tabbas a falon iya yake wanan tsawan. Tsit mukayi a dakin muna saurarenshi yana fada ina zan iya kwana cikin wanan kazantar haka iya sai doyi da bashi wajen keyi a nan dakin yusuf zan kwana yau. Muryan mama naji tana mashi fada akan ya koma ya kwana wajen matanshi ai dole su gyara tunda ya nuna masu bacin ransa a fili. Can dai muka daina jin muryanshi a haka barci ya daukeni sai washe gari na falka don akwai gajiya sosai a jikina na mulkan fulawan da mukayi jiyan. Hakan bai hanani fitowa nayi aiyukan dana saba yi ba anan suka dawo suka sameni part din iya suka nufo gaba dayansu shida ya Abubakar din. Wanan ya hanani komawa part din na nufi wajen yar uwata bayan mun gaisa na karbi aikin da takeyi din nacigaba ita kuma ta koma dakin kwanansu tana gyara. Har inda na gama bai shigo ba dakina na koma nayi wanka na gyara jikina lokacin naji muryan shi ya shigo yana fadin . Bansan ya matan can suke son mayar da kansu ba gidan nan miji ya dawo tun jiya yake bala,i dasu akan kazanta ki shiga ki saka hijab dinki kije wajen iya zamu zauna a nan. Ma,ana dai a fahintana zasu dan yi magana da dan uwan nasa nan part din antyna ke nan hakan yasa nayi sauri karasa shirina a gurguje na fito daga dakin kusan lokaci daya muka fito a dakin da ita. Muna gaisawa dashi take fadin naje kitchen na fito mashi da kayan karyawa ita kuma naga ta koma dakinta na dauko muka aje muka fito tare da ita daga part din. A wajen muka samesu shida kawu suna magana muka gaidasu tayi mai sannu da dawowa muka shiga ciki wajen su mama din dake falo suna duba tsaraba. Shi tsaraba ga iyali wani abune mai daraja dana sanshi tun ina kankanuwa a gidan hjy Fannah Abuja idan wani daga cikin iyalinta yaje tafiya ya dawo haka zai bimu da tsaraba gaba daya gidan ba wani raba kai ko nuna muba yan gida bane a wajensu haka zasu kawo muna tsaraba mai yawa da sunan mu. Haka kuma zamu dunguma anawa wanda yakawo din godiya group group yadda muke gidan tana saka muna albarka gaskiya don in tuna da wa yan nan mutanen arzikin a rayuwana. Naso antyna ta barni naje ko nidaya na ganosu tace min sai idan mijinta ya yarda da hakan dana kara tuna mata kuma sai cewa tayi dani wai yace tare zamu gaba daya da ita tun lokacin ban kara magana ba kuma. A wajen su mama din gefe muka koma sai can mama din ke fadin idan kin tashi maria ga taku tsaraban nan ta nuna mata wasu kaya harda na abinci shi yaya Habu din yazo ya kira mama din da kansa . Sun jima a can har iya yayin da antyna ta kwanta a nan falon tana barci don maganin da take sha a yanzu barci yake sata da zaran tasha maganin da safe. Lokacin da suka shiga falon Habu din Jafar ya shakin kamshin da falon keyi ya dan lumshe ido yana sauke ajiyan zuciya bin ko ina ya farayi da kallo komai gwanin ban sha,awa awajen, irin falon da yake muradin samu duk da part dinsa ya kusan ukun wanan din amma kazantar matansa ya hanasu tsayawa su gyara din. Duk da komai na zamani na more rayuwa ya zuba a falon gwaunin ban shawa amma komai yazo ya koma masu shara a yanzu don rashin kulawansu. Yana mamakin irin halin da matan nasa suka dauko yi mashi a gidan gaba dayansu ba wace zai buga gaba da ita a wajen tsabtan muhalinsu wanan abin yana matukar kona mashi rai. Nan ya Habu din yake gabatar masu da abin karyawan da aka aje mashi din a tare su ukkun suka karya a nan mama tazo ta samesu a part din don zancen dasuka zauna suke son magana da yaran nasu baki daya. Zama sukauyi na fahinta yadda ya dace din a tsakaninsu kan matsalolin da malami ya fada a zancenshi . Wanda kusan abin duk kamar akan shi yaya jafar zancen ke nufi da magauta suna binsa sosai bayansa. Sam bai dauki zancen da wani ma,anaba a wajensa don bai faye yarda da irin zancen malaman nan bashi kawune ma ke kokari ko yaushe akansa baiki yake karba. Yanzunma bai ki ta bakinsu ba don yasan dolene irin wanan harkan nasa ya samu irin hakan bayan sun gama kuma sukayi zance akan matsalolinsu inda harda zancen yayata ya fito cikin zancen. Don asibiti suna son su riketa a can wajensu sai zuwa lokacin data haihu sin yanke shawara kan mahaifiyar mu zatazo ta zauna da ita wanda already sunyi maganan hakan da hardo shine ya yanke shawara kan mahaifiyar mu zatazo ta zauna da ita din a asibitin. Azuciyarshi shi kadai yasan yadda yake ji a ransa a yadda yaga part din yar uwata din data gyara shi fes wanda shi a rayuwansa bai samu hakan ba duk da uban daulan da yake labta masu agidan. Haka yasa ya kara jin bacin rai a zuciyarshi yana tuno irin zancen da suke fada akan auren bafulatana da Habu din yayi saida wata rana ya fito ya tsawata masu akan irin maganan da suke yawan fada a lokacin kafin a auro yanda din a gidan. Yau sai gashi bafulatanan da sukewa dariya tazo da tsarin da su suka kasayiwa kansu suna tauye kansu da nasa hakan yasa a yanzu yakan sharesu na tsawon lokaci ya zauna a can abinshi yana harkokin gabanshi. Hakan kuma bai hana idan ya tashi zuwa gida zai tsaya ya sayo masu kaya na alfarma na kyace raini da za,a gani a fada a wajensu. Sai kamar bayan kwana biyune da faruwan haka ranan jumma,a kowa yaci kwaliya da dogayen rigunan daya sayo masu inda na dauki wani kampalana dinkin dogon riga na saka a jikina . Zaune muke muna kallon film tare dasu mama dubu suka shigo part din gaidasu muka farayi ban faye zama a falon ba idan suna falon nakan daga in koma ciki ko in fice zuwa wajen anty na muyi hira. Sai bayan sun gama gaisawa na mike na nufi cikin dakin kwanan mu lokacin mama dubu ke fadin niko Jafar ina ta son in maka magana akan wani abinda kayi da ban samuyi ba sai yanzu. Ya kamata ace kayan nan daka sayo ka hada da wanan yarinyar da zamanta yanzu ya dawo a nan bai kamata ace idan zaka sayowa matanka da yan uwanka abu kana debeta a ciki ba. Naji nauyi sosai da kunya tunda yau da kowa ya saka tsarabansa yai adon jumma,a dashi a gidan nan sam banji dadin hakan ba wallahi. Mama wace yarinya kike nufi tace kanwar matar habu din nan mana da take tare da yar uwarta gidan nan . Yarinyar da kwazonta wallahi ko wanan abin da kake ta yabon matanka sun hada itace yarinyar nan ta hada masushi . Hakan ma ba girma bane duk zancen da suke kanyi baice uffan ba don a saninsa ya fada masu cewa da matar Habu da yar uwar nan nata a cikin tsarabansu sai Habu din yake fadin . No ki barshi mana mama aiba sai ya basu abinda duk ya kawowa matanshi ba hakan wani sabon fitina zai iya kawowa kuma a tsakaninsu ai. Ke nan itama matarka ba a bata ba ke nan kake nufi ba,a bata ba gaskiya yaya Saare ta fada daga gefensu tana kallon yayyun nata. Nasan udan kince sai anyi hakan zai iya kawo matsala a gidan nan don Allah a barshi kada a kafa wanan hujjar don ni kaina ba zan iya hakan ba ko wani lokaci. Amma Habu kai kace kai ai karami sama dashi ba dole bane sai yabawa matarka amma yar nan dake tare da yaran nan hakan da nauyi gaskiya ace komai ba a bata ba cikin abindaya sayo a gidan nan . Mama ta dauki takakmana idan zai mata ban faye son takalma irin wanan ba dama Salima ta fadawa uwar nasu dake magana cikin damuwa. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K44JhTApwmM4gU33AbpqHC MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 1️⃣4️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Ranan monday da safe na samu labarin abinda ke faruwa a gidan koshi abakin anty Salima da yanzu muke dan shiri sosai da ita. A wajenta nake tsuntar labaran abindake gudana gidan nasu don ni ban damu da nasan komai ba abu daya zuwa biyu nafi rikewa a raina shine nidai yar tafiyace ma,ana yar rakiyar aure. Nazo gidansu a sanadin rako yar uwata aurene saboda debe kewa a gareta nasan kuma rashin gata yasa aka hadomu tare ba wani abu ba don a ragewa mahaifiyar mu nauyi a gabanta. Idan bashi ba a shekatuna goma sha nayi girman da zan zama yar tafiya na koma Murfin Jallo ga yar uwata da yanzu auren nan kamar ta danballene ma nake gani don da da dan kuzarin ta amma a yanzu ta koma wata sau da ita bata da lakka ko wayau. Don haka tuna sanadin zuwana gidan bai bari na wuce iyakata ba iyaka dasu halin zama tare sun bani mafaka ni kuma in basu karfina wajen abinda ya dace. Zance bai tasowa tun zuwan mu gidan kaji sunan yar uwata a ciki balleni musan yadda muke takon mu dasu bakaji zance a bakin mu saidai a kiramu don shedan muna wajen abin ya faru. Koshj wanan zancen a zaton salima nasan da zancen take fadin gobene za a kai Maria asibiti ko ? Azotana irin zuwan da sukeyi suje awone take tambayana sai nake cewa eh gobene sai naji tace dani Allah sarki ni tausayi mariya ke ban wallahi a daidai lokacin da mutum yake son zama da mijinshi ace za a rikeshi asibiti ya zauna har sai ya haihu wanan abin akwai takura ai a cikinsa wallahi ? Anty Maria din zata zauna cikin asibiti har sai ta haihu anty Salima tace ba haka akace ba Ramaah koke baki fahinci zancen bane wai Ramaah ? Kodana dago kai hawayene ya bata min fuska ban iya magana ba ta juya ta shiga bandaki don dama wanka zata shiga muke hiran . Mikewa nayi na fito daga dakin zuwa wajen yar uwata da akwanakin nake ganinta cikin damuwa zaune na sameta a falonta ta kifa kai a saman hannun kujera. Nayi sallama na shigo fuskanta kawai na kalla nasan itama tayi kukan a lokacin nafara fadin meyasa baki fada min abindake faruwa dake bane Yanda ? Duk da sunan yanda din da suka san ma,ananshi a yanzu sun mayar da sunan akaina a gidan ni kaina a yanzu ina kokarin karbe mata sunan nata da mahaifanmu ke kiranta dashi na yan mata. Mezan fada maki Ramaah tashin hankalin da nake ciki kema ki shiga amma ai ba yau muka fara fadawa junan mu tashin hankali ba yanda nakirata da sunan da muka saba kiranta dashi din. Nacigaba da fadin ko a yanzu ban cancanci naji damuwanki bane kamar baya yadda muka taso daga mu sai Allah sai mahaifanmu a tare damu. Ramaah me kikeso na fada maki nace dake likita yace ba zan iya renon ciki ba sai da kulawansu duk na tayar maki da hankali kamar yadda nawa yake a tashe ? Kallon kofan dakin su da takeyi yasa na juya mijintane a tsaye yanayinshi kadai zaka kalla kasan yana cikin matukar damuwa shima din a lokacin. Hakan baisa nayi shiru ba don da yare muke maganan nace kinsan matsalan ki yanda bata asibiti bace dole sai mun koma wajen baffa an suhunta dashi zaki zauna ki tauye kanki a nan kuma ? Ba wai hakana bane Ramaah abinda likita ya fada suke bi duk da nasan abin nada alaka da baffa amma su nan birnine ai ba zasu yarda da hakan ba su. Gyaran murya yayi na sake juyawa gareshi karasa fitowa yake zuwa falon ya samu waje ya zauna yana fadin lafiya dai ko ? Kalloshi nayi cikin yanayin damuwa ina fadin ina kwana ya amsa sai naji tace zance take akan tafiyana asibiti wai lalurana bana asibiti bane sai naga ya tsuke fuskanshi lokaci guda. Yana fadin idan bana asibiti bane na meye ke likitace Ramaah da zaki fadi taki hasashen abinda likita ya hasaso gareta ke nan ba zatayi wani dogon motsi ko daukan abu mai nauyi ko wani abu da zai iya taba lafiyan mahaifan dake dauke da jinjirinta ba a yanzu ? Don haka dole sai sun riketa a wajensu suna bata kulawansu su saka ido ga duk wani motsi nata a yanzu shine kawai dalilin da zata zauna a wajensu din ai. Ummah zatazo daga Jimeta a gobe insha Allahu itace zata zauna da ita asibiti don haka wanan ba wani abin damuwa bane insha Allah. Duk da naji ummah mu zatazo zama da ita hakan baisa naji dadin zuwan nata ba don nasan wahala kadai zatayi a can din tuno da lamarin baffa da zuciyana ke min. Akan bakin halin baffa a lokacin a gaban idona naga yadda yake tauye Hanne data shiga huruminsa abinda bai kai ya kawo ba amma haka baffa ranan don fada kawai akan yara da suka kora shanunsu zuwa kiwo suka samu hanne ta riga su zuwa da nasu shanun a inda zasu sake shanun mu. Sukai magana ta kwashe taki kwashe shanayen nasu tace aita rigasu zuwa dole suka juya da nasu shanun zuwa wani waje suka sakesu kiwo. Bayan an dawo gidane baffa ya taresu yana fadin yau shanu basu koshi ba yasan kuma komai shi Hanne zatayiwa tsageranci zai nuna mata ko ubanta bai isa ja dashi ba balle ita. A gaban mu ya fito da wani babyn roba mai gaba gaba zakice mutum ne kamar wata jaririyace a hannunsa ya shiga dakinsa dashi a hasale. In gajarce maki labarin nan duk lokacin da baffa ya murda wanan babyn roban idan kafa ya murda haka hanne zatayi ta tsala ihu da sai mujita a namu ruggan saboda azaba. Idan hannun roban ya murda ranan hannunce zata lamkwashe ta dinga ihu tana neman taimako masu magani sunzo kala kala ankai hanne asibiti birni an kashe kudi yafi a kirga amma hanne bata samu lafiya ba. Ranan da na girsheshi yana murda kan wanan babyn roban cikin mugunta daya bayyana afuskansa yana wasu suraita naja baya a hankali don baisan ina wajen ba. A ranan muka samu labarin wuyan hanne ya kare tana batun mutuwa haka da baffa din ya fito daga daki idonsa a kaina ya sauka yana min alaman gargadi ban nuna nasan abinda yake nufi akaina ba lokacin. Don zuwa lokacin na daina tsoron baffa tunda yake kirana da shu,umma idan dare yayi yaji ina rewa kira,an da muka koya a abuja don mu din mun sauke alkur,ani a lokacin gidan Alh tun barinka nono zaka fara bin yan uwa karatu don haka ya gargadeni da na daina naki sai dai in rage sauti yake kirana da shu,umma abakinsa ni kuma tsoron shu,umancinsa ya fita raina. A wanan case na hanne na yarda baffa shu,umine na gaske don dashi mahaifin Hanne ke fadi tashi dashi aketa zuwa asibitin birni ana kashin kudi wani lokacin shine mai zuwa amso maganin kan matsalan hanne din. Shiyasa bahaushe yace makashinka yana tare dakai ko wani lokaci muna tare da makiyan mu bamu sani ba a duniya. Haka Hanne ta wahala sosai dukiyan mahaifanta yana tafiya baffa yana mata dariyan mugunta yana bin babyn roban daya sihirce da sunan hanne yana lugudewa karshe shanayen mahaifin hannene sukai rauni. Saida Allah ya nufi hanne tana da sauran rabon shan ruwa a duniya ranan baffa din ya tafi Adamawan cameroon wajen wani amininsa aka ga wuta ya kama a bukkansa. Ko yaji tsoron kashewa andai zuba ruwa har angaji wutan saida ya lashe bukan Baffa kaf yadda wuta ya kona roban haka jikin hanne yaji amma ta samu kubuta. Da Baffa ya dawo daureshine kawai ba ayi ba don duk wani kayan tsafinsa ya kone a wanan gobaran wasu tun yana yaro wasu kuma da girmansa ya karbo sihirin yake aiwatar da sherinsa akai. Har yau kuma ba a san nice na hada baki da dan uwan hanne yazo ya saka wuta a bukkan baffa ba a cikin wa yanda suka samu saukin hakan har da mahaifiyar mu da yanzu take iya mayar da magana a cikin iyalan baffa din daya rufe mata baki haka yasa na gane muma baffa ya kullemune a lokacin da sihirinsa don a lokacin muka fara samun sauki a cikin hakan kuma zancen auren Yanda ya taso har ya rasa me zaiyi yace ya barwa hardo mu da sharadin baiba da ko Nagge guda don shanun babanmu sun zama nasa a yanzu. Baffa mugune ko cikin muggai nasan zai iya illanta anty Maria tunda ya kufulemu a cikin ransa zai iya aiwatar da wani mugun nufinsa akanta yanzu. Allah yafika baffa na fada a hankali wa Allah yafi Ramaah naji muryan ya Habu yana tambaya nace baffa na juya na fita daga dakin rai bace. Part din iya na koma suna zaune dukkansu a falo mamace ke tambayana da Ramaah kin karya kuwa tana kallona. Kai na girgiza mata don shiririta Ramaah zaki zauna da yunwa a cikinki har wanan lokacin maza dauko kofi kizo ki hada shayi kisha ga kuma dankali a wanan roban ki diba kici tafada. Nima takan ban mamaki wani lokacin idan tace bata karya ba mutum ya tashi yayi wanan uban shara da wanke wanke amma kuma yakai wani lokaci yace baici komai ba. Zama nayi kamar yadda mama dubu ta umurce ni dan zuba ruwan zafi kadan na hada shayin na dan dibi dankali ina tsakura a hankali. Suna hiran su sai iyace ke fada dani kan na dibi abu kadan kamar za abawa jariri murmushi kawai nayi don zuwana dake tuna min da baffa a lokacin. Banda natsuwa a yau ina tunanen shu,umancin baffa a raina zai iya fiye da hakan a kan yar uwata tunda ya fada da bakinsa taje koba aure ba taji tayi auren kado din data saka kanta ya gani. Waiba muryan anty Asmau nake ji ba anty Saare ta fada tun dazun nake jin muryansu ai inji salima sai mama dubu tace yau kuma me suka tashi dashi da wanan fitina ? Turo kofan da akayine yasa mu kallon kofan don kofan yana bada kara idan an tabashi wanda naciki zai gane anshigo dakin a lokacin. Asmauce matar ya Jafar ganin mu a zaune gaba dayan mu yasa ta soma gaida tsofin da kwana kafin ta dora da fadin mama kiwa Nusaiba iya dani dan Allah. Mekuma ya faru da safen nan kasa magana tayi sai hawayen dake zubo mata hakkuri suka shiga bata suna fadin kiyi hakkuri Asmau kinsan halin abokiyar zaman ki sai kici magananin zama da ita ta hanyar kawar da idonki a kanta. Mama don Allah wani irin kawar da ido ake son inyi ga Nusaiba yanzu kuma bayan wanda nakeyi yanzu akan mimi fa da yarta Nusaiba ta dokan min yarinya har wani wayau sanin haka mimi tayi mama saboda Allah ? Duka kuma me yarinya kamar wanan zatayi mata har da duka duka sosai tayi mata mama ki duba yadda bakin yarinyar nan ya fashe wai don kawai suna wasa a falo fada ya hadasu ta kayar da yar uwar shine Nusaiba ta fito ta duketa fa haka ? Tir da halin wanan yarinyar wallahi banda abin namiji banga abinda yaron nan ya gani a jikin wanan yarinyar mara mutunci ba wallahi. Iyace ke fadan wanan maganan inda tacigaba da fadin wanan yar yadda take baka haka zuciyarta yake baki ba digon rahama a tare da ita,,,,,, Iya baki san kan zance ba kin zauna kina zagina ai tana tsaye yaran suke fada bata rabasu ba har ta kayar min da ya tana duka don rama kuma shine wai nayi laifi ni wallahi ba zan yarda da irin wanan ab,,,,, Ke don Allah ku fita ku fita masu daga shiya kuje can ku kashe kanku da yayan naku kada kuzo ku tayar masu da hankali a nan kuma ? Ya Habune ke fadan hakan da yashigo part din ransa a bace yana binsu da idanu duk suka juyo suna kallo shi. Wanan wani irin rashin hankaline da zaku dinga fada akan yaya tun suna kanana ku koya masu mugun dabia wani irin halin banza kuke son yayan ku su taso a cikinsa ? Indai hakane zan karbe yaran a waje da zaran kun yaye kada wace ta raba min kan jikoki mama dubu ta fada garesu . Ace mata baku da abinyi sai fitina a kullum ku kwana jidali ku kwanta da jidali mama sin tacigaba da fada tana fadin maganganu akansu. Dama ace fitinan nan naku shine halin arzikiku da mijin ku zai dawo ya sameku a cikin farinciki da jin dadi da walwala ba yazo kulum ga jidali kuma ya sameku a cikin kazanta da doyi ba. Iyace take wanan katobaran a gabansu daya saka aka kwashe da dariya bandani dasu da suka hade rai tace Allah ko banda kazanta da tijara ba abinda suka koya ga uwayesu da zasu barwa diyansu gado suma. Iya da banda tarbiya ai Jafar ba zai auro niba gidan nan fada kuma kowama yanayi idan antabashi ai ta juya ta fice daga part din ranta a bace. Anan tabar kishiyar nata su mama suka haita da fada ya Habu yaja tsuki ya juya ya fice daga part din a hasale yana maijin haushin abinda yake faruwa din. Iya kin damemu da fada don Allah ki bari idan mijinsu ya dawo ki fada mashi mana Saare ta fada tana kallon iya din dake faman jinini ba fada bane fadan gaskiyane da bakwaso ayi mama ta fada. Nasan maganin su ai idan na hade kan yaran na tafi dasu can babban gida sai muga ta tsiya kuma da sauri Saare din ta kara fadin a,a mama barsu da yaransu don Allah matan nan basu da mutunci . Har sukayi suka gama ban ko daga kai na kallesu ba ina faman tunane kasan raina dan na dauka matsalan yayata din wani babban lamarine na tashin hankali lokacin. Duk da ance mahaifiyanmu zatazo zama da ita hakan baisa naji dadi ba a raina idsn na tuno da sheri baffa a ranan haka na wuni a cikin damuwa da fargaba ina zullumin abubuwa da dama a raina. A haka barci ya daukeni sai wajajen yamma na samu na tashi sallah nayi na fito da niyar zuwa part din anty na sai na samu sin fita da mijinta basu gida ban san dai fitansu ba a takaice. Ga kuma kaina yana ciwo don haka na yanke shawaran zuwa wajen matan ya J in samo ko paracetamol insha ya dan fada min. Sam ban kula ba da shigata nakeyi sallama anty Asmauce na sama kofa don hakan ban hango na cikin falon nake fadin anty don Allah kuna da Paracetamol insha kaina ke ciwo ? Ayya banda shi Ramaah ta fada a takaice nace ko maman sultana tana kusa sai ta dago murya tana fadin gaskiya bansan inda na ajeba a yanzu jin hakan yasa na juya zan fice daga part din. Muryan maigidan da bansan ya dawo ba a lokacin naji acikin tsawa yana fadin you are very stupid all of you ina maganin dana aje agidan don irin hakane wai ? Wai me kuke nufi da wanan halin bamzan a yanzu shekaran jiyan nan mama ta gama yi min complain a kan kayan dana bayar aba kowa gidan nan kun hanawa yarinyar nan da yarta. Niyi magana kunce ban lissafo da suba ai niko nasan abin da nakeyi da badon mama ba wallahi duk inda kuka shiga da kayan nan sai kun fito dashi a gidan nan. Yanzu kuma gashi to tazo neman magani kunce wai baku da magani for god sake wani irin halin banzane haka wai kukeyi kun kuwa san hakin makwantaka balle na wanda kuke rayuwa a gida daya dashi haka kuwa ? To aini bansan ko wani take nufi ba balle in bata Asmau ta fada itako saiba cewa tayi nifa cewa nayi bansan inda yake ba ba cewa nayi ba zan bata ba ai. Kaji takwal Asmau bansan irin bokon da kikayi duniya ba wallahi karatun ki ke kan bai maki amfani ba wallahi ke kuma Saiba bakin hali da iskaci ko ciwo ai yana kan kowa yasan kofan kowa a gidan nan. Ban tsaya jiran karasan zancen su ba na juyo zuwa part din iya na samu kujera na kife ina rufe idona an dan jima kadan sai gashi ya shigo iyace a gida mama tare suka fita dasu yaya Habu daga gidan. Ina yarinyar nan yana tambayan iya yakai zaune a kusa da ita tace wace ke nan fa yana fadin wanan yar uwar matan Habu din nan mana dake gidan nan. Dazun taje wajen marasa hankalin nan neman magani ta hade wai kanta yana ciwo don rashin hankali iya ace wai magani ma rowansa sukeyi a gidan nan sai cewa sukayi da ita wai basu dashi. Kaji marasa kan gado ko dazun fadan sukayi aikan diya nan ta kora mashi yadda abin ya faru ransa ya baci sosai ya mike yana mikawa iya din ledan maganin daya dauko yace tabani. Ai gata kwance iya ta fada tana nuna mashi inda nake kwance abayanshi au itace nan a bata tasha idan ta tashi ya fada ya fice daga gidan. Ficewa yayi daga gidan kai tsaye unguwar iyayyensu yaje ya samu abokansa na unguwar yakanyi hakan idan yana gari ya zauna wajensu suyi hira sai yayi sallah magariba da isha yake nufowa gida. Saida ya tsaya ya sai kayan sanyi dana tabawa ledoji daban daban ya nufo gida dasu kai tsaye falon iya ya nufo inda ya samesu zaune suna hira ni ina zaune a inda na idar da sallah na ina addu,a. Saare karbi wanan ledan kowa da nasa kada kociwa iya nata ya fada sai iya ke fadin ka sako dana yar nan wace ya tambaya yana rabon ido ta nuna mashini da ido yake fadin ya saka ya fita . ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K44JhTApwmM4gU33AbpqHC MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 1️⃣5️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Ledan ta fara budewa ya kara lekowa yana fadin ke Salima karbi wanan ki mika a part din Habu ta mike da sauri tanufi wajensa tana karba. Irin ledan daya mikawa saarece da farko mai tambarin shagon dayayo sayyya a wajensu yan banzan matan ka dole su zama haka kana gari ko baka gari kullum a cikin cin kaji suke gidan nan suna tauna dadi su zuki dadi da safe su tayar da mutane da fitina don gata. Iyace ke fadan hakan a gareshi shi Habu ya samu yar mutumci yarinyar nan kome ta kwaba a wurinta saita sako min shi a kwana banda wanan matan naka masu rowan tsiya da bakin gado. Shiyasa abotansu yazo daya tun farko halinsu dayane yanzu sunawa mutane iya shegen banza a gida haka ni yaushe zan tsaya ina kamarka ,,,,,,,, Iya ina ruwanki wai kema waya sani ko haka kikayi zamanin zaman ki da baban gona da kishiyoyinki ? Ke Saratu ki koma ki tambaya kiji da kyau a zamanin kurciyana kisha labari labarin arziki kuma bana tsiya ba ai maganin Asmaun ke nan bata da halin arziki gara da kawartata tayi mata hakan ai. Wanan yar akwai bakin rowa da kazantar tsiya kamar mai bakin uwa saare din ta katseta da fadin aikuwa nagani don saida kika korewa baban gona duk matansa kika zauna ke kadai a gidan don iya yi. Dakuwa mama tayi mata shiko ya kasa tafiya sai murmushi yakewa tsohuwar kamar yadda ta saba idan tana aibanta matan nasa. Iya ai yanzu nayi magana da Nura za a samo mai aiki gidan nan don kazantan nan nasu yayi min yawa iya kuma basu da niyar tsayawa su gyara hakan . Yar aiki kuma Mama Dubu ta fada irin fitinan nan nasu yar aiki ba zatayi karko a cikinsu ba ai don fitinansune zai koreta adai gwada din a gani kawai. Lalacewan nasu yakai ga sai andauko masu yar aiki a gidan nan kuma har yaushe da karfinsu da lokacinsu zasu tsaya ga aikin yar aiki kai kuma mijinsu ka yarda wanan kam tauye kaine da rayuwa Jafaru . Komai haduwan macen data amsa sunanta na macen kwarai to bayan ibada da tsabta sai girki kumadon yana daga cikin halaiyan mace tagari wace take iya bawa zuri,a tarbiyan da akeso. Duk da na kula kuma taku uwar tayi rauni a nan wajen bawa nata diyan gasu nan tarbiya da suke fakewa da sunan boko a yanzu basu iya hasalawa kansu komai a rayuwansu. Iya mu kuma Saare dake duke tana jagulan naman daya so daga inda nake nafahinci duba take koda bambanci ta wafce mai girma ko mai mai mai. Saidai ruwan idonta baiyi amfani ba don duka ledojin ina ganin iri dayane aka bashi wajene da ake amfani da kilo. Hakan yasa ta fara ajewa Iya nata tare da mama ta mikawa salima dake shigowa falon tana fafin sunce sungode yaya baiyi magana ba ta mikawa Salima din leda biyu tana fadin ki dauka ki mikawa Ramaah nata . Bata tsaya duban girman ledan ba kamar yadda yar uwarta din tayi take fadin Ramaah ga naki ta miko min nasa hannu biyu na karba tare da fadin nagode kana na dago kai ina fadin ya J mun gode Allah ya umfana. Zance banda gaisuwa sai wanan ranan ce magana mai dan tsayi ya shiga tsakanina dashi haka no kada ki damu ya fada yana tashi yace iya bari gobe ma karasa yanzu na gaji sosai wallahi. Ita Iya fa gulsu gareta sai saka ido da hana ruwa guda kowa a gidan nan idonta yana akansa yau wanan ce fara gobe waccan sai kwadayin tsiya bari na cinye namana na soma cin naki in debe ladan zagin mutane da kikeyi a nan. Ta mike tana kokarin daukan nagaban Iya din da sauri ta buge mata hannu tana fadin kaji muguwa mai zalaman tsiya kawai . Dariya yayi ya fice yabar falon yana masu saida safe salima daga kofa take fadin Ramaah taso muje daga ciki hakan yasa namike ina tattara kayan da nayi sallah muka bar falon. A falon kuma suka fara budan ledan suna sawa dan nasu albarka saida muka zauna naji salima na fadin wallahi ya J yana ban tausayi. Gashi dai mutum har mutum amma bai samu matan arziki da zasu debe mai takaici kazantasu shiyafi damunsa dan gayene fa na sosai Ramaah son baki sanshi bane a baya. Duk unguwan mu babu dan gayu irinsa lokacin baban mu yana raye muna cikin gatan mu da lokaci ba kamar yanzu ba da gidan mu kowa ta kansa yakeyi. Aiko yanzu anty Salima kuna cikin gata ku godewa Allah da hakan gaku da yayyu dake debe maku kewan baba din mu ina muka samu yayyu maza anty Yanda itace babba a gidan mu sai yayana Aley saini sai umar sanda. Ashe kuna da yan,uwa na dauka daga ke sai anty maria ce ai, nace a,a muna da yan uwa maza biyu mu mata biyu su mazan suna tare da maman mu. Kingani mu uku mata su maza su ukku yayan mu mace tana zamfara tana aure a gusau sai ya J ya Habu sai Saare sai ya faruq saini. Su dai ita babban kuce ban sani ba amma nasan ya faruq da mukazo gidan nan lokacin yazo hutu mun hadu dashi. Ita anty Rabi cikine da ita tsoho alokacin yasa bata zo bukin ba amma ance tana tafe cikin kwanakin nan amma muna da yawa a gidan mu ai kinga hakan da idonunki mukai ashirin da wani abu a wajen baban mufa. Wai kuna da yawa kan gaskiya ko gidan nan ai munkai mu nawa a cikinsa tace da matan su yaya ba suda suka cikawa mutane waje da bakin hali irin nasu. Kinsan ita Nusaiba itace best friend din Asmau da suke school a wajen Asmau tasan ya J shine daga baya ta nemesa ya aureta. Budan baki sai cewa nayi amma yar iskace ko mijin kawarki zakice ya nemeki dole biri yai kama da mutum ai bata da kunya ko kadan gadaranta yayi yawa wallahi. Duk macen data san kunya ba zata taba haka ba ai ko kinyi kuwa iyayyen ki in na arzikine ba zasu yarda da haka ba a rayuwansu. Dole su dinga fada gaskiya babu shiri kuma har abada a tsakaninsu nikan kikai min haka saina barki da mijin ku zauna inje gaba in samu wani mijin nawa. A,a Ramaah baki san kaddara bafa Allah ya rubuto tun farko itama matarsace ya kuma hada zamansu tun ba mijin a tsakaninsu. Ita Asmauce wawiya ai ance ta fita harkan ta tabarsu da Allah amma bata da hakkuri ga kazantar tsiya da rowa ita kuma Saiba ai kinga bata kai Asmau rowa ba saidai cin mutunci da gadara. Ga kuma hassada ko don hassada yasa tayiwa kawarta hakan na fada ina gyara zama da yanzu itama Allah zai sakawa Asmau ya jefo wata ta kusa da ita ta auri mijin sai kinga yadda zatayi haukan karya akai. Ba hauka ba wanan ko mutuwa tana iya yi wallahi tana bal,ain son yaya fa aida soyayyan da kissa ta samu ta yaudareshi wata ukune kacal a tsakanin su Salima ta fada. Zanyi magana Saare ta fado dakin tana fadin kai kai ina son yaya J yana gari bakin ka zai more kwana biyu da dadi wallahi. Kallonta mukayi gado ta fada tana fadin naso iya ta raga min amma tayi min kwalelen shi yau don munyi rigima da ita dana sani da sai mun gama in bata amsa. Sai kuma ta juyo tana kallon mu tace wai kuna nufin baku ci naku ba har yanzu kuke nufi wai nazo mu koma wurin yaya mu samo wani nagashi da ledoji da yawafa zai shiga part dinshi . Kai amma anty Saare din nan wai kina nufin sai mu koma muce dashi wanda ya bamu bai ishemu ba don munfi kowa kwadai ? Wanan ma din da kika samu don bai shiga hannun marowatan matansa bane don wallahi da guda daya zasu bamu kaf part din nan kuma dole a karba. Balle zai fada masu basai sun kawo muna ba ya rigada ya bamu namu nan kinsan kuwa ko kallo baki ishi Asmau ba . Taja tsuki tana fadin ni yanzu ai nasan maganin su shiyasa nake shiga kai tsaye in dibi abinda nake so a wajensu duk da kwakwazon da sukeyi kan hakan . Ina jiran ranan da zasu kai karana wajenshi suga tsiya a gidan nan don zan nuna masu nafi kusa dashi su godewa Allah da mama tana gidan nan aida sunga abu a wajena . Wayan ta dake ringing ya katse mata magana inda kowan mu yayi shiru a lokacin tunane na fara akwai bambanci sosai rayuwan gidan nan dagidan su hjy fanna da mukayi a Abuja don su komai moderate akeyinsa gidan . Sabanin nan da akwai waddatan amma ana hadawa da akidan bahaushe mai ban haushi akwai abin makin ayisa aci a wadace tunda Allah ya hore sai kuma a tsaya ana make make dama idan mama na gidan za ayi komai a wadace kowa ya godewa Allah. In bashi ba freezer part din yaya J din makil yake da nau,i nau,in namuka sunyi kankara harsun gaji sai idan anyi tsiyar wutane sai su yoye su fara bashi su wullakance a banza ba aciba. Ban fita waje ba dana gama ko yar uwata banje na duba ba na samu waje na kwanta ina faman kimtsa abubuwa da dama kasan zuciyata. Washe gari na tashi nayi aiyukana yadda na saba ina gamawa nashige wanka don har lokacin su ya Habu basu bude part dinsu ba balle naje mu gaisa da yar uwata. Dana kwana da ita a raina ina faman tunanen yadda zata zauna tsayon wata shidda a asibiti bata leko gidan ta ba. Kamar Saare tasan tunanen da nakeyi a lokacin data shigo daki take fadin ni har tausayi ya Habu da matarsa suke ban ace mace ta zauna asibiti har tsawon watani shidda don Allah ? Toke bakiji ance daurin mahaifa za ayi mata ba gudun kada ya balle a samu matsala a nan gida yasa sukace sai dai ta zauna a wajensu ai. Ras ras gabana ya dinga faduwa dan jin me suke fada ta yaya za a daurewa mace bakin mahaifa an taba yin hakan kuwa ? Dan lokaci na share a zaune wajen kamar zancen su bai dameni ba can na mike na fita na hango part din nasu a bude hakan yasa nagane cewa sun bude. Da sallamata na shiga suna falo sun shirya tafiya a lokacin don har mama tana falon itama suna magana nashigo ina gaidasu da kwana. Cikin harshen fulatanci nake tambayanta yanzu ita asibitin zata tafi ke nan ta yarda da zancen likita bayan tasan daga inda matsalanta yake ? Kamar ba zata ban amsa ba har na juya naji tana fadin yaya zatayi ita tunda sunce aje can din dole tabi umurninsu ai amma koma meye ai mahaifiyar mu tana tafe ranan. Allah ya sauwaka ta amsa a zuciya ba,a fili ba don gudun rashin kunya garesu da alkunyan nan ta fulani har yanzu ta ajini komai wayenwan bafillace kuwa. Dakin ta biyoni banji shigowanta ba sai muryan ta da naji tana fadin Ramaah don Allah ki natsu a gidan nan kada ki yarda ki canza a bayana kin dai san halin mutanen gidan nan don haka ki kama kanki dasu don Allah banda kuma shiga abinda bai shafeki ba don Allah. Zan kula insha Allah ke kuma ubangiji Allah ya baki lafiya tace amin ga kudin nan ki rike don kada ki zauna ba kudi a hannunki don Allah ki kula da kanki da mutunci har in dan ya nufa ina da rabon dawo gidan mucigaba da rayuwan mu yadda muka saba. Kasa dago kai nayi in dubeta don hawayen daya cika min ido a lokacin gasu har sun fara zubowa daga idona. Ta gane hakan naji tace idan kikai kuka Ramaah zaki kara min zuciya nima har mutanen gidan nan su dauka ban godewa gatan da suke min ba. Likita yace yanayi na ba zan iya rike ciki ba don haka sai sun rikeni wajensu suna bani kulawa daya dace daga yau din nan. kinga kuwa ba yadda zanyi da wanan umurnin nasu tunda sunan sun yaya habu sun yarda da tsarin nasu sunce ana irin hakan. Muryan mijinta dake kiranta a falon ya katsemu ta fita ta barni nan ina kukan da ba sauti itama din ashe kukan takeyi a lokacin. Muryan mama dubu ce naji tana fadin asha assha maria yaya da kuka haka kuma keda zaki neman lafiyan ki kuma zaki karawa kanki lalura. Zaman asibitin naki ai kamar gida kike a can din babu takura ko kadaici sunfi sone kawai su saka ma duk wani motsinki ido don yanayinki hakan insha Allahu aiba komai bane. Ina ji ina gani mama ta kirani nima tayi min fada sosai tare da kwantar min da hankali kuma tana fadin wanan abin mu anan yanzu ba bakon abune ai mata nawa aka kai suka haihu lafiya ? Haka itama insha Allahu zata sauka lafiya ita da abinda zata haifa don haka kada ku daga hankalinku har ku dagawa sauran yan uwan ku kuma. Ni dai ban iya tsayawa naga shirin su shi mijin nata da itane suka shirya tafiyan nasu ya hada mata komai da zata bukata yakai wajen mota. Saida zasu tafine ta kwala min kira na fito da yare muke magana tana kara fada min in kula da kaina a gidan sai gani nake kamar dai ta tafi ke nan ba zata dawo ba daga wanan fitan da tayiwa gidan. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K44JhTApwmM4gU33AbpqHC MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,, 1️⃣6️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Sai da suka shiga part din ya J ita da su mama dubu da mijinta nasan sallama sukayi dasu mijin nasu dake gari shine kadai ya fito har bakin mota yana fadin gashi nan zuwa asibitin idan ya shirya. Haka suka daga suka bar gidan duk kokarin dakewana saida hawaye ya zubo min ba lokacin ya J yazo ya wuce mu zuwa part dinshi lokacin nake jin muryan Asmau na fadin wai har sun tafine ? Sun tafi Salima ta fada saita amsa da Allah ya sauwaka dama ashe bata da lafiyane take yawan zama haka lukume a daki ko yaushe? A daidai lokacin Saiba ke fadin wai har ciwo ma sai an boyewa mutum a gidan nan abu har yakai haka muna gidan nan bamu sani ba ? Koda yake ance kowa ya samu rana yayi shanyinsa cikin ne za ace za aje asibiti a zauna har sai an haifeshi ni ban taba ganin irin haka ba gaskiya. Na kula da lokacin da Saare ke nuna mata ni da idanu naji tace ai gaskiya na fada Saare shi ciki ai har ka haifishi baka taba jin dadi a rayuwanka sai ranan daka haihu. Yadda take magana yasa naji ba dadi a zuciyana itako tacigaba da fadin kudi yayiwa Habu yawa koda yake ba zafinsa bane tunda Allah ya kashe ya bashi ta dubi kishiyanta tana fadi ita kuma tayi wani irin meda baki. Sai naji Saiban na fadi a to mana ke inbashi ba dai naga mu duk lalura baisa munje mun kwanta asibiti saidai asayo muna magani a hadamu dashi kawai ? Amma ai kowa da irin yanayisa ko yanayintane yazo mata a haka ai ko ita bada son ranta taje kwamciyan asibitin ba . Tunda gashi ta fita tana kuka dadi zaisa mutum kukane Salima ke fadan hakan cikin hasala data karbi zancen da yar uwarta ta soma yi dasu din. Zo muje Ramaah kinji mama tace idan sun tafi mu gyaro wajen mu kulle masu ato nidai ga gaskiya na gani ba za a hanani yin magana ba dai kan bamu tsaya karasa saurarensu ba sai dai muna gab dashigane mukaji muryan mijinsu na kiran Asmau. Shiyasa akace matan saure sunfi kishiyar miji daya kishi wanan ba karya bane don matan ya J da suka fito fili suka nuna bakin ciki ga yar uwata ranan. Ashe bani kadai naji haushin abinda sukayi ba din har da Salima don ina kitchen ina hada kayan datace in kwashe zuwa cikin gida naji salima din tana fadin. Shiyasa suke bakin kishi tsakaninsu ai ina abin dadi a zaman asibiti ga mutum har wanan abin yakai zancen banza haka ? Ciwone ai yasan kofan kowa sanda zaizo gunka baka sani ba tunda ba sallama maka zaiyi ba ai munafuncin banza da wofi kawai ? Ni dai banyi magana ba amma na rike hakan a raina akwai ranan magana matukar muna raye na nasa hakan a zuciyata. Bamu zauna ba nida Salima abinci muka dora don mama ta gargademu da hakan mu hada abinci akai asibitin da wuri basai na can sunji yunwa ba za a kawo masu . Kafin sha biyun rana mungama miya da abinci tana zaune tana yanka salad da kayan had iya na zaune tana jan tasbaha a gefen ta . Ni kuma ina kitchen na dora ferfesun da mama ta bugo waya tace a hada na kifi. Ya Habu ya dawo yana tambayan makulin part dinsu da muka rufo masu naji iya na tambayan ya mai jikin take ? Naji yace sun bata gado sun fara dorata a dokan sun kuma hana a aita yawan sintiri a wajenta don barcin da akeson ta dinga yi ko wani lokaci saboda lafiyan abinda ke cikin cikin nata. Bakaji ba mai lafiya yana zama haka don son rai ka zauna a hanaka mu,amula da mutanen arziki su wa yancan sakarkarun sun dauka hakan wani abune har suna tsayawa gulmam hakan . Shi Jafaru ya sameku can ko zai fita don bai tsaya jin zancen nata ba ya juyo yana fadin muna tare dashi iya shiya biya kudin komai ma har zuwa lokacin da Allah zai sauketa lafiya. Ai dama nasan ba zai bi kan matansa marasa kan gado ba tunda shiba sakarai bane irinsu wai iya anyi wani abin ne ya dakata yana tambayan tsohuwar ? Anyi mana Abu matan dan uwanka ke gani wai saboda makirci yasa yarinyar nan karyan zuwa asibiti ta zauna a can don kawai ta,,,,,, Haba iya ki bar yaya yaji da abinda ke damunsa don Allah matanda basu sawa basu hanawa idan an tashiyi sune basu san Allah ba cikin zancensu Saare ke fadan hakan ga kakan tasu . Koya gane me take nufi da zancen ta yasa kai ya fice daga part din bai jima ba ya fito a cikin shirinsa nan Salima ke fada mai mun hada abincin asibiti yace har angama ta amsa da ehh mama tace kada mu makara ai da hada abincin. Ku fito dashi na kai masu don kaduna zan tafi yanzu in sayo wani magani da za ai mata amfani dashi nan ban samu oroginal dinsa ba. Allah ya tsare mukai masa bayan mun saka kayan a bayan motanshi din muka nufi cikin gida nikan Allah ya gani ban iya cin abincin ba a ranan don har lokacin ban fahinci komai ga zaman da zatajeyi asibitin ba. Mahaifiyar mu bata iso garin ba sai dare wajajen tara muna daki salima dai waya takeyi ni kuma ina kwance naji ana mata sannu da zuwa . Muryan ummah na tsinkayo a kunnena tana amsawa hakan yasa na dubi anty Salima ina tashi zaune nace muryan ummah nake ji fa ? Waye ummah ta fada tana kallona nace mahaifiyar mu tare da ita muka fito falon tana zaune suna fira da iya dake tambayanta hanya ? Sannu da zuwa muke mata saidai ni a cikin yare nake mata magana ina tambayanta yan uwana tace suna lafiya taso tazo da umar sanda ai amma ta barshi agidan hardo saboda karatunsa . Ku kawo mata abinci ko iya ta fada sai ummah din tace sallah zatayi tukun a nuna mata ban daki tayi alwala na mike tsaye don bansan inane zan kai ta ba sai Salima ke fadin kaita bandakin mama mana ta sauka a nan. Lokacin anty Saare na part din ya J bata sanda zuwan ummah namu ba ni dai a yadda na dauka shine tana zuwa dan hirane part din. Amma sai inji Salima na fadin don kwadayi da munafhnci take yawan shigewa matan yayan nasu in bashi ba sau nawa suna masu wullakanci a baya lokacin da yayansu baiyi karfi haka ba? Amma yanzu wai duk anty Saare ta manta da hakan suta koma tana shigewa don suji dadin wullakantasu ke nan kuma. Dakin yana nan yadda muka gyarashi da safe nan ta shiga yayi sallah ta jima bata fito ba salima ta dauki kayanta takai mata dakin ba wasu kaya bane sosai sai manshanu da kindarmo mai yawa datazo muna dashi da nama soyayye. Abinci ma da iya ke magana nayi murmushi ina fadin ummah ba zataci abinci ba nan iya saboda kunyanki kinsan nan gidan surukintane ai. Salima tace shine kikai shiru Ramaah ta mike ta suri kayan ta sameta dasu a daki nan ta jera mata har da jawo kofan dakin don tasan babu mai shigowa hakan yasa ta dan tsankwari abincin kadan ta aje. Bata sake fitowa ba falon sai washe gari ta fito da shirinta tana dakon yaya ya shigo ya tafi da ita asibitin da zata zauna. Inda muke ta kokarin hada masu breakfast da za a kai asibitin haka kuma iya ta lasa muna tare da mu za,a tafi mu dubasu a can. Yasa mukai komai a gurguje inda na saka nonon kindarmon a cikin fridge na rakumi datace min don yar uwata tazo dashi ta dinga sha na diba a cikin wani gora da za akai mata ta dinga sha na kada a kulan kankara. Mun shirya tsab koda ya fito yazo gaidasu iya da ummah ya samu har iya din mun shirya muna jiransa bayan an gaisa muka fito da kayan muka kwasa zuwa asibiti gaba dayan mu yan part din aka rufe shiyan. Sam ummah bata sake ba har muka kai asibitin cikin nauyi da kunya take don ta shiga motar surukinta koshi don ba wanda ya santa a zaria ne yasa har ta yarda ta shiga Ya Habu ya jata. Duk ko da dan wayewan kai da ummah kedashi wanan baisa tayarda akidan mu ta fulani ba don anty Yanda yar farice a wajenta kuma yarta ta cikinta suruki zai dauka a mota haka ? Ba laifi gaskiya don ba zakice asibiti bane ba ,a kuma kilance wajen ba dakin masu irin lalurar yar uwata din itama aka ajeta munje daidai visting hour don haka kofa a bude take lokacin. Aka gagaisa da juna tsakanin ummah da mama ana satan kallon juna a tsakaninsu sukaiwa juna jaje akai tayiwa ummah yaya hanya da mutanen gida. Gadon da anty Yanda take mukaje gaida ita ga kayan more rayuwa nan an baza gwanin ban sha,awa zakice ba asibiti bane na fada a zuciyana ina kara bin wajen da idanu. Munkai kamar minti talatin matan ya J suka iso tare dashi suma da nasu abincin nasan shine yasakasu yi dole saidai yadda suka samu yar uwata din akwance haka ya tabbatar masu bata da lafiya dai kan saidai ba wani sosai ba. Ban da sakin jiki dagani har ummah a wajen su dai keta hiransu da kuma baza ido suna gulman wasu mata da muka hango dan nisa damu masu irin matsalan nata. Shigowan yaya J dakin da ya Habu ya sa duk akai shiru inda suka karaso bakin gadon yana gaida ita nan yake tambayan mama ko anzo an mata alluran da safe mama tace anya basuyi ba kan. Ya juya yana fada ya habu yabi bayanshi suka fice daga dakin sai lokacin saiba tayi magana take fadin. Wani kan ba zan yarda in kwanta a dinga surbuda min allura haka ba gaskiya daga can inda mama take zaune ta bata amsa da fadin itama ta kwancen ba da son ranta hakan ya sameta ba ai ? Komai da ya samu bawa mukkadarine nata kaddaran haihuwan ke nan yazo mata a hakan kuna magana kamar baku taunawa wani zubin duk wanda kika gani a nan ba dadin rai ya kawoshi wurin nan ba asibiti fa akace ba gida ba ? Shiru tayi don tasan abin ya taba zuciyar mama din don ba wanan karon suka fara tsegumi kan matan Habu din da mama din ba. Suna fadan mama tafi son matar Habu dasu tana nuna banbanci a tsakaninsu ta fifita matar Habu alhalin duk wani moriya a gidan mijinsune . Taba wace suka gulman da ita sakon da take kyautata zaton yakai masu da cewa ta fifita din don ance ka kyautatawa wanda yasan darajan ka. Kuma da sauki tunda ba habu ta fifita akan jafar ba ai idan sune aida sauki suyi mata yadda matar Habu din ke mata idan basu ga canji a wajenta ba. Wanan yasa suka kama bakinsu don ta fadawa yar sakon cewa su shiga hankalinsu don lokaci guda zata iya fyacesu gaba daya a gidan kirsis take jira ga hakan. Don saita sa ya j ya sakesu ta aura mashi masu hankalin ya zauna dasu tunda basu iya cin arziki ba su kuma su tambaya suji ita a ratuwanta bata gaji tsiya ba ko jafar din da arzikinta yake barazana. Aiko da J din yaji yai masu tsiya sosai lokacin har yana barazan sakinsu run wanan lokacin suka shiga hankalinsu da mama din ta samu lafiya dasu . Sai a yan kwanakin ma suke dan ganin fuskanta idan tazo gidan wanan yasa a yanzuma sukai gum kamar ruwa yaci su a dakin. Tare da likita suka shigo dakin hakan yasa muka fice waje sai mama aka bari a wajen nan muka zauna saman babban tabarma a wajen . Mai hali dai baya barin halinsa akace don ko a nan gulman wata mace mai tsohon ciki sukeyi ina mamakin yadda halaiyansu ya kasance a hakan. Banga abin tsegumi ba a nan duk da yake basu irin hakan ya sama ba a yanzu dole su mayar da abin kishin tsakar gida su da yar uwata da suke ganin ta shiga rigan arzikin mijinsu a yanzu. Don ni a zatona shine mai dukiyan gaba daya don bansan cewa dukiyan yan uwansa kaf da suka gada yana hannunsa ba lokacin. Sun dan jima ya fito yana fafin muje ko kafin ya juya wajen iya yana fadin to iya ni yau zanyi tafiya fa zan koma port,harcurt wajen sana,ata . Ayya Jafaru zaka koma yau ke nan sai kuma yaushe eeh to iya saidai kun ganni yanzu kam amma insha Allah kafin azumi zan dawo na dan fara azumi a nan din. Hakan na da kyau Allah ya tsare ya kare ta fada gabanta ya gurfana yana fadin to muka hannun ki mana a cikin hijjab dinta ya dunkula mata kudi sai murmushi iyan ta sake a fuskanta tashiga mashi sabon addu,a kuma. Ya mike tsaye yana kallon kannesa yana fadin to ku yaya za ayi nifa zan tafi yau din nan ana nemana a can . To yaya zancen kudin da nayi maka fa Saare ta fada yace ban manta ba saratun mama ba kince sai next mont bane saiki tuna min ko ina can din in turo maki. Ya dago ya kalli Salima yace yan mata nasan kedai na shan ice cream ne ko ko yanzu kin dainane tayi murmushi tana fadin ban daina ba yaya yanzu kan harda na powder da jan baki . Ya nunata yana fadin see you nine zan baki kudin jan baki ina saurayin ki dan karya ta kebe baki zakice wata karamar yarinyace kudi ya mika masu . Kamar zai wuce sai kuma ya kallo inda yake yana fadin nakan manta da sunanta fa Ramaah ko ka kirata da Rahama wai dama sunanta ke nan aka sauya da wanan din. Ke kuma kudin me zan baki ya fada yana kallona murmushi nayi ina fadin nagode yaya yace shike nan kin hutar dani ? To ku kunji yadda akeyi ba kamar ki ba Saare da kullum kedai a baki kudi nakan rasa me kikeyi da kudi haka wallahi yana magana yana kokarin cusa hannunsa a aljihunsa na gefe daya. Sweet J muje mana kasa mun taso kuma ka tsayar damu haka a rana ya juyo ya dan kalleta hakan bai hana ya fasa abinda yakeyi din ba Salima naga ta kebe baki data fadi hakan tana magana kasa kasa tace akgunguma duk ranta ya baci ana bamu kudi. Nice kusa da ita a zaune ninaji hakan data fada ya miko min kudin yana fadin kin gani ko kin fisu sa,a ke yan dubu dubu kika samu. Na karba da hannu bibiyu ina godiya rakasu mukayi har bakin mota suka shiga ko anan ma din saida ya tsaya da kannesa suka dan taba barkwanci a tsakaninsu suko duk sun sha toka a motan . Nice na fara juyawa ganin ya tayar da motan tare da mamakin irin zama da naga sunyi a tafiya dukkansu suna zaune a bayan motar shi kadaine a gaba da yake jan motar. Suka tafi su kuma suka dawo inda nake zaune da tsohuwar kakan tasu dake kiciniyar boye kudinta cikin lalitarta dake manne a jikinta. Kai yaya ho daga shi dai sai matansa shike nan sunyiwa kansu tsiya babu wace zata shiga gaban mota ta zauna tare dashi don jidalinsu din. Ai maganinsu ke nan yan iska masu fitinan tsiya kawai haka kawai akan shiga mota su kama dabe a gaban mutane sun zubarwa mutane da mutunci. Ni na rasa yadda mutum irin yaya jafar mai hakkuri da kirki yake iya zama da wa yan nan matan da basu son suga wani komu nan mun rabeshi. Jifa yanzu kudin nan da Saiba taga zaibawa Ramaah shine ta kasa hakkuri take fadin wai yazo su wuce ya shanyasu a rana wai ita yar iska mai wayau banza. Ai shima ya gane me take nufi bakiga ya fita batunta ba ko kwanaki daya dawo tafiya ta aikawa part din ya Habu da tsaraba suka ki saida ya dawo ya diba da kansa bayan yai masu cin mutunci yabani na kai masu. Tsam na mike na nufi wajen mahaifiyar mu dake can dan nisa damu a zaune cikin damuwa nasan ba komai bane sai halin data samu yar uwata a cikine ya daga mata hankali. Ina isa naji salima na fadin ummah kin zauna kinyi shiru kamar baki wajen tayi murmushi tana gyara mayafin jikinta da ya rufe mata jiki lif har kasa. Idan kinga Ummah duk da wahalan da take ciki zaki rantse kice ba itace ta haife mu ba sai kice ita din yar muce ba mahaifiya ba. A cikin yare take tambayana da shi wanan din yayan Abu ne ko na amsa da ehh shine babban yayansu namiji amma suna da yaya mace tana aure a wani gari ita. Ayyo suna ko da kama sosai da Abu din saidai haske dashi ya dan dara Abu din dashi nace shi Habu din kebiwa shima dan mamane su kuma su Salima da Saare kanne sune duk uwarsu daya. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K44JhTApwmM4gU33AbpqHC MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,, 1️⃣7️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Nan muka bar mama da ummah muka dawo gida saboda abincin da part din yaya suka kawo mama tace ba sai munyi wani abinci ba a ranan mu barshi kada ya zama barna. Hakan yasa koda ya Habu ya sauke mu gida barci sosai mukayi sai wajajen la,asar muka tashi mukai sallah Salima tace zan rakata kasuwa . Banyi mamakin hakan ba don nasan tana kudi ranan kudin da dan uwanta ya bamu da zai tafi ni banko tsaya duba kudin ba tunda na saka a kasan jakkata a lokacin. Kayan gyaran jiki ta kwaso su man shafi sabulai turare har ina mamakin hakan yadda ta iya fidda kudi ta biya kudin ba tare da jin komai a ranta ba. Saita tuna min da anty Salman Abuja a lokacin har nake mata hiran tana min shige da ita don haka halaiyanta yake itama. Bayan mun dawo gidane tace na kwashe wanda take amfani dasu da farko don ita bai mata ba a cikin murna na kwashe zuwa inda nake aje kayana na jera kamar yadda suka jera nasu gefe daya don kowa nada inda yake aje kayansa a dakin. Tun a hanya ta gargadeni da cewa kada in yarda in fadawa anty saare ko nawa aka ban in mace kawai dubu biyar ne ko goma. Nayi mamakin hakan data fada amma na share muka dawo gida a falo muka sameta zaune tare da iya muka zube kayan a nan falon. Duban kayan tayi tana fadin kasuwa kukaje Salima baki fada min ba aida na baku sako kun sayo min tana duban kayan take magana . Kudin ba zasu azu min ba hakana zan iya kashesu ban mora ba ko kuma in rasa me nayi dasu amsan data bata ke nan lokacin. Ga mamakina sai naji Saare din na fadin ke Ramaah nawa ya baki halan nace dubu gomane sai tayi shiru bata sake magana ba sai can take fadin baki sayo komai bane ke nace a,a ban saya ba anty Saare. Mikewa Salima tayi zuwa daki da ledan kayanta a hannu na dan kai kwance a inda ta tashi ina kallon tv dake aiki iya ke fadin ki lalubo muna Jafar muji koya sauka lafiya. Ta dauki wayanta tana neman layinsa din yashiga take gaidashi tare da fadin iya tace ka sauka lafiya ko yace Alhamdullahi ina kaduna sai yamma zamu shiga jirgin Rivers din . Muryan Salimace ke kirana daga daki na amsa na tafi ba tare dana san yadda sukayi ba kayane saman gado ta zuba dana shigo take fadin ki kwashi kayan nan Ramaah kiyi amfani dasu tun wanda yaya ya sayo muna ne da yaje tafiya da wasu na sallah ba amfani nake dasu ba don ban faye son dogon riga ba idan zan fitani. Godiya nayi mata na kwashe kayan zuwa wajena na aje ta mike zuwa gaban mirrow ta kwashe kayanta kaf ta miko min tana fadin zaki iya amfani da su zai maki kyau sosai ya gyara maki jikin ki don ni bai kara min wani haske ba. Na fararen mutanene na kwaso sai daga baya nagane hakan kinga idan ya karbeki kya dinga sayensa daga baya kina amfani dashi. Kwasa nayi na kai wajena tunda yanzu a nan dole zan rika amfani tunda yaya Habu yana nan sai gashima washegari shima ya koma wajen aikinsa . Duk daya tafi ban koma ba a nan muke kwana saida mama tayi wajen kwana uku asibiti tare dasu ummah ta fahintar da ita komai game da antyna ta dawo gida ta dan huta. A ranan ne kuma muka wayi gari da an shiga part din nasu saidai bamu san me aka dauka ba tunda masu wajen basa nan. Wanan dalilin yasa ya J daukan maigadi a gidan dama yana da niyar hakan ga iyalinsa din ya kasance a yanzu muna da maigadi sai kuma mama tace nida salima mu koma kwana a can har ya Habu ya dawo wanan dalilin yasa muka koma kwana din a part dinsu mu biyu. Acikin yan kwanaki na kara fahintar waye salima don gaskiya muna zaman mu na lafiya sosai tsakanina da ita duk da ba wani girma na sosai tayi min ba amma haka bai hana in bata girmanta ba. Itama din na fahinci tana daukana tankar yar yar,uwartace ta jini don yadda take zama ta fada min komai nata ta dai sake jikinta sosai dani tunda tasan ba wanda zan fadawa . Wani saurayi take so sunansa yazid amma iyayyenta da yayyu sunce yayi yaro kwarai a gareta ita kuma ta nace akan shi take so . Duk da yazid din zai girme mata da shekara biyar ko fiya da hakan amma sun nuna basu son alakanta dashi gashi kuma sun shaku sosai dashi din. Da muka dawo da kwana part din antyna sai hakan yai mata dadi sosai sai sukai wani lokaci dashi a waya nikan ina kwance ina sharan barci na. Idan ko idonshi biyune zata ban waya mu gaisa dashi ya dan jani da fira har in gaji in mika mata waya don bai gajiya da rokona in kafa masa gwaunatinsa gasu yaya. Shi baisan banda power hakan ba garesu nima cin arzikin yar uwatane ya hadani dasu idan bashi ba ina rugga tare da dabbobin mu da baffa ya kwace muna. Rai da kwade irin na dan adam a zaman mu wajen Baffa saida muka gano shanayen maihaifin mu kuma muke basu kulawa sosai a lokacin. Don sai ince yawancin shanayen da baffa ke alfahari dasu na mahaifinmune don sunfi yawa sune masu dabbara dabaran baki da fari a jikinsi kinsan shanun mu na can suna da babbanci da shanayen ku na nan mu namu gudale sinfi yawa sunci sun koshi sosai suna bunkasa don hakkin da suke samu. Yayin da yar,uwata take har lokacin karkashin kulawan likita kuma tayi kyau sosai su mama dabu da mahaifiyan mu suna kwantat mata da hankalinta. Hakan yasa jikinta yayi kyau ta murje ba kamar yadda aka kaita asibitin ba ga kuma rubutun da a kullum sai an wanko mata tasha. Yauma shiri muke don mama tayo waya da muje gidan malamin bayan kwatancen da tayowa salima tace tagane gidan zamu karbo mu sameta dashi asibiti. Zafin ranane a lokacin amma haka muka daure muka fita bayan la,asar dakyat kuma muka sami abin hawa da zai kaimu unguwar mu karba mukai asibitin. Gidane mai fadin baranda daga waje sai ciki inda tulin kayan da muka gani ya nuna na almajiran gidan ne muka karasa ciki kuma zaure biyu ne a gidan nan muka sami malamin muka karba ya tambaye mu mai jiki ? Salima tace da sauki idon da bawan Allah ya kura min yasa na shiga tsarguwa da irin kallon da yake min har dai muka samu ya mika muna mukai mai sallama. Karfe biyar a asibiti yayi muna mun samu su mama a waje suna shan iska muka gaidasu tare da mika mata sakon tana ta saka muna albarka. Nan take fada muna cewa almajirin dake kawo masu kullum yau baida lafiya ita kuma ba dadin jiki ta tashi dashi ba don saida tasha magani. Tausayi ta ban don akan ciwon yar uwata ta hade nata ta zauna a asibitin duk akan neman saukiwa danta take wanan abin mun dan jima a wajensu din. Nan mahaifiyar mu take min yare da inzo in mata kitso kanta yayi mata nauyi da yawa na bata shawara akan tazo gida zaifi . Don ta samu ta wanke kan saboda kitson ya jima akanta idan anyi sabo duk a cikin harshen fulatanci muke magana da ita don haka basa jin mu. Inda ummah ke fadin ya zatayi tazo gidan da sunan kitso gara dai inzo nan in lalaba mata kan nata duk da maman mu yar daji ce amma gaskiya tana da tsabta sosai kafata da kanta basu rabuwa da gyara kullum. Mamace ta mike take fadin bari ta duba ko ta falka ta bata maganin ta shiga nan nake fadawa Salima takaddaman da mukeyi da ummah din wai kada a zageta yarta na asibiti kwance ace tana batun kitso ita. Lah ummah kizo gida ki wanke idan ba zaki zo ba kuma sai a kaiki sallon a wanke maki a can tunda shi kitso dole sai anyishi. Murmushi tayi tana fadin boni jam saloon kuma yar nan meya kaini zuwa saloon a wanan shekarun nawa kuma yanzu ai garama inje gidan baku aimin a can din. Itama salima din tayi dariya tana fadin kukan filani Allah yayiku da kunya ummah meye a cikon kunyan haka kuma tunda ba tsufa kikayi ba ai nifa har yanzu zuciyata ta kasa yarda cewa kece kika haifi su Ramaah wallahi. Don kinfi kama da ace kece yayarsu dai ba mahaifiya ba ummah don sam baki tsufan haihuwansu ba haka tayi murmushi tana dukar da kai. Wai meyasa mutane da dama suke fadan hakane garemu bakece kika fara fada ba kowa haka yake fadi a kanmu idan ya ganmu da ummah din. Mama ta fito da kayan abincin da anty Yanda taci hakan yasa na tashi da sauri na karbo a hannunta tana fadin tagode kayan da zamu dawo gida dasu ta fara tattara muna waje daya harda wa yanda zan wanke masu. Karfe shidda a gida yai muna ban kuma zauna ba saida na wankewa ummah mu kayan nata dana anty yanda da ake kawowa gida in wanke ko yaushe. Abinda ke ban mamaki yadda na kula da matan gidan basu damu da zama yar uwata asibiti ba irin yadda na sani idan dan uwanka yana kwance ka dan rika lekasa din sam basa sunayin hakan gareta ba su ? Hakan yasa na kara nisantar lamarinsu iyakata dasu gaisuwame tun bayan da naje neman magani in hade saboda ciwon kan daya kamani ta dalilinsu suka hana min magani saida mijinsu ya sawo min har yanzu kuma ina amfani da sauransu wajena. Iya taje asibitin ta zauna da matan kawu dauda a ranan don su karbawa su mama zaman su dan dawo gida su dan sarara hakan yasa na samu daman banyewa ummah kai nayi mata kitso irin wanda na saba yi mata a gida. Sai wanan ranan yan gidan suka san dana iya kitso sosai har salima na fadin zan mata idan ta banye kanta. Port,harcourt rivers state ya J ne ya gama shirinsa na tafiya ma,aikatar da zaiyi singnig don kayansu su samu shigowa arewa a cikin wanan watan. Don sun gama duk wani proces din da akeyi dashi da maigidansa yana shiga wajen yana kiyasta irin dukiyan dake kasan nan ta Nageria da Allah ya bamu. Amma dan arewa yana zaune a cikin kunci yake rayuwansa zai iya rantsewa a wajan nan ba wani bahaushe saishi kadai duk da suna bat da kama da irin shigar mutanen wajen a yanzu. Don shine ba zai rantse da hakan ba a lokacin a madakatar da zai sadaka da wajen da za a sakama hannu din ya samu mutane birjit dake jiran su gana da babban mutumin . Wanda kowa da laluran daya kawoshi wajen bai dade da zama ba wani ya fito daga office din yana kiran sunan company nasu hakan yasa ya mike don ba wanan ne zuwansa na farko ba. Mutumin dake zaune a barin hangunsane ya bishi da kallon mamaki don a iya saninsa baisan mr Okah da wanan mutumin daya canjesa ba a baya. Wanda a yanzu shima yazo ganawa da wanan mutumin ne ta yadda zai samu ya dan jona ya fara business din don abubuwa da suke kokarin tsaya masa a yanzu din tun bayan barinsa wajen mr Okah da abayansa yake yana ci yanasha yana duk wani biyan bukatansa cikin mutunci har duniya ta sanda shi a lokacin. Saidaga baya da ya yaudareshi ta hanyar cuta mr Okah din ya watsar dashi na har abada da a yanzu bai aikin komai kuma sai dan buga buga don ya kare mutuncin kansa. Lalai babu tamtama wanan yaron mr Okah ya aza a matsayinsa na baya amma wanan yarone sosai anya kuwa tunanensa ya zo a gaskiya yasan halin mr Okah da kyau kamar yunwar cikinsa fa ? Mr Okah mutum ne da zai sakar maka dukiya kayi komai a kai kamar bai damu dasu ba sai ranan daya bukaci sanin kan dukiyan zai waiwayeka akansu. Wanan karon ma haka yaiwa Jafar din da kanwarsa tillo daya ta gabatar mai dashi kuma ya yaba sosai da hankalin yaron da baiwansa bai taba tsamanin zai samu yaro karami haka da zai rike wanan amanan da zuciya daya ba don yaron akwai basira da hazaka ga zafin nema. Haka hasken taurarinsu yazo daya kusan ma yace na yaron yana gab da taushe nasa yadda masana suka fada mai akan yaron. A bangaren jafar din kuma dashi da kaninsa Abubakar suke tsaye sai yan uwasa biyu daya yaba da halaiyansu sune suke gudanar da wanan sana,an dayanzu darajan gidansu ya soma farfafowa. Irin jajircewan Jafar din da taka tsantsan akan dukiyan mutane yasa idonsa yana kan komai yasan shige da ficen da yan uwan nasa sukeyi da dukiyan bai yarda ya shagala a kan dukiyam mutane ba yana hasaso masu jin dadinsu gaba. Har kawu dauda ya dora a wanan harkallan a yanzu a wasu jahohin dake kusa da kaduna din shima sai tubarkallah a yanzu. Nace ashe da zamu samu irin jafar goma a arewa ba za a barmu a baya ba indai dan uwa zai samu ya tunane saura azo aci tare a tsira tare da mun rage raddin talauci a nahiyar nan ta arewa. Saidai mutane a yanzu kansu suka sani sai iyalinsu mutum bai tunane zai iya mutuwa ako yaushe yabar baya da Kura ga magadansa. Har jafar din ya fito wanan kafirin yana zaune yana jijiga kansa a wajen ya fice abinsa ba zaka taba daukan wani abu maimuhinmanci yayi ba a lokacin. Jafar mutum ne daya bude ido da neman kudi tun yana karami suna bin mahaifinsu kasuwa suna ganin yadda ake harkan kasuwanci da har yazp kuma kawu dauda ya kara dorashi kan wata sana,an . Hakan baisa yayi sake da karatunshi ba don har masters yayi saboda daman da yake dashi na magani a ganan yaron don ga tushen ilimin a cikin garinsu. Hankalinsa yana kan tukin da yakeyi duk da a yan kwanakin hankalinsa gaba daya ya koma gida saboda azumi dake karatowa yaso a satin nan yashiga arewa saidai hakan ba zai samu a wajensa ba don kayan su dabasu daga daga kudun ba har lokacin. Wanan yasa bai samu shiga gida ba sai dole an fara azumi badashi ba ke nan hakan yasa ya jawo wayanshi ya soma kiran layin mahaifiyarsu dan yaji ya za ayi ke nan ? Tana dauka yaji muryanta da alaman ba lafiya ko barci kuma ta tashi a lokacin hakan yasa hankali tashe yake fadin lafiya dai mama ? Dan murmushin dole mama din ta kakaro a fuskanta kamar yana gabanta take fadin ba komai jafar yau dai na kwana da dan ciwon kaine kawai amma da sauki. Kina asibitin ne tace a,a gamu gida iya da matar kawunkune can da ita yau mun dawo gida mu dan huta muryoyin mu yaji a lokacin yace taba saratu waya take fadin bata kusa tana can wajenka. Salimace da Rahaam suke magana yace ta bashi salima din nan ta karbi wayan tana gaidashi ya amsa yake tambayanta idan ciwon mama din sosai ne don yasan ba zata fada mashi gaskiya ba ita. Gaskiya tun jiya take kwance da muka sameta asibiti amma dai kuma yau da sauki tunda tasha magani fada ya fara yana fadin shine baku kirani kun fada min ba salima ? Me saratu takeyi can bayan mama na nan kwance bata masan halin da take ciki ba yanzu zan turo Lawal yazo ya gani idan zai kaita asibitine ? Hakan yasa ya fasa fadan zancen da yake sonyi da mama din a lokacin ba a dauki lokaci ba mukaji sallaman lawal din yazo duba mama din da jiki . Abokinsa ne nasanshi sosai yana yawan zuwa gidan idan yana gari wajensa haka kuma sukanyi tafiya tare indai yana arewa. Shiya shigo ya dubata har sukai dan hira da mama din duk da ina kitchen ina hada girkin sara lokacin amma ina jiyo hiransu daga kitchen din. Ya fita bai jima ba ya dawo tare da wani ma,aikacin jinya ya dubata ya bata maganunuwan da zata sha a raina nace gata ke nan mai karami shike da babba akace. Anty yanda muke sa rai a cikin mu yanzu ta nunawa mama damu wanan gatan sai dai karfin mijinta bai kai ba amma duk da hakan Alhamdullahi gaskiya. Abinda yasa nace hakan dole indai da nagarine kai kaga yadda iyalan mama suke gudanar da rayuwansu dole abin ya baka sha,awa. Don ko ya Habu saida ya kira yana fadin zai taso ta hanashi tace ya zauna yayi abinda ke gabanshi ita lafiyanta kalau Jafar daine ya tayar da hankalinsa. Shima ya Salis ya kira cikin damuwa donshi yanzu yana ghana yana karatune daga can kuma ya kira yana gaida ita da jiki me zai hana bakaji sha,awan hakan ba yadda diya keba uwarsu kula. Bansan ya akayi ba saiga matan yaya din har saare sun shigo suna fadin mama ashe bakiji dadi ba yau yanzu sweet j yakira yake fada muna. Aina fada mai ni zaune nabar mama tana banyewa maman su Raamah kai da za aiwa kitso fadan hakan yasa na kalleta don nasan mahaifiyar mu zataji nauyin hakan data fada. Sun dai dan jima kafin su fice daga part din lokacin har na hada komai da za akai asibitin na shiga wanka don nice zanje nakai masu abincin . ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K44JhTApwmM4gU33AbpqHC MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,1️ 1️⃣8️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Bayan kwana hudu ya sauka garin da tarin alheri mai yawa dan tab motar dayazo dashi take da tsaraba. Mu mukai ta jidan kayan zuwa cikin gida dasu part dinshi muna tarawa a tsakar falo koda muka gama kwanciya nayi lokacin. Saida asuba da muka tashi yin sahurne nake jin yar wajensu anty Saare na fadin dama tasan zai dawo da alheri haka mai yawa. Don tana zaune yake tambayan su dame dame zai sayo a lagos don a rage kayan sallah suka lissafa mashi yace saura sai idan yazo nan zai saya. Anan na gane kayan da mukai ta jida zuwa cikin gida shi take nufi nikan ko kusz ban kawo da rabona a cikin kayan ba don haka ban tsoma masu baki ba nasan dai shima yaya Habu idan ya tashi saya zai sayo dani donshi ba zaice ya manta dani ba . Tunda sanadinsa nake zaune a gidan wanda kiri kiri matan dan uwansa suka nuna suna kyashin zaman mu a gidan mu kuma da muka fisu iya miskilanci muka nuna bamu san sunayi ba ma. Ruwan shayi kadai nake sahur dashi in kwanta ko ranan inga gama sha na shige daki na kwanta da yake azumi na kai bakwai ban fito yin shara ba saida gari ya kara haskawa na fito nayi shara da wanke wanke na koma na kwanta. Yanzu mama tana gida kamar yadda yayanta sukace ta dawo gida da azumi sai ummah mu da yar uwata ke asibitin gashi ita Yanda sai an hada mata abinci don ba halin tayi azumi din a lokacin. Abincinta na dora wanda a yanzu sau daya akeyi da ankai abin karyawa sai kuma na dare donshi nakeyin wanda ba zai lalace da wuri ba akai mata. Ina gamawa na koma daki na kwanta ban fito ba sai da azahar daidai lokacin kuma muke fara shirin abin buda baki a kullum. Saman gado naga kaya saidai ban tsaya ba na shige ban daki dana fitone na kula laces ne saman gadon ajiye a cikin leda ban kuma tsaya budewa ba na tayar da sallah ina gamawa na dauko dogon rigan da anty Salima ta ban nasaka dogon rigar atamface dinkin pitted ya dan matse min jikina kadan don zan fita kurman jiki. Falon na fito na samu mama tana gyaran kullum masa da za ayi ranan nayi mamaki ganin hakan gaida ita nayi ta amsa tana fadin Rahama kin tashi ashe yanzu nake zancen zuci a kanki ai. Natashi mama na kara fada masa zamuyiwa yayan ku yau tun da safe nake aikinsa na barkine ki huta tunda kin samu barci yanzu don Allah fitar min da kayan miyan can daga waje mu dora murhu zaifi sauki ba zan iya yin wanan aikin a saman gas ba . Na juya na dauki kayan miyan mai yawa a wani baho nauyin sa ya ban mamaki ina fita nake jin mama na kwalawa yan matan ta kira da su fito su sameta waje. Icen na hada da komao yadda ya dace a wajen gidan wajen wani dan innuwa kujera na dora mata sai na nufi wajen famfon waje da kayan miyan . Alokacin naga ashe naman kaine na saniya guda aka sare yasa roban nauyi sai kayan miya da aka zuba sama ya rufe wanan din. Mama ta fito tana fadin kinsan Jafar da hauka yace masa yake so ayi mai yau yasha ruwa da abokansa na lissafa mai tare da sako tun safe a hada mun wan kullum yanzu buhari ya kawo minshi daga can gidan da aka niko min. Nagane me take nufi yasa naci gaba da mamaki miyan muka fara hadawa tunda miyan naman kaine bamu tsaya sai markaden ya soyo ba irin miyan shinkafa. Wanda a lokacin mukai mashi hadin gaba daya bayan mun soya mai daban muka lema a saman markaden dake tafasa a wuta kayan kamshi da komai aka zuba muka shiga gyara wuta idan ya jaye. Saida mukai sallah la,asar ta fara suya da kanta a zatonta ban iya ba tunda ni bafulatanan dajice ai don a daji suka dauko mu. Sukan manta da kaddaran mutuwa ya mayar damu dajin da suka ganmu a ciki din amma komai na rayuwan bahaushe shine akidar mu. Saboda iya na koma ciki don tace ita sai an dafa mata shimkafa da miyan da zataci da ganyen salad kai azumi bakaci ganye ba aiba yi bane. Har nagama miya na dora shimkafa na fito anty Saare na samu saman tanda tana tuyar waina nace ta kawo in gwada wutan na gyara na bajeshi da kyau kafin na fara zuba man suyar cikin yan mintuna na tara waina karshe dai nice na karasa suyan mama tana ta masu kwakwazon hakan . Tace komai yar nan ta iya duk abinda kasa kanka a duniya zaka iya amma shiririta ya hana ku tsaya ku koyi girki da zakuyiwa mazajen ku nan gaba. Su wa yancan mashiririta kuna dai gani mijinsu yana son abincin gargajiya amma basu iya ba sai shirme daga taliya sai indomi wanan girkin macen arzikine ? Sai gashi kuma ya shigo da kayan shan ruwa niki niki aka jibgesu a nan inda muken yana fadin ke Saratu don shi da sunanta na yanka yake kiranta dashi. Ki gyara muna kiyi fruit salad a jefa kankara ta kalleshi tana bata fuska alaman itafa ta gaji lokacin mama din tace wai kai don me ba zaka kaiwa matanka wanan wahalan daka jajibowa mutane ba ? Ya dan marairaice yace mama ai sai naji kunya wa yan nan me suka iya don Allah banda shirme aida su fito su kama a samu a hada da wuri kada a makara. No please mama son Allah barsu a can suna zuwa wajen nan aikin zai tsaya ko su tafkawa mutane shirme yanzu dai a kara da ferfesun kifi irin na ranan da kika bani da safe. Ga wace ta hada can ai tana nuna mashi ni ta kara da fadin indai kaci abincin arziki a gidan nan itace ta hadashi ko yar uwarta . Mama wanda nace dake kamar hadin restaurants din nan fa itace na fada maka ko masa yanzu data karba tayi bakaga yadda ya fita gwanin ban sha,awa ba shine ma nasa su zuba maka. Ya juyo ya dan kalloni yana fadin don Allah ki taimaka kiyi min irinsa ga kifi nan a leda an wanke anyi komai sai ayi yadda ya dace ya miko kudi yana fadin gashi idan za a sai wani abune akara a ciki ? Da sauri anty Saare ta karbe kudin daga hannunsa uwar tace nan kikaci rani har damina ya sameki wajen son kudi tandan masan na sauke na shiga ciki dauko kayan hadin . Dan attah kadan da albasa sai kayan yajin mu na hausa da citta yafi yawa da tafarnuwa da species kadan na dauka daka na fito sharp sharp don lokacin daya karato na shan ruwa har na gama hadawa ina jiran ya tafasa. Naga suna shirme na karba uwar tagumi tayi ta zuba min ido tana kallon ikon Allah tsab na hada fruit salad din da yaji madara da kankanran da zai sakashi sanyi sai flavour don yayi kamshi. Tabarama manya guda biyu anty salima ta shimfida masu saman barandan part dinshi data share sai aka shiga jera kayan abincin harda shimkafan da miyan da mukayi da kunun tsamiya duk aka fita masu dashi wajen shan ruwan da alale da mama ta hada. Nikan tun da aka soma kiran sallah nashige ban fito ba sai suke kai da komo akan abokan yayan nasu abincin asibiti da za a kaiwa ummah na buda baki na fito dashi don dama na damu banji ana zancen kaiwa uwata abinci ba gashi lokaci ya shige wanda aka dauka don hakan yanzo lokacin dauka. Sai lokacin naga motoci zasu kai biyar a wajen nasan ashe yawa garesu don abokanshi na kurciyane dama haka suka taso sunayi a tsakaninsu. Ummah dataga har lokacin shan ruwa yayi ba a kawo masu abinci ba ranan yadda aka saba saita dan fita don tasayo dabino da ruwan sanyi a wajen asibiti. Ganinta yasa wata mace da suka saba take fadin hafsatu yanzu nake zancen yau banga an shigo maki da abinci ba kizo mu zauna mu buda baki kafin a kawo maki. Da kunya ummah tace da matar a,a ki barshi zasu kawo akwai abinda ya tsayar dasu ai kila amma suna tafe nasani haba hafsatu . Aiko ba sabo haka tsakanin mu akwai na musulunci don Allah zo ko dabino da lemu kisha ga ruwan sanyi kada kice a,a ki hana min ladan hakan ? Dole ta zauna suka sha ruwan tare saidai dabinon nan da lemon da ruwa kawai taci daga garesu suka mike don yin alwala. Nan suka zauna bayan sun idar suna dan hira matar tana buda bakinta tunda tasan baci ummah zatayi ba kota matsa mata. Ruwan sanyi ma gashi ranan tana ganinsu dashi amma haka taje gurin sayarwa ta sayo saida matar tagani take maganan bata kyauta mata ba meye amfanin zama taren da sukeyi kuma ? Irin halaiyan ummah na kama kai yasa matar sha,awan ummah din sosai gashi ita kome aka kawo mata saita nemi matar ta bata koda abin dan kadan ne amma ita bata saka ido ga kowa sai abinda ya kawota. Har mu dake zuwa mun san da shakuwar ummah da matar don bamu shiga mu fita sai muje mun gaida mara lafiyan su da matar a duk inda take. Ainihi matar daga kaduna sukazo ba a cikin garin zaria suke ba saidai suna da yan uwa sosai a garin don haka gidane masu zaria din. Tana zaune ta hango yaron yana nemanta ta kirashi yazo da basket da ledan poly bag yana gaisheta bai bata kayan a nan ba saida suka shiga ciki ya aje. Ya gaida yanda da ba,a bari su fita ko ina sai idan su suka bada umurnin mutum ya fita daga dakin zai dan fita yasha iska ya dawo ciki. Kai bawa ya godewa Allah aduk halin daya samu kansa a ciki rahamace hakan garesa daga Allah wata zatayi cikinta lafiya har ta dauka ta haife bata taka asibiti ba . Saiga wasu kuma don son haihuwan za a rikesu gun likita harsai sun haife cikin saboda tsaro irin hakane sa,an jahiliya mace tayi ta daukan ciki tana samun mata har mahaifa yazo a karshe ya kasa daukan cikin don wahala. Ita kuma yanda abinda Allah ya jerabeta ke nan dashi a rayuwanta har wasu naganin hakan samun wajena kawai da jin dadi irin na wasu matan da sukeyi da gangan. Bayan na idar da sallolina na shiga wanka na fito na zauna na gyara jikina ina dakin nake jin muryan Saiba a falo wai tazo idan masa da miyar sun rage a zuba masu su kara wanda aka kai masu sun cinyeshi gaba daya. Naji muryan mama tana fadin ba za a rasa masa da miya ba ai fruits salad din daine ban zata yaran nan sun rage ba ? Muryan Salimace ke fadin mama kinsan fa nida Ramaah bamuci komai ba sai anjima kada ki kwashe ki basu duka bamuci ba. Salima meyasa kike hakane masan nan mai yawa ina zaki kaishi don Allah azumi akeyi balle kice da safe zaki shi . Mama meyasa basu fito anyi aikin dasu ba aimu ba bayinsu bane da mukayi tunda aikin mijinsune ? Sai abin yaso ya zamo kamar fada a tsakaninsu da anty Salima din har Saiba na fadin ai dai mijin su ya kawo ai masu dole kuma suci ko bata so ai itama zata gidan wasu za a rama masu abinda take masu can. Muryan ya Habu naji sai lokacin nasan ya shigo gari ashe shima yana garin tunda yamma tare dashi akasha ruwa. Shigowanshi gaida su mama shine kashe fitinan da saboda sanyin hali irin na mama ta kasa kashewa a lokacin. Saida naji fitan ta na fito ina gaidashi da dawowa ya amsa min kamar kullum ba yabo ba fallasa a fuskanshi yana tambayan ya gida ? Na amsa da lafiya kalau nan dai muka zauna suna hira dasu mama wanda hiran akan saiba ce data fadi maganan banza. Naji ya habu din yace da mama daga yau duk abinda ya kawo ki barshi yakai masu can kome za ayi suyi masa da kansu sune dolensa ai tunda shiya ajesu. Nima dai a raina haka nagani mutum mai mata biyu kamar yaya jafar sai ya tsaya yana wahal da mahaifiyarsa da kannesa kuma ko kuma ya dauko yar aikin da yace zai dauka mana a baya ya dinga biyanta duk wata. Ina zama na debo masa kwara biyu da miya sai gashi ya shigo part din daga rakiyan abokan nasa ya ajewa mama leda yana fadin. Kai mama yau kun fitar dani kunya da bakin yan sherin nan kinji yadda Anwar yake santi kuwa ? Gata nan dai itace zaka godewa yanzu haka zancen ka samu munayi a nan matar ka tazo nan kan wanan abin tana fadan abinda bai dace ba. J don Allah daga yau din nan duk abinda ka samu na laluranka ka dinga bar masu can suyi ai suma matane kamar kowa ? Me zai gagaresu iyawa da har zata shigo nan gaban mama tana fadin magana haka komai na gidan nan suna zaton nakane don haka yaran nan basu da daman magana a kai ? Me tazo tayi nan Habu ba naga Saratu ta shiga masu da nasu ba dazun kafin a sha ruwa ? Koma dai meye sun din suke da alhakin irin wanan aikin gareka basu mama ba da yaran nan don a kaucewa fitina irin haka. Kuma ka kyaleta tunda nayi mata magana ba sai kaje kayi fada da ita ba ita wanan halintane gori da rashin kunya So ka barta don Allah. Ranshi dai ya baci amma ya kasa magana don yasan halin matan nasa sarai kome akace tazo tayi zata iya don yar rainin hankalice ita. Bai jima ba ya fice daga falon zuwa part dinshi shima ya Habu din ya fita saida mama ta tambayeshi koya leka asibiti ? Naji yace ai can ya jima daya shigo gari can ya fara zuwa ya dubasu kafin yanzo gida nan yake fada mata cewa likitocin sunce jibi zasu shiga da ita suyi mata scaning a duba lafiyan cikin ta din. Washegari kamar kullum ban fito da wuri ba kamar jiya daine kodana fito a falo na samesu ana ta kasafin kayan shayi da abubuwan more rayuwa na dan adam a falon . Nagaidasu nashiga kitchen har lokacin kayan da akaci ya rage suna wajen ba a samu wace ta saka a cikin fridge ba dole na tsaya tunda miyar baiyi komai ba na adanasu a cikon fridge din. Rahama ku karbi key kukai min kayan nan a part dina ya habu ya fada nida salima muka kwashe kayan a hanya take fada min wai ashe ? Jiya ya J sunyi fitana sosai da Saiba har ya mamareta yana fadin sai ya sake ta don ta isheshi tana son jawo mai matsala da yan uwansa. Ina gyaran falon take fadin ai har Saare yau mama taci mata mutunci sosai da safe tace ta daina shiga part din ya J din tunda duk tsegumi ya taso da sunanta a ciki. Wayanta da mama ta kira tana tambayanta ina muka tsaya gashi tana jiran mu mu mikawa makwabta munje can mun zauna take fada mata Ramaah ke gyarawa yaya part din. Bayan mun dawo muka dauki kayan da aka warewa makwabtansu niki niki muka shiga gidajen muka bayar ba hutu kuma muka dauki na tudun wanda wanan ya habune ya kai mu da motarshi muka ba kowa nasa ana saka albarka muka fito daga unguwar. Ranan kan bamu iya komai ba sai mace tayi muna abincin buda baki ita da Saare saboda mun gaji sosai a ranan wajen raba abin buda bakin da ya J ya rabawa yan uwa da abokan arzkin su tunda mune kamar yara a gidan. Sai bayan shan ruwa a buda baki iya ta soma magana tana fadin gidan nan kan ranan da yarinyar nan ta barmu zamuji daban . Yau kadai har munyi kewan girkin yar nan to iya kina nufin ni bam iya girki ba ke nan shiyasa bakici ba saiga mama kuma na fadin ke salima jeki kitchen ki dumama muna miyar jiya wanan kan ina zai ciyo ga yaji ga gishirin tsiya miya kamar an wanke kan mahaukaciya haka ? Fushi anty Saare din tayi tana fadin ita shiya bata zama duk abinda tayi yanzu sai ace bai yi ba Ramaah ta fisu iya komai. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K44JhTApwmM4gU33AbpqHC MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,1 1️⃣9️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Idan suna gida bamu da hutu sai sun bar garin zamu dan dafa abu mai sauki da zamu bude baki dashi a irin hakan na fahinci abubuwa da dama a rayuwa. Na farko komai arzikin ka a waje idan akwai wanda ya daraka naka sai ya zamo babu mai ganinsa saidai wa yanda suka zama dolen ka su gane maka hakan. Don yanzu da mai lokaci ake zamani harda wasu uwayen suna nuna irin wanan bambanci a cikjn iyalansu da suka duka suka haifa. Zakiga uwa kamar tana shakkar danta don kawai yana da hali shike daukan dawainiyar ahalinsu sai a koma jin tsoronsa shiya zama kamar bakece kika haifishi ba. Da yawa a yanzu ana samun hakan ga iyayye saidai akwai jijirtattun iyayye da har gobe suna a maysayinsu na iyayye din komai mutum ya zama kuwa. Zaki suma sauran diya suna nasu kokarin amma ba a ganin hakan da sukeyi hankali sai ya koma a waje daya anfi ba bangaren dake da maiko muhinmancin. Saidai gaskiya a nan din ina kallon abin kamar da dama sosai don dukka yaran nata biyu tana basu kulawa irin yadda ya dace uwata gari tayi din. Don ko shima ya Habu yana tsaye da dawainiya dasu sosai duk da kamar karfinsa baikai na jafar ba da akewa kallon maikudi a cikin dangi . Dan kowa ya tashi dai jafaru dai jafaru dai nazo a roka min jafaru abu kaza da yawa haka suke zuwa a cikin dangi wajen mahaifiyar nasa tunda Jafar din baida tsayayyar matar da yan uwa zasu buga gaba da ita. Zakiga abin mamaki a babban gida da abin haushi har dana takaici shi jafar dai ya kasance mutum mai ujula yanzune zaizo kuna magana sai kuma wani uzuri ya kamashi ya barka wajen. Ya Habu kuma akwai tsare gida gashi shiru shiru bai faye magana ba amma akwai tsayawa ya fadi gaskiya don hakane ma kowa yake shakunsa a gidan haka kuma na kula Mama Dubu tafi ba Habu din lokacin ta da daukan sha,aninsa da muhinmanci. Rayuwa tana ta tafiya a hakan dai inda azumin wanan shekaran ke muna bankwana akwai dadi kuma akwai wahala wajen aikin abin buda baki ga mata. Sallah saura sati daya suna zaine ranan dai duk iyalan mama dubu suna zaune a falo misalin karfe hudu bayan sunyi sallah azahar ina kitchen ina ta hada abin buda baki don yanzu ban tsayawa jira tunda jiran baida amfani karshe a kaina aikin yake karewa kowa dayasha ruwa zai nemi waje ya labe. Ka zamo mai zafin nama wani lokacin akan kwari mutum ga hakan kowa saiya sakama ido don amsan zaka iya din . Saida hakan bai damuna don da zuciya daya nake hakan, suma kuma sun sani, haka kuma wanan aikin yafi min aikin gidan baffan mu sauki sau dubu. Gidan baffa karfe hudu dole mu tashi mu fara surfe idan mun gama gari ya fara haske mu dauki jarkan diban ruwa muna gamawa da mun dawo zamu cika jallon mu da dan gudun kokon da zamusha wurin kiwo mu zamu daka amma kuma a hana muna. Shiyasa nake kallon wanan nagatane tunda ni zan dibarwa kaina iya cina don haka ai wanan ya zamo gata kuma ga hutun da nake samu nayi na tsawon lokacin. Rabon kayan sallah Jafar din da Abubakar sukeyi sai mama da iya da kannensu mata dake ta rubutu a takarda suna mannawa su kuma matan shi suma suna nade kayan. Mama nifa har yau banji ance ga kayan sallah Ramaah ba salimace ke fadin hakan wa mahaifiyarsu ta kureta da idanu ? Kamar ya ba,ace Ramaah ba ba yaya Habu zai mata ba ita da matarshi Saare ta riga uwar bada amsa . Habu kuma Saare don tana kanwar matar Habu za,ace shi jafar ba zai mata sutura ba kome ? Cak suka tsaya ga abinda sukeyi gaba dayansu suna kallon mama din da saratu au kece zaki tsara yadda abin zai kasance ashe ? Wai akan wa ake magana Jafar ya tambaya da sauri salima tace Rahama ranan full name dina ta fada kai tsaye. Ramaah ya juyo ya dan kalli dan uwan nasa yana fadin Rahaam bata da kayan sallah dama kuma baki fada min ba salima ?. Yaya na dauka ka sani ai shiyasa ban fada ba da wuri naga kowa kuma baiyi magana a kanta a yanzu ba yasa nayi magananta ai. Wai wa kuke zancene bai samu kayan sallah ba cikin mutuwam jiki da jin nauyi mama din tace wanan yarinyar wallahi . Ni abin gidan nan yana ban mamaki ta ya yarinyar dake dawainiya daku haka zaku dinga cewa kun manta da ita don Allah zama baice haka ba wallahi. Iya ta fadi hakan cikin hasala tana juyawa kafin mama din tace a,a Iya munyi da Jafar tun a waye yace kayan sallah nace na yaran nan su uku zai sayowa kinji yadda mukayi na dauka harda nata aka hado ai ? Wai dai wace yarinya ke Asmau dana kawo kaya mena fada maku da aka fitar dasu ? Nikan kace nasu Saare ko kace mu zaba mu basu saura kuma muka zabi namu muka basu nasu ta karasa a sanyayye tana dukar da kai. Toke salima waya baki kayan ki ta amsa da fadin Saarece tashigo min dasu takai dakin mu ko wani bibiyu ta zaba ta ban nawa shike nan. A,a ni ban gane ba Saratu ina na wanan yarinyar ya shiga don Allah J is enough idon kayane a barshi kawai ke salima kuje a sama mata kaya gobe shike nan . Ya zakace dani shike nan wancan karon ma haka sukayi aka raba abu a gidan nan suka hana mata har mama taga laifina gashi kuma again ankara yi don haka ina son ina kayan nan suka shiga ? Suna tsakanin makiran matarka mana ai kaji sunyi shiru ga baki dayan su sunsan yadda sukayi da kayan ke nan a tsakaninsu tunda suna bakin ciki da zaman boyar Allah nan gidan nan. Itako bata ko san sunayi ba don basu gabanta sun dauki kiyayyan duniya da kyashi sun dora akan matar kani banda tsiya harda kanwata zaku saka a kishi. Ita kanta matar Habu bata san kunayin haukan ku ba hakama yar uwar nata gashi dukkan mu nan gidan muna moran wanan yarinyar. Ko wanan aikin da take ga sharan nan ga girki yaci ace yarinyar nan ko albshi ake mata tayi kissa amma ina tunda suna da wankakken zuciya ba hakan a gareta duk iyace take fadin hakan garesu. No ba zancen da za ace a kyale bane wanan duk da ba zama nake a garin nan ba nasan irin kokarin da yarinyar nan takeyi gidan nan kullum. Ko a fito min da kayan ta inda suka shiga ko kowan ku ya kawo nasa nan yanzu ku har saratu din ban cireta ba ? Dama ai tunda koma meye da ita aka hada baki aka kulla hakan tasan komai tunda hanyar data zaba ke nan bakiji kunyan hakan da kukayi ba don Allah ? Ina yarinyar nan kamar yadda Iya ta fada duk gidan nan kowa yana cin moriyanta a yanzu ku duba zuwansu yadda yanzu gidan nan ya koma fes dashi don Allah ? To mama akan me zai sayo muna kaya iri daya da ita idan su Saare yan uwansane ita kuma meye nasa don kawai tana kanwar matan Habu ? A zabure ya tasowa Saiba din dake magana a lokacin, tayi saurin fita don ganin an taresa daga zuwa gareta ta fita tana maganganu masu zafi game dani. Hawaye naji sun zubo min don a yanzu kan ba fahinci zancen da sukeyi a kaina sai hukuncin ya Habu ya burgeni da yace to ai gaskiya ta fada kada kuga laifinta don Allah. Nine ya kamata in dauki nauyin matana dana yar uwarta dake zama da ita gidan nan ba J ba kowa yasan albatkacina sukazo gidan nan . Kai Habu ka bari a fanci inda zancen nan ya dosa dan uwan ya taresa da fadin hakan inda yaci gaba da fadin kowa dake wanan gidan har gidan kawu nauyin irin hakan akaina ya rataya don hadin kan mu da kowa namu don me zasu so zarta hukuncin dabani na tsarashi ba . Yau yarinyar nan kamar kowa take a wajena tunda zamaka takeyi zaman mu kuma a cikin gidan nan to ai yaya komai za a raba saidai na raba nawa biyun in bata haka akeyi kulum a gidan nan salima ta sake fada. Ke ina aka kai kayan yarinyar nan ya kallo Asmau yana tambayanta suna wajen mu ta fada kai tsaye ki daukosu yanzun nan ya fada. Kayan nan fa basu gidan nan nake gani Saare ta kara fada a bangareta sai iya dake kallon mamaki take tambayan . Nikan me yarinyar nan ta rageku dashine a gidan nan wai ? Bakin ciki mana Iya amma in aikin karfine kowansu ya iya zuwa nan yace don Allah Rahama kizo ki taimaka min da kaza amma ba a sonta da karuwa . To wallahi kuji ni ban raba kan yayana ba a gidan nan ba macen da zata shigo tace zata raba min kan gida haka yanzu wanan abin dame yayi kamane wai ? Rikici sosai sukayi a kan kayan ni kan ban kulasu ba na gama miya na dora shinkafa na shige dakin mu na kwanta don fada sosai ya J yayi ya kuma rantse idan basu fito dashi ba duk kansu ukkun zasuji mamakin shi wallahi. Bansan ya akayi ba sai ga kayan an fito dasu da yamma an kawo min mamace ta kirani ta ban na karba nayi godiya saidai a kasan zuciyana na nasa cewa ko zan tafi tsirara ba zan saka kayan ba don nima ta fulanin sun hau a lokacin. Duk da karfi bai kai ba amma zuciyan gado yana nan a jinina aiki kuma idan ba na cikin part din mu bane na dainashi daga wanan ranan . Har washegarin da aka ban kayan raina ba dadi da safe na gama shiryawa nace da salima zanje da kaina asibiti in duba yar uwata dama haka nake bayan kwana bibiyu nake zuwa yanzu tunda aka soma azumi din nan. Sam ban fadawa yar uwata komai ba game da abinda ya faru akaina gidan sun dai tambayeni ba komai konace ba matsalan komai. Na zauna a nan don na nasa irin zaman da zanyi ban bakin ciki da ko banda Saratu da bansan abinda na tsare mata ba a rayuwata ? Don haka nake bakin ciki da in girka taci a raina tunda nima yar adam ne kamar kowa gara in fito masu a mutum don a zauna lafiya. Kwatsam saiga anty salma daga Abuja ta bugo waya tana tambayan Yanda karfin jikinta suka dan taba hira take tambayan ina gida ko tace ina kusa ta mika min wayan . Mun jima muna hira in tambayi wancan in tambayi wanan har take ce min nazo mata sallah mana Abuja nace ba za a barni bane . Tace waye zai hanaki zuwa wajen mu Ramaah ? Nayi shiru take fadin naba Yanda waya sukai magana na daiji tana fadawa salma din zata fadawa mijinta idan yashigo insha Allahu zanzo din . Naji dadin hakan sosai yaushe rabona da Abuja koda Yanda taje da mijinta suka kwana hudu acan da yai wani zuwa basuje dani ba rabona da mutunen arzikin mu nida mahaifiyar mu tun rasuwan mahaifin mu da muka koma rugga da zama. Saida akai Azahar na soma shirin komawa gida na tattara kayan dana kawo mata abincin safe na fito babu abin hawa hakan yasa na soma shawaran takawa don komawa gida. Wani mai mota yazo ya tsaya ban kulashi ba yaja motarshi yayi gaba hakan yasa na soma tafiya da kafa ga kuma kaya niki niki a hannuna dukka biyu. Saida kyat na samu abin hawa nashiga ya kaini gida abin mamaki ashe mai motan nan yana biye dani a baya zan bawa dan mashin kudinsa naji yana fadin malam ta barshi kazo ka karba. Na dago kai na dubeshi shine dai ya tsareni a bakin asibiti na dangwarawa mutumin kudi na shige gida da sauri. Gidan kaca kaca ga ganin idona kaina kawar na karasa na shiga falon da sallamata suna zaune suka amsa min mama ke fadin yar halas yanzun nan nake zance ki fa a raina. Nadawo mama na tsaya rana yayi sanyi na dawo tace aikuwa yau ana kwada rana da zafi a garin nan kayan nakai kitchen na aje kayan dana dawo dasu daga asibiti. Kafin na juya zuwa dakin kwananu suna kwakwance suna barci adakin na tube kayan jikina nashiga bayi na watsa ruwa na fito na samu waje nima na kwanta. Sai barci ban tashi ba sai wajajen la,asar da karan wayan anty Salima ya tayar dani alwala nayo na dawo nayi sallah ina idarwa na fita zuwa part din anty na na gyaro don yaya Habu dake gari baya dawowa gida sai lokacin shan ruwa ko kuma idan wani abin ya dawo dashi. Kodana fito kitchen na samesu da mama din sai fada mama keyi tana fadin aiko wani rai yana son hutu a cikinsa shike nan kun mayar da yarinya yar aikatau din ku kowa ya mike kafa saidai ta girka kuci kuma babu kyautatawa. Hakan da tayi yau yai min daidai wallahi aiko shige yanzu ba awa gorin uban don da uban hanya a zamanin nan balle da gatanta mutuwa yasa kuka ganta nan tare da yar uwanta. Daga faloma iya na kada nata suna kurum nidai ban fito ba sai dana dan jima a daki na fito na samesu wanke wanken kwanonin dana gani suna fara daurayewa mama din na fadin ai in bari suyi meye amfaninsu suna mata dasu ? Saare tayi girkin a ranan don ita salima tace a raba ai idan hakane nidai ina wanke wanken ina jinsu har na gama na koma falo na zauna mirsisi da ido kuwa. Duk da nasan sun fahinceni ko basu bahinta bama nima so nake su fahinceni din zaifi sauki har aka kira sallah lokacin shan ruwa yayi bata karasa aikin ba. Sai faman fada da ita mama keyi karshe ma tunda mukaje sallah ni dai ban fito ba na zauna ina jiran ayi kiran isha,in inyi sallah in kwanta. Tun a wanjen diban kunun tsamiya dana fito yi nasan akwai matsala ranan don kawai shi nake soma sha na diba da kyat na sha rabin wanda na dibo din na mayar da saura kitchen. Na dawo na kwanta ke nan naji muryan su yaya sun shigo shan ruwa shi ya je duk da maganan da akayi anan part din yake shan ruwa har yanzu. Ita Saare din ta zubo masu abinci da kanta suna hira ya Habu ya fara kai cibi a bakinsa ya kasa hade shinkafan. Yayi shiru sai shi jafar dake magana da iya ya diba yakai shima a bakinsa furzowa yayi da sauri yana fadin wayayi wanan girkin mama ? Yana binsu da kallo suma duk kallo suka bishi dashi lokaci guda habu yace na rigaka ji shiru nayi kawai mama ta nuna saare tana fadin gata nan ita tayisa. To me girkin nawa yayi kuma tana turo baki zo nan kici kiji abinda yayi jafar din ya fada a hasale yana fadin shame of you Saratu. Badai wanan abincin aka kai masu asibiti ba ya habu tambaya yana kallon mama din a sanyaye mama ke fadin shine mana nina san tsiyan data kwabawa mutane ke nan ? Ba maggi ba gishiri komai babu a miyan nan fa mama da sauri mama din ta kallota tace na matane kila ban zuba ba. Rufe min baki sakariyan banza kamarki saratu zaki kasa dan wanan girkin da baida yawa ina ga mai yawa ke nan ? Ina wanan yarinyar ne yau da aka bari tayi wanan shirmen a hasale mama din ta juyo tana fadin yarinya kan aiba boyansu bace ko ? Da zata zaman girkawa suna ci kullum yau itama ta hutar da kantane su dandana suji wai shine wanan sakariyar ta kwaba muna abinci haka ? Tsam Habu ya fara mikewa yana fafin zai fita bai tsaya saurareb fadan da mama Dubu take yi ba lokacin da Saare. Yana fita ya tsaya ya hada wani take away da gasassun kaji biyu da drikis ya nufi asibitin dashi don yasan ba zasu taba iya cin wanan kwaban ba na saratu ranan. Hakanne kuwa don koya samesu a zaune sunyi zugun zugun sun gama magana kan abinda ummah zatayi buda baki da sahur sai gashi ya kawo masu wani abinda zasuci din. Da bai kawo ba haka zasu zauna da yunwa don ko ba zasuyi magana ba saboda kawaici irin na fulani da kunya suje tambayab surakansu ya hakan ya faru ? Shima ya J din fita yayi a hasale yana fadin wanan baki da maraba da girkin wa yancan idan zaki zage ki koyi girki ki zage har ace karamar yarinyar nan tafiki iya girki ? A hankali tana gunguni take fadin zaku hadani da yaran da suka bude ido da dafon abinci tunda zaman aikatau sukayi a abuja har suka iya abubuwa haka ? ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,, 2️⃣0️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Karfe tara na falka ba wanda ya motsa kowa na kwance yana barcin azumi na kewaya bandaki na fito na kitsa jikina na fito falo. Ashe iya na zaune a falon ita kadai jin motsina yasa iya juyowa gaida ita na fara yi kafin na juya zuwa kitchen don in hada kayan wanke wanke. Yadda naga kayan a wajen bakyau gani yasa na shiga hadasu har falo duk na kwaso cups din akai amfani dasu da asuba don ranan dai ba wanda yaci abinci zance a gidan. Saidana hada kayan tas na fara sharan part din nasharo ko ina har dakin Iya da mama dubu dana samu ta falka don jin motsina da tayi ina aiki. Falo ta fito ta zauna tare da iya na gama shara na koma kitchen din abincin na tsaya na kalla na tsayin lokaci kafin na juya zuwa wajen su ina fadin mama ya za ayi da abincin nan me yawa ? Ta juyo tana fadin kedai Rahama ina nasan yadda zanyi wanan iskacin na Saare aida yawa yake yarinya ki haramta muna cin abinci haka kiri kiri ? Ta mike tsaye ta biyuni zuwa kitchen din ina tsaye gefe daya na kura mata idanu ta nisa tana juyowa gareni tace ki barshi a tukunyan anjima idan Auwalu yazo yakaiwa almajiransu. Hakan akayi na wanke kayan tas na kara gyara kitchen din ina gab da gamawane naji muryan ya Habu a part din suna gaisawa na fito ina gaisheshi da kwana ya amsa min har zan wuce naji yana fadin. Ramaah ashe Abuja zakije sallah jiya suke fada min asibiti danaje da dare murmushi nayi kawai zan tafi kuma naji yana fadin . Sai kuje da salima kasuwa ki sayi tsaraba anjima gobe akwai wanda zan hadaku yakaiki Abujan nace nagode yaya. Nashige na barsu ina jin mama din tana magana saidai banji abinda tace ba wai ashe tace da alama yarinyar nan ta dauki zancen nan da zafi don banji tana zancen zuwa Abuja ba ai ? Sune suke son tazo masu sallah a can ita wace zataje gurinta ta bugo min waya jiya tana rokona Allah ya kyauta mama din ta fada. Murna yasa tun a lokacin na fara shirina yan kayan da zan dauka da sauran abubuwan amfanina da nake bukata na hada saman gado. Wanka nashiga nayi na fito nashirya zuwa lokacin sun tashi na samu salima zaune tabini da kallo tana fadin kayan meye haka kika hada ? Abuja zanje sallah anty Salima cikin mamaki ta maimaita da Abuja wurin wa nace anty Salma kinsan mutumiyatace sosai yanzun nan da safe ya Habu ke fada min ta bugo waya tana son inzo inyi sallah wajenta. Shiru tayi na dan lokaci kafin ta tashi ta mike ta fita daga dakin nagama shirina na fito falon na samesu suna zaune zama nayi gefe daya ba tare da magana da kowansu ba. Sai iyace ke fadin yar fullo ina za a hakane naga kinyi kwaliya kamar bakya jin azumin nan ke ? Murmushi nayi ina fadin asibiti naso inje iya inyi ,,,,,,, ina jiya kinje Rahama ku koyayyi zuwa asibitin nan fa kuna kanana daku mama ta fada. Naso naje kan tafiyan da yaya yace zanyi gobene kada in wuce banyi sallama dasu ba daidai lokacin ya J ya shigo yana fadin mama kinko ga gidan nan yadda yayi kaca kaca don Allah ? Inda nake mama ta kallo nayi kamar ina kallon tv da wani malami ke wa,azi akan zakkan fidda kai da za,ayi idan ansha ruwa. Sai naji tana fadin ato ita daice me sharan gidan ai tunda tazo gidan nan take wanan aikin bayan ita ba maiyi a cikinsu tana nuna yaranta mata. Suma matanka ba zasu iya komai bane wai Jafaru saidai suci su sha su kwanta su a dole ga bazan ta samu garesu yau da gobefa sai Allah jiki da jini kuma ? Yarinyar nan ta gajine fisasbillah kunga abin nan da yar nan keyi ba a banza zai tafi ba hakan duk gidan da tayi aure nakab fada ince sun huta wallahi. Mijin da zai aureta ya dace mace ba son jiki ba keta ba algus gako wani aiki ta saka kanta yi zata tsaya tayisa tsakani da Allah yarinya ce karama data san ciwon kanta. Haka zakuyi kuma a gidajen ku muddin baku gyara kada ku dauki hakan kamar wayewane kanku kuke cutarwa wallahi. Iya ta karasa fada a cikin takaici tana maida fuskanta wajen tv dake aiki balle dan mutum rana garesa ai, . Yau yarinyar nan bata kimu ba ta yaya zaku nuna baku kaunata kiri kiri haka ba kunya dan zanin da duk dadewansa yan shekaru a jikinta kuce ta kasa ramawa ? Itama fa rayuwane a jikinta kamar kowa yadda kuka rufe ido aka tozarta ta a gidan kowaye dole yaji ba dadin hakan don sai ince duk da sanin ku aikai hakan idan na debe shi namiji a cikin ku da bai bibiyan me ake ciki. Wallahi iya bansan da wanan shirin ba Rahama ai diyatace a yanzu bata da banbanci dasu Salima a wajena don itama a karkashina take rayuwa. Munafunci daine irin ta yaran nan da suka shirya komai da sanin saare aka hadashi a gidan nan makircin nan kuma yana gindinta. Kuka Saare din ta fara tana fadin mama ni ya zanyi tunda sunce ba zasu bayar ba kamar Ramaah zata saka kaya irin wanan tare dasu ? Dama Saiba har ta raba kayan a tsakaninsu ai lace din nan ne suke rigima a kansa jifa wai rigima don Allah akan abinda baku da hakki kansa mama ta fada. Ban raba daya biyu don ko rantsuwa nayi ban kaffara akan wanan zancen yarinyar nan zata tafi Abuja gobe aiba yau take gidan nan ba bataje Abuja ba saida haka ya faru. Wayan da yakeyi ya dakatar yana fadin Abuja kuma me zata tafiyi Abuja gab da sallah haka kuma ? Wai mutanen Abuja din sukace dashi ya bari tazo nan tayi sallah a wajensu niko nasan don wanan zancen suka fadi haka. Shi Habu kuma ya yarda da tafi din ya yarda mana tunda har yazo da safen nan yana fada mata ta shirya gobe akwai wanda zata bi su tafi. Ai nima goben insha Allahu zan shiga Abuja amma bai fada min ba yanzu muka gama magana dashi na shigo nan . Ku barta taje don Allah kada kuce zaku hana yarinyar nan tafiyanta iya ta juyo tana fadan hakan garesu mama dubu tace ai ba zance kartaje ba iya. Sam baiji dadin yadda abin ya kasance ba haka ya fita gidan da bacin rai wani kauye da ake kira da kinkinau suka nufa shida kawu . Wasu filaye ya saya a wajen sai daga baya kuma mai filin yake son ya tayar da ciniki don wani yazo ya kara masa kudi. Kudin da yaya ya ban ba wani sayayya nayi ba na dai sayi kayan kwaliya saura kuma na dunkule abina a jikina don banga wani tsaraba da zan kaiwa anty Salma ba daga bangarena. Sai traveling bag dana saya mai kyau don shi nake kwadayi dama na dawo gida na shirya kayana tsab ina jiran washe gari tafiya idan Allah ya kai mu. Ina barci naji Saare na kirana da dan karfi da in tashi yaya yace in fito mu tafi gabana ya fadi ina duban lokaci shida da wasu yan mintuna na safe. Da sauri na mike tsaye na shiga shiri Allah ya taimaka nayi wanka da asuba hakan dabi,atace watsa ruwa kafin na fara aiki don in samu kuzarin aiki da kyau. Simple dress nayi dogon riga sai hijab a jikina saboda sanyin safiya na fito da yar jakkata da zanyi tafiya nan na samesu falo har da yaya Habu a cikinsu suna magana da dan uwasa. Na gaidasu da kwana suka amsa min mikewa Jafar din yayi yana fadin ka barni dashi Habu nasan yadda zanyi maganinsa ai. Ramaah kin shirya ga yaya zaije Abuja yau shi zai wuce dake don shi wancan sai da karfe biyu wai zai tafi banyi magana ba shiru nayi. Rahaman ta fito kuwa mama dake fitowa kitchen ta fada na amsa da eeh mama tace toga wanan din tsarabarce da zaki dashi ki gaida muna su son Allah a kula da kai kuma aje lafiya a dawo lafiya. Na amsa da insha Allahu mama su har sun kai bakin mota a lokacin suna tsaye suna cigaba da magana da gani dai magana ce mai muhinmanci a garesu. Nida salima iya sai mama suka rakoni har bakin motan da kayana salima tayi mai magana ya bude bayan motan muka saka kayana a ciki. Kafin na zagaya na tsaya ina jiransa a gefe daya salima na min sheri da indai yaya ne yanzune zaku kai Abuja don gudu yake da mota sosai wallahi. Ai shine matsalansa ranan da ya kaimu kaduna ai fada nayi dashi sosai kamar wanda zai tashi sama damu mama ke fadan hakan nidai ina kurum sai ya Habune ya dago yana fadin bude mana ki shiga Ramaah . Baya na bude da zumar shiga naji yace a,a gaba zaki bude mana ai ina ganin kamar ba wanda zai tafi dashi ko ? Ta shiga mana ni kadai zan tafi ya fada daga mama har iya kudi suka dunkula suka ban suna min a dawo lafiya saiga ya Habu ya kara min kudi daya miko min wana rike a hannuna. Nayi masu godiya ya shiga motar suka juya don komawa cikin gida ya fara ribas da motar sai naga yaja ya tsaya. Ta karaso bakin motar rike da yarta a hannu tana fadin wacece kuma tare dakai naji yace ki fadi meye don Allah kada in makara banson rana yayi min a hanya. Lekowa tayi ta ganni kamar in shareta saidai nace da ita ina kwana anty Saiba bata tsaya amsani ba sai cewa ita kuma ina zata ? Tsuki yaja yana fadin gata nan ai ki tambayeta ya fisgi motar da karfi don maigadi na tsaye yana jiransa da get a hannunsa rike. Amma ai ka tsaya dai muyi magana sweet J bai saurareta ba ya fice yanawa maigadi horn da mota na lumshe idanuna na hankali a yadda nasan halinta zasuyi rikici sosai da daukata da yayi a motarshi yau. Ban ko kai karshen zancen zuci ba wayanshi ya katseni naji ya dauka yana fafin umm,humm ina jiki ta fara fada Jafar ina zaka da yarinyar nan baka fada muna ba ? What ki shiga hankalinki wallahi Nusaiba kina wuce gona da iri fa a rayuwata dolene sai na fada maki inda zani da ita ki je ki tambaya idan kin damu ? Naji ya kashe wayan yana tsoki dama nasan za a rina yadda take da zafi akanshi tunda Salima ta tayar dani tace dashi zamu tafi gaba saida ya fadi nayi wanan tunanen da sai wani abu ya faru kan hakan gashi kuwa. Tsuki ya kara ja yana lalubo wayan daga inda ya jefata da farko ya dauko yana tuki yana neman lamban da yake nema a lokacin. Can naji yace mama wallahi idan Nusaiba bata yi hankali ba yau din nan saina saketa kafin ta bata min suna a banza. Banji me uwar tace dashi ba naga ya kashe wayan nasa a hasale yana faman jan tsuki akai kai saida muka tsaya gida mai a kaduna ya tsaya magana da wani kafin ya dan sake. Hanya muka kama sosai inda barcin azumi yake dan dibana a wajen lokaci lokaci saboda sanyin AC motan nasa daya sake . Maganan Salima ya tabbata don ganin mun shigo Abuja ga signboard din THIS ABUJA baro baro a jikin allon shiga iyakar Niger da Abuja din. Wani unguwa zakije ya tambayeni ba tare daya kalloni ba na amsa da maitama kinsan gidan ke nan zaki gane na amsa da ehh . Har yayi shiru naji ya kara fadin idan ba zaki gane ba ki kirasu a waya suyi maki kwantace nace banda waya amma zan gane gidan. Cikin mamaki ya juyo da kyau ya dubeni yana fadin baki da waya fa shi Habu yana me da basu saya maki waya ba ? Shiru nayi don ko da zan taso saida mukai zancen waya da yayata da salima kuma har Salima tace zata ban karamin wayanta bansan meyasa kuma ta fasa ba. Shiga wanan lungin fada wanan muka isa wani katafareb shago yaja ya tsaya ya dauki abu naji yana fadin ina zuwa jirani kadan in dawo don Allah . Ya fita lokacin na sauke ajiyan zuciya a hankali ina bin wajen da kallo shagone babba don jama,a sai shiga da fita sukeyi a wajen. Can na hangoshi da ledoji kusan ukku rike a hannunsa ya nufo inda motarsa yake ya bude ya baya yana aje lodejin aciki kafin ya juya zuwa gaba wurin driver ya bude ya shiga. Sorry na dan dade a ciki na barki zaune bakomai yaya saida ya zauna da kyau ya dauki hanya muka bar wajen hanyan maitama naga ya dauka kai tsaye. Ajiyan zuciya na dan sauke an karaso gida ko naji ya fada na danyi murmushi ban dauka yana da saukin kai irin haka ba. Wancan layin na fada ya mike zuwa layin dana fada muka shiga dab tafiya kadan nace wanan gidan mai bakin get nan din gidansu hjy mamace daga waje ya tsaya ya juya yana dauko ledab a bayan mota naga ya fitar da waya sabo dal a kwalinsa ya fara duba lambobi a cikin wayansa yana lodawa kafin ya miko min wayar yana fadin layin mama dana Salima saina habu suna saka maki . Saida na dan dubeshi nayi kasa da murya ina mika hannu nace nagode yaya Allah ya kara arziki amin yace a uzurce da alama sauri yakeyi a lokacin. Horn yayi sai ga wani dogon sauriya ya leko yana duban mu kafin naji yace daga Zaria ko nace ehh sorry duk basu gida sun tafi umura last week amma anty salma tace idan kin iso a kaiki gidansu . Sai lokacin naji zuciyana ya dan sake da har nashiga vibration inane gidan nata yake naji yaya ya fada tana Aso rock muje ka nuna min ya fada. Saurin yace ga mota nan da tace in kai ta sai naji yace. No muje dai ka kai,mu naga gidan na ajeta baiki ba naga ya juya ya fito da mota muka bi bayanshi har gidan anty Salma din. Duk wanda yaji ance gida a Aso yasan ba karamin gida bane ke nan za a gidan ya hadu iya haduwa mijinta wani babban dan kwangilane mutumin maiduguri. Gaeinsu daya asalima yan uwa suke dashi itace matarshi ta biyu yanzu anty salma yaranta biyu dashi bayan barin mune akai aurensu dashi mun dai sanda zancen auren kafin Allah yaiwa mahaifin mu rasuwa mu koma gida. Ko kuma Allah na tuba ka yafe min inji mata gashi kuma zan fada ince Baffa ya cinyeshi don shi yai sanadin barinsa duniya duk da lokaci yayi dama. Tsayar da motar yayi yana fadin kice min gidan manya kikazo dama murmushi kawai nayi ina mashi godiy. Ledan ya dauko daga bayan mota ya cusa kudi a ciki ya miko min yana fadin rike wanan inda matsala ki kira gida a zo a daukeki . Na amsa da godiyana na fito daga motan ya fito ya bude baya aka fito min da kayana zuwa ciki ban shiga ba saida na kara mashi godiya naga tafiyansa na sa kai zuwa cikin gidan. Ina shiga saiga anty salma da gudun ta muka rugume juna da ita a cikin murna kafin ta sakeni tana fadin wai Ramaah tace nan haka ta zama yan mata ? Nayi murmushi ina fadin nice anty muka kwasa zuwa cikin gidan nasu tana nuna min kauna don haka muke da ita tun ina karamata . A zaria motarmu na dagawa ta juya zuwa part din su mama a hasale take babu ko sallama ta fado masu a falon ta samu kowa a falon zaune. Mama tana ganinta hakan hankali tashi ta soma fadin Nusaiba lafiya kuwa na ganki a haka hankali tashe ko wani abu ya faru ? Babu komai mama dama karan J na kawo maki mama ta dan sake kallonta tana fadin jafar kuma me kuma ya hadaku dashi ? Mama din ta tambaya cikin kulawa don ta kwantar da hankalinta tayi mata bayani yadda zasu fahinci abinda ya hadasu . Mama don ya dauki yarinyar nan Ramaah ina tsayar dashi zanyi magana amma J ya daka min tsawa ? Bai saurareni ba ina ruwana da inda zai tafi da ita tunda da ai an,san ya dauke ba a hanashi ba saboda ita zai dinga muna wullakanci haka mama ? Haba yar nan ki saurara mana kada kiyi furci irin haka ga mijinki don Allah koda kika ganshi da yarinyar nan Rahama hanya ya rage mata ai. To don me ina tsayar dashi in fada mai yarinyar nan jikinta yana zafi amma yaki tsayawa saboda Ramaah zai min wullakanci mama ? Point of correction ki gyara zancen ki kwarai da sanin su ya dauki Ramaah zuwa Abuja kada ki tsaya boyewa don kinj zafi ya dauki wata a tare dashi salima ta fada a hasale. Ki barta tayi maganan ta mana ke ina ruwan ki salima wajen mama tazo fa ba wajen ki ba Saare ke fadin hakan . Dole inyi magana don mu ba yan iska bane da kike son fadan hakan a gaban mama tana fadin wai saboda Ramaah ? Kinzo nan ne kiji dai ina zai tafi da ita to Abujan daya nufa can zai kaita gidan yan uwanta a can zatayi sallah In kuma ya Habu daya bashi ita yakai yaji an juya wanan zancen wallahi mama rai zai baci sosai a gidan nan don sai yaba kowa mamaki matakin da zai dauka kowa kuma yasan hakan . Kada inyi magana ita din muharamince halan da zai dauketa daga shi sai ita a mota da zakice kada inyi magana mijinane fa J dole inji dalili ? Mijin kwace ba da kika kwace wa kawarki mijin har zakizo nan kina kokarin karantawa mutane hauka kega mara kunya don ana kyaleki ? Wai Salima me kike nufi da bazanyi magana ba naga kamar dama kina jirace dani ashe ? Jinan Nusaiba tunda kinji abinda ke nan sallah yarinyar nan zata Abuja tayi gidan yan uwansu shine habu ya hadashi sa ita ya sauketa banga abin hayaniya ba a nan ? Mama niba hayaniya nazoyi ba kawai dai nazone in fada maki abinda yai min akan Ramaah saiya dinga nunawa mutane banza muke mu ? Wasa wasa zancen dai ya koma na Salima data gaji da halin Nusaiba fada sosai sukayi a gaban mama tana zagin Salima din don me zata hanata magana a kan gaskiyarta. Hayaniyan su ya fito da ya Habu daga part dinshi yashigo yana fadin wai meke faruwa hakane meye haka ga mama zaune ga iya kuke wanan abu haka ? Sam bata san yana gidan ba ta dauka ya fita ko bai gari ta don basu sani idan ba sun gashi ba tasan waye Habu din bai dariya da kowa a gidan balle aje ga wasa . Nace meya faru duk sukai shiru ya juya wajen Saratu yana fadin ke Saare meya hadasu fada da safen nan haka ? Bafa fada bane ita Nusaiba tazo wajen mamane da magana shine ,,,, Yaya zakice ba fada bane ita mama din sa,artace da zatazo tana fada akan ya J ya dauki Ramaah a motarsa salima ta tare Saare dake kwana kwana da zancen tana kokarin dora mata laifi. Kai ya girgiza cikin takaici yana fadin don J ya dauki Rahama shine abin fitina ba dan uwana bane J Rahama kuma tana zama kanwar matatace a gidan nan . So baki da right din da zakice kada ya dauketa wai ma a gaban mama kika zo kina wanan haukan ke yanzu bakiji kunyar wanan abinda kikeyi ba don Allah. Assuming nine yanzu zani kaduna saiga kanwanki zata sai ince ban daukanta don ina tsoron Maria kada ta shakeni ko ranta ya baci kome ? Ai yau naga mamaki ga yarinyar nan gara da Allah yasa kana gida ka ganewa idonka irin cin kashin da sukewa uwarku a gabanta ba zagin da yar nan bataiwa Salima ba yau don ta raina arzikin uwarku balleni ? Bazan ce komai ba sai mijinki ya dawo daga Abuja shida ya ajeki zanwa iyaka da shigowa part din nan idan ba alheri ke kawoki ba dama ? Fice kafin na canza zuciyana koda yake banganin laifin ku gaskiya waje kuka samu nayin hakan ni akwai matar da ta isa tayi min haka ko yar wacece ita kuwa an dauki wata a mota idan ya dawo yau ki kasheshi don Allah. Amma ke kan kibar wanan halin wallahi salima ta dubi yar uwarta ta fada tana mikewa don barin wajen. Mama duk hakan da laifin ki wallahi idan mutum zai dauki mataki kan irin zancen nan kice ina ruwansa ? Saida mama ta nisa tace aini yau yariyar nan ta nuna min iyakata a gidan nan don ,,,,,,,, dakata don Allah gaskiya danki ya fada tun farko na fada maki ba aiwa yaran yanzu haka. Duk kama girmanki da kikeyi kina kau da kai ga rayuwansu sun dauka baki da amfani a gidan nan yadda yar nan ta nuna ? Yau gashi salima da abin ya isheta itace ai tayi fadan akan ki don bata da kunya zatazo da wanan shirmen haka a gaban mu. Wanan hali naki dubu shiyasa mutanen gidan ku duk wanda ya dauko sharansa akanki yake juye tsiyarsa . Wanan sanyin zuciyar taki tayi yawa Dubu kima godewa Allah daya baki yayan da suka san zafin ki amma anyi mutum haka bai iyawa kansa katabus ? ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,, 2️⃣1️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Sallah nayi na kwanta saboda gajiya a dakin da anty Salma ta kaini don bamu ko zauna munyi wani hira da ita ba a lokacin saboda gajiya. Sallah la,asar ya tayar dani na falka kinsan hakan baiwane ga musulmai da zaran lokacin ibada yayi in barci kikeyi sai kin falka saidai shedan yayi kokarin rinjayanki ki koma barcin. Hakama idan idon ki biyu da zaran lokacin nan yayi sallah ce zata fado maki a rai musulmi na kwarai duk abinda yakeyi a rayuwa sallah tana a zuciyarshi hakan aka san musulmin kwarai dashi. Nima irin hakan yake kasancewa dani komai nauyi barci zan falka a daidai lokacin ko lokaci ya dan gwauta kadan in tashi in gaida ubangiji subbahanahu wata,alah. Bayan na idar da sallah ina zaune na jawo wanan karamin ledan da yaya ya miko min a hannuna lokacin da zan fita motan shi daya kawoni. Na fara budewa kudi yan dubu daya sabbi,fill dinsu duk daba nauyi kudi na sani ba a lokacin balle na kiyastasu nasan wanan yafi karfina a lokacin. Sai wasu sarkoki da bangus da yan kunne guda biyu bangus biyu masu kyau ga kudinsu nan a manne jikinsu ga yar takardan da akaiwa rubutu ja. Mamakine fal a fuskana na dalilin sayan kayan nan duk da nasan shi mutum mai alherine dama mutane na fadi ina ji uwarsu kuma ko yaushe tanawa abinta kirari wajen alheri kullum ina ji. Ban kara girgiza ba saidana mike da sauri na fara budan suran ledan gabana nafaduwa nake zaro dogayen riguna masu kyau da daukan hankali guda ukku ko wani da gyalensa a ledansa. Tsorone fal ya dira min a zuciyata mu fulani mukance alherin namiji gareka nuna alaman sone ko kauna sai wanda ka damu dashi kajin lamarinsaa zuciya kakewa alherin bajinta irin haka ? A take wani gefe ya gargadeni da ke wawiya wani so yaya Jafar nefa ina so zai shigo tsakanin ku kuma yadai nuna ke kanwarsace yasa ya saya minsu. Ko kuma don zancen da sukayi na cewa abinda matansa sukai min yake kokarin wanke min zuciya sai gashj nafi amincewa da wanan na karshen wanda kuma haka dinne ko a wajensa. Don yaya Jafar nauyi da kunyana ya dinga ji na abin daya faru yana sane kuma nima abin yayi matukar tabamin zuciya hakan yasa na tsame kaina ga lamarin kowa a gidan. Karshema sai gashi na yanke shawaran in dawo Abuja inzo inyi sallah wanda yaga sakacin dan uwansa Habu daya yarda nazo abuja din idan shine haka ya faru ba zai bari naje ko ina ba zai tsaya ya tura masu haushin abinda suka aikata wanda sai sunyi dasun sanin hakan da sukai min a lokacin. Koda muke tafe hanya yana da takaicin Saiba amma kuma yana sake saken ta yaya zai dan farauta min ba tare dana rikesu ba a zuciyana don cin fuska bai da dadi ga mutum irin haka balle ga yaro karami. Shine yana jin banda waya yaga rashin dacewan hakan gara ina da waya a hannuna aji halinda nake ciki a nan yayi shawaran saya min waya din sai ya ga wa yanan kayan kuma ya hado min dasu. Yarinyar ba laifi gaskiya tana da dadin zama ga tsabta ga ladabi ga hsanin ya kamata bata da hayaniya ko daukan magana duk abinda matansa keyi bai taba jin yaran sun tsaya sun mayar masu da martani ba koda agabansu akai abin. Hakan yasa yake ganin girma da kimar sarakuwar tashi da kanwata duban irin simple rayuwan yaran yakan burgeshi wallahi tundai tsabtansu da wanan yakewa matasa gori wanda sukuma suke kara jin kiyayyan yaran a zuciyarsu. Haka ya kama hanya bayan ya saukeni tare damamakin wani irin halakace tsakanina da mutanen nan haka ? Don da ganin gidan ba gidan karamin mutum bane dole akwai wata halaka mai girma a cikinsa koma meye ya godewa Allah da bai ajeni a wullakace ba. Gara da Allah ya bashi dubara danyi min sayayyan nan da yayi don a ganni a cikin mutuncina da kima ba zaiji dadi su ganni cikin irin suturan da habu ya barni ina sakawa duk dai da baisan daliliba amma dai babu wadatuwa gareni gaskiya. Yasan haka halin dan uwanshi yake tun suna kananunsu habu bai damu da wani rigimar duniya ba kan shima bai fitar da kanshi kunya balle wani. Wayanshi dake karane ya katseshi ya dauko yana duba dan uwan nasa da yake tunanene ya kirashi yana mashi ya hanya ? Alhamdullahi Habu na sauketa tun dazu na saya mata waya don ta rike don nace ta kira idan da matsala tace bata da waya a hannunta. Why habu zaka kasa saiwa yarinyar nan dan waya koda karamace da zata rika meyasa kake hakane wai ? Yaran nan kaika daukosu a karkashinka suke a gidan nan da anga kana darajasu da ba macen da zata nemi tozarta makasu a cikinsu. Bai kamata irin hakan na faruwa ba marayune fa Habu kasan yawan ladan da zaka samu a wanan taimakon da kayi gaskiya banji dadin hakan ba wallahi na dai saya mata da wasu kaya tunda banyi tsamanin ta samu dinkin wa yancan ba da zata saka. Shiru Habu yayi yana saurarenshi na dan lokaci saida ya kare magana yake fadin Nusaiba ta kira wayan kane ? Nusaiba wani abubya farune kuma dazun dai da zan fito tazo tana min rubbish akaina ban tsaya kulata ba don bata da hankali nake gani. Bata dashi kan akan ka dauki Rahama yau tashigo wajen su mama tayi tijara iya son ranta katse dan uwan yayi da fadin What ? For what reason zata samu mama to Salima dai bata kyaleta ba itama bata kyale salima din ba sunyi ba dadi a gaban mama wanan yasa na kasa hakkuri na kiraka . Irin wanan abin yana taba mutuncin mahaifiyar mu sosai don bata magana su kuma sunga ko sunyi ba mataki kake dauka ba yasa suke cigaba da hakan tundai ita Nusaiba din. Saiba saiba takai karshena wallahi amma bari laifin mama din ne dake hanani daukan mataki akansu kome sukayi mama tace inyi hakkuri haka mata suke basu da tunane komai girman su zankiraka habu ina zuwa don Allah ya fada a gagauce ya kashe wayan. Me wanan yarinyar take nufi danine wai yana neman layinta data kirashi danzun yana zancen zuci a fili ta dauka ni dan iskane irinta kome yaji ta dauki wayan cikin basarwa tana fadin hello J. Ke Nusaiba yanzun nan ki tafi gidan ku kada ki bari in dawo zaria yau in sameki idan ba haka ba wallahi saina katse duk igiyan dake tsakanina dake a yau din nan ya kashe wayansa yana huci bai jira cewanta ba. ABUJA Ina saka wayan a caji aka shigo na juyo yar aikin antyce wata yar budurwa mai guntun buje da ganin shigarta nagane ita din yar aikice agidan . Abinda basuyi muna ba ke nan a lokacin sam ba a gane cewa mu yan aikinsune kuma ta gargadi mama dake katobaran fadawa mutane hakan. Ranan da hjy taji tayi fada da mama sosai take fadin mu bamu daukeku a yan aiki ba a yan uwa muka daukeku kowa kuma yasan abinda nake fada ke nan don kun zama yan uwa a wajen mu yanzu. Tun wanab lokacin ummah bata sake wanan katobaran ba tana kafa kafa da abinda ke batawa hjy rai akai zama lafiya sosai a tsakanin mu. Wanan yasa na nasa a raina cewa yarinyar nan ta huta indai har anty Salma ta biyu halin hjy mama da yan aikinta zataji dadi sosai a wajensu. A falo na samu anty salma din tana waya alama tayi min da hannu inzo na karasa ta nuno min fuskan wayanta dake hannunta. Fuskan hjy mama a cikin massalaci zaune ga larabawa suna gittaiya mama kinga Ramaah kin yadda ta girma ta zama big girl yanzu. Mama ina wuni Ramaah ta lafiya lau ya kuke yaya yanda da jikinta yaya yan uwanku na amsa da Alhamdullahi. Ya ibada mama tace Alhamdullahi gamu a cikinta aini mamakin ganin yadda Ramaah ta girma nakeyi mama din ta katseta da fadin anyi sallah ki bari zan kira ku anjima. Ta kashe wayan tana fadin yau mama zataji dama ace tana garin nan ta ganki murmushi nayi ina dukar da kaina kasa. Take tambayana ya jikin Yanda da sauki ko babu dai wani matsala dai ko na amsa da taji sauki sosai lafiya na barta jiya muna asibiti tare a can na wuni dasu. Ta koma tambayana karatu nake fada mata nagama secondry school yanzu gaba zaki ko sai nayi murmushi ban bata amsa ba don banda abinda zan fada mata lokacin. Duk da nasan ana zancen zuwana gaba din amma ita ban fada mata komai ba tunda banda tabbaci akan hakan yanzu saidai abinda shawara ya yanke a kai. Tunda su Salima na karatu ni kuma yanzu rikona ya dawo hannun yaya Habu nasan yana da wuya ban je higher institution da nake son zuwa ba. Zamana gidan anty sallama a ranan ya tuna min abubuwa da dama a rayuwana wanda yasa jikina yayi sanyi don tuno da mahaifinmu da zaman Abuja da nayi. Zaria duk yadda Saiba taso ta kira mijin nata yaki daukan waya don yayi blocking dinta a lokacin karshema kashe wayan nasa yayi don mama ta fara kiranshi tana son taka mashi burki. Wanan karon yasha alwashin sai ya koyawa Saiba hankali sai ta gane ita ba kowa bace in ma rabuwace ai a rabu din ya gaji da wanan irin halin nata na rashin kwabo. Bata kara sanin da gaske bane saida ya Habu ya dawo yana fadin yace ta fita gidan kafin ya dawo har in ya dawo ya sameta gidan wallahi kowa yayi mata tsaye yau sai ya raba igiyar auresu ga baki daya. Iya najin hakan tace maza ki tatara ki nufi gidan ku kada kaddara ya zaunar dake yazo ya aikata abinda ya fada zaman ki gidan nan ya kare maki. Babu yadda ta iya don mama tayi shiru batace komai ba a wanan zancen hakan ya kara tunzurata ta shirya kayanta a cikin yar karamar jakka ta nufi kaduna. Ana magariba tana sauka gidansu cikin tashin hankali ba wanda yace mata komai don ta samu ana hada hadan shan ruwa a lokacin. Baya bata da kadan don ko tana fita ba,a jima ba ya iso gidan bai tsaya ba ya sauke abinda ya sayo a hanya ya nufi cikin gari don samun sallah a unguwarsu inda suke shan ruwa. Maigadi ya jido kayan zuwa part dinsa dana iyayyenshi iya take tambayan maigadi ina Jafaru ? Yace ya fita yanzun nan kayan kawai ya sauke ya juya ya fice daga gidan ba zai shigo ba ai tunda yasan abinda ya aikata uwar ta fada. Keko meya aikata kuma ba zancen ki bane asalima nasan saboda ke yaron nan yake son daukan mataki tunda kinji wayan da sukayi da dan uwasa don haka ki sa masu ido kawai yayi iko da iyalinshi. Yarinyar nan tana bukatan gyara a gaban mu tazo tana zagin yarinyar nan koke maisa ya dauki matakine kan abin nan data aikata ai. Shawaran Iyan mama tabi don koda Jafar din ya dawo batayi mashi zancen ba shiru tayi har ya gama hiranshi da iya ya nufi part dinshi. Takaicine ya kamashi yadda ya samu fslon nasu a ya mutse ga kujerun falon da basu dauki wani lokaci ba a gidan har sun fara ya mutsewa da auren Yanda ya sayo masu shi da akai gyaran gidan. Abin takaici ranan daya shiga falon Habu yaga nasu zakice ranan aka kawo masushi part din don komai ba suyi ba sai walkiya da sukeyi. Takaici ya kara kamashi haka ya taka zuwa dakinsa ga wani bashi dake tashi ba alaman ma tayi wani soye soye don shan ruwa a ranan. Yana gab da shiga dakinsane yaji muryanta a bayanshi tana fadin ai kadowone ashe na dauka ba yau zaka dawo ba ai naga Saiba ta tafi kaduna da yamman nan ? Bai tsaya bata amsa ba ya murda kofan dakin ya shiga ya rufo sai lokacin ya shaki kamshin dakin don ko yaushe shike tsayawa ya gyara abinsa yadda yake son ganinsa. Kayan jikinsa ya rage yashiga wanka yaso ya kwana a Abuja saidai saboda ya kure saiba ya dawo zaria a ranan tayi arziki daya dawo ya samu tabar gidan don daya shayar da ita mamakinsa a ranan. Why zata zargesa da irin wanan mumunan abin ta rasa wanda zataiwa sheri irin wanan saishi kuma ? Dashi dan iskane yadda take zato akanta zai fara nuna halinsa ai amma sai ya juya abin zuwa aure a tsakaninsu tabbas itace da farko ta fara nuna mashi so da kauna . Don tun bai gane ba har yazo ya fahinci me take nufi da farki yaso ya guje mata amma ta hillanceshi da dadadan kalmanta har yaji ya kamu da kaunanta itama saboda yadda take matukar bashi kulawa zakice ko itace matar nasa duk a lokacin ta fake ga besty dib Asmau take masa wanan. Tsoki yaja lokacin daya murda famfon ruwa ya kare hakan ya tabbatar mashi da ta kasa fita ta kunna ruwa ke nan a ranan . Dole yayi amfani da ruwan roban da suke tarawa acikin kyankyami saboda ruwan ya dade a rufi bayan ya fitone ya shirya kansa bai fito daga dakin ba nan ya zauna bakin gadonsa yana waya da wani mutumi da zasu hadu dashi a Onicha. Tashi yayi ya sakawa kofan key yana mai jin haushin matan nasa aransa a haka barci ya daukeshi don koda Asmau tazo tana murda kofan duk yayi barci a lokacin. Sai tsakar dare da yunwa ya tayar dashi irinta wanda ya wuni da azumi a cikinsa hakan yasa dole ya fito ya duba falo ko zai samu abincinsa aje sai dafa duka da ganye. Kitchen dinsu daya dade bai shiga ba ya nufa a can ma ya kwammace da bai shigo kitchen din ba a lokacin don kayan takaicin daya sama a kitchen din. Drinks ya dauko a fridge sai bread dashi yai sahur ya kwanta cike da takaicin duniya akan matan nasa. Idan kaga Asmau a zahiri zaka dauka mace ce mai tsabtan bala,i don iron yadda jikinta yake ashe abin ba hakana bane halittace kawai a hakan . Ita kuma saiba datayi mai dadin baki tana da dan dama saidai ba sosai ba ga kuma cin mutunci har na tsiya a bakinta. Abin yana daure mashi kai yadda mace tayi boko zata tsaya tana wanan kazantar haka sai wace batayi karatu an koya mata tsabta ba tafita. Da safe kuma asubanci yayi yabar garin zuwa Abuja inda ya shiga jirgin zuwa Rives don haka koda mahaifin Nusaiba ya nemeshi baya gari bai sameshi ba. Saarece wajen binciken ta ta dauko kayan nan da matan ya J suka dawo min dashi a cikin kayana tana nunawa mahaifiyarsu. Tana fadin wai mama kinsan yarinyar nan ashe bata dauki ko tsinke daga cikin kayan nan ta tafi dashi ba. Yanzun nan ina neman gyalena na gansu a kayan ta yadda aka bata haka ta ajesu a nan din bata dauki ko tsinke daga cikin kayan ba. Haba dai Saare yanzu bincike kikai mata a kayanta kema kinsan babu gyalen ki a kayan Ramaah wace take hada muna kayan mu itace zata daukar maki gyale kuma ? Mama yarinyar nan tana min katsalamdan a ciki zancena kwanan nan wallahi idan tana min hakan za a jimu da ita. A cikon takaici mama ta juyo tana fadi rufa min baki mara hankali ai gaskiya ta fada inba rashin wayau da tsegumi ba meya kaiki cikin kayan yarinyar nan yanzu don Allah. Wanan wani irin dabi,ace Saratu ina kula dake a gidan nan idan nabi ta naki yarinyar nan so kike ki hadani da yaran nan sam bansan meyasa kike haka a kansu ba. Haka yarinyar nan dake asibiti tun tana tambayana ke har tagaji ta kyale ta daina tambayanki kwata kwata a yanzu kinki zuwa ki gaida ita. In habu ya gane wana halin da kika tsiru nasan ba zaku kwashe dashi da dadi ba tsorona Allah a yanzu kada sunan ki ya fito cikin zancen yarinyar nan Nusaiba. Don ban tantama idan ba kece kika fada mata cewa yarinyar nan zatabi yayan ku ya sauketa a Abuja kika haddasa wanan fitinan a tsakanin su. Kallon uwar tayi tana fadin haba mama ni ina naga Nusaiba a ranan balle in fada mata ga Ramaah zatabi yaya idan ma kece ai ji zamuyi don Nusaiba fada zatayi kin sani. Wanan ai shashancine jafaru din ta zarga ko wanan yar komu ta dauka bamu san abinda mukeyi ba lamarin wanan yar yana ban mamaki ke kinyi kwancen mijin nan hannun kawarki kuma ki koma kina nuna kowa bakya son yai mu,amula dashi saboda me hakane wai ? Har kizo kina neman batawa mutane suna akan abinda bashi ba isan wani yaji wanan shirmen ai zancen zai juya wani abu daban kuma ? Iya na sauke zancen mama ta dauka da ai yanzu tagani nafi da son ya gani ko yaji ya dauki mataki da kansa kada ace na zubawa yara ido na hanashi zaman lafiya da iyalinsa amma yanzu ai zata gane uwa nake ga jafar. Tsuki iya taja tana fadin yaushe kuma ai tun za a ake shiri ba sai anje ba kin rigada kinyi kuskure tun farko ya kamata ki nuna ke uwace agaresu . Amma haka kike shaye duk wani wullakanci akan yaran nan kuma ki hana mijinsu ya dauki mataki akai waike kada a zargeki. Yo an dade ba a zarga din ba da wanan halin da yaran nan suke sakaki ciki a kullum wana karon dake dasu kunkai yaron nan makura don haka ki barshi ya dauki matakinsa ido kawai zaki zuba masu tundama baison zancen dake iyace tasa mama a gaba cikin fada ganin yadda ta daga hankali wai ga sallah ya gabato ga azumi ya tura yarinya gidansu. Abuja Rayuwan gidan anty sallama rayuwace ta turai tsantsanta don sai ankai karfe dayan rana kowa na dakinsa kwance ba a fito ba. Sai hakan ya zama min bakon al,amari a wajena don saboda wahala da jikina ya saba dashi na ba hutu gareni da zaran karfe hudun asuba ya buga. Don hakane a bangarena ba barcin na koma ba don ban saba da hakan ba idona biyu ina dai kwance ina faman tunanen duniya. Hakan yasa na jawo wayan nan na kunna ina shige shige a cikinsa har na fara gane kan wayan don ban san kan waya ba a lokacin gaskiya. Ban kuma damu da insani din ba don waya bai gabana a lokacin tunda nasan ba zan mallaki waya a lokacin ba kila sai gaba kamar yadda anty Yanda tasamu sanadiyar yaya Habu. Amma sai gashi nice da wanan wayan dake hannuna da yazo min a bazata wayan da kana kallonsa kasan babban wayace ba karamar waya bace bakace wulk da ita. Taba can tabo nan har na gano abubuwa da dama game da wayan na shagala sosai a lokacin har anty sallama ta shigo dakin bansan lokaci yayi ba na yarda da wasu ke fadan waya kanin shedan . Tabbas haka yake don ko sai gashi ya mantar dani duk wani irin damuwan dake zuciyana lokaci guda har na shagala da dakilanshi. Ramaah aina zata har yanzu barci kikeyi muryan anty salma naji a tsakiyan dakin har ta karaso bakin gadon da nake kwance rub da ciki. Na dago ina aje wayan tare da gaida ita da kwana duk da wunine lokacin ba kwana ba amma tunda ban gaida ita da safe ba dole na kira hakan da kwana. Lafiya Ramaah ta fada tana zama tare da tambayana i hope ba matsalan komai dai nace a,a anty. In kina da matsala fa kiyi magana flee free don Allah nan gidankine fa idan kina da damuwa ki fada kawai nasani ? A,a ba komai tace Ok akwai wasu perfume na dade da sayan su da kayan kwalliya ban amfani dasu ina maji har na aurena akwai a ciki idan kin fito sai ki duba ki zabi iya yadda kike so kiyi amfani dashi. Kinsan ni nafi son naga mutun so clasic ba irin yadda kika koma din nan ba anyi mace haka duk da azumine babu dan gyaran jiki haka Ramaah ? Ki gyara jikinki tsab ki saba da hakan ko har kin manta da tarbiyan mamace wai kinsan mama fa idan taji baka kamshi ko falonta baka shiga mata. Dariya na danyi ina fadin komai na rayuwan mu a baya ban manta dashi ba anty saidai a can gida rayuwa ta juya muna baya. Mun koma damu da bayi bamu da bambamci a idon yan uwan mu nan dai nashiga bata labarin rayuwan da mukayi a wajen baffan mu har zuwa lokacin da Yanda suka hadu da mijinta. Kafin muka samu yanci daga kangin bautan baffan mu da iyalinsa da mukeyi muka dan murje a yanzu. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,, 2️⃣2️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Sai daren sallah ya J ya dawo zaria don haka Habune ya gudanar da duk wani shirin sallah a gidan kamar yadda al,ada yake ga musulmin bahaushe. Part din iyayyensu dana yayanshi komai ya tanada musu a nan da daren kuma ya dauki mama ya mayar babban gida inda tace dakin mijinta zatayi sallah tare da yan uwanta. A can ma suyi hidima sosai daga sutura kudin cefane shimkafa dasu mai duk Habu yakai masu kowa nason samun albarka duk da karfin abin Jafar ya turo da kudn yi amma ya dora da nasa don samun akbarka. Nama kuwa a can aka kada shanaye biyu kamar yadda mahaifinsu keyi a baya shida mutanen unguwa a hada a saye a raba ko idan kana da hali ka yanka kai daya ka bawa wa,yanda Allah yaci dasu rabonka. Suma wanan karon dai sunyi hakan shanu daya nasu da babban gida daya kuma mutanen unguwa da yan uwansu masu aure aka yayyana sai albarka ake saka masu da fatan gamawa lafiya, Allah yasa mu dace Allahuma amin. Duk,da da dare mama dubu ta dawo bayan shan,ruwa hakan bai hana mutane suji dawowanta ba suka dinga shigowa masu godiya nayi masu yan koken abinda zasuci ta bude shimkafanta aka dinga diban mata don yanzu Nafisa idan mama bata nan itace ke zama a part dinta don haka koda ta dawo bata koma wajen uwarta ba nan mama din tace su zauna tare da ita. Saiga Jafar ya shigo wanda dawowanshi ke nan ya dai shiga gida sun gaisa da iya da matarshi Asmau daya samesu a waje da wasu mata da iya biyu da iya tasa aka dauko daga unguwarsu su taimaka masu da aikin gida dan aikin yayi yawa. A ranan Ramaah tasha ambata a bakinsu saidai ba Ramaah don tana can inda aka san darajanta wurin da ko kamshin aikon da akeyi bana ji saidai a debo anunawa matar gidan ko yayi idan bata nan kuma nice zasu tambaya ko yayi ? Tunda ya shigo ya zube saman kujera ya dafe goahinsa da hannunsa daya uwarta dubeshi tana fadin lafiya kake kuwa Jafar ? Saida ya nisa ya sauke hannu ya dubeta da idanuwansa da sukai ja jajir yake cewa uwar kansa ke masa wani irin ciwo wani irin ciwon kai da bai taba jiba yakeji da kyat ya iso Zaria yan,zuma dayasha ruwa saida ya hade magani ya samu fitowa. Allah ya sauwaka uwar tayi mai kafin ta dora da fadin aidole kayi ciwo Jafar tunda baka hutu ga azumi ga yawan tafiye tafiyen da kukeyi ga rana da zafi. Cikin karfin hali ya murmusa yana fadin dolene mama idan ka zauna sai a cuceka ai tafiyan da sauki tunda da jirgi nakeyi bada mota ba. Sallama akai mai ya fita wanan yasa bai dawo ba ya wuce zuwa gida da kyat yakai gida zuwa dakin shi cikin dare ya kira dan uwansa Habu da waya dole sukaje asibiti dashi a daren. Allurai akai mai da magani masu karfi aka bashi suka dawo gida don zaiyi barci sosai akace idan yasha maganin . Ba wani barcin ya samu ba amma ya danji sauki sosai zuwa safe haka yai karfin halin zuwa sallah idi a dadafe ya dawo gida ya kwanta. A kullum isan sunje sallah a ka,ida zasu wuto gidansune direct su gaida iyayyensu da makwabta da ake zaman arziki da iyayye tare da sauran yan unguwa. Wanan sallah rashin ganinsa yasa ake tambaya anan mutane suke jin baijin dadin jikinsa abokansa suka fara tururuwan zuwa gaidashi harma da manya. Mama dubu sunzo da abokan zaman ta da Habu ya kwasosu sunzo gaidashi suga yanayin jikin nasa suka sameshi a falo zaune inda abokansa suka barshi. Suka shiga yi mashi sannu da jiki basu jima ba don sallahne aka mai dasu gida har mama din don tabar Nafisa tana mata aiki a gida. Zuwa yamma kuma saiga Habu ya kirata yana sheda mata zasu koma asibiti da zafar don kan nasa ya matsa da ciwo. Sai lokacin hankalin mama dubu din ya soma tashi da zancen ta fahinci wanan abin ba karamin abu bane ke nan tunda za a koma asibiti kuma again . Da zatazo Nafisa ta boyota suka zo tare don asibiti suka nufa suma a lokacin suka samesu a can kai dai yake fadi yana mashi ciwo sai dafe kan yakeyi yana juye juye cikin damuwa da yadda yake jin wani irin azaban ciwo . Tun safe da nayi wanka na bude ledan kayan da aka sayo min din ina duba wani zan saka a jikina cikin jallabiyan dana ya saya min din. Don bandasu banda wasu sabbin kayan da zan saka a jikina lokacin inyi fitan sallah dasu na azo agani haka masu kyau gashi zamu tafi sallah idi gidan. Tsab kayan suka karbi jikina simple makeup nayiwa fuskana nayi rolling din gyalena ka,idan anty Salma nabi da take fadin idan zan fita na gyale kawai zan sakawa dan kamshi mai taushi yadda ba kowane zaiji ba sai idan nabar wajen za a iya gane hakan. Ire iren roll on oud din data ban na murza na koma gaban madubi ina kallon kaina a cikinsa ni kaina a ranan nasan na fito diya mace sak dani. Kila rabona da tsayawa inyi kwaliya irin hakan tun ina karama a gidan daddy da anty salma da hjy suke tasa mu a gaba dole muyi gyara. Don acewarsu ba a ganinsu fes a samemu a kazance cikinsu don dole ake gyaran mu fes a lokacin a gaskiya wasu mutane tun a duniya kake sanin su din na dabanne . Don wallahi nidai ba zan iya ko kwatanta alherinsu gareni ba tsakani da Allah bansan ta ina zan soma fada ba gaskiya saidai haka a ciki labari na dinga tsankwaro alherinsu garemu. Rita yar aikin antyce tazo kirana wai idan na shiriya in fito inji anty din nace gani tafe muka fita tare da ita na jawo kofata muka fice a dakin. Falo na samesu zaune harda mijinta da yaransu biyu ko wanin su yasha kwaliyansa gwanin ban sha,awa dasu sai photuna sukewa kansu . Gaida mijin nayi wanda anty salma tafishi hausa sosai a bakinta yake fada cikin hausan da bakuwar fulani kina gidan nan yau nake tambayan anty ki ai? Akwai wasan barebari da fulani shi yakan so ya zolayeni da hakan amma ban saba da in sake da mutum haka inta zuba ba saidai inyi murmushi kawai in soke kai. Na fita daban a cikinsu donsu bakakene sosai ni kuma din bafulatana don haka da gani ba sai an tambaya ba za a gane ba hadin kifi da kaska. Bamu jima ba muka fito shi ya dauki dan nasu babba na dauki karamin muka nufi wajen motanshi kusan kowane a gidan za a tafi mota biyu nagani a jere don haka aka bar mutum biyu sune basa sallah ta musulunci a ciki mu. Mota daya muka shiga dasu ni ina baya da yara su kuma suna gaba zuwa idin da baida nisa sosai mun samu an kusa tayar da sallah don haka bamu waji nima ba aka tayar da sallah. An sauko lafiya muka nufi mota aka dawo gida sai lokacin akewa juna barka da sallah gwanin ban sha,awa kudi masu yawa mijinta ya bawa kowa na gidan sai ince nawa yafi nakowa yawa a cikin mu har wa yanda basu sallah su Rita an basu goron sallah a ranan kuma ya wuce maiduguri wajen iyalansa nacan. Don ita tana tare da mahaifiyarshi bata zama a abuja sai maiduguri din a yadda anty salma ke fada min bayan wucewansa take fadin shine dalilin aurensu don ita ta zauna a nan Abuja kuma zaman nasu gaskiya akwai sauki sosai don kusan dukkansu yan uwane dama. Abincine na alfarma muka zauna akaci kafin dan wanan jigilan kowa ya nemi wajen hutawa don sun fita zata saukeshi a airport saina koma dakina na kwanta. A ranan na gwada amfani da wayana wajen kira layin nan na cikin wayan da bantaba kiran kowa a cikinsu ba na danna na salima yayi ringing gab da tsunkewa ta daga tana sallama tare da tambayan waye ? Nice Ramaah na bata amsa daga bangarena sai naji tace a,a Ramaah yau an tuna damu dadin abuja ya hana ki kira ko koda yake nasan ba waya a hannunkima. Dan dariya nayi nace abuja akwai dadi gaskiya anty salima na tambayeta kowa nagidan tace duk suna lafiya saidai ya J ne ya dawo jiya ba lafiya amma da sauki. Nayi Allah ya sauka nace ta gaida kowa ta amsa da insha Allahu zasuji muka kashe wayan yar uwata na kira muka gaisa na tambayeta jikinta tace da sauki ta ban ummah mun dade muna hira ina bata labarin anty salma din. Bayan mun gama waya nace Yanda ta turo min number ya habu in gaidashi da sallah ba a jima ba kuwa ta turo min muka gaisa a yadda naji muryanshi kamar yana busy a lokacin . Zan kashe naji yana fadin nagode Rahama gamu nan mun dawo asibiti ne da J da baida lafiya idan na shiga wajen Maria zan kiraki ku gaisa naji ya kashe wayan nasa dip. Tun lokacin nima naji hankalina ya tashi kuma lokacin sallah azahar nayi sallah na kwanta sai barci sai gashi ina mafalki da baffa. A wajena gaskiya mafalki baffa bai zama alheri a wajena don baffa ya tsaya min a rain har ya zamo shine singn of bad luck dina. Idan wani abu zai faru da na kusa dani ko wanda nasani zanyi mafalki baba yana aikata mugun abinsa to kwana biyu sai wani abu ya faru da wani na kusa dani ko wanda na sani. Baffa mugun bafulatanin dajine ba arabi ba boko sai duhun kai da yake amfani dashi dip yake baida imani ko na miskara a rayuwansa . Inda na shamaceshi kuma sai yafi ji dani saboda zafin namana don haka lokacin zaman mu wurinsa nice mai masa dake dake da kula da wasu kayansa na tsubbu da tarkacen tsafinsa Dage dansa daya biyo halinsa wajen mugunta. Shine kan nuna min aikin da sake sakin da nake dakawa baffa amfaninsu da aibunsu don yana bashi siri sosai kamar shine maganijisa dai zance. Don haka nima da zanyi amfani dasu da zan iya ba wani taimako akan hakan saidai ba wanan a gabana don na dauki hakan da tsubu shirka sukeyi a wajena. Tashi nayi na kasa komawa barcin ina faman tunanen wa kuma wani bala,in zai sama inda nakai raina shine yanda don itace a asibiti don haka hankalina ya kara tashi sosai da mafalkin. Bayan nayi sallah la,asar na fito falo anty salma na dakinta barci tayi tun bayan dawowanta sauke daddyn Imran ta kwanta. Sai wajajen biyar ta fito daga daki har lokacin ina zaune a falonsu ni daya da wayata a hannu ina game. Muryan ta naji a kaina tana fadin tsiyan abuja ke nan fa ranan sallah ba wani gurin da mutum zai fita yawo saidai kaje park da sauran wajajen yara saiko gidan yan uwa da abokai. Na dago ina gaida ita da fitowa wanan dabi,an gidansune muka gada ko wanka mutum ya fito sai angaidashi da fitowa . Zama tayi tana fadin wai Ramaah kinsan wanan rigar taki mai bala,in tsadane kuwa kwanaki nayi ta neman irinsa in saya ban samu ba sai gashi na gani a jikin ki. Murmushi nayi ina fadin yaya J ya saya min da zamu zo saboda ban samu dinkin sallah naba aiko wallahi yayi maki kokari sosai rigan nan yakai seventy fa Ramah gaskiya guy din yayi kokari. Anan muke dan hiransu jefi jefi har nake bata labarin yadda zaman mu yake gidan da yadda matansa suka tasamu a gaba da nuna kiyayya har yadda sukai mun kafin inzo Abuja da dalilin dayasa mijin nasu ya saya min kayan. Mesuke nufi dayin hakan nace sunce kamar ni zai sayawa lace mai tsada hakana matsayina baikai hakan ba. Don ya saya masu abu su da kannesa zai saya min ai rikona akeyi a gidan in gaskiyane Habu ya saya min mana ai dalilishi nazo gidan. Kaji jahilai zasu batawa mata tsarin diyanta idan mijin maria ya saya maki ai zaiga kamar ya shiga gaban dan uwansane tunda kansu a hade yake yadda na fahinta. Kin mun daidai wallahi laifin uwarsu bagani a nan don itace ya kamata ta fara magana ba wanan salima din ba gashi ai yanzu ya saya maki wanda kila yafi wanda suke fada a kanshi din. Kishine fa kada ki dada kishine irin namu na mata kawai suka dora akanku ku fita zancen su kawai yan iskane. Ni dai abu daya zan fada shine kada ki yarda ai maki aure bakije gaba kin kara karatu ba idan maria batayi ba ke zaki kara gaba din insha Allahu tunda kun fito wajen wanab mugun mutumin. Ai wasu yan yankin kune suka fadawa daddy lokacin yafita zancen ku don mutumin nan na iya halakshi da asiri wana yasa daddu ya bar zancen ya barku can zube a hannunsa amma idan bashi ba daddy yaso dawo daku hannunsa nan. To an fada mashi shine ya kama kurwan baba fillo shiya kasheshi don haka daddy ya barku ko ba mutuwa wahala ai baida dadi Ramaah. Mun dauko hiran baffa sosai a wajen har nake tunane kodai wanan hiran nasa da zamuyine yasa nayi mafalkinsa a ranan. A Zaria kuma abu ya koma tashin hankali sosai don ya J yana cikin wani hali ba barci ba zama sai kugi da yakeyi anyi mai allura amma a banza. Dole kawu yaje wani waje dama yan zaria badaga nan ba shirya suke da unguwa na malamai don akwai kasuwa a irin hakan . A wanan wajen ya karbo wani hayaki akai mashi shine har ya samu ya dan ci abinci da barci yayi ya kafin hankali ya kwanta amma a asibitin suka kwana dashi. Washe garima jikin da sauki saidai wajajen rana kuma lamarin ya kara dawowa sosai sai kugi yake yana kiran wai shi kansa zai mutu babban mutum yana raki yana kiran sunan Allah. Hankalin mutane ya kara tashi sosai kawu dauda ya shiga nan ya fada can kowa da kalan nasa aka samu ya samu dan sauki kawu yace a basu sallama tunda ba abin asibiti bane. Lokacin hankalin mama Dubu ya tashi sosai a wanan dawowan gidan dole Nusaiba ta dawo dakin ta ba shiri saidai basu ga maciji da Salima da take ganin itace ta sanar da dan uwanta fadan su har ya dauki mataki haka akanta. Salima bata damu ba itama shere Saiban tayi tunda ta fahinci me take nufi a kanta nan gida sukai ta magani har ya dan samu sauki ya daina buga kan nasa da yakeyi yana fadin ciwo kamar a cire mashi kan ya huta yake ji. Sai daga baya bayan munyi waya da salima data kirani take ban labarin irin halin da suke ciki na tashin hankali kan jafar din inda ta kare zancen da fadin amma yanzu abinda sauki yauma ya fita sallah jumma,a ya dawo. Sai banji dadin hakan ba ko banza ance ka damu da wanda ya damu dakai akace sai naji na damu da jin hakan hankalina ya koma Zaria din tunda a karkashinsu nake kuma ni banganin laifinsu akaina. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,, 2️⃣3️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Satina biyu Abuja na dawo a cikin mutunci tare da goma hataran arziki da mama da anty salma suka hadoni dashi. Nida naje da jakka daya karami sai gashi na dawo da jakkuna maya har biyu makil da kaya na mutunci da alfarma ire iren kayan anty Salma da sakawa daya wasuma ko sakawa batayi ba wai angama yayinsu a wajenta. A part din Iya na sauka don part din mu yana rufe sun nuna farin cikinsu da dawowana musan,man iya daketa fadin yar nan muji kewanki sosai a gidan nan . Gamu gida ya koma muna wani iri sai kace taron tsofi ba don zuwan Iyatu gidan nan ba aida bola ya rufemu tas don babu wanda yake iya gyaran gidan nan yanzu. Iyatu na samu tazo ta wuni min idan zata koma na hadata da abinci da kudin mota a raina nace yanzu ko ga boyanku ta dawo bako zan hana iyatun nan cin abincinta ba gaskiya. Saare ce tana shigowa ta ganin zaune gaban mama sai tarin kayana dake tsakiyan falon turus taja ta tsaya tana mamakina budan bakinta sai cewa tayi wai Ramaah ce haka ? Wanan da kinkai wata daya aiba zamu ganeki ba ke nan kin koma wata wise haka lokaci guda haba dai kamar wace aka saka ga injin . Gaida ita nayi ta amsa tana zama lokacin kuma naji mama dana hango damuwa a fuskanta tana tambaya yaya ya samu harci kuwa ? Wallahi mama baiyi barci ba yana nan dai kwance nasan ciwon ya lafa mashine amma ba barci a indonsa fuskan kowan mu tausayi ya nuna mukai mashi fatan samun sauki. Dagawa nayi na fara jidan kayana ina kaiwa dakin kwanan mu lokacin naji saaratu na fadin wai mu hudu kenan zamu zauna daki guda yanzu ? Ta sauka a dakina kafin yar uwarta ta dawo mana iya ta fadi hakan ba karin digo Saare ke fadan waiki kai kayan ki dakin iya mu ukune yanzu a dakin anty nafisa tana nan tare damu. Jin hakan yasa na juyo cikin mamaki tace dakin iya zaki kai wanan shirgin naki da kika kwaso ku kara cikin nata naji mama ta dan dubeta cikin damuwa tana fadin banson iya shege Saare. Kikai kayan naki dakin iya ku zauna tare dakin kunyi yawa yanzu nafisa na nan tare damu saboda ciwon yayan ku. Dakin iyan na nufa da kayan nawa ba laifi dakon don a gyare yake tas nasan wanan iyatun dake zuwa yanzu ke gyaranshi amma dai akwai shirgi a cikinsa yadda saare ta fada a gefe daya na tara kayan ban fito ba nashiga bayi donyin alwala saida na tsaya na tsabtace shi na samu nayi amfani dashi nafito na tayar da sallah. Kodana gama na fito ban samu su mama da iyan ba suna wajen dan nasu dake fama da jikinshi a lokacin. Tare da Salima da Nafisa muka shiga part din don gaida dan uwan nasu a can muka samu iya tare dashi suna magana matansa duk suna zaune da yaransu daga mai waya sai wace ke shan wani abu acup. Gaidasu nayi na isa wurinshi ina gaidashi tare da mai sannu da jiki ya dago ya kalleni cikin karfin hali ya soma fadin kin dawo ke nan ya kika barsu can ? Lafiya kalau yaya ya karfin jiki kuma gabana saida ya fadi don yadda ya dago kai mukayi arba dashi wurin ramin idonsa yayi wani iri na ban tsoro. Bansan lokacin dana kai gurfane ba gabana yana faduwa a yadda ya kalloni ya rame wajen idanunsa sunyi wani baki saboda azaban wahalan da yake sha a lokacin. Ba zakice yaya jafar bane wanan dan gayen dana tafi na bari a cikin lafiyan shi ko ince wanda ya kaini abuja sati biyu da suka wuce da kafansa ba. Sai ki rantse da Allah wanan din ya jima yana ciwo a kwance ba Jafar bane ya koma haka a cikin sati biyun sannu yaya ashe jiki kuma ba dadi haka ? Hannunsa yakai a kai yana dafe goshin tare da fadin da sauki a wahalce bansan hawaye suna zubo min ba saida naji Salima na fadin aiki bar kuka Ramaah jikin da sauki sosai yanzu ai Ramaah. Nidai zance har muka bar part din bawan Allah nan baya cikin hankalinshi saidai idan an mashi sannu ya amsa da kai koda hannu baiko iya magana. Gashi kuma suna fadin wai ai hakan da sauki sosai don dai shi musulmi da dangana aka,sanshi ko wani lokacin bayan hakan baga ta inda saukin yake ba. Allah sarki kallo daya zakiwa Mama da yaya Habu kiga tashin hankali karara a fuskokinsu yanayin gaba daya nasu ba dadi a yadda salima ke fada min yaya Habu da kawu dauda suna hanya ko yaushe cikin tashin hankali wajen malamai. Kai duniya ina zaki damu mutum kamar yaya J mai alheri da mutunci ga duk wanda ya sani yau kuma shine aka jeraba da wanan lamarin . Sunce anje asibiti har angaji ana cewa ba aga komai ba amma za,aje sakoto ko ibadan a aunashi don suna zargi a kwakwalwanshi abin yake inji likitawa. Ranan monday zasu tafi talata ake awon yasa zasu isa tun monday din don suje ayi booking kamar yadda aka shawarcesu. Nisawa nayi daga inda nake zaune a hankali na furta wanan ba juttoro bane a yarenmu ban zata wani zai jini ba lokacin. Sai naji Nafisa tana fadim meye juma juttoro Ramaah ? Nace a,a magauta nake nufi da hausa magauta kuma ni ai kin kara jefani a kwana Ramaah ? Kukan dai yaran yanzu baku san hausa ba magauta masu bin duduniyar ka take nufi koda ance hakan ne ai ba a mussawa iya ta fada. Iya idan hakane nima dai bance a,a ba don ko a cikin gidan mu kullum a cikin hassadan su yaya ake duk da alherin da suke aikowa ana karbewa kuma ayi lalura dashi. Amma da an bada baya zagine ba godiya ba yake biyo baya a zagi mama a zagesu ana binsu da sheri ni yanzu na hana inna shiga tare fadan suje suyi tayi donsu ke komawa baya a kullum Nafisa ke fadan hakan. Abinda nake fadawa dubu ke nan kullum amma tasa kada ta toshe kunnen yaran da suka taso tun suna kananu ake binsu da sheri meye ba za a iya yanzu akansu ba Allah dai ya kyauta kawai za ace. Kin dauka don dadi ake shan tsamiya akwai dafa,in sanmu a cikinsa idan kana amfani dashi lokaci lokaci yana da wuya wani abu ya samu jikinka. Hirana da Dage dan baffa da nake tambayansa a wurin kiwo maiye amfanin tsamiyane wai da mutane suke ta dibansa suna kaiwa birni ? Washegari ganin yadda mama tayi laushi da yawa yasa na shiga kitchen don na dama mata kunun tsamiya a hautsane na samu kitchen din komai ya barkace a cikinsa saida kyat na gano ledan tsamiyan na dauko na wanke na jika. Har na gama damawa suna zaune da kawu dauda suna magana na hado cups biyu na fito falon dashi na aje gabanta ina fadin mama kunun tsamiyane na dama ko zaki iya shansa. Allah dai yai maki albarka Rahama yau kusan kwana nawa ina son in tsaya indama na kasa samun sukunin hakan. Naji kawu shima yana fadin a zaba min na dansha don Allah ai abin marmarine saidai kunun da zafi hakan yasa tace don Allah in biyota dashi part din Jafar kila shima a samu yasha kunun. Ban fita ba saida na zubawa iya na dauraye kayan na fita na hango wanan matar iyatu tana faman sharan tsakar gidan ga girma ga shekaru ina zata iya tsayawa tayi yadda nake masa tsab. Nikan na fito na nufi wajen ya J da kunun don bata kusa dani balle in gaida ita ina saka kafa ina jin muryan saiba na fadin don ina kin rigani shigowa zaisa aje dake idan na shiga motar gobe kisa in fito. Saiba na fada maki idan banje ba kema babu inda zaki gidan mu zauna gaba dayan mu a gida don ba fina kikayi ba da za a tafi dake a barni. Wai menene haka don Allah har mijin ku yana kwance ba zakuyi ladab ku natsu ku komawa Allah ba sai yaushe zaku girmane wai don Allah ? Mamace ta leko daga dakin ita da kawu jin hayaniyan da sukeyi falo wai ashe cewa kawu yayi mutum daya daga cikinsu ta shirya gobe aje sokoto da ita sai Asmau tace ita zata wanan yakawo masu hayaniyar a tsakaninsu. Ni dai ina tsaye saida kawu yace shigo muna dashi nan kinji yar nan wanan ne kuma karo na farko dana taka zuwa dakin part din shi maigidan nasu. Yana kwance shida wani abokinsa dake zaune saman kujera na gaidashi ya amsa ba tare daya dago kai ba na aje kawu ke fadin a dan zubama kunun tsamiyane ta damawa dubu ko zata gyara bakinta a zubane kasha Jafar ? Sai lokacin ya sauke hannunsa daya dafe kai yana fadin a zubo kadan kawu kawu ya dan kalloni yana fadin zuba masa ko Allah zaisa ya yasha din. Yana da zafi kunun don haka na tsaya na dan huhuta masa na mike zuwa wajensa ina fadin yaya ga kunun da kyat ya sauke hannunsa yana kokarin karban kofin faga hannuna. Abokin nasa ya taso da sauri ya karba yana bashi yake kurba a hankali yayin da nida kawu muka zuba masu idanu sai ya shanye tas ikon Allah Allah dai yasa ya zaunama a ciki. Amin amin abokin ya fada na fito da cup din na dauraye wanda aka kwana dashi cikin wani hali sai gashi ya fara karyo zufa a jikinsa. Mama dake shigowa ita da iya da suka gama rabon fada take fadin ikon Allah meya faru yake zufa hakane ? Kunun nan da yarinyar nan ta dama aka zubaf mashi shine yasha yake wanan zufan haka Allah dai yasa ya zauna mai a cikinsa. Na dawo da kofin dana daurayo yayi yunkurin amai suna fadin subbahanallahi aman dai yana nan ke nan sai ya koma ya kwanta ya daina yunkurin da yakeyi da farkon na aman. Sannu a hankali yayi lamo a yadda ya dan kwanta din ganin haka nikan na fice daga wajensu babu kowa cikin matan nasa duk suna dakinsu a lokacin. Na samu yan matan mama sun tashi suna falo zaune su ukkun don yanzu zaman nafisa an karu a gidan ban dauki komai ba nake gayar dasu da kwana suka amsa min. Aina zata kina kwancene har yanzu nace a,a kunu na damawa mama nakai mata part din yaya J wai meya hadasu fada da safe haka ? Wallahi ban sani ba na fada Saarece ke tambayana sai naji tayi tsuki tana fadin ni wallahi halinsu ya fara fita min rai mutane kamar awakai sai surutu tsiya haka abu ba abu ba fada. Mutanen kine ai kunfi kusa gashi tun dawowan Saiba ta dora gaba dani don kawai na fadi gaskiya akan me zamu zauna kamar muna tsoronsu kullum. Ban fahinci zancen ta ba na danyi yan mintuna naji tanawa anty Nafisa bayani akan abinda ya hadasu fada ita din wanda nayi mamaki kwarai jin cewa akaina ake wanan abin. Bafulace da rikon gaba a take naji gaba daya na tsani wanan Saiba din don haka na mike ban karasa jin sauran maganganun da sukeyu ba na shige dakin iya na kwanta. Barci nayi don ba aikin da zanyi sai bayan azahar mama ta shigo tana tambayana daga dakin na amsa mata take fadin to yayan ku yace a kara dama masa irin kunun dazun din nan. Ai mama da zamu samu ganyen tsamiya fresh muyi amfani dashi da zaifi jin dadinsa sosai ace wanan garin kuma sabon dakane zaifi jin dadin shansa. Ni dubu Rahama yanzu ina zamu samu ganyen tsamiya a garin nan tsamiya da mutane kejin wahalan dibansa . Sai abin ya ban mamaki na tareta da fadin tsoro kuma mama niko hawa nake na debo to ai kuma kamar mutanen boye kuke Rahama in bashi ba yaya za ayi ku kwana dokan daji ku kadai. Kodana dama nakai yana zaune saman gado ya hade kai da gwiwa jikinsa saye da singlet fari na maza mai yan hannuwa iya damtse. Na samu matan tare dashi da iya na shigo dashi ina gaidasu na aje a gaban Asmau na fita ya kallota yana fadin ta zuba mai tana zubawa ta mika mashi ya bita da kallon mamaki kafin yace cikin karfin hali ba zaki iya fifita min ba ? Na dauka da zafi kake son shi ai ta fada tana mayar da kunun gefenta tama rasa yadda zata fifita kunun saida iya ta fada mata yadda zatayi. Yana sha yayi gyatsa ya koma ya mike zuwa falo saman dogon kujera hakan yasa suka fito daga dakin iya dai na zaune don mama sun fita da kawu a lokacin. Ganin basu da niyar gyara mashi dakin yasa yace da Asmau sai magariba ba a gyara min dakin ba ko ? Washegari dai suka tafi sokoto don yafi masu kusa jikin kuma gaskiya da dan dama sosai ya habu da kawu da mama suka tafi dashi sokoto din. Matansa an barsu a gida ba aje da kowa ba saboda fitinan da suka soma na wace zata yasa mama ta tafi ita aka barsu a gida. Asibitin sunyi aune aunensu basu gano komai a cikin kan nasa ba komai nasa yana normal hakan yasa dole washegari suka nufo gida. Nikan da yamma ina gyaran dakin iya da duk na gyara tulin komatsen dakin irin na tsofi ina wayan mopping dinsa lokaci lokaci sai dakin ya canza ma,ana a yanzu . Muryan Anty Nafisa naji tana fadin su mama sun dawo fa hakan yasa muka fito gaba dayan mu zuwa taron su yanayin mama kawai zaisa ki fahinci tana cikin tashin hankali lokacin. Gaba daya muka nufi part din ya J wanda yaya Habu ya rike mashi hannu zuwa cikin part din a hankali suke tafiya dashi a falo aka zauna. Kallo daya yaiwa part din ya kau da kai idan ba karya zai fada ba yana ganin tun tafiyansu ba a share falon nan ba. Duk da yana cikin halin ciwo tsabtan nan nasa yana nan mashi har yanzu gashi kuma Allah ya hadashi da kazaman mata a rayuwanshi. Wanan dawowan kan sun bazama wajen neman magani sosai idan kinga ya habu ya fita yacinsa sosai a yanzu don tashin hankalin da suke fuskanta na dan uwansa. Nikan sosai na mayar da hankalina wajen yar uwata da mahaifiyata zanyi girki a part dinsu in kwashe in kai masu sai iya da nake zubawa don mama ba zama takeyi ba. Wanan yasa koya kira yaji lafiyan matarshi take fada mai komai ina kawowa basai ya damu ba Allah yaba yaya J lafiya. Don sun kwasa sun tafi wani gari dashi a cikin Niger state nima kuma akwai kudi a wajena wanda shi ya J ya ban daya kaini Abuja. Ga kuma wanda mijin anty salma ya banda sallah da zan kuma dawo hakane ya kara ban kudi masu tsoka gidan daddy ma haka donshi banda wani matsala da kowa yanzu gidan balle in tsaya ina rabe rabe. Dakinsu kuma ban shiga ba tun wanan koran wullakancin da Saare tayi min na kora da hali abu daya shine na shiga na kwaso kayana dana bari a dakin. Na kwashi wanda na dawo dashi nakai duka can part din yar uwata na aje abina don haka na koma banda case dasu indai ya habu yana gari zan zauna nan wajen iya din amma kayana nacan wajesu. A can inda suka je wani kauyen agaye wajen wani banufe da wani ya turasu shine yayi masu bayanin jifansa akayi jifa kuma mai karfi koya mutu ko ya haukace ya koma bai moriya. Dalla dalla mutumin ya soma masu bayani yana fadin uwarsuce tayi sakaci har hakan ya faru ba kuma J ba kadai har duk diyanta ana kokarin ganin an raunanasu ga baki daya. Abin mu na mata abuna farko dayazowa mama a rai shine abokan zamanta mutumin yace ko daya suma gasu nan suna kallan nasu amma wanan ba irinsa bane. Don hadashi akayi da dodon tsafi dake shan jinin jikinsa don ma yana da tsarin ubangijine basu samu yadda suke so dashi ba ai. Ka tuna mutumin daka gaisa dashi ya kama maka hannu da sunan yana tayaka murna a yan kwanakin da suka wuce ? Shiru J din yayi yana tunane ko waye yace kadai tunana gashi nan baki gajere mai dan fadin kai da tumbi baida tsawo sosai dai haka dashi kafirine bai sallah bai chochi ? Still yana shiru yana tunane na dan lokaci don ya kasa gano ko waye wanan mutumin da akai masa kwatancensa saboda abokan hurdan nasa ai yawanci kafiraine. Hjy kinyi sakaci sosai akan yayan ki akwai matar data so fada maki gaskiya a baya amma baki mai da hankali ba kan hakan ? Itama mama nunawa tayi bata gane matar ba a daidai lokacin da J yace malam kwarai kuwa na tunashi tabbas anyi hakan bayan shan ruwa na fito na sayo abinda zanyi buda baki bakin wani shago na hadu da wani daya kira sunana ya nuna min sani ban sanshi ba amma shiya sanni. Yake min murna da cewa shiya dade da sanina ai muka sha hannu dashi sai malamin yace a lokacin ya shafama abin don da shirinsa ya fito dama. Yanzu malam yaya za ayi yace Allah shine maiyi mu saidai mu danyi namu dubarun da Allah ya hore muna ai. Yana ta jan tasbahan da yake aikinsa dashi kafin yayi murmushi yana fadin dewa ya,i wanan yarinyar da karanbani take saidai ba zasu iya komai da ita ba. Wace yarinya ke nan kawu ya tambayi mutumin yace gata nan dai a cikinku take wata mai dan tsayi da manyan idanuwa saura kiris ta kai ga nasara a shirinta. Amma baku bata daman hakan ba da zaku bata dama da anyi nasara koda baku zo nan ba saidai tana shakkun wani abu a zuciyarta kuma. Wacece ke nan malam gasu nan dai a tare daku su din alherine a wajenku kasan wani lokaci Allah kan muna wani baiwa amma bamu fahintar hakan sai muyi sakaci da abin. Amma shi nan gaba zai fahinci komai kai yake jijigawa yana fadin yarinyar tana da gwargwadon sani amma a yanzu tana tsoron aiki da hikimarta . Nafisace ko mama ta fada wata kila itace inji kawu ya fada daga gefenta sai mutumin ya dora da fadin hjy lalai ki samu wanan matar dake son maki bayani don tasan komai. Ya dai basu magani bayan surutan da yayi tayi a ciki harda zancen matan yaya din da abin ya kara daure masu kai suka maishi alheri yace dari biyu kawai zasu bashi sadaka in an samu lafiya su dawo su bashi abinda Allah ya hore a garesu suka fito suna mamakinshi. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,, 2️⃣ 2️2️⃣ 4️⃣4️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Basu iso zaria ba sai goma na dare nayi barci a lokacin don mun dan samu sabani da anty Saare inda Iya da anty Nafisa suka shigan min da cewa. Idan banyiwa yar uwata abinci nakai mata ba wa zai kula min da ita tunda mijinta lalura ya kamashi yanzu bai cikin hankalinsa akan dan uwansa. Hakan kuma sai ya zama laifi saratu ba dole bane duk abinda ta dafa ace saita zubo muna tunda abincin asibiti takeyi abinda mara lafiya ke ra,ayine ai ta dafa mata ni inama ganin kokarin yarinyar nan wallahi nafisa ke fadan hakan . Saare ta kallota tana fadin kada tayi kokari mana wa tayiwa ba kanta ba nifa dole in fada yarinyar nan tunda taje Abujan nan ta dawo ta canza gaba daya a gidan don taje Abuja zatayiwa mutane daukan kai kamar wace taje london. Abinki dai hassadane Saare inbashi ba wani daukan kai yarinyar nan takeyi gidan nan yarinyar da bata ko saka kanta cikin sha,anin kowa ? Dama ai hassadane hakan kada ki dada ki kara indai anty Saarece yanzu haka acan lungun yaya J akai haka tazo ita ta ara ta yafa abinda bai shafeta ba. Ramaah tun wancan case din da akayi na kayan sallah da kuka hana a bata ta kama kanta a cikin gidan nan sai tacewa yar uwar nata salima dake magana. Wa zata kamawa kai mufa nan gidan mune ba cin rani mukazo ba wanan yasa na fito daga dakin iya dana idar da sallah magariba nake fadin. Anty Saare nima gidan mijin yar uwata nazo idan ba haka ba aiba zaku ganin gidanku ba nasan baki kaunar zaman mu gidan nan kuma Allah yayi mu zauna daku din tunda Habu ya dauko yar uwata dole ki ganni a gidan in baki son ganina yau kisa Habu ya saki Yanda gobe idan kin ganni ki fadi abinda kikeso a kaina. Ke nikike fadawa magana haka Rahama ke yar gidan uban waye nace yar gidan ubana malam Aliyu bafillace rugga da kika fada. Shi kenan kun dauka mu fulani dabbobine bamu da wayau ko hankali kowa sai yaso ya raina muna hankali girmanki nake baki don abubuwa amma tunda baki so muje a hakan ai kowa ya iya rashin mutunci. Yanzu kin samu abinda kike so ai tunda kikaiga fada yarinyar nan ta fada girma kuma ya fadi ba salima ta karbe iya data soma maganan a lokacin. Bata daiji dadin kowa ba a cikin zancen donshine tunda na shiga daki ban fito ba tunda naji kawu na fadawa iya ba zasu kwana ba donshine banje part din su Yanda ba. Sun gaji da zaman jira suka kwanta sai anty Salima dake zaune tana kallon film wayanta itace taji dawowansu maigadi yana bude masu get. Ta tayar da iya tana sheda masu sun dawo taji maigadi na budan get din yana gaidasu da dawowa a lokacin hakan yasa suka bude kofan ni dai ban fito ba don idona biyu ina hadiyan bakin cikin Saare a zuciyana a lokacin kinsan bafulace da bakar zuciya dama. Sai washegari dana fito na gaida mama dake zaune falo tanawa iya bayani abinda mai magani ya fada ta juyo tana amsawa kafin na mike nakoma daki tabini da kallo. Kodai yar nan malamin nan yake nufi dai don wanan kunun tsamiyan da take damawa shi kadaine abinda Jafar yake sha ya zauna a cikinsa. Kai ba ita bace dai nafi sa ran Nafisace dai bata kai karshen zuci ba da takeyi taji iya na fadin jiya Saratu bata kyautawa yar nan ba. Akan abinci ta zauna taci mata mutunci a gidan nan wai tayi girki bata zubo masu ba ta zuba min ta kwashe takai asibiti zokiga yadda tayiwa yar nan falle falle a gidan nan jiya. Garin yaya haka ya faru kuma me saratu ke nema da yarinyar nan don Allah ai jiya takai ga bata amsa ta fada mata ba,a daji aka daukosu ba suma suna da uba ai dalili yasa ta ganta nan din tasa habu ya saki yar uwarta idan ta sake ganin fuskanta a gidan nan. Ai gaskiya ta fada idan ba dalilin yar uwarta ba ta yaya zamu ganta gidan nan da tana zaune ta mike kafa habu ya kawo masu yar aiki ko ? Bafulace zaka rainawa wayau ka zauna lafiya don ma yaran nan nada wayewan kai suna amfani da iliminsu aida ta dajinne datace data gane bata da wayau gobe ba zata kara raina masu wayau ba. Murya tasa tana kirana daga falon na fito take fadin Rahama daga yau nayi maki iyaka da sa,insa a gidan nan kinji nasan an bata maki rai amma kiyi hakkuri itama zan fada mata wanan halin banzan nan data koyo ba alheri bane ga mace tagani ta gaza shiru komai kace sai kayi magana akansa kana tare da wahala bance kuma inkiyiwa yar uwarki abu sai kin dibawa kowa ba tunda suna da hannayesu kiyi hakkuri kinji Rahama. To fadane dai gashi nan irin ta uwa mai son yayanta bata goyi bayana ba bata kuma nuna nayi laifi ba wanan shi ake fadin wanka da jurwaye ke nan. Na daiji amma nace nagode mama tace ba komai kinji gaba zai maki amfani yar nan hakkuri baya baci gabawa. Allah yaba yar uwanki da Jafar tare da sauran al,umman musulmi lafiya na amsa da amin nashige daki ashe ta samu Saare a can tayi mata ba dadi a gaban kowa. Saiba ke fafin amma mama kada kuba wanan yarinyar garati da yawa ta dauka daya take da mutane a gidan nan ko banza ai duk sun girme mata don me zataki masu girki. Ya J dake kwance sama dogon kujera mai ci mutum uku ya dago yana fadin wanan wani irin maganan banza kikewa mutane ? Kinfi nama sanin abinda ya dace tayine akan mu ko kinfi yarinyar wani darajane a wajenta ? Koko an fada maki boya aka kawo masu ina da niyar wanan maganan mama ta rigani don aikin da yarinyar nan keyi a gidan nan babu wace cikin ku dake yinsa tafiku wawiya kawai ko ta zauna tayi girki aci hankali kwance wanan ba daraja bane banda cin mutunci me kika koya ke ? Zancen nan dai ba naka bane jafar ka barta aina san abinda nakeyi ba zan zuba ido su saka yarinyar mutane a gaba ba ina kallo aiki ya wuce nawa da iya kona yar uwarta ba zata kara kauda kara a gidan nan ba. Wanan ma da iya ta dauko kwanan ta uku batazo ba son bata iya kallon ga mata zube amma basu iya komai wa zai zauna yana wanan wahalan haka ? Suna cikin wanan zancen muka shigo da Iya a cikin jam,i na gaidasu kafin nace yaya ina kwana ya karfin jiki ya amsa da Alhamdullahi . Yadda naga fuskokinsu yasa na fahinci akwai abinda ya faru don haka ban zauna ba na mike don barin falon don kusan ni dayace bare a cikinsu. Kin hada abincin asibitin ne Rahama mamace take tambayana na juyo ina fadin na rana zanyi masu yau sunce abar na safe zasusha shayi. Ai shike nan sun hutar dake aiki naso naje na dubasu saidai abinda hali yayi zuwa anjima tunda jikin jafar din da sauki sosai yau insha Allahu. Ya dace aje a dubasu kada suga rashin hankalimu iya ta fada mama din ta sake fadan insha Allahu zan kekasu yau ina ganin can Habu ya nufa tunda safe. Ban tsaya ba na fita naje aikin gabana sun dan jima zaune kafin ya mike zuwa daki yana fadin zai kewaya. Sumama suma suka bar falon don gaskiya maganin da alaman ya karbeshi sosai ba bugun kai da yakeyi a lokacin nafisa ta rigasu barin falon ta koma part dinsu. Salima na zaune tana dakilan wayanta suka fara magana Saiba tace dole tayi hakan don ta danje Abuja tayo clean baki ganin daga kan data fara yiwa mutane tunda sun iya asiri . Babu asiri sai iskanci a ina wanan zata samu asirin balle tayi Asmau take fadan hakan haka kike gani da asirinsu ake haihuwansu. Yar kauyece fa kibar yan kauyen nan inda kike ganinsu sis haka suke kiran junan su tun farko yanzu in ana dadin rai hakan ake furtawa juna sunan na sis idan fada yazo kuma za a kira mutun da sunansa na yanka. Boni ya tabbata ga mai zunde yanzu me yarinyar nan tayi maku da zaku sakata a gaba da zaki harda wanan irin zargin inma asiri tayi ai baku tayiwa ba dai ko ? Salima inma tana asiri tasan wanda zatayiwa nikan nafi karfinta har kowa nata kuwa haka dai kikace idan baka damu da mutum ba ai baka zaman kushesa haka ? Ke Saare bar part din nan kafin ranki ya baci yayan nasu ya fada yana nuna mata hanya don ransa ya gama baci da wanan halin nasu. Ke kuma Nusaiba abinda yarinyar ta tsare maki saiki kokarta ki koreta a gidan ki samu sanyin a ran ki tunda zamanta ya tare maki wani abu. Salima ce ke ban labari daga baya zamuce Alhamdullahi don gaskiya jikin nasa yayi sauki sosai sati daya ya iya yi a gida ya soma harkokinsa na yau da kullum. Haka salima da Saare sun koma wajen karatunsu ya rage gidan dagani sai Nafisa da zance zamanta ya dawo nan dai ke nan don tafi ganewa zama a nan din donko da mama zata koma gida bata bita sun tafi ba tace sai mama ta dawo ita tana nan ba yawan hayaniyan nan na gidansu. Shakuwa sosai na tsakani da Allah ne a tsakanina da Nafisa don tankar yar uwa ta daukeni inda har dan fi min salimama zance dadin zama don bata da son kanta tare muke komai da ita. Ba irin rayuwansu bane ita ba sai ta jira kayi mata abuba ita zata tashi tayi da kanta dama aikin dai iya girkine kawai inyi na safe tayi muna na dare wani lokacin idan tana gida tare zamuyi aikin da ita. Watan haihuwan yar uwata ya kama kowa hannunsa a gaba duk da likitoci sunce babu matsala ga hakan saidai komai a hannun Allah yake ai ba a wajensu ba. Allah cikin yardansa ta haifi danta lafiya lau ba tare da aiki ba ranan munyi murna sosai da haihuwan . Ya habu bakinsa yaki rufuwa duk daurin fuskan nan nasa a ranan babu wanan halin a wajensa sai washe baki yake kallo daya zakiyi mai ki gane yana cikin farin ciki. Matan yaya Jafar kusan sune sukazo a karshe daga gidan duban maijego da jariri sun samemu a dakin zaune tare da ita muna hira su mama suna waje da ummah mu zaune don an dauke wuta. Sun shigo sunyi barka basu zauna ba duk da dagawan da mukayi muka basu wajen zama sukace sauri suke zasu koma gida iyace da mai aiki suka bari a gidan. Bayan fitansu mama ta aiko Nafisa tazo sai gata ta dawo tana fadin zata bisu su sauketa gida ta karbo sako a wajen innansu. Don haka suka tafi tare dasu a hanya suka fara zagin yar uwata harni basu barni ba da uwarmu duk sun hada sun zagemu tas a lokacin kishin (saure) ke nan wasu suce dashi (Facal) matar wa da kani ko dan uba. Yafi zafin kishi wani lokacin ga mata har gara kishiyar da kuke mijin ku daya da matar dan uwan miji koda ko ba a gida daya kuke rayuwa da juna ba ana samun wanan matsalan sosai a ko wani kabila a duniyan nan. Mukan bamu san sunayi ba abinda dai na sani shine basu kaunan mu wanan yasa gaba daya bani shiga tsabgansu yanzu ko part dinsu tunda mijinsu ya samu lafiya rabona da wajensu ke nan sai inyi kwana gamu gida daya amma bamu hadu ba. Ina dakin nasan dai ya dawo garin tunda naga motar dayake amfani dashi haka kuma anshigo da tsaraba akace shine ya dawo. Sai asibiti muka hadu daya shigo ganin jaririnsu jikinshi a lokacin ya dan dawo sosai zakice bashine yayi wanan ciwon bala,in ba a watannin da suka shige. Gashi a yanzu yadda nake ji a wajensu arzikinsa sai habbaka yakeyi don har su mama da iya na kiran dan yar uwata da arzuka wai yaya J yace ana sanar mashi da zancen haihuwan kuma aka kirasa kudadenshi sun fito masu yawa daya saka hannun jari a wani harkan mai a can kudu. Don haka komai baja baja akeyinsa a gidan alherinsa ga mutane kuma bai daina ba kamar ma kada yai ciwom nan abin ya nunku masa. Ya shigo da mutane a bayansa yuuuu da suka taka masa naji Nafisa tana gaidasu nidai sau daya na gaidasu na mike tsaye na koma can wajen gado na tsaya. A cikin yare anty Yanda take min magana da na dauku dan nabasu don haka nake fadin nikan ina nasan haka akeyi. Yar fillo anyi da sintirin zuwa asibiti ya kare sai karatu yanzu ko abinda yaya j ya fada min ke nan a lokacin na danyi murmushi ina mika mashi dan cikin ladabi. Amsan shi yayi yana kallo ya jima dashi a hannu sai daga baya na fahinci addua yakewa yaron ashe naga yana mashi ikima da bin sassan jikinsa yana tofewa har dai ga al,auran yaron ya mikawa na kusa dashi yana fadin Allah ya raya muna Alh mu bisa kan sunna sunan baba na saka mashi dama alwashina ke nan idan na samu da in saka mai sunan baba sai ga habu ya rigani hakan. Ai duk nakane wani mai banbadanci ya fada basu jima ba suka mike don tafiya akwaisu da son kanninsu don haka ya yafito Nafisa da hannu ta biyoshi kome ya tuna naji yana fadin yar fillo zo muje mana. Dole na biyo bayanshi sam ba zan iya yadda suke da yan uwansa ba sosai suke sakewa dashi fiye da Habu donshi Habu ko yaushe fuskansa babu fara a cikinsa. Shiko yana da dama sosai yakan zauna dasu yayi hira su fada mashi korafinsu kuma yayi masu maganin hakan a take matane kawai za ace bai dace dasu ba. Amma yana iya kokarinsa ba zaki gansu da tufafi da bai dace ba saidai yanayin gyaran ne da basu tsayawa suyi kawai gara Saiba yar kadunace iya kwaliya a wajensu yake sai dai ita kamar bata amsa sunan yar kadunan ba. Mun fito yake fadin to yaya Nafisat party zamuyi ko walima ta kwashe da dariya tana fadin party kuma yaya kamar wata yarinya karama au to ke in bakiyi yar fillo zatayi ai ? Ko sai ki hada muna taron fulanin ku ayi sharo ayi rawan sanda nayi murmushi ina fadin yaya ai sai za aje neman aure ake sharo ba a haihuwa ba. Au ashe akwai kallo kuwa ranan da zaki kawo muna miji don sai munyi masa shadin nan dubu kafin mu bashi mata. Abokansa suka kwashe da dariya wani ke fadin ka ganta kuwa sai jarumi zai iya zuwa don wanan za a kashe nagge a kanta kana ganinta nan. Au Allah dai kace mu shirya kwasan nagge ke nan nidai sai murmushi kawai nakeyi don ban iya cewa komai idan yana min irin ba an nan. Yanzu ke Nafisa sai mun hadu a gida ke nan ko yar fillo dai wasan Nagge zatayi muna da kiwo ke kuma kince bakyayin party sai walima ? Tana dariya take fadin sai mun dawo yaya Allah yasa kana gari ba tafiyan zakayi ba mukai masu sallama har bakin mota bayan ya gama da su mama suka tafi. Da muka dawo dakin Nafisa ke muna hiransu irin rayuwanshi da yadda suka taso har wani labarin danake tsakwaro maki nasu da akayi bani wajensu. A gurin ta na kan danji tarihin rayuwan mama dubu da iyalinta don takan fada min komai salima ma takan fada sai da komai har haka ba. Hidama sosai yayiwa sha,anin sunan zakice matarshice tayi haihuwan farko haka kudi ya raba muna har anty Salima dake kara a birnin minna don ita bata samu zuwa ba ya tura mata da kudinta Saare kuma da ita akayi sha ,anin bukin. Babban yarsu tazo daga zamfara don da yayi ciwo a lokacin kuma mijinta yayi accident ya kare a hannu sai wanan zuwan muka santa dai zance amma muna gaisawa a waya da ita. Ummah mu ana gama hidimar suna ta nuna tana son komawa gida a lokacin saidai mama ta hana hakan sai anyi arba,in tace yan uwan mu sunzo mutum biyu da namiji guda . Sunzo da nasu abin arzikin daidai iyawarsu an kuma yaba mukan bamu da abinda zamucewa hardo daya rungumemu hannu biybiyu a yanzu . Sai a bakin iya nake ji wai ai ummah mu ta samu manemi a kaduna zatayi aure wani abu naji ya daki zuciyana nace iya ummah tamuce zatayi aure kuma ? Muna ga rasulu yar nan me zai hanata aure wanan da bata wuci haihuwa ba kar kiyi jahilci mana damuwan ku zai iya hanata samun lada . Da zaran kun nuna baku yarda ba zaku sare mata gwiwa da hakan taji auren ya fita ranta take fadin wanan matar da suke asibiti tare itace ta yaba da hankalin uwarku ta nemawa dan uwanta aurenta. Wai matarshi ta rasu shekara ukku ke nan yanzu ya kasa samun matar da zai aura ko wace aka kawo mai yace batayi ba amma yana ganin umnan ku ya yarda. Kinga ai hakan alherine ko har yazo suna asibiti ya ganeta a nan kaduna yake da zama dan jahanan ne shi kinga ai ta dawo kusa daku ke nan idan Allah yayi abin. Jinta kawai nakeyi ina tuna mahaifin mu daya rasu ta yaya ummah zatayi auren wani kuma yanzu ? ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,, 2️⃣5️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Anyi tsegumi sosai ga irin hidiman da Ya J yayiwa matar dan uwansa tsegumin kuma tsakanin can babban gida da wajen matan yaya sin yafi karfi. Ita mama kan dadin hakan taji a zuciyar ta harma da fili wanan kuma shawaran Kawu daudane hakan don kara samuwar hadin kan zuri,an tasu. Basu kara tsegumin ba saiga labarin zuwana school ya fito inda a take suka soma tsegumin hakan kuma ya za ayi in samu karatu a gurbin jami,a. Wanan kuma yaya Habune yayi min kokarinsa ya kuma tsaya saida yaga na soma karatun don let addimition dana samu karatu yayi nisa a lokacin ga kuma takardana sunyi kyau sosai ya baza kudi ya samo min a boye saiji akayi na soma karatu ai a nan jami,a. Anyi tashin hankali sosai a boye duk mu bamu sani ba inda yakai wani zuwa da akayi har akayi zama a falon Iya da kawu dasu yaya da matansu har Saratu dake gidan. Bayan an bude taro da addu,a mama data kirasu ta soma magana kamar haka na taraku nan don gano dalilin dayasa kai Jafaru ka nemawa yarinyar nan makarata haka irin wanan Jami,an ta garin nan ? Alhalin ga yan uwanka sunso karatu a nan haka kuma matan ka suma suna so gasu da yan uwa duk baka nema masu ba sai yarinyar nan Rahama ? Budan bakinshi yace ita Rahama ta fara karatune mama aini ban ma sani ba don ba a fada min ba dama ina da niyar ta soma ai tunda tana tare damu kuma kowa yana karatun nan kada tace mun mata banbamci ? Uwar tace yaya zaka tambayeni bayan kaika samo mata abu kowa a nan ya sani yanzu zaka nuna baka sani ba kuma ? Saiba ta gyara zama irin wanda ke nuna a to din nan kasan komai barkado kakewa mutane kawai. Yace wallahi Allah mama bansan ta soma karatu ba don bani na samo mata ba amma kuma ina da niyar hakan a ina ta soma karatun ? Kallon juna sukayi shima kallon Habu yayi yana son sanin wani abu akai da kyat Habu din ya hade wasu yawu don ransa ya gama baci a lokacin. Yace a A,B U ne yaya J Awar nasa ya samo mata don takardunta sunyi kyau sosai zata iya zuwa karatu ko ina a fadin kasan nan dama ina son hakan Anwar ya jima yana cewa nakawo mashi takardun wanda yai kyau a bashi gurbi a wajensu shine na kai masa nata takardun. Hakan yayi kyau sosai Allah ya bada sa,a yasa taci amfanin abinta ita da sauran al,umman Annabi sallalahu alaihim wasallam. To ke nan Jafaru bakai bane don ka nuna baka da masaniya akan hakan ya sake kallon uwar yana fadin wallahi mama ban sani ba amma ina da niyar hakan a gareta. To ku kunji shiyasa Allah da manzonsa suka horemu da munana zato a tsakanin mu wai tsaya mama don Allah ba katseki bayi ba a nan shike nan yanzu ba a da halin a taimakawa iyalina kome haka yake nufi ? Kai Habu dakata ai anbar magana baya kawu ya fada yana gyara zama yace toni Habu bai yi hakan ba saida ya sameni ya fada min kyakyawan niyarsa na son taimakawa yaran nan na kuma bashi goyon baya akan ya nemi shawaran mahaifiyarta da yar uwarta ko zasu yarda da hakan. Ka fada min yaya saidai a yadda suka hau din nan ba yarda zasuyi da hakan ba don zasu dauka na rufe masune amma ni Habu yazo nan da takardun ya nuna min haka kuma da zata tafi tunda dare ya sanar dani hakan. Mama kawu don Allah ku gafarce ya J ina son barin gidan nan don Allah ka tafi ina mama din ta katseshi da tambaya yace ko haya zan kama kafin na karasa gina nawa mama . Tir tir wallahi akan wa yan nan habu basu isa su raba mu da uwarmu ba muddin mama tana raye a doron kasan nan saidai su subar muna gidan tunda zama dasu ba dole bane. Ko akwai wace aka haifeni da ita a cikin ku kona fada maku cewa ni din ba dan dangi bane ke Asmau kin sani tun bude idon ki kinsan koni waye har iyayyen kunsan yadda gidan mu yake kika yarda kika aureni a hakan kona boye maki wani a cikin rayuwana wanda baki sani ba ? Kasa tayi da kanta tana fadin toni me kaji nace a nan munafukan banza da wofi kawai mama zatayi maki karyane ? Kyale ta dukkansu nan suka sameni da kukan su harda wanan sauniyar shakatafin wai kana son ka fifita yarinyar nan basu san meyasa haka ba ? Saboda ba kudin gidan ku nake amfani dashi ba yasa ban fada maku damuwata wanan maganan idan bakuyi hankali ba wallahi karshen zamana daku yazo ke nan a gidan nan. Kai haba meya kawo wanan maganan a yanzu ana sulhu kuma bari mama halin matan nan ya dameni ko alheri nayiwa dan uwana suka sani sai wanan shedaniyar tayi min korafin hakan me yasa zanyi ya nuna Saiba. Ni ai ba kace ni kadai ke hakan ba idan kuma kaji nayi maganan abu itace tagani ta fada min sai nayi magana tunda muna tare da kai. Nasan Asmau munafukace ta karshe macijiyar soshiyace yar sari ki noke kawai nasan halin kowa a cikinsu ke gaki mara kunya kece ke iya gaba da gaba dani don baki da kunya. To ai bamu muka soma magana ba Saarece ta samemu da zancen ita da Amina suke fada mana kaine kakai ta wanan school din. Suyi rikici a wajen sosai don Habu ya kafe da abarshi ya bar gidan don su din makiyansane sai da kyat aka samu ya lafa don Jafar bai ragawa matan nasa ba harda zancen sunan Abbati saida sukayi yace da yana da halinda yafi haka abinda zaiyi saiya fi wanan don baida wanda yafi mai dan uwansa a duniya. Jin hakan yasa dole habu din ya sasauta zuciyar shi har anci an sude yar uwata bata san abinda ke faruwa ba tana part dinta sai nice dana fara jin zancen wajen iya nake tambayan anty Nafisa ta fada min komai . Nayi mamaki tare da tunane abinda mukai masu don wanan kiyayyan yayi yawa haka a tsakanin mu dasu Allah ya taimaka ban faye fadawa yar uwata abinda ke faruwa a gidan ba. Nakan barwa kaina in shaye duk wani abinda za a fada game damu don ta zauna lafiya da mijinta wanda kowa hakan zai mata fata a zamansu din. Jin abinda ya faru din yasa na kara kama kaina sosai da yan gidan namu har anty Nafisa da muke dan shiri da ita a yanzu ba komai take sani game da mu ba. Karatuna nasawa gaba sai kuma lalurar yar uwata indai mun hadu zamu gaisa dasu idan bamu haduba kuma a zauna lafiya. Wanan halin ya karune a ranan wata jumma,a dana saka wasu kayan da anty salma tabani sawa daya tayiwa kayan ta kwabe ta mika min wai dinkin bai mata ba. Sai gashini kayan sun matukar karbuwana suna saka don girmama jumma,ata na ranan da wuri na dawo don haka na samesu a wajen gida inda suka tsiri zama yanzu suna shan iska. Gaba dayansu daga can inda suke zaune suka zubo min ido tun bude get dina shigowa gidan ban nuna nasan suna zaune ba na bude part din yar uwata na shiga da sallamata kukan Abbati nakeji nake tambaya meya faru kuma yake kuka Yanda ? Bansan meya sameshi ba tun dazun yake wanan kukan daukan yaron nayi na kwabe masa kayan jikinsa don yasha iska ko zaiyi shiru saidai a banza daukansa nayi na daurayeshi har na shafa mashi mai na sauya mai kaya na kaishi wajen uwar don ya dan rage kukan da yakeyi. Yaron ya kama nono sai kuma ya sake yana challara ihu yana kwandare kafa da shure shure hakan yasa na daukeshi zuwa part din iya ina jijigashi. Yaron a yanzu yayi wayau sosai dan kimanin wata bakwai ke nan da haihuwa anan na sake wucesu ban tsaya duban wajen ba nashiga iya tana zaine ita kadai a falo nasameta dashi nake gaisheta. Bata samu amsa min ba take tambayana kome ya samu yaron saidana zauna nake fada mata haka kawai yake kuka tundazun. Karban yaron tayi tana fadin na dauko mata jar kanwa ta hausa shina dauko mata tajika taba yaron yasha. Ta miko min shi nacigaba da jijigashi a hakan ya shigo ya samemu yaron yana dan sauke ajiyan zuciya gaidashi na soma naji iya na fadin. Ka dawo kenan Jafaru ko baka samu zuwa bane naje iya dawowan mu ke nan yanzu duban mu yayi yana fadin wanan kuma meya sameshi haka ? Iya tace ina ganin cikinsa ke ciwo kasan yaran yanzu ba kula suka iya ba sun dauka kukan banzane haka kawai mutum zai dinga kuka da gangan ya fada ? A daidai lokacin Saiba ta shigo part din itama yana fadin in miko mashi dan na banye na mika mashi ya karbeshi yana fadin yanzu me aka bashi ? Kanwa na jika na bashi yasha iya ta fada da sauri yace iya kanwa kuma ina maganinsa yake da aka bashi kanwa bari a kaishi asibiti dai a dubashi. Ai yasha kanwa ya fada mashi Saiba ta fada ke dauko mayafin ki mu kaishi asibiti kome ya tuna kuma yace kira min Saare mukashi asibiti . Batayi niyar fita ba yasa ya dubeta yana fadin badake nake ba ta juya cikin bacin rai ta fita sai naji iya tace kayi dabara don gara zuwa da Saratu din. Nasan halinsu da sheri ko yanzu abinda ya kawota ke nan ai ta dauka nasan wanan tana part din nan bar yan iska zanyi maganinsu ne. Kyalesu Allah ya dora masu kishine haka barsu sunyi ta haukansu akan hakan su girman su ke zubewa gareta ina fama da yaron ba jinsu nakeyi ba don na koma wajen kitchen dinsu ina jijigashi. Saida suka tafine naji iya tana fada na dan fahinci abinda ke nan ni kaina gaskiya da nasan yana gari ba zan ko shigo part din iya ba a lokacin don nasan wajen zuwansane bansa dayana garin ba sai ganinsa da nayi a lokacin. Sai bayan kwana biyune Nafisa ke mun hira da nasha zagi a wajensu ranan ganina da wanan lace din da sukayi har photona aka dauka ban sani ba ana tambayan kudin lace din aka fada masu yakai dubu dari. Tace hankalinsu ya tashi sosai da jin kudin ga kuma wayan hannuna shima sunyi zance akansa wai dole zasusa a canza masu waya ba zasu yarda in rike wayan da basu rike basu. Har cewa sukayi kila sata nayowa inda naje abuja din yanzu an hada plain din cewa za a turo saratu ta kwashi number anty salma a wayata su binciketa sai sunyi min sanadin da suka gujeni a can din. A wanan lokacin anty maria tasan irin kwaran din da nake fama dashi a gidan a wajen hiran mu da Nafisa din dole na kwashe komai na fada mata abubuwan da suka faru dani tana asibiti. Ance Dan Uwa Murfin Jallo guda bayayi saida dayan don duk wanda baida dan uwa a duniyan nan yayi babban hasara a duniya. Ran yar uwata ya baci sosai har tana ikirarin dole ya habu ya canza mata gida kada suzo su illanta muna rayuwan mu. Ita kyauta daga gurin yaya J ta daina amsa koda na dantane kuwa indai shine yabada da sauri Nafisa tace kada kiyi haka Maria. Inkinyi hakan nice zasu zarga dana fada tunda sunsan tare nake da Ramaah ko yaushe dama kuma suna zargina gashi ba uwa daya nake da mazansu ba sai ace nazo don in shiga tsakaninkune ashe . Wanan yasa ta hakkura da zancen saidai itama ta dauki zafi a nata bangaren yanzu ba sakin fuska ko wani ban girma ga matan dan uwan mijin nata kuma. Zama dai ya rike a gidan inda har yakai mama dubu tazo don jin ba,asi inda ta tarasu tana tambayan me yai zafi hakane a tsakaninsu ? Bata fahinci komai a zancen ta daiyi masu fada ta kwana biyu ta koma akacigaba a inda aka tsaya muna sha,anin mu suna nasu saidai mama din ta dauki anty Saare da Nafisa ta tafi dasu inda tace salima zata dawo hutu ta zauna da iya kafin gani kuma tare da iyan. Sai zaman gidan a lokacin ya soma fita min rai don ba abokan hira a gidan yanzu da zaran na dawo ina dakin iya ko wajen yar uwata ba zan fito ba kuma sai washegari. Allah ya taimakeni iya da kanta ta bugawa mama waya da Nafisa ta dawo mata idan ban nan zama ita kadai yana gunduranta. Hakan yasa nafisa ta dawo ita kadai amma ta kiyayyi duk wani abinda zai kaita part din yaya j a yanzu har na yar uwar tawa bata shiga ko ina a gidan. Har yakai mazajensu sun fahinci akwai abinda ya faru iya yaya j yake tambaya itace take fada mashi dan abinda ta sani ga zaman matan nasu. Ranshi ya baci sosai ga abinda iyan ta fada don tace hassadane kawai da kyashin juna ya kawo masu gaba a tsakaninsu. Rasa abinda zasuce sukayiwa iyan kowa da abinda yake kiyastawa a zuciyansa tsakaninsu dai komai lafiya yake tafiya koda akwai baraka basu yarda ko mahaifiyarsu ta sanda hakan amma ga iyalinsu nason kawo masu matsala kuma a hadin kan nasu. Saidai mama bata yarda da hakan ya faru ba a yanzu kan ta daura dammara wanan zuwan da zatayiwa iya data dameta ta kwana biyu bata zo ba zasu ga canj a wajan ta baki dayansu duk wace ta kuskura tayi wani abinda ba daidai ba a gidan. Basu kadai ba har saare ta shiga wanan fadan na mama a yanzu don gaba daya ta hanata shiga ko wani part a gidan. Saidai hakan bai hanasu hurdansu ba a boye tunda gulmane akwai waya a tsakaninsu sun dai kaucewa idon ita mama dubu din ne. A yanzu ko yaya Habu yana gari a nan wajensu nake kwana don na dawo da rayuwana gun yar uwata baki dai shigowa part din mu kiga wani abin kazanta a garemu ko wani abinda bai dace ba can. Yayin da arzikin mazajen nasu keta bunkasa sosai wai ashe ita anty saare ta samu matsala a karatun ta wanda yasa ta bar makarantar da takeyi a farko na gane hakan ne wajen jin ta koma da karatunta a nan F C E zaria. Saidai a hostel zata zauna tace kuma suka yarda amma tasha fada sosai wajen yan uwan nata don har shi J yana ikirarin idan bata tsaya tayi karatu ba wana katon ba zai sake bata kudinsa akanta ba. Kwatsam zancen auren ummah ya taso hakan yasa mu zuwa garinmu da tun zuwan mu bamu taba marmarin komawa ba. Munje kafin bukin inda yaya Habune ya kaimu da kanshi zamu dawo mu taresu a nan kamar yadda naji suna fada ba zance nayi farin ciki ko bakin ciki ba nidai na kasa tsayar da zance daya a zuciyata akan auren. Gaba dayan mu bamu so zuwa wajen baffa ba amma aka rinjayemu muka tafi dole ganin sa munyi arziki ya tafi Adamawan cameroon a lokacin hakan yasa bamu samu ganin shiba saidai mutumina kan Dage manga juna dashi har na karbi lamban wayanshi rakani toilet dayake shan kida dashi. Ban yarda na bar garin ba saida ya ban kata,un makaru da yayi ikirari dashi yace idan naje na juye a kyale kar na barshi a leda. Kudi na dauko na mika mai tare da gargadinshi akan kada kowa yasan hakan don na kara masa gobe nasan matsalan dan uwana wajen kwadayi. Jin dadin hakan yasa yace kai amma Ramatu kin kasheni yau to jo kiji wani magana na matsa ya soma magana kamar a cikin rada zakice yana tsoron wani yajimu duk da matarshi saida ya turata cikin gida ta samo leda ya san min dankali. Wanan daman muka samu ya fada min wasu sirika da zamu fito na dankawa matarshi itama dubu biyo don nayi mata faein sani dani akai nemanta a lokacin bayab mune akai aurensu. Na kurune da dani aka hadashi amma uwarshi tace sam bata yarda da hakan ba ita don idon mu ya bude da yawa zanwa danta wayau na hanashi aje Nagge. Nikan taimakona tayi a lokacin da irin gulman nasu da camfi na kauye da suka dora muna wanan yasa a kullum baffa ke fadin mugaye muke masu bakin jini a haka zamu kare a kiwo. Ni nasan Allah yana sonmu shine ya kawo sanadin da bamu hadu da baffan mu ba lokacin don da yaga yadda muka koma komai na iya faru a lokacin don baffa mugun bafulatanine sosai shiyasa mutane ke masa lakani da maita. Mun dawo lafiya baki alaikum da kamar ba zamu samu taro wajen yan gidan mu ba kome suka gani oho masu saiga Asmau itace ta fara shigowa yi muna sannu da zuwa. Daga baya Saiba tashigo a yatsene take muna sannu da dawowa ya hanya muka amsa mata da lafiya kalau. Acan gida mun shiryawa ummah sosai gaskiya yaya Habu yayi kokari ba kadan ba tunda ba wani sana,a yar uwata takeyi ba. Bayan dawowan mu da sati biyune ummah muta tare a gidan sabon mijinta dake kaduna a unguwar Dosa mama dubu dasu inna sukai mata rakiya a cewansu sunyi mamaki kwarai ashe mutumin ba karamin mutum bane . Ita matarshi data rasu ta barshi da yara biyar tsohuwar lauyace mai zaman kanta haka yayan nasa ma duk karatu sukeyi basu zama a gida. Nikan sai najiwa ummah tsoron hakan don yan bin nan ba ai masu shigen kutse haka duba ga yadda mu nan muke fama da facalan yar uwata a wajen kishi. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,, 2️⃣6️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Mu dai bamuje kaduna ba saisu mama dubune sukai mana kara ita da kishiyanta inna da yanzu itace kamar uwar dakimu gidan saboda tana nuna muna kulawa sosai kodon muna tare da yartane oho ? Koma meye damunzone gidan zata karbe Abbati tana angonta tana ba,a kasancewa itace amarya acikinsu. Wanan yasa muma muke zama a dakinta har dai shakuwa ya shiga tsakaninmu sosai da ita bamu gane ko mama dubu tana son hakan da mukeyi ko bata so ? Har dai yakai ya habu da kansa yakan dauki yaron yakaiwa inna shi don yawan tambayansa da takeyi lokaci lokaci kota niko gari tazo gida tace tazo duba maigidantane ita da iya. A kullum kuma inna tana kan muna nasiha game da zama tare zakice ita din yar uwamuce ta jini donshi shakuwa sosai ya shiga tsakanin mu da ita harma yayanta. Don haka ta takawa mama wajen rakiyan ummah gidan sabon mijinta akaduna sai gashi sunje sunga abinda basu zata ba a can din. Yanzu tsakanin mu da ummah wayane mu duka kowa na kiranta yaji lafiyanta tana ce muna lafiya kalau wanan ke kwantar muna da hankali. Gaskiyane da wasu mata idan mazansu sun mutu sun barsu da yaya koda iyayyensu suna raye suke fadin gatansu ya fadi gatansu ya tafi wanan zancen ba karya bane don mun gani a kanmu a rayuwan mu. A yadda hardo ke fada muna a yanzu duk shanayen mune wajen baffa shanayen da idan da zamu mallakane zasu taimaka muna harmu taimakawa wanin mu a rayuwa. Sai gashi badon ubangiji ya rufa muna asiri sanadin ya Habu ya auro yar uwata ba da rayuwan mu a bautan baffa da iyalansa zai kare muna. Sannu sannu yau nakai UG 3 da dadi da wuya haka karatun ke zuwa min a daidai yayin da Anty Salima take shirin zuwa bautan kasa a lokacin kuma muka shiga wani tashin hankali sabo dayafi na baya a gidan rikona inda yar uwata take aure. Don ko an samu sakon ya Jafar wanan ciwon kan nasa a yanzu ya dawo inda abin har yafi na farko ga fadan masu fada labari yazowa mama kamar hauka yayi a lokacin. Innalillahi wa inna alaihin raji,un tashin hakan da muka kwana dashi muka tashi dashi kr nan a gidan wanda yasa su kawu dasu yaya habu kwasan jiki zuwa garin da yake. Da alama ba dadi don duk lokacin da wani zai kira a gida aji halinda yake ciki amsa dayane shine jikin dai da saukin musulunci za ace kawai amma ba sauki sai a wajen Allah. Rana daya naga damuwa karara ga iyalinsa ranan da ya Habu ya kira yana fadawa mama cewa da wahalan da Jafar yake ciki mama gara a roka masa Allah kawai saukin mutuwa. Sai mama ta fashe da kuka kuka mai tsanani dole kowa a gidan kukane na tashin hankali ba maiba wani hakkuri a gidan lokacin. Duk muna falon iya gaba dayan mu in banda iyatu dake faman aiyukanta a wajen gidan nan saiba ke fadin mama ko zamu shirya mujene ? Ai yanzu ba zancen zuwa bane tunda gida zasu dawo dashi a gwada a gani abin na asibiti yaki suncesu basu ga ciwon komai a jikinsa ba komai nasa yana lafiya don haka bana asibiti bane abin iya take fadan hakan ga matar nasa. Dawowa dashi din garama da suke can labari kawai mukaji bamu gani ba don ganinsa a irin halin da yake ciki shine babban tashin hankali ga yan uwa da abokan arzikinsu. Kai innalillahi tashin hankali baida kyau don ciwon maimakon aga sauki sai kara sabon sallo na ciwo da yakeyi yau ya taba nan gobe ya canza waje duk a jikin nasa. Idan ya taso yana kugi duk inda mutum yake a gidan yana iya jinsa saboda zafin ciwo a yadda naji har salinta jikinsa ya farayi yana saba irin na macizai. Haka na shirya na bar gidan a cikin damuwa ganin mama yadda take kuka a gaban kawu da iya tana fadin wanan wahalan yai yawa in tafiyane Jafar gara katafi ka huta da wanan wahalan haka. Duk da nake yarinya banji wanan adduan ta mama yai min dadi ba musulumi sauki aka sanshi dashi da nema a wajen ubangiji ba zancen baki ba. Masu fadan hakan bawa yasan abinda zai tar a gurin Allah ne shidai bawa ya nemi sauki koma meye a wajen ubangiji shine mafita. Har nakai school da wanan zancen nake a zuciyana a karo na farko da kusan shekara biyu ke nan da zuwan mu gida ban taba gwada kiran layin Dage ba sai a ranan naji ina son kiran Dage in sanar dashi halinda dan uwar mijin yayata yake ciki don mutumin arzikine sosai ya J komai mutum zai iya masa don ya cetoshi daga wanan uku ban da yake ciki na bautan ubangiji . Gashi ashe sakacin su yasa basu koma can wajen wancan malamin daya taimaka masu ba da farko tunda sukaga sauki suka fita batun koda kawu ya koma yace ba abinda zai iyayi yanzu da ace tun wancan lokacin sun dawo sun karbi abinda yace din da sun bashi goron sa da wata kila hakan bai faru ba a yanzu don an riga da ancin masa ko ciwo yayi nisa wanan zancen tunda kawu ya dawo ya shedawa mama ta fita hankalinta ga baki daya. Cikin ikon Allah ina danna kiran layin ya shiga bai dauka ba har kiran ya katse a kasa nake tafe hakan yasa na kara danna mashi kira a karo na biyu. Sai gashi naji an daga ana faman fadin Alo alo alo murmushin karfin hali nayi ina fadin who is speaking au kafirata ka kirana ashe ? Naji Dage din na fadan hakan na sake sallama don na fahinci zai iya kashe wayan a lokacin ya amsa sallama yana fadin wake magana ? Nace budurwankace ta birni da kaba layin wanka koba dage bane yace kwarai kuwa nine Dage nace to ni aljannace na kirakane muyi soyayya shiru yayi da har yasa na daga wayan na duba koya kashene a lokacin. Sai naji yana fadin Aradu Ramatuce oho yar nema ja,ira sai yau kikaga daman kirata watau ? Ina gwada layinka Dage baya shigane nayi mai karya yace kai kinshan me Ramatu kudin da kika ban ardu kudin albarkane ai watau da wanda kika bani da wanda kika ba inneje na hada suk na sawo muna dan karo mace dana miji Ramatu bakiga yadda suka haifa muna diya ba wallahi kowa sai magana yakeyi nashe wa tsayahu wanan karon zumuncine tsakanina da Ramatu. Dariya na kwashe dashi na katseshi da tambayan mutanen gida har baffa yace kul ardu kun kuru da baku samu baffan nan a gida ba lokashin . Yayi cizon yatsa yashe ai zaku dawo shi za a kawowa shegan taka ita maria harda haihuwa da kado ko ? Gabana ya fadi nasan za a rina dama indai baffa ne da suke kira da magajin tauri duk wani maison maganin tauri yazo yaga baffa ya warke. Dage akwai wani bawan Allah dan uwan mijin maria da akaiwa makaru nan dai na tsaya nayi mai dan bayanin abinda nasani game da ciwon yaya din. Kai amma ke Ramatu a kwaiki da shirme wallahi ina wanan garin dana fara baki shi zaki dinga mashi hayakinsa haka kuma. Ki samo magarya kunne gomasha bakwai kada ki dada daga hakan a samu dutsen tama kinshanshi ko nace a,a amma zan nema yace kwara ukku kacal a saka kasan tukuyan a tafasa a tare saiya dahu sosai a sauke ya huce a diba hannu uku asha sai ayi wanka da sauran . In Allah ya yarda da zakuga sauki zan binciki baffa nayi mai karyan wani nason taimako a waje na bashi dan kudi sai ya fada min wanin. Bari na turo ma kudi a wayan ka ka sayar ka bashi ba sai ka taba naka ba Dage ayi haka kuma Ramatu haba dai ka barshi kawai nayi niyane ai. Wurin mai shago na tafi na bashi kudi ya turawa layinsa lokacin haka ake tura sakon kudi sai gashi ya kirani yana fadin arradu Ramatu kinyi lafiya kun ketare kaidin baffa shima baffa yana fada gaba dayan ku kunfi karfinsa ai. Ya gwada sa,ansa akanku ya kasa cin maku tunma ke yace ke iblishiyace da zaki kai wani lokaci a wajensa da kin kwance masa karfinsa. Haka dai muka rabu dashi yana ta shirmensa na tare abin hawa zuwa gida saidai kuma me a gidan dai badadi don wani tashin hankali na dawo na riska inda mama tayiwa matan jafar kaca kaca a ranan . Wai suna gudunshi suna kyamarshi don haka mama tace sai subar gidan ita zatayi jinyar danta in da rabo in yaji sauki su dawo mashi amma yanzu kan sai sun bar mata gidanta. Tunda babu wace keda hankalin da zata kula dashi iyakarsu su dan shigo suyi shaaaa su fice babu mai zama ta kula dashi a cikinsu. Hakan ya farune da Asmau ta shigo dakin da yarta yana dan cikin hankalinsa ya mikawa yar hannu da tazo wajensa sai uwar taki bari yar taje. Shi jafar din ya dubi matar nasa yana fadin inku kuna kyamana a haka har da yayana zaku hana su rabeni Asmau ? Kawu da mama na zaune lokacin da hakan ya faru mama tace sun ma isa sunce suna kyamar ka jafar ? Yace aigata nan idan akwai wace ke yarda ko gadon nan ta taba haka nake fama idan baku kusa kona kirasu basu zuwa su taimaka min komai zasuyi min a wullakace suke min shi suna gudun su dauki cuta a jikina. Wanan ya harzuka mama ta soma bala,i da tashin hankali har haka ya faru ita saiba sai ta fake da tayi yaji ta kwasa ta nufi kaduna wai mama na yawan takura mata . Ita Asmau bata tafi ba shine mama tace har ita din ta tafi duk mai zaginta ya zageta amma basu zama a gidan. Nima na kula da hakan a lokacin saidai sanin halinsu yasa ban dauki hakan wani abuba tunda haka yake zaune da abinsa. Na rasa yadda zanyi in aiwatar da maganin nan ga yaya j ina zance dasu na samu wanan abin ina part din mu mama ta kira waya da inzo mu kula mata da Jafar zasu tafi wani waje ita da kawu. Don a lokacin ita Saare tana school ita kuma Salima ta wuce bautan kasa saini da Nafisa ne a gidan muka shiga part din nasa tsit don matan gidan da basa nan kwana biyu. An dawo da Asmau mama tace taje ta huta kawai haka ba yana nufin zata raba mata aure da mijinta bane bata dai son ganin su gidan a yanzune. Lalai ankai hali dubu makura mace mai hakkuri ta iya yanke wanan hukunci don haka kawu yace suje din kamar yadda tace har ta huce. Anty Nafisa tashi mu shiga dakin yaya ayi komai a gabanki don Allah akwai taimakon da nake son yi ban samu daman hakan ba a gidan nan . Kallona tayi a tsorace tana fadin me zakiyi Ramaah nace zo muje anty Allah ya gani taimako zamuyi da zuciya daya. Dakin muka shiga da sallama ya kwance gwanin ban tausayi muka gaidashi ya amsa muna da kai dakin ya danyi shiru gabana sai faduwa yake ina kuma kare mai kallo nace yaya don Allah ka fahinceni. Akwai wani magani da aka bamu a gida nake son in jaraba mu gani amma ina tsoron hakan bansan me zan fada ba yasa yanzu na sameka ga anty Nafisa don Allah yaya ka daure ka dinga sha koda ban kusa anty Nafisa zata baka zamu fadawa iya kuma. Maimakon ya amsa min sai hawayene ke zuba a idonshi na fito da kullin maganin muka zuba mai a kunnu bai ki ba yasha muka kara kwantar dashi. Mun jima a wajen zaune sai sha biyu su mama suka dawo gidan kawu ya sauketa ta samemu a dakin wajensa zaune bamuyi barci ba. Mu muka taimaka mata tayi mashi komai a ranan daman dana samu kuma weekend ne don haka yasha maganin kusan na kwana uku ina bashi a boye. Mu gyara dakin mama tayi mai wanka kafin ta fito na kwashe zanin gadon na shimfida wani na feshe dakin da kamshi. Zakiga ya sauke ajiyan zuciya idan ya zauna na hada mai kunu ina bashi mama tashigo tana saka min albarka tare da fatan alheri a gareni. Take fadin Rahama indai ba karya nakeyi ba kamar jikin jafar yana saba (salinta ) alaman hakan kuma meye ? Mama duk ta rude daka ganta bata cikin hankalinta nace mama kila hakan wani sallon ciwon ya canza kuma ? Naji sauki sosai ya bamu amsa da fadan hakan yana gyara kwanciyarsa ya habu ya shigo dakin nayi saurin gaidashi yana tambaya ina Nafisa mama ke fadin yanzu take nan tace iya tace tayi mata shayi . Ya karasa bakin gadon yana fadib J ya karfin jikin naka ya bude ido ya dubi dan uwan yayi dan murmushi kadan hakan yasa ya Habu din yakai zaune. Mama bari naje na gaidasu iya na fada ina fita tace kima huta tunda ga Habu ai kafin kawun ku yazo ya kama min nima na dan jena huta. Bayan fitana yake fadin yarinyar nan habu yace wa Ramaah ya gyada kai alaman eeh saiya lumshe ido yace me tayi yaya yace kirki don bai dogon magana. Sai Habu din ya danyi murmushi mama daga gefe tace meyace wai Rahama yake fadin tana da kirki aini har tausayi ta koma bani yarinyar arzikice sosai wallahi. Barci nayi sosai don kwana mukeyi gadinsa a gidan daya motsa dayan mu dake falke zai tambayeshi me yake so ? Hakan yasa har zuwa school na dan dauke don maganin da muke gwadawa wanda dagani sai anty Nafisa dashi muka sani haka kuma yana sha sosai idan mun bashi din kuma yana shan wanda su mama keyi mashi. Hadari aka hada sosai a garin hakan yasa mama cikin damuwa ga yaya Habu ya tafi kaduna tare da kawu gashi ance kada a dage rana ga karbo maganin fita nayi kamar zan shiga cikin gida na fice bakin get ban samu abin hawa ba haka nayi ta sauri saida na kusa isa na samu mai keke ya karasa dani gidan mutumin. Na karbo haka na biyo ruwa da iska na iso tsamo tsamo da maganin gidan nakaiwa mama mamaki tayi sosai ta shiga yi min fada yadda na iya fita a cikin hadarin nan. Nace mama gani nayi lokaci zai wuce bai sha ba kuma ga ruwan nan ba a san lokacin da zai tsagaita ba. Maza kije ki kwabe tufafin nan kada sanyi ya kara kamaki mura ya sauka maki kin daiyi kasada wallahi bin hanya haka a cikin ruwan nan . Dakin ta shiga tana fada yake tambayan meye mama din tace yar nan Rahama ashe ta fita a cikin ruwan nan ta tafi karbo maganin nan dana damu akansa. Baiyi magana ba sai zuwa can yace mama yaran nan suna matukar kokari sosai wallahi a raye suke kwana gidan nan. Aini ban iya cewa komai a yanzu saboda ko yaran nan su saratu ba zasuyi min wanan dawainiya haka ba wallahi. Bayan kamar kwana biyu jikin nasa yayi sauki sosai a lokacin ya dan harda tafiya ba tare da an rikeshi haka kuma kumburin kafanshi ya fara sucewa kafan yana fadawa don yayi kamar turmi a lokacin ba dadin gani sai walkiya da yakeyi kamar zai fashe. A takaice bawan Allah nan yasha wuya fiye da tsamani sai zantuka akeyi marasa dadi game da ciwon nashi kowa da abinda yake fada. Shi kanshi mijin yar uwata duk ya fita cikin hayacinsa saboda jinyar dan uwasa din hankalisa duk a tashe yake haka kuma shike gudanar da komai na kasuwancin dan uwan a yanzu. Zuwan ummah biyu daga kaduna suna wuni a nab su duba jikin nasa ita da maigidanta sai ya ajeta ya shiga gari wurin yan uwansa. Ba wani rashin jin dadi ko takura a jikinta tayi fes da ita dama gwanar tsabtace ita don haka gyara a yanzu ya samu waje. A kullum ummah tazo takan min korafin yaushe zanzo naga mazaininta saidai inyi dariya kawai banyin magana. Ni damuwana yan uwan mu da muka baro a gida duk yadda birni ya lalace yafi kyau mu muna nan muna jin dadi su kuma suna can bamu san halin da suke ciki ba . Don ni a nawa ganin banga abinda zaisa ummah ta barsu a can hannun hardo ba tunda ita dai ba haihuwa take nema a yanzu ba. Har yakai na kasa magana da zata tafine nake fada mata damuwana akan yan uwan namu maza tunda ba wasu manya bane dai. Shine take fadin mijinta ya soma maganan hakan yana son su dawo wajenta don suci gaba da karatunsu itace bata bada goyon bayan hakan ba kada yan uwansa suce tana son mamaye masa gida. Ummah ai yasan kina da yara ya yarda ya aureki don haka a taimaka masu su samu suyi karatun nan suma bata dai ban amsa ba har ta tafi gashi ko wayansu muka kira ba,a samun su wasan dadi suna daji inda ba service. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,, 2️⃣7️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Wai habune aka fada a bayanshi jin hakan yasa ya tsaya cak yana dube dube ko zaiga wani fuskan sani ya kirashi. Saidai ba alaman wanda ya sanshi a wajen hakan yasa ya dauka bashi ake nufi ba ya kara yunkurawa zai shiga motan. A daidai lokacin ta karaso tana fadin Garba sadauki garaba gagare Abu bakari mazan fama baka shedani ba ko ? Yanzu kan yasan dashi take magana a lokacin don haka ya dakata tare da juyowa gareta duk da baudaden halinsa dabiansune gaida nagaba dasu. Ina wuni yayi mata cikin ladabi ta amsa tare da fadin kwana biyu shekaru da yawa Habu ba zaka shedani ba duk ku din kuna a raina don abinda na hango a zurian ku. Uwarku tana da yawan sakaci ga mantuwa habu tun a lokacin naso tazo na fada mata abinda ke faruwa bata zoba har nabar garin ku. Banfa ganeki ba boyar Allah ya fada yana kara kallonta sai tayi dan dariyan manya tace kagani na ganeka kuwa ni mutum ce da bani raina alheri komai kankantarsa idan anyi min. Balle alherin ka dakai da uwarka yasa naji ina dai son in taimake ku duk da nasan abin ya faru ko dan uwaka yanzu. Don yanzu haka yana kwance a gida rai a hannun Allah kuna shiga kuna fita kuna bata kudin ku a banza. Duk da kamar warkansa yana hannunka a yanzu amma baku san da hakan ba don mantuwa irin naku. Haka kuma cutarshi na jikin ku habu yana biye daku sauda kafa ako yaushe matukar ba wanan sadakan aka bada ba. Duk da akwai hannun maki don abune da yayi yawa a tare dashi shiya nasa ya kaishi kwance amma ko ku baku tsira ba gaba dayan ku matukar ba wanan sadakan aka biya ba. Ba na fada maka a ranan tafiyan ka a kofar gidanku ba na fadama alherin ka da nasara yana inda ka dosa a lokacin tabbas nasan zaka hadu da wani abin alheri a can da zai iya fin karfin abinda ke bibiyan ku. Wanan kawun naku yasan komai kuskuren daga gareshine shiyasa yake jin nauyi a yanzu yadda zai gyara kuskuren nasa. Haka kuma ku din kuna da kariya daga Allah don kuna da alheri sosai kaida dan uwanka harma ince shiya fika. Cikin yardan ubangiji kuma kayi nasara a nan Habu don baka bar alherin naka ya salwanta maka, ba a lokacin don a yanzu haka kana tare dasu a hannu . Matsalan saidai kada ka yarda kai sakaci irin na dan adam kamar yadda iyayyen ku sukayi a baya11q. Kallonta yayi kafin ya katseta da fadin Mama kece matar nan mai maciji da tazo gidan mu a baya ko ya tambayi matar cikin mamaki ? Sai yaga tayi murmushi tana fadin nice naso fada maku komai a lokacin tun hakan ba faru ba amma mahaifiyar ka bata maida hankalinta ba. Zanso kubar yarinyar nan ta bashi maganin hannunta don mai gaba daya akai mashi itace zata iya kwatoshi ba tare da komai ya sameta ba koya sameshi. Amma bayan ita duk wanda zaice zai taimaka maku akan matsalarsa karyane hakan saidai maishi yaci kudin ku kawai. Nata dai din shine maganinsa don shi wanda ya bata makarin bai san iya amfanin shiba dabai bata ba itama tayi arziki dauko wanan abin daga wata kasa zuwa wajen ku. Ka tambayi dan uwanka dake kwance zai fada maka komai don yasani a yanzu babu maganin da yake sha da yake mai amfani kamar wanan da take bashi a boye. Mahaifiyar ku kuma ka fada mata nace inda ta nemo haihuwata tayi gagawan zuwa ta biyansu sadakansu idan ba haka ba an dinga bibiyan ku a cikin sauki sauki ana halaka ku. Su kuma wa,yan nan yaran dake cikin ku a yanzu sune saukinku dob kamar kariyane a wajenku. Saboda abinda ke bibiyan naku basu iya masu komai akwai alkawari a tsakanin su dasu tun na asali amma suma basu sani ba akwai dafa,i a jikinsu dashi kuma ake haifansu . Ko wani mahaluki daka gani a duniyan nan akwai wani sirin rayuwa a baya a tare dashi tun na kakaninsa saidai yai ta mafalkin abin ya dauka mafalkine kawai. Saidai mutanen yanzu basu sanshi ba kamar na da saboda wayewan kai da suke amfani dashi a yanzu sun watsar da komai na baya. Wanan yasa kaga ciwo yayi yawa ga dan adam naba gaira ba dalili da asibiti saidai su camfa kawai don su lalaba mutum. Don haka kuma muddin suna tare daku a gida daya wani mugun abu ba zai taba cin maku ba sai alheri saiko idan aka samu akasin hakan kamar yadda ya samu dan uwaka din. Falkawa yayi yana zufa duk da sanyin AC dake dakin amma zufa yakejin yana tsiyayya mashi abinda ya gani a mafalkin nasane ke dawo masa wace yarinya ke nan wai ake nufi ? Amma zai gwada tambayan J din kamar yadda ta fada yaji idan da wata yarinya dake bashi magani basu sani ba ? Idan har hakan gaskiyane dole ya fadawa mama dubu wanan magana asan abinyi shi wanan maimagini na Niger abinda ya fada masu ke nan duk yadda akayi wanan abin yana da salsala daga mama din ke nan. Allah Allah yake gari ya waye ya nufo gida don yana katsina yai wanan mafalki duk da ya dauka karyan mafalkine hakan don dadin barci amma zai gwada tambayan J din kamar yadda matar mafalkinsa ta fada. Abinda ya faru tun haduwansu da matar ya kama dawo mashi sabo gashi kuma shi J wani lokaci saiya kama salinta jikinshi na saba irin na macizai. Abinda da daure kai a cikinsa duk yadda mutum yai tunane abin ya wuce hakan gareshi Allah dai ya bada lafiya kawai za ace. Watau akidar nan ta mutanen baya kakannin kakannin mu da sukai ta shirka wa yan nan abubuwa suke bibiya wani lokaci don suna biye da zuri,a har karshen duniya don alkawarin da aka dauka a kansu. Shine zakiji ana fadan wani nada iska ko wance iskansu na gadone ai ko wani ciwo ya kamashi ba a san takamaimain ciwon ba Allah dai ya kyauta kawai za ace. Mafi A,a lah shine bawa ya koma ga Allah a kula da addua da sadaka da taimakawa bukata nakasa dakai komai kankantan alheri wata rana sai hakan yai maka rana. Da irin wanan tunanen a zuciyarshi ya shigo garin zaria kai tsaye gidansu yaiwa tsunke inda maigadi ya bude mashi get yai arba da kawu dake tsaye yana waya. Suma ido suka zubo mashi suna mamakin dawowanshi a ranan don ya fada masu sati daya zaiyi a can saiya tsaya yaga komai ya kankama ga aikin gidan man nasu da akeyi. Sai gashi kwana guda sunga ya dawo garin kuma koda ya fito mota wajensu ya nufa suna mai barka da hanya ya runsuna ya gaishesu. Lafiya dai ka juyo yau kawu ke tambayansa yace lafiya kawu wasu takarda zan dauka kuma sai an bincika yasa na dawo da kaina. To aida sauki hakan sannu da hanya na dai dauka don jikin dan uwan naka kajuyo kuma ince Jafar kan jikinshi Alhamdullahi jiki a na samun sauki sosai ai. Mikewa yayi zuwa part din ya J din inda ya samu Nafisa na shara ni kuma ina mopping a bayanta ya shigo muna gaidashi da hanya. Ya amsa muna tare da shigewa dakin da dan uwan nasa yake kwance da sallama dan juyowa yayi yana kallonshi yace Habu ka dawone ? Na dawo J ya fada yakai zaune saman kujeran dake gaban kadon yana fuskantarshi yayi mai ya jiki shi kuma yana tambayanshi hanya ? Jiki da sauki ya fada a hankali cikin yanayin ciwo ya dan kura mashi ido na dan lokaci kafin yace J akwai wata yarinya dake baka maganine bayan su mama ? A hankali ya juyo kanshi ya kurawa dan uwansa ido yana nazarin fuskansa da tambayan daya jefa mashi kafin ya mirgina kai gefe daya yana fadin . Meyasa kake tambayana hakan ina son in tabbatar ne kawai don wanan zancen na dawo garin nan amsa kawai nake son ka bani ? Shiru dakin yayi na dan lokaci kafin ya furu iska daga bakinshi bayan dogon nazarin daya gama a kasan zuciyar shi don bai san dalilin tambayan da dan uwan nasa ke mashi ba ? Akwai ya fada a takaice yana kawar da kansa gefe daya don sauraren abinda zai fada din game da zance. Wacece ita J ya kara jefa mai tambayan shiru na dan lokaci kafin J din ya juyo gareshi cikin tsare gida yana fadin kai inda aka fadama basu sanar dakai ko wacece ba. A,a sun daice in tambayeka kasan hakan zaka fada min ina son sanine don a tsaya ga magani daya ba tare da dora wani ba akan hakan. Ok to Rahama ce ta wajen ka tace daga gida aka bata makarune amma sirine bata son wani yasan da tana min amfani dashi kada a fahinceta ta bai bai amma gaban Nafisa ta fada min don kafa hujja koda wani abu ka iya tasowa. Rahama dai Rahama kanwar maria Rahaman nan dai dake waje na itace kuma naji sauki sosai don tunda na fara shanshi gabban jikina suka daina ciwo hakama kaina . Da wanan abin dake rike min makogorona duk yanzu na daina jinshi sosai a jikina karfin jikin ne dai da banda. Rahama ikon Allah Rahama dai dama abinda ake yawan nuna min ke nan akansune shine alherin da ake nufi tabbas hakan ne kuwa don a wanan tafiyan na hadu da maria. Kana yawan mafalkin ke nan kai ma ban taba dauka ita bace amma ina yawan ganin rabin fuskan maishi tana neman taimako a waje. Idan nazo in taimaka mata sai kuma inga nita taimaka saidai ban dauki wanan mafalkin da ma,ana ba sai yanzu da kake wanan maganan . Amma idan Rahama ce kuwa ,,,,,,, Me Rahaman tayi muryan mama dake shigowa ya baiyana a dakin da sauri ya habu ya dago yana fasin zancen aikin da yaran nan keyi mukeyi mama . Ki duba yadda cikin yan kwanakin nan yaran nan biyu kacal sun gyara wajen nan haka gwani ban sha,awa dashi wallahi. Ai kaidai bari kawin kuma saida yai wanan maganan jiya ni yaran nan na rasa irin haukan kurciyan su yanzuma kawun ku a kansu yake min magana waje. Wai mahaifin ita Asmau ya matsa da zuwa gidansa akan ya ban hakkuri kaga dai rashin su yasa munyi magani a tsanake so nake kowacen su takoyi hankali a gidansu. Duk da ita wanan Nusaiban da alama ba hankalin zata koya ba tunda ta saba zuwa gida ta zauna shiyasa wanan karon nake son su dauki lokaci a gidajen nasu har iyayyensu su fahnci rayuwan da sukeyi a dakunan su. Mata ku zauna baku iya komai ba sai kazantar tsiya da sherin duniya kala kala bayan wanan basu iya komai ba sai daukan kai su wata tsiyace. Aiko yanzu sun horu mama ki barsu su dawo hakana don Allah abinda takaici shi bai gujesu ba don halinsa sai sune suke kyamatarshi habu ? A gaban mu wanan yarinyar ta nuna hakan fa haba dai don kwatoshi cikin bari a horasu tunda ba tsoron su akeji ba mana abin yayi yawa shege da hauka. Idan dai zasu dawone su dawo kawai duniyace ai zata gyarasu gaba ina kawu ya tafine habu ke wanan maganan shi jafar yana kurum baice uffan ba a lokacin tunda aka dauko zancen matan nashi. Ya tafi kaidai wai yana da daurin aure bayan sallah kuma muka tsaya muna magana bai fargaba har lokacin ya dan shige. Ok mama wai nace ba don Allah wani tambaya nake son nayi maki kuma kada ki damu tambayane kawai jin hakan yasa ta zauna tana kallon dan nata. Nace mama ko a baya kin taba yawon neman haihuwa haka ko amsan wani magani kan haihuwa a wajen wani ? Magani kuma gaskiya kona taba ba zan iya tuna hakan ba wani abune akace game da hakan eeh to ance gaskiya. Don yadda aka fada min kamar kin karbo maganin bisa ga sharadin cewa idan bukata ya biya zaki koma ki kai masu wani abu . Sai kuma da bukatan ya biya mama baki koma ba wanan yana daga cikin abubuwan dake damun J a yanzu in ma ba ai hankali gaba dayan mu wanan matsalan zai iya shafan mu. A ina kaji wanan zancen Habu tana tambayan dan nata cikin zuba mata idanuwanta don jin amsan da zai bata don zancen ya taba mata zuciya sosai. A baya kan lokacin da bata haihu ba anyi neman magani duk wanda ya kawo kuma tana gwadawa ita yanzu yaya zata iya tuna hakan. Mama ina son ki tuno kafin kiji yadda zancen nan yake san nan kuma zancen maganin da J yake sha a yanzu duk za a dainasu akwai wani wanda zan ba Rahama ta kawo maki yana a mota shi kadai za,a dinga amfani dashi har kwana biyu a gani. Ko me kikace mama shiru tayi kafin tace a sanyayye a gwada din aiba a ki ta magani ba sai an gwada akansan na kwarai inji ba haushe . Yanzun ai lalube mukeyi a cikin duhu Allah yasa a dace din ya bashi lafiya shida sauran al,umman Annabi baki daya suka amsa da amin. Sai aiwa kawu bayani ya dan tsagaita zuwa wajen karbe karben da yakeyi din yanzu a gwada wanan din sosai a gani ta amsa da insha Allahu. Sun dan jima kafin ya mike zuwa part dinshi a gajiye anan ya sameni dauke da Abbati dakinsa ya shige matarshi ta bishi hakan yasa na fito zuwa part dinsu iya don nasan anty nafisa tana part din. Ina shiga na samu Saare tazo nasan kuma a nan zatayi weekend tunda alhamisce Allah ya gani duk da gidansune banyi maraba da ganinta ba. Haka na gaida ita a darare ina kokarin zama take fadin kai dan fillo miko minshi nan kafin na kaiga mika mata iya ta karbe da fadin dan fillo kuma kun basune ? Ai dole mu basu dan nema baisan kowa ba sai uwayenshi bakin kiuyane dashi iya baya yarda da kowa a gidan nan. Ki daina fadan hakan ran mahaifisa ba zaiyi dadi ba ranan dayajiki da aida gidan ubansa aka san asalinsa ba fannin uwa ba. Ai fulanin basu kadai bane ko ita Asmau asalinta ai fulanine saidai sun zama yan garin nan yanzu don ko yare basu iya ba gidan su. Nafisace ta fito daga daki tana fadin Ramaah mamace kadai a wurin yaya wallahi ban sani ba anty nafisa tunda na fito ban koma part din ba ina shiyan mu. Saida ta mede baki take fadin yanzu kune kuma masu kula da ya j din duniya tai maku dadi matanshi sun tafi kun maye gurbi. Haba dai Saare wanan wani irin maganan banzane zaki fada haka idan munyiwa yaya hidima laifine yaya mukaiwa ko kan mu ? Shike nan don matansa ba zamu kulashi ba ko suna nan ai dole mu kulashi tunda lalura ya kama na hakan kin taba gani mutum ya guji dan uwansa ? Zaki mayar min da zance wani abin kuma niba nufina ke nan ba gani nayi dai bai dace ba inda baku kulawa din ai mama ba zata iya ita kadai ba ? Oky hakan laifine ko to ba don wani abu mukayi ba don Allah da mama dashi ya J din mukayi inma kina zaton wani abune. Ta mike tana fadin nifa Nafisa ba wani abu nake nufi ba ato shiyasa ban damu da zuwa ba son gudun hakan da kayi magana ayi kokarin juya maka zance zuwa wani daban. Kallon mamaki nake mata nasan dai sabodani take wanan zancen a kofa suka hadu da mama dake shigowa tana fadin hayaniyar me nake ji haka wai ? Banda wanan figagiyar mai zubin yan ruwa kinsan ita bata rabo da abin fitina na rasa yadda yar nan ta koyi tsegumi a gidan nan. Meya faru Nafisa tace ba komai mama ba zaki fada ba kina tsoronta ne tace wai cewa tayi munji dadi an sallami matan yaya mun maye gurbinsu da mu barki ke kadai da kika koresu kiyi jinyar yaya din . Allah sarki ke kan kinyi hasara wallahi baki san takaici ba sun maye din sai ki dawo dasu dakunan su insan kin cika yar nema mara hankali. Daga zuwanki kina son ki haddasa min bacin rai abinda yaran nan keyi min ko biyansu nakeyi zan iya basu hakkinsune jinya wasane halan ? Kedai baki san harara ba wallahi ashe kema kyamar dan uwan naki kikeyi yasa kina cikin garin nan kikaki lekowa ki gaidashi ? Haba mama kyamarshi kuma to na sani tunda zancen ku daya dasu baki wanka ki bushe kina wajensu kina koyon iya shege don bandashi banga abinda suka karaki dashi ba. Ke Rahama yayanku Habu ya baki maganin da za a dinga bashi din ? Jin ta ambaci sunana yasa na dago ina fadin a,a mama bai bani ba bari dai in koma in karbo mashi na sakai na fita na barsu zaune. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,, 2️⃣ 2️2️⃣ 8️⃣8️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Daga kwancen da yake yake tunanen halin rayuwa yau shine a haka ake fama dashi mutumin da baisan dadin zama a waje daya ba ko yace yasan dadin hutu shiko a yaushe cikin ujula yake haka ya taso ya kuma saba da wanan rayuwa hakan yabi jikinshi sosai kuma don bai iya zama ba tare da yana wani abin da zai taimakawa rayuwansu ba a gidan. Yau sai gashi ubangiji yana ikonsa a kansa hutun dole na wahala ya sameshi irin hutun da bawa bai kauna a rayuwanshi sai in dole ya kama irin haka din. Yaushine matanshi suka hada mashi kai suke nuna mashi kyama da yake gani a idanuwansu karara tun suna boyewa har ya fahinci hakan da gaske. Gashi har Asmau don wauta irin nata har yarshi ta cikinshi take hana zuwa gareshi don kada cutan jikinshi ya shafesu tunda ance dasu ana kamuwa da wanan cutan . Don haka su kiyayeshi kada su kama dashi suma bai taba zato ko tsamanin ko kowa ya gajushi a duniya su zasu iya gudun shi ba haka yadda sukeyi. Hawaye masu zafine suka zubo a idanuwanshi duk yadda ake kai zuciya nesa yana kai akan matan nasa da ba haka yaso dasu ba sai gashi shi bai watsa masu kasa a ido ba sune zasu watsa mai akan cutan da Allah ya dora mai na jerabawa imani. Ajiyan zuciya ya sauke yana kara kallon part din nasa da yai shiru alaman ba kowa a lokacin tare dashi mamace da a zaune wajen ita kuma ta fita zuwa wajen iya. Su kuma yaran nan tun safe baiga gilmawan su ba dama sukanyi hakan suje su dan huta mama ko kawu su zauna dashi din tashi yake son yi ya gaza tun dazun so yayi ya dan mike ya kewaya bandaki amma babu kowa a dakin wanda zai taimaka mashi ya tashi daga inda yake kwancen. Fitowana daga part din iya naji gara naje can din in dubashi don yaya Habu nagida kada in takura masu wanan yasa na zabi hakan na nufi can da yaro a hannuna. Falon babu kowa banda niyar shiga dakin amma naga na dan lekashi ko idonsa biyu in gadashi lokacin hakan yasa na yunkura saiga Saare a bayana batayi min magana ba nima banyi ba . Na leka nishinshi naji yana yunkurin tashi zaune itama ta fado dakin da nata sallaman tana mashi sannu taimaka min in tashi ya fada a cikin yar murya. Ba tare daya amsa gaisuwan da take mashi ba sai naga ta dubi inda nake tana fadin meyake fadane banji shi ba nace yace ki taimaka mashi ya tashi. Bari dai in kira mama ta fada tana juyawa da sauri har tana bangazana a lokacin yaron na aje a gefe na karasa na kama hannunsa da sai ranan na taba kamashi irin haka. Ina mashi sannu ya mike zaune yana nishi Allahu akbar wai yaya J ne Allah ya mayar haka cikin dan lokaci fitsari nake son zuwa don Allah ya kara fada. Zaka tashine na fada a rude ya kada min kanshi dake duke yana maida numfashi hakan yasa na kokarta na tayar dashi tsaye na kamashi zuwa bandaki yana kokarin zama a toilet na fito daga dakin saiga mama ta shigo da saurinta tana fada. Yaya zaice ki kamashi kice baki iyawa inba shashanci ba mutum kamar jafar yana da lafiya zai tsaya sai an kamashine ? To kedai kina kusa ashe ya samu ya mike ko nace ehh mama na kaishi bandakin kingani ba shiyasa banson mu barshi shi kadai wallahi. Ta karasa kofan tana kiran sunanshi ya amsa daga ciki banji meyace da ita ba dai a lokacin na dauko yaron na fito falo tana zaune tana waya nayi niyar zama a lokacin amma sai na canza shawara zan fita. Ke wallahi ni tsoro naji ina zan iya zanga kamar zai sai gani tayi shiru tana watso min harara a fakaice fita nayi daga falon gaba daya. Don yanzu ban kaunar wani abinda zai hadamu kuma da ita kowa ya tsaya matsayinshi a gidan shiyafi sauki baya da gaisuwa ba abinda ke hadani da ita kuma. Na fita muka hade kuma da abokanshi da suka zo dubanshi mun gaisa zan tafi suke fadin don Allah yi muna sallama munzo duba J ne magaishe shi kice su umar ne da musa . Na juya ina fadin ya kewaya amma bari in fadawa mama idan ya fito na shiga na samu mama a falo take fadin ashe kin fitane Habu ya bada maganin ? Ban shiga wajensu ba mama yanzu can na nufa dai akwai wasu a waje sunzo gaida yaya umar da musa gashi ko ya kewaya nace na fada masu ai yana bandaki. Bari mugani idan ya fito kice ya shigo ta shiga kuma naji tana kwala kiran sunana hakan yasa nabi bayanta ina amsawa. Kinga kayan nan nake son akwashe na manta dazun in shiga dasu ciki nace barin kwashe mama na gyara gadon kafin naji fitowansu tana mashi sannu take fadin ya taka a hankali dai. Magana yakeyi banji ba naga tayi dariya tana fadin yace ki fesa mashi kamshi a dakin kinsanshi sarkin son kamshine. Na dauko kamshin na fesa har zuwa bandakin sai kuma na shiga nayi flushing na wanke wajen nagama na fito yana zaune bakin gado yake gaidani da kai na kawar da kaina gefe ba tare dana amsa ba. Ni har ga Allah bala,in tausayin bawan Allah nake ji mutum mai kawaici da mutunci irinshi shine a haka yau lalai bawa ba a bakin komai yake ba a wajen Allah. Muryan mama ya katseni da take fadin kicewasu umar din su shigo na amsa da to na koma daukan Abbati in fita dashi saidai hannusa yana cikin nasa hakan yasa na isa nayi masu iso suka shigo. Ina gaba suna biye zuwa dakin hakan yasa naji jan tsukin da Saare keyi bandai kulata ba na dauko yaron na fito suna gaisawa don da shiga umar din ya soma fadin ikon Allah Alhamdullahi J kaine a zaune yau ? Masha Allah gaskiya jiki ya soma kyau Allah yasa hakan kaffarane a gareka mamace ta amsa da amin gaskiya mama naji dadin ganinshi a yau din nan ikon Allah mama ta karbe da ikon gaskiya. Na samu ya habu a falo yana cin abinci na sake gaidashi zan shige yake ambatan sunana hakan yasa na juyo gareshi alaman akwai maganan da zaimun ke nan na karasa gabab shi na tsaya. Ki zauna yace dani hakan yasa na samu waje na zauna dan nisa dashi kadan ya dan dauki lokaci kafin ya ture plate din yana aje cokalin ya kalloni yana daukan abin goge baki yace. Rahama tambaya nake son maki kuma banson ki musa ki fada min gaskiya iya abinda kika sani zanj dadin hakan idan baki toge ba. Gabanane ya fadi yace wani magani kike ba J a ina kika samoshi kuma waya baki ki bashi shi ya jero min tambayan a lokaci daya ? Magani ? Na fada a sanyayye ya amsa da eh magani wanda kike bashi nake son jin karin bayani daga bakin ki ? Ke Rahama kece keba yaya J magani as how hakan ya faru Ramaah waya baki magani ki bashi Ramash innalillahi wa inna alaihim rajiun kin kasheni Ramaah ? Kaina dago na dan kalleta da mamaki a daidai lokacin ya habu ke fadin haba mana maria ki bari mu saurareta. Dole tana da dalilin yin hakan wa zai turota wajen mu balle kiyi tunanen zatai poisoning din shi kawai ina son ji daga bakintane kawai yayi maganan a cikin hikima. Jin abinda ya fada yasa hankalina ya dan kwanta ina fadin ni ba kissa zanyi ba taimakonshi nayi don ganin irin wahalan da yakeyi. Ki taimakeshi Ramaah ina kika san wani magani da zaki iya taimakawa dashi Ramaah ? An fada maki haka ake shan magani ba tare da kasan aikinshi ba haba anty maria nifa Dage ya ban makaru lokacin da muka je ruggan mu shine nake bashi yana amfani dashi yadda yace ayi. Ina fadin Dage ne ya ban naga takai zaune rugwaf saman kujera tana dafe kirjinta da hannunta biyu ta kara maimaita sunan da fadin Dage Ramaah ? Baki na turo ina fadin to meye a dakin baffa fa ya debo maganin tunda yasan duk aikin da sukeyi ninace ya debo min shi kuma ya debo. Ramaah baki tsoron baffa ya sani koya sani tsakaninshi da dagene nidai na karba kuma na bashi kudinshi. Kasa magana tayi sai bina da kallo da takeyi baki sake ga kuma alaman tsoro a fuskanta saida mijin nata yai magana ta juyo da kallonta gareshi. Koma dai meye maganin yayi don haka shi za,acigaba da mashi har muga aikin maganin don tun ranan data fara mai amfani dashi ya soma samun sauki a jikinshi. Ban son wanan zancen ya fita ku kama bakinku kawai ku dai san halin gidan nan yanzu dai zaki dauko min maganin in kaiwa mama da sunan nina karbo mashi a daina bashi a boyen da akeyi. Jeki dauko maganin mu gani haka na juya jiki ba kwari zuwa cikin dakina na dauko maganin can kasan jakata inda na boye mai yawan saidana rage na fito da sauran na kawo mashi. Shane da kunu ko da madara ko wani abu dai hakka mai dan ruwa saidai idan ana amfani dashi mutum zai kiyayyi duk wani abu mai yauki kada ya cishi. Na bashi na magarya da dutsen tama da za a nemo ya amsa yana mamaki ya fice daga part din sai lokacin ta samu daman magana. Fada sosai tayi min tare da min kashedin irin wanan babban kuskuren dana tafka din da kada in kara irin wanan wautan idan wani abu ya sameshi fa ta sanadiyana ? Ni dai kasa magana nayi don sai a lokacin tsoro ya kamani don sam tunanen hakan baizo min ba da farko sai yanzu din data fada. Saare aka turo kirana nazo suna zaune har da kawu yaya Habu ke fadin ki duba wanab maganin da kyau kece zaki dinga ba yaya J shi safiya da yamma don Allah a kula akwai wani na wanka da za a kawo shima nayiwa mama bayanin komai. Na amsa da to ina karban maganin da yafito a wajena gashi kuma a yanzu ya sake dawo min mikewa nayi jiki na rawa sai lokacin naji yaya habu na fadin ita Nafisa don dan magana ya hadata da Saratu shine zatayi fushin zuciya tace gida zata tafi ? Ke Rahama kira min Nafisa na amsa da to na fita da sauri don a tsarge nake dama a falon ganin daga kawu har ita mama basuyi magana akan maganin da yaya din ya miko min ba. A zaune na samesu dasu iya ga jakkar kayanta a gefe daya tana duban wayanta nake fada mata sakon yaya din. Na fita don ban tsayawa saboda Saare dake falon kwance da waya a hannunta tana charting part din mu nakoma yayata tana zaune tayi tagumi cikin damuwa. Yaya kukayi dasu take tambayana maganin na fara nuna mata kafin na zauna ina fadin Allah ni da zuci daya na bashi wanan maganin kuma Nafisa tana wajen itama. In Nafisa na wajen fa Ramaah kiyi tunanen Nafisa aiba uwarsu daya ba dasu baki gudun ace an hada baki dake a cuta mashi. Shiru nayi ina wiki wiki da idanu don sai yanzu nake hango zalla yarintar danayi na daukan wanan risk din don ba karamin magana bane idan ya fita anji . To ya zanyi aikon gama ya gama sai fatan Allah ya kiyayye yanzu kan don mai faruwa ya riga da ya faru magani kusan sati daya ana sha yanzu meya rage kuma. Da yamma saiga su yaya sun dawo da wanan abinda na fada na karya asiri ba a bata lokaci ba mama ta dafa aka kai mashi ya diba yasha yayi wanka. Yana fitowa ina tsaye na kada wanan maganin kamar yadda yay habu ya fadi dokansa ya amsa ya shanye gaba daya ya miko min cup din tare da godiya. Ya tambaya ko magariba yayi mama tace kamar da sauran lokaci nafisa dake shigowa tace an fara kiran sallah a wasu wuraren ai. Saida yayi sallah magariba kafin ya kwanta kamar karamin yaro ya dunkule a waje daya lamo kallo daya zakiyi mai ya baki tausayi. Ina ganin haka na nisa ina fadin Allah ya sauwaka na fita da kayan wajen zuwa kitchen dinsu da yanzu yake samun gyara don anty Nafisa ko yaushe tana tsabraceshi. Tunda na dawo nashige dakina ban fito ba sai washegari nayi shirin school na fita na biya part din na gaidasu mama ke fadin jiya ina ta jira ki dawo baki dawo ba kodana aika akace barci ya daukeki. Nace ko kema kin damu da zancen shashan nan Saratune ai ita tazo muka kwana tare tunda Asuba ta gudu wajen iya wai batayi barci da dadi ba a nan. Nayi murmushi ina fadin mama maganin fa ina son shiga school kada in makara to sai ki hada din ki bashi tunda maganin yana da ka,idan sha ? Nayi mamaki jin furucinta na ka,idan sha watau yaya habu shima ya nunke su mama a baibai ke nan don kada su gano wani abu kome ya fada masu oho ? Da sallama nashiga duk sa safiyane sosai amma na samu har yayi wankan maganinsa yana kwance yayi rigingine jikinsa saye da farar jallabiya mai dogon hannu. Gaidashi nayi da yaya jiki ya amsa da Alhamdullahi nagode na sada kai kasa ina fadin zan shiga school ko za a hada maganin yanzu ? Har na gama kadawa idonshi yana kaina har na gama na miko mashi ina fadin gashi yaya don yanzu ba sai an rike cup din ba yana iya rikewa yasha da kanshi. Ya dan dago daga kwancen ya karba yasha ya miko min cup din yana godiya ya koma ya kwanta a yadda yake bankai ga fita ba naji yayi wani irin gyatsa yana hamdallah. Kodana fito ban tsaya ba nayi masu saina dawo na samu Nafisa zaune da mama suna magana a lokacin bandai san akan meye ba. Daga kwancen da take daki lamo jin ba motsin kowane ta daga waya yana ringing sai can aka daga ta wayan ke fadin ai wallahi Saare nayi fushi. Ta amsa da fushin me tace wai ace tunda nazo kaduna baki kirani ba haba saaratu amana baice hakan ba ai, na zata kece ta farko da zata nemeni sai naji shiru Allah nayi fushi sosai da hakan. Haba dai tawa nifa sai jiya na samu ya kara dawowa sai kuma na samu wai baku nan dukkan ku iya ke fada min shirme wai kuna kyaman yaya yasa mama tace kuje gida har ya samu lafiya. Humm ni bansan me zance ba banda wanan sakariyar Asmau data fitar muna da zance a fili yar iska ko an fada mata inma kanjamaune haka ake kamuwa dashi ? Ba kanjamau bane wallahi don yanzu yaya yaji sauki sosai ba kamar yadda nazo a ranan na sameshi ba yanzu har tafiya yakeyi da kansa. Don Allah ki bari ! Tace wallahi ko saidai abinda banji dadinsa ba shine wai fa Nafisa da yarinyar nan Ramaah suke taya mama jinyarsa. Su kuma wallahi iam telling you don nayi maganan hakan baiyi ba shine munafuka Nafisa waina nuna ba mama ta haifeta ba kar kiso kiga fadan da mamake min fada wallahi akanta. Nafisa fa ita har ta samu wajen hadaki da mama ke nan bari yar iska kanta zamu koma ksi ba ita ba har wanan mai ido kamar glove saita bar gidan nan shiri nakeyi sosai wallahi. Mutumiyar kin min daidai wallahi ina son ki wajen aiki da zafinsa ai dama kin gansune yadda suke rawan kafa su kakansu ta yanke saka yan iska don a yabeau wai ? Tsiyar banza wa zai yabesu din sunyi a banza wallahi zan matsa naga na dawo ko wata yar iska saina koya mata wayau a gidan nan. Ina yinki nawa Saare din ta kara fada har da fadin Allah yasa kin hada da wanan yar iskan duk su tafi su bamu gida wallahi ni gaba daya haushi suke bani Allah na tsani wanan maria din wallahi haushinta yasa bani kaunar kanwarta din itama. Sun dauki lokaci suna sherin su har mama ta shigo ta sameta duk da bataji sosai ba ta fahinci da Saiba take wayan a lokacin. Saida ta fitone tayi mata kaca kaca ta zageta tas tace kuma zata dauki mataki akanta tunda abinda ta daukowa rayuwanta ke nan munafunci. In ba rashin sanin ciwon kai ba dakece za a hada kai ana mugunawa dan uwanki saratu matan nan fa cewa sukayi suna kyamar shi. Watau ya dauko mugun ciwo kada ya saka masu shine nufinsu ko ? Mama ai cewa ake wai wanan ciwon mai karya garkuwan jiki ya kwaso a can wajen kwatakwali shine,,,,,,,,, Mama dubu bata bari wanan matar takai karshe ba ta karbe da fadin Allah ya kare al,umman Annabi baki daya. Duk wanda yaiwa yaron nan wanan sheri yaga abinsa insha Allahu watau su gasu sakatkaru shine suka yarda da hakan ko ? To mama kokece kikaji haka da ake fada ai zaki kama kanki tunda gari haka ake fadi sai lokacin Nafisa data shigo tayi magana take fadin wallahi ba kowa ba kan sai dai yan sheri . Amma kowa yasan ciwon yaya kamar sammu ko jinnu ke damunsa ta ina ciwonsa yayi kama da wanan ciwon don Allah ? Koma an fada banda jahilci ai suma ke nan suna dashi ko tunda mijinsu akace yana dashi har insun yarda. Rana mama tayi kuka sosai saida kawu yazone ake mayar mashi yace shima yaji wanan zancen kuma mutane dama haka suke meye na damuwa haka da zancen duniya. Ni sai da yamma dana dawo anty Nafisa take min hiran abinda ya faru nace Allah ya kyauta mutane akwai daukarwa kansu wahala. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,, 2️⃣9️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, A cikin yan kwana biyun nan na rage shiga part din yaya dubashi sosai nakan shiga da safe na bashi magani da yamma kuma in koma in bashi dama sau biyune shan maganin haka nice zan tsaya in gyaro dakin har bayi in wanke in hada kayan daya cire na wankesu. To dana gama nabar part din ke nan ba zan koma ba ina dakina kwace ina karatu ko kuma ina game a wayata don rage damuwa. Ba komai yasa hakan ba kuma don kaucewa surutun da anty Saare ta farayi a kan mu nida yar uwarsu saiga anty Salima ta samu pass ta dawo. Ina dakina naji muryanta suna gaisawa da anty na hakan baisa na fito ba saida naji tana fadin ina Ramaah namike na nufo falon a daidai kofa na tsaya na rike labule ina fadin sannu da dawowa anty Salima. Come up kina jina ashe kika share haka zakiyi min oyoyo daga nisa nayi murmushi na karaso tana dauke da Abbati a hannunta take fadin. Wai sannuku da fama fa mama ta fada min irin kokarin da kukeyi keda Nafisa Allah ya saka da alherinsa itama iya ance jikin ba dadi nace ai dole tana kallon masoyinta zai chala ai dole ta damu. Wallahi yaya kan yaji jiki Yanda tace wallahi maria saida naji tsoro dana ganshi wai kuma yaji sauki ke nan yace. Aiki bari abin akwai tashin hankali wallahi ni naga kokarin su Nafisa da Ramaah da ke iya zuwa ko wani lokaci dasu ake jinyasa din. Sunyi kokari ba kadan ba maria su yan iskan matanshi ai gara da mama tayi masu haka ta korasu gidajensu tunda jira suke ya mutu wai har sune zasuce suna kyamatar yaya don Allah fa maria ? In banda aure mukkadarine me yaya ya gani a wajen wa yan nan yan iska abin namijine kawai wallahi dama mama tace kada su dawo gidan nan tunda abin nasu iskancine haka ? Anty Salima kun gama ke nan nake tambayata saida kalloni tayi dariya tace da saura Ramaah saura wata hudu mu karasa yanzu. Nayi mata fatan Allah yasa a gama lafiya ta amsa min da amin ta mike dauke da yaron a hannunta don ta hadashi da sweet din da yake kokarin budewa a lokacin. Ramaah taso muje mana ta fada adaidai kofan fita daga part din data tsaya hakan yasa na yunkura na nufeta. Wayana da yai kara shiyasa na koma dauka har ta wuce ban samu binta ba wata course mate dina ta kirani take fada min zancen test da za ayi wanda asali ban samu labarin hakan ba mun dan jima muna magana kafin mu kashe wayan. Salima ta jima da fita don shi ban bita ba don bansan inda ta nufa ba a lokacin dama kuma banda niyar fita lokacin na share muna fira da yar uwata. Tana fita part din ya J ta nufa da yaron a hannunta suka shiga mama na falin ita da baki suna hira don haka direct dakin yaya din ta nufa ta kara dubashi don ta jima wajenshi dazun kafin ta fito zuwa part din mu. Zama tayi tana mashi ya jiki ya amsa da sauki yana zaune ya jigina jiki da gado laptop dinshi a saman cinyarsa ya mike kafa yana taba system din. A ina kika daukoshi yake tambayanta akan yaron take bashi amsa da part dinsu naje na daukoshi aina zata yana da kiuya har yanzune ? Bai yarda da kowa a gidan banda Ramaah sai uwarshi dasu kadai yake yarda su daukeshi. Tana ina ita Rahaman yake tambayanta ba tare da ya dago daga abinda yakeyi ba a lokacin. Tana can ai tare zamuzo sai ta tsaya recieve din call ba zata zo ba ai don yanzu itama kamar gudana takeyi . Gudunka kuma yaya No ba ina nufin na kyama ba kullum itace ke ban magani safiya da dare ta kuma gyara min dakin nan but saidai kamar akwai abinda wani ya fada mata game da hakan da takeyi. Haba dai ya J ban tsanmanin akwai wanda zai fada mata wani magana game da kai ta yardda kawai dai kila don taga ka fara samun lafiyane yasa haka ? Amma Ramaah mutum ce mai kaifi daya tana da gudun zuciya ai kaga duk abinda zai hadata da Saare tana kaucewa don nasu baizo daya ba . Duk kokarin yarinyar nan a kan mu wallahi saida Saare tasa ta canza mata indai ba yanzu a bayana suka shirya ba ko shiga komai daya shafi saare batayi a gidan nan. Laptop din ya rufe ya dago yana sauke ajiyan zuciya yace abinda nake zargi ke nan a zuciyana tun dawowan saratu gaba daya yaran suka dauke kafansu da part din nan don haka akwai abinda tayi masu da ba,a sani ba game da shigowan nasu. Sosai ya sake jiki da salima suna magana wanda ba wanan bane farkon hakan sukan danyi shawara a tsakanisu wani lokaci dama. Shigowan mama da bakin suke fadin zasu tafi Allah ya bashi lafiya ya kara tsarewa wanan yasa suka daina hiran da sukeyi din a lokacin. Koda yamma yayi anty Maria ce ta tuna min don ina daki ina duba takarduna hakan yasa na fito zuwa part din iya inda na samu anty Saarece kadai tana girki gaida iya da yanzu ba kasafai take fita ba ko yaushe zaki sameta a falonta zaune don bata dogon tafiya. Saidai da safe zata kokarta ta shiga wajen jafar din kafin rana ya haska kuma ta fito idan ta zauna sai kuma washegari zata koma fita wani lokaci kuma zaikai sau biyu tana lekashi. Lafiyane bata dashi yasa akace ta dinga zama a waje daya kada ta dinga yawan fita rana saita dauki hakan ya zamo mata dabi,a yanzu. Mun dan taba hira na fita don in samesu a can din ban kaiga fita nake jin Saare na fadin ashe iya mama ta hakkura ta janye kudirinta akan matan yaya J jibi zasu dawo ? Iya tace to ai gara ta janye din su dawo ko yaran nan zasu huta duk da ko sun dawo din aiba wani tsiyar zasu tsinana banda fitina da bakin kishinsu. Ai gara dai su dawo din duk wasu masu rawan kafa saboda kwadayi da munafunci suna jin dadin sun tafi ai zasu kama kansu yanzu kam. Keko kikan fara tsiyar ki ke nan na zata maganan kirki kike min ashe da wata manufa kike wanan maganan ? Da wata manufane mana in bashi ba iya daidaine ace wai don sun tafi su suzake haka suna wanan shishigin akan yaya don Allah ? Wai fa yarinyar nan Ramaah itace harda gyaran dakin yaya tayi wanan tayi wancan saboda kilibibi irin nasu. Inma kilibibine dai uwarki ta saka suyi ai don haka itace babban kilibabban ke nan ke bakiyi ba Allah ya kawo masuyi baki a laikum kuma zaki dauko sirfa ki saka a zancen waiko yar nan kina tuna mutuwa kuwa don Allah ? Yanzu laifine zaman amanan da yaran nan keyi damu a gidan suna iya bakin kokarin su wajen ganin sun kyautata muna amma ke ko yaushe kushesu kikeyi ? Anya kuwa saratu kinwa kanki tanadin alheri kuwa haka kikaga yar uwarki nayi gidan nan baki da zance sai bakin ciki da hassada da hade haden fada tsakanin matan yan uwaki da duk wanda ya zauna a gidan nan don ya lakaci arziki. Daga daki da salima take kwance tana jinsu ta fito tana fadin balle ba wanan zancen don yaya yace sai sun fadi wanda ya fada masu yana da wanan cutan a jikinshi a zauna kotu. To ai kinji irinta banga laifinshi ba wallahi gara yai masu hakan tunda basu da kwabo a idanuwansu banda shirme kalar tasu yau in yana da cutan nan ai sungama kamuwa suma yadda ake fada. To Iya ni kuma su sukace na fada masu hakan kome iya taja tsuki tana fadin ke arr tir da wanan halin naki tunda sunce a bakin yan gida sukaji wa zai fada masu in bake ba ? Sai ki shirya don ba zancen dawowansu gidan nan da har kike murnan hakan da zasu dawo ko zasu dawo gidab nan ba yanzu ba kuwa . Sam bata san Salima tana dakin ba da bata dauko zancen da iya ba don a zatonta Salima na can part din jafar din data barta yasa take wanan hiran da iya din. Tsuki taja ta koma daki kayanta take gyara dama tagama ta fito daga dakin a dan fahintar ta akwai kamshin gaskiya ga abinda suke zargi don wanan zancen da yar uwarta tayi tabbas da yarinyar nan Rahama takeyi. Suna falo zaune da baki da suka shigo daga wancan unguwar tasu don haka bayan na gaidasune nake gaida yaya din da jiki ya amsa da Alhamdullahi. Jikin idan yabi da hakan insha Allahu an take Allah ya mayar da aniya ga maishi wata daga cikin matan ta fada. Kai tsaye na nufi dakin na shiga na gyara na fito na gyara wasu part din da babu kowa a wajen lokacin matan suka mike har mama zasu tafi ita kuma zatayi masu rakiya. Bayan fitansu nayi kokarin share tsakiyan falon duk yana zaune muryanshi naji yana fadin meke hanaki zuwa gaidani yanzu ? Cak na tsaya da sharan na dago ina dan dubanshi yace bakiji me nace ba meke haki zuwa dubana kamar yadda kikeyi a baya ? Ba komai yaya ina zuwa school ne yanzu din na bashi amsa a saukake don gudun ya fahinci wani abu. Amma sai naji yace ba gaskiya bane da can baki zuwa school ne kike tsayawa kulani ? Shiru na danyi don ban san me zance dashi ba again ya sake fadin kin taba ganin likitan da bai duban mara lafiyansa a kai akai ? Hakan ya bani dan murmushi kadan wanda dana sakeshi a fuskana ba tare dana san da zuwansa ba ,wai nice likitanshi yake nufi. Sosai abin ya ban dariya Ramaah dama ashe nan kika nufo muryan anty Salimace na dago ina fadin nazo ance Iyatu bata nan yau shine nake dan gyaran wajen. Dazun fa naga Nafisa na gyaran wajen nan ban kula taba naci gaba da aikina ta zauna suna zancena da dan uwanta dake zaune ya harde kafafuwanshi saman table. Sai dana gama na fesa kamshi na dan rakube ina fadin yaya a zuba maganin yanzu ko sai anyi magariba ? No banda zabi ai duk lokacin da kika ban zansha idan yanzu ko sai anjima din duk dayane hakan yasa na juya zuwa inda flask ke ajiye a ciki muke zuba mai kunnu koda zaki buda yana turiri da zafinsa. Sabon flask mama taba Nafisa ta sayo don hakan suna kallona na dauko maganin na hada na dinga juyawa daga tsayen da nake. Saarece ta shigo falon fuskanta a daure saida ta kallo inda nake takai zaune tana gaidashi yace ina tashiga tun safe bai ganta ba ? Dan kame kame ta soma wai ai tazo yana barci sai kuma bata dawo ba lokacin dana kowa kai kunnu na mika mai ya karba yana min godiya bai tsaya jirab komai ba yayi bissimillah ya kafa kai ya soma kwankwada. Yana sauke cup din mukai mai sannu ya amsa yana gyara zama Saratun ke fadin amma yaya gaskiya kabar shan magani haka barkatai da baka san asalinsa ba . Wanan abu haka kamar wani,,,,,. Shima ai lalurane ya jawo hakan haka kawai mutum ba zai dinga turawa cikinsa magani ba ai, salima ke bata amsa. Ki bari na fada mashi tunda akwai wanda asibiti suka bayar a dinga sha wanan aisai a cutawa mutum wani ciwo na daban kuma yazo ya kama mutum wurin shaye shaye. Saare ko guba Rahama ta ban zansha a yanzu don kwai taji dadi saboda yadda hankalinta ya tashi akan ciwona lokacin da aka fara kyamatana su din basu gujeni ba. Suna tare da mama a part din nan suna taimaka mata ko ciki daya muka fito iyakar ke nan ai abinda yaran nan ke min Allah ne kadai zai saka masu da alherinsa amma ba zan iya masu kwatan kwancinsa ba. Baya na koma na sake shigewa cikin kitchen din nasu don banson su san da naji zancensu don saida ta bari na juya zuwa dauraye cup din ta soma fadin hakan. Ina jin amsan daya bata din yasa na fahinci ya gane me take nufi. Daidai ina fitowa naji ta sake fadin Allah sarki su anty saiba sun damu su dawo dakunansu wallahi amma mama taki yarda kome yasa mama takeyi hakan oho ? Shine ai Saiban ke fadin kodai ana zarginsu da wani abu na dabanne yasa mama cewa su koma gida su jira Allah ya baka lafiya. Da suna da wayau aida basu tafi ba saidai su turo mutane a bata hakkuri amma sun nuna abinda take zarginsu dayi hakan gaskiyane ke nan a yanzu. Nidai har na bar part din suna zaune ban kuma koma wajensu ba na fice zuwa part din mu na zauna ina tunanen kalamin ta tana nufin mune zamu cutawa yaya J din ke nan ko ? Dama abinda yar uwata ke gudu ke nan gashi ko hakan ya fara baiyana a bakin saare din nidai bansan me muka tarewa wanan matar ba na fada a raina. Da ace tasan cewa nice sanadin samun wanan maganin ga yaya aida abin yafi haka ke nan da yanzu ta zarga min wani sheri da zancen yar uwata ya tabbata ace mudin yan tsafe tsafe da gaske. To zancen yaya nasan kamar a kunnen matanshi ya fada don sai ta kwashe komai ta fada masu kamar yadda anty Nafisa tace ita ke kwasan sirin tana fada masu wanan wani irin sune takewa matan dan uwan nata hakane wai ? ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,, 3️⃣0️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Zan iya cewa a yanzu har da wasu aiyuka na daina shiga taya mama a part dinsu sai dai lokacin shan magani bayan maganin na rage yawansa nace kuma ya kare a karshe don haka na daina wanan sintirin na kama kaina. Idan na fita tun safe ban dawowa gidan sai ana gab da magariba zan shigo inyi sallah in kwanta sai kuma da safe idan zan fita zan lekasu inmasu ya maijiki wata ranama don sammakon dana tsiri yi nakan samu yana wanka a lokacin bai fito ba na gaida mama in juya abina infita. Itama Nafisa ta tafi bukin dangin mamanta a kauyen nan zaria din wani gari da ake kira da fanbeguwa mahaifiyarsu yar can garin ne sun kuma kwasa sunje buki. Sai ya koma daga mama sai yan mantata suke faman dawainiya dashi don sune dama doleshi ai mu karan taimako mukayi masu amma Saare bata gane hakan ba. Duk da ya danji dama yana iya wasu abin da kansa don bawan Allah nan Allah ya bashi karfin halin ciwo da dauriya a kwancen dayaji dama a haka yake gudanar da bussiness dinsa abinka da rai da guri. Amma sai hakan ya zama gajiyarwa ga kannen nasa dukkansu kowa na korafi a gefe da basu samun hutu ko kadan daga ayi wanan sai gyaro wancan mama ke sakasu. Anty salimace tashigo part din yar uwata a gajiye tana zama take fadin wayoni maria bayana zai tsage ? Anty maria take fadin garin ya ke kuma ta dan kai kwance tana fadin ke matar yaya kinsan irin wahalan da mukeyi kuwa mama bata bari mu huta sam wallahi dakin dan zauna yanzune zakiji tace tashi kiyi wanan ko dauko abu kaza ki gyara. Duk wanan mai bakar aniyarce Saare taja muna haka wallahi ni nasan Ramaah da Nafisa fushi sukayi din abinda saare din ke masu. Ai wani abu tayi masune maria ta tambaya tace bata fada maki ba ko dadina da Ramaah ke nan ai bata faye irin surutun nan ba ita. Maria ta sake fadan wani abin ya farune tsakaninsu tace ai kinsan halinta da sakin magana Nafisa kuma ta nuna mata ko ita waye. Nasan hakan da Ramaah ta gani yasa dauki zancen ta daina shiga itama tana aikin ladanta gabadaya ko dazun nan wallahi saida yaya yayi min zancen sun daina shigowa kome ya faru ? Sam bata fada min komai ba wallahi kinsan halinta da zurfin ciki ai haka kuke fulani sai dai in kun tashi fada baku duban bakin gatari kuke sarawa. Au sheri zaki min ke nan kuma yanzu ai naga kema da baki iya hakan ba da yanzu kin bar gidan nan akan sherin matan gidan nan. Nice na fado falon da sallamana ina ganin ta nayi murmushi na karasa shigowa ina gaidasu da gida suka amsa min take fadin. Cigiyar ki nazo yi Ramaah yaya yace kun dauke kafan da part dinsa bai san dalilin hakan ba a yadda na kula kuwa hakan ya dan dameshi. Ni kuma aiko dazun da zan fita nashiga mana da safe yanzun nan kuma dawowana ke nan ai ban zama yanzu zamu soma exam yasa hankalina ya dauko. Kyaleshi kinji kinsan halin yaya J ai da damuwa da wanda ya damu dashi yanzu dan kulashon da kukeyine yaga kun daina shine yake wanan magana shi haka yake da damuwa da mutane shiyasa ake saurin kamashi. Dan kallonta nayi na kau da kaina gefe ina wasa da Abbati daya zo ya fada jikina ban jima ba na mike da yaron zuwa ciki. Nasan dai ta fita tunda naga anty Maria ta shigo dakin gab da magariba take tambayana meya hadani da Saare na dago ina fadin Saare kuma ? Yaushe ba abinda ya hadani da ita take fadin in daiyi sannu ita ba don mama da ya habu ba ba zata yarda ina sintiri a part din yaya J ba. Tunda tasan halin matanshi ba mutuncine dasu ba hakama Saare din na dai share zancen zuwa don ban bata amsa ba. Saidai a kasan zuciyana ina tunanen me akace ya hadani da itane wai tunda bakina da nata dai bai hadu ba duk bare baren da takeyi a kaina din. Tunda bata nuna dani takeyi ba akan me zan tsaya nuna mata nasani balle yanzu dana kama kaina da shiga part din da sunan jinya. Shima kuma addua muke mashi Allah ya bashi lafiya ya mike don ba mai fatan ya tabbata a hakan da yake din. Na share hakan kwana biyu kuma ranan weekend na gama wanki nayi wanka sai gata again wai yaya J yana kirana. Saida na shirya naje suna falo zaune na shigo nake gaidasu da kwana suka amsa min yake fadin Rahama lafiya kwana biyu na daina ganin ki ? Ita Nafisa ance tayi tafiya amma ta dawo jiya sai a lokacin ma nake jin cewa su Nafisa din sun dawo daga tafiyan. Nake fadin ba komai yaya exam zamu soma yasa ban zama yanzu exam zai hanaki shigowa ki duba yayan ki Rahama ? Sai nayi kasa da kaina bance komai ba don mama data kura muna ido tana sauraren mu itace ta kawar da zancen tana fadin yace kiyi mai irin ferfesun da kikayi ranan ya tsaya kuma tareki da tambaya. Wayyo Allah da mama ta sani ko shi yaya din da basu sakani wanan aikin Allah bai hada jinina da kifi ba duk bafulatanin asali haka yake inba mu fulanin zamani ba . Sam bafulatani bai cin kifi ace zaki dauki spoon ki motsa miyar kifi ki kuma dauka ki motsa miyar naman dashi ko one spoon kikai a bakinki a ranan idan kin soma amai kamar zaki amaye duk hanjin cikiki. Amma don kawaici da alkunya haka na mike zuwa kitchen din nasu na soma aikin hada ferfesu din ina gamawa na bude fridge an kawo kifi mai yawa da gani sabon zubawa ne ballo na wanke na hada. Ban fito ba saida na kammala komai na zuba na nufo falon dashi na samu mama bata nan ta fita saishi da wani abokinshi a falon suna hira. Sallama nayi na aje tare da gaida abokin nasa ruwa naje dauko mashi naji bakon na fadin kai mutumina wai dama kayi sabon aurene ban sani ba ? No wander naga alots of changes a tare dakai da kuma yanayi yaushe ka auri wanan african queen din banda labari ? Yanzu daka sani ai bai baci ba gashi kun gaisa amma gaskiya ba ganin fuska ba wanan karo kan ka tsaya ka zabo abinda ya dace dakai. Allah ko ya fada hangoni dayayi tafe ruwa na dauko masu da drinks na aje gaban bakon daketa faman sabarin baki ga abokin nasa. Godiyana ga Allah banyi kwaron hannu na dafa kadan ba tunda nasan mama da yaranta na wajen sai kuma Allah ya turo wanan bakon nasa yazo. Furcina yasa bakon dan kallon mu da nake fadin nagama yaya shike nan ko akwai wani abin naji yace jeki Rahama zan nemeki idan mun gama. Zo amarya mana kada ki tafi ban sayi baki ba bayan abincin da kika karrama ni dashi haka tun ban ciba kamshi ya danne hancina kudi ya dibo daga aljihunshi ya miko min na dan dubi yaya din yai min alaman dana karba. Naji bakon na fadin kai akwai irin matan nan har yanzu ashe gaskiya J ka dace kwarai wallahi kudin ma sai ta tambayi izzinin ka zata karba ? Gaskiya kayi dace Allah yasa abin yacigaba a haka ni abokinsane sosai tare muka taso dashi saidai bani zama a nan yanzu shine ya rabamu har baki sanni ba na mika hannu kawai ina fadin wawa sai zuba yake haka na tsani namiji irin haka wallahi. Na fito na hango Saare tsaye kofansu tana waya ban sake kallonta ba na shige part din mu da kusan a jere suke a barin dama dana yaya J din sai dai akwai dan tazara sosai a tsakanin su. Inda part din su mama ke barin hagu yana kallon nasu yaya din da wanan dayan part din da ake cewa part din yaya yazid ne shi ko yaushe yana rufe saidai da yarsu tazo daga zamfara kwanaki aka bude mata ta sauka ciki da yaranta. Sai tsakiya dake da fili tsakanin gidajen duk girman wanan filin da haka nake tashi in shareshi tas amma yanzu na ba kaina lafiya ko ita wace akace yar aikin bata iya sharan wajen yanzu sai almajiraine ke zuwa kwana bibiyu suna sharan wajen. A basu abinci da kudi garama namu part din muna sharansa har wajen gidan mu zaki gashi tsab dashi saidai a tsarin ginan yanzu na ya J yafi sauran girma don filin dake bayanshi an hade dashi anyi gina da aka karawa wajenshi girma sosai donshine nasa part din ya fita daban dana sauran. Ina zama saare na fadowa part din saida gabana ya fadi dana ganta na dauka wata tsiyar tazo yi min sai naji tana fadin . Ai bansan kina part din nan ba Ramaah dana shiga me kika bar su yaya sunayi da zaki fito nace kila abinci zasuci na dai dafa mashi taliya fara da ferfesun kifi yace ayi mashi. Wai kinsan wanan yaya mansur din abokin yaya saurayinane kuwa ya tambayeki ni ko ince kinji suna magana a kaina don Allah ? Wallahi banji ba ni ina kitchen na gama na aje masu na barsu suna hira a wajen na fito sai naji tace barin koma na gani ko sin gama ? Har ta gama surutunta ta fita maria bata daga kai ta kalleta ba sai bayan ta fita taja muna kofa maria din tayi tsuki tana fadin wahalalla kawai. A haka zata kare ance ko saurayin arziki bata dashi ina ganin shine na Abujan data lekewa tana so din nan yazo ? Itama ke sonshi mama bashi ke sonta ba aiko akwai aiki wallahi gara kaso wanda ke son ka ba wanda kake so ba anyi ma kina so yana so yaya aka kare balle wanda kake cusa kanka wajensa. Kudin daya ban na aje ina fadawa yar uwata din abinda yace nace shifa ya dauka aure yaya yayi sai zuba yakeyi harda miko min yana fadin gashi na sayen bakine tunda bai san lokacin da akai buki ba. Maria tace don bai sanki bane yasan duk kannensu ai ba zai dauka kema a gidan nan kike zaune ba aje kudin nan ki nunawa mama tunda ta dalilinsu ya baki shi. Mama kuma na fada ina kallonta tace to Ramaah ina gudun abin maganane wallahi kada yaya ya fada masu abindake nan suce kuma wani abin. A,a wallahi saidai inba yaya din inji me zaice ai dukkansu kyaleni sukayi a kitchen suka fita da bakon yazo don me zan basu nikan ba zan bata ba don tsab zata karbesu wallahi. Nafisa fa tace in anyi muna abin arziki mu daina nuna mata tunda karba takeyi bata bamu sai naji tace ke Nafisace Ramaah ? Waima ko sai yaushe zasu dawone mutumiyata naji kewanta sosai wallahi na zata kwana biyu zasuyi kawai a can ai sai gashi suna batum share kwana goma. Sun dawo jiya naji mama tana fadin ance sun dawo tana garin nan yana da wuya dama ta dawo gidan nan gaskiya don anty saare din dake gida yanzu nasu baizo daya ba. Don cewan da takeyi wai don kwadayi an mamaye komai anayi ta ina za a bari matan yaya su dawo a yanzu shine sukai fada har tayi fushi lokacin ta kwashi kaya zata koma gida saida akaiwa Saare din fada. Kingani ko dama saida nayi wanan tunanen a raina don wanan abinda kukeyi za a dauka da wata manufa ake hakan kinsan mutane yanzu da sheri. Yar uwarsu ke nan Nafisa sun fadi hakan a kanta ina gake da ba yar uwarsu ba ai sai sufi camfaki ga zancen don Allah kadai yasan irin abinda take fadawa matanshi yanzu tunda suna tare. Banjin tsoron duk abinda ta fada saboda nasan ban aikata hakan don kudi ko don wani abuba saidai ban jimirin daukan wullakaci a kan hakan yasa na kama kaina tun bata kawo kaina ba. Ita din yar uwar ya Habu banson nayi rikici dasu don yana mijinki idan nayi hakan bartabanki ne zai tabu a wajensu. Shiru tayi min cikin damuwa ta kasa ban amsa ga zancen ganin haka kawai na mike nabar falon da kudin a jikina don ba zankaiwa mama din ba kome za ayi kuwa tunda nice akaba. Ranan ya Habu ya dawo daga tafiya ya dawo da abin arzikinshi kamar yadda yake akida wajensu duk garin da sukaje zasu sayo abinda ake amfani dashi garin. Za ,a sayo azo dashi gida ayi amfani dashi saidai gajiya ya hana a raba ba sai washegari ya fito dashi daga motansa . Nice ya kira na dauka zuwa part dinshi danasu mama duk da ina kyautata zaton mama tana part dinsu ya J a lokacin. Iya na sama zaune na gaida ita da kwana ta amsa tana fadin yar nan za,ace baki gidan nan wai meke faru hakane kun dauke kafanku gaba daya da wajen nan. Babu komai iya ina nan saidai a yanzu ban faye zama ba ina zuwa makarantane kin sani ai. Kayya yar nan akwai dai abin da akai maki kika dauke kafanki haka ni zuwanki yafi min zuwan wa yan nan marasa lissafin ai ki fada min idan an maki wani abin ne na dauki mataki kan maishi . Nace iya ba komai karatune yasha min kai duk kwanakin nan sai naga ta yafutoni da hannu alaman in matso kusa da ita na je din kuma ta tausa murya tana nuna min dakin su salima tace. Ita wanan sakariya tun jiyan ta shige daki bata fito ba wai abokin yayanta take so kiji min ja,iba baki bari a nemiki ba sai kece mai neman miji don sakarci irin na saratu. Iya tana sonshine tace jam,jam ai mace takan jira furtawan namijine ba ita ta nuna hakan ba shine yayanku Jafaru yayi mata tas jiya da dare ta shige daki tana fushin banza. Ni dai na fita ina dariyanta don yadda tai maganan sai kayi dariya tana kallon labulen dakin zakice saarece a wajen tsaye lokacin. Nasan takaicin hakan tsohuwar taji yasa take neman abokin hira ta amaye abinda ke cinta a zuciya don basu shiri da Saratu sam suna konewa junan su mai ko yaushe. Ban,san ya akayi ba na dawo daga school na samu Asmau uwargidan ya J ta dawo gidan inda na gane hakan yarta dana gani tare da Abbati a part din mu nake tambayan ita dawa tazo maria tace min ita da uwarta sun dawo dazun ita ta kaduna iyayyenta sunce sai karshen sati zata dawo. Nasan suna kara shiri irin nasune don ance ba karamin shige shige suka iya ba ko wanan dawowan nasu yabawa kowa mamaki don haka kawai akaji mama tace su dawo dakunan su. Ance ya j din ya nuna bai son dawowan su amma mama tace aiba tafiyanshi sukayi ba natane don haka dole su dawo dakunan su. Sun dai muzanta na fada ina nufar dakin mu naji tace dani ga wanda yasan hakan ba ai tun karfe biyu tana gidan nan wajen salima nake jin tace Saiba basu gama shige shigensu bane a can. Amma wai mijin yace idan ta wuce gobe ba dai gidansa ba nasan zata dawo ga goben itama ke nan gamu dai gani ai duk fa sun lalace ba kamar yadda suka tafi ba daga ita har yar nata . Ban fito ba ban kcuma da niyar zuwa yi mata sannu da dawowa ina daki ko falon yar uwata kika shigo ba zaki ganin ba don ban zama a falonta sai daki saboda ya habu dake garin. Kamar yadda yaba da umurni sai gata tashigo garin wajajen karfe biyar na yamma bata dade da isowa ba ni dawo daga school motan gidansu dana hangone yasa na gane cewa Saibace ta dawo. Haka kuma na samu anty Nafisa itama ta dawo gidan nayi mamaki kwarai data dawo gidan a lokacin a zatona ba zata sake dawowa da sunan zama ba. Wai ashe shi yaya Jafar da yaya Habune da sukaje gidan suka dawo da ita nayi mamakin jin ya Jafar din ya fita a ranan zuwa cikin gari dashi da dan uwansa lalai sauki ya samu sosai gareshi tunda har ya iya fita zuwa cikin gari. Ina sallah magariba naji shigowan su anty Salima da Nafisa part din mu suna dariya ban fito ba saida na idar duk da naji suna tambayan ina nake ? Suna dariya wai iya tana can tana sakin magana hakan yasa suka gudu zuwa part din mu kafin ta hada dasu ta zage. Daga kofa na tsaya ina fadin anty Nafisa munyi fushi ta juyo tana fadin kada ki fushi Ramaah kina raina wallahi wayarkice ko yaushe mutum ya kira zaijita a kashe. Haka dai yaya yace dazun salima ta fada dazun ya kira layin ki wayar bata shiga ai yace bai ganki ba duk kwanakin nan nace kina nan sammako kiyi kina fita zuwa school. Yadda maria ta kalloni yasa na kawar da kaina gefe daya nima dai naji zancen wani iri balle yanzu da matanshi suka dawo gidan hakan zai iya kawo zargi a zukatansu. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,, 3️⃣1️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Nasamu na gama exam dina haka na dukulo na dawo gida da ciwon kai ga yunwa da nake tunanen shiya haddasa min ciwon kan don ban iya cin komai idan na taka school sai idan na dawo gida. A haraban gidan na gansu zaune yadda suka sabayi wani lokaci idan sun bushi iska hakan zasu fito nan farfajiyan gidan su zauna a dasa daban hira da tsokona. Irin wanan zaman na fahinci da gaiya sukeyinsa wani lokaci idan suna da kudirin cin mutunci ga wani a gidan suke wanan zaman. Shigowana yayi daidai da karan budan get din gidan mota ta shigo hakan baisa na juya inga mai shigowa gidan ba a lokacin saida akai horn na gane ya J ne ashe ya fita ya dawo a lokacin. Daidai inda ya sameni kiris ya rage inkai lungun mu ya dakata da mota ya sauke glass sunana da naji ya ambata yasa na dakata na juyo ina gaidashi. Ko ban kalla ba nasan idonsu yana kan mu a lokacin shiko gaisuwan tawama bai amsa taba sai cewa da yakeyi dani wai Rahama meye matsalan da kike gudana a yanzu. Murmushi na dan sauke ina fadin yaya gudunka kuma wallahi exam muka fara sai yau din nan muka karasa wanan yasa ka daina ganina. Ya maki kyau shiga zanyi maganin ki ai daga ke har Nafisa zan zauna daku ku fada min idan kuji wani abu daga garemu ne kuke wanan halin sam banji dadim matakin da kuka dauka ba wallahi. Nagode yaya na fada ina dan rusunanwa na hau step ina murda kofan mu na shiga ban san ya akayi ba dai bayan sallah isha,i saiga Nafisa a part din mu tana fada min wai yaya J yana neman mu wurinshi. Yadda nake dagani sai wata dogowar riga mai v neck mara hannu sky colour hijjab dina fari danayi sallah na fito daga part din mu nake ce mata dama dazun yace zai zauna damu ashe da gaskene. Ok dama dazun din da gaske ya tsaya dakene rikici sukeyi da matanshi akan hakan nidai naji yashigo yana fadawa mama a hasale har ya tashi dukan Saare iya ta hana. Shi yaya har yaji sauki duka haka ke nan iya abinda na iya fada ke nan don ni zargin nasu ban daukeshi da wata manufa ba tunda a gabansu dai na tsaya dashi din suna gani. Kuma meye a ciki don ya tsayar dani na tsaya shine kuma zai zamo abin fitina har da zancen duka a ciki ? Kin gane Rahama wallahi yau ina ganin za ayita ta kare a gidan nan kila na bar gidan nan a yau din nan don ba zan lamuci zancen banza ba bari dai muje din muji kiran zakisha mamakina wallahi. Rashin mutunci da iskanci nida na taso gidan yawa kowa da halinsa ana nuna min iskanci in kyale saidai idan naso hakan shiru shiru aiba tsoro bane dama. Ke kenan Anty Nafisa nikan ai kila barin gidan zasuce nayi tunda zargi ya fara shiga haka ko basuce in bar gidan ba aini zan bar masu. Akan me gidansune bari dai muje muji ai mama da kowa suna can wajen hakan ne kuwa koda muka shigo da sallaman mu falon duk suna zaune harshi dake waya a lokacin inda na fahinci zai koma bakin aikinshi a kwanan nan yadda yake fadi a waya lokacin. A jam,i nayi masu ina wuni muka samu waje muka zauna a gefensu falon yayi shiru bin ko ina nakeyi da kallo har kasan da nake ganin tun dawowansu bai samu mopping ba kayane a ko ina yasha a falon wanda nasan aikin yaransune hakan. Suna da wani hali ko yaro yana barna ba za a tsawata mashi ba haka kuma idan dan wani yayi barna har inke uwa baki kwashe abin ba a nan zai tabbata wajen. Ba karamin wahala mukasha wajen gyara falon nasu ba lokacin har ya koma daidai yadda yake son gani kullum a rayuwansa. Muryanshi ya dawo dani na dago kai da yake fadin Nafisa kin dai gani ba falon da kukasha gyara shine ya koma haka saboda na tara jakkai da basu san arziki ba sai tsiya da bakin kishin banza a rayuwansu. Haba dai daina fadan hakan jafar ke Rahama dazun kun fitane tare da yayan ku da yamma ko shi ya daukoki daga bokon da kikaje ? Kallon ido da ido nayiwa mama din cikin mamaki ina fadin wani yaya ciki mama ni kadai nake zuwa in dawo yauma aida Aisha muka dawo ita ta bani lift a motan gidansu da akaje dauko ta. Ina kikaga yayan ku nace nan gida zan shiga part din mu yadda Saiba ta gyara zama irin bata yarda din nan ba yasa na yi shiru. Ya taba daukan ki ko yakai ki wani wajene bayan haka dakata mama ina da number Aisha din bata gidan Alh wada din nan ba sai ta kira layin Aisha din. Wai ke dama kina nan yau ai nake ji wajen kanwarku din nan dazun na ganta a hanya tana jiran mota na rage mata hanya kinsan yarinyar bata da sakin fuska. Aita fada min dazun din shine na kira inyi maki godiya haba dai akan wanan wallahi salima baki da kirki ko kadan kizo ga gida ga gida ki kasa shigowa ? Bari zan kiraki anjima don Allah ta fada tana kashe wayan ta kallo kowa dake saurarensu tana fadin kun daiji yanzu ai. Kinji ko mama kinji da kunnen ki wa yan nan jakkan suna son bata wa yarinyan nan suna a banza to bari kuji wallahi. Jafar dakata iya ta fada yau koka dauki Rahama a motanka laifine hakan nace laifine a garinku ? Wai meyasa samun waje yake son zama iskanci bari kuji in fada maku Jafaru dai namijine mata hudu Allah ya halasta mashi yi akansa. Ashe kuwa matukar hakan Allah ya yarde masa ku din nan baku isa kuce sai yadda kukeso zaiyi ba a rayuwansa . Ba a kallon mata ke Nusaiba kika kutso cikin rayuwansu da danyen aurensu kika saka saida ya auroki gidan nan aka kawoki don bakin ciki kada abuyarki taci bakici ba. Dariya anty salima keyi nasan hakan ya bata haushi ta soma magana tana fadin ai gashinan iya ki tambayeshi idan nina kutso kaina bashi yace yana sona ba ? Ke rufa min baki har yaushe na taba ganinki nace ina sonki Nusaiba bayan wasikun batanci da kike rubuto min kina bata kawarki wajena ? Har kikayi nasaran hada baki da abokina kuka,,,,,, Jin irin tonon asirin da yake mata a gaban kowa yasa tayi saurin katseshi da fada tana fadin bayan duk bina da kayi a yanzu zakayi min sheri. Ya isa haka don Allah wanan kanku kuke tonawa asiri bayan abinda ya wuce koma meye yanzu ai kun zama daya a tsakaninku don haka ki koyi hakkuri da zaman tare. Kinzo kina zargin mijiki da yarinyar nan yau idan Jafaru yace zai auri yarinyar nan ke kin isa ki hana hakan tunda ke ba,a hanaki ba ? Tun zuwan yarinyar nan da yar uwarta gidan nan kuka dauki kiyayya da hassada kuka dorawa yaran nan don mijinsu yana da dubaiyane aksn dan uwansa da ankai ga yadda kukeso . Ki duba yanzu bai ko sanda shigowan yarinyar nan ba amma kince wai tare sukazo gidan nan da ita ya sauketa a waje. Ni kuma na fada a cikin mamaki kwarai kuwa abinda suka fada ke nan cewa tare muka shigo dake na saukeki a waje saidaga baya na shigo gidan hakan bai mun ba kuma na dakatar dake muna magana. Tace ko a bayansu ina kwance ina jinya abinda mukeyi ke nan dake dama sai Saiba tace ai muma ji mukayi cewa komai itace ke maka ita da Nafisa . Ba ance bane kwarai sukeyi min komai ko yanzu ma a gaban ku su din ne dai zasuyi min kome nake so wace zata zauna ta zauna wace bata iyawa kuma ga hanya nan sai ta tafi. Kaina na sada kasa abinda yar uwata dai take zargi ya tabbata ke nan a kaina yanzu sai muryan saiban naji tana fadin . Ko sunyi fa sai me in zaka iya sweety ka aureta kaga wa hakan zai dama ? A zabure ya harzuko mata yana fadin haka kikace ko tace an fada din inka isa ka aureta mugani ko ba nufinka ba ke nan ? Wanda ya fada muna in bai gani ba zaiyi karyane nan suke ma komai ai wa,,,,, Ke yarinyar nan baki da kunya yanzu ke don Allah bai zuba maki kunya a idonko ba mijin da kika kyamata a gaban mu zaki dawo yanzu kice kina fada a kansa ? Nan fa kuka nuna kuna kyamarsa don ciwon da Allah ya jarabeshi dashi don baki da kunya ko kadan yanzu kin dawo kina fadin wanan zancen banza haka don samun waje. Mikewa nayi duk suka bini da kallo falon ban tsaya jin nauyi kowa ba na fice daga dakin kai tsaye zuwa part din mu na samu maria ta idar da sallah take fadin yanzun nake fadin in biki ai. Sai gaki tun dazun wayan ki keta ringing ba tare danayi magana ba na shige dakin na dauki wayan Sa,id ne ke faman kiran layina saurayin daya lake min saidai a ganina ba a yarda in tsaya dashi ba zasuce yarone don yadda naga sunyiwa anty Salima shiyasa ban damu da kulashi ba. Sai kuma ga kiran anty Salma ya shigo wayan na daga ina mata sallama ya kuma najiki a wani mood ko baki da lafiyane ? Lafiyata lau anty kawai dai sai nayi shiru meya faru ta sake tambayana sai naji kawai in fada mata ko zanji sanyi a raina ko kadan ne. Wallahi anty Salma sha,anin gidan nan ya isheni matan yayan ya habu sun saka min ido suna kokarin bata min suna ga abinda bashi ba. Cool down Ramaah kiyi min bayani yadda zan fahinta nan na kwashe komai na fada mata Maria tana tsaye tana saurarena saida taji anty salma ta soma magana da bataji ta juya ta fita daga dakin. Anty salma ke cewa da zaran kun gama exam dinki ki taho nan kiyi hutunki ki kyalesu can yan iskan mata kawai na bata amsa da mungama yau ai. Shine suka tareki da bacin rai ga gajiyan exam a tare dake goben nan zan turo a daukeki har gida ki shiri ba maria waya muyi magana . Hakan yasa na mike zuwa falo bata nan na duba dakinta nan ma bata nan sai na leka waje naji hayaniya yana tashi a wajen. Nacewa Salma ina zuwa na kashe wayan nabi bayan ta daidai da zan shiga naga mama ta sakota gaba tana fadin tayi hakkuri suma sun fadane don batanci amma ai fadan ya koma masu ciki yanzu don matakin da jafar din ya dauka. Ranan kan sunsan sun taba mata yar uwa don tayi masu abinda basu taba zato ba ta zagesu tas dama ance kunne ya girmi kaka ina jin muryan saiba daga cikin part dinsu tana fadin idan ta isa tasa a yau din nan a dauki mataki a kansu din idan habun ya dawo. Ranan dai da bacin rai kusan kowa a gidan ya kwana da safe nake fada mata Abuja nayi wurin anty salma inyi hutuna a can din. Bata koce mijin ta aibai gari ba yadda ta saba tauyeni shi kuma idan ya dawo yake hanawa sai cewa tayi hakan ma yafi. Sai can nace kuma kada in tafi na barku daga ke sai Abba ku kadai a cikinsu tace ki tafi ba abinda zasuyi min ki daga ki basu waje kawai zaifi sauki har a kwana biyu. Karfe daya da yan mintuna muna hanya ban tsaya sallama da kowa na gidan ba sai Nafisa data shigo taga ina shiri nake fadawa Abuja zan tafi ranan. Sai ga mama ta shigo tana tambaya yanzu maria kan wanan zancen da akayi ya wuce zaki tura yar nan Abuja tayi murmushi tana fadin badon shi bane mama dama tana da niyar zuwa tayi masu hutu a can. Yanzu haka driver da zai dauketa yana hanya tafe takai zaune tana fadin koda zata tafi ba dai yau ba kan zancen nan dai ya kawo wanan tafiyan shi Habu ya sanda zancen tafiyan natane yau ? Zan kirashi a waya mama dama yasan zata tafi ai ummah ma tace ta tafi din tace to shike nan Allah ya sauwaka ina daki ina jinsu sai mamakin hali irin na mama na sanyi hali nakeyi. Barma dawowan su din nan abin nata kamar ya sukurkuce ne gabadaya kardai abinda suke fada kan suna shige shige gaskiyane hakan ? Koma dai meye sun samu waje da yawa ni dai har tagama ta fita ban leko ba kuma ba a jima ba driver da anty salma ta sheda muna ya taso tun bakwai na safe ya iso daukana din sai da aka gama saka kaya a mota anty maria ta matsa min nashiga na sallami su mama na fito muka dauki hanya. Karfe hudu da wani abu muna Abuja don mun tsaya kaduna mun karbi sako na kuma shiga nayiwa ummah sallama na tafi. Tunda aka shiga min da kayana nashiga nayi sallah ban fito ba ina daki don har lokacin ina jin zuciyana a cunkushe abinci ma nan anty salma tasa aka biyoni dashi ta fita ta barni da yaranta zuwa asibiti duba wata kawarta. Wa jajen karfe biyar maria ta bugo take tambayana mun sauka lafiya na amsa da lafiya yaya na barsu kuma tace lafiya kalau ga Abbati yana kewana. Nace a bashi waya yana jin muryana yasa kuka nake lalashin shi a waya ina mashi waka nan uwar ta karbi waya tana fadin ai habu ya kira yana fada wai meyasa na tafi ban bari ya dawo ba. A raina nace tunda ubana yake ba amma a fili cewa nayi da ita dana bari ya dawo ba zai yarda in zo ba yanzu ko gani hankalina kwance saidai kewan su don ba karamin shakuwane tsakanin muba da ita. Shigowan anty salma dakin yasa mu dakatar da maganan ta karbi wayan suka danyi sharfi akan zancen na wani dan lokaci. Bayan sun gama take fadin wallahi sunyi arziki ba a gari daya muke ba da sunga tsiya don sai nayi karansu wallahi. A bakin iya yake jin tafiyana Abuja din daya shigo take fadin ina kashiga yau Jafaru yake fadin ina can kofan gidan mu iya da abokaina . Nikan nace da kana gida ba zaka bari yarinyar nan ta tafi ba ban zaton zasu barta ta dawo gidan nan kuma don wanan sherin na matanka Jafaru. Wace yarinya iya ? Yarinyar nan me take da suna Nafisa dake zaune take fadin wai Ramaah take nufi fa sunan ma ta kasa fada kullum sai an tuna mata sunan . Ina taje Nafisa tace Abuja dazun aka aiko da mota aka dauketa daga can yanzu kan ai ta tsufa Abuja ita kan saiga salima ta fito daga dakinsu tace . Nifa banga laifinsu ba gara data gusa ta basu waje wanan zargin ya kare hakana haba don Allah wanan iskancin har ina don Allah ku dauki kishin yar uwarta ku yabawa yarinya bataci ba bata sha ba don Allah dai. Humm, kawai yace ya mike tsaye yana fadin iya zan fita me zan sayo maki yau iya ? Jafar kaji saukin fitane irin haka naga dare ya soma yi a yanzu kardai don shedanun matan nan naka zaka tsiri fitan yamma haka ? Bai bata amsa ba ya fice daga gidan motarshi ya nufa ya shiga ya zauna maigadi ya bude mashi lokacin ya ciro waya yana neman number waya. Nidai ina waje tare da anty salma ya kira harya katse ban dauka ba lokacin dana dawo kuma ban koma takan wayan ba nayi sallolina na kwanta. Washegari tunda safe ya fito a cikin shirinsa ya nufi wajen su mama ya samu suna azzakar din safiya ya gaidasu yana fadin zai danje kaduna kila ya isa har katsina saidai yadda hali yayi sunganshi . Haka ya bar zaria zuwa Abuja don shi kadai yasan yadda ya kwana cikin bacin rai ya kulla wanan ya kwance ko iyalinsa sai a bakin kannesa suke jin baya garin. Sam bai manta da gidan anty salma ba direct ya dira gidan ya dan jima a kofa yana kiran waya ba a dauka ba yasa ya fito yayi sallama. Daga cikin masu aikin gidan wani ya shigo yana fadin wai anawa Anty Rahama sallama daga zaria bakuwar data zo jiya. ZAINANB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,, 3️⃣2️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Kallon juna mukayi da anty din don zaune muke muna karyawa muna dan taba hira da ita wanda hiran exam dina nake bata tana dariya. Shine wanan mai aikin ya shigo yana fadin sakon daga zaria je kace waye yake sallama da ita ? Ya juya ya tafi ita kuma tace kin fadawa wani zakizo nan ne na girgiza kai ina fadin banda yan gidan mu ban fadawa kowa ba. Suma kuma sai yau din nan suka san da zancen tafiyana ai da zan wuto kila dai ba daga can bane kodai kuma mijin anty Maria ne amma shi yana bauchi akace. Saiga dan sakon ya shigo yana fadin yace nace dake yayankine Jafar na gidan ku can zaria din wanan yasa na mike ina fadin ya J kuma meya kawoshi kuma ? Wanan me mata din na anty salma ta tambaya kai na iya gyada mata don bansan me zance ba ta dan tsuke fuska tana fadin je kace ance ya shigo. Yana zaune yana waya Isah ya sameshi a mota yake fada mashi ance ya shigo daga ciki jin hakan hakan yasa ya dan kalli Isah din dake fada mai sakon ciki mamaki yana fadin maigidan yana nan ne ? Baya kasan hjy ce da kadai sai yan aiki a ciki dan jim yayi kamar yana tunane kafin ya bude motan ya fito da kafansa daya ya tsaya gyara yanayinsa. Ya fito wanan isah din yayi mashi iso har zuwa falon na anty lokacin mun bar falon don tace dani tashi kije ki kimtsa yasan akwai banci da nan da can da basu daukeki da daraja ba. Idan basu kaunan ku mu muna kaunan ku tunda munsan darajan ku munsan kuma muhinmancin ku a rayuwan mu. Hakan yasa na mike zuwa daki na dan sauya kayan jikina din kamar yadda tace na fito fes dani sai kamshi nakeyi da daukan ido bakina na asalin fulanin mu na Cameroon ya kara baiyana sai golden eyes dina da samansu yake kamar ansaka min eyelashes garza garza dasu suka kara min ma,ana tsayina yasa ban saka takalma mai tsini a kafana sai yan ma daidaita haka. Yana tsaye cikin falon ba tare daya zauna ba ya juya baya yana kallon kofan shigowa daga falon kamar me tunane yana shakan kamshin da falon keyi a lokacin ga komai na falon white tsab dashi kamar ba mahalukin dake rayuwa a cikinsa saboda tsabtan wajen. Haka na fito na sameshi a tsaye na danja na tsaya ina kare mashi kallo duk daya ban baya amma ba zakice shine a yan kwanakin da suka shude yake cikin bautan Allah haka ba. Yar siririyar sallama nayi ina karasowa ciki hakan yasa ya juyo gareni ya zuba min idanuwanshi da har sukasa tafiyana ya fara hardewa lokaci guda saboda tsarguwa da irin kallon da yake min din. A hankali nace ka zauna mana yaya ai anty tana daga ciki ya dan kalli inda kujerun suke ya nufa ya zauna a daya yana fadin nagode fuskanshi har lokacin dauke da damuwa a cikinsa. Tiren dake hannuna na dire tare da jawo dan side table din zuwa gabanshi na durkusa a gabanshi na balle murfin goran na fara tsiyaya mashi ruwa a cikin tumbulan glass mai kyau da tsada. Ya miko hannu ya amsa tare da fadin thanks lokacin na mike can nesa dashi na zauna a darare ya zuke ruwan yana aje glass cup din ya sauke ajiyan zuciya. Idon da ya tsura min na wasu yan lokaci hakan yasa na dukar da kaina kasa cikin jin nauyin shi yadda ya kura min ido din a lokacin. Akwai damuwa sosai a yadda na kula da irin kallon da yake min din a lokacin don yanayin annurin nan nasa da babushi shimfide a fuskansa lokacin. Har tsawon wani dan lokaci muna zaune a hakan ganin wanan yanayin yasa na zamo saman kujeran nakai zaune kasa ina mai sada kaina. Ganin hakan yasa ya soma magana a cikin murya mai taushi kamar ansa shi dole ya furta ya soma fadin Rahama meyasa kika taho Abuja kika zauna ? Me zaisa ki bar gida ki dawo nan ba tare da sanin mu ba kina ganin hakan da kukayi ke da maria kun muna adalci ke nan ga amanan ku da aka bamu riko ? Fuska na dago na dago da hanzari na dan kallesa yace yes amana kuke a wajen mu don hardo bai boye muna komai game da kuba ya kuma roke mu da mu rike masaku amana kuma mun karbi hakan. Sosai naji hankalina ya tashi ga kalaman nasa dayace sunyi alkawari da hardo akan mu don nasan hardo zai iya hakan don yadda ya damu da lamarin mu. Kada kika ban dauki mataki akan abinda matana suke maku ba ki dauka sunfi karfinane a hakan ? A,a akwai matakin da nake son dauka wanda duk sai sun raina kansu a karshe kan wanan rayuwan banza na kazafin da suke kokarin maki. Dago kai nayi na kalleshi don jin abinda ya fada din ke nan shiya tsame kansa a ciki nice ma suke batawa ke nan hakan yasa hawaye ya soma zubo min don zuciya daya kawo iya wuya . Koma me suka fada maki nasan Allah zai wankeki ga sherin su Rahama don Allah yayi hikimarsa daya bar shari,a a hannunsa akan bayinsa. Ni nasan kin taimakeni taimakon da ko mama data duka ta haifeni ba taimin irinsa ba tunda ta kasa tsamoni cikin halaka saike Allah yaba wanan dama da ikon data sanadin a yau gani a saman kafata tsaye. Banda Allah waya isa hakan ga bawan shi Rahama toni na sani kuma ba butulu nake ba dan hakin da ka raina shike tsone ma ido inji manya. Suna maki kallon dan haki a wajensu ni kuma ina maki kallo na mutum sak a idanuna don wanan sirin banda habu da Allah ya nunawa dagani saike sai nafisane muka sanshi. Shiyasa nake matukar girmamaku a cikin lamarina girman da a gaban kowa kuke ba zan iya boye hakan a raina ba sai na fitar fili kowa ya sani. Yau kin kwaso kin dawo Abuja wajen anty ki Rahama kin zauna yaya kike son na kasance a can quite sure basu fadi karya ba a kaina nina sani Rahama. Akwai wani fleeling da ban iya boyewa a kanki matukar zan sanya idona a kanki ko a gaban wa kike kuwa zan kasa controlling din kaina a lokacin. Ina kike son kai alhakin hakan a kanki Rahama a yau nazo maki da wata tsiga ta dabance banzo nan da sunan dan uwa ko yaya a gareki ba na zo makine a matsayin jafar din da kowa ya sani. Don haka kiyi hakkuri kada kice zakiyi fushi da gidan mu Rahama ki dawo nan Abuja da zama akan laifin da bamu muka aikata maki ba . Su basu isa su fitar dake gidan muba sunzone kamar yadda kema a sanadiyan aure Allah yayi zaki zauna damu din haka suma suke zaune damu. Kaina yana kasa na dukar lokacin mukaji takon anty Salma ta nufo falon tana waya kafin ta karaso tana sallama. Shi ya amsa mata don ni kona amsa ma ba zataji ba a sannu da hanya ta fada tana zama kallo daya yayi mata ya kawar da kansa gefe daya. Dan zaria ina fatan ba kazo dauke min kanwata bace ya danyi murmushi yana fadin banzo daukanta i hope muma ba dauke muna ita kikayi daga can ba ? Eh to kusan haka gaskiya don ka canka da kyau saboda matanka sun saka min kanwa gaba da haushi ba zan lamuci hakan ba gaskiya har yaushe nawa Ramaah take balle wanan zancen banza ya taso kanta. Bakai naso kazo ba don banda case dakai da mijin Maria da aka bashi amana don aure amanane ya tsaya ana yi masu hakan yana kallo kai kan ai matankane ba zasu taba laifi a wajenka ba don da an dauki mataki. Hjy ko yanzu daukan matakin da nake son yi shine yasa kika ganni a nan zaune . Ok to muna jin ka nima abinda ya fito dani ke nan yanzu ka fada min manufar biyotan da kayi don ina da bukatan ji idan hakan zai gamsar dani. Amma taya don Allah bawan Allah mata zasu zauna suna ciwa yarinya fuska haka amma a rasa wanda zai daukan mata mataki a gidan har kai da abin ya sha ? Allah da nayi niyar yin karansu kan zancen nan amma sai nayi duba ga maria dake zaune daku naga rashin dacewan hakan da zanyi din. Shine yasa na daukota baki a laikum zuwa nan komai iskancin da suke ji ba zasu taba biyota ba nan suyi mata ai ? Ya langabar da kansa gefe daya yana saurenta sai da yaji tayi shiru ya soma fadin da kinyi hakan kin dauke ta hjy baki kyauta min ba donni abin zai shafa a karshe. A daiyi hakkuri ina mai bada hakkuri a both side amma a gabanta aina fada masu matakin da zan dauka ga hakan da sukai min ba zaiwa ko wacen su dadi ba a rai . Wanan yasa naki daukan komai da zafi hjy don in gasa masu kwakwansu a hannu kafin na kai ga daukan matakin ni zuwata nan ai yayi min dadi tunda acan boyewa takeyi bani ganin ta. Ba anty salma ba ni kaina saida na dago ina kallonshi da mamakin abinda yake fada ko banda hausa zan fahinci wanan magana amma kuma bai fadi dalili ba. Shike nan ai tunda har kayi tunane kamar nawa sai a je a hakan Ramaah dai zata zauna a waje na sai hutu ya kare insan abinyi a kai idan haya zan kama mata anan zaria din har ta karasa karatun ta tadawo nan ko kuma idan a hostel zata zaune dai zanyi shawara a san abin yi ko ita maria bata san kudirina ba a yanzu. Shike nan hjy ba sai ta zauna a hostel bama tunda ga gida nan dole dai matakin da zan dauka yasa kowansu natsuwa a yanzu. A yanzu a son samuna don Allah ba wani boye boye ko kwanaye kwanaye don so nake ta ban baki daga nan in wuce can wajen hardo mu gana dashi. Zubur na mike tsaye don jin maganan da nayi kamar saukan aradu a kaina na fara tafiya a baya baya ina kada kai na juya zuwa ciki da sauri na barsu a nan din. ZARIA Ringing din wayantane ya tayar da ita daga barcin data samu tun bayan fitan Saare a dakin da suka gama dariyan plan dinsu na jiya yadda yayi daidai da abinda suka hada din. Dauka tayi a cikin magagin barci tana amsawa wayan mamansu shiyasa tace hlo mama ke ba mama bace nice Rashida naga kiran kine ai dazun ban kusa da wayan. Jin hakan yasa ta watsake daga barcin tana fadin wallahi anty Rashida na kira in fada maki komai ya tafi daidai yanzu haka tabar gidan nan tun jiya ta tafi abuja wai hutu. Nasan ko ba hutu bane tagudune don kunya na dasawa shegu bakin ciki daga ita har yarta din yan iska . Ke kice min kinyi maganin shishigi ke nan gobe ta kara rawan kai ga mijin wata mugani ita gata sarki iyawa ko bari a koreku a yabeta ? Ta dauka zataci bulus ne ta tafi a banza rabuda yar iskan yarinya tana wani daukan kai kamar diyan wani da wata ? Yanzu ina mijin naku yake shi kuma wani dan iska guda haka kawai uwarka ta kore matanka kayi zaune a kwaso maka wasu yan iska suna maka karairaya kana binsu da kallo ? Haba dai dayan fa kanwarsace ya Raahida mahaifisu daya sai ita dayan mara kunyar su a dole ga jikan munafukai don ta gyarawa yarta hanya a yabeta mu kuma a kushe muna. Ni yanzu ko Asmau takai min ko ina wallahi yaya ina bakin ciki in bude ido inganta a cikin gidan nan a matsayin matar sweety. Ke na fada maki bar wanan shasha,shan makarine a wajen ki bar banza a haka ki fita zancen ta don yanzu kina kawar da ita gidan nan wallahi wata zai jajibo maki tunda ya saba zama da mata biyu a yanzu. Shima anyi rigimame dan wahala kamarshi zaije rigimar aje mata har biyu don Allah nifa idan ya jero daku nakan ga kamar ma kun girme mashi ga shekaru ? Haba dai yaya Rashida wallahi ya girmemu kawai dai rigimace irin ta maza dashi kawai ni dama nafi son hakan mu tsufa tare da abin mu. Wai yana inane yana nan yana fushin har yanzu ko ? Yanayi wai yayi tafiya dazun shine bai sanar da kowan mu ba sai a bakin sakaran nan saratu nake ji wai ya zo nan kadu daga can kila zai wuce katsina. What baki tunanen hakan plan ne dama ko tare suke da yarinyar nan tunda jiya ta wuce itama wallahi ba abinda namiji ba zai iya yiba Saiba. Kai haba yaya Rashida Allah ba zaiyi hakan ba kawai dai tafiyan yaje dama tun ranan ya fada zaiyi tafiya a yau din kafin zancen nan. To shike nan nidai kibi sannu kinsan dai kece mai dan maski maski a cikin mu kada kije ki jawo wani sabon wahala kuma abubuwa suzo su tsayawa mutane. Haba dai aiba zan yarda akai hakan ba kawai nima ido na zuba mashi ya kare fushinsa nasan ina nan zaizo aiya sameni dama mun saba . Ni wallahi tausayi ya ban sosai da ake maganan amma haka na badawa idona toka naci masa mutunci ga kowa nasa a zaune ya kasa daukan wani mataki tana fada ta kwashe da dariya. Ni dai shirun nasa ne nakewa tsoro wallahi kinsan halin Jafar fa Saiba dan duniyane na karshe wallahi saita tare yar uwar da fadin barshi ba abinda zaiyi wallahi haka yafi shegu su daina dagawa mutane kai ai yanzu gidan. In kinga yadda Habu din nan yake ririta wanan yarinyar da yar uwata zakice wani romiyone da juliya suke soyayya duk da sun haihu ba abinda suka rage ga komai wallahi. Ai shiyasa naji tsoro kada shima jafar yaje ya jajibo maku yar bafulatana boni ya cimu ina mu ina kishi da mugun iri ina ganin yadda yaya larai take fama da nata bafulatanan. Barshi ai kafin ya gama fushinsa ya dawo hanya nagama duk wani shirina da zanyi a kansa wanan karon zaisan ko wa nake kudina ba zasu tafi a banza ba. Sun gama hiransu yunwa ya fito da ita falon ta duba ko Asmau dake da girki ta karasa saidai ba motsin Asmau din kitchen ta leka nan ma wayau babu wani alaman girki a kitchen din. Ta fito ta nufi dakin Asmau din dake da tsohon ciki kwance ta sameta tana barci cikin daga murya take magana da nifa ban gane ba Asmau ba za ayi muna abinci bane yau ? Hakan yasa ta bude idanu tana kallon abokiyar zaman nata tace banji dadine akwai miyar jiya na nan a fridge idan na tashi zan dafa muna shimkafa ko taliya. Kinsan kuwa karfe nawa yanzun Asmau yanzu fa karfe biyu ake nema nifa wanan halin idan shi za ayi wallahi saidai kowa ta dinga girka abinda zataci yafi min sauki gaskiya da wanan halin . Kina iya zuwa aiki dafa ko yanzu ina jin jikina sai ibtashi in shiga kitchen dafa maki abinci to naki ki dinga dafa naki abinci mana sai me ? Haka kikace ce tace eeh na fada haka kawai ina barcina zakizo ki tayar dani daga barci ? Zakiga abunda zanyi din ta juya ta fita tsuki Asmau taja tana fadin haka kawai zakiyi kokarin yi min turaja. Cikin bacin ran da take ta kira wayan mijin nasu duk da tasan yana da wuya ya daga yadda yake fushin nan. Tayi sa,a kiran nata ya shiga yana tsaye bakin mota Isah na kwashe kayan dayazo muna dashi kiranta ya shigo wayanshi. Duba wayan yayi yaja tsuki har wayan ya katse bai dauka ba bai kuma dagawa din ko kira nawa zatayi ya fada a zuyarshi da tasan abinda yake ji game da ita da bata kirashi wanan lokacin ba. Yaja motansa ya fita a cikin sanyi sam bai tsanmaci hakan ba daga yarinyar nan ya dauka ba zai samu wani matsala sosai wajen shawo kanta ta amince dashi ba sai gashi gaba daya ta nuna bata yarda da tsarin nasa. Wanda yasan badon komai ta nuna hakan ba sai saboda wa yan nan baka more din matanshi daya tsani duk wani halinsu na banza yanzu. Amma zaiyi kokarin duk yadda zaiyi wajen ganin bata subuce masa ba a yadda ya hango hakan ayanzu gareta. Meye laifin da wanan hjyr zatace haka bai yuyuwa tunda ga yar uwarta a gidan itama tana fama da kanta balle ita kuma tashiga ciki. Ke nan saboda matanshi ke nan suke ganin hakan ba mai yuyu bane kome yarasa mesa mutane ke daukan al,ada fiye da addininsu. Hotel din daya saba sauka idan ya shigo Abuja ya nufa ya kama daki yayi kwanciyarsa saidai duk yadda yaso ya huta hakan ya gagareshi a ranan. Don ransa da yake bace da wani zaiji a zuciyarsa bacin ran saiba da yake ciki ko wanan abinda yake ganin yana nema ya zamo mashi matsala ? ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,, 3️⃣3️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Gado na fada ina sakin kuka ba zance ban fahinci inda ya J ya dosa da zanceshi ba maganan gaskiya shine ya J yana nufin yana sona idan bani bace ban fahinci zancensa ba ? Ina ni ina ya J me tarin mata har biyu inje ata uku yar uwata tana ta farko a wajen mijinta ai gara na yarda da Faruq dana buge ga auren ya jafar da wa yan nan mata nasa kome yake kuwa ina . Ai in an gani lahira maza suka kaini badani ba da wa yan nan dambun dankaron matan nasa ai kazanta zai kasheshini don ko ruwan goran part dinsu ba zan iya kaiwa a bakina ba yadda nake da tsandan tsiya din nan bakin kyan kyami ke gareni ta ya zan jefa kaina ga halaka ina gani. Me zan gane da auren ya J a rayuwata banda fiti ki duba yadda kullum ta Allah ta waye sai sunyi fitina a tsakaninsu anshiga rabon su can dai gasu gada inji bahaushe. Wai anty har da tsayawa tana saurareb shirmesa shirme mana ta yaya don tabin hankali zai tunkareni da zancen soyayya tunda aure ai soyayyan ke kawoshi toni ina soyayyan da ke tsakanina dashi ? Banki ba dai mutunci da tausayi saboda halinshi da kowa ke yabo na kirki ga kyautatawa na tare dashi yasan darajan dan adam fiye da tsammanin mutum. Baya da wanan ba wani feeling da nake dashi akansa banda zumunci sun rikeni kanwa na rikesu yayyuna aje a hakan. Na idar da sallah la,asar ina zaune a wajen nayi tagumi anty salma ta shigo dakin nawa tunkan ta karaso take fadin ke kuma meye haka ? Kin wani zauna kin buga uban wanan tagumin duk a kan zuwan wanan yayan naki kike haka kome ? Babu komai anty na fada cikin cool voice takai zaune tana girgiza kai gami da fadin ban yarda ba Ramaah ? Ta yaya zakice min babu komai bayan nasan abinda kikewa tagumi meye na tagumi a cikin zancen nan. Bayan duk wani mahuluki mamallakin hankali ya dubi zancen bawan Allah nan hanyan daya dauko itace hanya mafita a kan ku baki daya. Bafa ko wani namijine zai iya daukan wanan matakin da yake shirin dauka a yanzu ba zargi da tozarci babu kyau Rahama sam bashi da dadi wallahi. Let him prove himself to them yakai namiji namijin gwadawa gobe su kara irin wanan katobaran basu bama duk wata macen arziki zata kama kanta da zargin mijinta ai idan yayi hakan. Bayan haka duk wanda ya zauna dake kike fada masa irn halaiyan bawan Allah nan zaiso kasancewa dashi Rahama . Tun kafin na ganshi irin labarinsa da kike min yasa na fahinci kin kamu da kaunansa ba tare da kinsan hakan ba saidai kina gani kamar halinsa kawai burgeki yakeyi hakan ba kauna bace kike masa. Tun farko Rahama ke kika cusa kanki gareshi ba tare da kinsan maza basu san hakan ba sai su dauka kaunace ta soyayya kake nuna masu idan kana masu hakan . Wanda ke kuma a wajenki kin dauki hakan da ramuwar alherince zuwa gareshi don kyautatawan da yake maki fiye da mijin yar uwarki. Meye a ciki don kin aurensa banda alheri ke a kaddarama ba aure zakuyi ba aje a hakan wallahi kin rama abinda sukai maki don dole zukatansu ya kusa bugawa idan labarin kun sarku dashi ya riskesu. Kinga ko a nan kin dauki fansan bakin cikin da kika cusa masu idan yaso daga baya in za a shirya din a shirya idan ba shirin ma a zauna a hakan kin dai rama sun kuma razana. Balle d guy is handsome and wealth kinga akwai hutu a tare dashi so banga abin tsayawa kina wani saka kanki a cikin kunci irin haka ba ? Ta koma matsowa tana dafani tace ko da baki sonshi a yanzu let play a game to his wife ki nuna kin amince din da bukatanshi yan iska muga iya gudunsu. Ba sunce sun iya yiwa mijinsu zargi ba don suna kishin yar uwarki zasu hada dake to zamuyi wasa da hankalinsu fiye da yadda suke zaton sunyi muna a yanzu. Kici kudinshi kawai suna kallo saidai yaji daga baya kin tsayar da mijin aure amma don ramawa sai mun rama wallahi . Daga goben nan zaki fara fita wani vocational school dake nan cikin gari zaki koyi gogewa da wayewa ki iya tako da kowa a garin nan. Wanan hjy Yabi yar kawar mama itace ta bude wajen don tallafawa mata halin rayuwan nan da ake ciki saboda mace macen aure dayai yawa a yanzu so na kirata tace ba matsala in turoki kawai goben. Kinga kafin hutunki ya kare kin dibi na diba a wajen ai so ki maida hankali don Allah ki koyi abinda ya kaiki duk da nasan ke baki da shiririta irin haka. Naji naji dadi sosai a raina don ko banza zan rage zaman kawai da nakeyi zan dan shiga mutane in rage nauyim zuciyata . Har anty Salma ta fice dakin juya zancenta nake a kasan zuciyana ta yaya zan iya tsayawa da yaya jafar a matsayin soyayya mutanen da nakewa kallon yayyuna najini. Nafita na dan cakula abinci badon baki naso ba saidan ciki ya dauki nauyi na dan zauna da anty muka taba hira ranan hiran mama mukayi don suna germany sunje ganin likita a can. Tana ban labarin ga kafa na ciwo kuma mama taki daina cin nama da akace ta rage munyi dariya da take fada min tace ko taci ko bataci ba ciwo dole tayi. Ita kan namanta zataci gashi duk ranan da taci naman washegari kafan nata zai tashi da fitinan ciwo da sai tayi data sanin hakan. Lokacin sallah ya tayar damu muka shiga daki bayan na idar zama nayi ina lazumi a wurin har aka kira isha,i na mike nayi sallah don haka ko a gida da bi,an mu yake saboda kwadayin ladab dake cikin hakan. Zancen zuci na zauna yi wayana ya dauki kara na mika hannu na dauko a zatona yar uwata maria ce don a ranan bamu gaisa ba tun safe da ita. Number ce ba suna hakan yasa nake kwankwanton ko waye ya kirani lokacin na dai dauka ina fadin hlo muryan yaya J naji yana ajiyan zuciya yana fadin. Da fatan zakiyi hakkuri don nasan na barki a cikin zullumi da tunanen bukatan danazo dashi a kanki yau. Tsananin sonkine Rahama ya hana min sukuni don na tsunci kaina a cikinsa don haka na kasa sukini da natsuwa a tare dani ke kuma kika zabi guduwa ki barni a cikin damuwa. Rahama kiyi hakkuri ba zan iya boye abin da zuciyana ke ji akanki ba yanzu ko a gaban waye idan hakan dana aikata kuskurene kike gani ki ki daure ki fahince ni don hakan ba kuskure bane a wajen Allah. Ina son ki sani duk wani dan adam da yake rayuwa a doron kasan nan to kuwa yana tare da kalubalin rayuwarsa ni na dauka aure shine matsalana a rayuwata. Katseshi nayi da fadi a cikin kyarmar murya dana samu ba hada haruffan a bakina ina fadin don Allah yaya kayi hakkuri ba zan iya hakan ba kai yayana a matsayin yaya nake kallonka wajena. Amma sai naji yace nima haka ai Rahama har gobe har gata ke din kanwatace hakan ba yana nufin zamu daina zumunci mu bane saima mu kara donkonsa a tsakanin mu Allah kadai yasan mutanen da suyi alfahari da wanan hadin namu nan gaba. Kit na kashe wayan don na fahinci idan na biye masa da sauraren kalaminsa zan iya mashi rashin kunya girma ya fadi to kada akai wajen yasa na kashe layin ga baki daya. Na wurga wayan saman gado ina jan tsuki don na faginci tabas da ake fadan namiji baida kunya hakan gaskiyane saidai subar ke mace da jin nauyin idon mutane . Koda anty ke wani zancen wai na garasa inci abin hannunsa ni ba zan iya yaudaransa ba free,falo zan fito mashi fili in,nuna bani kaunan manufarshi kawai ya rabu dani A ZARIA Tunda ya habu ya dawo a cikin dare yana part dinshi bai fito ba har karfe goma na safe ya samu ya daga don tun bayan sallah asuba ya koma ya kwanta barci. Wanka yayi ya shirya ya fito falo matarshi na zaune tana ba Abbati abinci ya fito ya samesu a nan din dinning ya nufa don yayi breakfast kafin ya fita. Wai ina Rahama tun jiya banji motsin ta ba ya fada yana kallon matar nasa shiru tayi bata bashi amsa don har lokacin a kufule take da zancen. Bakiji bane nace ina Rahama ? Bata nan ta bashi amsa a takaice. Tana ina ? Tana Abuja tun lastweek . Abuja kuma meta tafi yi abuja ba a fada min ba bayan a karkashina take zaune ehh don a karkashinka take ai shiyasa ake muna yadda akaga dama a gidan nan. Kamar ya ban fahince ki bafa ? tace zancen ke nan ai tana Abuja tunda an hada kai ayi matasheri da kazafi don a tozarta mu tsawa ya daka mata ta fada mai meya faru ta tsaya tana wani zancen banza. Nan dai ta kwashe komai kamar yadda Nafisa ta bata labari bayan tafiyana don bataji ainihin yadda zancen yake ba da farko. Mikewa yayi ya bar abincin dake gababshi dagashi sai jallabiya a jikinshi da gajeren wando part din iya ya nufa yana tambaya ina Saratu ? Tana part din ya j salima ta fada yace good ya juya zuwa can din inda ya sameta rashe rashe saman doguwar kujera kwance. Basu ankara da shigowansa ba sai ganinsa sukayi gabansu fuska daure yace ke uban me kike a part din nan ? Saida ta dan jefo mai kallon rashin kunya take fadan ba komai tare da sauke kafafuwanta kasa ta tashi zaune hakan ya bashi daman wanka mata mari biyu masu kyau a fuskanta. La,illah kaiko Habu me tayi maka harda mari haba dai kai kuwa an hanata shigowa nan part din ne dama ? Shoute,up ya fada saida ta dan kadu tana ja da baya ya kallo Saare din yace get lost kafin na tatakaki a nan sakarai mara hankali kawai da haka zaki samu mijin aure. Bayan kina haddasana a tsakanin iyalinmu ko yaushe duk wani makirci da za a hada gidan nan kina cikinsa why kika bata kanki haka ? Ki rasa wanda zakiwa sheri sai J dan uwanki riban me zaki samu idan kin batawa dan uwanki suna ? Ni yaya yaushe na hada fada a gidan nan wani mari ya kai mata saida hancinta ya soma zubo da jini ganin hakan baisa ya kyaleta ba . Wai kasheta zakayi habu don ta fadi gaskiya ai ba itace ta fada ba nice nan don kowan mu ya gani da idanusa idan ba wani abu take nema gareshi ba zata tsaya tana magana dashi a gaban mu ? Au ke uwarsace ke nan bansan abun naki har yakai haka ba ai Nusaiba ashe doka kika bashi sai wanda kikaso yayi magana dashi a gidan nan zaiyi. Shiru tayi tana mazurai ya juya kan kanwar tasa yana fadin ki shiga hankalinki ni ba J bane na sake ganin ki a nan ba tare da yan uwank ba zaki gane baki da wayau. Wai kai ka zata wai zaman tsegumi muke yi a nan dama ai ,,,, Marin daya sauka mata a tsakiyan fuska da yasa ta ga wasu wuta sun gilma a gabanta yasa ta dafe fuskan ta soma hawaye tana fadin habu nika mara ? An mareki ko zaki ramane ya fada yana kara nufo inda take da niyar kara kai mata wani dukan su mama suka shigo falin. Tun daga kofa mama take fadin habu kai habu fa bada kai nake magana ba ko kayi haukane wai kul ka sake tabata ranka zai baci . Wai, Lafiya meye haka meya faru hakane ina daki iya kece min gaka can kana neman Saare zuciyata ya ban babu lafiya ? Wai meya kawo hakane don Allah takai kallo ga yarta dake kuka wiwi ta tare hancinta da hijab din jikinta. Bata san lokacin data nufeta ba hankali tashe tace munaga rasulu haba Habu dukane haka ko abu ka kwada mata ? Wallahi dukane mama a kan matarshi ta fada mai karya da gaskiya yayi muna hakan wallahi ba zan yarda ba karansa zanyi dan isk,,, Keko yar nan baki da albarka a gaban mu zaki bude baki ki zagesa ke wace irin mara tarbiyace wai ? Barta iya barta ta karasa yau sai an kwasheta a wajen nan duk kika bude baki kika zageni, zan gwada mata lalai dan iskan nake da gaske kuwa. Ai bata cika ba tunda ba ita tafito tayi muna haka ba idan ta isa ta fito mana ai gamu tazo an fada duk abinda ta fada maka an fada din . Ya kara zabura yayi wajenta mama dake tsaye tace habu kana kara dukan Nusaiba zan saba maka rai sosai wallahi. Ji abinda kaiwa yar uwanka ka kyauta ke nan habu ita din mace ce fa, habu, duka haka kamar ka samu jaka ? Ke Dubu ki rufe min baki a wajen nan kafin ranki yafi na yarki baci idan har ba zaki tayashi tsawatawa yar uwasa ba to ki fice daga nan. Haba Dubu ke wata irin uwace wai abinda yaran nan suka aikata alherine haka da sukayi dan uwanta fa aka hada baki da ita a bata mashi suna kan zina ? Na tambayeki nace kazafi da cin amana alherine fadansa koda hakan ya kasance gaskiya ? To balle kowan mu nan ya san babu kamshin gaskiya a cikin zancen su dole ran habu ya baci ya dauki wanan matakin ai. A hankali mama ta sake hannun saratu data kama tace ai yanzu kin gani idan kince ba zaki natsu ba sai ya illanta ki a banza ta juya ta fice daga falon. Kallonsu iya tatyi tace ku saurari sakamakon ku idan kuna jin dadin kunci gari balufacen mutum baya mata zance har mutuwa. Gaba kuma kun kulla dashi ke nan daga nan har yumal,imadi indai bafulatanin asaline zakuce na fada wata rana don sai sun rama shanmatan da kukai masu irin wanan. Ai saidai su rame na fada din suyi duk abinda zasu iya shi a dole gashi mai mata yazo daukan mata fansa zai gane ya mareni wallahi. Ki dai iya bakinki Habune dai kinsa zai iya fiya da hakan kidai san halinsa yanzune zai iya dawowa ya jibgeki Asmau data taso take fadan hakan ga Nusaiba. Malama rufe min bakinki ai tare dake muka hada plan din amma da kikaji yana jibgan mu lafewa kikayi daki ai gobema kusane zan rama . Ranan dai mama bata ji dadin iya ba don sai da tayiwa mama din tasa akan irin yadda take saka ido gida na kokarin lalacewa gasu kuma suna ganin hakan. Kowa ya shige daki daga mama har saare suka bar iya a falo tana fada saida Nafisa ta fito ita da salima suka samu ta dakatar da fadan nata. Ranan dana fara zuwa wajen training nasha dariyan zuci saboda wai wanke wanke ake tambaya yaya ake wanke kwanoni kafin a saka abincin da za aci ko anyi amfani dashi. Wanan yasa na dauki lecture a shirme ashe abin ba haka yake ba akwai yayan hutu da basu san yadda zasuyi abubuwa da dama daya kamata ace mace ta sani tun tasowanta ba. Irin wa yan nan yayan hutun da gata su sam basu san me auren yake nufi ba, sun dai dauka cewa kawai za,ayi aure aita soyewane da miji shine ma,anan auren. Cikin dan kwana biyu danake fitan sai gashi nima da nake ganin ai nasan wasu abin ashe bansan komai dagane da rayuwan mace a gidan miji ba. Shi aure ba yana nufi ki ba miji abinci bane ko kiyi ta aiki kamar jaka dole akwai matakan da mace zata bi don rayuwan aurenta yayi lasting a zamanance. Sosai na mayar da hankalina ina koyon abubuwa da bansan dasu ba ilimi ance gishirin rayuwa tabbas haka abin yake kuwa. Don ba karamin kuskure rayuwa matan gidan mu ke aikatawa ba har yar uwana kuwa dama ance zama da madauki kanwa shike kawo farin kai. Kar kice yaya ya hakkura ya daina kirana har wa yan nan kwanaki sakonsa kadai sun cika min wayata irin kin tashi lafiya kinyi sallah kinci abinci ? Kome kikeyi yanzu har yanzu baki barci ba wasu irin kaya yau kike sha,awan nasa Rahama ire iren wa yan nan maganan da sannu sabo hakan ya fara shigana ba tare dana sani ba. Inda har yakai kwana biyu banji wanan irin tambayan nasa ba da nake dauka daya mai dani karamar yarinya ashe ko hakan ne don da nuna damuwa da kulawa ake sace zuciya. Sai gashi rashin jinsa a yan kwanakin ya fara sakani dan danuwa kadan kadan zan tuna dashi a inda zuciyana ta fara raya min Allah yasa dai ba matsalan jikinsa bane kuma dai ?. To yanzu wa zan tambaya inji duk wanda na tambaya koda yar uwatace zata soma zargina a kanshi haka na dake dole da dan damuwa yayin da wani sashe na zuciyana yake ban shawara da in tambayi anty Nafisa ita kadaice ba zata taba fadawa wani komai game dani ba. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,, 3️⃣4️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Wasa wasa zancen sati biyu yake batun sharewa bai gida run bayan tafiyan wuni dako kila ya kwana yabar zaria dashi sai gashi kwanansa goma sha biyu da tafiya . Wanda yai daidai da tafiyana don tafiyana kwana goma sha,ukku ke nan yanzu hakan yasa matan yaya din a cikin damuwa . Ga iya dake sake masu zancen cewa saboda bakin ciki sun kora mata jika ya tafi shida ba lafiya ya isheshi a jiki ba amma masifansu yasa yabar gida dole. Irin wanan maganan da iya keyi yasa Nusaiba ta fito fili ta nuna damuwanta ga tafiyan nasa inda itama ta fara nuna damuwanta ko waya basu samun shi gaba daya ya daina amfani da sim din da aka sanshi dashi da farko . Daga Abuja ya wuce matatar mai don yin wasu cikin takardu daya dade yana neman daman cika hannu a cikinsa. Sai gashi kwatsam an kirashi yazo ya cika takardan an bashi daman yin hakan a lokacin don shi ya kwasa zuwa fatakwal din. Kwanasa hudu ya gama abinda ya kaishi daga can ya nufi lagos a lagos din ya samu aiyuka da yawa da suka shagal dashi wanan yasa su a zatonsu suke ganin ya bar gidane saboda matsalan daya faru din. Saidai Habu yana da labarin komai da yake gudanarwa don ya sanar dashi abinda ya taso masa don haka duk surutan da akeyi ido kawai Habu din ya zuba masu baicewa kowa kala ba. Nikan na zata ya hakkura da zancenane don jinshi shiru da nayi har anty salma namin sheri wai na kore yayana da hali ya kama kansa dani. Har take cewa Ni dama nasan za,a rina wai ansaci zanin mahaukaciya don matansa sun riga da sun girgizaki dashi Ramaah. Dama kuma ance kuskure daya mutum keyi a rayuwansa mai ban haushi don haka shi tun farko yayi kuskuren rashin daukan mataki a lokacin. Saidai ni a waje ke Ramaah irin matakin da yake son dauka din shine ake kira da gyaiyya don yafi wanda kika so ya dauka zafi don shi naso ki nuna masa aiba komai har su fahinci akwai kauna a tsakaninku ta gaskiya. Amma yanzu ai ba zasuji haushin komai ba tunda basu san kunyi hakan dashi ba kuma bame fada masu balle hakan ya damesu. Ajiyan zuciya na sauke ina lumshe idona a lokacin banjin komai a raina saina daukan fansa matukar ban dauki wanan fansan a garesu ba ina iya hade zuciyata duk sanda nayi arba dasu kuwa. Idona da suke a lumshe na,dan bude ina kallonta nace wanan saiba din ko don ita da saare zan iya hakan a yanzu anty . Nafisa ke fada min sunce wai kunya yasa na bar gari wai da bakinsu suke fadin sherinsu yayi aiki saura anty maria komai dadewa sai sunsa tabar gidan nan. Kutumuu,lesi ai uban kuturu yai kadan wallahi gida kuma zaki koma cikin sa tsunbul ba maria ba har ke sai sun gani a gidan tsakiyansu kuwa. Munyi hakan da kwana biyu na gaji sosai ranan don practical din da mukayi a training center din mu donshi ma na kwanta da wuri ranan. Misalin sha biyun dare a daidai wanan lokacin wayata dakr ajiye a karkashin filo ta dinga kara da alama kirane ke shigowa a lokacin. A cikin barci naji sautin karan yana shiga kunnena tare da verbiration din da yake fita daga wayan. Dan guntu tsuki naja tare da mika hannu cikin magiyan barci saboda dadin barcin da nake ji a lokacin. Jikina gaba daya tsami yayi nakai hannu na dinga lalubo wayar kasan filo ba tare dana tsaya duban mai kiran nawa ba na kara a kunnena bayan na dauka. Muryan yaya na tsinkayo yana fadin Ramatu Rahama tabbas kinci sunan ki don na fara sheda hakan a gareki. Ai na zata ba zaki daga wayan ba saboda dare yayi duk da dai dare baiyi ba a wajen matafiya ni gani nan yanzu haka airport ina jiran Jirgin mu ya tashi. Kalman da yake fada din yasa na gane yana shirin tafiyane wani waje lokacin shirun da yaji nayine yasa ya kara fadan hello kina jina kuwa ? Da kyat na iya bude bakina da yai min nauyi na amsa da ina ji yaya Allah ya tsare hanya aje lafiya a dawo lafiya Allah kuma ya bada sa,an tafiya. Masha Allah nagode kwarai Rahama kece kadai na kira a duk yan uwa ina sheda maki zancen tafiyan nan don ina kyautata zaton jin hakan dama a gareki. Rahama ke din Alherice a gareni sosai na fahinci hakan a yan kwanakin nan tabbas akwai alheri a taraiyana dake Rahama domin naga hasken dake tunkaro rayuwata tun zancen nan bai kankama ba sosai a tsakanin mu. Kiyi hakkuri da yayanki Rahama ki karbi bukatata dani dake din taraiyan mu akwai alheri sosai a cikinsa in sha Allahu zakice na fada wata rana. Kinsan meyasa nace hakan a gareki dole kinsan ina da dalilin hakan dana fada don kuwa nina san irin farin cikin da Allah ubangiji ya jefani a cikinsa cikin yan kwana kin nan. Rahama abinda na dade ina mafalkin samunsane Allah ya banshi a wanan lokacin . Don haka zuciyana taban ke din alherice a garemu baki daya don bani kadai ba kowa dake kusa damu wanan alherin zai shafa insha Allahu. Kalaman dayake fada min sunyi matukar daure min kai a lokacin saboda ban fahinceshi ba sam don haka sai nake fadi a yar siririyar murya da Allah ya kara tabbatar muna da alherin ya amsa cike da jin dadi da amin Rahamata. Sai naji abin wani bambarakwai a kunnuwata wai nice yaya yake kira da Rahamarsa haba dai maza ashe haka suke saboda soyayya sai babban mutum ya zamo yaro a gabanka. Akwai wayewan kai a yar fahintan da naiwa rayuwan mutum biyu a yanzu ma,ana miji da mata ko saurayi da budurwa. A tsakaninsu akwai kyautatawa da burge juna a lokacin taraina koda akwai sabanin hankali idan Allah ya hada wanan burgewan yana nan a zukatansu. Jin nayi shiru na shiga dogon tunane yasa yake fadin kina jina Rahama ina son dana dawo wanan tafiyan in sha Allahu za ayi komai a tsakanin mu. Fatana ki kwantar da hankalinki ki cire wani shakku da tsoro a zuciyar ki kada ki tsaya duban rayuwan wani ki duba tamu da nake kokarin ginawa a yanzu. Sam ban yarda da tsarin anty Salma na cewa ki zauna a hostel ko a kama campus ba nafi bukatan kai tsaye ki dawo Zaria a matsayin matar jafar. Gabana naji ya fadi da wanan kalman da sauri na tareshi da fadin a,a yaya don Allah kayi hakkuri ban taba wanan tunanen ba kuma ba zanyi a yanzu ba. Kai din a yayyuna nake daukanku yaya ba irin wanan zancen a tsakanin mu don Allah kamar yadda ka fada a baya ba a daukan hukunci a cikin fushi yaya. Haka kuma matanka basuyi karya ba yaya kaidin ba tsaran aurena bane sun fadi gaskiya da sukace naje na nemi daidai dani dan daji. Nima ai daga dajin asalina yake ko habu bai fada maku asalin mu daga kauye mahaifin mu ya fito yazo nan zaria ba. Sun san kin fisu da komai Rahama hassadan hakan yasa suka sakaki a gaba har sherinsu ya haska min hanyan da ban gani da farko saida kalamansu ya haska min hanya sun kwakwasa min kofa da zan bude sabon shafi a rayuwata. Don haka a cikin kalamina Rahama ba gudu ba ja da baya don a shirye na fito da makamaina kan mai uwa da wabi zanyi lokaci guda. Kasake nayi ga bugun zuciya dake harba min lokaci guda tunane barkatai suka taru min a kasan zuciyana . Tabbas idan na samu yaya a miji na more a rayuwata saidai bahaushe yace ana barin halas don kunya dolene naki karban tayin yaya a kaina don tsira da mutuncin yar uwata dake aure a gidansu . Yau badon hakan ba kai tsaye zan amsa tayin nasa sai dai wani sashe na zuciyana yana mai ban shawara da mai zai hana inbi shawaran anty salma ko girgiza imanin su indanyi. Muryanshi naji yana fadin zan barki Rahama an fara sanar muna da mu karaso kusa jirgin mu yana kan layi. Saina samu muryata da fadin to yaya Allah ya kaika lafiya ya bada sa,ab tafiya amin Rahamata in kuma dawo lafiya in sameki a shirye da tarona. Muka kashe wayan da karfin gaske nake jin zuciyata ta bugawa hakan yasa na sauke ajiyan zuciya ina lumshe idanuwa tunane barkatai nayisa a lokacin kan in yarda ko kada in yarda . Washegari da safe haka na tashi ina jin zuciyana tayi min nauyi don kwana tunanen dana zaunayi dogon riga dinkin dinkin atamfa mai A sharp na saka a jikina sai dan karamin gyale dana dora a kaina . Abujane fa birnin taraiya Abuja ko dame kazo anfika saidai kayi naka banjintar ka bari wani yazo da tasa kalan . A falo na samu anty Salma zaune tana ba yaranta abinci tun daga fitowana take fadin oya zo na zata ai kina kwancene wanan dan naki dan rigima wai ba zaici abinci ba haka zai tafi school da yunwa. Murmushi nayi na karasa na karbi abincin a hannunta ina lalashin yaron kafin ya soma karba yaci daga hannuna har suka gama na rakasu har bakin mota suka tafi. Falon na dawo don sai goma zan fita tana waya na kwashe kayan zuwa kitchen nakai na fito bayan mun gaisa da yan aikinta dake dauka ni din yar uwatarcen ta jini kamar yadda take fada a kaina din Don haka suke kirana da small hjy zama nayi a gefenta din ta juyo tana fadin kai Ramaah wai kinga yadda kikayi wani fresh dake kuwa wanan aiko yau kika koma zaria ba zasu ganeki ba Waini kan ya zancen mutumin nakine kwana biyu banji zancensa ko kin fita batunsane wai gaskiya Rahama ina sonki da guy din nan. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,, 3️⃣5️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Bayan sati biyu da hakan shigan bazata yayi masu don da safe yashigo gidan wanda ke nuna a garin ya kwana ke nan don duk wanda yagashi a zaria karfe takwas na safe haka yasan a cikin garin ya kwana. An kasa samun wanda zai tambayeshi ina ya kwana sai iyace take fadin amma a garin nan ka kwana Jafaru. Ya bata amsa da eh iya cikin gari na kwana nashigi da darene sai kawai na sauka wancan gidan nawa. Kana da wani gidane dama Jafar ban taba sani ba kowama bai sani ba iya idan ba yanzun din da nake fada maki ba amma na dade da ginasa ai komai kuma na saka a cikin gidan. Ina son in kai amaryata can ta zauna ita kadai sai masu tayata aiki kawai a gidan kinga na samu gidan hutu ke nan . Can zai zama Abuja kenan yaya nan kuma gidan kwamacala ya zama lagos ko don lagos shike daukan duk wani kwaram da amma. Salimace take fadin hakan a cikin barkwanci ga dan uwan nata data dauka zolayan iya yakeyi ya fadi hakan. Saiba dake zaune ta tsoma bakiga zancen da fadin babu wata shegiyan da zata shigo muna gida iyamu, mun isheka rayuwa muma din ya aka iya damu balle aje dauko wata. Ta fada tana turo baki dake nuna tana cike dashi har lokacin gashi ya sharesu kusan wata daya ke nan yanzu ya dawo kuma ba wace ya tsaya kulawa a cikinsu. Itako Asmau sai cewa tayi ai lagos din ma ba laifi indai zaka zauna lafiya ko a lagos ai akwai more rayuwa sosai ma don yafi wani wajen sau dubu. Salima tace amma ai kusan cewa Villa shiyafi dadi ko ? Don gaka ga gidan kudi kullum kana jin kamshin bugunsu haka kuma shine headquater da kowa ya sani dai dole yaya ya tare da amaryansa Villar ku kuma kuna nan da yara kuna kwamacalan ku. Dadin abin dai ba a canzawa tuwo suna haka kuma baka zama da miya ba tuwo don shine abokin hadinsa mu din dai mune dai ba wata yar banzan da zata sake shigowa gidan nan da sunan matan aure a part din nan sai dai can gaba kuma . Wayanshi dake kusa dashi ya dauka cikin rashin damuwa da zantukan da sukeyi lokacin can a ka daga yake fadin kai Habu kana inane wai gani gida zaria ? Ina nan kano tun shekaran jiya ana karasa sauke maine har yanzu to idan an gama kazo gida don ba dadewa zanyi ba zan koma . Ina tafe yau din nan in sha Allahu zuwa yamma Habu din ya fada yace Allah ya kawo ka lafiya yana kashe wayar tasa ya aje gefe daya. Sai lokacin iya ke fadin da alama dai wani tafiyan zakayi ke nan kuma Allah ya tsare muna ku Jafar a duk inda kuka nufa din ya amsa da amin iya. Yanzuma akwai abinda nashigo yi a nan zaria don da baku ganni maza ba saboda aiyukan da suka taso sosai a yanzu sai iyan ta karba da madalla haka muke son ji ko yaushe aiki ai alherine. Ta juya ta kalli salima data rakota tana fadin to ke zaki zauna nan ne kuna cika baki ko zaki maidani wajena don naga baku karasa cacan bakin naku ba har yanzu. Ehh lalai ma Iya cacan baki kika dauki zancen mu ashe yanzu akwai wata wace zatayi gigin shigo muna gidan nan da sunan kishiya ? Au kina wasa wuka a gaban doki ne don yaji tsoro ko to jafaru ba raggon maza bane yana da ikon cikawa da biyu a rana daya. Yadda aka auroki kika shigo kika hana wata rawan hantsi kema haka za a dauko wata a kawo bayanki don ba a haifi namiji don mace daya ba dama. Tashi muje yar nan ta dubi Salima bayan ta gama maganan daya harzuka Saiba din data gane nufinta ta zata asirin da take bankawa jikan nata yana tasiri akansane da har bai iya daukan wani kwakwaran mataki akansu. Jafar yasha yiwa iya korafi akan Saiba ko ince ya kawo mata karan sai ba din kan barbade barbade ga abinci ko cusa abu a gabanta bayab sun gama sunna ya ga abin tun yana mata fadan hakan dagashi sai ita har yagane hakan yabi jikinta ba zai iya lamuntan hakan gareta ba yakai karanta wajen iyan akan a tsawata mata ta daina wanan halin. Wanan yasa ciwon sa na farko harda zargin saiba din saida sukayi wanda dama hakane ga mace mai hadawa da surukulle wata rana har abata abinda zai cutawa abokin zamanta cikin rashin sani da sunan taimako a gareta. Ya Habu bai shigo gari ba sai wajajen la,asar ya dan gauta ya iso tun shigowansa gidan ya hango motan dan uwansa a kofan part dinsa. Nasa part din ya tsayar da motarsa ya shiga ciki inda ya samu matarsa da dansa don ita ba ma,abociyar son shiga jama,a bace wanan ya kara mata bakin jini a gidan suka kara tsanarta. Don sun dauka daukan kai take masu don tana ganin kamar ta fisu wanda ba haka bane haline saika zauna da ita na wani lokaci batace dakai kalla ba saika gaji kayi mata magana. A part din iya suka hadu da dan uwan nasa sun dan zauna na lokaci kafin suka mike da sunan zuwa wajen mama dake can tudun wada family house dinsu ita da Saare da Nafisa. Tun zuwa sunan matar yaya sani basu dawo gidan ba suka zauna can din wanda ita Saare bata so hakan ba amma mama Dubu tace ba zata koma gidan yayyun taba sai tare da ita wanan zaman takuran Saare take cikinsa duk kwanakin. Motar Habu sukai amfani dashi suka fice gidan a hanya Habu daya kula da rashin sakin jikin dan uwan nasa yake fadin kace kana son ganina J ? Haka kuma tun shigowana part din iya na kula da dan fadawan da kayi don kayi rama sosai a yadda na barka wani abin ya farune kuma ? Ya dan juyo daga barin kallon titin da yake yana mai dan tsurawa dan uwan nasa idanu na dan lokaci kafin ya mayar a hanya yaci gaba da tukin da yakeyi. Yayi wanan magananne don yadda yaga damuwa karara a fuskan dan uwan nasa don bai saba ganinsa a hakaba ko da yaushe yana a yanayin nishadi da walwala . A hankali J din ya kwantar da kansa jikin kujeran mota yana sauke ajiyan zuciya tare da lumshe idanunsa yace. Bari Habu ina cikin wani dan cakwakiyane a kwanakin nan duk da kaima nasan abin zai shafe ka duk yadda ka kauce kuwa . Subbahanallahi mene wanan abin J jikin nakane ya kara tashi kuma again ya girgiza kai yana fadin ba jikin bane Habu rigima dai na fada a ciki lokaci guda. Habu ya jinjina kanshi yace ina saurareb ka nasan dai duk rigiman da zaka jawo ba wanda zaiyi kasa da martaban mu bane a idon mutane in sha Allahu. In Allah ya yarda ba irin wanan da kake nufi bane habu rigiman soyayya na fada lokaci guda ka kangani a haka na rasa wanda zan fara tunkara da zancen nan saikai habu don nasan zaka sama min mafita in sha Allah. Soyayya kuma J kana da mata biyu fa a gida me zaisa ka fada tarkon wani soyayya kuma a yanzu again ? Nima abinda nake duba ke nan Habu abin mamaki ban taba tunanen zan fada tarkon soyayya irin haka ba lokaci guda sai gashi Allah ya jarebeni da hakan . Lokaci guda habu Allah ya jarabeni da matukar son yarinyar da kowa zaiyi mamakin hakan a gareni amma ubangiji cikin hikimarsa da buwayansa da masifan sonta haka lokaci guda. Guntun tsuki Habu ya saka lokaci guda yana fadin wanan ai baikai na tashin hankali haka ba ni harka firgitani wallahi . Aure a yanzu gareka ai wata mafitace ga wanan matan naka da basu san ciwon kansu ba Allah yasa dai ita wanan din ta kwaraice da zata fiddakai kunyan abokanka. Kaifa Habu dadina da kai ke nan ba sai kajira kaji ko wacece yarinyar ba a yanzu kana zaton zan yarda in kara jefa kaina a duhu irin hakane ? Wa yan nan ka dauka auren kaddara da kurciya nayi dasu yanzu ko aure nake so na kece raini a kaina wai kasan yadda nake zaman kaddara da kazaman matan nan kuwa ? Ankai fa nida part dina habu har gudunsa nake wani lokaci ka dai sanni da kyankyamin tsiya tun farko sai gashi ubangiji yai min wanan jerabawan kazantar akansu. Ankai habu ko ruwa na dauka koda a gora ina jin kyankyaminsa haka inda zan kwanta sain kakabe da kaina in samu in raba in kwanta sabo tarin jakkanci irin nasu. Ni nakance ashe shiyasa suke abokai tun farko haline yazo daya ashe babu wace zata gyara wata a cikinsu ranan ina jin kannen Asmau suna mata fada wai har yanzu ashe tana nan da kazantar ta suna ganin kokarina da nake iya rayuwa cikin wanan bolar dasu haka ka duba fa Habu yan uwanta ma sun shedeta da kazantan tanan ashe haka. Habu yayi kasake yana sauren dan uwan nasa tare da kara tausayawa irin rayuwan daya tsunci kanshi a ciki da matan nasa don zai iya cewa dan uwan nasa sam bai morewa aure ba. Haka kuma wanan zancen da dan uwansa ke son fada mashi a yanzu matsalace babba don abin bai tsaya akan soyayya kadai ba game da yarinyar da yake son ya aura din . Yaji J din yayi huci gumi yana dan tartso mashi saman goshinsa tankar wanda yake cikin mumunan yanayi da sauri ya kara waigo dan uwan nasa yace. J wai meke farune dakai haka nifa gaba daya ka rudani ma ka wani sauya kamar ba kai ba wanan wace yarinyace haka wai take son baka wahala ? Ko kuma ita din ba musulma bace kake tunanen abinda zai biyo bayan zancen ga iyayyen mu ko kuwa sun hana maka itace an samu matsala daga iyayyen yarinyar ne ? Murmushin karfin hali J din yayi yace haba Habu ba wata bace fa yarinyar da sonta ya rikitani min tulin tunane illah Rahama dai kanwar matarka da matana sukai min zargin kulata wanan abinda sukai min kamar sun ingizanine ko haske min hanya akan wanan yarinyar Rahama a yanzu. Saida Habu yaja wani uban burki a saman titi Allah ya taimaka hanya ba wasu motoci a cikinsa sosai ya juyo yana kallon dan uwan nasa yace. Rahama dai Ramaah ta wajen maria matana kake nufi J ? J din ya marairaice murya tamkar zaiyi kuka cikin yanayi na kyarmar murya yace Habu mafita nake so da zancen nan don har nakai kaina gareta garesu da ita yayan nasu nacan . Ban samu matasala ga yar uwar tasu ba saiga Rahama din ita ta nuna kaduwa da jin zancen saidai nasan yar uwar nata tasa yanzu ta soma saurarena. Shiru Habu yayi yana wasu tunane da baisan iya adadinsu ba lokaci guda kafin yaji muryan dan uwan nasa yana fadin . Habu ina son auren yarinyar nan a yanzu don irin halaiyansu nagari dako wani namiji ke fatan samun mace ta kasance a hakan. Bani barci da dadi akan tunanen yarinyar nan a yanzu duk abinda nake wanan abin ne yanzu a gabana na rasa ta ina zan fara nasan akwai cakwakiya sosai da rigimar auren nan idan hakan ya tabbata din saidai na matana mai saukine tunda ba waje daya zan ajiyesu ba don gudun fitina kuma ga yarta a gidan hakan ba zai yuyu garesu ba. Ina matukar jirkita akan zancen nan Habu rasa Rahama a wajena tankar rasa rayuwatane habu ban kara furgicewa ba saida naji ita wanan yar uwar tasu tana fadin. Koda Rahama zata dawo zaria school ba dai a gidan mu ba saidai ta zauna hostel ko kuma ta kama mata campus ta zauna ina hakan zai yuyu gamu habu ? Habu ya nisa yana fadin ni a ganina wanan ba matsala bane babba haka J matsala dai dayace shine ka samu yardan yarinyar wanda nasan da wuya gaskiya hakan ya faru a cikin sauki. Duk da haka idan matanka sunji wanan zancen yaya zasu dauki hasashen su akanka na baya zaka iya jure kalubalin da zai biyo bayan zancen. Idan har zaka iya ninasan hanyar da zamu bullowa ita Rahaman da yarta dama wani da zai iya kawo cikas a cikin zancen mafita dayace shine muje muga hardo bakin mu a laikum in yaso daga baya sai a baiyana wa kowa yasani. Amma kuma ni dai shawaran da zan baka shine idan kasan matanka zasu kawowa yarinyar nan nakasu a rayuwan ku gara tun wuri kayi hakkuri ka cire wanan zancen Rahaman a cikin zuciyar ka don na fahinci har da gaiya kake son aikata hakan. A harzuke ya soma fadin wai Habu su suka ajeni koni na ajesu dubaiya nakeyi nake zaune dasu kasani amma kuma yanzu kana fada min in hakkura da Rahama ? Kai Habu ya girgiza yana fadin J kayi hakkuri ba wai bani sonka da Rahama bane nima na dade inawa wani dan uwana samun wanan yarinyar Rahama saboda halaiyanta dayayi min. Amma yanzu kai daka bullo da wanan zancen akwai babban aiki nake hango maka agabanka don fitina kake son janyowa kanka a ganin ka ita Rahama yanzu bata da wanda take sone ? Haka kuma matan ka kana ganin zasu kyaleku ku zauna lafiyane wanan abubuwan nake hango maka J don tasu mama mai saukine matukar muka samu kan kawu ai an gama zancen. Wayan J din yayi kara amma ya kasa dagawa har saida Habu din yace dashi wayarkafa na ringing J ka daga mana. Sannan yakai hannunshi ya duba Saiba ce ta kirashi bai san lokacin daya saki wani dogon tsuki ba yana fadin wai meye kike kirana haka ba yanzu na fito gidan ba ? Ya katse kiran cike da jin haushinta da takaici don yasan sauraren wayan ba zai haddasa mashi komai ba a karshe sai bacin rai . Yanzu duk fadin duniya inba Rahamace zata kirashi ba baijin zai iya daukan wayan wani a lokacin fahintar halin da yake ciki da habu yayi yasa ya dan sasauta murya ga dan uwan nasa yana fadin. Kayi hakkuri J ka bani nan zuwa safe zanyi tunanen abinyi amma kabi komai a sannu kada a gane kana cikin wanan damuwa komai zaizo da sauki in sha Allahu. Nidai yanzu abinda nake so da kai shine ka kwantar da hankalinka saboda kasan ba lafiyane dakai ba sosai gaka kuma ka rikitowa kanka wani aure yanzu. Sai lokacin yayi dan murmushi yacewa kanin nasa ai wanan yasa nake son nuna masu iyakar kyamata da sukayi akan ciwon nawa don kowan su saita gane kuren yin hakan. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,, 3️⃣6️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Kwace nake saman gado na rufe jikina lif da bargo don yanayin akwai sanyin safiya a ranan gashi dai ina ganin kamar banyi barci ba amma kuma a zahirin barcin ne saidai ba sosai ba ya dibeni. Har anty Salma ta shigo dakin nawa amma banji shigowan nata ba lokacin zama tayi a bakin gadon takai hannu tana dafani tare da ambatar sunana lokaci guda. A hankali na bude idona ina yaye bargon dana rufa dashi nakai kallona da lumsasun idanuwa dake nuna ina jin barci a lokacin ga anty Salma dake zaune a kusa dani ta dafani. Ta bushe da dariya tana fadin lalai Ramaah ta yau don ba fita kika samu sakatan barci haka tun daga kofa nake ta sallama amma baki jini ba. Yunkurin dagawa daga kwancen nayi ina fadin kuma fa ban dade da kwanciya ba barcin ya daukeni haka ashe ina kwana anty ? Ta saki ajiyan zuciya ta dago idanunta gareni tana amsa gaisuwan kafin tace dani mijin maria ne mukai waya dashi game dake jiya da dare yau da safe ma ya kira shine nace barin sameki ? Ya Habu kuma na fada a sanyayye take yanayina kuma ya sauya lokaci guda nake fadin wai in koma zaria ko dama nasan idan ya dawo ya samu ban nan sai yayi barazanan fadan nan nasa yanzu cewa zaiyi an kusa komawa hutu kila ? Murmushi ta sauke a fuskanta take fadin kusan haka dinne saidai wanan ba wai zancen school bane Rahama zancen tsakaninki da dan uwansa yake min. Cikin firgici na sake kallonta nace ya sani ke nan anty ? Ehh ya fada masa komai har da zuwansa nan Rahama yanzu na yarda guy din nan da gaskiya yana son ki sosai wallahi kuma tsakani da Allah yake kaunan ki badon sha,awa ko wani abuba. Amma ke naga tsoron matansa kada su cinyeki danya yayi tasiri sosai a zuciyanki sun riga da sun firgitaki da mijin nasu. Ba haka bane anty ? To meye idan ba haka ba Rahama kin fada da bakinki guy din nan yana da mutunci sosai haka kuma yana kaunan ki din me ake nema ga aure. Kawai ki fita zancen matanshi ki bada kai bori ya hau musha buki mukan muga yadda zasuyi tunda dai da kurciyanshi har yanzu ba mai cewa ma yayi auren farko balle mata biyu. Kawai dai rigimace irin ta mallam bahaushe na atara mata a gida ana tunkaho shine kawai matsalan shi amma meye a ciki ? Ni abinda yasa nake maki kwadayinsa yadda naga dan uwansa da mutunci mijin maria shiyasa nake maki fatan ki sameshi a matsayin miji kema don nasan zasu rikeku bisa amana. Mutanen yanzu ba ka shedansu Rahama sam hankalina bai kwata da zancen Adamu ba shiyasa nanuna mashi bazan bashi ke ba gara tun wuri ya bari. Akwai da dama suna sonki ta wajena sam hankalina bai kwanta dasu ba ko kadan donshi nake kore zancesu idan sun nuna hakan. Daddy ya nuna muna cewa abu na farko da zamu fara yarda dashi ga mutum shine natsuwa da mutunci mutum a ganin farko da nayiwa bawan Allah nan Jafaru na hango natsuwa da kamala a tare dashi baizo gurin da wasa ba Rahama. Da niyar aure ya tunkareki don haka ba wasa a cikin zancen shi gashi yanzu kuma har ya gabatar da zancen ga dan uwansa alama ya nuna ke nan bai kaunan dogon dadewa da zai iya kawo maku cikas a zancen. Sam banji wani faduwan gaba ko darr na shakunsa ba donshi kikaga ina baki kwarim gwiwa akan zancen dan nasan a gaba hakan zaiwa kowan ku dadi. Kada ki duba bayan ki duba gaba a rayuwan ki ba lalai bane Allah yaba bawansa dama irin hakan sau biyu damankine a yanzu yazo maki don haka kada kiyi wasa da wanan daman a rayuwanki. Shidai din ba wai tsoho bane ina fada maki akwai sa,anshi da basuyi ko auren fari ba a wani wajen wanan kawai rigimace irin ta malam ba haushe. Don haka nidai ba zan maki dole ba Rahama kiyi shawara da zuciyar ki koda ita maria duk abinda kuka yanke mai kyaune don kece mai zama bani ba . Kallon da nayi mata take fadin No banson na fada maki ra,ayinane a yanzu daga baya ki dawo kina fadin nice na sakaki aurensa idan ba haka ba da zance kawai ki yarda ki amince da bukatan sa don dai zuciyana ya kwanta gaskiya da zancen guy din . Na fahinci shi mutumne mai saukin kai yana bukatan macen da zata kwantar mashi da hankaline yanzu akusa dashi wananne kawai yasakashi kara aure a fahintana. So ki bashi chances mu gwadashi mu gani don bai kamata ace kin kinki yarda da tayinsa ba in sha Allah hakan zai zamo alheri a gareku baki daya. Shiru dakin yayi na dan lokaci kowa da abinda yake tunane a zuciyarsa nikan a bangarena saina dauka anty salma ashe bata kaunana da zatace in shiga cikin kwamacalan gidan ya J a buga wasan dani. Matan da babu zaman lafiya a tsakaninsu suna su biyun suma basu bar kansu ba ni wani gulma ko kwadayi zai daukeni zuwa jefa kaina irin wanan gidan ? Idan har naga zata takura min da zance J gaskiya gara na hakkura da zama wajenta in koma wani wajen da zama nasan dai banda wani matsala ga zamana a gidana ta banda wanan zancen J daya bullo a yanzu. Shi din ne kuma zaisa na bar wajenta in koma gidan daddy don ban tashi komawa zaria a wayanzu saboda har lokacin ina jin zafin cin mutuncu da matan nan sukayi min duk da bani kadai bane da Nafisace. Amma ai sun labe ga sabarane suka halbi karsana don ni dai sukafiyiwa mumunan kazafi da alakantani da mijinsu kan kwadayi. Idona runtse naji anty Salma na fadin zan tafi in shirya nasan dai mijin maria din zai kirani yaji ya mukayi dake zan kiraki ki fada mai shawaran da kika yanke din. Ta mike ta fice daga dakin na daga kai ina binta da kallon mamaki da zargin yau inda yar uwarta na jini nake ba zata taba min fatan auren mutum irin yaya Jafar ba haka kwatsan in fada cikin cakwakiyar gidansa da gangan da gangan haka. Dolema ace saboda kudine nashiga ba wanda zai kawo cewa wani dalili na daban ne Allah ya hadani dashi ina kallon irin hassadan da matan sauran yan uwansu suke nunawa yar uwata dasu kansu matan yaya J din da idona nasan komai don ina gani kuma ina ji ai. Shawara nake tayi a raina dashi na wuni ranan shawarana yafi karkata da inbar gidan anty salma idan zata takura min da zancen J in koma gidan daddy baki alaikum. ZARIA To zance dai kawu dauda baiyi wani dogon mamaki ba da zancen da yayan yar uwar nasa suka zo mashi dashi tunda shina mijine yana hango dacewan hakan. Saidai shakuwan daya kawo shine anya kuwa Jafar yayi tunane kafin ya yanke hunkuncin hakan da zuciyarsa aure fa ba abin wasa bane. Tabbas nayi tunane kawu ko banyi tunanen yin hakan akan yarinyar nan ba kukanku masu hango hakan a garenine. Duba ga irin kyautatawan da yarinyar nan ta tsaya tayi a kaina lokacin da nake bukatan kulawan matana a gareni ba tare data nuna kyama ko gajiyarta ba kawu ? Tabbas hakane Jafar nasan wanan kwarai kuwa to amma baka duban zargin matanka akan kana yawan kula yarinyar nan zai zama gaskiya idan hakan ya tabbata. Kawu nafi tsoron Allah da mutum Allah ne ya halasta min hakan ba wani abin kaucewa addini zanyi ba a yanzu abune na raya sunnan ma,aikin Allah nake kokarin gudanarwa. Jafar na dai fahinci daka riga daka yanke hukuncin hakan a zuciyar ka tun kan kazo nan din nima kuma ba zan hanaka hakan ba duba da abin da ke hasashe akai. Amma kai Habu kana ganin ba matsala yun hakan game da naka auren matarka zata bada goyon bayan yar uwarta ta shigo gidan da take aure da sunan auren ahali daya kuma ? Sai lokacin Habu dake zaune yana kallon ikon Allah yadda dan uwan nasa yake abu kamar ba kai sake ba ya soma gyaran murya da fadin. Kawu ni ina ganin tunda Allah bai hana abin nan ba kawai ku kyaleshi yayi abinsa har in yarinyar zata amin ai kamar ba matsala dai. Kawu din yace ke nan akwai matsala daga bangaren yarinyar ke nan kana dai nufin bada sanin taba yake shirin hakan kome ?. Eh to gaskiya ta sani amma kasan halin mata dubaiyan halaka wanan ne suke duba a yanzu yasa sam bata amince ba duba ga yadda ake da matansa. Ita me dakinka fa tasan da zancen kawu ya tambaya da sauri Habu din ya girgiza kansa yana fadin bata sani ba gaskiya ban ma son ta sani ai yanzu gudun kada mu samu matsala. Don gaskiya idan har tasan da hakan yana da wuya ta yarda da wanan abin hakan yasa nake son mu rigata zuwa can garinsu muga shi hardo don yasan ta hanyar da zai bullo mata kafin ta ruguza abin nasan halin maria da wuya ta amince da hakan gaskiya. Hakan baida matsala tunda kana ganin hakan zaifi sauki yanzu yaushe kuke son ayi tafiyan sai ita nahaifiyar ku kun sanar dasu zancen. Kawu ni banson wanan zancen ya fita a yanzu sai idan Allah ya tabbatar dashi duk maiji ma yaji amma yanzu fitar da zancen yana iya kawo matsala a gidan mu. Kaga ga ita matar hakan ba zai mata dadi ba haka kuma ana iya samun matsala a bangaren mama ta kawo cikas a cikin zancen donshi don Allah kawu a bari sai munje can din idan mun dawo idan zaka fadawa mama din sai a fada mata abinda ke nan. To shike nan tunda kaga haka yafi Allah ya tabbatar muna da alheri shi lamarin aure da haihuwa haka mutuwa ba a son baki yai masa yawa. Yanzu yaushe zamu tafi kallon Jafar din Habu yayi sai kuma ya koma yace da kawu din ko gobe in Allah ya kaimu ai muna iya zuwa tunda kowan mu yana da tsabgogi a gabansa da zaiyi zuwa jibi. To shike nan Allah ya kaimu karfe nawa zamu fito ke nan da zaran an sallame sallah in sha Allahu zamuzo mu daukeka mu tafi da hakan suka bar gidan kawu din da wanan zancen. Nikan nayi jira banji kira ba karshe ma fita tayi zuwa wajen tsabgoginta ta barni gida da yara da yake weekend ne ranan. Don haka banji komai a gareta ba barxcin mu mukayi sosai saida Yanda ta kira wayana na falka muka gaisa take tambayana anty salma nace ta fita unguwa. Muka danyi hira take fadin tana son zuwa gidan maman mu kaduna, saidai bata son zuwa a yini kwana take son tayi idan taje ta dan huta. Kai ni gaskiya ba zan iya zuwa in kwana biyu wanan gida ba ko yaushe fa mijinta yana gida bai fita ko ina shi ni gaskiya saboda shine banson zuwa din. Kaji da wani zance kuma ? Ina kike son ya dinga zuwa dama banda abinki ai hakan ma mutuncine bai fita ba balle a ce yana dattijo yana kuma yawo a gari bai kama mutuncin kansa ba. Nan dai muka kauda zancen take fada min ai yaya J ya dawo shekaran jiya yanzu haka yana gari sunyi tafiya ma a ranan da yaya habu nace Allah ya dawo dasu lafiya. Take fadin yan iskan ai ance har yanzu fushi yakeyi dasu salima ke fada min dazun data shigo nace wai ita anty salima bata koma bane har yanzu ? Ai tayi relocation ta dawo garin nan da services din nata wai shi yaya jafar din ya hanata komawa kasan iyamuran tace. A raina nace tabdi nikan ai ba mai kawo min wanan idan na tafi na tafi ke nan ma saina gama indawo gida baki daya don ba zan yarda da irin haka ba. Iya fa na tambaya ta kwashe da dariya take fadin iya na nan shekaran jiya mun jima tare ai don na shiga wajenta gaida ita da kafa. Take min kwarmaton matan yaya din tace tana ganin yana gab da kara aure nace Allah yasa yan iska ya auro masu wace zata zama masu karfen kafa a gidan. Ke nifa Saiba nan takai min ko ina na rasa mena tare mata a gidan nan har Abba fa ta hada cikin rigimarmu donni har yanzu batayi min magana nima banyi mata. Sai gashi fada ya kaule tsakaninta da salima wai akan Abba don ya dauki tedy din yar ta da suka shiga part din tace ya aje aiba ubansa ya saya ba . Ita dai ta sani zata samu daidai da ita koba namiji ba aiya fita sanin kan sheri tana nan ta kasa zaman lafiya da kowa a gida sai masifan tsiya. Mun dan jima kafin muyi sallama duk tambayan da take min akan yaushe zan dawo ban fada ba don bazan iya cewa ba zan dawo ba ai saidai taji a bakin anty Salma. Su hudu sukai tafiyan zuwa Adamawan mu na cameroon wajen hardo wanda tun safe suka tashi sai da yamma suka isa ruggan hardo. Duk da garine harda wutan Nepa akwai dan kauyen namu taro na sosai akai masu tare da mutuntasu sai bayan sun hutane don a ranan zasu dawo. Kawu ya gabatarwa Hardon abinda ya kawosu watau neman auren diyansu da maria matar Habu take riko wanda kuma shi yayan habu din ne yake neman auren. Daga inda Hardon yake zaune sai faman girgiza kai da yakeyi yana fadin Allahu akbar tokai kawun yara a kwashe duka a baku gida daya. Muma nan ai muna da bukata hadin irin bawai muyi abin rashin hankali mu dauki yara har biyu ciki daya mu mikawa daki daya ba kuma ? Hardo ai Allah bai hana ba kawu ya fada hardon yace na sani ai donshine bani da ja dan sunnah ce babba hakan garemu musulmai. Maganan manya rabi da rabi hirace har da hiran jikin yaya da yai fama dashi suka tabo cikin zancen nasu hardon ke fadin Allahu akbar. Kawu dai yana ta masa hira a cikin hikima yana kara cusawa hardo zancen a zuciya hardon yace to ai baku fada muna ba da munyi namu na nan mugwada a gani ko za a dace. Kuna zube diya haka cikin duniya ba tare da kun tsumasu ba tayaya mutum na wanan irin shiga mutanen za a sakeshi kara zube yayi alkawarin zai basa sayyun itatuwansa yaje yacigaba da gwadawa har habu da kowa nasa zasu iya amfani dashi. Yasa murya ya kira shatu tazo yace ta debo masa wasu magani a cikin yaren mu na fulani ta juya taje bata jima ba sai gata dasu ta dawo. Ta mika mashi ko wani saida ya tsakura ya dandana yake masu bayani don su gane tare da aikin maganin . ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,, 3️⃣7️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Wanan dalilin karban maganin a hannun hardo don gaba dayansu sunsan cewa maganine mai tasiri wanda sunsan zai amfane su sosai nan gaba. Don akwai magani sahihi a wajen fulanin asali dama ance ba a hardon banza sai wanda yasan abinda ya taka yake zama hardon kewaye. Don haka suka dakata da tafiyan nasu aranan a nan ruggan suka kwana suna ganawa da hardo don kawai su mallaki maganin daga hardo . Wanda shida kansa hardon ya kwadaita masu din don ganin a yanzu yaran sun zamo a halinshi tunda suna auren yayansu. Yaga ya taimaka masu da abinda zasu kare kawunansu dashi daga magautansu wanda su basu san hakan ba sai kaura da kai da suke faman yi tare da makiyansu. Mussanman kawu dauda da abu yake cinsa a zuciya da dadewa game da diyan yar uwar tasa duk da bai fito fili yayiwa hardo bayanin akansu yake nema ba amma shi hardon ya san hakan ya boye mashine kawai . Kallon kawu din yake karr don hakane ya taya masu maganin da bakinsa da suka fito da zancen jifan da akewa ya jafar din kuma jifan yana cinmasa har yana kaishi kwance kamar ba za,ayi dashi ba. Hakan yasa irin hikimarsu ta manya ya fara kebewa da kawu yaji ta bakinsa inda ya bashi iya abinda zai iya bashi don shi kawu din cewa yayi a taimaka masa da wanda zai rika karban abu wajen wanda duk ya bukaci abin hannunsa an kuma bashi din. Saida kawu zai fita yace ya turo mashi Jafar yai wani magana dashi daya shafi zancen wajen aikinsa hakan yasa kawu din ya fadawa Jafar da ya shiga zai gana da hardo. Jafar din ya dan tsaya jim yana dauka akan zancen Rahamane kawu ya gana da hardo din sai bayan ya shigane yace aida sun shigo tare da Habu inda ya kira wani yaronsa ya nemo habu yazo shima. Bayan sun zaunane ya soma magana yana fadin ku saurareni kuji abinda zan fada maku don yanzu kun zama yayana tunda kuna auren jinina. Don abinda yasa na nemi ganawa daku shine kuna tafiya inwanku a waje don haka kowa ya taka ku lokaci daya zai sameku don ku din kamar yayan rokone. Suka dubi juna a tsakaninsu yace akwai wani abu da mata keyi yayin da Allah bai basu haihuwa ba sai su kasa hakuri suga kamar Allah ya manta dasune. Idan mace ta tsunci kanta cikin irin halin nan zata daga hankalinta har na tare da itama a lokacin kowa yace ya iya zata kai kanta gareshi neman haihuwa don ta samu taga jininta a duniya. Saidai kash irin hakan akwai hatsari a cikinsa indai ba malamaine suka bada wanan sa,an ta wani is,simin sani da baiwan da Allah yai masu daga Al,kur ani mai,girma ba. Mafi yawan mata suna halaka zurian su ta wanan hanyan zuwa wajen malaman tsubbu da yan bori dake aiki da aljannu da sunan samun sa,a su wa yan nan diyan sune yayan roko da nake nufi. Wani irin zufane ya tartsowa habu a gaban goshinsa take kuma mafalkinsa na baya ya fado masa a rai har hankalinsa na neman gushewa a garesa lokaci guda. Muryan hardo ya dawo dashi daidai hardo dake fadin irin hakan uwarku tayi shine kuma a yanzu yake shafan dan uwanka kai habu harkai baka tsira ba saidai saukinka gudane haduwan auren ka da maria shine hasken taurarinta ya hasko naka din. Zama ya gyara yana fadin nasani baba nasan hakan tun ban hadu da maria ba don a ranan da zan taho cameroon wata mace ta fada min kusan hakan a dunkule. Nan ya kwashe komai har da zuwa neman matan da sukayi da mama dubu da kuma mafalkin da yayi daga baya har yazo zancen bada maganin da nayiwa ya jafar din. Sai lokacin Jafar da yayi suman zaune ya iya budan baki yana kallon dan uwan nasa yace yanzu habu kasan da hakan kaki fada min komai na tashi tsaye inata wahala ? Baisan komai ba iya abinda aka sanar mashi ke nan amma shi wanan kawun naku yasani yasan komai a game daku saidai nasa manufan akanku ya hana ya fadawa uwarku gaskiya don amfanin kansa da yakeyi daku yanzu. Sanda dake gefensa ya dako ya aje a gefensa yace kunga haka hakan kuke tsakaninku dashi ba zaku iya komai ba saida izinin wanan mutumin. Saidai ku a wajen ku hakan biyayyane a gareshi wanda ba haka bane tsananin karfa ce dake tsakanin ku dashi yanzu dai idan Allah ya maida ku gida lafiya ku san yadda kukayi da mahaifiyar ku takai wanan sadakan da aka umurce ta dayi shine maslahan ku dasu haka shima abinda yayi a kanku din duk zai karye. Kofa habu ya duba kamar kawu din na tsaye yana sauraronsu yaji Hardo din yace wane shi nan ai tuni na hadashi da abinda zai sakashi kwana ba zai taba jin abinda muke fada ba a yanzu. Ku saki jikinku kuyi maganan da duk kuke son yi a wajen nan kun dai san baku tambayeni ba nice naga dacewan in fada maku gaskiyan abinda ke a duhu gareku. Shiru wajen yayi kafin habu din ya fara kawar dashirun da fadin baba na rasa me yake damuna haka kudi zasu shigo amma ban iya abin kwarai dasu zasu lalace min h,,,,,,,, Wanan sherin wanan kawun nakune da matarsa dake dorasa a hakan aiba halinsa bane sherin matane matarsa ce matsalan taku tana hassadan da za ace uwarku ta fita sa,an haihuwa. Jin zancen hardo sukeyi a wani bakon yanayi da basu taba zato ba a zukatansu wai kawune da wanan halin hardon ne ke magana yake fadin. Aishi baffa tsoron Anini yakeyi shine ya saka ya jata a jiki fiye da yar uwarta don da tana wajen shi har yanzu na tabbatarda sai Anini ta karya duk wani shirinsa akansu. Nan ya kwashe tarihin mu kaf yabasu da irin yadda baffa yaci kurwan dan uwansa mahaifinmu a cewarsu ya gwada na yaran saidai tasu kurwan duk a boye take don duk aka haifesu sai na boye inwarsu. Shiko dan uwansa ya samu nasaran samun damansane a cikin abin sha da magariba sa,an mugun duk wani mugunta da magariba mugu ke aiwatar dashi don a lokacin mumunai suna gagawan saduwa ne da ubangijinsu sun sake komai a lokacin. Taurarin Anini yafi duk taurarinsu karfi shi baffan nasa ya sani yau ko katsa ta diba taba mutum da sunan magani sai karbu ga mutum balle wanan dafa,in mai karfi. Sai daga bayane suka fahinci wace hardo din yake kira da Anini sunana na gado da suke kirana dashi a ruggar tamu ke nan. Zaka samu alheri sosai dan samari zaka ji dadin zabinka sosai koma ince haka dukkan ku auren ku da yaran nan alherine gareku babba. Saidai a hada da hakkuri yana fada ya dauko wani dan kullin magani a cikin jakkarshi ya banye kullin yake fadin habu ya miko mashi hannunsa ya dinga murza mashi abin a tafin hannunsa yana fadin da bafullace kake sai kowa yasan garakanka a nahiyar ku amma yanzu kai bansan abinda ka dosa ba. Hakan yasa Habu sakin murmushi yana ajiyan zuciya hardo na daure maganin Jafar yace nifa hardo saida hardon yayi murmushi yace wai ta Allah ta isheka bari dai kagani kofafinka zasu bude nan ba da jimawa ba da zaran kun hade da matar taka ai. Ai wanan baiwan taka yaja maka haduwa da hadadrun da kake fuskanta saidai Allah na karekane don ibadan da kake dashi hakama mahaifiyar ku. Duk da ana bata karfa kullum amma bata yarda tayi sakaci da ibadanta ba wanan ne ubangiji yake kwato ku har zancen dan kabilan ibon daya jefeshi a kafa ya kumbure saida hardo ya fada masu da zancen kawu dayasa suka kara shiga natsuwansu akanshi. Kusan dai raba dare sukayi a wajen hardo din koda suka koma masauki sun samu kawu yana ta sharan barci ba kwanciya sukayi ba alwala suka dora kowansu ya tayar da nafila. Washegari dasu akai sallah asuba a ruggan an idar jama,a zasu watse hardo ke fadin akwai daurin aure a kofan gidanshi da karfe bakwai na safiya. Gabadaya kowa yayi mamaki dajin sanarwan hardo din inda suka fito da mamakin hakan sam basu kawo cewa sune da auren ba don gidan hardo gidan jama,ane. Hakan yasa suka dakata da tafiyan don kara gasu hardo din sai da akazo daurin aure ne abin ya basu mamaki da hardo ke fadin kawu ya matso ya amsawa dansa auren Anini din. Sukuma sune waliyan amarya su kawo sadaki dubu hamshin daga garesu kowansu yayi mamakin hardo nan danan habu ya kirgo dubu dari ya mika a matsayin sadakin hardo yace baiki ba amma jafar ya bayar da kansa yake so don shine mai aure. Ya saka hannu ga aljihunsa ya ciro dauri biyu na yan dubu guda ya aje a gaban hardo din ka shiga hidimar daurin aure kamar yadda sharia ya gada. Kamar ance habu ya dago kai ya kalli kawu yayi mamakin yanayin daya hango kawu a cikinsa ya dan radawa J din daya dubi yanayin kawu din a lokacin. Anyi lafiya an watse sai lokacin sukaje godiya wajen hardo nan yake fada masu cewa idan sun koma sun saka ranan tarewa sai ummah ta bugo waya mata suje ayi bukin acan wajenta kaduna tunda tana kusa dasu shidai yayi nasa na uba a nan. Haka suka bar rugga cikin jin dadin halarcin hardo garesu suka nufo gida cike da farin cikin sa,ar tafiyan tasu zuwa ruggan mu. Har suka iso gida ba wanda suka fadawa ga abindake faruwa tsaraban da suka dawo dashine irin na wajen mu yasa Yanda tambayan ga kaya kamar na wajen mu dai ? Yana daga kwance yake fadin daga can suke ai har can din muke hardo ya hadomu dasu akawo maku. Yanzu yaya Habu zaku rugga shine baka fada min na bada sako zuwa wajen hardo ba saidai naji kunje kawai kun dawo hannu sake ? Waya fada maki hannu sake mukaje maria kinsan koni bankai abuba J zaikai don bai saba zuwa waje haka hannu sake ba,shi. Tashiga juya abin da mamaki saidai babu daman magana don haka ta kyaleshi ta shiga kawar da kayan zuwa kitchen dinta. A part din iya kuma washegari da aka shigo da tasu tsaraban take fadin kasan fulani kukaje ke nan daga zuwa tafiyan wuni sai kuma kwana haka matar dauda ta ishemu da waya bataga mijinta ba. Kamar wani yaro kuma yaran matanku basu damu kamar yadda ita ta damu ba ni Hansatu na rasa wani irin so takewa dauda haka har tsufa. Jafar ne ya shigo cikin wani dinkin shadda mai maiko ga laushi da santsi kallan ruwan konanen kuka sai kamshi dake tashi a jikinsa ya kafa hular data dace da kayan da bakin takalma half cover ta maza Ikon Allah wanan shigafa haka Jafaru sai kace wani ango dakai can kana zuba kamshi ya washe baki kafin ya kai zaune yana fadin ai ango nake Iya tsohuwa. Kema dai shigar tawa ta burgeki kenan iya ina amaryan tawa zataga shigan nan ta yaba haka kafin ke iya ki gani ki yaba din. Kunji ja,iri ni ba amarya bace ke nan kakarai ka fada wanan matar taka Nusaiba taji tayi muna dariya ko ita dai na rigata ganin wanan shigar tunda ita bata yaba ba. Ba zata jimu ba iya koda taji din ma ba zata samu hakoran dariya gareki ba a yau iya don nata ya sameta tunda kin kirani da ango ya fada don ganin irin kallon da iyar tayi mai. Itama iyan murmushi tayi tana fadin jafaru na dai gane kamar kana son kara aurene a yanzu don abinda yaran nan sukai maka ? Da dai kayi hakkuri dasu hakana don koka kara auren wa yan nan masu ido a tsakan kai ba fasa halinsu zasuyi ba yaran da suka bushe fitilansu suka iya dawowa nan idonawansu a bushe haka ? Kayi hakkuri ka shirya da matanka ku zauna lafiya tunda ita wanan mai idanu kwashi kwashin ido a kafe mata na rashin kunya kowa ka auro a gidan nan ba zata taba barin ku zauna lafiya ba. Iya komai kayi a duniyan nan saika samu wanda ya fika iyasa ai nata kuka gani bata san wace zan auro mata ba a yanzu ki saurara zaki sha kallo ne a gidan nan ai kwanan nan. Allah ya zaba maka mafi alheri a rayuwanka jafaru yace amin iya yama zaba har ya ban ki dai tayani da addua kawai iya shi nafi bukata a wajen ku yanzu. Jafaru uwarku ba zata yarda ka kara aure a yanzu ba yadda naga ta daukaka zancen yarinyar nan tun dawowanta gidan nan ni har tsoro abin yake ban. Wai mama ya tambaya yana mikewa yace mama kan ki tayani bata hakkuri don aikin gama ya gama a yanzu saidai adfu,a a tsakanin mu kuma. Ka daiyi niya baka jin kwabo nake gani Allah ya zaba muna abinda yafi zama alheri a rayuwan mu amma daka shirya da matan naka har dai wanan mai tsohon cikin. Aida cikin ta biyewa sherin yar uwarta a kaina iya ni sam ban ni tausaya mata don itama bata tausaya min ba lokacin da nafi bukatansu a kusa dani ai. Yasa kai ya fita iyan ta bishi da kallo ita kadai a falin take magana tana fadin tsiyan kakai namiji a bango ke nan ai shimai hakkuri bai iya bultsewa ba dama yaron nan yayi hakkuri a rayuwansa kusan dai ace a tauye yake. Salima dake jinsu taki fitowa su gaisa don gudunsa da takeyi kan kada su hadu don zancen saurayinta data turo mashi washegari daya dawo garin . Kuma ya tabbatar mata da cewa yaga J din sunyi magana amma kuma baice mata komai ba har yanzu game da zancen. Au damake idon ki biyu kina jin shigowan yayanki kikaki fitowa take cewa salima din saida ta zauna take fadin ina jin ku iya tsoronsa nake ji kada yayi min fada akan Yusuf. Haukar banza shi zai zauna maki dashi da zai maki fada tunda kin dage saishi shi meye nasa naki kece zaki zauna da abinki ai ba wani ba ? Iya nifa zancen yaya kamar aure yake bida har zance yayi nisa don irin amsan da naji yana baki a yanzu har cewa yayi ai Allah ya zaba mashi ko saidai addua. Yo saidai adduan mana tunda nasan uwarku wanan karon ba zata yarda ba ko wanan sakaran daya aure daga baya ai saida aka inmata. To ita mama meye nata a ciki tunda shi zai zauna da abinsa kya fada kema yar nan nidai banga abin sakawa yaro ido ba yana cikin lokacinshi. Kuma ko banza tara mata ai gada yayi tunda ubanku ras mata hudu ya jera a gidansa ya zauna dasu ashe ko aure gadonsa yayi. Habu ya dauka suka fita don suje wajen mama suna daukan hanya daga gefe inda yake zaune yake fadin muje samaru sai habun ya dan kalloshi. Amma baiyi magana ba ya dauki hanyar Samaru din kamar yadda dan uwan nasa ya fada da kwanta ya kawosu kofan wani gida mai dogon gina horn sukayi aka bude gidan daga ciki habu yasa kai da mota ya shiga. Bin gidan yake da kallo kafin ya dubi dan uwansa yana fadin wanan gidan fa J gidan waye haka baiyiwa habun magana don maigadi daya iso yana gaidasu lokacin. Hakan yasa ya bude motan tare da amsawa maigadin yace baba mun sameku lafiya habu din shima ya fito yana kara bin gidan da kallo . Ya juyo ya kurawa dan uwan nasa ido daga inda yake tsaye saida ya gama maganan da zaiyi da maigadi yace to yaya kaga Surprise din ? Kallon ban gane ba habu yayi masa yace ehh nina gina abina da kaina Habu da gurin in mama ta yarda na baro can na dawo nan. Yau shekara kusan biyar kenan ina wanan ginan ba tare da kowa yasan da hakan ba sai yau nake fada maka don na fahinci mama ba zata bari na baro can ba a yanzu. Wancan dayan ginan kuma na gaban wanan din kai da yazid na dorawa saidai rashin lafiyana yasa komai ya tsaya min a lokacin . A yanzu sam ba zan iya dauko saiba ko Asmau na kawosu gidan nan ba don na fahinci basu taba canza halinsu na kazanta din nan. Sai gashi faduwa yazo daidai da zama yanzu Rahama zan aje a nan ta zauna su kuma su zauna can din har abinda hali zaiyi muje mana ka ga cikin gidan sosai habu. Sai lokacin habu ya nisa yana fadin ninaso na riga wanan Surprise din ashe ka rigani saidai ni tawa gaskiya ko rabin wanan baiyi ba J. Tau ashe kaima kana da wanan dabaran ya ciro dan makuli daga aljihunshi yana bude falon suka shiga ido waje Habu ke bin ko ina da kallon mamaki a gidan. Don bai taba tunanen dan uwan nasa yana da irin arzikin da zai gina wanan mamaken gida haka ba a ransa muryan Jafar din ne ke kara fadin. Idan Allah ya nufa ina kuma rokonsa da yaban rayuwa na kammala gidajen nan Habu don na dankawa kowa dukiyansa a hannunsa in huta. Kaga wanan da kace ka fara ginawa sai na saye shi da sunan mama ta fito wancan gidan ta dawo nan gaba daya ta zauna. Wanan wacan kuma din sai mu barwa Saare da anty baraka da Salima a matsayin nasu rabon da suka samu ka tayani addua habu in sauke wanan nauyin dake kaina ba tare da an samu matsala ba . In sha Allahu habu ya fada a sanyaye kafin shima yakai zaune cikin sanyin jiki yake fadin kayi hikima da dabara sosai J . Could you believe not morethan one year saida kawu yayi min zancen kudin mu dake hanku inda na nuna mashi banda matsala da hakan ai. Yace ni yarone ya kamata yanzu nima na fara tawa plan din don haka zaiyi magana da mama a raba kudin nan abawa kowa nasa ya rike. Kawu kawu na dade a raina ina zargin mutumin nan ba tsakani da Allah yake muna wasu abubuwan ba dama ? Habu yace nina dade da fahintar hakan tun rasuwan baba ai na fahinci waye kawu don ba karamin abu yayi a lokacin ba da sunan karfin mu bai kawo ba. Quet sure yayi wanan maganan iyace nasan ta taushesu da zancen amma ina da tabbacin ya zauna da mama akan hakan lokacin. Ohh my god meyasa mutane suke kasancewa hakane a yanzu habu duk wanda ka yarda dashi sai ya ha,ince ka ni kawu zai zarga akan na taushe kudin magada a karkashina. Bayan yafi kowa sanin cewa ban wasa da wanan abin koshi wani lokaci daya bukaci da in bashi aron wasu abu daga ciki na fada mai cewa koni ban taba taba kwandala da dukiyan nan ba Habu. Nawa business dina na gashin kaina nakeyi habu shine kuma na dora ka kaima akai ka samu rabonka ban amfani da wa yan kudin don in kara kaina Habu a harkan business na shigo da kayan masarufi din dai na barsu a juya . Sun dan jima suna magana kan kawu nasu kafin su bar gidan bayan sun leka ko ina na gidan habu sai yaba kyawon gidan yakeyi yana ajiyan zuciya. Suka dauki hanya zuwa babban gidan nasu a can ma basu samu shiga maza ba don rikicin da suka samu anayi tsakanin dan umma da dan wanjen gwaggo kan gina sock away na masai daya dan shiga gefen umma din. Ita da diyanta suke fadin basu yarda ba tunda gidan dama rababene ai don me zasu shiga wajensu suyi gina. Sun dai tsaya an sulhuta inda shi Jafar ya roka da cewa suyi shawara sai a sayi wajen a gina ma gwaggo din tunda bayi za a yi mata zama ba bayi kuma baiyi a gareta. Daga gefe Habu ke fadin wai tsaya Isah yaushe aka raba gidan nan bamu da labari sai wanda aka kira da isah din yace ba dole sai kayi labari ba ai tunda ita mama dubu tasan kowa akan bangaresa yake ai gidan nan tun baba na da rai kuwa. To ban yarda ba yasa kai ya shiga yabarsu ana wani hayaniyan a wajen kuma iya gaskiyarsa ke nan akan bai yarda ba din a lokacin. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 3️⃣8️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Zaune suka samu mama Dubu da Saare a kasan kafet din falon suna cin shikafa da miya da aka zuba salad a gefe daya sai goran zobo a gefen kowansu da ruwa na leda. Mama ruwan ya kare ke nan ko kun koma shan na gora kuma Habu ya fada yana zama mama dake kokarin kawar da goran gabansa don ya zauna da kyau tace. To Habu a zauna ba abinyi sai shan ruwa a gora wanan ma ai samunsa gatane wasu na can suna neman irinsa basu samu ba ba kuma lafiya muka fisu dashi ba. Sanabene kawai irin na zamani da wani ruwa iyayyen mu samu kanmu muka sha muka rayuwa cikin sallaman ubangiji kuma. To ai yanayi yana saka ayi taka tsantsan mama Jafar ya fada daga gefe daya sun zauna aka gaisa take fadin saiga Rakiya hankali tashe wai kawunku yai tafiya bataji duriyansa ba ? Ai har nan tazo ashe Habu ya tambaya mama take fadin har nan take ai hankali tashe bataga mijinta ba ni abin na Rakiya har yana ban kunya kuma wallahi ?. Koda yake shiya saba mata ai dole ta damu don daya dawo baya numfasawa sai ya zube mata kaf abinda ya nemo ta lissafe itace mai tsara yadda za a kashe a tsakanin su. Ita har yanzu tana wanan halin natane wai Jafar ya tambaya tome zata fasa haline fa kuma ya daukar mata hakan ai kaga bata da laifi ke nan. Wayan mama din dake saman kujera a gefenta yayi kara ta dauka tana fadin kaga yar halak itace ma ke kirana ashe yanzu kuma . Habu ya dubi dan uwansa yana fadin Isah bai san halina amma zamu hadu wanan karon dashi rainin wayyon da sukeyi a gidan nan yayi yawa sai kace su kadaine yaya baba ? No saka masu ido duk abinda zasuyi suyi gida dai a yanzu kafi karfin tsayawa kana fada a kansa Habu suda suka tsaya jiran gado sai suyi ta zaman cinsa mu dai mun gode Allah munfi karfin hakan a yanzu. Lokacin mama ke fadin ai gasu gabana yanzun nan suka shigo amma basu fada min har can suke ba ai sai kuma tayi shiru tana sauraren bayanin da Rakiya keyi kafinta tace wai wani Jafar kike nufi dai ? Jafar yayi aure haka kowa bai sanda zancen ba jin hakan yasa su zubawa mama din ido lokaci guda suna saurarensu . Don Allah Rakiya ki bar zancen nan mana Jafar fa yai aure har yaushe ya taso daga ciwo da za a kakaba mashi aure a yanzu haba dai don Allah nawa Jafar yake da zai zauna da mata ukku biyun nan ma yaushe ya iya dasu balle yaje karo wani auren kuma ? Saare ta kafe mama da ido don bata fahinci takamaiman zancen mama din ba akwai mamaki ace yayanta J yayi aure haka basu da masaniya a kai. Mama wani masaniya zakiyi a zancen banda ki saka masu Albarka tunda Allah ya nufa dai matarsace daga zuwa nema aka sauwaka muna komai don nisa aka daura auren lokaci guda ai kinga anyi muna halarci a nan. Kai dakata min da wanan zancen banza don Allah ban haifi dana don wasu ba don haka babu wata gaiyan tsiya da za,a sake kwaso min kuma wanan aure bai dauru ba a wajena. Haba mama wani irin zance kikeyi hakane aure kan an riga da an daura yarinya na zamasa a yanzu saidai kiyi hakkuri da fatan alheri a garesu kuma. Habu wai meya hau kankane haka ina fada kana fada zan gani idan kaine ka haifa min jafar din waima wayaje har wanan gari ya auro banda labarin komai ? Shiru sukayi gaba dayansu sun kasa bata amsa don yadda ta birkice a lokaci daya a hankali habu dake mikewa yake fadin you have to be strong for dis issue if not ,,,,, Ai da ka zageni da hausa habu abin zaifi maka sauki da wanan yaren nasaran da kakeyi a yanzu ko bamu son jafar zamu so lafiyanshi ba tashin hankali a kansa ba. Tsam ta mike zata shige daki cikin wani tsaya yayi magana yana fadin ke dawo munafuka kawai ina zaki ana magana zaki daukan rahoto ki samu na yadawa ko ? Ai ka barta ta yada din duk uban da zata kira ta fadawa taje ta kira idan wani ya aura min matar mama ba kowa na aura ba sai Rahama dai da kika sani kanwar marian habu itace na aura zargi ya kare. Anty Nafisa dake shigowa don ta gaidasu taja ta tsaya a cikin mamaki tana bin yan uwan nata da kallo tace yaya J ka auri Rahama ? Tabbas Rahama ce na aura don wanke zargin da aka soma min iya matakin da zan dauka ke nan tunda ance dama farkatace ita dole in mata gatan hakan a idon kowa. Yanzu na gaskanta zancen da ake fadin fillo kakan sheri yau sherin nasu a kaina kuma ya dawo ke nan an fada masu ni na haifa masu diyana donsu ne ? Haba mama bai kamata aji hakan daga bakinki ba ai na dauka wanan abin da nayi albarka zaki saka min kan yadda nayi din ba irin maganganun nan ba ? Rahama dai kowa yasanta yasan halinta balle ta zama bakuwa a cikin mu ni kuma na ganta nace ina so ba wanda ya tilasta min yin hakan. Ni dai naga dacewan hakan da nayi duk da yarinyar bata sona ga hakan asalima daga ita har maria har kawo yanzu basu sanda zancen auren ba. Don bata ban hadin kai yadda naso ba hakama wa yanda take wajensu can basu bani goyon baya akan nufina ba yasa na dauki kawu da Habu da Nasir muka tafi tare dasu aka kumayi mai gaba daya. Kiran wayansa da akayi ya katse masu zancen ya mike yana fadin yana zuwa ya barsu a zaune zugun zugun kafin yasawa Habu kira ya mike shima ya fito daga dakin. Fada mama dubu ta soma tana fadin yau za ayita ta kare ba sai gobe ba wanan ai tada zaune tsayene yaushe aka taba yin hakan kagani. Kanin ka yana auren ya kai kuma kaje ka daura aure da kanwa don shashanci kana babba a garesa ka koma ka auri kanwa kuma ? wanan wani irin komawa bayane wai ? Ba kowa bane maria ce keda kisisinan nan mama tunda tana ganin ta samu waje bari ta cusa yar uwarta itama da hadin bakinta hakan ya faru . A,a Saratu ki kama bakinki wanan zancen manyace bata yara bace kin dai san halin yaya habu yanzune yaji abinda kike fada akan matarshi zai latsa ki wajen nan. Ai sai yazo gata tunda hauka yayi ya kara dukan mi ya kan matarshi wanan karon ba zan raga mashi ba . Mama ta daiyi shiru shine alheri ta kama bakinta tunda ba zancen ta bane gashi kuma sun fada daga maria har Rahaman basu sanda zancen ba ? Dazun nan muka gama waya da Rahama da safe a dakin nan mamakinji metace ai danace hutunsu ya kare tace saita kara lokaci zata dawo . Nafisa rabu da yaudara inda kika gansu sunsan komai maganan saratuce da gamin bakin maria akai hakan don haka ko ita ba zan kyaleta ba gidan nan yanzu. Ya jima a unguwar saidai bai yadda ya kara shiga cikin gidan nasu ba don habu ya fita tun bayan fitowansu ya nufi kaduna. A lokacin ya kira anty Salma yayi mata bayanin komai tare da rokonta zai turo mata kudi ta hado mashi laife. Hakan akayi ina daki kwance duk da ba barci nakeyi balokacin don haka kawai nake jin raina ba dadi aranan. Kafana taja tana fadin lazy tashi ki rakani outing wani ya ban aiki daga maiduguri haka na tashi na shiri muka fito ganin harda Samuel driver da yunusa zamu fita yasa nasan babban abu zamu fitayi kfaruwa lokacin. Bayanin da takewa yunusa yasa na fahinci meke faruwa a takaice dai wani ya sakata hada lefe na gagawa wanan sana,an mamace mahaifiyarsu anty salma. Donshi banyi mamaki ko kawo wani abu kasan zuciyata ba nakance alfahari da neman suna yake sa wasu fita waje don banjinta da daukakansuna. Amma komai da zaka sayo waje akwaishi a nan gida Nageria dan bambanci kudi kuma kadanne a tsakani don muda kan mu muke raina arzikin kasan mu da kan mu amma gaskiya matasan masu kudin Nageria suna iya kokarinsu wajen cigaban kasan nan saidai mu yan kasan ne bamu bada goyon bayan cigabansu. Don munfi ganewa alfahari da bajinta a koda yaushe wanan na kara durkusar damu a cigaban kasa da zamu samu. Tayani zaba Ramaah kada ki damu da kudin kayan ki duba qualities dinsu kawai ki dauka duk abinda yai maki kyau a zuciya. Nasan wanan akidar tasu tun muna kananuwa mama kanzo damu mu tayata zaben kayan da take hadawa din da gyaran wajen event dinsu da suke bada haya. Jin hakan yasa na zage na tayata zaben abinda nake ganin na fita kunya saboda furcinta sosai muka hada kusan akwati ukku da kaya na gani na fada a ko ina a fadin kasan nan a wanan shagon na el,samad kafin mu fito zuwa Sahad. Bamu shigo gida ba sai bayan ish,i akan washe gari za a koma a karasa sayan kayan tunda na shige nayiwa wanka da alwala nayi sallah na kwanta. Bandamu da neman abinci ba a ranan saboda gajiya dana debo har nake dariyan kaina ashe ko wani jiki yana son hutu a duniya ? Dan kwana biyun da nayi ina samun hutu a yanzu dan abu kadan yake wahal dani da gajiya kamar bani bace nake yawan aiyuka a yan watanin baya ba. Zaune suke dukansu a falin iya din da mama ta daga masu hankali saidai shi Jafar bai wajen don ya wuce a ranan ya bar gari zuwa kano zaibi jirgi da zai kaishi lagos . Sai habu da ya tsaya shima yace da safe zaibar gari zai tafi maiduguri mama ta nisa tana fadin na dai gane kuna son mayar dani mutumiyar banza habu ? Na fada maku hakan ba zai yuyu ba dole Jafaru yasan yadda ya walwale auren nan dayaje aka daura masa da yarinyar nan. Ko kuma har naka auren shima ya samu matsala akan wanan zancen da kukeson jawo min a yanzu ? Saida ya dan gyara zama ya shafo kansa ya sauke wani shu,umin murmushi a fuskanshi kafin habun ya kallo iya yana fadin a dai tsaya gana J shida yasawa kansa son yarinyar nan da karfi da yaji. Don dai Rahama Allah ya gani bata bada son ranta ko ra,ayin yar uwarta aka daura auren nan da Jafar ba tunda baiyi soyayya da ita ko ya nemeta wajen wani ba. Allah ne kadai ya nufa akwai hakan a tsakaninsu shawaran na zuwa mashi muka yanke shawaran daukan kawu muje wajen yan uwansu ko hakan yana yuyuwa sai gashi munyi sa,a muna zuwa har auren aka dauro lokaci guda saboda nisan waje. Asalin zancema wallahi duk kansu har yanzu basu sanda zancen auren nan ba don banji ita maria tayi min magana a kan zance ba kunga ke nan bata sanda labadin auren ba itama ? Ikon Allah abin farin ciki ashe yana zama na tsiya Dubu ? Na dauka wanan zance ke zakifi kowa farin ciki da alfaharin faruwan hakan a cikin mu ai don kece kika san halinda danki yake ciki na bukatan abokiyar zama tagari da zata bashi kulawa da kwanciyar hankali? Amma kaiyya dai abin takaici sai gashi kece tafarko da kike nuna halin uwayen zamani akan danki don kawai ya zabawa kansa farin cikin rayuwansa . Iya ba wai naki zancen nan bane sai duban irin yadda za a fassara wanan zancen a waje yar uwarta fa tana gidan nan tana aure iya yanzu kuma ace shi jafar ya auri kanwarta ? Zargin matansa saiya tabbata tunda dama sunce yana kula yarinyar har a gabansu bai son ranta kona yar uwata ya baci inaga yanzu ace ya aurota ? Dubu ban soki da wanan rayuwan ba a cikin yayanki kada ki manta ke dai ba ayi maki irin haka ba dagani har mahaifinku bamu takurawa rayuwan ku ba a baya. Yanzu ki duba bayanin yaron nan Habu yaran nan basu san da zancen nan ba daga tambaya akai masu halarci aka dauro auren nan ko wanan abin bai isa ki gane Allah dayane ba dubu ? Iya ina son ki tuna Jafaru hakkin yan uwansane a hannunshi yake juyawa suma yaran nan suna da bukata akan dukiyan su . Nina tauyesu na bashi dukiyan nan ya juya yau iya yana ta faman aure aure yaran nan bai aurar da kowa a cikinsu ba banda shi habu su sauran basu bukatan dukiyansune iya ? Kina kallo ko abu zaiyiwa yaran nan daidai dana matansa zai basu hakan fa ina kyaleshine kawai iya amma a gaskiya raina yana sosuwa da hakan wani lokaci. Au tanan kuma zaki fitowa dan naki kice min tun farko bakin ciki dashi kikeyi ko kuma yar kice ta zugaki akan hakan yanzu ? Wanan ma mai saukine ai mama in dai dukiyansu suke so nasan ko yau din nan aka bukata Jafar zaiba kowa kasonshi in sha Allahu iya ta amsawa habu da kwarai kuwa dan nan. Iya rabu da wanan tunda an kashe masa baki a yanzu komai zai fadi game da dan uwan nasa don bakinsu daya akan zancen. Amma gaskiya mama duk wanda ya canza maki ra,ayi akan yaya jafar zai iya cutan mu da dukiyan mu yayi maki mumunan hudu ba arayuwa. Ni sam ban taba wanan zargin akanshi ba mutumin da yake tsaye a kan mu da komai namu gidan nan shine za ace yana facaka da dukiya yanzu ? Rufe min baki salima tun ranki bai baciba wajen nan idan an tashi zance ki hana mutum yai magana don wani ra,ayi naki na daban. Gaskiya take fada maki mama don kuskuren da kike nema ki tabka a yanzu babbane da nan gaba zai dame mu bake bama don duk ranan da Jafar yaji zancen nan ba za asha da dadi ba. Kai dukiyan nan dai ina nina danka masa da hannuna ko nayi shawara dakai da zan bashi don haka ka kyaleni ba zan yarda Allah ya tambayeni kan hakan ba. To shike nan mama a samu lokaci a zauna dashi kan hakan amma ina bukatan ku cireni cikin zancen nan don Allah . Daga hakan ya mike ya fita daga dakin cike da bacin rai part dinsa ya koma cike da tunanen yadda zai tafi yabar yanda a cikin wanan cakwakiyar hakan yasa ya daga tafiyansa a ranan. Zama yayi da matanshi ya fara fada mata abinda ke faruwa tiryan tiryan inda ta kasa fahintar abin don a zatonta yana nufin yaya J yana son ya nemi Rahama da aure yake nufi. Inda ta fara fadin haba dai yaya habu ina hakan zai yuyu don Allah kabar zancen nan kafin ya kai ga zancen har an daura aure don haka Rahama a yanzu tana matsayin zaman matar J ce a gidan nan. Cikin tashin hankali ta fashe da wani irin kuka tana fadin amma bakuyi muna adalci ba yaya habu haba dai Rahama fa ? Rahama za,ace ta auri yaya Jafar don Allah ku daina wanan zancen saboda Allah don ba abu bane da zai yuyu garesu shima ya sani. Duk yadda yaso ta fahinci zancen ta kasa sai kukan tashin hankali da takeyi tana neman layin Rahaman data kasa samun layin. A lokacin wayan na wajen anty na barshi don haka bansan duk wainar da ake toyawa ba a kaina lokacin. Bai san ya akayi ba ya daifi zargin Saarece ta fada har matan J sukaji sai ashar yaji yana tashi muryan Saiba na zunduma zagi daga wajen part din tana kiran su da munafukai. Abinda yake gudu ke nan har ya hanashi tafiya a ranan dama yasan sai hakan ya faru a gidan idan labari yaje garesu duk da mama ta bar gidan a ranan da yarta saare . Sai iyace tayi karfin halin fitowa tana tambayan meke faruwane haka suke daga murya ? Kaji tsohuwar nan zakice baki san makircin da aka kulla bane gidan nan don kawai aga an tozarta mu ? To ai gamu gani idan gidan nan na shiguwa ga Rahama tazo gamu wanan kuma yanzu meye idan ance zarginsu mukeyi a baya ?. Jin yadda take fadawa Iya magana yasa ya bude kofa ya fito ya tsaya yana fadin iya ki koma daga ciki ki zauna. Suje suyi abinda zasu iya anyi aure da Rahama in ma baki sani bane ki sani an daura aure a shekaran jiyan nan kuma aure ya tabbata mai zama ta zauna . Wallahi baka isa ba idan ma nufinka kenan dama ka aurawa kanwar matarkashi kayi kuskure yin hakan habu gara tun wuri ku rufawa kanku asiri kawai zaifi sauki. Koki rufawa kanki asiriba a yanzu mijin dake da cuta kike gudun ya kamaki Nusaiba don yanzu ya samu wace bata gudunsa kome ke gareshi har zaki tsaya kina kumfar baki akansa yanzu. Sai hakkuri don aikin gama ya gama faruwa saidai ina son ki sani duk kika sake kika zageni ko matata a cikin zancen nan sai kin kwana a gadon asibiti ranan . Idan kuma kin dauka karyane ko wasa ki gwada ko a yanzu kigani abinda zai faru dake a wajen nan . Yaja wani guntun tsaki tare da jefa mata wani kallo ya juya zuwa ciki baiko tsaya ya fahinci tashin hankalin data shiga ba a lokacin. Don da farko ba aure suke zargi ba kamar nemanta sukaji ance yanayi shine ta kasa hakkura don ranta daya gama baci a lokacin. Sai gashi zance ya banbanta Habu ya fito yana fadin wani magana na daban da bata taba tunanen faruwan hakan ba wai jafar ne yayi aure ? Auren ma auren yarinyar data gama sanin sirinsu gaba da bayansu waiko da gaske habu ke wanan zance ko kunuwantane basuji meyace kan zancen ba ? Ta juya a fusace zuwa cikin part dinsu hankali tashe Asmau dake tsaye tana mata magana akan su tsaya su bincika gyale ta dauko da waya ta nufi hanyar fita daga part din. Wai ina zaki don Allah nusaiba ki natsu mana abi komai a sannu habu yana iya fada maki hakan don ranki ya baci kawai tunda ba shiri tsakanin mu dashi. Ko juyowa ta kalli Asmaun dake magana batayi ba ta fice gidan kai tsaye ta hau abin hawa sai tudun wanda family house ta samu mama da abin duniya ya isa lokacin. Da kyat ta daure suka gaisa da wasu daga gidan ta fada dakin mama Saare ce a waje tana wanke kwanaku tana ganinta ta mike tana fadin daga ina haka saiba ? Mama na ciki ta iya fada tana nan Saare din ta fada ta fada dakin ba gaisuwa sai kukan data fashewa mama dashi wanda ya jawo hankalin mutanen gidan. Suka nufo part din mama din mama dai tana zaune ta zuba mata ido gashi sai tambaya meya faru akeyi duk sunyi shiru sai Saarece ta iya fadin. Yaya jafar ne yayi aure ya auri Rahama kanwar matar yaya habu lokaci guda suke fadin Rahama dai Rahama aure yaushe hakan ya faru ? Haba yar nan akan wanan kika shigo da kuka haka me yaya zata iya yi akan hakan tunda anriga da an daura aure yanzu meya rage kuma bayan hakkuri inna ke fadin hakan. To ba a aure ita tayi ina mijin kawarta ta aura amma ai ita wacan batayi tashin hankalin nan ba da tayi hakkuri gashi an zauna lafiya . Duk wanda zaizo sai yayi kwatance a kanta da cewa hakkuri akeyi ai itama ai wata ta sama kuma tayi hakkuri haka ta mike bata iya fadan komai ba ta fice kuma direct ta nufi wajen shiga motan zuwa kaduna. Baifi yan mintuna da hakan ba yaya Habu ya dora yadda akai daurin auren a rugga ya rubuta Jafar and Rahama Allah ya bada zaman lafiya abin median nan danan aka san da zancen auren aka fara yadawa masu dorawa suna dorawa a saman wayansu. Ganin hakan Jafar ya kira habu yake tambaya yake cewa dashi yanzu kan ai kowa ya gama sanin abinda ke nan ya kwashe komai ya fada mai saidai ya boye mashi zancen da mama tayi game dashi don gudun bacin ransa. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 3️⃣9️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Kwance nake har lokacin cikin gajiyan da ba zance ga dalilinsa ba ina dai dangata hakan da fitan da mukayi da anty salma yasa jikina weak a lokacin. Nayi mamaki yadda wanan ya narka kudi aka hada mashi wanan lefen a cikin kwana biyu rak kayane dai aka zuba wanda zaki dauka cewa macen ba zata taba neman wani abu mai suna sutura ba ko kayan kwaliya. Gaskiya maishi ba karamin kokari yayi ba hakan ko banjitane ko kuma so an dai narka nairori a wajen nan gaskiya irin tunanen da nakeyi ke nan a zuciyana naji an turo kofan dakina. Muryan anty salma danafi zaton itace don ba kasafai yan aikinta ke shiga dakunan kwanan mu ba saida wani dalili mai karfi. Wai kwance kike har yanzu na yunkura ina mika nake fadin haka kawai naji duk jikina ya mutu nasan gajiyace na mike ina gaida ita. Mama ta bugo waya muje yanzun nan tana neman mu dani dake jin abinda ta fada yasa na kallota da sauri ina fasin mama kuma ? Lafiya dai ko anty Salma tace ai kinsan halin mama kilama ba wani zance bane tana dai son ta gamune kawai tace mu taso. Murmushi nayi don ko yana yuyuwa haka din ne sai muje tace ayya yaran nan ban ganku ba kwana biyu kuna cikin gaein nan kun shareni ko ku nemeni ? Hakan yasa na tashi na shirya da sauri don na fahinci a shirye anty Salman ita take a lokacin ba wani dogon shiri nayi ba wasu dogon riga da ya tsaya iya gwiwa tare da wandonshi sai gyalen dana rufa iya wuyana tunda daga mota sai mu shige cikin gidan mama din don haka ba saina tsaya wani bata lokaci ba. Karshema zata iya sakani wani aiki a hakan yasa ban tsaya wani dogon gyara ba kodana fito anty na zaune tana waya tana ganina ta mike tana fadin muje ko tana mike yaranta. Na dan marairai ina fafin kin rufo dakinkine anty wayata naso dauka a nan na barta tun jiya sai naji tace gashi na saka maki a jakata muje saina baki a can din. Ba wani dogon tafiya bane don basu da nisa sosai da juna sai gamu gidan daddy din tun a waje na fahinci daddy yana gidan a lokacin. Yan aiki keta kara kaina a tsakar gudan duk da yanzu gidan ba yawa sosai ko masu aikin su ukune yanzu ba kamar lokacin da mukai tamu rayuwan dasu ba da muka cika masu gida. Mama fa ta tambaya tsohuwar tace tana gun Alh suna nan falonsa zaune hakan yasa muka nufi can naso togewa iya ita ta shiga sai ta juyo tana fadin muje mana kin tsaya kuma kai wanan bakar bafulatanan dai ? Murmushi nayi don sanin sun rike wanan wasan ta fulani da barebari a tsakanin mu ko yaushe kuma har daddy suna tsokalan mu dashi. Daga mama har daddy din suna waya a lokacin muka shigo abinda kunnena yaji mama na fadi shine ai gasu mun kirasu daddy zaiyi magana dasu daga baya sai inkirani kiji meke nan. Ta kashe wayan ta dago kai muka fara gaisawa ranan fuskansu ba wasa a cikinsa don ko dan zolayan nan babu sai daddy daya mikawa dan salma hannu da yazo yaron ya leke a jikina. Mama ke fadin karka kama gaye ka sake reshe kwana biyu ba zaka ganta gidan kuba dan nema kawai salma ta shafo kan yaron tana fadin ai tare zasu tafi zaria da anty salma ko ? Akayi dariya muka zauna dai a cikin harshensu suke magana wanda duk zaman mu banda gaisuwa da dan wasu abu da muka rike har yanzu bamu jin yaren nasu sosai amma muna fahintar me suke fada da kanuri din. Don naji mama na fadin ban sani ba tace a,a har yanzu dai bansan komai ba amma sai ban kawo a kaina suke magana ba. Daddy ne ya ambaci sunana da Rahama hutu ya kare ko sai shirin komawa makaranta na dan dukar da kai ina murmushi yace to Allah ya taimaka na amsa da amin kawai . To Rahama nace yar uwarki tazo dakene nan don muyi maki magana irin ta iyayye yau a duniya dai kin sani ko Abdullahi mahaifinku yana raye ni Adamu ina iya yanke hukunci a kan ku ? Zama na gyara don nasan maganar kila a kainane zancen komawata gidan su Yanda da anty salma tace ba zan koma ba ke nan ta kawo gaban daddu din hakan yasa na amsa da baki da kai da alaman hakane. Yace madallah ina son kiyi amfani da tarbiyanki da natsuwanki da iliminki haka kuma ki zamo musulma mai ruguman kaddaran da duk ta samu bawa ta rayuwa walau mai kyau ko akasin hakan ? Na sake jin kaina ya kulle min lokaci guda har na fara tunanen ko nayi rashin wanine a lokacin falon yai shiru babu mai magana na dan lokaci. Mama ta zuba min idanu daga inda take zaune hakama anty salma ke kallona cikin wani yanayi na tausayi sai duk na kara tsunkewa lokaci guda. Yayin da suka fahinci tun bansan meke faruwa ba yanayina ya sauya tun soma maganan daddy a kaina. Yadda duk na fara fita hayyacina tunma basu fada min kome yake faruwa ba kaina dago cikin yanayi na damuwa da alaman tambayan ku fada min kome yake faruwa mana. Sai naji daddy yace kiyi hakkuri Rahama a matsayinki na musulma ya kamata ace kin yarda da kaddara mai kyau ko akasinta. Don haka ki kaddara hakan da zan fada maki kaddaran kine haka muma iyayyenki bamu isa mu sauya maki kaddaran kiba Rahama ? Kai na gyada a hankali haka kuma indai har kin yarda da mu iyayyenkine kinsan ba zamu cuta maki ba to ina son ki kara daukan hakan da gatan iyayye akai maki aka daura maki aure ba tare da sanin ki ba. Zubur nayi na mike dakyau zaune ina binsu da kallo ga anty salma kallona ya tsaya sai naga tana min murmushi da a lokacin na fassarashi dana kiyayya a gareni. Mama ta karba da fadin kakanku hardo ya daura maki aure kwana ukku da suka wuce da dan uwan mijin Maria yar uwarki. Ina fatan zaki dauki hakan a kaddaranki kin dai san ba za a hada kai damu a cuta maki ba Rahama ? Don haka kamar yadda daddynku ya bukata ki zamo mai biyaya ga mijinki haka kawai da zakiyi shine zaki nuna matsayin mu na iyayye a wajen ki yanzu. Haka muma zamu san Abdullahi ya bar muna marayun Allah mun kuma runguma a bayansa . A iya binken daddynku wanan yaron baida matsala asalima taimaka muna yayi a namu ganin da wani yazo wanda ba a sanshi ba ba asan halinsa ba ya aureki daga baya azo ana samun matsala kuma? Hakan yafi muna kwanciyar hankali dake har mu don ansanshi ansan koshi waye haka kuma ki zauna gashin kanki yafi zamanki a haka hankalin mu kullum a tashe kanki. Shi aure rahamane ga bawa alherisa yawa garesa don ba akanka kadai kaida kayi auren abin ke tsayawa ba yakan shafi har wanda baka taba sani ba. Allah ya taimaka hawaye sun zubo min don sune saukina a lokacin da ace ban samu sunzo min ba a lokacin komai yana iya faruwa dani wajen. Kinsan mu fulani da busashen zuciya toni a wajena wanan hawayen da suka zubo min sune saukina a lokacin saidai duk da hakan saida faduwan gabana yakaini ga sulalewa kasa cikin kaduwa. Salma da mama sukayo kaina da sauri suna kiran sunana da Rahama Rahama haba dai wanan abin ai bakai har na daga hankali haka ba ke nan baki yarda da hukuncin mu da kakanki hardo akanki ba ke nan Rahama ? Mamace ke fadin hakan cikin kaduwa da halin data gani a ciki shiko daddy namijine yana zaune ya harde kafa yana zuba murmushi kawai daga inda yake zaune yana magana a cikin yaren kanuri yake fadin. Su kamani zuwa daki ba komai bane kaduwane zan sake idan zuciyana ya samu nasuwa amma a kira doctor zainab ta dubata. Haka suka kamani zuwa dakin mama saman katafaren gadon mama din suka kwantar dani tare da kunna min AC dakin daya kara sakarwa jikina yanayin zazzabi sai gashi na fara rawan dari a hakan doctor din tashigo ta sameni kwance. Allurai tayi min dama shine nasu tare da maganin da zansha indan watsake tace a barni in samu barci idan na tashi komai zai tafi in sha Allahu. ZARIA Suna zaune gaba dayansu falon iya ga abin karyawa a aje amma sun kasa karyawa sai Salimace data fito ta zauna ta dauki kofi tana tsiyaya ruwan zafi a ciki. Iya ta nisa tana fadin tsiyaya min ruwan zafin nan yar nan kada hanjina ya nade ga banza banga abin tsayawa tashin hankali wajen nan ba. Don yarinyar na tafi gidansu kan mijinta ya kara aure za a zauna a daga hankali haka ? Ita da aka aurota ba hakkuri taga yar uwarta tayi ba wani irin iya shegene basuyi ba a gidan nan da aka kawota saida aka koma ba yan uwan uwargida hakkuri. Ke dubu lamarinki yana daure min kai wallahi ni banga abin daga hankali ba wajen nan Yaron nan aure ya kara ba wani mugun abu ya aikata a rayuwansa ba amma kin daga hankalinki haka ba tunane ? Iya ba haka bane ban damu da aurensa ba don shi yaga yana iyawa ni damuwata shine ya bada dukiyan yan uwasa dake hannusa . Ba zan zuba ido ina kallo yana facaka da dukiyan yan uwasa a saka mai ido Iya yaran nan sun san da dukiyan su yana hannun Jafar yau ace kuma Jafar baida aiki sai aure aure yana facali da dukiyan yan uwansa na kallo ? Haba mama haba yaya jafar ba zaiyi hakan da kike tunane ba wallahi in ma wani ya zugaki wallahi ya dauki alhakin shi don,,,, Ke kinci gidan ku zan saba maki rai yanzun nan kul kika kara tareni idan ina maganan nan me kika sani ke da shirmen banza ? Salima ta hada shayinta ta fita daga falon zuwa waje bayan ta mikawa iya nata part din ya Habu ta nufa ta samu ya fita tunda safe sai Maria data samu zaune ga Abba yana wasa a gefe ita kuma tayi tagumi idonta yayi ja jajir alaman taci kuka har ya isheta a lokacin. Haba dai Madam ba dai kuka kikayi haka akan wanan zance ba kada ki zama wata mara godiyan Allah mana naga hakan farin cikinkine gaki ga yar uwarki a gida daya. Yau dai kinsan ko waye yaya Jafar kinsan kuma tunda ya zabi hakan ya shiryawa duk wani barazanan da za a tunkareshi dashi gidan nan. Takai zaune da kofin shayinta a hannu tana fadin ni ina mamaki da kuka kasa gane waye yaya J ? Ai ki zuba ido kawai kiyi kallo ina fada maki duk abinda sukayi a baya suna ganin sun gama dashi a yanzu zasu girbi abinsu bawan Allah nan ya dade da bakin cikin wa,yan nan matan nashi a zuciyar shi amma an kasa gane hakan. Mezaisa kike fahintar yau da sune ya habu yaga yan uwansu yace yana so da gudu zasu bashi ya aura don kiyayyan da suke maki suna bakin cikin kasan ,cewarki matar yaya Habu. Nasani amma nidai a wajena hakan ba daidai bane Salima don ko rantsuwa nayi ban kaffara nice za ace na hada wanan abin. Ai ashe kinsan da hakan to me zaisa ki damu da abinda zasu fada a kanki damuwa ba naki bane don inkin nuna hakan za a samu sa,an gaya maki maganan banza. Amma idan anga kin dake ko za a fada ba yadda za a sake a fada maki cikin takaici ba don haka gara tun wuri ki marawa yar uwarki baya Maria. Sun dauki lokaci suna magana a tsakaninsu kafin ta mike zuwa part dinsu ta samu kawu ya shigo yana fadin abinda yafi dai yanzu ya fito da dukiyan a kasa abawa kowa nasa kaso ai yanzu kowa acikinsu yanaa iya rike nasa. Kaiyya yaya nifa ban tunanen akwai wanan dukiyan a yanzu illa kawai ya kawo abinda ya saura a hannusa a kiyasta a bawa kowa hakama wanan gidan. Kaga idan anyi haka zanga inda zai saka yarinyar nan in tunanesa wanan part na yazid to tun yanzu ya canza dabara nayi waya da Baraka ta taso tazo asan abinda za ayi dama mijinta ya matsa ta karbo dansu ya fara juyawa tunda ya gama karatu ba aikin yi. Hakan yana da kyau kwarai saidai nasan koshi nasa tunanen ke nan a yanzu wanan wajen na dan uwansa zai saka yarinyar tunda ba wani ginan yayi da zai sakata ba can na daban. Allah sarki idan kin hanashi saka mata a wajen dan uwansa haya kikeso ya fita ya kamawa matan nasa Dubu ? Duk yadda zaiyi shiya sani mama ai yasan baida matsuguni ya daukowa kanshi zancen aure kina gani iya ko wanan filin daya kara yayi ginan wanan daya dauko kaduna ai cikin filin gidan ya diba ya kara yayi. Iya sai a kyashi ya mamaye duk kason yan uwansa shi daya nan gaba su koma suna zargina nice na mara masa baya da yayi masu hakan ? Yanzu dai maganan gaskiya ke iya a bari ya kawo dukiyan a raba abawa kowa nasa idan yaso in zai dauki hanyan wajen shi yazid kafin ya dawo sai ya dauka a dinga ba uwarsa kudin ina ganin haka zaifi sauki tunda abin magadane . Anya Dauda kuyi tunane kafin ku yanke wanan shawaran yaron nan shine tsaye da gidan nan da yan uwansa yau don abin duniya zaku rufe ido kuyi mashi hakan ? Iya ai ba tozarci bane nauyine za a sauke mashi kada daga baya abin yazo yafi haka rayuka su baci tsakanin gara tun wuri ayi maganin abin zaifi. Kit Salima da tayi recording din muryoyinsu ta mike zuwa daki bayan ta kashe wayan bata jira komai ba ta bude ta turawa yayanta komai. Sun kai wani lokaci a falon suna tatauna zancen kafin suyi sallama da juna ranan mama bata nemi yar uwata ba saboda har ita wanan lamarin ya shafa. Sai take ganin laifin duk natane da badon ita ba babu inda Jafar zai ganni ai zancen kawune da yace da ita mudin fulani abin tsorone. Zamu mallake mata yaya ta koma bata gane komai ba har gara wa yan nan matan na J ai damu bata ganin habu komai da yake ciki ba a taba sani saboda boyon kurwa da yakewa mutune. Wanan zance mama ta haushi ta zauna sosai donshi ta kara hawa zancen cewa a raba gado a warewa kowa nasa kaso a yanzu don ta kula Jafar ya salwantar da dukiyan nasu. Bai tashi ganin sakon salima ba sai da dare bayan ya gama abinda yakeyi ya bude data yaga sakon mutane lokacin ya kula da sakon kanwar tashi. Ya bude yaga sakon muryane kusan guda hudu daya bayan daya yake bin sakon yana saurare a ranan kasa barci yayi don zullumi da tunane. Habu ya fara nema akan zancen ya nuna mashi yasan da zancen shima an fara a gabanshi amma ya nuna rashin dacewan hakan sai aka baryi dashi. Haba dai Habu shine ka kasa fada min komai a cikin lokaci tun tuni idan nasani da ban fitar da kudin nan an raba a bawa kowa nasa ba ? Yake tambayansa waya turo mashi wanan murmushi yayi shi habun yace salimace don ra,ayin mu daya da ita tun a waje ta fada masu gaskiya abar nata a wajeka kome zakayi dasu kayi. Sun dan jima suna zancen tun bayan kashe wayansa ya kira nura da yunusa abokansa da suke kasuwance a asirce ya bukaci da su hada mashi kan kudin a waje daya. Ya kuma kara umartan Nura da ya mayar da hankali wajen ginan daya saka suna gama waya ya kira wani ya bashi cigiyan gida. Allah sarki da ace mama tasan abinda ta haifa da bata yarda har kawu yayi amfani da damanta ya bata wanan shawaran ba duk da bai kyautata zaton shawaran kawune shi kadai dole akwai wasu yan uwa dake kwadayin dukiyansu a hannunsu. A lokacin kuma ya kara yarda da maganan hardo kalai kawu ya dade yana bin duduniyarsu ba tare da sanin hakan garesu ba duk da alama Habu yasan wani abu shikan dip yake banda kasuwanci baisa komai a gabanshi ba. Bayan kwana biyu ya bar kasan zuwa South Africa da niyar sati daya amma saida ya share sati ukku a can wanan yasa mama dake ta neman layinsa dare da rana ta kasa samun shi . Ta kira Habu shike fada masu baya kasan nan Saaratu ke fadin kin gani ko mama da kudin yake ta facaka ya dauki yarinyar nan sun fita ke nan yawon amarci ya barmu nan ko Lagos bamu taba zuwa ba. Shi kuma kawu cewa yayi dubu na fada maki yaron nan yana dawowa a kwace komai na hannusa a rabawa yan uwa ko gida in bai tsira da komai ba dole ya sayarwa yan uwa da part dinshi a basu hakkin su. Mama da bata data cewa sai kara hasala da zancen ke sakata a kan danta takeyi haka yasa ido rufe ranan data zo gidan ta shiga part din habu . Yanda na kwance sai ganinta tayi ta mike tana gaida ita cikin rashin walwala take fadin yar uwarki tana inane Maria ? Ta dan sasauta murya tana fadin tana Abuja mama tace kira min ita yanzun nan a waya hakan yasa yanda daga wayan takira layina na dauka na fara mata yarenmu na fullanci tace bani ita nan ta mika mata wayan. Naji muryanta a lokacin yasa tana karban wayan tace hello Rahama ina jafar yake ne ? Na maimaita sunan a cikin mamaki ina fadin mama bansan inda yake ba don rabona dashi tun dana barshi gida nazo abuja ban kara ganinsa ba sai naji ta kashe wayan. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 4️⃣0️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Kwana biyu a cikin zazzabi na samu sauki har lokacin ina gidan mama saidai anty salma takan zo ta dubani lokaci lokaci amma ba wanda ya kara min zancen auren Jafar dake kaina yanzu. Saina dauki hakan da kila gwadani sukayi ko zan yarda da zancen amma ganin ban yarda ba yasa aka fita zancen nasa. Hakan ya bani karfin gwiwan sakin jiki da har na fara fitowa falo muna dan hira da mama satina daya cur a gidan anty salma tazo a wani yammaci zata tafi na mike nima nace tare zamu tafi ai. Ta juya ta dubi mama mama din tace kuje mana duk da daddy bayanan idan ya dawo zan fada mashi ta koma gidan ki hakan yasa muka tattaro muka dawo gidan anty salma din. Sai a ranan kuma ta ban wayana dake hannunta duk da ina son wayan a tare dani ganin bata ban ba nima ban tambayeta ba saina share zancen wayar tawa din. Sai gashi ta mika min abina ba tare da kona tambayeta din ba wayan da cajin shi full haka yasa na kunna don a kashe take nayi tunanen mutane da yawa zasu nemeni sujita a kashe. Data na kunna na aje saman gado inda sakonni suketa shigo min kai tsaye bandaki na shiga nayi alwala don magariba daya kawo jiki idan na biyewa wayan za a samu matsala dani lokaci don shedan zai rinjayeni in shagala da zancen sallah. Na idar nayi addu a na shafa naji wayar tana sauti alaman kira yake shigo min lokacin na mika hannu na duba anty Nafisa ce akan layin. Ina dauka tayi sallama na amsa naji tana fadin haba matar yayana duk sallon amatcin ne haka ko waya baki dagawa sai kinga dama halan angon ya fitane. Ke kuma shike nan ko buki kinki fada muna muzo musha wallahi Ramaah ban zaci hakan daga gareki ba sam na dauka kome ke nan nice ta farko da zaki fadawa ai. Anty Nafisa ke nan nida ke kwance banda lafiya mezan fada maki satina daya ina gidan mama banda lafiya wallahi sai yau na dawo gidan anty salma dazun nan taban wayan na kunna kece ta farkon kirana yanzu. Haka madam Maria ta fada min cewa baki da lafiya to yaya jikin naki nace da sauki anty Alhamdullahi ya kuke ya su mama dasu inna ? Lafiyansu kalau Ramaah ga inna ma tana gaidake da jiki sai naji taba inna wayan ta soma fadin halo Rahama yaya jikin ya mutanen wajan ku ? Lafiya kalau inna na fada take fadin to kiyi hakkuri da kaddara kinji auren jafar alherine a gareki in sha Allahu ki fita zancen kowa ki kama mijin ki. Kada ki damu da zancen su yaya Dubu duk bari zasuyi tunda mijin ki yana kaunan ki kowa tasa ta fisheshi haka zaman gidan miji yake dama. Kada ki kula kowa kiyi abinda zaki burge mijinki dashi Ramatu ita wanan da tayi yaji karma ki tsaya kula ta ki zage ki nuna masu akwai banbanci a tsakanin ku. Barta can ko Allah yayi dawowan ta gidan kada ki yarda ki biyewa shirmensu na rashin hankali kin daiga yadda yar uwarki take dasu. Jafar mutumin kirkine yasan ya kamata kwanciyan hankali da kulawa yake bukata in sha Allahu zaki alfahari da hakan na gode inna na iya furtawa a cikin kyarmar murya. Na sake jin tana fadin na fada maki ki fita zancen su yaya dubu da sukeyi na asiri kikaiwa Jafaru keda yar uwarki har ya aureki. Lokacin naji muryan Nafisa tana fadin nikan inna zaki cinye min kudin waya bamuyi magana ba ta amshi wayanta badon inna ta gama zubanta ba. Naji tace min Ramaah to yaya jikin naki nace lafiya kalau anty Nafisa ta sake fadan yaushene tarewan naki koda yake ai kamar ba yanzu ba ko don ance yaya baya Nageria ya tafi kasan waje. Wallahi ban sani ba na fada maki ai dazun nan na dawo gidan anty sallma bansam komai a kai da suke shiryawa ba. To bari na barki saina sake kira mukayi sallama ta barni da waya a hannu ina mamaki a raina nace watau zancen auren dai yana nan a kaina ke nan ? Ni Rahama yaya zan iya rayuwa da yaya Jafar a matsayin mijina da fitinan gidansa ta ina zam soma wanan badakal auren da ya hau kaina yanzu kuma ? Har nayi sallah isha,i na koma saman gado na kwanta maganganun inna kemin yawa a kai na kasa hadasu a waje daya. Ni Rahama nice zanwa yaya Jafar asiri don ya soni ba yaya Jafar mai mata ba ko wani irin namiji ba zan iyawa a siri don na mallakeshi ba a ina ma zan samo asirin da zan masa din ? Zancen maganin na dashi ya fado min a rai gabana naji ya fadi na furta na shiga ukku shiyasa taimako yake da wuya a zamanin nan. Ko dai sun dauka maganin na asirine da zaisa ya soni nayi mashi a lokacin harwa yasan da zance haka banda nafisa da ya habu sai shi jafar din. Shigowan anty Salma ya katse min tunanane ta shigo tana fadin ke abinci fa bakya jin yunwa ne kika kwanta ,? A hankali na dago idona da sukai ja duk da ba kuka nayi ba a lokacin amma bacin rai yasa idanuwana sun sauya min lokaci guda ba yadda na dawo daga gidan mama ba. Meya faru kuma take tambayana muryan can kasan makoshi nake fadin ba komai anty tace ok ga abinciki nan nace jummai ta sako maki a kawo maki nan baki jin dadi ba lalai bane ki fito. Allah sarki anty salma ba abinda ya dameta ita hankalin ta kwance komai nata cikin gata ba tsamgwaman rayuwa nake fada a kasan zuciyana sai naji tace ke Ramaah ? Jafar din nan naki wani irin mutum ne shi gaskiya mutumin arzikine sosai wallahi a cikin matansa akwai mai cikine ashe ? Kai na gyada bata jira cewata ba taci gaba da fadin dazun nan ya turo min da kudi da za aiwa mai jego da jariri sayaya har daku daba haihuwan kukayu ba bayan lefe da na tausan gaba daya saka aka hada mashi. In wanine yana zancen aure a gabanshi aiba zai tsaya tuna hakan ba har ya tsaya hada kayan haihuwa kan wa yan nan yan iskan matan nasa. Ni wallahi Ramaah tun bangasu ba bakiji yadda na tsani halaiyansu ba haka kawai su hana bawan Allah shakat a rayuwansa don iskanci da samun waje wai meyasa matan hausawa akasarinsu suke hakane ? Naji ance wai ita dayan matar nasa tayi yaji tana gidansu tun ranan da taji zancen auren shi kuma yace a barta can ba inda zaije tunda bashi ya turata ba. Kala bance da ita ba akan zancen har jummai tashigo tana jera min abincin ta gaidani da jiki ta fice a dakin kallona tayi tana fadin ki tashi kici abinci kisha maganin ki. Kada mijinki ya dawo ya samu kin fada yace amanan daya ban ke nan na bari kika koma haka nidai banyi magana ba ta kare ta fita tana jaddada min da inci abinci fa. Sannu a hankali cikin hiran anty Salma nake ta tsuntar magana wai ashe har kudi yaya Jafar ya bayar a saya min wasu abubuwan da nake bukata. Saidai tace kudin suna hannuta don ita dasu mama sun hada min kayan daki komai daddy yaba da kudi a saya min gwargwadon hali ta kara ta sai min moderate din kayan kitchen na zamani dasu. Da anty Salma tasan zancen aurena akan jafar yana daga min hankalu da sam zata dingayi min zancen ba amma bamu zama bata sako min zancen shi a gabana duk dade gyarane irin ta yayyu take min a lokacin. Ina kuma karuwa sosai ga wasu abu da take ban duk da tare muke faman dirka da ita wani lokaci kuma ni kadai zata ba in shanye tas a gabanta. Training din rayuwan gidan miji aiko zama tsakanin mama da daddy dole kayi course sun tsufa amma rayuwansu zakice yarane har yanzu su balle anty salma dake cikin ganuwan kurciya a lokacin tana shanawa da mijinta. A cikin hakan muna waya da yar uwata har da mama saidai suyi ta kwantar min da hankali sam ban tsamaci hakan ga yar uwata ba na dauka zata shiga damuwa fiye dani sai gashi naga akasin hakan gareta. Ranan da mama ta kirani tana tambayana jafar ta kashe wayan ta barni da mamakin ta don dai ban taba tsamanin hakan wajenta ba yadda takeyi min maganan . Itace fa mai min addua Rahama Allah ya baki miji nagari inda zaki huta kema sai gashi a yanzu lokaci daya ta sauya min. Yandace ta kirani take fada min abinda ya faru har mama din tazo ta karbi wayan wai suna tuhuma Jafar ya daukeni ne mun fita tare dashi shine yasa tazo ta tabbatar da hakan a kaina. Bayan ta tambayi Nafisa tace da ita muna waya ina Abuja har yanzu amma hakan baisa ta yarda ba a yadda nake ji a bakin anty salma zancen tarewana wani satine insha Allah. Hakan ya kara saukar min da faduwan gaba ta ina zan fara ina zan kama yaya zanyi in zauna wanan gida da sunan auren jafar a kaina. Har wata zuciya tana ban shawara da ingudu in koma garin mu sai na tuna ai can aka daura min auren alkakan a kaina dole dai na tsurawa sarautan Allah ido. Sunje Zaria kwana su daya suka dawo saidai kaduna tace min zata ashe zaria sukaje gyara min daki saida ta dawo tana santin gidan take fada min ai sunje sun yimin jerene a zaria . Gaskiya Rahama kinyi sa,a sosai gidan ki ke kadai ba wani hayaniya ko saka idon da wani zai maki irin ta maria ke kadaice a babban gidan saidai gaskiya gidan nada girma sosai. Mun samu ya gyara gidan ya saka komai amma muka saka kayanshi a falonshi Kayanki da akai maki nan muka gyara maki naki falon hakama daki biyu muka gyara maki sai muka bar wancan a matsayin turakan maigida. Ni ba tsayawa saurarenta nakeyi ba ba don duk abinda zata fada ba burgeni yakeyi ba saukinsa ma yanzu da naji cewa ba a gida daya zan zauna da matansa ba . Sai abin ya dan min dadi a raina koba komai wanan zullumin da fargaba zai rage min akan ace muna zaune waje daya dasu. Nasamu training fiye da zaton ki mai karatu dan zaman da nayi da anty salma ta bude min ido ta wayar dani banda tsoro ko fargaba a baya har ina jin idan na koma zaria zamu kwashi yan kallo dasu. Sai gashi zancen auren nan na yaya Jafar a kaina yanzu ya jawo min cikas ga duk plan dina nima yanzu dole ta kaina nakeyi yadda zan kasance dasu . Balle nace zan taya yar uwata danayi niyar tayata zama da fitinansu yanzu kam nasan a kaina abin zai dawo gaba daya tunda dole in zauna kamar yadda daddy da mama suka roka a gareni. Shi kishi ko zaman aure ga ya mace halittane garemu mata wanda bamu san muna da baiwanshi ba sai in mun gwada. Haka kawai mace ke tsuntar kanta da iya irin rayuwan data zabawa kanta zatayi dma gidan miji don haka a bangarena idan na zauna ni kadai abinda nake tunane shine ta ina zan fara a gidan ? Da bangaren shi yaya Jafarne ko bangaren matanshi ko kuma bangaren mama da yaranta duk da nasan banda matsala dasu saida Saare amma yadda anty Nafisa ke fada min a yanzu mama ta canza sosai game dani. Nikan an sakani cikin tsaka mai wuya a wanan auren an tauye min rayuwata da yawa me zangane a wanan gida hakan ya zamo sonkai ga yaya Jafar duk da bansan ainihin manufanshi na zarga min abinda bai shafeni ba. KD Cikinta mahaifiyarta tayi da fada akan ta shirya ta dawo dakinta kafin tayiwa kanta aikin dana sani haka kawai zaki kwaso kafa kin dawo gida kin zauna don mijinki kawai ya kara aure ? Har uwar ta gama batace kalla ba don sai take daukan uwar bata damu da itaba yasa a kullum take nuna mata ta saita koma haka zikau ba wani magana akan shanmatan sa Jafar din yai mata. Saidai Halisa yarta ta shigone suka kebe tana fada mata irin matsin da uwarsu ke mata akan ta koma zaria din . Yaya takan fara magananta ke nan fa don me zaki koma zaria Jafar baizo ba ita bata tsayawa ta kwatowa mutum hakkinsa idan kuma za a kwato mashi ta hana,. Yanzu dai muje gidan anty Sabi,a muji kota samu aika sakon don nafi bukatan sai kin rikeshi zaki koma har in zaki koma din ne yar ta fada hakan yasa Nusaiba ta mike ta shirya suka fita ita da yar uwarta. Da kafa suka taka zuwa unguwar don ba nisa gidan Sabi,a din da alaman matar gidan tana da baki don motar da suka gani a kofan gidan. Sun shiga da sallama suna falo zaune suke amsa masu an fara gaisawa bakuwar Sabi,a ke fadin waiba Saiba umar bace ? Nice ta fada tana kallon mai maganan kafin tace sa,ade yakubu ko suka kwashe da dariya son tun barinsu makaranta rabon da su hadu don haka da murna suka rungume juna. Saiba ta kalli Sa,adatu tana fadin wai Sa,ade kece haka kinyi wani fresh dake kamar wata matar gwauna ? Murmushi wace aka kira din tayi tana fadin kaji ki dai da wani zance Nusaiba har yanzu dai halinki yana nan na zolaya ko ? Wallahi kina inane wai yanzu nusaiba ta kara tambayanta tace ina nan gefe daya ba kun manta da kowa ba yanzu haba dai ai kema kinsan hakan bai yuyuwa nakan tambayeki wallahi. Har yanzu kuna tare da mustapha ko haba dai daram kuwa muna calarba yanzu kinsan a can yake aikinsa . Kice min mutumiyar kinyi nisa da garin nan gaskiya na daina jin ki gaba daya wallahi lalai mustapha ya iya rikon aure kinga yadda kika koma wata babban mace ? Gaskiya da ganin ki kin samu kan mustaphan nan a hannu Sa,ade murmushin kasaita tayi tana fadin Saiba ke nan wani samunshi nayi kuma ? Takai zaune a gefenta tana fadin wallahi sa,ade kin kara hadewa ba irin mu ba nan ni gani wanan dan iskan zai kasheni wai wata kishiyar kuma ya kara auro muna yanzu . Cikin mamaki Sa,ade take kallonta tace saiba kanki daya kuwa da hankalinki kuwa ? Mijin naki kike zagi da dan iska meye a cikin kara aure don ya kara aure saiba ? Wai ina labarin Asmy ne har yanzu kuna tare kuwa ta bata rai tana fadin muna nan tana zaria muna nan muna bugawa da ita. Murmushi tayi tace kema Nusaiba kinsan ai dole ayi hakan kema kawarki ta kut da kut fa kika ciwa amana kina tunanen Allah zai barki haka ba jerabawane ? To amma ai naji ance kuna cikin rufin asirin ku don ina da labarin ku mijin ku bai rageku da komau ba na rayuwa. Naga tun haduwan ku kin kwacewa Asmy shi yana kuma yi maki yadda kike so to me kike bukata kuma ina ruwanki da kara aurensa ? Wallahi Sa,ade ba zaki gane bane ni yanzu ai nayi nadaman aurenshi uwarshi da yan uwanshine fa suke juya shi har mu . Haka basu kaunarmu ko kadan tundai ni basu sona musanman mahaifiyarshi da kaninshi wai shine yanzu don cin amana kanin nasa yasa ya auri kanwar matarshi fa. Ni kuma nace bai isa ba wallahi don ubansa sai naga yadda shegiya zata zauna a gidan nan ? Umm,umm subbahanallah Nusaiba har yanzu haka kike da wanan halin naki ashe wallahi gara tun wuri ki bari zaifi. Ni dai shawarata gaskiya dolene ki sauke wanan girman kan naki da wani jiji da kai har in kina son gane kan mijiki dole kiyi masa biyayya kamar yadda Allah yace ki kuma zauna lafiya da abokan zaman ki. Abincinsa shimfidansa da komai nasa hakama yan uwansa sai kiga kun zauna dashi lafiya amma idan kikace ba hakaba sai abinda kikaga dama zakiyi kinsan wallahi ko yar gwal kike ba zaku shirya ba ita Asmau fa da kika sama ? Na tabbatar ba haka take ba ita saidai yanayin zama dake sauya mutum wani lokaci don dai zuwa yanzu,,,, Bari kiji Sa,ade wallahi kinsan tun ba yau ba daga shi har Asmau basu isa su sake min halina ba don bawani mutuncin da zan tsayayi akan kishiya. Ke kika dauki wata tsiya wai biyayyan aure irin na matan da da suke wahala akan aure haka kawai in zauna ana juyani. Aure kuma nace bai isa ba wallahi kuma wallahi bai isan bane falon yayi tsit ana sauraronta a lokacin. Sai Sa,adatun tace waike hanashi auren zakiyi inace sai yaso zai zauna dake dai tunda ragamar auren yana a hannusa. Ai sai idan ya raga makine zai barki ki zauna har ki daga mashi hankali dashi da sauran matan nasa yanzu idan kin tada hankali yace ki bar masa gida fa ? Gabantane ya fadi sam ta mace zai iya yin hakan ta lamkwashe a waje daya tana tunane Sa,ade ta kalleta tana murmushi tace wallahi don haka kibi sannu. Gara kiyiwa kanki fada don namiji zai kara aure zaki tsaya kina wanan daga hankali haka duk gatan mace yau akace ta koma bazawara an gama dake. Don haka kibi sannu ku zauna lafiya kibar wanan cika bakin kada zance ya koma a kunnensa daga gefe halisa yarta tace shi nake fada mata. Shiyasa na kawota nan wajen anty ta dai dan bata dabarun mu na mata itama tayi kaddari kada dai ta koma baya a cikin kishiyoyi. Mafalki ke nan anty Halisa ai in banyi gaba ba babu shegiyar da zata shigo tayi gaba a wajensa bari dai in koma kawai ki gani. Haka dai suka zauna suna bata shawara amma a banza don ko daya bata dauka a cikin shawaran nasu ba lokacin har Saaden tayi masu sallama ta tafi. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 4️⃣1️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Tun bayan wayan ya habu da Jafar inda ya Habu ya fadawa Jafar cewa idan ya gama ya kamata ya dawo gida don har yakai mama ta tutseye maria ta kira Rahama tana tambayanta ina kake. Which means tana zargin cewa kuna tare da Rahama din tunda ana kiran wayanka bai shiga so kada su takurawa yar mutane da zargi a kanka . Wai meke damuwan mamane Habu ? Saida Habu ya dan fura iska a bakon shi yace da dan uwan zargina shine su kawu da yar iskan yarinyar nan Saratu. Saratu tana daga cikin wanda suke dagawa mama hankali akan zancen nan son basu shiri da Rahama tun farko kasani irin halin nan yasa nayi mata duka kwanaki ai. Ga yar iska taki karatu wai wanan mayaudarin mansur ta kwallafawa rai yanzu ni kuma nasan mansur bata isheshi kallo ba banda ya yaudareta kawai. Mansur kuma wani mansur kake nufi yace mansur dai naka mana ai tare suke dashi haka kawu ni sai yanzu nake tuna abubuwa da dama da mutumin nan yakeyi muna J. Amma mama bata gane hakan idan anyi magana tace ana son rabata da dan uwanta tillo sai ta nemi sabawa mutum a kansa. Ok wanan karon ku barni dashi nida kaina zan dauki mataki a kansa ai ba sai anyi wani magana dashi ba kawai nasan inda zan kamashi. Ka kyale kowa banson ka fadi wani zance daya shafi auren nan nawa don Allah Habu ka barsu duk abinda za a fada suyi ta fada a kaina. Kudi kuma na shirya tsab ranan da duk na dawo washegari in Allah ya yarda zan gabatar masu da kudin don haka ka lalabasu har in dawo don Allah. Ok zaka dawo kwanan ke nan ? Ehh saboda karatun yarinyar nan Rahama banson karatunta ya tsaya sun kirani sunzo sun gyara gidan sun saka mata abinda babu . Maria ta kirani tans fada min mutanen suyi masu kokari sosai sai godiyan Allah gaskiya mutanen arziki Allah ya hadasu dasu ba kowane zai rike amana haka ba ? Ya halakansu yake dasune Jafar ya tambayi kanin nasa yake fadi just mahaifinsune yayi aiki a karkashin Alh har ya rasu shi kuma tun yana raye Alh ya rikesu tankar yan uwanshi shine har yanzu suke halaka bayan ranshi. Kai Habu na dauka ai yan uwansu na jinine wallahi a,a fa kawai haduwan jinine duk da halakan ai ta zama ta jini yanzu ido ya lumshe yana raya abubuwa a zuciyan shi. Don sam bai taba zaton cewa ba halaka tajini bane tsakanin mu dasu ya dai dauka akwai zumuncin da muka rike akansu suma suka rikemu din. Sun dan kara tataunawa kan wani zancen kafin suyi sallama su kashe wayan kowa da irin abin dake cikin zuciyan shi a lokacin . ABUJA Ni mamaki nakeyi yadda anty salma take faman rawan kai a kaina haka sai kudi take kashi ga gyaran jiki da sauransu duk saboda zancen tarewana wanda nake sa rai bai wuce karshen satin nan da za a shiga. Duk da naji tana waya bayan mama tayi min buki a nan Abuja sai a koma can kaduna kuma ummah ta hada min walima daga can za a kaini gidan miji . Tankar ban wajen a lokacin saida ta gama wayantane ta kallo tana fadin waike haka zakita zama da angon nakine ba magana ? Shirun kifa ya fara ban tsoro Rahama aita magana kina zaune baki furta komai wanan wace irin amaryace wai ? To na dai bada dinkunan ki da zakiyi amfani dasu idan kinje kada ki fara idan kinje kice zakiyi amfani dako daya daga cikin tsofin kayan ki da aka sanki dashi gidan nan. Haka kuma kada ki yarda ki zauna gida ba kamshi ko jikin ki kwaliya ko baya gari ki kasance mai gyara Rahama don yana daga cikin abinda mazan yanzu ke so gyaran jiki. Abinci kuma nau,in daban daban zaki dinga dafawa kada kiyi rowa Rahama don haka duk wanda zaizo gidan ki ya kasance kin dan bashi wani abin sakawa a baki don Allah. Ban son ki da dogon hurda da kowansu a yanzu don kada ki yarda dayansu tace zata shige maki ki yarda sam irin hakan yana kawo matsala daga baya don haka ki kama kanki da kowa don Allah. Gidan ki babbane amma akwai maigadi kina kuma da makwabta makwabci ba kowane kake saurin yarda dashi ba balle nasan baki da matsala a wanan wajen don ke din kurace dama baki da saurin yarda da mutane. Rahama don Allah ki sauke komai a zuciyar ki kiba mutumin nan sallama abinda ya kawoshi gareki ke nan neman rayuwan inganci kada ki yarda a samu matsala a wajen ki Rahama. Kin daiji abinda mama ke fada muna kullum kada mu yarda mazajen mu su kuka damu a zuciyarsu idan muna son riban aure. Maza tankar magene sunfi taushi a inda aka san darajansu ko mutuntasu bawai ladabi da biyayya kawai ke kai mace da zama mowa ba sai mace ta iya kissa da na kwatar miji maza suna son haka kin dai gani da Alan,guguro yadda sai nayi dakyat yake barin gidan nan mu din kada ki manta da rainon mamace fa. Ya kama ace tun akan mama mun koyi rayuwa basai wani ya tsaya yi muna nasiha irin haka ba don mama a gaban mu kike ganin yadda takeyi da daddy bata hada komai da daddy ba a duniyan nan. Shiru nayi har ta gama ina saurarenta ni ina zan iya wanan abubuwan ga Jafar mutumin da ban wani saba dashi ina ma nasan abinda yake so da wanda baiso ?. Nikan dai ganinan zaki iya kirana da amaryan danko amaryan da aure yanzo mata kwatsam ba shiri shine wai ake so kuma naje na ririta mijin a hakan ? Kumshi ni kaina naji mamakin yadda kayan hadinshi ke kamshi kai mutanen maiduguri Allah ya hore masu sanin sirin kamshi a rayuwansu. Wallahi tun kamshi na damuna har nazo na saba don dole na wanka daban dana fito ga na tsuguni yana jirana haka za a yafa min wani bakin zani na zauna sai na bushe a hakan. Ina mikewa zata ban wanda zan fara murzawa a matse matse da kataruna hardasu hammata ni kaina saida na koma kamar zanyi kuka wani lokaci har kai akwai wanda tsohuwar zata rufe iya kaina da kasko tana turaramin kai in gajarce maki jin kaina nake kamar bani bace tundai da akai min gyaran kai din. Inda sumana na fulan ya samu gyara yayi baki wulk dashi sai kamshi ke tashi ga wani kasala dana zauna naji sanyi yanzune zan fara gyangyadi a wajen. Zan iya cewa Alhamdullahi Alhamdullah gaskiya dan irin ni,iman da Allah yai min lokaci guda na fahinci gaskiyan maganan da hausawa keyi na dare daya Allah kanyi bature wanan gaskiyane hakan. Cikin dan taki ubangiji yai min wani irin baiwa da ban taba sanin ina dashi ba sai a wanan lokacin gidan daddy na kwana ana gobe zamu tafi nan mukayi wani ganawan siri da mama da anty Salma mu biyu irin abinda da suka fada min a ranan yasa na kwana gabana yana faduwa. Washe gari da wuri muka dauki hanyan kaduna cikin tsalalun motocin gidan daddy dana mijin anty Salma mota hudu mukai tafiya dasu zuwa gidan mahaifiyata kaduna. Bisa rakiyan mama da yan uwa da abokan arziki data fadawa ni din yar dan uwansune daya rasu yabarmu . Manyan mata kanuri mazauna Abuja su shidda sai kawayen anty salma da ita kanta sune sukayi min rakiya mun sauka a gidan ummah anyi walima . Ni saida naji mamakin ummah ta waye ta zama yar kaduna a haraban gidansu akai walima ana gab da tashi saiga dagin ango sun iso suna bada hakkurin makaran da sukayi din. Wai ashe sai a na gobe yaya habu ya fada masu zancen tarewan wasu ma a ranan sukaji amma sunyi kokarin zuwa din duk da saida akai dan rigima don mama ta hau kawu ya samu ya lalabata tabada bakin azo din daga nan a dauki amarya. Nafisa tace yanzu mama tana can ta hake sosai taga inda za a ajekine Rahama don basu san da zancen gidan ki ba sai idan mun koma ko innata ban fadawa ba kinsan inna da surutu. Nayi murmushin yake zakice ba wani abu mai muhinmanci muke tataunawa ba da ita a lokacin don ko motsi banyi ba ina kallon yadda suka zuba min ido suna kallon sauyawata lokaci guda haka. Anzo da Salima da Saratu da sauran yan uwansu da suke uba guda karfe hudu bayan anci ansha aka dunguma zuwa zaria wajen kai amarya . Koda muka isa direct family house dinsu muka nufa saisu mama muka sama a gidan duk da gwargwado dangi sun dan taru lokacin. Wai mama tana can gidan Iya ita da wasu na kusa da ita nayi mamakin ganin harda anty Barakan zamfara ta samu zuwa bukin donni ban zata zasu yi hakan bama sai ina ganin komai makare akeyinsa ai. Hjy Yabi yar uwa kuma kawa ga mama tace akwasa a sameta can gidan daga nan a ba uwargidayena girman su kusan magariba muka kwasa zuwa gidan . A falon iya aka taru aka shiga gaisawa mama tana kallon bazata ko hajiyoyin ai abin kallone da kawayen salma. Taji mamakin ganin Salma nayi min yare ina dan amsawa a cikin kanuri iya sai haba haba takeyi damu tana kokarin ganin fuskana na boye. Tace yar fillo wayau kikai min haka kika kwace min angona ko da ina da ja amma yanzu na sake ance mai waje yazo mai aro ya tashi don haka nasake na barki da Jafar na kara noke kaina kasa cikin kunya. Hjy Yabi take tambaya ina kishiyoyin nata suke sai matar kawu ke fadin suna bangarensu ya fada maku inda za a sauke amaryan ? Basu fahinci me take nufi da zancenta ba hakan yasa sukace a gidanta mana ko ko a wani wajen ake fara sauka don su basu sani ba ko ana wani al,adane a nan ? Au ashe ya fada maku inda zaku ajeta din ai shike nan idan mun tashi daga nan gidanta zamu wuce da ita ai dama mama muka biyo nan din mu kawo mata amarya anty Salma ta fada. Basu wani tsaya ba suka mike duk da lokacin sallah yayi muka kwasa zuwa part din uwayen gidan nawa matan yaya jafar. Da irin kudansu na kanuri mai kada zuciya ya yamutsa hankalin wanda akaiwa girshi muka nufi part din matan yaya jafar din. Zakice basu san da zancen ba suna falo dukkansu muka shigo ita Asmau wani rigar abayane a jikinta sai ita saiba data saka wasu lace haka baki da adon golden jikinshi. Asmau kan tayi muna sannu da zuwa amma ita saiba ko kallo bamu isheta ba ba wani dogon gaisuwa hjy yabi ta fara fadin amaryace muka kawo kamar yadda al,ada yake . Da fatan samun zaman lafiya a tsakanin ku kuyi hakkuri da junan ku a zauna lafiya kwarai kuwa inji matar kawu ta dora da fadin amarya aiba bakuwarsu bace sun santa ta sansu. Matar kawu karma tazo da zaman lafiya mana mune dai ba wasu ba ai ta san mu mun kuma santa sai a dora inda aka tsaya. Mikewa anty salma tayi tana fadin su tashi zuje kada dare yayi muna aka barta nan tare da wasu yan gulma tana fada kamar karya. Bamu koma dakin iya ba muka nufi wajen motocinsu muka shiga ni dai kaina na rufe gwaggo Yatu najana duk abinda akeyi dai ina jinsune. Muna zama motan naji an soma fadin wai dama basu sanda zancen gidan bane anty salma na fadin bar yan iska idan basuyi hankali ba mace gidansu zata kwana ai wallahi. Sai gudan su hjy yabi ke tashi da karan motoci muka bar gidan na sauke ajiyan zuciya ina dan bude fuskana anty salma na fadin akara fesa turare wai zarni falon su Asmau keyi yasin da kyat idan batayi amai ba lokacin. Tare da matar kawu aka zo kawoni gidan dasu inna da anty Baraka basu jima ba suka tafi nan muka samu su Salima da Nafisa da maria an kawo abinci da abinsha kala kala gidan don taron baki wanda salima da Nafisa suka kai kwangilan dahuwan don fita kunya. Hjy Dubu yaron yau kaji tsoronsa kinga gida hjy dubu gida ai iyakar Aljannan duniya ke nan wannan gida ke kinga gida kuwa ? Kai lalai dan yau ka barshi inda ka ganshi ni sai ince wanan abu an dade ana shiryashi mune dai aka rufewa hakan. Kya fada kema hafsatu aisu salima na can ana sakin hanci kiji wai kamshin yar nan har yanzu dakin nan keyi don Allah kamar tana zaune wajen nan. Ga dai magana nan yana fitowa fili shine za ace wai a kyaleshi kada ai magana kada zumunci ya lalace zumunci ya dade bai lalace ba ya fito muna da hakkin mu ya bamu abin mu. In ma ya kama a saida wanan kayan karyan da yayine a sayar abawa kowa hakkinsa mu rike abin mu ai abin yayi yawa wallahi. Barshi kawai dai Allah ya kawoshi lafiya ai yazo yai bayani zamuji mai zai fada iya dake addua ta shafa ta juyo tana fadin. Kaiya Hafsatu shi babba gyara aka sanshi dashi ba barna ba kina fadin zancen nan kawai don ki tunzara yar uwar mijinki ta saba da danta. Baki tunanen kema kin haifa ai hafasatu na rasa dalilin da yasa kuke son a tozarta yaron nan yau ko ace yaron nan da dukiyan nan yayi auren nan aiba zakuyi masa haka a bainan jama,a ba dai. Jidalin nan tun daren jiya kuna abu daya a kansa har mutanen nan sunzo sun tafi yanzu ko hakan da kuka gani baku tunanen wani abu akan yaron nan Jafaru. Kuna nan kun kasa kun tsare kuba zai zauna wa dan uwasa wajeba tunda kusan babu waje a sashenshi ? Amma ya gwatsale ku ya nuna maku shi dan yaune ya riga ya tanadi inda zaisa matarshi ko ya barku nan zube da takaici. Naso ace yadda kuka shirya mashi ya faru da sai ince ke hafsatu da mijin ki ku fita min a gidana shi jafar ya gyara gidan su zauna sai Allah ya gyara hakan. Iya saboda jafar sai ki kori su yaya gida iya waya saka yaje yai auren da zakice su tashi su bashi waje Allah dai ya gyara nace dake iya ta sake fada. Matar kawu bata sake magana ba tayi shiru don dama itace mai dumi a falon kana jin muryanta yana tashi tana bada labari. Anty Asmau kikace yarinyar nan ce ya aura ni sai naga kamar ba ita bace wallahi wanan fa kanwar matar Habun gidan nan dai yar doguwar nan ? Ummm,humm bari ke dai safena wallahi itace ya narka kudi ta gyaru mana tunda ba abin kai sake bane abin daga can sukaji muryan Saiba cikin tashin hankali tana fadin. Wallahi bai isa ba yaya dama na fada maki akwai yaudara cikin zancen nan wai ki duba imaging gidane fa ita kadai a ciki ya kama mata sannan ace wai mutum yayi hakkuri ? Asmau ta dan dubi yar uwarta dake kusa da ita tana dan sakin murmushi don duk da zafin hakan da takeji tafi jin zafin saiba a zuciyar ta don da alama ta manta duk itace sillan hakan a rayuwansu. Abinda tayiwa rayuwansu na shigowa rayuwansu ta bata masu zama ita da mijinta da tun suna kanana suke soyayya sai gata kwatsam ta rusa masu duk wani mafalki nata lokaci guda. Wanan yasa bata kai Saiban jin zafin zancen auren ba da farko yadda Saiba ke cika baki yasa tana dan shan jinita ga zancen amma yanzu da tayi arba da yadda yarinyar nan Rahama tashigo a tsatsaye yasa ta ji wani dadi yana kume mata zuciyanta na muguntan kishi. Don haka zata koma gefe daya tasha kallo duk da ba zata yarda a mayar da ita tatakan gida ba zata dan turza itama ganin ba aimai da ita baya ba a gidan. Wanan abin yaiwa Asmau dadi a zuciyata duk da dai kishin kowa nadashi amma ko hakan da Jafar yayi ya nuna ita din ba kowa bace a yanzu kamar yadda yayi mata a baya yayi matukar mata dadi a zuciyarta. Ganin saiba data fito daki fuuu ta nufi hanyar fita tasan part din mama zata nufa aiko basu rufe baki ba wajen tafawa sukaji hayaniya ya kaure a gidan. Mikewa tayi da kyat saboda tsohon cikin dake jikinta ta marawa part din iya baya Nusaiba ta samu zaune gaban mama tana kwasan kuka tana fadin wallahi mama ba zan yarda ba. Tunda duk kan mu a nan gidan ya ajemu da kowa don me zai dauki yarinyar nan ya kaita wani gida wallahi Allah mama ban yarda saidai ya sakeni idan baisona ne ? Shigowan Asmau da yar uwata yasa ta sasauta zancen tana fadin don ya nuna muna iyakar mu muba kowa bane a yanzu zai muna haka ? Ikon Allah iya data dauro alwala zatayi sallah take fadin hakan yanzu ke Nusaiba namijine don yayi abinda yake gani daidai a gareshi zaki tsaya kina wanan bori haka ? Iya don Allah kiyi sallah abinki an tabasune dole suyi magana iya tace ina tabawa wajen nan ina nan kuke da safe kuna mashi dariya don uwarsa tace ba zata bashi wajen zama da yarinyar nan ba ? Jin dirin motansu matar kawu yasa iya tayar da sallah don kada su shigo su bata mata lokaci bayan wanda ta bata din a baya. Sai gasu sun shigo da sabon labarin da suke bayarwa wanda ya tayar da hankalin duk wanda ke wajen don Jafar yai masu bazata yau. Asmau da taji zancen yana batun hautsana mata rayuwa tacewa yar uwarta suje don a gabansu komai ya wakana. Saiba sai sabon kuka data saka lokaci guda cikin tashin hankali ba wanda ya farga da fitanta don kowa da abinda zuciyarshi keyi a lokacin . Matar kawu dai iya ta rufe mata baki haka mama tana ji a ranan in Jafar baiyi hankali ba zata iya mashi baki don saura kiris akai wajen yadda take jin yaudaran da yayi mata da yayanta yana ci mata zuciya lokacin. Wai ace yau Jafar ne yayi mata wanan tozarcin da bata taba tsamanin hakan gareshi ba duk cikinsu Yazid ne mai rawan kai da kuma tauri amma Jafar shine salihin su. Don haka wanan karyan da akace ance ya shimfida a gidan wanan yarinyar dole ya sayar da komai nasa a yanzu yaba yan uwansa hakkinsu. Kwandala ba zata daga mashi kafa daga ciki ko kudin bai kai miliyan goma ba zai san inda ya nemo aka basu hakkinsu inyaso shi ya zauna haka din tunda shiya jawa kansa hakan . Kamar Jafar ace mata ukku ina zai kai mata ukku da shekarun nan nasa sai taji duka matan nasa tana jin haushin su a lokacin. Ita saiba da tazo tana wani babatu ba zata yarda ba ta bari ta gani idan yaci dadin amarcib da yarinyar tunda harsu abin zai shafa yanzu taga karyan iskancin kowa a gidan yanzu. Itako maria tasan hanyar da zata fito mata ba tace ta iya kisisina ba daga ita har uwarsu suna ganin sun kitsa yar uwarsu tazo aci arzikin su dasu to za a ci din ta gani . Tasan dai gudu ya kare mai a yanzu tunda yarinyar nan ta tare gidanshi dole ya dawo garin yanzu taga ta iyakar gudun da yakeyi din nasu yanzu. Muryan matar kawuce dake fadin hjy Dubu ni zanje gida nabar kawun yara da tsaron gida tun dazun yana gidan shi muka bari da zamu fito. Mama dubun ta dago tana fadin hafsatu zaki komai in kinje kyaba yana labarin abinda ya faru ko sai ki sanar dashi da safe ya sameni nan ina wajen iya. Wai ina salima ta dauko maku ajiyan abin shan dana bata dazun ? Wai Salima ai tunda muka dawo kaduna suna wancan gidan da aka kai amarya gaba dayansu basu dawo nan ba anty Baraka ta fada . Kaji wata ja,iran watau tasan komai tun safe kallon mu takeyi shine ta kyale mu ta kara jin abinda ake fada to za a fasa fadane tunda ya kwamshe kudi shi kadai yana faca ka ? ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 4️⃣2️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Anan muka kwana dasu salima dake tayi min sheri wai itace ango din zata wakilci yayanta ita da Nafisa ko a cikin dare muna shirin kwanciya saida aka kara kawo naman gashi mai, mai da tsoka anyi mashi irin gashin nan mai ruwa ruwa ga yaji da su kabeji da albasa an cakudashi mai yawan gaske da abinsha na kwalaye. Daga dakin da muke muna jin su hjy yabi suna guda ganin irin gadan da ake baje masu a cikin bajinta don duk basu zaci hakan ba. Daga falo ina jin hjy yabi na kwalawa anty salma kira tana fitowa tace yoo Salma kinga abin arziki haka yaki karewa a gidan kanwarki ? Ai nace munga wajen zama mukam kila sai angon ya dawo ya tasamu gaba ya maida mu gida irin wanan gada haka aiba zamuso komawa gidaba mukan ana kawo muna wanan arziki haka. Fadawa yarinyar nan ta kara zage damtse taci arziki tabar arziki a inda ta ganshi don wanan wajen sakata da walawane ba irin na zubarwa ba. Ta fita zancen wayan nan matasa nata ta kama mijinta duk macen da take gidanta ita kadai sai taso saka kishi a kanta kan kishiya tasaka batama da wata kishiya a duniyan nan. Yo mai zai dameki yar nan tunda ba unguwa daya kuke dasu ba iyaka kiyi hakkuri tare da matanshi kika sameshi don haka kada ki yarda kiyi dakon kishinsu a zuciyarki ki wahala . Idan yazo miji ya tafi sai an dawo sai kiga an zauna lafiya duk abinda zai masu ko zaiyi da wata a cikinsu kada ki yarda wai ranki ya baci . Don haka wasu mata suke wanan yasa ake wahalan aure a yanzu ka samu mutum da iyalinsa kace saika rabasu da karfi da yaji. Wanan yasa matan yanzu da yawa basu son kishiya don basu san ko da wace ka shigo masu ba munji ta soma hauka kada ki yarda saboda da kishiya Allah ya konaki gobe kiyama ki barta ita tayi tayi duk abinda zatayi ke dai rike Allah da Annabinsa makami a gareki. Komai tsiya dai bata tasowa tazo nan sai ranan da kuka hadu in har wani abu ya haduku nuna mata kawai ke baki da lokacin shirmensu. Shiko miji da ance yau yana gidan ki ko baya gidan ki kyautatawa a tsakanun ku kada ki yarda kiyi sanya wajen ganin farin cikin maigidan ki. Sunyi maganganu masu inganci da in mutum nada hankali zai dauka don babu shege a cikin zancensu da farko inda daga baya kuma suka koma barkwanci anty salma na zolayansu da ko a koro masu naman ne ? Washegari tunda naga suna shiri na shiga damuwa don sammako zasuyi har matan kaduna su hudu da ummah ta hadomu dasu lokaci daya suka juya tare da tukwaicinsu na kawo amarya da anty su babba ta mika masu daga ango. SOUTH AFRICA Shi kanshi ya kadu iya kaduwa da ganin irin riban daya samu a wanan harkan ta ma,adanai daya soma tare da Maibei . Da farko yaki shawaran nata kamar dole tayi mai kan wanan halakan bayan dogon bayanin yadda abin zai kasace a tsakaninsu. Maibei tasoshi da arziki a rayuwansu ta kawo mai boyayyen sana,a damu yan arewa bamu faye daukanshi da muhinmanci ba a nan. Sai gashi shiga farko da kayansu yayi yaga ya samu abinda lissafin kan mutum ba zai iya kwatantawa ba wai duk a sunan riba. Ranan daya kira Meirbe yana sanar da ita irin yadda kayan suka samu karbuwa cewa tayi dashi ai dama na fada ma saidai ka zama boss ba zaka kara zama a karkashin wani ba idan har ka gane wanan sana,an. Ta fita da ma,adaine akwai wuya akwai hadari a ciki saidai amfaninsa yafi ga mutum yayi mata godiya suka kashe waya. Bayan satine ya kirata kuma again bayan sun gaisa yake fada mata ya gama komai yana son ya dan dawo Nageria saboda family dinshi. Take fadin haba dai family ai donsu ake neman kudin nan sunsan kana wajen neman kudi me zaisa ka damu ? Kinsan ina da mama kuma ina da yan uwa meaibe haka kuma matana a ysnzu ukku nayi sabon aure ina gab da tafiyan nan yanzu haka amaryan nawa ta tare a gidana ban gari. What kai at your age kamarka ke da mata ukku gentle man haba haba ina zaka kai mata ukku a rayuwan ka me kake so ga mata hakane ? Dariya ya kwashe dashi tace wait woo are you kidding me in wasa kakeyi ka bari please ina aure dai mutum ya samu mace daya is ok for him sai su haihu tare su dubi yaransu ? You know iam muslim my religion accept this for me our prophet comand us to marry four wives if posible for a man and there is special reward for doing that in islam . If you can feed them give them a shelter and cloth them and all there needs katseshi tayi da fadin is that all you can give a woman my friend stop telling me this ? Wai har kana fadin kayi sabon aure for where my friend wace mace zata yarda ka aureta kana wani duniyan ka barta a gida ? Iam telling you wallahi ni angone nayi aure kafin na bar Nageria kalman wallahin da taji ya ambata da suka san musulmin kwarai bai wasa dashi yasata fadin . Eeee way are you serious my friend ya kara furta wallahi i marry a young fulani girl but she is schooling now in A B U zaria ,,,,,, Ta sake katseshi da fadin so you are serious friend who is dis lucky girl that charm you heart ? Tayi sa,a data sameka a matsayin miji a rayuwanta duk da ka bata mata tsari don nasan ba zataso ta zauna a cikin mata haka da yawa ba tana educated ? Dariya yayi yana fadin mu a wajen mu musulmai wanan ba matsala bane don haka muka taso muka gani ga iyayyen mu. Sun dan jima suna hira kafin suyi sallama da juna akan zai kara kiranta idan tafiyan nasa zai yuyu a lokacin kamar yadda yake so. Bayan sun gama waya ya zauna yana tunanen zantutukan da sukayi da ita din haka dinne gaskiya akwai tauyewa a cikin lamarin wani lokaci amma zai iya kokarinsa wajen ganin bai tauyewa kowa hakkinsa ba. Yau da ace baida zarahin hakan ya kumayi hakan yasan akwai tauyewa sosai a cikin lamarin yadda zai daukota ya jefa cikin matansa da kansu har yanzu basu bari ba balle a dauko wata a hadusu zama a waje daya. Matan dakowa nasa baida mutunci a idonsu kowa suna masa kallon bai isa ba har dai Saiba daya dauko wace bai gama sanin halinta ba ta yaudareshi ta hanyar abokinsa. Wai kuma yanzu itace mama take nunawa goyon baya don saboda Saratu kome shiya rasa abinda ya rufewa mama ido har take masa wanan mumunan fahintar ayanzu. A iya saninsa ya taso cikin yiwa mahaifansa biyayya tun mahaifinsu yana raye har zuwa kawu da suka dauka mutum na uku mafi daraja a idanusu. Amma yau sai gashi an wayi gari duk hakan na kokarin ya tafi a banza wajen mama tunda har take iya zarginsa akan kudin da bai taka kara ya karye ba. Ya dan murmusa ya gyara zama don tuno ko dai saboda Rahamane har kiyayyanta da mama ya shafeshi haka amma a iya saninsa ai mama bata taba nuna bata kaunar yarinyar nan ba a gabansa. Don ko dan zaman jinyasa da sukayi ya fahinci kamar akwai kyakyawan halaka sosai tsakanin yarinyar da mama don yadda take yabonta a gabanshi yana daya daga cikin abinda ya kwadaita mashi yarinyar ta kasance daya daga cikin iyalinsa don ita mama din data nuna hakan . Sai gashi kuma abinda bai taba zato bane ko tsamani yake fitowa daga mama din yasan sun taso mahaifiyarsu na matukar sonsu a rayuwansu. Mama irin mahaifan nan ne da keda rayuwan da ran yaronsu ya baci gara nasu ya baci sau dubu a wuni. Haka kuma akan danta zata iya yin komai yasan da wanan don haka dole akwai wani abinda ya faru da baisan dashi ba game da mama din. Koma meye tunda har ba laifi yayi ba kawai don ya auri Rahama zaisa mama ta nemi tozartashi haka a idon duniya ? Zaije gidan zai yi kokarin ganin ba a kai ga samun matsala ba tsakanin shi da mama din ko yan uwan nasa in sha Allahu yasan wajen matsala gudane sai yayi da gaske akan matanshi don ko bai samu matsala da Asmau ba dolene zai samu da Nusaiba. Sau daya ya daga wayanta kafin ya baro Nageria irin ashar din data dinga mai tace zatayi a gabanshi yasan ba zai lamunci hakan ba gaskiya. Koma meye yana rokon Allah ubangiji ya kawo mai sauki akan komai ko wani bangare magana dayace a yanzu itace dole ya jajirce ya kara zama namijin gaske ako wani fanni. Yajima zaune yana zancen zuci har tsawon wani lokaci kafin ya mike zuwa ciki don ya watsa ruwa a jikinshi yana son fita da yamman zuwa wani waje. ZARIA Tun bayan tafiyan su anty salma gidan yai shiru duk da Nafisa da Salma suna gidan amma suna daki suna barci kasa kwanciya nayi na fito na gyara ko ina na gidan sai kusan azahar suka tashi banga laifinsu ba tunda akwai gajiya a lokacin koni ban samun sukuni idan ba naga waje da tsabta ba haka yasa na kasa kwanciya na gyaro ko ina . Wanka nayi tare da sallah na saka wani atamfa saiki rantse abayane rede made dinkin ya hadu sosai gashi kayan sun matukar karban jikina. Kalansu yayi min kyau sosai dama tasan hakan yasa komai ta zabo min abinda nafiso don sai incema na zabo a cikin rashin sanin cewa nice mai kayan a lokacin. Ban fito daga daki ba duk da ina jin muryoyinsu a falon sun kuna tv kuma suna hira saida nayi sallah la,asar Nafisace ta lekoni taga ina sallah take fadin har la,asar yayi ashe muna nan zaune. Bayan mun fitone na gabatar masu da dan dabaran da nayi muna don kada mu zauna da yunwa duk da ban tsamanin hakan akwai abubuwan da zamu iya ci a lokacin. Tunda ns fito naji salima tana fadin wai kan uban nan wai Ramaah ko dama course aka kaiki yine Abuja ? Nifa gaba daya wallahi kin sauya min sai nake kallonki kamar bake ba Allah tun jiya duk kin sauya min ga sanin da nayi maki ga baki daya kin juye kin zamo min wata ta daban. Dan murmushi nayi ina fadin kai anty salima wani irin sauyawa kuma don Allah ni din daice Rahaman da kika sani a idonki. Gaskiya akwai drama wallahi na yarda da ake fasin akwai wani rahama a cikin aure da sai wanda yayi yake fahintar hakan. Na duka na bude abincin dana aje a gabansu suka dago suna fadin meye wanan abincine na basu amsa. Salima dake kishingide ta kalleni tana fadin yaushe kikai wanan aikin Ramaah nace kuna barci tace wai yadda na gajin nan nima nasan nayi barci sosai wallahi. Tun shekaran jiya da ya Habu ya kiramu wallahi bamu huta ba muna tsaye ai dole mutum ya gaji don ma gidan anty Ai muke akwai yan mata a gidan da suka tayamu aikin . Wallahi naji dadin kai aikin nan da akayi gidan anty Ai ai kinga yadda take farin ciki kuwa sai kiran abokan arzikinta takeyi tana sheda masu abin arziki ya sameta. Da kikace ta bar komai daya rage a wajenta idonta kamar zatayi kuka a lokacin tama rasa me zatace a lokacin don mamaki Nafisa ke fadan hakan. Nafisa anty Ai mutum ce fa tafi mun su anty yar malam sau dubu wallahi baki taba jin zance ya tashi ace da anty Ai a cikin zance. Nima ai hakan yasa naji dadi da kika fada a cikin gida cewa yaya yace gidan anty Ai za ai komai har baki su wuce. Wai baki ji sakaran nan Saiba ba da nake fadawa iya tana tsaye sai cewa tayi wai dama ita ya dace aje can tunda taronna yan kauyene ai. Kuci abincin mana na fada ganin sun bar abincin a bude yana sanyi a lokacin saidai hakan bai hannusu hiran ba sukaci gaba da hiran yadda Saiba tayi ta iya shege tana cika baki. Salima ta kare da fadin saiga shegiya tayi lakwas dataga karyan bariki baki ya mutu ance bayan zuwan mu nan ai bala,i tasa don wallahi yaya yayiwa kowa bazata ga auren nan. Gaba daya ya nunke kowa a baibai don bai bari kowa ya fahinci komai ba su matar kawu ba a samu kafan iya shege ba wanan karon da bukin maria yaya habu matar nan tayi iskanci sosai wallahi. Ta hana komai karshe ta kwashe takai gidanta sukai ta amfani dashi muguwa kawai ni wallahi nasan itace ke kara yiwa mama fanfo akan komai. Itama mama ni har mamakin yadda ta sauya nakeyi ni yanzu har tsoro nake ji idan mun koma gida nasan ana jirace damu mu koma a zazagemu. Ina gefe daya na takure a waje daya ina sauraren hiransu wanda nake ta auna abin a zuciya da nice mama bataso komai me nayi mata haka ta tsaneni lokaci guda ? Sallah magaribane ya tayar damu a wajen nashige daki suna falo nan sukai sallah ina zaune na kunnu wayata naji karan budan get din gidan muryan maigadin gidan yana tashi. Wai ashe maigidan ne ya dawo a lokacin yake mashi sannu da zuwa salimace ta leko tana fadin ke ga yaya nan wallahi dama ya habu yace kila yau din nan ya iso ai. Mukan zamu tafi gida ke ban yau ashe sai lokacin na dago ina fadin haba anty salima ku tafi gida kamar ya ? In kun wuce dawa zan zauna kuma a wanan gidan kaji munafuka angonki ya dawo kice wai dawa zaki zauna inba kina son sai dare yaya ya gargadamu mubi hanyan tudun wada da kafa ba. Don wanan kwaliyan haka muddin yaya ya gansa yau wallahi idonsa rufewa zaiyi yace me kuma ya tsayar damu ? Na girgiza kai ina fadin anty Salima bamu haka dake fa keda kuma nake samun sauki a wajen ki kin maye min gurbin mariata yau. Tayi waje tana dariya na soma jin muryansu suna mashi sannu da zuwa yana amsawa a cikin muryan nan nasa da dan maganan shi da sauri da sauri yana fadin a,a Nafisa kuna nan ashe sannuku da kokari fa salima ya akayi kunsha hidima fa. Can dai na daina jinshi a falon suma hakan saidai baifi ko minti biyar ba kuma naji yana fadin ya haka kuma ina kuma zaku da daren nan . Muryan Nafisa naji tana fadin gida yaya wai kada dare yayi muna a nan mu rasa abin hawa yace gida yin me kuma don Allah ku mayar da kayan nan ba inda zaku yanzu kamar wa yanda ake kora kuma ina ita Rahama din ?. Muna ga rasulu na fada karda kirana zaiyi haka gabansu shifa haka yake ashe da kowa tsatsaye ba ruwansa. Ina zaune a inda nake na maida hankalina a wayata naji an ruro kofan da sallama ta dan dago mukai arba dashi naji gabana ya soma faduwa . Shima hakan yaji gabansa ya fadi a yadda ya hangoni din zaune saman kujeran dakin na dan dogara jikina ga hannun kujera din da wayata a hannuna. Ga wani irin ni,inttacen kamshi mai kashe jiki dake masa barazana da zuciyarsa ya tako har zuwa gabana na dago cikin sanyin murya ina mashi sannu da dawowa . Ya lumshe ido yana amsawa da yauwa amarya kinsha kamshi ya kika zauna ke kadai a nan gasu can a falo su ko duk bakuntace har yanzu ? Kamar yadda ya dake ya nuna ba komai nima hakan na dake na fara bashi mamaki nace a,a sallah nashigo inyi sai ban fita ba. Taso kije wai gida zasu yanzu amma nace a,a saboda me zasu gida yanzu daga dawowata muje falon mu samesu . Jin hakan yasa na mike tare da daukan dan yalolon gyalena dake gefe daya daga dagashi sai wani kamshi ke fita na daban a dakin hakan yasa ya lumshe idonshi. Ina mikewa naji ya cabki hannuna lokaci guda gaba dayan mu saida kowa jikinmu ya amsa yayi wani yarrr tundai ni da tunda nake babu namijin daya tana ko gwada rike min hannu a rayuwata. Inda shi kuma tsaban taushin da yaji a hannun nawane ya dimautar dashi haka muka fito falon suna zaune tsit a falon sun kurawa tv ido sukaji muryanshi yana fadin. Ga dai matar gidan na kawo muku tunda kuna son yi mata tawaye ku gudu zuwa gida Nafisa tace Allah yaya daka barmu mun tafi tunda ka dawo me zamu zauna yi kuma a nan ? To ke Rahama kinji sai ki basu hakkuri ni dai ban korar maki suba kada kice don ni suka tafi na dan kallesu nayi murmushin da nasan zai dagulashi aiko saida tsikar jikinsa ya tashi nace aiba zasu tafi ba su barni ni kadai. Bari na kawo maka ruwa yaya nan na zare hannuna daga rikon da yayi min a cikin dabara na nufi kitchen a cikin wani tako da ban ma san ina yinsa ba lokacin. Inda ya shagala da kallon bayana ga rigar ta daneni ta baya mazauna da nakan juyawa anty maria don taji haushi suna boucing a ciki. Ya zauna yana lumshe ido a cikin gajiya ga wani bakon kasala da yaji lokaci guda yana sauka mashi tunda yai arba dani ya koma daya sani hakan zai samu taro da yabar yaran nan sunyi tafiyansu amma yanzu ya riga daya kwafsawa kansa kuma ai. Ruwa na dauko a cikin tumbula da zaki iya ganin ruwan karara kwance a cikin madaukin sai cup din glass irinsa dana hado dashi na kawo gabansa na dan rage tsawo ina tsiyayya masa lokacin ya sauke hannunsa dake saman goshi ya bini da kallo tare da ajiyan zuciya da shi kadai yasan dalilinsa. Ya miko hannu ya karbi ruwan tare da fadin thanks ya kai bakinsa saida ya shanye ruwan tas ya aje kofin yana fadin Salima yasu iya dai ? Au bakaje can ba ke nan yace direct nan na nufo ai nagaji sosai yau salima da safen nan fa na dawo Nageria na kuma hau jirgi zuwa Abuja daga lagos yanzu kuma gani gida aikinga akwai gajiya. Kayan na kwashe zuwa kitchen na barshi dasu nan suna dan hiran zumuci can na gama yan dabaruna sai gashi na kata fitowa da da try din dana hada na sake direwa a gabanshi. Kazace data sha gyara wace taji albasa da kabeji su tattasai da kayan kamshi nayi warming dinta a ovorn ga kuma lemun kwakwa da madara na kwali na aje na kallosa. Naga duk hankalinsa yana kaina nace bissimillah yaya dare yayi kada ka kwana da yunwa suma nayi masu tayi. Ai kema ko dazun da mukaci bakici komai bs ki zauna kici Nafisa ta fada nace aiko naci mana anty Nafisa mamaki kamar zai kasheshi a lokacin haka ya daure ya jawo zuwa gabanshi yana cire foilpepper din dana rufa ya kai idonsa sama. Ya kara lumshe idanunsa tare da hamdallah ga ubangiji yake fadin duk tare za aci ai ki zauna muci ya fada yana masu bissimillah. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 4️⃣3️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Wani yanayi na wasan yar tsamane ke gudana a tsakanina dashi agaban yan uwansa a lokacin don saiki rantse da Allah dama akwai shakuwa ko soyayya sosai tsakanina dashi lokacin a haka muka nunke zuciyarsu da kasa fahintar mu. Suma din sai faman mamaki hakan kowansu keyi a zuciyanshi don yadda komai nakeyinsa a natse cikin wayewan kai nafisace ta fara mikewa wanan lokacin. Don barin falon wanan dakin da sukaiwa kansu masauki a cikinsa ta shiga da sunan kewayawa bandaki daga nan bata fito ba kuma. Kafin Salima itama tabi bayanta zuwa dakin suka barshi shi kadai a falon zaune yana waya. Don lokacin na mike ina kwashe komai da akai amfani dashi zuwa kitchen na dawo na gyara wajen nan na samu su dukkansu sun bar wajen a lokacin. Zuwa lokacin barcine duk a idona don nima hidimar bukin da jewadi ya kashe min jiki don sai a lokacin nake jin tsamin jikina na gama na nufi dakina na barshi nan a zaune falon kofan na rufo na fara zuge zip din rigan jikina na fada bandaki. Ina shiga na fara cude jikina da wani ruwan turarensu na madara irin tasu ta mutanem maiduguri wanda mama tabani tace dinga hakan dashi da dare kafin na kwanta. Bayan na gama na fito na dauki Rigan barcina dana dauko na dauka saman gado ina zurawa a jikina ji don barcine sosai ne a idanuwana nake jiba a lokacin . Ina kokarin zura rigarne naji anrugumeni ta baya ana sakar min nauyi da sauri na iya furta subbahanallahi na ambata a fili duk jikina yana rawa lokaci guda don tsoron hakan da naji . Danshina nayi kokarin juyowa cikin faduwan gaba don ganin ko waye haka ya razanani lokaci guda duk da ban faye tsoro ba amma hakan dai ya firgitani. Saidai haka din bai samu ba a gareni don irin rikon da akai min sam na kasa jiyowa din inga waye a lokacin. Amma saboda sautin numfashinsa dake shiga kunnena a lokacin naji a cikin wani yanayi wanan yasa lokaci guda jikina ya dauki rawa tsoro yana dada shigata. Wani abu naji yana min yawo tundaga tsakar kaina har zuwa yatsun kafana jikina sai kyarma yakeyi don ban tsamaci hakan a lokacin ba. Nauyin Kanshi da naji ya kwantar a kafadana yana fadin relex baby Rahama ba komai zan maki ba just live me to hug you. Na samu natsuwa kawai nake son samu a wanan lokacin yanzu gareki ya fada kamar mai yin rada a lokacin cikin kunnuwata. Kalman na natsuwa na sake maimaitawa a ciyana kamar wanda ya karanto zuciyana din naji yace please Rahama don't judge me accondin to my sin ina kaunarki har cikin raina ke din kamar zabinace Allah ya kawo min a sauwake har gida don Allah kada kice zaki hukuntani bisa kuskuren fahinta . Hawayen da nake kokarin tarewa kada su zubo daga idona sune suka dinga diga saman hannunshi haka ya sanar dashi kukan da nakeyi a lokacin mara sauti. Subbahanallahi are you crying Rahama sabodani No no no no don Allah ki daina nasan ni mai laifine a wajen na shiga maki rayuwa bada sanarwan ki ba. Amma ina son ki dauki hakan a matsayin kaddaran mu gabaki dayan mu Allah yayi sai munyi rayuwa irin hakan a tare dake koda iya hakane kuwa a rayuwan mu. So ki bari na gama dan abindake gabana kafin mukai ga matsaya a tsakanin mu ba zan maki dole a kaina ba Rahama ko haka Allah ya barmu nasan kinyiwa iyayye biyayya dani. Naji dadin natsuwan da kika nuna a gaban sisters dina ko iya wanan kika barni dashi nagode Rahama don kinyi min abinda ban taba zato ba a wajen ki. Na dauka sam ba zan samu kallon arziki ba ko tarbo sannu da zuwa sai gashi kin fitar dani kunya a lokaci guda wanda ni ban taba kawo hakan agareki ba. Yana maganan yana kokarin dago habana dake dage yayin dana gane nufisa na cije cikina a waje daya naki yarda hakan ya faru. Sai naji yayi murmushi ya dan rage rikon da yai min din da farko wanan karon hannuna ya kama zuwa bakin gado ya zaunar dani shima ya samu waje ya zauna a kusa dani. Dan shiru ya biyo baya a dakin kafin yace wallahi Rahama banyi haka don in tauye maki rayuwa ba nayi don ni a wajena komai naki wallahi yai min ina sonki sosai Rahama saboda halaiyan ki don haka ki ban hadin kai mu zauna lafiya. A raina nace bakai bane yanzu fa ya gama cewa jn bashi time in rufa mai asiri ya fara fuskantar abindake gabanshi yanzu. Yanzu kuma ya dawo yana rokona da mu zauna lafiya bisa amana kada dai ya zamo munafukin namiji mai baki biyu ? Wa yan can suma Allah kadai yasan irin dadin bakin da yaje yayi masu a kaina duk da ban tabbatar ba amma akasarin maza haka suke da baki biyu ga matansu. Me aka fada maki Rahama akan zargi wata zuciya ta tuna min da hakan daga bangaren zuciya tiryan tiryan nake tuno zancen su hjy yabi da sukai min a karshe don haka dole inyi taka tsantsan da rudin zuciya mai kai mutum ga halaka . Wanan aure dai matukar bashi yace ya fasa ba dole in hakkura da komai in zauna da yaya saboda biyayya kamar yadda su daddy suka rokeni dayi don haka alkawari na dauka in sha Allahu zanyi biyayya ga zaman aurena a gidan ya Jafar har inda rabon zaman a tare dasu. A zatona zai koma dayan dakin daba kowane kamar yadda anty salma take sheda min wancan dakin yurakanshine nan kuma nawa sauran dakunan biyu kuma na aje don baki daya kuma na dinga amfani dashi ni kaina daki biyu ke nan suka ware min ni daya ko ina zan kaishi oho ? Hannuna ya sake rikowa yana dan murza yatsuna a hankali kamar dai wanda ke wasa da hannun yaro yayin da wani boyayyen sakon da ban,saba dashi ba ke bin ilahirin jikina yana sakar min da kasala. Kan na tantance sai ji nayi ya sumbaci gefen wuyana nan da nan jikina ya fara rawa tsoron hakan karara ya baiyana a gareni lokaci guda. No kwanta ki huta akwai gajiya a tare dake ya fada yana kokarin kwantar dani saman gadon kamar karamar yarinya banki ba nayi yadda yacen na dunkule a waje daya ina mai kame jikina. Wani ajiyan zuciya ya sauke yana kaiwa kwance daga gefena nima din na sakankace da zancenshi hakan yasa na lumshe idona ina sauke ajiyan zuciya. Ido a rufe zuciya tab da fargaba da zullumin hakan dana tsunci kaina a cikinsa lokaci daya naji saukan hannunsa saman jikina a daidai wajen da nayi shekara da shekaru ina boyon abina da hijjabi ko gyale yau sai gashi a saukake hannun wani ya kai ga wanan abin. Bai dai min komai ba a ranan kamar yadda yace saidai nasha luguda kamar mangoron da akeson ya nuna a lokaci daya. Da misalin karfe hudun asuba naji tashinsa already na falka a lokacin don sabo da hakan danayi a rayuwata ban daki ya shiga ya dan jima kafin ya fito yana dan kiran sunna da intashi kada in nakara ganin na falka ya bude dakin ya fita hakan ya ban daman samu na mike na shiga bandakin. Wanka nayi ina hawaye har nagama na fito na dauko kayan sallah acikin wardrobe dina na tayar da sallah ina idarwa na koma barcin don idona cike yake da barci a lokacin. Alhamdullahi don ko na samu barcin nayi ban falka ba sai wajajen takwas na safe na tashi dakin na fara gyarawa duk da a gyarensa yake amma haka bai hana na kara tsayawa na gyara ba na sauya zanin gadon na sharo na kawo kamshi na feshe dakin dashi na shiga wanka. Bayan na fito na saka kaya wasu light green lace mara nauyi da akai masu dinkin riga da skirt na saka sunji duwatsu anyi kwaliya a gaban rigan da bakin lace din saina zauna gyaran fuskana a gaban mirro. Lokacin ya shigo dakin a cikin shirinsa na wasu fararen shadda da akaiwa dinkin gajeren hunnu sai bakaken takalma a kafasa kansa babu hula. Da sallama na amsa ina dukar da kaina kasa ya karaso yazo daidai bayana ya tsaya muna kallon juna a morron nayi kasa da kaina na zame kasan kujeran na duka ina gaidashi da kwana. Wani irin mamakine da yarinyar nan take kasheshi dashi yaushe rabon daya tunama ana gaida miji da kwana a addinance ko al,ada ? Wani irin son ta yaji yana kara shiga zuciyarshi don tunda yake koda tuntuben harshe matansa basu gaidashi da kwana wani lokacin ma da fada suke tashi tsakaninsu tun asuba. Hannuna ya kamo muka koma bakin gado muka zauna naji ya ambaci sunana yana fadin Rahama jiya kin shayar dani farin ciki a rayuwata kin tabbatar min ke din yar mutuncine data gaji hakan. Kin tsare mutuncinki dana iyayyenki ko a hakan da kikai min nagode sosai Allah yayi maki albarka nayi kasa da kaina a cikin nauyi da kunyarshi. Wallahi Rahama komai naki kara burgeni yakeyi ina son ki sosai wallahi don Allah ki ban hadin kai mu zauna lafiya Rahama". Abune a baiyane da kika sani tun bayan wata ukku da aurena da Asmau farin ciki ya gushe min ba zance banjin dadin zama dasu ba don su din matanane amanatace kuma su din. Amma sun kasa ban irin farin cikin dana taso ina mafalkin kansancewa a cikinsa sun hana min kwanciyan hankali sun kasa gyara kansu wanan duk ba bakon abu bane a wajen ki don kinsan komai. Wayanshi dake ringing bai kula dashi ba nakai ido na kalla sunan ya Habu na gani a wayan ganin ina kallon waya yasa ya dauka yana fadin. Hello Habu ganina shirya yanzu zan karya in fito kana gida ko ban daiji amsan da habu din ya bashi na daiji yace hakan yayi daidai zanzo da salima din. Mike tsaye yana fadin tashi muje ki karya yaran nan sun hada muna abin kari yana falo ina son in mugama zan shiga gida mu gaisa dasu don ban samu zuwa jiya ba na gaji da yawa. A raina nace ka daizo hanawa rayuwata shakat malam banki ba din na mike na yafo gyale a kafadata muka fito falon a tare dashi. Salimace a falon tana jera kayan breakfast din data shigo dana karshe jin motsin nu ta juyo tare ta ganmu munfito daga dakin ta fara gaida yayab nata kafin ta juyo kai muka gaisa a yar kunya da ita. Ina Nafiss ya tambaya take fadin tana kitchen ku zo ku karya zamuje gida dani dake mu dubo su mama ba zamu jima ba so Nafiss ta jiramu mu dawo. A gurguje naga ya karya da ruwan shayi sai dsnkali da kwai ds suka soya shi naga ya tutura ya juyo yana fadin ina salima din ta fito mu tafi kada mu kara, Barin lekasu indawo don Allah ya juyo yana fadan haka gareni a cikin kullawa nayi masa Allah ya tsare ya kare ya amsa da amin ya fita. A waje ta sameshi har ya shiga mota saboda kawu da yaya Habu yayo masa da text yazo ya gashi a falonsu mama suna magana daya shiga gaisheta. Koda suka kama hanya da salima ya kalleta yace salima kunsha fama ban nan ashe abinda kawu ke kulla min ke nan jiya ban fito da maganan bane don Nafisa dake zaune. Ai kawu gaskiya mugun mutum ne yaya makin ya taushe mama ya bata hakkuri wai amma shi da matarshi sune suke zuga mama a kanka ni shine ya bani haushi wallahi. Yadda kake kokari dasu din nan amma suka iya haka basu nuna mata gaskiya ba wai ace mama ta zauna tana shirin ci maka mutumci akan inda zaka aje matarka ? Me Rahama tayiwa mama don Allah tunda ba itace ta tillasta maka dole ka aureta ba kai kayi ra,ayin haka kuma iyayyenka suka bata duk fa yaya Habu ya fada mata komai amma mama ta yarda ta dauki zugi a kanta game dakai. Bakomai salima dukiyane yau zan mayar ma kowa da abinsa inyaso suyi abinda suke gurin yi dashi nadai godewa Allah da ban taba dukiyan nan ba. Yanzu yaya mayar masu zakayi wallahi yadda naga su kawu sun damu kamar suna da wani manufane akan kudin nan in bashi ba meue nasa a ciki don Allah ? Maigadi na bude masu get kawu din suka fara hangowa tsaye kofan part din Iya yana waya ya zubawa motansu ido har suka karaso. Da farko bai sheda waye ba saida J din ya bude motar ya fito tare da salima ya gane shine lokacin kuma waya yakeyi game da J din yana tambayan lamban a wajen abokin J din daya sani. A,a Jafar dama kana kusa ashe to sannu da zuwa ashe kana hanya dama ? Eh kawu ya fada yana hawo step din da zai sadashi da kofan iya bai tsaya ya gaidashi yadda ya saba bakawai yasa kai ya shiga wajen iya da sallaman shi. A,a a lale marhabin dan halas kaki ambato ashe ana nan ana faman cigiyan ka kamar wanda ya bata sai gaka kwatsam ka fado ? Ashe dama kana kusa ba nisa kaje ba to sannu da zuwa yaya hanya iyace ke wanan magana tana taba hannayenta daga inda take zaune. Iya wake cigiyata haka kedai ko don kada amarya ta daukeni ya fada yana zama gefenta sai wani annuri yakeyi da ganinsa kasan abubuwa sun zauna ana cikin lokaci. Iya tace ba dole ba Jafaru tunda ance ka gudu ba a san inda kashiga ba anyi kiran wayanka baya shiga kowa ya kira baya samun ka ka dauki dukiyan mutane ka salwantar ka kama gabanka ka bace wa mutane. Iya wani dukiya na salwantar tace to danga dukiyan magada dake hannunka mana masushi suna bukatan abinsu yanzu tunda ance sune kake,,,,,,, Haba iya wacce ya gudu da dukiya nai cikin mu waga dabi,a batayi ba iya mi da zaki hwada mai haka don Allah ? Anty barka dake fitowa daga dakice ta tare iya dake fadin zancen da dan fada fada iya tace yanzu kuma zakuce baku fadi hakan bane a gabansa ? Nan fa kuke keda yar nan saratu kuna fadin magana tundai saratun nan bakinta baya fadan alheri game da kowa saidai sheri. Anty Baraka ashe kinzone ya fada yana kallon anty baraka din da ta bata rai don abinda iya ta fada a gabanshi yaiwa kowansu zafi. Nazo tun karshen satin can jafaru an dawo lafiya ya hanya wai tace ance ka gudu to wayace banda abin iya da shirme baki san me ake fada ba kije gulma ? Murmushi yayi yana fadin da hankalinta ba shirme bane iya bata son wani ya sokeni kila inke baki fada ba taji wani ya fadi hakan ta rike a ranta. Inke baki fada ba ai uwarku sun fada ko zaki toge yanzu don kun gasa ya dawo a yadda baku zata ba ,,,,,,,, Iya koma me aka fada aishi yaja a fada mai hakan don babu yadda za ayi dukiyan mutane yana hannunka ka zauna baka kara maishi sai kanka kana ta faman auren daba riba don me ba za ayi magana ba ? Mama dake fitowa daki take fadin hakan ta murde fuska ga dan nata a karo na farko haka ya tabbatar mashi cewa kome akace mama din ta fada akanshi lokacin zata iya fada. Mama na gudu kuma ban kara kowa ba kamar yaya nabar kowa ban kula dashi ba mama wallahi banjin cewa a duk garin nan kaf akwai wanda ya fini kula da yan uwana da iyayyena ko banzo na daya ba ba zan wuce na biyu zuwa ukku ba in sha Allahu. Aure kuma da nayi ra,ayinane mama bana wani ba ban dauki kudin kowa na auro Rahama ko saiba ko Asmau ba ni na nemi kudina na auro matana dashi mama. Haka kuma lalurar da nake masu da kowa da abinda Allah ya hore min nakewa kowa tasa laluran dashi bada dukiyan wani ba. Fada masu dai Jafaru don kona fada ba yarda da hakan zasuyi ba tunda shedan ya rufe masu idanu akan dukiya suna son su tozartaka a yanzu don kawai abinda bai shafesu ba kanka. Haba dai Iya zancen nan dai nace na ari bakin kowa nace nina fadi hakan ko to abarshi mana a haka idan zaiga laifin wani yaga nawa ni kadai ? A lokacin hankalinsa yana ga waya da yake neman lamba a ciki ya danna kira aka dauka yake fadin kai Nura fadawa Salis kuzo min da sakon nan ganinan gida part din iya zaune. Meshi ya tsaya fadin kadawone ashe yace na dawo tun jiya ya kashe wayan yana dagowa yace mama ita anty baraka tace ban kulata ko habu ko yazid ko yaran nan su saratu ? Ya akeso mama anty baraka gaki dai har account naje nasaki gaba don in zan maki sako ina shan wahala naje garinku na dukeki muka bude maki account da nake tura maki kudi duk wata. Koda banda lafiyan nan ina kwance haka nake tura maki kudi ko yaushe daidai abinda Allah ya hore min shi kuma yazid dake sudan a kirashi a tambayeshi nawa nake tura mai ko wani wata. Balle yanzu da yake shirin dawowa gida din nan gaba daya yaran nan kuma a cikin su waye ban tare masa lalurashi mama ? Har wajensu kawu su fada idan akwai wano wanda ban dauke wa wani matsalan gabanshi ba don Allah shi habu wanan tsakanina dashine ba sai na fada ba nayiwa banza balle habu nawa ? Kai Jafaru anji kayi hakan wanan ai ina zumunci kayiwa ko yanzu zancen hakinsu akeyi ka,,,,,,,, Sallaman su Nura da suka zo da jakkar bako niki niki suke shigowane ya katse mata zancen data soma tana binsu da kallo suka shiga gaidasu suka zauna yace ku girka a gaban kowa a gani nawane a ciki. Habu ya shigo fuska daure yace Habu ka zauna a kirga kudin nan bari na leka su Asmau indawo acigaba in dauko wasu takardu a can ya mike ya fita a cikon kamshin turarebshi daya gauraye part din dashi. Jin fitan shi daya bayan daya suke fitowa daga dakin kowa ya samu waje ya zauna su Nura din suka shiga kirgan kudin hannunsu din tare da Habu dake lissafa masu suna hadawa a waje daya. Part din nasa shiru kamar ba kowa a cikinsa har ya shiga dakinsa ya dauko wani file ya fito dakin Asmau ya shiga tana kwance kasa saman tieles tana barci ya dan bugeta ta farka ta bude ido tana fadin ka dawo ashe ? Yace eeh ya gida lafiya kalau ta fada tana mikewa zaune yace ina zuwa yasa kai ya fita zuwa na Saiba daya sama kwance tana waya. Ta jiyo ta kalleshi taci gaba da wayanta ya dan tsaya cike da takaici ya kuma juya zuwa waje ba tare da yayi mata maganan komai ba a lokacin. Yasan idan yace zai tsaya mata magana a yadda yaga tayi din nan ransane zaifi haka baci haka yasa kai ya fice ya gama da wanan issue din dake gabanshi kafin ya dawo nata a yanzu. Kodaya koma an gama lissafa kudin kawu yana zaune sai faman gyaran zama da yakeyi yana harde kafa a waje daya ya shigo yana fadin ya kun kammala ko ? Habune ya bashi amsa da fadin an kammala J miliyan ashirin da takwasne da dubu dari biyar da hamsin da tara gasu. Yace good Nura wanan milliyan bakwai kenan dana baka ko yace ehh maigida Nura jirashi a waje salis kai ina wanda na baka milliyan biyar ka juya din ya nuna mai yace gasu yanzu sun kai miliyan ashirin da daya da da dubu dari biyu ga yadda muka lissafa su. Good Nura ina son ku zamo cikin sheduna tun a nan duniya don don Allah tunda na baku kudin nan a juya na taba karban kwandala a hannun ku ? Haba maigida wallahi banda lissafi da in kazo mukeyi dakai na riban da aka samu a shekara ka debewa shago da namu hakkin ka bamu nikan kam kwandala baka taba karba a hannuna ba. Shima salis ya fadi to na gode idan na fito zan nemeku a san yadda za a dawo da harkan ba tare da an samu tangarda ba in sha Allah. Suna fita ya bude file din hannunsa yana fadin mama ga kudin nan milliyan gomane akan ba a lokacin ni kuma na fara juyasu shine kikaji ribansu ya hau din nan sai na samu wani business naga gara kawai in bar masu shi su dinga juyawa su na kama tawa business din. Wani ajiyan zuvciya ta sauke ta dago kai tana kallon kawu daya kurawa kudin ido tace yaya kaji bayaninsa ga kudin nan yanzu meye abin yi ? ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 4️⃣4️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Wayansa yai kara alaman kira ya daga yana fadin ina gari ai jiya na dawo gani fitowa yanzu insha Allah ya gama wayan ya kallo Habu yana fadin musa ne ya kira zan fita yanzu muna son muje mu gana da mai,martaba dashi kan wani zance. Lokacin kawu da ya kasa motsi ya dago yana fadin ai baka tafi ba ba a san yadda za ayi da kudin nan ba yanzu Jafaru ? Yace a,a kawu ayi yadda ya dace a kasa kudi dai anga yadda suka kama ga takardan nan Habu sauran bayani suna ciki kaima kuma nayima bayani a baya. Akwai gina dana dora dakai da Yazid wanan nayi niya ba zan fasa ba in sha Allah don ma wanan gidan da zan maida matana a can da ake gyara da yanzu na kammala maku ginan ai amma na dakatar ina wanan gyaran a yanzu. Duk dai wani bayani leter on zakaji idan mun zauna yanzu barin je in samu musa mu karasa dashi don tafiyan nada muhinmanci sosai a wajena. Har ya daga ya juyo yana fadin anty baraka yau ne zaki tafi idan an raba ko kina nan tukunna ? Kafin tayi magana iya ta karbe da fadin yoo me zata zauna yi an raba an bata kasonta tunda dama donshi tazo mijinta nacan yana jira ta kawo mai kasonta shi da yayanta ai gara dai ta tafi tun yau din zai fi ai ? A gaskiya mama zamu samu matsala fa da Iya ni kadai iya ta gani da zata tsargeni kan zancen nan in ma tsarguwane ai saratu ya kamata ki tsarga iya bani ba ita data daga waya ta kirani inzo ga halin da ake ciki. Amma in aka tashi magana iya tace waini haba iya kada ki hadani da dan uwana mana don Allah ? Iya tace ai ke kikazo da zafi kina sakina sakin magana akan dan uwan naki yanzu aikin fada da bakinki cewa ga haddasanar data jawoki ta fada maki karya da gaskiya kuka hau ke da iyayyen ki da suka biyewa haukan ku. Har cewa kikayi a nan jafar baya taimaka maki da komai a rayuwa sai kin rokeshi amma baki fadi alherin dan uwanki zuwa gareki ba sai yanzu daya fada a gaban mu. Nina sani kuma na fada ko a bayanshi jafar namijine namijin dutse da ba a gane gabanshi sai dai bayanshi . Yaron nan kamar yadda ya fada yana iya kokarinsa wajen ganin ya daga gidan nan ya kare martaban kowa amma kuka fahinceshi a mumunan zato irin haka ? Yanzun dai aiga kudin nan ya aje maku agaban ku sai ku rike kuda kuka fishi iya rikon ya dai fita bakinku yanzu kan ya cinye kudi ya handame komai shi kadai yana aure aure yanzu sai ku samu sabon camfi ku zarga mashi kuma tunda kun zama yan sheri. Kai dauda ga kudin nan sai ka dauka tunda hakkinkane yadda naga ka damu akan zancen nan bai kamata yadda kake da yaron nan ace ka goyi bayan haka gareshi ba ai. Nifa iya ba goyon baya nayi ai masa wani abu ba illa goyon bayane tunda masu abu suna bukatan abinsu ai masu abin kafisu bukanshi nake gani iya ta fada. Habu ya mike da niyar fita lokacin mama da jikinta yai sanyi ta kasa magana tace kai kuma ina zaka ana batun kasa kudi shi ya fita yace yana da uzuri kai kuma zaka fita yanzu ? Mama ai dole sai an kira malamai a cikin harkan nan bamu zamuyi bugun gaban mu ba wani yazo daga baya yace an cuceshi kuma. Zanje tudun wada in dauko su malam idi suzo a yi yadda shari a yace bayan sunji abinda kowa ya mallaka da farko aka hada akai wanan abin. Wani malam idi zaka kira anan ko iyamu bamu isa mu fasala kudin nan ba ba tare da mun kira wani bare ya shigo ba kawu ya fada. A,a kawu Allah yace Annabi kuma ya fada ya umurce mu dayin adalci a cikin lamarin mu don haka kudin nan ba wanda zai tabashi sai masana sunzo su kasa subawa kowa nasa a hannunsa kamar yadda yake a shari,a. Kuka mama tasaka ta mike zuwa daki wayan habu dake ta haske a hannunsa ya kasa dauka saboda maganan da yakeyi a lokacin. Anty Baraka ke fadin wayan ka habu tun dazun ake kiranka fa ya kai hannu ya dauka yana fadin yazid ne ashe ? Ya daga wayan yana sallama yace yazid ya akayi suka tsaya gaisawa sai ya saka wayan a hands free kowa naji yazid din yace zancen kudi idan an raba a mayarwa J da nawa kason yacigaba da juya min sai nadawo. Nima yaya na fadama abawa yaya J ko kai nawa salima ta fada daga gefe kawu ya dago kai ya kalleta tace kada abawa kowa nawa abarshi a hannun ku don Allah. Kai wanan abin dame yayi kama yau ace yanda yaran nan suka taso maku a cikon biyayya wai kune kuma masu raba kan yayan nan yanzu ? Ban taba zato ko tsamanin haka ba gareku dubu yau ace kune kuka fitowa yaran nan da wanan lamarin don mutum daya ko biyu zuwa ukku sun zugaki suna son ganin farincikin ahalinki ya ruguje. Yau badon yaran nan wasu nada hankali a cikin su ba kin hada fitinan da koke baki iya rabashi dubu saukin abindai ba a taru duka an zama daya ba. Bayan fitan su da salima na kwashe kayan abincin daga dinning zuwa kitchen na tsaya ina wankewa nan anty Nafisa ta sameni a kitchen din. Muka gaisa take tambayana yayama ya fitane nace tare suka fita da anty dazun nan muka tsaya muka dora abincin rana wanda muka hada sakwara dakan hannu tunda ba wani yawa garemu ba leda hudune har maigadi itace ta daka nayi miya muka gama nashirya komai kafin mu shiga daki yin azahar. Daga nan na dan kwanta don in huta sai wajajen karfe hudu saura ya dawo gidan shima a gajiye ya shigo don tun fitansa bai samu ya huta ba yana ganawan da yace zaiyi din ya fito mutane kuma suka taru akansa. Tunda sunga har yayi matsayin da zai gana haka da mai,martaba to lalai yaron akwai kudi ko ilimi a wajensa ke nan dole dai yana da madafa. Irin kudin daya basu yasa suka gaskanta hakan da suke zargi ana tambayan dangidan waye ana fadi suka gane mahaifinsa kowa waye shi agarin. Ina kwance anry Nafisa ta shigo dakin tana fadin Ramaah ina son inje gida in dan leka su inna kada ace nazo nan na zauna kuma . Haba dai anty amma zaki dawo ai na fada da sauri tace bako yau ba sai idan yaya baya gari kada inyi rashin hankali mana Ramaah in yaya ya girmeni aike baki girmeni ba ? Hankali kuma hanjine ai mai yasa kikaga ya raboki da gidan yawa ya kawoki nan ke kadai aidon ku huta dukkan ku yayi hakan na noke fuska ina murmushi. Tace to kingani in sha Allahu idan bai gari nayi maki alkawarin zuwa har in kwana amma yanzu kan nima ina son dan uwana ya samu natsuwa a rayuwanshi ya gane yayi auren zamani shima irin na sauran maza. Na mike tsaye na sake fadin da kijira yaya din ya dawo sai ya kaiki mana tace ai banson ya dawo ya sameni dinne yasa zan wuce yanzu. Don Allah Rahama kiba marada kunya ga wanan aure ido aka saka aga matsala koda kadanne kema daga wajen ki ace mashi gwai don haka ki daure ki koyi son shi a zuciyarki. Har duk wani abinda kika iya ta bajinta ki gwadawa yayashi Rahama ki kawar da kunya dajin nauyi a yanzu shi mijinkine ba wa ba don haka saikin zage kin dai san bakin ramin kura kike. Haka kuma ki kara hankali da mu yan uwansa kindai san komai za azo a dinga bukin cikinki kamar da gaske sonki akeyi sai idan anji sirinki a koma bayan ki ana zunden ki. Duk abinda ya shige maki kai ki kirani in sha Allahu har idan na sani da yardan Allah zan haska maki shi a yanzu zan nisanceki kada a zargemu amma akwai waya na nan komai ke nan zamu dinga waya dake in sha Allah Na dago kai cikin yanayin damuwa ina fadin nagode anty Nafisa a gaida ummu amma ina zuwa don Allah na fada zuwa dayan dakin dake rufe turmin zani na dauko mata da wani dogon riga sai su sabulai da turare na dibo kayan buki mai yawa na kawo mata ina mata godiya. Har bakin kofan falon na rakata tace na tsaya nan ta tafi na sauke ajiyan zuciya na juya zuwa ciki ko ina na gidan nabi da kallo wai yau ni Rahama nice ubangiji yaiwa wanan baiwan a lokaci guda haka. Alkawari na dauka zan zauna da yaya tsakani da Allah in masa biyayya kamar yadda shari,a ya kidanyawa mace tayiwa aure biyayya kamshi na fesa a falon har zuwa dakinshi dana shiga ns gyara mai hakan yana daga cikin abinda ke hadashi fada da matansa nasani yasha korafi kuma a gabana cewa ko muhalinsa babu mai iya gyarawa a cikinsu sai inya gyara da kanshi. Na koma daki ke nan na tayar da sallah naji dawowanshi bai shigo ba sai daidai na idar ya shigo har dakin nawa da sallamanshi na na shafa addu,an na juyo ina amsawa tare da furta sannu da dawowa a gareshi. Yauwa amarya ta yaya kike ya amarci kuma ya fada yana karasowa inda nake zaune saman sallayata ya rage tsawonshi zuwa tsugunni yana fadin ya gidan Rahama hope ba matsalan komai dai ? A,a bakomai na fada ina kokarin dagawa ya mike yana miko min nasa hannun alaman in kama in mike ai zan iya na fada . Baki son na taimaka maki ke nan ya fada a,a kada dai in wahalal dakaine kawai banso amma da karfina ai zanyi iya mikewa. Wayau ko ya fada to ban yarda ba ya fada banyi aune ba sai naji ya sukuceni baki daya zuwa bakin gado dani ya aje zakice ba yaya Jafar bane a lokacin. Hijjab din wuyana daya kula ya tauyeni kamar ya shake min wuya don yaga inata kokarin sasautawa da hannuna hakan yasa ya dan kara rankwafowa saitin fuskana yana kokarin cire min daga jikina. Ina jin yadda ya sauke ajiyan zuciya lokacin da yayi arba da suran jikina daya dan baiya afili daga yanayin dinkin rigan jikina. Dagawa yayi daga rankwafin da yake naga yana shafo suman kanshi da hannunsu wani irin soyayyata yana fisganshi lokaci guda duk ya dan daburce yana fadin kinci abinci dai ko ? Bana jin yunwa na bashi amsa a takaice ina mikewa daga yadda ya barni a kwance don irin kallon da naga yana kare min sai lumshe ido yakeyi a cikin wani yanayi na gajiya. Da alama baki son cin abinci Rahama kosai na zauna kwana biyu ina baki da kaina zakicine ina kula ko dazun bakici komai ba koso kike antyn Abuja tace ina maki sakacin kiyon ki ? Ni ba sai ka zauna ba dama haka nake ba ko yaushe nake cin abinci ba sosai nafi son abu mai ruwa ruwa dashi na saba rayuwata da nake zuwa kiyo a rugga. Hannu yakai ya ja min hanci yana fadin bazan taba yarda da hakan bani donki na aje komai a gidan nan Rahama. Kici sai kince min kin gaji da nau,insu na cabza maki wasu don kanki saina turo baki cikon shagwaba ina dan kauda kaina gefe daya. Yayi murmushi yana fadin watarana basai nace kici ba Rahama kece dai zaki dameni da inci din ranan da kika haifa min kyawawan yaya masu kama dake ba zakiso ko kudi ya sauka a kaina ba lokacin. Saidai zanso ki haifa min ya mace mai kama dake sak mai irin tsayinki da hancin nan naki da gashin nan yakai hannu yana kokarin taba gashin kan nawa nayi saurin gwaucewa ina murmushi. Falo muka fito tare zuwa dining ya zauna na fara bude abincin ina kallon sanda ya lumshe idanunsa naci gaba da hada mai na aje komai na zagayo na duka a gabanshi yabini da kallo. Takalman dake kafanshi mai belt don na kula yana son saka irinsu shi din dan gayune na karshe idan yai shiga saikin tsaya kina satar kallonsa wani lokaci. Komai nasa a nutse yakeshi nasan kuma shida kansa ke tsayawa yiwa kansa lalura wani lokacin koda wanda ya kamata ace mace tayi masane ya rigada ya saba da hakan. Kafafuwan nasa ya kara miko min na karsa zare dayan ina kokarin mikewa naji ya dafa kaina yana fadin sharp kinga na manta da takalma a kafana na zauna. Allah ubangiji yayi maki albarka Rahama sunan ki yayi daidai da halinki na kirki da sanin ya kamata daidai da addini yadda ake son mace ta kasance harta bawa yara tarbiya ke nan. Nidai dai murmushin iya baki na sauke na juya da takalman zuwa dakinshi naji yana fadin wai ina Nafisane ? Ta tafi gida dazun nan ta wuce wai zataje ta duba su inna sai yayi dan murmushi ya kada hannu a ruwan dake gefenshi yana dauraye hannunsa . Na juya nakai takakman dakin na dauko mai wasu sifas masu kamar gashi a jikinsu wanan duk hikiman anty Salmace saida ta jaddada min kan wanan akidar na kula da bashi takalman tafiya a cikin gida ta kuma nuna minsu din hakan yasa na fara amfani da nasihar nata a lokacin. Na zo na aje masa a gefe inda inya daga zai saka na zauna a kujeran dake gefenshi abincin naga ya debo ya nufo bakina dashi na noke kaina ina fadin zanci ai idan ka gama. Bai tsaya saurarena ba ya mika min dole na bude baki na karba a haka mukaci abincin waya ya mikar dashi daga wajen wanda na fahinci daga matansace dake mashi cin mutunci a cikin wayan a kaina. Kayan na shiga tattarawa na nufi kitchen dasu ban fito ba saidana dauraye na kife na dawo nagoge dining din na nufi dakina don ya shiga dakinshi tun lokacin. Kayan jikina na sauya na kara muke jikina da dan kamshi mai saukin shaka na dauko riga cotton bubu mai gyale na daura a kaina lokacin wayata tadauki kara ina dubawa anty Salmace a layin. Na dauka da sauri muka fara gaisawa ina tambayanta yara da gajiyan hanya take fadin suna lafiya suna wajen lesson . Kafin naji ta dora da fadin to yaya ashe ango ya dawo sai ta kwashe da dariya nima a bangarena murmushi nayi kawai a lokacin. Take fadin komai daidai ko murmushi mai sauti na sake kawai tace ato na dai fada maki yanzune zaki koyi narkar mashi da zuciyanshi akanki kada ki tsaya wanan sanya da kauyanci. Kiyi kokari ki kafa taki gwaunatin a zuciyarsa ta yarda zai mata da irin ukuban daya saba dashi wajen wa yan can garorin matan nasa. Duk abinda kika sai zai farauta masa Rahama ki daure kiyishi don Allah kicire duk wani kunya da nauyi ki nuna masa kulawa fiye da zatonsa tunda abinda yajashi gareki kenan dama samun natsuwa a wajenki din. Muryanshine ya katse muna hiran da yashigo yana fadin kin kwantane Rahama ina son na leka gidancan in dubusu ban samu tsayawa dazun ba dana shiga abubuwa sunyi min yawa a lokacin. Saika dawo yaya agaidasu dasu dasu hajjaju da iya ya amsa da zasuji har yakai kofa ya juyo yana fadin kada kice zaki sake wani girki ki huta hakana sai gobe don Allah zan riko muna abinda zamuci da daren. Saida yakai kofa nake fadin da anty Nafisa zaka dawo ko ? Sai naji yace kina son ta dawone shiru nayi na kasa cewa ehh don irin kallon da yake jifana dashi lokacin ya juya yana fadin banjin hakan su dan huta a gida kwana biyu. Yana fita muka cigaba da hiran mu da anty salma din dake min sherin a,a komai zam kan ga alama nan naji da kunnuwana . Kin gane yanzu fa abin kamar compertion ne a tsakanin ku kowa ya biya allonsa ya wanke suma zasuyi kokarin ganin kin zama banzace a wurinsa don haka shiga gidan mata biyu akwai hatsari babba ga mace sai ka iya takonka sosai dasu. Mun dai dauki lokaci zancen ke nan guda akan zamantakewan aure ta yadda zan zauna da kowa kafin mu dauko hiran su hjy yabi muna dariya wanan ya shagal dani na manta da komai saida aka kira sallah na mike zuwa alwala. A gidan su kuma yana isa yaran ya sama a kofan ya Habu suna wasa da Abba ya fito mota ya nufi wajensu. Zaune yayi ya dorasu saman jikinshi yana dan jansu da hira irinta yara jin shiru yasa maria bude falon don taga ko Abba yana kusa. Sai tayi arba da ya J din ta dan daburce don tunda abin ya faru basu hadu ba sai wanan karon suka hadu dashi din. Shine ya fara gaida ita wanan karon taji abin wani banbarakwai tana fadin sannu da dawowa yaya ya hanya lafiya yaya gida dasu Abba koda yake gashi nan yana fada min wai yana son karatu . Tayi murmushi ta juya zuwa ciki ta barsu a wajen yake fadin gashi ai zamu shiga ciki take fadin dama wanka zan mashi nake nemanshi. Ya iza yaron zuwa gareta ya rike hannun yaransa zuwa part dinsa inda ya samu matan basa a zaune falo duk da suna a waje daya kowa da abinda takeyi a lokacin. Sallamanshi ma da yayi sai Asmauce ta amsa mashi da kyar itama dai a cikin basarwa tayishi bai kula da hakan ba ya zauna a tsakiyansu Yana fadin ya Asmau ya karfin jiki kuma sai saiba taja tsuki ta mike kafin ma asmaun tayi magana tabar falon a cikin hasala binta yayi da kallo ya dawo da dubasa ga Asmau sake fadin lafiya gamu dai muna ja ai. Ai watan haihuwan ki ke nan zai kama ko tace haka akace saidai idan Allah ya raba kawai yanzu Allah ya rabamu lafiya ta amsa da amin. Badai wani matsala ko tace da sauki gaskiya kinje asibitin da kikace tace naje naga likitan shima yake fada min edd dina ok ya fada. Yarshi data hau saman cinyarsa tashishi ya biye mata suna hira kafin ya mike ya shiga wajen saiban dake kwance ta kafawa siling din dakin ido tana tunane. Nusaiba ya wai meye matsalankine haka ta dago daga yadda take ta watso mashi harara tana fadin matsala matsalan me kagani a wajena ? Naga kin gani kina basarwa mana kamar baki ganni ba tace oh so kake in daukeka in goyaka tunda ka tuna damu kazo garemu yanzu ? Yayi murmushi yana zama a bakin gadon daidai kafafunta ta wani jaye kafanta da sauri gefe daya ya sake fadin wai meye hakane wai ? Cikin kyarmar murya ta soma magana tana fadin me kuwa ko kagawani abune a wajena kaje wajen wace kake tunanen ta fimu wani abin daka zabi tozarta mu a idon mutane . Tozarci kuma ya fada tace koma meye dai kaika sani da abin kunyanka tunda baka daukeshi komai ba ya mike yana fadin Allah sarki auren da nayine abin kunya kuma yau Nusaiba ? Ashe aure yana zama abin kunya a wajen ki don na auri wace kika sani na hadaku a waje daya a matsayin matana ? Wanan kuma kaiya shafa don ni wanan figagan yarinyar karamar yar iskan da kake kallo a mata bata isheni ko kallo ba balle . Allah ko niko kinga ko gajiya baniyi da kallonta da tayi min dari bisa dari ko kifta ido idan tana kusa ban iya yi yanzu . A hakan kai har kaga mata ke nan ita dai Ramaah din dana sani ko ancanza mata kamane kuma ? Ya gyada kai yana fadin itafa yanzu ai in ba itaba banganin kowa a mace yarinyat data san zafinka tasan ciwon ka ako wani hali ka shiga ina zanga daidai da ita. Don haka inma kushe min mata kike kokarin yi gara ki daina don ita din tauraruwanace a yanzu tunda ba zata taba guduna ba duk halin da nake ciki kuwa yasa kai ya fita ya barta tana ta zunduma ashar. Ya jima a falon kafin ya shiga wajen iya daga can ya wuce masallaci bayan an fito sallah ya dan sayo kayan sanyi da nama ya shigo masu dashi ya aje a falon yayi masu saida safe baijin akwai wace ta iya amsawa a lokacin. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 4️⃣5️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Mummy zulaihat Allah ubangiji ya baki lafiya yasa hakan ya zamo kaffarane a gareki ubangiji Allah yasa anyi aiki cikin nasaran ubangiji Allahuma Amin ya Allah. Mama Amina kema Allah ubangiji ya baki lafiya yasa kafarane yasa hannu ya warke a cikin kuduran ubangiji Allahuma amin sauran uwayena da bab kira ba da yayyun mu ya Allah ka basu lafiya masu damuwa Allah ka yaye masu kamai dashi alheti a garesu Allahuma amin jumma,at mubarak gareku yan uwa musulman duniya. Fada yake sosai gaban matarshi hafsatu tana kara zugashi akan Habu wanan karon fushinsa ya sauka don Habu din yake zagi saboda yana ganin shine ya kawo mashi cikas a ranan. Idan badon shawaran da habu ya kawo ba da duk yadda akayi a ranan saiya mallaki wani abu daga cikin kudin nan ranan. Amma ga kudi yana gani ido da ido amma dan banzan yaron nan Habu yai masa bakin cikin su shigo hannunsa saboda wata akidarsa ta banza dayace wai sai ankira wasu malamai can . To kai malam waisu yaran nan dake gagawan fadin yadda za ayi da tasu kason a sakebawa yayan nasu me suke nufi da hakan yanzu matarsa hafsatu ke tambayashi cikin katse mashi tunanen da yakeyi. Sai daya nisa ya kallota ta sake fadin yanzu kyalesu zakuyi da shawaran ya asake karban kudin kuma a hannunsa ? Kafa san idan suna hannunsa ba zai yarda agani ba balle a taba yakamata kayi wani abu akai hakana malam koda baka da gadon mai fata ai kaima dai ka wahala dashi gashi Yaron nan Jafaru fa malam kana sane ko kashi ya rika ya shiga kasuwa dashi sai sun zama kudi a wajensa na rasa wani irin albarka Allah yaiwa yaron nan haka ? Dan banza gashi da iya boyon kurwa wai ace akwai wa yan nan kudin haka amma yake daukan dan kudi ya mika maka kaine baka iya kashin kudi ba ke nan ? Abin ne da daure kai kema kin sani hafsstu ba irin karba da bayin da sunan yaran nan amma kamar ina aika dutsene ba abinda suka canza saima gaba gaba suke karawa. Wai, kinji yaron nan ashe harda gidaje yake kokarin ginawa yan uwansa bai fadawa kowa ba sai yau din nan yake fada a wajen haduwar nan. Sai nake ganin yanzu kamar ya fara fahintar manufarmu akansu don ya fara yin abubuwa ba tare da sani ba da farko ba haka bane na samu kansu fiye da tsamanina. Amma sai gashi yanzu da nake hango kudi sun zauna mashi haka yana kokarin ya juya min baya a tafiyan yanzu. Harshi ya isa malam wallahi bai isa ba komawa zakayi a kara nemo makashi a hannunka sai yadda kayi dashi a rayuwansa . Shi wanan Habu dai tauraronshi bai haskawa kamar nasa nake gani don har yanzu bai kaiga samun irin na Jafar din ba amma duk da hakan tunda bakinsu gudane shima ba barinsa zakuyi ba ai malam. Dole ai insan abin yi a yanzu ya zama dole na sake sabon shiri akansu kafin komai ya jagule muna don ina ganin wancan na farkon ya dushe . Kwance ya sameni da waya a hannuna har barci ya soma daukata lokacin ya shigo cikin dakin da sallama tsaye yayi a waje daya yana kare min kallo kafin ya tako zuwa bakin ya karbi yawan yana dubawa gamen din engela yana ta playin da kansa. Dan murmushi yayi yana kashewa kafin yakai zaune a gefe daya yana aje ledan daya shigo dashi a hannunsa sai lokacin naji motsin zaman mutum a kusa dani na dan zabura kadan naganshi . Komawa nayi ina sauke numfashi tare da dago fararen idona na kalleshi ina furta sannu da dawowa a bakina . Sai naga ya lumshe ido yana amsawa yace har kinyi barci by this time sorry na tsaya da iyane ban fargaba ashe lokaci yaja haka ban sani ba. Allah sarki Iya suna lafiya a cikin hamma dake nuna kasala ya amsa da lafiya lau suna gaida ke nayi dan murmushin da nasan zan tsokaleshi na yunkura da niyar tashi zaune . A lokacin naga ya dadirce da kyat ya iya sassauta muryansa yake fadin ina jin yunwa fa Rahama ? Na juyo da sauri ina fadin kace kada nayi girkin dare kuma yace ehh muje falo ki ban abu yana can na aje hakan yasa na yunkura na mike zaune daga kwancen har jikin mu yana gugan juna dashi na samu na mike tsaye. Zanin dana daura saman rigar barcina na gyara dauri zan fita ya bini da kallo tare da ajiyan zuciya ya mike ya fito falon shima ledan na hango saman center table din falon na nufi wajen ledan har na duka zan bude kuma na dago zuwa kitchen na dauko plate da su knife da ruwan wanke hannu irin wanan sallon mazan nasanshi a gidan anty sallama ai. Na samu ya zauna ya baje saman kujera irin zaman a bude kafa din nan ya dafe goshinshi da hannu dayan shi yana murzawa. Na duka na fara kiciniyar budan ledan naga take away irin wanda kake iya hango abinda ke cikin roban da alama dai kamar ganyece da wasu tarkace haka. Saidana bude naga rabin kazace da ganye da aka gyara yaji hadin turawa sai dan shinkafa manne a gefe daya ko wani roba haka yake da abin. Dayan ledan na jawo dake ta maiko da kamshi kayan cikin ragone a cikinsa mai yawa sai kamshi yakeyi anyi mai irin gashin zamani din nan dayan kuma shima dai namance ta rago gassassa a cikinsa yaji su albasa da kabeji da kayan kamshi. Saidana gama hada komai yadda ya dace na dago kai na kalleshi ina fadin bissimillah yaya sai naga ashe duk hankalinsa yana kaina shima a lokacin. Sai naji yace ki zauna tare zamuci ai dake nasan bakici komai ba na noke kai cikin kunya ina fadin idan ka gama zanje daki inci ai. No no wai kunyata kike jine yana magana yasa hannusa daya ya jawoni zuwa jikinshi ya zaunar dani saman cinyarshi. Noke noke na farayi ina kokarin zullewa don hakan da yayi min din bakon abune tunda ban saba hurda da namiji ba haka ko yan uwanmu maza ba tare muke rayuwa ba a rugga yunda su suna yawon cinrani. Kokarin kaimin a bakina yake a dole saina karba na dai karbi na farko amma taunawa na kasa hadewa a gabanshi ga idon daya tsura min wanda yasa na fara kwarewa lokaci guda. Ruwa ya miko min na dan kurba bai duk da haka bai yadda ya sakeni ba a rikon da yayi min dole ba sarki sai Allah na biye mashi ina karba a kunyace ina hadiyewa a cikin kunya. Saida yaga na koshi ya barni na koma gefe ina kallonshi yadda yake cin abincin ya tabbatar min daba karamin yunwa yake ji ba lokacin. Ya gama na kwashe kayan zuwa kitchen na dauraye na fito har lokacin yana zaune yana waya a wajen dana barshi daki na nufa harya gama wayan nasa ashe barci ya daukeni. Har ya gama ya shigo dakin ban sani ba a cikin barci naji ana tabani hakan yasa na dan yi niyar dagawa sai naji ya matseni a jikinsa yana wasu maganganun da na kasa iya tantancesu a lokacin. Ga kasa daya dora a kafadana ya sakarmin nauyinsa ban gama mamakin hakan ba naji yana sumbatar wuyana hakan jikinane ya fara rawa lokaci guda. Abinda ya kara dumatani jin wasan yau bambanta dana dareb jiyan da yake min yafi na daren jiyan don ya bambanta da wasan da zan tsaya fada da baki a nan. Sai karfe shida da rabi ya samu sallah safe balleni da saida nayi da gaske na iya lalabawa zuwa bandaki na tsabtace jikina. Ga zuciyana da tayi min wani irin nauyi da ba zance ga daliliba don nasan wani abu daga rayuwata ya tafi ke nan sabon rayuwa yazo min a yanzu duba ga yadda bani samun natsuwan barci a dan tsakanin nan. Har na idar da sallah na samu na mike na gyara gadon na sauya shimfida da kyar na koma na kwanta don zazzabin da nake jin yana son kamani a lokacin. Hakan yasa ina gamawa na koma na kwanta da niyar gari ya dan kara wayewa in daure in fito kitchen ashe barci ya daukeni mai nauyi irin barcin wahala din nan bana dadi ba dai kam. Sau biyu yana shigowa dakin yana samu ina barci gashi ko karyawa banyi ba ga abin kari dsyasa yaya Habu yazo muna dashi tun safe. Har yazo suka dan zauna kan zancensu da mama ban samu ganawa dashi ba a lokacin yaso ya ganni mu gaisa koda yaya ya duba mashini har lokacin ina kwance jikina yai zafi kuma ban falkaba balle insha magani. Har yaya Habu din ya tafi shima ya mike zuwa dakinshi yayi wanka ya dawo nawa dakin still ina kwance a takure ina barcin . Ya tsaya ya kura min ido na dan lokaci kafin ya kai hannusa a saman jikina yana taba temperature dina yaji jikin ya gashe sosai a lokacin. A dimauce ya fara kiran sunana a hankali hakan yasa na bude idanuwana a cikon nauyin barci na sauke a kansa yana zaune gab dani ya dan rankwafo jikinsa zuwa nawa yake fadin. Rahama baki da lafiyane haka har sosai shine baki fada min ba muje asibiti ? Idona dake lumshe na kara dan budewa ina fadin idan nasha Panadol zan warke basai naje asibiti ba.. No tashi dai muje kiga doctor zaifi ga jikinki yayi zafi haka kice in barki a gida ? Bari nasha magani idan bai bari ba sai muje asibitin na fada ina kokarin mikewa cikin karfin hali. Ina zakijene wai na bashi amsa da magani zan dauko a jakkata ina jakar take ya tambaya yana kallona don duk maganan da mukeyi dashi tun shigowan shi idona a runtse yake na kasa hada ido dashi. Gaban mirro yaje inda na nuna ya dauko maganin da goran ruwa ya dawo yana mika min dakyat na dago kai zan karba a cikin kunya. Yake fadin toki bude ido mana ki karba ya zauna gab dani jikin mu yana gugan na juna dashi na sakeyin kasa da kaina. Murmushi naji yayi yana fadin Ok har yanzu kunyane to bari na sake fitar da kunyan taki donki daina jin nauyina gaba daya don naga kamar da sauran ki har yanzu. Da sauri na kalloshi wanan karon ina fadin wallahi ba haka bane kawai ba zan iya bane nayi kokarin komawa saman gado don yanayin jikina. Yayi murmushi yana dafa goshina ya bare maganin ya bani nasha ya mike yana fadin ina zuwa falo ya fita ya hado min tea mai kauri ya kawo min saida ya tsureni nasha ya fita da kofin na koma na kwanta. Barci na koma ban falkaba sai wajajen sha biyu da rabi har lokacin yana gida ranan bai fita ba shima barci yayi ya rufe gidan don duk wanda yazo ya koma ya umurci maigadin daya rufe gidan kada ya budewa kowa. Jin motsin falkawana na shiga bandaki yasashi bude idonshi daga kwancen da yake yana barci a gefena kafin na fito na samu ya kunna wayanshi daya kashe. Don tunda zai kwanta ya kashe wayan don kada a dameshi barin maganan da yakeyi da wanda yake wayan yayi ya dago yana fadin to ya jikin naji zazzabin naki ya sauka tun dazun ? Da sauki na bashi amsa ina zama bakin mirro na don shafa mai saboda na tsaya nayi wanka a bayin kafin in fito. Ya mike zaune da wayan saidaya gama ya tako zuwa inda nake ya karbi man ya fara shafa min a hankali na lumshe idona a cikin kunyarsa. Saida yazo daidai kirjina sallpn da yake murza min man yasa na bude idona na kalleshi ta cikin mirro ido ya kashe min ta cikin mirro yana fadin in daina aikinane fa ? Dariya ya bani da yasa na danyi murmushi a fili nace nagode yayi hakana ai shafa man ya isa malam. Aikinane wanan don haka babu godiya abarni nayi da kyau nayi kasa da kaina kawai saida ya gama don kanshi yakai min kiss a goshi yana fadin bari na dan watsa ruwa nima tunda naga kinji sauki ya fita daga dakin zuwa nasa. Saiba dake zaune tana cika tana batsewa don haka ta kwanta takuma tashi a hakan ga kuma wani bakin cikin daya kara izo mata . Don tun safe bai shigo gidan ba har wanan lokacin haka yasa ta mike zuwa falo a cikon fushi ta samu Asmau da yaran suna cin indomie a plate daya. Ta zauna tana jan tsuki Asmau ta dago kai tana fadin kin tashi ke nan ta wani kallota tana fadin aiba barci nakeyi ba dama. Wai kinga dan iskan mutumin nan har yanzu bai leko gidan nan ba tunda ya aje dabbobi a gida yoko dabbobi ma muke ai ya bamu kulawa gari ya waye haka har daya da wani abu ? Asmau tace wa,kenan fa ? Ta yo mata kallo mai kama da harara tana fadin J mana don ranan bai samu sweet J din ba a bakinta sai J data kirashi dashi cikin hasala. Keko dai amaryace fa dashi Nusaiba yana can yana soyayyewa tukun ai dolesa dai ya lekomu dama don ya huta ya ki kawota nan cikin mu ya kebeta daban ai. Wata amarya har ina amaryan take abu haka kamar kara shi yaga mutum har yaje zubar da mutuncinsa akan wanan yarinyar. Ni wallahi ba zan dauki hakan ba shima ya sani akan wanan yarinyar ya dinga nuna mu bakomai bane itace mutum mu tashi tun safe yaki ko bugo waya ya tambayi lafiyan mu dana yaran nan ? Ruwa Asmau ta dauka tana bawa yar wajen Nusaiban ba tare data kula da abinda saiba ke fadi ba sai abincinsu sukeci da yaran. Taja tsuki ta rarumi wayarta dake gefe tana fadin wai don iskanci harda kashe wayoyinsa tun safe nake gwada kiransa ana cewa wayan yana kashe. To aina fada maki baki yardaba ke nan da zancena amarcifa yake sha ai dole ya kashe wayansa bakiji ance amarya kona kara bace amaryace balle wanan yar filoce fa. Koba hura sai asha nono don dara dara surbajo ce yana can ana gigitashi da abin na amare. Kiran ya shiga yayinda take watsawa asmau wani harara da take dauka sakarai bata san ciwon kanta ba ita kan taji ya dauki wayan ba bata lokaci tace dashi. Malam dabbobin daka aje a gida ba kulawa suna bukatan ka anan kan wanan sakaran yarinyar har zaka nemi ka wullakantamu kaki shigowa tun safe wajen mu ? Ohh Saiba Allah ko gari ya waye ashe shaf na shagala an rudani bansan har gari ya waye hakaba ai wallahi ashe kuna son ganina ? Na dauka baku da bukatana ai yasa na shagala a inda akasan muhinmancina namji mutumin dake gudun ka yake kyamarka kada ka shafa mai ciwo ya naka a yanzu ya samu wanda bai kyamarshi me kike gani ke nan zaiyi a yanzu ? Yar iska sallon yaudaran datazo ma dashi ke nan dama yasa akai munafuci aka koramu gida don a samu shige maka wallahi mu zubo dani da itace a gidan nan. Zakizo nan ke nan inda muke Ok fine sai kinzo din ai gara kizo kiga inda aka san zafina da darajana zaifi ta kashe wayan a cikin takaici da kunnan rai. Kinji ko meyana fada maki a yanzu yana cikin gigin amarci komai yana iya fadawa mutum idan yai magana dama kyaleshi kikayi . Tunda duk tsiyarsa dai baikai dare bai lekomu ba nan don haka meye zai damu mutum akansu yanzu. Taja tsuki ta mike tsaya zuwa dakinta har ta zauna kuma ta fito saigani Asmau tayi ta fita ta girgiza kai tana murmushi tana fadi a fili wahalala kawai ba dadi ashe ? Tasan dai ba fita zatayi ba a yadda ta fita don ko mayafi bata dauka ba don haka kila cikin gida zata tace ai cin tuwon kishiya rankone. Nusaiba kuma part din iya ta shiga ta samesu zaune dasu anty baraka suna hira iya ina mama take keya baraka ta bata amsa taja ta tsaya saiga habu ya shigo yana fadin. Ina mama karfe hudu mutanen nan zasu shigo a zauna na kira J yace dani zai shigo kafin lokacin yau hutu yakeyi yasa bai shigo ba. Ai dole ya huta yau angone fa balle jafaru da bai samun hutu kullum a uzurce yake da tsabga baida lokacin kansa balle na wani. Yanzu ko dole yabawa amarya hakkinta ai ya zauna tare da ita na dan lokaci su huta tare itama akwai gajiyan buki a tare da ita iya ke fadan hakan cikin rashin damuwa da saiba na wajen lokacin. Balle yau Rahaman bata jin dadi tun safe ya kirani na kawo masu abin kari daga nan nakai masu har na fito bata san nashiga ba tana kwance. Kai masha Allah kace abu yayi kyau haka yar albarka kenan haka muke son ji ko yaushe Allah ya shirya muna yayan mu a tafarkin addinin musulunci ga baki daya abu yayi kyau wallahi sosai. Ba a kawo amarya washe gari ka ganta kwashi kwashi da idanu ba kunya ba tsoron Allah tana rawan kai da guloto sakarai bata san mutane na mata kallon banza bane sun dauka hakan wayewane yanzu banda sakarci. Dariya habu yayi ya juya zai fita mama ta fito tana fadin Habu naji muryanka ina bandaki ya juyo yana fadin ehh mama dama zancen malaman nan da zasuzone nazo fada maku da karfe hudu sukace zasuzo yau. Don tsabga garesu saida J ya kirasu dazun da naje wajensa shine sukace zasu shigo da karfe hudu din in sha Allah. Yanzu fa nake tunanesa na dauka yayi tafiyane ai banga ya shigo gidan nan ba yau yana nan mama yana hutawane kawai zai shigo anjima. Yana dai jinya zakace anty baraka ta fada tana dariya mama dubu tace jinya kuma jinyarwa shidai habu ya fita yana dariya sai anty baraka ke fadin amaryansa mana. Itace wai yau ba lafiya saida shi habu yakai masu abinci dazun toooow Allah ya sauwaka tun yanzu an fara ciwo kuma haka ? Kaiya banda abinki dubu kaji ance amarya ba lafiya a daren farko ai kasan meya gudana kuma haba dai kina magana haka ba lissafi kuma dai ? To iya me kuma nace Allah ya sauwaka yakai yan baya ga danshinta mama dubu ta fada tana zama saiba ta juya kawai ta fita daga part din ba tare dayi maganan daya kawota ba. Munafuncin banza da wofi Allah iya nan idan batayi hankali dani ba wata rana saina faceta a gidan nan . Iya din Asmau dake kishingide ta dago tana fadi tace kada ki soma gangancin hakan ga iya don wallahi ba zakiji dadinsu ba kaf dinsu idan kika taba iya ko mama gidan nan. Kansu fa a hade yake jallone da mufinsa idan kin kula da tafiyan mutanen gidan nan daya bayayi saida dan uwansa . Kaf dinsu yaya J shike juyasu gidan nan kin taba iya donshi zasu kyaleki kike zato ki dai tsaya akansa shidaya munanana maki a yanzu. Tsuki taja ta mike zuwa daki a cikin wani irin jin haushin kowa a gidan don ba wanda ya damu da halin da J din keson nunawa akansu yanzu itako ba zata yarda da hakan ba. Don wanan yar fillon me zubin mayu daya dauko zai nuna su ba matane ko me gaskiya hakan ma ba zai sabu ba wallahi. Sai karfe biyu da rabi ya shigo gidan duk da sunga anshigo da wasu kaya sun san shine ya shigo gidan amma bai zo part din ba tukun. Asmau dake falo kwance tana wayane ita kuma saiba na kitchen tana hada abinda zasuci maigadi ya shigo da kayan ko kallon kayan batayi ba inda ya aje ya fita a kofan kitchen din. Saida Asmau ta shiga kitchen din take fadin au baki dauke kayan nan ba ina ganin yaya yazo dasu fa kayan miyane nasan aka sayo ta duka tana bude buhun kayan. Su kayan gwarine da nama mai yawa sai mai gallon biyu a gefe aje da kwalin taliya dana indomie zasukai shida duk a kofan kitchen maigadin ya zubesu wajen. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 4️⃣6️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Saida ya gaisa dasu iya tagama sakamai albarka ya juya wajen mama yana tambaya suna dai lafiya ko ? Ido ta zuba mai tana hango annuri da annashuwa a tare da dan nata da hakan ke nuna yana cikin walwala sosai a lokacin saidai har yanzu tana jin zafinsa a ranta wanda ba zatace ga dalili ba. Ita dai abinda tafi dauka shine yayi aure bada izininta ba ya nuna bata da tacewa gareshi ya isa yanzu bai bukatan shawaranta a yanzu. Inkin debe wanan ba zatace ga abinda da dan nata yayi mata ba da zata fada don Jafar shine na daya a kaf iyalinta dake mata biyayya. Zata iya fassara wanan abin da jin zafin abinda yaiwa matanshi na cin fuska don zata kira wanan auren da sunan cin fuska a wajensu yayi aure ba tare da sanin kowa a cikinsu ba inbada kawu da yaiwa dole ya daukeshi zuwa neman aure kamar yadda kawu ya fada mata. Jin tambayan da yake mata yasa ta nisa daga dogon tunanen da takeyi nasa a lokacin tace lafiya lau muke Jafar ya wajen ita Rahama din naji Habu na fadin bata jin dadi kuma ? Da sauki tasha magani kafin in fito ta samu sauki don taki yarda muje asibiti ai dama Rahama bata son ko magani balle zancen asibiti Salima ke fada. Ai naga alama ta daiji sauki da ranan nan don saida naga taci abinci nafito na barta zaune a falo tana gaishekuma. Iyace ta kara fadin amaryace mai batun hankali injin dai kazo min da tawa sauran kazan amarcin naku ya mike tsaye yana dariya yake fadin iya ke aiba saura za a baki ba taki dakwalwan za a kawo maki dai kema. Daga part din iya nasa part din ya nufa inda ya samesu a kitchen tsaye suna sa,insa a tsakaninsu kan kayan da aka shigo dashi din. Daga kofa ya tsaya rike da hannun yar wajen saiba yana fadin wai ya hakane kuma ku dai baku zama bakuyi fitina a tsakanin ku ba ? Wai cewa nayi a dauko wanan naman daya saura sai a soya kada a hada da wanan shine wai ban isa ba a hada waje daya duka Asmau ta fada. Don me zakice haka ba ita bace babba ita tasan yadda za a adana kayan ke meye naki a ciki tunda tace haka za ayi jafar ya fada. Au Allah ko ashe an fara babba a gidan nan yanzu to maji magani ashe ta fada tana mashi wani irin kallo na yatsune. Kedai baki zama a waje ba ai fitina ba saiba ni bansan abinda yasa kike wanan rayuwa haka ba juyawa tayi ta bashi baya tana juye abincin data gama dafawa a plate ya bita da kallo kafin ya koma fadin. Wait naga kin juye abincin duka sufa ba zasuci bane tace ka tambayeta mana ai dazun ta dafa itama taci da yaran ? Asmau yaushe kuka fara girki daban dabab a gidan nan gashi nan a cooler na zuba mata kuma ta gani ta dafa wani ai. Abincin da yayi sanyi kuke son inci ta juyo tana fada yace ke ba bawan gidan ku nake ba da zaki dinga min barnan abinci haka in saka maki ido. Gidan mu kan ai kaima kasan yafi karfin ka balle daga magana ka jefo gidan mu a ciki haka kawai daga zance ka nemi ka zageni tunda dama kana hasale dani ? Na dai fada maki kada na sake gani ko jin an raba min girki a gidan nan idan ba haka ba rai zai baci wallahi ya fada a hasale ya juya zuwa dakinsa. Asmau da saida ta gama gyara kayan ta fito tabar kitchen din ba gyara ta nufi dakin nasa daga kofa ta tsaya tana gaidashi da wuni ya amsa yana kwance ya dago yana fadin. Wai Asmau sai yaushe zaki daina zama hakane don Allah kayane baki dashi kome da kika zabi ki dinga zama a haka don Allah ? Kiwa kanki fada Asmau kece babba a gidan nan wanan halin da kikeyi yasa kike ganin kowa na rainaki don baki mayar da kanki abin kwarai ba Asmau don Allah ki gyara banson haka me kika nema kika rasa a rayuwanki ? Naji ta fada ta juya ta fita daga dakin tana jinini a zuciyarta cewa ai dama ban taba fari a wajen ka tunda baka kaunata yanzu kome nayi banyi daidai bane. Shiko tsuki yaja yana gyara kwanciyarsa haushine ya kumeshi Allah ya gani yana son Asmau amma halinta sam baiyi masa ba kazanta da yawan da abu da muhinmanci magana da har bata iya daukarwa kanta mataki shi yake damunsa da ita. Yaso tun farko ya sameta irin yadda rayuwansa keson matarsa ta kasance bai samu hakan gareta ba yayi gyara ta kasa gyarawa yakai karanta har gaban iyayyenta an tsawata mata amma bata sauya dole ya gaji ya sa mata ido. Yadda Saiba tazo mashi da karya ya dauka ta kwaraice ashe halinsu daya sak da kawar nata kishiya kuma a yanzu dole yai hakkuri ya zubawa sarautan Allah ido akansu. Gashi shikan idan ka ganshi tsab tsab dashi zakice inda yake sai kin wanke kafa ki shiga saboda tsabtanshi saidai kuma bai samu mata irinshi ba. Ji don Allah wai wajen miji tazo a hakan ga wani riga duk jurwaye ta kawo wani zani sama ta dora tayi daura gaba da shi wanan kayan takaicin ina zai kaishi don Allah. Jin alarm din wayansa dake sanar masa da lokacin sallah ya mike zuwa masallacin nan unguwarsu inda suke bi sallah. Ana idar da sallah ya shiga motarshi yabar gidaa tudun wada ya nufa ya gaidasu mama kana ya nufi gidan anty Ai da yake son zuwa ya ganta. Yana gidan Habu ya kirashi a waya yana fadin J kana ina gasu malam sun iso aina dauka kana cikin gidane saida na aika akace kafita. Habu kuyi yadda ya dace gani nan tudun wanda daga nan kuma zamu fita da Nurane kai habu ya daga ya dubi su mama da sauran jama,an dake wajen. Baiso ace J din baya wajen ba za ai wanan rabon amma zai dage yaga an fitarwa kowa hakkinshi yadda ya dace . Aka bude taro da addua tare da bayanin abinda ka,idan kado ya bada ikon abawa ko wani mai hakki kafin habu ya dora da kara masu haske kan yadda dukiyan nasu yake. Masha Allah wanan bawan Allah yayi kokari matuka abin a jinjina masane sosai duba ga irin rikon amanan da yayi da kurciyanshi. Abune mai wuya a samu kudi har riba a wanan shekarun don haka su godewa Allah su kuma godewa wanda yayi wanan jajircewan a garesu. Habu yace ba wani bane illa yayan mu jafar shine aka dankawa kudin tun lokacin akan ya juya har ya fara daga baya yayi shawaran gara ya bada wa yan nan kudin ga wani ya juya ya fara sana,an kanshi amma yana bibiya ko wani lokaci malamin yace Na,am . Shine dalilin da yanzu da yan uwan mu suka bukaci kudinsu aka fito dashi aka lissafa mun samu kudi ya ninka ninkin ba ninkin muke so a warewa kowa nasa kaso a damkawa masu shi abinsu. Daidai lokacin kawu ya shigo falon don bai samu karasowa da wuri ba saboda kauye daya tafi duk akan rabon kudin don yana son a daure bakinsu wai. Duka kudin su dawo hannunsa ba tare da an samu wanda ya mussa hakan ba a cikinsu don ya kula yaron sun soma sanin ciwon kansu a yanzu. Yazo ya zauna sai cicika yakeyi yana batsewa don me za a fara bashi daga baya daya fahinci ba a soma kasafin kudin ba ashe shine ya dan washe fuskansa. Malami na farko ya gyara zama yana fadi to ai abune mai sauki yanzu tunda da baya an raba ansan yawan abinda kowa a nan ya mallaka daga mazan har matan sai a soma cirewa kowa nasa kason ko kuma alabashin kasafa kudin a yadda wanan can kadon na farko yake har riban da kowa ya samu zuwa yanzu. Da yake aikinsune sun saba nan da nan aka fara lissafin yadda ya dace ana ajewa kows nasa gefe daya da sunan da mama aka fara sai su maza kafin a debewa diya matan akasafa masu yadda ya dace. Ba wanda aka cuta a cikinsu rabo na tsakanin da Allah malaman suka tsaya sukai masu inda Habu ya mika hannu ya dauki na farko yana fadin wanan na J ne. Jafaru kuma a yanzu ai baida abinda zaiyi da wanan kudin kan a,a hjy ba yana cikin magada ba ? Suka amsa da yana ciki malam yace don haka a kwashe mashi tunda yana da hakki anya Jafaru bai yafe kudin nan ba kuwa ? Anty baraka ke fadin malamin ya sake fadin babu zancen yafiya a nan tunda ya gada shima dole a bashi hakkinsa ai. Sai kuma wanan nawa saina yazid daya mika hannu zai kwasa mama tace kada ka dauki na yazid habu ka barshi za aci gaba da juya mashi kafin Allah ya dawo dashi lafiya ya karba mama ke fadin hakan. Kallonta Habu yayi a cikin mamaki kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru ya kasa furta komai daga can Salima take fadin amma yaya Yazid yace abawa J nasa kason ya rike mashi a hannusa idan an raba ai. Nina haifi yazid ba wani ya haifa min shi ba don haka nina san yadda zanyi dasu a wajena ta fada fuska daure habu ya ciro kudi daga Aljihunshi yana fadin wanan na maine J yace a baku ai maku godiya. Ya hada kudinshi zai fita yaji salima tace yaya Habu kada ka fita kudina nace a ba ya j ya aje a hannunsa fa ? Ba zan bashi ba akwai wanda zan ba a cigaba da juya maku kudin nan mama ta fada a tsawace ga salima din. Dakata hjy malamin da zai fita falon a karshe ya fada yace wanan hakine fa yarinyar nan yanzu ba yarinya karama bace don ko wace ta mallaki hankalin kanta a yanzu. Don haka yau ko cewa tayi ita zata rike abinta a hannunta za a iya danka mata dukiyanta don ita ta gaji abinta daga mahaifinta. Kawu ya hade wasu yawu yana gyara haban babban rigansa sai aikawa malamin harara yakeyi daga inda yake zaune ganin malam ya tsaya jawo dogon aya yasashi magana. Malam ina ganin kunyi abinda ya dace yanzu ai kowa yasan hakkinsa kamar yadda suka bukata don haka abarsu suyi shawara da uwarsu kuma. Ni wallahi ba wani shawaran da zanyi ya habu ka dauki kudina kaba yaya J na fada mai abinda nake sonyi dasu nan gaba. Salima zan safa maki fa ina fadin magana kina musayawa mama nace abu zan saya dasu idan sun kara yawa kuma har na nuna mashi abin ya sani . Habu ya dawo ya tsaya gaban kudin yace baraka kwashi naki ke saratu ki dauka a ban na salima din tunda abu take son saya da kudin. Idan abin bana amfani bane na tabbatar da J ba zai yarda ba baraka ta kwasa sai saratu ya duka ya dauki kudin Salima din ya fita dasu zuwa part dinshi. Ranan Salima tasha fada sosai wajen mama Allah ya gyara batayi maya baki ba duk abin nan anyishi iya bata wajen don kamar an kadata fita unguwa tabi J ya sauketa gidan wani dan uwanta dubiya. Yanzu yaya kaga yadda abu ya kaya kuma yaran nan kamar abin hadin baki kudin nan daga nawa saina Yazid koshi don bai nan,ne . Nasan da haka za ayi shima karban abinsa zaiyi sai na saratu itama naga take taken ta tun kan a raba take fadin sana,a zata fara tunda karatun yakiya gareta ko Allah zaisa mata hannu. Ni yanzu ai lissafin ya tsaya min saidai a kawo mu gwada ko zasu fara daukuwa a garemu hakana bai bar gidan ba ranan saida ya karbe kudin mama da yazid din. Dana saratu da mama ta raba biyu ta boye rabi ta mikawa kawu sauran ya daure leda ya tafi yana mata sallama kada iya ta dawo ta sameshi . Zance ya lalace yasan ko wanan rabonsane shiyasa yayi dabaran daya izata zuwa gidan dan uwan nata a ranan ayi a kare bata nan. Habu ne bayan fitansu ya dawo raka malaman yake waya da j yana fadin gaskiya j akwai abinda yake damun mama gaskiya. A nan dai ya kwashe komai daya faru wajen ya fada mai murmushi j din yayi yana fadin ba komai matsalanta a yanzu kawune. Iya ta fada min dazun a hanya cewa kawu shiya matsa a fito da kudin nan a raba don kawai wata bukatanshi. Dama ina hasashen hakan daga kawu mutumin nan ya kamata mu nuna mashi musan nufisa akan mu yanzu. No kada ka soma ba yanzu ba Habu idan kayi hakan ranka zai bacine da mama don haka ka kyaleshi har gaba. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 4️⃣7️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Zaune yake falin yaya Ai itama a nan cikin tudun wada gidanta yake saidai akwai dan nisa da family house dinsu din daga gidan daya sauke iya daketa bashi hakkuri akan rayuwa da kuma iyayye da yan uwa ya nufo gidan yaya Ai din. Da murnanta ta rasa ina zata sakashi a lokacin don jin dadin yau dan uwanta yazo wajenta abinda basuyi mata ke nan kamar yan uwana na gudunta take gani saboda talaucin da Allah ya dora masune. Don ita yaya Ai din mijinta dadtijone sosai kila kuma gami da talaucine yasashi tsofa a zamanin kurciyarsa ya danyi tashen kudi saidai irin na rufin asiri din nan za ace. A haka kuma iftila,i ya sauka,mashi a hanyansa na zuwa fatauci lokacin ya hadu da barayi suka karbe duk abin hannunsa tun lokacin yake fama da rayuwa shi da iyalinsa. Kasane bana hadin kai ba aure abu zai samu dan uwa maimakon a samu yan uwansa yan kasuwa su tallafawa mutum a dagashi sai dai a sakawa mutum ido har sai yakai kasa waras kamar jira ake hakan ya sameshi dama. Na tabbatar da mata Allah ya umurta da kasuwanci kamar maza za a ga hadin kai da taimakon juna a tsakanin su🙋. Sai ya kasance yan uwa ma sam basu damu da ita ba da iyalinta don bata da komai a rayuwanta saidai duk sallah nasan idan an fita ana zuwa gidanta boyan Allah ga son jama,a saita rasa ina taka saka mutum idan yazo wajenta. Yanzuma da J din yazo sai godiya take masa daga ita har mijinta da kishiyarta kamar wanda sukaga yazo masu da wani abu a lokacin duk da hannu sake suka ganshi amma sunji dadin hakan sosai a lokacin. Ta kakabe wajen da zai zauna tukun a dakin nata da babu komai a cikinsa sai dan gadon katako mai dungu da wani tsohon zani gado shimfide duk ya kode. Gefe guda wani tsohon kujerane da tsufanshi har yasa katakonshi ya fito fili ya zazzage an tula raga don ya danyi taushi. Nan aka gyara mashi ya zauna suka fara gaisawa da yar uwar nasa dake mashi sannu da zuwa a lokacin take tambayan dazun nake jin kana gari a wajen malam yake fada mun yaji ance kaine kabada gyaran massalaci kofan gidan mu . Yace shekaran jiya na shigo da dare jiya kuma abubuwa sun min yawa yasa ban samu zuwa nagai dake da gajiyan buki ba. Haba dai aiyiwa kaine ya kara mata da godiya take fadin Jafaru aini ka karrama a zancen nan da har ka tuna dani baka kyamace niba ka turo ayi komai a gidana akwai abinda yafi haka dadi a wajena. Wanan ai yafi dan uwa yazo ya baka kudi indai ana zumunci haka da zumunci bai taba lalacewa ai a duniya amma ina su isa gamu gari guda a waje daya sai inyi shekaru ban saka kowansu a idona ba garin nan kuma ana raye inaga yaya in sun taso kuma kaga ba zumunci ke nan ai a tsakanin su idan sun taso. Hakkuri ya bata yana fadan in sha Allahu za a gyara yaranta da suka dawo daga islamiya suka shigo su uku mata maza biyarne ta haifa a gidan. Wanan yasa tsufan wahala ya taso mata saika rantse batayi primary ba balle secondary idan ka ganta lokacinsu sune yan mata masu tashe a gari duniya ke nan yanzu saboda talauci da yara ta koma haka abin tausayi. Ya Allah ka duba muna wanan zamani cikon tausayinka ya Allah ka sakawa duk wata uwa da alheri kasa albarka ga zuria wa yanda suka kauce kuma ga tsufa ga zuria Allah ka shirya munasu badon halinsu ba ya Allah mun tuba kaiwa kasan mu da musulman kasan mu agajin wahalan rayuwan da ake ciki Amin ya Allahu. Yaya Ai me malam keyi yanzune na ganshi a gida a wanan lokacin ko har ya taso daga kasuwan ne ko yake tambayanta kan mijinta din ? Haba ta kama tana fadin malam kace Jafaru ai malam yaushe rabonshi da kasuwa yau kusan kimanin shekaru goma sha,ai tun wanan abin daya faru dashi. Da yana dan zagaya abokan hurdanshi na kasuwa don samun abinda mukaci a gidan har yakai sun gaji dashi sun fara kyamatarshi yazo ya daina fita yanzu dai sai abinda Allah ya kawo muna idan rabon mu ya ratsa. Innalillahi yake nanatawa a zuciyarshi har yakai fada a fili ya gyara zama yace yanzu kina nufin haka kuke zaune bai sana,an komai ? Haka muke Jafaru aiko nayi mamaki da baka san hakan ba duk zuwan nan da kukeyi ai kuna ganinsa gidan nan ko ? Na dauka dai don sallah ne kinsan nafi zuwa nan da sallah wani lokacin a,a wallahi halin da muke ciki kenan ai shekara da shekaru kai dai Jafaru. Allah ya sauwaka ya fada yarta datazo a karshe tana gaudashi zata kai shekara goma sha uku da haihuwa yake fadin wana takice tace tawa ce ita autata take biwa takwaran iya ke nan ai Habiba. A,a,a ashe kin samu mai sunan nan kema tace ina da ita ai gata nan yace ina ga ni zan dauketa kuwa ko ita ko wanan autan naki ko inbawa Amaryata rikon ta su zauna tare idan zaku ban don banson zamanta ita kadai don ni ba mai zama a garin bane sosai wanan yasa yanzun nan naji hakan ya fado min a rai. Amma abinda ya kawoni nan shine ina son dake da anty Rakiya kuzo wanan gidana da amaryana take ku dauki kayan tausan gaban wa yan nan kukai masu duk da nasan na daiyine kawai amma sai kuma yai shiru bai karasa fadin abinda yayi niyar fadi ba din. Sun dan jima ganin magariba daya gabato ya mike suka fito bayan ya aje mata kudi yan dari biyar biyar ya samu kishiyar ta tana bakin murhu ya ciro dubu ashirin ya bata ta bata ai kuwa suka shiga godiya. A waje ya samu malam sule na masa gadin motarshi saboda yaran unguwar sun dan jima dashi kafin ya fada mai makasudin zuwansa din gidan. Yaji dadin hakan don daga mijin har matan mutanene masu son zumunci saidai babu karfin yin hakan a yanzu dole yasa suka lafa. Shima dubu hamsin ya bashi ya barsu cike da tausayinsu a cikin ransa masalacin kofan gidansu da mahaifinsu ya gina da yake raye nan yayi sallah magariba tare da jama,an unguwar. Ana idar da sallah ya sulale ya fita bai zo gidana ba saida ya koma gidan daya sauke iya ya dauko ta zuwa gida haka kuma yana son yai ma iyalinsa saida safe duk da ba dadin rai ya samu ga hakan ba . Bai shiga part din iyan ba kodaya fito ya ja motarshi ya bar gidan don Nusaiba bata ko amsa sallamashi ba daya shigo. Sauri yakeyi yaje yaga halin da yar mutane take ciki donshi bai tsatsaya ba ya juya zuwa gidan amma duk damuwa akan halin daya samu yaya Ai su ya daga mashi hankali. Wa yan nan sune abin taimako a duniya shine amfanin samu a cikin dangi ina amfanin kana dashi dan uwanka na cikin irin wanan rayuwan kuma ? Tun fitanshi na shiga kitchen na dafa ruwan dumi na saka a flask na juye saura naje bandaki dashi naji dadin tsarki da ruwan dumin sosai don haka na kai har magariba ina gasa kaina da ruwan dumi hakan da nayi yasa na samu walwala na iya yin girkin dare dan abinda zamuci da dare din. Ko kafin ya dawo nayi tuwon semo da miyar busassan kubewa don shine gareni lokacin amma nayi amfani da nama dake shake a cikin freezer kitchen din. Inda na dan cika tattasai da albasa da dab attah kadan sai kayan yaji dana barbada don kamshin miyan yabada dan dano nama kuma na dafeshi sosai tunda miyar yaukine nayi ga kamshin daddawa dake tashi a ciki na hada komai na shiga wanka a gurguje na dade zaune a ruwan dumi kafin na fito nayi wanka sabulu da soso na dauro alwala na fito na tayar da sallah ina idarwa na mike kada jikina ya bushe sanyi ya sauka min na nufi mirro na gyara jikina sallah isha nayi na saka wani dogon rigan cotton mai mayafi rigan anyishi mai sharp na saka hula kalan kayan sky colour na dan yafa gyalen shi a wuyana. Nasan don inda yake a lokacin ya kusa dawowa gida hakan yasa na kara feshe ko ina da air freshener take gidan ya dauki kamshin dadi ban shafa turare a jikina saidai roll on a arm dina zuwa wuya don zufa. Karan bude get din gidan dake bada wani sauti saboda nauyinsa yasa na gane ya dawo a lokacin. Yana shigowa direct dakina ya nufo ina kwance nayi rigingine saman gado da littafi a hannuna da nake dubawa ya shigo dakin da sallama. Na dan dago kai ina mashi sannu da zuwa na sauke kafana daga saman gadon don in mike in karbi ledan dake hannusa don malaman mu Lubbunah ta fada muna hakan waje biyu yake da amfani karban kaya a hannun miji. Na farko ladan da zaki samu daga Allah don girmama mijin da kikayi da aure sai na biyu kuma hakan na saka wani irn kauna a tsakanin miji da mata na ban girma donshi ta horemu dayin hakan komai kankanta abu muyi saurin karba daga hannuwan mazajen mu. Mu,sanman mazan mu na hausa dake amfani da addini da al,ada lokaci guda hakan ya zama addini da dabi,an malam bahaushe. Ya gane me zanyi don idona na kan ledan hakan yasa da sauri yace No ki zauna abinki ba wani abu bane ai a ciki kazace sai fresh milk na kawo maki kisha. Ban dai zauna din ba na mike nazo na karba ina gasheshi da dawowa jikinsa ya hada da nawa ya matse waje daya yana fadin yaya jikin naki yanzu ? Naji sauki na fada a cikin kunya dajin nauyinsa don irin yadda ya hade jikin mu a waje daya din kamar yana neman wani abu a jikin nawa. Kin tabbatar ya kara fada nayi dan murmushi kawai ban bashi amsa ba yake fadin hankalina ya tashi sosai dazun Rahama iam sorry banyi hakan don kaina ba so sorry kiyi hakkuri da hakan don Allah ? Na boye kaina a cikin jikinshi yacigaba da fadin Allah yayi maki albarka naji dadi sosai jiyan kamar nayi kuwa ban sani ba koma nayi din ai ? Dariya yaso subbuce min na kara noke kaina saman jikinshi yace wallahi Rahama komai naki yai min a rayuwata ina sonki sosai mu sanman kamshin nan naki don Allah ki bani hadin kai mu zauna lafiya. Kaina gyada kana na furta a hankali da in sha Allahu yace ba zan manta da rayuwan daren jiya ba da komai na cikinsa har wanan cizon da aka gyatsira min a wuya . Ina son wanan daren har kullum ina son abinda ya faru a daren abinda ya faru a cikinsa wani irin nauyi da kunyane suka rufeni nasa. Yace Allah kuwa gaskiya nake fada Rahama na rasa inda zan saka kaina a jiyan kamar in bude cikina ki shiga naji lokacin don tsaban sonki dan Allah kici gaba da inganta min sauran dararen da zamuyi tare dake a rayuwan mu. Ya dagoni yana kokarin mu hada ido dashi yake fadan hakan na kasa yadda yake so din na daiyi kokarin daga mashi kai alaman in sha Allahu. Naji yakai min kiss a goshi yana fadin bari naje na rage kayan nan a jikina in dan watsa ruwa in dawo in baki abinci ya fada tare da sakeni ya juya ya fita daga dakin. Zaune nakai a hankali bakin gado ina sakin ajiyan zuciya wai yau ni Rahama mutum kamar yaya Jafar yake fadawa irin wanan maganan a kaina. Dama ace ni kadaine fa in more miji har miji a nan saidai kash kadara ta riga fata nidin a haka ragowa na samu ragowan wasu ma bako mutum daya ba. Take naji wani irin kishin matan nasa ya tokare min zuciya a karo na farko tun faruwan alakan hada aurena dashi sai wanan karon naji zafin matan nasa. Zafi na daban ba irin wanda nake ji nasu ba a baya akan matsin da suke min kan yar uwata wanan wani na dabanne ya ziyarci zuciyana. Kwance nake rigingine a yadda ya sameni da farko na soma tunanen ko yaya zamana dasu yanzu a matsayin kishiyarsu zai kaya oho ? Na sandai wata rana dole a hadu an kuma ce mai hali baya fasa halinsa sai yayi koda kadan ne ashe zan iya kyalewa in shanye duk wani cin fuskan da zasu iya min kuwa ? Kai ina dole in rama a yanzu ga duk wace taso barazana a kaina basu ba koma wacece indai akan yaya jafar ne ba zan taba kyale mashi ba kuwa. Haka ya dawo ya sameni Tsarki da aminci su tabata ga Allah na furta a raina lokacin dana kyala ido nagashi tsaye a kofana cikin kananun kaya wando da riga iri daya saidai wandon iya gwiwa ya tsaya mashi haka kuma rigan ya dan sauka ya dan rufe zuwa cinyarsa masu ruwan kalan dorawa da akaiwa rubutu a gaban rigan da gefen wando cikin manyan haruffa da FREE MAN. Na nanata kalman a bakina har lokacin yana tsaye yana waya yana fadin gaba daya za a kwarai massallacin na fada masu sai a kara mashi girman tako goma ako wani bangare tunda akwai sauran fili wadattace da za ai hakan. Duk wani kayan da za a kawata massalacin dashi na riga da naba garba kwangilansa shi zai sayo ya kawo banson aikin nan ya wuce nan da wata biyu insha Allahu tunda akwai komai a kasa. Aina fada mai Habu zai kawo mai kudin komai da mukai killisafi dana zirga zirgansa duka gaba daya ya dan jima yana saurareb bayanin abokin maganan nasa kafin yace hakan ba matsala bane ai ayi komai yadda ya dace kawai. Ya kashe wayan yana kallona ban farga daya gama wayan nasa ba saida ya ware hannayesa alaman inzo garesa niko na shagala da kallonsa ban farga ba lokacin na sauke wani irin ajiyan zuciya ina mikewa. Na tako zuwa wajenshi hannuna ya rike a cikin nasa yana rada min tafiyan nan naki ba daidai bane har yanzu Allah ya taimakeni ba kowa a gidan nan danaji kunyar hakan a idon mashi. Ledan daya shigo dashi din ya dauka nidai har mamaki yake ban yadda shi bai kunyata ko nauyina zakice mun dade da shakuwa dashine lokacin. Falo mukayiwa tsinke saida yaga na zauna ya nufi gaban tv ya kunna ya dawo ya zauna lokacin nake fadin a dauko abincine nan ? Abinci kuma ya dago da sauri yana tambayana nace na girka abinci dazun danaji sauki Ohho no no a hakan kika wahalal da kanki Rahama ? Baki da lafiya fa kin sani da badon karna shafa maki bakin jini ba daga zuwan ki Allah ba inda zan fita yau ina gidan nan ina jinyar abina nida nayi barnana da kaina. To amma rashin fitana din zai iya shafa maki laifi ga mutane da yawa musan man mutanen gidan mu sai a dauka kece kika hanani fita. Da ina nan ba zakiyi wanan wahalan ba haka na dan kalleshi cikin marairaicewa nake fadin don nayiwa yayana girki kuma shine wahala ? Haba dai ai naji saukina kuma ban iya badin ka da yunwa tunda nasan kai kafi son cin abincin gida ko yaushe meye a cikin dan girkin iya bakinka kadai ? Na mike zuwa dinning na dauko abincin zuwa inda yake zaune na aje a gabanshi ya kalli kayan yana fadin kinsha fama wallahi. Allah yai maki albarka Rahama sunan ki yaci ke din mai tausayice da imani da har kika iya fahintana wallahi kamar kin shiga raina kin gani ina tunanen abinda zanci mai dan nauyi da daren nan kafin in kwanta. Kinsan ni din rainon iyace ai ban wanka in bushe a gidan mu ina dakin iya duk da mahaifin mu bai yarda na zauna a wajenta dindindinba saidai in tafi in dawo gidan mu in kwana. Ya bude abincin daidai ina aje mashi ruwan sha dana wanke hannuwa ido ya lumshe ganin yadda semon yabada ma,ana a cikin ledan dana daresu a ciki kulli biyune na saka mai ya bude miyan yana furta masha Allah. Zaman dirsha yayi a kasa da alaman haka zaici abincin a lokacin ina kokarin kaiwa zaune kujeran dake kusa dashi naji yana fadin zo nan ki zauna yana nuna min wajen zama a gefensa kasa haka yasa na sauka na zauna kusa dashi din kamar yadda ya bukata. Naji yace waima in tambayeki don Allah Rahama kudin da gaskiyane kun taba zaman daji kuwa ni sam banga alamun hakan ba gareku amma ance a rugga habu ya gano muna ku ? Murmushi nayi ina fadin a can ya ganmu mana zama na shekara biyar mukayi a rugga tare da baffab mu na fada ina zuba mashi abincin a plate yana bin zanen hannuna da kallo cikin mamakin abindana fada. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 4️⃣8️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Washegari shi ya shiga kitchen da safe ya hada muna breakfast ruwan zafin shayi sai dankali da kwai suyan damke don duk ya wargaje kwan a wajen juyi saidai yayi dadin ci gaskiya a baki. Ina daki ya shigo ya sameni duk dana falka daga barcin safen dana dan samu amma na kasa dagawa daga kwancen ina kwance ina faman tunane ya shigo har dakin da abin kari. Da sauri na tashi cikin mamaki ina gaidashi kin tashi ke nan ya fada yana aje kayan hannunsa din na amsa da eh yaya ina kwana lafiya ya fada yana zama yake fadin dama nayi zaton baki tashi ba ai ? Yau muna da baki gidan nan duk da ba wajen mu sukazo ba zasu dauki kayane su tafi wanan kayan dake dakina kayan fadan kishiyace dana hadawa yan uwanki a a kai masu. Saidai ita Asmau don haihuwan da zatayi nasa an hada mata har da kayan baby na kuma dan kara mata ya dara na Saiba din. Kallonshi na danyi yace ehh ai kinga in Allah ya raba lafiya ba sai na koma sayan komai ba kuma shike nan na gama a yanzu. Allah ya sauketa lafiya na fada ya amsa a cikin dadin rai da amin ai watan haihuwan nata ya kusa kamawa Allah yasa lokacin kun samu hutu sai kawai in daukeki mubar garin nan na dan wani lokaci. Ita kuma dayan antyn fa yaya yace wai Saiba kike nufi idan na dauketa yanzu wazai kula da ita Asmau din, da hidima zaimata yawa ai ? Maza ke nan na fada ni zainab makawa sai kiga namiji ya koma yaro karamin a gaban mace yana sakin magana kamar bashi ba. Balle J da yanzu yana da madafa dan magana zai tunar dasu cewa sun nuna suna kyamarshi a baya don haka yanzu baida lokacin tsayawa dasu ai nasan dai abinda zai fada ke nan a karshen zancensa. Tare muka karya dashi bayab mun gama nakwashe kayan zuwa kitchen na tsaya wankewa na gyara kitchen din dana fito nima wanka nashiga na zauna bayan na fito na shirya tsab a cikin wani atamfa dinkin zamani don dogon rigace amma tellan ya tsaya ya tsara dinkin kamar ba hannune ya dinkashi ba. Dinkin akwai na ciki wanda zaki fara sakawa mai dan hannu saina sama mai adon da stely din dayasha duwatsu har kasa saiki rantse daga egypt aka shigo dashi haka. Hullane mahadinsa don dan kwali bai haduwa da kaya haka sai gyalena ainihin da akai amfani dashi a matsayin gyalen yafawa da kayan . A kyalen yadin kayan da akayi cin bakin gyalen dashi da duwatsu sai hakan yaba da mana,ana ga gayan sosai zai fito da duk macen data sa a jikinta abuja ke nan. Sallaman su yaya Ai yasa na fito don sunki zama sunata gwara sallama shima lokacin yana ciki dakinsa kuma kofa a rufe. Nice na fito ina amsa masu sallamansu suka juyo kofana muka fara gaisuwa nake ce dasu su zauna sai bayan sun zauna din na gurfana ina gaidasu da zuwa. Masha Allah anty Rukkaiya ta fada tana bina da kallo tace a,a lalai ba laifi gaskiya Allah ya baku zaman lafiya amarya. Na mike naje kitchen na dauko masu abinsha da snack gami da ruwa saida na ciko tire na kawo masu na aje na juya ina fadin barina sanar dashi isowan su na nufi hanyar dakinshi din duk suka bini da kallo anty Rukkaiya ke fadin. Akace yayan fulanin ruggane gasu kamar ya Niger mana sun waye sosai ba zakice asalinsu rugga bane tun wanan madin har tafi ta wajen habu wayewa ai. Itace daidai da matanshi ai don yaran basu da mutunci baka zuwa gidansu kasha ruwa balle abinci ni yaya Ai ko sun ban abincin su ai ban iya cima . Yana zaune saman hasonsa ya dora kafa daya a sama dayan na kasa yana latsan laptop nayi sallama nashigo dakin. Kai ya dago ya dan dubeni kamar zai maida hankali ga abinda yakeyi bayan ya amsa sallaman tasa sai kuma yayi saurin dagowa ya zuba min idonsa. A dan maraice nake fadin su yayane sukazo suna falo zaune hannu ya miko min bakinsa na fadin har sun iso ashe ? Na tako zuwa gareshi ina fadin yanzun suka shigo hannuna ya kama ya jawoni na fada jikinshi ya rugumini tsam yana fadin duk kayan da kika saka Rahama sai naga sunfi maki kyau ga wanda kika cire. Wai meye sirin hakanne Rahama jin hannusa ya fara yawo a jikina yasa nace dashi cikin wani sallon fitar da magana su yaya fa suna falo suna jiranka kada suga an barsu su kaidai zaune. Yaja numfashi yana dagani yace kece ai kika kashe min jiki yasa na kasa tashi na manta da zancen su . Cikin kissa na dan kalleshi ina fadin ni kuma yaya yanzu dana shigo don Allah me nace dakai da zakace laifinane kuma ? Au baki san abinda kikai min ba to ki duba nan da sauri na mike daga jikin nasa ina fadin nidai muje don Allah kada suga mun jima haka ? Kamahin nan naki Rahama ba karamin illanta min zuciya yakeyi ba har na fara tunanen yadda zan koma maraya ranan da bani kusa dake wallahi. Suma da kalan nasu a can da zaka shaka dama mata suna mukatara ai amma ba kalan mu daya ba a wajen abubuwa kowa da irin nasa fasahan ai. Wai ashe kina magana haka dama ya fada yana gyara saita jikinsa daya mike tsaye ni dai nayi gaba ina dariya ya biyoni da yaya Rukkaiya data dauki cup tana shan lemo muka fara arba tayi saurin ajewa yake fadi daga bayana ashe kun iso yaya. Mun iso Jafaru kasan halin yaya Ai ai da nabita nata aitin bakwai muna gidan nan ita bataki hakan ba a wajenta yayi dariya yana zama yace. Haka ake son mutum ai da cika alkawari jin suna gaisawa yasa na koma dakin nasa ana basu waje bandakin na gyaro kafin na fara gyaran gadon dakin nasa lokacin ya shigo dakin . Baki dai gajiya da aiki ke nafi son ki huta yadda nima zanbi jikin ki in huta da dare in sauke gajiyana yadda nake so amma sai ki wuni a tsaye kina aiki waike mai wayau don mutum ya tausaya maki ko ? Dariya ya ban sosai saidai ba halin hakan shi yana mamakin sakewana nima haka mamakinsa nake ji yadda yake abinsa da iyalinsa cikin sakewa haka ? Dama haka yake amma matansa suke kullum cikin fada ko dashi ko kuma a tsakaninsu kullum ba zaman lafiya a part dinsu can gida. Ganin ya gara akwatunan biyu yasa na garo masa sauran muka fito dasu falo zuwa gaban su yaya din ina ajewa na juya na bar wajen naje na karasa aikin da nakeyi na gyaran dakin. Shine ya shigo yake fadin su yaya suna tambayan ki don ba lalai bane su dawo ta nan din kije kuyi sallama dasu na fita na barshi a dakin. Kudi ya dauka ya fito ya samemu yana fadin suje ko suka fice tare dasu bayan ya gama kwashe akwatinan zuwa motanshi. Nan kofan gidan na dan rakasu suka shiga mota suka tafi ajiyan zuciya na sauke bayan tafiyansu din Allah yaso na hada masu leda su rike don basuci wani abin kirki ba ga abinda na aje masu a falon na motsa baki. Na tattara kayan na koma daki na kwanta tunda yace min sai yamma zai dawo gida don haka ba sai nayi abinci ba ke nan. Akwatuna shiddane suka fita dasu zuwa can gidan sai wasu jakkuna ban kuma tambaya ba tunda ya fada min kanun zancen cewa zasuje dasu yaya can gidan kai masu kayansu na tausan gaba irin da wasu mazan arewa keyi idan sun karawa matansu abokan zama. GIDAN IYA Gidan iya kamar yadda na samu suna kiran gidan da haka suna isa da mota Saiba da Saare suka hango tsaye saareb na magana kamar cikin fada. Ita kuma Saiban tana gyada kai ya kallesu yana fadin kingan suko yaya yarinyar nan Saratu na rasa meke damunta sam bata da tunane wallahi. Saratu ai kowa yasani ita da wana matar taka kansu a hade yake ranan da aka kawo yarinyar nan saida Iya ta shiga rigan arzikin ta a cikin mutane tayi mata kaca kaca ta shiga hankalinta. Suma a bangarensu ido suka zubo masu saidai basu daina maganan da sukeyi a lokacin ba har su yaya suka fito daga motan suka nufi hanyar part din iya suna wajen tsaye. Shiya fito a karshe daga motan bai ko kallo inda suke ba shima part din na iyan ya nufa ya shiga suna wajen suna shirya abinda suke gani shine daidai gulmata dana yar uwata sukeyi ba wani abuba. Inda Saare ke kara ingiza Saiban akan kada ta yarda ta ban daman da zan samu wurin shiga ga miji don nufin mu mugaje gida ko ? Tunda mu mama ta haifawa yayanta inda saiban ke jin tankar taje gidan ta sameni tayi min tsinanen dukan tsiya don a ganin ta tana iya murzata idan ta samu gamina. Sai saratun ta hana tace wanan su bari idan yaya ya bar garin ko ita zata rakata ayi hakan illa dai ya zageta dama an saba hakan ai kanta. Tasan kuma mama ba zata kyaleshi ya sakata a gaba ba zata tsawata mashi sun dai dauki mataki a kaina lokacin. Saiban ke fadin ita ta rasa me J ya gani a jikina da har yaje ya aureni ba tare da ya tsaya tunane ba ? Keko aiba kai sake bane wanan abin da gani ai aikin asirine asiri mukai mashi muka sameshi ai daba haka ba ai ina ni inashi da za ace wai nice yake aure. Gaisawa aka fara yi a tsakaninsu da iya mama dake daki taji muryansu ta fito suna gaisawan da ita lokacin shima ya shigo. A,a gaku kamar tare kuke tafe mana kun shigo lokaci guda haka mama dubu ke fadan hakan . Sai Anty Rukkaiya tace daga can gidansa muke ai tafiyan nasane dama munzone gun sarakan mu da kayan tausan gabansu. Kaya kuma kayan tausan gaba kamar wani abin bin bashi tunda anyi angama haka ba wani shiri har wani kaya kuma za a zo sayan bakinsu dashi ? Yau aka fara hakan idan mijinki bai maki bake shi yana da ra,ayin yiwa iyalinsa hakan kuma nice nan nasashi yin hakan gareshi ba wani ba. Meye amfanin samu dama idan kana da zarfin yin abu kayisa a cikin lokacinsa tunka lokaci ya kure maka don wata rana sai labari. Kwarai kuwa anty Rukkaiya ta fada daga ta karbe iya dake magana ai har yanzu mama dubu ana hakan ai silan zaman lafiya maigida yake nema ga iyalansa ga hakan. Suna dai ta fadansu dagashi har mama shiru sukayi lokacin kowa da irin abinda yake tunane a zuciyarshi idan yake auna zancen mama da rashin son hakan da yayi din karara. Ita kuma mama sai auna irin yadda dan nata ke kashin kudi akan zancen matansa ko wani lokaci har yaushe ya gama da zancen wanan auren daya dauko balle ya dauko wanan din ? Ina kayan suke yanzu ta fada tana sauke ajiyan zuciya tana kallon yaya Ai don tasan halin Rukkaiya har take ita ba kamar Ai din ba. Suna mota ta bata amsa sai lokacin ya dago yana fadin mama aina jima da sayansu tun lokacin dana hada lefen Rahama suma na hada masu nasu don ban garine ba a kawo masu ba. Allah ya kyauta ta fada tana daukan jug din kunnun kamu da aka dama mata tun safe bata sha ba salima yasawa kira daga falon. Ta fito tana gaidasu ta juya wajenshi yake cewa Salima kira saratu kuje mota kaya na nan bayan mota ku kwaso sai kije ki kira min su Asmau suzo nan. A,a kaiko a can za a kai masu bakaji bahaushe yace tausan kirjiba a yaren mutanen sokoto wanan ai na ban hakkurine ba zasuce dai bakayi masu ba ai iya ta tare da fadan hakan. Kai tsohuwar nan tasan komai wanan gaskiyane mu da mukai masu laifi aimu zamuje mukai masu har daki ko yaya Ai ke fadin hakan. Salima dai tana tsaye yace jeki ku dauko salima ku kawowa su mama su gani kafin a mika masu ya fada yana kallon Salima din. Ta samu saratun zata shigo don su gaisa da yan uwan nasu take fada mata zancen yayan nasu ta wani bata rai tana fadin kaya kuma kayansuwa kuma ? Ni inana sani ta bata amsa a takaice ta wuce ta bata kara furta komai ba zuwa wajen motan nasa ta bude bayan motar da dama saida ya bude ya fito. Dankari kayan su waye haka wai ta kara fada tana karasowa wajen motan ita dai salima takaicine ya kume ta sai gashi ya fito shiya taimaka masu ya fitar suna shiga dashi. A tsakiyan falon iya suka tara kayan shiya shigo a karshe da wani daya dauko ya aje gaban mama yana fadin mama ga naki nan. Yaya Ai ban fada maku tun can cewa wanan na mama bane wanan kuma nasu iya dasu salima ikon Allah kai Jafaru kace yan tausan gaban suna da yawa nikan naga abin da yawa. Salima jeki wacan na wajen ki dauka ki mikawa matar habu duk suka kalleshi ya fuske yayi niyar hakan shiyasa ya fada a gaban kowa yaya Ai wanan nasu Asmau ne idan kun tashi sai su kama ku mika masu. Ikon Allah lokacin abu ayisa kanina kayi kokari Allah ya saka maka da alheri anty Rukkaiya ta fada cikin nuna jin dadinta ga abinda dan uwan nasu yayi. Kai haba ai hakan ya zama riya nime zanyi da wani kayan tausan gaban uwargida kuma da sauri Rukkaiya tace a,a keko maman Habu. Wanan ai sai dan da yasan darajan iyayye da yan uwa yake wanan wani ai kome za aji bai dameshi ba albarka kawai a yanzu zaku saka mashi. Sai lokacin ta sauke ajiyan zuciya tana fadin Allah yayi albarka an gode anty Rukkaiya tace Allah kuma ya basu zaman lafiya ya kawo zuria masu albarka a ciki muzo suna haka kafin shekara. Ya mike yana fadin zan lekasu tare suka fita da salima daga part din ta dauki na Yanda ta nufi part dinta dashi cikin farin ciki. Lokacin anty Rukkaiya ta mike tana fadin bari mu bude muga abin arziki muba ido abincinsa abu yayi kyau wallahi jafar kayi ko yanzu da mama ta yarda tayi wani aurene bayan baba ai a kara haifo muna irin jafaru bamu fushi. Aka kwashe da dariya na mama aka fara budewa sai am barka sukeyiwa kayan turmi biyarne da lace har da dadduman sallah a ciki yaya Ai tace kin gani maman Habu a samu na muna addua kenan tana daga dadduman sama. Turaren ciki suka dan fesa dakin ya dauki kamshi wanan aikin anty salma ke nan gaba daya an yaba komai a wajen . Rigiji rakwaf inji hausawa don Asmau dake zaune a falon tare da maigidan don ita Saiba daki tashige tana jan kamshi. Shiko tunda ya zauna bai daga daga wajen ba yana zaune tare da Asmau da yaran suna hira sai gasu suka fara gaisawa yaya Ai ke fadin ina yar uwar takine ? Tana ciki ta fada tana kallon hanyan dakin Saiban ta yunkura ta mike zuwa kiranta lokacin ya mike ya shige dakinsa ya rufo. Saiga su sun fito tare suka samu waje suka zauna ta gaidasu a tsatsaye da ina wuni suma suka amsa da lafiya. Yaya Ai ta soma magana take fadin to Asmau Nusaiba gunku muka zo wanan kayan nakune na fadan kishiya aci da hakkuri don Allah. Tsuweee Saiba taja wani tsuki da kowa wajen ya kallota yaya Ai cikin rashin damuwa da hakan take fadin hakkuri dai za ayi tunda shi kowa keyi abinda muka gada ke nan. Da fatan zaku zauna lafiya da yar uwar taku itama daga can muke munyi mata fada daidai gwargwado da azauna lafiya don Allah tunda yanzu an zama daya. Yaya Ai zaman lafiya kam ai babushi tunda tun farko ba a nemi a zauna lafiya ba yanzu daidaine J yazo ya auro muna wanan yarinyar a matsayin kishiyar mu ? Haba dai don Allah ayi muna adalci mana don Allah abinda akai muna anyi daidai ke nan ga hakan ? Yaya Ai tace adaiyi hakkuri dama hakan muka gada ai a rayuwan mu tunda mun fito musulmai Alhamdullahi ai kishiya inga hakkuri abokiyar zamace saidai wanda basu gane hakan ba . Yanzu dai ga kayan fadan kishiya nan mun kawo maku don bai zaunu bane ba abayar a cikin lokaci ba a yi hakkuri don Allah. Babu komai yaya mungode Allah ya bamu hakkurin zama da juna mun gode ai muna godiya ta mike zuwa dakinta itama nusaiban ta mike tabar wajen a fusace . Anty Rukkaiya tace ikon Allah yar nan da karfin hali kike kuwa kema ai wata kika sama kika shigo kuma tayi hakkuri ba a hakkuri haka aka zauna dake ? Ashe taji sai ko ta dawo tana fadin in ita taga tana iyawa ta zauna ni banga ina iyawa ba dama anzo a fada muna maganane a fakaice yadda aka saba ashe ? A,a Nusaiba kar kice zakiyiwa su yaya rashin kunya a nan gaskiya Salima ta fada don tunda suka shigo da kayan ba wanda ya fita a cikinsu. Wanan hayaniyar yaji ya fito yana fadin wai meye meke faruwane wai haka ? Yana kallon Salima din . ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 4️⃣9️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Shiru tayi ta juya zuwa dakinta cikin hasala ashe baki ciki yar iska ba daki dawo ki maimaita abinda kika fada a gaban yan uwana. Yau in baki mamaki don da kinbar gidan nan na har abada su yaya zaki kawowa rashin kunyar ki sun wuce hakan a wajena balleke. Duk iya shegenki da iskanci ya tsaya akaina amma banda yan uwana don kamar iyayye suke wajena bazan daukar maki wanan iya shegen daki dauko yi a gidan nan ba. In zaki zauna kiyi hakkuri yadda kowa yayi ki zauna idan baki hakkuri kuma kofa a bude yake gareki tun yanzun nan kaji min sakarai mara lissafi ba a hakkuri ke akai hakkuri dake aka zauna koba wata kika shigo kika sama a gidan nan ba. Akwai yar cin aman data fiki keda kika yaudari kawarki kika hana mu zaman lafiya don son kai irin naki ? Yi hakkuri Jafar mu ai mun tashi ke nan muma tunda munyi abinda ya kawo mu. Mu yanzu idan bata so dai ruwanta Allah ya gani ka fita hakkinta ai ba kowani namiji ke wanan ba yanzu don ya kara aure. Yanzu a zamanin nan in bashi ba wani namiji zai kashe maki wanan galarin haka kuma baki shafa masa lafiya ba gidansa ? Shi ya daukesu don ya mayar dasu gida a hanya yayi fada sosai yake fada masu irim damuwan da saiban har asmau suke sakashi ciki. Sai hakkuri suke basu a nan family house suka sauka tare da nasu abin arzikin har yan uwan zaman mama dubu alherin ya shafa. Dama haka yakeshi muddin ya samu kudi sai kowa na tare dashi ya sani don zaibi yan uwa daga daga ya dinga masu dan alheri daidai gwargwado. Wanan yas arzikin yake bukansa kamar an bude masa kofofin arzikinsa ga baki daya shi mutum ne mai yawan alheri. To wanan alherin daya shigo maine yabi yan uwa ya raba masu abin arziki har mazan da yan unguwa abokan arziki ya samu abinda ya basu a lokacin. Kwana shidda ke nan yayi a gidana kuma zai koma washegari don aiki daya taso mai na bussiness dinsu lokacin sun samu kaya irin wanda suke fita dashi waje din zai tafi ya gani. Ance sabo turken wawa a yan kwanakin na saba da yaya Jafar sosai yadda yake jana a jiki hakan yasa na fara sakewa dashi inda ko fita yayi kafin ya dawo na shiga damuwa. Shiko sai shirye shiryen tafiyansa kawai yakeyi daga gidan iya har nan da nike ni kadai abubuwa kawai yake shigowa dasu yadda ba zamu nemi komai ba ke nan a bayanshi. Gwargwado yaya Jafar yana kamanta adalci a dan fahintar danayi mashi yadda yake a tsakanin iyalinshi din haka kuma ina ganin yadda yake mu,amulansa a baya kafin na aureshi. Missalin hudu ya shigo gidan nasu kai tsaye part din iya ya nufa wanan dabiansane yanzu sai ya fara shiga yaga kwanansu ya wuce zuwa wajen matanshi. Saidai ga mamakinshi a nan part din ya samu matan da kowa na gidan zaune inka debe yar uwara da yanzu ke zaman kadaici ita kadai don kamar an hada mata kaine a gidan gabadaya sai salimane ke kula lamarinta. Suna ganinshi sukai tsuru tsuru bakin dayansu kallo daya yayi masu ya fahinci akwai matsala haka ya daure ya gaida mama da iya ya samu waje inda saratu ta daga ya zauna yana fadin. Lafiya dai ko ? Ina fa lafiya Jafaru fitina su wa yan nan ai bata kwana a wajensu ko yaushe tsaye take suna figanta. Wai kayan nan daka shigo dasu suke fada a kai yakai harda bugaiya suna nema su illanta kansu sujawa mutane aiki. Fada kuma akan me iya to gasu nan dai kaji a bakinsu ance waka abakin mai ita yafi dadi dama. Duban inda suke zaune yayi yana fadin ke Asmau ya akayine tace ina daki Nusaiba ta sameni wai na rage kayan nan dakai muna su yaya suka shigo dashi. Wai da suka tafi na hurhura kayan cikin na kwashi masu kyau nabar mata marasa kyau don haka in fito da nawa ta dauki abinta niko bansan wasu kaya dana dauka a cikin nata ba. Innalillahi ya ambata a fili ya katse mata zancen da fadin iya kayan nan komai iri daya aka saka don gudun haka yanzu haka kayan haihuwan ita asmau suna nan aje don kada tazo ta haihu ban kusa a girsheni don hakane ban kawosu gidan nan ba na aje. Amma kuma wai kinji abinda wanan mara hankalin take fada yanzu komai fa kala dayane a cikin akwatin saidai a banbanta kala kawai . Samu sukayi aida Allah bai kashe ya basu kai ba daka zama bawan matam da basu godewa irin hakan ba zai faru ba to sun samu sai suyi iya shege ai mama ta fada cikin kunan rai. Mama laifine yau na samu banwa iyalina ba au duniya saita zageni kan hakan to ya zama laifi kan a wajen matanka yanzu . Yanzu idan nayiwa Rahama kayan lefe ban masu komai ba ni kaina nasan sai Allah ya tambayeni akan hakan tunda ina da halin yin hakan garesu duk da nasan karshe wullakantawa zasuyi tunda basu iya tattali ba a rayuwansu. Nusaiba baki da tsoron Allah a lamarin ki kayan nan bake kika rokeni ba ganin daman kainane na hado makushi yan uwana da suka kawo kayan nan ranan saida kika nemi yi masu rashin kunya. Don baki da kunya yanzu kece kika dawo kina fadan kayan kuma ke bafa dole bane zama dake Nusaiba koda duniya muka haifa dake kin sani ? Kawune ya shigo yasa yayi shiru bai cigaba da fadan da yakeyi ba lokacin gaidashi yayi ya mike yana fadin mama ni gobe zan koma daga can ina ganin har kasan waje zan fita don mun samu kaya zan bi jirgi in samesu can. To wani kasa aiki kuma kuka samu na fita kasan waje yanzu Jafar kawu ke tambaya yace eh ba wai kasan wajen turawa make nufi ba ai nan ghanane kawai na fadi hakan don ta gane. Ghana ba kawai bane ai Jafar ya fada yana dan dariyan yake a fuskansa zuciyarsa kuma tana mashi tafasa da wanan zancen da yaji don yasan a baya kome jafar din ya samu zai fada mai. Yana fita part dinsa ya nufa Nusaiba ce ta fara mara masa baya ta bishi ganin ya nufi part dinsu yasa ta biyoshi ba tare datayi magana ba . Dakinsa ya nufa ta bishi a baya ta sameshi duke yana daukan wani takarda a drower ya dan juyo jin anshigo dakin ya ganta tsaye a kansa. Yanzu tafiya zakayi baka dawo gidan nan ba kome komu bamu da hakkin ka dawo wajen mune inka gama kwanakin ka a can din. Kwanakina ai bangama ba zan tafi tunda saura kwana daya in mata a gidan ta kinga kuwa ko ita ban karasa mata kwanta ba ke nan ai ? Cabdi wanan ai zaluncine wallahi mu meka maishemune wai yanzu ? Abinda kika maida kanki shina mayar dake Nusaiba ke inkina da kunya har zakiyi wanan maganan a gabana to inama kikaga kunyan balle babu sam baki da kunya don ban taba zaton haka kike ba ai sai a cikin yan watanin nan nasanki tsab. Kome zakace zakace ai tunda anke an baka kasha ka lashe baki yanzu mun zama banza da bamu da amfani mu a wajenka. Au ba wankewa tayi ta ban ba, kaina kafa nasha na lashe ,ai ban tsaya saita wanke bama nina kafa kai na lashe komai da kaina. Lalai akwai kazan uban nan kuwa don gabadaya an sauyaka yanzu har da abinda baka yi ka fara yinsa gidan nan to mu zuba da ita wallahi. Ki dai zuba yadda zaki iya kwasa aurene dai nayi baku da kudin wani na kara aure ba yadda na auroki aka tara shedu haka itama na aurota gidana. Yazo ya wuceta da takardan a hannunshi zuwa falo nan ya samu Asmau ya zauna yana duban takardun nasa saiban ta fito ta sameshi tana fadin. Wallahi duk abinda mutum keyi Allah na ganinsa ka dauko yarinyar nan don ka bakanta muna rai kan abinda bamuyi ba akace munyi. Zancen da abakin yan uwanka mukaji suna fadin ga ciwon dake jikinka shine laifin ka dauka ka dora muna a kai yanzu ? Na fada maki ai zaki girbi abinki koban fada ba yan uwana da suka fada din banji a bakinsu ba sai naki. Badai dadi haka yakai yamma dasu a gidan yabasu kudin cefane dana sauran bukata yayi masu sallama ya tafi ya barsu nan. Ranan da ta sauka gida tayi mamakin ganin gidan a share tsab komai an gyara ba yadda ta saba tafiya ta dawo ta samu gidan kaca kaca ba wanan karon har da abinci aka aje mata shimkafa da miya da salad . Tabarma suka baza a tsakar gida tare da yaranta dake jiran ta bude jakkar tsaraban data dawo dashi ta bude jakka ta mikawa yaro guda kudi tana fadin amso min coca colan kwalba bata gora ba mai sanyi zakace a baka yaron ya karbi dari biyar din ya fita sai gashi ya dawo da kwalban cock din dake nason sanyi a hannunshi. Ya mika mata ta karba tasa baki ta balle murfin ta kafa kai tana zuka gyatsan da yazo matane yasa ta sauke kwalban a bakinta. Ta saki wani uban gyatsa tana hamdallah ta ture abincin gefe daya Aliyu dake gefe zaune ya zubawa uwar ido tun bayan shigowanta gidan yake nazarin abubuwa da dama game da mahaifiyar nasu. Daki ya shiga yasa mata kira take amsawa tare da juyowa ta hangoshi zaune saman kujera yana dakon shigowanta dakin. Saidai bata da niyar tashi daga inda take zaune din don sai hiranta take zubawa tana bada labarin abinda ta gano da wanda akayi saidai ba zancen rabon gadonsu da sukayi da yan uwanta a cikin hiran nata. Daga daki yaron ya kara fadin mama fa sai kanwarsa ke fadin mama yayana magana dake a dakifa tundazun kallon yar tayi tana fadin ina jinsa me zanshigo daki in mashi ? Muna nan zai shige daki yace inzo idan bai iya fadan abinda zai fadi a nan ya bari har lokacin dana taso yaron yana jin hakan ya mike tsaye ya fito daga dakin daidai lokacin mahaifinsu ya shigo gidan shima cikin murna da ganinta yana fadin wai baya batada kada ? Yanzun nan na fita fa ashe har kun iso mun iso malam mun mun sameku lafiya yaya gida da al,amura kuma ? Yana washe baki ya samu waje ya zauna a gefenta yana fadin kunsha zaria dai kam daga tafiyan kwana ukku gaku sai yau din nan muka ganku ? Tafiyane ya kama haka mun tsaya saida akai komai a gaban mu na samu na taso Aliyu dake tsaye dan nisa kadan da bayan mahaifinsu yana mata alama da ido sau daya ta kalloshi ta dukar da kai ta cigaba da magana da mahaifin nasu. Ganin bata kula dashi ba yasa ya fice daga gidan kofan gida ya koma ya zauna yana dakon fitowan mahaifin nasa . Saidai mahaifin nasa yakubu kamar yasan da hakan a lokacin yaki fitowa daga gidan suna can matarsa baraka na mashi hiran yadda zama nasu ya kaya a lokacin. Ya gyada kai yana fadin mena fada maki a baya malamin da naje wajen kafin ki wuce aiya fada muna zai bayar da kudin ba tare da yayi gardama ba. Yanzu dai aikin gane gaskiyan da nake fada maki cewa kune mata aka tauye su suna amfana da kudin ku sun gina kansu sun bunkasa sun barku a cikin wahala. Idan ba yasan ya samu ba wanan kudin za ace an tarawa wanan uban riban haka mai yawa ya dade yana moriyan abinsa shi kadai ba tare da kowan ku ba. Hakane ai kafin naje na samu saratu ta zuga mama sosai har mama ta yarda da zancenta cewa da dukiyan mu yake wanan abubuwan tunda ba binkcike akeyi kansu ba. Shima kawu daya zo haka yace da mama din shiya bada karfin gwiwan da har aka samu aka zauna komai kudin kowa ya fito a cikin mu. Yanzu kuma ai sai ya samu wanda zaiyi facaka dashi da yake dauka yafi kowa yaron nan baida kirki ina fada maki baki yarda yanzu ai gashi kin gani dama kyautan rufe baki yake maku don kada a tambayeshi kudin nan. Jafaru fa kafansa ya dafa kasa malam har kyautan gidaje naji yayiwa Habu da Yazid a wajen kufa ya tambaya da sauri tace mu ai matane ba zai bamu gida haka bakatan ba. A,a lalai dole ya kawo maku kudi haka masu yawa ya toshewa kowa baki amma ki rubuta ki aje zai dawo daga baya yana maku dadin baki ku hada kai a bashi yacigaba da juyawa . Cabdi yana da wuya hakan don yadda akayi din nan banjin zai karbi kudi a hannun wani kuma nasa kason ma jiya muke ji da dare wai yace a buge massalacim kofan gidan mu din nan a tayar da wani Allah ya kai ladan hakan ga baba. Kaji dan duniya ya fada yana mikewa yau kuma ina mota saratu ta kirani take fada min cewa wai yayiwa matansa akwatuna da mama dasu har iya na tausan gaba din nan da maza keyi. To shi sana,an me yake hakane wai indai ba smogal ko safara yajefa kansa a ciki ba yake wandaka da kudi haka ya kamata a buncikeshi dai gaskiya. Ance sana,an mai sukeyi yanzu kuma naji yana fadawa iya cewa yana kai kayan ma,adaine kasan waje akwai samu sosai ga hakan . Ni yamace yana son ganina kafin na wuce ban tsaya jiranshi ba na taho abina to me zai min yanzu tunda hakkina ya fito a hannusa ba abinda ya rage kuma ai ? Mena fada maki dama kudin nan yake son ya biyoki ya karbe yace ki bashi tunda yaga kamar kece mai taushi a cikin ku. Kofa ya nufa yana fadin ni zan fita me za a zo maki dashi a daidai lokacin wayanta ke haske bata dauka ba take bashi amsa da ba komai saidai dan abu mai maiko haka dai ? Tana duba wayan take fadin ikon Allah jafar dinne fa ke kirana yace aina fada maki zai saka rai ga taki dukiyan ta dauka da sallama tana fadin bari muji me zaice ai. Jafar ta ambaci sunanshi yake fadi a bangarenshi Anty baraka kin tafine ban sani ba ashe saida nazo ake fada min ai kin wuce naso muyi wata magana dake wallahi. Cabdi nikan gani Gusau ai jafaru da yake tunda safe na taso kasan malam bai son inyi tafiyan dare yace hakane to an isa lafiya yaya su malam iliya din suke ? Ta amsa da lafiya yanzu yaya akayi jafaru yace leter on zamuyi magana ai dama zancen Aliyu naso muyi jin hakan mijin nata yayi murmushi yasa kai ya fice Aliyu dake kofa ya fado dakin yana fadin uncle Jafar ne mama abani shi don Allah ? Ya mika hannu ya karbi wayan yana fadin Uncle ina wuni fita yayi da wayan a hannunsa sukai magana ya gamsu da maganan kawun nasa a lokaci. Ya dawo da wayan ya mikawa maman nasa yana fadin yace zakuyi magana dashi ya samu waje ya zauna a gefenta yana fadin. Mama ina ta maki kwantance da kada ki yarda da duk wani dadin bakin da baba zai maki kada ki yarda da baba don Allah . Yana fadin hakan tace babangida banson rainin wayau banson rashin kunya kaine zaka fada min zancen mahaifinka dana zauna dashi. Dana zauna dashi da farko har na haifeku kaine kake zuwa ka koya min dabarun zama dashi din ? Babangida ka fita min a ido tun ban saba maka rai a wajen nan ba wallahi ina ruwanka da sha,anina da mahaifinka ? Kallon mamaki ya bita dashi kafin ya mike baki a laikum ya fice daga dakin har ya nufi wajen fridge dinsu sai kuma ya fasa ya fice daga gidan baki daya Alkawari ya daukarwa kanshi ba zai karawa uwar tasa maganan komai ba dangene da abinda ya hango yana tunkarota kan mahaifin nasu. Yasan tabbas mahaifinsu dabara irin ta miji da mata yake sonyiwa mahaifiyarsu gashi kuma maman nasu ta kasa saurareb shi . Idan ya mata hankaline zai tashi a banza don ba fahinta zatayi ba lokacin saboda dadin bakon mahaifin nasu daya inma bakinshi wajen tsara mutum don haka yin shiru da bakinsa yana kallon irin bidirin da suke zubawa a gidan Tun dawowan mahaifiyan nasu aka tsiro cin dadi a gidan nasu inda baraka sai barin kudi takeyi shiko malam yana manne da ita yana mata dadin baki. Alkawari iri iri da labarai sai fitowa sukeyi a bakin mahaifinsu donshi yanzu Aliyu ya zama kamar makiyinsune a gidan don tun ranan da mahaifinsu yai mashi tas yana fadin ya facin Aliyu din yana bakin ciki da lamarinsa a gidan don haka zai dauki mataki mai karfi akansa yaja bakinsa yai shiru tare da saka masu ido ga duk abinda sukeyi. Babu zancen za a bashi kudin jari ko wanda akai mai alkawarin in an samu za a sai mashi offer wajen aiki da mata garin ma,aikantan gwaunati ke sayarwa. Hakan yasa ya nemi laban kawunsa Jafar ya kirashi yace yazo Zaria ya samu habu sun riga da sunyi magana a kanshi don haka daya taso daga gidan bai fadawa kowa ba sai kanwarsu da yace da ita zai tafi ya nemo kudi ya bar garin. Zarian ya nufo amma kuma ya samu ance Habu don yayi tafiya dole ya juya ya dawo gida ba tare da bukata ya biya ba. Inda Habu yana sane yaki bari ya gana da yaron a lokacin cewan Habu idan anyiwa yaron ai kamar ita Baraka akaiwa don haka taje taci barnan ta a yanzu tunda tace su diya mazan dakin su basu da taimako ko amfani a garesu. Don har matayesu sun fisu dara don akan matansu suke mutuwa ya dawo ya samu mahaifiyar nasu baraka ta dauki kudin daya rage taba mijin nata don ya juya matasu . ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/17, 08:36] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 5️⃣0️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Da dare bayan sallah sallah isha,i ina zaune dakina naji dawowan yaya J hakan yasa dana tabbatar da yashigo na mike na nufo fallo in mashi sannu da zuwa. Ashe sai lokacin yake shigowa gidan da wata yarinya a bayanshi bayan nagaidashi na kurwa yarinyar ido ina mamakin in ya fito da ita ? Shiko ya juya yana fadin shigo mana daga ciki habiba ga maman takima ta fito ai a sanyayye na furta mai sannu da dawowa yaya ? Yauwa Rahama an wuni lafiya ya gida wanan yar yaya Ai ce Habiba na dauko maki rikonta zaku zauna tare a gidan nan. Na daga kai na kara ksllon yarinyar ina fadin Allah sarki sannu da zuwa biba ko don ina jin sunnanta a bakin su anty Nafisa. Ta gyada min kai nace karaso ki zauna mana ina zuwa na mike ruwan sha na dauko mashi nata a babban gora sai ita dana daukowa karamin gora na hado masu da cups na kawo masu. Saidana zuba mai na mika mashi ya amsa yana godiya na mika mata karamin gora da cup itama tayi godiya ya kurbe ruwan yana lumshe ido. Zama nayi daga gefenshi ya kallo Habiba din yana fadin to Rahama ga habiba nan na karbo rikonta a hannun yaya Ai daga yau din nan zamanta ya dawo a karkashina dake zata zauna nan gidan tare dake da fatan zaki tayani rikonta cikin aminci. Ya kara maida hankalinshi a kaina kasa nayi da kaina ina fadin Allah ya tayamu riko yace amin ke kuma habiba ina son ki zauna damu a cikin amana banda wuce gona da iri banson ko kadan inji wani abu ya fito daga gareki don Allah. Idan kina da damuwa ki fadawa Rahama ko menene zata sanar dani ba sai kin fada a gida ba tun yanzu idan kinsan ba zaki zauna damu ki fada in mayar dake in samo mata wata da zasu zauna anan tare din don banson abinda zai taba min zumuncina da yar uwata. Tayi kasa da kai tana fadin zan zauna Uncle yace to madallah sai ki nuna mata inda zata zauna ya kasance shine dakinta a cikin daku nan can biyu. Ya mike ya nufi dakinsa na sauke ajiyan zuciya tare da kallon yarinyar nace taso muje dai kiga dakin duk biyu na bude mata donta zaba ta zabi daya ta dauko kayanta dake falo zuwa dakin. Wajenshi na koma yana tsaye yaba kofa baya yana waje na karaso a hankali sai na fahinci da daya daga cikin matansa yake waya a lokacin. Ban tsaya ba na nufi bandakinsa na hada mashi ruwan wanka da kara tsabtace wajen na fito a zaune yake yayi shiru ya kurawa kasa ido. Ya dago kai ya kalleni nake fadin ga ruwan wanka can na hada maka yake fadin yana kaiwa kwance yace kina shagwabani da yawa fa Rahama ? Zan ji daban daga gobe idan ban kusa dake kwana biyun nan kin shagawabani ina jin nima namijine a yanzu gidansa. Ko ruwan wanka da nasha sai an bani har kinsa na fara zullumin tafiyan nan da zanyi in barki duk daga yarinyar nan dana kawo maki amma nasan hakan ba zai tare komai ba. Daga inda nake tsaye din na danyi murmushi ina fadin ai gara dai a tafi din a nemawa iyali abinci yafi zama a gida ko yaushe. Wallahi har kin tuna min da mahaifin yarinyar nan Habiba ban yake ban labarin su da taimaka masu da yake sonyi ya kara da fadin yana daga cikin dalilin dana dauko yar nan don a rage mata wahala. Idan Allah ya dawo dani lafiya don Allah Rahama ki tuna min a san abinda za a taimaka masu dashi da zai tallafawa rayuwansu na amsa da insha Allah. Ya dan yun kura kamar zai mike sai kuma ya koma ya zauna yana fadin ina ganin dai yanzu ansai duk wani abinda zaki bukata a gidan nan can ma na gama dasu saidai sun bugo waya yanzu suna min korafi wai ban sayo masu gas ba nace Nura zai zo ya dauka yakai masu refilling . Ko har da naku zai dauka din yayo nace nan kan ina ganin ba yanzu ba dan banyi komai dashi ba idan dai ya kusa karewa ayi min magana yazo ya kai maku koda yake bari kawai ya sayo exctra ya kawo maku in case . A take ya bugawa Nura din daya karo mashi exctra a aje ako wani gida har wajensu mama ya mike yana cire tufafin jikinshi na dukar da kaina kasa cikin kunya ina mamakin yadda sam bai kunyana shi sai kice mun jima dashi da aure ko mun jima da sabawa. Ganin ya shiga yasa na tsunce kayan daya cire na adana a gurguje na gyaro dakin na fito falo abinci na jera mashi nakaiwa Habiba nata a dakin. Itama na samu harta sauya tufafin jikinta ta saka wani kodaden rigan barci haka a jikinta sai hula tana zaune tayi shiru nashigo dakin ina fadin har kinyi shirin kwanciya ashe ? Toga abinci nan kici kada ki kwana da yunwa na fito na koma dakina inda na dan zauna in huta yakai kamar awa daya sai gashi ya shigo dakin. Yana fadin badai har kin kwanta ke nan ba Rahama ? Na dan mike ina fadin a,a ina jiran kafito kaci abincine kai nake jiran ka gama sai in kwanta din yace kinci abincin ke nan ke kai na girgiza alaman a,a. Ki tashi muje muci abincin ya fada yana miko min hannun shi dolena na kama muka fito falo duk a tsarge nake kada habiba ta fito ta samemu taga abinda yakeyi din. Wayarshi daya zamo mai kamar rabin rayuce ta shiga ruri ya dauka yana tsoki yake fadin ibrahim ya akayine naji wanda ya kira da ibrahim din yana mashi bayani. Lokacin na samu daman mikewa zuwa kitchen da kayan dana kwashe na abincin da mukaci din dashi . Don dole yake sani gaba sai naci abinci kusan rabin ledan da nake sakawa don shine a yanzu nayi dabaran rage hannu wajen saka abincin. Har ns fito yana kan wayan a cikin dan fada fada yake bayani inda naji yana fadin wai me isa yake nufine haka lokacin na fito ya ya futoni da hannu alaman inzo gareshi. Dole na nufishi hannuna ya kama ya zaunar dani tsakankaninsa yaci gaba da wayansa yana wasa da sumar kaina wanda ni kaina kitson ya fara isata lokacin. Amma shi kuma hakan naga bai dameshi ba illa dadin hakan yake masa gaskiya gyara wani abune dake karawa ma,arauta daraja a idanun junansu wanda sai a yanzu na fahinci hakan. Don yana gama wayan ya kara kai kanshi saman wuyana yana shakan kamshin jikina da ko yaushe ban rabuwa da hakan yake fadin zanyi missing din kamshin nan naki Rahama. Jin hakan yasa na kara narkewa a jikinshi ina murmushi don nidai din na kasa sakewa dashi irin yadda yake min Allah yagani ban san ya zan iya daga ido nace nayi mai hakan ba a lokacin. Monday zaki fara fita school nayi magana da Auwal namu kanin Nafisa shine zai dinga zuwa ya dauke ku har yarinyar nan yana sauke ku a school idan an tashi ya dauko ku ya dawo daku gida saiki karbi key a hannunsa sai kuma washegari ya dawo ya daukeku din. Nagode na fada ya dan yunkura yana fadin ban accout number dinki zan tura maki kudin komai har na man mota da zaki rike a wajen ki. Tafiyan safiya sukayi inda yaya Habune yazo ya daukeshi na fito ganinsu zaune tare suna cika wani takarda yasa na dan koma da baya na lebe a cikin labule ina gaidashi da kwana. Lokacin ya dago yana fadin a,a Rahama antashi lafiya ya gida na amsa a kunyace da lafiya ina su anty Yanda ? Baki barin kira min mata da yanda ko aikece yanda din yanzu ba Maria ba look Habu kabar min matana da surutu taji da rashina da zatayi a yanzu kusa da ita zo Rahama ya fada saidai na kasa zuwan dole saida ya mike ya biyoni har dakin mun dade a rugume yana lalashina kafin ya Habu yasa mashi kira yana fadin zakabi ta Rahama wallahi ka rasa jirginka ka fito mu wuce kawai malam. Dole ya sakeni yana fasin zamuyi waya na amsa saida yaya habu ya fita na iya fitowa falon na dan labe ina mashi Allah ya tsare suka fice daga gidan. Sai kuma lokacin naga gidan yayi min girma duk da ga yarinyar nan biba daya kawo min ga kuma maigadi a wajen gidan. GIDAN KAWU Kawu dauda dake zaune yana lissafin kudi jin motsin matarsa hausatu yasa ya maida filo saman kudin ya taushe saidai yayi shuka a idon makwarwa don hausatu taga abinda yake nufi lokacin. Jug din furan data dauko wanda yaji nono da sukari tana ajewa ta mike tana fadin malam meye duniya naga tun shigowan kudin nan ka tsiro wani sabon dabi,a a zuciyar ka. Kana nuna baka son ma inmatso balle insan komai dangane da kudin nan karka manta komai daya faru har kudin nan suka shigo hannunka nice na shiryashi gidan nan ? Kai ya dago yana fadin yanzu me kuma nace ko nayi hafsatu me nace akan kudin nan dole in kula da dukiyan mutane ai don yaran nan kinsan ba kirkine dasu ba. Zasu iya hada kai nan gaba su binciko kudinsu a wajena donshine bani son wasa da wanan kudin kike ganin kamar wani abune hakan ? To yanzu dai ba wanan ba malam ta kai zaune tana fadin kasan dai Allah ne yayi damu zamuci kudin nan muma a gidan nan tunda ya kwatosu ya dawo muna dasu hannun mu. Katseta yayi da fadin to sai akai yaya ta kara gyara zama tana fadin to shine nakema tuni da yaran nan mardiya da dija kasan dakunan su yana son gyara ko kwashi muje din nan na bakin titi da ake kafawa aka kwasan masu zasuji dadi kasan mazan yanzu basu son ganin daki ba komai sai wullakaci da raini ya shiga tsakanin miji da mata. Ko wani miji dai a yanzu so yake yaga wurin kwanci gyarare da kuma mace mai dan maiko ba yar bani bani ba kadai san komai basai na fadama ba . Shi kuma yaron nan sale a samu abinda aka bashi ya huta da yawon tasha din nan da yakeyi idan kayi hakan ni kayi min komai wallahi nasan naci a gida ni in koshi tunda kai naga ba irin mazan zamanin nan bane da suke son ganin daki yana walkiya. Hakane fa to zan duba saidai zancen Sale gaskiya ban maki alkawari ba tunda ko an bashi a wajen shan wiwinsa zai kare don me zan dauki dukiyan mutane in danka mashi da sukarye a banza. Malam yau dai kome sale ya zamo dankane ba a canzawa tuwo suna su wa yan nan daka rike suka zamo abin kwarai ai yanzu sun gujeka sun nuna maka halin yan duniya. A,a hafsatu muka dai nunawa juna mu dasu tunda yakai har yaran nan yanzu kamar sungane me muke kullawa a kansu don gaba daya yanzu Jafaru ya daina fada min komai nasa kinga kuwa kamar ya ganeni ke nan yanzu. A bakin yan gari nake jin wai,wani harka ya samu na ma,adaine shine yaje gun sarki ya gabatar da kansa kinsan ko tunda kikaga hakan harkace babba amma yai bugun gaban kanshi yake gabatar da komai ba tare da sanina ba a yanzu. A,a,a,a aiba ido zamu saka mai ba son mun kwaci wanan dan kudin a hannunsa yanzu dole mu sake shiri a kansa a nemo makashi kamar baya ? Nagaji da wanan abin hafsatu tunda yaran nan ba mantawa sukayi dani ba gara dai in sun tuna dani inci din yanzu abin nan dana rufewa Halima yana damuna a raina tunda duk yadda nabi a karshe dai kwaliya bata biya kudin sabulu ba kan yaran . Kai ke ganin haka malam da badon hakan ba aida baka samu kansu hakan daka gama fadi ba a baya saidai kaima ka koma cikin yan kallo a yanzu. Haka dai ta gama dadin bakinta ta matsa mashi yasha furan yace zai sha don a yanzu ya fara zargin tana mashi asiri don bai iya kyatare zancen hafsatu din har wani shakkunta da tsoro yakeji nata idan ta fadi magana dole a bita koba dadi. Yanzu ko ya daura dammataran kwato kanshi kan abinda ya dade yana buri a zuciyarsa duk da yasan hakan ba karamin abu bane wajensu hakan zai jawo masu. Itama dai a bangarenta mikewa tayi cike da tunanen mijin nata da a yanzu yake kokarin juya mata baya don ganin ya damki kudin da suka dade suna shiryawa akansu sun shigo hannusa yake kokarin juya mata baya a yanzu. Yazama dole ta kara shiri akan malam din don bata tsamaci kudin ba a hannunta zasu zauna ba sai gashi duk da suna wajensa yana kokarin karta ganima da idonta hakan me yake nufi ke nan ? Takai wani lokaci a wajen tana tunanen hanyar da zata fitowa malam din dashi kafin ta mike ta shiga aikin gabanta tanayi tana saka da warwala a zuciyarta. Musalin karfe dayan rana Salimace data gama shirin ta tsab ta fito daga dakin kwanan su da yar karamar jakkar hannunta saidai ganin saiba tare da mama yasa ta kasa magana lokacin ta zauna. Kamar hadin baki saiga mariya ta shigo da abincin ranan data girkawa su mama din ta fara gaidasu iya ke fadin yar albarka yar tofon lada kamar kinsan tun dazun yunwa nake ji wajen nan zaune. Ruwan shayi da biredi mai zaiyiwa mutum a cikinsa ba wani abu mai nauyi da mutum yaci tun safe malalatan yaran nan sunki su girka abin kwarai da mutum zaici har yayi sauransa yaci da safe ya dora a cikinsa don kiuyan banza irin nasu. Amma iya ai kinji ina masu fadan dafa dukan da sukayi jiyan nima ba sonsa nake ba amma tace min wai ta zuba ko dole na kyaleta. Iya bata tankawa mama din ba dake magana tace bude min nan kinji ban iya bude abin nan takecewa maria din data aje abincin gabanta. Maria ta duka ta bude da sauri iya ta kyalla ido kan abincin tuwon alkaba da miyar danyan kubewa sai manyan nama guda biyar da miyan ja da ya cika kulan miyan bata san lokacin da hannunta ya dafa kan maria din ba tana fadin Allah yai maki albarka yar nan ya kareki daga idon mahassadanki alherin Allah ya bi rayuwan ku har karshen duniya. Kaji iya da wani zance shi kuma mijinta daya kawo abincin fa mama ke fadan hakan ? Iyan ta dago tacewa mama din ai kinji jam,i nayi mata ai bance rayuwanta ita kadai ba har kowa nata nake nufi a zancena dubu. Idan nayi mata kamar habu din nayiwa ai don duk daya suke wajen mu daya kuwa iya mama ta kara fada iya dai tace miko min plas in diba kinji takecewa yanda din. Ta mike zuwa kitchen da dauko mata plate koshi saidata tsaya ta wanke tas ta fito ta kawowa iya din ta zuba mata duk saiban tana zaune tana kallon abindake faruwa. Maria din ta mike tana fadin ke kuma gaki da jakka a gabanki mana kamar me tafiya tana cewa salima ? Kamar kinsan tafiya zanyi zan tafi Abuja yau din nan inje in huta da surutun iya da sauri suka kalleta suna fadin Abuja kuma ? Tace ehh gidan Rahama zan tafi dazin mukai waya da yaya yace ya wuce can zani na dan zauna da ita kwana biyu kafin ya dawo nan ai lagos ne gidan kwamacala gidan kowa da kowa can ko ai kinga gidan hutawane nayi. Maria kan tunda ta daga batace komai ba tasa kai ta fita tabarsu nan suna karawa da Salima din da Saiba dake fadin ohh dama nufin ku ke nan ashe gidan hutawane can din. To bari yayan naki ya dawo muji in hakane kowama ai yana son hutu a rayuwansa wa zaku mayar dan kauye bakauyama kun kaita abuja balle mu yan birni. Ke Nusaiba fita batun Salima don Allah shirmenta take fadi shi abujan dame yafi lagos din ? Yafi mana mama Saare ta fada daga gefeb da take kwance ai tunda kikaji Salima ta fada nufin yaya ke nan can ne gidan hutun nasa nan kuma na kwamacala. Wanan karon kingansa gidan nan sosai kamar yadda ake ganinsa idan yana gari komai dai mutum zaiyi ya tuna da Allah . Halan Rahama din tafi wanine ko wata kai da za a tsabareta a gefe daya a rabata da yan uwa akaita can mama don bakiga gidan bane fa shiyasa ba zaki gane gaskiya Salima na tafadi ba irin ginan zamani din ban komai tsone a gidan gwanin ban sha,awa. Kai haba don Allah akan dan uwanki kike fadin wanan maganan haka yar nan iya data cika baki da abinci take fadin hakan ga Saare din. Ta samu ta hade tana fadin shike nan Allah ya bashi ba zai nuna ba akansa aka fara hakan ina nan kukaso ku tozarta shi kuga inda zai saka yarinyar nan yayi maku bazata akan hakan. Yanzu kuma kuna son kakaro wani zance salima tace nima iya bada wani manufa na fadi hakan ba wallahi sheri dai nakewa mariya din ita kuma saare tana son maida zancen babba ta mike zata fita da jakkarta mama tace da ita dawo. Da sauri iya tace ta dawo kamar ya ke jeki Allah ya tsare ki gaida ita sai munzo duk sukai shiru sai Saarece ke fadin toke iya ina ruwan ki ai gara a hanata zuwa din don bata san ciwon kanta ba gidan kanwar bayanta zataje ta tayata zama gototo da ita Rahama sa,artace don Allah ? Ke ya isa haka don Allah mama ta fada a hasale sai saare din tayi shiru amma mama kin daiji abinda ake fada ko a bayan mu yau shi salima ta fada a gabana ko ? Don salima ta fada mijinki ya fada maki hakan wai akankune aka fara hakane miji ya raba gida in kubi a sannu indai Jafarune Allah yai masa budi tunda kukaga hakan koku yana da niyar raba maku din mutum ya kasance mai hakkuri koda yaushe ba gagawa ba zancen yaran nan zaki dauka ya wahal dake a karshe to ki zuba mashi ido inkinji ta tawa. Ta dade zaune kafin ta mike ta fice zuwa part dinsu a hasale take har lokacin tana shiga saiba na zaune tana cin abinci take fadin kinji ni da yar iskan nan Salima ? Me tayi Asmau ta dago tana tambayanta taja tsuki ta zauna tana fadin wai nan gidan shine gidan kwamacala don haka lagos ne nan can kuma gidan daya kai yar iskan nan shine Abuja gidan hutu. Dariya Asmau ta kwashe dashi tana fadin kai lalai salima dai yar takalo zancene yayin da nusaiba din kewa Asmau kallon shasha,sha tace wai ke ranki bai baci bane ? Tace akan me shi kanin miji kana fushi da zancenshine Nusaiba ai lokacin daya gane kana fushi da abinda yake ma lokacin zai kara abinda zai bata ma rai . Ina ruwan mu da Abuja ko lagos tunda nan ma bamu rasa komai ba nifa kinga raina bai baci da wanan abin bacin raina dayane shine ace shi mijin ya juya muna baya ya fita zancen mu bai kulamu bai damu damu ba amma ni duk wanan abin nasan wata rana kamar mu zata koma itama a dai fara aje yaya ki gani itama tabi layin mu din. Kafin tabi kina nufin mu zama yan kallo Saiba ta fada tace dama ai haka abin yake kin sani dole in ankawo wata kayi hakkuri don baka zamanin ka kaina wani ni wanan yasa kikaga ban wani damu kaina ba tunda nasan haka abin yake dama . Ohh Allah hakane ai bansan da cewa ni kadai ke yakina ba gara da kika fadi naji yanzu kai nusaiba ke nan da wani zance kike to ke wanan abinda kikeyi riban me kikaci wajen sa don Allah ? Ta mike zuwa daki tabar Asmau din data bita da kallo zuwa kurewanta tayi murmushi tasan abin ya taba mata zuciya amma ta godewa Allah data taushi zuciyar nata kan abinda take ji din. Da badon yan uwanta da iyayyenta da suka tsawata mata ba da haka zata biyewa Saiba din suyi ta hauka ana masu dariya tare miji dai na kowane ba na mutum daya ba don haka kowa tashi dabaran ta fitar dashi a gidan. Suna isa Abuja direct airport ya nufa dashi don saura kiris jirgi ya tashi yana fitowa daga mota kirana na shigo mashi ya dauka yana fadin. Amaryata ya kike ? Saida na sauke ajiyan zuciya na amsa a cikin sanyin murya da lafiya lau yayana yaya hanya yaya ya habu ya amsa da yaya habun ki lafiya lau yake Rahama to ya akayi. Na dan kashe murya ina fadin ba komai yaya sai dai kewa gidan yayi min shiru ya ba dadi sai naji yace ohh god ko in dawone to ? Ke Rahama ba zai dawo ba ki koyi zama ke kadai mana ita maria da nake tafiya na barta kin fitane da zaki wani marairaice murya da sauri na kashe wayan na kifa kaina a filo. ZAINANB IDRIS MAKAWA [5/17, 08:36] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 5️⃣1️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Saiba kuma ya habu ya fada don ganin Saiba again tana kiran dan uwan nasa a lokacin ya fadi hakan yana mikawa yayan nasa wayan. Ya karba yana mannawa akunnesa yace hello Nusaiba wallahi J sai Allah ya isar muna mucuci kawai azzalumi don yarinyar nan kake kokarin nuna mu ba komai bane a yanzu wajenka ? Yau har yakai a na fada muna cewa wai mu din kayi doping din mu ka koma wajen wace ake ganin tafi mu wallahi kai azzalumine J sai ,,,,, Dakata Nusaiba wanan wani irin zancen banzane kika kirani kina min mara amfani ina kan hanyar tafiya neman kudina ko wani yace daku da Rahama nazo tafiyan nan ? Aiko da itace ba a mussun hakan don zaka iya yin hakan a yanzu tunda ka iya ware ta daga cikin mu ka nunawa duniya tafimu wallahi ka dawo ansan wace za ayi don ni ba zan yarda da hakan ba kaji na fada maka. Ok ai ba sai na dawo ba Nusaiba ko yanzu kije gidan ku ba matsala na sake ki wuf Habu ya karbe wayan daga hannunsa yana haba dai J zaka biyewa haukanta ku zama daya ? Duniya ta zageka a kuma zagi Rahama a banza da bataji ba bata gani ba irin wanan abubuwan naji maka tunda ka kawo zancen auren Rahama a wajena . Nasan dama sai kun kwasa da Saiban sosai akan haka don haka don Allah ka kara hakkuri ka daure ka fita zancen ta kawai kaba banza ajiyan ta don Allah . A zaria ihun da Nusaiba tayine ya tayar da Asmau dake barci a falo ga yara sunyi kaca kaca da falon nasu da shinkafan da sukaci sub watsar ko ina sun zubar da ruwa samab center carpet din duk kiriniyarsu a lokacin baisa ta tashi daga barcin da takeyi ba sai ihun da saiba tayine ya tayar da ita agigice. Lafiya take fada tun kan takai dakin Saiban tayi dirsha kasa tana salati tana shiga take fadin lafiya maman ikiram ? Ita inda ranta yakai shine mijinsu wani abu ya sameshi tunda shine ke hanya a lokacin don haka tasa shi wani abin ya sama dai. Yaya J ne ko me ta kara fada tana matsawa kusa da ita a hasale ta dago ta kalleta tana fadin don Allah ni kin cikani da tambaya shine din. Burin ku ya cika yau tunda ya furta min saki amma ku sani wallahi yadda na rabu da J kowanku sai ta rabu dashi rabuwa na har abada gidan nan. Ba daini akaiwa haka ba to wallahi ki rubuta ki aje na fada maki har bafilatan nan da yar uwarta saina fitar da ita gidan nan dukkan ku . Wai me kike fada hakane don Allah meke faruwane sai wani magana kikeyi kamar wace ta samu laluran kwakwalwa ? Ehh hauka nayi ki fita kawai ki ban waje don Allah Asmau banson gulma tunda kinji meya faru dani ko ? Fita tayi daga dakin kamar yadda tace saidai bata zauna ba part din iya ta nufa ta samu Saare take fadin kijefa ina ganin mutumiyarki ba lafiya tsakaninsu da yayanki Ita da yaya kuma shida bai gari koya dawone tace ina ganin kiransa tayi da cin mutunci dai amma ki daije kiji ko meye ta mike da sauri ta fita daga falon iya din. Asmau takai zaune wajen iya tana fadin Nusaiba bata ji saida na bata magana nace tabar zancen nan taki nasan ta kirashi a wayane sukai cin mutunci ya saketa. Shine wai gaba dayan mu har mariya sai mu bar gidan nan yadda aka saketa daga kawai naje ina bata magana ta dinga fadan hakan akaina. Nasan za akai ga hakan don yarinyar nan bata da kirki ko kadan badai kan dan zancen nan da Salima tayi bane ta hakeshi ta kirashi da cin mutunci. Shine kuwa nasan ma shine iya saiga mata ta fito daga daki take tambayan meke faruwa kuma nan suke mayar da abinda ya faru ta mike tana fadin saki kuma ? Sakifa shi jafar ina ya koyo sakin mace daga dan magana ko da gaske kansa ya burgene ban sani ba kan yarinyar nan ? Wani irin zancene haka ga dan cikin ki dubu hau kika gansa dashi ko me da zaki fadi hakan kan danki dubu akan wanan yarinyar da batayi maki ragowa har kike kokarin aibanta danki ? To iya saki fa shi haka yaga mahaifinsa yayi daga zancen fatan baki zai furta wa yarinyar nan saki dama bai shiryawa fitinan mata ba ya tarasu haka gidansa ? Ki dai gyara kalamin ki ina horon ki da hakan matsalansuce can kinsan irin cin mutunci da tayi masa har aka kaiga hakan ? Saiga Saare ta dawo tana fadin wallahi kuwa wai sakinta yayi ta cikin waya daga magana kawai ya furta wai ya saketa. Gata can zata wuce kaduna yanzu dole mama ta mike zuwa part din ta bata hakkuri akan ta zauna sai kukan da takeyi . Bayan mama ta fitone yarta ta bugo waya take fadin wai ta dawo gida zaman me zatayi tunda yace ya saketa din me zata zauna yi kuma ta dawo gida kawai. Wanan yasa ta fita ba tare da sanin kowa ba tabar gidan zuwa kaduna din itako mama tana ta neman layinsa bata samu ba saina habu ta samu yake fada mata ya sauke j din har sun tafi. Shima gashi ya kusa isowa gida in sha Allahu sai batayi mai magana komai ba ta bari sai ya iso gida din taji meya faru. Koda ya iso ko part dinshi bai shiga ba ta tareshi da zancen cikin mamaki yake fadin saki kuma ita saiba tace sakinta yayi bayan agabana sukai maganan . Zaginsa takeyi tana ja mashi Allah ya isa shi kuma yace taje gidansu ta huta iya abinda na sani ke nan ya faru tsakaninsu. Kunj ko mena fada maku ba yarinyar kirki bace shikan ya juya zuwa part dinsu ya batsu nan ana zancen saiba din a part dinshine Maria ke fada mai abinda ta fada game damu din yace hauka takeyi kila ? Zamfara garin gusau. Kiri,kiri baraka ta hawa Aliyu kudin nan tace ya bari mahaifinsu ya fara juya idan sun kara yawa sai a samu abinda aka bashi shima ya soma nasa sana,an. Tun daga lokacin bai kara magana ba kuma yakawo ido yasa abinda bata sani ba shine shi Aliyu yasan mai mahaifin nasu ke aikatawa don wata bazarawace a nan makwabtansu daya taba nema taci mashi kudi ta koma zurmi tayi aure itace ta fito yanzu kuma bai daddara ba ya koma nemanta gadan gadan . Shine Aliyun yaso su zauna da uwar nasa ya hanata bashi kudin amma taki saurarenshi lokacin take ganin kudin yaron ke son ta mika mashi duka. Shiko Aliyun yadda yaso shine su samu dan fili su saye da rabin kudin rabi kuma ansan yadda za ayi amma batab basira ya kamata ta dauki kudin duka ta mikawa mijin nata da sunan zai fara sana,an hatsi dasu yana shiga kauyuka yana soyowa ya kawo nan cikon zamfara din tayi na,am da hakan. Balle dataga haikam ya bazama kasuwa sai dadi ya kara kashe mata zuciya gashi in zai dawo da dan cafanen su na kauye daga ita har yaran sun canza sosai a yanzu gaskiya. Zamana da anty Salima da habiba ba laifi gaskiya saidai matsalan daya shine banda saurin sakewa sosai har yanzu dai halin nan nawa yana nan a yadda takan fada ita saliman . Idan naje school na dawo ina daki ina hutawa sai dare zan dan fito mu zauna a ci abinci a danyi hira kuma in koma dakin karatu. Wanan yasa take ganin wai banda saki a bakinta nake jin abinda ya faru wai saiba tana gidansu yaya ya saketa. Gabana ya fadi sosai da jin wanan labarin don na tabbatar za ace saboda nice hakan ya faru tsakaninsu niko harga Allah ban sani ba. Nasan dai kafin yayi tafiyanshi yana lagos lokacin zai kirani mu gaisa wani lokacin ma shike tashina daga barci da asuba ko kuma ya kira da safe yana tambayan ko nafita zuwa school ? Amma tunda yabar kasan sai gaisawa yayi wuya a tsakanin mu dashi matsala dayace ban yarda na nuna masu hakan ba don salima tana yawan tambayana shi nace yana lafiya ai. Ranan wreekend ban fita ba ranan ina daki kwance ina barci anty Nafisa tashigo muryansune suna hira falo yasa nafito don mu gaisa da ita. Tunda na fito ta kyala ido ta kalleni take fadin wai wai wai Rahama kece haka wai lalai aure Rahamane sunan naki yabi zancen kinga yadda kika koma wata buleliya dake haka ? Cikon dan kunya nakai zaune ina fadin anty Nafisa sheri zakiyi min kuma bamu haka dake fa tace wallahi Rahama kin canza min lokaci guda ? Anty Salima na nuna ina fadin gata nan itace ke ban dadi na koma hakan ai muka dara gaba dayan mu nakai zaune ina fadin wai anty Nafisa daga barin je in dawo ranan kikai tafiyan ki ? To ai gani na dawo Rahama fitan ne yanzu ban faye sonshi ba mutane sun faye gulma yanzu tin anayi a bayanka har an fara fadama zance kamar mutun shine zai nemo miji da kansa ? Allah shiyasa banson fita ko ina aiko gidan iya ni tun bukin ki ban kara taka gidan nan ba har yau nocking din kofan da akeyi ya katse mata zancen. Habiba ta mike ta fita don ganin waye sai gata ta juyo tana fadin matar Uncle ce da wasu kafin ma ta gama zancen sun fado dakin cikin gadara da wani irin kallo. Duk da gabana ya fadi don ganinsu a lokacin saidai ban nuna hakan a fili ba naji wata daga cikinsu tana fadin a,a lalai kan Abuja ? Tunda na mike ban tsaya mu gaisa ba kitchen na nufa na dauko ruwa da abinsha na kawo masu tare da cups na aje a gabansu naji dayan tace to aimu ba ruwa mukazo sha ba. Haba dai kusha ruwa mana na sake fada cikin danjin nauyisu sai naji saiban tace ainan ba gidan da zamu tsaya bakunta bane balle a kama bamu baki musha ruwa. Kashedi nazo maki akan mijina Ramaah ina jin hakan nace to nakai zaune gefen hannun kujeran da anty Nafisa take zaune sama. Sai naji anty Nafisa tana fadin haba dai anty Saiba hakan aiba girman ki bane yaya zaki mata gida kice haka kuma ? Ke Nafisa dakata ban ambaci sunan ki ba dana shigo don haka ki kyaleni inyi da ita, ita da yanzu take ganin takai tunda tasan yadda suka shiga suka fita suka iya asirce shi har ya aureta ? Tunda sun saba da bakar bidan asiri suna mallake mutane har ita ta isa tasa J ya juya muna baya ya daina shiga duk wani harkan mu wallahi bata isa ba ? Daga ita har Maria din da kike takama ta samu habu ta mayar dashi saniyan tatsanku da kowa naku saidai ku tsaya ga habu shida kuka sama amma baku kai can ba wallahi. Ashe nakai har na usa kuma ke nan tunda har na iya mashi asiri daya kamashi don da bakiga hakan ba da baki tako har nan zuwa min kashedin ba ? Daga daga inda nake zaune nake fadan hakan tare da jin duk wani tsoronta da shakkunta ya fita a raina lokaci guda. Wallahi ke Ramaah karamar yar iskace baki isa ba wallahi ina ganin hakan na mike tsaye na sake fadin ai isan ya kawo haka tunda gashi har kin tako zuwa gidana ko kunyan hakan bakiji ba ko kin gani gidan ku ? Ta kwashe da wani irin dariya tana fadin wai gidanki kuji min yarinyar nan fa kije gidan mana idan kin isa mara kunya kike da gaske kije gidan ? Gida kan ko yau nake son zuwa zanje don baki da wuta baki da aljanna akaina Nusaiba kuma gida ba naki bane don haka baki isa ki hani shiga ba. Bansan ya akayi Salima ta kira mama ba na daiga tana fadin wallahi mama muna zaune suka shigo ita dasu anty ikilimanta. Niko ina fadin ai bansan kin dau abinda zafi haka ba dana rigaki yi maki takaka a gidan inga abinda zaki min din ? Haka kikace zan dawo ko don ki wallahi nace ki dai dawo don mijinki daya ajeki amma ba dai niba basan da tsiya kikazo ba dana tareki dashi tun farko ? Yanzu da kika sani ai sai kiyi wace zakiyi din tunda kin sani ke dai da tsiyan ta kawoki ai ina sauraren ki ? Anty salima na fadin wai ba zaku daina ba don Allah ke saiba duk inda akaje baki da gaskiya tunda ke kikazo har gidanta . Kaji wata munafuka na amsa da fadin munafuka tafiki Nusaiba ? Saida ta kalloni cikin mamakin jin abinda na fada nace keda kika yi munafuncin daya ciki kika fada ciki inkina ganin kin iya sheri an fi wallahi. Koda yake ba abin mamaki bane ai tunda dama kowa ta dalilin sheri da munafunci ya sanki a gidan. Don kawarki kikaiwa kwancen miji gashi har kina nuna kinfi son mijin fiye da ita a yanzu kin dauka zakiyi min sherine yaje a banza ko gobe kika kara min sheri zakiga fiyema da hakan wallahi. Sam ban yarda na raga mata ba kamar yadda anty Salma ta fada min inyi a duk wace tayi min takaka a cikinsu in debe tsoro da kunya inyiwa maishi tas don gobe karta dawo min gida . Hakan ko nayi mata don na debe tsorona a lokacin na shafawa idona tako na mayar mata da martani don a debe tsoron juna a tsakanin mu dama ina kule da ita a raina har lokacin. Jin wayan da Salima keyi da yaya Habu yasa suka bar gidan ajata ajani tana fadin bata zuwa ko ina sai taga karyan rashin kunyata gidan . Don naga na samu waje zan kawo mata iskanci zata gwada min ko ita waye ranan don sai ta murjeni kamar filawa nace mudai murji juna dake Nusaiba bari ganin kinzo da wa yan nan wallahi, in kuma kina iyawa ki gwada. Sai kuma ta juya kan Salima da Nafisa tana fadin ku kuma haka zasu kare a gurin bin kanwar baya bayanku don kwadayi da wullakanci . Su rasa wace zasu bi har gidanta saini suje suyi aure yafi masu zama gindin yarinya karama suna zugani ina daukan ni wata tsiyace ? Fadan ya koma namu duka kowa ya fadawa dan uwa maganan dake bakinsa data sani batai hakan ba da har gobe tana da matsayi a wajena na wace ta girmeni kuma take gaba dani a gidan aure. Saidai kash zuciya yakaita da girmanta ya fadi wajen kowa a wanan lokacin don ita kanta bata taba zaton zan iya bude baki inyi mata haka ba. Koda yaya Habu ya iso sun tafi ko yace zai dauki mataki kan hakan agabanmu yakewa maigadi warning da kada ya kara bari wanan matan su shigo gidan nan. Anyi haka da kamar sati zancen ya lafane don har kaduna mama taje da kanta suka dawo da ita bayan an tsawata har lokacin kuma shi bai dawo ba kasan saidai da alaman yaji duk abinda ya faru don daya kira yake tambayana cewa bata sake zuwa ba ko ? Na amsa da bata zo ba don yakan kira a sati saudaya ko sau biyu a cikin sati yaji lafiyan mu a dan gaigaisa da jama,a kuma. Hafsatu dake tankade a kofan kitchen taga mijinta ya fito da shirinsa ta bishi da idanu don yanzu gaskiya karara ya canza mata fuska gashi alkawuran da yayi na gyaran dakin yaransu bai cika ba. Wayanshi dayayi kara a cikin aljihu ya tsaya dauka daga kofan dakin nasa ta gane dawa yake wayan don jin sunan mama dubu daya ambata sun dan jima suna magana kafin taji ya soma fadin. Amma ita salima me zatayi da kudi har haka kudin nan fa gaba daya na dauka nasaka a wanan sana,an takin don yanzu kinsan shike shiga da sauri da daminan nan . Kallonsa da sauri Hafsatu matarshi tayi ganin hakan yasa ya karasa saka takalman shi dake kofan daki ya fita ta bishi da kallon tsarguwa. Wani kudi yake zancen yakai sayen taki dashi dazaice hakan amma ai gamu gani badai a kan kudin nan ya matse mata ido da wani hurda ya rikesu gaba daya ya sauya mata. Dakin dake kusa da hanyar bandakinsune wanda iya take rayuwa da a cikinsa kafin a sai wancan gidan da suke zaune a cikinsa yanzu. Shi taga ya gyare fes tayi magana yace bataga ginan ya rankwafo bane kada ya fadi saita yarda da hakan daya fada lokacin. Sunyi hakan da yamma yana cin abinci yake fadin ina ganin fa zamu karu a gidan nan hafsatu amma saidai yadda hali yayi tukun don bamu gama shiryawa ba tukum da bazawar tawa har yanzu. Aiko hafsatun tayi cikin shi da masifa ta inda take shiga banab take fita ashe duk lokacin ankai sati biyu da daura aurensa bata sani ba sai lokacin ya gwada fada mata aiko baisha da dadi ba a ranan wajenta ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/17, 08:36] Buhainat: Seenabu Makawa: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 5️⃣2️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Yaya J saida yayi wata biyu ya dawo lokacin muna gab da fara jerabawa shigowan yamma yayi garin don na dawo school muna falo da salima da Nafisa da yanzu zamanta ya dawo gidan tun bayan rikicin mu da saiba data zo har nan gidana taso yi min yankar kauna. Sai Allah yaban sa,a na aro rigan rashin mutunci na yaga mata nata haka ta tafi tana mamakina shi kuma yaya Habu da yaji ya sameta har gidansu yaci mata mutunci sukayi ba dadi dashi. Amma kuma da mama dubu taji bata ragawa habu din ba don cewa tayi halin kishine bai kamata shina miji har ya saka bakinsa ba yana nufin don ina yar uwar matarshi ya goyi bayana ke nan. Ita batace abinda saiba tayi tayi daidai ba amma sha,anin kishi ba yadda baya zuwa don kowa da irin tasa fahintar kada suce zasu nuna wariya a tsakanin mu tun yanzu. Baidai ji dadi ba amma kalla baicewa mama din ba lokacin ya mike ya fita bayan kwana biyu tasa yaya Ibrahim ya kaita kaduna ta samu iyayyen saiba din ta basu hakkuri kan abubuwan dake faruwa. Sukuma suka dunguma Saiba din suka mikawa hjy bayan tasha fada kan rashin hankalin datazo gida tayi min din ita da yan uwanta. Anty Nafisace ta fara fadin kamar muryan yaya Jafar nake ji a waje donshi na fada maki a baya haka yake maganansa a cikin dan sauri sauri tare da dan sarke harshe kamar me i,i,niya wani lokacin. Don sai ka saurara da kyau zakaji abinda yake fadi wani lokacin saboda saurin magana da Allah ya bashi. Shi din ne kuwa ya shigo yana sallama suit ne a jikinsa arsh colour sai farar riga daga ciki daya dan baiyana fili sakamakon balle anineyan saman rigan da yayi . Har muna hada baki wajen yi mashi sannu da zuwa ya amsa cikin jin dadi hankalinsa yana kaina kai namiji baida kunya wani lokaci. Batare da jin nauyin sisters dinsa ba ya miko min hannu wai inzo inda yake tsaye na noke kaina da sauri a cikin kunya. Kaji bakauya don Allah tashi kije miji ya dawo yana kewan ki anty Salima ta fada tana mikewa tsaye itako Nafisa dariya tayi ta mike itama sai biba tabi bayan su. Hakan ya ban daman mikewa zuwa gareshi don har lokacin yana tsaye ya ware da hannayensa alaman yana jira inzo gareshi din. A cikin wani tako na karasa wajenshi ya mayar da hannun nasa ya rufe na dora kaina saman kirjinsa ina lumshe idona a hankali tare da ajiyan zuciya. Kanshi ya dora a nawa yana shakan kamshin ni,intacen mangashi irin na kanuri da ake hadawa da wasu itattuwa da kayan yaji irin na gargajiya. Mai,ne na kitso mai inganci da ko ancen kasan nasu ba kasafai ake samunshi ba sai kinyi bucking dinsa don mamata aika lokacin anjima ba a kawo ba amma dai ana kawosa naga anty salma ta banye kai tayi kitso dashi. Nima akai min tun lokacin nake jin dadin amfani dashi ina jin ajikina shima hakanne don yadda yake shakan kamshin daga kan nawa a lokacin. Dakinsa muka nufa saman gado muka fada a tare don yaki sakina ya shiga lalubata ganin abin nasa nason wuce gona da iri yasa nayi dabara na shammaceshi nasamu na mike da sauri nabar gadon . A kasalance naga ya koma ya kwanta yayi rigingine yana kallon saman dakin saida na samu na saita kaina nake fadin . Ko ruwa baka sha ba yaya ? Saida ya furzo da iska daga bakinsa yake fadin ruwan da nake son sha an hana min debe kishina naga ya lumshe idonsa sai danyi kasa da kaina ina fadin. Ba a nan ya dace ka debe ba ai tunda ba gidan nan zaka sauka ba koka manta a nan ka tafi da zakai tafiyan ? Ok kawai yace min a takaice ya kara lumshe idonshi nikan na fice a dakin kada shedan ya ribance mu a lokacin. Anty Salma ta fada min duk abinda zanyi ko ma meye kada in yarda in shaga hakkin abokan zamana don alhaki yana waiwayan mutum watarana don haka nake kiyayye wanan huduban nata. Ruwa da cup na shirya a ture nakai mashi dakin inda na samu har lokacin yana kwance a yadda na barshi bai min magana ba kuma har na zuba na fita daga dakin. Duk da banji dadin hakan ba amma ya zama dole in kiyayye hakan kada mu fada ga halaka dama ta fada min su maza babu ruwansu da hakan wani lokaci matukar zasu samu biyan bukatansu. Dakina na koma inda a nan na zauna don kunyan su Nafisa da nake ji lokacin ban fito ba har akai sallah magariba ina dakin isha,i tayi nagabatar still bai shigo dakin nawa ba har lokacin. Wanka nashiga har na fito na shirya cikin wani dogon riga ina sai lokacinne ya shigo yana fadin ba zan samu abinci ba ke nan ma ? Cikin mamaki na dago kaina ina fadin abinci kuma yaya naga ba gidan nan kake ba shiyasa ban hada ba ? Baiyi magana ba ya juya ya fita yana fadin ina falo ina jira hakan yasa na mike na fito falon na sameshi zaune yana waya na shige kitchen din tare da tunane idan na fito zan kara fada mai bafa gidana yake idan ya mantane. Saida na aje komai dana san zai bukata inda naji yana waya yana sanar da yaya habu saidai da safe idan ya shigo yasa na koma gefe na zauna ya gama wayan na dan marairaice ina fadin. Yaya ya dago kai yana gyara kansa lokacin zai soma cin abinci nake fadin ba gidan nan yakamata ka sauka ba . Gidanwa zan sauka ya fada yana yanko loman abincin dake gabanshi yadda ya kalloni yai maganan yasa nayi kasa da kaina na kasa bashi amsa a lokacin don haka naja bakina nayi shiru. Haka falon yayi tsit lokaci guda har ya gama bai kara magana ba ya wanke hannu na mike na kwashe kaya zuwa kitchen. Saida na daurayesu na fito ban tsaya falon ba nashiga dakin su Salima ko wacensu na kwance da waya a hannunta salimane ta dago kai ta kalleni tana fadin. Da har zan maki tsiya ai ince don mijinki ya dawo kin manta damu yau nace haba dai anty Salima shida zai wuce can ya barmu nan tare daku yaya za ayi in manta daku kuma ? Ok a can zai kwana ke nan nace haka ya dace anty tunda da zai tafi daga gidan nan yai tafiya ranan wai wanan dogon lissfin sai ku masu kishiyoyi. Wanan yasa ban ra,ayin auren mai mata wallahi kinga kosu a can haka wata rana sukanyi ta fada akan kwanan nan ko dan zaman nan da yayi a nan da a can kike sai anyi fada a kansa yau . Tundai ace maki wanan Nusaiba da bata aje komai ba sai bakin kishin tsiya don jaraba kullum fadansu dai in yaya ya dawo akan kwanane sai iya ta raba masu gardama. To yaya mutum zaiyi salima in Allah ya kaddara mashi auren mai mata kamar dai irin na Rahama din nan ai kinga kawai za ace mukkadarine auresu da yaya nafisa ta fada. Hakane fa amma dai nikan gaskiya ban iya hakan baki ganin maria ita Allah ya rabata da wanan wahalan daga ita sai mijinta da dansu baki alaikum. Karan rufe kofan da yakeyine ya sa sukai shiru suka dubi junansu cikin mamaki Nafisa tace ina ganin fa a nan yaya zai kwana ?. Nace nan kuma tace to ba gashi ya rufe gida ba alaman ba can zai kwana ba ke nan tunda kinga hakan ? Na danyi shiru kafin in mike na samu yabar falon a lokacin dakina na nufa cikin mutuwan jiki tunda nasan hakan zai jawo min magana sosai a wajen matansa. Bandaki na shiga don na rasa me zanyi lokacin saboda jikina da yayi sanyi da hakan ruwan dumi na surka nayi tsarki dashi sosai na danyi shafe shafena na mata dana dan sani na fito na zauna na kara mulke jikina da kamshi na daban wanda sai nasan miji na tare dani dole zan shafa don ban ma taba amfani da humra din ba bakar humra ce dake da hadi a cikinsa don zaki iya ganin sassaken da aka hada da humran kasan kwalban. Ina bakin wardrobe dinane ina daukan rigan barcina ya kasa hakkuri ya biyoni dakin ban san da shigowansa dakin ba lokacin saida ya tabanine na dan razana ina dagowa. Yana tsaye ya saka hannu ga aljihun rigansa na dago ina fadin na dauka ka tafine ai ba tare dayayi magana ba sai jin nayi ya daukeni cak zuwa gado. ZAMFARA STATE zaune take saman kujera abakin murhu tana tsigan alaihu yarta karima tashigo da kayan islamiyansu a jikinta. Sallaman yarinyar ta amsa ta dago tana fadin har kun dawo ke nan amma yau kun taso da wuri karima ? Ba a tashi ba mama na dawone ta shige daki uwar ta bita da kallo ta juya taci gaba da aikin ta yar tana daki bata fito ba can tasa mata kira ta amsa ta fito tana fadin gani mama ? Kallo yar dake fitowa daga daki tayi ta juya taci gaba da yanka alaihun data tara a hannunta tana fadin ki wanke kwanukan can da aka tara. Ta amsa a cikin sanyin jiki ta sake juyawa zuwa dakin nan ta dakatar da yar nata tana fadin kin shigo sai tukuburi kikewa mutane kamar an maki wani abu ? In baki da lafiyane ai sai ki fada amma kya kamawa mutane hade rai a cikin gida haka mama ni lafiyata kalau karima din ta fada tana shiga daki. Ta fara wanke kwanukan ke nan yan uwanta suka shigo suna hayani suna fadin muna ta nemanki ashe kin dawo gidane ke muga suwaiba tace taga kin nufo gida kina kuka. Tashigo gida tana cicika na tambayeta tace ba komai ita ta sani tunda zurfin cikin tsiya yayi mata yawa ita. Kodai zancen baba kikewa kuka anty Karima kanwarta mai,gado ta fada tana kwabe hijab din ta nan uwar ta juyo tana fadin zancen baba da yai me kuma ? Kallon kanwar nata maigado tayi tana mata alaman kada ta fada amma ina bai mai,gadon taba da amsa ba Zarah ke fadin wai don ance baban mu zaiyi aure ? Wani baban naku baraka ta fada tana sake yukan dake hannunta baban na nan gidan mana mama su Rabi,a ke fada muna dazun da zamu islamiya. Wai har ya biya sadaki satin sama za a daura aure shida anty Safiyan gidan aska . Kirji ta buga take fadin babanku fa tace haka sukace shima baba wallahi ya rasa wace zai aura sai wanan mai zubin yan erea din don Allah ? Mikewa tsaye uwar tayi tana fadin a ina kukaji labarin nan wajen su Rabi,a mama ta nufi daki lokacin ita karima ta mike tsaye tana fadin a,a mama don Allah ina zaki ? Kada kije gidan su Rabi,a tunda a sace ta fada muna tace wai ba,a son gidanmu a san da zancen saidai muji an daura aure kawai wai inkiji ba zaki bari ba. Ni wallahi mama yadda baba yaje yana bataki wajensu shine yayi min zafi. Bata jin me yaran ke fada a lokacin ganin ta fito da hijjab dinta yasa yaran tareta suna hanata fita tare da rokonta da kartaje don Allah dariya za ai mata tunda duk unguwa sun sani ashe . Ke ban hanya gidan uwani zan tafi ta inji kome ke faruwa uwani tasani wata uwani kuma mama uwanin da kullum a nan gidan nata anty Safiya ke tsayi da maza. Da kyar yaran suka hanata fita ta koma ta zauna tayi tagumi tana jin wani irin abu yana rufe mata zuciya lokaci guda. Lalai in wanan zance gaskiyane malam ya cuce ta kuwa da kudin gadonta yake nufi zai auro mata kishiya ? Kishiyar ma Safiya da suka sha artabu da ita kafin ta samu tabar mata miji taje kauye tayi aure ashe data fito din nan ma suna tare bata rabuba dama lafewa yayi don ba ko sisi a hannunsa. Sai yaran suka karasa girkin ranan gashi maigidan yaje kauye cin kasuwa bai dawo ba ko zai dawo sai cikon dare sosai sunkan iso saboda nisan garin da suke zuwa din dauko hatsin. Zancen yaranta gaskiyane Safiya bata wanka ta bushe tana gidan uwani ko yaushe wanan yasa halakansu da uwani din a yanzu yayi sanyi sosai tunda ta fahinci hakan. Abincin da bataci ba ke nan ranan don yadda take jin kanta tana ji a ranta har in zancen nan gaskiyane hakan zai kawo masu matsala da mijin nata kuwa. Bata yarda ta kwanta ba tana dakon jiransa ga wayanta ba caji balle ta kirashi taji yana ina don ta fara tabbatarwa tun a wayan. Shiko a daidai lokacin suna cikin daji motarsu ta lakace masu a daji har barci barawo ya saceta bata san lokacin daya dawo ba sai asuba da yake tayar dasune ta gane ya dawo gidan ashe ? Ta daurene don kada su raba gari da asuba mutane suji hayaniyarsu har yaje sallah bai dawo ba kuma saida gari ya waye tangararan ya nufo gida da ledan kosanshi daya sayo ya hada da kunu. Tana jin dawowan shi din batayi magana ba saida ya samu waje ya zauna yana kiran zarah ta dauko mashi kununsa ga kosanshi ya aje tare da kullin sugar dari aganshi. Baba ba a dama kunu ba yau yarinyar ta fada cikin mamaki yake fadin ba dama ba saboda me ? Lokacin baraka ta fito daga daki tana fadin bandama ba don banjin hakan kana iya zuwa wajen karuwan ka ta dama maka ai ? Karuwa kuma Baraka a ina na sameta kuma ya fada yana mata kallon mamaki tace eeh karuwan unguwa da kuka saba sheke ayan ku da ita mana. Kaje ta dama maka dama ai kun saba da hakan dama malam cutata kaso kayi ka yaudareni kayi aure ban sani ba ? Aff zancen banza ke nan to tunda kinji baraka meye na yaudara a ciki aurene fa sunnan ma,aikin Allah zan raya kike kira da zina ? Lalai malam ashe kuwa zancen nan da gaskene auren kuwa zaka kara wallahi baka isa ba kaban kudina dake hannunka in yaso kaje kayi ta auren ka bai dameni ba ? Kai mata hooo yanzu ke wanan abin yar yakai kiyi min gori a kansa don kawai zan kara aure baraka ? Ai kaji abinda nace ba zancen gori a cikin zancen nan ka bani kudina kawai shine magana tunda da bakai zancen aure ba sai yanzu dana dankama gadona a hannun ka ? Gadon mu dai tunda ko mutuwa kikayi yanzu nida yaran nan muke da gadonki baraka kuma aure ba karya aka fada maki ba aure zan kara kiyi abinda zakiyi . Kudi kuma banda su yanzu a hannuna kin dai gani kema da idon ki sai ranan da kayan nan suka zama kudi na sayar in baki kudin ki. Aina dauka zaki min adalci shekara nawa ina zaman hakkuri dake a gidan nan ban kara maki kishiya ba ashe ban sani ba son kanki yayi yawa har haka baraka. Meye amfanin namiji kama ya zauna kullum da mace daya kamar laya a wuya ba kari kullum kana fama da abu daya kiyi min adalci ma ? Kuka tasaka sosai lokaci guda tana fadin malam ka cuceni ashe duk dadin bakin da kake min don ka karbe kudin nan ne kayi aure ? Kudi ban je gidanku na karba ba ke kika kawo min su nan da hannun ki ko kinga naje gidanku na rokesu subani kudin ki ? In zaki zauna kiyi hakkuri ki dubi diyan ki ki zauna in kuma baki hakkuri Baraka hanya a bude take kya iya tafiya nikan aure ba fashi jumma,a mai zuwa insha Allah. Shi munafukin dan naki daya fada maki bai maki karya ba na biya sadaki da ko mai Safiya tana matsayin matana a yanzu kije duk wanda zaki fadawa na karbi dukiyan ki a garin nan ki fadi bandai je gidan ku na tasa yan gidan ku gaba suban kudinki ba. Don haka ba a hanani ra,ayina a yanzu aurene ba fashi na fada maki na biya kudin komai na al,adan aure. Ya mike yasa kai ya fice daga gidan ya barta nan tana ihu hannu a kai wanan yasa Aliyu dake dakinsa na soro ya fito yana tambayan abinda ke faruwa ? Sai maigadone ke fada masa wai baba aure zai kara kuma da kudin mama fa ta fada cikin wani yanayin damuwa a fuskanta zuciya da rauni. Kasan me kuma yaya wai wanan matarfa yar bala,in shiya baba zai aura na sani ai bashi nake son fadawa mama ba lokacin taki saurarena. Don da bata nan wallahi kullum sai kowa ya rufe gida suna waje suna hira har ana gulmansu a shiya sau nawa ina haduwa da baba wajen mai nama yaje a yanka masa wajen hiran mu ? Cikin kuka Baraka tace shine baka fada min tun lokacin in sani ba sai yanzu da yaran nan suka jiyo sukazo min da labarin ? A,a mama nayi niyar fada maki a lokacin kikaga kamar kudin ki nake so a lokacin kika zageni ni kuma nayi shiru. Shima baba ya dauka zan fada maki tunda duk muka hadu sai yayi min kashedi duk yaji zancen nan a bakin ki sai ya saba min rai ni kuma na share nabar zancen tunda kin yarda dashi. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/17, 08:36] Buhainat: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 5️⃣3️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Kawu daudane zaune a gaban iya data kura mai ido cikin mamaki don jin zancen dayake koro mata a lokacin na karin aurensa dayayi. Saida ta nisa ta sake fadin dauda kace ka kara aure ma,ana har kayi auren ke nan ma ? Wallahi an daura auren yau kimanin sati biyu ke nan don dana tura su baffa neman aure shine iyayyenta sukai karamci tunda ba budurwa bace a daura auren gabadaya lokaci guda. Kwarai kuwa to me za a tsaya jira kace ka fasa hakan ai yayi sosai gara da aka daura din ma yafi sauki yana washe baki yace wallahi iya nima haka nagani. Ehh lalai abu yayi kyau tunda duniya sabuwa fil a yanzu gidan ka dauda ni ba zance kada kayi aure ba don Allah ubangiji ya yardan maka da hakan kaga kuwa ban isa ince don me ba dauda to amma ina fatan ba dukiyan yaran nan kake facaka dashi ba dauda ? Assha iya assha haba ina sane budi daine ubangiji yayi min a yanzu amma dama ina da niyar hakan a raina sai yanzu Allah ya nufa ayi. Wananfa shine damuwata da auren ka a yanzu karka samu dukiyan mutane kana facaka a cikinsa don amana da cancantan hakan yasa suka mika maka. Kaga ko amanace mai nauyi ya hau kanka dauda amana ko wuyan sha,ani ke garesa musan irin wanan amanan dukiyan marayu ba kowane ke yarda ya rika ba. Ina zan yarda iya asalima dukiyan nan basu hannu don ban yarda na ajesu a wajena ba don haka karki ko kawo wanan tunanen a zuciyarki iya. Ai Dubu mutumce samun mai irin halin dubu akan zumunci sai antona gaskiya donshine nake taka tsantsan da komai nasu dake hannuna. Ni dai Ka daiji abinda na fada kayi hankali a samu a rabu lafiya ni tun farko da kunji maganata da ba,a karbi kudin nan hannun yaron nan ba da an barshi dasu ya dinga juyawa a wajensa yafi kwanciyan hankali amma kunce a,a kai da yar uwarka Allah ya sauwaka ya amsa da amin. Sun gama hira zai tafi ya fito da goro manya farare ya aje mata a gabanta yana fadin iya ga wanan na biya na sayo maki da zanzo. Tayi godiya tare da fadin to a dai kula don Allah kuma a hada da hakkuri da iyali baki daya hafsatu dai kasan irin hakkurin da tayi dakai na tsawon shekaru a gidan ka don haka ayi adalci don Allah. Kitchen nake ina hada breakfast don ina son shiga school muna da test amma sai zuwa rana don haka na tashi da wuri ina yan aiyukan gida. Anty Nafisa ta fito ta sameni muka gaisa take fadin ashe har kin fito yanzu nace bari na fito na dora abin karyawa duk da bansan abinda zaki dafawa yaya din ba yau. Murmushi nayi ina fadin ai har na hada anty nagode yanzu ma miya nake son hadawa anjima dana dawo abinci kawai zan dafa. Banjin zankai rana a gidan nan da nace ki barshi amma da wuri nake son zuwa na gyaro dakin mama dan kila yau din nan zasu dawo. Allah ya dawo dasu lafiya na fada ta amsa da amin tace sai kuma zancen salima na jiya don Allah Rahama banson kina damuwa da irin maganganun su don su basu dauki hakan wani abu ba. Da mai mata da mara mata dukkansu biyun zaman lafiya akajawa ba wani abuba don haka kiyi zamanki a dakinki lafiya da mijinki Rahama. Itama Salim din nayi mata fadan irin wanan magana tace wallahi bata san zai bata maki rai ba don haka kiyi hakkuri don Allah dai. Abin tsaman dana dauka na juya dankali na aje ina fadin la anry wallahi ban dauki wanan maganan nata wani abuba sam wallahi. Ita ta tayani karasa aikin har na samu naje nayi wanka da wuri na samu na fito a daidai lokacin da yaya Habu yayo sammakon zuwa gidan. Na gaisa dashi kana na nufi dakin yaya don in fada mashi zuwan yaya Habu din kwance na sameshi yana barci dama yace min barci yake son ya samu ya danyi don ya gaji da yawa. Gashi kuma ya hana kanshi hutu da dare saida na yabawa aya zaki duk wani gajiyansa ya rage saukewa a kaina cikin daren. Na rasa yadda zanyi na tayar dashi hakan yasa na kai zaune a gefen shi a hankali nakai hannuna saman wuyanshi na shafa kana na mayar da hannun akan kirjinsa. Firgigit ya bude idonsa ya sauke a kaina ya dan motsa yana mika yake fadin wallahi nagaji Rahama banda time din hutu a can koda da darene balle da rana. Yaya habu ne yazo yana falo na fada tare da kura mai ido naga ya danyi tsuki yana fadin karfe nawa yanzu na bashi amsa da almost to nine fa ? Kai ya fada sai ya mayar da idonsa ya lumshe zakai wankane kafin ka fita yaya na tambayesa ? Ya bude idonsa yana fadin naso hakan amma bari na ganshi tukun in dawo ya kara kallona yana fadin har kinyi wanka ke nan ? Nayi ina shirin tafiya school ne yanzu abinci na falo na hadama ko bari na hada ruwan wankan kadin ka dawo don nasan fita zakuyi kila ? Na fada ina mikewa ya miko min hannu wai in dagashi dan murmushi nayi din nasan ina ni ina iya daga mutum kamarsa amma banki ba na mika mashi hannun nawa ya jawoni da karfi na fada mashi a jiki ya rungumeni. Bai sakeni ba saida ya dan jahagulani ta hanyar kiss na samu dai ya sakeni yana fadin barin je naganshi tunda korata akayi jiya aka nuna min ba a maraba dani nan . Na samu na mike tsaye ina fadin ba hakana bane yaya tsoron shiga hakkin da ba nawa ba nakeyi ga hakan baidai yi magana ba ya mike shima. Nakai kofan bayin naji yace nasan abinda nakeyi sarai Rahama duk abinda kikaga nayi ina da dalilin yin hakan so ki barni kawai na fiki tsoron hakan a zuciyana. Ni dai banyi maganan ba na shige bayin na fara gyarawa don amfanin da mukayi dashi da safe na wanko na fesa kamshi na hada mashi ruwan dumi na fice zuwa dakin shima na gyara shi fes kafin na fito daga dakin. Tsabta da yake so a zuciyarsa yakai karshe don haka nima nake ban son kazanta ko kadan abu kadan na kazanta yanzune zai tayar min da hankali har tsikan jikina sai ya dinga tashi kan hakan. Tare na samesu suna karyawa dasu don harda Nura ya shigo ashe nasan Nuran tun ban auresa ba don yana da wuya idan yana gari bai tare da Nuran abokinsane sosai shakikinsa. Hakan yasa na tsaya gaida Nura zan shige naji yaya din ba fadin Rahama karfe nawa zaki shiga school ne ina son yin amfani da motarki idan ibrahim ya saukeki ya dawo zan fita da ita don nawa ba zasu shiga ba yanzu sai an wanke min su. Yanzun nan zan shirya in tafi don test zamu rubuta yau Ok ya fada idan ya saukeki sai ya dawo ya daukeni ni dai na shige daki abina. Na karasa shiri daidai yaya Ibrahim yazo don bai saba time gaskiya inba lokacin da yakai mama kaduna dauko Saiba ba shine na biyo motan su Nuratu na dawo gida don basu dawo garin ba sai bayan isha,i a ranan. Nayi tuya na manta da albasa don da ta buga zata kaduna yaya Habu yace yayi tafiya shine mama tace zatabi motar haya yaya habu din yace ta kira ibrahim yazo ya kaita. A hanyarsu ta dawowane mamake tambaya dama makulin motar tana hannun ka ke nan ibrahim yace ehh mama kinsan Amaryan yaya ke amfani dashi ita ake kawai school da motan . Nan saiba taji wani sabon malolo ya tokareta a makoshi har suka kawo zaria bata kara magana ba sai ajiyan zuciya da take saukewa lokacin. Haka shima yaya daya shiga motar ya tayar yake tambayab ibrahim din da zai sauke ya akayi yaji motar a haka don indai iyaka school da yake kaini ai baci ace tana wanan karan ba ? Ya ibrahim din yace ranan da nakai mama kaduna da zata dawo da Saiba shine naji tana wanan kara na so nakaita wajen gyara naji kuma tabar kara yasa ban kai ba gashi kuma yau tanayi again. Da wanan motar kaisu kaduna ina motar dana aje donsu a can yace to ban sani ba nidai mama dince ta kirani inzo da mota in kaisu kaduna ita da saratu shine na dauki wanan na kaisu. Baiyi magana ba ya saukeshi shida Nafisa ya wuce da salima gida sai ganinsa sukayi kwatsam don ba wanda yasan da dawowan shi a gidan. Part din iya ya nufa tana zaune ta gashi tare da salima hannu ta fara tafawa tana fadin lale lale da Jafaru yaushe garin inji maki bako saukan yaushe jafaru da safen nan haka ? Iya jiya na dawo ta amsa da to sannu da zuwa yaya can ta dai shiga tambayansa irin na al,ada yana amsawa da alhamdullahi. Ga uwar taku ko yau zasu dawo sun tafi sokoto duba yar nan da take aure can tun shekaran jiya ko yau zasu dawone oho ? To sun tafi duba hauwa ke nan don yar wajen mamace ke aure a sokoto din akaiwa aiki wajen haihuwa shine suka tafi dubanta sai suka samu tana jin jiki suka kara kwana. Nan dai iyan tayi mai bayani ya mike yana fadin barin leka wa yancan ingansu ai ba gidan nan ka kwana ke nan ba ? Yace a,a iya wancan gidan na sauka yanzu shigowata kenan nan din a daidai lokacin Saratu ta fito daga daki tana fadin sannu da dawowa yaya. Au ke kina ciki ke nan jelar mama aina dauka tare kuka tafi dasu mama din ta amsa da ehh na dan kwantane naji muryan ka nafito. Kaji makira tana daki tun safe bata lekoni ba da badon yar nan matar habu ba wana shashashan data kasheni da yunwa a gidan nan tunda ba iya girkawa zanyi ba ba kafa kasani ta fada tana nuna mashi kafan nata. Saratu din ya kalla yana fadin saratu why zaki barta da yunwa don Allah meyasa kike hakane saboda Allah ? Idan wa yancan basu da hankali ko basu san zafin iya ba saratu ke baki sani bane ashe da gaskiya da ake fadin halaiyarsu kike amfani dashi ?. Yaya kafa san hali iya da surfa komai akai mata ba ai mata daidai ba ni shiyasa na kyaleta baki kyauta ba wallahi ya fada cikin daure fuska ya juya yana tsuki ya fita. Part dinsa ya nufa suna falo dukkan su a lokacin falon dai kamar kullum kaca kaca dashi Asmau ta amsa mashi sallama tana mashi sannu da zuwa. Ya amsa yana tambayanta ya suke da yaran ya dan raba ido ko zaiga yaran bai gansu ba yake tambaya yaran fa tace suna part din habu ina ji. Ok bakima tabbatar dako suna can ba ke nan ina zasu yaya banda can tunda get a rufe yake yaja tsuki ya nufi hanyar dakinshi kai tsaye. Saiban taja tsuki tana magana kasa kasa har yasa key ya bude dakin ya dawo baya yana fadin me kike nema a gidan nan ? Ki koma inda kika fito kinji na fada maki in a serious voice yake magana don bai nuna wasa ko sanya ba akanta fuskansa a daure. Ai saika bari mama ta dawo kaji abinda nakeyi don ita taje ta daukoni har gidan mu Ok zaman mama kikeyi ke nan to ki zauna zamanta din idan hakan yayi maki ya juya ya shige. Asmau ta kalleta tace kema da son rigima kike wallahi Saiba meya kaiki yi mashi tsuki don Allah ta juyo a hasale bayan ta mike tana fadin . Wa,azi zaki min kome ina ruwanki da zancen mu banda munafunci sai Asmaun tace a,a meko ruwana a ciki Saiba ni gaskiya na fada maki kibi abin nan a sannu fadan da yafi karfin ka sai ido ? ZAMFARA Tunda komai ya fito fili yanzu ba zancen boyo a wajen mijin anty baraka kuma ya fito fili yana soyewa da bazawaranshi da ake shirin daura masu aure. Ranan yarta tazo ta fada mata wallahi ga baba can na gani tsaye da Safiya kofan gidansu da leda suna hira duk da hararan da yaiwa yar saida ta fada data shigo gidan. Zuciya ya dibi barakan ta mike ta yafa hijab ta samesu a kofan gidan tundaga nisa ta hangoshi ya turo hula gaban goshi kafanshi daya yana ta cikin zauren gidan daya kuma yana ta waje ya dafa bangon kyauren na gidan. Yayinda bazawaran nasa ke tsaye daga ciki kadan amma ana hangenta waje ta karaso tana huci sai jin muryanta sukayi tana fadin. Macuci azzalumi Allah ya tona maku asiri kaida yar iskan taka yau ya juyo yana fadin baraka hauka kikayi ko me da zaki biyoni nan da rana tsaka haka ? Ba hauka nayi ba daga turu na fito ke kuma macuciya mai laluben ramin labewa ahir dinki da mijina wallahi don ba wajenki a gidan mu. Dakata baraka ki gyara zancen ki kice mijin mu don ya biya sadakina tuntuni in baki sani ba ki sani bakinki ya saba da fasin mijin mu a yanzu. Sadaki ko yaudara kudi garesa balle ya biya sadakinki dashi kudin nawa daya yaudareni yayi min dadin baki ya kawo maki wai sadaki ? Masha Allahu in hakane kema kin samu lada ashe tunda kin taimaka za a raya sunnan ma,akin Allah da kudin ki kai nayi maki murna gaskiya. Ke sakarai wa zakiwa dadin baki a baya badon baida kudin kika kisa ba sai yanzu an samu kudin banza za a dauko min wahala. Ke baraka ki koma gida tun kan ranki ya baci dani wajen nan don zanci maki mutunci fiye da tsamanin ki wallahi mijin nata ke fadan hakan cikin karfin hali ganin jama,a sun fara taruwa masu. Nan dai aka taru aka fara bata hakkuri da ban baki data koma gida tayi hakkuri har ya dawo gida hakan ba mutuncinta bane gaskiya. Dole dai ta hakkura ta koma gida din cikin hasala da mijin da bazawaran tashi tana zage zage kamar mahaukaciya da yawa sun san wanan aure za a daiyi ne amma safiyama bata da halin kwarai. Zata dai bata masu zamane kawai shida matarsa da suke zaman rufin asiri a tsakaninsu shekara da shekaru ba a jinsu ansan itace yan uwanta ke taimakonta take rike da gidan tunda shi ankoresa aiki tunda yayi siyansa dake kalubalanta ta gwaunati aka sallameshi aikinsa yake zaune gida. Yayinda wasu kuma suke jin haushin abinda safiya din tayi don me zata biyoshi har waje tana mashi tonon asiri haka a gaban jama,a ? ZARIA Tunda ya shiga dakin yake bin ko ina da kallo saboda kuran da dakin yayi duk da a rufe dakin yake yabar key din a gidana saida zai fitone ya dauko don idan ya barshi bude har yara suke bari suna shiga mashi suyi mashi barna shine ya soma rufewa ya wuce da key dinshi. Shi ta ina zai iya kwana daki haka kaca kaca donshine yasawa Asmau kira da tazo tana tsaye bayan ta shigo yace ki duba saboda Allah dakin nan yadda ya koma Asmau saboda kazantar ku ? Ki duba don Allah Asmau wanan wani irin rayuwane wai kika zabarwa rayuwanki Asmau ? To yaya ai dakin a rufe yake balle a gyarama yaja tsuki yace kona barshi a bude aiba gyarab zakuyi min ba ? Wanda bai iya gyaran jikinsa bane zai gyarawa wani muhalinsa ki duba yadda kuka mayar da falon gidan nan don Allah ku bakujin kunya azo a samu gida haka don Allah ? Ni idan na saba wanda suke shigowa sun saba da hakanne don Allah baku jin kunya a rayuwan ku ku ki duba jikinki Asmau son Allah ki dubi kanki ki gani don Allah ? Yaya ni yanzu bata gyara nakeyi ba nima tawa ta isheni don Allah falo kuma ko an gyara a bata donshi nima na bari kowa ya zauna hakana in gaskiyane. Bayan haka meye dalililnku na rashin sawa iya abinci da bakuyi har yanzu ya kafeta da ido yana kallonta don son jin amsan da zata bashi. Tayi shiru ya dago yace badake nake bane idan ita Nusaiba bata san darajan iya ba ke Asmau nace baki sani bane kome ? Kinsan fa mama bata nan yarinyar nan Asmau kuma yaushe zata iya girka mata abinda take so wai amma sai lokacin da matar habu tagama girki ta kawo mata zataci ? Ke yanzu bakiji kunyar hakan ba Asmau duk wanda yazo gidan nan a yanzu keya sama amma baki iya tunawa da hakan sai kanwar bayan ku ta tuna tayi hakan ? Yaya kafa san halin iya da surfa in an dafa abinci tace bai mata ba kuma ai ita tace a bar saka mata kada ya zama barna bata iyaci. Shout Up my friend don tace hakan ke baki san tsufa bane ko baki san yakamata bane ? Amma jeki ba matsala wallahi kowan ku will regret it don nasan abinyi a yanzu bai yuyuwa ina kawo komai a gidan nan amma ace ba za a iya girkawa aba kakata for what reason za zaman kashe jikina a banza. Kayi hakkuri yaya za a dinga saka mata idan an girka ko bataci din kayi hakkuri yaja tsuki ya dan kalleta ya juya yana daga filon saman gadon zai kakabd da sauri tana jan kafan don nautin da cikin yai mata ta karba ya fito daga dakin gidan ya fice ga baki daya cikin takaicinsu a zuciyarshi. A ranan mama ta dawo Zarian ita da abokan tafiyanta can family house dinsu suka sauka ganin Nafisa a gida take tambaya take fada mata ai yaya ya dawo jiya shiyasa ta dawo gida. Ko ya dawo aiba gidan zai sauka ba don me kuka dawo yau tayi shiru bata bata amsa ba don tasan halin mama din haka kuma tana gudun hadin hasumi. Saiga Nusaiba ta kirata tana kuka tana fada mata abinda yace ta bata hakkuri tace kar taje ko ina gata nan zuwa gidan ai. Haka yasa ta kwasa zuwa gidan don ta rutsa shi don saiba bata san fitanshi ba tace mata yana nan gida lokacin ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/17, 08:36] Buhainat: {2\25\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 5️⃣4️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Shiya daukoni daga school ranan muna hanyane aka kirashi a waya wai mama tana nemanshi saratu ce ta bugo wayan lokacin ya amsa da Ok ta dawo ke nan ? Tace ehh sai naji yace da ita gani nan zuwa zan sauke Rahama injuyo sai banji dadin hakan daya fada ba a lokacin saboda nasan halinta yanzune zata iya juya zancen ya zama babba. A samu na yamadidi dani a gari ana fadin magana ba dadi a kaina wanda bai dace kamar yadda akewa mutum fatan sheri a yanzu don har jira mutane suke wani sheri ya sameka a fara yawo da sunan ka har garin ku. Muko fulani kowa yasan mu kunya garemu badai tsoro ba dan bamu jin nauyi ko girman abu idan mun tashi yinsa kai Aaye muke abin mu ba boyo . Saida ya kaini din ya sauke ya shiga yaci abinci sanan ya tafi kiran da mama din ke mashi inda ya samu mama ta hau akansa don abinda saratu ta fadi har yaso zama fada a tsakaninsu da salima a lokacin. Saboda lokacin da yace gashi hanya ya daukoni zai kaini gida bayan ta kashe wayan tace ke mama kinji. Wai matarsa ya dauko sai ya kaita gida tukun zai zo wai Rahamace yaya yake kira da matarsa Rahama dai Rahama dai wanan ai abu a fili yake kowa yasan hakan aikin asirine gaskiya. Inba asiri ba me yaya zaiyi da Rahama don Allah wanan bagidajiyar yar kauyen yana da mata kamar Saiba. Aikin banza aiba wayewa akajawa ba hali na gari jarin mutum a hakan yar kauyen yake son abinsa don tafi bashi kwanciyar hankali. Balle ko makiyin Allah a yanzu baicewa Rahama yar kauye don koke tafiki wayewa sanin da dai kikai mamata yasa kika kirata da yar kauye. Tafini fa kikace Salima tace kwarai kuwa abu a zahiri ko kina gardaman hakanne koda yake ba mamaki don kin dade baki ganta bane yasa kike fadan hakan akanta. Ta dai fiki ko keda kika mayar da kanki banza wajenta saratun ta fada sai salima tace kona mayar da kaina banza ba kaina bane farau ai don kafin nayi da Rahama wasu sunyi da Saiba ai duk ko da cin mutuncinta da komai haka naga ana binta sau da kafa gidan nan. Balle Rahama dake ban girmana da mutuntani tasan darajana dana dan uwana da kowa nawa kinga ko kowa na son kyautatawa a rayuwa. Kukan dabi,anku baida kyau wallahi ku zauna kuna cin junan ku kamar kishiyoyi kowa kamar yana jiran dan uwansa ya fincika ? Bama shiba dai su daiyi kokari su kama nasu dakin shi yafi garesu ba shiga tsakanin matan dan uwansu suna saka ido ba iya ta fada. Fada masu dai iya wanan abin takaicin dame yayi kama yara basu san ciwon kansu ba kullun jidali da juna kamar kishiyoyi ? Wanan yasa ran mama ya kara harzuka da zancen dan nata don koda yazo yana mata sannu da zuwa a fusace ta amsa mashi zaice a yanzu hakane tsakaninsu da ita. Mama ance kina nemana ya fada cikin maida hankalinsa a kanta tare da natsuwa yana saurarenta cikin ladabi. A,a ka bari idan ka gama abinda ke gaban ka jafar sai kazo kaji me nake nemanka dashi yanzu ai kana uzuri tunda hankalin ka yana wajen yarinyar nan ayanzu. Kallon bangane ba yaiwa uwar tace ehh ance kace saika sauke Rahama zaka zo kiran da nake magaka shine nace kaje idan baka gama uzurinta ba kagama ka dawo. Mama da Rahama zanzo gidan nan koda aka kirani na daukota daga school zan kaita gidane don da motanta nayi amfani yau na bayar da datawa a wanke min. Allah sarki ita Rahama ashe harda mota ka saya mata su sauran ina tasu take take ? Baga mota a gidan nan na ajiye ba mama haka itama na aje mota ibrahim yana kaita makaranta dashi da sauran laluran gidan. Kadaiji tsoron Allah jafaru kasani dukkansu amana suke agareka baka nuna kana banbanci a tsakaninsu ba haka a fili. Kayi tafiya daga gidanta ka dawo ka kuma sauka gidan ta kayi adalci ke nan jafaru kana son kona kankane da hakan Jafar ? Mama kodana sauka gidanta jiya ai da hujjana na sauka a wajenta don kodana tafi kwanakinta bakwai da Allah yace ayiwa budurwa bai kare ba na tafi wanan yasa na sauka na karasa mata kwana dayan daya rage a can din. Kadai ka sani tunda abin ya zamo bin bashi har kana rankon kwana a tsakaninsu dolene akace kayi mata kwana bakwai dinta tunda uzuri ya kamaka na tafiya ? Wanan shine adalcin Jafar kake ganin su nan zasu fahinci hakan da kayi jahilcine ko tauye hakkinsu akan wata tunda daga gidanta kayi tafiyan? To ita kuma saiba dakace meta dawo yi a gidanka nice nan naje na dawo da ita don banga abinda tayi maka na wanan hukunci ba har da saki ? To shike nan ai mama ta zauna ga gidan nan amma ni abinda ya dace nayi akanta naga yayi don ba zan zauna da mace haka ba tana gurbata min gida. Au ita saiba ce kadai take gurbata maka gida su sauran basu wani mugun hali da baka dauki mataki a kansu ba jafar ? Ikon Allah ke nan kada ya dauki mataki akan iyalinshi dubu wanan wani irin rayuwane wai don Allah gaba daya kina neman hanawa yaron nan walwala a rayuwansa. Shin yar nan daya aurace baki so dashi ko shine yayi maki laifin da har kika tsaneshi hakan dubu don abin yayi yawa gaskiya shima fa yana da hakkin a kanki idan kin tauyeshi da yawa dubu ? Yanzu iya ni zakiwa sheri kina zargin ina zuga mama nice zan zuga mama kuma ? Iyan tace ke ungo nan yar banzan yarinya mara mutunci duk abinda kukeyi ina kallon ku keda uwarki . Ki dubeni da kyau banyi tsufan da ban fahintar komai a yanzu ba nan gabana yanzu kika gama zuga uwarki akan yaron nan har abin yaso zama fada tsakaninki da yar uwarki don haka ki shiga taitayinki dani na fada maki niba dubu bace dake daukan maganan ki. Shiru tayi don tunda taga iya dinbta juye tasan yanzu idan ta matsa ranta zai iya baci don haka tayi shiru, ya mike yana fadin yi hakkuri iya ki barta ai tayi Allah na ganinta. To wanan kalamin da yayine yasa saratu din kuka wai iya taja dan uwanta yana yi mata Allah ya isa kan abinda bata aikata ba. Bayan fitanshima iyan bata kyalesu taci gaba da fada tana fadin ta yaya zaki zauna kina bin maganan yara dubu ? Ko yaushe yarinyar nan ta zugaki kika aikata abinda ba daidai ba aka yaron nan idan aka taliyo sai a iske kune baku da gaskiya. Yaron nan yasan abinda yake yi dubu idan bai isa ba baya tara mata ukku a karkashinsa don haka daga yau ina son ku cire masa ido akan iyalinsa don Allah ? Ku barshi ya zauna lafiya da matansa ku barshi ya tsara irin rayuwan da yake so dasu a gidansa don Allah . Ke kuma duk abinda zakice kice saukin abin dai gidan wani zakije kema don ba a nan zaki tabbata gidin uwarki ba saratu dole dai wata rana kiyi aure ki barta. Kina wanan halin na hade haden fada saratu wa zai yarda da hakan a gidansa in wanan dan uwankine yayi hakkuri ya zauna dake da halinsa can inda zaki fada ba lalai bane suyi hakkuri da hakan. Yarinya tana abu mara kyau kina mara mata baya wanan hali idan tacigaba ba zai haifar mata da mai ido ba nan gaba. Ranan dai bai samu dawowa gidana ba sai kirana yayi yana fadin mu rufe gida ba zai samu dawowa gidan mu ba a ranan. Kishi kumallon mata a take naji wani abu a raina lokaci daya kishi ya rufe min zuciya naji wani irin ba dadi a kasan zuciyata. Zancen anty Salmane ya fado min da take cewa Rahama ki cire ido akan duk abinda mijinki zaiyi akan matarsa matukar kina son ki zauna lafiya ki tsira da aurenki. To sai kin dinga kawar da kanki ga rayuwansa dana matansa kada ki zamo mai bin kwakwafin abinda yake tsakaninsu har ki dinga tada jijiyan wuya akai don Allah. Mace mai wanan halin itake sayawa kanta bakin ciki da kudin ta itake sawa hankalin mijin da kishiya dana zagaye dasu su farga da halinki mara kyau a kan kishi. Duk abinda zakiyi Ramah kada kiyi wanda zaki yarda ki kona kanki ki kona mijin ku don Allah tare da matansa kika sameshi bawai bai sonsu bane ya auroki ? Suma so da kaunace ya hadashi dasu don haka kada ki yarda kuje lahira ana shari,a dake kan namiji don Allah ? Kiyi kokari ki yaki zuciyar ki akan zaman kishi donshi dashi aka halicce mata kishi tun muna kanana muke da abin mu a cikin jinin ko wace mace yake don kishi kamar hassada yake a zuciyar mace sai ka tsira daga sherinsa kake samun haske a rayuwan zaman auren ka. Tayi min irin huduban nan sosai taka min kwantace da kanta tace kingani nan idan D baya gidana kwata kwata nakan cire zancensa a rainane amma da zaran ya dawo gareni kuma ya zama miji sai ranan daya bar gidan nan . Take naji abinda nake ji a lokacin yana ragewa a zuciya inda na fara karanta wallahu Ghalibun har karshe ina jin wani sanyi a zuciyana. Karshe falo na fito nasawa Biba kira ta fito muka zauna nan muna dan hira da ita don mu rage dare karfe tara nace zan kwanta tace to bari ta je daki nace a,a ba zan barki ba ki dawo dakina mu kwana tare tunda ba kowa a gidan. A Gaskiya ina jin dadin zama da yarinyar sosai a rayuwata don gwargado tana da gudun zuciya sosai tun da safe da zaran ta sallame sallah asuba zata fito tayi shara da ta gyaro ko ina har kitchen idan na kammala abinci takaiwa su salima dake daki kwance ta dauko namu zuwa falo muyi wanka muyi shirin fita don tare muke barin gida da ita. Shiyasa nake son shakuwa na tsakani da Allah ya shiga tsakanina da ita tun yanzu kada ta koma tana shakkata har a zata ina mata wani mugun riko. Dakin Asmau ya kwana a ranan don saiba tunda ya shigo ta shige daki a zatonta zai biyota irin da suka saba tun tana jin motsinsu a falon har yakai ta daina ji ta leko ta samu daga shi har Asmaun basu falon a lokacin. Duk yadda taso ta taushi zuciyarta yadda kowa ke bata shawara ta kasa hakan a lokacin cikin daren nan ta kira yarta tana labarta mata abindake faru. Nan dai ta bata hakkuri akan ta bari da safe zata je gun wani malami suji yadda za ayi inya kama tazone da kanta saita san karyan da tayi tazo kaduna din suje tare. Zancen yar uwar nata ta yarda dashi har taji dan sanyi a zuciyarta inda ta kwana tana tunanen daga mijin har mu biyun don ko Asmau ba kyaleta zatayi ba tunda tagane tana munafuntar ta ko ita fitar da ita gidan zatayi ta huta da wata kishiya. Kaiya koda ta samu sa,an hakan ai wata zai dauko mata abinda mata basu gane ba ke nan don Asmau dai bata tare mata komai ba a rayuwanta. Don itace take kwarar Asmau ma idan za a fada tsakani da Allah amma tace dani din da take ganin shigowana gidan da bakar tsafi mu na fulani na juye kan miji ya koma gareni gaba daya yanzu da Asmaun da bata dauka bakin komai ba duk zatai muna kan mai uwa da wabine lokaci guda ta huta. Ita dai butinta shine ta bude ido taga ita kadaice a wajen miji sai yarta ban mantawa da case din da sukayi lokacin akan cikin da Asmaun ta samu ita bata samu ba kafin mijin ya kwanta ciwo. Case sosai akayi don saida kawu dauda shiya yazo gidan da sunan sulhuntasu aka zauna da mijin dasu akai case din. Wai ashe ita Saiba data haihu tace zatayi planning don karta samu ciki yarta karama mijin ya kaita sukaje sukai planning din. Sai gashi kwatsam taga Asmau na laulayin ciki tace sun munafunceta ita dashi ta tayar da bala,i ta hana zaman lafiya a tsakaninsu. Inda planning din ya sako mata reaction dinsa tana jini akai akai nan kuma hankali ya dawo ya tashi sukayi ta zuwa asibiti sai da kyat ta samu lafiya. Bai shigo gidan mu ba don yasan mun fita school sai karfe biyar na yamma yaje ya daukoni school muka dawo tunda na tunkaro motan naga yadda ya kura min ido nasan ya tsargu shima. Ina zuwa kan na bude motan nake cewa dashi ina wuni yaya ya mutanen gida kuma ? Ya dan washe yana fadin shigo mota mana kafin mu gaisa kya tsaya waje kina gaidani muje saimu gaisa a hanya ya bude min nashiga na zauna yaja motan muka tafi. Saida muka hau titi da kyau yake fadin ya kuka kwana nace lafiya kalau yasu mama dasu iya kuma suna lafiya iya ai tace dani wanan zuwan bazan koma ba saina kawota gidanki. Allah sarki nima haka nace ai kafin kabar gari zanje ina son zuwa na gaidasu ai don baka nan ne banje ba amma abin na cikin raina sosai. To dake da ita bansan wa zai fara zuwa ba sai kiyi hakkuri tazo gidan naki inyaso daga baya sai in kaiki ki gaidasu ko ? Abinda kace yaya shi za,ayi naga yayi murmushi ya kai hannunshi saman nawa yana murzawa yace iya sarkin rigima na kula ita kadai ke mara min baya sai salima da Habu game dake Rahama ? Nace to ayi hakkuri kowama zai mara ma idan sun fahince ka daga baya rashin fahintane a yanzu din don anyi masu ba daidai ba ?. Haba dai ni abinda ke ban mamaki dayane shine wai yadda mama ta kasa fahintar manufata har take zargin wai bani cikin hankalinane. Na zata manace zata fara farin ciki da wanan abin sai gashi makiran yaran nan sun shiga sun fita suna neman hadani da ita a yanzu kuma ? Bandai tambayeshi suwaye ba shi kuma bai fadi sunansu ba nace anty Yanda fa da Abba suna lafiya ko ? Wai maria kike nufi sai naga ya bugi bakinshi yana fadin wai sorry sister nake nufi nama rasa yaya zan kirata a yanzu sai abin ya ban dariya nace to ai surukarkace mana ba dole bane saika saya mata suna koka kirata da maman Abba kawai idan kana jin nauyintane a yanzu ? Fine sunan yayi min sosai maman Abba din zaifi sauki an wuce wajen yanzu ai maman Abba din yafi min saukin komai sosai wallahi. Bamu je gida ba naga ya dauki hanyar cikin gari wani waje mukaje ya tsayar da mota dan nisa da mutane ya fita ya shiga wajen . Ya dan jima a ciki sai can na hangoshi ya fito da ledoji ga wani a bayansa sun nufo wajen motar mu kai tsaye ya bude bayan motan aka loda mai kayan a ciki ya sallami wanda ya rakoshi din yana mai godiya. Yana zama yake fadin sorry na barki zaune ko na danyi murmushi na dago kai ina fadin ai baka jima sosai ba ya tayar da motar muka bar wajen. Mun hau titi yake fadin naso na dan tsaya in saiwa Asmau magani jiya taban tausayi sosai da dare shine naso in biya in karba mata magani wajen abokina. Bari dai in saukeki sai in dawo haba dai idan hakan yafi sauki muje mana Allah dai ya sauketa lafiya naji yace amin tana wahala sosai don tace min duk kwanakin nan haka take fama da dare. Allah ya bata lafiya na kara fada cikin rashin wani abu a kasan raina da nake tunane watau a dakin Asmaun ke nan ya kwana ba saiba ba yadda nake tunane da farko na zata gun saiba ai zai sauka ashe ba haka abin yake ba. Munje ya karbo maganin mun kamo hanya yake fadin yanzu da bakowa a gida ita habiba fa dawa take zama ke nan ? Na dan nisa ina fadin nima tunanen da nakeyi kenan a raina don nasan ta dawo tun karfe biyu gashisu anty salima basu gidan yau don da kota dawo suna gida zata samesu. Kai gaskiya hankalina bai kwanta da hakan ba don kinga diya mace ce kuma gashi ba wani gida kuke hurda dasu da zata zauna kafin ki dawo ba. Bayan haka nima ba zanso tana shige shigen gidaje ba gaskiya gara dai din a samo wata mace da idan ta dawo tana gidan tare da ita. Saidai banson kuma ai yawa a hana min hutawa na a gidan koda yake bari zan daiyi tunane akan hakan asan abinyi da zai dace. Mun isa gidan ban tsaya ba son fitsarin daya cika min marata a lokacin na shiga gidan saida na rage maratane na fito na samu ya shigo da ledojin an aje a falo. Biba kuma ta gyara gida har ta dora girki ruwa yana batu tafasa lokacin hakan yasa natsaya na tuka muna dan semo da zamuci. Haka kuma na dibar mata kayan miyan da zata daka muna inyi amfani dashi kana nafito na nufi dakinshi na sameshi yana zaune bakin gado yana waya ganin hakan na juya zan fice dakin da hannu ya kirani na dawo ya nuna min waje in zauna. Zaman nayi a gefenshi dan nisa kadan dashi kafanshi yasa ya tokaro kafata hakan yasa na kalloshi yayi murmushi yake tambayata da hannu wai na kara matsowa na make kafadata alaman a,a. Ganin zai kamuni yasa na mike tsaye da sauri na fice ina dariya kitchen na koma na samu biba ta hada miyan tana soya markade na tsaya na karasa na hada. Ina gab da karasawane naji yasa min kira a falo na amsa na fito bayan na fada mata yadda zatayi ta sauke idan yayi. A zaune na sameshi falon naji yace dani why kike guduna tun shekaran jiya Rahama na fahinci hakan. A,a ba hakana bane yaya ina dai guje muna shiga hakkine shiyasa amma ai ban gujeka ba akan me zan gujeka kuma ? Zonan ya fada yana nuna min kusa dashi duk da akujeran dake gefenshi na zauna a lokacin haka yasa na dan matsa kusa dashi din naji yace Allah sarki. Kisa a ranki mijin ki Rahama ba jahili bane duk nasan wanan kada ki tunanen hakan a kan mu don Allah baice don bake keda girki kada in tabaki ba. Iyaka dai kada mu wuce gona da irine a halaka da har zan shagala in manta da wata a gabana ko a da Rahama ni jafar banyi hakan a tsakanin abokan zamanki ba balle yanzu da shekaruna suka karu. Na san me nakeyi na kuma ji dadin hakan da kika san wanan a zuciyar ki don haka ki saki jikinki idan zaki saka amma tabaki saina taba gaskiya don ni mutum ne mai son hutu a jikin matana dake kusa dani lokacin. Ban daiyi wani magana ba yake fadin ga wanan kayab mana kira habiba ta dauke makushi zuwa ciki ki duba ki gani ban zaunu ba balle na san abinda za a karo maku na amfani. Mun gode na fada yayi murmushi tare da mamakin komai yayi min irin hakan na amfanin gida zanyi mashi godiya kamar ba kanshi yaiwa ba abinda bai saba dashiba ke nan ga matansa. Alam din wayanshi yayi kara ya dauka yana fadin bari yaje massalaci yayi sallah ya mike ashe yana da alwalanshi ya fita. Bayan ya fita na kwashe kayan naga lemukan sha masu sanyi a ciki har naman kaji da dai yan abin makulashe su yughut nakai kitchen na adana na tafi sallah. Bayan isha,i ya dawo gidan abinci nayi mai tayi baiki ba don ya samu biba tana cin nata a falon ya zauna ya soma ci yakai rabi wayanshi yai kara ina aje mashi ruwan sha a lokacin ya dauka naji yace gani tafe ya karasa cin abincin nasa ya mike. Yake fadin zan je gida wai Asmau ce ke jin jiki nace Allah sarki agaida ita dasu mama zasuji yace ya kara min saida safe ya fita. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/17, 08:36] Buhainat: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 5️⃣5️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, A cikin dare muna barci ya bugo min waya saidai wayan tana a silent ban samu dagawa ba lokacin sai washegari ya sake kira har na shirya lokacin naga kiranshi na dauka a zatona zai tambaya ko mun tashi ko kuma yai min ina kwana ? Sai gashi bayan mun gaisa yake min albishir din haihuwar matarshi Asmau data haifi da namiji a cikin dare . Da murnata nake fadin cikin farin ciki lah anty Asmau ta haihu Allah ya raya Allah yasa albarka ga yaron yasa mai akidar addini a zuciyar shi ita kuma uwa Allah ya bata lafiyan shayar dashi sai faman fadin amin amin nagode Rahama yakeyi. Nace a shafa min kan baby kafin nazo ganinsa yace zan shafo maki baki ganshi ba bouncing baby dashi kamana wallahi . Na kwashe da dariyan yake zakice yana gabana a lokacin sai bayan mun gama wayan nake fadawa Habiba zancen haihuwa tayi wani dunkunkun tana fadin Allah ya raya. Abinda su a kullum sukaga mutane sai su nuna basu sanka ba sai ka tsaya kana ta masu dogon kwantance karshe suce owooo ba zasu ba mutum ko ruwan sha ba. Kai habiba kowa da irin halinsa haka suke su halinsune hakana ai tace Allah anty shiyasa muka bar zuwa gidan gaidasu amma da ko wani sallah muna zuwa ai mu gaishesu muka daina. Shiyasa da akace zan zauna a wajenki na zata halinku daya dasu ai nayi ta kuka ina fadin ban zuwa maman mu tace in taimaka inzo kada ran uncle ya baci saida nazo naga ba haka kike ba ashe anty ? Da farko nazone in kwana biyu in koma sai naga ke kina son mutane kina kallon kowa da mutunci kai biba watau daba ba zama kikazo yi ba ashe tayi dariya tana fadin zan zauna ai anty ba inda zanje yanzu. Shigowan ya Ibrahim yasa muka mike gaba dayan mu muka fita ya sauke kowan mu ya juyo kamar yadda ya saba muna a kullum. Yar uwa na taushi zuciyana sosai akan yaya J da matansa ina kuma rokon Allah daya sassauta min zafin kishi irin namu na mata game da zaman takewan mu. Alhamdullahi kuma don ance Allah maji rokon bawane duk da abin dai sai a hankali idan ya kwanto zuciyana ina danjin wani abin lokacin da sauri kuma Allah zai tamakeni abin ya gushe min a kasan raina. Don haka tunane na farayi da me zanje idan zani barka don dole dai inje mata barka kuma zai kasance zuwana na farko tunda na auri ya J wanan zuwan zanga irin tarbon da zan samu daga kowa dake gidan. Bayan mun dawo gida na bude akwatin turamena na dauko wani zani daya dan burgini a ciki na aje saman gado niyata na kara bude na kayan kamshi in hada mata dashi inkai masu . Muna kitchen nida biba ne ya shigo har kitchen da ya same mu muka shiga gaidashi da wuni yana amsawa nake tambayashi maijego yace suna lafiya. Na karayi mashi barka da arziki yayi godiya ya juya zuwa falo ya zauna a nan na sameshi nakai zaune a kusa dashi yace a gajiye nake sosai yau banjin zan kara fita a yau da sauri na juya na kalloshi don nasan ba gidana yake ba da zaice hakan ? Ban gama mamaki ba ya kara fadin hada min ruwan wanka masu zafi in gasa jikina dana dawo sallah naci abinci inbdan kwanta in huta. Sam jiya bam samu barci ba muna asibiti saida ta haihune kusan asuba na samu na dawo gida ban kuma yi barci ba aka kira sallah na fito haka mutane ke shigowa suna muna barka da arziki. Tsam na mike zuwa hada mashi ruwan wankan dayace sai dai zuciyata a cunkushe don na kasa fahintar manufan hakan. Saidai ban sani ba ko zai kintsa daga nan gidanne ya wuce can din zuwa anjima kada in mai mumunan zato yasa na kawar da zancen kasan zuciyata. Har yaje yayi wanka bai kara magana ba nikan na fito naje maci gaba da aiyu kana naji lokacin dayake fadin shiya fita massalaci. Sai bayan isha,i yashigo gidan ina daki zaune a inda nayi sallah ina duba sakonnin wayata ya shigo ya sameni da sallama dauke a bakinsa. Na amsa tare da dago kai ina gaidashi yake fadin abinci zaki ban na dan kwanta kada in fadi a gajiye nake sosai yau wallahi. Na dai mike tare da taimakonshi daya miko min hannu muka nufi falon Biba nasawa kira ta fito daga dakin da take ta sameni a kitchen ina hada abincin abincin ta na bata don yarinyar nada wata dabi,a idan ban bata abinci ba komai yunwar da take ji bata taba diba taci sai lokacin dana bata din. Na fito na jera mashi lokacin har yakai kishingide a wajen yana waya saida na hada komai nayi mai nuni daya fara ci din yaja ruwa ya dauraye hannunsa ya soma ci ina gefe zaune ya kalloni da alaman tambaya inci mana na kada mai kai alaman a,a don na fahinci wayan da yakeyi yana da muhin manci a gareshi lokacin . Zance na miliyoyin kudi yakeyi don haka nayi gudun nayi interrupts dinsa a lokacin har ya kusa gamawa yana kan wayab ina jin maishi na tambayanshi abinci yake cine halan naji yace ehh new wife dina ta hada min delicious nake ci yana dariya yake fadin ko mai nata na bam mamakine ita kamar yadda take ai. Banyi aune ba naga ya haskowa wace yake wayan da itani yana fadin kinganta nan yana nuna mata fuskana nayi kasa da kaina cikin kunya. Yake fadin ku gaisa mana amma bata jin hausa fa turanci zaki mata zance ranan ya fara jin kalman turanci a bakina da abin ya bashi mamaki matuka. Har yake tunane wai ko da gaskene munyi zaman rugga da ake fadin munyi kuwa shifa al,amarin mu yana matukar daure mashi kai sosai wallahi. Kafirace na gane hakan ta yanayin shigarta da nagani suman dokin dake kanta daya zubo sai yanayin rigan jikinta kuma dana kara fahintan ba musilunci a tare da ita. Muka gaisa da ita take fadin gaskiya ina da kyau matuka dole handsome ya rude a kaina ashe a yanzu baida zance sai nawa a bakinsa meye sirin abin ne wai ? Koda yake ga sirin ta gani da idonta ai kurciyata yake diba da yake kara mai karfi take fadin in kara kula da shi sosai don Allah nayi dariya ina mata godiya ya juya da wayan yana cin nama sukaci gaba da magana dashi duk a kaina daine har sukayi sallama suka kashe wayan tasu. Ni kan harna mike ina tattara kayan abincin zuwa kitchen na dawo ya mike yana fadin a ina yarinyar nan take kwancine da cewa habiba yake tambaya ? Tare muke kwana da ita a dakina na bashi amsa yace to a dakina ke nan zamu kwanta ko mu bar mata waje ? Anan zaka kwana ke nan ya kalloni cikin mamakin da ni yakamata ace nayi mashi tunda nasan bai gama kwanakin da zaiwa matanshi a can ba tunda na fahinci two two days ne kwanan namu kamar yadda akasarin musulman hausawa sukeyi a gidajensu wajen raba kwana a tsakanin matayesu. Shi da kansa ya koma ban amsa da anan zan kwana tunda kikaji na fada ai ko akwai matsala da hakan ne ? Nayi lau da idanu ina rausaya kai nace gani nayi dai baka idda kwanakin ka bane a can ai tunda kwana biyu kawai kayi a wajensu ? To anan din da baki son in kwana zan kwana din ya mike ya nufi dakinshi kai tsaye yana barina wajen dana bishi da kallo marata dake dan yankawa ya kara yankawa alaman dai period yana gab da zubo min don haka yake min idan na kusa period akarshen wata. Daki na koma na kimtsa duk da dare baiyi ba sosai a lokacin saida na gama na nufi wajen biba dake takure daki kasancewar shi a gidan na samu har ta soma barci da littafi a hannunta. Dan bugun ta nayi ta tashi nake fadin tashi kije dakina ki kwanta uncle fa ya tafine anty naji ta tambayeni ? Sai nayi dan murmushi nace ba a nan zai kwanta ba yana dakinsa jin hakan yasa ta mike sai kuma tace da dai kin barni nan din in kwana anty ? Bazaki kwana a can din ba shiya kwanta tun dazun ai yana dakinsa hakan yasa muka fito tare zuwa dakin nawa da ban fita ba saida naga ta kwanta na rufo mata kofan bayan na kashe wuta. Dakinsa kodana shiga har ya kwanta kamar yadda yace barci ya soma dibansa na kashe wuta na rufo dakin na kwanta a gefen shi . Na zata barcin nasa yayi nisa sosai yasa nake komai a hankali don kada in tasheshi amma me banfi minti biyu da kwanciya ba naji ya mirgino guna yana rugumana tare da ajiyan zuciya. Saida ya shaki suman kaina dake a daure don ko kitso ban samu yi ba niyata sai zai dawo gidana zanyi kitso din da dan gyare gyare sai gashi abin ya zamo min bambarakwai ban fahinci meke gudana ba a yanzu gidansa. A yadda daina fahinta shine dole akwai matsala tsakaninshi da saiba har ya kawo haka kuma dole wanan matsalan babbane duk da ko suna hakan a da can ba fahinta zanyi ba irin yanzu dana shigo cikinsu dole a yanzu in fahinci hakan a tsakaninsu duk daba hiransu mukeyi dasu ba dashi. Kiss yakaiwa wuyana yana fadin I love you Rahama ina son kamshin nan naki sosai yana min dadi a raina nakan ji kamar bani bane idan na kasance dake haka a yanzu ? Cabdi jam watau gaskiyane anty salma da malam mu na vocatinal center da sukace wasu mazajen kamshi tsabta da iya girki ko iya magana yana sa su kasance da mace har a dauka kamar asiri macen take masu suke rikicewa haka akansu. Anty Salima da saratu sun taba hira mai kama da gulmanshi a gabana ita saratu take fadin takan rasa yaya yake kasancewa da matansa yadda yake dan gaye din nan su kuma san gasu kazamai tun dai Asmau dako wanka yake zama mata aiki koda yana gari zata iya maimaita kaya guda a kwanaki acewanta wai wankin ne yake mata wuya yasa bata saka kaya lokaci lokaci. Sai salima tace ni banga gara ba a dukkansu duk halinsu daya shiyasa sukai abota a school lokacin don kazantarsu iri dayane wallahi. Nayi dan murmushi ina juyowa gareshi nace a cikin muryata dake kara rikitashi love you too yaya J. Naji ya kara kameni yana fadin really ? Uhumm na iya fada don sallon daya saukowa jikina a lokacin haka muka samu raya daren dashi duk da nasan hakkin wata ya dauko ya kawo min amma sanin halinsa nasan yana da dalilinsa nayin hakan a lokacin. Washegari daga school naje gyaran jiki don nasan dole koda yamma ko washegari zanje gidan don haka dole in gyara jikina yadda zan fuskancesu don ba zan yarda inje masu a yakuce ba su samu abin kushewa a jikina duk da kishiya komai haduwan ki saita hango muni a jikin ko cikin shigarki. Kishiya bata taba hango abinda miji ya gani ya auro ki saidai akasin hakan agareki da zata rike a kamin yakarki wajen miji. Ni kaina nasan gyaran yayi ba laifi a shagon yazo ya daukeni zuwa gida sai sambatu yake duk da da farko na hango damuwa a fuskanshi amma muna hada ido dashi duk bacin ran dayayi dakon ya gushe a fuskansa din lokaci guda. Ina zama yake fadin nawa kika biya matan nan Rahama ? Saida na kalloshi nace dubu biyar suke karba sai naga ya bude mota yana fadin ina zuwa ya fita kai tsaye shagon ya shiga na bishi da kallon mamaki ko me zai masu kuma ? Sai gashi tare da matar tana gyara lafayanta zuwa kai tana gyara rufe jikinta tazo gabana tana dariya tace amarya oga ya kara muna kudin gyara fa. Kinga sako yakai ke nan shine na fito inyi godiya a gabanki don gobe ki dawo mu kara cancara mashi ke dakyau fiye da hakan ya shigo motan yana murmushi tare da gyada kai. Har da musayan lamba mukayi da ita a gabanshi yaja mota ya tafi sai wani kallo yake jefo min can yake fadin gaskiya matar nan ta iya gyara sosai Rahama kinga yadda kika kara fitowa fresh dake don Allah meye sirin da suke maku ne anan wai ? Kin ganki kuwa kin koma min yar filonki sak dake haka har yafi irin ganin dana fara maki Allah a ranan dana fara ganin ki haka kawai naji gabana ya fadi duk da a lulube jikin ki yake da wanan katon hijab din da kike sakawa lokacin ? Amma saida naji gabana ya fadi sak ke din na dade ina nema a rayuwata saidai a lokacin wallahi ban kawo komai game dake ba a raina tunda naga kamar Habu yai muna shinge a tsakanin mu ba yadda zai kasance in sameki ? Sannan kisan me wallahi duk lokacin da zan ganki sai dabi,un ki sun burgeni a lokacin don haka nidai kawai kina burgeni duk lokacin dana ganki amma saboda Habu mijin yarkice bantaba kawo komai a tsakanin mu ba dake irin haka ? Ashe ke dinma rabotace kedin daice mafalkin rayuwata Rahama sak yanayin ki da komai naki kalan dana dade ina mafalkine Rahama macen dana mallaka ta kasance a hakan cikin tsabta da sanin darajan kowa na tare dani ta kasance mai biyayya da dokokina Rahama . Sai gashi Allah ubangiji ya kawo min ke a saukake ba tare da wani shan wahalan komai ba Allah ya duba min kuncin da nake kwana dashi nake wuni dashi yaban ke a cikin ruwan sanyi. Wai ace mace don ta haihu ai irin gyaran nan da miji zai shigo yaji dadi amma ina babu shi Rahama yau saida nayiwa Asmau kaca kaca a gaban mutane. Wanan ai sai a zageni wallahi sai ace kaina kawai nake gyara na barsu a wullakance haka idan kai magana kuma ace mutum ya faye fitana. Zasu gyara ka barsu kawai ka daina fadan dan nan da kake masu a gaban mutane don Allah yayi tsuki kawai ya maida hankalinshi ga tukin da yakeyi din saida muka shiga get din gidan nake tambayanshi ? Yaushe zaka kaini inyi barkane yaya kada ace banje ba ko ina bakin ciki da haihuwan yasa ban damu ba ? Saida ya parker mota naji yace gobe baku fita gobe sai ki shirya in kaiku ku wuni can keda habiba ko daga can idan kun gama zaku dawo in biya daku gidan mu ku gaidasu mama can din. Naji dadin hakan yasa nace har gidan yaya Ai sai muje da anty Rukkaiya yace duk a goben Allah ya kaimu lafiya idan da lokaci sai mu biya ai ku gaishesu. Wanan yarinyar ma ai taso taje taga mahaifiyar ta don ban tsamani ai ta tafi tunda tazo gidan nan ko ? Gaskiya bataje ba tunda tace min ta zata ba haka halina yake ba da tazo da niyar komawa gidane sai taga ashe ba haka abin yake ba ? Aina sani ya fada yana bude mota ya fitar da kafansa daya waje yana fadin koda naje daukanta ai da kuka tafito bata so zuwa nan din ba. Sai gata ta fito daga cikin gidan da dan murnanta tana dariyan ganin dawowan mu tana gaidashi ya amsa yana fadin Habiba dagani dai ba zancen komawa gida yanzu ko anty ta karbewa yaya ke ke nan ? Tayi murmushi tana boye fuskanta nace tazo ta dauki kaya a bayan mota lokacin ta juya da sauri zuwa wajen bayab motan ya bude ta kwaso kayan da nake gani kamar na baby ne yaso lokacin. Saida tayi gaba yake fadin abokina ya aiko minsu daga kaduna yau saidana biya na karbo naje daukoki ai nace dama bai wahal da kansa ba tunda ba amfani zasuyi dashi ba sai dai a jibgesu don basu gyara kansu ba balle yaransu. Ni dai nace rabon sune don haka abar zancen nan ai saida naje dakina na rage kayan jikina na fito na hada mashi abincin da muka girka don rana wanda har lokacin yana da zafinsa saboda kyau warmers din nake amfanin dasu. Banyi wani girkin dare ba fruit salad da nama shi muka sha muka hada da naman muka kwanta ni dai ido na kawo na saka kawai ban kara magana ba tunda na fahinci bai son maganan a lokaci amna dole nasan akwai masa dayasa hakan . Washegari ko tunda safe mukayi aiyukan mu don fitan da nasan zamuyi din yana daki yana barcinsa shigowan kawu gidan yasa naje tmna tayar dashi daga kwana. Hakan baisa mun zauna ba shirin mu mukaci gaba dayayi bayan na gabatarwa kawu da komai na koma kitchen don mu rage aiki tunda nasan sai yamma lis zamu dawo gidan kila ranan . Daga kitchen din na ke dan fahintar abindake faruwa zuwan kawo kan matsalansa da Nusaibane don naji yana fadin ai na fada mata saita gane kureta kawu. Ta dauka da wasa nakeyi ko wanan karon ba zanji ta kowa ba tunda ni ba mai tausayina akan matsaloni dasu sai zance ya tashi ace nayi hakkuri don haka in zata zauna ta zauna tunda zaman mama takeyi ni ba zan koreta amma ba ruwana da ita kowa ya sani. Banyi wani abin asha ba don na tare a nan gidan Asmau ce ta haihu don haka ina da inda zanje in huta a yanzu babu takura a gareni kuma kun gani. Kawu din ya tausa murya yana fadin abinda nake son ka gane tunda har mahaifiyar ka ta nuna hakan bai mata ba kayi hakkuri kai Jafar ka shirya da matar ka kada ka shafawa wanan din laifin daba itace ta sakaka yin hakan ba. Sai naji yace kawu ina yarinyar nan dai nine ke auren ta ba wani ba kuma zamana takeyi a gidan nan don haka ina rokon kowan ku daya saka min ido da ita don Allah ? Nidai har kawu ya tafi banji sunyi maslaha akan zancen ba tsakaninsu saidana gama na fito kitchen din nasawa Biba kira daga dakina. Ta shigo ta sameni kayan dana dinka mata don gudun kada a girshemu haka na fitar mata da kala daya komai set da gyalensa da takalma har yan kunne na mika mata ina fadin taje tayi maza ta shirya nasan yanzu yaya zai fito mu tafi. Ta karba da murnanta tana min godiya murmushi kawai nayi ta juya zuwa dakinta don ta shirya din . ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/17, 08:36] Buhainat: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 5️⃣6️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Wasu jajayen atamfan super wax mai dan surkin flower yellow a jikinsu da akai min wani dogon riga yaji kwaliya har yagaji don kyau zakice jallabiyace rigan don yadda aka fitar da shi. Takalman kafata kuma half cover ce ta mata mai duwatsu new design sai gyale yellow mai duwatsu dana yafa hakama kunnena fashion na saka dayai shige da kayan sai agogo a hannuna da yar karamar jakkata yello. Ki firhita kishiya ga shiganki ko ta yaya yafi ace sai mace tagani ga kishiya taji haushi inji anty salma take fada min hakan ko yaushe. Donshi na tsaya na gyara yadda ya kamata ga wani kamshi da nakeyi na ban mamaki a haka na fito na rufe dakina kamar kullum idan zan fita daga gidan duk da muna rufe falon da ko ina amma ban yarda saina kulle dakin nawa kuma hankalina yake kwanci. Ya fito yana waya mukai arba dashi ya sake wayan yana fadin dankari wanan kwaliya haka Rahama ai sai ace yau din ne sunan ma ga baki daya. Yau ba suna bane yaya amma yau din ya kasance rana mai muhinmanci ce a gareni na juya wajen Biba ina fadin dauko basket din da muka shirya ki fita min dashi waje sai ki dawo ki dauki sauran ledojin nan kuma. Ta juya zuwa kitchen din ta fito da basket din dana shirya din da zamu jewasu iya da mama dashi na tsaraba ba komai bane yasa hakan don basu taba zuwa gidana sunci girkina ba yasa nayi wanan dabaran hada masu abincin muje masu dashi. A kofan gidan ma saida ya tsaya yana tambaya meye wanan kuka dauko hakane wai yana nuna basket din da nake gyarawa biba zananshi a bayan mota da take zaune. Na juyo ina fadin iya da mama zan kaiwa girkina suci sai yayi murmushi ya bude mota muka shiga maigadi yana tsaye har muka fita yana muna a dawo lafiya . A hankali yake jan motan har muka kai wani shago ya tsaya yace mu jirashi ya fita sai gashi da drinks na kwalaye masu sanyi saida ya zauna yake fadin ki hada masu da wanan din idan kuje nayi mai godiya a fili. A raina kuma nace Allah na godema da dabaran hakan yazo min nayi wanan abincin don iyayyensa din. Tunda muka doshi gidan na fara jan addu,a a bakina na neman tsari gako wani irin fitina daka iya tasowa ga zuwan namu har ya dosa kan motan zuwa cikin gidan muka shiga. Da Saiba muka fara ar,ba tsaye da wasu matan abokanshi da sukazo barkan haihuwan da farko inaganin bata san tare muke ba saida dayan take fada mata haka yasa ta dago tana bin mu da kallo. Da alama tayi matukar razana da ganina don ba karamin tsoro shigana ya bata ba tagama fada masu akan yar kauye yake son ya wofintar da ita itako zata nuna mashi ko wa take. Sai ga matar Nura na fadin kai Nusaiba kardai ince wanan kike kira da yar kauye ina itace amaryan taku ai ko ? Jin hakan data fada yasa ta dago da sauri ta kallomu tabbas din kuwa nice nake fitowa daga motar ina dariya don cewa da yayi bai ban bakin shiga wurin yanda ba sai wani lokacin nake fadin haba yaya kaima kasan aiko don Abba da akace baida lafiya zan shiga ai yace don kinsan ban iya hanaki zuwa duba babana ko kikace haka ? Part din su iya muka nufa da kayan dana dauko din muka bar saurab a cikin mota don ba anan zanyi amfani dasu ba na abokan zaman mamace da yace zamu je gaidasu daga nan. Shine agaba muna biye dashi mukai sallama muka shiga iya na zaune da tasbaha a hannunta mama na kasa zaune tana waya saidai shigowan mu yasa ta katse wayan da takeyi din cikin bacin rai ta amsa gaisuwan da muke mata din. Don tun kan na zauna na rusuna ina gaida ita kana na juya wajen iya dake fadin kai kakai amaryace yau a gidan namu haka ? Lalai marhabin da amarsu ta ango bakya laifi ko kin kashe yar masu gida kuwa laifinki kadanne a wajen ango nayi murmushi ina fadin iya mun sameku lafiya ya bayan rabo ? Yaki nan ki zauna ta fada tana nuna min kusa da ita a gefen kafan mama dake zaune a kasa din nace a,a iya nan ma yayi min barkan mu da arzikin saukan anty Asmau Allah ya raya muna. Tace amin yar nan haka akeson Allah ya sauke sauran al,umman Annabi baki daya na amsa da amin iya na sake juyawa wajen mama din nace mama barka da arziki ? Ta amsa da barka dai Rahama tare kuke tafe ashe ban amsa mata wanan ba din take fadin barakace ta bugo waya tun dazun suna rikici da mijinta akan kudin ta wai dake wajenshi. Ta fada tana kallon dan nata dake kokarin zama a gefen iya inda tace in zauna da farko din naki. Naji yace jam rikici kuma akan me ba ita tabashi kudin ba son me kuma zatace suna rikicii kan hakan ai dole suyi rikici ya karbe mata dan kudin ya cinye yanzu kuma ya dauko mata kishiya. To meye laifinshi a nan Dubu yayan kima ai kusan haka dinne shima ba aure ya kara yanzu ba da kudin ku ya shiga hannunsa abinda duk nakewa gudu ke nan ai tun farko gashi ko ya faru. Shima kawu aure yayi kome yana tambayan iya din cikin mamaki tace au bai fada maka ba ke nan to ina zai fada tunda yasan bai da gaskiya koshi ? Na juya wajen anty Saratu da fuskanta ke hade kila don zancen anty baraka dinne ko wani abu ke damunta nace anty saratu mun sameku lafiya ? Ta sauke ajiyan zuciya tana fadin ke dai Rahama lafiya kalau yaya gida ya amarci kuma ta fada tana kokarin gyara yanayinta din na farko. Ta dora da fasin wai wanan yar kamar yar wajen yaya Ai ko da cewa biba data aje basket din nace tazo gefena ta zauna itama a kasan da nake zaune din. Itace habiba na fada don ban tsaya wani sanyin da zataga hanyar sakar min wani zance ba don nasan zata iya indai anty saratuce shiyasa na sake ina magana ta bajin nauyin su kamar yadda suke zato da farko idan mun hadu. Wanan yasa na zake na shanye duk wani kawaici a idona ina bata amsa a lokacin saidai bana wuce gona da iri ba irin hakan . Iya zancen yaya daban da wanan fa don yaya ko yayi aure bai farawa ya taba muna kudin mu dake hannunsa ai wanan kuma fa duka kidin ta dauka ta mika mai don sakarci. Akwao kudinku ke nan a hannun kawu ya tambaya sai tasha kunu a fuska tana fadin akwai mana zai fara ya taba min sune tunda yasan yadda kudin suke? Mama meye rashin zama dayansu ai gaskiya iya ta fada gashi ya ban kudi daga cikin kudina ya hana kusan wata daya ke nan fa ana binsa ya bani sai yace wai suna hannun wanda ya dankawa. Saratu nikan wai meyasa baki da hankaline wai don Allah haba kinyi maganan kudin nan yace ga uzirinsa ba sai a jira kayan su zama kudi a kawo maki ba ? Hakafa kike abinki wani lokaci baki tunane idan abinki ya motsa saiki koma kamar da yaso fitowa ciki ranan ni banson irin haka wallahi yanzu da zancen yar uwarki zamuji data dameni da koke koke ko naki da kike son dagawa mutane hankali dashi. A,a mama ni bance zan dagawa ko hankali ba ai adai bani abin dana tambaya ko aban kudina duka tunda abin ya fara zama haka ? Ke tashi muje ki gyadasu ya fada ya mike tsaye ba tare daya tofa komai a cikin zancen ba sai na mike da sauri kamar yadda ya umurceni din na juya ina fadin iya ga abinci nan na girko maki tunda baki zo kin ci a can ba ? Kai kai kai kice girki amarya yau zanci gidan nan ke nan bari na kurkure baki nazo na dandana ko kin iya girkin muka fita muna dariya. Bayan fitan mu takecewa yar kin gani ai abinda kike nema ke nan dama har dan uwanki yasan abindake gudana yai muna dariya ana zancen yadda za a kwantarwa yar uwarki da hankalinta a samu kudinta ya fito kin dauko wani zance kina son tayarwa mutane da hankali. Mama nifa bance komai ba kudin nan tunda kikace kawu za aba nace maki a,a kika hakeni na yarda yanzu kuma kinsan abinda nake sonyi da kudin nan kuma za a ga laifina ? Don ganin iya ta mike zuwa baya yasa mama din tausa murya tanawa Saratu fadan abinda take kokarin yi din akan kawu gaban yayan nasu duk daya nuna bai damu ba amma sai bataso hakan ba a lokacin. Tare dashi muka shiga part din akwai mata sosai a wajen nasu yan barka wanda na sheda wasu don harda salima da Nafisa suna part din tare da yan gidansu Asmau don a unguwa daya suke don haka ansan juna. Ihu suka saka min ita da Nafisa kafin su shiga gaida yayan nasu na dan dara muka rugume juna aka gaisa su suka kaini dakin mai haihuwa dake zaune kanta babu ko dan kwali balle hulla kan ya dankare da kitson da akai mata din zanen yawo. Muka gaisa yar uwarta na fasin ga waje in zauna a gefen gado da aka shiga tattara kayan wajen saidana zauna nida habiba aka miko muna yaron muka dauka. Nayi mashi addu,an Allah raya mun dan kai kamar minti ashirin a zaune shiru na mike na karbi ledan dake hannun biba na mika ina fadin ga zanin daukan yarona. Yan uwan nata suka shiga godiya muka fito daga dakin dake wani irin bashi duk da kanshin turarena ya bi dakin lokaci guda amma haka bai hanani jin wanan bashin ba kona meye oho ? Falon muka fito muka kara zama banjin ya fita lokacin nafi zaton yana dakinsa don can ya nufa tunda ya gama gaisawa da mutanen falon. Ina anty Saiba tana ciki kije ku gaisa kizo muje wajen yandan ki Anty Salima ta fada na dan kalleta ta mike tsaye tana fadin muje ai yanzu tabar wajan nan itama duk muna nan zaune. Bata dakin da alama tashiga bandakine dataji shigowan mu muka fito bamu tsaya jiranta part din muka fice zuwana yar uwata dana matsu muyi arba da ita a lokacin don a yanzu nasan tasan munshigo gidan tunda munyi waya kafin na fito gida. Wanda a yanzu zaune take kawai gidan bata wani dogon hurda da kowa sai salima da iya dama dai kusan hakan ake zaune saidai na yanzu din yafi worse ne kawai saidai haihuwan nan na Asmau tace dani ta danga canji ga Asmau don data shiga barka Asmau ta mata bazata don ta mika mata yaron wai ta shafa mai man zaitun donta samu an mashi wanka lokacin. Iyace dai mai wankan yaran idan sun haihu dama ba wata ake daukowa ba tunda da dan karfin ta har yanxzu shine tana shiga iyan ta gamawa yaro wanka tace a ba Yanda din tayiwa yaron shiri ita kuma tashiga nata wankan. Wanda bata zaci hakan ba tunda da farko duk sun dauki zafi a kanta kan zancen aure masu miji dani yar uwarta nayi a cewansu asirine mukai mashi muka sameshi haka a bagas din. Koda muka shiga ashe Saiban na tsaye ta windon dakinta don shike facing din part din yanda din tana kallon mu zaune takai saman gado ta jawo waya ta dannawa yar uwarta ikilima kira. Tana dagawa tace Saiba ya akayi yazo din anyi magana tace anty ikilima inafa ya dai zo da wanan yar iskan yarinyar tayi barka. Anty Iklima kinga yadda yarinyar nan ta koma kuwa cikin dan kwana biyun nan wallahi koke kika ganta sai kince ba ita bace Ramaah da kika sani a baya. Takoma sak irin manyan matan nan da yake korafin son yaga mun koma da kullum yake fada yana son ganin hakan a kan mu. Mena fada maki Saiba ai dama nace kibar biyewa Asmau kuna wanan rayuwan kidadancin kamar wasu jakuna kinki ji ? Yanzu gashi dan hakin da kuka raina na nema ta tsone maku ido keda bakinki kin fada ko wanan baisa ya fita batunku ya baku baya tunda abinda yake so ke nan dama ? Tundai ke kice baki da aiki sai cusa mai bakin ciki ance ga yadda zakiyi ki tsaya kina takama da kin gama dashi bai iya komai sai abinda kikace dashi ? To yanzu kin gani masu iya magana sunce ko kana da kyau ka kara da wanka kin dai san Jafar yayi kokarin zama daku haka Nusaiba ku zauna yayi takashe maku kudi amma a banza baki amfani dashi saidai ki sayar ko ki kimshesu cikin akwati tun farko abinda inna take maki gudu ke nan amma baki ji Nusaiba ai yanzu kin gani. Anty Ikilima nagaji da zuwa gidan malam nan wallahi bani ganin biyan bukata gaba daya yanzu abubuwan sun juye min yadda ban tsamani ba sam inayi kamar banayi wallahi don banko gabanshi balle na samu aiwatar da abubuwan dana karbo din. Ki bari ai zan shigo ana gobe suna kuma naji inna tace zasu zo barka kinga nasan zata zauna dashi ai donshine ma bazan biyosu ba don ina son inzo in kwana din idan nazo sai musan yadda zamu bullowa zancen nasa. Sun dauki lokaci suna waya kafin dai ta taushi yar uwar nata ta bata shawaran da ita saiban take ganin yana da wuya ta iya hakan ga jafar din da take gani idan ta sameshi yanzu saita hukuntashi fiye da tsamaninta. Zai gane shayi ruwane idan ya shiga hannunta saita bashi mamaki sosai ta rama duk wani takaicinshi dake zuciyarta abugeka a hanaka kuka shine abinda jafar yai mata a yanzu kan Rahama. Muna shiga maria na zaune tana ba Abba abinci tun daga kofa nace da yaron baby na ya juyo da sauri yana kallona sai yai kamar zai dago zuwa gareni sai kuma ya noke zuwa jikin mamanshi yaki zuwa wajena din. Wai Ramaah kece haka abinda Maria din ta fada ke nan tana min kallon mamaki na dan bata rai ina fadin kinga duk na lalace ko ? Ta watsa min harara tana fadin wani lalacewa kuma gaba daya kin sauya kamar bake ba ummah nacan tana damuwa akanki kullum sai tayi min magana a kanki wai naki zuwa in duba matake . Ni kuma ya Habu ya hanani zuwa gidan duk sun sakani a gaba kan maganan ki na karasa ina fadin to ai gani nazo yau muka fara gaisawa da ita lokacin Nafisa ta shigo part din tana dariya tace. Wai ashe bakuga saiba ba da kuka shiga yanzu ta fito tana fada dake Salima wai zakuyi tsiya idan kina shiga huruminta dolene saita gaisa da yarinyar nan da zaki kwasheta zuwa dakinta ? Allah sarki shi gaisuwan ma wani fitinane ashe banzata haka bane da bance muje a gaisa ba ai ? Mun bar zancenta aka dauko hiran anty baraka data dagawa mutane hankali tunda safe wai tun cikin dare ta kira waya ashe zata dawo gida ita mama dubu ta hanata dawowa dagani har yar uwata bamu ce kala ba don ba abinda ya shafemu bane . Muna zaune kanwar Asmau matar yaya J tashigo tana fadin amarya angonki yana neman kifa ? Wai ashe suna zaune falon gaba dayansu ya fito yake fadin ina Rahama ? Sukai shiru ya bisu da kallo kafin yace ke Rashida kira min ita part din habu don Allah ya juya ya koma dakin nasa shine ta taso tazo kirana din . Jiki a sabule na mike cike da mamakin don me zai aiko nemana a wanan lokacin gidan matanshi irin hakan zai iya kawo wani matsala kuma tunda dai gidansune na shigo ai ba nan din nake ba. Namiji oho donshi ko a jikinshi a dole zai saka mata kunci a zuciya ya nuna hakan ba komai bane ai tunda nima hakinsace na karasa falon na shiga gabana sai faduwa yakeyi suna zaune ana surutu sai sukai tsit lokaci guda. Yana ciki Rashida din ta kara fada na nufi hanyan dakin nashi da sallamata yana kwance yana waya na sameshi ya dago yana fadin. Kije wajen Iya ki dubo min abincin da kikazo masu dashi din nan yunwa nake ji zuwan kawu dazun ya hana in tsaya in karya da kyau a gida. Na juya zan fito muka hade da saiba da zata shiga fuskanta kawai na kalla nasan akwai magana a tare da ita lokacin. Ni dai kala bance da ita ba na dan rabe ta shiga ni kuma na fito daga dakin yan falon ko na samesu sunyi tsit sun kashe kunnuwa suna sauraren abinda zai faru a lokacin. Part din iyan naje na samu har lokacin dai ba dadi a yanayin dana samu mama din don itama waya takeyi lokacin don haka da iya na samu yin magana ina fada mata sakonshi din. Iya ke fadin shi kuma jafaru baici a gidan bane da zai kwashe muna wanda aka kawo muna nace kadan zan dibar mai ai iya. Na bude na kyafata mai komai na rufe ina jin Saratu na fadin bari dai in diba kafin ya kare naga an fara kwashewa haka kowa baici ba. Kai wanan matar bata san harara ba ban taba kawowa a raina zata ko kalli abinda na daho din ba balle tayi fadan taci har nakai kofa naji mama na fadin idan kinje ki kira min shi daga nan ana magana ya mike ya fita ni zasu bari da tashin hankalin da baraka ke son ta dauko muna akan mijinta ? Tunda na doshi kofan nake jin muryansu daga dakin hakan yasa naja na tsaya naji yana fadin har ke kin isa ki kafa min doka a gida Nusaiba ? Na fada na kara Rahama matatace kamar yadda na auri kowa a cikinku tana da ikon shiga duk inda taga dama a cikin gidan nan ko da kudinki na hada na gina gidan nan ne ? Nace ki koma gidan ku kince ba zaki koma ba to ki zauna tunda zaman mama kikeyi bazan koreki ba don kin zauna zamanta amma kada kice zaki takurawa kowa a gidan nan cikin iyalina kinji na fada maki . Kikace zaki tayar min da fita a yanzun nan ba sai anjima zan shayar dake mamaki cikin gidan nan oho ashe ba dadi lokacin da kika zarga min ciwon fitana a kaina ita kuma sakaran nan ta mara maki baya kuke gudana. Don yanzu na samu wace bata gudana tana iya zama dani ko wani hali nake ciki zaki kuma ce baki yarda da hakan ba kije nace ki samu mai lafiya irin ki don Allah ki barni in huta hakana a rayuwata. Dakin na fada dauke da abincin ta zaburo kamar zatayo kaina na gwauce Allah ya gyara abincin bai zube ba har na falon duk suka mike tsaye saboda muryan yaya dake fadin kika taba ta wajen nan yau sai kin kwana asibiti Nusaiba na fada maki inkon zata karyane ki gwada taba Rahama ki gani a gidan nan. Ni basai ka rama min na ina da hannuna nice zan ramawa kaina ai amma wanan abin baikawo kallo ba a tsakanin ku a cikin jama,a don Allah . Kaje mama tana magana da kai idan ka gama na fada na aje abincin na fito daga dakin na barsu a ciki yan falon tsuru tsuru ban tsaya ba na fita daga part din. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/17, 08:36] Buhainat: [3/5, 8:46 Yamma] Seenabu Makawa: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/C8kkr4INYY7FydHKKKRVhL [3/5, 8:50 Yamma] Seenabu Makawa: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 5️⃣7️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Kinji meta fada ai ashe baki cika yar iska ba tunda baki doketan ba a yanzu get out of side kafin ki kaiga abinda kikeso ki samu a gurina yanzu. Tana tsaye har yaci abincin yayi hamdala a gabanta yasha ruwa ya mike don ya fita a kofa ya tsaya baiji kunyan idon da yan falon suka kafa masu ba a lokacin. Nan ya tsaya tafito ya rufe kofan nasa dakinta ta nufa rai bace ta kira yar uwarta nan ta karfafa mata akan tayi hakkuri duk abinda zai mata don ya kureta kada ta yarda ta kara barin gidan har suzo. Zuciya dai bata da kashi duk maganan da yarta tayi mata haka baisa ta hakkura ba can dai ta sameshi part din mama suna magana kan zancen anty baraka din ta fado falon cikin fitina. Nan ya wanwanka mata mari duk da mama na magana ido rufe yake fadin shi zata kawowa rashin mutunci yana magana da mahaifiyarshi ta zo mai haka. Sai lokacin ta fahinci irin kuskuren da tayi don duk abinda sukeyi bai taba daga hannu ya duketa ba sai wanan ranan kuma a gaban kannesa dani da muke dakinsu muna kallon wani dinki da salima ta jawo mu gani. Abin dai ba dadi a lokacin wanan yasa ba a jima ba yace mu fito mu tafi duk da iya tayi mashi magana akan ya barmu yace yana son muje mu gaidasu mamane can family house din su. Dole iyan tayi shiru ita mama abu yai mata yawa saukinta ma shi J din daya kira anty barakah din ya bata hakkuri akan ta daina zancen ta bari zasuyi magana dashi daga baya . Wanan ya kwantarwa mama din da hankali saidai muna fita daga gidanne kuma Habu ya kirashi yana fadin kada yace zaiyi wani abu ya kyale yar tasu sai ta koyi hankali. Shima bai samu dogon magana a wajenshi ba saboda ranshi dake bace na daiji yace dashi zai kirashi idan ya sauke mu . Nidai nasan badon hudubar dana samu gun anty salma ba dana kade a wajen Saiba don yadda ta sakani gaba dani da mijin. Amma sai Allah ya taimakeni nayi amfani da wanan huduban na anty salma nacire tsoro da fargaba ina bata amsa ba tare da rashin kunya ba ko fitsara daidai da yadda tazo min nake daurewa ib dauki mataki a lokacin. Wanda ni kaina har mamakin irin daurewan da nayi din nake ji ina fuskantanta garan da garan gaba da gaba ba shamaki ko tsoronta. Mun shiga cikin gidan da kedojin da muka riko masu inda ko wani daki muka shiga muke aje masu sabulun wankine da omo sai manshafi dana hado dashi din. Ina dakin inna inda na yadda zangona dama tun kan na auri ya J idan nazo gidan nan muke dasu anty Nafisa kiran Maria ya shigo min. Da harshen fulatanci muke magana don su inna dake dakin zaune inda maria din ke tambayana ashe abunda ya faru ke nan. Yanzu take ji a wajen iya cewa Saiba tayiwa yaya rashin mutunci a kaina ya mareta har idonta daya ya rufe wai sun tafi asibiti da Saratu. Nan na fada mata abinda ya faru don ganin su salima ban samu mata bayanin komai ba har na fito a lokacin. Take fadin dama ta fada ashe duk ranan dana zo gidan saita wullakantani a gaban kowa gashi ni ban wullakanta ba ita ta samu duka haka. Inda take fadin yanzu ta shiga duba jariri ake fada mata abinda ya faru nace a cikin yarenmu na fulatanci ban taba bin kowa da mugun nufi a rayuwana yanda amma idan kace zaka bini da wani nufi akanka abin zai kare ai. Shigowan Nafisa har lokacin ina waya nan ta zube tana fadin ke kunbar gida da jidali Saiba ido ya kumbura saida mama tace a kaita asibiti ashe fada sukayi sosai har yaya na fadin zaman mama takeyi ai a gidan ba zamanshi ba. Kiji min mata wai kuma ashine take zaune bata tafi gidansu ba ko hakan aita wullakanta dai data sani ta bar zancen nan tayi hakkuri har lokacin da aka gama hidiman nan sai tayi abinda zatayi din. Amma yanzu har wanda bai wajen sai yaji zancen nan ta dauka irin bayane da take kada iskancinta yadda taso kuma a zauna lafiya. Wai ita Nusaiban ce ta tayar da fitina inna ke tambaya don ni tunda ta soma magana ban bata amsa ba nan take fadawa mahaifiyarta abinda ya faru zancen bai tsaya a nan ba don duk gidan kowa saida ya tofa albarkacin bakinsa. Maman fambeguwa uwar gidansu mama Dubu ita ke fadin duk wani shashancin da matan Jafaru keyi laifin dubune. Don bata son a fada bata kuma yarda wani ya tsawata masu idan matsala ya faru haka kiri kiri suka tauye yarinyar nan Asmau a gidan bata da wani power matsayinta uwargidanshi sai abinda yar nan Nusaiba tace shine yanzu suke son ya faru da yarinyar nan. Idan Jafaru ya yarda aka hadashi da yarinyar nan bai kara samun mace irinta a rayuwanshi diba a yan watanin nan yadda shi kanshi ya koma ya samu natsuwa da kwanciyan hankali a tare dashi fiye da baya. Aini ina dauka tana hakane kan son da takewa yayanta din amma sai daga baya na fahinci wani abune na daban ga hakan kamar yarinyar nan ta asirceta za ace. Daga daki nake jiyo zantukansu irin na yan babban gida da idan an samu magana kowa saiya tofa albarkacin bakinsa inda na kula da rikon Biba da yaya ya dauko muna yaiwa kakan yarinyar dadi sosai. Sai haba haba takeyi da jikan nata duk da nasan an sakata daki an mata bincike akan zaman namu da ita duk da nasan ba zata fadi wani mugun abinda rai zaikai ga baci ba saidai wanda ba aka rasa kawai dan dole a samun hakan ga rikon da. Daga gidansu muka wuce gidan anty Rukkaiya taji dadin zuwan namu sosai bamu jima ba muka nufo gidan yaya Ai nan mukai magariba muka koma gida a cikin dadin rai don ya zauna da yar uwarshi sunyi magana ta fahinta kan yaya baraka da matsalanta inda muka bar gidan da shawaran da suka yanke a kanta inda yaya Ai da yaya Rukkaiya zasu can garin wajenta din duk wanan hukuncin mama dubu bata sani ba a lokacin. Saidai na kula da yanzu kamar yaya ya tsame kawu a cikin lamarinsu a hankali yake abubuwa bada sanin kawu din ba wanda a baya ba haka suke dashi ba. Tunda muka dawo gida ban tayarda zancen matarsa ba shima haka baiyi wani zance kan abinda ya faru din tsakanin mu ba. Ranan dai da dare yake fada min su yaya Ai zasu tafi gasau wajen anty barakah dan tarewan amaryanta da za ayi kada ayi babu kowa nata a kusa. Allah ya kaisu lafiya hakan kuma gaskiyane don ba dadi ace ba kowa naka kusa irin haka ya faru don koba komai zasu dan rage mata damuwa da zuwan nasu. Zanje gida in sanarwa mama koda abinda zasuje mata dashi don tunda safe ibrahim zai kaisu gobe in sha Allahu nayi mashi a dawo lafiya ya fita. A zuwa lokacin na sakankance dai kamar aurensu da Saiba yana rawa kamar yadda naji wajensu nafisa da salima shima kuma ya fada ranan a gabana da yace zaman mama takeyi gidansa aiba zamansa don haka tabar saka baki a matsalanshi da matansa. Na dauka a ranan zatayi yunkurin barin gidan don cin fuskan da yayi mata a gaban mutane sai gashi naji Salima da muke waya tana fadin wai Saiba ta samu yaya kan abinda za ayi na suna yace a gidana za ayi komai nasa da jama,anshi don haka zasu shigo su tayani aiki ke nan. Nayi mamakin jin ta saura a gidan ashe batayi fushin zuciya irin na mata masu jan aji ta tafi ba har lokacin wanan ya kara min wani haske game da zamantakewa. Don hakan ya nuna itace mai cutarshi bashine yake cutarta ba don da shine ke cutanta nasan ba abinda zaisa ta zauna tunda har hakan ya faru koma dai maiye tsakaninsune ba zan saka hakan a raina ba don tare nagansu bani kuma fatan a sanadina tabar gidan in sha Allah. Koda ya isa wajen mama yake sanar da ita cewa gobe da safe su yaya Ai da anty Rukkaiya da inna amarya zasuyi sammako zuwa Gusau wajen anty Barakha don suga halinda take ciki. Budan bakin mama cikin mamaki sai cewa tayi da dan nata akan me zasuje duk bai isa mu walwale matsalan ba sai sunje ba Jafar ? Kafin yai magana iya ta bata amsa da fadin keko dubu wani lokaci kikan yi abu kamar mara tunane . Idan su yan uwanta basuje sun nuna mata gata ba kece zakije da kanki kowa wanan shawaran da yaron nan ya yanke ko ita barakha din zataji dadin hakan ai idan ta gansu tare da ita. Hakan kuma zai kwantar mata da hankali don za a san tana da gata idan anyi mata hakan don Allah kadai yasan bakin cikin da take can ita daya take kumsa ? To shike nan idan hakan yafi ni a zatona iya za ai mashi magana akan kudin tane ya bata abinta idan anje ai sai ya dauka ayi na,am da zancen aurensane yasa sukazo din. Kaiya ni kikan bani mamaki wallahi dubu sai in rasa ina hankalinki ya shiga ki barshi da dabaran nan da yayi namijine fa yafi tunane abinda zaije ya dawo akan komai . Tunda kikaga ya shirya hakan dole akwai wani hikima da hakan ke nufi ai ga Barakhan dole idan za ai wata tsiyar ganin idon yan uwanta dole a raga mata ai . Banda abinkima Dubu yau in ba Jafar din da kuka samu kamar ruwan sanyi ba wa zai tsaya har yai hakan yadda kuka rufe ido ke da yayanki kuka so ku tozartashi gidan nan kan kudin nan . Gashi ai shi baici ba wani kato yaci a banza har da tukwaici ya dora maku dashi kuma ba yadda kuka iya dole ku barshi da kudin ko don haihuwan dake tsakanin su. Irin abinda nakewa gudu ke nan tun farko da yaran nan suka zo da zancen a fito da kudin nan a raba abawa kowa nasa to gashi an raba din sun kuma salwanta don da kudin na hannusa da yanzu tana tsakuran abinta tanaci hankali kwance ai. Kuma da duk haka bai taso ba ai irin wanan abu ina yai dadi in zaki sake hali gara ki canja akan mu,amulanki da yaran nan. Shi miskilin daki ai kinji amsan daya bada ko yace ai mijintane don yaci kudinta to meye aure kuma aiba za a hanashi ba tunda yana da ra,ayin hakan aita sani ta bashi kudinta din. Kai iya wake zancen habu don Allah koshi Jafar din ai nasan yaki saurarensane ya yanke wanan hukuncin amma Habu ai sam baiyi ba wallahi. To koke fa amma yaro yazo da abinda zai fishemu kina wani zance so kike ke kije idan su yan uwanta basu je ba kome gashi har da abokiyar zaman ki za a tafi me yafi haka dadi don Allah kin kuma san ba zai kyalesu su tafi hakana ba ai. Yanzu dai zan hada da Saratu ko salima su tafi tare don kada ya kasance nan dakin ba wanda yaje a cikin mu hakan zai kara kwantar mata da hankali ai idan taga dayan yaran nan cikin su. Yanzu dai ke akeji kuma shi dai ga abinda yazo ya fada ai idan saratun zata tafi ba sai a fada mai ba idan akwai waje ? Akwai waje mana iya tunda su uku ya lissafa zasu tafi saida ya dawo take fada mai cewa da saratu ko salima za a tafi yake fadin . Mama banson abinda za aje ayi tashin hankali a can don Allah wanan yasa ban saka kowa acikinsu ba har Nafisa. Ka dai bari dayansu taje zanja masu kunne kada hakan ya faru bashike nan ba shi dai baice komai ba saida zai tafine yace da karfe bakwai zasu wuce fon haka mai zuwa ta shirya a cikinsu din. Washegarin din kuwa hakanne ya faru bakwai na safiya suka biyo daukan saratu din don ita tace zata salima tace itama ba zata ba don zasu tsaya shirye shiryen suna a nan kafin a dawo. Yaba dukkansu dubu ashirin inda inna yabawa kudin tabawa kowa don haka saratun nashiga motan ta mika mata nata kason tayi wani kata ta bata rai alaman don me za aba inna din kudi ta bata. Haka dai suka dauki hanya karfe dayan rana suna gidan barakha din inda suka sameta cikin tashin hankali daga ita har yaran nata. Taji dadi sosai da ganinsu tayi kuka tana masu bayani inda suka bata hakkuri kan ta daure namiji yafi danan idan ya tashi kumsawa mace bakin ciki ai. Ta shareshi ta nuna ba komai tunda Jafar ya nuna zai dauki mataki akan kudin nata miliyan biyar da dan kai dayayi mata dadin baki ya karbe. Ai kafin wani lokaci labari ya karade unguwa na zuwan yan uwan Barakha din kinsan halin mutane nan makwabta suka fara shigowa suna fadin albarkacin bakinsu. Yaya Ai tace ba komai ai tsakanin miji da matane ai aure karuwane idan akwai fahinta don haka fatan zaman lafiya suke masu yanzu. Wanan zancen sai a kunnen Iliyasu ya shigo yana fadin kwarai yaya abinda naso barakha ta fahita ke nan taki fahintana aure mukkadarine banyi auren nan don in tozarta taba wallahi. Ba wani kadai bata kudinta aiba auren akace kar kayi ba kudinta dai take bukata kawai a hannunta saratu ta fada don tana kule dashi tun shigowanshi gidan. Haba saratu ke da na dauka zaki goyi bayana kuma har dake cikin wanan tunanen yanzu dai ayi min hakkuri nasan nayi laifi don Allah. Ai haka zakace dama yanzu kai don Allah dama haka amaryan zatazo ta samu yaya daki kamar zauren malam ? Daki ba komai alhalin tana da kudin ta ka rike kana kumsa mata bakin ciki haba saratu yayanki fa taki kwantar da hankalinta muyi magana. Yanzu dai kawo wani abu a shiga kasuwa ko kayan amfanin daki a saya mata sai ya kwashe da dariya yana fadin saratu hoo ? Ya shura takalmanshi ya fita matar zata fara fada yaya Ai dai ta tausheta tayi shiru sukayi sallah sukaci abinci sai suka dan fita. Kudin da Jafar din ya turo masu da suka sanar dashi abinda suka sameta ciki suka dauki babban yarta tare suka fita basu dawo gidan ba sai yamma lis. Sun sayo gado har da sabon katifa dasu zanin gado kula haka dai suka hado mata kaya kamcankam kamar amarya. Allah sarki tana ganin hakan kuka ta saka don murna dama wanan ne burin mace da za aiwa kishiya kada kishiya tazo ta sameta hondadakwai daki kamar zaure. Basu zauna ba suka shiga gyaran dakin nata hakana ko fenti babu amma ba laifi kayan saiya haska dakin ya fito neat dashi nan aka zaune hira saratu ta samu bakin fadawa yar uwar sakon mama din tana fadin ai kingani yanzu dai sai ki san zamanki da mijin nan naki. Yau badon ya J ba da kunyan duniya yaciki kan mijinki donshi ko a jikinsa bai damu da halin da kike ciki ba balle yayi tunanen hakkinki yana hannunsa ba ya fidsake kunyan hakan. Bari saratu har kunyan jafar nake ji idan na tuna da abinda ya faru yadda mukai ta sakin magana a lokacin kan kudin nan amma hakan baisa yayi fushi dani ba sai ga hawaye na zubo mata. Tana kuka saratun tace ai mama zaki godewa tunda ita ta tsaya yai hakan don badon mama ba wallahi Ya Habu ba zai bari ya kalleki ba mamace ta datse shi yai hakan . Muryan inna da basu san da zuwanta wajen bace tace ko yaya ta saka yayi in baiyi niya ba aiba zaiyi ba. Ji inna don Allah saratun ta fada tace kwarai ku dai godewa Allah daya bamu Jafar a cikin mu wallahi ya kamata a dubawa bawan Allah nan irin kokarin da yakeyi din kan yan uwa. Bawai dakinku ba kawai duk wani abu na gidan nan yanzu Jafar ne jigo ko wani daki kuma ko haihuwan matan isah shine ya aiko da komai da akayi ga hadin kan yan uwa da yake kokari yi a yanzu. Barakha a cikin kuka take fadin ai gaskiya inna ta fadi saratu ko mama ta saka yayi inbaiyi niya ba aiba zai min ba ko ? Ni sai ince auren nan na jafar alheri ya zamo muna yanzu wallahi tunda kan gida ya haduwa ta dalilinshi ba kamar baya ba da kowa yake a watse gidan. Wanan zancen da inna tayi bai kwana ba saida saratu ta faki ido taje tayi waya da mama tana zuzuta maganan ga abinda ya dace ta fada ta tsaya tana haddasana a tsakaninsu kuma. Washegari dasu da yaran anty baraka din suka taru suka kara gyara gidan tsab da wasu makwabta aka dora girki ta saka les din da mama ta aiko mata dashi ta hanyar saratu. Wanan yasa duk wani iya shegen da aka dau damaran yi ba samu yiwa barakha din ba don dan uwanta da yafitar da ita kunyan duniya lokaci guda. Sai ga kayan kallo da frdge sabo ibrahim ya shigo dashi haba anty Barakha a gaban yan unguwa tasa sabon kuka tana fadin Jafar jafar yau ka zamo min uwa da uba a cikin duniya na gane ba abinda yakai dan uwa dadi a duniya. Dan Uwa Murfin Jallo Ya J ya dinke wanan wanjen sai kuma wani. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/17, 08:36] Buhainat: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/C8kkr4INYY7FydHKKKRVhL{2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 5️⃣8️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, A cikin kwana biyu yaya Jafar yayi wani irin rama lokaci guda na kula da hakanne da safe dana sameshi a dakinsa zaune yana shafa mai zaisa kaya. Bandai yi magana ba inda na karbi man ina fadin ya kawo na cika ladana bai kiba ya mika min na shiga shafa mai a cikin sallo da hilla irin ta zolaya yana lumshe idona na gama na zabo mai kayan da zaisa naji yace dani . Rahama da kin bani kaya mara nauyi in saka zaifi don ba ko ina zani ba yau zan daije gida in dubosu don Asmau ta bugo min waya jiya wai idon jaririn yana ciwo kuma. Amma iya tace normal ciwone da akasarin yara keyinsa lokacin haihuwa zan dai je nagani idan zamuje asibiti dashine a dubashi yau. Allah sarki yaro ke nan ya shigo duniya ya fara karo da matsalolin rayuwa ke nan yanzu Allah ya bashi lafiya ai iya zata san hakan tunda sun saba da ganin hakan su. Na taimaka mashi ya zura rigan a jikinshi ya tashi muka fito falo ya zauna muka karya dashi din yau ba zaki fita ba ke nan nace sai zuwa shabiyu zan leka don banda lecture da safe. Zan dawo in kaiki ya fada nace zanbi motan kasuwa ai ka huta da sauri naji yace no don Allah kada ki soma banson hakan ba mutuncina bane aga matata a cikin motar haya. Ya mike tsaye yana fadin dolema in koya maki mota ai don gudun haka koda ibrahim bai gari zaki iya fita ke kadai ina ganin hakan zaifi sauki amma banson zancen shiga motar haya din nan tunda Allah ya hore min abinda zan iya saiwa kowan ku mota a yanzu. Nidai yadda naga ya dauki zancen da zafi yasa bance kalla ba koya min mota kuma na yaushe nidana koya a abuja kuma saidai naja bakina nayi shiru bance komai ba. Yaje can gida din dubasu nan suke magana kan yaron dasu iya yace a dai bari ya kaishi asibiti a dubashi inda abinda zasu bashi. Saidai yadda ya samu maijegon a jagalce ana mata kumshi da kitso yasa rai bace yace da kanwarta ta dauko yaron suje asibitin dashi da salima. An duba yaron an bashi magani suka dawo ya ajesu ya juya ya koma gida lokacin harna shirya ina jiran dawowanshi don har lokaci yaso ya kure min. Gaskiya da ba don irin hakan ana ganin tauyewa bane da sai ince nikan gaskiya haka yayi min daidai a gidan miji don irin zaman nan bakama tuna kana da kishiya sai idan kasawa ranka damuwa da hakan. Hausawa sunce kazantar da baka gani ba sunan shi tsabta to ban gani ba ban kuma damu da in sani ba tsakanin rayuwan can gidan da iyalinshi don haka nake jin kaina kamar banda kishiya duk da ba,a cika baki da zancen namiji da sai ince nidai a yanzu na cika ban sanarwa gaba dai idan zama yai zama a tsakanin mu abinda zai biyo bayan zaman namu nan gaba. Duk haukan saiba hankalina sam bai daga ba da rigimar ta don hakane ma na yanke shawaran ko ranan sunan ba zanje gidan ba duk da naga alaman hakan shima agareshi. Yadda yar uwata take tayar da hankalinta kan aurena da ya J ni a wajena sam abin ba haka bane kila dai don tana cikinsu tana gani kuma tana jin irin barazanan da sukeyi a kaina ne hakan ke daga mata hankali nikan a waje a yanzu da saiba ta gwada min hakan muka zoje da ita ko darrr kuma banji yanzu a kansu kamar farko da nake da tsoron a zuciyana. Dama ance da ka bari a raina ka kayi taba kishiya tsoro da mataki yafi ka fito kana sa,insa da ita a gaban miji irin hakan raini saiya shiga tsakaninku da ita gashi kuma yanzu na gani a kaina hakan gaskiyane. Haka kuma na yarda samun waje ga mace yana fitowa daga matsayin da miji ya daukeka dashine tun farko. Don sai ince yaya J bai bada daman da wani nashi zai kawo raininsa wajena ba don nasan da zuwa yanzu tuni mun gwada hakan da anty Saratunsu din tsakani da Allah dai ita bata kaunanane a zuciyarta don sai ince tafima kishiyoyin nawa daukan zafi dani. Nata sam bai damuna don bankula ta ba balle wani abu ya shiga tsakanina da ita don koda naje gidan banda gaisuwa ba abinda ya hadani da ita ranan . Ina kallonta yadda take bina da kallo mai kama da harara wanda ko wace take tayawan saiba batayi min irinsa ba a fuskanta don ita saiban banda shigan da nayi na samu suna fada a kaina bata yarda mun hadu ba a ranan don haka bancewa tayi min don da mijinta ta tsaya fadan da takeyi din. Karfe hudu ya daukoni zuwa gida inda na koma na samu tarin sayayyan da yayo na abinci nasan don in hakkura da school a ranan. Daki nashiga dan sallah inda na samu period dina yazo min don haka na watsa ruwa na fito na shirya kaina saiga kiran anty salima take fada min gobe zasu shigo nan zasu kwana don aikin da zamuyi din mun dan kai wani lokaci muna waya don ita idan tana waya bata gajiya da surutu koda baka bata amsa kuwa. Haka nake ganin ta daukeni kamar aminiyarta a rayuwa don tun ba zancen auren dan uwanta akaina ni kadai take fadawa damuwata in kuma bata shawara yadda ya dace da zancen. Saidai sam duk da ta girme min a shekaru ban yarda zancen mijina yana hadani da ita ba ko taso bugun cikina akanshi nakanyi dariya kawai in basar da zancen a wajenta. Mun gama na fito falo zaune na sameshi yayi shiru kamar me tunane har saida ya ban tausayi a raina ba karya koda na zargi hakan akwai damuwan yan uwa dana iyali a zuciyar bawan Allah nan saidai baida wanda zai fadawa danuwan nasa yaji sanyine kawai yake bari a zuciyarshi. Har na tako zuwa inda yake na shafa kanshi kamar yadda anty salma take min hira idan D dinta yana cikin damuwa itace takan zauna ta kwantar mai da hankali har ya gamsu ranan kuma biba bata nan don tace zataje gidansu kitso da kumshi daga school don haka ban sa rai da dawowanta ba don haka mu biyune kawai a gidan lokacin dagani saishi a lokacin. Ajiyan zuciya naji ya sauke yana kamo hannuna zuwa jikinshi na biye mashi na zauna saman cinyarshi ina fadin . Tunane yaya na kula tun shekaran jiya baka cikin dadin rai ina fatan dai bani bace nayi ma laifi haka don Allah ? Murmushi yayi yana gyara zamanshi ya dora kanshi a saman jikina yana fadin me zakiyi min Rahama da zai bata min rai kawai dai akan matsalan mu dasu mama kika ganni haka a kwanakin nan. Subbahanallahi na fada na zare jikina daga nashi nakai zaune saman kujera ina fadin har me yayi zafi haka yaya kaida nasan kana kokari akan kowa naka ? Kema da kika shigo rayuwata a yanzu kin fahinci haka tun yanzu balle su da aka haifemu a tare yanzu fissabillah za ace mama kawai yayanta mata ta damu dasu muko mazan ko oho ?. Duk da wani lokaci nakanyi tunanen kamar hakan ba laifinta bane laifin kawune yake kokarin shiga tsakanin ya rabamu da mahaifiyar mu a fakaice amma mama din bata gane hakab ba. Kawu kuma amma gaskiya da bai kyauta mata ba tunda shima aiya haifa kuma shima naga kuna girmama lamarinsa gwargwado. Yanzu ki duba akan yaya barakha ta sani a gaba dazun nan saida na nuna mata raina ya baci duk abinda nayi Rahama wai ace mama bata gansu da hakan ya ake son inyi don Allah ? Matar nan tazo garin nan da cin mutuncu na cinye masu kudin gadonsu dake hannuna ita da saratu suka tada hasumin sai in fito masu da kudinsu in basu suma suna bukata. Na basu kudinsu cikin salama ta dauki kudi takaiwa mijinta ya cinye ya kuma dauki mata kishiya Rahama banyi fushi ba tunda naga ran mama din ya baci na tayar dasu yaya Ai suje suga halinda take ciki ko zataji sanyi da zuwan su din. Bayan sunje din suka bugo suna fada min labari ba dadi na bayar da kudi asaya mata duk abinda ya dace anyi din tun jiyan wai amma kuma mama saita nuna yanzu meyasa na tura su yaya Ai da inna ? Don Allah hakan kuma laifine wai suwa zan tura idan basu ba amma sai mama ta nuna wai nayi hakan don in fallasa asirin sakintane kawai ? Umm,umm gaskiya akwai dai kila wani ya fadi wani abu kan zuwan nasu har bataji dadi ba ta nuna hakan na fada ina kallonshi. Naji tace wa zai fada banda yar banzan nan saratu data bisu nima hankali akanta yaje direct don nasan itacema zata fadawa mama wani abinda ranta zai baci don ban yarda na tura mata kudin sayayyan ta account dinta kona barakha din ba. Amma ba komai idan bakin cikinsu ya kasheni ai kowa zai huta sai su nemi wani kuma su kadarmashi zancena da Saiba nace ta tafi gidansu amma mama tace bata zuwa ko ina Rahama ? Haka zan zauna da mace a kullum ba ranan shiryuwa a gareta sai cin mutunci da tonon asiri ina duban saboda iyayyenta nayi hakkuri na kai wanan lokacin da ita hakana yanzu kuma matakin da nake son dauka mama ta hanani daukanshi akanta ya akeson inyi don Allah ? Nikan gabanane ya fadi da jin furcin mutuwan daya kirawa kansa nasan abu yakai mai ko ina a rayuwansa tunda har ya furta hakan . Cikin dan marairaicewa nake fadin don Allah yaya kabar ambato mutuwa akanka yanzu in ka mutu yanzu nima ai zan mutu ne nasani . Murmushi yayi yana shafo fuskana yace Rahama baki son in mutu ne mutuwa ai dole ayishi tunda munzo duniya ko ? Shiru nayi ina tunane tare da jin wani zafi yana fita min a jikina lokaci guda ni kadai nasan irin tunanen da nayi cikin dan lokacin kafin muryanshi ya dawo dani da yake fadin. Ba lafiya ke jikin nan nawa ba amma mama ta kasa gane hakan karfin hali kawai nakeyi Rahama kike ganina a tsayen nan amma nina san abinda nakeji. Naje asibiti har nagaji amma likitoci sai suce dani banda matsalan komai a jikina donshi na fawalawa Allah lamarin a yanzu amma idan ka ganni haka sai ki dauka mai lafiyaneni a tsaye. Har lokacin na kasa magana sai wayan da nake latsawa ina neman lamban Dage daya fado min a rai lokaci guda nayi sa,a ya daga na fara magana a cikin yaren mu dashi. Da farko fada muka soma yana fadin naje birnin zaria na mamta dashi cikin wahala bai dauka rashin mutuncina yakai haka ba ai ? Ace har aure hardo ya daura min amma ban nemesa ba ga baffa yanzu ba lafiya ke gareshi ba shima dai a tsaye yake dai. Nan dai na bashi hakkuri na nuna mashi nima bansan da zancen auren ba yadda yaji haka najishi ban sani ba shine ma yanzu na kirashi akan mijin nawa ai don baida lafiya a jikinshi. Yace Jam jam Anini kada ki auri gawan fari fa nace ba akai can ba yayana Dage tunda ina da Allah dasu ai hakan ba zai faru ba in sha Allahu. Sai ya dirka min zagi yana fadin ohho yar damcen uwa taga kudi taga wajen ci ku kadai kecin kudin ku sai mahaifiyar ku da yan uwanku duk da nasan ba karya ya fada ba amma nace wani kudi dage in akwaisu ai kasan tare dakai zamuci. Ni dai yanzu kiranka nayi daka taimaka min ko da wani abu da zaka bamu ko nawane zamu turo maka dashi yanzun nan yace koda Fam dari nace Anini ? Wucema hakan ai Dage kai din ai dan uwanane banda wanda ya wuceka dage donshinema na nemaka yanzu ai ? To ki kwantar da hankalinki ina kuna da dawakai a garin ku nace kwarai kuwa ba za a rasasu ba in sha Allahu tunda akwai sarakai a garin . Dadina dake akwai kiran Allah to ku nemo ruwan da doki yasha ya rage sai ki kirani zan fada maki yadda zakuyi dashi godiya sosai nayi mai nace ga fam darin ka da kace din zan turo mashi hardana goro dubu goma na tura mai a layinshi take a wajen . Don nasan komai zaiyi zaiji karfin gwiwan bani har abinda baiyi niya ba saboda kudin donshi ne banji komai ba na tura mashi kudin haka. Na dago kai ni ya J ya zubawa ido kafin naji yace dawa kike wayane haka na lumshe ido nace Dage ne dan wajen baffan mu wanda ya taba ban maganin dana baka kwanaki. Sai naga yayi murmushi ya gyara kwanciya kanshi na saman cinyana har lokacin yace ai matsalan nawane Rahama yana da daure kai. Idan mutum baiyi hankali ba sai yayi shirka gara ka dogara da Allah duk abinda ubangiji yayi ga bawa daidaine dashi Rahama. Amma kinki duk inda naje sai ace matsalata na gidane kuma mamace kadai mafitan matsalan nawa amma ta kasa kwantar da hankali ta gane hakan. Wanan yasa kikaga zuwan ilimi a yanzu ba karamin amfanan al,umma yayi ba sosai a yanzu don malumanmu suna kokari wajen wayar da kan mutane sosai a yanzu na su daina irin shirkan da akeyi a da can baya a cikin duhun kai. Don gashi abin baibi kowa a cikin muba saini yake bibiya haka kuma mun kasa tsayawa mu fahintar da mama inda matsalan namu yake . Hardo ya fada min komai lokacin danaje zancen auren ki mutum dayane zai iya shawo kan mama a yanzu itace iya. Don da zan zauna in fadawa iya abinda ke nan daga kawu har mama din zata zaunan dasu ta bincika maganan . Katseshi nayi da fadin wanan mai saukine ai yaya idan har baka iya zama da iya kafada mata a can gida sai mu daukota nan ta kwana biyu daga hakan sai ka samu daman fahintar da ita komai dake damun ka din. Shiru naga yayi na dan lokaci kafin yace hakane gaskiya don zance ne dake son natsuwa da fahinta nakanyi tunanen zancen hardo da yake fadin duk matsalan yana ga kawun mu dauda. Kawu dauda kuma na fada cikin mamaki ina kallonsa yace hakane kawu yasan komai amma yake boye hakan don wani nufinsa akan mu da bamu san na meye ba ? Munyi magana sosai a lokacin inda na fahinci yana cikin damuwa akan matsalan lafiyanshi dana iyali dana sauran yan uwa dake cinsa a zuciyarshi. Nake fada mai dage yace ya nemo ruwan da ake ba doki wanda yasha ya rage idan an samu mukirashi zai fada muna yadda zakayi dashi. Naji yace sai yanzu na yarda ba banza fulani suke zaune a dokan daji ba ashe da shirinsu suka zabi zaman dajin da sukeyi ana masu kallon basu san me sukeyi ba ? Waya fadama basu san komai ba su suna ganin ku dake cikin gari a zaune kune suka kwara ai yace naga alama ai. Wani abokin mahaifin mu bafulatanin nan dajin zaria ne kwanaki da nazo har wajensa muke da yan uwana yake fadin nayi dace tunda na auro bafulatana a gidana. Murmushi nayi nace baka sanin hakan ai shi daya san irin wahalan da bafulatani yakeyi kafin ya mallaki mace ai dole ya fadi hakan. Kiran sallah da aka fara a wayanshi yasa ya mike ya shiga yin alwala yayin da nake zaune a wajen ina charting da anty salma. Har ya fito ya sameni a zaunea inda ya barni yake fadin amma kinji lokacin sallah yayi nace yanzu zan tashi ban fada mai ina fashin sallah ba kai tsaye. Kodaya fita munci gaba da hiran mune da ita har ya dawo ya kara samuna wajen zai dauka na dawone na zaune a wajen kuma. Tun bai zauna ba dana gaidashi nake fadin a binci na saman dinning na hada yace ok barin gama waya da Meabei tana kirana ina masjid dazun ban daga kiran nata ba lokacin. Na saba jin wayarsu don haka na mike na shiga kitchen na dauraye yan kayan da mukayi amfani dasu da rana koda na fito wanan karon yana waya da matarsa Saiba. Naji yana fadin ok sai gobe idan nashigo zamu gaisa a raina nace miji da mata ke nan sai Allah dama idan kace zaka shiga tsakani kai za a bari a cikin zancen. Da mama ta sani tasa masu ido ba zata san lokacin da suka shirya ba a tsakaninsu dazun nan yagama min korafi kanta yanzu gashi suna waya kamar ba komai a tsakaninsu. Tsawan daya daka mata yana fadin nace maki ba zan shigo ba sai safe ko bakiji mena fada bane ban dai tsaya jin abinda ta fada a bangarenta ba na nufi wajen abinci na zauna ina jiransa don ko abincin kwana biyun nan ya rage zama yaci soai don haka nayi hikimar yin wanan dabaran don nasan dole ya taso yadan tsankwara koda kadan ne. Naji yana waya da yan gusau suna fada mai washegari zasu taso yayi masu ban gajiya lokacin ya mike ya sameni mukaci abincin a tare. Bayan ya gama na mike na hada kwanonin zuwa kitchen don ya shiga dakilan wayarshinema lokacin hakan ya ban daman tsayawa in wanke kayan na kife ina gyara wajen najishi a baya. Ya rike min kwankwaso yana fadin sarkin aiki ke baki gajiya da aikine wai ko yaushe kina sa kanki busy na kula ko yaran nan ke ke faman dawainiya dasu a gidan nan idan ban nan ko ? Nace a,a nida su duka munayi bani kadai suke bari da aiki ba ai ga kuma habiba tana taimaka min sosai itama. Tsoman hannuna ya karba yana fadin gashi bata dawo ba nace ta kira da wayar yayanta dazun wai kumshine basu fara da wuri ba nace tabari sai gobe ta dawo ba matsala. Jana yayi muka koma falo bayan na rufo kitchen din muna zama kuma ya shiga waya hakan ya ban daman samu na sulale zuwa daki don lokacin a tsawale nake jin kaina wanka nayi na shirya sosai na lakace jikina ko ina da humran mama na maiduguri a jikina. Yana falo kishigide yana waya a cikin natsuwa idonsa yana kaina harna karaso ina fadi a hankali na kawoma ruwan shayine yanzu ? Kai ya gurgizamin yace ki bar shayin nan a koshe nake yau Rahamce ashe da yaya Habu yake waya na dai ga yayi murmushi yana miko min wayan na karba. Naji muryanshi yana fadin Rahama kina son J yafini kiba ke nan kike faman dura mai abinci haka ? Murmushi nayi don ban iya wasa haka dashi ba da yake jana dashi a yanzu tunda na zamo matar dan uwanshi din. Munkai wani dan lokaci a falo kafin mu koma daki da sai lokacin ya gane fashin sallah da nakeyi tunda ya fahinci hakan naga mood dinsa ya canza . Ya lafe yai shiru sai can naji yana ajiyan zuciya yace na dauka cikine dake ai Rahama da sauri na jiyo ina fadin ciki kuma yaya ? Kamar ba zai ban amsa ba sai kuma can yace baki son haihuwa yanzu ke nan nayi kasa da kaina ina fadin ba wai banso bane yaya in Allah ya ban ina so mana . To Allah ya bamu ni ina son haihuwa sosai wallahi ina son ganin kema kin samu rabonki dani tun ina raye da raina. Yaya kana kashe min jiki idan kana wanan maganan dazun ka fada yanzu kuma kana fadan hakan sai naji yace ana son bawa ya dinga tuna duniya ba matabbata bace a gurinsa ai. A raina nace lalai akwai abindake damun mutumin nan abin kuma babbane daga Allah saishi saiko kila yaya habu suka san komeye matsalan don bai fada min ba. Haka na kwana da damu akanshi washegari zuwan su Salima yasa na dan sake shi kuma ya fita ya barmu a gidan bai dawo ba ashe yana can gidan da yan uwan saiba suna fafatawa dashi kanta. Da yamma kuma yan gusau suka dawo zuwan Ibrahim daya dawo da mota yasa muka fahinci hakan sai gashi shima ya dawo suka zauna tare sukaci abuncin rana dana aje mashi. Aiki mukayi sosai har dare ba hutawa duk mun hada komai don washegari suna sai dare na samu na kwanta da asuba kuma muka dora abincine don yan zanen suna da za a fita dashi da safe. Na aikawa makwabta dashi duk daba shiga gidajensu nakeyi ba kuma sunji dadin hakan da mota su ibrahim suka jida zuwa family house dinsu. Muka dora wani kuma da za akai part din mama duk da suna abinci suma a gidan sai wajajen two na rana suka kwasa suka tafi nace dasu in ya dawo zan samesu daga baya duk da nasan yana da wuya inje. Koda ya dawo din bai nuna alaman zuwana ba sainice nace dama kai nake jira zancen zuwa can gidan ? No ba sai kinje ba tunda kinyi aiki a nan kowa yasan kin gaji ai ban kara maganan ba sai darene mama takira waya tana tambayan dalilina kin shigowa suna ? Naji yace shine ya hana don munyi aiki mungaji donshi yace in zauna ba sai naje ba din ni dai nasha jinin jikina ina mamakin mama da halinta a kaina yanzu ? Don nice dai bata so da danta har bata iya boye hakan acikin ranta na kula duk abinda zanyi laifi mama zata kirkiroshi a kaina. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/17, 08:36] Buhainat: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/C8kkr4INYY7FydHKKKRVhL{2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 5️⃣9️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Barci nasamu nayi sosai washegari don babu kowa gidan har biba a can ta kwana wajen su anty Salima dagani sai shine a gidan shi kuma ya fita tunda safe . Ina kyautata zaton yan uwan saiba ce zasu koma gida a washegarin suna din don haka na samu nayi barcin gajiya mai isata da yake ina fashin sallah donshi na samu har karfe hudu ina kwance saidai fitsari ya tayar dani kawai. Karfe hudu na samu na mike na shiga wanka na fito na shirya na fada kitchen don girka muna abinci ina gab da kammalawane naji tsayawan motanshi alaman ya dawo ke nan lokacin. Ko ina na gidan fes yake sai kamshi ke tashi ga kuma na girki dayake dan shigowa ciki lokacin muryanshi naji yana shigowa a zatona na dauka waya yakeyi ashe shida iyace da habiba suka shigo. Ina tsaye daga kofan kitchen da niyar gaidashi da dawowa sai ganin iya a bayanshi nayi habiba na biye da ita da dan jakar kayanta . Cikin murna na hada ina masu sannu da zuwa na dauka ganin idon iya din zai hanashi yadda yake min idan ya dawo saidai hakan bai hanashi ba don saida yazo ya rugumeni yana fadin how are you ? Fine na fada ina dan nokewa ya gane me nake nokemawa din don iyace sai naji yace wai iya ai zataji dadin ganin yadda kike ban kulawa don itama hakan take son na kasance. Ni dai na wuceshi ina murmushi zuwa wajen iya din ina kara mata sannu da zuwa na nuna mata kujera ta zauna a sama tana fadin masha Allah abu yayi kyau sosai wallahi haka ake so a rayuwa dama cigaba aiba wanda yakishi. Zonan mu gaisa da kyau tana nuna min gefen da take zaune na zauna kamar yadda ta bukata din ina fadin iya yaya gida ya taro kuma ? Taro Alhamdullahi ke dai anyi lafiya an kuma watse lafiya sai abinda ba a rasa ba dai wanan kuma ai an saba dashi kuma ko ? Habibace ke gaidani na juya ina fadin biba yan suna nayi ta zuba ido jiya inga dawowanki shiru ta danyi murmushi tana fadin ban samu wanda zai dawo dani bane har dare yayi na kwanta a can. To bagashi yau kin dawo ba bata da sabo kin ganta nan taki sakin jiki da kowa amma yanzu kinga tana zuba kamar ruwan sama. Mukai dariya na mike kayan da Biba ta aje gefe na dauka zuwa dakin da iya zata zauna wanda a nan Biba take gyara dakin nayi sosai tare da Biba din na shimfida sabin zanin gado dana dauko daga dakina na wanke bayin tas duk da dama baida datti sosai amma na kara gyarawa nasa kamshi. Falo na dawo na sameshi tare da iya yake fadin ina kika shigane haka nace ina gyarawa iya dakine sai naji tace kaji arziki ba a inda aka santa Allah dai yayi maki albarka kinji. Kitchen nakoma na kwashe abinci na hada miya ina tsaye biba ta shigo ta sameni zata kama nace jeki huta aina kammala tun dazun kafin ku iso. Ke kuma ai da gajiya a jikin ki tace banyi komai ba a can wai anty ai gara da bakije ba wallahi ana ta fada dasu anty salima da matan uncle wai ta aiko a dibi abinci mummy salima ta hana shine tashigo tana ta zaginsu harda ke da bakije ba din. Maman tudun wada kuma ta farwa mummy salima din da fada har ta kira uncle shima tace wai an kawo abincin mai kyau gidanki andafa ba akai can ba gashi kuma yanzu abincin ya hada fada. Ikon Allah nafada cikin mama sai tace ai uncle yace duk abinda ya sawo nan gidan shiya saya a can kuma na can din yafi yawa tace dai ya dinga adalci. Bayan haka kuma aka zauna da yan uwanta akaita fada da uncle din tana ta kuka shine mama tudun wada tace wai in tashi in fita na koma part dinsu Abba na zauna. Biba irin hakan dama dole zaki gani tunda kina tare dani ko kingani kibar damuwa saivyarinyar tace Allah mama tudun wanda bata sonkine anty haka shima uncle ya fada yace me kikai masu meye matsalansu dake ne wai ? Muryanshi naji yana kirana nazo yake fadin to bakuwanki zaki kai daki zatayi alwala na amsa da to iya muje dakin kiyi ko ? Tafiyan nata daine yasa dole nima na taka a hankali muka shiga har dakin sai fadi take masha Allah kinga arziki dole ai yarinyar nan tayi hauka sunzo jiya da yan uwanta sai koke koke suke muna wai Jafaru ya fita batunta ya maida ita bora a gida. Uwarku kuma kamar sun gama da ita sai wani noke noke takeyi makin ta fada masu gaskiya ta tsaya marawa karya gindi ita da yar nan saratu mara hankali. Duk abinda dubu keyi da zugin saratu takeyinsa ni yaushe zan zauna yaro karami yana min wanan shegantaka in dauka yarinyar dako auren fari batayi ba. Kinga ki daure kibi mijinki yadda yake yabon nan naki karki yarda ki canza halinki ko gaba haka nake fadawa yar uwarki wanan zancen don yadda suke hattaranta a yanzu gidan. Dan dama wanan Asmau din naga kamar ta fita wanan shirmen nasu tunda tasan Allah dayane taba da kai bori ya hau har abin suna naga ta hado akawo maki amma uwarku ta rabewa mutane duka. Naman daine na suna nayiwa Jafar magana tasa a debo maku har muka fito bata bayar ba nace iya nagode ba komai wallahi Allah dai yabashi lafiya tace amin kafin kuma tace dani. Wai har yanzu dai jikin nasane kome ni naga yana rama a tsaye nake tambayanshi yace min damuwane kawai da abubuwa da sukai mai yawa kuma. Haka yake fada iya idan anyi magana baidai fada maki gaskiya bane amma da abinda ke damunsa gaskiya sai kin zauna dashi kila zai sanar dake damuwansa din . Jam jam Allah kaza gata a garemu shiko abu na cinsa bai fada tun abu bai baci ba ni yaron nan tausayi yake ban don da kurciyarsa nauyi ya hau kansa haka ? Na dai nuna mata ban daki ta shiga tana mita na fito na samu biba ta kammala komai a kitchen din dakina nanufa na zauna ina azzakar na yamma. Ban fito ba saida akai isha,i na fito na dauki abincin nakaiwa iya din har ruwan sha dana wanke hannu duk na aje mata a nan inda take sallah din. Na koma gefe muka zauna da biba muna hira ta gama addu,a ta shafa ta juyo tana fadin shi dai mutunci gadarsa akeyi haka yar uwarki take faman dawainiya dani kullum gashi na fito ban samu sallama da ita ba. Ayya bari na kira maki ita kuyi sallama din tace hakan shiyafi kada taga rashin hankalina nasan yanzu ta shigo bata sameni ba. Itama uwar naku naji tana fadin gobe zata gida ai saigashi Jafar yazo yace dani ai in shirya muzo nan in kwana biyu daku in huta hakan yai min dadi sosai wallahi. Kwana biyu kuma iya nida nasha kinzo ke nan baki komawa a nan zamu zauna dake tace haba ina haka zai yuyu ai sai a zageni nazo nan na tare don kwadayi kamar yadda ake zagin yar nan salima tunda na saratun nan ba mai ido a tsakar kai. Na fadawa dubu ai tayi mata aure ta huta da ita yafi zaman ta sai gulma tsakanin yayyun ta da hadin hasumi da takeyi a gida. Aure lokacine iya idan yazo koba shiri sai anyi nata harda ruwan ido kinji aiba maneman ne ta rasa ba ruwan idone kawai ta dafewa yaron nan da akace baida kirki sai karya yake masi ko yaushe gashi turo magabatanshi ayi zancen aure. Ina ji masu tsoron irin na barakha ta fada hannun baragurbi azo ana dana sani daga baya ido ya raina fata shine ya dawo yasa namike zan fito sai gashi ya shigo yana fadin kina nan ashe ? Na amsa da ehh yake miko min goran ruwan dake cike da ruwa nabi goran da kallo kafin na karba don ruwan ciki bai min kama da ruwan goran ba. Ganin na karba da mamaki yake dan wuceni yace ruwan da akace a samo na hadin maganine ai nace au ruwan doki ko ? Ya amsa shine Auwal ya samo min a gidan makwabcin su yanzu ya kawo minshi daga inda iya ke zaune take fadin ruwan doki kuma ? Yace iya banjin dadin jikin nan nawa wallahi shine wani yace mu samo ruwan a hada magani dashi ina jin kamar wancan ciwon yake son ya dawo min kuma a yanzu. Muna ga rasulu ni yar mutum biyu kaga abinda nake fadawa uwarku ko amma ta kasa fahintana sai shirme ta tsaya yi ita da wanan shashan dan uwan nata. Wai yanzu ace kamar dauda zai kara aure don jaraba mace tazo ma da goyo har da yayyu a gida ka wani haukace kana sabari kamar karamin yaro ? Jiya nan hafsatun take ai tana muna kuka wai dauda ya juya mata baya kan ya kara mata da yaya ko yaushe yana rugume da dan da akazo mai agolanci dashi. Har yana batun sabawa Hafsatun da yaranta kaji min abin kunya waya saura wanan auren kazantan yanzu banda shi mara hankali ? Ba rashin hankali bane iya abinda yake ra,ayine kinsan mu maza idan muka hangi abinda muke so sai aga rashin hankalin mu kan abin da zuciyarmu ya zaba. Kaiya ba irin haka bane wanan yarunyar daya kwaso yar duniyace kaji banda duniyanci da samun waje zakizo aure da yaya ukku ? Sai kace wani attajiri dashi a zamanin nan da kowa keta kansa ina dai dan dukiyan nan daya kwamsa na uwarku da yan uwakane ya ke rudansa har yake ganin shiya isa a yanzu baijin has ? Kawu aiya canza gaba daya iya ni har abin nasa yana ban mamaki wallahi zai baka kuwa kaida kasan kanka amma dama ai haka dauda yake kune baku ganesa ba dai sai yanzu. Kaga matar nan nasa hansatu to makiran matace tun aurensu gaba daya lamarinsa ya canza bari naga abu zama da wanan yarinyar. Don akanta nasan dan kauye bala,ine duk abinda ake fadawa bakauye gaskiyane ko wanan zancen auren naka waya zuzutashi ga uwarku haka banda ita da mijin nata ? Duk wani makirci da aka kulla nasan ga hansatu ya fito kallon su nakeyi kawai sai ranan da dubu ta gano gaskiyan zancen da idonta. Don yanzu kowa baida kima ko mutunci a idanunta banda dauda a duniyan nan ko kara dauda ya gitta dubu bata iya ketara mashi shi a yanzu na dauka zumuncine na tsakani da Allah sai yanzu na fahinci makircin hansatune hakan. Habiba taso muje falo na fada don wani zancen da suka somayi ba jin Biba bane harni wanan yasa na fadi hakan muka fito don mu basu waje su samuyin zancen da kyau. Aikuwa dai sun samu kuma har ya amaryar mata da abinda ke damunsa din inda yace mama taki fahinta a tsaya ai bincike kan zancen gashi duk inda yaje magana daya ake fada mashi. Jikin iyar yayi sanyi cikin damuwa tace Jafaru kasan da wanan maganan baka fada min tuntuni ba ta ina yanzu zan somashi dole a zauna dasu muji yadda abin yake ? Ka bari nasan yadda zan bullowa wanan zance din dauda dauda na fada maku kune baku san dauda ba ai komai dauda zai iya idan akace tunda yana rayuwa da muguwa. Kirikiri kaika sani saida Allah ya kawo rabuwan muna dawo gidanku da zama na samu sa,ida da kaidin wanan yarinyar duk da hakan ta riga tayi min illa a rayuwa saidai aina musulinci kawai a zauna lafiya. Abincinsa nan nakai masa yaci don har biba tayi barci a nan falo da muke kallo saida ya fito daga dakin na tayar da ita taje ta kwanta na rufo masu kofan dakin nina na sameshi a dakinsa. Washegari dole zan fita school ga kuma iya a gidan donshi tun karfe biyar natashi na fara aiki kafin gari ya haska na hada mata abinci har na rana na samu nashiga wanka saidana shirya na shiga mu gaisa da ita. Inda na sameta zaune a kasa tafi ganewa zaman kasan nake gani muka gaisa nake fadin zan shiga makaranta iya gashi zamu barki ke daya na wani lokaci a gidan . Allah dai ya tsare ya kare tayi min na koma kitchen na kwaso kayan abincin ta na kawo mata dakin na jera take fadin duk yaushe aikai wanan aikin haka yar nan ? Murmushi nayi ina fadin yanzu da safe nan na girka ai har na rana don kada infita in jima a can din ban dawo da wuri ba. Allah yai maku albarka ta fada tace kwarai magananki gaskiyane mijinku yana cikin damuwa yar nan jiya mun zauna dashi ya fada min komai kuma hankalina ya tashi. Tun za a ke shiri ba sai an dawo ba habu nake son yazo garin nan ina gidan nan ya tara min iyayyenku muyi zancen dasu muna kallo yaro zai halaka ba a dauki mataki ba ? Sam basu da tunane wallahi dan nan shine jigo a garemu kaf amma sun kasa tsayawz su fahinci gudun kada in makavjqra nace ina zuwa don ina biyewa zancen iya ba zan samu class ba ranan. Dakinsa naje na sameshi yana barci na fito wayan yaya ibrahin na kira shi yazo ya kaimu school ranan din ban tayar da shiba muna tsaka da lectures ya kirani yana fada na bashi hakkuri na kashe wayan nawa gaba daya. A gidan kawu fadane sosai sukayi ashe ranan da iya tazo gidan mu har saida mama dubu ta kaiga zuwa gidan don sulhuntasu inda take fada sosai kan yadda abubuwa suke taso mata a yanzu . Cikin fada take fadin abin yayi yawa mana zaman lafiya yana nema ya kaurace muna ayanzu shigowan yarinyar nan cikin mu ni bai min dadi ba wallahi. Na kula da zance nan nason zama gaskiya don tun ranan da jafar yace ya auri yarinyar nan Rahama abubuwa suke nemansu tabarbare muna. Ko sam hakan ba zai yuyu ba wallahi ba zan bari akan wanan abinda mutane suka camfa ace kan mu ya tarwase ba dole yasan yadda zaiyi da ita ya rabu da ita. Yar uwa mai karatu Ina kike tunanen wanan zance na mama ya fito da har mama din ta riks tansa bakin saratu data fara furta hakan a lokacin aurena da abin yai mata zafi take fadin . Iren fulani irin tsiya zasu tara muna a gida fulani da akace aurensu matsalane don sai gida ya watse ta dalilinsu shine su zasu kwaso muna su suna cika gida ? Ko ita yarta banda matsala da fitinan tsiya meta kawowa mutane ga ya habu nan kullum jiya wa yau ba a ganewa samunshi haka aurensu yake kamar auren buzaye wallahi baban wata kawarmu yayi ai mungani. A take zancen saratu din yayi tasiri a zuciyar mama don a ganin ta gaskiya saratu take fada don gashi habu dai ba ruwanshi da taimakawa kowa saishi da matarshi suke cin abinsu. Hakan kuma itama matarshi YANDA bata yarda kowa yasan sirinta ba balle aji a zauna gulma sai haushin hakan ya zamo biyu ya hade ga saratu din . Wani lokaci kiyayyan abin hannunka yanasa a kika, haka kuma kiyayya kan baiwa ko daukaka da Allah yayima yana sa mutane suji sun tsaneka. Abubuwa da dama suna saka mutane sukika saboda hassada da bakin ciki da kyashi da sukeji naka ,wani lokacin kuma rashin gamon jini nasa kaji haka kawai ka tsani mutum a ranka irin wanan yana cikin dabi,an saratu don idan mutum bai mata ba zata fara bakin ciki dashi dole kuma dole kaida ke tare da ita ka nuna kaima baka kauna wanda ta tsana din. Exam din mu yazo dole na maida hankali ga karatuna idan na fita gida sai yamma zan dawo gida cikin irin haka wata rana shi yazo daukana lokacin matarshi nada sati biyu da haihuwa. Bayan mun kama hanyane naji yana fadin Rahama ina ganin yau a can gidan zan kwana ba sai kinyi girki ku dani ba. Duk da naji zancen a bazata amma na daure ina fadi a fili Allah ya bamu alheri iya abinda na iya fada a bakina kenan lokacin. Shiru ya dan biyo baya kafin yace mama ta matsa min akan Saiba ta karbi girki zuwanta biyu ke nan gidan ki wajen iya akan hakan yau iya tace bayi hakkuri nabi abinda take so din. So don Allah kada ki dauki hakan wani abu a zuciyarki haba dai yaya ni hakan ma yayi min dadi don laifina da ake gani kan hakan ? Na banza tunda sunsan bakece kikasani yin hakan ba ai duk wanda zai zageki ya rage maki nauyine ya daukarwa kanshi alhaki don ra,ayinane naga daman hakan. Ko yanzu kuma hakan bashi zaisa ta samu yadda take so a gareni ba na fada masu har Asmau din ta karbi girkin ta . Allah ya kyauta na fada ina gyara zama cikin dan siririyar murya sai naji yace me kuke bukatan a sai maku ne a gidan ? Dan kallonshi nayi nace ba komai kamar a hasale yake don yadda ya hauni da fada yana fadin ya zakice ba komai ? Komai ke nan kuna dashi a gidan nace to yaya me zance tunda nasan komai muna dashi yanzu saidai in za a karo munane mun gode amma ba abinda babu gaskiya. Alright bari in naje masu sayayya sai a hado da naku barin saukeki sai in fita in duba abinda ya dace kinsan iya na gidan yanzu. Duk da nasan banda matsalan hakan don kina iya kokarin ki a kansu amma ina son ki kara kula don Allah iyace makamina Rahama kin sani idan ta tsaya muna komai zai tafi yadda muke so don haka nake son ki kara kula don Allah har ta gama zaman ta kada ki yarda a samu wani matsala daga wajen ki please. Ni dai banda insha Allah ba abinda na iya fada lokacin don na fahinci kamar akwai matsala ko kuma ranshine a bace dai yake hakan. Koda ya saukeni bai shiga gidan ba ya juya ya fita na shigo na samu su iyan da Biba a falo zaune gaidasu nayi na zauna suna min sannu da dawowa. Bayan na zaunane take fadin aina fada baki tsayawa ko ina yanayin karatunkine kawai haka amma baki barin mu da yunwa ko wani abu. Dazun uwarku tazo gidan nan naji dadin da bata sameki a gida ba duk da taso ta dauki hakan da zafi ta juya zancen da wai baki zama gida ? Nace ba inda kike zuwa banda makaranta ai tazo ranan da ba karatu idan bata sameki gida ba wai banson a fadi zancekine nace hakan. Wa yan can gantalalun da take magana meye amfanin zaman gidan nasu ba moriya ke ai neman abinda zai zama maki alheri ga rayuwa kike fitayi. Su kuma fa da zaman gidan bai amfana masu komai sai komawa baya a kullum miji na kumsan bakin ciki a kansu. Batayi fadan hakan ba sai ke da kike fita gun amfanin rayuwanki su yayanta da sukai karatun har wani gari waya matsa masu ? A raina nace aisu yayantane basu laifi niko tsintana sukayi daga sama dole ta kyashewa karatuna din don tun farko ai bataso hakan ba Allah dai ya nufa da sainayi kuma in zauna a karkashin danta da bata so. Ni dai a fili mikewa nayi ina dariya nace iya bari in dan rage kayana in watsa ruwa na nufi dakina ina kwalawa biba kira data dauko min ruwa insha. Naji iya din na mata fada akan hakan da bata ganin yadda nakewa duk wanda ya shigo ai kaba mutum ruwa arzikine ba sai ya roka ba. Wanka nayi na fito na zauna ina cin abinci muna dan taba hira da iyan take fadin mijinki ya fada maki yau matanshi zasu karbi girki ko ? Don sun kaishi kara yafi a kirga wai yazo ya tare a gidan ki ya fita batunsu nace yayi hakkuri ya koma can din Allah ya isar masa da duk tsiyar da zasuyi mai tunda haka uwarsa ke so. Ga abin magana da zata tsaya tayi magana akansa ta kasa sai inda ake ganin mutuncinta nan take neman barar da mutuncin nata. Yaron nan Yazidu ya kyauta min ashe duk dadewan nan aurensa yayi a can bai fadawa kowa ba sai kwanan nan ya sanar da yayansa hakan. Harda haihuwansa yanzu gashi zai dawo gida saita sake maki mara ita da magoya bayansa su farwa matar nasa kuma tunda karuwane basu so cikin zuria. Yayi aure iya na tambaya cikin mamaki tace yayi aurensa wallahi matarsa harda haihuwa biyu tayi mashi mace dana miji yara masu kyau kamarki haka ? Taso tayi fada nace fadan me zakiyi abinda yake sone yayi banga dalilin sakawa yara ido kan zama da iyalinsu ba don ita aiba haka mukai mata ba. Zai dawo dai yanzu wanan gidan na kusa daku da ake gyara a nan zai zauna shima habu ashe duk nan zasu dawo din da zama. Ai Jafar shine maganinta da yake abinsa yanzu ba shawara sai ya gama yake fada masu wai kuma sun samu hakan sun tsaya fadan jin dadi. Nayi masu tas yau haka kuma nace dashi munafukin yayi gagawan kai yar uwarsa inda sukaje can wai wani bakin ruwa wajen wasu masunta masu bin ruwa . Har can yaje ya samo abinda ya zama wahala a yanzu garesu tun lokacin na fada mai suyi hakkuri komai na Allah ne amma basuji ba Allah dai yasa su samu matar a raye ? Amin na amsa dashi yayin da gabana ya fadi don in bata raye hakan yana nufin rayuwan yaya yana cikin matsala ke nan ? Har ya dawo da kaya niki niki Biba ta fita tayi ta kwasowa har abinda muke dashi da yawa duk ya karo muna anzuba a kitchen din mu na mike mukai ma komai muhalinsa nan yayi magariba da isha,i sai wajajen tara ina daki kwance ina waya ya shigo dakin nawa. Kamshin da yakeyi yasa na dago kai duk da nasaba ganin hakan amma na danji ba dadi a raina kishi kumallon mata watau kishin nan akwai ga ko wata mace saidai ka danne kawai shine mafita. Ni zan tafi ya fada ya tsaya akaina ban dago ba nace Allah ya bamu alheri sai naga yayi tsaye yana kallona. Ganin hakan yasa na dago na kalleshi ni din yake kallo yayi murmushi ya girgiza kanshi yana fadin in fasa zuwa ke nan ko ? Da sauri nace nina isa in samesu da mijinsu ince kada kaje gunsu ai sai ace da gaske nice ke hanaka kulasu din da ake fada. Ok kin yarda ke nan kema ban kulasu ko nace ai haka ake fada don na fada shine na yarda to haka zaki sallemi idan ba fushi kikeyi ba ? Har lokacin fuskana ba annuri nace to wani irin sallama zan maka yaya ok to barin zauna idan kin tuna sai kiyi min in tafi. Ganin yana kokarin kaiwa zaune mannin jikina hakan yasa na dan zabura ina fadin wallahi ba ruwana kada kasa gobe mama tayi muna sammako a gidan nan. Bai kaiga karasawa ba naji ya hade bakin mu waje daya danasa yana tsotso na samu na kwace kaina gareshi yana fadin rowan jikin ki kike min ke nan yau ko ? Banice da jikinka ba shiyasa ban maka rowa ba aika sani haka dai ya gama dan kame kamenshi yana fadin naje na rakashi dole na taso har wajen mota na rakashi nayi mai saida safe ya tafi. Dakin iya na leka ina mata saida safe take fadin Jafarun ya tafi ko nace ehh iya na dan zauna na dan wani lokaci kafin na mike zuwa daki na kwanta. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/17, 08:36] Buhainat: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/C8kkr4INYY7FydHKKKRVhL{2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 6️⃣0️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Nagama shiri zan kwanta kiranshi ya shigo min nayi mamakin ganin kiranshi na daga tare da sallama a bakina ya amsa yana fadin baki barci ba ke nan har yanzu ? Na amsa mai da fadin yanzu dai zan kwanta ina wajen iya muna hira yace keda kike da exam gabanki zaki tsaya hira da iya ? Murmushi kawai na iya yi ba tare da furta mai komai ba sai naji yace nima gani nan ina kewarki yau duk sai naji dakin nawa daban kamar ban saba kwana a cikinsa ba. Na miji ke nan wanda keda mata biyu a kusa dashi ya fake da fadin hakan don dadin baki irin na maza don kawai ya faranta min rai nasan ya fadi hakan. Ban karasa mamakinsa ba na sake jin yana fadin kilama zan dawo nan in kwanta abina don kewanki a kusa dani da banji ba duk ya kashe min jikina yau. Ni dai yaya saida safe don Allah kada kasa mai girki tace ko a can kana tare dani manne a waya ina fadan hakan naji yana fadin . Baki yarda da abinda na fadaba ke nan kashe wayan nayi ina jan tsuki na wurgata gefen filo waini yaya ya mayar karamar yarinya ya faki odon matansa yazo yana min dadin baki . Nasan zai kira yaji wayan a kashe kamar yadda na saba tofe dakina da addua haka nayi don tunkan inshigo na rufe ko ina na gidan biba kuma zata kwana da iya don tare suke kwana a dakin dama da ita. Haka na kwana ina juyi washegari na tashi kamar kullum karfe bakwai duk nagama komai har na shirya don tafiya karyawa ne ya rage muyi nida Biba . Ina saka hijab naji muryanshi a falo nayi mamakin hakan sosai yadda ya baro can gidan a wanan lokacin haka ? Ya leko dakin yana waya na dake ina mashi ina kwana ya amsa ya kashe wayan yana fadin meyasa kika kashe min waya jiya Rahama nazo kuma na samu kun rufe gida ? Kazo fa yaya haba dai kadai fada ina zakazo karfe goma fa da yan mintuna lokacin ai Oh kina zaton karyane banzo ba din to ki tambayi maigadi idan kin fita. Banso ina waya da mutum ya kashe min waya hakan yana bata min rai sosai wallahi ba wani gargada nace dashi iam sorry gani nayi zamu shiga hakkin wace ke tare dakai lokacin. Ni hakkina da sukeci fa ya fada yana nufoni sai muryan iya mukaji tana fasin wai Jafarune da safe haka ince dai lafiya ka fito gida wanan lokacin kuma ? Iya nine ya fada yana kutawa ya fita ina jinshi yana fadin nazo nakaisu makarantane kada su makara don da motarsu na tafi can jiya din. Allah sarki nikan nace to lafiya ka fito a yanzu da safe haka to ya kwanan mutanen gidan ya amsa yana zama falon yace lafiya kowa yake sai yaron nan Abba dan wajen Habu shine dai jikinshi ba dadi har yanzu wallahi. Yo ina zaiyi lafiya dama yasha allurai da kwayoyi tun a cikin uwarshi dole sai an zuba mashi ai yayi lafiya ai illan asibitin ke nan dama irin hakan baku ganewa ne dai . Banji dadin jin Abba ba lafiya ba don mijin yar uwata bai gari shi yanzu habu sam baya zama gida ko kadan ko yaushe yana wajen aikinsa ni har takan ban tausayi wani lokaci saidai ita sam bata damu da hakan ba. Naji kamar in tokesa ya kaini idan mun fita saidai kuma zan iya makara idan nace hakan muka karya a gurguje muka fito munawa iya sai mun dawo. Tun a gabana yake fadin zan biya gida in dauko maki salima tazo ta tayaki zama kada a barki ke kadai . Amma sai naji iyan tace ka barta zanyi ibadana idan nagaji kuma sai in dan kwanta kafin su dawo tunda ba har dare suke kaiwa ba a can. Muna gaba zaune biba tana bayan mota zaune yaja motan muka fice a gidan saida muka sauke biba yaja mota banyi aune ba naji hannusa cikin nawa yana tuki da hannu daya kallonsa nayi na dan sauke murmushi naji yace dani. I love you with all my heart yana lumshe idonshi naso ki rubuta exam ina garin nan gashi zan koma next week don kayan mu ya kammalu. Yanzu mutane su fara gane harkan donshine bamu tsayawa bata lokaci da zaran kayan ya kammalu nake mikashi can wajen masaya. Zan barki da iya don zamanta a nan tare daku hankalina yafi kwanciya da hakan nasan babu wani wanda zaiyi ganganci zo maki gida da izgili tunda tana tare dake yanzu duk da nasan mama ba zata yarda da hakan ba amma zan fara zama da iya din inji ra,ayinta. Nasan ba zataki ba ai saidai idan taki kada ka matsa har ayi tashin hankali Allah yana tare damu ai ba abinda zai samemu in sha Allahu. Tafiyan da yakeyi da motan a lokacin ba wani gudu yakeyi ba har muka kai muna zance guda ya saukeni nayi mai godiya yaja mota ya tafi. Kwananshi hudu can gidan tare da iyalinshi inda nayi kokarin danne zuciyana ban yarda na nuna hakan ya dameni ba a fili amma kasan raina akwai kishin hakan sosai da nake ji. Don idan yazo yana dan kame kameshi sai na dinga jin haushin hakan bayan ya gama masu abinda kilama yafi wanda yake min nan zai dawo yana nuna min irin damuwan da yakeyi dani din. Ranan da zai dawo gidana duk shawaran da anty salma taban shinayi na kuma ga farin cikin hakan a tare dashi sosai don ga iya a falon amma duk inda nabi idonsa yana kaina tunda yazo kuma bai fita zuwa can gidan ba kamar yadda yakan muna zai dawo yakai goma ya koma gida sai kuma da safe idan ya dawo. Niko nasan nayi shiri din don ni aka bari da tsamin jiki a karshe inda Allah ya taimakeni ranan ba school donshi na dan kai wani lokaci kwance ban fito ba sai takwas da rabi. Inda nafito na samu Biba har ta dafa ruwan zafi tana fere dankali donshi a rayuwanshi nafahinci yafi son dankali irish da safe wanan yasa nake kokarin soyawa wajen karyawan mu. Nakan sarrafa masashi nau,i nau,i wani lokaci haka kuma duk yadda na sarrafa din zai zauna yacishi sosai da safen . Faten dankalin da kayan cikin da nasa biba ta yanka kanana nayi muna inda na dan sakewa dankali ruwa sai kuma muka hada ferfesu kai shanu da ya kwana saman wuta a hade. Sai ruwan shayi mai kauri da yaji kayan kamshi wanda mukeyi a gidan maman Abuja mun kammala na jera a dinning din don ko iya ban dibar mata nata daban ba a ranan saboda ina son mu zauna a karya gaba daya yau a gidan. Wanka na shiga na tsala kwaliya a cikin atamfa da akai min dinkin buje da riga kayan yayi matukar karban jikina sosai dan takalma flat na zaman gida na fito dashi zuwa dakinsa. Barcinsa na samu yanayi hankali kwance na kai zaune a gefenshi yadda zaiji motsina a lokacin. Hakanne ya faru don ko second banyi da zama ba naga ya dan bude idonsa dake cikin nauyin barci yana kallona murmshi na sakar mashi ina fadin barcin ya isa haka yayan mu ka tashi ka watsa ruwa iya tana jiran ka mu karya don tare zamu karya yau da ita. Ido naga ya lumshe yana jawoni zuwa jikinsa na dan fada ya sauke nufashi yana fadin bason haka ba sai ince ki bari in biyaki kudin wanan kwaliyan naki don Allah ? Ba saika biya ba tunda ka yaba ka tashi dai a karya kada iya taga nawana wajen bata abin karyawa yau ta dauka ban damu da ita bane. Yau ba school ke nan nace ehh ina mikewa ban faye shiga ba irin yau don lecture gudane gareni malamin ma kuma ance baya gari yayi tafiya. Ok ya fada yana miko min hannayesa biyu da alaman wai in dagashi daga kwancen banki ba na mika mashi hannayena din ya mike zaune bandaki ya shiga na mike na wce wajen iya. Tana zaune tana dan hira da biba nashigo ina gaida ita da kwana na samu biba tayi wanka tana shafa mai nace kiyi ki shirya ga uncle nan zai fito muje falo mu karya a can yau. Bidiri yau da mai gidan za a karya ke nan nayi murmushi nace iya ai hakan sunnane a musulunci zama tare da iyali a danji korafin kowa hakan yana kuma kawo shakuwa a tsakani akace . Don sammakon da mukeyine muna fita yasa ba a samun yin hakan wani lokaci don yadda muke karyawa a gurguje kadin mu fita. Dolene miji ya kulaka ai yar nan duk sauri da abinda ke gabanki baki gaza bashi kulawanki haka nima nan da yar nan me zai hana mace ta sace zuciyat mijinta tana hakan. Abinda suka gaza ganewa ke nan ba asiri bane ke sa miji karkata sai tsaban kulawan mace wata mace bata dogara ga asiri ko wani siri ba akan miji sai zalla tsaban kyautatawa da take masa yake sa miji ya ahagala a kanta haka . Dan zaman na fahinci komai game da zamantakewan ku gidan nan akwai banbanci sosai a gidan nan da can gidanmu . Wa zai zauna ya baka kulawansa irin hakan da kikeyi mace tasan muhinmancin da darajan namiji haka ace miji ba zai bata kulawansa ba wanan ai karyane. Barsu can su zauna suna kishin hauka da bai fishesu ga abinda ya dace suyi amma haka zasu barshi har sha daya wani lokacin wai ba a gama abin karyawa ba. Toke iya waya tambayeki muryan Biba ya katse mata maganan ta mika mata dakuwa da hannu daga inda take zaune tana fadin ungo naki nan yan nema idan zaki mai da hankali ki koya a wajen yarinyar nan gara ki koya ki tashi da wanan halin duk da naga kina da kwazon kima kinayin komai yadda ya dace. Ni dai ina gefe zaune bakin gado ina murmushi nace iya kinsan taji kina zancen iyayyenta shine ranta ya baci. Kai anty ni da nake shan harara wajen mummy ko ranan sunna gani zaune tana raba abu data kawo kaina ta tsalakeni taba ta kusa dani ko ruwa saida dare mummy salima data ban abinci nasha ruwa a gidan nan ranan. Kinji ko ai kinji tsiyar basu da hankali ke meye naki a ciki ina mijinsu ya kawoki nan zama ko wajensu kuma yana iya kaiki ai inga halin arziki ai. Sun kasa gane hakan da sukeyi suna bata kansune a wajen yan uwa duk da yan uwan suka nuna masu sunfisu daraja bakomai bane kuma hakan sai kwadayin duniya. Ai kinga uwarki da yar uwarta da suka kama kansu inba wani dalili mai karfi ba basu zuwa gidan balle su shiga shirginsu din bakiga suna mutuntasu ba dole tundai Rukkaiya da bata daukan raini. Shigowansa ya katse masu zancen yashigo yana fadin iya kedawa ke fada haka tunda safe tun ina falo nake jin muryan ki ? Nida sarakunan kishin nan mana matanka su nake zankada tunda safe matarka tace damu yau tare zamu karya dakai shine abin yaban sha,awa nake fada dasu. Murmushi yayi yana kallona yace haka tace ta hanani barci wai in taso kada mu barki da yunwa kiga laifinta ? Ina laifi yar nan kin maisheni kamar basaraka ko sarakuwar uwarku ban samu rabin gatan nan a wajenta ba gashi na samu ga jikokina. Iya ai dole muyi maki kece fa gatan mu ga baki daya in ba ai maki abinda zakiji dadi ba aiwa,washi iya na fada na mike ina jin tana fadin cikin raha ashe gaskiyane akwai mata masu tsoron kishiya gashi ko nagani a yau. Falon muka fito gaba dayan mu nan aka zauna saman babban shimfidan da nayi maimakon danning din saboda tsohuwar na fara zuba abincin sai kamshi ke tashi . Yayin da iya ke faman zuba cikin washe baki da jin dadi muna tsaka da cin abincin sai sallaman mama mukaji da kawu sun shigo. Kawu yana fadin a,a lalai iya kan ba zata koma gida ba ana haka duk wanan didiman haka iya ? Kayi bakin ciki da hakan ne tunda ka kasa danka ya dauka yanayi ko iyan ta fada na yunkura na mike ina mai barin abincin tare dayi masu sannu da zuwa. Na gaidasu suka amsa kawu yana fadin nina isa in bakin ciki iya tunda jafaru ya kama muna ni dama nace da wuya iya kiyi zancen gida a yanzu tunda mukajiki shiru haka ashe dadi jafaru ke narka maki a nan haka ? Ta sake fadan kayi bakin ciki ke nan nace aka kwashe da dariya mama idonta yana kan plate din abincin kowa take fadin. Ai dole ta koma gida tunda a can take gamu sai zaraya ta barmu munayi zuwa nan dubanta sai iyan tace na hutar daku ku zauna gidan ku nan kan banda ranam bari inma daukana kukazo yi to ba zani ba. Kitchen na nufa na barsu suna drama da tsohuwar tasu har na dawo na aje plate din a gabansu ina kokarin zuba masu abincinne mamatace nikan a koshe nake ban fito da yunwa ba. Ai badon yunwa zata zuba maki ba dubu tunda tasan mijinta bai kaza dake ba kamar yadda ya bayar nan ya baku a can ai. Amma karrama bako yana cikin koyi da sunnan ma,aikin Allah ai ko kin isa kija da hakan kuma yanzu baki zuwa gidan nan kice wai a koshe kike baki fito gidanki da yunwa ba ke ? Iya idan ban koshi ba ai zanci koda yaya yazo daukata ya samu ina cin abinci gashi nan ki tambayeshi ? Amma ba irin wanan bako nidai na zuba nakai plate din a gabansu ina daukan nawa na mike inacewa biba ta taso muje daki muci. Shidai yana zaune yana jinsu sai abincinshi yakeci kawu ya fara jawo nasa plate din ya kawo gabanshi ya soma ci ya fara fadin dubu kici abincin nan kada mu kwareki don Allah. Ina iya zata yarda ta koma can tana hada wanan a rana haka kafin yakai karshe tsohuwar tace ance kaci mai dadi idan ka samu daman hakan. Can babu mai dadin ne iya wanan ai sai a dauka can bamu da irin cimar nan a can din sai dai ace kawai gyaran ba daya bane kawai. Ina gyara zaizo daya dubu tunda ilimin abin ba daya ba kefa dubu duk abinda zaki fada iya ba jinki zatayi ba a yanzu don haka kiyi shiru kawai da zancen nan . Iya munzo akan maganan yaron nan Yazid ne da Jafar ya sanar damu dawowanshi wai kuma har da iyalinsa yanzu iya ga Jafar fisabilillah abinda yaron nan ya aikata muna yayi daidai ke nan ? Ace wai yazid daga zuwa karatu yaje kasan mutane yayi aure a can bada sanin kowa ba a cikin mu ina shi ina zuwa auren wani kasa iya don Allah ? Zakija da ikon Allah ke nan ko duk abinda bawa yayi mukkadarine garesa dama dalilin hakan yaje kasan da sunan karatu don ya hadu da matar nasa hausawa sunce matar mutum kabarinsa ai . Koda rarafe sai yaje tunda Allah yayi a can matar nasa take kuma dan uwansa ya fada maki dalilin hakan to meye na damuwan zuciyarki ke a yanzu ? Iya ba hakana bane naga kayi aure a gida ka auri matar da akasan dabi,u sunzo daidai yaya aka kare balle ka dauko a wani kasa kazo da ita nan ? Idan yazo kuma yace saman kanki ko a karkashin wani zai zauna da iyalin nashine wai meyasa kukewa aure shigan kutsu dubu aurensane bancin ranki a yanzu ko dawowansa kusa daku ? Iya abinda nake son ki fahinci dubu a nan shine da yaron nan ya dawo gida yayi aurensa a cikin gata kamar yadda kowa keyi zaifi mutunci kinsan halin mutanen yanzu da maganan da bai shafesu ba iya. Sai abarsu suyi tayi yanzu ai tunda aikin gama ya gama ko aure harda haihuwa biyu yanzu meya rage don Allah ? Ni kawu banga abin tayar da hankali ba a nan tunda shi zai zauna da matarshi na fadawa mama addua kawai zata bisu dashi yanzu don Allah. Yaron nan da karatunsa inma yace bai sana,an nan sai aikin gwaunatine yana dai da ilimin sa ko da zai iya rike iyalinsa tunda acan aiba mu ke rike mashi dasu ba. Yarinyace karama kwarai matar nasa yar wani malaminsune yaga kirkinsa ya aura mashi yarsa ba ba tare daya san kowa nasaba fa mama . Yanzu kuma munan sai muce hakan bai muna ba mu nuna bamu ksunat yarsa mu don kawai bata fito cikin nahiyar mu ba amma dai ai musulmace ko ? Nasan dama bakin ku daya dashi tunda kai ya iya fadawa zancen ai dole ka fito da wanan zancen yanzu baka son a fada tunda kuma kun auro matanda suke son sunfi karfin mu. Zancen duk a kunnena yake muke nan mama ke nufin muna son fin karfinsu da mukai mata me na rashin mutunci don kawai mun fito yayan fulani ba zage zagi ba kome ? Saidai kafin nakai karshen maganan zucina naji iya na fadin shi auren kabila ai ba bakon abu bane don kowa yayi a cikin mu dagani har ke kuwa dubu ? Mahaifinki ai asalinsa banufene suka dawo nan da zama aka saje kuma na aurensa tun asalin yarensu bai bace ba haka kema kuma kika auri mahaifin yaran nan kowa garin nan yasan zuwa Alh yayi garin nan nema daga Adamawa koba haka bane meye bambancin zance a nan ? Sai mama din tasa kuka don me iyan ta fadi hakan Biba najin kukan mama ta mike tsaye kamar zata fita a dakin na zabga mata harara ina fadin karki soma haka ace dake munafuka. Yaya irin abinda nake gudu ke nan tunda Habu yazo da zancen aurensa naso hanawa amma ka daure masa gindi akan babu komai gashi. Jin dadin auren har kanwarta ta cinnawa shi Jafar a yanzu gaba daya kowa yasan yaran ran sun juye min kan yara don ba haka na tarbiyarta da yarana ba duk kun sani a nan ? Dubu ki shiga hankalinki wallahi kafin na saba maki a wajen nan meye hadin auren Yazidu dana jafaru kona habu yanzu ? Kin fa kusa kai yaran nan makura akan zancen nan idan yaran ku sun sauya ku kuka sauyasu ai ba wasu ba ? Ko har kin manta da cin mutuncin da kukai mai keda diyan ki da dan uwanki gashi ? Nace kin mantane in tuna maki yanzu yadda suka zugaki idonki ya rufe akan danki dake tausayin ki kan dukiyan da yake kula maku dashi yanzu ina dukiya nan ku yake ina tambayanki dubu ? Iya meya kawo wanan zancen ai taimakonshi akayi don an karbi dukiya a hannunsa haka kuma shi bai nuna komai don an karba ai kawu dauda yake fadan hakan ga iyan. Haka zakace tunda ka damka kana bushashanka dasu ai dole kace bai nuna bacin ransa ba ko tunda shi ba mutum bane ko ? To in baku sani ba ku sani duk da kuna ganin bai sauya ba dole abinda akai mashi ya bata mashi rai don haka kuyi kuka da kanku kada ku dora laifin ga yayan mutane da basuji ba basu gani ba . Aure kuma mukaddarine ko a ina matanka take sai kaje ka aurota don haka ina son ku fitar da idon ku akan yaran nan daga yau jafar dai yana zaune da matanshi lafiya inma wani abune kece dai dashi dauda gashi kune matsalan yaranku nan ba wasu ba. Kuka mama din ta kara dorawa sosai tana fadin meye zaisa aga laifinta shi kuma kawu yana yan kame kame nan dai basuji din zuwan ba don tsohuwar bata yarda da zancen da suka zo dashi ba din. Tace kowa ya fitar da idonsa kan yaran nan da matansu inba rashin hankali ba yaran nan meye matsalansu da auren yayan ku da kuke son sakasu gaba hakane ? Ke in kina da hankali yadda yaran nan keda tarbiya ai abin farinciki ne ya sameki ba wanan hakan da kikeyi a yanzu ba haka akan matan yayan ki. Sai yanzu na kara tabbatar da kinfi bukatan ganinsu cikin tashin hankali da matayen nasu sama da zaman lafiyan da sukeyi ashe ? Ga dan uwankinan inba ya zama munafuki ba da bai iya fada maki gaskiya sai akasin hakan ko yaushe shi yanzu daya samu wata da take dadada masa ai gashi da tsufansa yana sabari a kanta da yayan angolan datazo mashi dasu gidansa. Kiyiwa kanki karatun ta natsu tun kafin yaran na su gane nufinki a kansu dubu su fara mayar maki da martani don dai yayanki ba rabuwa zasuyi dasu ba kin sani. Ba kansu ai aka fara irin wanan hadin ba tunda Allah bai hana ba har uba yakan auri kanwa da ya auri ya duk bai zama illa ba sai a gidan ki dubu kina kokari kija da ayar Allah da Annabinsa a nan kinki kwantar da hankalinki kiki bari na yaro ya kwanta kuma ? Yazidu kuma kinsanshi kinsan halinsa to ki matsa dubu kikai ga abinda ba aso akai din har yan uwanki su samu shiga kina kallo ke kikajawa kanki hakan kuma ba wani ba ? Nina rasa gane matsalan ki idan na tariyo sai inga duk laifin na daudane don ke kamar kanki a burge yake yanzu tun mutuwan mijiku kuwa nake hango hakan dama shine katangan daya tare duk wasu matsalolin da za a fahinci hakan a gareki. Yanzu dai shawaran da zan bayar a nan shine ita mama tayi hakkuri har yazid din yazo da matar nasa aga mata wace irin rayuwa ke gareta don Allah a fanci juna shine zaifi tunda ya riga yayi wanan kuskuren ko ? Banso dubu ta matsa akan zancen nan ba amma tace sai mu taso a san yadda za ayi ya baro matarsa ya dawo nan shi kadai kawu ke fadan hakan . Iya tace kaji shirme ko na fada maku dubu ta canza a yanzu ina kuka kwana da zancen da nayi maku zuwa biyan bashin dake kankune dauda ? Wanan ya kamata ace kunyi ba wanan shirme ba dakukeyi a yanzu auren da aka samu zuria a tsakani ina ke ina shiga tsakaninsa kuma yanzu ? Zamuje iya wajen ne yake da wahalan zuwa amma za aje din tace sai yaushe zaku tafi ko sai kunga sun fara zaran yaran daya bayan daya zaku maida hankali ga tafiyan ? Goben nan ko jibi nake son duk abinda kukeyi ku maida hankali a tafi wajen nan don naji jafaru yana zancen komawa wajen sana,anshi cikin kwanakin nan. Zubur kawu yayi yana fadin gobe iya iya tace kwarai kai harni zamu tafi ba wai ku kadai ba idan baku shirya ba kuyi kwatance mu tafi nida yaran nan . Ku diba yaron nan ko bai fada ba ansan da abinda ke damunsa don yana namijin tsayene baku gane hakan sai ya fadi kasa kuji dadin hakan ? sorry for missing me wlh iam surfering for tooth pain all dis days yasa kukajini shiru. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/17, 08:36] Buhainat: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/C8kkr4INYY7FydHKKKRVhL{2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 6️⃣1️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Motsin kwarai na kasayi a lokacin gashi dai naji fitansu amma jikina ya mutu jikina ya mutu na kasa motsin kwarai sai dubawa nakeyi ina aunawa me nayiwa mama dani da yar uwata a zaman mu da ita ? Saidai na kasa hango inda laifin namu yake gareta matsala dai daya shine zance ko yar uwata data dade a tare dasu bata taba kai korafin mijinta gun mama ba yadda sauran surukanta keyi . Haka kuma bata taba fadawa mama wani matsala daya shafi aurensu har asani manya su zauna dasu ayi sulhun hakan . To balleni da ko shekara banyi a cikin su ba ince mata me akan zama da danta me zan fada ya hadani dashi ko abokan zama da ba waje daya muke rayuwa ba balle kuma ai bai mun wani abinda zankai karanshi wajenta ba yadda take so. Ni dai a ganina wanan ne kawai matsalan amma bansan abinda ke boye ba a zuciyarta amma tsanan yayi yawa a zuciyar mama kan mu. Ban san hawaye na zuba min ba a idanu ina dai kwancene kawai naji muryanshi a kaina yana fadin kuka kuma Rahama meya sameki kike kuka haka kuma ? Dan yunkurawa nayi ina kokarn mikewa zaune saidai kukan yaki tsaya min naga yakai zaune gefena ya sake fadi cikin kallona meya sameki Rahama ? Cikin muryan kuka na daure na iya furta ba komai ina sheshekan kuka tare da kokarin kauda kaina a gefen da yake zaunen. Umm,humm Rahama idan kince kuka zaki dingayi kan mama zaki sha wahala sosai a rayuwan ki don inkin duba bake taiwa hakan ba ni tayiwa don nine zaune dake. Duk abinda takeyi bake takewa ba don nine take hakan kuma zata bari in sha Allahu ki dai kara hakkuri nasan kinayi baga mama ba harda kannena musanman Saratu nasan duk abinda ke gudana a tsakanin ku. Yanzu haka ina shirin zancen auren sune da zaran Allah ya dawo dani lafiya shine abinda nake son aiwatarwa ke nan a kansu. Ki tashi ki shirya zamu fitane yanzu dani dake jin hakan yasa na dan kalleshi ya gyada kai yace ehh akwai inda nake son mujena kafin na tafi tare dake. Naji hannusa cikin nawa yana dan murzawa alaman bani hakkuri yakeyi a zuciyarshi hakan da yai min sai nake jin sanyi a raina har ya mike yana kara fadin in tashi in shirya kafin ya fito ya fice daga dakin. Can falo nake jin muryanshi da iya suna hira ban tsaya saurarensu ba na shiga shiri simple makeup nayiwa fuskana na fito na samu bai falon saidai ban jima da fitowa ba sai gashi ya fito yake fadin kin fito ? Iya zamu dan fita yau har gidan malam Bala nake son mu leka nida amaryata don yayi min korafi ban kaita sun ganta ba sai labari yaji cewa na kara aure. Yakamata kam ku dinga zumunci don zumunci a kafa yake kuko yaran yanzu kun dauka wanan tangarahon ya wadatar maku kuma ba haka abin yake ba. Don baku da kamar malam bala a fadin garin nan kaf shi zaku diba ku tuna da mahaifin ki nakan so nayi wanan zancen sai in mata gashi yau Allah ya tunar dakai hakan Allah yayi albarka kaji ya kare tsare muna ku. Nuna mata tasan darajanka wajenshi don dama mu mata aka sani da zumunci ke kuma don Allah ki rike ki dinga tunatar dashi tunda shi din ba mai zama bane sosai garin kamar uba yake a wajensu bama kama ba ubanne ai. Tunda mahaifinsu dashi Allah kadai yasan tsakaninsu har mahaifinsu ya kwanta dama suna tare abinsu suna zumuncinsu. Sai mun dawo mukai masu har lokacin zuciyana bai sake ba muka shiga mota ya tayar nan yake fadin na rasa kalman da zanyi amfani dashi na baki hakkuri Rahama ? Naga har yanzu zuciyarki yana da kunci akan zancen nan mama fa matukar tana tare da kawu bamu taba gane kanta yadda ake so don kota dauko hanyar daidai kawu dulmiyan da ita zaiyi so banga abin tsayawa bata rai haka cikin zancen nan ba ? Na dan kalloshi ina sauke ajiyan zuciya da kyat bakina ya budu na iya fadin for god sake me nayiwa mama kome yar uwata tayi mata data tsane mu haka ? Naji yayi murmushi yana kallon hanya na sake fadin nasan tun zamana a gidan ban taba samun matsala da ita ba why a yanzu take nuna min hakan ? Saboda kin auri danta take ganin kunci amananta keda yan uwanki don kuci dukiyata shine kawai kada ki kara haka mama take tun muna yara bata son muyi abokin da zai dauke muna hankali da ita. Ko yaushe mama tafi son ta bude ido ta ganmu a gabanta baki ganin yadda take da yaran nan wanda bai san halinta ba sai yace ta shagwabasune amma halinta ke nan ita taji komai namu tasan duk wani motsin mu kuko ba hakan kuke ba keda Maria. Kawai dai tana ganin a yanzu kune kuke kokarin shiga tsakaninta damu yasa take son sakata a gaba a fahintar ta dai kamar kuna muna wayau ne ko wani abu maka mancin haka dai. Wani kwana naga yabi kafin ya sauka daga titi ya juya zancenshi da fadin kinga tsohon gidan mu da muka taso inda aka haifemu daga baya da mahaifinmu zai auri inna shine muka koma wancan unguwar da muke yanzu don nan din yayi mashi kadan da zama da mata hudu lokacin. Suwa ke gidan yanzu na tsunci bakina da tambaya yace su isa da lawal ke zaune ciki da iyalinsu su suka gaji gidan da akai rabon gadon mu. Suna ganin a lokacin sun kware mu sun samu gida ba irin rigimar da ba ayi ba karshe da muka hakkura sai gashi Allah yai muna sakaiya da mafificin hakan. Dama ance mai hakkuri yana cin riba a rayuwa hakkurinkune yaja maku hakan a yanzu ganin kofan gidab daya tsaya yasa nayi shiru ina bin gidan da kallo. Wani tsoho mai farin gemene zaune saman wani babban tarba da shimfida yana fitara da faifain kaba a hannunsa ya cire babban rigan dake jikinsa saboda zafi . Gashi ya kurawa motar mu idanu nasan yana son sheda mai fitowane yake fadin ga baba Bala can zafin nan ya dameshi sai fifita yakeyi ya samu sa,ida. Nakanso taimaka mashi wallahi sai kuma kamar abinda aka mantar dani sai in manta dashi gaba daya . Fita mukayi daga motan dagani har shi muka nufi wajen tsohon da saida muka matso kusa dashi sosai ya gane dan nasa. Murmushi yayi yana fadin yaro mai sunan manya ashe har yanzu dai halin naka yana nan kamar yadda nasanka a baya. Shima jafar murmushi yayi yana fadin baba anyi mun afuwa dan Allah bawai haka bane abubuwane suke shige mingaba yanzu. Tsohon da duk farin gemune a fuskanshi yake gyara zama yace nasani jafaru ina da labarin komai game daku duka ina tambayan lafiyan ku aiko yaushe gun yan uwanku. Tare muka zube kasa gabanshi muna gaidashi ya amsa yana fadin wanan ce amaryan taka ko don dai ba yargidan registara bace wanan ? Kuma ba wace mukaje kaduna daurin aurenta bace yace baba wanan yar Gembuce can yolan cameroon na aurota. Masha Allah ya fada yana kafeni da ido nayi kasa da kaina a cikin nauyinsa kafin naji yana fadin maddala abu yayi kyau sosai Allah ya bada zaman lafiya. Amarya sai hakkuri kin shigo gidan yawa don haka sai kin hada da hakkuri a zauna lafiya da kowa don Allah bisa ga amana sai kiga Allah na tare maki duk wani farmakin da magauta zasu kai maki a boye. Nagode baba na fada daga inda nake zaune ya maida kallonshi kan Jafar yana fadin man Jafar ya al,amura kuma naji duk abinda ke faruwa game da yan uwanka. Ina son ka kara zama namiji haka kuma lamarin iyayye musanman uwa gashi kuma ita ta rage maku a yanzu da kuke tare da ita don itace zaku kalla kuyi bugun gaba da ita koda bata raye balle tana raye to a kara da hakkuri a samu a rabu lafiya damu dai din don wani lokacin sai an hada dole da hakkuri ake cinma manufa irin yadda kakeyi a yanzu din. Duk daba wai naji taka maimain zancen bane saidai ina son jan hankalinka a nan daka kara daurewa dai ayi biyayyan nan dai da aka saba yi ko yaushe. Haka kema amarya don Allah ki bashi hadin kai ya samu ya aiwatar da manufansa na alheri da yakewa yan uwa da abokan arziki naji komaine a bakin Rukkaiya da Ai don su har gobe basu yadani ba suna min bayayya kamar yadda aka taso a cikinsa. Kwanaki sunzo gaidanine suke ban labarin abinda ke faru shine na nemi ganawa din dakai don in kara ja maka kunne akan hakan nasa kuma kazo min da ita wanan yarinyar na kara tausanta taci gaba da hakkurin da takeyi dai. Nan dai ya danyi nasihanshi muna mashi godiya kafin mu muke zuwa cikin gidan inda naga gidan babban gidane shima kamar na mahaifin su Jafar din don da gani anyi zamani a baya tsufa da karayan arzkine ya taso yanzu. Matan nasa duk sun tsufa ba kamar su inna da su mama dake da dan sauransu ba don basu cikin wahalane nasan irin nasu yasa hakan. Dakin uwargidan nasa mukayi masauki anan muka gaisa da kowa wanda Allah yaba ikon zuwa mu gaisa a gidan don wasu kan basu zo ba suna tsabgansu a lokacin. Wata dattijuwa mai dan tsayi take fadin Jafaru an kun manta damu yanzu koda yake Alh yace baka zama garin ashe har aure ka kara kuma duk bamu da labari sai daga baya. Naji yana fadin iya ayi hakkuri auren ne yazo a haka ba kowane yasan da zancen karin auren nawa ba don daga nemane don nisa iyayyenta sukai muna sauki aka daura auren daga nan. Kai masha Allah kaji mutanen arziki ba masu tunane ai nima nace dai akwai dalili da har Alh baiji ba ashe haka abin ya kasance. Ina kallon ikon Allah don yasan duk wani babba na gidan duk wanda yazo zasu tsaya su gaisa sosai dashi yayi masu alheti ashe dama da shirinsa ya fito ke nan ? Sai biyu saura muka bar gidan bayan ya cikasu da alheri muka dauki hanyar gidan wani wajen gida ukku muka je a ranan sai bayan karfe hudu muka dawo gida. A hanya yake cewa dani bayan ya sauke ajiyan zuciya sai naji yace wallahi sai naji kamar an cire min kaya da naje gidajen nan. Nan ya fara min bayanin yadda alakansu yake nagane zumuncine ya koma kamar yan uwantaka wanda a yanzu mafiyawan sun yarda wanan akidan ta zumuncin haduwa da mutanen da keyi a baya. Bai kai ga ida tunane ba naji yana fadin yanzu sauran mu kaduna kuma in sha Allahu idan na dawo zamuje muyiwa ummah nata wunin acan mu zaga wasu yan uwa a can din don yan uwan mama akasarinsu suna zaune ne a kaduna su. Murmushi nayi don nima hakan yana cikin raina ga mijinta da kokarin kirana mu gaisa kwana bibiyu zai kira waya ya tambayeni muna dai lafiya ko idan mun gama gaisawa kuma yaba umma waya itama mu gaisa. Ganin haka yasa nima yanzu nake kokarin kiransu akai akai tunkan su kirani din mu gaisa don kada ya fahinci ban ra,ayin shi da mahaifiyar mu. Shiko gashi yana kamanta muna din har yaransa mata ya tayar da aka kwana biyu akan suzo su dubani suga yaya zaman mu yake ? Inda wata daga cikinsu take fada min ai tasan Saiba da Asmau a school daya sukayi nan Queen Amina zaria. Take fada min cewa abokaine fa sosai don har provition dinsu a lokacin tare yake saidai kazamaine na gaske kowa yasan su da kazanta ko yanzu sun barine take tambayana hakan ? Nayi murmushi ina fadin wallahi ban sani ba don ba shiga wajensu nakeyi bani koda na zauna gidan kowa da part dinsa saitace ki daiyi hankali dasu don ba karamar yar shige shige bace Nusaiban nan. Don abinda tayi ke nan ta kwacewa kawarta miji ance kuma zaman nasu ba dadi a tsakaninsu itace ke juya kan gidan sun mayar da Asmaun kamar shasha ita da mijin ku. Nan ma dai dariya nayi ina fadin ba gaskiya bane anty kowa dai da irin tasa ai sai yar uwarta da suke kira da Laraba tace nikan dai haka zance kina nufin in bata gane komai zata kai hakane a gidan ai da ta bar gidan don cin fuskan yayi yawa ai ? Gaskiya kowa da irin nasa suna dai rigima sosai amma kuma ba wai yadda ake nufi suke zaune ba don naga yana kokari da kowansu sai yamma ranan suka bar zaria. Murmushi nayi don tuna hakan nasan mutane akwai fadin abinda bai shafesu ba nasan ko yanzu nima da akwai abinda ake fada a kaina zama tare dasu din. Muna shiga gida iya ke fadin haba dai har ina batun soma cigiyar ku a gari haka shiru daga fadin bari muje mu dawo yanzu sai kuma shiru ? Yakai zaune yana fadin iya wanan mai kukan banza dince na fita da ita taga dangi dangina su ganta kada in barta gida ta cika muna kunnuwa da kuka haka . Kuka kuma jam da akai mata me yayi dariya yana daukan ruwan da Biba ta aje muna yana balle gora yace kinsan duk abinda mama suka fada dazun ai tana ji nasan shine yasata kuka kila ? Ehh banga laifinta ba don ko nice hakan zanyi tunda nasan banyi komai ba don na auri danki kawai zaki dauki karan tsana ki saka min ? Ba laifin kowa bane kaifin Daudane shike zugota anzo nan sai ya noke zai jini ai don bashi na basu dama so nake mu kebe dasu in masu iyaka da hakan . Ta bari daga yau idan ka taka kafa wajenta ta fadama duk abinda tayi niyar fada amma a gaban yarinyar nan haka kiri kiri ? Tajuyo gareni tana fadin kinga mutumiyata irin hakan ba kuka akeyi ba nasan akwai cin rai amma ki daure kada ki kara yarda ki nuna abin yanaci maki rai don in kin yarda tasan hakan ba zata daina ba tunda halintane hakan ai. Abunda na dauka shine harda son da Dubu keyiwa yaranta shine yake sakata hakan a yanzu tana ganin auren yaran nan da kukayi yana son yasa kan yayan ta ya juye ta kasa gane masu. Wanan shine kawai abinda tunanena yake bani akan halin nan nata don ko zama kayi da ita a yanzu kace mai yaran nan sukai mata ba zatace ga laifinsu ba amma zan zauna din inji inda matsalan yake don a gyara. Iya da kin barta don kada ta dauka kuma anyi wani abune yasa kike tambayanta idan anyi hakkuri ai abin mai wucewane in sha Allahu. Matsala dai a yanzu shine na farko kan auren yaran nan Saratu da Salima ya kamata suyi aure hakana zaman nasu ya fara damuna har ita Nafisa nake son a hadasu lokaci guda in hakan zai samu. Wanan shine daidai don matukar wanan saratun na gaban mahaifiyar ku a kullum zancen bai karewa tunda itace mai kai mata tsegumi akan matanka saidai taki yarda itace matsalan rayuwan nata. Nan na mike na barsu suna zancen sun jima don bai fita ba sai kusan magariba nasan daga masalaci can gidan ya nufa wajen matanshi yakai goma na dare bai dawo ba. Koda ya dawo din muna falo zaune ana hira ya shigo da ledoji a hannunsa a gaban iya ya aje ya mika mata daya yana zama yake fadin na rasa irin sakaci na Asmau iya ? Wai ace mace na jego bata iya kula da kanta balle yaron nan koda naje gidan gashi tace baida lafiya amma ta sake fanka har karshe ko rigan kirki bata sakawa yaron nan ba iya ? Asmau ai halinta sai Allah na rasa meye matsalan yarinyar nan ko wanan babban ai Allah ne ya raya mata ita don komai safiya haka zaka ganta da dan pant a jiki in anyi magana tace zafi. Yaja tsuki na kalleshi a gajiye ina fadin abinci fa ya dago yana fadin bar abincin nan Rahama wanan dai zan danci in kwanta tunda naje muka fita zuwa asibiti sai bayan isha,i muka dawo. Yanzu dai likita ya fada mata ai idan kasheshi take sonyi ai sai ta matsa kada ta kula dashi din na rasa meye matsalan Asmau wallahi ? Bata da matsalan komai sakacine kawai yake damun ta inka duba kamar ai haka yan gidansu suke a watse kowa abinda yaga dama yakeyi a gidansu. Rayuwane na zaman kishin matan yanzu ya haifar masu da hakan tunda kowa dansa ya sani a gidan ba mai tsayawa yayiwa dan wani fada kan abinda ya dace yayi makyau in bashi ba ko ita wanan ma,aikaciyar matan mahaifin nasu ai naga zata iya basu tarbiyan daya dace ai amma ina sun yafawa kansu zama na cin kai a tsakaninsu kowa na jiran wani sheri ya fito daga dan uwansa. To irin abinda akewa gudu ke nan ga wanan zaman ko kuna abinku kada ku yarda ku hada da yaran ku kuyi kishin ku ku kadai su kuma yara ku barsu suyi zumuncin su tunda Allah ya hada zama a tare. Na mike a kasalace zuwa kitchen na kwaso plate na kawo masu na iyan na fara budewa sai kamshi ke tashi na zube mata namane na rago da aka gadashi da zafinsa da yaji sai abinsha. Haka sauran ledan kuma suma suke ina kokarin zube masa nasane wayanshi ya dauki kara ya duba naga ya dauka a yanayin yadda yake magana don jin da nayi yana fadin ni gani gida ai. Ba nashiga sallama dake kina ganina kikaki aje wayarki ba na juya nikan wajen biba ina fadin hjy habiba ko kin koshine sai gobe zakici ? Da sauri take fadin haba anty saida idan zan aje naci na iya gobe naci nawa na fita dashi zuwa school ko ? Kaji yar wayau nice bansan dadi ba miko min nata in karama dashi nan kinji iyan ke fada muna dariya muryanshi ya katsemu don tsawan da yayi yana fadin. Wai kina da hankali kuwa Saiba in dawo in maki me tun dazun da nake gidan meyasa baki fada min ba sai yanzu wai meye matsalanki daine dani haka ? Look Nusaiba duk abinda kike nema dani fa zaki sameshi ina jin ta kashe wayartsne shine yasa yaja tsuki yana aje wayan a saman table din gabanshi. Matarkace ko iya ta fada yaja tsuki yana fadin itace don rainin wayau wai sai in dawo in sayo masu magani ita da laila yanzu wai ai suma basu da lafiya na kyalesu. Murmushi iya tayi tana fadin karma ranka ya baci halintane hakan kayi hakkur da abinka wasu mata basu da hakkurin saka ido akan abinda akaiwa yan uwa sai sun maganta wanda hakan ke jawo bacin rai a karshe. To iya haka zan zauna da ita kullum a cikin matsala ban isa inyiwa wata abuba sai tace don me ni wanan abin ya isheni wallahi kullum ita dai ban mata daidai ba a rayuwanta. Shiru falon yayi na dan lokaci ya karaci fadanshi shima yayi shiru din don ba wanda ya tanka masa kuma dama kuma ai iyance daidai ta tanka ta kuma bashi amsa ai. A raina nake fadin ke nan har yanzu badani kadai take kishinta ba ashe dukkan mu ta tasa a gaba tana yaka da kishi tunda naji ya fadi hakan. Wanan ke nan yasa anty salma fada min cewa zamana kishi irin namu zamane na kowa tasa ta fusheshi a gurin miji don ba zancen hadin kai a nan don ko an hadadin wata rana sai anji kanku da wace kuka hada kai din. Bai jima ba ya mike zuwa daki sai lokacin iya ke fadin ninasan wanan yarinyar ba zata canza ba ai don kishinta na haukane . Kinzo kin samu yarinyar nan da mijinta kince ba zaman lafiya ankawo wata daga baya kuma kince dai ina miji ya fito irinsu saidai a zauna dasu kawai da halinsu. Aida agida daya kuke zaune na tabbatar da yanzu dole dayanku tabar gidan saboda fitinan wanan yarinyar da kowa baida daraja a wajenta. Tsugul naji muryan biba tana fadin iya ai shiyasa maman mu tace mubar zuwa gidan tunda ko muje bamu samun taron arziki a wajensu. Tun wani zuwa da mukayi da sallah uncle yace a dibar muna nama muda maman mu a gabanmu tace an raba nama ya kare har muka fito bata bamu ba . Habiba daga yau karna kara jin kin tsoma baki cikin irin maganan nan abinda akayi ya wuce ina ruwanki da kawoshi yanzu ki daina bana so don Allah. Shiru falon yayi na dan lokaci sai can iyan ke fadin kinji tarbiyan kwarai haka ake son ya kasance kanayi kana kwabon bakin yaro ko yaushe baka kyale yaro na tsoma baki a zancen manya ba shine matsalan dake damun uwarku. Kada ki kara bayan haka duk uwa tace bata kwaba yaro duk abinda ya fada shine daidai a wajenta to itako da zaman lafiya sunyi ban hannun makafi ke nan. Ki bari gaskiya ta fada maki ko ita da zancen ya shafa inkin kula bata fadan kallal kahu a ciki idan anayi don haka kada ki kara kinji. Iya idan na kyaleta watarana a kaina zatayi kuma ta dauka ai hakan daidaine ban taba zama dake ba habiba ina maki zancen wata a gidan don haka ki daina don Allah hakan ba halin kwarai bane kinji. Bazan karaba anty ko yanzu ma subutan bakine mamanmu ta kwabeni da hakan kullum naje kuma sai tayi min fadan hakan ta fada a dan maraice. Saida mukaci muka sha donshi bai tsaya yaci abin kwarai ba na kwashe kayan tare da biba kafin mu fito iyan ta shiga dakinta na leka ina fadin har zata kwanta ke nan ? Tace meya rage min kuma yar nan baku barni da komai ba sai godiya ga Allah Allah dai ya tashe mu lafiya kuma ya karawa mai nemowa dake mai dafawa lafiya na amsa da amin na kalli biba ina fadin saura ki kwanta da kayan nan baki sauya ba don har yanzu kina da matsalan haka biba kije ki watsa ruwa kiji dadin kwanciya don Allah. Akwance na sameshi yayi shiru jin motsina ya kalloni na karaso ina fadin a hadoma ruwan shayine naga bakaci komai ba kai ? Naci abinci da habu a wajenshi ya dawo da yamman nan anfito da abinci ya matsa sai naci shiyasa banjin yunwa. Ashe ya dawo ke nan yace ya dawo dazun ashe maria din bata jin dadin jikinta shine ya dawo da sauri nace bata fada min ba kuma munyi waya da yamman nan tana fada min zancen haihuwan yar mijin ummah a kaduna. Ta boye makine gobe sai ki shiga ki dubata idan zaki dawo school amma taji sauki don naga tana aiki da kanta ai. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/17, 08:36] Buhainat: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/C8kkr4INYY7FydHKKKRVhL{2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 6️⃣2️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Rayuwa kenan haka take tafiya da dadi ba dadi ga dan adam amma idan ka saka hakkuri ka dauki komai a saukake sai Allah ubangiji yasa abubuwa su dinga zuwama a cikin sauki ta yaddama baka zata ba. Haka shima rayuwan aure ya kumsa garemu mata idan kina tausan zuciyarki akan kishi zakiga abubuwan suna zo maki a cikin sauki matuka zaki daure ki ba komai baya ki dauka a ranki cewa aure bautan ubangijine a gareki. Hakan ya kasance a rayuwan auren dana tsunci kaina a cikinsa na yaya Jafar auren da bantaba zato ba ko tsamani nasa akaina. Haka kuma nake daurewa da duk wani abinda zasuyi min dashi da matanshi ina nuna ba komai bane hakan a wajena. Idan yazo wajena mijina idan ya koma gidan matansa kuma mijinsune ban damu da irin rayuwan da sukeyi a can ba dasu din zan kawar da kaina ba tare da son sanin yaya yake ciki dasu ba can ? Duk da yan tsegumin da nakan tsunta nasu abakunan dangin miji cikin zance hakan ban yarda na sakawa zuciyana damuwa akansu ba. Bazance bamu haduwa ba mukan hadu can ba a rasa ba don ina zuwa ganin yar uwata a gidan kuma saiba bata daina kawo muna hari ba da sunan kishi. Balle yadda na dauki lokaci ban samu ciki ba shima wanan din ya zamo kamar abin gorine a wajenta don takan sakar min magana a kansa wani lokaci. Yau,ma daga school nan na nufo don in duba yar uwata dake fama da laulayin ciki a cikin yan kwanakin wanda hakan ya zamo mata dabi,an da zaran ta samu ciki babu zaman lafiya a rayuwanta ke nan. Don ko yanzu likita yace dole sai tayi zaman asibiti irin wancan din da tayi a baya donshine nazo gidan muyi shawara da ita don ni ta fara nema da zancen hankali tashe. Yunwar dake cina yasa ina shiga na fara neman abinda zan aikawa cikina agaji dashi tace na duba fridge dinsu ko zan samu abinda zanci a ciki . Yoghout din Rufaida na dauko da cake na dawo saman kujera na zauna na bude ke nan yaran su saiba din suka shigo part din. Sun biyo dan wajen Yanda suna wasa ba zance yaran basu sanni ba saidai babu sabone yanzu sosai tsakanina dasu kamar da amma don sani sun sanni ai. Haka kuma kowa yasan yaro da daukan ido idan yaga wani abinci a hannun wani hakan yasa na rasa yadda zanyi saboda idon da suka zuba min din ga Rufaidan dake hannuna ina sha. Banda kyakyamin yara donshi nake diba ina basu a baki wanda hakan yayi daidai da shigowan Saratu part din tazo amsan hairdryer a wajen yar uwata din. Haka kuma bata sanda na shigo gidan ba sai a lokacin don banshiga wajensu ba tukunna na nufo wajen yar uwata din. Har ta karba zata fita sai kuma ta dawo baya tana fadin jimun yan iskan yara da saka idon tsiya me kuka rasa a wajenku da zaku dawo nan ku rufawa wanan abin ido haka ? Tsawa tayiwa yaran suka fice a cikin kuka nace da kin barsu ai munsha tare aini na basu bata ko tsaya kallona ba ta fita a fusace ta tasa yaran gaba. Sai bayan sun fita naji maria tana fadin yanzu wanan abin ya isa uwayensu jidali bansan meyasa saratu take halin nan ba ko shigowa yaran nan sukayi sai tayi masu jan ido akan su fita zakice ina masu wani mugun abune a nan. Kyaleta kawai neman maganane irin nata idan da sabo ai yaci ki saba da halinta bata so a zauna lafiya ita ko kadan dama. Na mikawa Abbanta roban gaba daya na gyara zama ina fadin yanzu yanda dolene sai asibiti zaki zauna ? Ba zaki zauna gida a dauko maki wace zata kula dake ba ninaga kamar hakan zaifi sauki da zaman asibitin nan tunda kinga dole wancan karon ummah ta zauna dake yanzu ko ummah tana da aure. Idan ance tazo ta zauna akwai takura acikin hakan yana da wuya mijin nan nata ya yarda da hakan gaskiya. Tace Ramaah abinda nake tunane ke nan mama dai yanzu kinsa ba dadi a tsakanin mu don tunda ta kula da cikina samu nake wanan wahala naji tana fadin. Ai hakan ya zama takura ace duk ciki sai an wahala dama abinda akewa yaran nan gudu kenan kaje ka daukowa kanka wahala yanzu gashi abu ya zamo fitina wa zai iya wanan wahala ace duk ciki sai mace taje tayi kwance ta mike kafa asibiti. Dama ai kinsan zata fadi har abinda yafi hakan ai tunda ba yan sonta bane sukayi hakan kofan da aka turo a fusace yasa duk muka juya lokaci guda. Ita kanta a yadda ta shigo din ta samemu saida ta raina kanta don jikinta saye yake da wani dogon riga na atamfa baki daya kode. Roban youghot din dake hannun Abba yana sha ta kalla ta soma fadin ai dama nasani akan wanan tarkacen kwadayin zaki mayar muna da yara kamar marasa galihu ? Haba dai anty Saiba meya kawo wanan maganan kuma anty Maria ta fada cikin tsawa take fadin don Allah rufa min baki kinji malama. Shi Rufaida din inba abin yaro ba nawa suka sha da zasuzo nan ana yan masu a hannu kamar wasu almajirai dasu ? Ku ya zamawa bakon abu har kuke kwadayinsa koda yake ba abin mamaki bane don ba asaba ganin hakan ba sai a nan din ake samu kuma dai kudin ubansune dai ake ci ko saukin abin ke nan dai daga yau bance wata ta kula yata ba balle a bata wani mugun abinda za a sabauta min ya in rasa gane kanta yadda akaiwa ubansu. Wanan kuma ke kika sansa ai don bamu gaji mugun abuba balle muyiwa yarki don baki tsarewa kowa komai ba balle yarki To mara kunya nasan idan ita bata tanka ba dama ke zaki tanka ai nace kwarai tunda ba tsoronki nakeji ba kuwa baki da wuta baki da aljannan sakani akan me zanji tsoronki Saiba ? Kazan uba nice ma Saiba haka gatsau a bakinki nace kina da wani suna da yafi hakan ne a bakin mutane Nusaiba. Na fahinci sanyin da yar uwata keyi masu ya jawo raini a tsakaninsu tun ina gidan wanan yasa a yanzuma nake son in kakabe hakan a tsakanin mu tun a yanzu din. Idonta ya fifito na masifa ta soma jefa muna zagi na wullakanci ina rama abinda take fada min din cikin hikima da nasa mata bakin ciki a rayuwanta dama ance magana zaran bunu. Nasam karshe tace zata dora min hannu a jikina don haka takewa kishiyarta a baya nasani kuma hakan yasa tunda naga tana nufoni na mike tsaye cikin masifa nima ina jiran karasowanta a kaina. Sai fadi take yau zan murji rashin kunyar nan taki da kyau dana jima ina jiran wanan ranan zan gwada maki nafiki iskanci ke karamar yarinyace wallahi . Yariya ai tana bayan uwarta kin sani nikan ai daidai nake dake saiba kafin hannunta ya sauka jikina don yanda data shiga tsakanin mu hakan yaban daman samun shammatarta nakai mata wawan mari a tsakiyar fuska tauuuu. Saida ta duka kasa kokarin kare yar uwata don kada mu illantata nayi nakai gareta muka hade ana gwadawa yar filo mai kiwo a daji kokawa ? Ai kunya garemu badai tsoro ba sai gashi Allah yaban sa,a na dagata sama na zuba saman kujera nabi na danneta ina aikawa fuskanta naushi a iya karfina da bansan na saura dashi ba har lokacin . Ihun yanda ya fito da mutanen gidan mama a rude babu kallani akanta tana rige rige da yayanta suka nufo part din cikin tashin hankali. Salimace ta soma fadin ayya girma ya fadi ke Rahama daga mata hakana don Allah garin yaya haka ya faru kuma yaushe kika shigo gidan nan ma inji mama ? Jin abinda suke fadi din yasa na daga akanta ga idanuwanta sun firfito waje tana haki ta soma fadin wallahi ba zan yarda ba yau gidan nan za ayi bala,in da ba a taba yiba kuwa kun tarar min ke nan ? Da keda yar uwarki ko nace kunji munafuka har me za a tarwa anan mace haka kamar faifai ba nauyin komai nidai din da kikace zaki murza na murjeki son raina yau din. Tayi kukan kura akaina tana fadin wallahi baki isa ba kizo har gidan nan kice zakiyi min haka karyane wallahi na tattare bujena zuwa gwiwa don kada ya takura min nako here hannuna nakai mata wani naushi sai a gefen fuska duk suka jaye baya dama salima da Asmauce ke rikeni mu din don sunfi kusa damu. Na kara samun sa,anta na taushe a kasa amma wanan ai zaluncine ku dagata mana tunda kunga bata in mata kun tsaya kuna lallonsu kuma tana dukanta ? Saarece ke fadan hakan cikin hasala tayi kaina wai zata dagani jinta kasa yasa ta kai min duka nako juyo na aza mata duka iya karfina saida ta saka ihu tana fadin kika dukeni Rahama ? Keda kika dukeni fa ina can ina bata amsa ta samu sa,ana ta kai min cizo a hannu tana dagowa na koma na kaimata shaka a makogoranta ta soma kakarin kamar zata shude. Haka na zama masu yar daban gaske a gidan inkaiwa saratu duka inkaiwa saiba maria ta dora hannu akai tana kuka duk da suma suna dukan nawa amma Allah bai basu sa,ata ba yadda suke so don na fitarwa kowa da jini . Saida kyat mama da su salima suka samu rabamu fadan salima ke fadin an daiji kunya yau tunda har kuka tararwa mutum daya ke Saare meya kaiki shiga fadan su don Allah ? Ke rufa mana baki mama ta fada a cikin tsawa tana fadin mara zuciya kawai da iya fadan tsiya ki tsaya kina kallo kin kasa rabasu daga rabon fada zata hau yar uwarki da duka haka kina tsaye ? To mama so kike mu zama daya meyasa takai mata duka haka ake raba fada kakaiwa mutum duka muko muna can muna aikawa juna zagi na tashin hankali ido a rufe duk a gabab mama din data kasa komai . Sai ranan na fahinci waye mama da kyat suka samu na fito daga part din cikin masifa don banson na bar gidan su mayar da abin akan yar uwata dake fama da kanta aiki daba kan ranan sungashi wajena don ban raga masu ba. Asmau tazo har inda nake tana fadin kizo ki bar gidan nan don Allah don in baki tafi ba fadan nan ba karewa zaiyi ba wallahi. Na budawa idona yaji nace ba inda zan tafi saina tashi so nake tazo ta murjeni kamar filawan datace an fada mata shiru shiru tsorone dama niba maria bace da take kyalesu duk wanda yai min zan mashi nima ban kaunar a zauna lafiya din. Kawune ya soma zuwa cikin wanda mama ta kira tun a get ya soma fadin asshaaa subahanallahi garin yaya haka ya faru kuma ke dubu ? To kadai gani ace yarinyar nan ta biyosu da masifa har gida irin haka don ta rainawa mutane wayau komai ? A,a mama inda ita ta biyosu ai part din mu zata nufa ko amma a wajen yar uwarta fa ta sameta saida nace kada Saiba ta fito don Rahama taba yaran nan abu shine wani abu don Allah ai,,,,,,, Kaji munafunci ko zaki juya zancen yanzu Saiba datace taje ta shirya tafito da wani bakin dogon wando da t,shirt ajikinta take fada ta nufoni kawu yana mata tsawa. A lokacin kuma motan su yaya ibrahim ya tsaya suka shigo gidan ankira mazajen mu an fada masu abinda ke faru shine yace yan uwansa din suzo gidan. Tare dasu na koma gida inda suka jawa kowa kunne kan duk wanda ya kara tayar da zancen wallahi su zasu dauki mataki mumuna akan mutum. Jin hakan yasa na yarda na bisu badon naso barin yar uwata ba da naga suna da niyar illanta muna ita haka kuma mijinta dake kusa ya kamo hanya zuwa zaria hankali a tashe kar wani abu ya samu matarshi din. Gaba dayan su na barsu da tabona a jikinsu zakice ko wani abu na samu nayi masu illa haka dashi duko hannunane yayi masu wanan aikin haka ? Ana gwadawa bafulatani hanyar keta muda in muje daji muke gwada karfin mu da juna don gudun ta taso a garemu . Kodana koma gida daki nashiga bance da iya komai ba jin hannuna yana son takura min da tsami yasa na gasa jikina da ruwan dumi na shafa rob na sauya tufafina wajajen karfe biyar na fito falon. A lokacin kuma kawu ya shigo gidan shida mama sukayi sallama sai lokacin iya kejin abinda ya faru a bakinsu don irin fadan da mama din take min akan me zan hada har saratu don tana rabamu ? Dakata Dubu ban fa fahinciki ba shin da saratu akai fadan nan koda yar nan Nusaiba don zancenki yana nuna da mutum biyu akai fadan nan haka ? Iya dasu biyun nefa duka tayi fada haka daga maganar fatan baki zaki dinga kai masu duka kamar kina jirace dasu dama ? Kaiya iyan ta fada ta kara fadin nace kaiya dubu ina hankalinki ya shigane wai har hakan yakai ga faruwa ? Ba yau ba kinsan halin yaran nan haka suke wanan dabi,an takaiwa yar uwarta duka daga magana kadan sai duka ita saratu ya akayi ta shiga zancen shine ban gane ba ? Wai rabasu takeyi shine kawai ta,,,, dakata muji daga bakinta ai tana da hujjan yin hakan tunda ba hauka tayi ba ko ? Jin abinda iya ta fada yasa na soma magana banji nauyi ko tsoron idon mama ba don zuciyana daya bushe a lokacin komai zai faru ya faru shike nan nace. Ina school Maria ta kirani tana fada min zancen rashin lafiyanta shine na kira yaya nace zanje na ganta dana isa ina jin yunwa na dauki youghout ina sha nan dai na fada masu komai tas har dukan da saratu din takai min. Kaiya iyan ta fada a hasale ta kara da kin min daidai gobe ta koma in halintane tunda bata da mutunci ita a fakaice ta shigarwa masoyiyarta fadan ko saita hadu da fulani sukai mata maigaba daya. Ta dauka ta hada fada zataci bulus ko tunda ta zata irin sakarancan ne da suka saba tauyewa su zalunceta tayi ta kuka ana dariya gobe su kara in halinsune iyan ta fada. Amma iya wanan abu yayi yawa ta yaya zata bisu har gida tayi masu wanan aikin kamar an turota tayi masu hakan sai iya ta dubi mama tace kila nice na turata tayi masu hakan ko ? Bakiji kunyar wanko kafa zuwa gidan nan kina wanan maganan ba dubu aure fa ba bauta bane dubu duk abinda ya faru dama an shirya a tozarta yarinyar nan ne sai Allahnta yafi nasu ya dorata kansu duka shine kuma yanzu don an daki yarki data saya aka sayar mata kikazo fadan haka ? To ki bari mijinta ya dawo dubu sai kisa a ranan ya saketa ina shike nan tunda kina da power hakan a hannun ki idan bashi ba wanan abin kunyan ina na taba jin haka ? Fada ya hadata da abokiyar zamarta yarki ta shiga ta saya an mata dukan tsiya yanzu kinji haushin hakan tunda ba ita bace aka samu sa,anta akaiwa hakan ? Iya na yarda yaran nan da goyon bayanki suke haka tana ganin tafi kowa a yanzu don an nuna mata fifiko akan abokan zamanta har take ganin zata iya dukan saratu a gabana ko ? Yau muna ga rasulu shine zancen mamakin iya idan abu ya daure mata kai shi kuma ta furta a lokacin cikin mamakin mama dubu din dake gabanta. Tace yanzu ai gata nan idan kinzo sakintane saiki bata takardanta kowa ya huta ina zance ya kare tunda baki iya tsayawa can ki tsawata yarki datayi abin kunya ba haka ? Iya ai abin bakai can ba don dai kawai abinda ya faru kar a koma hakan ne yasa mukazo mu tsawata mata don gaba kada a ,,,,😑😑 kai dakata don Allah ta fadawa kawu daya soma magana. Tace bakinku daya kowa ya sani kunji zafi ba itace akaiwa duka ba don baku da kunya kuka kwaso jiki zuwa nan kuciwa yar mutane mutunci ko ? To Dubu kin kai ga yadda kike so ai yau gari ya dauka ga abinda yarki dake kuka taru kukaiwa matan danki har da kishiyarta abin kunya kamar yar nan zakuyiwa taron dangi haka dubu ? Ganin yadda iya bata basu daman magana ba yasa mama ta soma fadin iya kinsan dole in tsawatawa saratu ai duk abinda ya faru itace ta jawoshi. Don anba yaran nan abu zataje ta fadawa uwarta ita kuma don bata da hankali takwashi jiki zuwa fada duk nayi masu fadan hakan amma yadda yarinyar nan tayine bata kyauta ba tunda muna wajen muna tsawata mata ai. Daga gefe na bude baki nace mama kuyi hakkuri don Allah amma ni banje gidan nan da fada ba itace tazo ta sameni ta soma zagina ganin tana da niyar kai min duka nima nakai mata. Amma da nazo yakamata ki dubi tsufana ki ji me nake fada aiko ayi hakkuri nayi kuskure hakan ko gobe ta kawo maki kada ki kyalesu tunda da niya sukai hakan iya ta fada. Keko iya inji kawu ni tayi min daidai yau don Allah ya nuna masu mugun abinsu a fili gobe su kara in halinsune gida kuma ba zata fasa shiga ba tunda gidan mijintane kuma yar uwarta na gidan zaune dole ta shiga. Ai don haka muka taso iya amma kin hana ayi magana kamar kina zugatane fa iya irin abinda kike fada yanzu ? Dauda so kake su daketa taki ramawa kome don ban fahince kaba har yanzu yarinyar nan kowa yasan halinta magana ba magana ba duka ne zata kaiwa mutum . Ba haka tayiwa Salima ba wani lokaci kan dan maganan fatan baki kuma yarinyar nan tasani suka dai samu suka tafi don magariba daya kawo jiki lokacin. Tunda na shiga daki ban fito ba don gaskiya jikina yayi tsami abinda na dade banyi ba biba tashigo ta sameni take tambayana ta kawo min abincine nace tea zansha. Zata fita nace ta miko min wayata a jaka ta dauko min miscal din dana gani a lokacin bana lafiya ba duk kuma nasan akan abinda ya faru dinne ake kirana din. Nasa kiran kusan goma sha hudu gana yaya habu har ukku sai na Nafisa da anty salma na anty Salman na fara dauka . Tana dagawa take fadin ke Ramaah meya kaiki hada jiki da kishiya ashe bana fada maki hakan tsiya yake kawowa ba ga mutum ko ga miji ? Idan ban dauki mataki ba dukana zatayi anty tace taci bulus aida kikayi kadan sai ki bari amma duka haka kamar wace taci tauri Rahama ? Maria tace min taji tsoronki dazun ta dauka ko kina da iskane tace fuskansu da jikinsu kin masu illa sosai a wajen fadan ? Na kwashe yadda abin ya faru na fada mata sai naji tace kin min daidai wallahi ya kirani hankali tashe yake fada min shi a zatonshima wai ciki gareki kikaje kina fada haka ? Tsuki naja jin abinda ta fada tace Allah yace with dis condition naki zakije kina fada a illantashi idan wani abu ya samu cikin jikinki fa ? Kyashi anty ni banda komai a jikina na fada muka kuma koma zancen su din inda tace wani lokacin irin haka idan ba haka ya faru ba dama ba a samun natsuwa ai. Yanzu tunda ta gwada hada jikin taga baci zata koma wani sallonne kuma in bi a hankali don zata fara makirci tunda taga uwar mijin tana kama mata. Ita kuma yar iskan nan sai taji a jikinta ai nace na dauka ai sakina zaiyi idan ya dawo tunda haka uwarshi ke so na daki yarta a gabanta ke kin min daidai wallahi. Maria tace ai mijinta ya dawo ya zo ya karanta masu hauka iya son ransa yace wallahi duk wani abu ya samu matarshi sai yayi karasu kuma yace zai bar masu gidan ya koma gidansa ya gaji da jidali kullum. Ashe ya dawo a gurinta nake ji tace ai ya dawo kuwa yayi masu cin mutunci sosai don saida ita Saiba ta rufe daki akace saboda yayi niyar dukanta dakyat aka samu ya hakkura amma yace zai bar gidan don ba zai yarda ba. Mun kai wani lokaci da ita wayan shi dake shigowa ne yasa na katse kiranta din na dauka don inji me zai fada a ranan kowa ina iyawa dashi don abin ya isheni gaskiya gara dai kowa yasan matsayinsa zai fi. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/17, 08:36] Buhainat: [3/18, 8:26 Yamma] Seenabu Makawa: Open this link to join my WhatsApp Community: https://chat.whatsapp.com/JeOQfGohQLdKTUlsWMqXoZ [3/18, 8:28 Yamma] Seenabu Makawa: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 6️⃣3️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, A sanyayye na amsa mashi murmushi naji yayi sabanin fadan dana zata zai min a lokacin yana fadin ashe yar kokawa na aje agida ban sani ba ? Abinda ya fada din yasa na sauke murmushi lokaci guda yace baki kyauta min ba Rahama with your condition zakije kina fada haka idan wani abu ya sameki fa baki tausaya min ne don Allah ? Kayi hakkuri don Allah ya daurone idan ban rama ba a lokacin sai su dauka ina tsorone shiyasa na rama dukan da sukayi niyar yi min din. Nasani amma kinsan illan hakan ai ina daukanki mai hankali sai gashi kuma kina son kifi Saiba hauka agaban kowa kuka dinga fada kuna zubar da mutuncin ku why zaki biye masu kuyi hakan don Allah. Na sake fadin kayi hakkuri yaya muryata tana nuna alaman karya a lokacin is ok amma don Allah kada a maimaita hakan naji komai nasan ba laifinki bane zuwa gidan kuma har in zai kawo matsala idan ban nan don Allah Rahama ki daina. Katseshi nayi da fadin saboda su ba zanyi zumunci da yar uwata ba ke nan banje donsu ba kuma ban takalesu ba sune suka kirkiro abinda zamuyi fitina har haka ai. Nasani amma itama Maria din dole subar gidan ai tunda har haka ya fara faruwa yanzu haka mun gama magana da habu zai gyara gidansa su koma ciki zuwa next week in sha Allahu . Bance kicewa kowa komai ba duk da ance mama da kawu sun sameki a gida saidai banda fargaban hakan tunda iya tana gidan a tare dake yasa wanan bai dameni ba amma ki kula don Allah hakan ba mutuncin ku bane please ? Nagode na fada sai nayi shiru shima dan shirun yayi ina jin yadda yake sauke ajiyan zuciya a bangareshi kafin yace ina dai baki ji ciwo ba kema ? Banji ba na fada a takaice yace sure nace umm,umm Allah ya tsare ya jikin ita maria din duk da ance kun dai fasa mata kaya amma ba a tabeta ba kinga illan fada ke nan bakyau don Allah. Tausayi ya bani yadda yake maganan sai naji ba dadi a raina karon farko da nayi nadaman faruwan abin kenan a kasan zuciyana wanda hakan ya ja na rage irin zafin da nakeji kasan zuciyana nasu. Washegari saiga maria a gidana ita da yaya Habu sukazo nan muka zauna falo dasu da iya nan naji yadda ransa ya baci ya fada ya kara zai bar gidan tunda mama bataga laifinsu ba sai na matarshi da yar uwarta. Habu kuyi hakkuri akwai abinda ku baku sani ba game da uwarku ina nan ina mata addua Allah ya kwatota daga kaidin da take ciki a yanzu duk wani abinda za a fada a yanzu banzane don bai tasiri azuciyarta don tana ganin ita daidai take. Amma kaga Dauda da matarsa hansatu ka barsu nan inda ka gansu su dade sunawa uwarku bandan kasa. Yanzune abin yake yawo akanta haka kuma yar nan matar Jafaru itama da akwai wani shu,umancin datayiwa Dubu a zatona wanan abin shine duk ya rikita kanta a yanzu din. Kaga kuwa wanan abune dake son addu,a don ba yarda da hakan zatayi ba koda an fito mata fili an lurar da ita zata iya mussan hakan mutum abin tsorone. Ni kaina a lokacin ai hafsatu bata barni ba nasan komai ido na zubawa gudunsu tunda yadda suka so dai bai samu ba. Sunyi hakane don ku da yan uwanka ya kasance duk wani nema naku yana a hannusu sai yadda sukayi daku da uwarku din sai gashi ku ba a kama kuba ita abin yafi shiga jikinta. Nina sani iya don ko kowa bai yarda ba nina yarda kawu zai iya hakan fiyema da hakan sai yayi don irin yadda yake muna wani lokaci sai mutum yakai zuciyarsa nisa don azauna lafiya. Yanzu dai zan bargidan ba zan zauna ina gudun zuciyarsu ba ninawa yana baci a kullum don haka zan kwashe kawai na bargidan ina ganin shine mafita a wajen mu baki daya. Ita kuma saratu kai salima na fadawa yaya su fito da maza a daura masu aure kowa ta kama gabanta zaman ya isa hakana musanman ma saratu da duk wani fitina itace ke kawoshi a gidan nan kuma mama bata yarda da hakan . Yanzu da safen nan saida muka kwasa da ita wai mun kadarwa saratu bamu kaunarta abu kadan ace saratune har tana batun yi min kuka fa iya wai akan saratu. Sai naji iyan tace kafadawa uwar taku zancen tashin naka yace ehh to cikin fada na fadi amma ina ganin bata dauka da gaske nakeyi ba. Don kyata da bala,i irin nata wai a falona Nusaiba zataje fada duk sun fasa min kayan falo amma duk mama bataga laifin hakan ba sai fada rakeyi wai Rahama tazo har gida tayi masu rashin mutunci. Me yaranan suka tarewa mama haka don Allah iya ta nisa tana fadin habu kayi hakkuri na fada maka inda matsalan yake don haka addua zamu bita dashi a yanzu. Ya juyo wurina yana fadin ke kuma baki da hankaline da kika biyewa haukansu Rahama idan suka illataki fa badon Allah ya doraki akansu ba yadda ake fadi sun tarar maki ai saisu nakasaki a banza tunda ba wajen hukuma za a kaisu ba a daukar maki fansa. Don haka daga yau ki kama mutuncin ki dama ita abinda take nema ke nan abinda za ayi ta bata maki record a idon mutane ba haka kikaga yar uwarki tana zama dasu ba. Bayan haka ke kinsan yadda akai auren ku da J dole haka ya faru tsakanin ki dasu don ma ita Asmau a yanzu ta daina saka kanta cikin iskancin Nusaiba don na kula ita a yanzu bata irin abubuwan nan don haka kada nakara jin hakan daga gareki. Duk abinda zatayi ai yanzu tunda ta gwada ba sa,a a wajenta aiba zata kara bari su hada jiki ba kuma da dai ace ta samu sa,antace bata da sauran numfashi kuma a gidan nan yanzu. Sai Allah ya kawo saukin abin kika rijayesu don haka yanzu iskancin zai rage akanki saidai ta fito wani hanyar kuma nan gaba. Ai tasha fadancewa saita wullakantani dake a gaban kowa amma ban taba tsayawa na kulata ba ina jiran ranan da zata kawo iskancin ta akaina ta gane kurenta bata san naki dan maline ba don nafiki hauka kyalesu kawai nakeyi. Maria data karbi zancen iya take fadin hakan sai iyan tace gara dai kada akai ga hakan ai yanzu na fada maku zasu shiga hankalinsu sosai tunda basu sha da dadi ba. Na daiyi fama da tsamin jiki tunda jikin a yanzu ba wahala irin da can baya inda gadan gadan ya Habu ya shiga gyaran gidanshi da zai koma da iyalinshi. Unguwa dayane amma akwai dan nisa da inda nake saida yayi wani dawowan ya samu mama da zancen tarewansu gidan akan ga gobe. Me kake fada Habu zaka kwashe ka koma gidanka watau ban isa da kaiba yanzu saida yaran nan sukai nasaran raba min kanku a gidan nan ? Wasu yara kuma mama ta kalloshi a yatsune tana fadin wasu yara banda shu,uman yaran nan da kuka dauko min a gida ? Dama gurinsu kenan su raba min kan yayana gashi ko sunyi nasara na farko a gareni shigowan yaran nan cikin ahalina bai haifar min da komai ba sai tarin bakin ciki da takaici . Kowa yasan asalin nono dama daga ruga yake ashe gaskiya ake fada akan fulani ba a fadi karya ba duk wanda ya auri yar filo sai yabar kowa nasa gashi kuwa nagani a kaina. Saita fashe mashi da kuka ya mike ya fice daga dakin bata kara ganinsa ba saida yammane saratu ke fada mata da gaskiya yakeyi fa tafiya zasuyi don ashe har sun kwashe duk wani abin amfani nasu sunkai wancan gidan. Ranta ya baci ta mike tsaye da sauri saratun ta tareta tana fadin mama kada ki fita don yaya ya ganeni zaice nice na fada maki. Yace mana idan yace fa shi har ya isa ince ban yarda da hakan ba yace min don me koshi jafar daya dauki wanan yarinyar ya kaita can tunda abin ya zamo iskanci ai nan zai dawo da ita dole yanzu. Tunda tana ganin hakan da yai mata kamar tafi kowane a yanzu har take iya ganin zata tako har cikin gidan nan taciwa mutane fuska jiransa nakeyi ya dawo garin nan ai,,, Sallaman ya Habu dake shigowa dauke da dansa a hannunsa sai maria dake bayanshi sabe da jakarta na hannu shiya saka suka juya suna kallonsu. Zama yayi yana gaida ita ta amsa a dakile kafin yace yaune zamu tafi wancan gidan mama na fada maki zamu koma gidana to yaune komawar tamu insha Allahu. Kai habu saboda ka auro yar gwal mai takobin raba zumunci zaka ture dokana kace zaka bar gida don ra,ayinta tunda su da manufa suka shigo cikin mu dama ? Meye laifin Maria anan mama tunda ba itace ta gina min gida ba ninayi ra,ayin hakan don haka a barni da shawarana don haka nake son tsarina. To ba zaku ko ina ba kaji na fada maka wace zata iya zama a nan ta zauna wace bata iyawa kuma hanya a bude yake ta fice ta kama gabanta. Ashe gaskiya da ake fadin dangin filo dangin bala,i yanzu don matarka har zaka iya kyatare dokana don kada ranka ya baci. Mama ba ra,ayinki nazo nema ba a yanzu don na riga dana gama shirina ba zan bar iyalina gidan nan kina kallo ana ci mata mutunci ba tare da daukan mataki ba. Yanzu zanyi abinda ya dace a zauna lafiya kuma zakice ban isa ba a zatona hakan abin farin cikine a wajenki ai mama tunda har Allah ubangiji ya hore muna muhalin kanmu haka da taimakon dan uwanmu dake son cigaban mu a rayuwa. Ashe hakan ke a wajenki ba abin godiya bane yau don danki ya samu farin ciki mama kinfi bukatan ganin rayuwan mu ko yaushe a tauye ? Habu ni kake musayan harshe dani yau haka kan wani tsari da aka doraka sama yace ba wanda ya dorani na fada maki ra,ayin kainane hakan. Banda ra,ayin zama a cikin yawa haka shima jafar din da aka tauye ya zauna ai banga wani abin karuwan daya samu ba ga haka. Abinda yakamata ace kin dage akansa mama kin kasa dage muna akan masifan dake bibiyan rayuwan mu ki sa kawu gaba zuwa garin matan nan dayaje ya karbo maki haihuwa kin kasa haka mama kin tsaya ana zugaki a kan mu don mu lalace . Ba laifi idan yau kin min baki kan na bar gidan nan na koma muhalin kaina na zauna don in samu zaman lafiya a rayuwata. Kullum kana wajen aiki hankalinka ba a kwance ba kana tsoron abinda zaije ya dawo na samu Allah ya hore muna kuma zakice baki yarda ba sai dai kiyi hakkuri donnni na tashi ke nan bafasawa zanyi ba. Haka kuma dolene muje wajen nan a wanan karon abada duk wani abinda akai alkawari bayarwa don dan uwanmu dake cikin matsalan rayuwa. Zuwa lokacin kuka sosai mama takeyi akan ya daina amma ya tsaya sai daya gama fadin abinda ke bakinsa ya kallo maria yana fadin tashi muje. Maria kinyi nasaran rabani da dana yau har yakai habu bai saurarena sai ke hakan bai maki ba kin shiga kin fita kin cusawa Jafar ra,ayi akan yar uwarki to ki saurari shirina yadda kika rabani da dana haka kema zaki rabu dashi indai harni na haifeshi. Tsoro ya kama maria din dajin furcin mama ga kowa dake gidan tsaye an fito haka ya cusata mota ya shiga yaja motar suka bar gidan . Nan suka shiga bawa mama hakkuri mai sunan zugi suna fadin aidama haka aka tsara tunda anan idon kowa na kansu ba a samu yadda akeson a mulkesu ba yanzu ko ai shike nan sai dai mama din tayi hakkuri. Jin irin abinda saiba ke fadi har tana cewa su dai da aka mayar shakatafi ai an tauyesu an hanasu walawa din ga yan kauye don samun waje sunzo sun karya dokan da aka kafa kuma ba ai komai ba. Haba keko Saiba wanan maganan bai dace ba mana samunefa koshi ya J ai ra,ayinsane zama a nan din don kowa yasan yana da halin hakan baidai da niyar dagawa nan din ne kawai. Ai dole kice haka tunda bake bace akaiwa hakan kuma ai aure zakuyi indai a tauye mutum ne kowa ai zaije gidan mijin ya gani takecewa salima. Shiko habu suna barin gidan ya hau maria da fada don me zata tsaya taki shiga mota karshe ya gama fadanshi ya kira dan uwansa yana fada mashi sun bar gidan zasu koma sabon gidansu lokacin. Murmushi J din yayi yana fadin Habu baka jin magana meyasa ka zabi fushin mama a kanka tunda tace bata yarda ba ai saika saurara har lokacin da zata amince din da hakan gare mu. J nifa ban iya daukan wanan abunda kake dauka a rayuwanka idan ba badin gidan nan nayi ba za a samu rigiman da sai Allah zai iya maganinsa don raina ya gama baci da yadda mama takewa iyalina kasani. Ko yanzu ai laifin maria din ta gani which means kaga da ita dai take adawa badani danta dana ce zan bar gidan ba irin wanan ne zakuce nayi hakkuri in bar yar mutane a gidan nan ? Maria tana da zurfin cikin tsiya da ace Rahamace zata iya zama dasu din hakana amma maria zurfin cikinta yayi yawa wallahi. Duk abin nan maria bata san gidan ba tunda bai taba kaita tagani ba saida suka shiga karamin get din gidan da hasken wutane ko ina a gidan tarara ta bude ido tana kallon mamaki. A ranta take tambayan kanta yaushe har yayi wanan gina haka bata sani ba bata da labari a bakinsa ? Bin ko ina take da kallon yadda gidan ya tsaru dan maidaidaici dashi komai na more rayuwan zamani ansa harda filin tsakar gida da wajen aje mota ba abinda ya kara burgeta irin hasken da gidan yake dashi wadattace. Saida suka shiga ciki ta kara tsunkewa da lamarin yadda komai ansaka ashe ya jima yana shirinsa ba tare da kowa ya sani ba ke nan . Bayan sun natsune tayo min text tana fada min sun tashi a family house gasu sabon gidansu yanzu haka zaune. Ina falo zaune da iya ina cin abinci sakonta ya shigo min na bude lokaci guda nake hamdalla suka kalloni nace iya wai yaya Habu ya tare sabon gidansa yau din nan. Habu fa kikace ta tambaya cikin mamaki nace yanzu maria ta aiko min da sako hakan yasa na daga waya na kirata . A cikin yare nake mata murna tare da tambayan ya haka ya faru tace kedai bari kawai Allah ya rufa min asiri yau Ramaah . Zagi da mugun fata nasha shi nidake a wajen mama na katseta ina fadin ga iya na mikawa iya wayan ta dauka tana fadin maria kun tashifa naji ance ? Tace wallahi iya ina zaune dazun da yamma yace min na shirya kayan mu ya kwasa saida ya dawo yake fada min nafito mu tafi. Akwai magana ashe Habu yakai dakare ya shamaci kowa dayin haka idan ya fada yasan ba barinsa zasuyi ba aiya kyauta daya fito mata ta hakan yanzu ai kowa zai gane gaskiyan abin ku dai kara hakkuri ku zauna lafiya da mazajen ku. Shiya karbi wayan yana fadin tsohuwa me kike fada ina nan shigowa da safe ai bamu da nisa daku da safe zanshigo in baki labarin komai. Ja,iri bakajin taro duk tangwanka da mukayi saida ka nuna halinka na gagare ka gudu kabar uwarka can ? Dariya yayi yace dolene iya matukar ana son zaman lafiya tunda Allah bai hana muna abinda zamu kula da rayuwan mu ba akan me za mu tauye kanmu haka. Sundan jima suna wayan wanan yasa ban samu wani zance da maria din ba don dare yayi lokacin da tunanen abinda ta fada na kwana a raina. Gaskiyane idan akace mutum yayi hakkuri wani lokacin hakkuri ba cutarwa bane ga bawa yinsane keda wahala. Da ace ban biyewa Saiba nabi zugin ziciyana ba da duk hakan bai faru ata sanadina ba tunda ashe dama ya habu yana da niyar tashi gidan lokacin. Amma yanzu nasan danice mama dubu zatayi kuka nice sanadin komai da har haka ya faru danta yabar gidan a sanadiyar abinda ya faru a part dinshi damu. Sam ba za a gano gaskiya ba nice dai laifin zai koma kaina zata kara tsanata nida yar uwata fiya da wanda take muna a baya. Don haka zan koyi hakkurin nan da kowa ke fasin muyi hakkurin saidai nasan hakan yana da wuya ace na iya gaskiya akan cin fuskan da saiba ke kokarin yi min a kullum. Washegari duk da ina son shiga school amma na daure banyi sammako ba don zuwa gidansu Maria din da mukeson yi. Shi yaya habu din yazo misalin karfe tara ya daukemu nida iya don habiba ta wuce ita tunda safe iya kuma a can zan barta gidan awajensu. Gida yakai gida Allah yasa da nisan kwana akaiga wanda yafi hakan gaba iya ke fadi na amsa da amin muka shiga ko ina yana nuna muna nan nabar iya na fito ya ibrahim yazo ya daukeni zuwa school. Muna hanya yake fada min yayanshi yace ya kamata na koyi mota idan ya dawo zai koya min donshi zai fara aiki dasu zaman garin a yanzu zaiyi wuya a gareshi. Dan murmushi nayi ina fasin kyaleshi ya ibrahim kullum haka yake fada amma ya kasa tsayawa ya koya min din ya zata ko ba zan iya bane. Na cirewa kaina damuwan dana so sakawa zuciyana kan mama tunda kome nayi dai ba haske zanyi a wajenta ba tunda ta nuna bata kaunana da danta. Ni kuma gani a yanzu son danta ya kamani ta yadda nake jinshi a wani bangaren na zuciyana dadin abindai ba a waje daya muke rayuwa ba balle in shiga takuranta. Koma waje dayane tunda ba zamanta nakeyi ba zan kauda kaina ga duk wani cin fuskan da suke min a yanzu din kan mijina. Miji daine Allah ya nufi aure a tsakanin mu dashi ba soyayya mukayi ba amma fahinta da kulawa yasa muna kaunar junan mu. Don haka rabamu a yanzu ganganci a wajen mama don nasan hakan zai haifar da abinda yafi na yaya habu a tsakaninsu. Sai dare iya ta dawo koshi da kwantancen da nayiwa Habiba ne taje gidan ta dawo da iyan don yaya habu din ya fita tun safe ya shiga kano. Nazata mama zatazo gidan a ranan sai gashi har dare banganta ba kuma bata kira waya ba don haka nima na watsar da zancen komai a raina. Anyi haka da kamar sati kwatsam ina hanyar school naga yaya Habu ya kira layina na dauka da mamakin dalilin kiran nawa lokacin na dauki wayan. Muryanshi ba dadi yake fadin Rahama kina school ne na amsa da ehh yaya amma gani hanya dawowa na jira yaya ibrahim ban gansa ba na biyo yar kura. To kizo nan teaching hospital ki samemu idan kin shigo muna dakin maza ki kirani zan fito abinda ya fada ke nan ya kashe wayan. Innalillahi na dinga maimaitawa a bakina tare da tunane barkatai a lokaci guda ina fadi a gigice asibiti kuma wake can asibitin kuma yanzu ? Gabana ya fadi don tunowa da yaya J da nayi rabon da muyi waya dashi kwana ukku ke nan kuma kona kira wayansa baya shiga na dauka baya wajen service ne. Mai keke nayiwa magana ya wuce dani cikin asibitin tunda dama daga school nake muka doshi hanyar shiga asibitin gabana sai faduwa yake min. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/17, 08:36] Buhainat: [3/18, 8:26 Yamma] Seenabu Makawa: Open this link to join my WhatsApp Community: https://chat.whatsapp.com/JeOQfGohQLdKTUlsWMqXoZ [3/22, 10:45 Yamma] Seenabu Makawa: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 6️⃣4️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Yan gidansu dana hango a wajen yasa na doshi emergency din kai tsaye takawa nakeyi amma bansan inda nake takawan ba har nakai wajensu. Suna min sannu da shigowa ga kallon tausayi karara a fuskokinsu inda nikan har lokacin zuciyana sai harbawa da take min tana wasi wasin ko waye a wajen ? Ganin yar uwata dake cikin taron yan uwa yasa na dan fahinci bata ita bace kuma ba mijinta bane ras naji lokaci guda da matansa da suka iso a daidai lokacin suma hankali a tashe. Wuni sukayi don na tsaya gaidasu yaya isah dake tsaye suna magana da ya Habu suka amsa min hayaniyar da saiba keyi tana fadin akan me ba za a bari mu shiga muganshi ba ? Wanan yasa ya habu katse maganan da yakeyi ya doshi wajen hankali a tashe yana fadin ke Nusaiba kada kiyi kokarin daga muna murya wajen nan fa ? Kowa da kika gani wajen nan abu daya ya kawomu nan saboda shi muka zo nan din kowa kuma yayi hakkuri yabi dokan likitan . Ko in an barki kinshiga suna aikinsu da abinda zaki mashine a yanzu wanda yafi nasu din don haka kada ki kawo muna rigima a wajen nan don Allah ? Har na taka nakai inda su maria suke tsaysaye din cikin damuwa a cikin yare nace yayane ko ta amsa min da shine tana rike hannuna . Cikin yare take fada min in natsu in kwantar da hankali Allahne mai komai kada inyi abinda zan zubarda imanina a gaban mutane don Allah. Yanzu likitocin nan suna dubashi ne su can sunce basu ga komai ba shine nan suke nasu kokari ko zasu gano abinda ya sameshi din. Ajiyan zuciya na sauke ina bin bangon dake bayanta nakai tsugune a wajen tare da noke kaina cikin gwiwana salima ta dafani tace kiyi hakkuri ki natsu kinji Rahama don Allah. Kamar dai irin ciwon nan nasane na baya ke son taso mashi amma wanan karon ya canza sallo ne yazo mai da wani nau,in kuma . Ruwan dake hannunta na mika hannu na karba na dan tsiyayya na shafawa fuskana ban sauke idona akan kowa ba sai mama dake zaune a kasa tayi tagumi a cikin tashin hankali. Kallona ya koma kan saiba dake fada har lolacin saidai ba cikin daga murya ba haka nayi tabin mutanen wajen da ido ina nazarinsu daya bayan daya a takarshe idona ya tsaya kan Saare dake magana tana murmushi na juyo a hankali na dubi yar uwata ina fadin . Akan me zasu kawoshi asibiti Yanda bayan sunsan ciwonsa bana asibiti bane komene ai mama ta sani da kawu . Maman dana ambata da kawu yasa salima kallona itako maria sai fadi take ta fada min kada inyi wani abinda zan jawa kaina matsala fa. Koma meye ga yaya Habu nan ai dole zai dauki mataki ba zai kyalesu ba shima don haka inyi shiru kawai don Allah. Itako salima din cewa tayi dani ai mama tunda taga halin da aka iso dashi take zaune wajen nan bata daga ba don baki cewa yana da rai fa ko motsi yaya baiyi Rahama idonsa a kafe suke waje daya. Innalillahi na ambata a cikon tashin hankali ganin an bude kofan yasa kowa kallon likitan daya kira ya habu suka nufi hanyar office dinsu dashi. Ya dan jima a wajensu ya dawo tare da likitan lokacin ya habu din kewa yan uwansa bayanin abinda likitan ya fada. Su maza suka fara shiga saibama ta kusta sai naji maria ta rike min hijjab dina na dago na kalleta don na yunkura na tashi nima tsaye lokacin. Ki bari su shiga ai dole ya habu ya bari ki shiga ki ganshi a natse wanan yasa na tsaya ba don naso ba zance kusan mune karshen shiga wajensa din. Kuka masu kuka keyi irinsu saiba sai da wasu yan uwa tunda naga yanayinsa naji duk jikina ya mutu a wajen muryan ya lawal naji yana fadin tun a can fa haka yake bai motsi bai komai ko ka nuna hannu da alaman ma bai san kayi ba. Komai ya bace min akai sai wanan kalman ta (Lillahi ma,fis samawati wama fil ard) shine abinda ya fado min a zuciyata lokaci guda nake faman nanatawa a harshena. Na doshi wajen gadon da yan uwa da matansa suka zagaye ku dan bata waje ta isa wajensa don Allah ya habu ya fada daga bayan mu hakan yasa wasu juyowa suna kallona. Har na karasa ban iya furta komai ba sai wanan kalman daya tsaya min a saman baki don komai ya bace min a lokacin. Shi din ma daddy Abuja ya koyar damu hakan aduk lokacin da wani abin damuwa ko furgici ya shigemu dashi na taso a bakina don haka kila yayi saurin zuwa min a kaina ayan karshe a cikin bakara. Tsaye nayi ina mai kura mashi ido tare da nanata kalman a cikin bakina sannu a hankali na kara matsawa kusa da iya ina fadin sannu yaya Allah ya baka lafiya ya sahalema wanan halin daka tsunci kanka a cikinsa. Magana nakeyi amma abinda iya da yaya Isah suka fada lokaci guda yasa nayi shiru na kurawa bakinsa din ido don cewa da yaya Isah yayi wallahi ya amsa mata adduan nan da amin. Wallahi bakinsa yayi motsi kuma wallahi amin yace da sauri mazan suka matso sukace yayi magana fa kace iya tace kwarai ya amsa nima naji hakan wallahi. Dama likitan yace a gwada kawo mai na kusa dashi agani ko za,a samu reaction indai hakane kuwa dole Rahama zata tsaya kusa ke nan . Yaya Auwal ke fadin hakan ki kara magana mugani ko zaiji don Allah yaya isa ya fada daga gefena din. Saida na dan kara matsawa kadan na rankwafo nace yaya kana jin mu don Allah idan kana ji ka dan nuna alaman hakan ? Nakai hannuna na shafa fuskansa a hankali yayi wani irin ajiyan zuciya mai karfi da kowa ya firgita saina fashe da kuka na kifa kai a jikinsa. Ku dagata kawu ke fadi daga inda yake tsaye muryan iya ne tace ku barta dashi hakan na dan lokaci mu gani ? Hawaye yakeyi fa yaya isah din ya fada hakan yasa wasun mu da dama kara kuka a dakin har iya duk dauriyanta saida ta fashe da kuka ta soma fadin. Allah ya saka maka Jafaru ga dul wanda ya sakaka cikin wanan halin ubangiji yabi maka hakkinka akan mai shi ga alamu sun nuna karara akwai wani boyayyen lamari a cikin matsalanka. Duk wanda ya sanka yasan a yan watanin na baka daidai kamar kulum kana yawan fada min iya banda lafiya ni kadai nasan yadda nake ji a jikina . Iya bana barci wani lokaci har tunane gushe min yakeyi iya ina jin na kusa barin ku wallahi tana kuka sosai take fadan hakan. Iya ki daina wanan maganan don Allah ai sai a dauka ba ayi imani da Allah ya kawo mashi hakan ba imani ya kamata ace munyi ayanzu ba irin wanan zancen ba don Allah ? Me kake son in fada akan abinda nasan shine sila akan matsalan yaron nan dole in fada tunda abu ko yaushe sai kara gaba yakeyi akansa. Kiyi hakkuri iya in sha Allahu za a dauki matakin hakan ya habu ya fada nikan a hankali nayi kokarin dagawa daga jikinsa amma sai naji kamar hannunsa dake sarke da nawa ya dan rike hakan yasa na dan dago ina kallonshi. Tabbas hannun nasane ya rike min nawa a hakan da yake din na bishi da kallo kamar yana son kifta idanunsa saidai ya gaza hakan a lokacin . Na fahinci yana kokarin yi min yadda yake min ne lokacin da yake da lafiya idan mun kasance a hakan dashi nayi yunkurin dagawa daga jikinsa zai rikeni ya hanani wani lokacin yace mu tsaya a hakan dashi shine yanzu abinda yake kokarin yi mi a lokacin. Muryan Asmau naji a bayana tana fadin sannu yaya J Allah ya baka lafiya jin hakan yasa na dan dago ina fadin ga anty Asmau nan yaya tana gaida kai. Hannuna na zare na hada da nata dana kamo na daga daga wajen takai zaune inda na daga tana mashi makamancin abinda nayi mai din a lokacin. Idanuwa kur akan mu dakin yayin da saiba ta karasa itama ta zauna kamar yadda Asmau ta zauna din tana maganganu gareshi. Dole kowa zai tausaya a wanan halin ga dan uwa a cikin wani hali babu mai halin ko ikon kwatosa daga jerabawan nan sai Allah sarki buwayi gagara musali kafai yakai ya kwato maka dan uwan daya fada cikin irin halin nan. Kuka ka munyi shi har mungaji mun godewa Allah mun koma muna rokon Allah ya bashi lafiya sai dare karfe tara na bar asibitin zuwa gida. Koshi yaya habune da yai tsaye a kan mu cikin daure fuska yake fadin duk mu fito mu wuce a kaimu gida babu wace zata tsaya a nan cikin mu . Za a bar iya da yaya Auwal da yaya isah su zauna dashi a ranan naga dadin kyautatawa yan uwa da yaya J keyi don suma sun nuna mashi kauna kwatankwancin yadda yake nuna masu din. Tare da yanda muka bar asibitin a motarsu suka saukeni gida tana ban baki da lurar dani na dangana nayi aikin hankali. Don taji an fara surutu da tsegumi wai duk halinda yake ciki saida nazone yayi motsi har aka gane wani abu a gareshi. Kinga ke nan suna nufin wani abu ke nan a kanki yanzu kwarai kuwa nima naji suna fadan hakan wai badon zuwa ta ba ko motsi baiyi ba tunda suka daukoshi tunma a can din da hakan ya sameshi Nasir kanin su yaya din daya dauko mu yake fada. Maria tace na kula suna son kawo wani zance ga hakan sai tace amma ai yaya Isah yace itace ya kamata ta zauna tayi jinyarsa idan hakan ya taso . Saidai sunsan wanan matar tasa yar kaduna zatayi fitina akan hakan amma yaya Habu yace a barshi da ita kawai yanzu naji suna maganan idan anga asibitin baiyi sai a koma gida a cigaba dana gargajiya. Sun dan jima a gidan wajena muna magana kafin suja mota su tafi maigadi ya tareni yana fadin ashe abinda ya faru ke nan ? Yaso ya bisu zuwa asibitin sai yaga ba kowa a gidan Allah ya bashi lafiya ya tada kafada na amsa da amin nashiga ciki. Habi bata gida nasan tana gidansu donshi na shiga dakina kai tsaye wanka nayi na fito na gyara jikina a yanayin da nake ciki banko tuna da abinci ba a ranan . Tea na hada da niyar insha kada in kwanta da yunwa saidai na kasa shan koda rabin kofi ne a lokacin don bakina da nake jin ba dadi. Ina ganin kamar ko wani lokaci zasu iya kirana suce min ya cika a yadda na barshi din ga gidan ba kowa sai hakan yasa tsoro ya kara shigana duk da maigadin mu yana daga wajen gidan a lokacin falo na dawo na zauna a cikin zulumi ina jan tsabaha tare da tunanen yanayin da yaya din yake ciki. Daga karshe dai na mike na rufe kofa na koma cikin daki bayan na kashe wuta ko ina a gidan ina cike da zullumi a zuciyana. Alwala na dauro nazo nayi sallah nafila nakai wani lokaci ina nemawa yaya sauki a wajen Allah kafin dan barci ya saceni zuwa dare kuma na falka ban kara runtsawa ba har safe ina idar da sallah na fito zuwa kitchen abinci lafiyayye na hada inda shi kuma nayi dabaran dama mashi kunu ko za a samu ya dan sha. Karfe bakwai har nayi wanka nashirya na fito na kulle gidan na doshi asibitin gabana sai faduwa yakeyi. Tunane kan nayisa kala kala a zuciya yau idan na rasa yaya yaya zanyi da rayuwata ina zan shiga a duniyan nan mutumin da nake mafalkin shimfida rayuwa mai inganci dashi nan gaba gashi kuma Allah ya jarabeshi yana cikin halin hau,ula,i a rayuwansa yanzu. Zance nice ta farkon isa kota biyu na samu su yaya na ciki suna tsabtace masa jikin daya bata Allahu akbar bansan lokacin da kuka yazo min ba. Sammakona yasa na samu daman shiga gurinsa kai tsaye yana kwance kamar yadda muka barshi dai a jiyan dan bambanci sun sauya mashi kayan jikinsa zuwa jallabiya tufafin nasa da suka cire mai yaya isah ya miko min na karba. Iya tashigo tana fadin ga abin karyawa nan tazo muna dashi shikan ai ba abinda zai iya ci a hakan da sauri nace na dama koko ko zai dan karba a gwada a gani. Shawaran hakan suka karba na hada kunun na dan fifitashi saidai mazane sun rasa dabaran da zasuyi su bashi. Nice dai cikin karfin hali na gwada karban kofin a hannun yaya na doshi gadon ina sunkuyawa nace sannu yaya ya karfin jikin kuma Allah ya bako ikon cin jerabawan nan . Suka amsa da amin amin yaya ka dansha koko gashi na dama maka koda kadan ne don Allah cikin ka babu komai a cikin sa cikin ikon Allah sai yai kamar ya lumshe idanunsa a lokacin. Na dibo na fara dan dago kansa a hankali ina dura mashi kokon yana shiga cikinsa har muka samu ya dansha kamar spoom biyar haka dai suna fadin Alhamdullahi wanan dabaran yayi kuwa na shan koko din. Iya ke fadin aiko yunwa ya isheshi mutum kwana nawa cikinsa babu komai a lokacin su mama suka shigo dukkansu da kishiyoyinta aka fara gaisawa. Yaya Auwal ke fadin amarya tayi dabaran bashi koko ko zaisha gashi ko mun samu cikin ikon Allah ya dansha din sai mama tace nima nayi tunanen hakan a raina. Nan yan uwa suka fara cika dakin da abinci da kayan dubiya ina zaune a gefe takure har kishiyoyina suka iso saidai su Maria sun rigasu isowa tana fadin mun biya mu daukoki maigadi yace muna kin fito tunda safe ai. Kafin na amsa iya ke fadin zuwata ai yayi muna rana tunda an samu ya dansha kokon data damo mashi ta bashi ya karba sosai yasha. Irin maganganun nan da ake fada akaina mai kamar da ana yabona shine ke kara hadasa min kiyayyana a zukatan wasu a wajen irin kishiyoyina da su Saare dake gani iyyye iyye ne kawai irin nawa da son nuna ni din watace datafi kowa. Itako iya kamar zuzuta zancen takeyi a lokacin don suji haushi don sai kara cusa magana takeyi tana fadin ai ko dazun da yarinyar nan ke mashi addua ya karba. Muryan ya habune ke tambayan kawu ya fito akace bai karaso ba tukun yace iya tazo suka fita ashe zancen zuwa wanan wajen yai mata. Take fadin ya kamata kan aje din aiko wancan karon banso ya tafi tafiyan nan basu je ba amma da yake Dauda munafukine sai yakawo uzuri ga tafiyan yace wai yana gudawa lokacin. Koma dai meye yau din nan iya nake son muje din don nayi mafalki jiyan nan ba dadi wallahi ciwon nan haka zaita bibiyan mu bawai Jafar kadai ba kowan mu sai hakan ya nadesa idan har ba a dauki mataki ba. Ga zancen nan ba kowa ya kamata yasan dashi ba tunda ba zancen da za a fito a fada a fili bane har wani yaji abune daya shafe mu mu kadai wanan. Amma saidai naga kamar dole a fasa din don yau idan kawu ya kawo min uzuri wallahi za a jimu dashi a wajen nan wanan yasa na kiraki iya. Wanan shine daidai na rasa me dauda kewa noke noke ga zuwan nan gashi har ankai ga yadda ba ason akai din dole kayi masa jam ido ko zuwan zaiyi amfani a dace. Har ya juya ya dawo yana fadin sai kuma kula dashi ina son aba Rahama daman hakan ta dinga bashi kulawa idan tana kusa tunda yana jin muryanta yana bada responding kinga hakan ai alaman saukine. Shina fada jiya da dare ko yau kuma muga alama hakan don tabashi koko yasha da kanta hakan za ayi yanzu dai idan mun dawo idan babu cigaba nan asibiti sai mu koma gida dashi iya. Aje ayi na gargajiya a gani don ko lokitan nan dan Zamfara shawaran daya bani ke nan jiya yace abin nasa kamar akwai sihiri a cikinsa din haka sai mun hada dana gargajiya. Kawune ya doso wajen da matansa biyu sai dan amaryan nasa dake dauke a hannunsa iya ta kallesu taja tsuki tana fadin babu komai yanzu a cikinsa banda tabara akan wanan auren da yake ganin yayi. Suka karaso suna gaisawa tare da tambayan ya mai jiki din yace da sauki zai shige iya race barsu su shiga kaika tsaya muyi magana dakai ke hansatu idan kin shiga yi min magana da Dubu ina nemanta nan. Lokacin ne kuma muka fito dakin nida maria muka kebe muna magana dan nisa dasu sosai saidai jin yadda ya habu ke daga murya yasa hankalin mu ya koma akansu. Duk da bamu ji sosai amma na fahinci zancen tafiya sukeyi nasan kuma can din inda nakwana da tunane suke shirin zuwa. Sai lokacin nakewa maria bayanin komai tayi mamaki kwarai dana san hakan nace shiya fada min komai wallahi kamar yasan hakan zai faru dashi har dalilin dawowan iya wajena saida na bata labari. Take fadin kinga bambancinsu da ya Habu ke nan shi bai zama ya fadama damuwarsa ko wani abin rayuwansa saidai yayi tayin abu noku noku a zuciyarsa. Ya habu din ne yazo ya wuce mu a fusace ya shiga dakin bai jima da shiga ba likitocinsa sukazo hakan yasa aka fito daga dakin. Sun jima a ciki sosai kafin ya habu din ya leko yana kirana hakan yasa na mike zuwa dakin na samesu tsaye a kanshi na gaidasu. A cikin harshen turanci likitan ke fadin itace wanan ko ya amsa da eeh ya kalloni yana fadin madam sannu ko ya kuma mukaji da jimame don Allah wani aiki zaki danyi muna a yanzu. Muna son kiyi magana da maigida ko zamuga responding din hakan a garesa kinga in akwai improvement zamu dan gane musan abinda zamuyi mashi. Kin gane Rahama ana son kije kusa dashi yanzu ki danyi mai wani abinda zaisa ko ya dan motsa koya bada amsa ya habu ke fadin hakan a cikin damuwa. A hankali na motsa zuwa bakin gadon gabana sai faduwa yakeyi suko duk sun motso kusa sun zuba min idanu sai addua nakeyi a zuciyana. Hannunsa na koma a hankali na hada da nawa nakai zaune bakin gadon ina fadin sannu yaya Allah ya baka lafiya na shafo fuskansa sai yayi kamar ya lumshe idanunsa yana ajiyan zuciya. Great naji wani likitan ya fada a gefe ki kara yin wani abin madam wanan bahaushen ya fada gareni na lumshe ido nace dan gyara zama ina fadin. Yaya zaka kara shan koko ko abinci zakaci suna tsaye kamar sojoji sun kurawa ko wani part din jikinsa ido wanan karon da hannunsa yayi min alaman don hannun ya dan motsa yasa na kalli wajen hannun nasa da sauri danaji ya motsa din don hannaye mu suna harde lokacin. Sosai suke fadin akwai cigaba insha Allahu in bashi kunu din su gani hakan yasa na hada dan kunun koko din na fara bashi saidai wanan karon baisha sosai ba kamar farko. Suka daiyi dan bayanan su kafinsu fita zuwa inda suka fito aka barni da yaya Habu sakin dake cewa dani kada ki yarda kina matsawa kusa dashi Rahama ko yaushe ya kasance kina gurinsa . Ni zamu tafi wani waje dasu mama kila zamu kai dare bamu dawo ba don Allah ki kula kada ki yarda da zancen cewa ki matsa a nan din. Kin dai gane me nake nufi duk wanda ya kawo abinci ko wani abu kada ku bashi idan bakece kika hado mashi ba a daidai lokacin Saiba ta banko kofa tana fadin. Ai batafimu ba da za,ce sai ita kadai zata dinga shiga don ana son a nuna mu bakowa bane za ai muna haka tayi shiru don kallon da yaya Habu din ya banka mata yana fadin. Ke kin gane ba ko wani lokacine zaku dinga shigowa daki nan ba haka kuma ba ason hayaniya a wajensa donshine Rahama kawai sai yaya isah da yaya auwal aka amimce yanzu su dinga shigowa. Rahama din tafimune kome ta fada cikin kafeshi da idanu idan ma tafikune ke zakibawa kanki amsa mu yanzu lafiyansa muka jawa kawai ba wani abin kishin ki ba can don haka ki kiyayye a zauna lafiya yadda likitoci suka fada din. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/17, 08:36] Buhainat: [3/18, 8:26 Yamma] Seenabu Makawa: Open this link to join my WhatsApp Community: https://chat.whatsapp.com/JeOQfGohQLdKTUlsWMqXoZ [3/18, 8:28 Yamma] Seenabu Makawa: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 6️⃣5️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Wani kallo tayi mai ta juya ta fita daga dakin bata tsaya ba ta nufi hanyar fita daga asibitin kai tsaye Saarece ta hangonta ta nufeta tana kiran sunanta. Ta juyo a hasale tana fadin akan me za ace bamu shiga wajen miji mu ko Rahama ta fimu ne don kawai tana kanwar matarsa zai dinga nuna muna bambamci da ita ko me ? Haba dai kinga haka yana yuyuwa ita kadaine halan da za ai hakan wananma ai maganam bamzane watafi a cikin halan da zaice hakan ? Idan bata fimu ba aiba zai fadi hakan ba zaman me zan zauna nayi tunda ba rako mata nayi duniya ba zo muje ga mama can kada ki tafi idan kin tafi ai taci bulus ke nan a kanku ? Jin hakan yasa ta biyo saare din zuwa wajensu mama din inda suke zaune saman tabarma da abokan zamanta suna tattaunawa kan jikin jafar din. Mama kinji wai ya Habu kada su saiba su shiga dakin da ya J yake sai Rahama kadai aka yarda ta shiga wajensa amma banda su ? Wai meke damun habune haka mama dubu ta fada kafin ta rufe baki mama tace haba dai dubu tunda kikaji yace hakan ai dole akwai dalili tunda ciwon yaron nan baison damuwa ko dogon motsi a kusa dashi. Amma sai ace matansa ba a yarda suje kusa dashi ba sai wace aka so taje din zata tafi wanan wani irin danyen hukuncine haka yaya ? Habu din ne ya fito daga dakin da saurinsa hankalinsu ya koma kanshi ya karaso yana fadin ya isah fa lafiya dai suka tambaya don yadda suka ganshi a hargitse. Baba Tanimu ne yayi waya akan wani yaje ya karobo wani abu azo dashi banda lokacin zuwa yanzuni don tafiya zamuyi dasu mama zuwa wajen wani mai magani kuma. Aiga Auwal can ya dawo ina ganin gida suka danje zai tafi mama ke fadin kai habu meye hujjanka nacewa yaran nan kada suje kusa da mijinsu sai wace zuciyar ka ya yarda da ita ? Ni kuma mama yaushe nace hakan aina fada dole akwai dalili yanzun nan saratu tazo da wanan tana nuna Nusaiba tace wai kace kada su shiga mama uwargidan su mama dubu ke fadan hakan. Mama yaya za a bari suna shiga haka barkatai wajen mutumin dake son natsuwa a yanzu tashigo tana fada wai ko don me zansa likita su kira Rahama ? Nace don itace kadai ke zuwa kusa dashi ya gane tazo hakan laifine ko tsoronta akeji da zata dinga zuwa tana tayarwa mutane da hankali bayan wanda muke ciki saboda bakin kishi irin nata ? Bako za a bari ba tunda haka dama jinya ya gada ba kowa bane zai shiga haka kai tsaye aiko lokacin da Alh ke jinya ke dubu daga ke sai nice muke bayayyan shiga gurinsa a lokacin. Jinya abune fa da yake son natsuwa da maida hankali illa iyaka a bishi da addua Allah ya bashi lafiya ya mike shine abinda yake bukata garemu yanzu. Ke kenan da kika san hakan ai kin fada iya ta tsoma baki daga gefen da suke zaune suna saurarensu . To umma tsoronta za aji tunda ga gaskiya aki fada saboda ana gudun kada zuciyarta ya baci ita idan tana da tunane ai wanan abin yanzu na kowane bana mutum daya ba. Ke Nusaiba ki natsu kada ki tayarwa mutane da hankula a nan muna fama da kan mu da abinda ya damemu ke inkina da kunya ya kama aji hakan a wajen ki yanzu ? Ina wanda kike fadan kansa shine a kwance rai a hannun Allah idan kina da tunane har aji wani zance haka a bakinki yanzu kuma ? Meke faruwane mama ya Auwal yake tambaya bar yariyar nan tana son dagawa mutane hankali bayan wanda muke cikinsa a yanzu don ance su fito aba majiyanci waje ya huta take fada da Habu. Dama naso cewa a rage wanan shigowan da akeyi abar wa yanda zasu tsaya kawai tunda ba ganinsa akeyi ba zama kawai ake zuwa ayi ta hira a zauna gida abishi da addua zaifi. Wanan yarinyar amaryan shi ita damu zamu iya kulawa dashi tunda zuwanta yana da ma,ana a wajen nan ko dazun ya gane tazo don ya amsa mata adduanta da take mashi . Kunga gara din tana zama a kusa dashi ko yaushe zaifi mama ta katseshi da fadin abinda likitocin da habu suka fada ke nan ya zama matsala a gareta. Ai ba ance kada ku shiga bane hayaniyace ba a so a wajensa yasa aka fadi hakan amma ku da mijin ku a hana ku shiga ku ganshi. Dole dai me jinyar tasa idan tana da tunane ai ta bada wuri kuma ku zauna dashi din tunda jinya shina kowane bana mutum daya ba . Saiba tana gefe tsaye tana sauraren mama din don a gaskiya zatace wanan matar tana yawan shige ma lamarinta ko wani lokaci ta gaji da irin halin da mama ke nuna mata ko yaushe idan magana irin haka ya taso zata nuna itace mara gaskiya a cikin zancen. Wani bangare na zuciyarta ya gargade da kada ta yarda ta soma yiwa mama rasgin kunya duba ga yadda gaba daya family din suke ba mama girma. Yin hakan zai iya haifar mata da wani matsalan da zai jawo barin ta gidan kai tsaye donshi tayi shiru kamar tana daukan nasihan da mama din ke mata a lokacin. Saiga mama din ta koma magana kamar na lalashi a gareta tana fadin kuyi hakkuri wanan aiba komai bane idan anyi hakkuri duk hakan mai wucewane fatan mu dai Allah ya tayar da kafadan yaron nan ya samu lafiya ku koma zaman ku yadda kuke shine fatan mu kinji a dinga hakkuri da kuma saka basira cikin lamari. Hakan yasa ta danji sanyi a zuciyarta har ta nemi waje ta zauna daga gefe tana sauraren kowa a wajen . Har zuwa lokacin dasu mama har iya suka mike suka bar cikin asibitin tare da habu suka tafi inda ba wanda yasan inda zasu din sai su kadai. A cikin rashin sanin hakan na fito da wanan kayan nasa da aka cire mashi da niyar zuwa in wanke su a bakin famfo saidai kada in barshi shi kadai yasa dana fito na nufo inda suke zaune na dan duka a tsakaninsu ina fadin. Zanje in wanke kayan nan daya bata ko wata a cikinku zata shiga ta zauna dashi mama din ke fadin ke nusaiba ki shiga tunda yar uwarki nada goyo. Kamar ba zata mike ba ni dai na bar wajen na nufi wajen famfo don wanke kayan a can Maria da salima suka sameni mun jima tare dasu a wajen don dana gama zama mukayi muna hira dasu duk akan ciwon yaya din. Maman tudun wadace ta mike ta shiga dakin inda ita da umma inda suka sami saiban zaune tana waya sundan jima tsaye a kansa suna kare mashi kallo kafin mama din ta fara magana tana fadin. Gyara mashi hannun can daya taushe ta dakatar da wayan tana kallon hannun nasa tace haka na sameshi na zata ko hakan yake jin dadin kwanciya din suka barshi. Suwa ke nan fa ke yar nan ki iya kanki don Allah abinda ake fadi ke nan kuke ganin kamar an barku baya shi jinya kula yake so kaba maishi kinga ko wayan nan bai dace ace kina daga murya haka ba gabanshi. Wani irin kallon rashin kunya ta jefawa mama din kafin ta mike tsaye ta nufi wajen hannun da suke magana din tana kokarin dagawa a cikin karfi. Haba dai yi mashi a hankali mana kinsan jikin ba karfi sai a sannu dole za ai mashi komai yanzu umma ke fadin hakan a gefen mama din. Ganin ta kasa dabaran yadda zata dagoshi yasa ita umma din mikewa suka kama mashi daga shin da zasuyine suka gane yayi lalura a lokacin . Umma din ke magana tace yanzu yaya za ayi don sai an dagashi gaskiya daga inda mama take zaune take fadin sai takira yar uwata su dagashi a sauya mashi kayan tunda ya bata wa yan nan. Gabatane ya fadi ta yaya zata iya hakan amma bari ta nemo Asmau tagani suma su nuna tasu bajintan da ake ganin basu iya din. Fita tayi ta nemo Asmau din ta shigo take fada mata abinda zasuyi abinda Asmau ta fada shine ta yaya zamu iya daga shi har mu cire mashi wanan kayan Saiba ? To ya zamuyi su mama sunce mu canza mashi in bamuce haka za a barshi cikin lalura tunda mazan basu kusa a yanzu kune dai dole a yanzu zaku sauya mashi ai. Kayan da ya habu din yasa nazo dashi suka dauko sai nan suka tsaya dabara fita su mama sukayi suka barsu dashi a dakin saidai sun rasa yadda zasu fara tsarkakeshi balle su sauya mashi kayan jikinsa din. Ita saiban ce ta fito nemana dole nice nazo a cikin karfin hali na tare da taimakonsu muka samu aka sauya kayan na goge mashi jiki muka saka mai wasu tufafin a ranan na kara sheda cewa dan Adam ba a bakin komai yake ba a wajen Allah. Iya kar dan adam a lokacin da yake a raye shine yake cikin koshin lafiyansa yake jin kansa dashi wanine ashe da zaran ka rasa lafiyan ka ka rasa komai ke nan a rayuwanka. Yau yayane haka ake dagashi kamar dan jaririn da bai taba sanin duniya ba balle abinda ke cikinsa shine yau yake lalura a kwance har ake kyamar tabashi haka ? Komawa nayi still na wanke kayan daya bata din na nado wa yan nan din dana wanke da farko saidana dawo na zauna mama ke fadin waiko kinci abinci yar nan ? Maria ta kalleni take fadin bansa taci komai ba mama don tunda safe tazo wajen nan gara dai kici wani abin a cikinki kada ke ma ki kwanta ciwo . Shi jinya saika daure kana kula da kanka kaima in ba haka ba sai anyi haihuwar guzuma da kwance uwa kwance. Ki duba ko zuwan nan yan uwanki naga sunsha su lemo da kayan sanyi kada ki yarda ki bari ciwo ya kasheki hakan ba damuwansu bane su . Kece dai din a tsaya don sauya masa tufafi ita mai fadan gashi ta kasa mashi komai amma don daurin gindin iskanci nan tazo tana muna sababi dazun . Yanzun gashi don bata da kunya ta kasa daukan kayan ta wanko ina nan iskancin nan ba zan lamunceshi ba idan ta samu dubune tana juyata yadda take so niba zata sameni hakan ba . Yaya da dai kin saka masu ido don koda kikace su sauya mai kaya ta kuma daina daga murya bakiga irin kallon da taimaki ba ? Amina na sani sarai shiyasa nake son nayi maganin rashin kunyar yarinyar nan a wajen nan tea maria ta hado min mai zafi ta ban nasha don haka mama idonta yana a kaina. Su ummah da mijinta da maria ta kira a waya ta sheda masu halin da yaya J din take ciki suka taso daga kaduna da yaransa maza biyu suka zo ganinsa. Mun jima dasu a cikin dakin yayin da saiba din tazo ta zauna ta kafemu da idanuwa saikice taji labarin zamu bashi wani mugun abinne da bata yarda da hakan ba. Koda suka fito donsu wuce mun jima da ummah tana bab magana banda kuka ba abinda nakeyi shima mijinta haka ya ban baki danayi hakuri hakan jerabawane a gareni. In dage da addua da rokon Allah ina nema mashi saukin hakan a wajen Allah inda ummah take fadin sunyi magana da Hardo yace akwai abinda zai turo muna zuwa gobe. Sun tafi ina jin kamar kada su tafi su barni a cikin wanan halin dana tsunci kaina a cikinsa don gashi ina kallo farin cikina a cikin wanan halin . Haka anty Barakha ta iso zuwa yamma itama inda tasha kukanta tare da nuna alhininta ga halinda dan uwan nata keciki nice na debo mata abinci ta samu tayi sallah ta zauna taci suna zancen da yan uwanta mata su salima da saare. Gudu kawai ya habu ke shegawa tun suna dan hira a motan tsakanin iya da yayanta har yakai duk sunyi shiru saboda tafiya da nisan wajen da suka dosa din. Sai iyace da tayi barci ta tashi take fadin kai Dauda a ina kasan wanan wajen da har kazo a lokacin ? Iya me nema ai baya ganin nisan waje idan yana da bukata nima wata yar uwar Hafsatuce ta nuna min wajen don ita wajen zuwantane a lokacin. Hafsatu ke mata hiran ita halima shine tace da za aje wajen za a dace don ba wanda yajen bai dace ba . Kinji dalilin dayasa na shawarci ita halimatu din da mijinta a lokacin don da a tare zamuzo dasu sai bai bada goyon bayan hakan ba yasa nazo ni kadai a lokacin. Saidai bayan nazo dinne na fahinci irin aikin mutanen da garama da banzo dashi ba ashe don ba zai yarda muyi irin abinda akace ayi ba lokacin. Kinsan halinsa zaice shirkane ko wani abin kaucewa hakan yasa na karbo mata baki alaikum nakai mata tayi amfani dashi Allah kuma ya kawo rabon. Kaiya rabon wahala ko tunda lokaci yayi idan akai hakuri ai samu za ayi tunda komai dan lokacine Allah ya riga yayi tana da rabo don haka ba mahalukin daya isa ya hana yaran nan zuwa duniya nan. Don ni tun a lokacin ban so irin wanan abinba dauda kaida matarka kuka kafe akan hakan har kukafi yar uwar taku damuwa hakan a lokacin Yanzu ina dadin hakan don Allah abinda a karshe ake wanan irin wahalan yaron nan Allah kadai yasan irin halin rayuwan da yake tsintar kansa a cikin sa. Yau har abin yakaishi ga halin da ba aso yanzu dadin kuke nan anyi ba ayi ba ke nan wanan abin kana ganin idan yaron nan ya mutu a halin nan zai yafe maku dauda . Iya kinsan halin hafsatu fa kinsan ta da yarda da irun abin nan balle da taji ance ba zanyi arziki ba sai yar uwata ta haihu a duniya tun lokacin hafsatu tasakawa kanta damuwa. Kaji wani shirme dan Allah diyan dubu diyan kune kai da hafsatu ko diyan Dubu ne ita da mijinta ko yanzu da sunan ku suke amfani ? Ni dama nasani nadade da sanin da manufa kuke wasu abubuwa akan yaran nan ka taba jin inda dan wani ya zamo jinin wani inba shirmen ka ba dauda ? Yaron nan Jafaru yana da kawaici yasan komai ya dade da sanin komai da kuke kulawa akansa kaida matar ka amma ya kyale yake binku a hakan . Yau na tabbarta da ba jafuru bane abin nan ya sauka a kansa haka har ya sani kana ganin bayanshi akwai wanda zai kyaleku haka a cikinsu ? Dauda kaji tsoron Allah ka daina wanan rayuwan banzan yau gashi saboda son kanka dana matarka kun jefa rayuwan mu a cikin wani hali mara dadin fada ? Yaran nan sun san komai ido kawai suka saka maka dauda saboda kawaicinsu da uwarsu ita kuma tana shirme kamar tababiya ta kasa kwantar da hankali ta fahinci hakan a gareka. Sun sani fa iya kikace kawu din ya juyo yana tambaya tace kwarai ga habu nan sun jima da sanin komai a kanka har uwar tasu sun dai kyaleku kawai ne . Zufane ya fara karyowa kawu lokaci guda da har yakai ga cire fulanshi dake kanshi yana fitara dashi lokaci guda. Kalloshi Habu yayi yana gyada kai kafin yace kawu abinda nake so dakai yanzu shine ka fada muna gaskiyan zancen nan tun a nan ba sai munje gaban mutanen nan ba ? Menene asalin abinda ya kawo hakan don Allah don a gaskiya ni dai ina yawan mafarki da wata mace kai bama mafalki ba wallahi matar nan sau biyu ina arba da ita a zaria . Na farko a gidanmu nan tudun wada ta shigo da kwalan maciji tana tallah muka bata sadaka a ranan da zanyi tafiya zuwa kasan su maria a bakinta naji cewa zan hadu da maria. Bayan na dawo kuma da kwana biyu na sake haduwa da ita take fada min in fadawa mama tazo ta ganeta tun kan mai faruwa ya faru damu. Saina dauka zance ne kawai irin na mutane don haka ban dauki zancen da muhinmanci ba amma na fada ma mama a lokacin. Koda ka fada min ai munje bamu sameta ba ta tafi mama da damuwa ya dama ta tsoma masu baki karo na farko a motan . To bayab haka ban kara tuna komai ba akan zancen sai lokacin da Jafar ya kwanta ciwonsa na farko nayi mafalki da wanan matar tana min gargadi sosai kan wanan maganan . Kodana dawo kuma saina samu J a cikin wanan halin tun lokacin na san zancen nan ba karami bane haka kuma yana cikin abinda yasa kukaga J ya auri wanan yarinyar Rahama. Don yadda matar ta fada haka ya faru bazan boye maku ba yau don boyo baida amfani ita Rahama itace tayi amfani da wani magani a lokacin da j ya kwanta wancan karon itace wace tayi amfani da daman data samu ta dinga mai amfani da wani magani na gidansu har ya samu sauki. Rahama mama ta fada yace wallahi ba wanda ya sani sai Nafisa dani a lokacin don saida ta kafa huja kada a zargeta yadda wallahi nayi mafarki akan gun Rahama za a samu maganin nan haka abin ya faru shi j ya fada min komai a lokacin. Shine kukaga yayi hanyar daya aureta ake ta zarginsa dayaci amana ya fifitata akan matanshi. Amma ai baku fada muna ba mama ta fada yace ko mungaya maki mama ba yarda zakiyi ba saima ki juya zancen ta wani tsiga tunda gashi kuna fadan sun mallakemu. Ni dama nasani wallahi nasan dole akwai jafaru ba zai amfakawa yarinyr nan haka a banza ba dole akwai abinda kuke boye muna wanan ai taimakon kaine tayi balle ace za a zargeta akai iya ke fada. Iya kinsan su wanda suka tashi wajenshi aikinsa ke nan bada magani kaf nahiyarsu asan dashi zuwan da mukayi nakaisu ganin gida lokacin dansa ya bata maganin akai dace kuma ta gwadawa jafar din yayi amfani. Dole taji tsoron fitowa fili ta nuna tana bashi magani irin haka don gudun zargin matansa shi kuma dayaga ya mike shine ya ban shawaran yana son ya aureta tunma da ita Saiba tayi masu wanan zargin suna tare saiya kasance kamar ta zugashine akanta. Aida kun fada da duk hakan bai taso ba nasan Rahama zata iya komai daka fada habu don yadda ta nuna damuwata akan shi lokaci ko ciki daya suka fito ya tsaya a hakan mamake fadi. Tacigaba da fadin na dauka daga baya tayi hakan ne don kawai ta samo kansa ya aureta tayi wanan ladabin shegu din a lokacin. Ko ladabin shegu tayi ai ta cancanci hakan don ni jafaru yayi min daya aureta kece dubu yakamata ace kin gane hakan tun lokacin. Yarinyar da bata kyamarsa bata gudun ta dauki ciwon dake tare dashi wanda matansa na sunna da yan uwansu suna gudunsa don yadda fatan jikinsa kuraje suka feso masa banda ita da Nafisan a lokacin waya tsaya ya taimaka masa bai kya macesa ba ? Amma haka kika rufe ido kina nuna baki kaunan yaran nan har jininsu kada kice ko ba a fahinciki bane har yaron nan dan wajen Habu kirikiri kike nuna laifin iyayyenshi ya shafeshi kowa kuma yasani. Yanzu ga komai ya lalace maki magani a gonan ki kin kasa tsayawa ki fahinci hakan sai bin yarinyar banzan nan da kikeyi tana cusa maki bakin ciki a banza. Idan har Jafaru ya mutu a halin nan wallahi ki nemi gafaran ubangijiki biyu don alhakin yaron nan sai ya kamaku dake da dauda bama shi kadai ba tunda alama ya nuna akan diyan kaf abin yake. Innalillahi mama din ta ambata tana fadin nifa iya ba wanda ya taba tsayawa yayi min bayanin wanan abin haka inba yanzu ba. Ni yaya ake son nayi don Allah shi yaya bai tsaya ya fada min gaskiya akan maganin ba lokacin daya kawo min balle in dauki abin da muhinmanci a raina ? Dubu laifin hafsatune wallahi kuma ba komai yasa hakan ba ta hana in fada maki hakanne don cewan da akayi da arzikin yaran ki zamuyi namu arzikin . Saita dauka idan har mun fito fili mun nuna maki abinda ke nan keda yaran naki zaku juya muna baya ko nayi yunkurin fada maku saita kawo min musalai na banza akan illan dake cikin fadin da zanyi din . Kuskure kan nasan nayi wallahi saidai kawai ayi ,,,,, kai rufe muna baki shasha kawai kaji kunuan duniya wallahi sauran ka na lahira ka rasa wace zaka cuta sai yar uwarka tillo ciki daya dauda akan matar ka ? Hansatu mutumiyar banzace kasani kuma kake take sanin don son kai meye yaran nan suka rageka dashi don Allah koma meka boye muna yanzu ai zamuji tunda anzo wajen insha Allahu. Don Allah ku gafarceni nasan nayi kuskure kuma nayi nadama ku yarda dani hakan nima banyin kaina bane laifin hafsatune wallahi. Wani dogon tsuk iyan taja tana kauda kai yayin da mama keta wani irin gumjin kuka ta kasa magana sai can tace yaya daka fada min tin farko da banyi amfani da maganin nan ba tunda baka fada min ka,idanshi ba a lokacin. Habune ya kallo kawu dake faman zufa rai bace don har lokacin kawu yana hitarane kanshi yana faman zubar da zufa . Yace munzo ta wani hanya zamu dauka yace ka dauki hanyar dama shi zai kaimu garin da zamu dauki hanyar zuwa kauye daga nan. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/17, 08:36] Buhainat: [3/18, 8:26 Yamma] Seenabu Makawa: Open this link to join my WhatsApp Community: https://chat.whatsapp.com/JeOQfGohQLdKTUlsWMqXoZ [3/18, 8:28 Yamma] Seenabu Makawa: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 6️⃣5️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Wani kallo tayi mai ta juya ta fita daga dakin bata tsaya ba ta nufi hanyar fita daga asibitin kai tsaye Saarece ta hangonta ta nufeta tana kiran sunanta. Ta juyo a hasale tana fadin akan me za ace bamu shiga wajen miji mu ko Rahama ta fimu ne don kawai tana kanwar matarsa zai dinga nuna muna bambamci da ita ko me ? Haba dai kinga haka yana yuyuwa ita kadaine halan da za ai hakan wananma ai maganam bamzane watafi a cikin halan da zaice hakan ? Idan bata fimu ba aiba zai fadi hakan ba zaman me zan zauna nayi tunda ba rako mata nayi duniya ba zo muje ga mama can kada ki tafi idan kin tafi ai taci bulus ke nan a kanku ? Jin hakan yasa ta biyo saare din zuwa wajensu mama din inda suke zaune saman tabarma da abokan zamanta suna tattaunawa kan jikin jafar din. Mama kinji wai ya Habu kada su saiba su shiga dakin da ya J yake sai Rahama kadai aka yarda ta shiga wajensa amma banda su ? Wai meke damun habune haka mama dubu ta fada kafin ta rufe baki mama tace haba dai dubu tunda kikaji yace hakan ai dole akwai dalili tunda ciwon yaron nan baison damuwa ko dogon motsi a kusa dashi. Amma sai ace matansa ba a yarda suje kusa dashi ba sai wace aka so taje din zata tafi wanan wani irin danyen hukuncine haka yaya ? Habu din ne ya fito daga dakin da saurinsa hankalinsu ya koma kanshi ya karaso yana fadin ya isah fa lafiya dai suka tambaya don yadda suka ganshi a hargitse. Baba Tanimu ne yayi waya akan wani yaje ya karobo wani abu azo dashi banda lokacin zuwa yanzuni don tafiya zamuyi dasu mama zuwa wajen wani mai magani kuma. Aiga Auwal can ya dawo ina ganin gida suka danje zai tafi mama ke fadin kai habu meye hujjanka nacewa yaran nan kada suje kusa da mijinsu sai wace zuciyar ka ya yarda da ita ? Ni kuma mama yaushe nace hakan aina fada dole akwai dalili yanzun nan saratu tazo da wanan tana nuna Nusaiba tace wai kace kada su shiga mama uwargidan su mama dubu ke fadan hakan. Mama yaya za a bari suna shiga haka barkatai wajen mutumin dake son natsuwa a yanzu tashigo tana fada wai ko don me zansa likita su kira Rahama ? Nace don itace kadai ke zuwa kusa dashi ya gane tazo hakan laifine ko tsoronta akeji da zata dinga zuwa tana tayarwa mutane da hankali bayan wanda muke ciki saboda bakin kishi irin nata ? Bako za a bari ba tunda haka dama jinya ya gada ba kowa bane zai shiga haka kai tsaye aiko lokacin da Alh ke jinya ke dubu daga ke sai nice muke bayayyan shiga gurinsa a lokacin. Jinya abune fa da yake son natsuwa da maida hankali illa iyaka a bishi da addua Allah ya bashi lafiya ya mike shine abinda yake bukata garemu yanzu. Ke kenan da kika san hakan ai kin fada iya ta tsoma baki daga gefen da suke zaune suna saurarensu . To umma tsoronta za aji tunda ga gaskiya aki fada saboda ana gudun kada zuciyarta ya baci ita idan tana da tunane ai wanan abin yanzu na kowane bana mutum daya ba. Ke Nusaiba ki natsu kada ki tayarwa mutane da hankula a nan muna fama da kan mu da abinda ya damemu ke inkina da kunya ya kama aji hakan a wajen ki yanzu ? Ina wanda kike fadan kansa shine a kwance rai a hannun Allah idan kina da tunane har aji wani zance haka a bakinki yanzu kuma ? Meke faruwane mama ya Auwal yake tambaya bar yariyar nan tana son dagawa mutane hankali bayan wanda muke cikinsa a yanzu don ance su fito aba majiyanci waje ya huta take fada da Habu. Dama naso cewa a rage wanan shigowan da akeyi abar wa yanda zasu tsaya kawai tunda ba ganinsa akeyi ba zama kawai ake zuwa ayi ta hira a zauna gida abishi da addua zaifi. Wanan yarinyar amaryan shi ita damu zamu iya kulawa dashi tunda zuwanta yana da ma,ana a wajen nan ko dazun ya gane tazo don ya amsa mata adduanta da take mashi . Kunga gara din tana zama a kusa dashi ko yaushe zaifi mama ta katseshi da fadin abinda likitocin da habu suka fada ke nan ya zama matsala a gareta. Ai ba ance kada ku shiga bane hayaniyace ba a so a wajensa yasa aka fadi hakan amma ku da mijin ku a hana ku shiga ku ganshi. Dole dai me jinyar tasa idan tana da tunane ai ta bada wuri kuma ku zauna dashi din tunda jinya shina kowane bana mutum daya ba . Saiba tana gefe tsaye tana sauraren mama din don a gaskiya zatace wanan matar tana yawan shige ma lamarinta ko wani lokaci ta gaji da irin halin da mama ke nuna mata ko yaushe idan magana irin haka ya taso zata nuna itace mara gaskiya a cikin zancen. Wani bangare na zuciyarta ya gargade da kada ta yarda ta soma yiwa mama rasgin kunya duba ga yadda gaba daya family din suke ba mama girma. Yin hakan zai iya haifar mata da wani matsalan da zai jawo barin ta gidan kai tsaye donshi tayi shiru kamar tana daukan nasihan da mama din ke mata a lokacin. Saiga mama din ta koma magana kamar na lalashi a gareta tana fadin kuyi hakkuri wanan aiba komai bane idan anyi hakkuri duk hakan mai wucewane fatan mu dai Allah ya tayar da kafadan yaron nan ya samu lafiya ku koma zaman ku yadda kuke shine fatan mu kinji a dinga hakkuri da kuma saka basira cikin lamari. Hakan yasa ta danji sanyi a zuciyarta har ta nemi waje ta zauna daga gefe tana sauraren kowa a wajen . Har zuwa lokacin dasu mama har iya suka mike suka bar cikin asibitin tare da habu suka tafi inda ba wanda yasan inda zasu din sai su kadai. A cikin rashin sanin hakan na fito da wanan kayan nasa da aka cire mashi da niyar zuwa in wanke su a bakin famfo saidai kada in barshi shi kadai yasa dana fito na nufo inda suke zaune na dan duka a tsakaninsu ina fadin. Zanje in wanke kayan nan daya bata ko wata a cikinku zata shiga ta zauna dashi mama din ke fadin ke nusaiba ki shiga tunda yar uwarki nada goyo. Kamar ba zata mike ba ni dai na bar wajen na nufi wajen famfo don wanke kayan a can Maria da salima suka sameni mun jima tare dasu a wajen don dana gama zama mukayi muna hira dasu duk akan ciwon yaya din. Maman tudun wadace ta mike ta shiga dakin inda ita da umma inda suka sami saiban zaune tana waya sundan jima tsaye a kansa suna kare mashi kallo kafin mama din ta fara magana tana fadin. Gyara mashi hannun can daya taushe ta dakatar da wayan tana kallon hannun nasa tace haka na sameshi na zata ko hakan yake jin dadin kwanciya din suka barshi. Suwa ke nan fa ke yar nan ki iya kanki don Allah abinda ake fadi ke nan kuke ganin kamar an barku baya shi jinya kula yake so kaba maishi kinga ko wayan nan bai dace ace kina daga murya haka ba gabanshi. Wani irin kallon rashin kunya ta jefawa mama din kafin ta mike tsaye ta nufi wajen hannun da suke magana din tana kokarin dagawa a cikin karfi. Haba dai yi mashi a hankali mana kinsan jikin ba karfi sai a sannu dole za ai mashi komai yanzu umma ke fadin hakan a gefen mama din. Ganin ta kasa dabaran yadda zata dagoshi yasa ita umma din mikewa suka kama mashi daga shin da zasuyine suka gane yayi lalura a lokacin . Umma din ke magana tace yanzu yaya za ayi don sai an dagashi gaskiya daga inda mama take zaune take fadin sai takira yar uwata su dagashi a sauya mashi kayan tunda ya bata wa yan nan. Gabatane ya fadi ta yaya zata iya hakan amma bari ta nemo Asmau tagani suma su nuna tasu bajintan da ake ganin basu iya din. Fita tayi ta nemo Asmau din ta shigo take fada mata abinda zasuyi abinda Asmau ta fada shine ta yaya zamu iya daga shi har mu cire mashi wanan kayan Saiba ? To ya zamuyi su mama sunce mu canza mashi in bamuce haka za a barshi cikin lalura tunda mazan basu kusa a yanzu kune dai dole a yanzu zaku sauya mashi ai. Kayan da ya habu din yasa nazo dashi suka dauko sai nan suka tsaya dabara fita su mama sukayi suka barsu dashi a dakin saidai sun rasa yadda zasu fara tsarkakeshi balle su sauya mashi kayan jikinsa din. Ita saiban ce ta fito nemana dole nice nazo a cikin karfin hali na tare da taimakonsu muka samu aka sauya kayan na goge mashi jiki muka saka mai wasu tufafin a ranan na kara sheda cewa dan Adam ba a bakin komai yake ba a wajen Allah. Iya kar dan adam a lokacin da yake a raye shine yake cikin koshin lafiyansa yake jin kansa dashi wanine ashe da zaran ka rasa lafiyan ka ka rasa komai ke nan a rayuwanka. Yau yayane haka ake dagashi kamar dan jaririn da bai taba sanin duniya ba balle abinda ke cikinsa shine yau yake lalura a kwance har ake kyamar tabashi haka ? Komawa nayi still na wanke kayan daya bata din na nado wa yan nan din dana wanke da farko saidana dawo na zauna mama ke fadin waiko kinci abinci yar nan ? Maria ta kalleni take fadin bansa taci komai ba mama don tunda safe tazo wajen nan gara dai kici wani abin a cikinki kada ke ma ki kwanta ciwo . Shi jinya saika daure kana kula da kanka kaima in ba haka ba sai anyi haihuwar guzuma da kwance uwa kwance. Ki duba ko zuwan nan yan uwanki naga sunsha su lemo da kayan sanyi kada ki yarda ki bari ciwo ya kasheki hakan ba damuwansu bane su . Kece dai din a tsaya don sauya masa tufafi ita mai fadan gashi ta kasa mashi komai amma don daurin gindin iskanci nan tazo tana muna sababi dazun . Yanzun gashi don bata da kunya ta kasa daukan kayan ta wanko ina nan iskancin nan ba zan lamunceshi ba idan ta samu dubune tana juyata yadda take so niba zata sameni hakan ba . Yaya da dai kin saka masu ido don koda kikace su sauya mai kaya ta kuma daina daga murya bakiga irin kallon da taimaki ba ? Amina na sani sarai shiyasa nake son nayi maganin rashin kunyar yarinyar nan a wajen nan tea maria ta hado min mai zafi ta ban nasha don haka mama idonta yana a kaina. Su ummah da mijinta da maria ta kira a waya ta sheda masu halin da yaya J din take ciki suka taso daga kaduna da yaransa maza biyu suka zo ganinsa. Mun jima dasu a cikin dakin yayin da saiba din tazo ta zauna ta kafemu da idanuwa saikice taji labarin zamu bashi wani mugun abinne da bata yarda da hakan ba. Koda suka fito donsu wuce mun jima da ummah tana bab magana banda kuka ba abinda nakeyi shima mijinta haka ya ban baki danayi hakuri hakan jerabawane a gareni. In dage da addua da rokon Allah ina nema mashi saukin hakan a wajen Allah inda ummah take fadin sunyi magana da Hardo yace akwai abinda zai turo muna zuwa gobe. Sun tafi ina jin kamar kada su tafi su barni a cikin wanan halin dana tsunci kaina a cikinsa don gashi ina kallo farin cikina a cikin wanan halin . Haka anty Barakha ta iso zuwa yamma itama inda tasha kukanta tare da nuna alhininta ga halinda dan uwan nata keciki nice na debo mata abinci ta samu tayi sallah ta zauna taci suna zancen da yan uwanta mata su salima da saare. Gudu kawai ya habu ke shegawa tun suna dan hira a motan tsakanin iya da yayanta har yakai duk sunyi shiru saboda tafiya da nisan wajen da suka dosa din. Sai iyace da tayi barci ta tashi take fadin kai Dauda a ina kasan wanan wajen da har kazo a lokacin ? Iya me nema ai baya ganin nisan waje idan yana da bukata nima wata yar uwar Hafsatuce ta nuna min wajen don ita wajen zuwantane a lokacin. Hafsatu ke mata hiran ita halima shine tace da za aje wajen za a dace don ba wanda yajen bai dace ba . Kinji dalilin dayasa na shawarci ita halimatu din da mijinta a lokacin don da a tare zamuzo dasu sai bai bada goyon bayan hakan ba yasa nazo ni kadai a lokacin. Saidai bayan nazo dinne na fahinci irin aikin mutanen da garama da banzo dashi ba ashe don ba zai yarda muyi irin abinda akace ayi ba lokacin. Kinsan halinsa zaice shirkane ko wani abin kaucewa hakan yasa na karbo mata baki alaikum nakai mata tayi amfani dashi Allah kuma ya kawo rabon. Kaiya rabon wahala ko tunda lokaci yayi idan akai hakuri ai samu za ayi tunda komai dan lokacine Allah ya riga yayi tana da rabo don haka ba mahalukin daya isa ya hana yaran nan zuwa duniya nan. Don ni tun a lokacin ban so irin wanan abinba dauda kaida matarka kuka kafe akan hakan har kukafi yar uwar taku damuwa hakan a lokacin Yanzu ina dadin hakan don Allah abinda a karshe ake wanan irin wahalan yaron nan Allah kadai yasan irin halin rayuwan da yake tsintar kansa a cikin sa. Yau har abin yakaishi ga halin da ba aso yanzu dadin kuke nan anyi ba ayi ba ke nan wanan abin kana ganin idan yaron nan ya mutu a halin nan zai yafe maku dauda . Iya kinsan halin hafsatu fa kinsan ta da yarda da irun abin nan balle da taji ance ba zanyi arziki ba sai yar uwata ta haihu a duniya tun lokacin hafsatu tasakawa kanta damuwa. Kaji wani shirme dan Allah diyan dubu diyan kune kai da hafsatu ko diyan Dubu ne ita da mijinta ko yanzu da sunan ku suke amfani ? Ni dama nasani nadade da sanin da manufa kuke wasu abubuwa akan yaran nan ka taba jin inda dan wani ya zamo jinin wani inba shirmen ka ba dauda ? Yaron nan Jafaru yana da kawaici yasan komai ya dade da sanin komai da kuke kulawa akansa kaida matar ka amma ya kyale yake binku a hakan . Yau na tabbarta da ba jafuru bane abin nan ya sauka a kansa haka har ya sani kana ganin bayanshi akwai wanda zai kyaleku haka a cikinsu ? Dauda kaji tsoron Allah ka daina wanan rayuwan banzan yau gashi saboda son kanka dana matarka kun jefa rayuwan mu a cikin wani hali mara dadin fada ? Yaran nan sun san komai ido kawai suka saka maka dauda saboda kawaicinsu da uwarsu ita kuma tana shirme kamar tababiya ta kasa kwantar da hankali ta fahinci hakan a gareka. Sun sani fa iya kikace kawu din ya juyo yana tambaya tace kwarai ga habu nan sun jima da sanin komai a kanka har uwar tasu sun dai kyaleku kawai ne . Zufane ya fara karyowa kawu lokaci guda da har yakai ga cire fulanshi dake kanshi yana fitara dashi lokaci guda. Kalloshi Habu yayi yana gyada kai kafin yace kawu abinda nake so dakai yanzu shine ka fada muna gaskiyan zancen nan tun a nan ba sai munje gaban mutanen nan ba ? Menene asalin abinda ya kawo hakan don Allah don a gaskiya ni dai ina yawan mafarki da wata mace kai bama mafalki ba wallahi matar nan sau biyu ina arba da ita a zaria . Na farko a gidanmu nan tudun wada ta shigo da kwalan maciji tana tallah muka bata sadaka a ranan da zanyi tafiya zuwa kasan su maria a bakinta naji cewa zan hadu da maria. Bayan na dawo kuma da kwana biyu na sake haduwa da ita take fada min in fadawa mama tazo ta ganeta tun kan mai faruwa ya faru damu. Saina dauka zance ne kawai irin na mutane don haka ban dauki zancen da muhinmanci ba amma na fada ma mama a lokacin. Koda ka fada min ai munje bamu sameta ba ta tafi mama da damuwa ya dama ta tsoma masu baki karo na farko a motan . To bayab haka ban kara tuna komai ba akan zancen sai lokacin da Jafar ya kwanta ciwonsa na farko nayi mafalki da wanan matar tana min gargadi sosai kan wanan maganan . Kodana dawo kuma saina samu J a cikin wanan halin tun lokacin na san zancen nan ba karami bane haka kuma yana cikin abinda yasa kukaga J ya auri wanan yarinyar Rahama. Don yadda matar ta fada haka ya faru bazan boye maku ba yau don boyo baida amfani ita Rahama itace tayi amfani da wani magani a lokacin da j ya kwanta wancan karon itace wace tayi amfani da daman data samu ta dinga mai amfani da wani magani na gidansu har ya samu sauki. Rahama mama ta fada yace wallahi ba wanda ya sani sai Nafisa dani a lokacin don saida ta kafa huja kada a zargeta yadda wallahi nayi mafarki akan gun Rahama za a samu maganin nan haka abin ya faru shi j ya fada min komai a lokacin. Shine kukaga yayi hanyar daya aureta ake ta zarginsa dayaci amana ya fifitata akan matanshi. Amma ai baku fada muna ba mama ta fada yace ko mungaya maki mama ba yarda zakiyi ba saima ki juya zancen ta wani tsiga tunda gashi kuna fadan sun mallakemu. Ni dama nasani wallahi nasan dole akwai jafaru ba zai amfakawa yarinyr nan haka a banza ba dole akwai abinda kuke boye muna wanan ai taimakon kaine tayi balle ace za a zargeta akai iya ke fada. Iya kinsan su wanda suka tashi wajenshi aikinsa ke nan bada magani kaf nahiyarsu asan dashi zuwan da mukayi nakaisu ganin gida lokacin dansa ya bata maganin akai dace kuma ta gwadawa jafar din yayi amfani. Dole taji tsoron fitowa fili ta nuna tana bashi magani irin haka don gudun zargin matansa shi kuma dayaga ya mike shine ya ban shawaran yana son ya aureta tunma da ita Saiba tayi masu wanan zargin suna tare saiya kasance kamar ta zugashine akanta. Aida kun fada da duk hakan bai taso ba nasan Rahama zata iya komai daka fada habu don yadda ta nuna damuwata akan shi lokaci ko ciki daya suka fito ya tsaya a hakan mamake fadi. Tacigaba da fadin na dauka daga baya tayi hakan ne don kawai ta samo kansa ya aureta tayi wanan ladabin shegu din a lokacin. Ko ladabin shegu tayi ai ta cancanci hakan don ni jafaru yayi min daya aureta kece dubu yakamata ace kin gane hakan tun lokacin. Yarinyar da bata kyamarsa bata gudun ta dauki ciwon dake tare dashi wanda matansa na sunna da yan uwansu suna gudunsa don yadda fatan jikinsa kuraje suka feso masa banda ita da Nafisan a lokacin waya tsaya ya taimaka masa bai kya macesa ba ? Amma haka kika rufe ido kina nuna baki kaunan yaran nan har jininsu kada kice ko ba a fahinciki bane har yaron nan dan wajen Habu kirikiri kike nuna laifin iyayyenshi ya shafeshi kowa kuma yasani. Yanzu ga komai ya lalace maki magani a gonan ki kin kasa tsayawa ki fahinci hakan sai bin yarinyar banzan nan da kikeyi tana cusa maki bakin ciki a banza. Idan har Jafaru ya mutu a halin nan wallahi ki nemi gafaran ubangijiki biyu don alhakin yaron nan sai ya kamaku dake da dauda bama shi kadai ba tunda alama ya nuna akan diyan kaf abin yake. Innalillahi mama din ta ambata tana fadin nifa iya ba wanda ya taba tsayawa yayi min bayanin wanan abin haka inba yanzu ba. Ni yaya ake son nayi don Allah shi yaya bai tsaya ya fada min gaskiya akan maganin ba lokacin daya kawo min balle in dauki abin da muhinmanci a raina ? Dubu laifin hafsatune wallahi kuma ba komai yasa hakan ba ta hana in fada maki hakanne don cewan da akayi da arzikin yaran ki zamuyi namu arzikin . Saita dauka idan har mun fito fili mun nuna maki abinda ke nan keda yaran naki zaku juya muna baya ko nayi yunkurin fada maku saita kawo min musalai na banza akan illan dake cikin fadin da zanyi din . Kuskure kan nasan nayi wallahi saidai kawai ayi ,,,,, kai rufe muna baki shasha kawai kaji kunuan duniya wallahi sauran ka na lahira ka rasa wace zaka cuta sai yar uwarka tillo ciki daya dauda akan matar ka ? Hansatu mutumiyar banzace kasani kuma kake take sanin don son kai meye yaran nan suka rageka dashi don Allah koma meka boye muna yanzu ai zamuji tunda anzo wajen insha Allahu. Don Allah ku gafarceni nasan nayi kuskure kuma nayi nadama ku yarda dani hakan nima banyin kaina bane laifin hafsatune wallahi. Wani dogon tsuk iyan taja tana kauda kai yayin da mama keta wani irin gumjin kuka ta kasa magana sai can tace yaya daka fada min tin farko da banyi amfani da maganin nan ba tunda baka fada min ka,idanshi ba a lokacin. Habune ya kallo kawu dake faman zufa rai bace don har lokacin kawu yana hitarane kanshi yana faman zubar da zufa . Yace munzo ta wani hanya zamu dauka yace ka dauki hanyar dama shi zai kaimu garin da zamu dauki hanyar zuwa kauye daga nan. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/17, 08:36] Buhainat: [3/18, 8:26 Yamma] Seenabu Makawa: Open this link to join my WhatsApp Community: https://chat.whatsapp.com/JeOQfGohQLdKTUlsWMqXoZ [3/18, 8:28 Yamma] Seenabu Makawa: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 6️⃣6️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Kuka kan kallo daya zakiyi min kisan nasha kuka a wanan wunin don yadda idanuwana sukai hulu hulu saboda kukan da nake kebewa inyi, Tare da tunanen duniya kala kala dake sauka min a zuciyana game da halin da yaya Jafar din yake ciki. Ina zaune nayi shiru a gefe tabarman dasu mama ke zaune sama bayan mun idar da sallah la,asar nagama maman tudun wada ta miko min kofi cike da fura har da kankara a sama . Kaina girgiza alaman a,a don banson komai a lokacin take fadin maza karbi kisha ina kule dake tun karyawan safe baki kara saka komai a cikinki ba yar nan. Masu fadin suke dashi don suke da diya dashi aun zage nan suna ciye ciyensu a gaba kowa balle ke din da sukewa arashun baki aje ko kwai a tare dashi ba balle ki fisu nuna damuwa sun zage suna kai abu ga bakin salatinsu. Maza ki karba kisha ki danji nauyi a cikinki kinji Allah ya kareki da takaban kuriciya da suke maku fata hakan don yafi komai daci da muni ga ya,mace . Hawayene suka sulalo a idona take fadin ki daure ki daina wanan kukan haka Allah ya tada kafadan mijinku yasa hakan zakan jikine a garesa. Karbi maza ki shanye ba a jinya da yunwa don saika fadi mai ciwo yazo ya mike Allah ya tsare dole na karba nasha din datace min saidai ban iya shanyewa ba na rike sauran a hannuna take fadin maza na shanye na miko mata kofin . Dole na kara kurbe sauran ban kaiga idawa ba Asmau ta kwala min kira da nazo daga kofan dakin hakan yasa na aje kofin da sauri na mike tsaye na nufi dakin . Don na fito saboda karmu saida hali a waje don yadda take nunawa lokacin dana shiga dakin ko abu zanyiwa yaya din zata taso da sauri tace dani na bari kawai ai zasuyi mai ko idan na dauki abu zatace na miko mata abin. Ganin hakan yasa na fito daga dakin don zuciya bata da kashi zan iya kasa hakkuri na biye mata muyi abinda ba daidai ba har mutane suji a tafi damu a baki. Koda na shiga dakin na zata wani abune sai take cemin wai na duba ko ya sake bata jikinshi wani kallo nayi mata mai nuna baki isa ba. Kin fimu karfin hali yasa muka kiraki Asmau ke fadin hakan gareni nace na zata ba saini ba zaku iya hakan ga mijin ku ai. Ke don mun kiraki kada ki fadawa mutane maganan banza don Allah idan ba zaki iya ba kice ba zakiyi ba kada ki kawowa mutane wani zancen banza a nan ? Banda lokacin ki don haka kiyi haushin ki ke kadai dama kin saba ciwon nasa aida alaman ba damuwanki yayi ba don da baki zauna kina damunsa da waya haka ba akai. Ashe kinji zafin wayan da nakeyi din inkin isa kizo ki karbe wayan insan kincika yar jin haushi kaji min yarinya da zancen banza har wakike inbashi dayaga abin banza ya nace akanki ba ? Subbahanallahi dama nayi tunanen hakan ai yasa na biyo ku, yanzu yarinyar nan har bawan Allah nan yana kwance haka cikin wanan halin ? Amma baki saduda da wanan halin naki ba sai kin dagawa mutane harshe a nan kuma ? Muryan mamace data biyoni bayan shigowana take fadan hakan tana tafa hannu don bata jini ba saiba din ta sama tana fada min maganganu a bakinta lokacin. Wani daga harshe nayi yanzu kuma mama ita har waye da zata tsaya tana fada min magana akan abinda zanyi yaushe ta samu wanan power din take ganin takai ? Amma kin kai sakarai ashe ? har yaushe wanan taga lokacin fadan wani magana gareki a nan yarinyar dake ta faman darzan kuka tun dazun a waje . Gadon da yake kwancene ya fara jijiga gaba dayan mu hankalin mu ya koma kanshi hakoransane ya datse a waje daya yayin da idanuwansa suka firfito waje ma,ana dai ya kara shiga wani sabon hali lokaci guda kuma. Ko salatin mama ya isa ya rudamu a lokacin inda Asmau ta fita waje da gudu tana neman taimako ga mutanen dake zaune waje cikin rudewa da tashin hankali. Ba maza a kusa iya mu matane da muka cika asibitin a lokacin sai salima data hari dakin likitocin hankali tashe don kiransu. Rasa me zanyi nayi saina tuna da dan anty salma ya samu attack irin hakan yadda mukai masa a abuja da sauri na juya na dauko spoon na nufeshi ina kokarin bude bakinsa na tura spoon din ya datse tsakanin harshensa da hakoransa. Kanshi yana saman jikina muryata a cikin tashin hankali na soma fadin don Allah ku rike min kafansa daga mama din har ita saiban sun kasa hakan shigowan Maria da Anty Barakha ya taimaka min suka rike kafafuwan nasa dake halbawa. Innalillahi nake maimaitawa saiga likitocin sun shigo a rude nurse suna fadin a rage daga dakin a fita don koke koke da yai yawa a lokacin dakin duk kowa na tsaye cirko cirko a cikin tashin hankali. Ruwan sanyi ko kankara nake fada ina nuna hanyar waje likitan ya kamo hannayesa yana dubawa har lokacin yana kwance shambal a jikina. Ruwan da nake fada din suka miko min a daidai kanshi na manna ruwan sanyin lokaci guda ya sauke wani irin ajiyan zuciya mai karfi ya daina wanan gurnanin da yakeyi da farko. Dukkan mu matansa mu ukku muna tsaye a dakin a cikin tashin hankali har likitocin sukai mashi abinda zasuyi din ganin ya lafa suka soma magana a cikin fada. Ba mun fada maku a daina shigowa ba haka da yawa dakin muna son ganin farfadowansane a ko wani lokaci zai iya yuyuwa yana jin komai saidai nisan fita hayacinsa da yayine ba zai bari a fahinci hakan ba zai iya jin wani magana da zai iya daga mashi hankali kuma har hakan ya faru kunga ciwon yana son canza sabon sallo kuma ke nan. Na yarda da maganan ka likita don matar nan tasace ke sa insa a dakin lokacin da abin ya faru kaga ke nan zancen ka gaskiyane ke nan a nan mace ke fadan hakan. Kuka saiba ta saka mai karfi tana fadin don kawai ba a kaunata za ace nice nayi sanadin hakan ya faru ya zata fada min magana inki ramawa don ina tsoronta ko me ? A nan kowa ya raina mata wayau don fahintar itace silan faruwan hakan ashe a lokacin da mama ta fada. Anty barakha ke fadin indai hakane aisai duk su fita wallahi tunda ba zaman Allah da annabi sukeyi a nan ba zasu kashe muna dan uwa da bakin kishinsu kawai ? Ya zama dole duk su fita likitan ya kalleta yace ita wanan na zaune bida gadon data bashi taimakon gagawa ina matarshi ce ? Yana da kyau a barta a kusa dashi na fadawa brother nasa dazun don tana taimakawa sosai wajen abubuwa da dama ko yanzu badon tana wajen ba da zaiji ciwo sosai wallahi. Don zai iya fadowa daga gadon haka kuma harshensa zai datse din ya ja masa wani matsala babba kuma sabo amma taimakon data bashi din ya taimaka muna sosai a yanzu wajen magance matsalan don haka abarta a tare dashi please . Amma kowa ya fita daga dakin nan a yanzu sai mutum biyu kawai za a bari a ciki tare dashi da zasu zauna su duba halin da yake ciki. A daidai lokacin kuma su yaya Auwal suka shigo a rude don an kirasu a waya ana sheda masu halin daya shiga din a lokacin suna wajen karbo maganin da ya habu yai magana a kai. Ankara masu bayani ya isah bai tsaya likitan yakai karshe ba ya soma magana yana fadin amma na fada ai kada wanda ya shiga bayan amarya saike mama din me za a barsu su shigo har haka ya faru ? To ya zanyi inyi magana yarinya tana batun zagina don kawai na fada mata gaskiya ku yanzu ai ku tsawata mata ta daina kila amma halin yarinyar nan ai baiyi ba wallahi. Kishi har mutum yana kwance gadon asibiti ba zaki saduda ba yanzu da likita daku kuka fada ai zata fahinta ko ? To kuji don Allah duk wanda yazo ya gaidashi ya fita don ba zamu hanaku shigowa duban mijin ku ba amma a shigo a tsanake a fice daga yau don ba zamu lamuci rashin hankali ba a nan lafiyan dan uwan mu muke duba a yanzu ba kishin banza ba a nan. Wanan abinda ya faru yasa jikin kowa sanyi har saiban da take jin take gani mamata lauya mata laifin komai a kai duk da tasan ba gaskiya bane nice dai na fara gasa mata magana gashi kuma Asmau taki magana har lokacin sai kukan da take faman yi akan laluran mijinta din. Basu jima ba ganin ya samu barci ya koma normal sukayi sallama suka koma gida nikan ina asibitin tunda naga maman tudun wada ta kama min na samu shiga a idanuwansu kishi ke nan dama. Da kwatance kawu dauda suka tsaya a wani gidan zana dake can dan gefen garin wajen dake dauke da wasu manyan itatuwa dake karawa mazauna wajen ni,ima. A gaban gidan ya tsayar da motarshi yayin da mutanen dake zaune a innuwar suka zubo masu idanu suga masu fitowa daga motan. Kawu ya fara fita har hulansa na faduwa kasa kafin ya bude bayan motan iya ta sako kafa ta fito tare da mama shi yaya habu shine ya fito karshe suka nufi wajen mutanen bayan ya rufe motar tashi da key. Kawu ya fara gaidasu suka amsa tare da masu sannu da zuwa da yaya hanya bayan gama gaishe gaishensune yake fadin don Allah Tuni fa da cewa matar kamar yadda ake kiranta dashi a wajen. Wani daga cikin mutanen ne yace wai Tuni kan ai ta dade da barin mu saidai yarta kudidi ke aikin a yanzu tana ciki in wurinta kuka zo? Innalillahi iya ta ambata tare da fadin shike nan dauda son kanka ya halakamu ga baki daya yanzu kuma ya habu yacewa mutumin kana nufin bata raye yanzu ita tuni din ? Ai kaji me nace yau shekara kusan biyu ke nan da rasuwanta ai amma yarta na ciki itace ta gajeta ga aikin yanzu aifa shike nan kuma kai habu namu ya samemu kuma a yanzu iya ta kara fada a rude mama kan hawayene suka soma zubo mata lokaci guda takai tsugunne a waje daya cikin tashin hankali. Dayan mutumin ke fadin ku karasa ciki koma meye yarta kudidi tana nan zata saurareku ai don ganin yadda fuskokinsu ya nuna damuwa da tashin hankali lokaci guda jin mutuwan tsohuwan da sukayi. Yaro aka tura yayi masu iso da matar da aka kira da kudidi din ta dan jima bata fito ba don tana ganawa da wasu bakin a lokacin . Yayin datayi masu ison su shigo kawune ya fara shiga dakin da take karban bakinta sai iya sai mama dubu habune yayi karshen shiga dakin da sallama a bakinsa. Neman inda zai zauna yayi ya kai tsugune don ita wace suka zo wurinta din tana neman wani abu a lokacin don haka ta basu baya ba zasuce ga fuskanta ba . Lokaci guda gabanshi ya fadi yayin da yai arba da wanan matar mai maciji a kwalla na shekarun baya ba zai taba mantawa da fuskan wanan matar ba. Ba annuri a fuskan nata gata saye cikin bakaken tufafi irin na mutanen dauri tun daga sama har kasa sune a jikinta. Yau Allah yayi kun samu zuwa ke nan abinda ya fito daga bakinta ke nan lokacin data juyo garesu shiru dan dakin yayi na lokaci guda. Ta mika hannu ta dauko wani dan kwarya ta girke a tsakiyarsu tana fadin tabaci ke nan tunda na ganku nan kai habu aina fadama dole saika nememu dama tun abu baikai haka ba har kun bari komai yakai ga lalacewa. Sunan habu data kirane ya basu mamaki gaba dayansu har habu din da har lokacin kallon mamaki yake binta dashi . Kawune yayi kokarin soma magana cikin wani murya ta dakatar dashi da fadin kai mana shiru don Allah kome ya faru laifinkane . Da yar uwarka kazo nan neman sa,a kayi dace an karbama anyi a cikin sa,a amma ka bata komai da hannunka saboda son kai irin na yan adam daka sawa kanka a rayuwanka. Kaki yar uwarka kabi ra,ayin matarka duk da gargadin da mahaifiyana tayi maka a wancan lokacin akan yar uwarka da kake son cin amananta. Amma ka yarda ka,biyewa matarka kuka cutawa yar uwarka duk irin biyayyan da take maka kaida matarka amma kukai amfani da biyayyanta kuka cuta mata ba tare da sanin taba. Naso na taimaka tun abin nan bai kai haka ba amma shu,umar matarka ta hana hakan a lokacin don bata bar yar uwarka a banza ba ita da zurianta. Kai kanka kasani kasan irin yadda take duke kan wa yan nan mutane duk akan abin duniya kuke hakan duk da kusan cewa karshen hakan ba zai maku dadi ba nan gaba. Yanzu ba wanan ba kun zone akan dan uwaka dake fama da jikinsa ko habu ? Saita kada kai tana bata fuska kafin tace shi an riga da an sameshi saidai ba yadda akaso samun nasa ba. Don ansone ayi mashi karaf daya wanan karon saidai hakan bai samu ba saboda wani dalili kai haba kasani na fadama wanan yarinyar da ka aura tana da wani siri a tare da ita. Hakama ita wace ke tare da dan uwar naka naga kamar yar uwar matarkace ita tana da natukar kokari sosai don Allah ya kyauta zamata tare dashi matuka da komai ya jagule akansa wanan karon don Abin nasa yayi masa yawa gida ajefeshi haka wajen neman halak dinsa a jefasa, ga makiya yan hassada suyi masa yawa, haka kuma a gidan matansa basu barshi ba. Ta sake girgiza kai tana duban wanan faifai din gabanta data rike tana fadin yanzu ba lokacin wani bincie bane dole bakin rafi zamu a fara bada sadaka . Saidai idan karyan nan yaki tafiya ya tsaya a waje daya haka na nufin sadakar bai karbu ba ke nan saidai mu zurwa sarautan Allah ido gaskiya. Amma da zaran an saka wanan kwaryan ya tafi yabi ruwa insha Allahu wanan sadakan ya karbu ke nan don haka sadakan zai kasamce biyune a yanzu. Da wanda zamuyi don dan uwanka dake fama da lalura a yanzu sai kuma naku kaida sauran yan uwanka da a yanzu ba aikai gareku ba. Don haka dole muyi gagawan yin riga kafin akanku kamar yadda al,adan abin yake murya iyace ya katse matar da take fadin. Aah, Ikon Allah inda ranka kasha kallo dauda nan kuma ka kawo yar uwarka da zurian ta don son kai irin naku dauda ? Tsohuwa kiyi halkuri ayi wanan hadayan kafin komai ya kai ga jagulewa a yanzu daga baya mayi duk wanan bayanin daku a tsanake. Ta juya gun mama dubu tana fadin kece zaki saka komai a cikin kwaryan nan zaki saka da niyar fansan rayukan yayanki daga mutanen ruwa masu bada sa,a da yarda,,,,,,, Kallon juna sukayi tsakani mama da iya har habu sai matar tace shi yasan komai don shi ya dauki alkawarin hakan garemu tun farko. Dole mama ta mike ama fada mata duk wani abinda zatayi suka dauki kwaryan dake da abubuwa a cikinsa hardasu masa kosai alawa ayaba sukari da turmin zani zuwa bakin rafi . Tun bayan isarsune wajen dole mama dubu din ta taka zuwa ciki ruwan tana bin matar da kwaryan farko wanda zata fara sadakan dashi akan jafar din . Gaba dayansu gabasu na faduwa wajen son ayi abin cikin sa,a ba tare da an samu matsala ba matar ta karbi kwaryan ta fara jera kirari tana daga kwaryan sama tana saukewa . Suna tsaye suna kallon ikon Allah a gefenta can ta mikowa mama dubu tace tayi niyar ga sadaka ta kawo masu idan sune sanadin rike danta jafar tana rokon da su sakeshi ta biya sadakan da suke binta akanshi . Saidai yadda ta aje kwarya a saman ruwan ko alaman motsi baiyi ba hakan yasa gabansu ya fara faduwa cikin tashi hankali. Wanda hakan ke nufin cewa da alama jafar din yana da wuya wanan abin ya barshi hakan na nufin dai sai abinda ya fito daga Allah gareshi kuma. Anyi anyi kirari kwarya yaki matsawa daga inda aka ajeshi hakan yasa aka miko mata na sauran yaran nata wanda shima yake da nasa kalan tarkacen abin mamaki a na dorawa a saman ruwan kwaryan ya soma tafiya yana bin kabin ruwa da sauri. Gani hakan yasa habu dake tsaye gefe daya bakinsa dauke da addu,oinsa ya tako daga inda yake zuwa wajen kwarya farko da aka aje don jafar din ya cira shi ya daga yana fadin ka tafi kaima kamar dan uwanka ya dora saman ruwa suka bishi da kallon mamaki. Suna jin tausayin irin halin dayake ciki da har baisan abinda yakeyi ba a lokacin ciki yardan Allah sai kwaryan ya fara dan juyawa sannu a hankali saman ruwa ya soma tafiya shima . ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/17, 08:36] Buhainat: [3/18, 8:26 Yamma] Seenabu Makawa: Open this link to join my WhatsApp Community: https://chat.whatsapp.com/JeOQfGohQLdKTUlsWMqXoZ [3/18, 8:28 Yamma] Seenabu Makawa: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 6️⃣7️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Dan uwa murfin jallo inji manya wasu sukace rabin jiki kuma don hakan ne ya kasance ga habu lokaci guda don ganin kwaryan da ake nufi ta jafar taki motsi yasa ya dinga karanto addua da sunayen Allah mai girma sai gashi a fusace ya daga kwaryan ya tura ya fara tafiya saman ruwa cikin yardan ubangiji. Abin mamaki suke kallo daga iyayyen har mai maganin sun zubawa ikon Allah ido suna bi da kallo tun wanan kwaryan yana kokarin turjewa ya tsaya a waje daya har yakai ya fara dan tafiya da sauri sauri yana bin igiyar ruwan kamar yadda dayan kwaryan ya mike tsaye yabi ruwa suna kallo. Lai habu kakai shu,umin yaro iya ta fada daga gefenshi hakan yasa ya dan kallo iyan yana fadin komai zanyi akan dan uwana iya. Amma baka ganin kayi kasada da shiga hurumin daba naka ba habu iyan ta kara fada a hankali yayinda duk hankalinsu yake kan kwaren dake saman ruwan suna tafiya . Kaga wanan abin kamar rayuwace malam habu haka ruyuwan bawa yake a wajen ubangijin mu shi ciwo ba mutuwa bane wani lokaci. Wahala kawai bawa yake gudu da fitinar ciwo don sai kaga mai lafiya ya tafi ya bar mai jinya a kwance inda rabon mikewa sai majinyacin ya mike shi wanda yake tsaye yakai kwance. Kallonta iya tayi kallo dake nuna akwai magana ke nan ga wanan zancen nata bata kula ba tana surkullensu na yan bori har zuwa lokacin da ta dago garesu tana fadin da alama dai sadaka ya karbu ke nan sai dai ayi fatan Allah ya tsare. Akwai abubuwa da ya kamata ace kun sani tun wajen amsan maganin nan wanda nake ganin kai malam dauda ya sani a lokacin. Kawu dauda yana jin hakan ya gyara tsayuwanshi yana dan kame kame ta karbe da fadin baida matsala tun lokacin da abin ya damu maman mu ta sanar dani komai akan haka har zuwan da matarka tayi daga baya tana neman a bata aikin a mayar dashi wani nau,in sai daga bayane hakan ya damu maman mu kuma bayan tayi aikin abin ya koma yana damunta wanan yasa na fita neman ku don kwantacen da matarka tayi muna a lokacin . shi nayi amfani wajen nemanku nazo har zaria din a wajenta naji komai a cikin hikima don yadda najata a jikina sosai a lokacin. Naso ace kunzo lokacin da mahaifiyar mu take raye saidai hakan bai samu ba don kaddara ya riga fata a cikin lamarin. Kai yanzu ga yar uwarka bata san abinda kai da matarka kuke shiryawa akanta ba duk dadewan nan ya kamata ace ka fito fili a yanzu ka sanar da ita manufarka a kanka dakai da matarka. Me zai fada a yanzu ai gara kawai yayi shiru don hakan ma ai maganace don jin baida amfani a wajen mu yanzu tunda ko yanzu Allah ya baiyana muna nufinsu a kanmu. Ban taba zaton hakan ba yaya ko mutuwa nayi na taso akace kaine kayi min hakan akan zuri,ata zance kazafi akai maka don a shiga tsakanina dakai. Wai sai gashi da raina da lafiyata hakan ya faru yau a gabana yaya ka kasa mussa wanan zancen da aka dade ana fada min ina fadin karyane zalla zumuncine kawai a tsakanin mu. Ashe abin ba haka bane yadda na dauka kai a wajenka da wani manufa ka ke nuna min zumuncinka a kaina don kawai,,,, Kukane yaci karfin ta wanda yasa habu ya taso daga inda yake yazo ya rike mahaifiyar tasu da komai yake iya faruwa da ita a lokacin don yadda yanayinta ya nuna a lokacin kamar bata cikin hankalinta. Shima kawu dauda din sai fadi yake na dade da nadaman haka Dubu tun bayan dana fahinci cewa kamar yaran nan sun gano irin abinda Hafsatu ke izani inayi akansu din. Tundai ma shi Habu da har ya fara fitowa fili yana fada min magana a fakaice wanan yasa na fara neman mafita daga kaidin ita hafsatu na yanke shawaran in kara aure,,,, Daga baya ke nan dai dauda kaji kunya wallahi ka rasa wanda zaka zallunta sai yar uwarka akan abin duniya me yaran nan suka rageka dashi a matsayin ka na kawunsu ? Malam dauda kadai fadane amma hakan bashine nadamarka ba ko in fada a nan gaban kowa wanan abinda ka fada bashi bane nadamarka mai magani ta fada. Kinga idan abinda ya kawomu har an gama a barmu mu tafi don dan uwana dake can kwance ba lafiya munzo nan da sunan wunine don bamuzo da niyar kwana ba nan da zaria akwai nisa sosai don haka zamu koma yanzu . Ya fada yana kokarin mikewa tsaye don duk wanan bashine a gabanshi ba zancen dan uwansa shine ke zuciyarsa din yana ganin kamar wani abu zai iya samun jafar din kafin su dawo zaria a yadda suka barshi din. Ba yanzu ya shirya daukan mataki a gun kawu ba sai bayan komai ya lafa yake son su tunkari dan uwan mahaifiyarsu din da matarshi. Don tunda sukai waya da yaya Isah ya sanar mai halin da suke ciki asibiti da jafar din hankalinshi ya tashi yake ganin ai kamar baida rayuwane sun boye mashine kawai. Sai bayan sunyi nisa yake sanar dasu irin halin da akace Jafar din ya shiga bayansu wanan ya kara daga masu hankali sosai. ZARIA Tun bayan faruwan hakan muna dakin zaune nida mama da inna don ita umma ta koma gida don basu watsewa su bar gidan ba kowa sukace. Inda yaya isa ya gargada yan uwa yace su koma gida ayi masa addua tunda likitoci sunce ba zasu bar kowa ya shiga ba kuma dakin da yake kwance din. Bayan na idar da sallah magaribane inda nake zaune makure a cikin damuwa wayata dake cikin yar jakata ta dauki kara na dauko ina dubawa abin mamaki dan uwana Dagene ke kirana a lokacin. Na dauka murya ba dadi ina amsawa yake fadin yaya yaji muryata haka kamar banda lafiya ? Ban iya bashi amsa ba sai kukan dana fashe dashi lokaci guda a cikin harshen fulatanci nake masa bayanin halinda mijin nawa yake ciki. Wai tsaya Anini ko dai zancen mijinkine naji hardo da nayi da baffa dazun nan yake fada min yaji hardo ya bugowa baffa waya suna zancen don ya bashi wani makari da zai masa amfani dashi. Asalin maganin baffa ya dauke daga kakansu shi kadai kedashi a hannunsa yanzu nan dai yake fada min a ranan idan baffa ya fita yawon darensa zai shiga ya dauko min tun da safe zai shigo mota yazo zaria dashi . Naji dadin hakan sosai don nasan tunda yayi alkawari har in ya samu daman daukowa zai kawo din naja bakina nayi shiru don ba abinda zan fadawa wani bane zancen daya shafeni ni kadaine wanan saiko yar uwata. Karfe goma yaya Auwal yace na fito mu tafi su saukeni gida don zai mayar dasu mama da inna gida a lokacin ba zan iya rokonsa ya barni ba . Saidai furucin mamane yasa naji sanyi don ita ke fadin Auwal kubar yarinyar nan ta zauna kusa dashi don ko dazun daya rikice badon itaba bamu san yadda zamuyi ba. Taje dai ta shirya ta dawo nima zan tsaya a nan din tare da ita ya kasance ta samu mace a kusa da ita sai yaya Isah yace amma mama kinga,,,,,,, Abinda na fada ke nan isah kubar yarinyar nan a kusa da mijinta har in kuna skn ganin cigaban lamarin nan ga dan uwanku. Hakan da mama ta fada shine yayi sanadin zamana da ita a kusa da yaya din ko wani lokaci don mama irin matan nan ne masu tsare gida ga bada umurni ga iyalinsu wanan yasa take jan girmanta akoda yaushe. A can gidan su Jafar din kuma tun bayan barin su asibiti da suka isa gida Nusaiba ke ta kuka tana waya da yan uwanta tana fadin cewa an kita ana son hada mata kai yan uwan jafar sun tsaneta suna kinta. Da korafin yayi yawa uwar tace taba Asmau waya zasuyi magana shine Asmaun ke fada masu abinda ya faru uwar tayi masu fada dukkansu kamar yadda ta saba tace ai dole zasuce hakan tunda kuna nuna kamar baku damu da halinda yake ciki ba a yanzu. Ta yaya zaku tsaya karamar yarinyar har tazo ta fiku iya fallako ta karbe maku miji kuna gani ai ba sunce bane inda suke ganin kauna suke jin taushi tunda rayuwansa ake nema a yanzu koma meye ku bari gobe zamu shigo ai. Da haka suka samu ta hakkura don cewa tayi da zata dawo gida tunda an nuna mata kiyayya a nuna bata da amfani ga jafar din. Ranan sunyi shirin da suka jima basuyi ba a tsakanin su don sunyi zama na shawaran kan abinda zai fitar dasu daga kallon tuhuman da yan uwa suke masu din. Su mama basu dawo Zaria ba sai karfe biyu saura na dare ina zaune a dakin da hasken wayata ina karatu mama tana kwance a gefena suka shigo don basu nufi gida ba asibitin suka nufo kai tsaye . Jin an turo kofa yasa na dago kai ina duban kofan dakin sune dasu yaya suke shigowa hakan yasa na dan taba mama da barcin ba nisa yayi ba a lokacin ta tashi muna masu sannu da zuwa. Suka amsa da tambayan ya mai jikin aka basu amsa da saukin tun dai dazun din barci yakeyi a hakan yadda yake bai kara wani abuba kuma har wanan lokacin. Iya ta karaso tana fadin Allah ya baka lafiya jafaru ubangiji ya tada kafadan ka a cikin mu suna amsawa da amin kafin ta juya gun mu tana fadin Salamatu ashe kina nan mama ta amsa da ehh iya zuwa gidan ai baida amfani gara na tsaya a nan din tare dasu. Rahamatu kina zaune baki barci ba ke nan ta juyo kaina tana fadan hakan cikin nuna kulawa nan mama ta karba da fadin . Ina ai yar nan akwai kokari ko dazun din daya rikece itace tayi namijin kokari akansa kafin likitocin su iso tayi dubaran datse hakoran nasa da cokali daya taune harshen nasa ai duka don ba mai dabaran hakan acikin mu kowa ya rude. Nan tashiga rabtabo masu labarin yadda abin ya faru zaune habu yakai a gefen dan uwan nasa ya zuba mashi idanu yana kare masa kallo a cikin tausayi. Can ya juyo yace ko dan kokon daya dan karba yanzu ya daina sha ke nan ko mama tace ina ai tunda sukai mai alluran nan ya samu barci hakan nan daka ganshi yake tun dazun din. Saida kyat suka samu suka bar asibitin don mama data matsa masu suje gida su huta tunda muna nan asibitin mu hakan yasa suka tafi. Har iya dake son hutu a lokaci tabisu zuwa gidan yaya habu duk a nan suka kwana ranan sai kawu da suka sauke gidanshi har lokacin ya kasa furta komai a garesu. Tun da asuba na jona ruwa na gyarawa yaya jikinsa da taimakon mama na samu na tsabtace masa jikinsa muka saka mashi wasu kananan kaya sai ya fito dan few dashi don rama da yanayin jikinsa yayi. Nabi dakin na gyara na fesa kamshi da yaya Auwal ya sayo ayi amfani dashi na gyaro har ban dakin koda suka dawo daga sallah sun samu har nagama komai a lokacin. Lokacin kuma yaya habu yayi sammakon zuwa asibitin shima don duba dan uwan nasa daya kwana dashi a rai. Ásmau ce data kira layina tana tambayan ya mai jikin nake fada mata idan zasuzo suzo da koko don Allah ban jira me zatace ba na kashe wayan. Sai wajajen takwas suka shigo asibitin da yaransu mun gaisa lafiya suna muna ya mai jiki mama ta amsa da sauki nan rake fadin . Tunda kunzo sai ku kamawa yar uwarku taje ta huta ke Asmau saiki zauna dashi zuwa karfe biyu sai ita nusaiba ta karbe ki zuwa yamma don ita yar nan ta huta don batayi barci ba a jiyan. In yaso zuwa dare saita karbe ki atakaice dai mama ta raba muna wanan taggadaman a tsakanin mu ke nan kuma hakan ya zaunu saidai ina jin hakan na fara haraman zuwa gida don ina son dama gyara jikina robona da wanka tun da zan fito gida zuwa wajensu a jiyan . Ina saka hijjab nake jin suna zancen bashi kokon dasu da mama dubu na gama kimtsawa na dauko jakata ina fadin zan tafi sai anjima bisa ga umurnin mama duk suka juyo suna kallona zaki gidane naji mama dubu ta fada . Ehb zanje na dan watsa ruwane mama na bata amsa take fadin ibrahim yana kusane ya kaiki zan fita ko zan samu wanda zai saukeni na bata amsa sai naji tace min to indai babu kowa saiki dawo habu ya saukeki ko ? Nayi masu sai anjima na fita daga dakin cikin sanyin jiki cike da mamakin sanyi mama a kaina lokacin ina fita na hadu dasu anty Barakha da yan uwanta nan muka tsaya muka gaisa suna tambayan jikin dan uwan nasu. Muryan Asmau naji tana kirana hakan yasa muka isa tare dasu take fadin mama ke magana dani nashiga take fadin kada ki tafi ai ki tsaya abashi kunun nan don kece kikafi sanin yadda yake kamawa idan anbashi. Hakan yasa dole na kwabe hijjab dina na muka soma kamashi don mu dagoshi dole saida na dan hau gadon na rungumeshi duk sun zuba min ido na soma da kiran sunanshi a hankali ina mashi sannu. A lokacin su yaya habu suka karaso dakin suma sai yayi kamar ya bude idonsa ya kalleni nace ka daure ka dansha koko koda kadan ne don Allah yaya ? Wani irin ajiyan zuciya ya sauke lokaci guda duk hankalin kowa ya dawo kanshi da sauri ya habu ya karaso yana tambaya hankali tashe da yaya dai ? Murya a kare nake fadin ajiyan zuciya ya sauke na kallo Asmau da jikinta ke rawa nake fadin ta bani kunun ta miko min na kara fadin ka karba yaya don Allah kashe kada ka zauna da yunwa haka tunda bai shiga ta roban da ake baka din. Bskin nasa naga yana bukatan a kara wankewa hakan yasa na nuna mata ruwa ta miko min na diba a hannu ina dan wanke bakin nasa . Ya kara sauke ajiyan zuciya a hankali nake fadin ya taune halshesa ashe jiya har yaji ciwo a bakin muka gama na bashi kunun ya karba sosai kamar cibi biyar aka samu yasha ya habu yace in barshi hakana zan saukeshi a jikina yayi alaman a,a . Ita Asmau ke fadin kamar ya girgiza kai fa nace hakane ya habune yace ki zauna dashi haka yake nufi. Nan anty barakha ke fadin Allah sarki yasan itace ta rikeshi ke nan ya habu yace ya sani sosai idan tayi mai magana ai yana nuna ya ganeta. Ikon Allah ai dole inda zuciyarsa take ke nan dole ya shedata ai mama dubu ke fada hakan ta matso tana fadin sannu jafar ya jikin kai ya kara dagawa a cijin karfin hali. Suka shiga gaidashi daya baya duk daba amsawa yakeyi ba sun dai gaidashi din ne kawai irin na al,ada da akeyiwa mara lafiya. Yaron Asmaune aka shigo dashi yana rikici suyi lalshi yaki shiru mama ke fadin ta fita waje dashi. Hakan yasa na karbeshi daga inda nake zaune daidai fuskan uban na nuna mashi shi ina fadin ga baba yana gaida kai yaya sai kawai ya bude idanunsan tarr akan yaron . Da karfi saare ke fadin wallahi yaya ya bude idonsa hakan yasa duk suka matso garesa a cikin farin ciki sai kuma ya mayar da idonsa ya lumshe a hankali. A hankali ya habu ya leko yana fadin J ya jikin sai ya kara bude idon ya sauke ga dan uwan nasa ya sake sake lumshesu ya bude ya kafawa Habu din ido na wani dan lokaci. Likitocine suka shigo dakin suka sameshi a hakan sunji dadi sosai a yadda suka sameshi hakan yasa aka rage a dakin harni a lokacin na samu na fice na nufi gida. Ban dawo asibitin ba har yamma don saida nayi barci bayan nayi wanka na kwanta na samu barci sosai sam na manta da zancena da dan uwana Dage saida kira ya shigo min a wayata yana fada min gashi ya shigo zaria hakan yasa na tashi da sauri ina salati. Kwatace yayi min inda yake maigadi na tura yazo dashi tsamo tsamo don da ganinsa a tsorace yake saida ya hangoni tsaye kofan gidan mu ina dakon dawowansu hankalinsa ya kwanta. Nan falona muka zube na bashi abinci yaci yayi wanka saida akai sallah muka samu kebewa dashi ya soma yi min bayanin abinda yazo dashi din . Haka kuma ya sanar dani cewa sammako zaiyi ya koma washe gari don gida ba a san nan ya nufo ba yazo min da abubuwa masu amfani sosai. Nayi godiya nayi mai alheri iya abinda zan iya wanda yake ganin kamar na tsomashi a aljanna ne tare mukaje asibitin dashi da yaya habu dana kira nayi mai bayanin komai . A saibitin ma ya habu bai boye ba don yace hardon mune ya toroshi ya kawo muna maganin da za ayi amfani dashi ya fadawa yan uwansa haka tare suka koma zai kwana a wajensu dasafe ya sakashi motar farko ya koma gida suma sun mashi alheri ya tafi. Kuyi hakkuri din Allah ba yawa anty Samira gashi da fatan kinyi hakkuri da kanwarki hakana yanayin jikine ya kawo hakan. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/17, 08:36] Buhainat: [3/18, 8:26 Yamma] Seenabu Makawa: Open this link to join my WhatsApp Community: https://chat.whatsapp.com/JeOQfGohQLdKTUlsWMqXoZ [3/18, 8:28 Yamma] Seenabu Makawa: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 6️⃣8️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA bWANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Duk saurina ban manta da zancen maganin dana hada na ruwan dokin da Dange yayi min bayani ba a kwanaki bamu samu amfani dashi ba yayi wanan tafiyan daya dawo a cikin rashin lafiya. Rashin lafiyan daya zamowa kowa a cikin family na tashin hankali don ga mutum kwance sharkaf baida wani moriya ba umm,uuumm asalima baisan a hanlin da yake ciki ba na tsawon kwanaki. Za a iyacewa dai kamar ya shiga common ne ko kuma jinnu sun shafeshi kamar yadda hausawa kefada in mutum yashiga irin wanan halin da ba asan kansa ba. A iya binciken asibiti sunce su basuga wani abinda ke damunsa ba saidai suna hasashen ko kwakwalwansane ya tabu ko kuma ya bugu a kai hakan ya sameshi. Bayan hakan su basuga komai a tare dashi ba bayanin da sukaiwasu yaya Habu ke nan a karshe irin hakan wai amma zasu ajeshi acigaba da bincke ko za a gano inda matsalan yake. Jin hakan yasa hankula ya kara tashi sosai ga yan uwa kowa ya saduda a yanzu don irin hakan yana da wuya ace mutum ya mike sai yawancin rai da rabon mikewa din. Kowa kika gani fuska ba annuri don labari ya karade kowa ga abinda likitoci sukace game dashi din sai koke koke ke tashi tsakaninsu. A cikin irin hakan ne na karaso asibitin tunda na tunkaro naga yanayin fuskokinsu sai jikina yayi sanyi na rasa wanda zan tambaya meya faru dakin na nufa da sauri a zatona ko ya cikane na gansu a hakan . A yadda na barshi haka nayi arba dashi kwance shambal saman gadon ba motsi na gaidasu a tsatsaye na karasa bakin gadon ina kallon numfashinsa dake sauka wani iri. Muryan mama tudun wadace naji a gefena tana fadin yana nan ai a raye saidai lamarin nasame keta kata muni kamar dai wanan ciwon bana asibiti bane. Bana asibiti bane mama na fada ina juyawa wajenta rabin da take na sake gaida ita da wuni nakai tsugune cikin girmamawa muka gaisa na aje jakata a gefe daya inda nata yake . Ta cigaba da fadin ni lamarin nan yana ban tsoro dazun don yadda gaba daya yanayin jinyar tasa ya canza a yanzu yana sauyi da kamar iska ko hannu a lamarin. Binshi nayi da kallo a yanayin da yaken tacigaba da fadin ni a ganina kawai abar asibitin nan a koma gida dashi zaifi idan an koma sai a surka ayina gatgajiya dana asibitin. Abu daine da baka da iko a kansa da ina da ikon da zan fada aji dana bayar da shawara a kwasheshi zuwa gida ayi na gargaji yafi zaman asibitin nan da akeyi a cikin duhun kai. Ni tunda naga sun kwashi jiki sunyi tafiyan nan shekaran jiya nasan akwai inda suka tafi game da lamarin jikin nan nasa amma kin san ba fada muna kome ke akwai cokon lamarin zasuyi ba nidai abinda nagani kawai su kwasheshi a koma gida aje ayi na gargajiya zaifi wanan zaman da akeyi nan. Mikewa nayi daga inda nake tsugunne a kusa da mama din zuwa bakin gadon ina kare mashi kallo zakice ba Jafar din nan bane da kikeson karawa kallo duk ya fita hayacinshi. Ga kamsuba da suka fito mai a fuska yayi wani baki sai dogon hancinsa kawai zaki hango zaram bandashi ba wani abu daya rage a cikin jikinshi. Abin dai dana saba nayi mai addua donshi duk wani mosoyinsa zai mai a lokacin donshi yafi bukata garemu. Yayin da zuciyana yake wani irin halbawa a cikin fargaba da tashin hankali don gaba daya nikan na sallama a raina mun rasa yaya a wanan lokacin don gara wancan ciwon na baya yana a cikin hankalinsa wanan kam baisan wanda yazo ba baisan wanda ya tafi ba. Sai bayan tafiyansu mama dan yanzu dagani sai maman tudun wanda da iya muke kwana su yaya kwana biyu suna gidajensu amma basu barin asibitin sai wajajen karfe daya da wani abu na dare koshi sai iya ta matsa masu akan su tafi zasu wuce din. Iya na daga waje tana sallah bata shigo dakin ba tukun na na dubi mama a cikin karfin hali nace mama naso nayiwa yaya wankan magani a gwada a gani amma ina shakkun hakan da zanyi din. Kwana uku zanyi mai hakan amma sai abinda kikace shiyasa ban fada ba a gaban mutane ta yunkura ta mike zaune tana fadin idan zaki iya ki gwada a gani mana yar nan ai sauki ake nema ba wani abu ba dama kuma zaman hakan muke a nan din. Tana zaune tana kallona na hada komai sai naji ta mike tana fadin bari naje daga waje in tare tsohuwar nan kada ta shigo. Ta fice ta barni dashi a cikin karfin hali hakan kuwa na cude mai jiki da ruwan hadin maganin na kuma bashi ya sha sosai na mayar dashi ya kwanta a nan na kife a jikinsa ina kuka. Sai da mama taji shirun yai yawa ta leko tana fadin yayane har yanzu cikin karfin hali na dago ina fada mata angama. Sun shigo sun tsaya akanshi suna kare mashi kallo tare da fatan alheri a gareshi kafin suka juya suka samu wajen kwanciya don ni ban faye kwanciya ba ina zama a kujeran dake gefen gadon nasa koda yaushe. Tsawon kwana ukku muke a hakan dashi kullum da safe kafin su shigo zan shafa mai na bashi yasha bayan na gama mulke masa jiki ko ina da wann ruwan da doki yasha ya raga don ba karamin magani da alfanu yakewa mutum a jikinsa ba. Kamar yadda dage ya tabbatar min ni kuma na fadawasu mama da iya ance ka,idan maganin har in akwai alaman sauki kwana ukune kacal za ayi amfani dashi ga mutum aga alfanun maganin. Don mutum zai fara nuna wasu alamomi na jin sauki ko wani sauyi nadaga ciwon halin da kake ciki din Allah da ikonsa kuwa ranan na gama mashi amfani dashi na bashi yasha na zauna ina rufe goran nakai idona akanshi sai na ganshi ya kura min ido kuri yana kallona. Da sauri na cusa magani a cikin jakata na karasa wajensa ina kiran sunansa saidai bai amsa ba illa idon daya kafa min din baya kyaftawa hakan yaban tsoro na nufi su mama ina kiransu hankali tashe. Suka shigo dakin gurinsa suka nufo cikin kidimewa suna mai sallati da kabbaran iya ta karasa tana fadin Jafaru idon kane nan ? Sai ya dan lumshe idanuwan nasa kamar ya sauke ajiyan zuciya ya mayar ya rufe can kuma ya kara budewa yana kallon mama dake mashi sannu a lokacin. Ya Allah yadda ka nuna muna hakan ka tayar muna da kafadan yaron nan a cikin mu cikin salama da kudirinka ya dawo muna a hayacinsa ya koma walwala kamar kowa. Hawaye kawai ke fita min daga idanuwana na kurasa masa ido a cikin tausayi ni kaina a lokacin abin tausayi nake na sani amma duk bacin ran da bawa zai shiga matukar yana lafiya ya godewa Allah don na kwance ya fishi shiga tashin hankali. Ganin yadda ya kura min idanuwanshi din yasa iya min magana tana fadin ki daina wanan kukan ki karasa kusa dashi kiji ko wani abin yake so don ke yake kallo a yanzu din. Hakan na dan karasa gabanshi na dan rankwafa ina fadin yaya kana son wani abune da idon daya kifta min na gane yana nufin a,a sai ya maida idonsa ya rufe a hankali. Ya Allah kasa hakan saukine a gareka jafar Allah ya kaddara tashin ka a cikin yanayin nan ya baka ikon cin jarabawan nan da Allah ya aiko maka muka amsawa mama dake fadan hakan da amin. Munyi tsaye cirko cirko a kansa sai iyace take fadin ko abinci yake bukatane ni dai banyi magana ba don nasan yana da wuya idan hakanne. Saidai na karasa gaf da fuskanshi ina fadin a hado maka ruwan shayine zaka sha yaya sai naji iya tace keko dai ai basai kin tambayesa ba a dai hada mashi din a ga ko zai sha din. Shayi mai kauri na hada mashi don ya kama mashi cikin nasa na mikawa mama na kamoshi tare da ita muka bashi shayin. Alhamdullahi don yasha sosai ya maida idon sa ya rufe kuma alaman ya isheshi ba zai kara ba a haka mazan suka shigo suka same mu dashi ina zaune rike dashi na dan dagashi ya fada mai. Sunyi farin ciki da halin da suka sameshi sai mama ke fadin dama yar nan tace insha Allah maganin nan datake mashi kwanan nan ance da yardan Allah a cikin kwanaki uku za aga fa,idanshi gashi ko mun gani. Alama ya nuna wanan matsalan bata asibiti bace ke nan don haka gara in an kara ganin hasken hakan a mayar da yaron nan gida aje acigaba da neman na gargajiya a gani. Ya Auwal yace haka kowa ke fada shima Habu jiyan nan yake fadin ance wani zubin idan an rasa gane kan ciwo kawai mafita abar asibitin da mutum don shedanu da miyagu masu sihiri suna son hakan. A asibiti suke samun galaba don sunsan babu wani maganin tsari ko riga kafin da zai taresu a nan din sun daita maganganu a tsakaninsu har yan uwa suka taru asibitin kowa na murnan cigaban da aka fara gani akansa din. Lokacin tafiyana gida yayi don ganin matansa sun iso don ina kaucewa duk wani abinda zai iya kawo muna fitina a tsakanin mu a lokacin tun bayan rabon duty da mama tayi muna a kansa din. A haka kuma na kan dan samu daman leka school cikin damuwa da farga ban dai fahintar komai a hakan bayan attendees din da nake dauka kada karatun nawa ya samu cikasa da yawa a lokacin gashi zamu fara final exam din mu next week. Abu ya taru yai min yawa a kai ga zuwa asibiti ga karatu duk nabi na fige hankalina ba a kwance ba umma tazo kusan sau uku tana dubashi. Hakama mutanen abuja sunzo dubashi din don a gaskiya zance a yanzu akwai sauki sosai saidai na fahinci kamar hankalinsa ya dan gushe masa kuma bai magana bayan bude idon da yakeyi din . Gashi kusan satinsa hudu ke nan asibiti har wasu kwararun likito suka consultants aka dauko don shi suyi duba iya abinda zasu duba a kansa din magana dayace sun kasa gane ainihin abinda ke damunsa din. Exam din dana soma yasa sam banda lokaci ga yaya habu dasu mama sunyi min fada cewa na maida hankalina wajen exam din tunda akwai mutane a tare dashi. Amma matsala daya shine tunda ya fara dan budan idonsa din nan a ni kadai ake gane wani abin da yake bukata wani lokacin ko ban kusa zasu kirani in zo in duba masu shi din. A cikin hakan har exam dina yayi nisa sosai ga jinya ga kuma karatu wata rana ina zuwa mama ke sheda min cewa tana ganin za a bar asibitin nan don tayi masu bayanin cewa su gwada dagashi daga asibitin a gani kuma. Munyi hakan da ita kamar kwana biyu na dawo ina hanya maria take fada min cewa an bar asibitin da yaya an mayar dashi gida. Jin abin nayi wani iri sai kuma na barwa zuciyana komai nake tambayan yanzu yana ina ke nan tace yana gidanshi wajen matansa. Saidai ance a tsohon part dinsu da suka tashi aka ajeshi ba a kaishi ainihin part dinsa ba don kada a dameshi a nan din . Ajiyan zuciya na sauke ina fadin to yanzu yaya zanyi Yanda tace dani ya habu yace dole can zan koma nima mu kula dashi tare dasu saidai na dinga yi ina zagayen gidana. Sam banji dadin hakan ba a raina amma na bar zancen kamar yadda tace nayi sai idan sun nemini da maganan hakan na karaso gida a cikin bacin rai. Don kuka dai nayisa a yanzu har na daina saidai tunanen zuci kuma dana koma yi wanda yafi kuka wahala donshi yana cin jiki. Nashigo nayi wanka tare da alwala nafito ina kimtsawa yaya Habu yayi salma a gidan hakan yasa na fito daga dakina don ni kadaice yanzu a gidan Biba ta koma wajen uwarta tun faruwan al,amarin nan a can take yanzu saidai tana zuwa kwana bibiyu da yan uwanta su gyara muna gida suyi min wanki da sauran wasu aiyukan. Na fito muka gaisa na samu wuri na zauna yake fadin bayan ki dazun mun bar asibiti da jafar yana gida yanzu haka. Na dago kai na kalleshi yace ehh saboda mun yanke shawaran a mayar dashi gida acigaba da wanan na gargajiyan tunda duk munsan ciwonsa dai bana asibiti bane. Don haka zaman nasa a asibitin baida amfani banda zaman kashin kudin da akeyi kawai naso a kawo shi nan don zaifi jin dadi a nan din sai kuma nayi tunanen cewa mutane ba zasu gane hakan ba zasu dauka da wata manufa muka kawo shi nan din. So shiya dai na kaishi can aka bude masa part din mu a nan yake yanzu don haka nazo in fada maki dole kema din zaki koma can din a yanzu har muga abinda hali zaiyi. Idan ya kama din mu fita dashi wajene sai mu fita dashi din aje can a gwada sa,a kuma yanzu dai zuwa nayi na fada maki zuwa dare sai ki shirya zan dawo in daukeki nida maria mu kaiki can din . Hawaye na soma sakewa yake fadin kiyi hakkuri hakan jerabawan mune mu daku saidai shi dake kwance ya fimu shiga wani rayuwa. Don haka ki natsu banson kije ki biyewa Nusaiba kuna saida hali har mutane suyi Allah waddai da halin ku ki natsu kisa ido ga jinyar mijinki shine abinda zai kaiki gidan. Ya barni da zulumi ya tafi na rasa abin yi dole maria din na kira ta ban shawara na dauki dan abinda zanyi amfani dashi a can din tunda ba zaman dindindin zan tafi yi ba gidan. Hakan ya faru sunzo bayan sallah isha,i suka daukeni bayan yaya yayi gargadi ga maigadin mu na nan gidan sosai akan ya kula da gida kada ya bari kowa yazo gidan ya shiga idan bani bace na turoshi. Mun isa mun samu motoci biyu a gidan hakan na nufin akwai baki a ciki lokacin haka muka karasa ciki da sallama abokanshine suka zo daga abuja dubansa suka samu an sallamishi suka zo gidan. Suna zaune a falo dasu mama sai yaya ibrahim da zai zauna a na shima tare damu din suna bayani saiga ya habu don shine a gaba aka gaisa ya kara masu bayani halin da ake ciki nan suke fadin har idan za a fita dashi waje din ne don Allah su sani. Da zasu tafi suka kawo kudi mai yawa suka bayar Asmau suka mikawa akai masu godiya suka tafi. Sai bayan fitansune maman tudun wada ta juyo tana fadin kin iso yar nan sai kikaji shawara ya canza mun bar asibitin ? Ai nace habu ya kiraki ya sanar maki tun dazun din yace kina makaranta a lokacin idan kin dawo dai zai sameki. Ya habune ya shigo da kayana dan troler ne dana saka kayana a ciki sai sallaya da al,qura,n dina dana dauko yana shigowa ya nufi ainihin dakin da suka zauna da maria don gadon dakin da komai yana nan a dakin yadda suka barshi. Ya fito yake fadin dakin nan zaki zauna ke Rahama mama dubune tace a nan zata zauna ke nan kuma ? To me zata tsaya yi can mama tunda yana nan sai mama tudun wada ta karbe da fadin inba ita ba waya san yadda zaibi dashi haka yadda takeyi ai itace dai karfin jinyar nasa ko . Asmau ta miko kudin tana fadin habu ga kudin nan dasu Mansur suka bada ki bawa mama koda wani abinda za ayi nan koda yske mu gani nawane ya mika hannu ya karba daga hannunta. Dubu dari biyune yace ya juyo yana fadin ga dari da ashirin ku raba ku ukku sai wanan su mama kuma su raba ya mika mata sauran. Ina waje daya nida yar uwata a takure yake fadin tundazun barcin yakeyi ke nan mama tace ya bude idanunsa dazun kafin magariba nan dai ya zauna suna hira dasu mama din da iya data shigo . Saiba ce ta fara mikewa bayan ta sauke ajiyan zuciya tana fadin aina zata ko mu nan zamu iya jinyarsa ba sai wata tazo ba don me za a kawo Ramaah ace itace zatayi jinyarsa. Keko kikan fara abinki ke nan mama dubu ta fada tace a,a mama abinda ake muna a gidan nan yayi yawa ke nan dai mu bamu da amfani garshi yanzu sai Rahama ko ? Yanzu meye abin fada cikin zancen nan wanda ke fama da kansa a yanzu har kun ga wajen wani fitina a nan kuma ? Ba fitina bane mama akan so a raina muna wayaune wani lokaci aiba a gidan nan take dashi ba saita zauna gidanta tunda ba nan take ba. Don me za a mayar damu yan kallo ace wai itace tasan kan jinyar sa to ai sai mu barta dashi tundaan kawotane ita data iya ta kuka dashi. Umm,uhmm duk abinda zakuce saidai kuce amma ba inda yarinyar nan zata a yanzu tunda itama mijintane don haka wace bata hakkuri ga hanya nan mama ta fada. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/17, 08:36] Buhainat: [3/18, 8:26 Yamma] Seenabu Makawa: Open this link to join my WhatsApp Community: https://chat.whatsapp.com/JeOQfGohQLdKTUlsWMqXoZ [3/18, 8:28 Yamma] Seenabu Makawa: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 6️⃣9️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Kasamcewar manya a wurin hakan yasa na rakube gefe daya kokai ban dago na kalleta ba mama ke fada da ita sosai hakan yakai ga tace da iya . Lamarin yarinyar nan dole in kasance a gidan nan tare dasu don abin nata ba hankali sam a cikinsa . Ga yaron nan kwance amma yarinyar nan bata saduda ba sai banzan haukan kishi da take kokarin nunawa mutane ina ita din dai matarshice ko ? Ko har da hakan baki yarda dashi ba na taba ganin wanan rashin hankali wanan ba kishi bane haukane ai har yaushe mijiki yana kwance haka sharkaf a hannun Allah kika samu bakin kishi ? Koda yake bata da laifi laifin Dubuce dake kama mata duk abinda tayi yarinyar ko yar gidan uban waye aini bata kai min hakan ba na rasa meke damun Dubu akan wanan yar ? Irin haka ai dole ta dauka kowa baida daraja a nan tayaya zan zauna matan dana tana wanan iskancin a gabana ban dauki mataki ba ? Har idan an barki dashi din uwar me zaki tsinana masa a nan din banda fitinan da kika saba don kinga Dubu tana kama maki kafan iskanci. Mama ba sai kin tanka mata ba ai ku barta muga abinda zatayi din a nan Rahama zata zauna har zuwa lokacin da Allah zai bashi lafiya to ai shike nan mama ta kara fada. Da farko banyi niyar zuwa dakin da kayana suke ba don wata zuciya dake dibaba akan na koma gidana kawai in zauna yafi min sauki da zama nan tare dasu din da zanyi. Sai kuma nayi tunanen idan nayi hakan ban kyautawa yaya habu dasu mama din ba wanan yasa naja bakina nayi shiru saida aka rage a falon na shiga dakin komai a gyare yake tsab a dakin. Sai yar jakata dake saman gado aje na dauka na bude wardrobe na saka a ciki na shiga bandakin nayi akwala na fito sallah nafila nayi na roki Allah ubangiji ya tsare ya kareni daga duk wani fitina daka iya tasowa a gidan. Muryan mama dake kirana a falon yasa na fito take fadin zoki gyara muna wajen kwanciya ita wanan mai sababin da a haka zata barmu mu kwana a zaune ke nan ? Na gyara masu shimfida don a kasa sukace zasu kwana ni kuma na zauna a saman dogon kujeran da aka bari a falon don zama don an kwashe sauran kujerun falon ankai ta bayan ginan . Asmau ce ta fara shigowa da yaran ta ta zauna an dan jima kuma saiga saiba din ba wanda yayi magana don kowa ya gane manufarsu a nan zamu kwana dukkan mu dasu ke nan abindai ba tsari gaskiya. Ni dama ace rabawa akayi akan duk ranan da girki ya dawo kaina sai inzo nayi aikin da zanyi in koma amma ba ace in dawo nan din in zauna haka a tsakaninsu ba. Na dan jima a zaune na mike zuwa dakin bancewa kowa komai ba na kwanta don duk a gajiye nake addua nayi na lumshe idona ina tunanen duniya. A hakan barci ya daukeni ban sani ba barci ko sosai nayi don ban falka ba sai tsakiyan dare sosai da fitsari ya tayar dani dana kewaya na dauro alwala na fito. Ina sallah nake jin muryansu a falon sama sama hakan baisa na fito ba don ina son kama kaina don gudun zargin kishi . Har yakai ina jin muryoyin nasu sosai hakan yasa na daure nafito don na fahinci akwai matsala a lokacin shina sama yanata kwara amai daga kwancen da yaken wani irin bakin amai kamar an wanke bayan tukunya ga yawan yunkurin da yakeyi din sai ya baki tausayi don da gani cikin wahala yake zuboshi. Daki kamashi ya dago mama ta fada saita juyo ta dan dubi mama din tana fadin ni yaya zanyi in kamashi haka mama ? Ke yar nan amma baki da kunya dazun nan kike fada akan wata tazo ta taimaka yanzu kuma kice ke baki san ya zaki kamashi ba ? Duk yadda zaki kama ai kin sani tunda wace ke iyawan kin yakinceta da zuwa kusa dashi din yanzu ki dagoshi kada ya sarke don Allah ? Tayi kamar zata dagoshi din sai kuma ta fasa ta juyo gun mama din tana fadin sai wani ya taimaka min hakan yasa mama tashi ta kamashi a hannunta ya karasa aman saida ya gama ta wanke mashi bakinsa. Washegari kuma dai haka mama tasata gaba akab tayi mai wankan magani din a wahalce ta karasa kwana biyun ta sai gashi wai ta kwanta bata da lafiya tunkan lokacin ta ya kare Asmau ta karbeta din . Dole mama tasa na kama don Asmau ko wahalan goyo ya isheta haka dai ake rayuwan a jigirce don kowa mama bata bari ba a cikin mu wanan zaman sai gashi an daina zuwa kwanan da aka fara saidai wace zata karbeshi itace zata shigo koshi na dolene nikan da rana bani wuni dasu ina wajen exam dina . Wani lokaci kona fito da wuri zan wuce can gidana in huta sai yamma zan dawo sun wahala lokacin don mama zaune suke suna bada command kuma dole ayi din . A hakan na gama exam din na a wahalce abin farun ciki amma yazo min da rashin walwala don ba wani farin cikin da nayi da hakan asalima nasan dai faduwa zanyi ga jerabawan nan don banyi karatu ba . Dole na mayar da hankali gun jinyar yaya don yadda ko ganina yayi na gitta ya kafawa wurin ido ke nan bai kawarwa sai idan ya daina ganina . Don a yanzu yana gani saidai ba magana ba kuma wani motsi jikinsa a sake yake kamar jikin ya mutu nakan kebe in samu wuri inyi kuka mai isata in fito. Tun dai ranan da Saare da Saiba sukai min habaici a cikin magana da Saiba ke fadin kwadayin wasu baiyi rana ba don an kare a wahala. A dama ai ance kuda wajen kwadayi yake mutuwa wanan kudan da alama kan a kwadayin za a mutu don an fada ruwa tsundum . Kudaje dai don ba kuda bane kawai mai kwadayi akwai sauro mai dafi yasha jinin na tare dashi acan ake makeshi wajen kwadayinsa . Wanda bai ko fara allon sa ba balle ya biya shikewa mai sauka shagube ai gara da wanda ya sauke yafi wanda bai gwada saukan ba. Ai Gara da kudan ya san dadin kwadayi don dai ya lasa din koda pdll Qwya mutu, don ba duka kuda bane suke mutuwa a wajen kwadayi. Balle shi wanda ko masunsuni bashi da yaje zagin mai kamshi,daji bai ga ma cin wuta balle aiwa kututure barka da arziki. Me kike nufi da hakan amsan zancen ku na baki indai kwadayi ya shigo dani gidan dan uwanki ai gara dani na lasa keko dako gidan da zaki baki sani ba fa ? Kina nufin bata aure ke nan kome duk yadda kikace inma haka kuka dauka don ba wace zatace cas bance da ita kule ba a cikin ku. Salatin da Anty barakha ta saka yasa mu kallon kofa ta karaso tana fadin wanan wani irin rashin hankalone mijin ku na kwance haka a wani hali kuke haka a gabanshi don Allah ? Anty yarinyar nan yar rainin wayauce daga muna magana da ta sako muna baki a zancen mu tana son fadawa mutane maganan banza don tana ganin yanzu daidai take da kowa a gidan nan ? Haba dai kamar ya daidai take da kowa dama ai daidai taken da kowa tunda itama aure take kamar kowa a cikin gidan za ace ba zatayi magana ba kuma idan ya shafeta ? To shike nan dama kuke nuna mata hakan shiyasa take kokarin dagawa mutane kai bar ganin a kwanaki kin shanmace mu kina ganin kamar kinci galabane a kan mu lokacin ? Ko zaku gwadane a yanzu ko zaku rama duk macen datace zata sakani gaba a gidan nan mu zuba da ita ban shiga tsabgan kowa a cikin ku ba balle mace tace zata fada min magana na kyaleta ? Abinda kowan ku ke takama dashi shine miji nima ina takama dashi a yanzu don haka kikai min ba daidai ba sai dai muji zafin a tare dake wallahi. Ramaah ki kyale zancen nan ku duba bawan Allah nan a kwance a tsamanin ku baya jin abinda kukeyi ne don baya iya fadane kawai amma yanzu yaya yana fahintar komai da akeyi gabansa. Anty Salima idan kwadayi yasa na auri yaya itama kwadayinne yasa ta auri mijin kawarta ai don ta fini zalama tunda ita tanace saida ta aureshi . Dani dake waye makwadaicin a yanzu ciwo kuma Allah ne ya dora mashi shi kuma zai yaye mashi aduk lokacin da yaga daman hakan gareshi ita kuma Saare rashin sanin zafin dan uwanta yasa har take furta hakan gareni a yanzu. Idan fitsari banzane kaza tayi mana aiko ida nufi bajintane ga mai rabo aurena da dan uwanki nufin Allah ne a garemu mu biyun duka inma cutane ni kuka cuta da mugun nufinku a kaina daya koma min hakan a yanzu. Don haka ni ban raina kyauta da baiwan da Allah yai min na matsayin mata ga yaya ba duk da halin da yake ciki a yanzu kuwa. Lafiyanshi najawa ba abin duniyan dayake tsone maku ido ba don ban taba saka abin duniya a raina ba aure nayi da yaya na tsakani da Allah ba don komai ba iyauyena sun amince dashi a gareni a matsayin miji nima na amince da hakan don bansan baiwan da Allah yai min na dalilin hakan ba ? Ku dake ganin kwadayi ya kawoni na aureshi yau gashi ya fada jinya a halin rai kwakwai ku hakan yaiwa dadi har kuka fada baki sake don ba Allah a zuciyarku. Haba don Allah ina wanan zance ya fito haka kuma lafiyan ku kalau kuwa muna da mutum haka a gaban mu har kuka samu wajen fitina haka don Allah ? Asmauce take fadan hakan a cikin zafin rai na juya gateta a zafafe ina fadin anty Asmau matukar Nusaiba bata rike girmanta a kaina ba nima ba zan taba girmamata a idona ba har ita da Saratu zasu zauna suna sakar min magana don ina tsoron su in kyalesu niba irin wace zata zauna kiwa abinda ranki yake so bane. Ya isa hakan tunda sunyi shiru kadama ta bari don Allah taci gaba tunda ita tafi kowa baki dama dan kauye ai bai iya wayewa ba aka ce . Allah sarki dadin abin kowa asalinsa kauyene abin bukata shine ilimi koda yake ba abin mamaki bane don kince hakan tunda baku tsaya kun ilimantu ba dole kuyi halin marasa hankali. Wanan maganan dana fada shiya harzuka su muka koma cacan baki da karfi dasu har mutanen gida suka farga da abinda ke faruwa a lokacin . Anyi daidai maman tudun wada ta dawo suka shigo suna salati da tambayan meke faruwa nan suka so juya zancen da cewa nice na jawo fitinan nan mama take fadin. Assha Rahama ina ganin ki mai hankali ya kuma haka a gaban mara lafiya kuke jidali haka cikin rashin hankali nan nima na mayar masu da yadda suka tsokaleni na kasa hakkuri. Tir da halin ki Saratu halin nan naki baiyi ba wallahi ko dai me kikayi Jafaru dan uwankine na jini baki kuma da kamar shi yarinyar nan kowa ya sani tana iya bakin kokarin ta wajen kawar da kanta ga duk wani fitina ga zancen nan. Amma saida kuka san hanyar da kuka bi akaji bakin ku haka hatta kayan amfani ina kule ke Nusaiba kwashe abinki kikeyi don kada tayi amfani dashi saida ta sayo nata ta aje a nan . To tsaya kuji wallahi daga yau tunda ciwon yaron nan ba damuwanku, yayi ba gaba dayan ku banda shigowa gaisuwa ku duba shi kada wace ta kara zama a wajen nan tunda ba damuwa da ciwon nasa kukayi ba. Na dauka abinku na lokacine zaku saduda ku natsu ta dalilin wanan abin daya samu yaron nan sai gashi rashin hankalin ku yafi haka ashe. Ke kuma ki koma can gidan ki idan kinso kizo ki dubashi ki koma kullum inma ba zaki zo ba dai kiyi zamanki a dakinki ba sai kinzo ba. Mama dubu ce ke fada cikin bacin rai damu duka ina yunkurin mikewa naji dayan maman tana fadin ai idan wanan yar mai kulan ta barmu zance ya baci don ko gyaran wajen nan da take wuni yi a kullum ya ishemu balle irin dawainiyar da takeyi da yaron nan . Ba wanu zancen raba kwana tunda rabon baida amfani mu dake nan da ita zamuyi ita su kuma da rana su dubashi dama ba yau ba na jima ina son yin wanan maganan. Don da gaiya za a shigo a bata wajen nan sai a barta da gyaransa ni abinku yana daure min kai yau ko auren kiyayya kukayi da yaron nan ai kwa tausaya masa halin nan da yake ciki haka ? Ai wa yan nan banjin zasu canza halinsu don na dade da fahintar hakan garesu ba kurciya bane ba kishi bane kawai dai rashin hankaline ke damun yaran nan iya ta fada. Tun wancan ciwon nasa na farko na dade da fahintar hakan tun karkice wanan Nusaiba sam kwakwalwanta baya ja karatunsu da suke kurin sunyi baida amfani a wajensu . Yau yaron nan koba mijinsu bane suke ganinsa a wanan halin ai duk mai hankali zai kara tsoron ubangijinsa ga hakan amma sam babu wanan a garesu sai sha,anin gabansu sukeyi cikin jin dadi da walwala kamar babu fitina irin haka a gabansu. Ku in kuna da hankali abin bakin ciki da tashin hankalin babba ya sameku a yanzu don bamu kadai wanan abin ya shafa inma kuna ganin mune da hasaran hakan kuje kuyi tunane kun fimu hasara kuda yake mijin ku. Ba kamar ke Nusaiban nan da wanan sakariyan mara hankali Saratu wace bata san ciwon kanta ba ban taba ji ko ganin dan uwan dakewa dan uwansa wanan halin da sunan so ba . Idan kinayi don wani manufane na zuciyar ki saiki matsa kiyi tayi dan uwankine dai jafaru kafin kisan Nusaiban nan Jafar kika taso kika sani ta dalilin shi kuma kika san Nusaiban . Kuka saratun ta fara sosai amma mama bata saurara mata ba daga mu har mama Dubu harma Salima duk mama din ta hada ta zagemu tas iya na tayata. Wanan ne dalilin da aka daina robon kwanan da akeyi din inda mama ta kafa dokan cewa sai su shigo su dubashi da rana zuwa goman dare bata bukatan ganin kowa a part din kuma. Daga wanan ranan komai ya sauya haka shima mai jikin a dan ganin sauki sosai ga lamarin nasa don dai yanzu alaman sauki yana baiyana a gareshi . Matsalan dai shine har zuwa yanzu din bai magana ba kuma motsi zai daiyi alaman yana son abu da idanu . Masu magani kuma kasuwan su ya bude a dauko wanan yayi bajintarshi wani yazo abu dayane ban fasa yi mashi amfani da maganin gidan mu ba din wanda daga iya sai maman tudu suka sani sai kuma ya habu da mahaifiyarsu. Kawuma yana zuwa dubanshi sai dai yadda iya kan zage tana nuna masa bacin rai yasa ya daina zuwa sosai yanzu din don ko yazo daga waje yake tsayawa wani lokacin bai shigowa. A cikin hakane wata rana ya habu ya shigo yana fadawa iyayyen nasa matsalan da aka samu da dukiyan yaya din dake can ikko . Ida yace zaije da kansa ya gano halin da ake ciki duk da bawai yasan komai bane akan dukiyan nasa amma dai zaije da kansa shida yaya Auwal zasuyi tafiyan sai wani abokin shi jafar din. Sun je din sai dai basu gane komai ba don da alama kamar dai dukiyan na shirin salwanta sun dawo a cikin bacin rai suna bayani ga iyayyen nasu kan abinda sukaje suka sama a can din. Wanan ya kawo cecekuce ga yan uwa inda wasu ke ganin kodai ya habu yabi bayane ya karbe dukiyan ba da sanin kowa ba. Wanan tsegumin daga yan uwansu na dakinsu ya fara fitowa har maganan ya dawo kunnen iyayyensu ranan maman tudu tayi fada sosai inda taketa ta,alka laifin hakan ga mama akan duk ita tayi sake da har hakan ke faruwa. Hakan yasa ya habu din yayi fushin zuciya yake fadin har na nan arewa da yake kulan mashi dasu zai dawo da dukiyan a tara a waje daya. Ana cikin haka Allah ya jefo Yazid a wani dare ya iso zaria dashi da iyalinshi ni dai ina zaune ina murza mashi magani a kafa naji ihu a cikin gida. Saida na saurara nagane ba fada bane wai ashe murnan zuwansune sukeyi saigashi anzo fadawa iya zuwan nasa iyan ta fita ta bar mu dagani sai mama tudu dashi. Ki natsu ki kara mayar da hankalin ki kinji yar nan insha Allahu ladan ki yana ga Allah shine kadai zai saka maki da alherinsa Allah ya tayar da kafadan mijinku lafiya. Nagane dani take yasa na amsa da amin tacigaba da fadin a kullun nikan ina gani sauki a cikin lamarin yaron nan kibar wa yan can marasa hankalin suje suyi ta gulma da zasuyi iya ka su zageni shine kawai amma ni ina da hankali ba zan bari a batawa yaron nan maganin saba. Ba tauyeki nayi na dora maki laluran nan ke kadai ba nasan kece kadai zaki masa abu tsakani da Allah uwarsa ma ta sani amma tana jin tsoron magana yasa na ari bakinta nayi hakan. Sallaman bakin nasune ya katse mata maganan take masu sannu da zuwa sau daya na dago kai na dubesu na mayar da hankali wajen abinda nake masa. Ya karaso yana fadin ya subbahanal dan uwa kaine a cikin wanan halin innalillahi wa inna alaihim raji,un maman tudu take fadin ai kaga sauki a yanzu yazid. Nan na juyo ina mashi sannu da zuwa ya amsa har lokacin hankalinsa yana ga dan uwansa dake kwance sambal a saman katifa Suna da matukar kama da yaya habu har kamar tasu ma ya baci don sai kace ko tagwayenesu da yaran nasa biyu sai matarsa da gabinta irin bakaken larabawan nan na sudan akwai kyau sosai gareta gaskiya. A nan dai muka gaisa da ita din don itama hankalinta na kan dan uwan mijin nata dake kwance nagama na gyara wurin na kwashe kayan zuwan kitchen . Nafito na samu iya ta dawo falon suna kara gaisawa yana zaune daidai satin kan dan uwan nasa dake kwance . Naji yana tambayab koya ganesu ita mama din ke fadin ya gane ka baka ga yana kallon ka ba yana murmushi. Wanan matarshi ce yake tambaya mama take bashi amsa da itace matarshi ta ukku sauran fa ya tambaya take fadin suna part dinsu. Zasu shigo yanzu tunda sunji kazo yake tambayab yanzu wani mataki ake ciki dashine mama munyi waya da habu yace min yana kaduna tun safe. To yazid matakin ke nan mu zubawa sarautan Allah ido kome Allah yayi daidaine don asibitin da kansu sun bamu shawaran agwada na gargajiya a gani suna zuwa kuma nan gida ana dubashi ko wani lokaci halin da muke ciki ke nan a yanzu. Wa iyazu billah ya fada yana girgiza kai ya mayar da kallonshi ga dan uwansa a lokacin ne matan yaya jafar din suka shigo yi masu sannu da zuwa ita Saiba ke fadin ashe kuna hanya bamu sani ba ? Yace mun taso tun shekaran jiya yau muka taso sai yau muka samu karasowa sannun mu da wanan halin da dan uwa ya shiga ciki suka amsa da sannun mu dai din . Kalman data fito a bakinsa shine shi kawu din yana zuwa dubab shi har yanzu iya ko kun hanashi zuwa don in ina nan ba zaizo ba ? ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/17, 08:36] Buhainat: [3/18, 8:26 Yamma] Seenabu Makawa: Open this link to join my WhatsApp Community: https://chat.whatsapp.com/JeOQfGohQLdKTUlsWMqXoZ [3/18, 8:28 Yamma] Seenabu Makawa: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 7️⃣0️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Da zafinsa ya dawo kasan ba irin bakuntan nan wai ya dade baya gida din nan sam shi baiyi hakan ba da ganinsama karatu ya hudashi sosai magana kadan zaice Allah yace Annabi yace yanzune zai katse mutum shi ba ruwanshi. Iyaka dasu gaisu idan sun shigo ban dogon motsi ballema yasan dani a gidan har kishiyoyina duk sun kama kansu dashi suma. Kannesu ma sun kama balle mu din yana da kwana biyu da zuwa yayiwa Saratu tas a gaban kowa yake fadin tayi hankali yana da labarin komai akanta fa don haka ta shiga taitayinta dashi. Akan zancen abincine da yace matarshi bata cin tuwo kada a kawo masu sai saratu din tace ita din yar gidan uban waye ta tashi ta girka mana da kanta ita tuwo mama tace tayi shi kuma zatayi ta dafa ta kai masu.. Shine ya biyota har part din da abincin ya kwashi fadanshi yace kuma ta tashi ta girka masu wani a cikin lokaci dole ta tashi ta dafa masu din kamar yadda yace din. Ta kuma kawo bai kyaleta ba nan ya hau fada yana fadin zaman me sukeyi a gida haka tsawon lokacin basuyi aure ba sai shiga maganan manya da takeyi tana hada mutane fada. Hakan yasa zuwansa yai min dadi don kwana biyu bakijin motsin yar iska don kamar bata gidan ma zakice saboda ta natsu sosai a yanzu saina gane ba shiri a tsakaninsu kenan ashe ? Ranan dayayi wani shigo ya samu ina gyaran part din nagaidashi da wuni nacigaba da aikina ina jin yana tambayan mama wai ni kadaice ke jinyar dan uwansu. Mama ta nisa tana fadin kaidai fadi dan nan aini abin yafi karfin ganina yanzu nan dai ta zauna tana koro mashi labarin abubuwa da suka faru da farko. Sai kada kai yake faman yi yana acting a cikin mama kafin ya dan gyara zama yana fadi yanzu da wanan halin yake zaune dasu mama ? Tayi dan murmushi tana fadin to yaya zaiyi Yazid tunda mamanku tana hanashi daukan mataki yayi wani shu,umin murmushi ya gyara zamanshi yana fadin. Wanan Asmau tafi ban mamaki har da ita cikin wanan shirmen waiko tsoron kawar nata take ji da har ta yarda ta aure mata miji ? To za,ace dama dai ita din za ace tunda yanzu bata yarda da iskancin wanan dayan da suka hada kai da saratu suke iskanci ni in anbarni sai ince duk asiri tayi masu da basu ganin laifinta. Na rasa me Jafar ya gani a jikin yarinyar nan tun farko daya leke mata a lokacin sam zuciyana bai yarda da wanan yarinyar ba dama. Shigowan iya tare da matan kawu part din ya katse masu hiransu dashi sun gaisa da mama yana zaune ko kallonsu baiyi ba sai mama hafsatuce cikin karfin hali take fadin sannu yazidu anzo lafiya kwanaki munzo gaisheku da zuwa bamu sameku ba ance kunje bauchi kaida habu ? Ehh ai gara da baku sameni ba ko yanzun ma ba zaki taba samuna ba kiyo sabon shirinkine kikazo kaina kuma ? Basu mama ba harni dake shirin shigewa daki saidana juyo ina dubansa cikin dakewa ya mike tsaye yana fadin banga dalilin da zaku bar mai mugun nufi tana shigowa nan ba asalima gidan nan gaba daya ya kamata matar nan ta daina shigowa. Wani tsawa mama dubu tayi mai tare da ambatab sunab shi tana fadin kai Yazid kanka daya kuwa matar kawun naka kake fadawa wanan magana haka ? Mama don tana matar kawuna ba zan fadi gaskiya a kanta ba matar dake da mugun nufi akan mu kun sani kuma kuka barta tana shigo maku gida haka ? Ko Allah yace mu nisanci makiyan mu idan mun gansu yasa kai ya fita sai hafsatun ta fara salati tana kuka tana fadin . Ni wanan yaron ya kira da muguwa me yake nufi nice na dorawa jafar wanan laluran kome ? Iya ta amsa da fadin ,Yanzu ai gashi can baiyi nisa ba sai kije ki tambayesa ai hansatu mukan ina muka sani tunda bamu shiga zuciyarki mun gani ba ? Ba a gane mugu a goshi amma ana gane gaskiyan kowa a fuska don kowa na nuna shi nagarine ako wani lokaci kuka ta dan fara tana fadin . Zargina akeyi kan Jafaru kome iya haba shiyasa ashe duk nazo gaidashi sai a nuna min ba zan samu ganinsa ba ko ace min yana barci ko kuma ana mashi wani abu ashe ana zarginane da maita ? A,a haaa mukan bamu kiraki da manya ba amma koma meye kin sani ai koda yake shi maita bawai saika kama kurwa bane kake maye ko mugunta ai maitane shima. Da kyat mama ta samu hafsatun ta fita daga part din banyan mama tayi ta bata baki tana tausanta akan koma meye ba yadda take nufi suke nufi da itaba dole akwaidai abinda. Mama dubu dai tana zaune ta kasa cewa komai akan hakan nima ina tsaye daga kofa nakasa shiga dakin da zanyi a lokacin sai bayan fitansune mama din ta mike ta bisu. Iya ke fadin haka kawai yaron nan yayi min daidai daya fito mata fili da mugun nufinta ta dauka ba asan me take ciki bane ta kwaso kafa don bata da kunya zuwa munafunci. Wai iya hafsatun ta hurhurane yanzu maman tudu ke tambayan iya din cikin bacin rai iyan ke fadi ko maita take ai ba a mussu tunda kwadayi kekai mutane ga halaka yanzu. Hakanane fa idan kafaye saka abin duniya a rai sai ka tsunci kanka ga mahalaka yanzu mutane da yawa haka ke faruwa dasu ai mama ta fada ta kare da Allah ya kyauta . Ni dama naso nace bafa kowa ya kamata yana shigowa part din nan ban ganin yaron nan tunda muna ganin sauki a cikin lamarin nan. Yakama ace saina gida sosai zai dinga ganinsa a yanzu mutane basu da kyau kana tufkane ana maka walwala don haka kada kuga laifina a yanzu matakin da zan dauka don shigowa wajensa inma son samune zan daukeshi zuwa wanan dakin da matarshi ke kwana ya koma can din sai wanda aka yarda dashine kadai zai shiga wajensa. Barin shi falon nan hankalina ya daga sosai ina take tazo ta gyara dakin a mayar dashi cikibinyaso mu muyi amfani da dayan dakin shike nan aga abinda Allah zaiyi kuma. Tun wanan ranan aka dauke yaya a falon zuwa dakin wanda hakan yayi min dadi sosai don Allah ya gani zamanshi a falo sam bai min ba dama don ba dama nayi masa wani abin idon tsofin yana kanmu saidai yayi ta faman bin na da kallo duk inda na gilma da idanu. Haka kuma duk wanda yazo iyakansa falo yanzu ba kowane suke yarda ya shiga wajensa ba sai su shakikyansa kadai sukan shiga su jima a ciki wani lokacin tare dashi ni kuma in samu barci koyin wani abin. Na samu daman zama dashi a yanzu nayi maganan da zan mai duk daba amsa min yake iya yiba haka dai zai kafeni da idanuwansa . Bani kadai ba dukkan mu matanshi muna shiga gunshi mu kebe dashi na dan wani lokaci za,a zauna nan tare dashi koda barci yakeyi saina fahinci wanan tsarin na mama bani kadai yaiwa dadi ba ashe yanzu. Abin dana fara kula wata rana ina zaune da dare bayan nagama shafa mashi magani zamu kwanta sai kawai tunane ya dibeni sai kuka na fada jikinsa in kuka a hankali kamar a mafalki naji hannunsa na kadawa a hankali yana dagasu zuwa kaina. Innalillahi na samu ambata tare da katse kukan da nakeyi ina binsa da kallo amma ya kasa abinda yake son yi din don hannun nasa ya kasa daguwa yadda yaso din. Naja bakina nayi shiru daidai a yanzu nakan kama yatsunsa din ina masa massage dinsa har dana kafafu da duk inda jijiyansa suke kafin mu kwanta . Cikin irin haka ranan banyi aune ba su mama tare dasu yaya Habu da sukai tafiya suka shigo suka sameni ina masa hakan. Muryan Yazid ne ke fadin gaskiya wanan kina da fasaha sosai nayi wanan tunanen ince ko za a dinga dan masa hakan sai gashi ashe kina masa hakan zai taimaka sosai wajen karfin jikin insha Allah. Ni dai ganin sun shigo yasa na daina na sakeshi na koma gefe na rakube can dai na mike na dawo falo na samu iya zaune ta idar da sallah muka dan fara hira jefi jefi. Hiran dai bai wuce akan jikan nata ba take tambayana ko biba ta kara shigowa nan nace ninace ta daina zuwa don ranan da sukazo kuka tayi sosai har saida ta kwanta ciwo hakama yar uwarta da sukazo tare wai iskanta ya tashi itama da suka koma gidana a ranan . Ba kaji ba iya ta fada ai duk wanda keda iska yaga jafaru yasan da iska aka hadashi bashi kadai bane don irin yanayin da yake ciki duk mai hankali zai gane hakan. So sukayi suyi mai farat daya Allah bai yarda ba shine suke wahalal dashi haka insha Allahu Allah yafisu yafi sherinsu ai kinga har yau kawun ku ya kasa zuwa gidan nan . Da yasan ba komai aida tuni yazo gidan nan da fada tun ranan yace anwa yar gwal dinsa kazafi yaciwa mutane mutunci haka itama kinga ba wani mataki aida ta dauka ga abinda yaron nan Yazidu yai mata. Nan suka fito suka samemu muna maganan mun dan jima suna zancen kafin su fita muka rufe part din namu yaya ibrahim shike kwana a falo yanzu. Mu kuma muna daga ciki sai daga baya bayan yan gidan su Saiba sun kara zuwa dubanshi sai ga zance ya tashi saiba din taje wajen mama wai suna son a basu hakkinsu suma su dinga kwana dashi kamar yadda nakeyi. Mama dubu din tazowa su mama da iya da zancen iya ranan tayi fada sosai take fadin na kula dubu kema ba lafiyan yaron nan kike soba ? To anki a raba kwanan su mayar muna da jinya baya muna ganin sauki suja muna hasara ba za a yi hakan ba data zauna dashi a baya wata uwar take tsinana masa a lokacin banda sharan barcin ta da takeyi a nan saman dogon kujera. Dole dai akaci gaba da hakan don dai kada tsegumin yayi yawa na fara komawa gida ko gidan yar uwata in zauna sai dare zan dawo gidan. Ma,ana dai su, su wuni dashi da rana ni kuma in kwana dashi da dare saiya kasance wahala da dawainiya ya fara komawa kan tsofin don su zasuyi ta fama dashi hakana har zuwa lokacin dana dawo. Suko matansa excuse din girki ko kula da yara suke bayarwa abindai ba dadi wallahi don gaskiya bai cancanci haka a garesu ba za ace dai ina fadane kawai don in yaba kaina in bata su gaskiyan zancen ke nan nake fada a yanzu. Burin su a fili yake shine yaya zai mutu su kuma suci gadonshi don takan ce kura da shan bugu gardi da kwatan,kudi. Gara dasu dai kome za ace ace su dai keda riba tunda su suka haifa sune kuma keda Jafar aje ayi ta aikin wahala din don neman yabo . Alkawari nayi insha Allahu ba zan kara biyewa shirmensu ba idan sunayi ko da dangwarana mace zatayi matukar muna cikin wanan halin na rashin lafiyan mijin mu. Gata da wani hali kamar tashin kauye da yawan habaici da sake magana kowa tana iya yiwa hakan abindana fahinta ke nan yasa naba banza ajiyanta yanzu. Ni kadai zan iya cewa ga cigaban da aka samu yanzu kan matsalan nashi saidai ban fadawa kowa hakan ba har maman tudu dake kula dashi din. Don ita mama dubu iyakarta ta shigo ta dubashi inda wani shawaran da zasuyi kuma zasu zauna suyi a kan matsalan iyakartavke nan tunda mama ta nuna ita din uwace gareshi. Ankai yanzu yana dan iya daga hannu tun iya iya motsawa har yakai ya fara dagasu yana dan juyawa saidai ba bakin magana gareshi har lokacin. Anty Salima ko nafisa sai idan sunzo gidan zakiji bakina ko in muna tare da iya wani lokacin tare da salima din mukan fita muje can gidan mu wuni. Ranan ma mun shirya din zamu fita don na kwana biyu ban leka gidan ba yasa nacewa mama din zanje in gyara gidan tace ya kamata shine muka shirya zamu tafi din. Suna falo zaune a lokacin dana fito duk daba wani shigar azo a ganine a jikina ba amma ta dago kai ta kalleni ta kawar da kan nata gefe daya. Tsanar da tayi min take jin yana karuwa a zuciyarta duk zata kalleni takan ji kamar ta daina ganina har abada a duniyan nan don bata kaunan ta bude ido dai ta ganni saboda haushin da takeji nawa din kishi ke nan. Nima dai din ina jin haushin ta saidai baikai nata ba don ma taki zaman lafiya danine ya kawo hakan da zan iya rufe ido in kawar da duk wani kishinta da nake ji a raina. Kishi mukayi da itakata kwashe ranan ta zauna ta kwashe min kaina da tsiya da komai haka na zauna tayi min kitson a kaina sai kusan goma muka dawo gida. Tunda muka shigo da sallama naga irin kallon da mama tayi min nasha jinin jikina tana zaune tana cin abinci muka gaidasu nake tambayan iya tace tana ciki. Na mike zan shiga naji ta kirani tana fadin Rahama ina kuka shiga haka dan Allah keda kike da mara lafiya ki bar gida don gudun bacin ran wasu ba zaki dawo gida da wuri kiga halin da mijinki yake ciki ba ? Yau jikin nasa da zazzabi ya wuni saida likitanshi yazo yai mashi allura ya samu dan barci yayi amai yakai sau uku gashi kin barmu da tabararrun nan a gida sai shirme suke muna sin kasa anyana komai akansa. Da sauri na fada dakin ban tsaya jin karasan zancen ta ba yana kwance yana barci nagaida iya ina karasawa wajensa na dan dafa wuyanshi da hannuna. Zubur ya bude idonsa ya sauke min yana kallona sai kuma ya mayar da idanun nasa ya lumshe a hankali sannu nayi mai na zauna a kusa dashi hakan baisa ya bude idon ba. Sai lokacin muka gaisa da iya dake zaune a kasa tana lazumi take fadin yau jikin nasa ya tabu bayan fitan ki masassara ya kamashi. A hankali nace haka mama ta fada min yanzu amma da sauki ki daina wanan fitan don kawai kina gudun zargi ko wani abu yau ai uwarsa taga amfanin ki don kwasan amaima jidali ya zamawa wavyancan balle kula dashi din kinga ai tun kafin magariba da suka gudu basu leko ba . Duk yadda kikayifa sai an zageki wasu kuma su yabaki ki daure kici jerabawan duk nan mun san dalilin dake saka kina wanan fita din hakan kuma ba wankeki zaiyi daga zargin kishiya ba tunda anki mata yadda take so. Na dan waigeshi yaban tausayi matuka na mike na kwabe kayan jikina dakin da akace yayi ta aman nashiga gyara na tsabtace shi na saka kamshi. Har ban dakin saidana gyaro na koma dayan dakin da suke amfani shima na gyaro masushi likitan ya dawo tare da Yazid sun kara dubashi sai lokacin nasan ya daao garin . Sun dan jima suka fito na samu nashiga wanka na fito na zauna na dan gyara jikina na saka rigan barcina falo na fito na hada mai shayi mai kauri koma dakin. Cikin dabara na samu na tayar dashi na bashi yasha saidai na kula kamar yana fushi ko kuma yanayin ciwone hakana yake damunsa oho ? Saida kafa ya dauke na rufe part din don mama ta fada min ya Ibrahim bai nan yaje Abuja da safe cab zai kwana kuma. Na jima zaune bayan na fafa mashi magani ina mashi addua nakan koma saman kujera in kwanta amma haka kawai nace na kwanta a kusa dashi ranan don yanayin da yake ciki din. Nakai kamar minti goma da kwanciya a gefesa kamar a mafalki naji saukan hannunsa saman jikina saida na dan zabura nayi mamakin jin ya rikeni a ranan. Cikin fargaba nake fadin yaya kaine kuwa ba bakin magana kai kawai ya daga min bai iya ban amsa ba hamdala nayi a zuciyana jin yadda hannunsa ke motsi a jikina din. Sannu a hankali naji abin yana rikida zuwa wani yanayi don ya wuce tsamanina a hankali na runtse idanuwana acikin fargaban abinda zai iya faruwa a lokacin. Ba lakka bane a jikinsa ko wani kuzari don haka na kyashi yana abinda yake tsamani zai iya a lokacin amma ya kasa sai ajiyan zuciya zuwa can kuma bayan mun rugume junane naji saukan hawayenshi a saman jikina. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/17, 08:36] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 7️⃣1️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Kusan hakan yake faruwa a tsakanin mu tsawon wata daya saidai na kasa fadawa kowa wanan maganan. Wa zan tunkara da wanan zancen nace ga abindake wakana a tsakanina da mijina alhalin yana kwance haka sharkaf dashi bai ko wani dogon motsi balle magana. Har abin yakai ya fara damuna da zaran dare yayi banda katabus dashi ya dinga bina da ido kenan harsai yaji mun hada jiki dashi a sannan zai dinga jero ajiyan zuciya yana saukewa a fili. Dole zan biye mashi da abinda yake so na fannin wasannin aurataiya a tsakanin mu har zuwa lokacin da naga ya samu gamsuwa na jaye jikina daga nasa in koma gefe ina hawaye a cikin kunci. Ganin dai a kwai sauki sosai dake shigansa na gane hakan kuma nadaga cikin karuwan samun kuzarinsa a lokacin don yakanyi barci a daren da duk hakan ya kasance a tsakanin mu sosai. Washe gari nakan kula da fara,a a fuskanshi da walwala idan anyi magana zakiga yana dan murmushi a gefen fuskanshi sai gashi kwatsam naji suna zancen cewa zasu fita dashi kasan wajen. Nafi kowa sani a yanzu ciwon yaya bana asibiti bane ciwone dake da alaka da jinnu ko sihiri da akewa mutum wani lokaci. Ranan babu kowa nake fadin mama niko sai naga da an dakata da wanan fitan da za ayi da yaya a yanzu don yana samun sauki sosai kawai dai kamar baison a gane hakan ne a yanzu. Nayi tunanen hakan Rahama ina kula da kusan hakan a tsakaninku saboda a yanzu kin rage yawan tashin hankalin da kika shiga a baya game da rashin lafiyan nan a yanzu duk babu shi sosai wanan yasa na mayar da hankalina a kanku dole nasan akwai dai ? Dan murmushi na sake a gefen fuska ina kawar da kaina gefe take fadin ai bari almuri zan samu lokaci nayi magana dashi shima sai kuma ta koma tambayan . Yanzu wani cigaba kike gani ga lamarin nasa wanda ke nuna akwai sauki sosai ga laluran nasa don hakan ke nuna alaman lafiya idan ya fara wani abu ? A zuciyana na amsa da abu ko mama tunda ya iya raye dare daga kwance yake iya biyan bukatanshi nada namiji a hakan amma a fili cewa nayi da ita. Yanzu mama yana iya daga hannunsa wani lokaci har yana kokarin yunkurawa ya tashi zaune ko yayi kokarin kiran sunana idan yana son wani abu. Masha Allah koda ya boye hakan ba laifi bane don zamanin nan da muke ciki wanda baka zata ba bakayi tsamani ba shine zai ha,ince ka banga laifinsa ba idan har ya boye hakan gare mu yanzu. Yanzu matsalan shine ni kinga kamar sun ma fara gajiya da nine nan a yanzu yadda dubu da sarakuwarta ke nunawa zamana daku a yanzu yakai masu ko ina don na tare gaba na tare ba a garesu. Matsalan dai tasan tun Alh yana raye irin dokan daya kafa muna a gidan nan da kuma irin hadin kan daya sanya na dole tsakanin mu. Aida dubu nada hankali da bata karbe zancen da duk wani laluran jafar da iyalinsa a hannuna ba din ko shi dan dakinane kamar yadda kikaga Nafisa yar dakinta a yanzu tun Alh yana raye irin dokan daya kafa muna ke nan . Idan ke mace zaki yaye danki zai kira wace zaki ba yayyen dan haka kuma rikonsa zai koma hannunki ke nan har girmansa. Sai bayan rasuwan Alh ne kan mu ya dan rabu tun wajen robon gado da kowa ya nuna nasa halin akan abinda Alh ya barmu dashi. Yanzu da kokarun mijinki yayi dabaran dawo da hadin kai a tsakanin mu donshi haka halinsa yake kamar na mahaifinsa . Shigowan matan su yaya Auwal ya katse muna hiran mu don haka mukan zauna wani lokacin muna hira tsakanin mu saboda shakuwa da ita da yanzu nayi sosai takan ban labari irin na kunne ya girmi kaka a yadda na kula zamane akayi a baya irin zaman mumuke a tsakaninsu. Irin a fili ana son juna ana nuna babu matsala amma ana kishin mumuke irin zaman kakanin mu da iyayyen mu da ba a gane kan gida din nan . Anan falon aka zube da matan su yaya din ana hira lokacin Iya da matar Yazid suka shigo falon sam bata da marmari don bata sakin jiki da kowa sai iya da mama kadai take dan zama dasu bayan hakan ko yaushe tana part dinsu bata shiga mutane. Zakice tana gudu mutane fuskanta kuma sam ba fara,a acikinsa matan gidan suyi gulma sun gaji sun saka ido don sun fahinci itama ba kanwar lasa bace ashe. Bayan sun gaisane da iya suke tambayanta ko itace matar Yazid din iya ta amsa da fadin itace to bai zauna ba balle ya kaita wajen yan uwa a cewan iyan. A nan muka wuni dasu abinda yasasu tafiya yunwa don an jima ba a gama abinciba kamar kullum haka kuma da za a kawo aka zubo dan kadan waina mu dukan mu part din ke nan. Ina jin lokacin da mama takece masu suje gida su nemi abinda zasuci don wanan ma komu ba zai isa ba balle su din kullum haka ake abincin kamar na rowa a kawoshi bai isn mutane saukin abin ma yanzu wani lokaci ita nan takan yo muna dabara daga can gidan ta idan ta tafi shi muke samu muci. Da zasu tafi na yafa mayafi na rakasu har bakin get amma saida suka shiga suka sallami mama dake can part din ance wai tayi bakine bandai san ko suwaye ba. Sun tafi na koma don in gyara part din na samu Asmau da yara sun shigo muka gaisa na gaida ita da aiki take fadin tun safe tana tsaye bata huta ba yasa wai bata leko ba. Dakin na fito na barta da mijin don in suna ciki nakan dawo falo ko dayan dakin in dan kwanta wani lokacin kuma inyi barcin gajiya . Hakan ne ya faru don ban tashi ba sai wajajen karfe biyar saura na tashi nayi sallah na fito na fara gyaran falon har lokacin suna ciki da mijinsu da yaransu na dai shiga mun gaisa dasu din na fito naci gaba da aikina. Nayi mamakin rashin shigowan mama a wunin ranan don tun safe data shigo bata samu dawowa ba wai tana can tare da baki ake fadi ashe ba wasu baki bane ita da yarantane a lokacin. Saida dare iya bata shigo ba naji mama na fadi cikin kashe murya yau akwai abinda dubu da yaran nan suka samu don tun safe suke hayanita tsakaninsu. Jin hakan yasa na dago na dubeta take fadin kinsan mu ba a son mu sani don kamar makiya ake daukan mu duk da iya ta dan kyankyasa min . Wai yaran nan matan Jafar to har dake dai ke nan ake nufi ko sunce Habu da yazid din sun dulmuye dukiyan dan uwan nasu suna ci su barku a haka a kula daku dashi. Ko ita mahaifiyar taku ta kama masune shine habu kin sanshi ya dawo da komai na jafar da yake juyawa yanzu yace ya daina kula da dukiyan a baya ba an taba wanan maganan ba yanzu kuma sun tayar da zancen ke ban kuna nake tambayan ta ? Ke dai bari abune da baka isa yau danice ai wace ta ta fito da zancen nan data san bata da wayau a gidan nan ? Ina batun yarona dake kwance ina naga wani batun dukiya can har in bari karamar yarinya ta dagula min lissafina haka ? Shiru nayi ina tunane wai wanan matsalan haka daga ina yake fitowane wai na kula fa ba damuwa sukayi da bawan Allah nan ba sunfi damuwa da dukiya kawai akansa. Muryan maman tudun ne dake fadin kinsan ita iya ba ruwanta fadin abinta takeyi kai tsaye tace duk munafuncin daga Nusaibace da saratu ya fito. Kamar a mafalki mukaji murya kamar nasa da karfi saidai yanayin kiran daya kwala min din ya sauya da harshensa da muka sani sai gashi a ranan ya ambaci sunana . Dagani har mama da sauri muka karasa zuwa dakin yake fadi cikin badaniya kamar me koyon magana da Allah ya bashi ikon furtawa yace ko akwai kunama a gadon nan ne ? Da farko bamu gane me take fada ba saboda yanayin dan saurin maganansa haka kuma yanzu da harshen nasa yake kamar a karye. Sai can nace ko kunama kake fada ya daga kai da karfi yace a wani irin yanayi eehh wani abu nake jin kamar yana cizona na yunkura in dagashi na kasa hakan yasa mama fita daga dakin da sauri . Ashe taje nemo koda yan uwansa suna gidan sai yazid ta sama ya habu ya fita tun yamma ya tafi gidansa sai gasu tare da yazid din dasu mama da kowa don mama tudu tace dasu Jafar yayi magana yau. Saidai ba a cikin dadin rai ba sabo harshensa da yake kamar a karye wanan yasa duk gaba dayansu fitowa lokacin . Koda suka zo Allah ya taimaka na samu na cirashi daga gadon zuwa kasa suka shigo sai wani irin nishi da yakeyi mai karfi a cikin kugi na wahala. Mun duba gadon ko ina har jikinsa da komai karkashin gadon duk an duba babu komai gashi kuma a cikin wani wahala duk ana tsaye a kansa ana binsa da kallon tausayi. Hankalin duk wani na tare dashi tsakani da Allah ya tashi a lokacin Asmauce ta fara kuka ta juya zuwa falo don yazid dake mata tsawan yaya haka kuma kada ta tara masu jama,a ? Hakan yasa ta koma falo ganin yadda wahalan yai yawa ga wani irin zufa da yakeyi yasa na shiga neman magani a cikin wardrobe din da sauri na juya na fita zuwa kitchen na dora dan ruwan dumi na sauke na fito. Nan falo wajen Asmau na zauna muka fifitashi tare da ita na koma dakin lokacin yana wani irin wulle wulle nace wa yazid din ka kamashi a bashi magani ? Shiya kama min shi ya dago ina kokarin bashi naji muryan saiba na fadin wanan wani irin maganine kuma a daina bashi abu barkatai don Allah haka ?. Ki bashi kinji naji muryan yazid yana fada hakan yasa na bashi din naku fara shafa mai a duk jikinshi yana nishi muna mashi sannu har na shafe mai ko ina ban damu da wai su mama na wajen ba. Ga jikinshi har wani rawa yakeyi a lokacin hankalin kowa ya gama tashi da kuma tsoracewa lokacin ya habu suka shigo da maria. In fada maki mai karatu maria bata kyauta min ba nake gani a wanan gabar yadda takan share lamarina a wanan lokacin sai shiru shirun ta ya zamo min illa a zuciyana. Son nasan ko batazo don dan uwan mijinta ba ai zatazo don ni akai akai amma saita dauki sati biyu har ukku ba tare data leko mu ba taga yanayin da muke ciki dashi. Har na fara saka hakan a raina daga baya don sanin halinta yasa na share zancen nacigaba da al,amurana. Wanan yasa koda suka shigo ma a lokacin ban kulata ba ina gurfane a gaban yaya din mama da iya sai faman fadi sukeyi Allah ya baka lafiya ya tayar da kafadanka cikin iyalinka jafar. Ko asibiti zamune yaya habu ya fada a firgice ko anje asibitin me zasuyi da wanan lamarin saidai idan za a din daga gefe kuma yazid ne ke faman karanto mashi addu kala kala daga bakinsa. Sai zufan ya kara tsananta can yayi wani irin ajiyan zuciya ya lumshe idanunsa idabuwan mu yana kansa har lokacin acikin tashin hankali dayawa duk sun koma falo anyi zugun an tsurawa sarautn Allah idanu. Don ba wani mai iyawa ko gwaninta sai Allah gabadaya kowa ya tsunke yayi kamar yana barci har yazid din yana fadin ya samu barcine fa. Can baya na koma na zauna nayi tagumi daga inda nake ina iya hangonshi daga inda nake zaune din suna shawaran fita zuwa asibiti dashi . Sai lokacin suka tabbatar da ya soma magana da gaskiya don yadda ya bude ido yana ambatar sunana da karfi hakan yasa har wa yanda ke falon shigowa da sauri. Jiki a sabule na karasa din wajenshi yana fada min amai yake son yayi in daga shi mun kasa fahintar me yake fada a lokacin sai can nagane ina fadin amai kafin ma na rufe baki ya soma zubo amai ba kaikautawa wani irin bakin amai yake zubowa a bakinsa din. Ya Allah yasa dafin wahalan kake amayarwa jafar Allah yasa karshen wahalankace hakan maman tudu ke fadin hakan a gareshi sai yayi kamar ya lafa kuma ya can ya fara kakarin amai din. Oho har muna fadi kafara jin sauki sai kuma ga wanan lalura kuma yanzu nan fa muke zaune da yar nan muna hiran akanshi. Don yanzu akwai alaman sauki sosai a yanayinshi sai gashi munji daga ciki yana kakari ashe kuma zancen ya baci . Allah dai yasa saukin ke nan yazo da hakan mama tudu ta karasa zancen nata dashi tana kara mayar da hankalinta kanshi. Muryan yazid dake fadin amarya ki daga daga wajen wata daga cikinsu ta kwashe aman nan hakana ya fada yana kallon inda Asmau da Saiba suke zaune. Dan jim sukayi sai Asmau data yunkura tana daga danta daga jikinta yace No ke ki zauna ki rike danki wanan ta kwashe ita. Ai zancen ke nan wanan abin kowa ya shafa ba ita kadai ba amma sun mayar da zancen ya koma wani abu na daban a wajensu yanzu iya ke fadin hakan. Yace wace bata iyawa ta koma gidansu mana iya mu lafiyan shi mukajawa ba wani kishi ba can koda sun bar mata din ai wanan zata iya ma tunda gashi tanayi ba tare data kula da abinda suke nufi ba ai. Na lura da hakan sosai tunda na dawo garin nan iya dama ina son gaskanta hakanne da idona gashi ko nagani a yau. Tun safe daya fara aman nan yarinyan nan itace tsaye a kansa suna binta da kallo me hakan ke nufi ke nan maganganun da kukeyi a kanshi damu yan uwansa ya zama gaskiya ke nan jira kuke ya mutu ku wawashe dukiyan nasa yasa har kuke ragen dan uwansa daya kama komai ya rike a hannunsa yana ci da iyalinsa. Dagowa tayi tana fadin mu muka fadi hakan mu akace ma mun fadi hakan a ga habu din wazai fada in baku ba inda kuka fada sako yazo kunnen mu ai ? Kallon Saare tayi da sauri yace kwarai friend din munafuncin ki kenan ai ita ta fada inda za aji cewa mun kama komai mun rike dani da habu koda mun rike din laifine hakan ? Wanan magana ina kuma ya fito magana haka babu dadin ji mu da ke neman rayuwan dan mu ina zancen wani dukiyansa kuma ya fito a yanzu haka ? Ga sakaran nan mara mutuncin yarinya mana mama bada ita suke zama suyi gulman muba tunda ta zama banza a cikin mu banga laifin maza dake gano halinta su gujeta ba don munafuncin saratu yayi yawa mama. Idan anyi magana mama tace an mata kazafi da sheri ba abinda take nufi ke nan ba yanzu tunda ana zaman jiran gado ai sai kowa ya san zafin gadon da zaici din ke nan tunda ba wanan ce kadai zataci gadon nasa ba. Juyawa mama tayi gun saratu din tana fadin amma saratu abin yai maki yawa wai meyasa kike nuna baki damu da dan uwanki bane ke ? Kin taba ganin wanda yaki nasa yaso bare dan uwa marfin jallone fa yau jafar da sauran yannan ki sune zaman mahaifin ku a gareki sabodawa kika san yarinyar nan ma a gidan nan ? Wanan da kuka tasa a gaba da tsina tafiku sanin ciwon kanta don da biyu take kula dashi haka na farko daukan da tayi masa na dan uwa wanda ya kamata ace kune kuke hakan sai na biyu alakar aurataiya daya shiga tsakaninsu kinga riba biyu zuwa ulku ta samu a gareshi . Kun dauka gulmace gulmacen ku da kyashin da kuke nuna mata zai sa ta gaza dashi hakan bai kara komai ba illa karfi da kuzarin da kuka kara mata ga hakan yanzu. Kada ku dauka bai san meke gudana bane a hakan wallahi yana fahintar komai dake faruwa wajen nan ni ba yau ba yaran nan sun jima da zube min a idanuna . Karku dauka gari ba a san me kukeyi bane ansan komai an kuma sakaku a baki tundau ke saratu kaf yan uwa sun tsanaki a yanzu. Ido rufe maman tudu take fada masu magana iya son ranta yazid na kamawa inda yakewa mama bayanin cewa wai har saratu take fadawa salima cewa sunyi shawara cewa zasu kai karan habu kan ya danne komai na jafar ya hana masu gaba ya hanasu baya basu san komai da ake ciki da zancen dukiyan jafar ba ki duba fa mama da saratu za ayi wanan maganan haka idan ba sun saba hakan ba da ita dama ? Shine salima ta samu habu da zancen take fada mashi abinda ke nan wallahi sunki shawaranane da tun jiya ba wace zata zauna a gidan nan gaba dayab su. A,a yazid ka cireni cikin zancen nan ai gasu nan idan suna abin su ban kulasu ina can ina aikina komai aka kitsa nikan bada sanina bane wallahi tunda nice ke girki kullum saboda su mama dukiya yakai min uban diyana da bai da lafiya Asmau take fadan hakan. Dama na kula da hakan tun kwanaki cewa yarinyar nan ita kadai ke girkin nan don ko yaushe ka shiga itace a kitchen tsaye . Yau nasan ke munafukace Asmau dama kina hakane don munafunci ashe me nakeyi don munafunci da kikace ba zaki kara girkawa kowa komai ba tunda mama tudu tace ba za a kwana dashi ba mena fada ki fadi a gaban kowa mana yadda mukayi dake ? Nan dai tonon asiri ya tashi a tsakaninsu inda har sunan saratu din yafi yawa komai da ake kitsawa ita da saiba ce ke kitsawa har zuwa wajen malam da sukeyi duk Asmau ta fallasasu a bainan kowa yanaji harda abinda basu zaci zata iya fada ba game da suratansu na hassada . Ranan dai rayuka ba dadi a gidan ga mai ciwo ga kuma tone tonen maganan da yazid yajawo akayi na fallasa inda mama dubu a karshe tafi kowa bakin cikin hakan jin saratu abinda take kullawa don kawai ta bata tsakaninta da yayanta din kamar yadda Asmau ta fada. Saida yaya jafar yayi kwana biyu a cikin wanan halin aman har yakai dole aka kara mashi ruwa leda biyu manya ko zaiji karfin jikinsa. Don gabadaya a wanan gabar duk yan uwa an debe rai ma a garesa gaskiya ga badama a koma asibiti dashi haka tunda ansan ciwonsa dai sai Allah saukinsa bana asibiti bane don maganan likitoci gudane su basuga abinda ke damunsa ba suke fada. Barci yakeyi yanzu sosai tun bayan shigan wanan ruwan a jikinsa idan na bashi magani da safe zai koma yayi barci mai nauyi na tsawon wani lokaci idan ya falka in bashi abinci yaci . Allah sarki a hakan kuma fa tunda ya fara dan motsi sallah baya wuceshi zai min kwatance da zaiyi sallah a dagashi yayi idan ya idar kuma ya koma kwancensa. Kan zancen nan saida yan gidansu Saiba suka shigo zaria suka nuna bacin ransu ga abinda ya faru suka bada hakkuri yazid yana zaune yace ai su batayi masu laifi ba wanan tsakaninta da wanda ya ajetane da kuma Allah. Tun daya fara jin sauki yake cin abinci sosai a yanzu don ya fara karban abinci da alaman ma kokon dayake sha ya gunduresa a yanzu din. Asmauce a lokacin take bashi abinci don ita ta girka duk wace ta firka zata zauna ta bashi yayin da kuma wace bata girki zata zauna dashi a wunin . Sai tsarin hakan yayi min dadi sosai don jikina ya fara nauyi da laluran gaskiya a yanzu ko ina samun hutu sosai inyi ta barci. Ina zaune a gefensa Asmau tana bashi abinci dan Asmaun na goye yana a hannuna ina mashi wasa a gefe yaron yasa kuka uwar tana tsaye a gaban mijinta tana fadin saita gama ta kamashi. Sam yaron baida yarda da kowa hakan yasa uwar take dauke dashi ko yaushe mikewa nayi dashi ina jijigashi a cikin kafin naji yana badaniya da nufin na mika mata dan ta karba mana kukansa ya isheshi ke nan yake nufi. Ni kaina karfin hali nakeyi a lokacin don warin abincin nan ya isheni a hancina ina jin kaina wani iri a lokacin. A wurin karbansane na shaki turaren dake jikinta kuma wani irin amai ne naji yazo min lokaci guda karo na biyu ke nan a yanzu dana ji abu mai kamshi zanji zuciyana yana tashi . Da sauri na mika mata na nufi bandakin nayi mamakin irin aman da nayi a lokacin duk dan abinda naci a lokacin saida na amayeshi a wajen haka na fito a galabaice ina share fuskana . Idon su a kaina yake na samu waje na zauna a gefe tana min sannu kamahin ne ya kara dakan hancina na mike da sauri na koma bandakin idonshi yana kaina har na shige ina kakarin aman da ba abinda ya fito min a wanan karon. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/17, 08:36] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 7️⃣2️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, A galabaice na fito daga bayin wanda yakai har mama tudu saida ta shigo tana min sannu yayin da gogan ya wani tsareni da ido yana kallona daga kwancen da yake din. Mamace cikin kidima take fadin me kikaci ko baki da lafiyane nace ina ganin zazzabi ke son kamani don harda kaina yake min ciwo sosai. Jam aima kikana da karfin jini ko yaushe kina tsaye tunda mukazo laluran nan ban taba jin kince ga inda ke maki ciwo ba. Bari a duba in akwai panadol saiki sha ki kwanta ko zai fada maki ta kara min da sannu na amsa da kyat tare da fadin nagode. Asmau take fadin balle kwanakin nan akwai sauro ko jiya saidana kunnawa yaran nan maganin sauro muka samu barci dasu. Ina gama shan maganin na nufi dayan dakin na kwanta barci mai nauyi ya daukeni har yamma ban falka ba don na samu barci mai dadi a lokacin. Kodana falka na danji dama wanka nayi na dauro alwala na fito na tayar da sallah ina jin marata tana dan yanka min lokaci lokaci hakan yasa stil nake expecting din zuwan period dina na monthly da mata keyi tunda yakan zo min da ciwon mara wani lokacin. Abinci kasa ci nayi duk yadda mama ta matsa min kan naci amma na kasa ruwan zafi nasha na samu waje na kara kwantawa banyi barcin dadi ba a ranan don yadda jikina ya gashi nake jin zazzabi. Cikin ikon Allah zuwa asuba ya fada min sai gashi na tashi nayi aiyukan dana saba na dauraye mai jiki yadda na saba yi masa don ban yarda in barshi da najasa a jikinsa ko datti hakan kan kasance ko da mun yi aurataya nice zan masa wankan tsarki bayan na umurceshi da daura niya kafin kowa ya fito na gyara ko ina kamar komai bai faru ba tsakanin mu. Koda gari ya kara haskawa na gama da daki har falo lokacin ne mama ta fito tana fadin yar nan keda kika kwana da zazzabi kece ke aiki haka tunda safe daki bari ai zan iya in kama maki ai ? Murmushi nayi na dago daga sharan da nakeyi nace naji sauki mama na gaida ita da kwana take tambayana karfin jiki nace Alhamdullahi . Nagama komai na shiga nayi wanka na saka wani dogon riga na samu waje na kwanta a dakin duk wanda ya shigo a gidan zamu gaisa dashi yayi min yaya jiki ? A haka har aka kawo abin karyawa ina jin iya na fada tana fadin doya haka a bushe babu komai da zaca hada dashi kaci ya gogema makoshi. Hakan yasa banji sha,awan fitowa na karya din ba don nasan kayan takaici zan sama a wajen yasa banko fita da sunan karyawa ba a lokacin. Barcina nayi sosai a ranan don idona dama da barci ban samu barci da dadi ba da daren don zazzabin dake damuna din. Muryan mamace dake tsaye a kaina take fadin ki tashi haka tun safe baki karya ba kina kwance ko jikin ne har yanzu ? Na daga ina fadin a,a na mike da idona da sukai min ja zuwa bandaki nan kuma na kara jin aman yazo min saidai ba komai a cikina haka na wahala na fito daga bayin . Dashi muka fara arba ya kura min idanu yana bina da kallo kamar maye ni kallonsa har damuna yake a yanzu idan ya kafeni da idanunsa. Wai Rahama aman ne har yanzu badan mijinki na kwance haka ba ai sai ince ko Abba ya samu kani ne Asmau ke fadin hakan. Duk da gabana yayi wani irin faduwa amma saina dake nayi murmushi a fuskana kawai na samu waje na zauna ina goge fuskana da dan kwali a cikin wahala. Ki samu abinda kikaci kisha magani ya fada yana mai bina da kallo na dan sauke ajiyan zuciya na mike tsaye na fita zuwa part din su mama. Suna falon mu ita da mama da iya dasu inna na gaidasu na fita zuwa wajen anty Salima ko zan samu abinda naci a part dinsu don ko shayi ba zan iya sha ba a lokacin saboda yadda zuciyana ke tashi. Nan ma din ba wani abinda suka dafa a lokacin ma take girkin abincin ranansu take fadin bari ta hada min tea da sauri nace a,a ta barshi nashiga dakinsu na kwanta. Ina jin zazzabin na son ya dawo min haka na daure nayi sallah na koma na kwanta sai gata ta shigo min da furan gora mai sanyi shi nasha sosai don yayi min dadi a bakina sosai lokacin. Barci na koma sai zazzabin ya kara rufeni kuma mama tudu ce mai tambaya ina ina don bata ganni ba ake fada mata ina can dakin su salima kwance. Duk mun dauka dai zazzabin gajiyane haka kinsan halin malam ba haushe ba komaine ake saurin kaiwa asibiti ba sai anga yan dabarun gida sun kiyane za a kai kafa asibiti. Don kuwa ciwon kwana biyu ina kwance ragaraga dani abani wancan a bani wanan sai yayi dan sauki zai dawo kuma gashi banson yawan hayaniya ga tara miyau a baki saina faki ido na zubar shiyasa ban ma zama a cikin mutane a kwana biyun nan. Na idar da sallah a dadafe na dawo part din mu inda na samu su mama dashi a zaune shi kuma yana kwance a inda yake tunda na shigo mama ta bini da kallo tana min sannu ta dora da fadin. Ni dai ko ince an samu dan jinyane wanan ciwon Rahama kamar na mai shigan ciki haka komai kaci baya zama a ciki sai an amayeshi ? Daga inda mama dubu take zaune ta dago kai da sauri tana fadin ciki kuma yaya don Allah ki daina zancen nan . Wanda ke kwance haka rai a hannun Allah ina zancen ciki kuma ya fito nan gareta kuma ciwon daine yazo a haka balle dama wanda yai jinya haka ai sai yaji jiki daga karshe shima. Dadina dake sai ki dinga magana kamar karamar yarinya dubu to ko cikin ne Allah ba yana iya kawosa ba ko a hakan akwai abinda ya gagari Allah ne ? Iya ke fadan hakan ga mama din mama tudu tayi murmushi tana fadin shi dai nagani nawa akayi irin hakan muna gani dan wajen Rakiyana da mukaje jinya sokoto kwanaki da kariya ba sai anyi dori ya gwauce ba sai daga baya likitoci suka gano inda matsalan nasa yake dole aka rabashi kwana da matarsa a dakin . Ai kariya kikace yaya wanan da yake kwance haka shatkaf dashi bako motsi ina wanan zance ya fito haka kuma ki tashi ki danci wani abu kafin ki kwanta ta fada a karshe. Gabana sai faduwa yakeyi duk da zancen ban dauka zai iya faru haka ba na mike zuwa falo ban iya kallon abincin ba na samu wuri na zauna nayi tagumi. Sai a wanan ciwon na tsani halin maria ta da mama ke zaginta dashi ina kareta ashe wani shirun idan yai yawa wa mutum akwai illa don bata iya tabukawa kanta komai balleni ni kadai ta bari ina zugata a cikin dangin miji tana gefe ta fake da laluran ciki ta fita batuna yau wa zan tunkara in fadawa wanan magana. Ban koma dakin ba saida su mama din suka fara fitowa don neman wurin kwanciya a nan falo suka sameni kwance maman tudu take fadin ayyah dama aina fadi mu baki waje ki kwanta . Na dai daure na kawar da kayan da komai dana saba na koma dakin kwanan mu na fara shirin kwanciya a ranan har wani sanyi nake ji a jikina hakan yasa na nemi waje na kwanta na lafe a kujera. Da farko na samu barci amma da tsakar dare barcin gagarata yayi na soma kaduwa hakan yasa ni kuka ni kadai a inda nake din. Cikin karariyar muryasa naji yana kiran sunana yana tambaya yayane nace ba komai na kara nadewa don komai haushinsa nake ji a lokacin. Dole ya gaji ya kyaleni don bai iya tasowa zuwa inda nake nasan yadda banyi barci ba shima baiyi barci ba a ranan haka ya nade dai don ba yadda zai iya. Washegari mamace ta shigo jin bataji motsina ba tashigo tana tambayan ko jikin ne da kyat na iya daga kaina na bata amsa takai zaune tana dafani tace kina ko shan magani Rahama ? Na dai amsa mata ta dade zaune tana kare min kallo kafin ta mike ranan ita da kanta ta gyara muna part din su suna aikinsu na karfi yayansu daine sai a hankali gaskiya kuma abin kamar a jininsune yake haka gaba dayansu yayansu mata basu da moriya sam. A ranan itace ta bashi abinci na dai daure na gyara mai jiki da shimfida na koma na kwanta sauran aiyukane har bashi abinci duk mamace tayi a ranan tana falo tasa min kira nazo mu karya dole na taso nazo din. Cibi daya nayi na taliyan da aka dafa muna wai abin karyawan safiya na dawo dashi da gudu naje na amaye na jima na fito ina haki na kwanta mama ta dubeni tace anya Rahama kuwa. Yanayin ki ya nunafa kamar cikine dake komai da kikeyi na masu cikine fa Rahama baki na turo ina fadin haba mama na gyara kwanciyana . Ina wajen nade na dunkule yazid ya shigo suka tsaya suna magana dasu mama da matan yaya Jafar yake fadin Ke yaya dai mijinki yace nazo na kaiki asibiti baki da lafiya gata dai kan kamar maman biyu zazzabi kamar na mai ciki haka ta kwana tana wahala . Ciki kuma mama kamar wace tasha a ruwa aida an saka mata ayan tambaya akan cikin nan kuwa Saarece ta fada tana turo baki gaba har ta fara tafiya ta nufi dakin ta juyo tana fadin watan yaya J na takwas ke nan fa mama hakan kwance ake zancen wani ciki kuma yanzu gareta ? Dakuwa mama tayi mata tana fadin ja,ira mara kunya kinbi kina wani hakilo inma cikinne ina ruwan ki yarinyar da mijinta zaki kama wani zance can ? Har ta shige mama tudu naci gaba da fadin nina rasa menene tsakanin yar nan Rahama da saratu sam bata kaunar yarinyar nan da alheri ko kadan wallahi. Daga inda iya take zaune ta karbe da fadin ina zata kaunaceta tunda sheri yana ranta ita saratu watake so Amina ai banda wanan mara kunyar da halinsu yazo daya banga wanda saratu ke kallo da gashi ba gidan nan har yan uwan nata kuwa. Abu kamar asiri zakice yarinyar nan ta asircesune ita da uwarta yadda suke kafa kafa da zancenta yanzu ba taji hakan ba tana fita zakiga takai zancen nan wajen ta su dinga yiwa yarinyar nan kwakwaf inma cikinne ai Allah ya kawo abinsa. Ina lafe ina jin duk abinda suke fada a lokacin gabana ya soma faduwa ina tuna taraiyan mu da yaya a asirce wanda mukeyi a yan kwanakin samuwan saukinsa wanda daga Allah sai mu muka san abinda muka aikata din . Kai ina hakama ba zai yuyu ba har wani abu mukayi da za ace ciki ya shiga ga hakan mutumin da baida lakkan wani abin kwarai karfin haline irin na maza da yan adam kawai na kwakwa a wajensa. Barci nayi abina bansan wainar da ake toyawa ba a gidan saida wani zazzabi ya tayar dani na falka ina makyarkyata babu kowa a part din sai mama da shi dake kwance dakin na koma wajenshi na kwanta agefensa na dunkule. Ya zuba min ido da kyat ya mika hannunsa a kaina jikina ya gashe yayi zafi kamar garwashi ya soma fadin on tashi a kaini asibiti sai naji sam banson zancen wani asibitin nan da suke min kamar yana son a kara tsanatace a hakan gashi na fara jin zancen banza a bakunan su duk da banda yakinin cewa ga matsalata nasan kuma zazzabine kawai na wahala ba komai ba yake damuna. Shigowan mahaifiyarsu part din don ba kasafai take zama ba a nan saboda mama dake mata kara takanas ta baro komai nata ta dawo nan ta tare saboda danta dole ta kawar da ido tayi kawaici akan hakan dama kowa yasan jafar dan maman tudu ne inbada dan hatsaniyar rabon gado ya dan shiga tsakaninsu ba a kwanaki bayan rasuwan mijinsu yanzu ko an daidaita hakan an koma kamar komai bai faruba a baya. Yar nan ku kaita asibiti fa muryan mama dubu naji tana fadan hakan a gefe taci gaba da fadin ciwon nan kada yaci jikinta duba yadda ta fada a cikin kwana biyun nan ? To shi dai da zai kaita gashi a kwance yana fama da kansa tun safe yaiwa Yazid magana tunda ya fita da motan bai dawo ba tun dazun. Dama yazid zai kaita aiko dai ya fita da nasa iyalan tun dazun nan J din ya fara danniyar fadanshi akan dan uwan nasa a cikin karfin hali ya jawo wayarshi ya tura mashi text ba a jima ba sai ga yazid din ya shigo yana fadin afuwan madam mijikin ya hauni da fada na bar mashi mata na ciwo a gida ? Sannu tashi muje asibitin please ba zai barni in huta ba yadda ya hasalan nan dani yasa kai ya shiga dakin wajen shi na mike ina son shiryawa mu fita. Tare da mama muka tafi asibitin itace tayi min rakiya zuwa ganin likita da zanyi ancewa na kawo fitsari aka kuma debi jinina tun lokacin nashiga damuwa . Ni abu biyu najiwa tsoro na farko kar zancen ciwon ya J ya zamo gaskiya abinda kawai ya fado min a rai ke nan yasa sukace zasu dibi jinina . Munyi zaman jugun muna jiran sakamako saigashi anfito dashi ankaiwa likita Yazid ya shiga akai mai bayani cewa ai akwai shigan ciki a tare dani dan wata daya. Abinda yaba likitan mamaki shine da yazid dake fadin likita kun duba da kyau kuwa don mijinta fa yana kwance baida lafiya almost eight month ke nan yanzu. Shine me hakan bai iya ganetane ko bai sheda kowane har yanzu jin hakan yasa yazid din yin shiru na dan lokaci ya mike yana murmushi sukai sallama da likitan bayan ya bashi takardan da za a sai min magani. Tunda ya fito yake min wani irin kallo daya sani tsarguwashi dan irin yadda yake kallona din mota muka koma nida mama muka zauna shi yaje sayen magani. Ya dawo muka bar sibitin saida muka dauki hanya da kyau naji yace mama akwai matsala fa don nasan za ayi tsiya da sauran yayan ki idan suka samu labarin abinda ke damuwar yarki. Subbahanallahi akan me za a samu matsala kuma wai wasu yayan nawa kake magana ban fahince ka ba ? Mama ki barshi kawai har mu isa amma sai anyi da gaske don kada hakan yajawo rikici barin dan faka in sayo mata lemo ko zataso shi nan ya tsaya ya fita naji mama din tana ajiyan zuciya. Kodaya dawo bai kara maganan ba har muka isa gida don waya da yakeyi a cikin harshen larabci mota na tsayawa na sauka na barsu da mama din kodana shigo falon ba kowa hakan yasa na nufi daki kai tsaye. Nayi sallama na shiga yana zaune da matanshi ranan Nusaibace tayi girki tana zaune tana bashi abincin don angamashi late evening sosai . Ina shiga sukayi min ya jiki shike tambaya da hannu yaya nace da sauki na samu waje na zauna saida yazid ya shigo min da magani da kayab marmarin da ya sawo muna mai yawa ya aje a gabana yana fadin. Ki kula da shan magani likita yace asha na kwana ukku a gani idan bai bariba a koma Allah ya sauwaka yace zai leka part dinshi ya dawo. Sai bayan ya tafine anty Asmau take min sannu da jiki na amsa gami da murmushi ina gyara kwanci shigowan mama tayi muna sannu da dawowa take tambayan yaya jikin nawa ? Tunkan in bata amsa ta juya wajen mama tana tambayan me likita yace wahalan jinyane ko ke damuna sai mama tace anya ban tsamanin hakan gaskiya ? Don yazid dai akaiwa bayani an kuma auna fitsarina da jinina akai gwaji shinema ya tsayar damu bamu dawo da wuri ba. Awon fitsari kuma sai kace mai ciki daga zazzabi Nusaiba ta fada maman tudu ta amsa da fadin abinda nake tuhuma ke nan saidai ban san me sukace dashi yazid din ba. In ma cikin ne dai Allah ya raba lafiya ya kawo masu albarka haba dai sai kace wasan yara mama don Allah ku bari dai ina zancen ciki yanzu mijinta na kwance haka ? Anty Asmau ke fadawa mama haka cikin katse mata zancen da takeyi din ita kuma saiba cewa tayi haba dai ciki a yanzu haka kuma drama ke nan ai ? Ta fada tana wani mere baki ta juya zuwa cikin daki ta samu mijinta don itace da girki a ranan ni dai ina kwance ina jinsu bancewa kowa komai ba. Saidai a lokacin banda natsuwa don maganganunsu sun fara tsaya min a raina na fara tunane barkatai a kan hakan ina yanke shawaran nisantan shimfidan yaya a wanan maran kada wani abu yazo ya auku dani inga boni. Yazid bai shigo ba sai bayan sallah isha,i ya shigo ya samemu dasu mama sai anty Asmau yayi min ya jiki ya wuce zuwa wajen dan uwansa dake daki ya shiga ya samu dan uwan nasa yana sallah ya zauna zaman jiransa. Bayan ya idarne suka gaisa dashi nan ya zauna suka dan soma hira kafin ya fito mashi da zancen daya kawoshi wurinshi din da farko cewa yayi dashi. Ya dan uwa baka tambayeni abinda asibiti sukace game da matar kaba dazun da mukaje don dana dawo akwai mutane a lokacin kuma maganan yana son in fara kebewa dakai tukun. Ya dago ya kalli dan uwan nasa alaman meya faru a fuskanshi yace don gaskiya gwajin da akayiwa amarya ya nuna tana da shigan ciki na wata daya a jikinta shine ke bata matsala a yanzu. Cikin muryansa daya koma kamar a karye ya zaro ido yana fadin kana nufin cikine da Rahama yazid din na kallon yanayinsa yace cikin gyada kai haka sukace dani gama takardan daya bada result din nan. Ya fito dashi ya mikawa yayan nasa dan murmushi yayi ya karba yana bin takardan da kallo kafin ya tura karkashin filon da yake kwance. I hope dai kasan da hakan ko kada rayuka su baci daga baya kai kawai ya dagawa kanin nasa ya mayar da idonsa ya lumshe har dan uwan nasa yaso ya fita. Saiga mama ta shigo dakin tana fadin ashe ka dawo yanzu naga mota a waje dazun da kuka dawo ance kuma ka fita yace ehh na shiga garine . Yanzuma sakamakon asibitin na kawo mashi to maleria ne ko yake damun ta yace a,a kamar dai cikine sukace ga dai takardan nan hannunshi nabashi. Ciki ciki name cikinta ke ciwo kome donni ban fahince ka ba ai kayi min magana haka a dunkule yace mama me kike son in fada maki yanzu tunda nace ance shigar cikine da ita yake sata zazzabi haka ? Cabdi jam ciki ciki fa ita kuma yar nan a ina ta dauko ciki kuma a wanan lokacin badai cikin Jafaru bane ko da sauri Yazid din yace wa,iyazu billahi mama ke kike wanan maganan kuma kanar wace bata da aure mama ? Hakan ya jawo hankalin mu a falo harsu mama suka taso da sauri zuwa dakin suna shiga yazid na fitowa mama na biye dashi a baya. Tana fadin kuji min wanan zance don Allah wai yarinyar nan cikine da ita ashe take wanan laulayin haka ina Rahama din takene wai ? Kiyi mata me zuwa zakiyi ki tambayeta dubu ta yaya ta kwanta da danki kome kike nemanta kiyi mata yanzu ? Asmau dake zaune a kusa dani dakin mama ta mike tsaye da danta a hannu tayo waje ta saurara abinda ake fada lokacin mama dubu tana fadin. Haba iya wanan ai abin a tsaya a dubane yaron nan kwance fa yake rai a hannun Allah ta yaya zamu ganta da ciki ace hankali ba zai daga ba kuma ? To kina da ja da ikon ubangiji ke nan dubu ko kin isa ki hana Allah ikonsa yadda yaso a kuma lokacin daya ga dama wanan tambayan ba a bakinki ya kamata ya fito ba har in ana zargin hakan awajen mijintane ya kamata ajishi bake ba ? Akul naji wanan zancen ya koma fita a bakinki zan saba maki kafin ki shaganta masu da daga bakinki bake ba kuwa duk wani baji ya fadi wani zancen aibancin daga bakinsa a gidan nan kan zancen cikin nan zan fito masa a maryamuna ya sanni . Shiru fslon yayi yayin da mama tace iya baki fahinceni bane gani nayi dai yaron nan yana kwance haka mama ta ina zancen ciki yafito ? Baki daddaraba ke nan dubu yarinyar nan da mijinta take kwana ko gadinsu kikeyi da dare bahaushe yace tsakanin miji da mata sai Allah dama to ki kama bakinki da zancen nan kinji na fada maki. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/17, 08:36] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 7️⃣3️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Yadda naga dare haka naga safiya a ranan don ko ban runtsa ba har safe tunda na idar da sallah asuba na dauko wayata ina kiran maria. Duk da banso hakan ba nasan tana fama da kanta a wanan lokacin saidai haka ba zaisa ta shareni da yawa ba nayi magana tace mijintane yace ta natsu a waje daya saboda laluran cikin jikinta da take fama dashi. Tana dauka na hau kuka ina fada mata cewa ni zan tafi abujane nagaji nagaji ba zan iya ba hakkurina yana gab da karewa a gidan nan yanzu. Subbahanallahi meya faru Ramaah ta fada cikin rikicewa ta dora da fadin kun sake wani rigimane kuma yau din dasu ? Bamuyi ba zamu daiyi nan gaba kiris don har mama wanan karon zata san halina tunda bata kaunan mu to wai meya hadakune haka Ramaah ? Saidai kinzo zakiji na fasa ina kashe wayata a cikin takaici hankalintane ya tashi dan jin mena fada a lokacin don tasanni da karfin hali tasan halina idan na rikice kuma. Hakan yasa ta kira mijinta Habu take fada mai akwai abinda ke faruwa a can gida don na kirata hankali tashe har ina mata ikirarin cewa zan tafi abujane ko wajen ummah kaduna. Cikin tashin hankali yake fadin ohh lord mekuma ya faru matan nan basu bari a zauna lafiya baga Yazid a gida ba na kuma fada mai yasa ido a kansu. Bari na kira yazid din naji abindake faruwa zan kiraki daga baya da hakan suka rabu ya kashe wayan yana dannawa yazid don kira saidai bai dauka sai wajen kira na ukku ya daga suka gaisa. Suka gaisa sama sama ya soma fadin yazid meke faruwa a gidanne baka fada min ba ko dazun munyi waya da kai ai ? Wani gida ke nan yace nan mana yarinyar nan Rahama amaryan J ta kira hankali tashe tana kuka yace gaskiya ban sani ba dan uwa . Amma zan shiga in bincika yanzu habu yace dole akwai abinda ke faruwa gidan don dai ta kira a cikin kuka dazun nan har sun kare wayan zai kashe yace wait dan uwa. Kodai akan cikin jikintane suke magana dama nasan za ai hakan saboda jahilcin su irin na mata amma bari na shiga inji dai ? Ciki habu ya fada cikin mamaki yace eeh ciki gareta mana kuma na bincika na J din ne so me zasu tsaya sunyiwa rigima kuma ? Matarsa ce ba zina sukayi ba don me hakan zai zama abin tashin hankali kuma har su sakata kuka akan hakan su barta taji da abinda ke damunta mana ? Ciki fa kace habu a hakan har ta samu ciki dariya Yazid din ya kwashe dashi yace miji da matane fa meye kakewa mamaki kuma sai habu din yayi murmushi mai sauti yana fadin no banyi mamaki ba ai amma nayi kabar guy din nan inda kaganshi gaskiya J yakai dan iska haka ashe kana kwance haka ka dirkawa diyar mutane ciki ka barta a cikin tashin hankali da surutun mutane. Bari dai in shiga din inji kome ke faruwa ya daga daga kwancen yana zura jallabiyarsa a jikinsa zuwa cikin gida. Duk da bai saba ganinsu hakan a part din da safe ba yasan dole akwai wani abinda ke faruwa ke nan da gaske saidai ana ganinshi kowa yayi shiru sun gaisa dasu mama ya nufi cikin dakin inda dan uwansa yake kai tsaye. Ya jima a dakin suna tare dashi kafin ya fito ya fice daga part din don yayi nazarinsa baiga wani abin daga hankali daga gareshi ba don haka ya kyaleshi bai fito mai da zancen ba. Mama tudu ta sameni a daki ina kwance take fadin wai ba zaki tashi ki fito bane kina daki tun dazun kin dunkule ai sai hakan yasa baki gane jikin kiba ? Tsayuwan da tayi a kaina yasa dole na tashi na fito zuwa dakin kwanan mu inda na samu yaya J din shidaya a dakin yana kwance. Haka kawai naji ina ganin bakinsa tare da takaicinsa lokaci guda naji gaba daya ban kaunar ganinsa a rayuwata Saboda yadda zuciyana yake raya min duk wani kunci da tsana da nake fuskanta a rayuwa kusan nace saboda shine nake ganin hakan a yanzu. Banda ganin kutse da katsaladan din shigo masu rayuwa da matansa suke ganin nayi haka kuma a yanzu suke ganin na yaudaresu ko ina ha,intansa nakwaso ciki a waje nace shine dashi. Abu dai da yawa suka taru sukai min yawa a lokaci guda bake ganin gusawa daga nan din shine kawai mafita a gareni da zaisa in samu sallama. Ina jin muryanshi yana badaniyan magana dani dana shigo hakan baisa na juyo na kalleshi ba lokacin na dauki abinda zan dauka zuwa ban daki na shiga. Nayi kuka sosai a ciki kamar yadda na kwana ina sharban kukan a lokacin gab da in gama wankan naji zuciyana tana tambayana akan yata din da yanzu shi meye nasa a cikin zancen nan ? Da har na hada dashi nake fushi mutumin da ko a kwancen da yake yana nuna ina da muhinmanci a zuciyarshi aiko bai cancanci nayi mashi hakan a yanzu ba wata kilama wani abu yake so na shareshi baki kulashi anya kuwa Allah ba zai tambayeni dalilin hakan da nayi ba ? Ga mama nasihanta a gareni kullum idan mun kebe shine kada in yarda a ji kaina da mijina inyi hakkuri dashi dako wani irin hali na daure kada in taba bari a san tsakanin mu. Yau kuma sai taji akan abinda ba laifisa ba suji cewa ina fushi dashi har mun samu sabani a tsakanin mu nasan ranta ba zai taba dadi dani ba. Kodana fito abin mamaki yana kokarin dagawa daga saman gadon da kanshi da sauri na isa gurinshi nace kai kuma meye haka idan ka fadifa kaji ciwo. Maganan kamar an kwatoshi daga bakinsa yake fadin me akai maki meya faru naga kinyi kuka binshi nayi da kallo nace ina turu baki gaba ni banyi kuka ba. Ya koma ya zauna yana nishi na juya zan nufi wajen kayana haka kawai aka banko kofan dakin kamar a cikin fushi duk muka bi kofan da kallo cikin mamakin ko waye ? Saiba ce tana wani huci a fuskanta tana ganina taja tsuki tana fadin ai duk abinda mutum keyi a boye Allah naganinsa kuma ba azzalumin kowa bane. Inma wani kato yaba yarinya ciki take kokarin dafawa mutane sai Allah ya baiyana maishi ta nufi wajensa ta aje kayan abincin data dauko na karyawa. Ban kulata ba yi nayi kamar bansan ta shigo dakin bama a lokacin don ko gaisawan dole da mukeyi da aka tillasta munayi a tsakanin mu bamuyi ba a lokacin. Kokari nayi na taushi kaina ban kula mata ba na juya na fita bayan na saka tufafi a jikina nakai kofa take fadin iskancin banza sai asirin yarinya ya tono a gidan nan. Azo ana daga muna kai ashe ba class ba aji nakowa clininc cema kowa ya hau ya wuce hakan data fada yasa na tsaya na juyo ina fadin komai zaman mutum nakowa ubanki yayi kadan ya shiga wanan clinic din. Ke dawa kike wakike zagi nace da wanda ya amsa min da ita nakeyi kamar su mama suna jirace sai gasu sun fado dakin ita da iya. Kai kai lafiya wai meke faruwa hakane kuma daga shigowan ki nifa irin fadan nan na cacan baki na kauyanci na fada maku ba a nan ba don bashine a gaban mu ba yanzu. Har ita ta isa ta zagi ubana ita din me abin banza ke inkina da kunya har kina da bakin magana banda abin kunyar da kikaiwa kanki din nan ? Miji yana kwance haka sharkaf kije ki dauko mai cikin shege ki kawo mai zaki mana mashi don an kiraki da yar iska zagi akayi ko halinki aka fada ? Ai shine nace da ubanki mukayi iskancin ko don sune manyan gidan yan iskan da muke zuwa,,,,,,,, Muryan yaya jafar dake badaniya a saman gado ya dakatar damu duk daidai shigowan mama da tawaganta yake fadi da karfi ba cikin shege tayi ba nine da kaina nayi abina. Yana fada yana kokarin nuna kanshi da hannunsa don a gane me yake fadi to kinji abinda ya fada dai yace cikinsane abinda yake fada ke nan yayu wani kada kai alaman ehh kamar wani tsohon kadangare dashi lokacin. Yana kokarin cigaba da maganan da yake son fada kowa a dakin yai shiru yana kallonsa yace saiba kiyi hankali idan kika kuskura kika sheganta min cikin nan zan sakeki ya fada kamar maganar tana kwato mashi a bakinsa. Haba dai wai meye hakane kin gani idan kika jawo muna wani matsala a cikin zancen nan wallahi ranki zai baci sosai yaron nan tun farkon maganan nan ya nuna cikinsane yasan da hakan ba shike nan ba ke meye naki a cikin zancen wai ? Ciki dai Allah yayi lokacin zuwansa duniya yayi a haka ba wani mahalukin da ya isa yace kar yazo yau ninaji karfin halin maye da hauka. Akadara ma bash yayi cikin nan ba ke meye naki a ciki zancen nan yanzu tunda aurene kawai ya hadaki damu yarinyar nan kina da karfin hali sosai wallahi. Maman tudu take fadan hakan a cikin hasala iya dake salati tana fadin yanzu yarinyar nan sheganta masu cikin nan kike kokarin yi ko me ta cabe zancen mama da fadin. Yarinyar nan wai hankalinta daya meye a cikin zancen nan ke kishiya tunda dubu ta nuna kinfi kowa a wajenta har yakai zaki wuce gona da iri ? Ke Nusaiba ku fita daga nan, na fada maki ai inma ba cikinsa bane ganewa za ayi tunda ba a bace jinin gidan nan suke ba. Ni dai nafice tare da nazarin lafazin kowa a wajen nayi koka sosai a ranan daga baya naba kaina shawara akan zancen sai zuwa karfe ukku ya Habu da yanda suka shigo gidan. Ina jin muryansa suna gaisawa dasu mama suna tambayan yaushe ya dawo yace da ranan nan ya wuce ya shiga wajen dan uwansa. Ya jima a ciki ya fito yana fadin amma mama abinda yarinyar nan takeyi a gidan nan yai yawa Yazid shima ya shigo ya sameshi suka hade nan wajen iya da mama din suna fada muna daki da Yanda alokacin tana faman ban hakkuri. Habu sai fadi yake ban taba gani kojin irin wanan abin ba su lokaci da sukai cikin su wayayi kokarin sheganta masu cikin su duk da kowa yasan abunda take zuwa yi kaduna lokacin. Haba haba kada ka biye masu a zama daya mana kome mutum yayi don kansa ai ba za a biye mata a zama daya ba . To tabari yarinyar nan dai bata shiga zancen ta don haka itama ina son tafita zancen ta tun muna sheda juna tsakanina dasu a gidan nan . Ranan naga haukan kannan miji a gaban kowa akai tujara har saiba na fadin ashe su ake cuta da aka hansu kwana daki dashi ansan abinda aka kulla ayi yasa aka kakabesu da karfi da yaji karshe dai yazid yai tsaye yace. Wallahi bata kwana gidan idan kuma mama tace sai takwana sai ya kusa kasheta a ranan hakan da tajine yasa ta fice daga part din. Don daga inda yaya yake kwance shima bakinsa bai mutu ba a ranan fadi yake matatace nayi abinda nake gani daidaine a gareni anyi din kije kiyi duk abinda zakiyi. Yana magana kamar zai daga daga inda yake kwancen ya karaso gareta ganin da mama tayi auren saiba zai iya mutuwa yasa ta izata zuwa wajen. Nan Yazid ya dage kan lalai sai tabar gidan a ranan inba haka ba sai ya halaka ta dole da yamman nan ta nade tabar gidan don tdoron yadda taga yana kokarin cin mata a lokacin. Bani ba har yar uwata tayi koka sosai da tsohon cikinta don a yanzu tana cikin watan haihuwantane ummah muka iya kira muka sanar da ita abinda ake ciki tace tana zuwa. Ashe daddy ta kira abuja ta fada masu saiga kiran mummy tana fadin mu shirya gobe zasu zo su tafi damu duka idan basu son mune suda suka haifemu sun san darajan mu ai. Hakan ne ya faru don kamar hadin baki saiga iyayyeb Saiba sun dawo da ita suna bada hakkuri ana cikin wanan zaman su daddy da mummy suka iso tare da anty Salma. Sai ummah da mijinta da suka shigo suma a tasu motar suka hade duka a gidan gaba daya iya tace yau dubu kinkai ga yadda kike so ke nan Don ba sassauci a wajensu daddy yace dagani har Yanda tafiya zasuyi damu tunda uwar mazanmu ta nuna bata kaunarmu to abashi diyanshi ba zai barsu inda ba a kaunarsu ba. Nan mama ta fara kame kame tana salati tana fadin ita itace za ace tana nuna halin kyara da hattara a garemu don bata kaunar mu ita saidai a dauki alhakinta ga hakan. Daddy da mummy sun kafe akan sufa tafiya zasuyi damu don amana muke a wajensu don haka ba zasu saka ido ana tozarta nu suna kallo ba gara kowa ya kama gabanshi. Banda kuka ba abinda nakeyi a lokacin dole aka shiga ban hakkuri ana tausan su daddy din da suka hakikance lalai tafiya zasuyi damu. Iya ta soma magana da fadin to dubu yaukan sunanki ya cika dubu don dubu ya cika dake saidai ki sani yau ana daukan yaran nan su koma hannun iyayyen su ke kuma zaki rasa dan ki guda tunda baki yarda da kaddara ba a zuciyar ki. Dama irin ranan nan nake maki gudu ranan da hakkurin yaran nan da iyayyensu zai kare a kanki ranan da zasu fito fili haka su nuna maki sun fahinci me kike nufi dasu. Ace ka zauna baka da tunane kai maganan yara kake amfani dashi duk abinda yaran nan suka fada akan abokan zamansu ya zaunu a wajen ji dubu baki bincike sai dai ki goyi bayansu. Narasa me yaran nan suka tare maki haka dubu duk wani kyautatawa da akw bukata a wajen yaro yaran nan suna maki shi a gidan nan amma baki ganin hakan ke abinda nake maki gudu ke nan a kullum dubu ? Yanzu dai Alh kuyi hakkuri kubar yaran nan a daku nan su don Allah tunda kowa ya gane kuskurenshi cikin zancen nan a taru ayi hakkuri don Allah dama haka zama ya gada wani lokaci. Daddy yace ai yayi hakkuri amma tafiya damu ya zama wajibi a garesa tunda har aka nunawa yarsa haka shiba zai lamunci hakan ba gara dai ya dauke diyansa ya tafi dasu. Mijin ummah na fadin kwarai tunda abu yakai har ana kokarin shegantawa yarinya cikin jikinta ai gara kawai ayi hakkuri aje a zubar da cikin kowa ya kama gabansa. Jam jam Alh kana dattijo bai kamata ka fadi hakan a bakinka ba ai kai mai bada hakkurine cikin nan kasai ya ishi mu nan ishara don wani hikimace ta ubangiji ga hakan. Ace cikin nan bai samu ba saida yaron nan ya shiga irin halin nan haka kadai ya ishi bawa ya kara yarda da lamarin ubangiji ai don Allah Alh kuyi hakkuri da zancen tafiyan nan ku bar yaran nan a daku nan su zaifi. Yunkurin da yaya Jafar yayi don ya sauko zuwa wajen daddy ya bashi hakkuri sai akai rashin sa,a ya fado saman gadon saida yan uwansa suka tare shi hakan yasa hankalin kowa a falon ya koma kansu kuma . Ihu mama tasa tana fadin a ceceta don Allah kada ta rasa jafar don suman da yayi a lokacin mahaifin Saiba yace to Nusaiba kin gani kinga inda fitinan kishi ya kaiki yau ? Rashin hakkurin ki ya jawo mijin ju zai rasa ransa saboda bakin ciki ke yanzu wani dadi kikaji ga hakan don Allah ? Ki tunafa mutumin nan Allah ke talkafe damu shine tallafe damu ta sanadinsa muke a cikin gidan da muke a yanzu shine cin mu da shan mu amma sha shancun ki ya hana ki natsu ki kwantar mashi da hankalin gidansa. Komai ace nusaiba ce silla ke wani riba kika samu ga hakan wai haba dai baba ai wanan kyautatawan tsakanin miji da matanw ba kuma sai ka fada a nan ba tunda kowansu yanayiwa ai ? Wallahi a,a don ni baiyiwa iyayyena hakan ba Asmau take fadan hakan cikin jin haushin abinda taji din a lokacin don ranta ya baci matuka. Ke yi shiru nan sulhu akeyi mama tudu ta fadawa Asmau din daddy yace tana da right din da zatayi maganan ta yadda bai maki ba haka muma sai bai muna ba a bangaren yata kinga ashe yarsu itace da riban shiya take fadan wani yazo ya rabeshi shima yaci arzikin nasa .. Habu da yazid suka fito daga dakin suke fasin ya samu barci don Allah daddy kuyi hakkuri yanzu dai ai taji abinda take son ji haka kuma kowa yasan cikin nan da ubansa tunda ga matakin da maicikin akaga ya sauka wajen sheganta masa cikin sa din. Magana ta gaskiya duk ranan data kara wani magana akan acikin jikin yarinyar nan ta kwana da sanin zamata a gidan nan yazo karshe. Nan dai aka samu aka lakashi daddu yayi hakkuri bayan ya kafa hujja akan duk ranan da wani dan uwansu ko wata mace ta fadi wani maganan daba daidai ba kotuce zata rabshi da maishi a rayuwansa ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/17, 08:36] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 7️⃣3️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Yadda naga dare haka naga safiya a ranan don ko ban runtsa ba har safe tunda na idar da sallah asuba na dauko wayata ina kiran maria. Duk da banso hakan ba nasan tana fama da kanta a wanan lokacin saidai haka ba zaisa ta shareni da yawa ba nayi magana tace mijintane yace ta natsu a waje daya saboda laluran cikin jikinta da take fama dashi. Tana dauka na hau kuka ina fada mata cewa ni zan tafi abujane nagaji nagaji ba zan iya ba hakkurina yana gab da karewa a gidan nan yanzu. Subbahanallahi meya faru Ramaah ta fada cikin rikicewa ta dora da fadin kun sake wani rigimane kuma yau din dasu ? Bamuyi ba zamu daiyi nan gaba kiris don har mama wanan karon zata san halina tunda bata kaunan mu to wai meya hadakune haka Ramaah ? Saidai kinzo zakiji na fasa ina kashe wayata a cikin takaici hankalintane ya tashi dan jin mena fada a lokacin don tasanni da karfin hali tasan halina idan na rikice kuma. Hakan yasa ta kira mijinta Habu take fada mai akwai abinda ke faruwa a can gida don na kirata hankali tashe har ina mata ikirarin cewa zan tafi abujane ko wajen ummah kaduna. Cikin tashin hankali yake fadin ohh lord mekuma ya faru matan nan basu bari a zauna lafiya baga Yazid a gida ba na kuma fada mai yasa ido a kansu. Bari na kira yazid din naji abindake faruwa zan kiraki daga baya da hakan suka rabu ya kashe wayan yana dannawa yazid don kira saidai bai dauka sai wajen kira na ukku ya daga suka gaisa. Suka gaisa sama sama ya soma fadin yazid meke faruwa a gidanne baka fada min ba ko dazun munyi waya da kai ai ? Wani gida ke nan yace nan mana yarinyar nan Rahama amaryan J ta kira hankali tashe tana kuka yace gaskiya ban sani ba dan uwa . Amma zan shiga in bincika yanzu habu yace dole akwai abinda ke faruwa gidan don dai ta kira a cikin kuka dazun nan har sun kare wayan zai kashe yace wait dan uwa. Kodai akan cikin jikintane suke magana dama nasan za ai hakan saboda jahilcin su irin na mata amma bari na shiga inji dai ? Ciki habu ya fada cikin mamaki yace eeh ciki gareta mana kuma na bincika na J din ne so me zasu tsaya sunyiwa rigima kuma ? Matarsa ce ba zina sukayi ba don me hakan zai zama abin tashin hankali kuma har su sakata kuka akan hakan su barta taji da abinda ke damunta mana ? Ciki fa kace habu a hakan har ta samu ciki dariya Yazid din ya kwashe dashi yace miji da matane fa meye kakewa mamaki kuma sai habu din yayi murmushi mai sauti yana fadin no banyi mamaki ba ai amma nayi kabar guy din nan inda kaganshi gaskiya J yakai dan iska haka ashe kana kwance haka ka dirkawa diyar mutane ciki ka barta a cikin tashin hankali da surutun mutane. Bari dai in shiga din inji kome ke faruwa ya daga daga kwancen yana zura jallabiyarsa a jikinsa zuwa cikin gida. Duk da bai saba ganinsu hakan a part din da safe ba yasan dole akwai wani abinda ke faruwa ke nan da gaske saidai ana ganinshi kowa yayi shiru sun gaisa dasu mama ya nufi cikin dakin inda dan uwansa yake kai tsaye. Ya jima a dakin suna tare dashi kafin ya fito ya fice daga part din don yayi nazarinsa baiga wani abin daga hankali daga gareshi ba don haka ya kyaleshi bai fito mai da zancen ba. Mama tudu ta sameni a daki ina kwance take fadin wai ba zaki tashi ki fito bane kina daki tun dazun kin dunkule ai sai hakan yasa baki gane jikin kiba ? Tsayuwan da tayi a kaina yasa dole na tashi na fito zuwa dakin kwanan mu inda na samu yaya J din shidaya a dakin yana kwance. Haka kawai naji ina ganin bakinsa tare da takaicinsa lokaci guda naji gaba daya ban kaunar ganinsa a rayuwata Saboda yadda zuciyana yake raya min duk wani kunci da tsana da nake fuskanta a rayuwa kusan nace saboda shine nake ganin hakan a yanzu. Banda ganin kutse da katsaladan din shigo masu rayuwa da matansa suke ganin nayi haka kuma a yanzu suke ganin na yaudaresu ko ina ha,intansa nakwaso ciki a waje nace shine dashi. Abu dai da yawa suka taru sukai min yawa a lokaci guda bake ganin gusawa daga nan din shine kawai mafita a gareni da zaisa in samu sallama. Ina jin muryanshi yana badaniyan magana dani dana shigo hakan baisa na juyo na kalleshi ba lokacin na dauki abinda zan dauka zuwa ban daki na shiga. Nayi kuka sosai a ciki kamar yadda na kwana ina sharban kukan a lokacin gab da in gama wankan naji zuciyana tana tambayana akan yata din da yanzu shi meye nasa a cikin zancen nan ? Da har na hada dashi nake fushi mutumin da ko a kwancen da yake yana nuna ina da muhinmanci a zuciyarshi aiko bai cancanci nayi mashi hakan a yanzu ba wata kilama wani abu yake so na shareshi baki kulashi anya kuwa Allah ba zai tambayeni dalilin hakan da nayi ba ? Ga mama nasihanta a gareni kullum idan mun kebe shine kada in yarda a ji kaina da mijina inyi hakkuri dashi dako wani irin hali na daure kada in taba bari a san tsakanin mu. Yau kuma sai taji akan abinda ba laifisa ba suji cewa ina fushi dashi har mun samu sabani a tsakanin mu nasan ranta ba zai taba dadi dani ba. Kodana fito abin mamaki yana kokarin dagawa daga saman gadon da kanshi da sauri na isa gurinshi nace kai kuma meye haka idan ka fadifa kaji ciwo. Maganan kamar an kwatoshi daga bakinsa yake fadin me akai maki meya faru naga kinyi kuka binshi nayi da kallo nace ina turu baki gaba ni banyi kuka ba. Ya koma ya zauna yana nishi na juya zan nufi wajen kayana haka kawai aka banko kofan dakin kamar a cikin fushi duk muka bi kofan da kallo cikin mamakin ko waye ? Saiba ce tana wani huci a fuskanta tana ganina taja tsuki tana fadin ai duk abinda mutum keyi a boye Allah naganinsa kuma ba azzalumin kowa bane. Inma wani kato yaba yarinya ciki take kokarin dafawa mutane sai Allah ya baiyana maishi ta nufi wajensa ta aje kayan abincin data dauko na karyawa. Ban kulata ba yi nayi kamar bansan ta shigo dakin bama a lokacin don ko gaisawan dole da mukeyi da aka tillasta munayi a tsakanin mu bamuyi ba a lokacin. Kokari nayi na taushi kaina ban kula mata ba na juya na fita bayan na saka tufafi a jikina nakai kofa take fadin iskancin banza sai asirin yarinya ya tono a gidan nan. Azo ana daga muna kai ashe ba class ba aji nakowa clininc cema kowa ya hau ya wuce hakan data fada yasa na tsaya na juyo ina fadin komai zaman mutum nakowa ubanki yayi kadan ya shiga wanan clinic din. Ke dawa kike wakike zagi nace da wanda ya amsa min da ita nakeyi kamar su mama suna jirace sai gasu sun fado dakin ita da iya. Kai kai lafiya wai meke faruwa hakane kuma daga shigowan ki nifa irin fadan nan na cacan baki na kauyanci na fada maku ba a nan ba don bashine a gaban mu ba yanzu. Har ita ta isa ta zagi ubana ita din me abin banza ke inkina da kunya har kina da bakin magana banda abin kunyar da kikaiwa kanki din nan ? Miji yana kwance haka sharkaf kije ki dauko mai cikin shege ki kawo mai zaki mana mashi don an kiraki da yar iska zagi akayi ko halinki aka fada ? Ai shine nace da ubanki mukayi iskancin ko don sune manyan gidan yan iskan da muke zuwa,,,,,,,, Muryan yaya jafar dake badaniya a saman gado ya dakatar damu duk daidai shigowan mama da tawaganta yake fadi da karfi ba cikin shege tayi ba nine da kaina nayi abina. Yana fada yana kokarin nuna kanshi da hannunsa don a gane me yake fadi to kinji abinda ya fada dai yace cikinsane abinda yake fada ke nan yayu wani kada kai alaman ehh kamar wani tsohon kadangare dashi lokacin. Yana kokarin cigaba da maganan da yake son fada kowa a dakin yai shiru yana kallonsa yace saiba kiyi hankali idan kika kuskura kika sheganta min cikin nan zan sakeki ya fada kamar maganar tana kwato mashi a bakinsa. Haba dai wai meye hakane kin gani idan kika jawo muna wani matsala a cikin zancen nan wallahi ranki zai baci sosai yaron nan tun farkon maganan nan ya nuna cikinsane yasan da hakan ba shike nan ba ke meye naki a cikin zancen wai ? Ciki dai Allah yayi lokacin zuwansa duniya yayi a haka ba wani mahalukin da ya isa yace kar yazo yau ninaji karfin halin maye da hauka. Akadara ma bash yayi cikin nan ba ke meye naki a ciki zancen nan yanzu tunda aurene kawai ya hadaki damu yarinyar nan kina da karfin hali sosai wallahi. Maman tudu take fadan hakan a cikin hasala iya dake salati tana fadin yanzu yarinyar nan sheganta masu cikin nan kike kokarin yi ko me ta cabe zancen mama da fadin. Yarinyar nan wai hankalinta daya meye a cikin zancen nan ke kishiya tunda dubu ta nuna kinfi kowa a wajenta har yakai zaki wuce gona da iri ? Ke Nusaiba ku fita daga nan, na fada maki ai inma ba cikinsa bane ganewa za ayi tunda ba a bace jinin gidan nan suke ba. Ni dai nafice tare da nazarin lafazin kowa a wajen nayi koka sosai a ranan daga baya naba kaina shawara akan zancen sai zuwa karfe ukku ya Habu da yanda suka shigo gidan. Ina jin muryansa suna gaisawa dasu mama suna tambayan yaushe ya dawo yace da ranan nan ya wuce ya shiga wajen dan uwansa. Ya jima a ciki ya fito yana fadin amma mama abinda yarinyar nan takeyi a gidan nan yai yawa Yazid shima ya shigo ya sameshi suka hade nan wajen iya da mama din suna fada muna daki da Yanda alokacin tana faman ban hakkuri. Habu sai fadi yake ban taba gani kojin irin wanan abin ba su lokaci da sukai cikin su wayayi kokarin sheganta masu cikin su duk da kowa yasan abunda take zuwa yi kaduna lokacin. Haba haba kada ka biye masu a zama daya mana kome mutum yayi don kansa ai ba za a biye mata a zama daya ba . To tabari yarinyar nan dai bata shiga zancen ta don haka itama ina son tafita zancen ta tun muna sheda juna tsakanina dasu a gidan nan . Ranan naga haukan kannan miji a gaban kowa akai tujara har saiba na fadin ashe su ake cuta da aka hansu kwana daki dashi ansan abinda aka kulla ayi yasa aka kakabesu da karfi da yaji karshe dai yazid yai tsaye yace. Wallahi bata kwana gidan idan kuma mama tace sai takwana sai ya kusa kasheta a ranan hakan da tajine yasa ta fice daga part din. Don daga inda yaya yake kwance shima bakinsa bai mutu ba a ranan fadi yake matatace nayi abinda nake gani daidaine a gareni anyi din kije kiyi duk abinda zakiyi. Yana magana kamar zai daga daga inda yake kwancen ya karaso gareta ganin da mama tayi auren saiba zai iya mutuwa yasa ta izata zuwa wajen. Nan Yazid ya dage kan lalai sai tabar gidan a ranan inba haka ba sai ya halaka ta dole da yamman nan ta nade tabar gidan don tdoron yadda taga yana kokarin cin mata a lokacin. Bani ba har yar uwata tayi koka sosai da tsohon cikinta don a yanzu tana cikin watan haihuwantane ummah muka iya kira muka sanar da ita abinda ake ciki tace tana zuwa. Ashe daddy ta kira abuja ta fada masu saiga kiran mummy tana fadin mu shirya gobe zasu zo su tafi damu duka idan basu son mune suda suka haifemu sun san darajan mu ai. Hakan ne ya faru don kamar hadin baki saiga iyayyeb Saiba sun dawo da ita suna bada hakkuri ana cikin wanan zaman su daddy da mummy suka iso tare da anty Salma. Sai ummah da mijinta da suka shigo suma a tasu motar suka hade duka a gidan gaba daya iya tace yau dubu kinkai ga yadda kike so ke nan Don ba sassauci a wajensu daddy yace dagani har Yanda tafiya zasuyi damu tunda uwar mazanmu ta nuna bata kaunarmu to abashi diyanshi ba zai barsu inda ba a kaunarsu ba. Nan mama ta fara kame kame tana salati tana fadin ita itace za ace tana nuna halin kyara da hattara a garemu don bata kaunar mu ita saidai a dauki alhakinta ga hakan. Daddy da mummy sun kafe akan sufa tafiya zasuyi damu don amana muke a wajensu don haka ba zasu saka ido ana tozarta nu suna kallo ba gara kowa ya kama gabanshi. Banda kuka ba abinda nakeyi a lokacin dole aka shiga ban hakkuri ana tausan su daddy din da suka hakikance lalai tafiya zasuyi damu. Iya ta soma magana da fadin to dubu yaukan sunanki ya cika dubu don dubu ya cika dake saidai ki sani yau ana daukan yaran nan su koma hannun iyayyen su ke kuma zaki rasa dan ki guda tunda baki yarda da kaddara ba a zuciyar ki. Dama irin ranan nan nake maki gudu ranan da hakkurin yaran nan da iyayyensu zai kare a kanki ranan da zasu fito fili haka su nuna maki sun fahinci me kike nufi dasu. Ace ka zauna baka da tunane kai maganan yara kake amfani dashi duk abinda yaran nan suka fada akan abokan zamansu ya zaunu a wajen ji dubu baki bincike sai dai ki goyi bayansu. Narasa me yaran nan suka tare maki haka dubu duk wani kyautatawa da akw bukata a wajen yaro yaran nan suna maki shi a gidan nan amma baki ganin hakan ke abinda nake maki gudu ke nan a kullum dubu ? Yanzu dai Alh kuyi hakkuri kubar yaran nan a daku nan su don Allah tunda kowa ya gane kuskurenshi cikin zancen nan a taru ayi hakkuri don Allah dama haka zama ya gada wani lokaci. Daddy yace ai yayi hakkuri amma tafiya damu ya zama wajibi a garesa tunda har aka nunawa yarsa haka shiba zai lamunci hakan ba gara dai ya dauke diyansa ya tafi dasu. Mijin ummah na fadin kwarai tunda abu yakai har ana kokarin shegantawa yarinya cikin jikinta ai gara kawai ayi hakkuri aje a zubar da cikin kowa ya kama gabansa. Jam jam Alh kana dattijo bai kamata ka fadi hakan a bakinka ba ai kai mai bada hakkurine cikin nan kasai ya ishi mu nan ishara don wani hikimace ta ubangiji ga hakan. Ace cikin nan bai samu ba saida yaron nan ya shiga irin halin nan haka kadai ya ishi bawa ya kara yarda da lamarin ubangiji ai don Allah Alh kuyi hakkuri da zancen tafiyan nan ku bar yaran nan a daku nan su zaifi. Yunkurin da yaya Jafar yayi don ya sauko zuwa wajen daddy ya bashi hakkuri sai akai rashin sa,a ya fado saman gadon saida yan uwansa suka tare shi hakan yasa hankalin kowa a falon ya koma kansu kuma . Ihu mama tasa tana fadin a ceceta don Allah kada ta rasa jafar don suman da yayi a lokacin mahaifin Saiba yace to Nusaiba kin gani kinga inda fitinan kishi ya kaiki yau ? Rashin hakkurin ki ya jawo mijin ju zai rasa ransa saboda bakin ciki ke yanzu wani dadi kikaji ga hakan don Allah ? Ki tunafa mutumin nan Allah ke talkafe damu shine tallafe damu ta sanadinsa muke a cikin gidan da muke a yanzu shine cin mu da shan mu amma sha shancun ki ya hana ki natsu ki kwantar mashi da hankalin gidansa. Komai ace nusaiba ce silla ke wani riba kika samu ga hakan wai haba dai baba ai wanan kyautatawan tsakanin miji da matanw ba kuma sai ka fada a nan ba tunda kowansu yanayiwa ai ? Wallahi a,a don ni baiyiwa iyayyena hakan ba Asmau take fadan hakan cikin jin haushin abinda taji din a lokacin don ranta ya baci matuka. Ke yi shiru nan sulhu akeyi mama tudu ta fadawa Asmau din daddy yace tana da right din da zatayi maganan ta yadda bai maki ba haka muma sai bai muna ba a bangaren yata kinga ashe yarsu itace da riban shiya take fadan wani yazo ya rabeshi shima yaci arzikin nasa .. Habu da yazid suka fito daga dakin suke fasin ya samu barci don Allah daddy kuyi hakkuri yanzu dai ai taji abinda take son ji haka kuma kowa yasan cikin nan da ubansa tunda ga matakin da maicikin akaga ya sauka wajen sheganta masa cikin sa din. Magana ta gaskiya duk ranan data kara wani magana akan acikin jikin yarinyar nan ta kwana da sanin zamata a gidan nan yazo karshe. Nan dai aka samu aka lakashi daddu yayi hakkuri bayan ya kafa hujja akan duk ranan da wani dan uwansu ko wata mace ta fadi wani maganan daba daidai ba kotuce zata rabshi da maishi a rayuwansa ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/17, 08:36] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 7️⃣4️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Nayi kuka har nagodewa Allah a wanan ranan daya zamo min kamar na tonon asiri a wajena ranan da nake jin kamar kasa ya bude inshiga saboda kunya daya lulubeni a lokacin don hakan ya zamo kamar wani bakon lamari a society ake gani. Yayin da miji yake kwance a lokacin ni kuma Allah ya nufeni da samun karuwa dashi karuwan da nake jin tankar i hadiye raina a lokacin . Wanda bake jin tsanar mijin fiye da kowa don ina ganin shine ya kaini ga wanan abin kunyan a yanzu wanda a sanadin haka har ya barni da nauyi da kunyar iyayyena. Wanda ko kafin su daddy su wuce a ranan saida su kai ta zolayata a bakin mota ina hawaye badai kamar anty Salma dole ganin yadda nake kuka yasa takai ga rikeni a lokacin. Haka suka tafi suka barmu a cikin tausayin mu don sun fahinci muna zaman hakkuri a wanan gidan gidane da baida alkibla baida tsayayyen babba da zai tsawata akai yaran maza sune tsaye da gidan kuma su din dai tunda akwai uwa da kaka dole komai zasuyi akwai taka burki da tauyewa ga irin zaman nan. Zamane da wasu iyayye ke zabawa iyalinsu don gashin kan zuciyarsu su wanda akasari ya sabawa al,ada da shari,an mallam bahaushe. Zakiga iyayye masu irin halin nan suna nisanta iyalen su da yan uwa suna kamesu daga shiga dangi ko wani harka na zununci wanda uwace zata zauna ta dinga shimfida doka iya son ranta ga zurianta. Irin wanan rayuwa muka tsunci kan mu a cikin gidan nan matukar ba naku yazo daya ba da irin matan nan mata da yawa suna fuskanta bacin rai a zaman aurensu koda ya kasance kuwa miji na aon matarshi uwa ba zata bari a zauna lafiya ba irin haka aji dadi. Abin mamaki na zata maria zata dan zauna dani ta kara min shawara ina tsaye wajen bayan wucewan su daddy saiga Habu ya fito yana cewa da ita muje ko tsayuwan nan kada yai maki yawa. Haka suka shiga mota suka tafi suka barni ina kallonsu a cikin mamaki har suka bacewa ganina naja kafata zuwa ciki inda na samu mama da iya zaune a falo suke fadin Allah sarki mutanen kirki sun tafi Allah ya saukesu lafiya. Amin kawai na iya fada na shiga dakin yana kwance shi kadai a dakin yayi shiru yana kallon saman dakin yanayin kwanciyarsa zai nuna maka cewa ya shiga zurfin tunane a lokacin . Kwanciya nayi ba tare dana kallo inda yake kwance din ba nima na fada nawa tunanen muna wajen a haka har aka kira sallah magariba. Na mike zuwa bandaki na hado komai da nake mashi alwala na fito saida nayi mai ya tayar da sallah nashiga na dauro alwalata nima na fito. Falo na koma ranan nayi sallah haka kawai nake jin tsanarshi na karuwa a zuciyna ina zaune ina addua wayata ta dauki kara bayan na duba naga ummah ce a layin lokacin na dauka take fadi bayan mun gaisa. Ramaah yaya na batku dazun kiyi hakkuri kinji kowa da tasa kaddaran kar kiyi mamaki duk sanadin wanan cikin Allah ya kwantar da mijinku jinya irin haka saboda hakan kawai ya faru a tsakani ku. Wani dan, taurine dashi kafin yazo duniya sai uwa da uba duk sun girgiza wani lokacin ubane kan fara laulayi da jinyar ciki kafin a sakawa uwa ta karasa saukin haka manya suka fada. Ance sai uba yayi jinyan fitar da kwansa kafin ya samu ya fito daga jikinsa kamar yadda mace kanyi wahalan haihuwa suma maza din suna da tasu jinyar kalan fitar da kwai a jikinsu. Don haka nake ganin duk wanan jinyar kamar ta wanan halittan dan da a yanzu kuka samune dashi sai kiga in har hakan gaskiyane a cikin yan kwanakin nan insha Allahu mijin ku ya samu lafiya ya mike kamar bashi ba. Ta jima tana rarashina kafin mukai sallama ina aje wayan kiran mummy yana shigo min a wayan na daga itama din dai hakkuri ta bani kamar yadda duk wani masoyina iya hakkuri zai iya ban a yanzu kawai don dama shi muka gada tun kakanin a arewa. Na dai idar da sallah ina zaune naga shigowan mahaifiyarshi hakan yasa ban damu dana koma ciki ba na zauna a falon abina ta jima a ciki zaune kafin ta fito da bacin rai ta fice daga part din. Ikon Allah naji maman tudu ta fada daga bayana don iya bata falon namu lokacin zuwan Yazid da family shi yanzu bata faye zama damu ba ko yaushe. Amma akwai aiki a wanan rayuwan kice komai yaro keyi da iyalinsa idon ki yana kai a wanan zamanin ka kawar da idonka ma yaya aka kare dakai balle kace saka ido zakayi. Dubu tana da wahala a rayuwanta zancen nan da mutumin nan ya fada shine yanzu take faman hasala akai duk da yaron nan yana kwance bata duban hakan ita. Saida ta sameshi da wanan zancen bata duban zancen nan bana yau bane balle ta duba halin da dan nan yake ciki ta tausaya mashi ga hakan. Amma wai haka dubu ta rutsa yaron nan yanzu akan zancen nan dubu sam bata kaunar diyanta suna alheri wayema me alherin ciki banda shi jafar din ? Jafar din dai mijinku shine ya buwayeta yake alherinsa ba tare daya fada mata ba kada ki dada ki kara a wanan tsanar da tayi maki a yanzu kan rilon yar nan diyan baby da kikeyi yana daga cikon abinda yasa ta tsaneki haka ? Ta dauka ban sani bane har mutunci taci masa daya dauko maki yarinyar nan ta manta Nafisa na gidan take fadin ta rabasu hurda da duk wani dan uba nasu amma baya jin hakan . Tunda mutumin nan yayi zancen gida a gabanta nasan ya bambarowa yarshi magana har su kuwa indai dubune ki zuba ido kiga yadda zasu kwashe da ita a gidan nan yanzu. Ai tunda ta gane inda take hasashen yana narka kudinsa ba a nan abin yake ba yar nan a yanzu nata ya sameta kuma da dubu a gidan nan zakice na fada maki wanan zance kuwa indai itace . Sai lokacin na dan murmusa ina gyara kwanciya tace aiki barsu zakice na fada maki don sai ta zazzagewa yarinyar nan fushinta tas zataji saukin hakan a ranta yamzu. Sukan ba zakice tsohuwar nan iya ta haifesu ba son sam basu dauko halin iya ba ta ko ina sai jikokin ne suka dauko iyan a wajen sanyin hali sam iya baka rashin gaskiya ita a gabanta. Ni dai har barci ya daukeni ban sani ba a wajen sai dare sosai naji mama din tana tayar dani inshiga daki na koma daki na kwanta sai safe. Kamar yadda na saba a kullum hakane ya faru a wanan karon nayi sallah ban zauna ba na shiga aiyukan cikin daki saida na kawo wirin gada kamar a mafarki naji ya rikeni da hannusa da bai iya dagawa lokacin sai gashi ya rikeni dasu gam. Na dago ido ina kallonshi shima ni yake kallo idonsa a cikin damuwa yake magana fushi kike danine Rahama da nayi maki laifin me kike wanan fushi haka dani ? Ni ka sakeni ba fushi nakeyi ba na fada ina kokarin kwace hannu na daga rikon dayayi min din sai naji ya sasauta rikon yana murmushi yace. Da kina da wayau Rahama da baki fushi dani ba a wanan abin ko kinyi fushi dani ni bana fushi dake saidai ina son ki sasauta fushin nan naki don bake daya ke rayuwa a yanzu ba. Hakan daya fada yasa na kalleshi a lokacin ya daina kallona hakan yasa na kyaleshi na share dakin ruwa na hado nazo nayi mashi wanka dasu yadda na saba nagama na goge dakin na saka kamshi kafin na hado magani na zauna nayi mai addua na bashi ya sha na kuma hada mashi tea mai kauri kamar yadda na saba yi mashi kafin duk su kawo abinci sai na tabbatar da yaci wani abin a cikinsa kafin na bude kofa a kullum. Bugun kofan da akeyine yasa na nufi kofan don in bude saidai kafin na bude din naji muryan maman tudu tana fadin haba wanan dukan ai sunji dole a bude indai Rahamace yanzu haka ita ta tashi tunima tana aiyukanta ai. Ina budewa Saiba ta kutso kai a cikin dakin kamar zata bankeni naja gefe daya ta kutsa kai ciki tana fadin munafuncin banza da wofi kawai. A labe da sunan yaudara ana ha,intan mutane ga hakan Allah dai ya tona maki asiri ai kowa ya gama ganin ki da abin kunyar da kikayi . Abin kunya ai yana a gindin kowa don gara da nawa bada katon waje nayi ba da mijina nayi wasu kuma zarginsu akeyi da mazan waje ai ? Allah yafiki yafi sherinki nusaiba don ya kwatoni daga sherin da kikaso ki kulla min shigowan mama ya hanata ban amsa don mama ta shigo cikin daga murya tana fadin . Yarinyar nan kina da hankali kuwa ina zancen nan an kasheshi tun jiya yanzu kuma kizo da farar safiyan nan ki tayar da mutane da fitina haka ? Aina fada maku yar nan bata da mutunci dama nasan ba zata bar zancen nan ba ai kishin mahaukata kawai ta iya ita. Niba fitina nazo yi ba nazone a raba kwana abawa kowa hakkinsa tunda ba ita kadai bane kuma bata fi kowa da za a barta tana abinda taga dama haka ba ? Kanki daya kuwa to anki a raba kwanan yadda aka saba din haka za ayi ai dama ba wanda ya hanaku halinku shine ya koreku ba wani ba ko kun tsaya din me zakuyi mashi? Ki duba ki gani yadda yarinyar nan ta tsaya ta gyarashi ta gyara mashi muhalinsa a cikin ku wa zai iya wanan din ? Keko Amina tace hakan mana sai an raba kwana a yanzu mana tabi dare tayi mai fyade tace sai yayi mata cikin dole yadda yayiwa yar uwarta tunda ba Allah ta sani ba ita ? Saida na daga kai na dubi iya dake wanan maganan lokacin kafin na mayar da kallona gareshi yana kurum ya zuba ido yana saurarensu a cikin takaici. Ashe hayajiyar su yasa mutanen cikin gida sunji sai gasu gaba dayansu sun shigo part din yazid ne a gaba yake tambaya da iya lafiya da safen nan kuma ? Inafa lafiya yazidu wanan mara kunyar ta buga muna kofa da tijaranta tunda safen nan wai tazo a raba kwana a tsakanin su a hakan . Halama jiya nasan batayi barci ba da zancen hakan ta kwana a ranta shiyasa ta bugo muna wanan uban sammakon da tijara yarinya haka ba kunya ? Kawai muji kin turmujeshi cikin dare kina kwantan hakinki wurinshi koda karfin tsiya kuwa hakan data fada yasa su salima yin dariya a fusace yazid ya juya a kansu yana fadin . Ku kuma yan abu kazan uba dama shiya hanaku aure ai don iskanci karya iyan ta fada ba abinda zai faru ba kenan aga kawai ya zubewa mutane. Wai me take fadane meya kawo fitinan nan kuma haka yanzu da safen nan mama data shigo karshe ita da Asmau take tambaya cikin son sanin abindake gudana. Tazone itama a bata hakkinta yazid ya fada yana nunata da hannunsa yace tazone danki ya bata ciki itama ya fada cikin halin ko in kula a gaban manya. Wani irin zancen banzane kai kuma abata ciki kamar yaya haka ake bada cikin gatsau kamar tumakai ta juya wajen saiba din dake tsaye cikin tijura tace nusaiba lafiya kika shigo masu haka da fitina da safen nan ? Mama niba fitina nazo dashi ba daga kawai nazo akan zancen raba kwana tunda abin hakane amanan mu takeci shine iya take min sababi haka . Ai dole Nusaiba dole iya tayi maki hakan tunda aikin hankali bai hakan ke wace irin fitsarariyace wai Nusaiba ? Mama niba wajensu fa nazo ba wajenshi shida ita nazo don kowa zai karbi girkinshi tunda cutarmu akeyi ashe ace mu bamu iya kula dashi ba sai ita. To ba za a raba kwanan ba nace ai gara ita Rahama din Allah ma ya gyara yaya ta gane tun farko data yanke wanan hukunci don da kun halakashi tun,tuni ban sani ba. Ta dai halakashi mama tunda ita take ha,intarmu kowa kuma yagani ai yanzu ke r,,zz,z,,z,z,z,,z,d,zd,z,z,z,, muna mu sheda juna dake a gidan nan .dzzzzzzzzzzzzzzzdzzzz,zzzzz,z,z,z,z,d,zzzzzzzzd,z dzzdddz,zdzzzzzzz Malam bafa dakai nake ba magana nazo yi dasu za a hade min kai kuma a hanani magana hannu yazid din ya daga da nufi marinta da sauri maman tudu ta hana hakan tunda mu,,,,,,,,,, Daga saman gadon da Jafar yake kwancen yana saurare sai ji mukayi yana fadin Nusaiba enough kije gida nasake don Allah. Cak ta tsayar da maganarta tana saurarenshi itama hakanma yafi wallahi taje kowa ya huta haba me ake da wanan hali naki don Allah abu haka ba marmari saboda Allah ? Yau mamace ke fadin hakan akan nusaiba wanda ba nusaiban ba duk wanda ke dakin saida ya kalleta tacigaba da fadin me ake da halin yarinyar nan mama ? Yarinya ba abinda ta rike sai cin mutunci a kullum kuma tafi kowa cin riba a gidan nan amma babu godiyan Allah kasheshi zakiyi a kwancen ko me ? Ai dole kiyi hakan tunda kina bakin ciki da wani ya rabeshi ya samu na fahinci yarinyar nan bashi ta damu dashi ba abinsa ya dameta yanzu ? Dama shita biyo ai hakan yasa ta shiga ta fita tayiwa rayuwansu kutse ta hanasu zaman lafiya gashi dai ubanki ya fadi har gida ya saya maku amma duk hakan bai isheku ba. Saikin kashe min shi da ransa kin karasashi don bakin cikin yana tare da wata a ranan dai Nusaiba taci zari agun mama ido rufe ba ita ba har mu dake wajen saida ta hada damu din . Ta kuma kafe sai Nusaiba tabar gidan kota bata mamaki a ranan haka kawai wajen bakar jaraba irin namu ita ba zata yarda ba in abin ya koma haka duk mu watse mu koma gidan iyayyen mu. A,a dai su meye nasu a cikin zancen nan ita dai da tayi din ai ta samu abinda take nema ga yaron nan yau hakkurinsa ya kare ai. Sun jima suna surutunsu nidai na koma falo tun saiba na dakin nida salima tana fita Saare tabi bayanta suka fita ta jima bata dawo ba sai daya kai wajen awa biyu sai gata tashigo rai bace tana cewa. Abu haka ba adalci don Allah aimaka laifi kayi magana kuma ace za a sakeka wanan aida gani kasan aikin asirine wallahi. To wa kike nufin yayi mata asirin yanzu waya damu da ita balle ya tsaya yiwa Nusaiba asiri salima dake zaune kusa da iya ta fada. Sai iya ta amsa da kinsan dan fara daya suke da ita dole su dauka abinda sukeyi shi kowa keyi a gidan wakeda lokacin hakan a yanzu kowa abin gabanshi ya dameshi. Kedai saratun nan baki da halin kirki wallahi yanzu cin mutuncin dan uwanki da tayi bai sa kinji haushinta ba sai namu ? Nifa iya kada ki daureni don ban ambaci sunan kowa ba a nan maganata dai nakeyi yaya za a taru a bata rashin gaskiya bayan kuma ga gaskiya a fili su ake cuta kowa yasan haka ? Tas tas taji saukan mari a kumatunta saida takai gurfane a wajen yazid dake tsaye kanta yana huci daga kofa muryan mama ke fadin kara ma yar iska mara kunyan banza kawai . Ko hakan ma aiya isa iya ta fada yayin da take tsugune tana wani irin kuka a dafe da fuska duk mun zuba mata idanu cikin mamaki. Ta jima a wajen su mama na zaginta kafin ta mike ta fice a cikin kuka a hankali na lumshe udanuna ina nazarin abubuwa da yawa dake faruwa a gidan . Ranan ko gyaran part din ban samu yi ba don wanan fitinan da muka wayi gari dashi sabo ga yan uwansa maza sun zo dubashi sun jima a wajenshi basu tafi ba sai kusan azahar muna tare da salima a dakin mama muna hira. Wanda hakan yasa na dan sake jikina a nan Asmau ta same mu taso a dauko zancen saiba amma sai duk muka share zancen . Nasan halinta tun ban auri mijin su ba tana da son kananan magana ayi da wani a bayansa wanan yasa ban yarda inyi dogon hira da ita. Saida darene muna zaune mama ke fadin ai mahaifin Nusaiba ya bugo waya yana bada hakkuri amma sunce a barta gida har tayi hankali tunda bata da mutunci kowa bata ragawa a gidan. Wanan yasa na kara sanin cin mutunci baida alheri ga mutum don idan ya tashi tambayanka saika raina kanka. Ko yayane ka koyi girmama na gabanka don wanan halin rashin ragowan shiya kaita ga hakan don wata kila databi abin cikin mutunci dole tsofin namu su tsaya su duba masu a raba kwanan a yanzu yadda suke so. Itako Asmau don munafunci sai cewa takeyi wallahi ni sam ban damu da hakan ba kici gaba da kokarinki Raamah don Allah ya gani ba zan iya yadda kikeyi ba ni. Da wuri na kwanta ranan don gajiyan dake tare dani har barci ya soma dibana Yanda ta kirani sai lokacin take tambayana yaya jikina tare da fadin ashe kuma wanu fitina akayi a gidan ? Ehh kawai nace mata tare da fadin ni bai shafeni ba shiyasa ban daukeshi komai ba na kashe wayana ga baki daya na kwanta. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/17, 08:44] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 7️⃣5️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Baifi sati daya ba da wanan rikicin Maria ta haihu ta haifi danta namiji na shiga cikin sahun yan murna amma banje barka ba. Don halin,mu na fulani daya motsa ance rikon magana sai bafullace gaskiyane wanan maganan don kuwa muna da hakan a cikin jinin mu idan kai muna abu zamu ajeshi a ran mu na tsawon lokaci komai dadewa sai mun dauki fansa akan abin gareka wanan haka yake. Nima ta haihuwanta na haketa don naki ko nuna zanje barka har akai kwana ukku da haihuwa ta bugu tana tambayana wai lafiya nake kuwa ? Amsan dana bata shine ban jin dadin jikina kawao don itama haka takan fada a lokacin Allah ya baki lafiya Ramaah ta fada ta kashe wayan don ta fahinceni. Aka kai kwana biyar yaya jafar da kansa yake fadin kinko je gidan Habu kinga jariri Rahama a takaice na bashi amsa da banje ba yaya kuma ban zuwa. Ya kalloni da sauri tare da furta subbanallah lafiya meya faru nace dashi ba komai kawai dai banjin zuwa gidan ne kawai a yanzu. Nasan dole dai akwai wani abu amma yar uwarki ta haihu zakice ba zaki ba Rahama ko akwai abinda ya farune ban sani ba yake tambaya ? Ba komai hakan dai nace ba zani ba na sake fada ina kokarin fita daga dakin bansan ya sukayi da mama ba sai gashi naji maman tudu tana min maganan tace. Mijinku ya fada min kina fushi da yar uwarki nima nayi tunanen hakan tun shekaran jiya da naga bakije gidanta ba har wanan lokacin saida raina ya bani akwai dalilin hakan ? Kiyi hakkuri da yar uwarki kada ki bari har a gane kuna da matsala da ita a gidan nan ki shirya gobe kije ki dubata in ma wani abu tayi maki ki boye hakan kada ki yarda a gano hakan ayu maku dariya. Wanan maganan da mama din tayi min yasa na shirya naje tare dasu da iya ina gidan mahaifiyar mu ta bugo waya nake ce mata ai gani gidan acikin harshen fulatanci nake fada mata abinda maria din tayi min. Take fadin wai nasan halin maria ai wanan halin nata ai yasa aka hadota dani zuwa aure katse ummah nayi da fadin dana san haka zai cika dani ta dalilinta ta kuma gudu ta barni da ban biyo ta zuwa garin nan ba. Baki yarda da kaddara ta riga fata ba ke nan ko ina kike tunda Allah yayi jafar mijinki ne sai kun hadu don haka ki daina cewa itace tayi sanadin haduwan ku Allah ne ya hadaku tun farko. Wani malolon bakin ciki na hade ina goge fuskana ban tsaya ba duk yadda taso in tsaya muyi shawara na koma gida tare dasu mama hakan yasa ta fadawa habu mijinta halin da muke ciki da ita din. Ba kunya sai gashi ya shigo da yamma gidan muna zaune saman baranda muna shan iska don ba wuta shi yasa muka fito daga wajen ginan mu samu iska. Bandashi yaya da yake ciki zaune tare da mama suna hira bayan mun gaisa dashine har dan shiga sai kuma ya dawo yana fadin zo nan Rahama ya shige ciki ya barni ina kallonshi ta baya. A dakin na samesu su ukku tare da ya J da mama suna zaune na shiga ina kara gaidashi bai karba min ba ya hau fadin Rahama meya faru tsakaninki da yar uwarki ta kirani tana kuka wai kinki tsayawa kuyi maganan komai a tsakanin ku. Saida na lumshe ido ina hadiyan zuciya nace ni din nan kuwa yace look Rahama banson irin haka dole akwai wani abinda ya faru tunda har tace hakan. A,a habu ba zaka shiga tsakaninsu kayi saurin yanke hukunci ba yanzu ka nuna kamar laifin na wanan yarinyarce ita kadai ita matar naka bata fada maka dalilinta nayin hakan ba ? Tace ita bata san tayi mata komai ba haka kawai ta tsiri fushi da ita yaushe ma maria zata tsaya yin haka ga wani balle Rahama ? Kaji ai mama ta fada niko a cikin yaren mu na soma magana ina fadin ai dole kace hakan tunda dukkan ku baku dauki hakan wani abu ba tunda niba mutum bace. In zaki fada da hausa ki fada kina muna maganan da bamu ji so kike ki tayar mata da hankali bayan kinsan halin da take ciki a yanzu. Ina jin hakan bansan lokacin da hawaye yazo min ba na soma fadin niba mutum bace ai tunda ta kasa yi min abinda ya dace lokacin da nake neman wani na kusa dani a wajena. Kamar yaya ya fada ya kura nin ido zuciya yazo min na ci gaba da fadin ashe ba dadi itama ta shareni kamar bata san inda na fito ba ? Dama ai ,,,,,, kai habu kada ka matsawa yarinyar nan don Allah kasan dai a yanzu halin da take ciki don Allah ka daina maganan nan tunda tace ba komai kasan dai ba fada maka abinda ya hadasu zatayi ba . Nayi mata magana dazun taje ina shike nan koma meye ai ya wuce dai yanzu ko so kke ta tare a gidab ka baki daya tabar mijinta a nan kwance ? Amma mama ai gaku tare dashi kinsan mama ta hana kowa irin zuwan nan da akeyiwa mace idan an haihu sai daga can gidane suke zuwa nan tace tunda salima taje taga baby bata koma kuma ace itama din bata zuwa ai hakan baiyi ba mama. Amma habu ban zace zaka shiga tsakanin yaran nan ba harka nuna kana goyon bayan matarka haka kiri kiri inma laifine matarkace ta fara mata ai kasan su fulani da riko nasan shine take nufin zata rama itama ga nata wautan ? Sai lokacin yayi magana tunda dan uwan nasa ya soma magana yana zaune ya kura mashi ido yace dashi habu bakaji me mama tace dakai bane wai ? To ka barsu kawai banson irin hakan Rahama dai dole taje wajen yar uwarta baka san sanda suka sami matsala ba haka ba zaka san shirinsu ba kuma . Yanzu kazone ka daga mata hankali kuma kome tunda dai an tillasata mata zuwa kuma ta tafi ka fitar da bakinka a cikin matsalansu don Allah. Su kuma yaran nan da basuje ba don kansu ai sun kumayiwa kansune ba wani ba suma matane ai kamarsu ko ? Shina so in fada ka rigani abinda basu kulaba shine maganar da ya J din yayi a lokacin mai tsayi wanda tunda ya kwanta ciwo zance karona farko ke nan da naji yayi magana mai tsayi irin haka ? Haka kuma kariyar harshen nan nasa a ysnzu ya rage harafin bakinsa yana dan fita daidai a cikin yan kwanakin nan tunda ya soma zama da mikewa din nan . Sai dai kuma na lura da wani yanayi idan ya mike ko yai magana zaita yin zufa yana dan haki na dan lokaci kafin ya koma daidai. Wanan karon ma hakan ne ya faru dashi idon dana kura mai shiyasa mama fadin daidai habu din yana mikewa tsaye tace. Kazo har ka saka dan uwanka magana yau yaran nan da abin dariya kuke wallahi kowan ku a nan ya shigarwa matarshi ke nan ko ? Muryan iyace ya katseta tashigo tana fadin yanzu saratu kece muna gaka nan ka shigo nasan fita zakayi abin ka kuma yasa na taso. Iya fushi fa nakeyi da kowa gidan nan yanzu fisabillahi iya ace har dake matana ta haihu bakije kin zauna da ita ba kina gida abinki zaune iya ? Yi min adalci mana dan nan iya din ta fada a marairaice tana wani irin lagabe kai tace yaron nan yana haka ai in nabar gidan nan sai a zageni ? Hakane yanzuma aida nashigo anan din na sameki bakomai ai iya don kawai na dauke iyalina mun bar gidan nan shine kowa ke fushi dani ko ? A,a habu idan kowa yayi fushi daku kasan bandani a cikin shirmen nan wanan abin dana fada shine kawai dalilina amma kai min aikin gafara gobe zan je insha Allahu in rai yakai. Sun dan jima suna zance dashi ya fita bai kara bi ta kaina ba nima ina zaune ban daga daga inda nake zaune ba tare da iya ya fita mama kuma ta mike zuwa bandaki . Hannu ya miko min alaman inzo inda yaken zaune banki ba na mike zuwa gareshi na zauna a gefenshi ya soma fadin kina son raina ya bacine Rahama. Fushin nan da kikeyi da kowa ya isa hakana nine mai laifi ba wani ba kuma nabada hakkurin ai niba fushi nakeyi ba na bashi amsa ina kokarin mikewa sai kuma na koma na zauna ina fadin. Na kula kamar maganan ka yana son dawowa daidai amma kuma kana wahala ga hakan don zufan da naga kanayi da yawa yace haka nima nagani . Saidai gaskiya ina jin saukin jikin nawa sosai a yan kwanakin nan karfin jikin daine sai a hankali amma Alhamdullahi gaskiya. Na lumshe idona ina tayashi yin tasbihi ga ubangiji subbahanahu wata,ala daya nufemu da ganin hakan . Wa zaisa bawan Allah nan zai mike haka yau shine Allah ya tayar a cikin ikonsa haka har yake iya wasu abubuwan daya shafi rayuwan sa dana iyalinshi haka. Muryan mamace data leko tana fadin to kina ciki bari na leka wajen dubu ance tana fama da kai yau tun safe data shigo bata dawo nan din ba . Hakan ya kawar da shirun namu da yake fadin agaida mama din ni dai bance komai ba don nashiga na samesy zaune da saratu suna magana da ita da saratu nagaida ita naga ta amsa min a dakile. Na saba da hakan da mama ke min tun abun yana damuna har yanzu na share na fitar da komai a raina abu dayane kawai ina kare abinda zaisa ta taba min mutuncina. Iyakarmu gaisuwa inma tazo waje ina kokari na kaucewa wajen don gudun samun matsala a tsakanin mu a bakin maman tudu na kara fahintar wasu halaiyan mama din daya kara sa nake taka tsantsan da ita. Mun jima a tare dashi dakin zaune kafin Anty Asmau ta shigo da yara suka zauna suna hira hakan ya bani dama samu na mike nabarshi dasu na fara gyaran part din dana gama kuma wanka naje nayi na fito. Saida darene mama ta samu daman yi min fada sosai kan nayi hakkuri da yar uwata kada na yarda aji kan mu har a gane muna da matsala tundai saratu taji zancen zai juya wani abu na daban a bakinta . Na fahinci ba saratu ba har salima mama tudu ta tsana acewarta mahaifiyarsu ta sagartasu sunki aure suna abinda suka ga dama a cikin gida zaune. Dole washe gari na shirya na tafi saidai ban barta ba don yadda nayi kuka itama saida na sakata yi don na fada mata abinda ke zuciyana. Inda ta nuna ba hakana bane wai mijinta ya hanata fita saboda matsalanta yasa ta kiyayye dole dai na zage nayi abinda ya dace ace nayi a wajen duk da karfin hali nakeyi a lokacin. Saidai nasha zunde da sheri a wajen yan uwansu a ranan kowa da kalan sherin da yake min akan cikin dana samu a yayin jiyar miji ni dai nawa kawai murmushi. Ban dawo gida ba kamar yadda kowa ya zata daga gidan ya habu gidana na nufa a ranan a can na kwana don ina son gyaran gida nida Anty Nafisa da wata yar yaya Auwal mukazo gidan muka kwana. Koda mama ta kirani a waya nace dasu gani nan gidana mama ina son inyi gyaran gidan ne duk yayi kura yana bukatan gyara take fadin ga mijin ki nan yana fada dake hakan baisa na dawo ba a ranan saidai nayi mata bayani maganinsa daya dace a bashi na shafawa kuma su san yadda zasuyi. Ba komai yasa na koma gida ba sai gulman da akai min kan wai ina ha,intar kishiyoyina na fake ga sunan jinya na karbe masu miji dama mu fulani haka muke da kwatar maza . In badon cikin daya baiyana min a jikina ba da ba,a gane muna cutasu gashi najawa Saiba saki saida ya fara samun lafiya nasa an sake ta saura Asmau itama in batayi hankali ba korata zanyi in zauna ni kadai kamar yar uwata. Naji dacin wanan maganan sosai da naji hakan yasa na yanke shawaran komawa gidana tundai da naji ance Asmau dince take fadin wai sun zama yan kallo yanzu basu gane komai a gun yaya din dul na tare komai banson kowa yazo kusa dashi saini kadai ashe mun san abinda mukeyi ni dashi ? Nasha alwashin duk abinda za ace saidai ace don ba zan koma gidan ba kuma zan dai dinga zuwa in dubashi a can din iya abinda nasa a raina ke nan. Washegari na tashi da aikin sosai su anty nafisa suka tayani a yadda na fahinta kamar ta samu manemi a yanzu din don bini bini sai ya kirata a waya sun dade suna hira dashi. Misali karfe biyu na rana mama ta kira waya tana fadin har yanzu bamu gama bane karya nayi mata nace mama gaba daya gidan yayi kura saida muka fitar da koma ana kakabewa . Da dare kuma ta kira tana tambaya nace mama ina ganin sai gobe don da sauran aiki ban koma ba dai har kwana uku gana hudu nayi abinci da safe na shirya zuwa gidan. Acikin kwaliyata na shiga da basket din abincina tiwon semo da miyar egushi nayi dayaji nama na aje basket din a wajen su mama da iya. Muka gaisa tana min sheri tace kice kin koma gidane da wayau yar nan daga zuwa suna saimu nemeki mu rasa ? To meya rage yaya tunda sun gama aika aikansu dashi kuma ai saita koma gida tayi jinyar cikin yanzu kuma ? Tana jinyar ciki ita daya ga miji a nan na mike ina murmushi zuwa ciki na samu yayi fushi sosai dani hakan bai dameni ba na gaidashi da kyar ya amsa min . Duk daya ban tausayi nasan banyi daidai ba don ko kallon dakin kawai da nayi dakin ma kansa yayi missing dina don sai ince bai samu gyara ba daya kai sau biyu. Har wani dan bashi dakin keyi a lokacin zaune nakai ina gaidashi bai amsa ba ya kyaleni nima nayi shiru muryan mamace ke kirana tana fadin kizo ki dibarwa mijinki abincin nan nasan zaici sosai tin shekaran jiya yake maganan tuwo gidan nan an kasa yi mashi. Na mike naji yace No ki barshi ba zanci ba nayi murmushi ina fadin yaya fushi kakeyi dani ke nan bai daiyi magana ba harna fita. Na debo abincin a plate zuwa gabanshi na aje yadda yake kallon abincin yasa na mike na koma na debo ruwa a gabanshi na zauna na fara dibowa ina bashi da kyar na samu ya karba bayan ya gama fadanshi cikin zafin rai yana fadin nasan inba niba wazai samu yana taimaka mashi yadda nake mashi ? A tausashe na soma magana ina fadin yaya ka tuna bafa ni kadai bane matan nan suna da hakki a kanka tunda yanzu ka dan samu lafiya har kana dan iya mikewa ya kamata suma a basu hakkinsu ladan nan kowa fa yana son samunsa don Allah kayi hakkuri in zauna gida itama ta dan taba ta samu ladan hakan . Na jima da loman abincin a hannuna saida na gaji nakai bakina na sake debowa na mika mashi ya karba ya kumaci sosai ya gama na kwashe kayan. A wurin mama nake jin cewa ashe zuwan da Yazid yayi shiya turashi ya daukoni sai yaje ya samu muna gyaran gidan da gaskiya ranan tace dani. Ranan munga tashi hankali ai na zata ai inkin dawo zaiyi fada sai kuma naji shiru koda yake dubu ta taka mashi burki ai tayi mai tas tace ya barki mana idan zaki koma can ne ki koma da yake fadan mu nan ba mutane bane a tare dashi ? Ko ita Asmau bata iya mashi komai da kike mashine ta dai kwana nan din sau biyu jiya banga tazo kwanan ba wai danta baida lafiya tace . Oho dai na fada a raina ba dai zan zauna ba kuma a nan na wuni na gyara masu ko ina tas na shiga wajen kowa da yamma kuma nace ni zan tafi kada yamma yayi min. Kallona yayi Asmau tana zaune ba daman yayi wani abu yace saida safe kawai saiga iya take fadin yanzu dai kinyi hijara ke nan kardai kin gudu ke nan fa ? Iya gara ingudu inbarwa anty mijinta tunda ya samu sauki a yanzu itama ta samu nata rabon na tare waje da sunan jinya na hanasu ganawa da mijinsu yadda suke so . Kamar yaya kin hanasu ganawa da mijinsu yanzu ko da aka ga idanunsa sun bude aka san wanan da kikai wahalan ki a lokacin wayace zai kama maki hakan ? Gulman nan yazo kunneki ke nan don wanan dama kika koma can ke dai ai gulman nan ya jima da fita gidan nan yanzu da kika tafi din waya iya abinda kikeyi masa din ina zaune yake cikin takaici da kazanta kawai ya isheshi gidan nan . Zai dai tattaro ya cin maki can mamaku ma tace gida tayi tunda Allah ya kawo sauki na hanata tafiyane don in kun tafi gaba dayan ku abin bai dadi gara dai ta sauna har akwana biyu. Banda gulman me suka iya sunan son miji ne kawai abaki amma babu hus a garesu mutum bai kula da kansa ba balle wani saida yazid yayi cin mutunci yadda suka bar gaban gidansu da kazanta dazun . Murmushi nayi na saba gyalena ina fadin ni zan tafi shiru yayi kamar bai jini ba a raina nace kaji dashi ba dai zan zauna ba din a kara zagina duk a yanzu dai zagin bai kankaruwa a gareni ba riga dana shafawa kaina wanan kuma ? ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/17, 08:44] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 7️⃣6️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Haka abin ya kasance duk da ya nuna baison hakan dana yankewa kaina amma saina dake da safe zan shigo inyi mai duk abinda na sabayi idan yamma yayi kafin magariba saimu koma gida da Biba ko anty Nafisa. Tun yana daure fuska idan nazo har yakai ya dan sake ya fara daina hakan da yake min ina daga ciki tare da mama nake jin hiran mutanen gidan dake zaune falon da ake jinyasa din salima ke fadin. Kefa Asmau na kula kwanan nan sai wani sheki kikeyi kina wani budawa meye sirin hakan kuma ? Koda yake duniya taki yanzu an watse an bar maki miji ke kadai kina shanawa ba dole kiyi sheki ba haka ? Wani anbar mata miji a ina saida aka gama abinda za ayi don dai ita bata san zafin kanta bane ai ina zan zauna mace na shigo min gida tana min feleke da yanga ana iskanci da sunan jinya wallahi ba a haifi wanan yar ba tukun . Komai sukayi ai don kansu saratu balle ma me akeyi duk abinsu dai basuyi da ranana balleni kome zasuyi yanzu ai na saba da ganin hakan akan mutumiyarki Nusaiba bai kuma daga min hankali ba balle wanan din. Sai naji salima tace ballema me akeyi maganan kice dai kawai saratu da wani tashin tashin dinki can daza ki kawo za,a hanata zuwa duba mijintane kuma ? Wayace za,ya hanata yanzu don Allah ni dai banson abinda zai hadani da wanan yar kauyen yarinya dake ganin daidai take da kowa yanzu gidan nan. Jin nayi shiru ina saurarensu yasa mama soma fadin zaku fara takale takalenku ko ku jawa kanku zagi a karshe a juya maganan kuma . Ko yaushe ina muku fadan irin wanan maganan dabai shafeku ba amma baku jin kashedin da nake maku ina ruwanku da shanawanta yanzu kuma ? Sallon ku hada wani fadan kuma kenan a yanzu tsakaninsu ana zaune kalau maman tudun wadace take fadin hakan a garesu rai bace. In sun jawo magana ai suji dashi ni ina ruwana tunda ban aikesu ba sun daiji abinda yazid ya fada game dasu ai ya karya yarinya ba wani abu bane wajenshi. Ballema mama waye zai dauki zancen su tunda ba sakarai nake ba kawai dai magana ce mukeyi sai kawai saratu din ta mike tana guna guni ta fice . Ashe fadi take don an mayar da mutum baiyi aure ba za a dinga mashi abinda akaga dama karya ta fada ba cin amanan akeyi ba inba hakaba ya akayi tayi ciki yanzu ? Na jima a zaune nayi shiru kaina kasa gaskiya wanan mace tana son shiga min rayuwa duk dana tattarata na watsar gefe daya iyakata da ita gaisuwane wata rana kuma bamu ko gaisawa din da ita haka zamu share juna. Tace ita danyar kai nace na fita muje zuwa sai hakan da nake mata kuma a yanzu ya koma bata haushi tana jin kamar ta shakeni ta kwantar. Wai ashe bayan tabar part din takoma nasu shine taje ta kira saiba a waya tana labarta mata duk abinda aka fadi abu ga mara hakkuri saiga saiba din ta kira Asmau tana zagin ta. Muna ciki din mukaji Asmaun na fadin ita saratun din tace hakana wai meyasa saratu keda tsegumine wai ? Shiru daga ita har mu wajen yayi can ta soma fadin Nusaiba na fada din ina ruwana da duk abinda zasuyi ke bakiyi min wanda yafi wanan din bane aiba karya na fada ba ko ? Mama tudu ta mike ta isa tana fadin wai meye kuma yanzu ita yarinyar nan dan maganan nan saida ta kira yarinyar nan tun ba a bar wajen ba ta fada mata ? Anya kuwa saratu kanta daya kuwa da wanan halin ke mara kunya an fada din ai idan bakiyi ba ba zata fada ba ai wanda ya mutu akewa karya. Mikewa nayi na fara hada kayana don tafiya kallona yayi yana fadin ina kuma zaki yanzu na amsa da gida rai bace ban yarda na kalleshi ba. Abin yana ban haushi duk da nasan yana cikin halin ciwone a yanzu amma kuma a yadda na fahinceshi shine gaskiya duk cikinsu kamar kannensa sunfi raina shi don me zatayi ta min hakan ko watan mu ya kasa daukan mataki idan kuma ka dauka da kanka abin ya zama laifi a gun mahaifiyarsu. Ganin ban kulashi ba yasa shi fadin ke Rahama kada ki bari raina ya baci dake gurin nan badake nake magana bane wai ko sunyi dakene yanzu ? Jin abinda ya fada yasa na kara dagowa na dubeshi cikin mamaki banga laifinshi ba kila son yana namiji yasa bai fahinci zancen daga farko ba. Ko kuma wata kila baiji farkon maganan tasu bane sai tsakiya yasa yake fadin zancen bai shafeni ba ai ni dai na hada kayan na koma falo na zauna na barshi nan. Tunane nakeyi a raina ya zama dole nasan yadda zan daukarwa saratu mataki ta daina aibantani ga bakinta a yadda na fahinci maganan ta dai shine. Ina fakewa da cewa ina jinyar yaya ga hakan na shammaci abokan zamana ina kwana da miji ni kadai har ciki ya shiga ba yau ta fara fadan hakan ba karo na biyu ke nan da irin hakan ya faru. Wata rana muna zaune a haraba ana hira ake bada labarin wata wai bata da umma asalinta me saratun zata fada daga inda take zaune tana dakilan waya sai cewa tayi ai ance basu bane shegu. Shegu suna gidan aure inda ake daukan kwanan wata a samu ciki a haifi mutum wanan dan da aka haifa ya zama shege sune shegu na asali da akasani ba wai wanda aka haifa a wajen iskanci ba haka ? Wanan abin ya tsaya min a rai tun lokacin duk da maman tudu ta tsawata mata don ta katseta da fadin to malama inji wano nafsin ya baki wanan fatawan kuma ? Kinhanki saratun nan a yanzu kan gaskiya baki iya zama babban gidan mu saidai ki koma rabe rabe a nan tunda har kin san wanan kikaki kawo miji kiyi aure ki huta. Ai mama Allah ne bai kawo mijin bata fada cikin tsigar rashin kunyarta datakewa mutane nan mama ta rufe ido tayi mata tas a lokacin tace sai inci ubanki wajen nan niko uwarki bata fada min maganan banza haka ? A wanan lokacin har mama tayi fushi tana fadin gida zata koma bata zama tana kallon wanan fitsaran haka saida sukai ta bata hakkuri shine yazid ya kusa halakata din a lokacin sai kuma wanan karon da ta sake maimaita abin shigen hakan. Tunda na zauna a wajen baiyi magana da kowa a cikinsu ba ga Asmau sai maimaita abinda Saiba ta fada mata takeyi amma hakan baisa na tanka masu ba don zuciya daya zo min a lokacin. Ba karya nasan ina da wanan zuciyan wanda idan nace zanyi magana a lokacin tabbas hakan zai iya jawo muna gagarumin rigima a ranan. Saidai kashh jin yadda Asmau ta matsa da zancen har take fadin indai don wanan da akeyi yanzune ai ba ai komai ba balle ko a gabana akeyi hakan bai taba damuna ni. Ai yin ma isace idan fitsari banzane kaza tayi mana Allah ne sheda ta koda hakan ya faru nasan kaddaratace a hakan amma a cikin kiyayyewa nake don ni din ba jahila bace kamar wasu nasan abinda nakeyi ban shiga hakkin kowa ba har na samu wanan cikin . Da za a zauna ana fada min magana inma shegen ne nayi tare da yayanta muka aikata hakan don ba zina naje waje nayi ba balle a zauna a fada min magana haka kamar nice farau. Sai a bari tunda yaya yana kwance nayi cikin idan na haihu aje asibiti a auna dan idan ba nasa bane sai a ban in tafi da abina . In kuma nasane zan shayar daku mamaki a gidan nan don sai nayi karan saratu a wajen hukuma na bata min suna da take kokarin yi a gidan nan. Yau dai ko saratu kishiyatace ya tsaya a hakan irin abinda take min kawai ta koma can gidan takama daki daya mu zauna a matsayin kishiya da ita insan zaman miji daya mukeyi da ita a gidan nan. Naji ina cin amanan su saidai zaki bada dalilinki gobe gaban Allah don ba yafe maki zan taba yi ba saratu sai kin fadawa Allah cin amanan da kika sheda nayi masu a gidan nan. Ke kuma Asmau indau zuwa duban yaya da nakeyi gidan nan ne na daina daga yau ba zan sake leko gidan nan da sunan gaidashi ba balle na kwance maki mijin ki duk ranan da Allah ya bashi lafiya in zai iya zuwa gidana yazo idan ba zai iya ba kuma yasha zamanshi nima nagaji da wanan wahala haka . Na juya zuwa ciki na kwaso kaya ban ko kalli inda yake ba balle su mama get din gidan na nufa na fice ban sake juyowa na kallesu ba . Yau nasan yarinyar nan tsatsan bafulatanace ashe haka ai basu iya fada ba ransu bai iya baci ga abu ba to yanzu dai ankai ga yadda ake so ai ina kula yarinyar nan ko zuwa tayi gidan nan an kama sakin magana ke nan ana mata haibaici tana sharewa tun farkon lamarin nan . Shin garekune farau zama da matan yayyu koko kun zama yan idone da ba a kwaba muku ku auren dai ai kowa zaije yayi yaji abinda ke cikinsa. Ba yarinyar nan ba koni yau zan bar gidan nan tunda Jafaru ya fara samun lafiya nake ganin abubuwa daban daban daga gidan nan hadewa kawai nakeyi . To Alhamdullahi tunda Allah ya bashi lafiya a yanzu Allah ya kara mikar muna dashi lafiya amin daga kofa ya dogaro yana fadin ta wuce ko ? Maman tudu tace dole aita wuce tunda sherin har yakai na sheganta mata abin cikin cikinta a gabata kuma ba a dauki wani mataki ba ko nice ai zanwa kaina gata. Saidai ku sani yau abinda baku sani ban kan yarinyar nan tayi abinda duk cikin mu nan kaf babu mai iya yinsa ga yaron nan. Itace zata hana kanta barci ta kwana tana masa karatun kur,ani tana sallolinta tana bashi magani tana tofeshi ko yaushe ka falko kana iskata a kan shi tana mashi addu,a. Tau ku sani idan jinyar yaron nan ya koma kasa kada kuyi kuka da kowa kuyi kuka da kanku wallahi don daku aka hada kai aka koreta a gidan nan yau. Dama makiran kishiya tafi mai fitina hatsari don gara mai fitina tana fitowa fili ka fahinceta amma wace ke sari ka noke itace guba mai cutarwa farat daya. To yanzu fissabillahi yaya daga dan maganan fatar baki saita kwasa tayi fushi tana fadin magana haka dama dai ai sallon ta samu hanyar kubucewace tayi don ta nuna ta gaji hakana ? Yanzu idan bata zo ba sin yadda tace ai zai nade ya bita can din inda ta saba cin karanta babu babbaka ana kallonta can ko sai abinda taga dama tayi. Itama yar kauye tasan tayi wanan shirin ga mutane balle muna da aka haifa a cikin gari taje wa zuwanta ya dama a gidan nan koda ita ko ba ita in Allah ya bashi lafiya sai ya mike da yardan Allah. Kaico iya dake tafe tana gyara daurin dan kwalinta take fadin haka badai da abokiyar zaman naki ba kuma kike wanan abin kunyan haka ? Aa,ha iya badani bace da dai sarakuwartace da yaranta tunda su ba ai masu fada nikan ai kafin nima su koreni din yau zan koma dakina insha Allahu kar abin ya juyo kaina yanzu kuma ? Yaya sai kinso saka kanki cikin zancen nan gaskiya don wallahi dai bada ke akeyi ba kin sani yaran nan kuma kin dai san dan yau banice zan turasu sunawa matan dan uwansu haka ba ? Wai sai meyasa matan jafar ne ko kafin yarinyar nan ta auri Jafar ai yar uwarta habu ya fara aurowa gidan nan da zaku dauki karan tsana ku sakawa yarinya guda duk kokarinta ga dan uwanku. Aike Amina baki sani bane dan uwanne nasu basa so shiya kawo haka kiyayyan jafar dasune ya shafi amaryansa . Haba iya in antashi magana kiyi ta hadawa dani don Allah ni yanzu mena cewa Rahama anan daga muna maida maganan zagin da Nusaiba tayiwa Asmau shike nan fa tayi fushi inma maganane ai ita Asmau itace ke fadin magana da har ya shafeta ni meye nawa a cikin zancensu. Tun bayan fitana daga gida kuka baizo min ba asalima taxi na tare zuwa gidan saidai inata faman sakawa da kwancewa a kasan raina. Ina shawaran barin garin a ranan in nufi abuja ko adamawan cameroom gun yan uwan mu zaifi min sauki a rayuwata sam ban taba nasa cewa zanwa wani shige shige a wajen boka ko malami da sunan in kuntatawa wani. Amma sai gashi ban tsira wajen sherin abokan zama ba kullum duba sukeyi ina da asirin da nakewa mijin namu yasa bai yarda yaga laifina. Duk magana idan zai taso nice wai za a bawa gaskiya na sani ai na kuma san irin azaban da Allah zaiwa mutum. Nagama komai na shiri kwance na dawo falo don in danci wani abu duk da bakin nawa ba dadi a lokacin amma haka nake daurewa kamar yadda manyana suka fada min. Ance in daure ko bakina ba dadi in dinga cin abincin ya kasance ina da kuzarina dan kada na lalace abin cikin cikina kuma zai wahala . Fruits din dana sayo a hanya da zan dawo na yanka nake sha naji bugun kofa don munyi da Biba saida safe zata dawo ranan don haka ni kadai ke nan zan kwana a ranan sai megadin gidan dake waje. Daga ciki nake tambayan ko waye muryan ya Yazid naji yana fadin bude mune da iya hakan yasa na dauki gyalena dake gefe na yafa akaina na bude kofan. Shida iyace sai matarshi da yaransu sukazo na danyi murmushin dole a fuskana ina fadin kune a gidan yau ? Ba doleba ance amarya mu tayi fushi harda rantsuwa ba zata sake taka gidan muba murmushi yake na komayi ban daiyi magana har lokacin. Muka samu waje muka zauna dukkan mu a falo na mike na dauki sauran fruit din a cikin fridge din na kawo masu sai bin ko ina na fidan sukeyi da kallo. Iya ke fadin kagani ko na fadama ko acan din tauye take don laluran nan ne kawai yake kaita amma yaran nan yau saida suka kure hakkurin yatinyar nan. Ai tunda nadon su takeyi ba iya ba zatabi ta nasu ba tace bata kara zuwa ganinsa yanzu gashi can kun barshi ya rikice bayan tafiyan ku ita mama tayi fushi ta wuce gida ke kuma kin dawo nan ke kadai ina yarinyar da kuke zama da ita din ? Saidana hade wani malolon bakin ciki nake fadin tana gida yau yar uwarta ta haihu suna suna sam banyi tunanen zaki bari suci galaba akanki ba ai tunda kinsan da gaiya suke abinsu. Kowa yasan meyasa Saratu take hakan ni dai na dauka ba banza take hakan ba don ban taga ganin inda mutum yaki dan uwasa ba haka ? Amina tun bata kai gida ba nasa aka dawo da ita kema munzone da safe idan Allah ya kaimu ki shirya yadda kika saba kizo ki duba mijinki kinji na amsa masu tare da godiya. Sun dan jima a zaune iya ta matsa akan su tafi dare yayi don sam ita bata fitan dare wanan fitowan ma ya kanane haka. Nayi masu rakiya akan washegarin zan shigo suka tafi matarshi sai bina da kallo takeyi kawai don hausan a lokacin take koyonsa. Bayan sun wuce ina shiga daki na jawo dan jakkata na hada kayan bukatana a cikinsa nayi ready komai na saka a jakar safiya kawai nake jira a lokacin. Barci sama sama nayishi a ranan don abinda na yanke a raina gidan ga baki daya ya fice min a rai abin cikin cikina kuma yana ban tausayi. Don nasan haka zai taso da kalubali idan ban dauki matakin hakan ba tun yanzu don haka dole in kauce in samu a daukar min mataki akan saratun nan da kowa ma don har mama gaskiya. Washegari sallah kawai nayi na zauna addua na jira gari ya dan haska na fito inacewa maigadi zani can gidan kila in kwana biyu a can din waman zuwan. Yana ta min adawo lafiya yana gaida maigida shiya tare min keke na hau ina sauke ajiyan zuwa dana bar wajen muna fita titi nacewa mai keken kaini tasha in shiga motan kaduna. Ya dauki hanya sai tasha din muna zuwa ga mota saura mutum biyu zuwa kaduna na sallameshi na biya kudin mota na fada. Saiga cikon na karshen yazo muka daga na sauke ajiyan zuciya ina jan hijjab dina zuwa hancina saida muka bar zaria na sake gyara zama ina lumshe idona. Mai karatu abinda yasa banje abuja ba son zuwan dasu daddy sukayi na nuna masu zan daure da duk wani abinda zan gani amma yanzu na kasa hakan . Gara inje wurin ummah zaifi min duk da banson zuwa gidan nasu don yadda mijin nata yake like da ita kamar wasu yara hakan kan ban haushi idan na tuna da mahaifin mu da basuyi irin wanan rayuwan barikin dashi ba haka har ya tafi kullum shi yana kofan gida yana tsaro wajen aikinshi ko in daddy yana gari su fita tare dashi din. Amma shi wanan ya samu wanan daman da mahaifin mu bai samu ba Allah ya gani ina taya mahaifin mu kishi a kansa gaskiya. Ashe yazid ya biyoni zuwa gidan ya daukeni ya samu ban gidan maigadi ke fada mashi ai tun safe na fita da jakata nace can gidan zani a lokacin. Gidan mu tace dakai zata ni yanzu daga gidan nake ai fitowana ke nan nazo nan don jikin mijin nata ya dan tashi subbahanallahi maigadi ya fada ya dora da fadin har da jakar kaya ta fita ai nina saka mata a mota don tace wanan karon zata kwana biyu a can din. Waya ya daga ya kira yana tambaya ake ce mai to ban iso ba ya juya ya fita sun kira wayana a kashe yasa suka kira Maria ta dauka cikin sanyin muryan nan nata suka gaisa bai tsaya ba yace ko amaryan J tana wajenkine sister ki ? Rahama ta fada cikin mamaki ta dora da fadin wallahi bata zo nan ba ai mun kwana biyu gaskiya yake fadin habu bai dawo bane ? Ta amsa maida yace sai jibi zai dawo bai tsaya ba ya kashe wayan ya karasa gida sun ta maganan maman tudu ke dadin dama nasan zatayi gaba tamayi kokari tunda har takai war hakan. Bafulacene zai tsaya ana gardaman abinda yake da gaskiya a kansa tayi kokari dama ta zauna ai tunda tana son mijinta yanzu dai kubar zancen nan kada yaji don Allah mama ta fada. Basu sameni ba sai zuwa yamma nayi barci na tashine suka sameni kira ukku na dauka da sallama muryan yazid ne yake fadin Amaryan J kina ina don Allah ? Hanyar garin mu na bashi amsa na kashe wayan ban tsaya saurara mashi ba don ban son yawan magana tunda mun kwasa da ummah tun isowana. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/17, 08:44] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 7️⃣7️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Ban san ya akayi ba ummah ta kira Maria ta sheda mata ina kuduna wurinsu nace daga nan kasan mu zan tafi amma sun hanani tafiya gida. Hakan yasa hankali a tashe maria din ta dinga lalubar wayana ina ganin kiranta na shigo min naki dauka a karshema na kashe wayan nawa gaba daya. Ina nan dakin ummah kwance sai gata da waya tana fada min in karba yar uwatace a layin, fuska na bata ina fadin banyin magana da ita a yanzu ummah. Kina da kafuwa Annini ita meye hadinta dasu da zaki ki fada mata damuwanki kuma ko baki fada ba ki karba ku gaisa mana da ita. Dole na mika hannu na karba ummah ta juya ta fita daga dakin ta batmu muna waya ina dauka a dakile nace hello naji tana fadin Ramaah baki kyauta min ba yaya zakisa kafa ki fito gidan mijinki bayan kinsan yana kwance ba lafiya. Kin kuma san yadda ya samu dake a zuciyarsa dole in kikai hakan ya shiga damu gashi ko ya shiga damuwa din don ana kokarin boye masa tafiyan ki har yanzu ya gane abinda ke _fa_ ruwa. To ya gane mana Maria ke kika damu da hakan ni yanzu ta kaina nakeyi bata shi ba don gara dashi yana gaban kowa nasa a gabanshi kuma akeyi min abinda akaga dama bai dauki mataki ba kin kuma sani. Haba Rahama wani mataki kike son ya dauka shida yake kwance bayan haka kinfi kowa sanin yadda suke tsoron mahaifiyarsu ai dukkansu mazan matan ne dai basu faye tsoronta bama nake gani. To suje can suyi ta jin tsoron ta ni ban sake komawa gidan nan wallahi da sauri naji tace ki daina rantsuwa don Allah haka Rahama idan baki koma ba yaya zakiyi da cikin jikinki ke nan kuma ? Nace ciki ciki ai zubarda shi zanyi don ba zan yarda in haifi cikin da zaizo duniya yan uwan ubansa na kirasa da shege ba . Ke Rahama wanan magana ina ya fito kuma nace a bakin Saratu don tace ba a shege waje sai a gidan miji macen data hada kwanan yan uwanta tayi ciki wanan dan ake kira da shege. Innalillahi ta fara ambata tana fadin ita Saare din ta fadi hakan gareki lalai kuwa inta fada akwai magana ke nan gaskiya amma don Allah ina rokonki da kada ki taba cikin nan don Allah saina kashe wayan don takaici daya rufe min zuciya. Sam ya J da kowa nasa har maria dake tare dasu a yanzu sai naji gaba daya sun fice min rai lokaci guda ina dana sanin saninsu ma baki daya don yadda nake ji din. Zuciyana ya dake sosai ba wani zancen kuka a gareni yanzu kawai solution nake nemawa kaina a yanzu wanda kuma zuciyana yafi yarda da in zubar da wanan cikin kaddaran dake jikina lokacin. Kwanciya nayi na lafe muryan ummah yasani dagowa don tashigo tana fadin ki tashi ki saka wani abu a cikinki tun dazun kina daki dunkule. Wayarta na miko mata na dago daga kwancen da nake ina jingina da gado ga abincin nan falo ki fito kici ki watsa ruwa ta fada a cikin tsigar umurni a gareni. Bin bayan ummah din nayi da kallo ina son in fahinci fushi takeyi ko goyon bayana don tunda nazo bata furta min komai ba. Kuma tana falon nayiwa mijinta bayanin zuwana din mikewa nayi zuwa falon inda na hango abinci a kuloli tsakiyan falonta waya takeyi daga kofan dakin ta juyo tana kallona kafin ta karasa fita daga falon gabaki daya. Abincin na bude inda naga shimkafane da miya sai ganyen salad amma miyar na kifine ko ta manta cewa ni bafulatanan asalice ban damu da kifi ba oho ? Su sun iya ci a gidan daddy Abuja tun wani ciki da tayi a yadda take fada muna a baya saini da Abban mune bama son kifi dan gara danima nakanci miyar kifi din wani lokaci ba tare da nayi amanshi ba . Shiko mahaifin mu har ya rasu sam baya cin kifi a rayuwansa na gwada ci din duk da budewana naji yana hawa min kai amma haka na daure na kai a bakina. Kamar kada ya sauka a cikina da sauri na mike zuwa waje dakin inda keda kasa da fulawowi na duka na fara shega amai na fitan hayaci. Sai mai aikinsu ummah dince tazo tana faman yi min sannu daga inda ummah din take taji kakarin aman nawa ta fito da sauri tana tambayan yaya haka kuma ? Na kasa bata amsa a lokacin don yanayin aman da nakeyi din saida ya dan sarara min suna tsaye kaina don har mijin nata ya fito yana tambayan ba,asin aman ? Na lalaba na koma zuwa daki na zauna a falo ina maida numfashi ummah ta shigo ta zauna takara min sannu kafin ta dora da fadin kardai wani abu kika sha don sakarcin da kikeson yiwa kanki ? Idona na kasa ina karewa jan lalen hausa dake kafanta yayi kyau ya karbi kafan nata da kyau na dago a cikin mamaki ina binta da kallo. Sake maimaita tambayan tayi daidai mijin nata yana shigowa dakin ga yar aikinsu a bayanshi dauke da ruwan sanyi ta kawo min shiya cabe tambayan da bata amsa . Yana fadin haba dai har me zata iya yi yanzu kinsan mai karamin ciki da jin tashin zuciya ai na sauke kaina kasa a ciki kunya na nuna mata abincin dake cikin plate din tabi da kallo. Kafin tace abincin bai maki bane in badon ummah bace sai ince tayi min ba daidai ba wallahi wanan tambayan don tafi kowa sanin bancin kifi tun fil azal a rayuwata tundai wanan na tekun mai bakin karnin nan haka ? Bai mata bane nasan tsohon ya fada yanawa kansa matsuguni a daya daga cikin kujerun falon a kasalance na basu amsa da KIFI ? Kifi ta fada a cikin mamaki tana bina da kallo muryan na gwada mamakin hakan tace dama har yanzu ke baki cin kifine Rahama ? Kaina gyada mata tace sam na manta wallahi na zata ai ta daina wanan matsalan na rashin cin kifi a yanzu tunda naga an dade ai ashe matsalanta guda da mahaifinta. Ai dama na fada maki akwai dai wasu sam basa son kifi a rayuwan yanzu me zataci ke nan ko akwai abincin da ba kifi a bata taci ? Yanzu aka dora abincin dare ummah ta fada sai tsohon ya mike zuwa part dinsa ya dan jima sai gashi da furan gora mai sanyi ya kawo min yana fadib ko zata sha wanan din a gwada a gani ko zai tsaya mata. Shina karba nasha na gama na koma daki na kwanta ina lumshe idanuwana rayuwa ke nan rayuwan yanzu sai a hankali yau wai ummah ce zatace ta manta da wasu halaiyan mu na baya data san mu dashi. Ina jin muryansu a falon da alama waya takeyi don naji shima tsohon ya karbi wayan yana fadin haba dai ta dai fadane ai akan me zata zubar da cikin dake da ubansa ? Bacin raine kawai yasa ta furta hakan amma ai Rahama yarinya ce mai hankali kawai dai sun tabatane take son ta rama abinda sukai mata din. Can naji ya koma fadin haba dai ba inda zamu barta ta tafi tunda tazo nan ai shike nan ku barta din ta huta hankalinta ya dawo daidai kawai ? Hawayene suka gangaro min a idanuwana naji wani bakin ciki ya tokare min zuciya da niyata shine in samu da safe in karasa inda na nufa don banda niyar zama wanan gidan gaskiya. Saidai nasan wa yan nan kattan sojojin dake gadin get din gidan yana dawuya in fice wani baiga fitana ba a cikinsu don haka na fara lalubo hanyar da zan gudu nan din don bansan illan daya kaini tsayawa a nan din bama da har na tsaya. Wana furan dana nasha ya rike min cikina bayan nayi sallah magaribane ummah ta shigo tana fadin kada inyi barci fa in tashi inci abinci nakoshi nace daga kwancen da sauri ta kalloni tana fadin me kikaci bayan furan dazun ? Shiru nayi ta koma fadin ki tashi ga Saudi nan tayi maki miyarki daban na nama kici abincin dole na tashi zuwa falon nata. Tuwon shimkafane miyar kuku yaji daddawa da kayan yaji kamshi shi kawai zai sanarma da hakan tsaye tayi a kaina tana fadin ko bai maki bane miyar ? Na dago a hankali ina kallonta a sanyayye na bata ama da yayi min ina lasan miyan tace to kici don Allah kada ki zauna da yunwa don Allah kinsan yanzu bake kadai bane. Ki kula sosai ko baki son abinci ki daure kici don Allah kada lafiyan ku ya tabu daga ke har abin cikin cikin naki kai kawai na iya gyada mata ban iya amsawa . Har zata fita sai kuma ta dawo ta zauna tana fadin ke banda abinki Rahama me zaisa ki bar gidan mijin ki saboda wasu yan uwansa can ke baki ga yadda yar uwarki ta koma masu kurma bane tunda ta fahincesu. Nasan ba haliku daya da ita ba duk da hakan ya kamata ace kin koyi hakkuri hawaye suka soma zubo min ga loman tuwo a hannuna. Falon yayi shiru zuwa can ta mike ta fita tana kiran saudi mai aikinta wai tazo ta zauna dani zata duba tsohon mijinta abinsu a yanzu ya daina ban mamaki. Nasan sauyi rayuwane Allah ya kawowa ummah a yanzu yadda tasha wahala rayuwa a baya saudi din tazo ta zauna dani a falon tana dan jana da fira sai dai ban saki jiki ba. Ta soma fadin wa yan zaria ai ai kasan halinsu kake iya zama dasu kina ganinsu kamar gidadawa sai kin zauna dasu zaki fahinci bakin kishi dasuke dashi ga sakar da haibaici ga mutum Allah ma yayi maku gyadan dogo mazan naku suna son ku ai da baku kai labari ba. Haka suke da sa ido ga abinda yayansu keyi da matayensu su koma kamar kishiyo dasu saidai ba a taru an zama daya ba don wayayyun basa haka gaskiya. Banda murmushi ba abinda nakeyi kawai na gama na wanke hannuna ta koma fadin kai gaskiya mijinku dai yaji jiki wallahi wasa wasa fa yakai shekara da rabi yanzu ai nace za a kai gaskiya ciwon ya dade a jikinsane . Tace balle abu ya kasance na jifa ai sai yawancin rai irin hakan son ma dai suna tsayene suma ba a samu yadda ake so ba dashi. Hamma na soma yi hakan yasa take fadin tashi kije ki kwanta ki samu hutu yar nan nima bari na kwashe kayan nan zuwa kitchen hakan ya rabamu da ita ranan na fahinci tana da son surutu gaskiya. Washegari kodana tashi nayi sallah na koma na kwanta abinda ban sababa nayi barcin safe mafarkin da nayine ma ya tayat dani misalin tara da rabi na safe sai nake ganin ai rana yayi sosai lokacin. Mikewa nayi zuwa bandaki ban fito ba saida nayi wanka na tsabatace jikina nafito na shirya zuwa falo ina neman abin karyawa. A falon na samu ummah zaune tana karyawa itama tana waya tun kan na karaso na fahinci wayar dai a kainane har lokacin gaida ita nayi da kwana ta amsa tana fadin. Yanzu nake zancen na tayar dake ashe ki dade da falkawa ga abin karyawa nan ki zauna kici ta fada tana nuna min abincin a bakin table nakai zaune kamar zan bude sai kuma nace daddy fa ya fitane ? A,a manjo ai bai fita ko ina shi indai baya kama ba ko ina bai zuwa shi ko yaushe yana gidan nan dan dama da yamma yana zama ta wajen gidan nan da mutanen unguwa. Balle yau da yasan yana da baki koda fitan ya kamashi ai bai zuwa ko ina sai sunzo sun wuce ban tambaya suwaye bakin ba tunda ba abinda ya shafeni bane. Sai misalin karfe sha biyun rana saiga sallaman mama da iya tare da yazid maria da habu suna bayansu suka shigo gabana ya fadi daki na tashi na koma da sauri don a falo nake kwance ina kallo abinda na dade banyi ba ke nan a rayuwata. Ummah ta kunna min wai in rage rana a nan din tunda ni kadaine bata san hakan baya damuna ba don na saba ko a gidana wani lokacin ni kadai ke zama ai. Sun shigo naji ana gaisawa dasu suna tambayan ina inane tace ina ciki maria ta mike zuwa uwar dakin ta sameni ko kallonta banyi ba a wajen . Take fadin yanzu ke haka yayi maki ai gashi saratu taji dadin hakan can yazid ya kamata tana waya tana fadawa Nusaiba yai mata dan kareb duka jiya ya hade mata haushi biyun ta da yake ji. Dama nayine taji dadin ai abinda bakina ya fada ke nan nace kinga saita dawo da nusaiba din tazo tayi ta haifa masu yayan halas a gidan. Ki bar wanan zancen don Allah jiya aita kwammace da bata fada ba din don yadda akai mata dukka yan uwa kuma sunce wata daya suka bata ta fito da mijin ko suyi sadaka sa ita. Ke jiyafa da yaya J ya mutu wallahi don faduwa yayi harda jin ciwo wai abarshi ya biyo ki ko yanzu ma dakyat aka samu ya zauna don mama tayi mai alkawarin dawowa dake yau din. Cab aiko tayi kaffara don wallahi ba inda zani barin fada maki wanan gidan har shi sun fita raina wallahi suyi da wata kuma badai Rahama ba kuma ? Wasa dai kikeyi kina son bawan Allah nan ya shudene Rahama baki ganshi bafa mama tayi fada duk da bata so laifin Saratu amma tun jiya take kan zaginta gidan nan akace. Su wanan ya shafa ko ince ku amma ni na fada maki ba zan koma ba gaskiya nagaji wallahi neman sanadin abinda zai zubar da cikin nan nasa nakeyi yanzu a jikina na daina tuna komai nasa ga baki daya. Wai kanki daya kuwa Rahama kodai kema din Nusaiban ta hada da kene wajen mallaka ta yamutsa maki hankali baki komawa kamar yaya ? Nusaiba fa kikace Yanda in an fada maki nusaiba zata iya min wani abu ya kamani a duniyan nan baki mussawa ko kin manta dani yar baffa ne ? Saidai ta Allah bata mutum ba kin sani amma mutum ya gwada idan yana ganin haka sai kace ba diyar fulanin asali nake ba muryan ummah ne dake kirana tana fada akan banji zuwansu bane naki fitowa mu gaisa dasu. A daidai lokacin kuma mijinta ya shigo falon suke gaisawa dashi na fito na gaidasu duk sun kura min ido suna bina da kallo ? ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/17, 08:44] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 7️⃣8️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Ya kasance mun shigo falon a tare da daddy muka gaisa nan mama ta soma fadin haba diyata don me zakiyi min haka duk hakkurin da nake baki ? Dukar da kai nayi kasa a cikin jin nauyinta ina wasa da yatsuna ta cigaba da fadin kin kamo hanya kibar min dana a cikin tashin hankali jiya ? Gaba daya jiya sam bamu gane kansa a gidan nan don ya rikice muna ciwo yana kokarin ya dawo saba a jiyan Allah dai ya gyara. Alh ayi hakkuri a bamu yar mu mu yafi da ita don Allah ko zamu samu ya kara kwantar da hankalinsa don in ba komawa tayi ya ganta ba gaskiya yana iya samun matsala. Murmushi daddy yayi ya gyara zama yana fadin ai hjy banki ta takiba don babu iyayyen dake son yarsu ta taso daga gidan aurenta ai gata nan zaune idan tace zata biku din wa,lillahi hamdu udan kuma tace a,a to ba dole don ni banwa yaro dole akan rayuwansa. A,a Alh kada kace haka adaiyi hakkuri shima ya tareta da fadin yes iya gaskiyata na fada don yarana kaf banwa kowansu dole akan matsalan aurensu. Don bani ke zama dasu ba a can amma ba inda za ace asa ido yarinyat dako auren farko batayi ba tana kokarin sheganta jinin dan uwanta amma ba a dauki wani kwakwaran mataki a kanta ba. Inaga idan dan yazo duniya sai abinda taso zatayi mai na wullakanci ke nan don tun jiya datazo da zancen nan da ace nine na haifeta da wanan yar ta kwana a cell . Taje can ta koyi ladabi da kama baki na kwana biyu kafin a sakota saidai za ace don banina haifi Rahama ba a yanzu idan nayi hakan. Alh dan yaune kanayi kamar bakayi in bashi ina wanan zancen zai fito haka a bakin yaro adaiyi hakkuri don Allah an tsawata mata ai. Nan Habu ya tsoma baki yana fadin daddy yarinyar kamar wata mai motsi a kai don tsaban iskancin da takeyiwa matan mu saida na taka mata burki a gidana. To kagani kai kayi mata iyaka da naka gidan gidan dan uwanka ke nan ta koma ashe gaskiya zancen yayi muni ace a bakin yara ya fito bako manya ba ban taba gani ko jin yadda dan uwa zai batawa dan uwansa jininsa haka tun baizo duniya ba ? Yarinyar banzace daddy ayi hakkuri don Allah hakan ba zai sake faruwa ba da yardan Allah kwanan nan duk aure za ai masu su kama gabansu. Kaiya ko kun masu aure ai suna tare daku kun taba ganin inda wuya yabar kai sai gangan jiki kawai ? Yanzu ga yarinyar nan ai a kusa muji ta bakinta na fada maku tun farko ba zan mata dole bani don bani shiga hakkin mutum a rayuwata. Kafin ya rufe baki na amsa da daddy ni gaskiya ba zan koma ba su aiko min da takardana kawai in huta ina fada a cikin kuka sai salati mama da iya sukeyi . Mama na fadin yar nan da bakinki kike fadan haka a gaban mu me mijinki yai maki da zaki yanke danyen hukunci haka tsakanin ku ? Iya take fadan hakan kuka sosai nasa ina fadin iya niba zan koma ba inda ba a kaunata ba kuma ba mai daukan min mataki ga hakan saidai aga laifina idan na dauka ni gaskiya ban komawa gidan nan kuka sosai nakeyi a lokacin. Haba yar nan kiyi hakkuri zancen nan ya mutu a nan ki shirya mu koma gida amma zancen ba zaki koma ba ai bai taso ba mama ta fada. Mama nagajine nagaji nina san abinda ake min kan ya jafar ina hadewa gara kawai in bar gidan zaifi ni dai bani bace na dafewa yaya saina aureshi shi yaje yasa iyayyena suka aura min shi bada sanina ba kuma nayi hakkuri na zauna dashi duk da irin barazanan da nake gani a gidan wallahi ba zan koma ba. Cikin bacin rai don ya nuna min shi wanine a gareni lokacin ya mike tsaye yana fadin Iya ku tashi muje tunda hakane don taji ance ba zata koma ba udan bata so zata tsaya tana muna wanan shakiyancin haka ? Habu ke fadan hakan cikin bacin rai ya mike yana fadin su tashi suje nan dan uwan yace a,a bros ba za ai hakaba dole mu lalashe ta tunda laifi akai mata. Me kake son muyi yanzu tunda an fada mata matakin da za a dauka kan abin tace ba haka ba ba saita zauna gidan ba ban taba mashi rashin kunya ba sai a ranan . Nima a hasale nace dashi a barini mana sai me idan na zauna gidan ai yafi min sauki da zama inda ba asan darajata ba sai wajen amfani . Ko an barni aiba mutuwa zanyi ba hakan ma tafi min dadi da zama inda a kullum laifina ake nema a gorantawa iyayyena don ana daukan mu marasa gata. Rahama ni kike fadaqa wanan maganan yau haka ya fada yana kallona da sauri mama tace kai habu gyara mukazo yi ba barnawa ba don haka kabi abin nan sannu don Allah. Nima shina gani tunda har yarinyar nan tayi haka an dade ana cusguna mata tana hakkuri yanzune take ganin tagaji koma waye gaskiya haka zaiyi. Baiyi magana ba har matanshi shiru tayi shiko ya juya ya fice falon yana fadin ummah nina tafi ke nan sai anjiman ku ya fita. Daddy yayi murmushi yana fadin ga alama nan ya nuna kanshi ko a yanzu yarinyar nan an tabata a rarasheta amma yana son ai mata dole ta koma ? Ba dole yayi min hakana ba tunda kansu hade yake da dan uwanshi amma aishi da aka tasa matarshi gaba ya dauketa yabar gidan a lokacin duk da ban gidan ban huta ba tunda har inda nake ake biyoni aci min mutunci akan gaskiyana. Dashi da jafar din waya taba daukan mataki udan ba iya ke kusa ta tare min ba bagaji wallahi ni ba zan iya ba gaskiya na fada na mike zuwa ciki ina kuka . Ajiyan zuciya ya daddy ya sauke yana fadin wanan abin dole a tsaya a natsu abawa yarinyar nan lokaci don Allah harta sauko don na fahinci ranta abace yake yanzu. Idan munce zamu mayar da ita da karfi da yaji abin ba zaiyi dadi ba gara dai a bari ta dan huce zaifi sauki saita koma din. Abinda nakewa gudu ke nan nasha fadawa dubu hakan tana ganin bai zama komai ko kuma ta dauka ai basu da gatan irin haka yau gashi dai din ya faru ai. Amma na dauka akan Saaratune da abokan zamanta matsalan ai yazid ya fada yana kallon iya iya din tace ai kaji metace ko yanzu kokai matanka ai don suna ciki kullene ko yaushe basu kwasa da ita. Bar dubu inda ka ganta akan yaran nan da kawun ku hardai ace maka sun hade da shedanin nan guda dauda to ka barsu kawai na gayama . Ni yanzu aiba mu koma babu yarinyar nan bace yaron nan Jafar ya rikece muna yadda yayi jiya ni shine tashin hankalina a yanzu. A to mama tunda ance a barta ai dole mu barta din har ta huce yaya zaiyi kuwa banda hakkuri tunda ba tare aka haifesu ba dama ? Yasan yana sonta haka yarinya tana kokari dakai baka iya kareta ga kowa anatayi mata cin fuska yana kallo bai dauki mataki ba da nine gobe wata ba zata kara ba ai idan anga irin matakin dana dauka. Yaren fulancin da mariya tayi tana mikewa tsaye shine yasa suka bita da kallo itama ummah yaren tayi mata tana bata amsa don fadi take wai akan me zanyi haka tunda an biyoni bari ta ganni. Shine ummah din tace gaskiya itama bata son a barni in koma kawai kowa ai hakkuri yakeyi a gidansa shine ta nufi dakin wajena. A kwance ta sameni na kifa cikina ina hawaye tashigo ta tsaya a kaina tana fadin yanzu ke kinga haka yafi maki kizo ki zauna nan ? A fusace na dago na tareta da fadin ai dole kice haka tunda bake bace akewa abinda akemin a gidan koda yake ke naga hakan bai dameki ba ai dama toni ban daukan hakan . Kiri,kiri mama ta nuna bata son zaman mu da diyanta abinda take muna idan ayiwa diyanta zata dauki hakan ta kyalene ? Ko gaida matar nan nayi duk zuwan da nakeyi gidan nan bata amsa min sai taga dama duk abinda sararu tayi min da sanin mama . Tunda sunce ni ba alheri bane ga yaya Jafar sanadina abubuwa da dama suka sameshi na barshi don abubuwan su wuce din garesu tuda nice matsalansu. Ashe in kina bin zancensu ba zaki zauna da mijinki lafiya ba kuwa don su ko ajikinsu kuma kina gani tun baki aureshi ba ai yadda sukeyi damu a gidan . Ku kikace Yanda ni baku nane ai don ban iya daukan hakan nagaji wallahi amma baki mashi adalci ba Rahama udan kinyiwa yaya haka ? Naji ke kije kiyi mashi adalcin bashike nan ba ta tare da fadin akankifa ya saki Nusaiba jin hakan data fada yasa na dago na tsareta da idanu ina fadin. Aikanafa kikace Maria kaina ya rabu da matarshi tace akankine mana nace akanshi dai idan baki san abinda yasa yakai ga sakinta ba nina sani kuma ban fadawa kowa ba duk da fadin da akeyi kainane ya saketa din dama yana da niyar hakan. Ki dai tashi muje kawai kinga har habu yayi fushi dake yau na sake jefa mata kallo a cikin mamaki tare da mikewa zaune nace habu ubanane ko yayana maria ? Shigowan ummah dakin ya hanani cigaba da maganan tashigo tana fadin habu ba ubanki bane amma kamar uba yake gareki ai don shine gatanku acan din. Kememe na kafe duk abinda suka fada ban yarda na bisu ba mama tashigo muyi sallama da ita a cikin dabara nan take fada min kin mun daidai Rahama dabaki yarda kin koma ba a yanzu sai dubu ta kawo kanta gidan nan da kafanta. Lokacin zata gane kina da ma,ana a wajensu idan ba haka ba bata da niyar barin wanan halin banzan da dan uwata ke dorata a kai na fahinci gaskiyan tsohuwar nan dauda ke zuga dubu ga duk abinda tayi mara kyau don ya zama dattijon banza. Wanan maganan na mama yasa na kara kafewa kyam ban yarda na bisu ba ina jin suna sallama da su ummah suka tafe . Ummah harda fushi dani don bayan tafiyansu yinin ranan daure min fuska tayi ko nayi mata magana a dake take amsa min yasa nima nayi shiru na kyaleta. Saida safe taga ina shiri take tambaya nace gidan mu zanje can garin mu nan kuma ta hauni da fada wai na rainata in tafi gidan indai kawune ai nasan abinda zanje in sama a gidansa . Ina kuka nake fadin koma meye ummah yafi min tunda gidan mune ko yayi min kansa yayiwa da in zauna mama tanaci min fuska don kawai danta ya aureni shike nan ta dauku kiyayyan duniya tasa min. Ni abinda saratu ke min bai damuna kamar na mama dake fadin zamu mallake mata diya su koma sai abinda mukace kamar yadda kika maida daddy nan haka mun asirce su daddy Abuja sai abinda mukace sukeyi akanmu shine itama za a kawo mata ga iyalinta. Nan ummah din ke fadin matan nan fa na dade da fahintar ta tun zaman mu asibiti da mukayi da yar uwarki ? Agabana in kun kawo abinci zata kama fada tana fadin ana barnan abinci ana saki abin miya haka da yawa don ba asan wahalan nema ba. Bayan wanan kashin kudin da aka dauko masu a yanzu kuma a koma ana barnan abinci haka ita ba zata yarda da hakan ba a diga kirga nama kafin a saka a miyan. Wanan ma kadan ke nan ai na fada na dinga bata labari ta hau tana fadin ita wallahi ba zata yarda da wanan cin fuskan ba ai muma yayane kamar diyanta bawai bata son mu bane ai koda sukaga tana nuna hakan kawaicine kawai nasu na fulani take muna. Wanan yasa ta dauki zafi akan zancena din take fadin ki zauna sai tazo gidan nan da kafanta ta sameni na fada mata abindake raina nima kafin ki koma din. Tun bayan barunsu gidan habu ya fisgi mota yana gudu Iya ta lekoshi daga bayan mota inda take zaune tana fadin kai hanu kajamu a sannu don Allah ? Kana zuciya kamar an maka wani abu yarinyar nan tana da gaskiyanta inma laifine ita dai akaiwa shi ba karya ta fada ba ai. Tunda yarinyar nan ta kafe haka abin ne ya isheta don Allah nasha fadawa uwarku ta guji irin wanan ranan kada haka ya faru amma bataji ba. To wai ni iya ban gane ba me akewa yarinyar nan haka wai naga gidanta daban mana yazid yake tambayan hakan ? Kadai fadi duk yadda akeyi Yazid J yayiwa yarinyar nan amma wai shine don jin dadi zatawa mutane rainin wayau haka din taga yana yinta haka sosai a cikin matanshi. Allah sarki dama hakane ai idan namiji ya nuna kai yakeyi sai ace komai yi maka akeyi ita fa baku fahinceta bane har yanzu nake gani habu ? Yarinyar nan takafe akan ba zata dawo gidan nan bane kan irin cin fuskan da uwarku take mata a gaban kowa Dubu take nunawa yarannan hattara da kyamansu tana sakin maganganu akansu. Kasani kowa kuma yasani idan matsafane ko mayu aida yanzu sun baiyana daba hakaba da sauri iya ta dafata tace madallah Amina kin gane matsalan kenan ke ashe ? Shi wanan bai san komai ba sai zuciya a gaban yaran nan take nuna bata kaunarsu batayin lamarinsu su din ba kowa bane sun shigo rayuwanku zasu juya mata kanku . Wani tsuki yayi yana fadin nasan wanan mama aiga maria nan wani irin cin fuskan mamane bata gani ba a gidan nan kan matan J da bako kyautata mata sukeyi ba kamar ita kuma tayi hakkuri ta zauna . Ba zaka hada ba habu don idan anyiwa matarka kana tsayawa tsatin daka ka nuna bacin ranka kan abin shiko jafar fa bai iya komai saidai ya juya ya wuce kawai har can gidansu fa take binta itada dauda suyi mata kaca kaca su dawo zakace kadata nuna itama mutunce don Allah ? Inda laifi daga Jafaru har dubu da yan banzan yaran nan duk suna da laifi saidai kawai ace ayi hakkuri kawai shine yanzu amma abinda yaran nan sukeyi banga sarakuwar gidanmu dakeyin hakan ba gaskiya. Yarane da suka san mutunci da kimar babba da darajan dan adam mutum indai daga bangareku ya fito yaran nan zasu darajashi yaya ake son mace tagari ta kasance wai ? To mama ai na dauka don kawai wanan abin daya hadata da Saaratu ne take wanan zuciyar ashe bashi kadai bane tarawa tayi ta amaye muna komai lokaci guda haka ? Inda zata amaye din ne aida ta amaye muna idan watace ba tas zata fada a gaban kowa ba cewa ga abinda ke nan amma ita kaga tayi hikima takafe akan bata komawa kawai ? Dole aiwa abin tufka gaskiya bansan yaushe mama ta juya ta koma hakaba bayan tafiyana koda yake ance kawune matsalan komai a yanzu shike hura mata kunne yake zugata. Tundana dawo nake son a zauna naji zancen kudin mu dake wajenshi matsalan nan na j yasa na kyale amma yanzu ai dole mu hadu tunda ina son kudina na fara dan bussiness dasu . Habu na fada maka kabar zancen kudin nan don babu su rayukane kawai zasu baci a karshe don ko mama ta sani babu kudin nan a yanzu. Babu fa kace bros haba dai wanan wasane kawai kubar zancen agama wanan don Allah kada ku tayar da wani zance a yanzu muna fama da wanan ? Shiru sukayi don habu ya fahinci iya saboda mamace dake cikin motan abin daya shafi iya sune zancen kudin nan bai kamata ace wani na wajen dakinsu yaji zancen nan ba. Shiko yazid bai gano hakan ba sai fada yakeyi yana fadin kawu zaisan koshi waye bai sanshi bane wallahi jin kowa a motan yayi shiru yasa shi fara fahintar akwai matsala. Sai mama din ke fadin kai yazid ai kaji iya tace ka bari agama zancen nan toka bari mana hakan ya isa ba sai ka bata ranka a yanzu ba ai. Koda suka isa zaria la,asar tayi don haka su basu shiga part din ba saukesu Habu yayi yace zaikai matarshi gida ya dawo. Shi kuma Yazid part dinsa ya nufa saisu Iya da mamane suka shiga ake masu sannu da zuwa don nan suka samu kawu da mama dubu a zaune tare dashi. Tayi masu sannu da zuwa tana fadin ina yarinyar ko an sauketa gidan can ne don bata ganni ba iya tace wani gida yarinya kan na hannun iyayyenta sun rike abinsu kamar kowa . A,a duk da kunje basu baku itaba ke nan kuma yau ga mutanen banza marasa mutunci har anbi bayan yar ku kuma ku hanata dawowa akan wani dalili wai kuma ? Shi nake son ji kawu ya fada a cikin bacin rai iya ta juyo tana fadin akan dalilinku na cin fuskan da kuke mata ta hakkura tabar maki gidan da danki a zauna lafiya. Sallah ya sallame daga inda ya zauna ya juyo yana fadin wai bata dawo bane iya da gaske ko tana can gidan kun sauketane ? Bata dawo ba Jafaru ta nuna bata dawowa gidan nan a yanzu ban sanarwa gaba ba inda rabin dawowanta ? ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/17, 08:44] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 7️⃣9️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Wani shewa ta sake wanda yasa hankalin mutanen gidan ya dawo gareta inda take zaune tana waya bayan kiran da Saare tayi mata din. Don tana ganin itace tasan da magana hakan yasa ta mike tabar wajen ta koma gefe daya don taji meta samu ta kirata kuma yau ? Nan ta fara sheda mata albishirinki Anty Saiba tace goro cikin zakuwa tace yar iskan nan Rahama tabar gidan nan tun jiya . Ke ki bari don Allah saiba ta fada tace wallahi yau su ya habu sunje kaduna wai su dawo da ita tace dasu bata dawowa gidan nan wai ? Haka suka juyo suka dawo su kaidai taki ta biyosu shine dslilin shewan nata da har ta dawo da hankalin mutane gareta. Saida sukaji tana fadin aina fada maki saaratu bashi taci wallahi indai nice yadda tasa nabar gidanku itama saita barshi wai abin haushima yayanki ai yafi ban mamaki saaratu. Wai ace yaki zuwa yaki ya turo tunda nabar gidan nan kamar dama yana jiran haka ya faru tsakanin mu to shegeb cikin jikintafa yana nan kota zubar ? A kema kinsan yana nan ai tunda tana son ace ta haihu da yaya ba dole tabar cikin ba saiban ta amsa da fasin shegiya ai bataga komai ba. Gara dani ba goyo ba ciki nabar gidan itako yar banzan ko zaman ciki ai ya isheta yar iska tana wasa dani saina mayar da yar iska ko abin sayen goro. Waima meya farune tabar gidan take tambaya ? Wani irin dariyan shakiyanci Saare din ta kwashe dashi tana fadin kin manta dani ke nan ai dana saka yar iska gaba saida naga bayan shegiya . Wallahi yarinyar nan baki san irin haushinta da nakeji bane ai hana shegiya shakar iska nayi ko walwalan kwarai ban bari tayi ba. Nusaiba tace dakyau nawa ina sonki irin wajen nan wallahi a aina fada maki ki barni da ita ita a dole tazo cin arziki to taci din mugani yar iska kawai. Saura wanan shashan matar habu din itama haka zan ta zuga mama akanta sai naga bayan shegiya su tattara subar muna gidan yan iska muggan iri kawai. Aini ba barin gidan wanan yarinyar ba Saratu naso har munafukin cikin nata ya zube banson ma tabar wani alaka a tare dashi wallahi ai in ta haihu dashi taji dadi kota abinda zata haifa ba a rabuba ke nan dai ? Barta aiko haka an nunawa yar iska iyakarta don daga kan yarinyar nan yayi yawa tana daukan kanta ita wata tsiyane kiga tanayi kamar tana jin warin mutane ita gata maidigiri. Sun jima suna zagin kansu waini a wajen kafin suyi sallama su kashe wayan uwar ta kallo Saiba tana fadin wa aka saka tace wai amaryan Jafar ce tabar gidan subbahanallahi uwar tace. Nusaiba wanan zaman gidan baisa kinyi sanyi kin koyi darasi ba ashe ? Na dauka wanan halin da kike a gida zaisa kiyi nadaman abubuwan da kika aikata a baya ai ? Yanzu akan abokiyar zamanki kikewa wanan mugun fatan haka har kina fatan Allah ya barar da cikin jikinta don Allah keda kika haifa wani yayi maki bakin ciki da hakan ? Sai yaushe zaki hankaline ke Nusaiba irama wace ke turu maki tsegumin tafiki rashin sanin ciwon kanta ai da zata zauna duk tsegumi da sirin gudansu tana aikawa waje. To ki guji naki a wajen ta ranan da zata kwaye maki baya tayi maki tonon sililin abinda kuke shukawa a tsakanin don tayiwa dan uwanta ciki daya balleke ? Dama sam rayuwan yarinyar ni baimun ba wallahi don na fahinci itace ta shiga tsakanin ki da Asmau tun farko ta hanaku zaman lafiya duk amintakan dake tsakanin ku. Duniyace ai ita ke koyawa wawa wayau koda baida fahinta wata rana duniya zata fahintar dashi keda ya kamata ki natsu a yanzu ki komawa Allah inda rabon komawamki gidan ki komawa uban yarki kin zauna kina wanan hauka haka ? Katse uwar Nusaiba tayi da fadin mama ke saiki dinga ganin laifinaita da tayi min fa ta hanani zama dakina ta rabani da mijina ? Oho ba zakiji ba kenan ko ta ina ta hanaki halinki dai ya hanaki zama a gidanki Nusaiba waye baisan halinki ba yanzu ? Duk hakkurin yaron nan da kawar da idonsa jan abinda kuke mai saida kika kaishi bango ya koma komu yanzu bai ganin darajan mu a idanunsa kuma ? Ai duk wanan sherin yaeinyar nan ce da baku son a fadi kaifinta har yaushe za a tsaya goyon bayan wace aka san itace matsalata amma baku son a fadi laifinta sai saratu dake kaunata ni gabadaya naso subar gidan ba ita kadai ba don ko Asmau munafukace ta gaske dole sai ta fita tabarni dashi. Tsuki uwar taja ta juyo tana fadin na yarda abin nan ya tabaki Nusaiba ki matsa harki samu tabin hankali Asmau dince zaki fitar a gidam jafar ? Shiko Yazid tun bayan dawowanshi yana part dinshi tare da iyalinshi dan baison yayi nusa dasu sosai hakan yasa tunda ya shiga bai sake fitowa ba. Sai washegari daya fito yaje gaida j din suka dan zauna dashi ganin yadda J din yake kwance yasashi fahintar yana jin jikin nasa ranan. Muryan J ce ta katseshi da yake fadin yarinyar nan taki dawowa ashe nayi mamakin hakan ban kuma san abinda taje ta fadawa iyayyen nata ba har suka riketa. Me zata fada J abinda kuke mata kai da mama da yan uwanka da matanka shine zata fada mana ai basuce ta fada masu komai ba . Illa dai tace ba zata dawo bane ita tagaji da abinda ake mata kai baka daukan mataki koda kana zaune kaga bata da laifi anan . Don kaika daukota J yakamata ace ka nema mata daraja a idon kowa gidan nan duk da suna ganin sun girmewa shekarunta amma dai shi zama tare baice hakan ba ai. Bsice don mutum yana kasa dakai yana auren danka ka dinga muzantashi kana nuna shiba komai baine haka kuma kowan ku yana kallon yaran nan da matanka sinaciwa yar mutane mutunci nasan da gidan nan ne ba zamu taba yarda aiwa kannin mu hakan ba a gidajen auren su. Shi habu wai yayi fushi don yarinya ta dage akan bata dawowa har saida yakai sunyi musayan baki dashi don gaskiya inda shine bai yarda aiwa matarshi hakan ai. Shiru jafar din yayi yana saurarenshi kamar yana tunane kafin ya jefowa dan uwan tambaya yana fadin atakaice dai yanzu nida mamane masu laifi a wajensu. Kwarai kuwa bros lafinka anan shine baka tsawatawa lamarin koda kana kusa akayi mata baka daukan matakin daya dace koda gobe ba za a maimaita irin hakan ba sai yayi murmushi ga dan uwan nasa dake magana. Yazid din yace kwarai kuwa bafa wai kai ka nuna mata concern a bangarenka alhalin tana samun musgunawa a wajen mutanen gida shine kawai abinda zakayi ba . Yama dole kabata kulawa a ko wani bangare kamar yadda kakeba kowa tunda kaika daukota cikin gidanka. Haka kuma ita mama kamar da saninta ake komai ga yarinyar nab banda wanan itama kanta tana yawan aibantasu a gaban kowa don ko gaida mama sukayi ance bata amsa masu wani lokaci kaga ba wanda haka zai faru dashi yaji dadi har ya zauna itace uwar mijinsu fa ni nasan halin mama idan ta tsargi mutum bros ka sani kaima ? Baiyi magana ba saici gaba da kurawa dan uwan nasa ido yayi kawai a inda yake zaune yayi shiru ya kafawa kasa ido yana tunane. Mikewa Yazid din yayi yana fadin yakama a gyara zancen nan abinda na guda kenan da matana kaga ban yarda ta shiga kwamacalan gidan nan ba don ina da labarin komai a wajen iya. Yanzu ya rage naka idan kana son matarka saika gyara ka shirya da abinka idan kuma ba yadda zakayi don Allah bros kabar yarinyar nan ta tafi taje gaba ta samu wani mijin . Sai a lokacin ya dago kai da sauri ya dubi kanin nasa dake magana Yazid din yace hakane mana ka sallameta ka zauna da wa yan nan mayayen naka lafiya tunda itace matsalanku. Ko dai makaho yasan irin hakkuri da sanin ya kamatan yarinyar nan kai kanka kasan ka tauye mata rayuwa a gidan nan don ba kalan macen da za a dauko a takura haka bace ita. Yazid idan da bansonta zaunan aureta gashi ka fadi kaima ko makaho yasan halinta na alheri balleni da kusan a yanzu yarinyar nan itace rayuwanta. Me nake tsunta a wajen wa yan nan marasa hankalin tunda na auresu sunan nayi aurene amma ba wani jin dadin rayuwa na ma,aurata a tsakanin mu. Na tabbatar da Rahama bata tare dani haka ya sameni gaskiya ko kwanana bai kare ba dana wullakanta ita kanta mama tasan hakan don tun bata aureni ba take dawainiya dani a kwance kan lalurana. Na zata dana yanke shawaran aureb yarinyar nan mama zatafi kowa jin dadin hakan a ranta ashe ba hakana bane a wajen mama don sai gashi ta juya zancen da cewa sihiri sukai min don suci arzikina kawai. To ashe kasan hakan ka bari ana mata hakan a gaban kowa bama kamar yar iskan nan Saratu da kawu da sune suka canza muna mama daga nan gidan kawu na nufa zanje amsan gadona dake hannunsa ko ba zanyi amfani dashi ba ina bukatan abina a hannuna yadda kowa ya karbi nasa . Da sauri yace da dan uwan nasa No Yazid kokaje kudin nan a yanzu ba samuwa zasuyi ba Yazid don haka ka barshi kawai don Allah. Duk abin nan da kawu yake muna sam mama bata ganin hakan a idonta saima idan mun matsa taga laifin mu zancen iyace datace ba banza suka barta ba. Kaga na dauka akan zancen nan nawa da kawu keda hannu a cikinsa zaisa mama ta gane waye kawu sai gashi naga yanzuma suke wani shiri na daban a tsakanin su don haka karkaje ku samu matsala da mama don Allah. Dolene inje bros so nake in kawo karshen mutumin nan ai masa iyaka damu yadda zai fahinci yanzu mun girma ya fita daga tsabgan mu gaba daya. Mamace yar uwarsa bamu ba ka bari na latsashi na dan lokaci zai shiga hankalinsa kasa muna ido kawai kaga yadda zanyi dashi don Allah ? Yana fadan hakan bai tsaya ba ya fice daga falon da saurin binsa yayi da kallo yana sauke ajiyan zuciya tare da lumshe idanunsa na dan lokaci. Muryan maman tudu ya dawo dashi hayacinsa tana tsaye take fadin yazid ne ko ina daki nake jin muryanshi ai shine ya fita ya bata amsa. Can ya dora da fadin yazone yana fada dani kan tafiyan Rahama wai laifina bani daukan mataki idan an mata cin fuska koda a ganane ? Fissabillahi mama wani irin mataki take so in dauka bayan wanda nake kokarin yi mata a yanzu na rabata da zama nan gidan duk da mama da sauran yan uwanta sun nuna min rashin yardansu da hakan amma na cije naki dawowa da ita gidan nan . Abinda take nufin anyi mata ai in Nusaiba tayi mata ita da bata gajiya da lorafin anyi mata ba daidai ba koda yaushe nakan tsaya kuma nayi abinda ya dace amma duk bata ga hakan ba mama ? Watau abinne naku yake son natsuwa da fahinta jafar duk wanan laifin na Dubuce data ba dakariyar yarinyar nan saratu dama da yawa haka a cikin matanka. Har yaushe zan zauna in sakarwa yarinyar da batayi aure ba dama zama da matan yayyun ta haka zaman daba na Allah da Annabiba kuma ta sani ta kyalesu suna aikata abinda ba daidai ba. Har ace kamar Saratu tana kokarin aibanta jinin dan uwanta tun a ciki da nice yarinya tayi min wanan aikin a dakina ranan danasa yan uwanta sunyiwa ja,ira dukan kawo ruwa da gobe bata komawa . Amma dubu ina taji fa amma sai kokarin kare yarta takeyi daga karshe wai aiba da ita sukeyi ba tsarguwane kawai irin nata data sabayi tana kokarin daukan laifi ta dora akan yar mutane. Irin maganan sherin dake fitowa a bakin saratu kan yarinyar nan ko waye dole ya dauki matakin hakan tunda ba a gidan nan aka kare rayuwa ba. Gaba dayan ku kuna da laifi gaskiya yanzu baga habu ba ko ince yazid tayiwa dayan su irin abinda takeyi tsakanin matanka mana idan gaskiyane ? Dole har in kana son yarinyar nan ka dage ka kwatar mata ince ga kowa a gidan nan shine mafita amma baka zura ido haka abubuwa suna faruwa ba ? Sun dauki karan tsana sun dorawa yar mutane da za a tsayar dasu a tambayesu babu mai kawo wani dalili mai karfi a wanan zance kishine kawai irin na mata don sunga ta fisu da komai sai kuma samun wajen iya shege din. Shiru yayi yana sauraren zancen da mama din take kwararo mashi a lokacin shi dai a iya sanin sa ai yana kyautatawa zamantakewan mu dashi ba zaci zance abindake faruwa tsakanina da mama ko saratu da matanshi zai zama laifi a wajenshi ba. Wanan yasama bai yarda ina yawan zuwa gidan ko shiga wani harkansu da bai zama dole ba amma kuma duk bai tsira daga hakan ba a wajena. Da mama ke zancen idan har yana sonta ai itama tasan yana kaunar yarinyar nan saidai ba zai iya cewa yana fito na fito da magaifiyarshi ba kan abubuwan da suke mata din. Yasani ba a kyauta mata amma yasota da yin hakkuri da kullum yake bata kan wata rana sai labari tunda har mama ta kasa hango alherin yarinyar a yanzu yasan ba zata taba hangowabane kuma. Yau duk wanda ya tsaya yayi maka haka akan naka aiko komai yayi ma zaka iya masa ragowa don hakan amma sam sunki su fahinci hakan ita mama tana ganin komai takeyi tanayinsane don ta mallakeshi da abinsa. Har ta ina Rahama tayi wayau haka duk ance kabar mace indaka ganta amma yasan halin matanshi yarinyar da komai kankanta abu ya batashi zaiga farin ciki a wajenta bata taba raina hakan. Nan ko zai basu kuma a raina a kumazo a wullakanta abin daga karshe yana kallonsa an nakasashi baida bakin magana kan hakan har ya gaji ya saba don ba zai sayo abu ayi amfani dashi yagani yaji dadi ba. Shawara sosai masu amfani mama ta bashi wanda yaji dadin hakan sosai har cikin ransa ya kuma godewa mama din don yaji dadin wanan shawaran data bashi a lokacin. Shigowan mama dubu yasa suka canza zancen take tambaya bayan sun gaisa ta tambayi karfin jikinsa da Yazid ya fitane ta shiga part dinsa bai nan ta dauka yana nan wajensune ai ? Anya kuwa Yazid bai fita ba don yace min daga nan idan ya fita gidan kawu dauda yake son zuwa ya gansa ina ganin ya tafi can din ne ? Gidan yaya kuma da safen nan baiko fada min can zai tafi ba yau ya tuna dashi ke nan shima yaya din yanata korafin tunda ya dawo baije gidansa ba. Yaran nan zumunci yanzu bai damesu ba akan zumunci sai Allah ya hana maka alheri suna yawan wasa da zumunci a yanzu wanda basu sani ba yana cikin abindake habka rayuwan dan adam sosai. Yanzu sai kika ko kana da zumuntan sai a sarema gwiwa a zaci saboda wani abin hannun mutum kaje gidan don a baka akama daurema fuska don gobe karka dawo. Haka kuma zakiji mutun yace ko naje banda abin bayarwa don haka ba zani ba duk wanan halaiyan su suka kawo koma bayan zumutun a yanzu. Kedai bari yaya irin fa hakan ke bata zumunci a yanzu ko baka mutum komaiba yaje wurinka ai ya kyautama haka kuma kai da zaka ai ba ace sai ka rike komai ba da zaka dashi. Har iya ta shigo ta samesu a dakin aka zauna ana hira a nan wanda hirane akan lamarin ciwon shi jafar din da mama dubu take fadin yanzu kan jiki yayi dama daba zancen yarinyar nan daya saka a ransa ba aida sauki ya kara samuwa mashi sosai ? Dole ya saka keko Dubu ance ka samu da wanda ya damu dake kodana munafuncine kuwa yarinya data san yakamata yau ta tafi ta barshi ace ba zai damu ba ? Ki duba da gari ya waye din nan yanzu karfe nawa don Allah amna ba a kawo mashi abin karyawa ba har yanzu fa aiko wanan ya isa mutum ramewa haka ba sai ciwo ba ? Halin Asmaune baki sani ba kuma iya yanzu haka tana can tana barcinta na safe sai tayi mai isanta tace zata tashi ta dora abinci ko kuma an dora din an koma an kwanta ana jira. Dukkansu haka suke har wacan data tafi indai kinga an karya da safe gidan nan to yarinyar nan ce ta tashi tayi muna dabara lokacin da take nan din tana kwana samu . Shine zata dan samo mana abu mai sauki da zamu karya dashi suna zancen Asmau ta shigo da kayan abincin da missalin tara da rabi na safe . Mama din ke fadan cewa wai meyasa suke haka suna da mara lafiya amma ba za a daina wanan barcin safen na lalaci ba sai lokacin da akaga dama a dora girkin abin karyawa ? Wayanta ya shiga kara tana fada tana dauka tana jin muryoyi na tashi a cikin wayan wanda yasa hankalinta tashi har ta furta Yazid da yaya kuma me yayi zafi haka kuma ? ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/17, 08:44] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 8️⃣0️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Idan nace dake ban shiga damuwa ba karyane don dole akwai damuwa da kadaici balle yanzu dana shaku da yaya haka ko yaushe muna tare. Sai naji dan kwanakin da nayi gida ya zama min daban a rayuwata ga wayana na kashe don kadama ya kirani in kulashi. Kusan kwana shidda a gidan ummuh inda na sake raina kamar yadda kowa ke ban shawara ina samu ina barci haka kuma babu aikin komai duk da nakan dan shiga kitchen wani lokaci da Saudatu mai aikinsu. Haka yaran daddy mata su anty Baby su ukku duk sunzo gidan dubani kamar yadda mahaifinsu ya umurcesu dasuyi min din mun zauna na fada masu damuwa ta suka kuma ban goyon baya kamar ta mahaifinsu da inzauna sai sun kawo kansu in kuma sake jikina na kama harkokin gabana kawai ba a sa zancen namiji a zuciya don sai ka lalace a banza. Naga karamci a wajen mutanen nan sai yanzu da zamana ya dawo gidansu na fahinci halinsu ashe ban fahincesu bane da farko mutanene masu halarci da sanin darajan dan adam. Inda ko wacensu take a gidan hutu gwargwadon hali don basu cikin wahala ko talauci kadaram kada ham a rayuwa . Gashi a fahintana suna nuna kamar mu kanninsune na jini haka sai naji kunyar kaina ya kamani a ranan na yadda bamu kullasu duk da suna bin mu amma ya dace ace ai muma muna maida kara a garesu shine mutunci. Ina kwance daki ranan misalin karfe biyar na yamma saiga ummah da wayanta a hannunta ta shigo dakin tana fadin wai barci kikeyine Rahama ? Na dago ina fadin a,a ummah na dai kwantane ta miko min wayan tana fadin mijinki a layi na dago na kalleta nace mi zan mashi kuma ni ina ruwana dashi ummah ? Ki karba saiki fada mai ta fada tana dangwaro min wayan a hannu na da sauri na cabe ina karawa a kunne yana kan layin naga ta juya ta fita daga dakin ta barni da wayan. Na manna a kunnena naji yayi murmushi yana fadin baki san me zaki fada min bama Rahama shiyasa kika kashe wayarki kenan ashe don kada indameki ko kiji muryata ? Shiru nayi ina saurarenshi na sake jin ya furta are with me na amsa da ina jinka mana rai bace cikin wani yanayin murya a daure. Naji ya sake murmushi yana fadin fushin hardani ke nan akeyi da nayi maki me kuma Rahama bawan Allah dake kwance haka har zai iya batawa wani rai don Allah kiyi hakkuri please ? Nace da kai fushi nakeyi ni kawai nagajine da cin mutuncin da akemin kuma a hana mutum ramawa ba a kuma daukan mataki a kansa. Ba gaskiya bane Rahama wanan bai isa hujja a gareki ba nidai abinda zuciyana yaban game dake shine kin gaji da halin da nake cikine a yanzu kawai kike nemawa kanki mafita ? Ohh abinda tunanen ka ya baka ke nan kai to shike nan in haka kake tunane look Rahama idan kin gama hutun ki dawo nima ina bukatanki a nan tare dani kin sani . Ashe zaka zauna zaman jirata kuwa don ba zan dawo wanan gidan da baida saiti ba sai abinda kowa yaga dama yayiwa mutum kuma a hana ka daukan mataki nagaji na hakkura na kashe wayan. A bangarenshi shiru yayi yana tunane yaushi nake fadawa hakan a gabanshi da farko bai yarda ba amma yanzu yaji gaskiya da kunnuwanshi. Maganan mamansu ya zama gaskiya ke nan ba wanan yasani tafiya ba saidai kawai gajiya da halin da yake ciki din da nayi inbashi ba baiga abinda zaisa nace haka ba shima tunda yasan yana iya kokarinsa damu ai. Shigowan mama tudu dakin yasa ya nisa ita ke fadin Jafar yau ina son in koma gida don na shirya zuwa gida in duba yaya da jikinsa dan uwanta da akace hawan jini ya kayar dashi. Ya dago yana fadin mama kema tafiya zakiyi ke nan yanzu muka gama magana da diyarki ai tana a bankanta na cewa ita ba zata dawo gidan nan ba. Ni abin ya daure min kai mama iya kokari inayi da yarinyar nan amma ace Rahama bata ga hakan a kaina ba yanzu. Shiyasa nake tunanen zancen mama gaskiyane da tace kawai dai tagajine take neman hanyan guduwa a yanzu din. A kul dinka Jafar na kara jin wanan zance irin haka a bakinka kai yanzu bakaji kunyan furta wai yarinyar nan ta gajine ba tunda ka fada yanzu a nan nasan zaka iya fadin hakan a gaban kowa Jafaru. Jafar ka tuna iri alherin yarinyar nan a gareka kana a cikin ciwin kama bata yi haka ba sai yanzu da Allah ya kawo maka sauki ana gani ? To mama ni banga abinda nayiwa yarinyar nan bayan wanan da zatace ban mata adalci ba a yanzu wani irin adalci take so a rayuwa kuma ? Ehh lalai Jafar da sauranka sosai wanan yasa har ake ganin damanka dana matanka ashe sam baka tsayawa kayi tunane akan abu ? Yanzu kai ya dace ace kanwaka da mahaifiyarka suna yiwa yarinyar nan cin mutunci kana kallo amma baka tsawata ba sai wani cikin yan uwanka yazo shine zai tsawata masu ? Kaga hakan yayi daidai ke nan a rayuwa don Allah kofa waye akewa hakan a gaban wanda yayi dalilin zuka gidan baka dauki matakin daya dace ace ka dauka ba a matsayinka na mijinta. Kayi tunane wanan dalilin kadai dana baka idan kana da tunane zaka gane gaakiyan yarinyar nan nayin hakan dolene ta kufuleka a zuciyarta. Sanadinka fa take zaune gidan nan yanzu amma irin hakan yana faruwa baka taba daukan matakin daya dace ba kan hakan Jafaru ? Shiru yayi yana sauraren mama din saida ta gama ya nisa yake fadin mama nagode insha Allahu za a gyara dama gudin nayi magana ace banda ta ido . Mama kin fa san halin mama sarai mama banyi bama tace nayi akan Rahama ni ina kyalewane don kada na gogawa Rahama bakin jini amma zan gyara insha Allahu. Daga wajen suka kara tattaunawa da mama din inda a karshe yake fadin saikin dawo zaki dawo nan ke nan mama da sauri take bashi amsa da fadin anya kuwa Jafar ? Shi kuma yace haba mama ki dowo don Allah kinsan zaman ki nan a yanzu yana da amfani sosai a garemu ta dan dago kai tana murmushi take fadin Allah dai ya dawo damu lafiya ya amsa da amin. A ranan ta tafi hakan yasa ya koma zama shiru shi kadai a daki sai idan iya tashigo dakin dayake yakan dan samu abokin hira bata zama kuma take fita. Makin Asmau tayi amfani da wanan daman ta mami mijin nata sai ya kasance a lokacin ita kuma take ikirarin wai aiyuka suna mata yawa saidai ta dan lekoshi ita da yaran ta koma . Hakan yasa ya shiga damuwa mai din bin yawa zaman kadaici ya dinga damunshi a dakin dole yasa zaisa a fito dashi kofan wajen part din ya zauna yana shan iska. Gaahi zuwan Yazid ya hana a dinga tayar da injimin da rana sai idan dare yayi ko zafi yayi yawa tun lokacin da matan yaya Jafar din sukace ai ana cutansu ana cin dukiyan mijinsu ba tare dasu ba don anga yana kwance baisan abinda yakeyi ba su kuma an mayar dasu mata ba a daukesu a bakin komai ba. Yazid a mota ya tsaya bai fito ba ya tura aiwa kawu sallama jin hakan yasa kawu ya fito don yaron ya fada mai wani mai mota ke sallama dashi a waje. Sai gashi ya fito da sauri yana dan waige waige ya hango motar dake tsaye nisa da gaban gidansa kadan ganin hakan yasa Yazid din fitowa daga motan dayazo dashi. A,a Yazid dama kaine ka tura ayi sallama dani baka shiga ba ka tsaya waje ya karaso yana fadin eeh kawu to bussimillah mana mu shiga daga ciki kawu ya fada. A,a kawu aiba wani abu ya kawoni ba nazone akan wani zance shiya kawoni to yazid ai da dai mun dan shiga daga ciki akan ita matar Jafarne daine ko ? Yaran nan basu jin shawara ai shi jafar tunda yazo min da zancen auren yarinyar nan banso ba naso hanashi amma ya nuna min yayi niyar hakan na barshi yayi abinsa ko uwarku bai kaunan ta sani. Dakata kawu ba wanan zance ya kawoni ba ninazo zancen kudinane da mama tace min suna hannun ka ina bukatan kudin a yanzu don ina son na kara jari ga sana,an dana soma. Kudi kuma yazid ita uwar taku tasan da zakazo tambayan kudin ka don ba kudinka bane ta ban balle yanzu kazo tambayana haka kai tsaye ? Ok hakane to zata zo din da kanta har in kudina yana hannunka ka tabbatar da ka bata kafin mu sake haduwa irin haka don ina bukatan kudina a yanzu don Allah. Yana fadan hakan ya juya a fusace ya bar kawu din da mamankishi tsaye yana bin bayanshi da kallon can Allah ya bashi ikon budan baki yake fadin. Waiko yazid kan ka daya kuwa koka fara shan wani abune haka jin hakan yasa Yazid din juyowa a cikin mamaki yake fadin. Yana nuna kanshi yana fadin ni kawu a hayaci nake don ko goro bana ci balle wani maye nayima kama da wanda ke shan wani abu makamancin hakan yanzu ko ? Sai yayi murmushi kafin kawun ya bashi amsa ya juya ya tafi har lokacin kawu din yana tsaye a inda ya barshi har ya tafi. Nisawa yayi ya juya yana wasi wasin a zuciyarshi don yasan bai jima da wanan maganan da dubu ba akan zancen kudin yayi mata maganan da yake ganin hankalinta zai kwanta yadda ya saba . Yanzu kuma kwatsam saiga Yazid yazo da wanan zancen kudin yadda yaga yaron yazo mashi tsatsaye a yau shine abinda ya daga mashi hankali. Yasan inda zai kamo shirinsa ai da uwarsa zaiyi amfani itace logon diyan da ita kawai zai hadashi ya daina wanan zancen. Shiko yazid yana tafe yana faman shirya yadda zai fitowa kawu din tunda ya hango rashin gaskiya tsantsa a idon kawu din zaiko gwada mashi bai isa ba wanan karon. Tafiyan maman tudu yasa hankalin yaya Jafar komawa gareni ko yaushe zai zauna zugun yana tunane ta inda zai bullowa zancen tafiyan nawa gida. Don ya kulla da mama sam bata son wanan maganan haka shima habu yayi shiru da alama yayi fushi akan rashin dawowana gidan tare dasu lokacin. A lokacin mama ta shigo dakin ta sameshi hakana a cikin halin tunane ta soma fadin Jafaru na horeka da zama haka kana faman tunane ? Kasan jikinka ba lafiya gareka bafa ka daina tunanen yaran nan dukkansu yan banzane don jinyar kane duk suka gujeka da kuma fitinan su ya koresu idan wani abu ya sake samunka a yanzu ba hasaransu bane. Haba mama ki daina zagin yaya mutane haka ita Nusaiba ai kowa yasan abinda ya hadani da ita gidan nan harta fita haka kuma ita Rahama saboda matsinki da saratu akantane ai yasa ta tafi. Amma ba don jinyana ba ko za a fadi hakan kuma banda Rahama yarinyar da tayi tsaye a kaina har Allah yaban lafiya. Yanzu kuma ace don kada tayi jinyana ko ta gaji da jinyata yasa tabar gidan nan kawai dai irin maganan da kuke fadi a kantane yasata fushin zuciya ta tafi amma ba,,,, Wai Jafar kanka daya kuwa yau kake fadin wanan maganan haka kamar wanda wani abu ya sama shima jafar din katseta yayi da fadin a,a mama maganan Allah udan yazo a yishi don kina gani a gabanki saratu da Nusaiba suka matsawa yarinyar nan amma ba a tsawata masu ba . Lalai anyi gaskiya da akace macen bafulatana hatsarice ga mutum don basu shiga gida ba su hada kan kowa a gidan ba idan basu sami hakan ba kuma sai suyi yadda zasuyi suga sun halaka duk wani wanda ke gidan ,,,,,, Wayanta dai daya dauki kara shiyanata karasa zancen datakeyi din ta tsaya daukan wayan a cikin mamakin dan nata datakewa kallon tababe a ranan kan bafulatanan matarshi din data tafi yasashi gigicewa hakan. Ganin layi kawu daya matsa kiranta yasa ta dakatar da zancen ta dauki wayan da sallama tana karawa a kunnenta ya amsa. Gaisuwa ta fara mai ya amsa a gagauce ya soma fadin Dubu kina da masaniyar zuwan yaron nan gidana kuwa ? Ta mayar mai da tambaya itama da wani yaro ke nan kuma ya amsa da yaron nan Yazid mana wai yazo tambayana kudinsa da akace suna hammunsa. Kudinshi kuma shi yazid din yazo tambayanka kudi yaya ya amsa da kwarai yazo shekaran jiya nace bari dai in kiraki in tambayeki ko kina da masaniya ga hakan ? Wallahi summa tallahi yaya banda masaniya ga zuwanshi wajeka shi yazid din yaje gidan ka yaya yana tambayan kudi kuma bayan na fada mai kada yayi wanan maganan a wajenka . Kwarai kuwa yazo min nan a fitsare wai yazo karban kudinshi a wajena nace yaje sai munyi magana dake Dubu dama abinda nakewa gudu kenan gashi ko ya faru tun yanzu ? Har yaushe aka bada kudin nan don Allah dubu da za a dinga matsawa da a bayar dasu bayan an juya kudin zuwa kaddara yanzu. Yaya kayi hakkuri dan Allah zan mashi magana sai faman fada yakeyi Jafar yana zaune gefe yana kallon ikon Allah a tsakaninsu. Saida ta gama wayan ta dago tana fadin kaji min kuma wai yazid ya samu kawunku yana mashi zancen kudinshi . Ok kawune kuke waya dashi yanzu ta juyo a cikin damuwa tana fadin yanzu haka kawai yaron nan muna zaune lafiya da dan uwana yana son hada tsakanin mu. A,a mama ku natsu ku bincika kuji meye dalilishi nayin hakan dole yana da dalilin dayasa yayi hakan ai ba zai tashi haka yaje wajen kawu kai tsaye zancen kudi ba. Jin abinda Jafar ya fada yasa uwar kallonsa tana fadin barshi ya dawo ai zai sameni bai yarda dani ba ke nan danace kudin suna hannun yaya yaje da kanshi ya bincikeshi ? Fada sosai mama din keyi ga yazid din ya fita tun safe bai shigo ba har mama dubu ta fito zuwa part din don diba jikin jikannata nan ta samu mama din tana fada saidai tana ganin iya taja bakinta tayi shiru. Don da jafar da yazid suna dasawa sosai da tsohuwar habune kadai suke yawan fada dashi lokaci lokaci wanan yasa ko yanzuma da yazid ya dawo da iyalinsa suke kadaici itace mai zama dasu tana debe masu kewa. Sai bayan la,asar ya dawo gidan part dinsa ya nufa inda ya dan zauna da iyalinsa yaci abinci kafin ya fito don tun safe bai leka dan uwansa ba. Ya shigo da yaronshi a hannusa cikin fara,a yana fadin yaya ka ganni sai yanzu na tafi duban masu aikine can nake tun safe don kada su sake maimaita shirmen da sukayi a baya. Ya dan rankwafa yana fadin ya karfin jikin naka brother badai matsalan komai ko yake tambayan dan uwan ? Ya juyo wajen mahaifiyar tasu a sake yana fadin mama barka da gida yaya gidan kuma da iyali ? Suna lafiya Yazid yaushe kaje gidan kawun ku tambayansa kudi don dazun ya bugo min waya yana tambayana ko ina da masaniyar zuwanka wajenshi ? Ya samu bugo maki kenan naje ina son kudina dake hannunsa akwai abinda zanyi dasu a yanzu don ba zan tsaya ace sai kawu ya juya min kudina ba mama ? Yazid ni kake fadawa hakan kai tsaye ko kana son nuna min cewa mu bamu isa rikema abinka ba ke nan ko ? A take ya daure fuska yana fadin da karfina mama zan tsaya kawu yana juya min dukiya aban abinna yadda akabawa kowa nasa in rika don ina da abinda zanyi dasu yanzu . Yazid kafita min a ido akan kudi kada ka tsaya kana min rashin kunya a gabana yanzu da sauri yazid din ya katseta yana fadin . Mama kudina fa nake zance ba wani abu ba ya ban ina da bukatansu tunda hakkinane anbawa kowa nasa nima ina bukatan nawa a yanzu. Kudi a yanzu kaddara aka mayar dasu don haka banson jin zancen kudin nan a yanzu ka bari sai ranan da ya sayar da kaddarorin daya saya ya baku kudin ku. Ba zai yuyu ba mama kudin nan fa kudinane bance aban na wani nayi amfani dashi ba don haka a ban abinna don Allah ki fada mashi. Yana fadan hakan ya juya a fusace ya bar dakin da danshi a hannunsa yana shiga part dinsa ya zauna yana fada yana fadawa iya abinda ke faruwa . Karshema ya dauki waya ya dannawa kawu waya yana fadin kawu zancen kudina nake maka ina bukatansu nan da kwana biyu in Allah ya kaimu yana fadan hakan ya kashe wayar tashi rai bace. Shima a bangaren kawu bin wayar shi yayi da kallo yana mamaki yadda dan nasa ya kirashi babu ko sallama yana mashi zancen kudinshi. Yasan akwai matsala ke nan akan hakan don dole yakai kanshi gidan su zauna a gaban mahsifiyarsu ta takawa yaron burki don yasan ita kadaice zata iya takawa yaran a yanzu. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/17, 08:44] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 8️⃣1️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Nayi sati hudu a gidan mijin ummah banda dan damuwa da sabo da zama a dakin aure banda wani matsala a gidan kamar yadda na fada a baya. Ganin hakan yasa na kirkiro tafiya Abuja na samu ummah da zancen take fadin anya daddy ku zai yarda da hakan kuwa ? Ace kina nan mun barki zuwa kuma abuja amma zan fada mai naji ko zai yarda da hakan idan ya shigo yanzu ya tafi rigasa wajen abokinshi. Ina kwance dakinta da yamma sai gashi har dakin ya shigo ya sameni tare da ummah yana saye da coffe colour din jallabiya mai dogon hannu a jikinshi. Saida yakai zaune saman kujera ya soma fadin diyata maman ke fada min kina son ki karasa Abuja ? Nace ko anyi maki wani abune a nan din da sauri na dago kai na dubi ummah kafin na girgiza kai ina fadin ba komai daddy . Kawai dai ina son inje can din ne kawai nagansu sai ya gyara mike kafanshi yana fadin ayi haka kuma Rahama ? Bayan mijinki da yan uwansa sunsan ki wajen mu yanzu kuma suji cewa kin koma Abuja yaya kike son su dauki zancen a zuciyarsu ? Sai na sake kasa da kaina na dukar yacigaba da fadin kinga hakan ba zai masu dadi ba don hakan na nufin cewa mu nan mun gaza dake hakan ke nufin da sauri na kara dago kai na dubeshi yayi murmushi yana fadin yes idan mun barki zuwa abuja hakane zancen. Ba zani ba daddy na fasa yace good girl Allah yayi maki albarka kinji kiyi hakkuri har ki koma dakinki saiki tafi da bakin mijinki daga can na amsa mashi da toh kawai. Ya dan min nasiha nayi hakkuri don Allah na saki jiki kuma tunda nasan a yanzu bani kadai banr a jikina yasan kuma bada jimawa ba mijina zaizo mu koma. Ya dan jima nayi mai godiya ya mike ya fita daga dakin ummah tabi bayanshi suka fice a hankali na sauke ajiyan zuciya na koma na kwanta ina tunane. Sammako kawu ya bugo masu a gidan duk dai akan ya samu yazid din a gida a gaban mama don kada ya fita suyi sabani donshi yafi bukatan ayi komai a gaban mama din don ya hango rashin mutunci a idon yaron . Kamar kullum saida mama tasa yan matanta sukai mashi abin karyawa yanayi yana tambayan kada Yazid ya fita fa dubu gara a aika a fada mai ana nemashi. Kada yazo ya fice daga gidan ba tare da sun sani ba kuma yazo daga baya ya bishi gida yayi mai cin mutumci har wasu suci. Da mama dubu taga ya matsa yasa ta tayar da salima akan taje part dinsa ta kira matashi suna nemanshi ita da kawunsu. Salima taje ta samu har lokacjn basu bude part dinsu ba don yana ciki hakan yasa ta dawo ta fadawa mahaifiyar nasu cewa basu tashi daga barcin ba. Karfe nawa yanzu kije ki kwankwasa masu kofa ya bude muna son ganinsa a nan hakan yasa ta koma ta kwankwasa kofan . Suna zaune suna karyawa a falon nasu sukaji nocking matarshi ta mike ta bude kofan kamar kullum fuskanta yana a daure kamar yadda suke kiranta da mai dauraren fuska haka suka gaisa a tsatsaye da ita . Gashi kuma tana tsaye ta tare kofa alaman bata son ta shigo daga ciki fuska a daure donshi suke kiranta mai dauraren fuska bata da saki ko kadan. Dan uwanta ta tambaya take fadin yana ciki hakan yasa tayi kokarin kutsawa taja gefe ta bata hanya tashiga gaisawa sukayi take fada mai mahaufiyarsu da kawu ke nemanshi . Yake fadin yazo ke nan kice ina zuwa daga haka ta juya ta fice duk da kayan dadin dake zube a gabanshi yana ci da ace marainintane datace wanan fa yaya ? Shikuma jafar zaice zoki zauna kice kodama batayi magana ba idan ta shigo hakan zaice da ita bissimillah salima zauna mu karya. Haka ta juya tana kunduma masu zagi tana fadin yaya J duk yafisu mutunci yan iska masu tsoron matayensu kawai ? Ta koma ta shedawa mama cewa yana tafe tashige dakin kwanansu ta bar falon a lokacin iya na can tare da Jafar a part din da suke jinyarsa don maman tudu tayi tafiyanta gida tabarta dashi. Saida Yazid ya gama karyawa ya shigo part din dauke da dansa a hannunsa ya gaisa dasu ya samu waje ya zauna yana fadin fuskatan mahaifiyarsu yace. Salima tace kina nemana mama kafin ya kaiga rufe baki uwar tace ehh ga kawun ku nan yazo akan zancen kudin daka sameshi gidansa. Ok kudin ya kawo ke nan yazid din ya fada yana gyarawa dansa dake gefenshi zama ya kyalla ido a gefensu ko zaiga kudin sai dai baiga komai ba yasa ya fuskanci uwar dake magana. Kaida kaje gunsa da zancen kudi kaika bashi kudin da zaka sameshi kai tsaye don rashin kunya ? Amma ai mama kudinane ko hakkina don naje na sameshi ai ba zai zama laifi ba ko gyara zama kawu yayi yana kallon yazid din cikin mamaki. Eeh lallai yazid ni kake fadawa kudinkane ko yanzu da sauri yace haba mama kudinane fa hakkinane na tambaya ba wani abu ba idan yazo da kudinne sai aban su mana shike nan don Allah ? To baizo dasu ba mara kunya ko kuma radhin kunya zaka kawo muna yanzu tunda hakkinkane ta yaya an mayar da abu kaddara zakazo da rana tsaka kace kana bukatansu a yanzu. Mama ko kaddaranne a nuna min insan yarda na juyasu zuwa kudi don ina da bukatan kudi a yanzu ni banja ba bance aban na kowa ba nawa nake maganan abina a yanzu. Kai Yazid kagane ko kudin tun lokacin data bansu nayi dabaran sakasu a kaddara na sai filaye da gidajen kango sai a sayar a kara sayen wasu a jingine haka nayi da kudin. Ok to a kaini filin sai na saka nawa a kasuwa don kudi nake da bukata akwai kayan danayo oda zasu shigo min zuwa wasu sati insha Allah. Kai habu na fadama ka shiga hankalinka ba zancen kudin nan a yanzu sai ranan da kawu ya sayar ya kawo maka kudinka idan lokacin hakan yayi. Mama kudin nan kudinane hakkina da Allah ya wajabta a gareni ba don haka ina bukatan abina a yanzu ko hannun wa suke kuwa ? Kawu ina son kudina nan da sati daya kacal kudi ko kaddara a ban abina don ina da bukata akansu yanzu. Yazid ni kake mussu dani mama ta fada ya mike tsaye yana fadin Allah ya kara lafiya da nisan kwana mama ni na isa inyi mussu dake kudina nake bukata kuma shina fada nan da sati nake da bukatansu. In kuma har aka wuce sati gaskiya za,a samu matsala a tsakani gaskiya don kudina ba zasu wuce wanan rana ba in sha Allah. Yasa kai ya fice daga part din kallon juna sukayi tsakaninsu kawu ke fadin kingani ba Dubu aina fada maki kamar yasha wani abu daya zo min gashi kuma ya maimaita agabanki kuma. Ai kuwa bai isa ba yaya don na kula bayin kanshi bane don na fahinci an zugo yaron nan ne mai zaiyi da kudi a yanzu hannunshi ? Tunda kaf komai na dan uwansu yanzu hannunsu yake suke juya mai komai tunda ya kwanta din nan dole akwai wanda ke zugashi yayi wanan abin haka . Mama fa saare data dade tsaye kofan daki ta saurarensu tun shigowan Yazid takara fada hakan yasa uwar ta juyo a hasale tana fadin meye ke kuma ko kema zancen kudinne zaki tayar min da hankali kuma ? Mama in tayar maki da hankali kuma kawai dai nima zance idan za a sayar da kaddarorin a hada nawa don na fada maki ina son in fara sana,an kayan kitchen ne irin na Fatiq . Lokaci guda kawu ya debe hulan kanshi yanawa kansa fitara a hankali ga zufa daya tartso mashi a goshinsa salima tana kallon ikon Allah don ita kadai ta fahinci halin da kawu din yake ciki. Jin yadda Mama din suke fafatawa da saratu yasa ya samu da kyat bakinsa ya budu yana fadin dubu barinje sai dai kinjini kuma. To yaya har zaka tafi kyale yaran nan kada ka daga hankalinka ga zancen nan don Allah rashin hankaline irin tasu kawai sukeyi. Ya dai samu ya fice daga gidan amma hankalinshi ba a kwance ba don yasan akwai magana yau ko kaddaran da yake fadan ya saye baisan inda zaikai Yazid din ba. Hana rantsuwa dai akwai wani fili daya saya amma karamine da niyar ya gina nasa gidan na kansa su tare ciki da iyalinsa don wanan din da suke ciki ya tsufa sosai gashi kuma nagadone da yan uwansu dake jahar Naije zaune saukin abin basu taba bin ta kan gidan ba tun bayan rasuwan tsohonsu da aka dan samu matsala saboda makwabta sun sheda kudin iya yafi yawa a gidan nasu dasuka gina lokacin. Hakan yasa suka fitar da ransu ga wanan gidan harma da yan uwan nasu sai Jafarne ma yake yawan maganan cewa zai kaisu wajen yan uwan nasu shi kuma jiki yaki lafiya a yanzu. Su din kuma ba wai damuwa da zuwan sukayi ba don kawu ya tsorata mama din akan bin yan uwan nasu yace su din matsafane zasu iya tsafesu. Iya kance komai tsafinsu kawu yafisu tsafi ai don zuciyarshi bata da kai zai iyayiwa koma waye mugunta akan abin duniya idan ff,za,ff,fafamfaaftana masu wraffada kalaminta ke nan ga dan nata. Kwantar da hankalina da nayi yasa nayi fresh dani nayi kyau farina ya fito fili da kyau idan kika dubeni sai kin koma ina zaune a falon ummah nida saudatu mun na kallo da rana. Ummah ta shigo falon ta zauna tana fadin Yanda ta kiraki na dago na dubeta kafin na bata amsa da a,a take fadin munyi waya dazun take fada min cewa. Mijikin yanzy ya koma abin tausayi duk ya kara lalacewa ya rame halama kamar ciwonsa nason ya dawo mashi saboda rashin kullan da bai samu yanzu sosai dama kece dai karfin jinyan nasa ai ? Kaina kawar na mayar a tv ba tare danace da ita komai ba a lokacin saidai a zuciyana na fada nakeyi ina fadin wanan shiya shafa a yanzu don sun fini sonshi ai idan ya halaka sun huta don kowa saiya kama gabansa. Haba dau uwata aida kinyi hakkuri kin koma Saudatu ke fadan hakan gareni da sauri na juyo ina fadin in koma ina saudatu gara dai kowa ya taba yaji a yanzu ai. Ba komai ya kawo hakan ba don itama maman tudu ta koma gida sati biyu ke nan yanzu kingako inba iya ba a yanzu ba mai tsayawa ya bashi kulawan daya dace ? Iyan kuma ba karfine gareta ba sai naji ummah tace mahaifiyarsu saida na juya idon nake fadin in kawu ya bari ta zauna har ta kulashi ba ? Ni dai sai ince auren ki da bawan Allah nan uwata auren kaddarane kawai amma ba wani jin dadi ga hakan sai bakar wahala kana amaryan ka ko haihuwan farko bakayi ba zaka tsaya jinya irin haka don Allah ? Haba saudi ai hakan ma bautan aurene tasan irin ladan da zata samu a wajen Allah jinya takeyi fa kuma na mijin aurenta. Duk abinda kagani ya faru da bawa da sanin ubangiji Allah kadai ya san dalilin haka ga bawansa Allah yasa hakan alherine gareta damu baki daya ummah ta katse maganan da hakan duk muka amsa da amin lokaci guda. Take fadin ni kingani nan saudi bawan Allah nan tausayi yake ban abu daine na dan yau wallahi da yarinyar nan da daddy sunbi ta tawa datayi hakkuri ta koma dakinta hakana . Duk abinda zasuyi ko suce mata ta sharesu kawai ladanta yana ga Allah haka kuma wata rana duk sai labari insha Allah don gaskiya mutumin nan yana sonta banga abinda zata tsaya duban iskancin wasu ba dama su ba son ganin ki sukeyi tare dashi ba ai. Hakan da kikayi kuma ya basu daman samun kafan da zasuci gaba da musguna maki ai mutum in makiyinkane kada ka yarda ya samu kafan galaba a gareka ? Ina kurum ban tanka mata ba don nasan indon tasuce ita da yar uwata basuki in shirya kwatsam ince na koma ba a yanzu din ba tare da anyi min gatan da daddy keson ai min ba. Ummah kodana koma wanan matar bawai zata canza halinta bane a garemu na sani amma hakan zaisa na samu dan dama a wajensu ai. Ita Yanda mijinta yana tsaye garesu shiko wanan fa ummah bai iya katabus ga iyalinsa sai abinda tace dashi zaiyi haka kanninsa mata. Saidai hakan amma dai gaskiya ya ban tausayi sosai wallahi zan samu lokaci ai in kirashi mu gaisa inji yaya karfin jikin nasa. To hjy idan kinyi hakan ba laifi bane amma ya kamata kowa ya sharesu nan yadda suma suka share kamar basu damu da itaba yanzu idan kin kira zasuga kamar kina bikonsune suzo nan. Shiru nayi don gaskiya saudi ta fada ba karya a zancen ta don ko kowa bai fada ba mama zata iya fadin hakan kuma naga zancen yayi tasiri ga ummah . Don tace hakan ne kuma tunda matar ba mutuncine da ita ba ta fahinci hakan tun haduwanta da Hjy Sa,a data hada ummah din da mijinta na yanzu da take aure. Don yadda mama taso kushe abin sai Allah ya kawo ciwon Jafar na farko a lokacin hankalinta ya dauke da jinyarsa har aka samu akai auren don hankalinta daya dauku wai a cewanta ga kawu nan ya nuna yana son ummah din a lokacin. Ganin yadda ya rame a kwanakin yasa mama din mayar da hankalinta gareshi saidai tafi saka rai da fadan cewa saboda nabar gidan yake son ya halaka kanshi ga banza ? Har yakai ranan ya bata amsa da fadin mama koda tunanenta nakeyi ai hakan ba laifi bane ki duba yadda aka barni haka ba gyara ba komai kamar mara gata mama ? Ace Asmau bata da lokacina saidai kwanciya idan anyi magana tace aiki yayi mata yawa a hakan kuma take son in barta ita kadai ba tare da wata ba ? To ai tasan hakan ba zai yiyu ba ita dai waccan mara hankalun idan ta gama shashancinta ai dole ta dawo a zauna tare ai yanzu tayi hankali hakan ? Wa kike nufi yarinyar nan Rahama kowa iya ke tambayan mama din tace Rahama kuma uwar yarsa dai ta dawo ta samawa yarta abokan shawara hakana. Bako a gidan nan ba mama don na gaji da fitinan Saiba hankali a kwance yake banson abinda zai raba min hankali biyu yanzu kuma. Rahama dai nake Habu nake son ya dawo daga legos zuwa jibi inbi bayanta in dawo da ita bakai kadai zaka tafi ba dole uwarku taje har yaran nan suyo maka bikon matarka kamar yadda mijin uwarta ya fada. Iya kikanso kamawa karya yanzu don ance sai naje shine zakice har dani zasu tafi in yabi ta tawace ai ko zuwanma ba zaiyi ba shi balle aje zancen wai nima in shirya inje din. Anya biyu kina kaunar dan nan kuwa duk cikin yayanki na kula Jafarune baki damu da damuwansa ba dubu ? Yau da kina da tunane da yarinyar nan batakai wanan lokacin ba a gidansu zaune da akace kece matsalan dake da yayanki da tuni kin tasa keyan yaran nan kun dawo mashi da matarshi. Amma da yake haka rayuwanki take kamar mara kwakwalwa Dubu baki san mutanen nan tarko suka dana maki ba don su gaskanta abinda yarsu taje ta fada. Ki barshi ya taka a hakan har kaduna tunda sakariya kike baki da lissafi kiga abinda zai biyo bayan hakan a karshe. Don ke da kanki zakiyi dana sanin rashin zuwa din duk ranan da tunane ya kara turmuze yaron nan har ya kwanta a gidan nan don saura kiris a kai ga hakan yadda yaron nan ya koma don tunane. Matukar kika bari har ya taka yaje bikon matarshi aka hana masa ki saurari naki bakin cikin da zaki tara akan hakan tunda yaran nan suna son junansu. Har yanzu kina wani zancen wanan mara hankalin ta dawo ta dawo a yanzu tayi mashi me yarinyar da bata san Annabi ya faku ba har yanzu. Matukar Rahama taki daaowa gidan nan dubu bake ba harmu ga baki dayan mu sai abinda zai biyo baya gidan nan ya shafemu kaf a gidan nan . In kuma kince a,a kada kije tunda kece sauniya mara hankali kawai ina mamaki matuka sauyawan yanayin ki dubu ? A yanzu kowa ya zuba maki idone yana kallon wautanki dubu kinsan farin cikin yaron nan kin kuma san komai game da hakan ? Ke yanzu ba abin kunya bane a gareki dubu yadda kowa yasan zancen da irin dawainiyar yarinyar nan a gidan nan kan yaron nan amma ace wai har kin yarda haka ya kasance da ita akan yayanki. ZAINAB IDRIS MAKAWA MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 8️⃣2️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Ya kasance jumma,ace ranan hakan yasa nayi kwaliya na dan gyara fuskana duk da ba inda zan fita don tun zuwana ban fita ko ina ba. Duba ga zancen daddy a gareni hakan yass na kara kama kaina ko marmarin fita daga gidan banyi dama ba gwanar fita irin haka baceni. Wasu material da ummah ta saya min duk da nace da ita kayana suna nan banyi amfani dasu bama a lokacin saidai hakan bai hanata ta saya min ba. Suna dauko na saka ance yaba kyauta tukwici kayan sun karbi jikina sosai zaune nake muna shan ferfesu kwatsan muryan salima ya daki kunnena. Wani irin faduwan gaba ya ziyarci zuciyana lokaci guda a daidai lokacin data tsaya kofan dakin tana kara kwada muna sallama akaro na barkatai ana kuma amsawa tare da fadin tashigo mana. Anty salima don har lokacin ina saya sunansu a yadda na saba kiransu dashi da farko tashigo ta sauke idonta a kaina inda nake zaune kasa saman carpet tare da bin plate din dake gabana da kallo wanda yake shake da koda zallah da saudatu ta gyara muna. A,a kune a tafe salima tace eeh tare muke gaba daya ai harsu yaya da mama jin hakan yasa naso tashi a inda nake zaunen . Saidai na makara da hakan don sun riga da sun fara shigowa falon ko da sallamansu anayi masu sannu da zuwa tare da dan kauce kaucen abubuwan dake gaban mu duk daba muni a cikinsa. Saare da tayi zuwan dole tana ta faman mede muna fuska tana wani dube dube a falon suka zauna kafin ta mayar da hankalinta a kaina. Kallo daya nayi mata na fahinci ranta a bace yake wai ashe tun shigowansu kaduna ta soma fadin amma mama yakamata mu leko su mami muga lafiyansu. Shine ya yazid ya bata amsa da fadin ke saratu nan makirace watau kin kulla gulma duk wanda kikayi a waya bai isheki ba sai kinyi na face to face a gabanta toba zamuje ba din din ba shi ya kawomu ba . Saratu ai zaki iya sauka ki karasa idan kin gama saiki samemu mami kuma idan suna son mu ganta ai sunsan hanyar gidan mu ko ? Yatace mami amma bakin jinin dake zuciyana na uwarta ya sa a yanzu har ina mantawa da ita a yanzu daga inda mama take zaune ta sake wani sallati tana fadin subbahanallahi kanka daya kuwa Jafar kake fadan haka ga yarka. Yarkace fa koma me uwarta tayi ma karka manta yarkace ai dinshi nace ina mantawa dasu a yanzu ya sake fadan hakan. Ita kuma mama sai cewa tayi lalai kanka ba daya bane Jafar na yarda akwai abindake damun kwakwalwanka a yanzu to sai ita,,,, Haba dai dubu don yaron nan ya fadi haka ai kinsan bacin rai yakaishi ga fadin hakan ku bar wanan zancen tunda ransa har yanzu a bace yake game da yarinyar nan Nusaiba. Ai don jan magana munafukar nan ta dauko zamcen Nusaiba din don irin haka tunda tasan abinda ya kawomu garin nan . Tasan ba wurin Nusaiba muka zo ba munzo bikon yar mutunci da sanin ya kamatane wacce tasan metakeyi ba wace son abin duniya ya dama ba Yazid ke fadan hakan. Wanan abinda yazid din ya fada shine yasa ta shigo gidan tana fushi duk gaisawan da saudi ke masu fuskanta a daure yake ita. Kafin komai har saudi din ta cika masu gaba da abincin karyawan mu da akayi hakan ba karamin daukaka saudi din ta ja min ba duk da sunsan ba gidan ubbana bane nan din amma ko hakan yayi min dadi har cikin raina. Mazan suna waje basu shigo ba daddy ya fito suka gaisa dashi shi yayi masu jagora zuwa cikin gidan nasu inda suka samesu a falo suna karyawa nan yazid ya hau masu sheri da sunshigo sun buge da cin abinci. Saudatu ce ta shigo take fada min yaya Jafar dashi akazo yana nan yana baza ido yaga ta inda zan fito a gidan ai sai ya matsa na fada ina tsuki. Uwata ba aiwa miji tsuki haka don shiryawa zakiyi da abinki adaiyi hakkuri din bawan Allah nan yana kaunarki matuka ki duba yadda akazo dashi a daddafe haka daganinsa har yanzu yana jin jikinsa. Amma ya taso saboda ke zuwa nan don Allah ki sassauta mashi kinji kada kice ba zaki bishi a yanzu ki koma dakinki hakana kinji ? Daidai lokacin ummah ta shigo ta samu tana fadan haka sai cewa ummah tayi gara dai ki fada mata donni banga laifin wanan mutum ba. Kada fushin daba nasa ba fushin yan uwasa ya debe maki ladanki ga banza saboda kawai suga kun samu barka dashi suke fata. Saudi ta kara fadin shiyasa nake bata shawara ta koma idan an shirya idan anji abinda ya kawosu sai kiyi hakkuri don Allah ? Muryan Abba daya dawone yake fadin ina ummah yasa ta fito falon aka zauna naji falon yayi shiru iya ta soma magana tana fadin to Alh . Kamar yadda nayima alkawarin dawowa gashi Allah ya dawo damu cikin ikonsa tare da iyalina da kowa don muzo muyi bikon yar wajenka da fatan an huce zuwa yanzu ? Don Allah ayi hakkuri wanda yace zomu zauna kamar yace zomu sabane sai an hada da hakkuri zama ke dadi in sha Allah abinda ya faru da farko ba za a sake maimaitashi ba in sha Allahu. To hjy naji aimu ba fushi mukayi ba kun sani illa iyaka so muke a tsawata akan abubuwan cin fuska da izigilanci da akewa yaran nan yayi yawa. Ina son ku gane bayin yaran nan bane gaba dayansu kaddaransuce hakan aure a gida daya hakama yaran ku maza suma hakan tasu kaddarance tazo a hakan. A zatona yau duk wanda yaso naka haka yagama dakai a rayuwa ba sauran zargi ko wani hasashe ga wanan bawa ko don alherinshi gareka zaka daga mai kafa ka kawar da kai ga duk wani abu tunda yaso naka tsakani da Allah. Ayi hakkuri don Allah a zauna da juna a cikin mutunci sai aji dadin juna a gama da duniya lafiya ga zuwairatu nan a gidan nan ba haihuwa tayi damu ba amma ta kama kan diyan nan ta hade min kamar itace ta haifo abinta. Tsohuwa meyafi wanan farin ciki a wajena yau na samu macen data san darajata data yayana tasan zafinsu tankar itace ta haifesu yanzu haka saisu shigo gidan nan suyi shawara da ita ba tare dana sani ba wanan ai kwanciyan hankalina ko bana raye a duniyan nan haka yan uwana kaf dinsu kowa na zuwa gidan nan yanzu ta dalilin wanan macen da Allah ya ban. Don haka ni a ganina wanan abin farin cikine yau a gareku don duniya ta sheda yarinyar nan bata bar mijinta a wullakace ba daidai lokacin da yake bukatan soyayyan na tare dashi. Duk wanan bayanjn da Daddy yakeyi saratu sai wani harare harare takeyi tana yatsunan fuska tana basarwa tana nuna maganan zucin da takeyi a fili. Ba daddy din ba duk wanda ke falon ya kalketa yasan abinda take nufi da hakan mai karatu ba saratu bafa har mama dake zaune irin shigen wanan yanayin take itama a lokacin. Yazid ne ya karba da fadin Alh munsan kokarin Rahama a gidan mu duba ga yan kwanakin nan da bata gidan bashi da yake mijinta take jinya ba kowan mu a yanzu ya fahinci ranan ta a tare damu. Kwaraima don wallahi ba sai an fadi ba mutum ko yaya yake ai rana gareshi ba a sani kuma sai ranan daya bar wajen za a gane hakan. Balle yar nan data zama tauraruwar gidanmu a yanzu ta share ko ina tas ba kyashi ba hassada kafin gari ya waye tayiwa mijinta komai saidai a zo a sameshi a gyarensa duk wake hakan ita ? Yanzu fa Alh yaron nan sai yabaka tsusayi kamar ka zubar mashi da hawaye don wani abin yana so ba,,,,,,,,,,, Humm,ummm ya fito daga bakjn Saratu hakan yasa yazid fadin tayi karya ko ta juyo tana fadin me nace yanzu don Allah kuma ? Sai in karyaki a nan ta godewa Allah taga nata rayuwan auren ki saurara naki ke kuma saukin abin dai auren sai bawa yayi matukar yana raye . Zaku fara halin naku ko me kaji ta fada yanzu da kake kokarin mata baki har kana fadin ,,,,,, A,a dakata hjy don Allah dama yarki ce matsalan yarinyar nan kaf dinku kun sanda hakan a wajen nan to gashi a gaban mu ta nuna maganar banza akeyi a yanzu. Ina ganin abin nan kawai a hakkura hjy don yarinyar nan ta nuna muna bata da tarbiya da zataji sulhun da akeyi a wajen nan balle a koma a zauna lafiya. Wallahi bata isa ba Alh ita dinme harta isa ta hana min matana zama a gidana saboda ita abu dayane yanzu a gaban kowa tunda tace haka zan mata iyaka da matana dukka don ba ita kadai bace kanwata ai ? Ina da yan uwan dake kaunan zumuci dani sai yayi kamar ya sarke don maganan da yakeyi a cikin bacin rai hakan yasa da sauri dan uwansa mikewa zuwa gareshi tare da goran ruwa a hannunsa. Ya bashi suka hau lalashinsa akan yai shiru don Allah yazid sai fadin yake wallahi kikai sanadin yaya kowaya tsaya maki sai kasheki Saratu. Kin gani dai mama tazo ta nunawa mutane rashin tarbiyanta a nan yanzu haka kuma tana kallon yadda dan uwan mu ke wahala amma wai yarinyar nan tana neman bata muna tafiyan mu don tana yar iska kawai. Kananan maganganu ta soma yi daddy sai murmushinsa yakeyi irin nasu na manya yana kada kafanshi irin yasan za a rina ? Saida iya ta samu sukai shiru ta hau fada yake fadin dakata tsohuwa wanan abu ai mai saukine yanzu kai malam Jafar kaje kayi hakkuri don muna son yar mu gaskiya. Rahamatullah ba zata koma gidan ku ba da wanan halin da kuka nuna muna a gabanmu which means koda ta koma dai halin yana nan bai caza zani ba. Yar mu tana fama da laulayin ciki don likitoci sun bata hutu komai batayi a yanzu sunje asibiti da uwarta an sakata a rest don haka kuje kawai Allah ya hada kowa da rabonsa. Don wanan abin ba zamu mayar da yarunya wajen da babu kwanciyan hankali ba alhalin mun sani kuma mun gani wani abu yazo ya sameta. Saiga iya a kasa tana hada daddy da Allah yaiwa Allah yayi hakkuri ya bar Rahama ta koma dakinta kodon mijinta tayi alkawarin ba abinda zai faru insha Allahu kuma. Tausayin iyan yasa daddy din ya sauko yake fadin tsohuwa kuje insha Allahu zata dawo amma ba yanzu ba saita kara samun lafiya za a dawo da ita. Yazid da aka hana magana sai lokacin ya samu furta don Allah Alh ayi hakkuri kodon halin da bawam Allah nan yake ciki da cewan Jafar. Sai daddy ya gyara zama ya soma fadin ai nace zata koma amma ba yau ba sai ta kara lafiya saidai ina son ku sani matukar uwarku gata a zaune bata daina wanan halin ba ba macen da zatayi marmarin zama da iyalinta. Mama din ta kallonshi yace yes ni ban tsoron kowa da kuka ganni nan ya fara karanto masu mukaman daya rike da yake aiki inda ya dora da fadin . Yau a duniya mutum ya fito filli kiri kiri ya nuna nasa yake so dan kowa ba da bane a wajensa sai duniya ta barshi da dabaranshi a hakan . Banga inda zaka dauko dan mutane ba ko danka ya dauko ka nuna naka kake kauna a fili duk mutum mai wanan halin abin tsorone gaskiya. Anso dai ayi ba dadi a wajen don daddy ya tsaya ya fadawa mama gaskiya shida iya sai gata tana kuka tana fasin a gafarce ta ita ba a a fahince ta bane yakawo hakan. An dai basu hakkuri akan su koma daddy yayi masu alkawarin shi zai kawoni har zaria da kanshi idan na kara jin dama don kada abi hanya dani a jijigani wani abu ya faru da cikin jikina. Saida zasu tafine daddy yasa na fito wai inzo mu gaisa dasu din banso fitowan ba amma don gudun bacin ran iyayyena din dole na fito muka gaisa dasu. Najin dadin yadda daddy ya nuna masu akan mu yana iya sharia da kowa koda duk abinda ya mallaka zasu kare saidai su kare din . Amma matukar aka kara muzanta ni ko yar uwata a gidan yadda akayi a baya zai dauki shari,a dakoma waye ba ruwansa da kankantan mutum ko tsufanshi. Sukayi sallama damu haka suka tafi donni tun bayan gaisuwa ban kara kallon inda yake ba asalima haushinsa naji ya karu min a zuciyana don yadda sukazo din sukayi. Ban kuma rakasu ba na koma dakin ummah na kwanta ina hadiyan bakin rai daya tokare min zuciya tare da tunanen mama ita wata irin macece wai ? Anya kuwa ko Jafar din tana kaunarsa kuwa a zuciyarta gashi ya rame ya zama baki sai kasumba daya tara a fuskanshi dama nice maiyi mashi aski yanzu ko nasan bai yardane kowa yayi mashi. Suma a mota da fada sosai aka dawo gidan inda suka taru sukaciwa saratu mutunci don kuwa suna barin gidan mu saiga wayan Nusaiba tana tambayan ance sun shigo kaduna din zasu karaso gidansune suga mimi yarta ? Nam yazid dake jin abinda ya fada ya soma fada yana kantamawa saratu zagi yana fadin idan batayi hankali ba saita rasa mijin aure tunda ta zama iblis ? Uwar taso fada wai don me zai kirata da iblis iya ta tare ta kara fadin aita zama iblis don inda rahama yake bata a wajen sai hadin hasumi shine nata. Nadai gane baku kaunar yaron nan da alheri daga ke har uwarki saratu duk yadda akayi kinkai uwarku wajen malam da kuke bi dake da yarinyat nan da har bata ganin laifinki a yanzu ? Nikan iya ku kasheni ku huta yafi wanan aibantanin da kukeyi haka ai bata karasa ba shi mara lafiyan ya juyo yakai mata mari tas sai da kowa na motan ya kadu. Cikin irin maganarsa na saurin harshe ya soma magana yana fadin kar kiga ina kyaleki ki zata ban iya daukan matakine a kanki tausayin ku nake ji ba komai ba ? Iskancin nan ya isheni daga yau ki kama kanki dani da duk wani abu daya shafeni don kinga ina kyaleki zaisa har ki wuce gona da iri ? To muzu ba dani dake a gidan nan kuma na baki nan da wata daya ki kawo miji kona aurar dake ga duk wanda naga dama a zaria. Haba dai kuyi mata fatan samun mijin mana sai mugun fata kukewa yar uwarku haka ko yaya take dai ai yar uwarce sai kuyi hakkuri da halinta. Kema bakin tsiya yayi maki yawa meya kaiki fadawa Nusaiba mun shigo tunda kinsan ba wajenta muka zo ba don kawai ki tayar da wani hasumin wa kanki kome ? Kaji ko J mama bata ga laifin yarinyar nan ba sai namu shike nan ai ranan da duk kika iskancin ki a sai kin iskamci ki tsaya dashi iyasu da saba yiwa amma bani ba don ban iya daukan wanan halin banzan naki. Na rasa yadda akayi yarinyar nan ta koma haka jafar yake fada cikin takaici sai iya ta amsa mashi da fadin dama hakan take ai halintane a hakan . Wanan yasa mama tayi shiru har suka kai zaria bata kara magana ba mota na tsayawa suka shiga ciki nan tahau fada da yar nata tana fadin . Da wanan halin kike tunanen zakije aure Saratu na dauka abinda zaki barine ashe abin naki bana bari bane ke a gurinki. Bansan baki da wayau ba sai yau din nan ki rasa wanda zakiwa tsiya sai Jafar duk irin kokarin da yaron nan yakeyi daku sakaiyar da zaki mashi ke nan ? Kallon mamaki saratu ke mata tace kwarai indai kinayi don Nusaibace tun wuri ki daina don bani kaunar yarinyar nan mai bakin wayau tsiya ta dawo gidan nan . Taje abinda sukaci a gareshi ya isa hakana naji da wanan dake son tsaya min a makoshi don na kula Jafar baisan ciwon kanshi ba. A zatonsu naje bikone saboda Allah na daije kawai don kada ya halaka a yanzu tunda ya kwallafa ransa ga yarinyar nan don shi kawai naje kadunan nan . Dukkansu biyu kallon mamaki sukewa uwar har dai Salima dake kallon ikon Allah yanzune fa suka bar kaduna tare da alkawari akan dawowan Rahama dakinta amma mama take fadin wanan magana kuma ? Tsam ta mike zuwa daki cike da tsoron halin mahaifiyarsu din tabbas wanan hali na mana yasa bata shiri da saurab kishiyoyinta ashe ? Da wanan tunanen ta wuni ta kwana sai washegari data je gaida yayan nasu da kwana take basu labari shida iya. Iyace ma ta hau fada yana zaune baice komai yayi shiru yana tunane a zuciyarshi kafin ya umurci ita salima din data gyara masu part din don yasan idan ba ita ya saka aikin ba Asmau ba zata taba tunanen zuwa ta gyara masu ba dama kuma yana jin haushin halin ko in kula da take nunawa a kanshi. Shidai abinda ya dauka hakan wani jerabawa a rayuwansa Allah ya kawo mai dan ya kara imani da hukuncin ubangiji ga bawa. A yanzu yasan masoyanshi da kuma masu nuna hassada akanshi dan zaman jinyar nan da yayi gida bai fita ko ina. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/21, 07:47] Aisha Srtr Mt: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 8️⃣3️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Sai daga baya na fahinci daddy daya fada masu cewa banda lafiya don haka sai naji sauki saudi ce ke fada min ai gata yayi min da fadin hakan . Yanzu kinga ko kin koma gidansu bake ba sauran wanan aiyukan da suka bar maki ke kadai dole za a canza tsari yadda ya dace ko kuma ya dawo naki gidan kamar yadda akeyi a baya tunda ya samu lafiyan fita a yanzu. Saidai wanan kaunar tashi kamar har yanzu tana da sauran ja don yanayinta ya nuna bata saduda ba ? Bam tsamani cewa zasuje wancan gidan dayar matarsa yada sukaiwa yarinyar nan caaa a kai ita kuma munafukace dai ta karshe watau ? Kinsan ya rabu da ita meye na kiranta a waya kina fada mata sirin gidanku koda yake uwarma da alama goyon bayanta takeyi yadda takw ba diyan nata amsa. Murmushi nayi kawai bansan me zance a zancen ba tunda gaskiyar ke nan ta fada na rasa gane mama ko wace irin uwace ita ? Da bata iya tsawatawa Saratu wanan halin yan wutan da takeyi na hadin hasumi gashi ta sani ba abu mai kyau suke aikatawa ba ita da Nusaiba amma sai ta tsare kada ayi mata fada. Saidai wani lokacine ita kan dan tsawata mata idan ta wuce mata gona da iri a lamarin ta koshi ba ko yaushe ba sai can ba a rasa ba zakiji tana tsawata mata din. Nidai har barci ya daukeni tana zuba bansan tashinta a dakin ba saida na falkone na ganni ni kadai a daki ina barci hakan yasa na tashi na kashe tv na koma daki na kwanta duk da dare baiyi ba sosai a lokacin . Sai bayan kamar kwana biyune da zuwansu ina zaune ina shan iska a waje da yamma saiga ummah da kudi a hannunya ta zauna a kusa dani tana fadin. Ungo wanan daddy yace a baki koda akwai abinda zaki saya a nan kafin ki koma zaiwa antyku Nuratu magana tazo ku fita tare da ita . Kudin nabi da idanu ban karba ina mamaki nace ummah me zan saya kuma komai yaya J yana sayo muna a can ? Kingani ai munsan da hakan shiya muketa baki hakkuri don shi bai maki komai ba uwarsace da kanninsa sukai maki laifi bashi ba ? Don haka ba zaki hada duk dashi kice kina fushi ba ko ranan har suka koma baki kirashi kinji yadda suka isa baiyi fushi ba ya kira kuma kikaki dagawa ? Da sauri na dago na dan dubeta na maida kao kasa na sada tacigaba da fadin banga dalilin da zaki hada dashi kina fushi haka ba ? Su dai da suka tabaki ai dasu zakiyi bashi ba ummah idan banyi hakan ba ba zai dauki mataki ba wata rana kuma har sai kuji cewa sun kai ga taba jikina tunda suna da niyar hakan dama a manufarsu ? Kinga kuwa da ace sunsan bai kaunarki da yanzu sukai ga abinda suke so don ba wanda yayi tsamanin cewa zaiki kai har wanan lokacin a gidan ? Yau gashi har Allah ubangiji ya kawo rabo a tsakanin ku abinda basu taba zaton zai faru ba ke nan don ance suna fadi wai saidai kiyi zaman wahala kina jinyarsa din da kikeyi a kare ga hakan. Kwatsam saiga shigan cikin nan na jikinki koshi bai isheki godiya ga Allah ba a sanadin cikin ne ai ita dayar kishiyar taki ta fita tabar gidan ko ? Don Yanda na fadin sosai suka girgiza lokacin da baiyanan wanan cikin na jikinki don haka dole ki daure ki koma dakinki a yanzu koyi goyon cikin nan a gidan ubansa yadda basu kaunar gani din suga Allah ya fisu. Don Allah Rahama ki koma kiyi hakkuri a dakinki ki dubi mijinki dake fama da kansa don Allah ko sun kiraki da yar wahala kinfisu morewa Rahama don ladanki yana ga Allah. Allah ya gani mu munsan da zuciya daya kike zaune da Jafar kosu sun sani abu daine na hassada akan mutum kawai sukeyi. Don ni uwarsu na kasa gane alkiblanta har yanzu na rashin kaunarku da yayanta da batayi ban taba ganin uwar da bata da tunane irin wanan matar ba a rayuwana. Tanayine don zugin da dan uwata ke mata a kanmu ummah tanayin ne kuma don kawai an sakata tayi muna hakan kada mu mamaye masu gida kamar yadda dan uwanta ya fada. Dan murmushin yake ummah din tayi tana fadin kaiya ta makaro wallahi ai tunda ta haifa sai an mora din yadda bata so. Yanzu dai ki karbi kudin nan ki shirya din gobe ku fita da antyn naki don jibi zasu mai dake dakinki in sha Allahu. Jibi kuma ummah na tambaya da sauri ta mike tana fadin me zaki zauna nan kiyi Rahama ga mijinki can yana bukatanki a kusa dake. Ta juya ta tafi nabi kudin dake hannuna da kallo zasu kai dari biyu kila da dan kai don nauyinsu da naji a hannuna din. Koda na shiga daki na samu wayata dake makale a caji tana ta rigin na duba shine a kan layi yake kirana har yayi min three mis called a lokacin ina waje. Kamar zan share sai kuma na daga da sallama ya amsa yake fadin ina ta kira baki picking ba tun dazun dama nace in tura habibane ta gyara maki daki ? Ai Key din suna wajena na bashi amsa da hakan yace saida nayi tunanen hakan saidai falon da sauran dakuna ko nacewa Yazid a kawo maki kayan abinci fresh a kwashe wa yan nan tunda sun dade . Nagode kawai na fada a darare yake fadin please Rahama kiyi hakkuri kada kice baki dawowa yanzu rayuwana tana bukatanki a kusa dani wallahi. Da sauri nace dashi aiba ni kadai bane bayan haka akwai yan uwa kaida kake cikin gatanka ga kowa naka a kusa zakace kana cikin wani hali a yanzu ? Haka dai kikace idan kika wuce satin ban Allah saidai in dawo kaduna daddy ya bamu daki a nan mu tare baki dayan mu. Kit na kashe layin cikin takaicinsa don ni dai shine ya jefani a wanan halin da ya barni yadda muke da shike nan yanzu muna zaman mu lafiya da kowa a gida yaje ya kawo zancen aure a tsakanin mu daya jawo min bakin jini a cikinsu yanzu. Zama nayi ina tagumi a bakin gado tunanen abinda zan koma in tarar yanzu kuma a gidan nakeyi duk da nasha alwashin cewa ba zan kara kulasu ba duk abinda zasuyi min nasan wanan karyane muje dai din don dole wata rana in kula. Nusaiba kuwa daga ranan da suka shigo kaduna din zuwa wanan ranan tashiga tashin hankalin dayafi a girka duk iya shige shigenta bukata bai biya ba yadda malamta suke mata karyan zai faru din. Don gashi har kaduna suka shigo amma ba wanda ya kula da lamarinta har waya da tayi da mama ta fahinci maman batayi na,am da hakan ba. Koda basu zo donta ba ai zasu shigo su duba yarsu dake tare da ita amma kememe tayi ta jiransu sai sakon Saratu data samu cewa sunma kusa shiga zaria ai. Hakan yasa ta kasa hakkuri ta dinga tura masu sakon bakar magana a cikin bacin rai tana kara dasa kiyayarta a zuciyarsu wanda ta dauka hakan gwanintane a wajenta ai. Abinda nake son mata su kulla a nan shine matukar kina shuka gaskiya cikin lamarin ki ubangij Allah yana tare dake a ko wani hali saidai idan kece kika raina abinda kika gani din a kanki. Ban taba zato ko tsamanin cewa zasu shigo haka kamar yadda daddy ya bukaci ganinsu ba amma sai gashi Allah yayi ikonshi dole sunzo din har gaban su ummah suna bada hakkuri. Washegari anty Nuratu tazo gidan ta daukeni farko wajen wata mata muka tafi yar maiduguri ina dai kallonta a raina nace nu dake da mummy a abuja ana gwada min wanan abin ? Saidai lokacin da matar ta fara fitar da kayanta na fahinci kowa da nasa sabin ashe ita anty Nuratu din ta biya da kudinta muka fito daga gida. Muna mota take fadin ni naga no need asai maki wasu sutura a yanzu haka zaifi kyau bayan kin haihu muyi wanan shirin . Nima ban ra,ayin wasu sutura wanda aka dinka a baya suna nan cushe ta juyo tana fadin wallahi ki dingawa mijinki kwaliya kanwata. Kada ki yarda ki saje da wa yan nan matar nasa marasa kan gado ga miji tsab tsab aje aga matansa kamar rainon kauye ba kyau gani . Ni tun a nan na raina masu wayau wallahi suna ganin don yana kwance yana jinya ba zaiji dadi bane idan sun gyara jikinsu ? Krdai abinda nake so dake ysnzu Rahama shine kada ki yarda ku zama daya dasu don Allah ki bambanta kanki dasu ta wajen kwalliya abinci da gyaran gida. You are lucky ma ba a gida daya kuke rayuwa da kazantannan ba don wallahi dazaki sha wuya ga hakan don haka ya kasance ya zamo yana mararin dawowa gareki ko yaushe wanan ne kishin zamani ai ba zama ana hauka ba. Haka kuma zancen yan uwansa daddy ya fada min komai kada ki kara damuwa da lamarin su don Allah shi dan uwa marfin jallone basuyi saida shi haka kuma shi bayayi saida yan uwansa. Ki dai dauki matakin zama da kowa don Allah kada ki kara bada daman da zasu rainaki kuma ki daina cacan baki dasu haka ko yaushe. Sufa yanzu takaicinki sukeyi sister suna ganin kece star din gidan duk wani shawaransa dake yakeyi so kinga dole suyi bakin ciki dake haka ? Yaushe zaki wuce servuce dinki jn haka yasa na gyara zama ina nsawa nace zuwa next month ne in sha Allahu. To ki mayar da hankali don Allah Rahama ki dage sosai ki zamo wata a cikin family dinku don Allah kece Allah ya zabo kila da zaki tallafi kowa. Ki daina yawan shiga cikinsu sai un wani abu mai muhinmanci ya faru ke leka kada ki jima ki fito sosai zaki dauki girmanki fa Rahama . Ita wanan kanwar tashi ba komai bane illa zallan hassadanki da takeyi tunda taga kin tsaya kinyi karatunki tasan zaki zama wata abu nan gaba a cikinsu. So ina son ko baki dauki shawarana dukka ba Rahama kiyi amfani da wasu don Allah a karshe takaini wajen gyaran jiki aka lugudeni tas na fito kamar bani ba . Anan take fadin ki kula ki dinga shigowa kina gyara jikinki ko nan ko kano din duk da nasan zarian ma ba za a rasa ba amma ba zaikai nan dinba ai. Kamar yadda ummah ta sheda min wanan sister din daddy da muke kira da gwaggo Laraba itace dasu anty Nuratu suka mai dani gidana na kaduna ranan jumma,a . Nayi mamaki kwarai yadda naga yan sauye sauye a gidan anyi min hakama wajen gidam anyi sabbin abubuwa na zamani a haraban wajen gidan. Saida aka fito daga jumma,a sukai shirin komawa kaduna a lokacin kuma ya bugo min waya yana min barka da jummah yake fadin sun fito daga sallah yanzu ya dora da fadin. Watau har satin nan ya shige Rahama bakiji tausayina kin dawo ba ke nan Allah ina wahala rashinki a kusa dani sosai Rahama goben nan zaki ganni a kaduna ai. Idan kaje ka gaidasu nikan ina zaria yanzu haka tun karfe shadayan rana muka shigo garin nan nidasu anty Nuraru. Kina ina yanzu na sameku nace gidana a takaice sai naji yace wasa kike min dai ki dawo garin nan ace ban sani ba Rahama ? Duk da ina daurewa a yanzu don fada da nasihan danasha a kanshi na dan daina jin haushinsa da nake ji kamar farko amma hakan bai hana na dankara mashi magana ba. Don Allah wai da gaske kin dawone ya sake tambaya nace kazo ka gani mana yanzun nan ma su anty ke shirin komawa kaduna su. Ina jin yana fadin kai mu gani koda gaske takeyi ya kashe wayan tashi da sauri muna falo suna batun fita suka shigo shida Yazid. Har yanzu dai saida dabara tafiyan nasa haka kuma kallon daya zakiyi mai ki fahinci yana sauran jin jikin nasa karfin haline kawai yakeyi irin na dan adam. Fuskamshi kyam a nawa yake fadin wallahi na dauka wasane kike min baki dawo ba suka shiga gaisawa dashi gwaggo tayi mai nasiha sosai kafin ta mike tana fadin Allah ya bamu alheri. Sun tafi Yazid ya rakasu har gidan mai ya kara cika masu tanki da mai ya kuma basu tukwaicin kamar yadda dan uwan nasa ya umurceshi dayi garesu. Muna falo zaune dashi mama ta kira wayansa tana fadin wai ina kuka tsayane baku dawo kunci ahinci ba kasha magani ga wanan mutumin yazo fa ? Ina nan gidana mama gidanka naji ta tambaya da mamaki yace eeh wajen Rahama data dawo yau nazo daga masallacin inyiwa wa yanda suka rakota godiya. Ta dawo fa shine zata wuce can gidan don ta raina mutane muryan Saratu ce karara a wayan take fadan wanan magana ga uwar. Kallon juna mukayi dashi kafin muryan mahaifiyar tasu race dashi ke nan basu kawota nan ba sai can gidan suka ajeta wai ko sun manta kana da uwane wai ? Kit naji ya kashe wayan ya kalleni yi nayi kamar ban fahinci me hakan ke nufi ba yana nan zaune muna dan hira jefi jefi har yazid ya dawo ya daukeshi nake fadin. Ya kira yaya Ai ya sheda masu na dawo a turo min Biba yace nayi tunanen hakan nima anji zan zo da ita insha Allahu suka fice a gidan sai annashuwa yakeyi da kaninsa yazid. Bandai nuna a gabanshi zancen saratu yaci min rai ba da alama kuma har mama ta hau zancen saidai na share kawai na nuna ba komai a fili kamar ma banji ba. Ya zama dole a matsayina na diya mace in kara hakkuri in daure in dinga shanye duk wani bacin rai da iskamcinsu yanzu tunda nasan manufarsu a kaina yanzu matukar ina son zama da mijina lafiya. Wanda su basu ko iya boyon hakan har salima din da muke dan shiri wani lokacin bata iya boye hassadanta a kaina saita fada a cikin wasa. To tunda na fahinci Basu da wani guri saidai suga an samu matsala a tsakanina dashi ke nan tunda na fahinta zanko tura masu haushinsu akai a yanzu zan nuna masu kan mage ya waye ashe ? Duk da bansa a raina zai dawo gidan ba a ranan don yadda naji kalamin mama da nayi sallah la,asar na fito na gyara gidan tsab duk da ba wani datti na feshe ko ina na rufe window da kofa tunda sanyi akeyi tuwo kawai na dora don ummah tasa saudi tayi min miya mai yawa nazo dashi . Ga kuma soyayyen nama da sauran abin bukata don haka aikin ya rage min a lokacin ina kwance falo muna waya naji horn din motarshi gidan yazid ya kawoshi. Bibace ta fara shigowa sai su a baya da gudu tazo gareni tana rugumana nayi murmushi don naji kewam yarinyar sosai dan rabuwan da mukayi din. Nan yazid ya zauna yake muna sheri donshi akwai son barkwanci damu haka don koda su Asmau nakanga yana dan taba hakan saidai ba kamarni ba da sosai yake wasa din dani. To ni zan tafi yau akwai sanyi wallahi ga sahiba na barta ba lafiya na fito yau dai za a barni na huta tunda madam ta dawo yaya . Zaka koma ka samu jidalin mama kuwa don dai nasan yau kokai ba za a barka ba wajen fada haba dai ina jira ai sai kaji na balla yarinyar nan saratu zuwa gobe idan tayi wani rubishi akaina zanci kaniyarta sosai wallahi. Biba je kitchen ki debi abinci kici nace don basar da zancensu nan yazid din ke fadin what dama iya ta fada ai ko jiki ka mayar a yanzu. Don Allah Yazid idan ka koma iya ta shiga cikin gida ta kwanta don kada a barta a nan ita kadai kwanan nan duk bata kwana da dadi wallahi zazzabi yake damunta a cikin dare haka muke kwana da ita. Abinci fa na fada ga yazid din yake fasin naso in zauna naci abincin nan amma kuma ina gudun makara me kika dafa mai nasan yau ai sai didima a gidan nan. Murmushi nayi ina fadin tuwone kawai donshi nake so shi kuma nayi yace a zubo mai yaje dashi hakan yasa na mike na hado mashi tuwon ya tafi. Saida na zauna nake fadin iya ba lafiyane kuma yace wallahi takai kwana biyar a hakan kafin yaci gaba wayanshi ya dauki ringing lokaci guda ya dauka yana dubawa. Mamace take fadin Jafar ina ka fita da sanyin nan kuma nazo baka shiyanka mana ya bata amsa da fasin gani nan yazid ya kawoni gidam Rahama. Sai naji tace dashi gidan Rahama kuma da daren nan wai kanka daya kuwa daka je can din maganin kafa da sanyin nan ka kwashi kafa zuwa gidanta don kawai ta dawo a yau kome ? Mama wanan ba abinda ya shafeki bane fa ni hakan ya shafa Rahama matatace kuma dole inzo gidanta tunda Allah ya ban lafiya a yanzu. Anzo inda ba a son azo din ranan da zai fara ba mama amsa irin haka dama daddy ya fada a karshe zata gusar da wanan biyayyan da yake mata ita da kanta lokacun daya fara hakan kuma ba zataji dadin shi ba kuma. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/23, 14:10] Aisha Srtr Mt: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 8️⃣4️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, A cikin zancensu da mama a wayan na fahinvci baida niyar komawa gidansu a ranan yana nufin a nan wajena zai kwana ke nan. Banyi magana ba a lolacin saida yayi sallah duk a nan falo na bashi abinci yaci an dan jima nake fadin Yazid din bai dawo ba har yanzu ga dare nayi kuma baka sha maganin ka ba kuma !? Kin ce ya dawone ya kawo mj magani ya tambayeni cikin tsureni da idanuwanshi da sukayi mugun fadawa a yanzu saboda raman daya karayi kuma yana son jin amsan tambayansa a gareni. Saida na sada kaina kasa nake fadin ni bamuyi hakan dashi ba naga dai kana shan maganine bai kamata a kyatare ba kuma ? Rahama ko kema gudana kika farayi yanzune kamar wa yan can dama da wanan maganan yakanci galabata idan irin haka ya taso a tsakanin mu. Gudunka kuma ban guje ka ba a baya sai yanzu na fada ina daure fuskata to ba inda zan tafi yau nazo ke nan dama ai kece mai jinyata din suka koreki ko ? Ka daiyi kwanakinka ka koma ni kada ka jawo min wata magana kuma a sakani a faufai ana tallah na bayan wannan da nake cikinsa. Suyi tayi mana waya damu da zancen mutu ni yanzu ban kara jin nauyi ko idon mutane a irin haka abinda zai fitar dani zanyi idan sun damu dani su biyoni nan su dubani ai. Wani kallon mamaki na sake mashi amma ban furta komai ba saboda gudun rashin fahinta amma nasan hakan ba abu bane da zai yuyu a garemu a yanzu. Bayan hakan nima ai ina bukatan hutu don haka ba zan sake wahal da kaina ba irin danayi a baya koma yace din zai zauna a nan nasan mama ba zata taba barinshi ya zauna din ba. Mikewa nayi na shiga bedroom dinsa har lokacin banyi magana ba ya bini da kallo na jima a ciki na gyaro mai ko ina na sauya zanin gadon nasa mai duhu saboda maganin da ake bursune masa jiki dashi . Ruwan wanka na hada mai na fito na samu yana waya na wuce zuwa kitchen na dan kawar da kaya na fito na samu ya gama wayan nake fadin ga ruwan wanka can na hada ma saidai ban sani ba ko saida magani kakeyi har yanzu. Yanzu da ba maganin a kusafa ba sai in watsa hakana ba yaushema rabona da wankan dare tun tafiyanki ai sai inkai kwana uku ma yanzu ko wankan maganin banyi ba. Da sauri nace saboda kaji sauki ko ka daina magani bayan ciwon bai gama fita a jikinka ba har yanzu ? Saida ya langabe kai yake fadin bari kawai Rahama shiyasa manya ke fadin Allah ya kawar da ranan yabo ga mutum aini naga abu dan tafiyan nan naki saidai kawai a kyale kawai ba a cewa komai. Amma ai yanzu na fahinci kowa a duniyan nan ki bari kawai Rahama sosai zakiga halai yana ya canza a yanzu don darasin dana samu a kwanciyar nan da nayi. Zance da bansan dawa yakeyi ba don haka ban yarda na zake sosai ba illama cewa da nayi ka tashi ka watsa ruwan kada dare yayi. Yai shiru kamar yana tunane kafin naga yana kokarin mikewa tsayen daga inda nake nake fadin kona taimaka makane ka mike ? Yace bari na dafa kujeran ai yanzu dole na koyi hakan tunda ba mai zama dani sai iya, iya kuma aiba zan bata karfina ba tunda itama ta kanta takeyi yanzu. Haka dai ya samu ya mike ina bashin a baya a dakin daya kai saida ya zauna yana ajiyan zuciya nice na taimaka mashi ya mike tsaye zuwa ban dakin nayi set up din komai don har kujara da zai zauna saida na cudashi na fito na barshi ya kara din. Daki na koma na jawo goran ruwan zam zam din da anty Nuratu ta bani na diba na fito zuwa dakin shi na samu har lokacin bai fito ba nayi magana ina fadin har yanzu baka fito ba ashe ? Sai naji ya amsa da fadin ina kara zubawa jikina ruwan zafinne don sunyi min dadi sosai a jikin zama nayi na fara jero adduan data koya min . Wanda kowa ya sani ga sauki ga falala ga musulmi shine suratul fatiha da ikilas sai la,ilaha illah anta subba hannaka innin kummtu minal zallimin kafa 41 da daya data kira shi da raina kama kaga gyaya . Koda ya fito ya samu ina sauke falaki da nas da kulluhullahu kafa uku uku ina tofawa yana zuwa ya zauna na mika mashi ya sha . Saukin abin sam baida gardama shi kam ya karba daga hannuna yana bissimillah ya kafa kai ya fara zuka nace ka dan rage in shafama ya amsa da kai ba tare da yayi magana ba. Saida ya shaye ya miko min na karba na fara shafa mai a jikinsa ko ina sai faman ajiyan zuciya da yake saukewa ana son ya bushe a jikin mutu don haka na barshi nace kada ya rufa sai ya sha iska. Na leka dakin Biba na samu tayi barci nayi mataa addua na fito a yanzu in shha Allah ban sakaci da addu,a abakina tunda aka tunatar dani hakan.. Na kashe mata wuuta na fito daga dakin nawa dakin na koma na kimtsa kaina tsab na rufo kofan zuwa dakonshi na saami ya kwanta shima a bakon gadon na zauna ina karanto addu,oin dake bakina na neman tsari daga Allah. Shina fara tofawa kafin ni nabi bayanshi na kwanta a hankali ina jin yadda yake sauke ajiyan zuciya jefi jefi zakice yayi zuciya akan wani abune ? Shigowan mijin nata ta gaidashi ya amsa yana tambayan yaranshi ta bashi amsa da sunyi barci abinci ta mike ta kawo mashi saida ta hada mai komai ta samu waje ta zauna tana fadin. Dazun su anty Nuratu sunzo daga kadun wai sun dawo da Rahamane yau har ya dauki kofin ruwa zai kai a baki ya dakata yana kallonta kafin yace. Dama yau zata dawo ashe ta bashi amsa da ban sani ba nima saida suka biyo nan ni suna min fada wai ina nuna ban damu da Rahama ba yanzu? Ni yaya suke son nayi don Allah kowa yana ta ganin laifina akan Rahama yanzu shiyasa wallahi ban so auren nam nata da yaya ba tun fatko don gudun irin haka. Kai baka gama daukan naka laluran ba ace sai ka dauki laluran wani ita Rahama ai tunkan ta auri yaya tasan abinda dake cikin gidansa. Kuma ta yarda ta zauna dashi shiya tare ta da fadin kanki daya kuwa kalau kike kike fadan wanan maganan ko so kike ta bijirewa iyayyen ku da suka bada goyon bayan hakan ? In ma laifine su hardo suvkeda laifin ai da suda basu binckeki ba suka daura mata auren dashi amma ita Rahama umurni tabi ta zauna dashi. To ni dai wanan auren a yanzu yasani tsakiya gaskiya nan yan uwanku naganin laifina cewa dani na hada komai nayi sheri data auri yaya . Can kuma gida sun koma ganin laifina a yanzu kan naki tsayawa yar uwata in mara mata baya murmushin da mijin yayi yaci gaba da zuba abincinshi shiya katse mata magana. Sai binshi da kallo da tayi a cikin tuhuma saboda me yayi murmushi bai tsaya kulata ba ya soma cin abinsa falon yayi shiru na dan lokaci kafin taji muryanshi yana fadin. Yanzu dai na fahince ki so kike ta kashe auren ko ? Ko kuma bakiyi na,am yanzu da dawowan datayi gidansa bane da sauri ta tare da fadin ka rufa min asiri don Allah ni ba haka nake nufi ba kawai dai gani nayi a yanzu kowa ya dora laifin hakan a kaina. Ko anyi hakan daidaine Maria ja rasa irin halinki nako in kula har yar uwarki da kika san kece sanadin zuwanta gidan nan kina nuna halin ko in kula irin naki a kamta. Dolene Rahama tayi fushi dake ta nuna bacin ranta duk abubuwan nan dake faruwa kin taba tsayawa kika nuna damuwanki a kai ? Rahama ce fa ku kenan ku biyu ga mahaifiyar ku sai yam uwanku maza amma zurin ciki ya hanaki fitowa ki kare yar uwarki don kada a zargeki ? Nima nazo daga baya nayi tunanen rashin kyautawa yarinyar nan mu ya kamata ace mun tsaya mata ba sai tabar dakinta zuwa wajen ummah ba. Nasan Saratu yar banzan yarinyace sosai idan ta saka abu a gaba daki sai taga bayan abin wanan yasa nayi mata iyaka daku tun farko . Wanan kuma yanzu ni ba mai zama bane balle insan abindake gudana ke kuma baki kirana ki fada min to yanzu gashi ta gane hakan ta dauki zafi dake kuma abin ya dawo ya dameki. Tana da gaskiya idan tayi hakan don mu muka fara nuna mata rashin kullawan mu su kuma aiba fushi sukayi dake ba tunda har sun biyo nan sun duba lafiyan ku. To amma baban ,,,,,, dakata haka maria don Allah wanan zance ya isheni ki barni inji da wanda ke gabana a yanzu don Allah yaci gaba da cin abincin kafin ya daga ya barta tana kuka a wajen. Nima haka na kwana ina tunane akanta don tun bayan zuwan da sukayi gida bamuyi waya nida ita ba saboda ta hau fushi dani wai naki girmama mijinta indawo a lokacin. Kiran sallah asuba na farko na tashi zuwa bandaki na dauro alwala na dawo na fara nafila saidai saidana dubashi yana barci har lokacin cikin kwanciyan hankali hakan yasa banyi dogon motsi ba kada yaji ya tashi a lokacin. Don a lokacin barci ake son ya samu issashe a rayuwansa idan ba hakan ba daya tashi shima tunkan na tashi din din na shedeshi gaskiya akan addini sosai. Shi mutum ne da aiyukanshi basu hana mashi tsayawa bautan ubangiji hakan kuma yana raya dare wajen bautan Allah saidai ba kullum ba. Muryan ladabin unguwar na kira na biyu naga ya falka ina zaune ina lazumi a inda nayi sallah nasan idan ma ba yanzun daya dan ji sauki ba bai iya dagawa da kanshi ko alwala a baya saina kawo wani tasa mai fadi nayi mashi kafin naje gida dana koma gidana kuma maman tudu ce ke taimaka mashi. Zance hakan kamar shagwabane wanda ba hakana bane saukin daine kawai ke shiga a hankali lokacin don yanzu yakai yana dan lalabawa yaje da kansa. Saidai ina ganin hakan na mike zama ya fara yi ina gaidashi da mashi sannu da jiki ya amsa yana fadin koya makarane nace ba a tayar da sallah ba ai a lokacin. Yana kokarin mikewa tsaye ganin yanayinsa yasa na tuna da zancen likitoci da suke fadin idan mutum ya tashi da dare koda safe daga barci ba a son ya mike farat daya sai ya dan zauna jininsa ya sauka don gujewa faruwan sturk a gareshi balle wanan dake halin ciwo a yanzu. Daka zauna tukun na bashi amsa yake fadin wallahi naso tashi kuma na kasa kinga yanzu abin dake damuna shine duk ilahirin jikina sai na dinga jin yana min majirya wani lokacin. Wani lokaci kuma sam banjin hakan a tare dani amma hakan yafi faruwa gareni da safe haka ko da yamma idan na dade a inda nake fitowa insha iska. Kinsan yanzu sun daina tayar min da injin don kawai Asmau tayi magana ranan kan an jima ba a tayar da injin din ba wanan yan iskan yaran suka fadawa mama shine tace samun wajene ai ? Ko gidan ubanta ana tayar da injine haka balle ta kawowa mutane iskanci to injin din ma an daina tayar dashi idan akwai wutan nepa aga haske din. Idan babu kuma kowa ya zauna hakana kinga ni basu damu dani ba koda mutuwa zanyi ke nan Rahama kansu kawai suka sani sai naga yayi murmushi yana hada hannayesa a waje daya. Kafin ya dago kai yace amma kinsan me kuma duk sati sai ansaka kudin mai a cikin buget din da za a fitar nidai kawai kallonsu nakeyi fatana a yanzu shine. Idan ina da rabon tashi a ciwon nan Allah yaban lafiya mai amfani gareni da iyalina idan kuma hanyar tafiyanane hakan Allah ubangiji yasa na cika da imani Rahama. Tausayi sosai ya ban a zuciyana wanda nagane maza da yawa ashe in sun kwanta ciwo suna ganin takaicin duniya a kan iyalinsu ban ji tsoro ba saida naji yana fadin kinsan me kuma ? Nace a,a yace duk basu zata Allah zai ban lafiya da zan mike kamar haka bama a yanzu ba karamin illa sukaiwa dukiyana ba Rahama zancen dai kawai ayi shiru tun Habu yana hanawa yazo ya fada min har yakai yanzu shima ya soma nasa hada hada a ciki saidai nayi kamar ban fahinci hakan ba garesu. Yau dan uwakane yayi ma hakan da mahaifiyarka to don wani yayima me zakace mamafa wai har cewa tayi a ware wasu kudi don auren yaran nan kada nazo na mutu kudin su shiga cikin magadana ? Ki duba wanan zancen don Allah Rahama wai mahaifiyace takewa danta hakan me zan fada a yanzu suyi min hakam waye ba zai min ba nasan wanan shirin kawune sarai shike turata duk wanan abubuwan . Bansam lokacin da bakina ya furta to wai ku baku iya maganin kawu din nan ne mutum yana cutan ku kun sani amma kuna taushewa don Allah ? Bai ban amsa ba sai murmushin da yayi yana fadin kamani inje inyi alwala kada mu makara ga sallah lokaci naja hakan yasa na kamashi ya mike tsaye zuwa bandaki. Bamu fito ba saida yayi komai ya fito na gyara mashi inda zai zauna yayi sallah na koma na dauro alwala na fito nazo na don har an tayar da sallah a lokacin. Na idan na dan zauna nayi addua kafin na mike zuwa kitchen tea mai kauri na hado mashi nazo dashi dakin yana zaune a wajen har lokacin. Na mika mashi bayan na fifita ya karba ya shanye yana min godiya ruwan dana tofe da addua na mika mai ya dora a sama bayan yasha na shafe mai jiki dasu tsaba na kamashi zuwa gado ya kwanta. Na gyara mai kwanciya yadda zaiji dadin samun barci zan mike yake fadin ki kwanta mana ki huta nace ina zuwa kawai na fice daga dakin zuwa dakin biba na tayar da ita don tayi sallah. Duk aikin da nakeyi zancen mu dashine na dazun ya tsaya min a rai na na fahinci wanan abin sai an koyawa mutanen nan wayau a rayuwansu. Wani abin ko baka da niyar yi mutane suke sakaka yinsa don fansan kai matsala guda kishiyoyina haka take garesu duk inda aka juya mu can suke. Haka kuma ba zamu taba rabuwa da wanan matsalan bafa matukar talikin nan yana raye sai mun rabu da mutanen nan kamar yadda yaya habu ya tsame kansa cikinsu a yanzu. Dan zama da igiyar auren Jafar yasa na fahinci abubuwa da dama game da zaman gidan wanda a baya ban kai fahintar hakan ba a lokacin don abune dabai shafeni ba lokacin. Don haka ya zama dole na fito da halin fulatanci na mugunta da nuna wayau wawaye yanzu garesu don tsirar da mutuncin mu ga baki daya. Mama ko a gaban mu da yar uwata idan abinta ya tashi zatace ita makircin fulani ai duk ta sanshi ita da tayi zama da inna amarya ana gwada mata fulatanci ? A yanzu zata fahinci fulantanci ba komai bane sai zalla wayau da kissa da iya duniyanci akauyance muke shammatan mutum. Abinci lafiyayye na shirya mashi wanda nasan zai kara gina masa jiki ya samu lafiya don ramansa tayi yawa a yanzu ba son nakai zuciya nesa ba saima na zargi zama a kusa dashi din. Kamar yadda saudi ta ban shawara na zage in kula dashi idan yana wajena ta yadda ba zai iya boye komawansa wancan gida ba a fili ta hanyar bashi kula ta musanman. Don ita saudi irin mantan nan ne da suka kare rayuwan kurciya a bariki har lokaci ya kare masu basu sani ba sai a koma yan kame kame saboda girma. Wanan ya kaita ga aiki gidansu ummah ita din ance wata yar uwar su daddyne ta haifeta gashi tana bala,in jin tsoron daddy wanan yasa a yanzu ma don ta natsu ya zaunar da ita a gidansa yana kuma yi mata albashi. Alhamdullahi din ta natsu kamar yadda yan uwa suke mata fatan hakan wanan yasa bata da shamaki a gidan din nasu yazo daya da ummah sosai saboda bata takura mata ko kadan. Itace kuma a irin hiran mu ta kara min haske akan zama da irin su mama da iyalanta wanda wanan huduban hakan yai min tasiri sosai a cikin zuciyana a lokacin. Na lekashi a dakin na samu ya samu barcinsa sosai har baisan inda yake ba a raina nace har yunwa a cikin lamarinsa na fito falo na tsaya muka gyara da biba don gudun girshi a gareni azo a samu gida ba shiri wanan kesa macen kwarai ke gyara gida tunda safe kazama kuma malakaciya itace ke zama har wani lokaci gida ba gyara ko jikinta nakoma dakina nayi wanka. Bayan na fito na zauna na shafe jikina da mai sosai na zauna nayi kwaliya kafin na fito daga gidan har jikin mu duk ya dauki kamshi yadda nake so . Ina cikin irin mutanen dake son kamshi a rayuwansu don hakane ban wasa da kamshi a lamarina ko don tashi a wajen mummy Abujace na kasance a hakan oho ? ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/23, 14:10] Aisha Srtr Mt: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 8️⃣5️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, A gaskiya zamuce ba laifi don amarya ba zata gwadawa anty barakha komai ba na rayuwa saidaima anty barakha din ta gwada mata don ta fita komai na zamanin nan. Hakan yasa da farko anty barakha daga kai tana ganin cewa ba wani abinda amaryan zata gane aiga mijin nasu don haka ta shiga aika yan dabarrun data iya na kisa don kawai ta sace zuciyar miji a bangarenta. Saidai kash ta manta da haljn da namiji a lokacin dayayi aure idonsa gaba daya makancewa yakeyi wani lokacin ya koma akan amaryan ke uwargida duk gwanintaki ba a ganar maki hakan. Bature yana fadin don,t mind the body mind the engyne matukar gidan aikin na kalau ba a damu da kyau jiki ba. Don kuwa maigida illiya kan amaryansa datayo masa tsaraban kayan hadin matanmu na hausa na gargajiya sune suka haukatashi har yakai yana fitar da sabon rayuwa da ba a sanshi dasu ba a gidan. Mutumin da aka sani yana fita sallah asuba yanzu duk ranan girkin amarya babu mai ganinsa wajen jam,i sai rana ya fito kiri kiri zasu fito yin wanka da ita dashi a cikin bayi daya duk kuwa da yan matan da yake dasu sakwa sakwa baya kunyar hakan. Haka kuma zasu fito zuwa daki don shakiyanci wani lokacin amaryance ke goyashi a baya tana fadin shi babyntane wai a cikin shakiyanci suna wasa da dariya a tsakaninsu. Dare kuwa karfe takwas da rabi sun kargame kofan daki sai kuma safiya idan sun fito ga yaran makwabta kawayen yayansu dake shigowa gidan kallon tv. Amma bawan Allah nan ba kunya haka zasu shige daki su rufe da magariban fari ido na ganin ido ba tare da yaji nautin diyansa ba ko matarshi. Ire iren wanan halin yasa ko yaushe waya yana manne a kunnen anty din tana kai karan mijin a gurin mahaifiyarta ko kanninta. Gashi duk wani kissa da akace tayi tana kokarin yi amma ga banza randama ya dawo dakinta zai tsiri fushin banza da ita da yaranta dan abu kadan ya hausu da fada da cin mutunci. A ranan kuma sai dare bayan sha biyu zai shigo gida ya kwanta da safe kuma inya fita sallah asuba ba zai shigo gida ba sai wajajen tara da rabi na safe ko goma daya shigo ya karya zai fice idan ya fita kuma sai karfe hudun yamma zai dawo gidan. Allah sarki macen bahaushe don mata da yawa suna fuskanta wanan sauyin a wajen mazajensu yayin da akace miji ya kara masu abokiyar zama . Wanan yasa matan mu na hausawa a yanzu saboda halin maza basu kaunar ace miji zaiyi aure sai su dauka abinda ya samu waccan shine zai samesu suma ? Tun tana magana har yanzu ta jinginashi ga Allah ita da yaranta ga wani sabin doka dayasawa yaranshi zuwa kasan layinsu don su dibowa amaryansu ruwan bohol wai bata shan ruwan rijiya tace. Haka zasu fita da safe suje bun layin ruwan bohol din da take so din shiko suna daki kargame da ita sai lokacin da sukaga dama su bude su fito. Zuwanta duban jikin jafar data dan jima acan zaria din ta danyi dabarun ta irin na mata ta dawo dashi amma halin bai canza ba saima wasu sabbin sallon data dawo ta sama a gidan lokacin. Wanan yasa ta rame ta lalace ta fita hayacinta don yanzu ta gaji da kiran gida tana fada masu halinda take ciki saida a yanzu ta daina wahalan kashe kudin da takeyi na gyara girkinta a ranan da yake wajenta haka iya abinda ya bayar kawai take girkawa kowa yaci. Wanan kuma ya kara haddasa fitina a tsakaninta da maugidan ya sako wani bakin kiyayya da yake mata a gaban kowa saidai abokiyar wayarta saratu tace ta daure ta fita batun dan iska kada ta bashi komai nata har yaran ta barsu ai diyanshine. Yanzu kan fitina sosai sukeyi da mijin akan hakan har yakai ana bugaiya tsakaninshi da anty barakha din zai dirke ta a gaban kowa a taru a gidan suna tonon asiri. Tun mama na boyon wanan abin har yakai ga ta fara sakin magana tana jawa surikin nata Allah ya isa a baina. Na samu ya falka dana shigo yana kwance ya zuba min ido har na karaso gaban gadon Allah kadai yasan tunanen da yakeyi a lokacin. Gaidashi na sakeyi da kwana ina fadin da zaka lalaba ka tashi kai wanka sai kaci abinci zaifi ya dubeni yana murmushi kawai yace bayan karyawan da nayi dazun din ? Awa uku da dan kaifa yanzu naso ka yi wanka sai kasha wancan maganin dakazp dashi jiya haka dai na samu yaje yayi wanka ya fito na dauko mai sabon jallabiyansa dake wardrobe wanda bai taba amfani dashi ba ciwo ya kasheshi don a baya yana sayo kayan shan iska ya aje a gida. Wani baki mai addon zaiba maikyaun desine na dauko mashi ya saka muka fito falo na gabatar mashi da abinci . Yadda yake nuna farin cikinshi a fuska yasa nasan yana cikin nishadi a lokacin har ya gama ina gefe ina taimaka mashi a wajen ci bayan mun idarne na mike na kwashe kayan zuwa kitchen nasa biba ta wanke. Falon na dawo na kamashi muka koma saman dogon kujera mai cin mutum ukku muka zauna wayansa ya shiga kara ya dauka hakan ya ban daman mikewa daga wajen na shiga shawagi a cikin falon zuwa kitchen din mu. Duk wayan da yakeyi idonsa yana kaina har ya gama lokacin ina tsaye a kitchen din Biba tana min hiran wasu makwabtansu da sukai fada ina dariya. Jin shirunsa yasa na fito falon na sameshi na zauna a kusa dashi ina fadin naji kana fada yace bari Rahama bansan me mutane suka dauki hakki ba a yanzu Rahama ? Mutane basu tsoron Allah ko kadan kowa dai kokari yake ya gina kansa koda haramun ne a duniyan nan yanzu wai suna fada min kayan dana tura kafin ciwin nan ya kaini kwamce an sace rabi. Ba dole a sace ba kayan da in nakai abina bai wuce inyi wata biyu zuwa ukku sun samu shiga ba amma tunda vani wajen kowa yayi abinda yaga dama dasu. Shi Habu na rasa irin zuciyarsa ya hau ya zauna yana fushi wai don mama da Nusaiba sun jefa masa zargi a dukiyana yau idan habu ko yazid basu tsaya min ba Rahama wa zai tsaya min a garin nan ? Na dauka koda ace ban raye su masu tsayawand suga sun kare min hakkin iyslina da nasu gaba daya amma sai abubuwa akeyi barkatai wanda hanlali bai tunanensa. Na kansa a raina wanan ciwon wani jerabawan rayuwace Allah ya aiko min dashi da zan fahinci yadda lamarin duniya ya koma a yanzu. Don mutane ko da ranka ashe sai kana da amfani ake rayuwan komai dakai sai kana cikakken mutum duniya har dan uwanka zasu dama dakai Rahama ? Sosai nagodewa Allah da dabaran da Allah ya ban nayiwa kaina haka kema haduwata dake Allah kadai na barwa sanin dalilin hakan a tsakanin mu dake. Don ta dalilin aurenki Rahama har Allah ya ban dabaran boye kudina a gidan nan ba tare da nakai banki ba har ke dake zsune gidan ma bakin san da hakan ba don da suna account dina yau Rahama da kudin nan dana aje anan suma an batar dasu kamar yadda wa yan nan suka salwanta min mun koma banda komai. A lokacin kallon mamaki nake mashi yayi murmushi ya gyara zama yana fadin wallahi haka kawai nasa aka kawo min kudin nan nan gida kamar wani abu da niyar idan na dawo daga tafiyan da nayi basai na tsaya shiga bank ba wajen miliyan ,,,,,, Sallaman Yazid daya shigo lokacin ya katseshi duk muka bishi da kallo lokaci guda don yaja ya tsaya daga kofan shigowa falon yana tafa hannayensa. Kafin ya soma fadin wai don Allah yayane nan nake gani haka ko dai wani yaya J din kika sauya munane yau din ? Tsuki Jafar yaja yana kawar da kai ya karaso yana fadin to ina mamanka dake can tana fada a kanka ko ita taga wanan sauyi yau haka sai tayi mamaki zata daina fadan da takeyi dakai tun jiya. Na fada mata dama kai keda jikinka da iyalinka ta barka kayi abinda ranka yake so amma tace ba haka ba tunda bakaji sauki ba don me zaka dawo nan ka tare kuma ? Bayan kasan har yanzu magani kake sha ni itace ma da fitinan ta ta tayar dani tunda safe yau wai na kawo maka maganin nan kasha ya miko mai wani leda dake hannusa fari. Yace ba Rahama ita mama fadan me takeyi a kaina ko na zama yarone yau kuma da za ace sai yadda akayi danine wai magani ko a nan nake ba zan sha maganin bane ? Na rasa meyasa take haka wai akaina wallahi to dai kan ka shirya don wallahi fada ta kwanayi ba don iya ba jiya data biyoka da daren nan iyace ta hanata zuwa sai abin ya ba jafar din dariya haka yasa ya dan sake murmushi a fuskanshi kadan. Don sheri sai ya juyo gareni yana fasin wai don Allah amarya nima ba zaki samo min wata yar filo ba kuwa in kara don dai wanan abin akwai ban mamaki gaskiya ? Ki duba mutumin ki don Allah yau shine a haka yayi clean wallahi yayi kyau kamar bashi ba jiya jiya nan da daren nan fa yazo gidan nan amma dubashi don Allah ? Idan ka gama ka kira min emanual zanyi magana dashi a gabanka yace abinne Allah da ban mamaki kwarai da gaske ya J baka yadda kayi wani fresh ba ? Kaji mena fada ai yake fadawa kanin nasa shima yazid din ya dubi wayanshi yana fadin shi nake kokarin kira ai yanzu hakan . Mutumin ya dauka suka fara gaisawa da yazid yake fada mai mr Jafar yake son magana dashi yana fadan haka ya mikowa yayan nasa wayan ya soma magana na mike ina fadin ya yazid a kawo breakfast ne ? Wallahi madam dina ta cika min ciki kafin in fito amma zan dan taba kadan saboda kwadayi ya fada yana dariya nidai na shige na kwaso mai kayan abincin da dan uwan nasa ya karya dasu din na aje mashi a gabanshi. Duk da ina aiki ban tsaya ba lokacin amma ina cankar maganan da Jafar din keyi da mutumin akan kudine yake tambayanshi ba,asin su. Zance na dashi tun dawowana jiya nake nazari a raina wanda na gama kai karshen tunanena wanda abinda zuciyana ya ban shine dukiyan sun samu matsala saboda dalilin kwanciya rashin lafiyan nan nasa. Indai za a rasa dukiya Allah ya bar muna shi Alhamdullahi rayuwa ya nema dama sai anema din daga baya in Allah ya nufa da sauran rabon hakan. Kirana da yaya din keyi yasa na fito daga daki tare da amsawa cikin dan muryana din nazo gareshi yake fadin don Allah dauko min wani file na nan a dakina a drower kasa ki kawo min . Na nufi dakin na duba nagashi na kawo mai ya karba yana budewa na juya da niyar barin wajen naji sallama ko ban juyo ba nasan muryan yaya habune a lokacin ya shigo gidan shima. Hakan yasa na dakata don mu gaisa na gaidashi daga inda nake ya amsa min kan kadaram kadaham nima na juya zuwa daki ba tare dana tambayeshi iyalinsa ba. Ina shiga dakin naji ya sun soma magana tun baniin me suke fada har na gane musayan magana sukewa junan su karshe dai na barjin muryan yan uwan saina jafar din dake magana a cikin fada da bacin rai yana nuna sakacin da sukayi aiba shi kadai hakan ya shafa ba dukkansune. Ni dai naji yana fadi a karshe cewa yasan matakin da zai dauka idan ma na waje sun cuceshi har dasu baiyi tsamanin hakan ba ai. Nan na soma jin muryan ya habu yana fasin J ya kake son nayi kana sin kaga laifinane a banza cikin zancen nan. Kafi kowa sanin bakin jinin da nayi a zancen nan gida ba a barni ba J kasani balle waje mutane yanzu basuwa Allah . Ni dai tun ina saurarensu har barci ya daukeni bansan fitansu daga gidan ba barci na samu sosai nayi a lokacin yana zaune falo bai tayar dani ba don yasan harda laluran cikin dake jikina a cikin barcin. Ban falka ba sai wajajen karfe daya na falka nayi mamaki yadda na samu barci mai dadi haka a lokacin na fito falon na sameshi a inda na barshi yana duban takardun dana dauko masa dazun din. Gaidashi nayi hakan yasa ya dago yana fadin kin tashi na amsa da eeh ina zama nake fadin sun tafi ashe yace tun dazun suka tafi me zasu fada min tunda suyi shirme . Zaune nakai a hankali ina fadin na zata ai azahar tayi yace da sauran time kin fara zuwa awo ne ya jefo min tambaya ? Hakan yasa nima nake mai kallon mamaki yaushe zan fara zuwa awo bai sani ba duk da dai bangarin ai a lokacin don haka nayi shiru ban bashi amsa ba. Saida aka dan dauki dan lokaci ya dago yana fadin bakiji mena fada ba na dan rausaya ina kawar da fuska nace ni banjin komai ai yanzu. Ko baki jin komai baki zuwa asibiti a duba lafiyan ki dana baby din a gani dole ki fara zuwa awo zanwa yaya Ai magana tazo kuje tare ko kuma maman tudu . Ni banje na gaidasu ba sai a kirasu suzo kaini asibiti kamar banda lafiya nidai ka barsu karka kira kowa don Allah na fada a karshe. To me kike nufi ba zaki ba ke nan ko dole kije asibiti don lafiyan ku idan can gida zaki biya ki dauku mama din fine amma asatin nan ki je a dubaki please. Shiru nayi na kasa cewa kkmai saidai nasan tunda ya fada sai anyi haka din don idan ban manta ba sun taba fadan zuwa awo da Asmau a gabana kafin na aureshi da shigan cikin dan nan nata data yaye din wanda aka haifa bayan an aureni . Yana tafe a gajiye ya fito filin kwalo rigansa na kwalo yana rataye a kafadansa saidai yana sharo kwanan gidansu ya hango dandazon yaran unguwa a kofan gidansu. Sauri ya kara ya iso kofan gidan fada ya fara da yaran yana korasu duk daya fahinci fadan da akeyi a cikin gidan nasu da yanzu ya zama kamar gidan haya suka zo kallo. Gidan ya shiga kanninsa mata ya fara hangowa a rakube cikin damuwa wucewa yayi zuwa bakin randan ruwan mahaifiyarsu yana diban ruwa a cikin takaici a fili kuma halin ko in kula yaron ya nuna ga abindake faruwa gidan tsakanin iyayyen nasa . A yadda ya fahinta da kishiyar maman tasu da mahaifinsune suka tararwa uwar nasu ake wanan masifan da zage zage a yanzu inda sabo ya saba da ganin hakan dashi da yan uwansa din don zaman lafiya ya kaurace a gidan nasu tun shigowan wanan matar gidansu. Karan dukan da yaji mahaifinsu nakaiwa mahaifiyarsu tana kakarin neman taimako ga yan uwansa na ihun ceto yasa ya yarda mudan ruwan kasa ya nufi wajensu da sauri yana fadin . Baba a,a baba ya haka kuma ka barsu suyi fadansu mana tunda bada kai akeyi ba zaka kamata da duka kuma haka a gaban mu. Uban ya nuna baima san yanayi ba shima haka baisan lokacin daya kai hannu yana banbare hannun mahaifin nasu ba a jikin mahaifiyarsu. Aminu zaka shigarwa uwarkane kome amayar baban nasu ta fada bai kulata ba sai kokarin kwatar mahaifiyar da yakeyi rai bace ganin mahaifin nasu kasheta yake son yi yasa ya nuna mashi karfi ya kwaci uwar yana dagota daga kasa inda uban ya shake ta. Baiyi aune ba yaji an kwala mashi abu a kai hakan baisa ya sake mahaifiyar ba sai juyawa da yayi ya rike tabaryan dake hannun amaryan mahaifin nasu da hannunsa daya yana fadin kika dukeni ? Dan iska zaka ramane kai ga mai karfi kazo ka tureni ka ceci uwarka ko ta kasheka ta kashe banza da iska mai halin uwarsa kawai. Bai kulasu ba yaja uwarsa dake rusa kukan takaici zuwa dakinta rai bace yana fitowa don bai tsaya a dakin ba suka hade da uban nasa ya soma fadin. Kai san iska yau din nan saika barmin gidana ni zaka nunawa ka kawo karfi a yanzy har zaka tureni don kana dan iska ka zabi uwarka dani ko ? To ka fito dakai da uwar naka kubar min gidana bai kula uban ba ya nufi wajen ruwan da yake diba din ransa a bace nan ma uban bai kyaleshi ba yabishi yana fadin . Nafika iskanci dan banza kawai kai har kana ganin kai wata tsiyace ko a yanzu ni zaka daga kan uwarka dan banza kawai. Shi dai yaron bai kula uban ba ganin hakan ran iliyan ya baci ya nufi inda suke aje icce ya rarumo ya nufoshi nan yan uwansa mata suka hau ihu suna fadin ya gudu ga baba nan da icce tafe hankali tashe . Bai gudu din ba ya nufi bayi ai kuwa yakai mai duka da iccen zafin hakan yasa dan dakatawa yana kallon uban dake fadin. Nace ka fice min daga gida mara mutunci wallahi baka zama gidan nan damu dan iska daga kai har uwarku ku barmin gidana gayan tsiya kawai. Uwar ta leko ta hau bakin ta har yaron ya shiga bayi sai kuma ya fito ya nufi hanyar waje ya fice daga gidan cikin bacin rai. Hausawa sunce kowa yace ruwan wani bai tafasa nasa ko dumi baiyi ai. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/24, 10:32] Aisha Srtr Mt: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 8️⃣6️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Nasa a raina ranan zai koma wancan gidan donshi ma banyi motsin girkin dare ba don nasan a ka,ida dai kwana bibiyu mukeyi ga girki tun muna mu ukku. Balle yanzu da mu biyune tare dashi muna falo zaune tun bayan fitansu yaya Ai da sukazo min sannu da dawowa a cewarsu. Muna zaune maigadi yayi sallama ya tsaya daga kofa yana gaidamu bayan ya amsa yake fadin akwai wani yaro a waje tace daga zamfara yake a fadama sunansa Aminu ? Kallon sa nayi naga ya daure fuska yana fadin to me yazo yi nan da baije can gida ba wajen su mama zaizo nan kallonsa nayi nace ko dan yaya Barakhane ? Yace shine mana don me zai biyuni nan kuma yaushema yazo garin na dubi maigadi dake tsaye nace dashi ce ya shigo malam don malam nake kiran maigadin dashi. Ya juya da sauri ya fice fada yaya keyi yana fadin don me zaizo nan barshi yazo najima meya kawoshi ni ban daukan wanan iskancin a yanzu gaskiya. Haba dai ba girmaka bane yaya yaron nan ai ya gansu ya nufo nan inda kake don Allah dai kayi hakkuri kaji abinda yazo yi din. Yaron ya shigo tun a kofa ya zube yana fadin kawu ina wuni ya amsa mashi fuska daure yaron cikin in,inniya yasoma fadin dama naje can gidane na samu baka nan su mama ma sun fita akace sai mama salima ita kuma tana barci. To sai akace me ita Asmau bata nan ne ya tambayeshi naga yayi kasa da kai ganin na mike tsaye yasashi fadin mummy ina wuni na amsa da Aminu anzo lafiya yaya su anty ? Suna lafiya kalau ya fada kafin mu gama gaisawa ya sake jefo mashi tambaya da mekazo yi zaria ko baka fara school din bane har yanzu. Nayi jam kawu basu fara dauka bane ya fada na katsesu da fadin kaci abinci kuwa Aminu yace yanzu na iso mummy naje can ban samesu ba nazo nan. To shigo mana kaja ka tsaya can a kofa kamar wani bako bari na kawo ma abinci kaci ka huta sai ku tatauna ko na nufi kitchen din mu abinci na hado mashi mai lafiya yaji ganye a sama da kayan hadi. Inda yake zaunse nakai mashi ya karba yana godiya na juya na kawo mai ruwan sha ya soma jan plate din zuwa gabanshi na juya zuwa cikin dakina . Na dan jima a dakin na fito na samu yaya na fadin to yanzu yaya kake son ayi ke nan shi ubanka ya koreka gidansa shine ka nufomu nan ? Bayan haka kai baka da hankaline ko kasheta yayi ina ruwanka da saka masu hannu a cikon fadan da sukeyi dashi ? Mahaifinkane fa Aminu baka da hankaline koka fara shaye shayene yaya yi hakkuri don Allah kasan uwa ba yadda za ayi yana tsaye yana kallon zai kashe masu mahaifiya ya kyalesu ? Nice na tsoma masu baki a zancensu bayan na gama sauraren maganganunsu da dansa din abindana fada yasa ya dan kalloni yana fadin. Haba Rahama baida hankaline da zai ture ubansa ubansane fa don kawai yaga suna rigima zai saka baki a cikin zancensu hakan ya nemi albarkansa ke nan ? Zaune nakai cikin sanyin jiki ina fadin yaya ceton mahaifiyarsa kuma yana iya saka yayi komai a lokacin rabu da irin gidan nan da ake irin haka a gabab yaya abin yakan saka yayan shiga cikin zancen wani lokaci. Don babu mahalunkin da zai zauna ana dukan uwarshi bai dauki mataki akai ba kai ya girgiza yana fadin Rahama na gane da sauraki kema kina da kuruciya a tare dake . Har yayi shiru ya dago yana fadin meyasa su yan uwansa mata basu sa hannu a rikicin ba sai shi zaisa hannu don gashi mai karfi ko zai iya fada da ubansa. Ba hakana bane yaya yayi kuskure don Allah da gani a jigijce yake a barshi yaje ya huta bari nasa maigadi ya bude mashi dakin baya guda ya zauna kafin asan abinyi. Da sauri naji yaya din yace No don me zai zauna muna nan baga can gidan ba ya zauna mana da iya nace don Allah yaya tunda yazo nan din ka barshi ? Kayi hakkiri ya zauna nan din bai min magana ba na dade a zaune wajen ina sauraren amsan shi baice komai ba har lokacin. Haka yasa na mike ina fadin inka gama taso muje kaga inda zaka sauka din na fice ba tare da nace komai ba. Shima kuma baice komai ba sai wayanshi da yake duba ya fita batun mu daga bayan mu akwai dakuna hudu kamar boys quaters a gidan da suke rufe sai maigadi dake dan amfani da guda don adana abubuwansa. Tambayasa nayi ina kayanka ko suna can gidan ka bari yace haka nazo mummy don bai bari na shiga gidan ba balle in dauki wani abu . Ok shiga kayi wanka ka huta zuwa anjima kazo ka fita nan titi ka samu kananan kaya ka saya na juya na bar wajen ina jin yana fadin nagode mummy nagode. Na koma ciki na samu yaya a zaune zama nayi ina fadin an bude mashi dakin tsakiya zai zauna a cikinsa shiru yayi ba amsa hakan yasa naja bakina nayi shiru a cikin tsarguwa da hakan da yayi min din. Kamar daga sama naji muryanshi yana fadin ke har yanzu baki fahinci mutanen nan ba naga kina kokarin jawo muna yaron nan a gidan nan banson wani abinda zai kawo muna fitina ko tsegumi ki barshi can ai kakansa tana nan yaje can wurinta ya zauna mana don me zai nufo nan gidan haka kai tsaye. Shiru nayi ina nazarin zancensa a kaina tabbas gaskiya ya fada don ba mutanen arziki bane alheri sai ya zama tsiya a wajensu. Zama na gyara ina fadin ni naga ba zaizo nan mu koreshi ba ai yaya tunda yazo din sai ayi hakkuri don kai ba za aga laifinka ba sai nawa tunda yariga da yazo kayi hakkurin hakan don Allah. Bai kira yace dasu yaron na gidansa ba hakan yasa hankalinsu ya tashi lokacin da uwar ta bugo waya tana tambayan ko yaron yazo nan ? Duk hankalinsu ya tashi haka ba wanda yai dabaran kiransa ni dai ganin har magariba banga yana shirin komawa gidan can ba sai mamakin hakan da zaiyi nakeyi a zuciyana. A bangaren yaya barakha an nemi Aminu a nan gusau ba a sameshi ba har washegari hakan ya daga mata hankali ta bugo waya nan zaria tana tambaya ? Mama Dubu hankalinta ya tashi har dare suna buga waya gusau din suna tambaya ko an ganshi sai ace har yanzu dai ana nemansa ba,a sameshi ba. Ga jafar da suke sa ran shigowan gidan har goma na dare ba labarin shi hakan yasa mama sa a duba mata ko yazid ya dawo aka dubo yana gida. Da kanta taje part din yazid din ta sameshi tana tambayan malam fa don sunan malam Jafar marigayi da sukai jahadin da,awa a cikin kasa yasa duk wani Jafar yawanci ake saya sunan nasa a cikin girmamawa ga malam Jafar din dake tashe alokacin. Yagane dan uwansa take tambaya donshi ake kira da wanan sunan na malam din take fadin malam fa yace yana lafiya ta amsa da aina sani tunda naji shiru ? Tambayanka nayi har yanzu bai shigo ba kai gaka ka dawo gida ko da kansa zai dawo yau ya kamata ace yana nan ga zancen yaron nan da har yanzu ba a gansa ba ko za ayi wani abu a nan ? Mama J aiba zai dawo gidan nan ba yau ban ma tsamanin nan kusa gaskiya kin ga a yan kwanakin nan yadda ya koma kuwa ? Dakata don Allah nasan duk bakin ku daya shi zai fara yace bai dawowa gidan nan a yau da kuwa na sameshi a can naci masa mutunci. Acan kikace mama kwarai ko kana tsamani ba zan iya bane kagani ya dan dubeta ya kawar da kai ya soma tafiya yace zaki iya masa hakan nasani to kira min shi yanzun nan . Ko kaje kazo min dashi yanzu gidan nan yanzu fa mama gomafa ta shude da nan da can ai dayane nagani meye ruwanki da zamanshi can din ke ? Yazid kai abin da nace kada ranka ya baci dani a wajen nan Ok yayi bari na kirashi naji in zai dawo sai naje na daukoshi din. Ya kira wayansa bai shiga ba haka yasa ya fada mata gaskiya itama kuma taji matar computer tana sanar da hakan a wayan . To kinji wayansa a kashe yake yanzu yaya ke nan kaini gidan idan ku ta shanye ku aini bata shanyeni ba har ita karamar yarinyar ta isa ita da masu taimaka mata din kar nake kallonsu. Bai haifawa jikokin fulani diya ba balle suzo su mallake min yaya da raina da lafiyana ina kallo shi kuma J far din zaizo ya sameni ai zai jini. To bari in shirya in fito ya fada ya koma ciki itama ta juya zuwa dauko hijabinta don tafiya ya shige ciki yana dariya. Har ta fito yazid din bai fito ba nan kofa ya tsaya yana kallonta yana gyara rigansa hakan yasata daga murya tana kirasa a hasale tana fadin zata saba mashi fa idan bai fito sun tafi ba. Iya dake cikin tana jin sautin muryan mama ta fito tana fadin lafiya anga yaron ko don tana cikin damuwan rashin ganin yaron a lokacin. Karan budan kofan da iyan tayi yasa salima dake kwance tana charting ta biyota tana fadin iya lafiya ? Iya sai fadi take anganshi ko cikin rawan jiki a lokacin Yazid ya karaso yana fadin mama shiryawa fa nakeyi don nayi shirin kwanciyane kika zo . Nace kunga yaron ne iya ta sake fada karo na uku ba a ganshi ba iya gidan Jafar zamu mama ta dauko shi ya dawo nan. Jafar kuma ta daukoshi kamar yaya iyan ta tambaya to ni dai tace in kaita ta daukoshi can din wai nan ya kamata ya kwana a yau ? Dubu iya ta fada cikin mamaki tana kallon yar nata da wani irin kallon dake baiyana mamakinta karara ga yar nata dake wanan magana. A,a iya rashin hankali yake son ya tafkawa mutane waishi ga salamame zaije gun yarinyar nan Rahama ya tare don rashin hankali ya daukarwa kansa zunubi. Zunubi a wajenwa Dubu wajen ki ko wajen wa zai dauki zunubin da kike fadi dubu ? Dubu dubu kanki daya kuwa da yaron nan yayi wata da watanni a gidan nan meyasa bakice a kwashshi a kaishi can ba lolacin kada ya kwashi zunubi sai yanzu ? Iya wanan ai lalurane itama din ai tana tare dashi a nan kuma, zaman nan din aida ita akayishi da yanzu zatace a maimaita mata hakan da akayi ? Ta fada maki cewa sai an mata maimaicin hakan a gidanta wai dubu meke damunkine haka wai ? Kai Yazidu koma dakinka ka kwanta don ba inda zaku a cikim daren nan da wanan rashin hankali na uwarku don kina mara hankali zaki gidan surukarki da wanan zance na hauka idan kinje kice masu me yanzu ? A,a iya ki bari nayi maganinsa tunda yana ganin ya isa ne yanzu har zai kwashi kafa ya koma can ya tare bai fadawa kowa ba ? Kamar yaya Dubu don ni ban fahinci wanan rashin hankalin naki ba har yanzu waiko dubu akwai hankali akanki kuwa ? A fahintana Dubu kamar kishi kike da yaran nan fa don abin nan da kikeyi bana kai sake bane dubu ban taba gani ko jin irin wanan rashin hankali naki ba gaskiya. Iya yanzu sai a kyaleshi yaeinya karama tana juyashi ana kallo ba a dauki mataki ba jinyar da tazo nan tayi nasa ai yan uwanta dashi ta cuta ga hakan ? A,a ba juyashi tayi Dubu mulkeshi tayi iyakar juyawa dai ko aiki ya sameki babba idan kikace kishi zakiyi da matan yayan ki ? Duniya da mutanen cikinta suna shirin maki dariya jeki dan mutuncin dake gareki a idanun yarinyar nan ya zube aikin banza aikin wofo kawai da rashi kamun kai ? Kai yazidu koma wajenka ka kwanta ba inda zaku ni naga rashin hankali yau a filin Allah ashe ke ba zancen yaron nan daya batane ya dameki ba shirmenki kike a zuciyarki ? Yau ni naga hauka na rubutawa a jarida Dubu baki tsoron bakin duniya ko wanan halin da kikewa yayan mutane ya tambayeki nan gaba ? A,a iya don Allah abar zancen nan baikai har kiyiwa yaran nan baki ba a gareni yaje ya zauna tunda ya zama sallamame a wajenta. Karamar yarinya kamar wanan yau zata juyawa Jafaru hankali yana wanan abin a gaban kowa iya dole inyi magana abin yayi yawa dama an fadi matan fulani haka suke idan sun shigo waje. Kai Yazidu dawo ka kaita ta dauki matakin da zata dauka iya ta katse mama din dake magana ta juya tabar wajen yazid kuma bai ko juyo ba ya shige part dinshi. Washegari da safe kodana tashi kamar kullum na hada mai abinda zai rike mai ciki kafin mu gama breakfast ya dan kwanta. Hakan da nake mashi ba karamin kara mai lafiya yake masa ba ga sunan Allah da zaibi jikinsa da ruwan zamzam ga kuma kuzarin da jikinsa zai dauka yana daga cikin abinda Yazid ya hango na annuri a garesa yake fadin yaga ya canza mashi lokaci guda. A gurguje nake aikina ba don wani abu don kawai nasawa raina cewa suna iya zo min gida a ranan don Aminu dake nan wajen mu. Mun gama na jera mai a kasa don na fahinci a yanzu yafi son ci a kasan don kamar baijin dadin zama saman kujera yaci abu a yanzu da baida lafiya din nan. Na gama na shirya kaina na umurci biba data jetayi wanka har tace ta dauki abincin Aminu takai mai ne da sauri na juyo nace a,a ki barshi nan kitchen har ya shigo. Ba son komai nace haka ba saboda ban manta wani case din daya faru akan wata uwa dake tura yarta kaiwa saurayin gidan abinci ba. Amma haka mutumin yayi amfani da wanan daman ya batawa wanan matar yarta akaita case din karshe dai an cuci yar da uwar don har yakai ga dirkawa yarinyar ciki dole aka haifi dan hakana kuma yarinyar karamace sosai a lokacin. Wanan ya tsaya min a rai yasa nake kafa kafa da yar mutane ban yarda ko maigadi tayi wani dogon mu,amula dashi iyaka gaisuwa a tsakaninsu. Gareku mata wanan abin ya faru da gaske wallahi mutum koke kika haifeshi yanzu ya zama dole a gareki ki saka ido ga mu,amulansa na yau da kullum Allah ya tsare ya kare amin. Wasu dogon riga na saka a jikina _onion_ colour da adon zaiba har kasa anyi rigan mai dagware a sama kamar alkyaba yana daga cikin dinkin da anty salma tayi min na aure a Abuja. Zaune na samu yaya a dakin na shigo ina fadin ka tashi ashe yake fadin yazid ya tayar dani da waya wai yaron nan sun dauka ya batane ashe basu san yana nan ba ? Aminu na fada cikin mamaki yace shifa kiji ba yace muna ya tafi can ba ashe karya yakeyi ke nan nan yayo direct wajen mu. Ikon Allah amma cewa yayi ai yaje ya samu baka nan ace kana nan yace karya yakeyi yanzun ka fada masu yana nan dai ko ?/ Na fada masu ya fada a sanyayye nasan zasu shigo yanzu ai tunda sunji yana nan amma Aminu bai kyauta ba daya dagawa mutane hankali haka ? Bar dan iska kilama abinda ya fada karyane barshi kawai bari suzo din muji ai nasan za a fada masu abinda yayi ya gudu nan yau din nan zai bar min gidana. A,a yaya na fada da sauri ya katseni cikin tsawa da fadin ke karki tsoma min baki cikin maganan su ki barni kawai dasu. Nayi shiru kafin nace wanka zakayi ke nan yace haka naso na mike zuwa bandaki na hada mai ruwan wanka ya mike ya shiga saida ya gama na cude mai jiki da ruwan addua ya saka kaya muka fito falo. Mun zauna ke nan na zuba mashi ya fara ci biba tana gefe daya tana cin nata don sosai muke sakewa da yarinyar harshi sukan dan taba hira wani lokaci da ita. Muka ji sallaman Salima shigowa gidan ashema dukkansune tafe sai Asmau ce sai matar Yazid suka bari a gida lokacin. Ban daina mika mashi fruit din dana gyara ya zama juice ba da nakeyi na amsa sallaman nata ba tare dana juyo ba suka karasa shigowa gidan gaba dayansu. Nagama na dago ina fadin sannuku da zuwa ina kwanan ku a cikin jam,i bansan waya amsa ba ko wanda bai amsa ba a lokacin don na basu bayane ina zaune amma naji muryan yazid. A,a a a mutumina inafa zaka koma gida wanan riritakan da yar nan keyi shine ka gudu ka barni ba azo cin dadin amarcin dani ba ? Iya ba gaki kinzo ba yanzu saiki zauna muci dadin yanzu kada in kwareki kaidai tunda ina da rabo a cikin na yanzu sai in zauna inci amma zan barwa amaryaka aronka kwana biyu ai don tasan ina da kara amma fa a tuna damu muma kada a shagala suka kwashe da dariya. Ai fakaice baiyi iya gara ki fito mashi fili tasan yabar wasu a gida ba nan bane kawai gida a gareshi don shi naga hanyar konewa ya zaba yanzu. Bani ganin hakan cikin zuria,ata insha Allahu daidai lokacin namike a kusa dashi zuwa gaban mama na durkusa har kasa ina gaida ita. Kamar dole ta amsa min ba kin dawo lafiya na juya wajen kawu na gaidashi sai iya dake fada na rike hannunta sai lokacin ta dakatar da zancenta take fadin. Ke dai yar nan kin dawo lafiya yaya kika bar yan gidanku duk suna lafiya dai ko naso nazo banda wanda zai kawoni in maki sannu da zuwa. Iya ba komai na fada ina mikewa tsaye na nufi hanyar dakina muryan ya J naji yana fadin ina kuma zaki ? Daki zan tafi har ku gama na bashi amsa sai yace abincin fa wazai ban kizo ki zauna muci kema baki karya ba ai bari dai ku gama na fada. Kizo ki zauna nace me zamu fada wanda ba za aso kiji ba iya na fadin zo ki zauna abinki ai ba komai zamuyi ba ballema ina zata iya ? Yadda yake magana hakan yasa na dawo na zauna a inda na tashi duk suka zuba muna ido gashi sai magana yake min a cikin rashin damuwa da suna wajen a lokacin. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/24, 21:15] Aisha Srtr Mt: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 8️⃣6️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Nasa a raina ranan zai koma wancan gidan donshi ma banyi motsin girkin dare ba don nasan a ka,ida dai kwana bibiyu mukeyi ga girki tun muna mu ukku. Balle yanzu da mu biyune tare dashi muna falo zaune tun bayan fitansu yaya Ai da sukazo min sannu da dawowa a cewarsu. Muna zaune maigadi yayi sallama ya tsaya daga kofa yana gaidamu bayan ya amsa yake fadin akwai wani yaro a waje tace daga zamfara yake a fadama sunansa Aminu ? Kallon sa nayi naga ya daure fuska yana fadin to me yazo yi nan da baije can gida ba wajen su mama zaizo nan kallonsa nayi nace ko dan yaya Barakhane ? Yace shine mana don me zai biyuni nan kuma yaushema yazo garin na dubi maigadi dake tsaye nace dashi ce ya shigo malam don malam nake kiran maigadin dashi. Ya juya da sauri ya fice fada yaya keyi yana fadin don me zaizo nan barshi yazo najima meya kawoshi ni ban daukan wanan iskancin a yanzu gaskiya. Haba dai ba girmaka bane yaya yaron nan ai ya gansu ya nufo nan inda kake don Allah dai kayi hakkuri kaji abinda yazo yi din. Yaron ya shigo tun a kofa ya zube yana fadin kawu ina wuni ya amsa mashi fuska daure yaron cikin in,inniya yasoma fadin dama naje can gidane na samu baka nan su mama ma sun fita akace sai mama salima ita kuma tana barci. To sai akace me ita Asmau bata nan ne ya tambayeshi naga yayi kasa da kai ganin na mike tsaye yasashi fadin mummy ina wuni na amsa da Aminu anzo lafiya yaya su anty ? Suna lafiya kalau ya fada kafin mu gama gaisawa ya sake jefo mashi tambaya da mekazo yi zaria ko baka fara school din bane har yanzu. Nayi jam kawu basu fara dauka bane ya fada na katsesu da fadin kaci abinci kuwa Aminu yace yanzu na iso mummy naje can ban samesu ba nazo nan. To shigo mana kaja ka tsaya can a kofa kamar wani bako bari na kawo ma abinci kaci ka huta sai ku tatauna ko na nufi kitchen din mu abinci na hado mashi mai lafiya yaji ganye a sama da kayan hadi. Inda yake zaunse nakai mashi ya karba yana godiya na juya na kawo mai ruwan sha ya soma jan plate din zuwa gabanshi na juya zuwa cikin dakina . Na dan jima a dakin na fito na samu yaya na fadin to yanzu yaya kake son ayi ke nan shi ubanka ya koreka gidansa shine ka nufomu nan ? Bayan haka kai baka da hankaline ko kasheta yayi ina ruwanka da saka masu hannu a cikon fadan da sukeyi dashi ? Mahaifinkane fa Aminu baka da hankaline koka fara shaye shayene yaya yi hakkuri don Allah kasan uwa ba yadda za ayi yana tsaye yana kallon zai kashe masu mahaifiya ya kyalesu ? Nice na tsoma masu baki a zancensu bayan na gama sauraren maganganunsu da dansa din abindana fada yasa ya dan kalloni yana fadin. Haba Rahama baida hankaline da zai ture ubansa ubansane fa don kawai yaga suna rigima zai saka baki a cikin zancensu hakan ya nemi albarkansa ke nan ? Zaune nakai cikin sanyin jiki ina fadin yaya ceton mahaifiyarsa kuma yana iya saka yayi komai a lokacin rabu da irin gidan nan da ake irin haka a gabab yaya abin yakan saka yayan shiga cikin zancen wani lokaci. Don babu mahalunkin da zai zauna ana dukan uwarshi bai dauki mataki akai ba kai ya girgiza yana fadin Rahama na gane da sauraki kema kina da kuruciya a tare dake . Har yayi shiru ya dago yana fadin meyasa su yan uwansa mata basu sa hannu a rikicin ba sai shi zaisa hannu don gashi mai karfi ko zai iya fada da ubansa. Ba hakana bane yaya yayi kuskure don Allah da gani a jigijce yake a barshi yaje ya huta bari nasa maigadi ya bude mashi dakin baya guda ya zauna kafin asan abinyi. Da sauri naji yaya din yace No don me zai zauna muna nan baga can gidan ba ya zauna mana da iya nace don Allah yaya tunda yazo nan din ka barshi ? Kayi hakkiri ya zauna nan din bai min magana ba na dade a zaune wajen ina sauraren amsan shi baice komai ba har lokacin. Haka yasa na mike ina fadin inka gama taso muje kaga inda zaka sauka din na fice ba tare da nace komai ba. Shima kuma baice komai ba sai wayanshi da yake duba ya fita batun mu daga bayan mu akwai dakuna hudu kamar boys quaters a gidan da suke rufe sai maigadi dake dan amfani da guda don adana abubuwansa. Tambayasa nayi ina kayanka ko suna can gidan ka bari yace haka nazo mummy don bai bari na shiga gidan ba balle in dauki wani abu . Ok shiga kayi wanka ka huta zuwa anjima kazo ka fita nan titi ka samu kananan kaya ka saya na juya na bar wajen ina jin yana fadin nagode mummy nagode. Na koma ciki na samu yaya a zaune zama nayi ina fadin an bude mashi dakin tsakiya zai zauna a cikinsa shiru yayi ba amsa hakan yasa naja bakina nayi shiru a cikin tsarguwa da hakan da yayi min din. Kamar daga sama naji muryanshi yana fadin ke har yanzu baki fahinci mutanen nan ba naga kina kokarin jawo muna yaron nan a gidan nan banson wani abinda zai kawo muna fitina ko tsegumi ki barshi can ai kakansa tana nan yaje can wurinta ya zauna mana don me zai nufo nan gidan haka kai tsaye. Shiru nayi ina nazarin zancensa a kaina tabbas gaskiya ya fada don ba mutanen arziki bane alheri sai ya zama tsiya a wajensu. Zama na gyara ina fadin ni naga ba zaizo nan mu koreshi ba ai yaya tunda yazo din sai ayi hakkuri don kai ba za aga laifinka ba sai nawa tunda yariga da yazo kayi hakkurin hakan don Allah. Bai kira yace dasu yaron na gidansa ba hakan yasa hankalinsu ya tashi lokacin da uwar ta bugo waya tana tambayan ko yaron yazo nan ? Duk hankalinsu ya tashi haka ba wanda yai dabaran kiransa ni dai ganin har magariba banga yana shirin komawa gidan can ba sai mamakin hakan da zaiyi nakeyi a zuciyana. A bangaren yaya barakha an nemi Aminu a nan gusau ba a sameshi ba har washegari hakan ya daga mata hankali ta bugo waya nan zaria tana tambaya ? Mama Dubu hankalinta ya tashi har dare suna buga waya gusau din suna tambaya ko an ganshi sai ace har yanzu dai ana nemansa ba,a sameshi ba. Ga jafar da suke sa ran shigowan gidan har goma na dare ba labarin shi hakan yasa mama sa a duba mata ko yazid ya dawo aka dubo yana gida. Da kanta taje part din yazid din ta sameshi tana tambayan malam fa don sunan malam Jafar marigayi da sukai jahadin da,awa a cikin kasa yasa duk wani Jafar yawanci ake saya sunan nasa a cikin girmamawa ga malam Jafar din dake tashe alokacin. Yagane dan uwansa take tambaya donshi ake kira da wanan sunan na malam din take fadin malam fa yace yana lafiya ta amsa da aina sani tunda naji shiru ? Tambayanka nayi har yanzu bai shigo ba kai gaka ka dawo gida ko da kansa zai dawo yau ya kamata ace yana nan ga zancen yaron nan da har yanzu ba a gansa ba ko za ayi wani abu a nan ? Mama J aiba zai dawo gidan nan ba yau ban ma tsamanin nan kusa gaskiya kin ga a yan kwanakin nan yadda ya koma kuwa ? Dakata don Allah nasan duk bakin ku daya shi zai fara yace bai dawowa gidan nan a yau da kuwa na sameshi a can naci masa mutunci. Acan kikace mama kwarai ko kana tsamani ba zan iya bane kagani ya dan dubeta ya kawar da kai ya soma tafiya yace zaki iya masa hakan nasani to kira min shi yanzun nan . Ko kaje kazo min dashi yanzu gidan nan yanzu fa mama gomafa ta shude da nan da can ai dayane nagani meye ruwanki da zamanshi can din ke ? Yazid kai abin da nace kada ranka ya baci dani a wajen nan Ok yayi bari na kirashi naji in zai dawo sai naje na daukoshi din. Ya kira wayansa bai shiga ba haka yasa ya fada mata gaskiya itama kuma taji matar computer tana sanar da hakan a wayan . To kinji wayansa a kashe yake yanzu yaya ke nan kaini gidan idan ku ta shanye ku aini bata shanyeni ba har ita karamar yarinyar ta isa ita da masu taimaka mata din kar nake kallonsu. Bai haifawa jikokin fulani diya ba balle suzo su mallake min yaya da raina da lafiyana ina kallo shi kuma J far din zaizo ya sameni ai zai jini. To bari in shirya in fito ya fada ya koma ciki itama ta juya zuwa dauko hijabinta don tafiya ya shige ciki yana dariya. Har ta fito yazid din bai fito ba nan kofa ya tsaya yana kallonta yana gyara rigansa hakan yasata daga murya tana kirasa a hasale tana fadin zata saba mashi fa idan bai fito sun tafi ba. Iya dake cikin tana jin sautin muryan mama ta fito tana fadin lafiya anga yaron ko don tana cikin damuwan rashin ganin yaron a lokacin. Karan budan kofan da iyan tayi yasa salima dake kwance tana charting ta biyota tana fadin iya lafiya ? Iya sai fadi take anganshi ko cikin rawan jiki a lokacin Yazid ya karaso yana fadin mama shiryawa fa nakeyi don nayi shirin kwanciyane kika zo . Nace kunga yaron ne iya ta sake fada karo na uku ba a ganshi ba iya gidan Jafar zamu mama ta dauko shi ya dawo nan. Jafar kuma ta daukoshi kamar yaya iyan ta tambaya to ni dai tace in kaita ta daukoshi can din wai nan ya kamata ya kwana a yau ? Dubu iya ta fada cikin mamaki tana kallon yar nata da wani irin kallon dake baiyana mamakinta karara ga yar nata dake wanan magana. A,a iya rashin hankali yake son ya tafkawa mutane waishi ga salamame zaije gun yarinyar nan Rahama ya tare don rashin hankali ya daukarwa kansa zunubi. Zunubi a wajenwa Dubu wajen ki ko wajen wa zai dauki zunubin da kike fadi dubu ? Dubu dubu kanki daya kuwa da yaron nan yayi wata da watanni a gidan nan meyasa bakice a kwashshi a kaishi can ba lolacin kada ya kwashi zunubi sai yanzu ? Iya wanan ai lalurane itama din ai tana tare dashi a nan kuma, zaman nan din aida ita akayishi da yanzu zatace a maimaita mata hakan da akayi ? Ta fada maki cewa sai an mata maimaicin hakan a gidanta wai dubu meke damunkine haka wai ? Kai Yazidu koma dakinka ka kwanta don ba inda zaku a cikim daren nan da wanan rashin hankali na uwarku don kina mara hankali zaki gidan surukarki da wanan zance na hauka idan kinje kice masu me yanzu ? A,a iya ki bari nayi maganinsa tunda yana ganin ya isa ne yanzu har zai kwashi kafa ya koma can ya tare bai fadawa kowa ba ? Kamar yaya Dubu don ni ban fahinci wanan rashin hankalin naki ba har yanzu waiko dubu akwai hankali akanki kuwa ? A fahintana Dubu kamar kishi kike da yaran nan fa don abin nan da kikeyi bana kai sake bane dubu ban taba gani ko jin irin wanan rashin hankali naki ba gaskiya. Iya yanzu sai a kyaleshi yaeinya karama tana juyashi ana kallo ba a dauki mataki ba jinyar da tazo nan tayi nasa ai yan uwanta dashi ta cuta ga hakan ? A,a ba juyashi tayi Dubu mulkeshi tayi iyakar juyawa dai ko aiki ya sameki babba idan kikace kishi zakiyi da matan yayan ki ? Duniya da mutanen cikinta suna shirin maki dariya jeki dan mutuncin dake gareki a idanun yarinyar nan ya zube aikin banza aikin wofo kawai da rashi kamun kai ? Kai yazidu koma wajenka ka kwanta ba inda zaku ni naga rashin hankali yau a filin Allah ashe ke ba zancen yaron nan daya batane ya dameki ba shirmenki kike a zuciyarki ? Yau ni naga hauka na rubutawa a jarida Dubu baki tsoron bakin duniya ko wanan halin da kikewa yayan mutane ya tambayeki nan gaba ? A,a iya don Allah abar zancen nan baikai har kiyiwa yaran nan baki ba a gareni yaje ya zauna tunda ya zama sallamame a wajenta. Karamar yarinya kamar wanan yau zata juyawa Jafaru hankali yana wanan abin a gaban kowa iya dole inyi magana abin yayi yawa dama an fadi matan fulani haka suke idan sun shigo waje. Kai Yazidu dawo ka kaita ta dauki matakin da zata dauka iya ta katse mama din dake magana ta juya tabar wajen yazid kuma bai ko juyo ba ya shige part dinshi. Washegari da safe kodana tashi kamar kullum na hada mai abinda zai rike mai ciki kafin mu gama breakfast ya dan kwanta. Hakan da nake mashi ba karamin kara mai lafiya yake masa ba ga sunan Allah da zaibi jikinsa da ruwan zamzam ga kuma kuzarin da jikinsa zai dauka yana daga cikin abinda Yazid ya hango na annuri a garesa yake fadin yaga ya canza mashi lokaci guda. A gurguje nake aikina ba don wani abu don kawai nasawa raina cewa suna iya zo min gida a ranan don Aminu dake nan wajen mu. Mun gama na jera mai a kasa don na fahinci a yanzu yafi son ci a kasan don kamar baijin dadin zama saman kujera yaci abu a yanzu da baida lafiya din nan. Na gama na shirya kaina na umurci biba data jetayi wanka har tace ta dauki abincin Aminu takai mai ne da sauri na juyo nace a,a ki barshi nan kitchen har ya shigo. Ba son komai nace haka ba saboda ban manta wani case din daya faru akan wata uwa dake tura yarta kaiwa saurayin gidan abinci ba. Amma haka mutumin yayi amfani da wanan daman ya batawa wanan matar yarta akaita case din karshe dai an cuci yar da uwar don har yakai ga dirkawa yarinyar ciki dole aka haifi dan hakana kuma yarinyar karamace sosai a lokacin. Wanan ya tsaya min a rai yasa nake kafa kafa da yar mutane ban yarda ko maigadi tayi wani dogon mu,amula dashi iyaka gaisuwa a tsakaninsu. Gareku mata wanan abin ya faru da gaske wallahi mutum koke kika haifeshi yanzu ya zama dole a gareki ki saka ido ga mu,amulansa na yau da kullum Allah ya tsare ya kare amin. Wasu dogon riga na saka a jikina _onion_ colour da adon zaiba har kasa anyi rigan mai dagware a sama kamar alkyaba yana daga cikin dinkin da anty salma tayi min na aure a Abuja. Zaune na samu yaya a dakin na shigo ina fadin ka tashi ashe yake fadin yazid ya tayar dani da waya wai yaron nan sun dauka ya batane ashe basu san yana nan ba ? Aminu na fada cikin mamaki yace shifa kiji ba yace muna ya tafi can ba ashe karya yakeyi ke nan nan yayo direct wajen mu. Ikon Allah amma cewa yayi ai yaje ya samu baka nan ace kana nan yace karya yakeyi yanzun ka fada masu yana nan dai ko ?/ Na fada masu ya fada a sanyayye nasan zasu shigo yanzu ai tunda sunji yana nan amma Aminu bai kyauta ba daya dagawa mutane hankali haka ? Bar dan iska kilama abinda ya fada karyane barshi kawai bari suzo din muji ai nasan za a fada masu abinda yayi ya gudu nan yau din nan zai bar min gidana. A,a yaya na fada da sauri ya katseni cikin tsawa da fadin ke karki tsoma min baki cikin maganan su ki barni kawai dasu. Nayi shiru kafin nace wanka zakayi ke nan yace haka naso na mike zuwa bandaki na hada mai ruwan wanka ya mike ya shiga saida ya gama na cude mai jiki da ruwan addua ya saka kaya muka fito falo. Mun zauna ke nan na zuba mashi ya fara ci biba tana gefe daya tana cin nata don sosai muke sakewa da yarinyar harshi sukan dan taba hira wani lokaci da ita. Muka ji sallaman Salima shigowa gidan ashema dukkansune tafe sai Asmau ce sai matar Yazid suka bari a gida lokacin. Ban daina mika mashi fruit din dana gyara ya zama juice ba da nakeyi na amsa sallaman nata ba tare dana juyo ba suka karasa shigowa gidan gaba dayansu. Nagama na dago ina fadin sannuku da zuwa ina kwanan ku a cikin jam,i bansan waya amsa ba ko wanda bai amsa ba a lokacin don na basu bayane ina zaune amma naji muryan yazid. A,a a a mutumina inafa zaka koma gida wanan riritakan da yar nan keyi shine ka gudu ka barni ba azo cin dadin amarcin dani ba ? Iya ba gaki kinzo ba yanzu saiki zauna muci dadin yanzu kada in kwareki kaidai tunda ina da rabo a cikin na yanzu sai in zauna inci amma zan barwa amaryaka aronka kwana biyu ai don tasan ina da kara amma fa a tuna damu muma kada a shagala suka kwashe da dariya. Ai fakaice baiyi iya gara ki fito mashi fili tasan yabar wasu a gida ba nan bane kawai gida a gareshi don shi naga hanyar konewa ya zaba yanzu. Bani ganin hakan cikin zuria,ata insha Allahu daidai lokacin namike a kusa dashi zuwa gaban mama na durkusa har kasa ina gaida ita. Kamar dole ta amsa min ba kin dawo lafiya na juya wajen kawu na gaidashi sai iya dake fada na rike hannunta sai lokacin ta dakatar da zancenta take fadin. Ke dai yar nan kin dawo lafiya yaya kika bar yan gidanku duk suna lafiya dai ko naso nazo banda wanda zai kawoni in maki sannu da zuwa. Iya ba komai na fada ina mikewa tsaye na nufi hanyar dakina muryan ya J naji yana fadin ina kuma zaki ? Daki zan tafi har ku gama na bashi amsa sai yace abincin fa wazai ban kizo ki zauna muci kema baki karya ba ai bari dai ku gama na fada. Kizo ki zauna nace me zamu fada wanda ba za aso kiji ba iya na fadin zo ki zauna abinki ai ba komai zamuyi ba ballema ina zata iya ? Yadda yake magana hakan yasa na dawo na zauna a inda na tashi duk suka zuba muna ido gashi sai magana yake min a cikin rashin damuwa da suna wajen a lokacin. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/25, 12:44] Aisha Srtr Mt: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 8️⃣7️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Aminun yana inane mama ta kawar da shirun dake falon kaina a kasa ya J yace da ita ga uwarshi nan itace ta bashi mafaka a nan . Don ni tun jiya da yazo gidan nan ban yarda dashi ba koransa nayi don yadda yazo min nan a gigice sai hakan bai kwanta min ba. Itace ma ta saukeshi ta bashi wajen kwana a nan gidan dan idan tannei zai koma tun a jiyan ai da bai kwana a gidan nan ba . Wai dama ita Rahama tasan yana nan shine bata kira ta sanar da mutane ba don isa kuma ta ajeshi tabar mutane suna wahala hankali tashe ? Ke zanci abu kazan ubanki wajen nan ke meyasa kike yar iskane wai kamar kinfi kowa baki ban hanaki idan manya suna magana ki tsoma baki a ciki ba ? Me kika dauki kanki ko kin fi wanan biyun ya nuna salima dani baki da suka kama kansu agaban manya basuce komai ba ? Na dago kai nace ya Yazid don yaya ya kori Aminu ni sai na yarda ya bar nan din a yadda na ganshi nasan inda zai nufa kuma idan ya bar gidan nan ? Kwarai kuwa kedai yar nan kinyi daidai haka ake son macen arziki ta kasance dama ta kula da mijinta da kowa nasa wanan shike nuna halin alherinta . Bar sakaran nan da bata san komai ba sai rawan kai da iya makircin banza meye na ganin laifin yar mutane a nan daga ta taimaka muna da bata rikeshi ba yanzu har muzo a sameshi nan. Bakin saratu shi zaija maki matsala bansan irin bakin wanan yar ba a rayuwana yaron nan a nemansa an kuma ganshi a inda ya dace . Barta kawai dai idan itace mai mugun halin nan irinsune masu iza dangin miji nisa da dan uwansu wanan zata iya haka tsab yazid ya fada. Yanzu ina Aminun yake mama ta sake tambayan nasan don Yazid ya katse zancensane kan yarta ta fadi hakan a lokacin. Biba je baya ki kira yayanki Aminu kiyi maza ki dawo don Allah kada ki tsaya da sauri Biban ta fice don kofan a bude suka barshi saida ta dawo ta rufe tana fadin gashi nan zuwa anty. Bai jima ba shima ya shigo da sallamanshi yayi kyau a cikin kanyan dake jikinshi duk suka juya suna kallonshi sai yayane tun bai zauna ba yake tambayanshi. Dama da kaya kazo shine ka shigo min gida jiya da shigan iskanci kamar dan ginan zinari mutsu mutsu dakai ba dadin gani. Da sauri yaron yace a,a uncle mummy ta ban kudi jiya naje nan kasa na sayo kayan nan ya fada yana kallona daga inda nake zaune nace kudi na bashi nace ya sayo yan suturan sauyawa don yadda yazo. Ba dole ku gamshi hakana ba uwarshi tace ya dawo daga wajen ball ne ai ya samu a na rikicin ya kwaceta sun tarar mata kamar jaka zasu kasheta ya bambara uban daga shakar da yaiwa uwar shine haushinsa da dan don me bai bari ya kasheta ba ya bambarashi . Allah ya saka maki da alheri yar nan aiko hakan kin wadatar wallahi angode kinji kinyi komai wallahi iya ke fada min hakana. A Rahama ai dabance gaskiya ni halinta yana mun sosai wallahi wai har wanan sakaran zatawa mutane maganan iskanci don samun wuri. Tayi mana tunda ta sabayi tana cin banza naso ai ace bakai magana bane takai karshe a dazun din naci muruncin ta idan ba Rahama din datayi masa haka ba ni yaushe zan tsaya kallon dan Barakha yanzu ? Kallom J din kowa yayi da yake wanam kalaman nasa yace kwarai ko a zaron ku zan manta da cin mutuncin da kuka so min ne a baya ? Yau gashi wace kukai min donta itace kuma ta kama dan barakha aitayi amfani gareku kuje kuyi tayi idan muna funci abin yine ni dai nasan ban hada dukiyana dana kowa ba ? Yanzu kuma meya kawo wanan zancen ga yar uwarka Jafaru jinin barakha jinin kane hakama naka jinin natane dole ka rile dan barakha a duniyan nan itama ta rike naka. Ma tukar ana son ayi zumunci mai,,,,,,, Wani zumunci kawu irin zumuncin ku da mama kake nufi kome yan uwana dai masu kaunana saboda Allah zanyi zumuntan dasu . Kyaleshi kawu wani abu ya hau kanshi nake gani a gaban mu Jafar yake wanan magana yanzu ka yankesu ka soya so wa yanda baka so din. Basu dai sona mama ai su suka nuna min hakan ke zan fada maki da ga yau ki fita hanyana da duk wata iyalina Saratu. Na fahinci lamarin ki babu alheri a cikinsa ko daya don haka ba ruwan ki da iyalina na fada maki bake kika auro min mata ba ba a karshinki take rayuwa ba ko gaisuwa na yanke tsakanin kedasu. Bake kika ban abin hannuna ba balle ki kawo min izza da isa a cikin iyalina na fada maki . Basu ba harni yar kallon lankwas nayi ina mamakin yaya J a lokacin don irin maganan da yake zarowa a bakinsa. Eeh lalai Jafaru yanzu na kara yarda cewa an wanke na fulani kuwa an baka kasha don yadda ka zare din nan kai da bakinka kake fadan wanan maganan ga yar uwarka ? Don tayi magana fadan gaskiya da wanan wawa yakasa fahintarta shine kake fadan haka a gaban kowa yamzu ? Mama nine wawa kuma sai yayi murmushi baiyi magana ba yazid ke nan ashe akwai abindaya kulla a ransa ranan. Shiko yaya yace meta fadawa Rahama yanzu in ita bata da hankali ai ita da iya sun bata amsan daya dace ina magane akan shiga da tayi part dina jiya tasani meya hadata da Asmau jiya ? Waini karata ta kawo a wajen ka dama ni kike tambaya karanki aka kawo wajena don kina yar iska ni zaki tambaya don ban isa a kawo karanki a wajena ba ko ? Wai meye hakane kukeyi yau zaku tararwa mutum daya kamar kuna hake da ita dama kun zauna baku barmu munyi abinda ya kawo mu ba kan yaron nan sai zagin yar uwarku kukeyi. Sakaiyan da zakuyi min ke nan a yanzu na fatana inga kanku ya hadu tun da raina kai jafar kake fadin wai ka yanke alakarka dasu don mace ? Ita Asmau ta kasa fada min ko meya sai ta kiraka nan don munafunci ta shiryama karya da gaskiya ko mama akan me zata kiraki tunda bake kika ajeta ba . Eeh lalai kuwa na tabbatar a yau din nan haka kace Jafar mama me zance tunda wanan yarinyar bata son a zauna lafiya itace kadai kika dauka a yanzu kin haifa cikin mu ? Yaya tashi muje ta fada tana mikewa tsaye cikina duk ya duri ruwa a lokacin don yadda naga ranan ya rikide min ya koma malam jafar dinsa na gaskiya dake tsayawa ya fadawa ko waye gaskiya. A,a fa mama nima dana ganta dashi sai da nayi mata magana nace hakan bai dace ba ace ta shiga har dakinshi ta dauko mai abin amfaninsa haka ? Tace ina ruwana ai ba nawa bane ni kuma na kyaleta tunda kona fada maki kema zakice aiba nawa bane ta taba salima ke fadan hakan bayan sun mike din. Mama ta juyo ta watsawa salima din harara sai kawu ke fadin a,a dubu abin amfanisa fa akace ta dauka cikin zafin rai tace yaya don Allah ka barni ko ran jafar saratu ta dauka laifineb? Balle kayansa ai bansan a jirace yake damu ba gidansa ka zauna a gindin mata suna rabaka da yar uwarka dama ai haka suke so don burinsu ke nan ? Gaskiya kai Jafar kuma bai kamata ka fadi hakan akan yan uwanka a gaban mu ba don dai kokarin uwarku duk a kanku yake karewa taga ta kammalaku a waje daya. Wasu kalamai yazid ya fada a cikin larabci wanda shi yasan meya fadi kai dai fada masu in aya ka jawo koda yana da hakkon kan iyayyensa don tauye hakki bala,ine ? Muje yaya mama ta kara fada tayi gaba ya biyota a baya suka fice gidan kallon Aminu yaya J yayi yana fadin ka tashi ka bisu. Sai yaron yayi kasa da kanshi bai motsa ba ya kara fadan bakaji me nace bane ka zauna kuma ? Uncle ayi hakkuri don Allah a barni nan ni ba baeun ka gidan nan ba ban son abinda zai jawo muna magana kan zamanka nan kaga yar iskan nan yanzu ta fara fadan ba daidai ba. Ba abinda zai faru ka barshi a nan har aji ta iyayyensa jafaru tunda nan din yake son zama gashi anzo ba a gane komai ba yar banzan nan mai bakin tsiya ta hana akai ga matsaya kanka ? Waikai meya farune fada muna muji yazid ya fada aiyo yanzu naji maganan hankali wurin nan nan din Aminun ya shiga basu labarin abinda ya faru kamar yadda mahaifiyarsa ta fada a waya. Yazid yace ni yanzu yaya abinda naga yafi tunda har shi yace ya bar masa gidansa kan wanan zancen a barshi nan ya zauna mugani uban zai dawo hankalinsa ya nemeshi idan bai nemasa ba fine sai a rikeshi a nan din dama da gida biyu aka sanshi ai. Yanzu kai ka saurareni kaji abinda yaya ya fada wallahi naji wani tsegumi ko kyam daga gareka game da zamanka a gidan nan ko yaya bai koreka ba ni zan turaka kabar gidan nan. In shaAllahu uncle ba za a samu matsala a wajena ba ya fada wanan dalilin yasa Aminu din zama a gidan mu kuma yake amfani da hudubarsu a gareshi dama halinshine hakan shiru shiru bai magana . Haka burin da mama taci akan zataci min mutunci nida jafar ya tafi a fushin da takeyi dashi gashi ya nuna bai ma san tanayi ba. Zai kira Asmau da safe kafin ya karya su gaisa yaji lafiyansu haka kuma da rana zai kira suyi ta hira da yara don ita dai za ace gata nan daine da halinta. Ban faye damuwa da lamarin su ba don haka banyi mamakin rashin zuwanta gidan mu wajen mijinta ba kamar yadda shima din bai je gunsu ba a cikin sati biyun da yayi a gidan mu. Duk da dama ba fita yakeyi ba illa iyaka dai idan wasu da baiso shigo mai gida suka zo shine yake fita kofar gida ya samesu. Saida yayi sati ukku cur a gidana ranan kwatsam naga ya kira yazid yana fadin yazo ya kaishi gida ya dubu su daya gama shiri kuma yace min sai ya dawo. Sai bayan fitansu nake ji a bakin Aminu daya shigo gaida mu da kwana yake tambayan uncle fa nace ya fita yaje gida yau. Sai naji yace dama iya tace in fada mashi yayi kokari yazo don rikicin kawu da uncle yazid da sukeyi da sauri na juyo ina fadin rikici kuma akan me ? Yace to ni dai naji kamar ana fadin rikicin kudin gadonsu uncle da mama saratu wai kawu din ya cinye masu kudinsu na gado. Wanan magana babbane ashe naji iya tace uncle yazid yana da gaskiya ita kuma mama tana fadin uncle baida mutunci. Allah ya kyauta nace dashi na karasa da abincin ka yana kitchen ka dauko ya mike zuwa kitchen din ya dauko a nan falo ya zauna yana cin abincin nasa. Yake ban labari akan zaman su yaya barakha da kishiyarta shike fada min yadda tayi da kudinta itama da aka raba ta karba. Yadda mijinta ya cinye kudin kaf babusu babu dalilinsu a yanzu ga kuma ba zaman lafiya a tsakaninsu yanzu ya kare da fadin kowa gari ya sani da kudin ya kara aure ai. Haba dai Aminu haka na yuyuwa kuwa ya dauki kudinta ya kara aure dashi shine ya shiga ban labarin irin rikicin da akayi lokacin auren. Yaya bai dawo gidan ba tun safe har dare nina daukama ya koma canne sai gashi wajajen magariba ya shigo kwatsam kuma na gaidashi ya amsa ya samu waje ya zauna a cikin gajiya. Na mike tsaye naje kitchen na dauko mashi ruwan gora da kofi na kawo mashi gabanshi ya dube ruwan yana fadin anya kuwa zansha ruwan nan banci abinci ba tun karin safene a cikina fa ? Na waro ido cikon mamaki ina fadin garin yaya kaiko kasan fa jikinka ba lafiya ko banza ni magani da bakasha bama shine nake tunane ai ashe har abinci bakaci ba. A kasale yake fadin kinsan Asmau bata da wayau taga na wuni a gidan ko ruwa ban samu ba a wajenta balle abinci ina can muna fama da rikicin yazid da kawu tun safe don yazid yakai kawu koto. Subbahanallahi na fada cikin kaduwa yace wallahi na mike ina fadin Allah ya sauwaka na nufi kitchen don dauko mashi abincin rananshi dama na aje muci da darene. Na dawo na zuba mai na zauna a kusa dashi ya soma ci yana fadin kinsan yazid tun ranan da sukazo nan da mama tace mashi wawa shine yayi fushi ya samu kawu gida sukayi ba dadi zancen kudinsa. Kudinsa ke wajensa ke nan ya dauki ruwa ya kora ya aje yana fadin duk abin nan baki sani ba a nan ya koro min kan zancen tun farko. Shi nake fada maki wanan kawu din ba mutumin kirki bane ya dade yana cutan mu ai yanzu mama ta gani koda yake duk abin nan kamar bayansa take goyo har yanzu. Yanzu sunso nasa baki nabawa Yazid kudin don rashin tausayi bayan kudin dayasa mama tayi ta karba da sunan nema min magani yana debo ganyen banza yana kawo muna. Shine na nuna masu ni a yanzu banda komai ga yazid ya hau gashi gobe za a koma kotu shine hankalinsu ya tashi iya kuma taki sa baki a zancen. Sai cewa tayi yaje ya nemowa yaro kudinsa duk inda ya sakasu jin haka ita kuma saratu ta sawa mutane kukan banza munafuka kamar bada ita aka shirya hakan ba. Na salima na fada masu yanzu kudin sun kusa ninkawa don na kara mata kudi a lokacin ake juya mata abinta lafiya lau. Lalai yau ashe kunyi shari,a babba ni karshe dai don kada suce zasu jani gobe zuwa kotunsu na nuna masu banda lafiya don haka ba zanje ko ina ba. Amma yaya dakasa baki a zancen ko baka bada kudin ba a maida case din nagida zaifi shiru yayi yaci gaba da cin abincinshi. Saida ya gama yake fadin nasa baki in biya ke nan hakan ya nuna bansan zafin kaina ba tun lokacin ai ido nasa masu nasan haka za a kare don nafisu sanin waye kawu ? Amma ita mama sam kome yayi daidaine a wajenta saboda ya gama da ita shida wanan bakar matar nasa hafsatu munafuka ke nan ta karshe. Dazun iya ke fada min ta kamasu suna fadin wai kece kikazo min da farar kafa komai ke samuna a yanzu nan iya tayi masu tas ta fita. Wa,iyazu billahi ni kuma nikan me nayiwa mutanen nan haka basu kaunata ina ruwanki da kaunar wasu tunda ni ina kaunarki. Nagane nufinsu ba yau ba duk abinda suke kitsawa a kunnena yake basu sani ba Allah dai ya ban lafiya donsu yanzu a zatonsu duk na koma banda komai tunda basu ganin ina facaka irin da. Addu,a nayi a raina Allah ya bashi lafiya ya koma harkokonsa da yakeyi Allah kuma ya buda mashi fiye da baya ubangiji ya fitar dani daga zarginsu. Ashe in ba a son mutum komai ana iya mashidon kawai a bata mashi suna nikan naga makirci ga mutanen nan da shekaruna bakai ace ya dauka ba. Amma nasan na farko mace tasa tsoron Allah a cikin lamarinta na biyu kuma ta rike gaskiya komai dacin ta ta kama kanta da mutuncinta ta zauna lafiya da kowa. Mun gama ya mike don yin alwala nikan cike da bacin ran wanan kazafin daya fada min suna min gashi Yanda tunda sukazo da yara sau daya ta dubani bata dawo ba har wanan ranan ni kuma banje gidanta ba. Saidai mukan danyi waya da ita wani lokacin ta kirani ko ni in kirata hakan kuma ban saka komai a raina ba iyaka na dauka a yadda ta dauka din tana gudun ace mun hade kai. Ko wani magana ya tasone ace da ita don ita tun muna yara Allah yayita da ruwan ciki sosai a cikin mu don tsoronta har ya baci donshi yasa ma nasa a raina zan daina biye mata don bafa zata gyara ba. Anty salma na kira akan zancen ta bani shawara tare da kwantar min da hankalina akan zance na in sharesu yadda nakeyi su da kansu zasu biyoni. Indai daure in fita batunsu kada kuma in fasa alheri ga wanda yazo wajena inda nake. Mun gama na kira yar aikin ummah itama mukasha hiran mu ta fada min wasu dabaru namu na mata da zan kara dauka. Ya shigo ya sameni kwance muna waya da ita yake fadin na zata barci kikeyi naji shiru ga danki nan ya shigo yana neman ki ! Hakan yasa na fito falon a ranan na fahinceshi sarai so yake mu kasance tare dashi dama tunda na dawo haka yake min idan yana son kasancewa dani da daren. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/27, 07:17] Aisha Srtr Mt: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 8️⃣8️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Wajajen shadayan rana muka iso gidan nida Biba da Aminu dana jawo yazo yaga gidan don ya sani irinsu Yanda sune marasa marmari irinsune masu batawa fulani suna. Sam bata da sabo ita bata da sakewa da kowa abu daine idan ance so to shi hana ganin laifine a wajen wanda aka jefa da wanan kalman. Don ko son da habu kewa yanda yasa shi bai ganin wanan halaiyan nata na daban da mutane ke fadi kamar ace komawansu gidansu su kadai a yanzu din nan . Ya kara nisanta ta da kowa yara kawai muka samu a falo suna waaansu ita kuma tana dakin kwananta muka tsaya nan muna sallama yaron ya ruga daki ya kirata shi mai wayau din kaeamin kuma ya tsaya yana kallon mu. Haka ta fito sinkinkin da ita tana ganina ta dan yi murmushi tana fadin ashe kune tafe sannunku da zuwa nima kwana biyun nan kina cikin raina wallahi. Ban kulata ba na juya harshe da yare inawa danta Abba yaron baima san inayi dashi ba don bai san abinda nake fadi da yaren ba na juya ina fadin amma kinyi sakaci da baki koyawa yaran nan yare ba nan gaba zasuji haushin hakan. Take fadin babansune bai so a koya masu yana fada idan yaji ana masu yare nace filatancine bai so kome ? Bata tanka min ba take fadin bari ta kawo muna ruwa ki barshi saidai su nikan a koshe nake ta dai mike zuwa kitchen dinta wajen fridge dinta sai gata da gora biyu na ruwa ta aje muna . Nan suka fara gaisawa da yaran kamar mintuna goma na mike da gaiya ina fadin zamu tafi dama munzo kawai mu duba sune. Haba Rahama tun yanzu ko zama bakuyi ba ina ce a nan zaku wuni ai a,a nazo duba yaran nan ne kwana biyu bangansu ba. Suma suna kewanki baba yace in ya dawo zai kaisu which means bada ita ba take fada min hakan kai tsaye to ni zan tafi zamu biya gidan yaya Ai mu gaida ita. Sai lokacin take tambayana waya kawoni nace Nape muka hau take fadin kuma yaya ya yarda to yaya zaiyi tunda ba zai hanani zuwa in dubaki ba matukar ina da lafiya ? Idan kinga ya hanani fitowa ya fahinci banjin dadin jikina shi kadai zaisa ya hani zuwa gidanki ko kuma yana jin jalin maza a lokacin. Dan kame kame ta farayi don itace ko yaushe take fadin mijintane yake hanata zuwa dubana ko tayi mashi magana. Daga gidanta gidan yaya Ai muka tafi saida mukai azahar muka fito zuwa family house dinsu mugaidasu maman tudu. Takuwa ji dadin zuwan mu din sosai don sabo a yanzu ya shiga tsakanina da ita duk da munci wani abu gidan yaya Ai amma saida mama tasa mukaci dambun shimkafa a wajenta. Ta sayo muna sobo mai sanyi mu kora sai hira take jana dashi bandai yarda na fadi wani abu mai muni game da mijina ba ko mahaifiyarsa. Mun jima na bata alherin dana rilko mata koda muka dawo gida mun samu ya rigamu dawowa halin mazane don ko yayi fadan dadewan mu sosai. Har in kaga yayi fada akan abu ransa ya baci da abin donshi nayi shiru na shige daki na sauya kayana zuwa kitchen don yamma da yayi muna lokacin. Har dare bai sauka ba yana fushi dani nidai ya dawo daga sallah na hada mai abincinsa na aje mai daki na koma nayi sallah dana idar kuma na kwanta abina. Daga falo ya kwala min kira nasan abinci zan zuba mai lokacin na fito na sameshi nima fuska a dare nazo gareshi ya dago ya dubi fuskan nawa yana fadin abinci zaki zuba min ? Nan ma banyi magana ba na duka na soma zuba mai abincin har lokacin ban cikin sakewa sai naji yana fadin kin san bake kadai bane zaki fita tun safe har yamma haka ? Idan jigila yaja maki wani matsala fa tunda jikinki ba karfine dashi ba har yanzu gashi ance ba,a son mai ciki fitan yamma ? Gidansu mama muka fito fa mun jima a gidan yaya Ai har kusan la,asar muna can gidan ta ya tare da fadin bandai sin hakan na fada maki nayi shiru. Munyi hakan da kamar kwana biyu ya sameni da zancen a gobe in sha Allah yake son ya koma can gidan ban nuna komai ba duk da naji abin a bazata. Kinsan mu mata ko yayane sai mun dan nuna halin kishin nan gashi kuma sati biyar cur yayi a gida dole ko kome naji in taushe a lokacin don yayi min ba zance ga kara ga ittace ba irin namu na mata. Donshi nace Allah ya kaimu gobe lafiya shiko gogan ya tsureni da idanunsa yana kallona ko zai fahinci wani abin daga gareni. Yaron nan iyayyensa basu ce komai akansa ba har yanzu donshi nake son a nema mashi makaranta ya fara zuwa a nan in kuma uban bai yarda ba ya koma gida gabansu. Me zai hana ya yarda tunda yaran ba damuwansa sukayi ba yanzu inda ya damu aida ya bugo waya yaji ya fada nayi magana a sama mashi gurbi a nan saiki fada mai ya aika su turo mai da takardunshi daga can gida. Naga ke kina son zaman yaron a nan iba haka ba niba zan barshi nan wajena ba saidai ya koma can gida wajen mama su zauna abinci daine Allah ya hore min in basu. Ai yiwa kaine dan yar uwarka ai dankane ba a san moriyan da za a samu ga hakan ba yace badai a wajen barakha ba kuwa a daiyi din kawai don zumunci Allah yace wanda ya yanke zumunci zai azabatar dashi . Donshi nake duba ina dan rage wani abu amma su suna ganin hadani da boka da malam din da sukeyine yake tasiri a kaina. Ita saratu yanzu naji ance ta turawasu yaya mai nemanta wani mutumin sokoto ta samu yana aikin banki a nan garin . Masha Allah nace ashe aure yazo ke nan tunda har yaje gida sai naji yace ita dai ta sani niba ruwana da zancen yar iska yanzu tunda bata son farin cikina. Bance ban mata komai ba amma ba dai irin na salima ba kan da sauri nace hakama ba zai yuyu ba tunda su biyune kadaiyi din a fitar da hakkinsu akanka. Wani haki take dashi a wajena yarinyar data hada min banga a tona min asiri ai duk naji komai shiyasa kikaga ban saka kaina a rikin kawu da yazid ba dukko yadda mama taso naki hakan dole sun kyaleni yanzu. Shi kawune bai kyauta ba ai tunda yasan amana aka bashi don me zaisa kudinsu gaba ya cinye har da aure da dukiyan marayu don Allah ? Murmushi yayi ya mike tsaye yana fadin ke aurema da yayi shiya dameki ai auren amman da matarshi tacine ya fita mata tanan . Da kinji abunda yayi da gudin aida baki kara kallonshi da daraja nace to Allah ya sauwaka ya fita yana fadin zaije family house dinsu a can zaiyi magariba. Nayi mashi Allah ya tsare ya dawo lafiya da haka ya mantar dani takaicin kishin daya fara min tukuburin a zuciyana . Don kodaya fita ban koma takan maganan tafiyansa ba sai zancen kawu da yayi min ne ya tsaya min a zuciyana. Ni dama mutumin yana da zubin munafukai inkin gashi haka kuma tunda ya fara sukan Yanda akan kwanciya asibitin ta na farko yasa na fara kinsa a raina. Lamarin yaya kuma nasan dole dai ya koma wajen matarshi dama tunda yanzu alama ya nuna ya samu lafiya sosai tunda na dukufa da mashi addu,oi da bashi makarun dana amsa a gida tun wancan lokacin da gardama yayi yawa na kwashe abina na boye sai yanzu nayi mai amfani dasu yadda akace. Don kiri kiri mama ta nuna a daina mashi amfani dasu tafi amincewa da wanda suke karbowa da kawu ko kawu din ya kawo shi kadai ayi amfani dashi. Kamar yadda yace din kuwa washe gari karfe biyar yayi muna sallama ya nufi can sai naji gidan ya koma min shiru a lokacin. Na dawo falo na zauna har akai magariba kafin na shiga dakina nacewa Biba idan ta idar ta sameni daki sallah magariba nayi na jira isha nayi kafin na shiga wanka na fito na gyara jiki ranan banjin cin abinci bread da gesha gwagwani nake so shi muka zuba a plate na dan kara garin yaji mukaci. Saidai su sun kara da abincin ranan dana aje masu don Aminu bai wasa da cikinsa abinci yake kwasa sosai abinshi. Tunda na gane haka kuma nake shake mashi abinci a kulansa sai yaci ya koshi tas yake share abincin sai kula. Ashe dayaje can gidan ya shiga gaida mama take fadin yau ko ya bace hanyane yazo da yamma gidasu tunda matarshi ta hanashi kula kowa nasa yanzu sai ita kadai da yan uwanta ? Yan uwanta kuma wasu yan uwansu ke zuwa wajensu kuma mama tace nasani malam kaban mamaki kwarai wallahi da wanan yarinyar har zaka iya zama ta juya ka ? Nasan zaka dawo ai tunda nima ban zauna ba don ba zan saka ido ina kallo na haifawa yan daji kai ba su suka iya balleni ? Iyawan me kuma mama dama kwanakin dana diba ke nan zanyi a wajenta don irin hakkurin da tayi dani da banda lafiya na kuma ba Asmau hakkurin hakan kafin naje kuma ta yarda da hakan itama. Inma kinje wani wajene akan hakan mama sunci kudinki a banza wallahi kafin yacigaba ta katseshi da fadin . As,maun me can don Allah ana batun mutanen arziki Asmau wayau da ita ko wauta koma meye saina nunaqa yarinyar nan tayi kadan wallahi. Dama tafi yar uwarta rawan kai ko a yanayinsu ba daya bane da yar uwarta don yar uwarta na boye halinta zaki dai bata kudinki ga banza mama. Kawu dai ya sauya maki halin ki a yanzu da karfi da yaji wallahi irin abin nan baida kyau mama komai mutum yace bai barwa Allah sai wanin Allah yafi masa wanan hanyar halakace babba wallahi. Au ashe kai malaminefa mai da,awa ai ban sani ba saika kafa munbari kofan gidan nan kace ina wanan aikin mama ai gaskiya yaya fada salima dake zaube ta fada. Ta mika mata hannu tana mata dakuwa tace Allah mama har an soma gulman ki yanzu a gida kan hakan don Allah mama ki bari hakan baida kyau. Gashi yace Asmau tasan zaiyi hakan ashe kullum mama ke kika tashi shine anci amanan Asmau da yake munafukace ba ? Waya sani ko sayar mashi da kwanan tayi don jakkanci haka kawai zan sake namiji zuwa gidan kishiya tsawon wata da dan kai doluwa kawai na banza. Yarinyar nan badon mutuncin iyayyenta ba da tuni nayi gaba da wagarar banza kawai mara aji mace chusu kamar an shuka dusa tunma data kara kiban nan sai duk ta koma wani iri da ita wallahi. Haka kuma danki ke son taba saratu ta fito tana fada jin ya dade da fita dakin tunda salima ta soma magana ya fice abinshi. Ni banga abinda yaya ya gani gun Asmau ba tun tana da kurciyarta ita ba kyau ba ba tsarin macen shiga gaban mota ba ita dai gata nan wace iri da ita ba kuma gyara. Ummh mai kyau da gyaran kuma ance karuwa yar kauye kowa dai yaji da nasa ku barshi da matansa son Allah salima ta fada tana mikewa tsaye. Ni mama salima tana ban mamaki wai sai taita nunawa kamar tafi kowa son yaya j a gidan ni abin yana ban mamaki wallahi. Salima din dai bata juyo ba ta shige daki sai saratun ke fadin wai ya dawo nan ke nan kome naji yana fadin wai sun shirya hakan da Asmau ne dama ? Munafuka amma bata fadi ba idan taji kina fada sai dai tace ba komai ai mama ashe da saninta yake can duk dadewan nan ? Allah ba din mugun fata baida kyau ba danace yadda tayi makircin Saiba ta fita itama Allah yasa wacan bafulatanan banza ta futar da ita gidan nan don bata da amfani sai zuba wasu yaya masu gajerta dasu. Iya ruwa dai fidda kai abinda ke hada ki da yan uwanki kenan kuke fada zaki soma kuma aibanta mashi yayanshi ke meyasa kike hakane wai ? Shiru tayi don tasan tunda mama ta kwabeta zancen yaci mata rai da gaskene da ake cewa mama din tana da son jinin ta ita tasan hakan ba karya bane da ake fadi. Don indai yaro dantane ko jikinta tana son abinta ta gano hakane tun akan diyan habu duk yadda taki maria tana son yayanta data haifa da danta wanan yasa ta kame bakinta tayi shiru. Tun a lokacin ba wanda ya kara wani zance a kai game da daaowanshi gida din kamar yadda suka dauko zancen da farko da ace mama ta kama zancen saratu ta fitone tayi maganan aminiyarta lokacin. Sai gashi uwar ta katseta da zancen yasa tayi shiru can kuma bangaren itama Asmau daya shiga wajensu ta nuna bacin ranta a irin sallon nata kishin don cewa tayi dashi aida ya zauna can din ya kara kwanaki. Ba abinda ya dameta sai takura masu da zaiyi a yanzu da gyara wancan kinyi kaza kinyi ba daidai ba ke kazamace hakan kuma baisa ta gyara halinta. Aiko yana shiga daki ya fito ya fara fada yana fadin tunda ya kwanta jinya baijin an taba share mashi dakin nan ma ? Ta yaya mace zata zauna bata da aiki sai kazanta da lalaci ya nufi tsintsiya ya dauko ba abinda yafi bashi haushi kamar bandakin dayaje alwala har wani renewa yayi saboda kazanta. Ganin hakan yasa ta karbi tsintsiyan a hannusa yasan ba gyaran kwarai zatayi ba amma ta fara kore wanan kazantan dake daga mashi hankalinsa. Koda ya dawo bayan sallah isha,i ya samu tana girki wai dama basu da niyar dafa abincin dare sai kuma gashi shine ta dora girkin dafa dukan shimkafa tayi. Ya shiga daki tagama ta kirashi take fadin ga abinci nan an gama ya dan jima ya fito ya dubi yaran dake kwance har sunyi barci cikin tausayi yasan basuci abinci ba sukai barci. Yake fadin sunci abincu tace kafin tagama sunyi barci nan ya soma fada da ita waike Asmau wata irin mace ce ke don Allah ? Wanan hali naki dole mutum yayi aure ko bai shirya hakan a rayuwansa ba ai ki duba yaran nan kefa kika haifesu Rahama dana fito gidanta yaran dake tare da ita irin dadin da sukeji a wajenta. Ke yaushe zaki hankaline wai Asmau kefa kika haifi yaran nan zaki barsu su kwana da yunwa shiyasa a kullum suke fige kamar kar Saiba tabar gidan nan komai naki a yanzu ya kara tabarbarewa ga baki daya wallahi. Dama ai ka saba fadan tafini don kafadi haka matanka sunfini aiba yau ka saba fada min hakan ba ? Ni wanan bai taba damuna tunda nasan ina kokarina kaine baka ganin hakan yaja tsuki ya bude plate din abincin data kifa wani saman wani da niyar yaci. Abinda ya gani shiya tunzurashi ya mike kawai yabar falon zuwa dakinshi dama tsamin falon ya isheshi a cikin daurewa yake karfin hali. Haka a yadda yaken ya dan kara gyara dakin ya feshe da kamshi har zuwa ban daki ya samu waje yana maida numfashi. Haka ya kwana da yunwarsa cikin dare kodaya falko ya ganta a bayansa tana nasari da safe ya fice sallah daya dawo wajen iya ya nufa. Ya kai karan Asmau din iya dai hakkuri ta bashi tace idan ya matsa ni zai shafawa laifin yanzu don kowa zaice ban barshi a banza tunda ance so nake in kore su in mamaye gida ni kadai yadda yar uwana take zaune ita kadai. Iya din dai ta kira Asmaun tayi mata fada sosai ta kuma gaya mata ta kama kanta in har ta bari ta tunzurashi ya kara aure ita tasani. In kuma so takeyi Saiba ta dawo ta hanata kwaciyan hankali to ta matsa tasan komai yana iya faruwa don da ya auro wata gara ya dawo da saiba din dakinta. Wanan zance shiya daga mata hankali sosai in akwai abinda ta tsana taji anyi zancen dawowan saiba gidan gashi iya ta fara fadin hakan kuma . Taji fadam iyam don kuwa a ranan ta wuni gyaran gidane tun safe ga girki data daukeshi wani jar duniya a wajenta runda yace bata iya girka abin kwarai ba shine ta zage tayi masu tuwo da miyan shuwaka. Yazo gidan mu ya dubmu lokacin sha dayan rana har ta gwauta koda ya shigo ina daki ina barci naji ana ja min kafa hakan yasa na falka. Yana tsaye cikin fararen kayan daya saka a jikinshi annurunsa daya fara dawowa lokacin sai naga ya dan gushe min ga gani. Kun tashi lafiya ya fada na tareshi da fasin ina kwana ya amsa min yana fadin kun bar gida bude kun shige daki kowa na barci. Nayi mika ina fadin mun karyane naji kasala ya kamani nazo na kwanta bansan nayi barcin bama wallahi na fada ina kokarin tashi zaune. Falin muka fito tare mun dan taba hira ga kuma girkin dana dora muna na rana yana gidan saida akai sallah azahar ya fita. ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/29, 07:53] Aisha Srtr Mt: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 8️⃣9️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Zan iya cewa cikina a yanzu yakai wata takwas a jikina a lokacin kuma zancen services din mu ya fito haka na shiga na fita na samu result dina yayi kyau. Wanan daman na ciki akai amfani dashi banje ko ina ba ga sha,anin bukin saratu wanda ya taso a yanzu don mijin data samu kamar a shirye yake da zancen auren . Don bai tsaya jan wani lokaci ba duk abinda ya dace ayi na al,adan aure yana gabatarwa ba bata lokaci wanan yasa hjyn rawan kai don ganin tayi sa,sn mijin aure. Don ita salima mijin bai karasa ginan shi ba don shine ba za a hada bukinsu ba a cewan mama wanda ya shirya ayi kawai kowa da sa,anshi yake zuwa duniya dama. Wanan yasa suka tsayar da ranan aurenta ita kadai ba tare da yar uwarta salima ba tunda mijinta bai shirya mai karatu dama na fada maki yarone kusan sa,an juna suke dashi a cewarsu alhalin kuma ya girmeta da shekara biyar shi din. Don dai basu sone suke fadin hakan akanshi wai yan sa,a guda suke da saurayin nata ai bata damu ba tunda tana son abinta har ankai ga zancen aure yanzu tsakaninsu. Ni fargaban haihuwa da yadda nake jin labarinsa ya dameni a yanzu ba wani zancen auren saratu ba can donko na sa kaina ba ama yi dani din don me zan matsa kaina da zancen abinda bai shafeni ba. Saidai duk da hakan ban tsira ba a wajen matar yazid nake ji wai nice ke zuga yaya kada yayi mata abin arziki na hanashi kashe kudi ga yar uwarshi kiji alhaki fa don Allah yar uwa ? Ni dako zancen bamu tabayi da yaya ba wai amma mama ta dauki laifin komai ta dora akaina kuma yanzu koda naji zancen ban damu ba saboda nasan karan tsanar da mama ta dora min a kai tun shigowana a cikinsu. Yanzu nagane taso tayi amfani dani kawai inyi ta bautawa rayuwansune kawai a baya bata so zancen aure ya shiga tsakanin muba da danta shi kuma sai ya shamci kowa yayi abin ta baibai ba tare da sanin kowa ba. Zancen kayan electronic sukazo nai dashi yake fada masu har kudinsu ya bada don haka shi ba zai kara komai ba su barshi da abindake gabanshi na haihuwan matanshi kuma. Daga wanan zancen ina ruwan zafi su sakani daga uwar har yar nasha zagi a bakin su ko ina sai batani sukeyi wai na hana yayiwa yar uwarshi komai a yanzu. Wai kuma ashe ya bada kudin saitace gadon da za a sai mata bai mata ba shine mama ta biye mata suka sai gadon da takeso kudin ya kare gaba daya yanzu suka koma suna kame kame . An lalubo Habu yabada dubu dari uku sukara shi kuma yazid yace ai sun san baida kudi tunda da mama aka hada kai kawu ya cinye mashi kudi ta kuma hana yayi magana. Haushin hakan yasa suka shiga wani rayuwa na tashin hankali a lokacin su a zatonsu komai yaya J zai mata sai gashi ya make hannu yace iya abinda zai bayar ke nan ya kuma basu don yanzu ta kanshi yakeyi shi. Ga buki sai karatowa yakeyi kamar yadda ko wani aure kan kankama har dangin ango sunzo sun kawo lefe a family house dinsu wanda mama ta koma can a lokacin aka tari lefen da ita . Tun wajen kawo lefen tsegumi ya fara ana fadin da gani yan kauyene don ba wata wayayya a cikin matan da sukazo din . Mijin kan na nunawa a cikin tsara saidai haline ba mai cewa ga halinsa tunda ganinsa akayi garin yanzo aiki kuma baifi shekara a garin ba suka hadu. A cewarshi itace ta biyu don haka ake fadawa kowa a ta biyu zata shiga gidanshi din ni dai ina gefe ban sa kaina ba kamar yadda ba a sani ba. Na dai sayi zanin gado masu kyau manya guda biyu a wajen anty salma wanda zan bada gudun mawana ga bukin har kuma sun iso a hannuna na aje. A wajen mama nake jin wai yaya j yaje kaduna don yar wajen Saiba da bata da lafiya yarinyar ta koma kamar sikila yanzu . Shine mama tace wai ya dawo da uwarta su dubata a gabanshi maman tudu ta dora da cewa kinga ke nan tana son ayi bukin yarta tana gidan ke nan ? Duk da naji wani iri a raina ban yarda na bar abin a zuciyana yadda zai dameni ba yima nayi kamar ban san wanan shirin da akeyi ba na sharesu muna dai zaune kamar yadda muke dasu duka har shi. Asmau cema suka kwasa dashi sosai da zancen ya fito cewa Saiba zata dawo gidan har sukai fada yace idan yayi niya ita bata isa ta hanashi ba . Wanan zancen kuma yazo min shima na nuna kamar banji ba saidai a wanan karon na kasa daure hakan tunda nima mutym ce mai jini a jika ai. Na danyi fushin hakan kuma ya fahinceni saidai tunda banyi mai magana ba shima ya shareni akan zancen ya nuna ba komai. Ranan daya dawo gidan muma ban bashi wani kulawa sosai ba kamar yadda na saba bashi abinci kafin ya dawo daga sallah na aje mai komai na koma dakina na kwanta. Ina jin motsinshi daya dawo ya zauna falo yana waya amma ban fito falon ba yanayi yana kallon kofana har ya gama yake tambayan Biba ke ina antyn ki take ? Tana daki uncle naji muryanta tana bashi amsa lafiya take kuwa ya tambaya yana mikewa naji tace in dai ba yanzu ba lafiya kalau take. Mikewa yayi ya shigo dakin ina kwance kasa da tasbaha a hannuna da nake ja ya tsaya daga kofa yana fadin yaya dai lafiya kike kuwa ? Na dago na bashi amsa a takaice kamar yadda Biba ta fada mai don ba halin karya gareni yanzu nace lafiya sai yabini da wani irin kallo na shareshi tunda na bashi amsan. To yaya abinci fa ya fada a inda yake din nace yana falo na aje ma yayi shiru kafin yace ba za a bani ba yau ke nan ko ? Nayi shiru can naji yace bakiji me nace bane kin kyaleni yana falo na ajema ai na fada kamar a hasale hakan yasa ya karaso yana fadin wai lafiya kike kuwa Rahama ? Lafiyata kalau nace maka ban dai jin tashine yau Allah ko yau ban samun gata ke nan nan ma ban bashi amsa ba na kyaleshi. Ya dan jima tsaye a kaina yana kare min kallo kafin ya gama nazarina ya tabbatar da lafiya din nake sai naji ya juya yana murmushi ya fita. Har yakai kofa yake fadin idan kin gama saiki taso ki ban abincin ban amsa mashi ba ya fice ina jinshi ya jima a wajen zaune naki tasowa in sameshi din. Saida na tabbatar daya gama ya shige na fito don kawar da kayan na kwashe zuwa kitchen a lokacin na farga da kamar bai taba kayan abincin ba kenan haka na nufin baici ba ko ? Na bude warmer din abincin naga bai taba ba nima na shareshi shiya sani tunda duk kyautatawan da nake mai bai gani yafi bukatan ya dawo da yar cin mutuncin matarshi azo a dora inda aka tsaya tunda ba barin halinta zatayi ba. Na juye abincin nasa a fridge don kada ya lalace na koma dakina na kwanta ban ko tayar da Biba tazo dakina mu kwanta ba yadda muka saba da ita idan baya gidan. Barci ko a ranan rabi da rabi nayisa don haka bai taba faruwa a tsakanin mu ba inba lokacin da baida lafiya din nan ba sai wanan karon. Washegarima ban lekashi ba bai fito ba har na kare abin karyawa na aje mai na koma daki nayi wanka na gyara jikina na kwanta ina jin biba ta gama gyaran gida har ta saka kamshi yana tashi na lumshe idona tagama shirinta zuwa school lokacin ta shigo dakina tana fadin anty nagama zan tafi. Hakan yasa na bude idona da sukai ja a lokacin don bacin rai dana sakawa kaina ina fadin ga kudin motarki nan dana kashi saman mirrow ta nufi wajen ta dauka. Da yake tayi wayau a yanzu harta dan juya zata fita sai kuma ta tsaya tana fadin anty lafiya kike kuwa ko jiya uncle yana tambayana da bai ganki ba nace ban jin dadin jikinane Biba tayi min sannu ta fita. Ina jinshi ya shirya ya fito ya leko dakina ina kwace saman lafiyayyen gadona daya sha gyara na harde kafa nayi makari da hannuna na rufe fuskana. Ya dan juma a tsaye kafin ya juya ya fita can naji karan motarshi ya tayar ya bar gidan na sauke ajiyan zuciya ina jan tsuki. A lokacin yadda nake jin haushinsa a zuciyana komai zai faru ya faru din tsakanun mu tunda ba kwanciyan hankali yake kauna bashi. In mama bata damu da kwanciyan hankalinshi ba aishi yasan abinda ke nan da zai biye mata don kawai taga farin cikin mu ya ragu a gidan. Tunda yanzu tana zaton rashin Saibane duk ya jawo mata wani matsalan da take ciki na rashin samun hankalin danta yadda take son ta mulkeshi. Sunce da Saiba tana nan wani abin dole yayi don dole ko yaushe yana gidan ai amma ita Asmau da ita da babu duk dayane a wajenshi tunda bata maida kanta abun kwarai ba a wajen kowa. Shigowan Aminu da yayine yazo ya tsaya daga kofa yana fadin mummy ina kwana yasa na fito falon na zauna a tare dashi yana karyawa yana ban labarin zirga zirgan da yakeyi don cika takardunshi a school din . Bayan Aminu ya gamane nan ma ban shiga daki ba nayi zaune a falon lokacin ya shigo Aminu ya gaidashi ya mike ya fita ni kuma nayi zaune ban dago kaina bama balle in gaida shi. Abinda yasa nake baki wanan labarin shine wani lokacin mu mata idan haka ya faru bamu tsayawa mu duba mu,amulan mu da namiji akan ai zancen bai shafemu ba shiya shafa makin mu kara kyautata hakan sai mu barar da daman mu daga wajen jan ajin da muke nema wajen miji din. Dakinsa ya shiga ya fito ina kallo bai taba abin karyawan dana aje mashi ba alama ya nuna shima ya hau dani lokacin ban kumayi dabaran yi mashi magana daya karya ba . Har ya fito saida yakai kofa ya juyo yana fadin shi zai shiga kaduna wani abu wani zafinsa na kara ji a zuciyana a yan kwanakin nan ya matsawa kaduna din nan sosai yana shiga lokaci lokaci ashe bikon matarshi yake zuwa yi na raya hakan a zuciyana bance dashi komai ba dai har ya fita. Ashe hakan yaci masa rai bai bar zaria ba saida yakai karana wajen maman tudu akan tayi min fada kan halin dana dauko mashi tunda abin bai shafeni ba a cewarshi. Matsalansuce shi da matanshi baiga abin da ya shafoni ciki ba tun nan mama tace dashi ya shafota takan malami tunda in haukan Nusaiba ya tashi kowa hadewa takeyi tayi dashi. Ita dai ta bari tunda bata da matsala da haka sin tana gidanta daban meye nata a ciki sun jima da mama kafin ya fito ya bar gidan zuwa inda zashin . Da rana tsaka saiga mama a gidan nayi mamakin zuwanta don in zasuzo aida safe suke zuwa yaya Auwal daya kawota tace dashi ya tafi idan ta gama zata hawo motan kasuwa ta dawo gida. Tun nan na gane akwai magana kuma gashi ita kadai tazo ba Nafisa dake rakota idan zatazo din na dai tareta yadda na saba na aje mata komai na koma kasa gefe muna gaisawa. A lokacin ta fara yi min maganan daya kawo ta din wajena wai yace baiso ya fadawa iyayyena tunda haka bai taba shiga tsakanin mu ba dashi. Mama ya fada mana sai me ko cikin nan da nake jira in haife yace ba zan haifa a gidan nan ba ina da wajen haihuwanshi ai. Ni dai ba zan shaganta abina ba tunda Allah ya sheda shi yayi min cikin wallahi ban taba zina ba balle kishiya ta kira min zina da aurena. Shiyasan abunda yake tsunta a wajenta har yake ganin a yanzu ya dace ya dawo da ita dakinta tazo taci gaba da aibanta min abinda zan haifa a gidan. Kukane yazo min da nake fadan hakan a lokacin da sauri mama tace tana farashi yadda ta kodu din nan bata farawa ai inane bataje kamun kafa ba don ya maidota dakinta. Anyi na malamai da bokaye baici ba yanzu ta koma na lalama ga yan uwa da abokan arziki har sukaciwo karfinsa ta yarinya yanzu ya yarda. Mama shi ya shafa cikin nan kawai ya tsayar dani gidan nan wallahi da ba zata sameni a gidan nan bama to a nan na sameshi nan zan haifeshi in wuce. Ke yar nan kada ki soma wanan gangancin da kike kokarinyi a yanzu don Allah ki wuce ki bar dan ko yar dawa hannunta ta kama maki ko me ita bagata ta dawo don yarta ba ? Sai kece da baki da mafadi zaki bar naki ki tafi a yadda na amsa kuma nakeyi tasan zan aika don sanin halin mu fulani da karfin hali da tayi. A,a Rahamatu kada ki hakan don Allah kina aon mijin ki yana sonki kada ki yarda fushin zuciya ya rudeki ga banza kan wata can da bata shiryawa aure ba. Sau nawa zan fada maki hakan ne ita fa abinda take nema taga ya samune a tsakanin yau ko wani shirin tayo a kanku nuna mata kinfi karfinta ke. Sai Allah ba boka ba malam kike lamarinki barsu badai dubu ta kafe sai ya dawo da ita a yanzu sukace ba to zai fita a tsakaninsu. Kusa ido kuyi kallo kawai indai dubu ce ita kuma itace kwana nawane za a fara jin tsakaninsu ? Nayi kuka sosai haka na nunawa mama din na hakkura amma itama ta fahinci da sauran zance a zuciyana saida tayi sallah la,asar na rakota zuwa titi nidasu Aminu muka daukar mata drop har gida na biya . Koda ya dawo gidanta ya fara zuwa take mayar mashi da yadda mukayi tace kasan halin fulani malam to kada kace zakaja zancen nan a bangareka don Allah ? Don yarinyar nan ta nuna min cewa haihuwan cikin nan na jikinta ya tsayar da ita tafiyanta zatayi ta barku . Har ya soma fadin ta tafi mana mama halan tare aka haifemu da ba zan iya rabuwa da ita ba ko an fada mata idan ta tafi rayuwana zai bar,,,,,,, Karka soma wallahi don ka yarda yarinyar nan ta subuce maka malam saika dawo ka raina kanka wallahi ana zama da mace don wasu abubuwa nata daga ciki da zan iya fada na farko ga yarinyar nan shine hakarci ko iya wanan kadai ya isheka shiga wani hali idan ta barka a yau din nan. To mama me nayiwa Rahama da zata dauki fushi dani haka in ma fadana da Asmaune takewa ai,bada ita nayi ba don me zata saka kanta a zancen mu ita. Yanzu dai na fadama yarinyar nan kasansu fulani da riko don haka kabi sannu idan ka yarda ta subucema kuma sai kayi nadama wallahi. Duk mutumin da zai zauna dakai tsakani da Allah shine abokin zama ba mutumin dake son ka a fatar baki ba kaidai kasan wanan yarinyar kaduna din komewa halinku zakuyi da ita ko yanzu. Ya dago ya dube mama din tace kwarai kaika yarda da tuban mazurun da tayine a yanzu ai hali zanen dutsene amma mama tayi alkawarin daina duk wani hali nata na baya za a zauna lafiya sosai da ita yanzu . Aifa ni yanzu bance kada ka dawo da matarka ba malam amma kada kayi saki reshe kama ganye a gidan ka tunda uwarka tace ka mayar da ita meye nawa yanzu a cikin hana hakan da zanyi. Da tun farkone wallahi malam zan hanaka ka dawo da yarinyar nan gidanka duk da nasan harkan aurene idan bai mutu ba ba mahalukin daya isa ya raba tsakanin ku yanzu ko mahaufiyarku ta riga da ta ciwo kanka ka yarda da hakan kaga idan na hana a yanzu Allah ba zai barni ba nima tunda uwa nake nima ga wasu yayan. Wa yan nan maganganu na mama tudu sun tsaya mai a zuciya don har sun sakashi wasi wasin a lokacin. Nayi abincin kamar yadda na saba amma a ranan ban aje a falo ba kamar kullum kitchen na barshi na koma daki na kwanta bai shigo gida ba sai bayan isha,i ya biya can gidan yayi masu saida safe. Ina jin shigowanshi amma ban fito ba har ya shiga daki ya dan jima a ciki ya watsa ruwa kafin ya fito ba zance maki yaya ya warke garau ba a yanzu. Har yanzu akwai sauran jin jiki a tare dashi idan ka sanshi a baya ka kalleshi yanzu kasan da sauran ciwo a jikinshi karfin hali yakeyi irin na dan adam mai tafiya da buri a tare dashi. Dakina ya nufo direct ya shigo sai kamshi yakeyi cikin dakewa da sanyin jiki yake fadin kwance ake ne kingani sai yanzu na dawo na biya can gidan nayi masu saida safene. A raina nace ai dole ka kai dare a can tunda an mannaka da bokaya ance mai kishiya bata mutuwar Allah haka zancen gizo bai wuce na koki ba ai. Jin bance komai ba yasa shi fadin banga abincina a falo ba mana ko yau baki iya girkawa bane kuma sai lokacin nayi magana nace. Naga ka daina cine yasa ban aje falo ba amma nayi girki tun dazun ai dan murmushi yayi cikin tsigan neman shiri a tsakanin mu yace kai Rahama kina dai son zance ni banga abin fushi a cikin zancen nan ba ? Nusaiba ce fa ba wata mace zan dauko wace baki sani ba kin riga da kinsan halinta saidai ban san abinda dan gulman naki yazo ya fada maki ba kika hau fushi haka. Wani dan gulma aini ba wawiya bace da wani zaizo ya zugani ni mutuncina da darajan abinda zan haifa na jawa tunda ita dabbama ya fita hankali. Taso kiban abinci don Allah tun safe dana fita ban karya ba har yanzu har ji nake kamar banda lafiya yau a jikina tunda an saba cika min ciki kwana biyu kuma anki kulani ? ZAINAB IDRIS MAKAWA [5/31, 05:44] Aisha Srtr Mt: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 9️⃣0️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Zance ya tabbata kuwa don Nusaiba dai Aminu ya fara fada min yana ganin kamar wanan dayan matar uncle fa ta dawo. Don yaga motoci da mata sun shigo sunata guda zuwa part dinsu a hakan kuma salima ta kiran ita da Asmau da yanzu tun bayan kiran da Asmau din tayi min muke dan gaisawa da ita sama sama don data kira cewa tayi dani. A Amarya Rahama dai kin sharemu gaba daya ko kizo gidan nan ki duba yaranki inmu ba dubamu ? Nace ban shareku ba anty gani nayi dai ya kamata naje gida na dawo kece yakamata ace kinzo kin duba jikina ai sai naga ba haka ba. Lalai kuwa anyi haka to amma ai kinsan halin gidan mu Rahama yanzu da anji nazo gidanki sai a fassara min abin da wani manufa ta daban shiya ban zo ba. Anty in baki zo ba saiki turo min yaran ba tayi dariya kafin tace to kinji dai mutumiyar mu zata dawo ko mama ta matsa wai ta dawo tunda dukkan mu bamu da amfani kanmu kawai muka sani mu sai yan uwan mu. Ikon Allah mudin to da wa zamu sani banyan kanmu da yan uwan mu dake kulamu wanda bai kaunanka ai kaima kayi nisa dashi ni ban damu wani yasoni ba bayan Allah. Son Allah kadai da Annabinsa nake nema sai mijina ban damu da son wani ko wata ba can don basu a gabana don Allah anty ki sa masu ido ki daina kula kowa da shirmensu neman bakinki sukeyi dama aji dadin bata labarin idan ta dawo. Ta dawo mana ba daina halinta zatayi ba ai saima abinda zai karu a yanzu don hakani dawowanta bai taba damuna ba anty ni kawai abinda nake so dake anty shine kiyi hakkuri don Allah. Ban dai daukeki makiyana ba don zama tare ya hadamu a yayata nake kallon ki har yanzu naji tana fadin wallahi nasani Rahama. To kiyi hakkuri abinda kika san baiso ki daina don Allah kema ki zage yadda kowa keyi a zama daidai ki fita batunsu kada ki biye mata yaran nan sunyi wayau a yanzu sun fara fahintar komai fa. Mun jima da ita muna magana har ina mamakin ko nawa ta saka a wayanta lokacin data dade haka tana magana dani din. Tun bayan haka muke gaisawa shine a ranan ta kirani take fada min zancen dawowan Saiba din ita ma na fahinci nufinta so take ta hada kai dani a yanzu ni kuma ba zan yarda da hakan ba hadin kai da kishiya cutane adaiyi zaman lafiya kawai kowa ya mutunta juna shike nan a zauna lafiya. Munyi hakan na kashe wayan tare da dimbin tunane a zuciyana a ranan yaya bai gari yayi tafiya amma ya kirani tunda safe yana sheda min cewa zai dawo a ranan . Don yanzu tafiyanshi ba irin na dadewan nan bane da yakeyi a baya iyankashi yayi kwana biyu ko ukku ya dawo gida. Duk da nasan tunda Nusaiba ta dawo bai garin don haka idan ya dawo a can zai sauka donshine ban matsawa kaina da mashi girki ba duk da nice da girki idan ya dawo din. Ashe wai hakan plan din Saratu ce na saiban ta tare a lokacin don su bata muna plan su hadani fada da yaya don dole sun san in anyi hakan zamu samu matsala a tsakanin mu dani dashi. Tun yana can ya samu labarin dawowanta din don suna waya yake jin hayaniya yake tambayan tana ina tace zaria dakinta don ta dawo tun jiya daga haka baice komai ba. Koda ya dawo din kuma gidana yayo direct ana ruwan sama a lokacin muna daki nida Biba dake zaune tana assignment ya shigo ita naji tana fadin uncle ya dawo. Jin hakan yasa nace ina take fadin taji muryanshi a falo kafin nayi wani magana sai gashi a dakin nawa yana fadin nakan fada maku idan kun shiga ku dinga kula da rufe gida. Kasan nan yanzu ba wani sequrity kwarai a yanzu Aminu muke jira ya shigo ya dauki abincinsa na bashi amsa. Idan yazo ya kwankwasa mana ko a aje mashi daga waje ana ruwan nan sai mugu yayi amfani da daman yazo ya cuta maku a raina nace cuta yafi naku kuma ? Na dan dago nayi mai sannu da zuwa ya amsa yana fadin ya kuke Alhamdullahi na fada a cikin basarwa ya juya ya fita mai karatu har zuwa lokacin ba wani sakewa a tsakanina dashi irin baya qda muka dan shaki yanzu duk na daina hakan duk da shawaran da mutane ke ban wai yana sona don haka kada in nuna abin ya dameni a bamgarena. Dole in nuna don yiwa dan cikina gata baka sanin halin mutum ka zauna ya shanmaceka nasan waye Saiba da Saratu hakama mama da danta. Don haka ban sanyaya a wanan zance ba gaba daya na kara dagula mashi lissafi idan ya dauka ni ruwan sanyice zan nuna mashi kalan tafasana a yanzu. Bafulatana fa nake ta asali ba muna fulani ba zuciya gadan shi mukayi a jinin mu yake ba ara min akayi ba idan kayi min sai nayima don bamu yafiya kona kara balle na fili. Ki tashi idan ya fita saiki rufe kofan nacewa Biba daga inda nake kwance jin hakan yasa ya dan juyo yana fadin idan na fita ina ? Nina rufe kofan aidana shigo ko Aminu din bai dauki abincinsa bane baya gidanne har wanan lokacin biba data mike don barin dakin take fadin ina ganin yana nan don da aka fara yayyafi yana falo yana cin abincinsa. Tana fita shima ya fita hakan yasa na mike zuwa kitchen na shirya mai abinci na kawo falo na dauko ruwa na samu ya fito yana waya naji yana fadin na dawo mana tun dazun ina nan gidan wajen Rahama. Yadda ya tsaya sauraren wayar yasa nasan maishi na koro mashi zancene a ciki na juya naji yana fadin mama wanan kuma ra,ayinane fa bansan da dawowanta a jiya bani ? Kai kai kai su mama dubu dai anga lagwai da tsohuwar nan nada ikon kasheni na tabbatar data halakani ta gama a duniyan nan. Yanzu uwace ke fada da danta haka akan matarsa a fahintana sunyi mai bazata shima ya mayar masu da hakan idan Saiba ta dawo a ranan girkina don su nuna min isa to Allah ya hau dani kansu ga baki daya yanzu. Da wayan yayi yawa bayan ya kashe aka kara kira naga ya dauka yana fadin na dawo ina gidan Rahama. Karshema yaja tsuki ya kashe wayan tashi baki daya ya aje gefe daya yacigaba da cin abincinsa ba dai wani hiran da mukeyi na zauna ya gama in kwashe kayan a wajen. Ina zaune kamar ban fahinci meke faruwa ba a lokacin har ya gama na kwashe kayan bance dashi uffan ba shima haka baiyi magana ba. Na fito kitchen yake fadin maganina fa da ruwan addu,an da kike ban ban hada ba na bashi amsa na shige daki na barshi a falon zaune . Kayan kwanciya na sauya a jikina na kwanta can dare wajajen sha biyu da rabi barci ya soma daukana sai gashi a dakin yana tayar dani. A cikin idon barci na bude ido na sauke a kanshi yana tsaye kaina saye da farar jallabiyansa mai dan hannu yake fadin wai meye haka Rahama kinfa san ina jiran ki kinzo nan kin kwanta kuma ? Ido na mayar na lumshe kamar ban san yana tsaye a wajen ba sai jinsa nayi ya fita daga dakin na soma barci ya dawo ya kwanta a bayana don jaraban maza daya motsa mai ya kasa rike fushinsa da yakeyi dani ko dai wani abu. Washegari da safe har muka zauna karyawa bai kunna wayansa ba saida ya fito ya zauna naga yana kunna wayan kamar ana jiransa a lokacin kira ya shigo. Tarr naji me take fada lokacin don kusa dashi nake zaune lokacin saibace take fadin ba sai ka nuna min kafi jin dadin abu kazan yar fulani ba zakai min haka. Yace ashe kin sani to tunda kin sani kisan matsayinki yanzu kada ki hada kanki da ita don ita din ba tsaran yinki bace look Saiba mena fada maki game da yarinyar nan kafin in yarda ki dawo ? To udan bakiji ba kada kiyi mamaki yau din nan ki kwana gidanku na har abada ba dai kinga na kyaleku ba kada ki dauka bokan da kike bine aikinsa yaci a kaina karr nake kallon ku wallahi. To in kwana mana sai me dama ban saba kwana bane a gidan namu wallahi akan wanan yar dajin matar taka ba zakai min wullakanci in kyaleka ba Jafar. Tunda banga abinda tafini dashi ba da zan dawo ka dauki kwanana kakai mata don ita tafi ko wace mace a idonka yanzu kome ?. Kwanafa kikace gashi kin ba kanki amsa tafiki komai ke nan ashe kin gane hakan keda kukace zaki dawo ki zauna zaman yarki ina ruwanki da kwanan da nakeyi da matana yanzu kuma ? Zaka dawo gidan ai ta fada a hasale kamar wace idan ya koma zata dukeshi a ranan ta kashe waya yaja tsuki ya dauki plate din abincin dake gabanshi yana fadin mahaukaciya kawai wanan ba zata taba canzawa ba tayi hankali ba wallahi. Wacece na samu kaina da tambayar karya tankar banji me sukeyi a wayan ba da ita ya dan kawar da kai kafin ya ban amsa da Nusaibace mana mahaukaciyar banza da wofi. Naja bakina nayi shiru don ba abinda ya shafeni bane zancen har ya gama kamar kurame haka muka zaune a wajen ba wanda ya kara magana a cikon mu. Saida ya dan jima ya mike yana fadin bari na leka gidan in dawo ina yaron ki yakene nace ya fita school tunda safe ok yana da lectures ke nan ko ? Ban tsaya bashi amsa ba don zuciyana dake famam sake sake a lokacin ko don wanan mahaukaciyar zan daure in biye masa mu kara haukatata kafin nasan abinyi. Lokacin kuma na fahinci dole akwai wata a kasa cikin zancen dawowanta gidan dole a kaina ta dawo ko wani abu amma yadda naji magananta haka a tsaye bawai irin na wacce tayi nadama bace gaskiya. Koda ya isa gidan ya samu mama ta hau ta cika don me yayiwa matarshi haka da wanan zancen ta tareshi da fada ga matarshi ta dawo don ya nuna masu iyakarsu yaje gidan wata ya kwana ya barta nan ? Amma dai mama gidan matana na kwana ko da zata dawo wa kuka fadawa dawowanta ga shekaran jiya din ? So tunda banda amfani ga da zata sanar min zata dawo ai gara inje inda akasan darajana ko kai ji nan malam naga yarinyar nan gaba daya ta juyema kai to ka natsu kasan abinda kakeyi yanzu. Rahamace zata juye min kai kuma mama ya tambaya fuskanshi dauke da murmushin mamaki ga maganan mahaifiyar nasa. Inda mama din tace ba dole ince haka ba tunda kai baka san me kakeyi ba ta ina ka taba jin anyi hakan itama inba makira bace ai tana da labarin matarka ta dawo data karbe ka . Ina ruwanta da zancen dawowan Nusaiba mama tunda ba a unguwar nan take ba ina zata sani koma dai ta sani ko bata sani ba dai tunda tasa kayiwa wata wullakanci itama ta saurarinata ai yana tafe. Mama wai meyasa kike saka kanki cikin irin shirmen nan bafa dake ake zancen nan ba banga abinda zaisa kina saka kanki irin wanan maganan ba girman ki na zubewa ? Ooh yanzu don na tsaya gyaran gidanka shine girmana ke zubewa malam to ya tude karshen zubewa ke nan badai ga yar gwal din matarka zai zube ba kawai to aida sauki tunda iya nan zai zube din. Mikewa yayi yana tambaya iya tana can bangaren ne har yanzu salima ya samu ta amsa mai da tana can yau ta tashi bata jin dadin jikinta tun jiya. Subbahanallahi ya fada ya dakata yana tambayan ta meke damun iya din take fadin gudawa tayi sai jikinta ya mutu . Shine baku kaita asibiti ba mama kuka barta a gida haka amma haka baiyi ba wallahi ya fada ya fita da sauri zuwa part din da iyan ke ciki. A kwance ya samu tsohuwar cikin wani hali na ban tausayi da sauri ya kamota zuwa asibiti shida salima da mama din akaje asibitin dole aka kwantar da ita aka saka mata ruwa. Lokacin ya kira yazid a waya ya haushi da fada kan rashin kula tsohuwar da baiyi ba kuma yana gari fada sosai yayi da kanin nasa yana bashi hakkuri. Sai lokacin jikin mama yayi sanyi ta shiga kame kame tana fadin wallahi na dauka irin yadda yakan dan bugeta ta mikene kawai. Mama bidon Allah yayi iya da tsawon rai mai lafiya ba jikin iya a yanzu ba komai zaku bata taci ba ya kamata ace ana duba irin abincin da zataci tunda tana da gatan hakan a yanzu. Ya bugo min waya a gabansu yana fadin in shirya abinci gasu nan asibiti da iya an basu gado hankalina ya daga anyi dace nagama abincin rana ke nan na kwashe na cika kula Aminu yakai masu. Wanan ciwon na iya ya kwantar da fitinan da akaso tayar mashi wanda shima a hake yake dasu ashe kan hakan da dare tare mukaje dashi duba jikin iya din don yazid ya kawo wa yancan da zaizo da matarshi sun duba iya din. Akwai haske tar a lokacin duk da shigana ba wani shiga nayi ba a lokacin amma hakan ya tsonewa mama da iyalinta idanu . Duk dago kai zanyi zan samu dayansu yana satan kallona a cikinsu bamu jima ba ya soma fadin wa zai kwana a nan din nida Dubu zamu kwana Hafsatun kawu ta fada. A,a mama ki koma gida abar mama ta kwana don ko maman tudu taso tazo ta kwana sukace basu son mutane da yawa a nan din. Da dai ka barmu mun kwana mu biyu din tunda ba a san me dare zaiyi ba a hankali na fara takawa don barin dakin cike da mamakin hali irin na mama din . Ke nan tana nufin jinyar mahaifiyarta sai wani ya saka mata hannu a cikinsa bayan tasan ba shiri bane a tsakaninsu ko banza. Ya jima a tsaye kan iya ya dago yana fadin bari nakai yarinyar can gida indawo bai tsaya ba ya fito zuwa wajena ina tsaye na dafa mota ya iso yana fadin muje ko ? Saida muka soma hanya nake tambaya yaushe iya ta soma ciwo duk ta rame haka yace waya sani ko yanzu ai salimace dana shiga take fada min da haka zata halaka a daki ita kadai. Daga asibiti idan an sallamota nan gidan zan kawo maki ita don ta samu kula mai kyau don Allah ace abar tsoho da yunwa ga tsufa ga ciwo sai lokacin da akaga dama za a bata abin karyawa taci ? Ni dai banyi magana ba har muka isa gida duk abinda zan fada idan ba zagin mahaifiyarsa zanyi a gabansa ba me zance don laifin duk natane game da hakan gaskiyaa. Tunda ya dawo bai koma ba kamar yadda yace don har mama ta bugo waya wai in zai dawo yazo masu da ruwan zafi a flask. Yace gaskiya ba zai samu dawo ba don har ya kwanta saboda yana jin rashi dadin jikinsa. Hakan yasa tayi fushi ta fara zage zage tana fadin Jafaru baida ta ido akan wanan yarinyar don in yana gabanta tankar yana gaban Allahnshi ne Haba dai dubu kada kice hakan kawai dai zuciyace take kaunan mai kyautata mata duba ga irin kokarin yarinyar nan gareshi ba tsoro bane hakan kyautatawace kawai a tsakaninsu. Kin dai tsani yarce har baki ganin kirkinta a yanzu amma ai tayi kokarin da ba kowa zai daure yayisa ba kinga ko dole yaso abarshi a yanzu yadda tayi fama din nan a baya kanshi Na kula kema hafsatu a yanzu kamar kin fara shakku da tsoron yar nan koda yake ba laifinki bane koda kinyi hakan don kanki kikewa yaki hakana din. Kwanan iya biyu ta samu lafiya kamar yadda yace yaso ya wuto da ita gidan mu sai iyan tace dashi a bari agama bukin Saratu in muna raye sai tazo ta zauna dani har in haihu shiyasa yayi na,am da hakan ya barta. Sun fara shirin buki gadan gadan har lokacin ana neman abinda ake nema din na wasu abubuwa ga yan uwan duk kowa yaja bakin aljihunsa ya tsuke yana kallo. Shine mai saukin da suke saka ran zai fitar dasu kunya shi kuma din ya nuna yanzu Habu ma ya fishi karfi don dukiyanshi da aka wawashe yana kwance bai gane komai ba. Ga karyan da take sonyi ta burge mutane a wajen bukin nata ba abinda ya kamkama daga wajenta shima angon ta rasa gane kanshi a yanzu datayi magana zaice ba kudi bai son karya a sha,ani. Tana sonshi kamar me don haka saita kyale ta kasa tambayansa komai abu yayi yawa ya taru masu lokaci guda. ZAINAB IDRIS MAKAWA [6/1, 21:12] Aisha Srtr Mt: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 9️⃣1️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Banda niyar zuwa ko wani event a cikin sha,anin bukin donshi ko gyaran jiki ban tsaya nayi ba amma da nayi tunanen kada ai min girshi naje amin kumshi da kitso da gyaran jiki don haka a wahalce na wuni a ranan. Yana can gidan da ake jiransa bayan yayi min kwana biyuna da zaiyi gidan sannan ya koma can gidan don haka an fara sha,anin bukin yana gidan nasu a karshene zai dawo gidana har a daura aure yana gidan. Duk da iya ta dawo gida daga asibiti amma bamu daina saka mata abinci daga nan ana kai mata ba don surfan tsufa tace abincina kawai take iya ci hakan yasa na dage ina girkawa da ita ko yaushe. Kwance nake ina barcin gajiya lokacin da maman tudu ta bugo min waya da basu ganni gidan wajen taro ba na rasa abinda zance mata karshe dai na fito fili na fada mata gaskiya cewa ina gudun fitina yasa na zauna gida. Kada ki hakan yar uwar mijinkice fa ko meye ki shiga koda ba duka ba ki daije a ganki yafi kice kin zauna gida baki tafi ba ba zaiji dadin hakan da kike nufin yi ba gaskiya. Nayi mata godiya barcin da ban koma ba ke nan a lokacin tunda ranan kamune don haka zanje da yamma ayi kamun dani ke nan sunsa a kofan gidansu na cikin gari za a hadu zuwa dan wani wajen event a unguwar. A makare naje wajen don ban fita ba saida na gama har abincin dare don gudun yamma na fito shiya turo da motarshi aka daukemu na samu a cika wajen sosai amma ana ganin zuwan duk wanda yazo taron a yadda tsarin wajen yake. Aminu ne ya jawoni zuwa wajen don haka ya shiga dani sosai inda za a ga fitowana daga motan ya tsaya kafin na saka kafa na fito a hankali. Tankar ba ciki a jikina irin kwaliyan dana caba duk da nauyin cikin da nake ji yana hanani sukuni wanan ban yarda na biyewa hakan ba na lalace don ban bari an barni baya ba gaskiya. Yar uwar Asmauce ta fara tabata tana nuna matani kafin saiba ta farga da abinda suke kallo a wajen. Nida Biba munsha kwaliyan mu muna fita ya juya ya nemi waje yayi packing a can nisa kadan da wajen nan gulma ya dan fara tashi ga matan dake wajen wasu na magana da nice amaryan jafar ai. Wasu kuma suna zance akan cikin jikina yadda na sameshi a cikin jinya yayin da wasu ke fadin yanzu ya fisheni daban a cikin matansa nice ke yadda naga dama a gidan. Kamar Aminu ya sani yana fitowa ya kawo min key din motan ya mika min don yaron akwaishi da gudun zuciya sosai bai yarda ace yayi laifi ta bangaren kawun nasa yana da taka tsantsan sosai wallahi. Sai a wanan wajen muka hadu da mahaifiyarshi ya fada min tazo kwana ukku ke nan a lokacin don haka ta taso daga inda take zaune muka gaisa a cikin mutunci da ita. Wanda nasan ba komai bane yaron nata ya fada mata yadda muke zaune dasu a gidan ya kawo hakan a yanzu. Salimace ta taso ta kamani tana min sheri wai ciki ya boyeni ya hanani shiga mutane koda yake ita ai kyau taga cikin ya kara min na dan harareta ina murmushi. Wajen zama ta sama min daga inda yan gidan suke ban zauna ba saida nabi matan yayyunshi su yaya Auwal na gaidasu na dawo na zauna. Nida biba muna kallon abinda akeyi a wajen hango yar uwata da nayine yasa na kara mikewa zuwa wajenta muka gaisa take fadin yanzu take cewa idan bata ganni ba saita biya ta gidan mu ta dubani. Share zancen nayi na basar ina fadin ina yaran tace suna gidan makwaciyarta ta barsu duk a cikin filanci muke maganan da ita lokacin. Na hango Saiba a cikin wani dogon riga tana kai kawo a wajen taron kafin can na hango tana magana da Aminu sai naga ya nuna matani tana magana kamar da tsawa dashi. Wai ashe cewa tayi ya bata key din mota zasuje wani waje su dauko abu yace makullin yana hannuna kuma uncle yace kada abawa kowa motanshi bayan ni. Shine take fada kamar ya yace kada a bawa kowa motarshi ita din tafimune data shiga sai gashi yazo yace in bashi key inji saiba yake mayar min dame tace nace ta kira mai motan ta fada mashi sannan na bata key din. A shirye nake dasu nasan hakan plan ne yasa ban bata key din kai tsaye ba da ace akwai girma da arziki a tsakanin mu sai in bata key din ai kayan mijintane itama . Amma dana fahincesu saina hana key din yaron ya juya ya koma yana fada mata abinda nace game da amsan key din a wajena. Fisge fisge ta soma tana nunani ana riketa daga wajen muna tsaye maria na fadin kai Rahama ki mike mata mana kafin ta tara maki mutane a nan. Ba zan bata ba don ba ita ta ban ba wasa wasa sai gashi an taru a kanta tana ta zage zage wayana dake vibration na dauko a jakkata shine akan layi na dauka a fusace sai naji yana fadin. Kina inane ke nace wajen buki mana yace ance saiba na fada dake a wajen don kin hanata key din mota ? Au dani take nidai naga tana fisge fisge na zata iska ta hau ai look kada ki yarda kibawa kowa key din nan idan abin baiyi ku dawo gida kawai don Allah ? Na zata kin biye mata don ba hankaline da itaba bata duba condition dinki saboda hauka na cika masu motan da suke amfani dashi tun shekaran jiya yau kuma na basu kudi su kara mai a cikin motar. Don tana mara mutunci hakan bai mata ba saita karbi key a hannunki don kishin tsiya zata gamu dani wallahi dif na kashe wayan ina fadin banjin ka yaya. Munafuncin maza kawai ai baka fada min kayi masu hakan ba sai yanzu nuna min yayi naje da motarshi kada in hau motar haya zuwa wajen kawai kuma mu kula mai da mota kada in yarda inbayar mashi da motanshi ga kowa. Sai kawai mukaga fada ya koma da salima ga saiba can da nata nan kuma ana fada da salima abin ya bamu mamaki matan yayyunsu suka shiga fadan salima din ana ta cacam baki a wajen. Bamu san meke gudana ba acan din don muna da dan nusa dasu matar yazid da aka fara fitinan tazo ta samemu muna tare harda ita. Saida wata kanwarsu yaya matar aurece ita tazo tana fadin bafulata kin yamutsa wajefa da fitina ga amarya can na fada dake wai zuwanki taron nan bai mata rana ba ya bata mata buki. Kishiyarki na fada a dake a barta tazo ta dukeki ana riketa can, nan kuma suna zaginki da mijinku ashe salima tana wajen ta basu amsa shine shine abinya zama fitina ya barke a tsakaninsu har ana batun bawa hammta iska a tsakaninsu. Muryan maria naji a hasale tana fadin Au haka tace ashe, bamu ko sani ba ai ba zata kara ganin mu ba ai kuwa, koda Rahama tazo wajen nan ba wanda yaji bakinta da wata, Ta daiyi da wace ta tayar mata da fitina don itace ta bata mata bukinta ba Rahama ba watau Rahama itace marainiyar tako ? Mariyace ke fadin haka a hasale taci gaba da fadin tun zuwana naga saratu na harare harare a wajen nan, sai sun san dai wanda ya bata masu sha,anin bukinsu don ba Rahama ba dai kam. Dani da mariya din da matar yazid muka bar wajen bukin a ranan ne kuma rana ta farko dana fara jan mota a garin zaria don ko biba ban tsaya nema ba tunda tana tare da yan gidansu Aminu kuma ya bace a wajen taron. Saida na saukesu gida na nufo nawa gidan kai tsaye yayi kiran wayana ban daga ba saboda hayaniya banko ji kiran ba a lokacin yasa ya nemi Aminu . Aminu din ya kirashi yana sheda mashi na bar wajen bukin da dadewa kodaya dawo gida ni ya sameni gidan abinda ya fara tambaya shine waya jawoki zuwa gida ? Nina jawo kaina mana na bashi amsa ya tsaya yana min kallon mamaki baiyi magana ba ya nufi dakinshi kai tsaye don a gidan yake sai daya gama ya fito ya fita zuwa massalaci sallah magariba da isha,i. Ya dawo ina dakina jin shigowanshi gidan yasa na fito daga dakin ina gaidashi abinci na dauko na kawo mashi falo inda yake zaune yana waya. Ya harde kafafuwansa a waje daya a mike yana dan jujuyasu yake wayan yana fadin shi gaskiya yasan dama za ai haka ai wallahi ya fada mata tabar mashi gidansa tunda bataji meyace da ita kafin ta dawo ba. Ai ya fada mata datayi kuskuren akan yarinyat nan tace zatayi mata rashin mutunci ba zai kyaleta ba saurare naji ya tsayayi kafin yace shin mama ana aure dolene ? Ni dai na kawo yarinyar nan gidan nan yanzu kuma nace ta tafi gidansu tunda basu da mutunci itafa ta rokeni motan nan banyi mussu ba nax bata key harda kudin mai da zasuyi jigila dashi. Don naba Rahama tawa motan Aminu ya kaisu abinda zatajeyi shine kuma zai zama jidali a wajenta yanzu a bainan jama,a har ana kamata tana barin a bari taje ta duketa. Watau bata damu da halin da zara iya shiga ba ko ba ruwanta da cikin jikinta ke nan ita idan an barta da Rahaman badon ciki ba me zata diba a wajenta ? Saurare ya somayi na dan lokaci kafin naji yana fadin dole inyi fada mama cikine jikin yarinyar nan fa mama idan tayi mata illa fa hajan bai shafeni ba ke nan ? Sai in tsaya tayiwa yarinyar mutane illa tunda ta kudurta hakan a ranta Rahama bata taba damuwa dame nake masu ba ita dion banyi mata ba itayi fushi Kuma ta sani tasan ina masu ai ko ita ba mutum bace koba aurenta nakeyi bane itama akwai wanda yakai nusaiba wahal dani a cikinsune mama ? To wallahi ki fada mata duk ta kuskura takai hannu a kan wanan yarinyar again na barta har abada ke nan a rayuwana tunda ita mutumiyar banzane na fahinci hakan sosai yanzu. Tana magana bai tsaya saurara mata ba yacigaba da fada karshema ya kashe wayanshi yana huci ya ja plate din abinci zuwa gabanshi. Yau da ace ina yawan korafi akan abubuwan da nake gani kansu ashe da ban samu wanan shedan ba daga bakinsa a yanzu ? Ashe yasan nasam komai nunawane banyi a gabanshi sai in nuna komai banji ba akan harkanshi da matanshi koda sun bugo mashi waya a yana gidana ban yarda na taba nuna mashi kishin da nake ji kan hakan ba a fili. Saida yayi cibi kamar biyu zuwa ukku naji muryanshi yana fadin yaushe kika iya motane ke ban sani ba ? Ajiyan zuciya na sauke kafin nace dashi ya jima mana tun ban aureka ba na iya mota lokacin da nake zuwa Abuja hutu anty salma tasa aka koya min driving. Lalai kin kai bafulatanan asali Rahama amma baki taba nuna min kin iya ba har nake zancen a dinga koya maki keda wa yancan kafin Allah ya hore min in sayawa kowa nata ? To idan na nuna meye faninshi yanzu ai gashi daya kama ka sani kasani din ai, kuma don Allah kabar sa kanka a cikin zancen mu da matanka don hakan yana kara min bakin jini a wajen yan uwanka na saya zancen bance mama ba nace yan uwanshi. Rahama kada in magana ta illantaki don ana tsoronta ita din me har waye Nusaiba yar iskan banza kawai dama haka mama ke son gani yasa ta takura min sai in dawo da ita. A zatonsu idan ta dawo zata kwatar masu wani abu dayafi wanda nayi masu a yanzu a wajena kyalesu nayi naga plan din nasu basu san waye Nusaiba ba har suke tunanen hakan a wajenta. Yarinyar da bata son taga duniya naiwa wani alheri koda kuwa ita mamane da kanta har inta sani sai mun samu matsala da ita ta nuna nata iyayyen fa don wauta ? Wai ita suke sa ran tayi masu abinda ban tashi yi akansu ba yanzu kyalesu daga su har ita jira nake ya fito a tsakaninsu ai wanan kan dole inyi mata kashedi a kansa tunda bake kadai bace. Nasan aiba zata iyaki ba tunda sun gwada syn gani yanzu so take tayiwa cikin jikinki rauni a fahintana shiysa take nemam jidali dake. Tayi da wani ai nibama zan koma zuwa wajen bukin ba balle ace ga kuma laifina wanda naje din nan ya isa hakana kuma. Abinda nayi niya bayarwa zanbawa Aminu yakai masu shike nan a zauna lafiya tunda basu son ganina a sha,aninsu. Saboda me ba zaki ba gidantane ko bukin yar uwarta akeyi da zakice ba zaki ba zaki tafi in takai yar iska ta kara tankawa a kanki kuma ? Ai baki san Nusaiba bace tayi hakane kawai ta baki tsoro amma komai bata iyawa na gaya maki ita Asmauce har yanzu bata fahinceta ba. A,a mai bukin tace munzo da yar uwata zamu bata masu sha,aninsu suna bukinsu a cikin dadin rai zuwan mu yasa muna son bata mata buki ? Ita Saratun tace hakana har wani buki bukin da suka sawa kansu karya a kanshi daga ita har mijin bar yar iska karya yazo ya shimfida masu suka hau suna hauka. Daga ita har mama kallonsu nakeyi itace fa a matsayin ta hudu matansa ukku itace yanzu ta hudunshi sai taje ido ya raina fata irin gidan nan ne kuma family house zai kaita. Musu kai kaya ai suna can yaya Ai ta kirani dazun nan tana sheda min sunje sunga abu na daban ba abinda aka fada masu bane ko kayan basu shiga dakin da aka nuna masu ba a matsayin nata yanzu suna can dai ai na kirasho yace wai bai gama ginansa bane kiji makaryaci hakan ne daidai da ita yar iska dama sai mai karya irinsa zai iya kwasanta ai suje can su karata dashi tunda mutumiyar banzace ita. Wai yaya tana cewa ko za a kama mata haya ni zan kama masu haya ya zauna da matarshi ke nan duk shekara inbiya ko ? Shi habibin ashe makaryacine don haka take kiransa da habibi kowa dashi ya sanshi a fanninta. Ya amsa yace babba kuwa aini da ganinsa nasan mutumin banzane yanayinsa kadai ya nuna min hakan a kanshi makaryacine yace shine manager a bankin ashe karyane. Haka akace mana manager ne na bankin manoma ta kasa karya yakeyi ya fada yana mikewa yace tadaiyi auren shine burin mu a yanzu. Sai banji dadin hakan ba don za ayi a dawo ana da an sanine a karshe naja bakina nayi shiru ban sake uffan ba akan zancen shima kuma ya fada min ne don yasan ba za a taba jin zancen a bakina ba indai nice. Can gidan kuma ashe labari yazo masu daga yan jere irin abinda sukaje suka sama a gidan hakan yasa hankulansu ya tashi ita kuma wawiya bata yarda ba wai ai yace dama bai gama gina inda zasu zauna ba. Shiyasa yaso a daga auren amma su yaya Auwal sukaki yarda da hakan sukace ayi haka dai a wuce wajen. Karshe dai dole kowa yayi shiru amma mama hankalinta bai kwanta da irin yadda ina hafsatu ta labarta mata komai ba har matanshi da yaransa da suka gani. Hakan yasa ta kirashi take kara fada mata ina shiga dakin naji yana fadin to yanzu mama ko hakan gaskiyane yaya zamuyi tunda ita tace tana sonshi . Hakkuri za ayi da fatan zaman lafiya su sauran matan da suke zaune dashi ai basu mutu ba ka saurareni malam wanan zance abin a dubane tun yanzu. Mama ba rawan kanta ya kaita ba koma yaya abin yake ai dole dai hakkuri za ayi yanzu tunda ba za a fasa auren ba. Ya kashe waya don tunda na shigo na fahinci da ita yake waya na juya zan fice daga dakin yayi min hannu dana dakata kar in tafi na dawo na zauna don banda jimirin tsayi a lokacin. Mama ke nan ta fahinci inda saratu takai kanta hankalinta ya daga a yanzu shine suke ganin laifin mutane kan anki kara kudi ayi karya niko ko a jikina don ita ta kanta ta nace sai shi a barta taje ta gani ai yanzu. Nima wallahi na damu irin hakan babu dadi ai maka karya sai kaje ka samu ba haka abin yake ba kuma babu yadda zakayi an riga da anyi din. Sherintane yake shirin cita shiyasa ake son bawa da tsarkake zuciyarsa akan kowa nan tace dake ai tana yarinya karama ba kwadayin da zai jata ya kaita auren mai mata koda gudane ? To, gashi yanzu ita bako mai mata daya ta aura ba mai mata har ukku itace ta hudu kinga Allah ya ceceta da irin rayuwan abokan zamanki na kazanta kuma. Ai, Ba,a kula irinsu anty saratu yaya ni harga Allah ta ban tausayi wallahi don babu walwala ko jin dadi dai a gareta yanzu gidan yawa ai fitinane babba ya tunkaro ta. Aita iya makirci sai su saje dasu suyi tayi niko a jikina na jima da sallama lamarin yarinyar nan a rayuwana tun lokacin da tace da kudin gadon mu nake aure na sallama lamarinta. Haba dai kai babbane hakkuri za kayi bata da wani gatan daya wuce ku a yanzu ai ko yanzu kuma ta fahinci kai ba irin mutanen nan bane tunda kai mata komai a rayuwa. Ke kika fahinci hakan ita ai fushi takeyi dani daga ita har mama na kuma rantse a yanzu dai ban kara mata komai saita gane kurenta . Gara dai dakace sai gaba don duk yadda akayi saika saka hannu a wani abin shi dan uwa ai MURFIN JALLO NE don ko wakake a duniya wata rana sai dan uwa ya taimake ka. Rahama mu bar zancen nan idan munci gaba kina tuna min abubuwa akan yarinyar nan yarinyar data dafa min mugun ciwon da kowa yake gudu a duniya wani murfi take gareni a rayuwa ? Shiru nayi ban kara cewa komai ba washe gari tunda safe yasa kai ya fita gidan nasan hakan nada nasaban kiran da mama din take ta mashi tunda dare yaki daga wayan. Wani abu sai mahaifa don kuwa ko yaya ranka ya baci da hukuncinsu dole kai hakkuri idan kana neman rahaman ubangiji. Saratu dai tun bata yarda da zancen da ake fadi ba har ta soma yarda gashi washe gari daurin aure saida maza suka nuna ikonsu akan mama ta yarda ta amince aka daura aure a washegari. Duk cikin sarakan mama mu biyar ni kadaice na bada gudun mawa a harkan bukin aiko yaya barakha tana ta yabawa tana fadin kin gani ko ita da nasu baizo daya ba da saratun itace ma ta bada abin arziki. Aini tuni na gano yarinyar arzikine na daina biyewa zugin mutane akan zancen duniya ba dole ki daina ba tunda tana ma danki rikon munafunci a yanzu ? Komai zaki fada kan wanan yarinyar wajen malam da mukaje dazun cewa yayi hannu akasa aka dambala mijin don ba haka yayi niya ba da farko ? Haba mama don malam yace ansa hannu sai ace kuma Rahamace tasa mata hannu yanzu don Allah me ta tsare mata inma hannune ai saidai tayi wanda zata tafi ta zauna dakinta har abada. Don Allah mama a yanzu ya kamata ki rage irin wanan magana na malamai shekaru fa sunja mama ke in kin fada ai ba za aga laifinki ba ni wanan halin wallahi yana damuna sosai komai ace a je wajen malam ba a barwa Allah lamatin komai yanzu gidan nan. Can Saratu ta dauki mama sukaje wajen malaminsu da Nusaiba yace wai sai Nusaiba ta dawo abubuwa zasu kamkama ga zance kasan hadin bakine amma mama ta yarda da shirmensu. Salima ke fadin hakan aiko mama tayo cikinta da zagi na bacin rai tana batun tsine mata saida anty barakha ta kare tana fadin nikan mama zan kira Jafar yazo kan zancen tunda banga abin zagi ba a nan ? Ai gaskiya salima ta fadi ni yanzu na gane malaman nan macutane wallahi don suci kudinta sai su kakaro karya su sharawa mutum don hankalinsa ya tashi a banza. Haka dai akai komai har daurin aure ba tare da sun samu yadda suke so ba din salima kuma tunda ta fita har ranan buki bata leko part din ba tana wajen iya zaune har yan kai amarya suka wuce da amarya bata fito ba. Anje dasu yaya barakha da maman tudu sai mama hafsatu matar kawu wace zuwanta din yaso ya jawo matsala tunda taje wajen jere don kawu yace amayarsane zata kai amarya. Su yaya suka tsaya sukace da inna hafsatu za a dole ya kyale ya bari ta tafi mutum biyar dai suka je raka amarya dakinta a ranan. Duk daba gida daya muke ba saida baji shakat da tafiyan nata don nasa an rage wani annoba a yanzu matar yazid ce ta fara magana ta soma fadin. Wai an rage wani kaya a nan wanan matar batayi min ita sam kamar ba ciki daya suka fito da yan uwanta ba ta fita daban a cikinsu komai nata baida kyau wallahi. Muna wajen iya har yamma nidai koda aka fito wai aje a sallami mama kin zuwa nayi na zauna nan a barandan iya har suka fito muka fice daga gidan. ZAINAB IDRIS MAKAWA [6/4, 07:42] Aisha Srtr Mt: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 9️⃣2️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Ba cewan da akayi kauyen sokoto za akaita bane abin mamaki sai irin gidan da mota ya tsaya dasu a garin tambuwal. Daga wajen gidan kawai zaka fahinci inda sukazo gidane na gandu irin gidan yawa din nan mai dauke da tun kaka har jikoki a cikinsa in akwai. Haka aka fito da ita zuwa cikin gidan wanda ko gidan gadonsu dasu mama ke zaune a cikinsa yafi don a can family house dinsu shimfide yake da siminti lungu da sako na gidan ga baki daya har bayi a shimfide yake da siminti. Sun samu dakin nata saboda kayanta tsohuwan gidan ta tashi daga dakinta an gyara dakin an hade mata shi da nata ya koma ciki da falo mai kama da babba da jakka dakin nan da tsawo can ta kuryan uwar dakan da akaiwa kwaskwarima yana kasa. Maman tudu dake rike da ita tun tana fadi a ciki har zancen ya fito fili tana fadin ikon Allah aure shiya gaji haka yau Saratu Allah ya nufa aure ya kawota nan kasan kuma ina ji sunan garin nan a redio amma ban taba tunanen zuwanshi ba. Sai faman gaidasu da zuwa yan gidan keyi har suka kai dakin nata suka zauna kallon juna kawai suke a tsakaninsu sai yaya barakhace ta iya fadin . Shiko dai wanan mutumin a gidan yawa haka gidan kowa da kowa zai kawo saratu ina laifin ya kama mata haya a wajen gidan don Allah dai. Ke dai bari ai wanan dalilin yasa muka koma muka fadawa Dubu abinda idon mu ya ganan muna ai baki san abin takaici bama barakha ni hada ban dakin nan shine ya tayar min da hankali fiye da komai. Ga matansa kauyawa gidadawa dasu ke bari kawai abin bai faduwa dai wallahi daki ai kun samu an gyara komai dafa ciki gudane iya falon nan. Gaskiya mutumin nan bai kyauta ba wallahi haba dai a,a barakha idan baku sawa auren nan albarka kuyi shiru don Allah tana fa son abinta ita don haka ku daina wanan magana. Idan matansa kauyawane ita yar birni saita koya masu komai a sannu harsu gane ai dama shine amfanin surka auren da maza keyi yanzu. Nusaiba ce ta fito daga kuryan da suke tana fadin nikan zafi kamar zan suke wallahi dakin nan idan na kwana a cikinsa haka ai ina sankarewa kafin safe ? Meyasa wa yanda ke gidan basu sankare ba sai ke ku dai iya bakin ku a rabu lafiya don Allah irin maganganun nan babu dadi gaskiya. Mama tudu ta tarewa Nusaiban numfashi abinda take fada a lokacin yasa taja bakinta tayi shiru ta tafi tana guna guni nan mata suka fara shigo masu da kulan abinci dama a gajiye suke don nisan tafiyan da sukayo. Wasu sallah suka farayi wasu kuma neman abinci irinsu Saiba ke nan tun wajen bude abincin sukai arba da bakin miyan dake cikin katon kula girke a gabansu miyan dai ga abin miya amma gaskiya yana da wuya yakai bakin mutum ko don bakinshi. Inda Allah ya taimakesu kunun daka da aka kawo masu hade da abincin wanda yaji kayan kamshi ga suga zaikai mudu biyu da robobin sha shi suka dinga afkawa cikinsu don yunwa abinci kan abin miya suka tsame sukaci. Akwai gaji don haka suka fara shirin barci tun a can amarya saratu ta fada masu idan anzo za ayi dinner don haka kawarta da akazo da ita take tambaya zancen dinner din ? Take fadin itama har yanzu angon bai kirata ba kota kira wayanshi yana kashe bata samunshi har barci ya dauketa ba zancen dinner din. Washegari hayaniyar mutanen gidan ya tayar dasu wajen kewayawama fitina ne haka suke bin lafiya har amaryan suka dai samu sukai alwala sukai sallah. Su mama suna falo suna dan gaisawa a daidai lokacin sukaji amarya ta fasa kuka daga kuryan daki hankali tashe suka isa gareta banda mama tana zaune tana azzakar din ta na safe. Sai dai ta jefa masu baki daga inda suke saida ta idar ta mike ta samesu tana fadin shifa aure mukaddarine duk inda Allah ya nufa zakayi aure saika taka wajen. Abu guda ya rage maki a yanzu shine hakkuri wata nacen tana neman hakan bata samu ba ke kuma gaki kina son butulcewa Allah yanzu da baiwan da yayi maki. Kinsan alheri dake cikin aurenki da bawan Allah nan da Allah ya hadaku tare shine mijinki aure ba kyalkyalin duniya akajawa cikinsa ba zama na amana matukar akwai so a tsakanin ka miji. Ki bar komai ga Allah kisa hakan shine alherinki a yanzu kinsan tanadin da yake maki ai yasan gidan daya dauko ki da inda ya daukoki don haka halinki yanzu shine jarinki saratu ki natsu kibar wanan shirmen da kikeyi. Kowa nan da kalan zabin da Allah yai mashi duk abinda kika gani ya faru da bawa rubuttace tun asali gareka. Ni banga wani abin damuwa ko shiga tashin hankali ba saratu kinafa son mijinki so ba inda baikai mace a duniyan nan . Da kalaman mama ta samu natsuwa suma din su saiba dake sakin magana duk mama tayiwa kowa gugan zana a wajen kowa ya kama bakinsa. Don cewa da mama tayi da wani zaman burni ko cikin daula ai gara kauye din inda hankalinka yake kwance a san kana kauyene ba sunan kana cikin daula ba wanan zance ya tabawa Saiba rai inda tace da ita mama keyi a zuciyarta. Kamar ana koransu kafin takwasa na safe duk sun shirya tafiyan komawa zaria a gagauce ga matan gidan duk da safiyane sai dake dake sukeyi suna wakokinsu a cikin raha na nuna murnan auren daya daga cikin ahalin gidan ana fadin su jira a gama furan barna sukace akwai nisa tsakanin zaria da nan gara subi hanya da wuri. Sai wajen shiga mota suka samu ganin ango yazo sallamansu nan mama tayi mai dan nasiha yana ta godiya suka tafi suka barta a nan din cikin mutanen da bata taba sanin kalan rayuwansu ba haka ya mace ta gada dama a kaika inda baka zata ba a rayuwa Allah yasa mu dace amin. Ranan yan uwan Aminu mata da yaya barakha tazo dasu wajen bukin suka zo gidan mu dama ranan zai koma can gidanshi ya gama kwanakinsa a nan. Abinci lafiyayye na shirya masu ba wani daure fuska koma ba sakewa sosai kada raini ya biyo baya na barsu sunyi yadda suke so tunda gidan kanin uwarsune suma kuma basu wuce gona da iri ba yadda nayi zato. A can gida kuma mama hankalinta a tashe yake har saida yan kai amarya suka iso a wahale kowa na neman abinda zaici a cikinsa maman tudu bata tsaya ba ta wuce gida da ita da yaya Rukaiyya. Sai mama hafsatu da yaya barakha da Saiba data nufi part dinsu suka rage a gidan yadda suke neman abinda zasucine ya tayarwa mama da hankalinta sai dai batayi magana koma meye ai zataji su kuma basu cewa kowa komai ba kar yadda maman tudu ta kwabe bakinsu tun can din. A nan gida kan wajen mama ba wanda yai magana sun daici abinci sun kuma ce sun barta lafiya tana can sun barota ita kadai. kamar yadda ake barin ko wata diya idan an kaita gidan miji nan mama tayi shiru na dan lokaci ai kuwa can part din yaya jafar kuma gajiya bai hanasu fada ba. Don saiba na shigowa ta kula da kayan da yaci abincin rana ta soma fadin halan gidan nan sweet J ya kwana ? Asmau tace ehh cikin ko in kula daki ta nufa har ta tube tufafin jikinta kamar an tsikarota sai gata ta fito tana fadin . Asmau ya kwana a nan kuma kinsan nice da girki kika yarda ya kwana a nan ban gari ke dai yar cin amanace ta gaske wallahi ? Cikin mamaki Asmau ta dago tana fadin tau fa kaji manya don baki gari sai kada ya kwana a nan ko ai bansan haka kika kafa doka a gidan nan ba ? Aida zaki tafi saiki fada min kada na kuskura in karbeshi idan ya dawo tunda kinsan jiyan zai dawo gidan nan kuma kikayi tafiya ? Fada sosai sukayi tsakaninsu wanan kawai ya isa ya tuna maka saratu don da tana gidan da tun a lokacin ta iso part din ko kuma ta bugawa saiba din waya tun tana can ta fada mata abinda ke faruwa a gidan. Har suka gaji suka kyale juna akan a bari maigidan ya dawo tunda shine munafukin da yayi hakan saiban ta shiga tayi wanka ta fito don tunda sukaje sun kasa yin wanka a bayin gidan. Abincima da Asmau ta bata kin karba tayi tabar matashi a falo ta fito zuwa part din mama ta duba ko akwai abinci a can taci . Ta samu don mama tayi girki don isowansu din ta zauna taci tana cicika a lokacin mama ke fadin mutumiyar ki dai tana can ta zama mutanen sokoto ? Mama aida sokoto din take da sauki wani shegen gidan yawa ya kaita fa gina kamar na mutanen dauri abinda babu dadin fada gaskiya. Kai Nusaiba bakiji me maman tudu ta fada ba albarkan aure yafi riyan dake cikinsa kayi abu daidai karfinka ba karya yafi kayi karya girman ka ya zube. Meye laifin gidan tunda yana da gidansu aurene fa ba inda bakai diya mace ta mike tana fadin yaya ai gaskiya na fada . Ita mama da take fadin hakan ai ta fadane kawai tunda bata yarda akai yarta wanan wajen gaskiya kam abu daine bai faduwa kawai sai ayi shiru hafsatu ta fada daga gefe. Wai ku tsaya me ake kokarin boye min ne mama din ta fada tana duban saiba din ta mike tana fadin mama ni me zance yanzu ace kuma ina kushe aure sunana yakai tasa kai ta fita. Munafuka dadai ki fada din mana tunda gulma na ciki ai gara dashi yana da gidan ke ko gida iyayyenki nada shine balle nina dawo rakiyan yarinyar nan na kula ba mutumiyar arziki bace ita . Barakha meye laita yanzu har kina kokarin zaginta ai gara da ita ta fada min halinda yata take ciki kuda kuka boye min fa don yaya tace kada a fada ? Laifine mama don mama tace kada muyi surutu mu tayata da addu,a sai hakan yazama laifi ni naga ai abinda yakamata muyi ke nan mama ta fada. Lalai Barakha dole kishiya ta dinga cin galabanki indai wanan halin naki na saurin yarda da mutanen yanzu kikeyi a can ? Yayace zatace kada ku fada min abu ke har ki yarda kiki fada min don kina bi can sun san halinki ke sokuwace da sauri ta dubi uwar tana fadin ni mama me kuma nayi na sokonci a nan don na fadi gaskiya ? Damu fada maki abinda zai tayar maki da hankali a banza ita saratu na can zaune dakinta ai gara muja bakin mu muyi shiru tunda nan Allah ya nufeta da aure. Wani malolon bakin ciki ya tokare mata makoshi ta kasa ba yar nata amsa don bakin ciki ta mike zuwa dakinta barakha ta dubi mama hafsatu tace wallahi mama kada ki yarda kice komai kada tashiga wani hali su jafar su sakaki gaba a gidan nan. Jin hakan yaba hafsatun tsoro tace ni kingama bari bazo nabar gidan nan yanzu da nace sai yamma zan karasa gida amma yanzu zan wuce. Dubu na shiga daki waya ta jawo ta dannawa saratu kira gidan cike yake don a ranan suke wunin buki tunda amarya ba a gari take ba. Hayaniyane dakin nata sai cewa take bata jin abinda mama din take fada don idon mutane dake kanta a lokacin dakin tap yake da yan uwa da abokan arzikin gidan yan zuwa gani amarya. Gashi duk sun isheta amma ba daman magana yarasu sai hawa saman kujera sukeyi suna takawa iyayyeb da diyan anci shimkafa an wawatsar mata a dakin nata. Dole ta koma kuryan dakinta ta kwanta tana kukan zuci Allah ya gani tana son habibinta don irin mazan nan ne da mata basu dauke ido akansu don kyau. Wanan yasa duk inda yaje ya taya mace yake samu da sauri gashi iri mutanen nan ne manema mata ko yaushe tsab yake komai nashi neat tun daga kanshi har takalma zaki gashi neat dashi clean . Saidai shi dan karyane na gaake kuma manemin mata dama idan kaga na mijin kauye ya faye wayewa hakane dabiansa neman mata. Ko ita saratun da karya yaje mata saita lake mai har abin ya zama masu aure bai boye mata ba da abin yayi nisa ya fada mata shifa dan kauyen sokoto ne haka kuma bawai wani mai kudi bane shi. Ta dauka yana zolayantane kawai don ya barta sai gashi tace zata daiyi din ko yaya yake don ita a zatonta kawai yana fadane don ya gwadata ashe haka abin yake. Allah ya dora mata son habibi a zuciyarta don haka ko yanzu da tan uwa suka watse suka barta bataga laifisa ba tunda ya fa mata din abu dayane har lokaci bata tantance ba cewa da akayi itace ta hudu a gidansa. Bata gaskanta ba saida yan uwan mijin suka hadusu waje daya ana tsawata masu kan zamantakewa nan tasha mamaki ganin su hudune dai matanshi kamar yadda mama hafsatu ta fada data koma daga jere. Wanan yasa hankalinta tashi sosai har saida ta kasa daure ta kira mama da kuka tana fada mata itama uwar kasa daurewa tayi nan ta nemo kan iya tana labarta mata a zatontama Jafar bai gidan saboda rudewa ranan bata tsaya yin lissafin kwanan mu ba don ga yarta cikin bala,i. Ke dubu ki natsu dob Allah zama da kishiyoyi haka kan saratu ne farau din haka keda kika zauna a cikin kishiyoyi meya sameki nace ? Iya ba daya bsne da nawa don ni a cikin gari nake kuna jin duriyana kuma ina ganin na gida wanan kuma wani uwar duniya fa take bako kusa da yar uwarta hannatu ba can fa kauye ya ajeta. Sai akace kauyen ba a zama ko aure inane bai kai mace wai don Allah ana ce baki ga zuma kina ina badaci yarinyar nan dai tana son mijinta ko batace dake bata iya ba dubu ? Suna zancen jafar da habu suka shigo part din suna gaidasu nan iya ke fadin to kuyiwa uwarku magana tun bata jawo maku abin kunya ta kashe auren saratu ba ? Kashewa kuma akan me mama jafar ya fada yana kallon uwar iya ni baki fahinceni bane abinda nake nufi don me yayi muna karyan mata daya gareshi ? Haba mama ai hakane daidai da saratu gidan mata da yawa inda zata ji dadin yin gulman ta da makirci ba ta iya tsegumi ba tun nan tana shiga matan yan uwa tana hada fada yau gata Allah ya kaita inda zatayi nata. Habu nagane saboda matarka ka tsani yar uwarka to koma meya samu saratu yar uwarkace dai mama ta katse ya Habu daya soma magana. A,a mama ba wai zancen tsana bace kece kika damu akan wanan abin yarinyar nan itafa ta gabatar da mutumin nan tana son sa banga abinda zaisa ki damu kanki ba yanzu don Allah ? Habu yana nufin cewa zata iya zama a duk inda ta tsunci kanta tunda ta koya a gun matan mu da suke rayuwa tare a gidan nan shi kuma sai bai fada ba kai tsaye. Iya sai murmushi takeyi tace banda abin dubu saratu mace ce fa yau ko sha biyar aka wanketa a zamanin nan a kai cikin mata ukku ai tsab zata zauna dasu balle mace kamar saratu. Ai maganan habu gaskiyane zata zauna tunda ita ta saka kanta auren nan idan kika sa damuwa har ta fahinci hakan ta kaso aure tazo ta zauna maki gida shike nan. Addu,a yakamata kiyi mata mama yadda ko wata uwa kewa yarta in yaso sai a saurara aji ko zatayi korafi aka zaman nata kinga sai a san matakin dauka a lokacin. Wanan magana ta jafar ya kwantar mata da hankali suna cikin zancen saiga Saiba ta fado masu tana huci take fadin mama naje can ban sameki ba ? Ashe kina nan dama karan su na kawo maki kowa yasan dai nice zan karbi girki a jiya amma sai J yasan ban gari ya dawo yaba Asmau girkina. Wooo,hwahoo ni jikan mutum biyu yar nan kina data ido kuwa Iya ta katseta sa fadin hakan wani kallo tayiwa iyan kafin tace da hankalina wajen mama nazo. To meye a cikin hakan kuma Nusaiba akwai mana mama tunda ban karawa Rahama kwanan ba na dawo nan bata samu yadda take so ta bata min suna da yar mutane ba. Na dawo na kwana da Asmau ko kike nufi idan na tsaya can kuma ki dorani a ture ki yawata kina fadin na saci kwanan ki ? To na kwana din kiyi abinda zakiyi marata ido kawai bansan baki da mutunci ba ai da bandawo na samu kinwa Asmau duka ba yau. Tsuki habu yaja ya mike yana fadin ni zan tafi iya yaya karfin jikin naki dama nazo na dubakine zan tafi ya mike yana fito da kudi cikin aljihunshi ya mika mata. Da sauri ta mika hannu ta karba tana godiya hakan yabasu dariya aka wasance J ya mike suka fita da habun sun jima a wajen motar suna magana kafin ya bar gidan. ZAINAB IDRIS MAKAWA [6/5, 13:47] Aisha Srtr Mt: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 9️⃣3️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Ina jin irin cakwalin da akeyi cikin dangi game da zancen aure Saratu ban taba furta komai ba game da zancen shi zance a yanzu tafiya yakeyi. Bayan haka alhaki kwikwiyone don bin mutum yakeyi koshi yaya shiyasa na katseshi da irin nuna haushin ta da yakeji yana mata gwai da hakan data fada ciki. Na nuna mai tankar uba yake a gareta duk abinda ya cika da ita a yanzu ya sameshi don shine matsayin babba a bangaren mama yanzu. Ya kance dani haka kike gani Rahama amma su a bangaresu ai yanzu tunda banda komai ai basu ganin hakan kowansu kar nake kallonshi a yanzu. Habu ma yafi kowa ban mamaki yasani sarai nina sakashi a wanan harkan asalima sana,atace ta baya na bar masa amma wai habu nan nace ya cika min kudi nayi wani bussiness ko Allah zai taimaka un daga yaki ban . Nayi mamakin wanan zancen da naji duba ga yadda nasan ya taimaka masu sosai a baya koda yake ba abin mamaki bane idan ance yaya habu yayi irin hakan donshi mutum ne da bai kwantuwa ko kadan. Ko iyalinsa gaskiya din tana da hakkurine ba a jin kansu da ita don da watace yadda yake tauyeta din nan da anjisu tuni wajen irin halin nan. Mutane sukan manta da arziki na Allah ne duk akace mutum mai arzikine daga Allah bana haye irin na zamanin nan ba kabar maishi kawai kada ka jefa hassadanka akanshi. Ire iren halin rayuwan da bawan Allah nan yake fuskanta suna da yawa gana yan uwa a gida don wasu har yanzu basu san da baida hali irun na baya ba gani suke shi maishine akoda yaushe. Ga fitinan iyali a kullym sai anyi ance ya samu ya shiga wani hali balle yanzu da abu biyu zuwa ukku sune a gabanshi na farko zancen haihuwana daya nuna damuwa akai sosai tun anan nasan lalai bada kudi kamar da. Sai zancen jikin iya da shine tsaye a kai yana bata kulawa sai kuma salima dake kula da ita din da mama sai kuma zancen jikinshi da halin rayuwan matsi dake tunkaronshi. Cikin haka dai ranan na tashi da nakuda gashi ba a gidan mu yake ba gashi saboda alkunyan mu ta filani na kasa kiranshi in fada mashi duk da jaddada min da takeyi tunda watana ya kama akan in naji wani abu in buga mashi. Kasa zama dakina nayi na koma wanan dayan dakin da babu kowa ina sintiri ina gudun wani yazo ya ganni aga gazawana. Ya kira waya tun asuba kamar yadda ya saba ban daga ba har rana ya fito gashi hankalinshi yaki kwanci hakan yasa ya fito zuwa gidan namu. Kofa na rufe har lokacin ban bude ba yayi ta nocking saida kyat na iya zuwa na bude kofan kafin ma ya shigo na duka a inda nake don taso min da abin yayi a lokacin sanadin dan tafiyan da nayi din. Salati ya sake yana tambayan meya faru meyasa ban kirashi ba shi haka kawai jikinsa ya bashi akwai abinda ke faruwa dani tun dare. Tashi maza muje asibiti ya fada a gigice na dago ido da kyat na dubeshi ina zufa nake fasin zan iya ai ? Zaki iya me kin taba sanin haihuwane common tashi don Allah muje asibiti jin hayaniyarsa yasa Biba dake ta sharan barci fitowa daga daki. Turus taja ta tsaya tana kare muna kallo tace baki da lafiyane anty ya juya wajenta yana fadin ke dauko mata wani zani daki da sauri ko kuma tsaya in kira mama dai tazo. Maman tudu ya kira ya sheda mata ta shirya gamu nan zuwa a dauketa zamu asibiti take fadin a,a yau abin yazo ke nan ubangiji Allah ya raba lafiya ya amsa da amin take fadin ai a shirye take. Saidai ka dauko zannuwa kamar uku da kayan jariri a je dashi ya amsa tare da kashe wayan a cikin sauri yama rude ya dannawa yaya Ai kira kuma. Yake tambayana ina zanga zani din da kayan baby akwaisu kaina na dago da kyar na dubeshi ina gyada masa kai alaman akwai. Ina zamu dauko zanin suna a cikin kasan closter dina don yakai sati dana hada komai don gudun irin girshi haka nayi wanan dabaran gashi yayi amfani yanzu. Da kyat muka kai wajen motanshi a nasa yaso ya daukeni naki hakan dole ya barni na taka zuwa bakin motan muka shiga yake fadawa biba ta kula da gida da kanta. A hanya muka saida ya tsaya saboda wani yunkuri da nayi kamar zan rike mai hannunsa da yake jan motan ban tsanmanin ya taba ganin matarsa tana nakuda urin hakan yasa ya gigice sosai a lokacin duk da dauriyan da nakeyi kuwa. Saidai tunda mama ta shiga motan dole na daure ga duk abinda nake jin din saboda alknyan mu ta fulani ban yarda nayi koda dogon motsi ba sai shine ke dan juyowa yana fadin sannu ya lafa ko saidai in gurgiza mashi kai kawai ban iya magana a lokacin don mama kada taga raunina a cewan mu. Sun karbeni sun duba kiran da likita yayi mai ya kara daga mashi hankalinsa inda likita ke fada dashi kan cewa yasan matanshi nada matsala meyasa basu zuwa awo ? Tana zuwa awo saidai asibitin can na mata take zuwa a dubata likita yace to yallabai gaskiya matarka ba zata iya haihuwa da kanta ba saboda yaro nason fitowa amma ba hanya. Anyi arziki ma da yaron yake da rai har yanzu bai mutu ba don haka dole sai munyi mata aiki an cire abin dake cikin nata. Zufane ya karyo mashi son haka yanzu idan ka shirya sai ka saka hannu ga takardan nan a nemo muna jini da wanan maganin muyi shirin aikin yanzu dole sai aiki za ayi mata a cetosu ita da dan nata. Zufane ya karyowa yaya din lokaci guda yacewa likitan go ahead ya mika hannu aka miko mashi takardan aikin yasa hannu sai kudin magani da sauran abubuwan da zai sayo din na aikin. Lokacin daya kira gida yana sheda masu mama na zaune dasu iya tana jin ance aiki tace jam kukan yaran nan kun daukowa kanku jamgwangwan ace mace bata iya haihuwa sai anyi aiki wanan wani irin masifa suka jajibo haka wai ? Assha dubu asha abin naki har yakaiki ga rashin tausayi akwai macen da son kai zai kaita ga askan likita inba dole ba wata mace ke fatan a fede ta don Allah ? Kema fa uwace dubu kin haifa kuma za a haifar maki ki tuna kina da yayan nan gasu nan maki har yanzu a gaban ki kike irin wanan magana. Keda ya kamata aji furcin alheri na Allah ya tashesu lafiya kike wanan maganan haka nasan ko agaban yaran nan zaki iya fadan hakan cikin rashin damuwa da abinda kika fada. Haba iya ace ga yadda yarta take ita kuma yanzu ace sai anyi aiki wanan idan an samu mai karamin karfi don Allah yaya ke nan za ayi kullum kashin kudi kan mace ? Rufa min baki don Allah mara imani da tausayi kawai Allah yana nuna maki abinki hakan baisa kin saduda kin koma gareshi ba har yanzu ? Da kike aibanrta yaran nan haka yasa mazajen nasu sun tsanesu ko sun rage son da suke masu din ke dai ki kama girman ki tun bai bare ba kin kasa kwasa. Balle yanzu ai mama wayewane ga mata mace taje asibiti ko tana iya haihuwa a fedeta don kada tayi saurin tsufa a idon mijinta balle wanan da nasu yake da dalili salima ta fada. To iya kinji ko nikan nace haba gaskiya dai a yanzu yawan aikin ga mata ya yawanta wanan wani irin zamanine muke cikinsa wai tsufan banza da komai wayau ki sai kinyishi. Ki daiji dashi idan kayane kada ki bari don Allah ki matsa kinji har su gane kina kishi dasu irin haka raini ya shiga. Kishi kuma Iyaa su zan tsaya kishi akan me zan tsaya kishi dasu suna yayana da sauri iyan tace, a,a dubu kowa yasan kina kishi da yaran nan akan yayanki maza waye gwanarki cikin sarankanki kaf ? Babu gaba dayansu kishi kikeyi dasu kowa yasani ko don ba,a iya fada maki a gabanki ? Ta mike tsaye da kyat tana fadin salima tashi ki kaini asibitin don Allah kada mu barsu su kadai a can gashi ance aiki za ayi. Ke iya ina kuma zaki keda ke fama da kanki tashi nace ki kaini ta fada da tsawa bata tsaya kallon mama da mamakin furcinta ya kashe a zaune. Duba min Yazidu idan yana nan ya kaimu in kuma bai nan mu samu motar haya mu tafi salima dai ta mike tasan mai iya hana Iya tafiya asibitin wanan lokacin sai Allah. Dole salima ta mike ta shirya suka fito duk da safiyane matan yaya na waje da yaransu suma kansu don tsamin shiyan basu faye son zama a cikin part din nasu ba wani lokacin. Yanzun ma ruwan wake da Saiba tayi alale shine bata zubar ba part din ya dauki wari su kuma basu gane kome ke wanan wari ba saboda kazanta suka fito daga waje suka zauna. Ganin su iya sun fito yasa Asmau tambayan yau iya fita za ayi ke nan tunda safen nan ta juyo tana fadin asibiti zamu abokiyar zamanki aka kai asibiti haihuwa za ayi mata aiki. Aiki kuma har abin yakai can ne shi sani gaibu aisai Allah yanzu Jafaru ya bugo waya yana sanar damu hakan suna can aaibitin dai tun dazun. Allah ya raba lafiya ya kawo rayayye Asmau ta fada samun waje itama bata iya haihuwan ke nan da kanta ko irin na yar uwarta ? Aikan tunda akace aiki za ayi kema kinsan hakane to shine don munafunci ya fita bai fadawa kowa ko yana tsamanin wani abune ? Wa zai tsaya yin wani sheri a kanta ko yar da zata haifa Nusaiba ke fadan hakan cikin hasala tana fadin shiyasa ake jin mu ni banson harka da munafunci wallahi ? Kila shima baisan aiki za ayi mata ba Asmau ta fada ta juyo tana fadin kamar ya baisan aiki za ayi ba tunda haka ta zaba wai ita wayewa oho dai su suka sani ta fada cikin bacin rai. Allah akbar kishin ke nan fa mata kishiya idan ba ta daina ganin numfashin kishiya ba ko taji an fasa ihu shine kawai zata numfasa amma wani ciwo ko wani kakanakayi bai hana kishi ga wasu. Asibitin kuma habu ya fara kira yake cewa dashi muna asibiti da Rahama idan akwai kudi a wajenka don Allah turo min an rubuta min magani. Yana hamma don barci yakeyi yace kudi gaskiya ba wasu kudi a hannuna sosai yanzu amma bari in duba yace ba matsala. Shiru yayi bayan sun gama wayan ranshi a bace ya kira abokinsa na nan dake juya mai kudin Salima yace dubu dari biyu yake so don Allah ina asibiti da matana aiki za ayi mata yanzu. Subbahanallahi aiki kuma gani nan zuwa amma ai sha,anin asibiti dari biyu baiyi gaskiya bari dai in karaso yanzun nan zan watsa ruwa in sameka kuna wani asibitin ne a ciki ? Ya fada mai yace gashi tafe har yazo aka shiga aikin bayan ya kawo mai dari hudu duk wani zirga zirgan asibitin akayi dashi saida aka fito mai da jariri ya tambaya akace za a fito dani yanzu yayi godiya ga Allah. Mama da Salimace suka tafi gida da yaron don ai mashi wanka suka bar iya da inna data biyo mu daga baya ita da Nafisa. Duk abinda yakeyi hankalinsa yana ga dan uwansa yana mamaki furucin yaya habu din don mamaki shi kwarai yake a zuciyarshi. Yana aiyana lalai kudi sune rufin asirin bawa yau shine dan uwansa na jini yayiwa hakan gara yazid ya san baida kudin amma ya turo mashi da abinda ke akwai a lokacin. Haka yayi ta sintiri da yunwa a cikinsa sai karfe biyu ya koma gida don ya watsa ruwa ya samu abinda yaci lokacin abokin nasa shima zai tafi yace dashi zaka jini insha Allahu sulaiman nagode kwarai da taimakonka. Haba dai dole muyi maka ai J waye silan zaman mu hakan a yau i bamuyi ma ai Allah zai tambaye mu ni wallahi ba wancan kudin bane kyauta na baka wa yan nan din. Abinda bai tsamata ba hakan ya sama don koda ya shigo gidan da saiba ya fara cin karo tana shayi a wajen haraban gidan har ya aje mota ya fito ko kallo bai isheta ba. Saida ya shiga ciki ga wari ga komai ya fara kwalawa Asmau kira da ita yana fadin wanan warin fa tun safe nake jinshi a part din nan ? Asmau ta fito da danta a hannu tana fadin kadawo ashe yaya mai jikin kuma yace da sauki ashe an sauka Allah raya ya amsa da amin yana fadin. Wanan warin fa na meye do Allah yaya zaku zauna cikin warin nan kuna ji zai iya illanraku amma kun kasa duba kome ke wari haka don Allah ya fada yana bin falon da kallo. A,a warin ruwan waken da Saiba tayi alale dashi jiyane na fada mata yana wari ta dauke taki to munafuka kina fada mashine don ya dakeni kome ? Hauka nayi da har na fara duka waike Nusaiba wace irin macece da baki son zaman lafiyane komai naki nacin mutuncine ke ? Yanzu ina shigowa asibiti na fito amma kika bini da kallon wullakanci din kina yar rainin wayau ko ke gaki issasa ki shiga ki dauke ruwan nan yanzun nan kafin na fito. Ina ruwana da ka fito asibiti tunda ban aike ba asibiti wanan ruwanka kai ya shafa bani ba name zaka kuma dafa min wai nayima mugun kallo ? Ai nasan ruwana tunda bai shafeki ba niko daya shafa ai kinga naje har kuma kin gune da hakan ni yanzu na gane ki sarai kanki kawai kika sani ke saukin abin kowa dai na ciwo aiko ? Wata sabuwa za a dora min laifin da banji ba bangani ba akai kaje kaji da wace ta jaka zuwa asibiti ta kwanta don samun waje bani ba ? Ai kinji nace niya shafa kuma naje ba sai kinyi hakan zaki nuna min ranki a bace yake ba ai dani taje ta kwanta kuma naje na tsaya din anyi mata aiki ina shike nan koda kudinki nakai ta asibitin ? Meye nawa malam mu dai da aka raina idan munyi magana ace damu babu kudi gashi yanzu anyi kudin kai mata asibiti ai tunda tana yar gwal. Au bakin cikinki ke nan ashe na samu kudin dana kaita asibiti akai mata aiki to kije ki kwanta kema asibitin sai in kashe maki kudin ko ? Kai kai kai wai haniyar meye kukeyi hakane kai da kake da mara lafiya kazo nan kana wanan hayaniya haka kuma kuna saida hali ? Yarinyar nan mama yar rainin wayauce ya juya yana fadawa mama din yace har da asibiti mutum ya dawo ba zata barshi ya huta ba nina gaji wallahi tunda bata da ranan gyara halinta ? To ka gaji mana sai me keko kikan fara halinki ke nan wallahi tunda kinsan hankalinshi na a kwance yake ba baki kyaleshi koma meye ? Mama kodaya fita gidan nan bai fada muna matarshi tana asibiti ba ko zai kaita asibiti don ina tsoronsu yanzu sai ince mashi yaya jikinta ko an haihu ? Kallon mama din yayi cikin mamaki yaji abinda zata fada sai yaji tace towa ya fadawa ga abinda ke nan muma saida yaga za ayi aikin aiya kiramu tunda bamu da amfani a zancen ? Ina dai fadama kayi hankali da mace balle irin shu,umar yarinyar nan data iya kisisina iri iri tun bata kai nan ba. Mama kin goyi bayanta ke nan fa zancenki ke nufi ba zancen goyon baya a nan tsoranka akeji daba za a fada maka gaskiya ba tunda an nayar daku shanun tatsa ko yaushe kuke nan cikin wahalan mata ? Yarta ta kwanta tace bata iya daukan ciki balle haihuwa yanzu gashi itama ta tsiri hakan farawa da iyawa saika koma kaita kashe jiki ana tatsanka kaiga mata asibiti. Ballema ita bata haifo a sa,a ba tunda taszo da kissan ba kudin ta gaji da kwanci ta taso don kanta idan taga ba abinda sukewa din ta makara wajen wanan kissan. Kai ya girgiza ya juya zuwa dakinsa ya rufo ya barsu tsaye cirko cirko a wajen sai nusaibance ta kawar da shirun take fadin wallahi Asmau muna fukace ta karshe wai mutum bai fada muna komai ba take mashi wani kashe murya yanzu . Wanka yayi ya koma asibitin Nafisa ya kira yake fada mata taje can gidanmu ta shiryo abinci a kawowasu mama nan ya bata kudin mota ta tafi. Koda ya shiga dakin ya samu na farfado ina ina kwance mama tana gefe da jaririn a hannunta tare da sauran yan family house dinsu da sukazo ya shigo suna gaisawa dashi suke mashi barka da arzikin fitan kai lafiya. Ya amsa kafin ya aje masu ledan daya riko dan abinda zasuci a lokacin ya nufi wajen gadon yana min yaya jiki na lumshe ido cikin gajiya tare da amsawa da kyat nace da sauki. Ya juya gurin mama yana tambaya yace wai kuwa matar habu tazo mama mama din tace yanzu na kare zancenta a raina da ban ganta ba nima. Waya ya dauko yana bugawa habu din wayan ta kusa katsewa ya dauka yana dauka yake fadin sorry J wallahi kudin ne basu samu ba kajini shiru. Yace nerve mind nace ka fadawa Matarka cewa muna asibiti anyiwa kanwarta CS an cire da dazun ? Wai dama aiki za ayiwa Rahama din na zata kunje ganin likitane kawai fa ya katseshi da fadin don Allah fada mata anyi aikin an cire da tun dazun muna nan Royal da ita ya kashe wayan . Ya juyo gareni nake fadi a hankali dama ka kyaleta ai yace No a dai fada mata din kada ayi laifi donshi bai fada ba wai baisan aiki za ai maki ba. Shigowa likita yasa sauran fita aka bar mama dashi a dakin likitan na fita mama ta soma fadin matanka fa da dubu koda yake ga iya ai da salima sunzo ba zance basu sani ba. Sun sani mama ya fada a cikin wani irin yanayi na bacin rai kafin ya juya zancen da fadin yaron yanzu mai za a bashi ga dai ruwan zamzam nan na sayo da dabino a leda. Nagani salima zata bashi likita ya shigo barci ma yakeyi tun dazun dai yayi dan kuka kuma aka lalasheshi yayi barci. Likitan yace ya gaji da yawa hutu yake so ai an auna arzikine aka sameshi raye yarinyar nan tana da taurin kai mama tana nakuda tun cikin dare amma bata kirani ta sheda min ba ? Murmushi mama tayi tana fadin bafulatancefa Malam aiko inba ta zama bafulatanan zamani ba baka taba jin ta bude baki tacema ga matsalan ta wanan halinsune alkunya da kawaici shi mutane suke dauka rashin wayewa nan ko alkunyace irin tasu ta fulani da akasani. To mama kana cikin wanan cindition din baka kikirana kunya hardani zata hada mama haba mama tayi murmushi tana fadin daga ita har matan habu ai basu yarda akidojinsu na fulani ba. Mama ni yau ai ina a cikin mamaki sosai wallahi ashe idan baka dashi ba kowa kake a wajen ko yan uwanka ba mama ni habu zauwa haka. Ban gama mamaki ba kuma naje gida na samu wanda yafi wanan abin mamaki ace maman mu har da asibiti take adawa akai wai da gangan Rahama tazo ta kwanta akai mata aiki. Don kawai a kashe mata kudi da ganganfa mama ta katseshi da fadi yace wallahi mama ita kuma shashashan nan mai bakin kishi ta dora nata sai Asmau ce tayi min Allah sauwaka kuma sukaga laifinta. Ita dubu har abin yakai haka gareta to Allah ya sauwaka don abin nata sai addua iya fa ta fara ban labari dazun ashe ta fada maka hakan kaima Allah ya sauwaka toh. Mama ni habu zai hanawa kudi sai wani banza can na waje bare aboki dana taimakawa taimakon da baikai nasa danayi mashi ba shine zai dauko kudi ya ban masu yawa inyi lalurata dashi. Amma ko habu bai kyauta ba barshi insha Allahu ko talauci zai kasheni bani kara tambayanshi komai a duniyan nan in Allah ya yarda. Habu ko bai kyauta ba ko ana mashi kirarin rowa har dakai zai hada yayiwa rowa a duniyan nan meye bakai masu ba a rayuwansu kaf dinsu gidan nan. Barshi babu komai mama ya fada cikin wani irin murya ina kwance ina jinsu ya ban tausayi a yadda yake fadi yana bata labarin yadda yabar mashi aikinsa na farko na mai da habun keyi yanzu . Haka kuma suka kama dukiyansa suka durmuye dashi dasu kawu har kayansa suka salwanta baiyiwa kowa korafin hakan ba kuma. ZAINAB IDRIS MAKAWA [6/7, 20:37] Aisha Srtr Mt: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 9️⃣4️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Kwana biyu muka samu sallama dama da iya da mamane sai salima muke zama asibitin da inna dake zuwa itama ta wuni damu wace a yanzu na fahinci taga kamar mama ta karbe matani don da farko itace muke tare da ita. Amma zamanmu jiyar yaya dasu maman tudu din sai muka saba sosai da ita fiye da inna duk da dukkansu suna da halin sukan mama dubu da iyalinta a gabana saidai ina nuna masu hakan bai damuna don ba halina bane zama yi da mutum. Wanan kuma nasan cewa halin kishin mu na matane yasa suke hakan tundai mama gaskiya tana yawan magana da korafi kan halin mama amma wanan matsalansuce ta manya ai bai shafeni ba amma kuma tana da fadin gaskiya dasa mutum a hanyar da zai fusheshi. Din haka koda muka dawo gida mama tudu itace ta biyo mu zata zauna dani ke nan yan kaduna sunzo tun washe garin haihuwan sun dubani hakama Yanda a ranan da dare tazo ta dawo kuma washe gari har dare tana wajena kafin ta tafi. Duk da bai fadi ba kana kallonsa kasan akwai damuwa a tare dashi a yanzu ba lokacin da zai iya fada min ko maye don ko yaushe muna tare dasu mama idan zai shigo wurina. Yayi kokari sosai zamana asibiti haka abokainai da yan uwa suma sunyi nasu rawan ganin a lokacin gaskiya gashi wanda duk yazo da alherinsa mama ke karba idan yazo ta mika mai da farko ya nuna abarmin aimu aka ba. Amma mama ta nuna mai ai damu dashi dayane don haka ya karba ya rage lalura dashi ga asibitin na kudune sai demand suke saka mashi na kawo kudin kaza kawo kawo dai a asibitin har aka sallamo mu muka dawo gida. Ina barci da dare ranan yaya habu yazo dubamu ya jima suna hira dasu mama don lokacin yana gida nabar labari a baya don kuwa mama dubu itama sun shigo a ranan da aikai min aiki ita dasu Asmau da Nusaiba . Ta dauki dan ta kare mai kallo mama ke fadin dubu kinga farin miji kin kasa ba uwayensa su dauka su gani budan bakin mama sai cewa tayi ga faein miji kam amma yazo a yanayi. Baizo lokacin daya dace ace fari yazo ba walwala ba maman tudu tace jam meye na rashin walwala kuma dubu ga yaro da uwar kafiya kalau dasu. Ummm,hummm yaya ke nan nabar zancen don ba zaku fahinta ba Allah dai ya raya muna shi ta amsa da amin tace mikoshi kada ki shaye zakin angonane dai ni kadai ko Ladi tayi ta barni da abina da cewa inna. Da haka aka wasance zancen nata lokacin iya tana waje tana sallah akai hakan suma suka karba sai Asmaucema ke fadin kai lalai mama kinyi ango wanan aiya kosa a ciki sosai tubbarkallah masha Allah ta juyo tana min sannu nayi murmushi ta mikawa Nusaiba ta dan karbi dan a dakile ko minti daya baiyi a hannuta ba ta mayarwa matar yazid dashi ta fice daga dakin wai tana waya. Basu jima ba suka tafi wai yaya na gida yana jiran a kawo mashi mota ya fita don dayan motan tashi da suke fita ta lalace lokacin. Haka zancen mama ya tsaya min a rai don na kasa fassara abinda hakan ke nufi lokacin saina bar zancen a raina. Tare da mama muka kwanta a gado iya kuma falo ta tsaya don lazumin da takeyi da dare washegari tunda safe mama ta tayar dani nayi wanka don anty Nafisa na gidan har lokacin. Ya shigo suka zauna da iya a falo suna gaisawa mama ta fito suka gaisa yake tambayansu dare tace Alhamdullahi maigidan nawa ai bawan Allah neshi baida fitina ko kadan. Kamar dai sak nacewa dubu kai ya biyo amma take fadin wai baku da kama yaron nan kaine ai sak babu inda yaron nan ya rageka gaba daya diyanka ba wanda ya daukoka irinsa duk da uwayensu sukai kama sauran ba dai kamar wanan mai yawan ciwon ita bata rage uwarta ba ko ina ? Ya mike da zuman zuwa daki wajena wayanshi yai kara ya tsaya daukan wayan yana karawa a kunnensa a cijin harshen turanci ya soma magana da maishi har ya shigo dakin ina zaune nayi zufa na gama shan tea ke nan a lokacin. Hannusa yakai yana share min zufan tare da fadin eh nine kwarai kuwa nike magana ya tsaya ya saurra da kyau ga bayanin da mutumin yake mashi na daiji yace Allahu akbar kabiran . Jin hakan yasa na dago na dan dubeshi daga inda nake zaune din ya hannusa yana rike da nawa har lokacin godiya ya somayi kafon ya kashe wayan yana rungumeni ya furta Iam back Rahama in sha Allah kayana da suka salwanta anganosu yanzun aka kirani daga can. Farin cikine ya kasheni ina murmushi na furta Alhamdullahi Allah abin godiya wai Allah mun godema. Ya sakeni ya juya falo zuwa falo wurinsu mama yana shiga ya daga hannu yabawa Allah kirari da godiya ya duka yayi sujadan godiya ya dago yana fadin me zance mama wanan mijin naki lalai arzikine an gano kayana da suka salwanta a can kasan aka kirani ana sanar min. Masha Allah suka dinga furtawa a cikin murna budan bakin mama sai cewa tayi Allah ka rufa wanan asirin dama na fadawa dubu hanya Allah yawa gareshi yanzu me zatace don Allah kuma ? Tace wanan dan bai zo a sa,a ba don yazo ba a cikin walwala don haka ita batayi dashi nace mata hanyan Allah da yawa yake yanzu gashi ? Ita dubun ta fadi hakan yaushe tayi wanan zancen banzan haka banji ba a ranan da sukazo asibiti mama taba iyan amsa tana labarta masu yadda akayi. Yoo kuji zancen bamza don Allah jininka zaka tsaya fadawa wanan zance haka abin kunya abin takaici wai meke damun dubune kamar wace kwaro ya hau kanta don Allah jinin ja zakaiwa wanan furcin ? Wanan kam saidai a kirashi da arziki yaci babban suna mohammad za,a saka mashi insha Allah dama dashi nayi mashi hudu babane ya dawo . Gaskiya kam yaci wanan sunan wanan da arzkine yasha sara da suka da sassaka da kushe tun yana cikin ciki har fitowanshi duniya ba a bari ba kai jama,a Allah na gwadawa mutane isharanshi tun a duniya. Dubu dubu meya samu jan yarinyar nan ne nikan sai ince ko mutanen boye sun shafetane wai ba a sani ba dariya taba kowa datake zancen nan . Kubar dariya don Allah iyan ta kara fada tana fadin nifa abinta ya fara daure min kai jama,a kutayani duban zancen nan na dubu jininka yazo duniya ka nuna bakin ciki a fili kana wanan furcin haka abin dubawane zancen nan ? Ta fada don nima abinda tace min ke nan a lokacin wai Rahama bata da sa,a gashi ta haifo da a cikin rashin sa,a yazo babu komai sai wahala. Duba fa wanan zance haka ina ya fito ki kyaleta iya komeya faru kaddaratace a hakan ai Rahama tayi hakkuri sosai da abubuwan nan don haka ki kyaleta muyi mata addua inma wani abin ne ya hau kanta Allah ya yayye matashi iya. Ina ganim gobe insha Allahu zan tafi lagas zan bar nan zuwa Abuja inshiga jirgi don suna nemana ai ina ganin suna ba satin nan ba ko yake tambayan mama. Ina sai maijego ta kara samun lafiya dole a dage sunan nan don aikin da akai mata saita mayar da karfin jikinta . Haka nayi tunane ban fada bane kada ace wani abu ya fada mama ta bashi amsa da fadin haka abin yake ai sai an mayar da sati daya ko biyu maijego ta murmure ake suna idan aiki akaiwa mace. Sun zauna nan suna hiran yadda abin ya kasance haka lokacin daya kwanta ciwo yana processes din fitan kayan nasa ciwo ya kadashi sai wani abokin hurdanshi kirista ya dauki kayan ya boyr a can da suka isa. Nan kuma ankira a tura kudi habu yabi don kada kayan ya salwance yace ba kudi a hannusa a turo mai daga wajensu sun turu din kuma aka kama amfani dashi wajen magani. Har kudin sukai rauni koda habu ya samu zuwa kuma ba issasun kudin da zasubi kayan shi kuma baiyi dabaran karawa da nasa ba a samu kudin su fito don maganan su saiba a lokacin kan yana tausan dukiyan su kadai shida yazid ba a basu komai. Ke mai karatu kinsan harkan wani zumunta da zama a babban gida gidan yawa yana tara mabanbantan mutane masu banbancin ra,ayi sai a cakude ayi ta zaman tsama a tsakaninsu. Irin wanan halin shiya shafi habu donshi dan no case ne suna wanan maganan ya shafi dan uwashi har kowa nasa ya hau fushi tun a lokacin ya fita batun komai daya shafi J din saboda zuciya. Tunda ya bar gidan yake zirga zirgan neman kudin tafiya don dan kudin wajensa daya tsira dasu lokacin ya saka a wani aikin kuma don dai a samu a karu din kada akai kasa warwas. Saiga Allah yayi ikonsa kayan sun fito ba abinda ya samesu yayi sadaka ya godewa Allah yayi hamdallah har yamma basu da labari don ko mama bai fadawa abinda ke nan ba. Saida Aminu yaje gidan take samun labari da yake fadin wanan haihuwan maman zaria ya jawowa uncle alheri ta juyo tana kallon yaron shekeke don jin furucinsa. Amma kai yarone wani yaro yazo a sa,a yaron da zuwanshi duk ba alheri a cikinsa sai tsiya Jafaru dake cikin walwala auren yarinyar nan da samun cikinta ya zamowa mutane tsiya yanzu a gida. Don baka san yadda muke bane a baya kama sani ai kana zuwa kana gani ko bakazo ba uwarka daku kuna gani a tallen ku yanzu fa wakeci banda ita, ? itama din yanzu ina ma ya gansa balle waninta yaci din ? Amma dai tsohuwar nan uncle da dukiyansa ya fito zaki tsaya kina fadan hakan ya fito gidan ubanka mama ta jefawa yaron zagi. Haba mama wanan abinda kike fadi kan jaririn nan wallahi bai dace ba shi yaro ai Allah kadai yasan arzikinsa sai masu hassashe ke fara fahintar arzikin yaro tun yana karami. Amma kina fadan hakan iyayyensa sukaji ba zasuji dadi ba wallahi haba dai don Allah mama salima ke fadan hakan ga uwar tasu. Mummy wa zai tsaya saurarenta ma yaron da uncle ya bude baki ya kirashi da arziki sanadin haihuwanshi dukiyan uncle ya fito jiya kowa na murna da farin ciki ke kina kirawa yaro mugun abu ? Wai tsaya Aminu me kake fadine mama fa bata gane ba naji kamar kana son fada mata wani magana ita kuma bata gane hakan ba sai fada takeyi. Ai shine mummy jaki brain kega tsohuwar nan no school kayan uncle da suka bace a can kasan waje sune aka kirashin angani kowa na murna da farin ciki ita tana kirawa yaro tsiya. Gashi har anata zuwa mashi murna ana kiran yaro da arziki ke kuma kina nan kina zuba shirmen tsufa a gida baki gane ba kanin mu arzikine babba sanadinsa yazo muna da alheri. Aminun ta kurawa ido tana sauraren bayanin shi don a yanzu ta fahinci me yaron yake fada mata ga katobaran datayi game da yaron kala kala laifin uwarshi ya shafi dan jinjirin da baiji bai gani ba a duniya. Allahu Akbar kai Aminu kace min alherin Allah ya sauka muna a gida lalai wanan yaron arzikine tunda alheri ya baibayemu a yau. Salima ke fada cikin jin dadi tana nuna farinciki nisawa mai karfi mama tayi tana fadin lalai da ya zamo arziki kwana uku da haihuwanshi alheri yazowa mahaifinshi. Kai kuma duk kai min karya kam abuda bashi ba saina saba maka a gidan nan ta yaya abu irin haka zai samu amma mu bamu sani ba saikai zaka jiyo kazo fada muna shi. Shi yana fadin a,a ni banzo fada maki ba cewa nayi kanina arzkine don zuwamshi duniya alherine a garemu tunda ga irin hasken da muka gani a sanadinshi kai, arrrh mamata ta katseshi da fadan hakan. Salima kuma tace mama ai dole yace haka tunda yaga baki san alherin da ya samu ba amma ai tunda,zun yake zaune gidan nan bai fada ba. Tayi shiru na dan lokaci ta nisa take fadin abinda ban gane ba shine kudine masu yawa ya samu ko kuma wani aikine ya samu a kasan wajen ? Ban fada ba don ban sani ba nidai naga mutane suna zuwa kuma naji ana murna a gidanmu din nasan kuma alherine insha Allah. Ni baein tafi karki matsa min da tambaya ace kuma nice ba ruwana ban fadi komai ba tayi mai dakuwa ya fita yana dariya salima tasa mai kira ya dawo take fadin gida zaije ko wani waje a lokacin. Yake fada mata ba gida zaije ba tudun wada ya nufa yanzu mama ta aikeshi ya bada kudin abincin dabbobinta can ya nufa. Har yakai kofa yaji mama na fadin can kuma ka koma kaima ana kullawa dakai yanzu na fara tsoronka a rayuwata. Ya fita yana dariya baice da ita komai ba bai jima da fita ba yaya ya shigo ya samesu a waje suna magana mama na tambayan su abin arzikin meya samu Nusaiba tace bata da labari bayan wanan haihuwan wahalan da akai mashi. Haba dai haihuwar kuma itace wahala Asmau ta fada cikin nuna mamakin jin hakan a fili Nusaiban tace ban daiyi dake ba don Allah don ai nima bance kinyi dani ba kalman takice dai ke bukatan gyara gaskiya. Naga kowa na haihuwansa ai ba wanda aka aibantawa sai ita da babu ko ruwanta da kowa batama saka kanta a cikin duk abinda akeyi gidan nan ba. Kai ku rufa min baki don Allah ku wasu irin marasa hankaline wai baku da kishin juna saina abin banza ana maku kokari mijinku ya dawo hannun ku. Amma kuda baku raina abin fada nazo ina tambayan akan abinda da naji game da mijinku kun tsaya kuna min shirme yanzu . Yanzufa yaron nan Aminu yake fada min ta kwashe abinda sukayi da Aminu din ta fada masu abinda Aminun ya fada saida ta kai karshe Asmau tace gaskiyane dazun naji yana waya da yake cin abinci saidai ban kula dameya faru ba. To kunji abinda ke nan Saiba ta tareta da fadin yanzu shine bai iya fada muna ba koke mama saidai Aminu yaji a wajen wacan yarinyar yazo nan ya fada. Ke nan mu dai duk bamu da amfani yanzu idonsa gaba daya ya rufe akan wanan yarinyar ita kadai yake dauka a matsayin mace ke nan ? Har yana kiran danshi da arziki ko mu ke nan namu yayan ba arziki suke ba shiyasa bai damu dasu ba ko sai yanzune aka haifa mai dan gwal. To ni dai banga wani abu cikin zancen nan ba tunda abin nan in an samu kowa zai amfana dashi ai Asmau take fada ta juya zuwa kitchen duba girkinta lokacin ya shigo ya samu mama da saiba din a tsaye. Kallo daya yai masu ya fahinci wani abu na faruwa ya dai bude baki yana fadin sannu da gida mama lafiya dai na ganku haka tsaye. Ai dole ka ganmu nan Malam tunda har alheri na iya samunka ka boye muna saidai muji a wajen wace ka maryar mata yanzu ? Menene kuma akayi mama yake tambayanta cikin mamaki tace yanzun har wani abu zai iya samunka sai dai inji ga ahanun talla Malam ? Yaron nan Aminu yazo yake fada min wani zance dazun shine abin yake ban mamaki nake zance da matanka ko sun sani ? Meya fada maki kuma zancen wai wani aiki ko kaya yake fadi ni bam dai gane zamcen ba gaskiya don kasan haka yake kamar shu,umi wani lokaci. A,a mama yake dai gyara maki zance amma ai Aminu bai zo don ya fada maki maganan ba da kike irin maganganunkine fa yace shi kam kanninsa arziki aka haifan masu yake kora maki maganan salima ce data fito a cikin shiri ta samu suna zancen take fadin haka. Wai zancen kayana eeh anga kayana da akace sun bace wani abokina ya rike a wajensa dama kada su salwanta shine yanzu da yaji naji sauki ya fito min dasu ya kirani. Yanzu na gama shiri gobe nake son zuwa cika wasu bayanai don ina son inbi kayan idan angama sha,anin sunan nan da za ayi. Haba malam zancen nan baiyi ba badon yaron nan ba kilama ba zamuji ba ina zai fada kuwa mama tunda ba dole bane sai mun sani ai ba dai wa yanda yake son su sani sun sani ba. Ashe kin gane nufina wanda zasuyi min addua da fatan alheri suna fadawa don nasan ko banza suna farin ciki da samuna ko rashi. Zata fara masa haushi ya dakatar da ita da fadin kina sake fadin tak wajen sai kin bar gida bari na har abada kuwa in kuma kin dauka karya nakeyi ki tanka a yanzu din ? Shiru tayi tana mazurai da ido ta kasa magana ya juya ya dubi mama kamar zsiyi magana sai kuma ya fasa ya shige ciki zuwa dakinsa. Barshi kada ki tanka mashi don baya cikin hankalinsa yanzu komai yana iya faru dama haka akeso to ki kyaleshi. Salima ta kawar da zancen da fadin mama ni zan je kasuwa in dubu wani yadi da nakeso bata bata amsa ba ta juya ta tafi. ZAINAB IDRIS MAKAWA [6/9, 06:52] Aisha Srtr Mt: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 9️⃣5️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Yar uwa saidai ince Alhamdullahi masha Allah don abubuwa sun kankama cikin dan kankanin lokaci abinda ake fatan samu a rayuwa an sameshi don kuwa tafiyan nan da yaya ya samu yayi ba karamin alheri ya jawowa rayuwan mu ba sosai mussanman mashi dani. Don abinda yasa nace ni anyi sunan moh,d a cikin walwala da dadin rai anci ansha anyi alheri kuma baby ya samu alheri wanda zance a sanadinsa na samu hakan . Ubangiji Allah ya tsallakeni daga kaidin mama hassada ko bakin cikine ko kiyayya da ake min kasancewa da yaya ya zamo min taki a rayuwa lokacin haihuwan dan nan. Don ba karamin alheri na samu ba ga haihuwan dan da mama da kishiya suka sare min gwiwa tun a cikinsa ba abinda na samune farin cikina ba sai irin yadda kowa ya dauki dan zai furta masha Allah wanan photocopy ne kawai na Jafar da mutane ke furta a bakinsu don dan tun yana karami ubansane sak ya kwaso a kamanninsa. Ga kyauta ta inda ban zata ba da yake shigo mun in kuma an kawo din uban yace a ban nice na wahala ai na rike ba kamar yadda muka soma zaman asibiti ba a takure yana karba din a lokacin. Ni dai banda tacewa ina zaune mama ke fada min na dauki duk wani abinda zan dauka don ba a nan za ayi taron suna ba can gida zamu tafi ayi taron don mama tace mu dawo nan ayi taro a gabanta. Don haka tun daren suna muka dawo nan gidasu inda matanshi dasu iya da mama suke zama a gaban mama a part din iya muka zauna. Na samu salima ta gyara wajen tsab tsohon dakina a nan akai min masauki dani dasu mama da Biba tun kan muzo saida mama ta gargadeni akam koma meye manufar mama in daure inyi hakkuri kada in nuna hakan ya bata min rai don Allah. Nidai kawai murmushi nayi bance komai ba tunda gidan ba bako na bane ai duk wani abu da nasan cewa zan bukata a lokacin na dauki ba saj na tsaya nema ba a nan din. Don haka koda ya iso a nan ya samemu don tun yana can ta kirashi ta gaya mashi umurninta haka yasa daya iso ya nufo nan din ashe saida ya biya can ya aje duk wani abu da baison ya kawo masa fitina kafin ya iso nan din ya samemu don tunda ya tafi bai dawi ba sai a daren sunan komai a waya aka shirya yadda za ayisa a taron dashi. Ina zaune ina bawa yaro nono mama tana zaune kasa tana cin abinci muna hira mukaji muryanshi suna gaisawa da iya a falo ya gama ya shigo suka fara gaisawa da mama har yake tambayanta ba dai matsalan komai ko a nan ? Ai ba a rasaba yanzu dai ai gashi an kwaso mata maijegon an kawo mata bari muga iya gudunta kuma dubu kam lamarinta sai addu,a gaskiya. Kibar yarinyar nan ta zauna dakinta ayi suna kin kafe sai ta dawo gudan nan agabanki nan ayi komai ko anyi nan gabata zata iya hana komaine ni ban sani ba ? Ba komai iya gara da aka dawo din nan zaifi sakewama don can karshe a bata mata kayanta da sauran abubuwa ba daida anyi suna gobe saita koma ba ? Akace maka nifa nasan dubu nasanta sarai yanzu zata iya cewa kuma sai a bari har wani lokaci sam iya hakan ya zama takurawa ai idan anyi suna su koma can kawai zaifi nan banda tsegumi me zata zaunayi kuma ? Daga kofa mama data mike ta fita ta saka masu baki tana fadin tunda anyi suna me kuma za a tsayayi nan kuma ta koma dakinta kawai mana tunda ba wani wanka irin na da can yaran yanzu keyi ba ai. Shina gani mama an daice sai tazo nan anyi suna tunda nan kowa yake anzo gobe da yamma idan an watse zan mayar dasu gida insha Allahu. Ya gama dasu ya shigo muka gaisa nan yake tambayan lafiyan mu dana yaro nace Alhamdullahi ba inda ke maki ciwo kuma yanzu ko ya tambaya nace naji sauki sosai ai. An kawo dinkunan naki nace ehh tun jiya anty salma ta ba driver Aminu ya karbo a gareji good ina hanya na tuna wallahi na sake fadan ankawo ai. Ya dan tsaya mukai hira kafin yai muna saida safe ya fita don gidan akwai baki da zasu kwana ga yaya barakha da sukazo daga zamfara ita da kawarta. Wai dan shigan da yayi ya jima hakan ashe ya zamo laifi kuma wai anshiga hakkin madam Saiba saida sukai fadan hakan a cikin daren nam dashi yayi mata tas . Don harda cewa tayi ana tauyesu ana nuna masu banbamci ga komai yazoyi saiya nuna bambamci a kaina ya fifitani dasu don me zai yanka saniya a hada wajen bukin. Nan yace koda sunan Buhari ban yanka shanu ba ko wanan ne zakiwa bakinciki kuma koka yanka ai baikai wanan girma ba yake fadin. Ooh ashe ke diyar sarkin fawane ban sani ba har kin fita kin duba shanun kinga wanan yafi girma ko to komai da sa,anshi yake zuwa ina dashine yasa na sayi babba. Ai Allah yana ganinka duk zaluncin da kakeyi da fifitata akan shi kuma zai saka muna wallahi tunda haihuwa ai baifi haihuwa ba ? Wanan yakawo masu fada sosai ya gama ya shige dakinshi don akwai gajiya a jikin yasa ya rufo dakin da key ya kwanta bayan ya gama komai don ko abinci ita mai fadan bata aje mashi ba. Koda ta fahinci ya kargame kofan dakinsa hakan ya kara bankata mata rai kuma dakyat taga safiya a ranan ba abinda ke damun ta banda irin yadda labari yazo masu cewa katon shanun da jafaru ya yanka a shagalin. Akan shagalin sunan da sukaiwa ikirari da farko haihun rashi saiga ubangiji ya sauya abin a lokaci gashi yaya Auwalne jagoran abin ba wanda ya isa ya kawo mai raini akan zancen aikin da akeyi din. Kamar yadda jafar yace ayi da naman hakan akayi kowa don an rabawa yan unguwansu makwabta na kusa dasu sadaka kana ya aika gida gida dukka tan uwa dake cikin gari asa albarka. Kafin abinda ya rage ya aiko da wanda zayi aikin shagalin dashi nan gidan mama sai abin ya bakantawa mama rai sosai don me Auwal yayi bugun gaba da abin danta haka bayan gasu ga tan uwasa zai shige masu gaba. Allah ya taimaka yaya barakha ta iso lokacin ita ke fadin mamanmu yaya Auwal nefa wallahi kina cewa wani abu yanzun nan duniya zatajiku dashi. Gara ki kama bakinki tunda shine a matsayin babanmu a yanzu shine babba kowa na bashi girman shi yau don danki ya yanka shanu yaya Auwal ya raba zakice baki yarda ba da hukuncinshi. Aishi jafar yasan me yakeyi da yake sakasu gaba a komai nasa mutanen nan duk da yan ubanci da adawan da suke nunawa a garemu basu yarda sun nuna cewa muba yan uwansu bane. Komai namu ya tashi suna gaba sunayj gwargwado yadda duk wani dan uwa zai tsaya yayima a cikin gata tanzu akan wanan abin saiki nuna ke baki yarda ba. Ke kuma Nusaiba zan fada maki wani magana da baki sani ba akan yan uwanmu uban mu daya dasu dukkan mu kuma a tare kika zo kika samemu muna zumuncin mu. Har idan ba zakiba mama shawaran alheri akansu ba to don Allah ina tokonki da kiyi shiru ki daina kawo mata tsegumi tunda kinsan tana daukan zancenki kada ki hadamu fada da yan uwan mu don Allah ? Ubanmu ya mutu ya barmu a tare dasu kada kiyi sanafin raba wanan zumuncin namu don kin zama mai yukan yanke zumunta ke ? Nina gane a yanzu tunda kika shigo gidan nan lamarin mama ga baki daya ya sauya wallahi a,a anty barakha kada kiga laifina mana don Allah ? Kafa biyu da kayan ciki fa aka kawo gidan nan ba dole inyi magana ba ace an yanke shanu wanan kadai za a kawo muna ayi komai dashi ? Kuyi amfani da iya abinda kuka gani mana wai tsaya ma in tambayeki kokin manta da bakece mai haihuwan ba waib? Don ita data sha wahala ta haifi danta inma korafi itace ya kamata ace ta fito tayi wanan tsegumin baku dai da yunwan wani nama ko wani dangin abinci a cikin gidan nan to ki bari ayi taron nan lafiya don Allah yadda ya tsara abinsa a tafi a hakan yafi ? Gaskiyane dai baku so ni tsoron Auwal nake ji baby bani tsoron Auwal balle uwarsa karane kawai nake masu tunda suna muna suma . Ni dai na fada maku kada ayi wanan zance in kuma kince sai kinyi zakiga abinda zai biyo bayan hakan muna dai zaune kalau dasu don Allah mama kada abin duniya ya rufe maki ido kuma yanzu. Wallahi maman mu yanzu ya kamata ki natsu girma ya kama komu da kuka haifa muna kawar da idon mu ga abinda mukasan ba hirminmu bane a yanzu don Allah ki barbin ta yaran nan suna bata maki suna. Ita mai haihuwan haka kuka sakata gaba da abinda ta haifa dakinkine fa ya ajeta itama ba wani bare ba wace tafita gidan nan yadda kowa yazo aure haka itama tazo aure danki don Allah mama ki bari ayi wanan abin lafiya a watse lafiya kada aji bakinki ga komai don Allah ? Kin daice sai nan za ayi suna yaran nan basuki ba sunzo nan din babu jayayyan komai don haka kada inji bakinki ga komai don Allah ? Wanan yasa dole ta kyale batayi fada ba da Saiba ta zugata wai an kwashe nama an kawo masu kadan a gidansu tunda so tayi akawo shanun gaba daya a nan gidan. Yaya barakha kuma a yanzu nagama da ita tana bayana akan diyanta don da sukazo bukin saratu suka kwana gidana na kwaso duk tsofin kayana na basu ga Aminu dake karatunshi yanzu ta sanadina idan ba butulu ba ai hakan dole ta soni ? Washegari kuma tunda safe da nayi wanka na saka wasu atamfar super cikin wanda da akayo min a Abuja mama ta hada min shayi mai zafi taban ina sha. Lokacin anty barakha tashigo take labartawa iya abinda sukayi da uwar da fadan Jafar da nusaiba din a dare har take fadin ta fahinci saiba bata bar uwar a banza ba. Maman tudu ta tsoma baki da fadin Dubu ko banza bata bincke abinda aka fada mata dashi take amfani haka take tun farko Alh yayi mata fadan hakan bata daina ba. Saukina a yanzu ke Amina da yake dubu tana shakkunki har yanzu iya ta fada nagode wa Allah daya barku tare da bansan iya inda abin nan na dubu zai tsaya ba. Yarinya karama tana amfani da ita don ciwa manufarta akan yayanta amma dubu bata gane ba tana ganin hakan sone bata san tana dafa kanta bane da kanta yarinyar nan tana cikin silar tabarbarewan komai na gidan nan a yanzu. Shi yayi sallama ya shigo yadda ya samesu ya bashi mamaki yaya barakha bata boye mashi ba ta labarta mashi komai yace ta barshi kawai da ita yasan komai ai. Ya shigo mun gaisa dashi ya tambayi jiki ya dan jima ya fita yana fita kai tsaye ya nufi wajen masu aiki girki ana gaisawa yake tambayan ina naman da aka kawo aka fito mai da dan nama kadan da aka soya. Ina naman kafa biyu da baya barakha tace matanka suka karba aiba mu suka bawa ba Asmau ya nema yake tambaya akan me suka rike komai a hannunsu ga yaya barakha a gari ? Ni nikan ban san komai ba na daiga ana yankan nama a gidan nan amma ba wanda tace dani komai ta fada a cikin sanyi murya. Ina Nusaiba ta fito tana fadin gata yace don me kika karbi komai da yaya ya aiko dashi ga yaya barakha gari ? Don me na karba fa kace don na karba shine abin magana kuma eeh ya fada a gadarance sai tace to ita yaya barakhan ta kawo karana kome ? Ke ina kayan suke nake tambaya ba dogon magana ba ta kawo karanki har kin kai wanan matsayin da zakiwa yayata abinda zata kawo karanki a wajena ? Ban aje wanan matar datafi karfina har ta wullakanta min yan uwaba tukun nazo ina tambayan nama aka nuna min dan wani abu can a kasan kwano ? Shina bayar ta fada a cikin gadara ki fito da sauran yanzun nan to idan na fito dashi mufa ta fada baki sake cikin namaki yace kufa ? Kufa name donki na yanka naman nan ko don sadaka ke koke kika haihu a gidan nan ba zaki min iko da abina ba tunda ina da yan uwa fito dashi nace . Tayi tsaye ya juya ya nufi part dinsu din tare da kiran Asmau tabi bayanshi ita Saiban ta bisu a can fada ya turnike yayu mata dukan tsiya a gaban mutane aka fito da naman a cikin wani jan kula data shake da nama har bai rufuwa. Ga iyayyen suna magana sai zagi take aika mashi da cin mutunci ya kyale har ya juya take fadan ba dole kayi min cin mutunci ba tunda matarka ta zugoka ? Dama wani dane ba dan ,,,,,,,, ya juyo gareta kamar wani tsohon zaki yasa bata karasa ba yace karasa mana tayi shiru yace ke Nusaiba kije gidan ku don Allah na dai sakeki wallahi. Dama nasan shirinkine kika takura sai ayi suna a nan don kiyi muna tozarcin da kika saba saboda mama dake kama maki kiyi min iya shegen da kike so tana sakeki wallahi. Salati aka dauka muna tsaye bakin window daga dakin da muna kallon duk abinda ke faruwa a gidan nida biba a hankali na juya zuwa bakin gado na zauna. Ba zance ga yanayin da nake ciki ba a lokacin shigowan mama yasa na dago take fadin sun sami abinda suke nema dama masu iya magana sunci idan zaka gina ramin mugunta ginashi ya zam gajere. Sunyi hakan don su bakantawa mutane rai yanzu gashi abin ya juye a kansu ba komai bane na sani wanan abin shirine dama don kawai su bakanta baki su bata shirin ga nasu ya baci a yanzu. Ina dadi danka ya tsawata maka a gaban mutane dubu bata da hankali da har take kokarin batawa danta ta goyi bayan wata gashi a gaban kowa ya bata kunya yau. Fadan hakan yasa na fahinci bayan barin inda nake kallonsu wani abu ya faru kuma wai ashe mama cewa tayi ba inda Saiba zata udan yace ta bar masa gida saidai shiya bar gidan baki daya yaje inda aka tsafeshi ta sheda an tsafeshi din . Mama matukar kika hana saiba fita wanan karon zanko nuna an tsafeni din ya fada ya shige cikin part dinsu har ya shiga dakinshi ya fito ya kira Asmau tana zuwa yace ta fara tattara kayanta ta kalloshi yace zamu bar gidan nan ya juya ya shigaciki. Da wanan zance dai suka bata min plan fin sunan da sukeson raina ya baci sai gashi nasu ya bacisu yan garin mu da sukazo suna suka sauka wajen mama kaduba sun iso zuwa rana. Tare da tawagan mama har na debe rai da zuwan anty Salma sai gasu sun iso bayansu kadan naji dadin hakan sosai a lokacin. Muna tsaka da shagalin suna yan uwan saiba suka iso da tashin hankali yaya barakha ta tare zancen ita da yan uwansu suka fara fada a tsakaninsu ko leke yan uwana basu leko ba har sukaci suka sude saiga mama ta koma kuka don yadda yan uwanta ke zaginta da danta a gabanta sukace inma munafuncine mamace ta hada ai. Yanda da anty Nafisa suka shigo da girkin da akayi don yan uwana na kudi muka bayar don abincin yayi dadi sabodasu don haka ba wanda yasan da hakan sai lokacin da suka shigo da manyan kulolin abincin. A nan kuma sai hakan yaso zama laifi yaso zama don saiga sakon mama wai naki debo abincin inbawa mutanen cikin gida. Anyi ba dadi da hakan ya dagawa yan uwana hankali har suke fadin zasu daukeni zuwa gida shan ruwan zafi tunda nan din ba kwanciyan hankali. Tun basu fitar da zancen ba maman tudu da suka fara fadawa ta hanasu yin maganan acewanta irin hakan a yanzu tsegumi yake kawowa su barni a dakina dana haihu ai haiwan tiyatane ba wani wankan jego zanyi da ruwa masu mugun zafi ba. Magananta yasa suka kyale zancen da wai kona koma kaduna ko can gidan camerro zan koma basu kwana ba a ranan suka koma kaduna anty salma kuma ta nufi Abuja. Munso brin gidan tun a ranan amma wai dare yayi mu bari sai washegari hakan yasa muka kara kwana amma tun cikin daren mama ta tattara komai da muka samu aka kai wancan gidan da muke. Nidai ban san don me tayi hakan ba don haka ido na zuba mata don ta fini sanin waye mama haka kuma kayan suna irin wanda akance daga miji ko yan uwansa bai fitar ba a nan bayani kawai yayi min cewa kayan suna gida ya aje min idan yan uwana suna son gani suje can gidan wanan yasa kafin su tafi Yanda ta kaisu suga kayan daga can suka tafi sam ba a shigo da kayan gidan ba. Koda daren sun kara fitina mu dai mun kwanta don ko mama bata fita ba har iya don mun rufe part din mu don gajiya. Washe gari kuma sallah sukayi mama tace azo a kaini gida don kada kayan da iyayyena sukazo dashi ya lalace ban nan gida duk da su anty Nafisa sun koma da biba da Aminu. Ko a lokacin duk da safen na suna kan rigima dai an taru a part din mama ana faman shari,a muka bar 'masu gidan muka dawo ba kuma zance mama ta shigo ta duba moh,d ba har muka bar gidan. ZAINAB IDRIS MAKAWA [6/9, 22:18] Aisha Srtr Mt: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 9️⃣6️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Tunda na dawo gidana ba zance hankalina ya kwanta ba don abubuwan da suka faru a lokacin nasan gidan aure wani jami,ane babba na daukan darasin ya mace. Don ba lalai bane kiyi dacen gidan miji mai kama da naku gidan da kika baro dole akwai banbancin ra,ayi dana tafiyar da rayuwa duk da yadda muke yan daji ra,ayin iyayyen dana saba zama dasu ya fita daban dana nan da yanzu nake rayuwa. Abinda ya faru babban darasine a kaina dama ke da nake ba labari yayi da kaddara ta sameki yar uwa fauwala lamarinki ga ubangiji ki bar komai gareshi yana sane zai maki gata da fitar dake cikin kuncin da kike yar uwa. Kwarai kuwa nasa da saiba kadai zan samu matsala wace ke ikirarin cewa dan cikina a lokacin shege ne don ta hanyar haramun na haifeshi. Don haka nake dari darin zuwan baby duniya sai gashi duk abinda suka kitsa zasuyi mi na tozarci ya koma kansu yadda basu zataba ma don gashi sanadin hakan gadara da isa da izza yaja mata saki kan dan karamin abu. Ita kuma mama ta shiga tozarci duk a wanan ranan duk da mutane sunsan komai amma ita uwace ba a fito fili anyi mata zunde da nune yadda aka wuni yiwa saiba shi ba a ranan. Don kuwa sa ido da hana ruwa ido da kaskancin da suka kulla zasuyi yazo ya kare a kansu karshe su suka fada a wanan ramin na tozarcin da aka shirya yi min nida maman tudu da akace itace ke goya min baya take iza jafar yake kara haukacewa don ba itace ta haifeshi ba take hakan don koma bayansa. Na yarda nice dai ba,a kauna da Jafar don matsayina ko kimata baikai na zamo matarshi ba don ko Yanda duk da nasan mama bata wani kaunanta cin fuskan da ake min yanzu ita ba ai mata irinsa ba. Duk ina wanan tunanen ne a dakina kwance bayan zuwan salima gidan mu da kwana biyu da yin suna tazo take labarta muna zancen saratu. Saratu dai ba dadi ashe zaman gidan don tunda taje ake fitina da ita mutanen gidan sun hade mata kai ga miji ashe ba wani maishi ba dan karyane kawai yana amfani da kyan da Allah yayi mai yana tara mata. Ance uwargidansa kamar tafi kardinsa don shine saratun bata samu yadda take so ba a gidan don taso tayi iya shegen datakeyi a gida na nuna daukan kai. Ita kuma uwargida tace ai bata fisu ba aurosu akayi aurenta akayi don haka aiki daidai da kowa zatayishi a gidan tunda ba funsu tayi ba. Taso nuna batayi miji kuma yabi bayan iyayyensa da matashi ya fara juya mata baya shine wai washegarin dawowan mu ta bugo waya tana kuka cewa ita tagaji wallahi bata iya wanan auren ? Don a rana mutum baida huta ko yaushe cikin aiki yake yana aikin wahala ita da bata da da amma tana bautan diya da wahala akan yayan wasu . Hankalin mama ya tashi sosai tana rarashin saratu din akan ta zauna zataga yan uwanta ta fada masu halinda ake ciki kada ta dawo tayi hakkuri ta zauna dai har ta jisu. Gashi kuma tun ranan sunan Amir da wanan fitinan ya faru yaya J bai zaunu a gida ba take fadin kamar akwai wani abu da yakeyi wanda yasa gaba a yanzu don sai dare yake shigowa gidan. Maman tudu tace me kuwa yasa a gaba kila don yarinyar nan da dubu taki barin ta fita yake hakan ai rabu da namiji idan ta tsani mace garama ke mace ki tsaneshi da sauki akan namiji ya tsaneki salima Allah dai ya kyauta abune bai faduwa kawai amma dubu tana bukatan addua sosai. Bandashi yarinya na dakinta kice sai ta koma gabanku anyi suna kinga komai yanzu da taje din riban mai hakan ya haifar don Allah ? A rayuwa na tsani sa ido da hassada ga bawa don duk ma hassada bai taba cigaba kullum a baya yake bai taba ganin daidai a rayuwanshi. Salima tace tun ranan da na fito mama ke fada min wai can Rahama zata dawo ayi suna nake tambayan saboda me tace saboda ita ta haifi danta ba zata yarda azo nan a juya mata shiba. Duk abinda za ayi azo gabanta ayishi nace a,a mama ki barsu don Allah ta dura min zagi yasa kikaga na kama bakina ban kara magana ba. Tun a lokacin nasan duk shirin Nusaibace hakan ita ta zauna da saratu suka shiryawa mama hakan ta hau gashi a karshe yadda ta kaya ai. Yanzu dai mama tace ba inda zata shi kuma yaya ko kallo bata isheshi ba tunda ya sake mama tace aita zauna zaman dubu a gidan tunda tace ba inda zata ko ? Wanan hiran tasune ya tsaya min a rai yanzu ke nan Saratu tana can cikin wani hali amma mama take kokarin ganin ni saita sakani a matsala kota halin kaka a idon duniya. Haka da take min nakayi tunanen in bar mata danta kawai in tafi amma kuma ina yi tunane shi jafar din a kullum hanyar kyautata min yake bida a tsakanin mu sai in ji wani iri a raina don banda laifin da zan fada ince yayi min a yanzu. A cikin jegon na fara yanke shawaran da anty salma taban na fara sana,a kada in zauna zaman housewife in neme abinyi ko a gidane tunda ta fahinci rayuwan mazan mu rayuwan mazan hausawane a kulle mace a gida ana juya ta kawai sai kin nema a miji. Zannuwan gado ta ban shawara na dinga sarawo masu kananan kudi don haka na zauna na lissafa yan kudin dake hannuna naga sun kai dari biyar a lokacin. Donshi na tura mata a saro min zannuwan gadon a turo min dasu duk da ba wani shiga mutane nakeyi ba hakan zai min wuya amma anty Nafisa tace min akwai matar da zata hadani da ita indan an kawo min. Sai bayan dana bada kudin daya shigo nake fada mai abinda nake son yi yace min nayi tunane kuwa nida ba fita nakeyi ba ina zan saida su ? Dana fada mai da ban tura kudin ba sai ya bayar a kasuwa a dinga juya min irin na Salima nace a,a nafison in juya abina da kaina don gudun zargin mahaifiyarshi da abokan zamana. Sati daya da bada kudin sako ya iso min wanda naji dadin hakan tun daga can anyi packed dinsu an saka a leda an mana kudin ko wani a jikinsa. Washegari Anty Nafisa tazo ta kwasa ta tafi dasu bansan ya akayi ba salima taje tagani sai gashi ta zabi har kwara biyar a ciki tazo tana min labari wai ta gida tabiyo taga Nafisa na sayar dasu ta kwaso. Sunyib kyau don yadinsu masu laushine sosai suna da quality ni kaina na zabawa yaya guda biyu a ciki na bata kudinsu. Anan take bamu labarin cewa Saiba tana nan taki tafiya wai saki biyune tsakaninsu da yaya don haka ba zata tafi ba nayi magana dashi yace hakane amma zamanta bada miyau bakinsa ba zaima dauke Asmau daga gidanne kwanan nan. Ina zasu koma na tambaya sai tace ke ki barsu kawai ba haka ya habu yayi a lokacin ba sai kawai gani mukayi suna shirin tashi suka bar gidan. Kai ranan naga tashin hankali wajen mama kamar zatayi hauka har gobe tana fadin hakan idan zance ya tashi take fada balle ace yau yaya j shima ya bar gidan nan ai kila mama sai ta kusa bugawa. Kinsan me Rahama nace a,a anty wallahi ni abin mama yana ban mamaki yau idan ance meye laifin ku dasu yaya ba zatace ga aunihin abinda akai mata. Shiyasa nake ganin laifin saratu don harda saratu cikin mayar da mama hakan itace mai zuwa ta fada mata karya da gaskiya kan mutum yanzu ai gata can tana girban abinda tayi amma mama bata son a fadi hakan. A nan na fahinci saratu tana cikin wani hali a gidan aurenta haka kuma mama na kokrin boye hakan saidai salima din ban sani ba koni kadai take fadawa zancen oho ? A nan takai magariba bayan munyi sallah ta nufi gida mama tana ta fada da ita akan tayi dare haka da subar barin dare nayi masu a waje. Nayi mamakin rashin shigowanshi ranan har goma na dare wai gashi tun safe daya shigo bai dawo ba hakan ba dabu,ansa bane sau ukku yake ziyartan mu a rana idan yana gari. Ashe a ranan suka kwashe ana can ana rikici a gidan don yana komawa yaje da mota yacewa Asmau ta fitar da duk a binda zata dauka a gidan. Ya wuce wurin mama ya sameta tare da iya suna magana kan saratu nan ya shigo ya gaidasu yake fadin to mama yau nake son Asmau ta koma wancan gidam dana gina guda. Cikin mamaki mama din ta dago tana fadin gida wani gida yace aina jima ina gina sa an gama komai dama can kusa da habune da yazid wajen kamar unguwa dayane dai zance. Jafar ni kake fadawa ka gina gida zaka dauki matarka daga gudan nan zuwa can kan dan zancen da akayi ya wuce kai yana a ranka ashe har yanzu ? Wani zance kuma ni ai nagama wanan maganan a bamgarena dama ina da niyar hakan kudine da bandashi lokacin ban gama saka wasu abubuwa ba yanzu kuma na saka shine zasu tare a ciki. To ban yarda ba ba inda zaku idan kaga Habu yayi na kyaleshi kai ba zan kyaleka ba Jafar don baku isa kuce zaku raba gida dani ba matukar ina raye. Kamar ya mama nan din fa karki manta gidan gadon mune namu dukka da yan uwana can ko nawane dana ginasa da kudina don iyalina . Kwarai kuwa shi muke fata hakan Allah ya kara arziki da rayuwa mai amfani yasa afi hakan kowa na fatan hakan a rayuwansa da zuri,ansa baki da hujan cewa ba zai daga daga nan ba yanzu dubu. Duk yadda akeson biyayya dan nan jafaru yayi maki shi a rayuwansa don haka ban son in ji ko in gani cewa kin kara tofa mashi kalman baki yarda ba. Da bakin ki nan gaban mutane gaban kowa kikace saidai ya bar gidashi amma ba sarakuwarki ba yar so a gareki yace ya yarda yanzu zakice kuma bai isa ba ? To iya ana son a nuna min iyakata ke nan da ban isa dasu ba yanzu tunda sun girma suna ganin sun kai iyan tace na dai fada maki kar inji kar in gani duk kika tofa wani kalma akan zance irinsa zai biyo bayan ki dubu. Tabbas idan naji kona gani kinsan zancen kema don haihuwa baifi haihuwa ba dubu kin tauye yaran nan dayawa dubu tun suna maki biyayya yadda akeso har yanzu yakai sun daina suna ra,ayin kansu tunda sunkai mutane suma ? Kuka sosai mama keyi saida iya tace tashi kaje Allah yasa ku shiga a sa,a nina taba ganin haka danka ya samu karuwa irin haka ke mahaifiya kice ba a isa ba ? Yau ko kango mutum yana son ace ga nasa balle ke da Allah ubangiji ya yayi maki Rahama ya fida diyan ki cikin yan uba kece kuma da kanki kike son ki bata abinki yanzu da hannun ki ? Iya ba hakana bane koda nace su zauna nan don hadin kansune ba don komai ba amma tunda hakane ai shike nan suje Allah ya bada sa,a . Ya daga yana fadin mama kiyi hakkuri ni dama ina da niyar hakan wallahi ba don zancen nan nayi haka ba tsawa iya tayi mai tana fadin jeka nace ubangiji Allah ya tsare mun koma godewa Allah daya nuna muna hakan gareku tun muna raye. Yau idan mahaifinku yana rayene akwai wanda ya isa yayi maku wanan rayuwan tauyewan da ake maku yanzu komai yaro zaiyi naci gaba sai a hanasu ? Haka ya mike yabar part din ya samu samari nata daukan kaya suna fita dashi yace ke banda tarkace ba zan yarda yadda kuka bata nan ku bata can ba yanzu iya kayan amfaninki dana yara kadai zaku dauka wanan tarkacen duk ku barsu nan. Yayi mamakin rashin ganin Saiba da baiyi ba ashe ta fita zuwa unguwa har aka gama bata dawo ba sai bayan tafiyansu kadan ta shigo gidan tun a waje take ganin tarkace hakan ya bata mamaki ta karasa ciki da mamaki a fuskanta zuwa cikin gidan. Ba kowa a waje nan ma tayi mamakin ganin falin a hargitse haka tadai shiga ta aje kayanta ta fito tana kiran Asmau shiru da taji ta koma kiran yara shima shiru hannun yarta ta kama zuwa part din mama. Mace kadai a lokacin gidan Salima tana gidan mu iya kuma tana nata wajen taki fitowa tunda ta gama magananta a lokacin. Mama lafiya ina Asmau na dawo na samu waje a hargitse haka wani abu akayine bayana kuma ban sani ba ? Da kyat mama ta iya bude baki tace Nisaiba ni Jafar zai nunawa iyakata da nace ya bar gidan ba zaki bari ba shine yau ya dauki Asmau wai ashe ya gina gida tun tuni ban sani ba ? Kam uban nan ya dauke tafa mama wallahi sunyi kadan dagashi har ita sunyi kadan wallahi duk inda suka koma nima zan samesu yau din nan me jafar yake nufi dani . Harta juya zata tafi sai kuma ta juyo tana fadin koma meye mama laifinkine na nuna maku so da kauna an hada kai dake an cuce yan uwana basu fadi karya ba kece ke amfani dani bani ba ? Nisaiba kanki daya kuwa tace kwarai kuwa nagane kinyi amfani danine don wata manufa taki ta daban mudfin aure na ya mutu mu zuba auren kowa ma zai mutu wallahi. Ta juya zata fita suka hade da kawu kamar zata bangajeshi ya kauce gefe daya ya bata waje ta shige shi ya bita da kallo yana mamakinta. Kawu ya karasa falon yana fadin wai gidan nan lafiya meke faruwa naga duk gidan a hargitse yaya iso dolene kaga gidan haka hargitse yaran nan sun gama dani kuma iya ta hanani daukan mataki ? Meya faru ni baki fada min kina kawo min zancen iya to zance iya mana wai Jafarne ya dauki matarsa uwargidan suka bargidan nan kamar yadda habu yayi a baya ? Suka bargida ya koma ina gidan haya ko can inda ya aje wanan yarinyar ya kaisu aida canne ban mamaki haka yaya ? Gidafa jafar ya gina ban sani ba kamar yadda Habu yayi min sai daukan matarshi su tare kawai naji zanyi magana iya tace ban isa ba ina na fito yanzu yaya abinda iya keyi min kan yaran nan yayi daidai ke nan don Allah ? Zaudowa yayi zuwa bakin kujera ya dubi yar uwar tashi yace yanzu shi jafar yana da kudin gina gida shine ya bari dan uwansa mara mutunci na kokarin daureni gidan yari ! Haba yaya kasan bakinsu daya na yarda bakin su daya shike nan ni Dauda yaran nab duk sun bata min shiri kaiya bukata bai biya tako ina je nan ? Bukatan me kuma yaya kedai bari Dubu bar zancen kawai shike nan ai komai ya tafi yanzu bar wanan zancen kuma yanzu ina jafar yake ? Sun kwashe ta fada a sayayye cikin bacin rai sun kwashe fa to ita wanan data fita yanzu kamar zata bangajeni fa ? Ai kasan ya furta saki a tsakaninsu nace ta zauna shine yabar min ita nan baije da ita ba yanzu ta dawo take masifa kasan bata da kwanciyar hankalin fahinta. Naso ince ki rabu da ita ki kama wacan yar fulanin muyi makami da ita a gareshi yanzu tunda wanan din ta koma bata da fada wajenshi a yanzu bata da sauran amfani a garemu. Muryan wa nakeji kamar na dauda muryan iya ya katse masu magana iya nine shigowana ke nan yanzu nake zance naje na gaida ke ai. A,a ina zaka gaidani kana nan kuna kulla shu,umancin naku da bansan sai yaushe zakuyi hankali ku daina bibiyan yaran nan ba tunda ita uwarsu ka gama da ita dakai da matarka. Iya mungama da ita kwarai kuwa ko kana zaton ban sani ba ita din yar uwarkace dauda duk surukullen da kaiwa dubu ya hau kanta yar uwarkace dai kanka kayiwa. Godiyana ga Allah dana yaran nan baiyi tasiri ba kun halakata kun koma kuna neman halaka mata diya koka dauka duk dadewan nan ban sani bane ? Nasan komai dauda ina kuma kai kukana ga Allah ganin na yaran baiyi tasiri ba yasa kaga na sakama ido kuna ta bace nasan mai hansatu takewa kuka lokacin daka kara mata kishiya ai ? Shiru yayi iya ta zuba ta zuba yana zaune baice komai ta kare da fadin dauda na dade da kumsan bakin cikin ka a zuciyana sai ince ni banga amfanin haihuwan da namiji a rayuwata ba don hansatu ta shiga ta fita ta rabaka da kowa naka a duniyan nan. Ni kuma na dade ina kai kukana ga ubangiji Allah ina fada mashi damuwata akanku har gashi yau kana fada da bakinka komai yana da iyaka banda ikon Allah da manzonsa. Tana fadan hakan ta juya ta fice takai kofa take fadin Allah yasa yaron nan yazidu ya daureka a kotun nan dan makulin ya bace ka mutu can dan banza mara imani ka halaka kanka ka halaka yar uwarka saboda macen macen ma figgaga kamar hansatu wai daba gaba ba baya. Kun gani ai dakai da ita kaso diyan yar uwarka su tabade kamarka da Allah yafiku sai yabaku tambadadun diyan ku ya shirya mata nata. Tasa kai ta fita ta barshi yana hawaye sai mace da bata san kaiba take fadin ni iya fadan ta yakan ban mamaki wani lokaci bata barin mutane suji da abindake damunsu a rayuwa. ZAINAB IDRIS MAKAWA [6/11, 06:34] Aisha Srtr Mt: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 9️⃣7️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Tana kwance aka fara dukan kofan da karfi taki budewa sai maishi ya wuce taja tsuki tana gyara kwanciya. Ba,afi mintuna biyu ba taji bugun kofan dayafi na farko karfin kara a kunnenta hakan yasata magana tana fadin wai waye don Allah zai fasa min kunne ? Ke ki bude da wullakancin banza ke shige daki kin kyale mutane ana buga kofa konki ki bude jin muryan minjinsu yasa ta mike da kyar ta bude kofan dakin. Ya fado ciki kamar an turoshi daga waje yana fadin wane irin iskancina yasa kinka hitowa a dora girkin abin kari dake ? Ke shige daki keyi kwanciyanki kin mike kafa wa kika son ya dafa ya baki kici da kinkaki hitowa a dora girki ko wa at bawanki gidan ga ? Nagajine Habibi nagaji wallahi ke dakata min don Allah ke gaji ba aure kin kazo yi ba ke nan koso kike ki kwanta daki ki mike kafa a girka maki keko ki kwashi gara daga kwance ? Habibi nifa ban saba da irin haka ba a gidan mu wallahi ban girki sai naga dama kuma baifi gwango biyu muke girkawa ba sai taliya da indomei ko macaroni. Kina mace kika rakin girki ashe saratu baki shiryawa aure ba kin kayi an fada maki zuwa dai akai aita harkan gado baci waka baki abinci kina kwance ? Nifa habibi gaskiya ba zan iya ba don wallahi,,,, dakata min don Allah ba habibiba wallah habibu in kina hitowa kitai girki yara suna jin yunwa ki hito ? Wallahi ban iyawa ta kara fada tana juyawa yace haka kinkace baki iya girkin tace gaskiya indai wanan girkin gandune ba zan iya ba ? Wai baku hitowana kaje ka zauna kana rarashinta a daki kunyi bukui cikin daki wa zaku kawowa bulunkoto a nan ka shiga kana rarashinta akan ta hito wa kunka aje bawanku halan ? Duk yadda ya raya saratu taki fitowa dakin jin muryan uwargidansu da tayi a kofan ya kara bata haushi mata yar tsurut da shegen doka ga iya kissa da kisisina irin na mutanen hausa. In an barta sai tace itace uwar yan daudun duniyan nan kaf saboda marmadin ido da iya tafa hannu idan tana magana baki magana hannci magana ido magana. Bayan fitan mijin taji muryan uwargidan tasu da ake kira da nunu tana fadi a cikin fada taki hitowa ko to walle mu zuba da ita a gidan nan wa taka son ya girka mata taci ? Ko wa a bawanta gidan ga ta iya shigewa daki ta kwana da miji a girka mata yanzu aiki yazo kanta tace batayi asheko zakiga iskanci a gidan ga walle ? Ta mede baki tana zama bakin gadonta cikin takaici da dana sanin auren mansur da tayi inba don sulaiman daya taudareta yayi ta amfani da zuciyarta yaki aurenta ba a karshe da ina mansur zai ganta har ya kwasota zuwa nan ? Dama ance rabu da bakauye iskanci da duniyanci yana wurin bakauye tundai in yana ganin ya fara wayewa sai abin ya hade mashi da wawanci yayi ta abu ba fasali. Bata fito ba tana jin hayaniyan yan gidan har barci ya dauketa sai wajajen sha biyun rana da yunwa yacita ta fito don ta samu abinda zataci. Saidai ta kula duk dan data kira donta aikeshi sai yaro yaki zuwa don uwayensu sun gargadesu akan hakan sai wani saurayi ta samu maraji yaje ya kwaso mata indomei tazo ta sullala saman gas a kuryan daki taci. Jin kamshin indomei din da matan sukayi kuma yasa yan gulma samun uwargidansu suka fada mata ita kuma ta samu mijin da sababi duk ya rude irin matan nan ne dake kammala mazajensu sai abinda sukace gata dai bakauyace amma miji idan tana magana har rawa jikinsa keyi wajen bin umurninta. Shi kuma ya taso ya samu saratu din a daki da fada kan don me zata dora girkinta daban suba haka sukeyi a gidansu ba ta fito ayi aiki da ita yadda kowa ya fito a girka a zauna aci a cikin taro. Wanan halin yasa bata ko iya loma ukku da anfara zata mike tace ta koshi ita dan dama ranan da miji ke dakinta inyaci ya rage takan samu taci itama a lokacin. Ga wata rayuwa ta daban da sukeyi keda miji ke wajenki ba zakiyi girkiba a ranan sai wace miji bai dakinta itace zata girka abinci ta ciyar daku. Gashi kuma mata sunkai goma sha tara duk girkinsu a hafe yake mutum ukku ulku ke girki a rana su ciyar da gidan yadda suka tsara kuma komai da za ayi wajen uwargida ake karban komai itama hannun uwar miji zata karboshi. Irin wanan rayuwan na daban yasa zaman gidan ya karawa saratu kunci tayi tayi ta daure ta kasa hakan wata rana da dare bayan isha,i ta hada kayanta a dan karamin bag dinta makwabtansu takai ajiya. Washe gari ana fitowa sallah tayi kamar zata kewaya ban daki ta aje buta ta fice sai wanan gidan ta ari nikaf ta rufe fuska tana zuwa bakin titi ta samu mai acaba ya kaita tasha zuwa garin sokoto tashiga mota ta nufo sokoto inda zata samu motar zaria. Don tayi kiran mama don su kawo mata agaji ba abinda sukayi kullum magana dayace mama tace mata tayi hakkuri tana tafe an amma shiru. Allah ya gani tana son habibi shima haka amma yan uwansa da matansa sun bata masu shiri don a gaskiya idan tace zata daure tasan karshe zata halaka a wanan gidan. Don aiki kawai zai kasheta gashi bata saba hakan a gida mama tudu in tazo ko sukaje family house daniyar kwana biyu tankayi fada da mama tace ba aiwa diya mace wanan sakacin don ba,asan inda aure zaikai mace ba gashi ko bakinta ya kamata don ga inda aure ya kawota yanzu. Salima da tayi mutuwan tsaye don mamakin kalaman da take ji bakin kawu yasa ta koma da baya zuwa part din iya. Ta kwashe ta fadawa iya shine mafarin tasowan iya tazo ta samu kawu tayi mashi tas barci ta kasa kwanan ba haukan Nusaiba ya hanata barci a lokacin. Sai zancen da take ji yana fita bakin kawu din wanda da alama kuma uwarsu bata damu da hakan ba kamar ma bata gane manufarsa ba take gani. Allah Allah take gari ya waye taje ta samu yan uwanta ta labarta masu komai sai da tagama komai ta shirya batacewa kowa komai ba ta fita daga gidan . A waje ta ciro wayanta cikin jakka ta kira lanban yayanta tayi sa,a ya dauka yana fasin Salima yaya akayi ? Kana ina yaya gani nan zuwa wajen ka ya amsa da gani nan zanje gidan Rahama in dubasu lafiya dai ko ya tambaya ta amsa da yaya bari dai inzo akwai magana gaskiya. Ya shigo ke nan mama zata fita suka hadu a get Aminu zai rakata sarakuwarta ta haihu zata ganin jariri yace barin kaiki mama tace a,a malam kaje ku gaisa da iyalinka tun jiya ta damu bata jika ba jeka na yafe maka harga Allah ga Aminu nan zai rakani in samu mota. Hakan yasa basuje tare ba lokacin ya shigo ina falo don ban koma ciki ba yake sallama na amsa tare da gaidashi yake fadin kun jini shiru ko jiya? A kasalance na juyo ina fadin nina dauka baka garine ai don baka hakan ya kai zaune bayan yagamawa yaron dake bayan biba yana barci wasa ya juyo yana fadin. Ina nan ina jigilan wacan gidan jiya dai su Asmau sun tare a sabon gida ita da yara saura wanan idan na samu kudi ko a gyara maki ko kuma a gina wani don nasan ba zakisu zama a cikinsu ba ? Murmushi nayi na mamaki nace gida ka gina masu ashe yace an dade da ginasa ai gyarashine ban gama ba dama yanzu kuma an gyara din. Wanan kudin dana aje wanan gidan kwanaki aikin gidan nayi dashi kada kudin su salwance min ban more masu ba shiyasa ban fadawa kowa ba . Sallaman Aminu da Salima ya hanashi cigaba da magana inda ya juya yana fasin au salima kin karaso kinga na manta munyi waya dake fa yanzun nan kince kina tafe. Suka gaisa ta juyo ta gaisa dani nake mata takoma lafiya jiya tace lafiya kalau kedai na koma na iske rigima yaya ashe zaka kwashe baka fadawa kowa ba. Na koma na samu saiba na fada da mama tana fadawa mama maganganu muna tsaye saiga kawu kuma ya shigo duk basu ganmu ba dani da Hauwan ya yazid a duhu. Nace barin shiga shine fa na samu wani zance da kawu ke fada na ban mamaki amma sam mama bata damu da kalamansa ba balle ta tambayeshi me yake nufi da shiri ya baci wai ? Shirin me ya baci shima dan uwan ya tambayeta tace waya sanar mai yaya akwai dai abinda haka ke nufi ina fadawa iya ta mike ta sameshi cikin fada tadai kwashe duk yadda akayi ta fadawa dan uwan nata. Ina zaune ina sauraren ikon Allah ya nunani yace kin ganta nan itace mafarin lalacewan komai garesu yanzu idan kin kula tun shigowan Rahama rayuwana abubuwa suka canza a gidan nan. Dago kai nayi da dauri ina kallonshi yacigaba da fadin shiyasa kike ganin basu shiri da ita yana zuga mama akan Rahama tana hawa tana zaunawa tare da wanan shashashab Saratu. Ya san komai a yanzu matukar Rahama tana tare dani ba zai taba cinma manufarsa a kaina ba yasa kikaga ya koma kamar mahaukacin zaki yanzu. Nasani Salima nasan komai har abunda shi kansa bai sani ba duk an fada min duk ciwon nan da kikaga inayi Allah ya nufa sai nayi amma da hannun kawu a cikinsa. Ta kwalo ido waje cikin tsoro tace mayene ke nan ko yace ba maye bane amma yana kama dashi don mugun mutumne sosai wanan matar nasa ta halakashi da yawa. Ba zan boye maki mamace basu so da karuwa sun kulle bakinta ba zata iya magana ba akansu koda ta gane abu saidai ta bisu kawai ba zata iya fada akanshi ba. Salima abu tun muna kanana akeyinsa har yanzun kuma basu daina ba ki rabu da wanan matar na kawu kawai ba mutumiyar arziki bace duk ita ta jawo wanan abin sam da ba haka kawu yake ba ai daga bayane ya koma hakan. Zan fada maki wani magana yau don irin hakan nake son na kakkabe Nusaiba tun yanzu a rayuwana. Sam ban ra,ayin maiyin shirka mai hada wanin Allah da Allah yana ganin shine daidai na tsani wanan rayuwan tun ina karami salima na tsani masu irin halin bin boka da malami sai gashi na tsunci Nusaiba dumu dumu da wanan rayuwan. Zan iya hakkuri da halinsu in zauna dasu hakana amma banda zuwa wurun boka ko malam gashi har takai ga koyawa Saratu wanan rayuwan . Yana da wuya idan ka fara ka bari donshi kikaga gaba daya a yanzu dana samu kaina ban iya taimakawa kawu ko kadan . Wayan da aka kirashi yasa ya fita daga falon ta nisa tana kallona tana fadin Rahama na suma a zaune ashe yaya yasan komai da sukeyi saiya nuna kamar bai sani ba ? Tun dai gabanin auren nan da saratu zatayi sune har zuwa katsina wurin malamai subbahanallahi na fada tace wallahi. Gashi sunje din kuma abubuwa sunki dadi ga auren kullum cikin bugo waya take tana kuka ashe gidan yawane matan shi hudu kuma dukka zube suke a gidan gado tare da iyayyenshi da kowa nasa duk a babban gida kamar ace ku matan yaya dasu marian ki da hauwan yaya yazid da matan su yaya Auwal duka gaba daya. Kirji na buga irin na bam mamaki din nan tace ai bashi ba duk kinga yawansu girkinsu to a hade wai yake waje daya ake girki gaba daya har kowa gidan. Ance yara cakwal ba iyaka kowa kuma a wanan tukunyar zaici nace innalillahi ai zaka halaka ato ai tagani nan da aka auroki aiba abinda bata fada ba akanki lokacin. Yanzu ita gashi ta fada ga wanda yafi naki sau dubu hankali ya tashi saiban da take tayawa kuma yanzu itace ke gulmanta ranan ina jin tana fadawa wata kawarta tana dariya . Shigowan yayan nata baisa ta fasa maganan da takeyi din ba har saida ta kare yace dama idan kace hassada ka iya sai Allah ya barka da dabaranka. Ni tacewa Rahama da kurciyarta kwadayi yasa ta aureni tsoho ita tana kamar Rahama bata ga kwadayin da zai kaita auren mai mata ba. Duk ta dauka duk abinda da take fada banji irin abinda take fada ba ai shiyasa yanzu na sakawa yar iska ido ai . Allah bai hana min abinda zan kama mata haya ba a garin sokoto yanzu amma na kyale yar iska ta dandana barnanta taji. Haka mama nason muyi zancen da ita amma sai in zame mata sam ban yarda an zauna dani ayi wani magana ba game da ita. Ko shekaran jiya tunda safe ta kira mama tana kuka injinsu nayi kamar banji ba lokacin dana fada mata gaskiya ai wucewa tayi tana fushi dani wai kazafi ake mashi ba gaskiya suka fada ba. Su yaya Ai ne zasuyi mata kazafi ko mama hafsatu mama ta goyi bayanta sukaci min mutunci a lokacin. Ni zancesu ma ya hana in tambayi yan sabon gida wai wayaga Asmau cikin sabon gida Allah yasa dai ta daina kazantar nan nata . Yanzu fa kika gama maganar wata na munafuncin halin ya bita ke kuma gashi zaki dora na anty Asmau tun ba a daga ba ? Ta kwashe da dariya tana fadin bari Rahama abinsune sai addu,a don ban taba ganin kazaman mata irin Asmau da Nusaiba ba. Lokacin mama da dan sauranta ai ko sunyi abinci bata iyaci saboda kazantarsu amma yanzu ni banma ko kula ko tana ci tunda ko yaushe Nusaiba suna tare tunda Saratu ta tafi. Ke dai bari ana abu a duniyan nan wallahi yanzu ai zan je naga gidan da yaya barmu da mamakinshi ace har an gina gida kowa bai sani ba ?. Habu ya sani don tare na fara ginawa da nashi dana yazid lokacin daya samu matsalan nan yasa ya karasa nashi da kanshi amma tare aka soma aikin gaba daya. Dama yaya kai ka ginawa yaya habu gida ashe amma ban taba jin wani na wanan maganan ba sai yau daka fada to kibarshi nan inda kikaji. Shima yazid insha Allahu zasu koma a nasu kwanan nan kafin yacigana tace to yaya gidan mu fa yace nakune mana salima dake da mama da barakha da saratu ku hudu za a barma shi. Binshi tayi da kallo ba ita kadai ba harni dake tunane da fulanin mu ke fadin dan uwa MURFIN JALLONE daya baiyi saida dayan komai bacin zumunci kuwa ga mutum wani abin don dole saida dan uwanka na jini. Wanan kalman tun bayan komawan mu wajen baffan mu nake jinsa idan gorinsa ya tashi a kanmu zaice shi dan uwan mahaufinmune na jini don haka mun zamo mashi marfin jallo a yanzu don ba yadda zaiyi damu . Tare suka fita don kiran da akayi mashi yace gashi tafe suka tafi suka barni da mamaki da yawa a zuciyana har na rasa wani zan kama a ciki don abubuwan mamaki naji a dan zaman nan da mukayi lokacin. Daki nashigo tun bayan fitansu muka kwanta da Amir nake wanan tunanen ranan da yake nasan mama bata gida barcina nayi sai bibane tayi muna dahuwan da zamuci. Ban fito ba sai wajajen biyu da rabi ukku saura nafito daga daki koshi kukan Amir ne ya tayar dani sam ban iya kiran sunan gatsau don sunane mai tsada a ga kowa yasa na laoerl akawa yaron Amir. Koda suka bar gidan can suka nufa su yaya Auwalne sukazo dukkamsu ganin sabon gidan don kowa bai san da zancen ginan nasa ba bayan habu shi kuma ba magana yakeyi ba haka yake dunkum a cikin yan uwa ba wani sakewa sosai dashi. Sun zagaya ko ina sun duba suka dawo falo suka zauna duk da gidan bai gama jin kayan alatu ba amma ya hadu sosai yayi kyau ga abinda aka saka a lokacin don ginan kawai abin kallone . Yaya Auwal ya dubi salima yana fadin ke kira min Asmau ta mike zuwa kiranta din bara jima ba sai gata ta sake gaidasu a matsayinsu na yannin miji da kuma yanninta na cikin unguwa da aka taso a waje daya. Ya nuna mata waje yana fadin zauna magana zanyi dake a gaban kowa yaji ta samu wuri ta zauna a tsarge ya soma fadin to Asmau nasa a kirakine a matsayina na yayanki tako wani bangare. Munzo munga waje masha Allah abu yayi kyau sosai Allah yasa afi haka a rayuwa muna fatan hakan akoda yaushe don Jafar mutumne da kowani mahuluki dake tare dashi zai mashi wanan fatan. To amma ke kuma ina rokonki da ki natsu ki gyara halin nan naki da kowa ya ahedeki dashi na kazanta da son jikin banza. Duk da Jafar yayi hakkuri yana kuma kanyi kuma bai taba kawo karanki kan ya gaza dake ba kema haka to ina son ki sani ba zamu saka ido kina cutar da dan uwan mu ba don son jikinki. Jafar namune kema tamuce a yanzu don koba aure akwai hakkin makwabtaka daya zama zumunci tsakanin gidan mu da gidanku a yanzu donshi nake gargadin ki wallahi in har baki canza halinki ba Asmau zan shayar dake mamaki sosai wallahi. Ganin kallon da yan uwan ke mashi yace wallahi kwarai da gaske don sai tabar gidan nan wallahi kuma in saka Jafar auro mata biyu a lokaci daya su maye ko ina yadda ba zata dawo gidan nan ba. Meye ranan kazanta don Allah kun tauye yaro ba dama ya dawo gidansa ya huta wari da ganin takaici ya hanashi zama don tsaban sakarcin tsiya kawai yayi mata tas a gaban kowa tana hawayen munafunci. Bashi ba duk wanda yazo gidan korafin da yake mata ke nan ko a gabanshine kuwa za aja mata kunne akan kazantansu. Ni dau bance zanje ba tunda batazo nawa gidan ba idan ita watace mai lissafi ya kamata ace da muka dawo asibiti ko daga gidansu tazo ta duba jikina ai ? Amma sai ta share wanan yasa nima na sharesu ban kula da inje in gano ba ga kuma kummalon mata da yake cina a zuciya duk da gidana baida wurin da ya kasa amma wanan halin matane ko yayane sai naji wanan abin koda kadan ne kuwa. Ita kuma saiba da tambaya da yake mutane da munafunci saida ta samu wanda ya nuna mata gidan ta tafi ya riga dayayiwa maigadinshi magana don yasan zata aikata hakan yace koda wata tazo ya nuna mashi photonta yace kada a bari tashiga. Donshi washegari ta juya ya koma son zai fitane lokacin sunan Amir kawai ya tsayar dashi sai zancen tarewansu wanan gidan kuma yazo. Tana zuwa maigadi ya shedata yako hanata shiga gidan ashe harda shirginta ta kwaso nan ko maigadin nan ya rufe get ba ita ba duk wanda yazo a ranan sanadinta ya hanashi shiga gidan. ZAINAB IDRIS MAKAWA [6/12, 05:57] Aisha Srtr Mt: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 9️⃣8️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Karfe biyar na yamma ta shigo garin zaria a by pass ta sauka ta nemi shatan mashin zuwa gida kai tsaye tana bin ko ina da kallo. Kofan gida ta sauka bayan ta gyara mayafin kanta da kyau don kada a shedata don ita kanta tasan ba daidai take ba balle wani ya ganta a hakan . Dakatar da mai mashin din tace tana zuwa bayan ta dan shiga da kayanta ciki kadan tafiya take tana bin gidan ko ina da kallo indai ba idonta ke mata karya ba a yanzu sai tace gidan nasu a yakuce yake kamar babu kowa dake zama a cikinsa yanzu. Daba don sautin karan tv dake aiki shiyan Yazid da shine fara isa ba da taja da baya ta koma waje don sai tace gidan kaf babu mai zama cikinsa yanzu. Cikin sanyi jiki ta karasa kofansu ta dan buga tanayi tana waigen kayanta data baro a kofa don kada mai mashin din ya gudu dashi a tunanen ta uwar zargi. Bugun kofan da mama dubu taje ga kuma muryan saratu dake kiran sunanta da mama yasata mikewa da sauri zuwa kofan ta bude. Itace dai saratu din ce a tsaye tana ganin uwar take fadin mama akwai dubu biyu in biya dan mashin kudinsa bata samu magana ba illa juyawa da tayi ciki don dauko kudin ta mika mata. Jun maganan su yasa salima bude kofan part dinsu ta leko tana fadin umm,ummm saratu dama zaki zone bamu sani ba tana magana ta karaso wajen ta kama mata kayan data jawo niki niki zuwa ciki. Ban karya ba tun safe wallahi ta fada ta nufi kitchen din mama da salima suka dubi juna suna mamaki akwai abinci shi ta debo tare da ruwa ta nufo falon. Ta zauna ta fara ci duk sun kafeta da ido yadda take aika cibi a bakinta kamar mayunwaciya sai lokacin mama ta nisa ta soma fadin wai sararu lafiya kuwa ta dauki kofin ruwan data zuba tana fadin ba dai kun gani ba mama ku godewa Allah dana samu kaina gida a yau. Ta duka taci gaba da cin abincinta can kuma saiji duka ta fashe da kuka mai karfi irin na tashin hankali din nan da sauri salima ke fadi ke kuma daga magana sai kuka ai saiki dagawa mutane hankalisu kuma ? Ni take son ta dagawa hankali bayan wanan da nike ciki yanzu ace mutum baida kwanciyan hankali akan yayansa duk kokarin da nakeyi kanku karshe irin abinda zan gani ke nan kuma ? Da wani zanji da zancen yan uwanki da suka juya min baya suka bi matayesu koda naki dana yar uwarki barakha ko salima dake gabana ba aure ? Mama ai gara salima da bata da auren hankalinta da nake a kwance yake nida suna nayi aurene fa tunda naje ba kwanciyan hankali kullum cikin tashin hankali da fargaba nike wallahi . Tana kuka ta shiga labarta masu irin abindake faruwa ta basu labari kaf na irin zaman da takeyi gidan aurenta da abubuwan daya faru da ita a can din. Salima ta nisa tana fadin wai wanan lamari dame yayi kama don Allah sai kace wa yanda akaiwa baki kamar mu kadaine a duniya yau a tashi da wanan gobe wancan za a tashi dashi kuma ? Ga wanan sakaran taki barin gida sai fitina takeyiwa mutane kuma yaya yace bai mayar da itakuma ta zauna tana hauka akan sai ta koma sabon gida itama. Ta saci kallon uwar tana fadin kici abinci kije kinyi wanka ki kwanta ki huta in kinyi sallah har su yaya su dawo dan basu garin nan gaba dayansu ba kowa garin nan suna wajen tafiya. Salima kona kwanta ban iya barci yanzu sai inga kamar za a zo min da sabon fitina kuma wallahi na gaji niba zan koma gidan nan ba kuma . Ki daiyi hakkuri yanzu ki huta kafin su dawo asan abinyi akai amma don Allah ki daina wanan kuka haka kina daga muna hankali in kina wanan kukan ?. Kallon salima din mama tayi don tafita karfin hali a lokacin don ita jikinta ya gama mutuwa da zancen tana zaune tana ganin kamar a mafalki take gani saratu di a hakan. Hankalin salima duk ya tashi auren har yaushe akayishi da yar uwarta zata koma haka ba dadin gani da badon tasan waye saratu ba da sai tace gaskiya hakan ba zai faru da ita ba. Sun zauna shiru falon kafin saratu ta kawar da shirun da tambayan naga part din su yaya kamar ba kowa mana ? Sun kwashe sun bar gidan nan ai suna sabon gidansu daya gina sabon gida yaushe ya gina gida kuma bayan tafiyana ? Waya sanar mashi ance gidan ya jima ashe yana aikinsa bai fadawa kowa ba sai yanzu da zasu tare shida iyalinsa shidasu suka tare ke nan ita Rahama har yanzu tana gidanta daban koya hadasune ? Haba dai tana nata gida Asmau kuma tana sabon gida saiba fa shiru salima din tayi bata bata amsa ba ta kawar da kai hakan yasa ta juya ta dubi mahaifiyarsu. Saiba fa mama bada ita aka tare bane a gidan mama din ta nisa kafin tace jiya ta tafi ta koma gidansu kaduna jiyan . Gidansu kuma a to tunda tace bata da mutunci bata iya bin abu sannu ba sai tayi tujara ai taga karshen tujara a wajenshi kuwa. Nifa ban gane ba don ta kwana biyu bamuyi waya da ita ba ranan ma na kirata waya na ringing bata dauka ba nace ko bata kusa da wayan ne ? Ta dauka tunda kowa laifin ya shafa a wajenta yanzu rashin mutuncinta ya karanto mata karya kuwa a wanan lokacin don cikinta yayi. Kema banga dalilin kiranta ba kina fada mata sirin ki tana baradaki a gari tana yawo da sunanki kan cewa bakiyi dacen gidan aure ba ? Mama ta juyo a hasale tana fadin ita data dace ai halinta yasa ta zauna a gidan daula ko banda dai sherin kishiyoyi ai ita Saratu ba a ji tayi cin mutunci ba. Wai mama meyasa ta koma kaduna kuma ana zancen tarewa sabon gida ko sunyi fada da yayane kuma yace ta tafi ? Salima ta mike tsaye tana fadin kin damu da ita ke nan matar da tabi kowa tana fada masu duk abinda kike kiranta kina labarta mata a waya zaki tsaya jin meya faru ? Ko ba,a fada ba aikin sani rabuwa sukayi mana dashi zata kawo mai iskanci ya nuna daidai yake da ita ya sallameta ta kuma koma ganin laifin mamanki a karshe ta hadasu ta zage tsula har tana fadin mama ta tanka in bata shigo ta murjeta ba a falon nan. Yau ga yar iska mama din zata duka ai ga mama din kiji a bakinta in,ni baki yarda da zancena ji da kanki don Allah fita batun wata mara mutunci can . Mama wai don Allah da gaske salima takeyi haka akayi ta dago tana fadin Saratu don Allah kiji da abinda ke gabab ki bar min zancen wanan yarinyar mara kan gado. Eeh lalai kuwa Saiba takai yar iska mamace zata zaga har da fasin ta yi magana ta murjeta duk halarcin da mama tayi mata a gidan nan. Aita manta hakan yanzu tunda dan mama yafi karfin mama tace don yabar yarda da ana labawa ga mama ana tauye mashi hakkinsa . Nikun isheni da rashin hankalin ku don Allah mama ta fada a tsawace garesu shigowan iya yasa duk sukai shiru a dakin. Wa nake gani nan iyan ta fada ta amsa da nine iya ko baki shedani bane kema zamani ke amarya har yaushe aka kaiki da zaki zo gida ? Jiya ta amsa ma iyan tana daure fuska don ba shiri sam tsakaninsu wai yaushe tazone iyan ta juya wajen salima tana tambatanta kafin ta mayar da idonta kan kayanta dake gefe daya aje. Iya dazun nan ta shigo mama taba iyab amsa takai zaune tana fadin lafiya dai ko sai saratun ta mike taja bag dinta zuwa daki tabar mama na mayarwa iyan da zuwanta din. Kwance yake yana barci a dakin matarshi ta biyu yaji sallaman uwargidanshi a kofan dakin ya mike zaune yana fadin shigo mana fati ta karasa shigowa daga ciki tana gaisheshi cikin hade rai wanan dabi,antane matukar ba dakinta yake ba yana wani dakin har in ta fahinci ya kwana da mace zata wuni tana hade mashi fuska a gidan . Bashi ba har yara a wunin ba zasu gane kanta ba lokacin gata haihuwansu takwas amma yana bala,in shakkunta ta riga data shige mai gaba sai abinda tace za ayi a gidanshi. Hakan yasa sauran matan da suka san irin rayuwan kishinsu sukaci maganin zama da ita suke binta sauda kafa don a zauna lafiya. Amma ita saratu taki hakan ta dubeshi tana fadin ina ganin fa amaryanka kamar bata kwana gidan nan ba jiya ? Da sauri ya dubeta yace bata kwana ba sai wanan matar da yake dakinta tace ta kwana mana don ko dazun da zan shiga bandaki na ganta har mun gaisa. To zan mata karya kika nufi ko mai dakinta dai a rufe take inko ta kwana ina take yanzu shiru matar tayi kada a dora mata laifin daba nata ba a kai. Ya mike tsaye yana fasin ina zata amma koni naga haske a dakinta da zanje sallah maganan jamilata sai dai inda sahena tabbar gidan ya mike zai fita ta hararoshi tana fadin in kuma zaka ? Ya koma ya zauna da sauri yana fadin wai da in dubuta ko tana gidan su ladi don can naga ta lakanci shiga kwanan ga ? Na tura ance batazo ba yasa nacema bata nan ta juya ta fita sai lokacin ya samu ya mike tsaye yana zura riganshi dake rataye. Dama naji tana waya tana fadin ita gida zata bata iyawa sai ya hauta da fada da kinkaji shina baki fadamin ba ai dauri ki hwada min in sani. Ya fita yaga dakin kargame da kwado ya nufi wajen gidab nasu ya tsaya idon matan dake zaune waje suna aiyukansu duk a kanshi bai damu da hakan ba wuce wajen gidan yana dube dube. Allah ya gani yana son saratu amma ba yadda ya iya da fati matarshi ta farko don macece ita mai tsananin kishi da dokoki matukar bata amince da mace ba, bata taba zama gidan. Don ta shiga gallaza maki ke nan sai kinbar gidan don kanki kuma iyayyen miji suna matukar son ta don ta iya kissan sace zuciya. Ajiyan zuciya ya sauke ya dawo cikin gidan hankalinsa tashe yana bada baya yaji matan sun kwashe da dariyan shakiyanci gareshi baidai juyo ba ya shige dakin daya fito. Wayanshi ya dauka ya kira layinta ana cewa layin a kashe yake haka ya wuni kira ko wani lokaci amsa dayane shine kashe layin nata yake. Ya kira layin yaya J shima ance mai baya samu nan hankalinshi ya kara tashi kada yar mutane ta bata a hannushi ya daiji idan ta isa gida hankalinshi ya kwanta. Bashi ya samu wayan nata yashiga ba sai wajajen goma na dare kuma taki dagawa ya tura mata text tana ina ta bashi amsa da gidansu zaria sai lokaci hankalishi ya dan kwanta. Ina kwance a falo muna hira da mama Aminu ya shigo cin abincin dare don duk fitanshi bai wuce karfe takwas a waje ya dawo gida. Shikewa mama hira da cewa ashe mummy saratu tazo ne dazun na ganta da naje gidan su kauwa anty salima sako wai yau din nan tazo . Na dago kai nace Saratu fa kace tazo yace wallahi na ganta har mun gaisa ita kuma matan uncle ance jiya tabar gidan bayan taciwa mama da uncle mutunci ba irin zsgin da batayi masu ba. Kai Aminu mamafa taciwa mutunci kace to ba zata iya bane don ance taciwa dubu mutunci aiba abin mamaki bane tunda bata samu yadda tayi tsamani ba yanzu. Dama shirin aiba na Allah da Annabi bane akeyi na munafuncine dama yanzu kuma Allah ya nuna masu abinsu sai haka zai biyo baya rabu da abinda ba a farashi da gaskiya ba dama a haka ake karewa. Mama dubuce ke dogon sharfin da yasa duk muka tsaya muna saurarenta shi Aminu ya dora da fadin wai har cewa tayi mama ta tanka a dakin nan tashigo ta murjeta. Kai fa yace iya ke ban labari kinsan iya ta tsani wanan matar donshi tace azo a sakawa kofansu makulli kada ta dawo tace zata zauna nan yake bamu labarin taje gidan da suka koma maigadi ya hanata shiga don an fada mashi ya kulle gida yace ba zata shiga ba tayi cin mutunci ta dawo gida kuma ta dora wani don mama tace tayi hakkuri ta hau zagin nama din har kowa bata ragawa jiyan ba. Shine yau tunda safe ta tafi tana fadin ga gidan nan tabar masu abinda mama da danta sukai mata sai sungani a rabon su kuma wallahi sai ta hanasu zaman lafiya a rayuwansu. Bata isa ba maman tudu ta fada tace yarinyar nan bata da mutunci ko kadan aniyartane ya koma masu daga ita har dubu din data marawa karya baya. Dama ta dawo gidan nan da niyar fitar da Rahama dakinta sai Allah ya nuna masu yana bayanta duk abinda sukeyi bai taba samunta ba kuma baisa ta saduda ba ga hakan rabu da wanda Allah ya tsarkake zuciyarsa kaji. Wai koda ake cewa na fadawa yarinyar nan ta tashi tsaye tayi hankali da ita sam ban taba fada mata ba balle hankalinta ya tashi hakan yasa nayi murmushi ina fadin. Mama nifa bafilatan asalice bani sheri ga kowa in kaimin ya bika haka nima idan nayi ba zai barni ba donshine mu fulani bamu damu da yiwa mutum mugunta ba muke kuma cikin daji zaune da dabbobi lafiya. Kai Anty kikace fulani basu mugunta karshe ke nan Aminu ya fada yana dariya Aminu bamu mugunta saidai ramuwan gaiya a cikin fushi. Bafulatani duk ka cuceshi da safe shi kuma zuwa yamma sai ya dauki fansa ko shekara nawa akayi sai mun rama abu ga mutum don bamu mantuwa. Saida ya tashi mama ke fadin akwai dai ba banza yarinyar nan saratu tazo gida ba dole akwai dai don in zatazo ai tare da mijinta ko wani nasa ya kamata ace tazo zuwan farko. Amma haka kimkam ace Saratu tazo dole akwai dai ba bamza ba gaskiya koma meye ai zamuji bari dai mijinku ya dawo zamuji ko meye don duba ba zata fada ba yanzu. Allah ya sauwaka nace na dora da fadin ni nazata tazo ganin gidane tace wani ganin gida har yaushe tabar garin nan da za ace tazo boyewa sukeyi amma auren ba dadi tunda aka kaita. Can dana je gida nake ji wai ashe yazid yasa an kulle kawunsu gidan yari ko kudinsa ko fursuna yanzu jafaru ake jira ya dawo aji. Kuma ance shi yazid din ya koma abuja abinshi ya zauna bayan yasa an kulleshi amma ai kinga dubu bata fada muna ba sam bata son asan komai kan diyanta. Shi kuma mijin ku bayayi saida yan uwansa yanzu shi yayanku shike kokarin a sako kawunku din amma suki sunce sai wanda ya kawoshi kara yazo nasan kudi ya basu don suyi mai haka din. Yayan ku yace Yazid ya fada mai kudinsa yaci yaki fitowa dashi idan yaji matsi zai fito mashi da abinsa so yake a bada hakkuri a manta zancen ya cinye kudin daga baya shiko bai yarda da hakan sai ya bashi kudinsa koda zai sayar da gidansune. Kaj amma yazid bai kyauta ba kawu zaisa a kulle ai yaci ragowa a wajensu ko don mahaifiyarsu dan uwan haihuwantane fa ? Baki san yazid ba ko yazid baida kunya haka ya tashi da rashin mutunci tun yana karami zuwa karatun nan da Alh ya turashi waje shinema saukinsa yanzu . Nashiga daki ina mamakin wanan rayuwam na mutanen gidan mu na yau daban na gobe daban kullum a cikin rikici suke zancen kudin nasan dashi na dau boyewa mamane kamar ban sani ba ashe abin har yakaisu ga haka. Ni yanzu a kwanakin nan ba abinda nakeyi sai tuno da yan uwana da muka bari a rugga cikin wahala musane ya taba zuwa maria ta haushi da fada lokacin don me yazo ace mun taru mun cika masu gida . Haka tashi gaba muna kuka ta sallameshi washegari ya koma gida tun lokacin bai kara dawowa zaria ba banjin koda mama tayi aure kaduna sunzo kin san mu fulani da rikon tsiya a zuciyar mu. Saida naba matan hardo sako da sukazo sunan Amir akai masu tare da wasika a ciki nace su kirani har zuwa lokacin banji kiransu ba ni duk yadda yaya jafar yake da yan uwansa ina son yadda suke rayuwansu a waje daya din nan amma mu tamu kaddarance mu taso ba tare da yan uwan mu ba. Dan uwa fa rufin asirine yau da dayansu zaizo ba zan taba korashi ba zan rike abinane duk abinda mama zatace saidai tayi matukar ba mai gidanne ya koreshi ba. Amma ita tsoro da zurfin ciki yasa tayi masu abinda ba zasu taba mantawa da ita ba a lokacin saida mukai karamin gaba da ita na gaji na sake zancen yanzu ko ina son ganin su sosai a raina. Ina dadin muna cikin daula su suna cikin wahala ba tare da mun taimakawa rayuwansu ba sun fito fili tunda tare mahaifin mu ya barmu dasu. ZAINAB IDRIS MAKAWA [6/13, 09:24] Aisha Srtr Mt: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, 9️⃣9️⃣ GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Dare daya Allah ke nashi ikon idan ya tashi ba wani mahalukin daya isa ya hana wanan faruwa a duniya saishi daya bayar ya isa ya karbe abinsa duk lokacin dayaga daman hakan ga bawa kamar yadda ya bayar din. Wanan tafiyan da yaya yayi sati biyu kacal ta daukeshi ya dawo a cikin tarin dukiya mai dinbin yawa tare da abin arziki ga yan uwa da masoya don tafiyace data zamo wace ba za a manta a cikin tarihi ba. Wani lokaci Allah kan jerabi bawansa ya dora mai jerabawa a rayuwansa wace zata zamo mai alheri a gaba matukar bawan nan ya iya juriya ga hakan ya samu ikon cun jerabawansa da hannu biyu a karshe sai Allah ya juya hakan ya zama mai alheri a rayuwansa. Don kuwa zance da ciwon yaya da shiga fatarsa da ganin wasu halaiyan da bai zata ba ga yan uwa duk hakan jerabawane daga ubangijinsa Allah. Don sanadiyan wanan ciwon da yaya J ya kwanta abubuwa da dama Allah ya jerabeshi dashi yaga duniya sanadin hakan dukiya ya salwanta lafiya ta kubce masa yan uwa sun gujeshi don baida iyali sun nuna nasu halin a gareshi abokai ba kowa ke saurarenshi ba duk da halarcinsa garesu a baya. Sai gashi Allah ya dawo mai da dukiyansa inda ubangiji yayi ikonsa kayan sun ninka kudinsu sama da lissafin mai lissafi abin baiko faduwa. Wani saurayin Maibe dake can ya adana kayan a wajensa kamar yadda ta bukata yayi daga baya da suka samu labarin jin saukinsa aka baiyana mashi inda kayan suke yabi kuma suka shiga a cikin lokaci aka samu alherin daba,a taba tsamanin hakan ba gareshi. Ruwa aketa shega muna a garin hakan yasa bamu tsaya wani dogon hira ba duk da ba matsalan mu da ruwan muna cikin rufin asirin Allah mu bamu ganinsa balle ya tabemu. Amma yanayi yasa mun kwanta da wuri a ranan nagama shirya Amir nima na kimtsa kaina zan kwanta naga wayana yana haske na dauka. Yaya nagani yana kirana lokacin na dauka yaron kuma yana min kukan nono na fara daukan wayan nakara a kunnena kafin nakai hannu na dauki yaron ina mashi sallama naji yana fadin kun rufe gidane nace ehh yaya ki bude min gani nan zuwa ya fada. Na amsa da to cikin mamakin yadda ya iya tafiya a cikin wanan ruwa ga dare haka duk da shadaya ake nema a lokacin amma gari yayi tsit a lokacin. Na saba yaron a kafada na fita zuwa falo na bude kofan a daidai lokacin maigadin mu ya bude get din gidan motoci ukku suka shigo a jere lokaci guda haraban gidan. Dawowa nayi na zauna don Amir daketa tsala min ihu hakan kuma ba halisa bane shi yarone mai hakkuri yana da wuya kiji kukansa sai can ba a rasa ba amma akwai zuciya gareshi mama kance ya gado na fulanin a gareni watau zuciya. Haka ya shigo ya sameni zaune na fara ba yaron nono yana tambaya ina key din dakunan boys quaters suke na mike na dauko mashi ya fita na zauna nacigaba dabawa Amir nono a falon. Ya dan jima ina falon zaune ina tunane a cikin raina Aminu ya dinga shigo da wasu manyan jakkuna shida mai gadin gidan kusan biyar kafin shiya shigo daga baya don ruwan ya dan tsagaita a lokacin. Tun kafin yakai zaune yake tambayana mama fa tayi barcine nace ta kwanta tun dazun nima wanan ya hani barci yau da sauri yake tambayan meya sameshi kuma ? Nace dashi yau dai kuka yakeyi tun yamma mama tace kila cikinsa ke ciwo anbashi balma kuma bai bari ba. Ya mika hannu ya karbi yaron nace abinci fa yace bar zancen abincin nan yanzu bamu da yunwa hankalinshi na kan yaron yana dan dube dube a jikinsa yake ban amsa. Yakai zaune yana fadin ko zamu kaishi asibitine a dubashi da sauri nace da daren nan a dai bari da safe mugani yanzu ko mun fita a cikin ruwan nan wa zamu samu a can ? Baki da tausayi don ciwon ba a jikinki yake ba zakice har saida safe idan bai bar kukan nan ba dole mukaishi asibiti nayi sa,a yarin yabar kukan shima ya mike zuwa dakinshi yana gyara kayan da suka shigo dashi din ciki. Yaron na goye a bayana na shiga na sameshi ina fadin yaya bafa gidan nan zaka zo ba naga kazo muna a cikin daren nan baiyi magana ba saida ya gama dora kayan ya juyo yace Allah ko ? Ina ya kamata in tafi nayi shiru tunda nasan tambaya dai kawai yakeyi saida yakai zaune nace saura kwana ashirin da biyu muyi arba,infa yanzu. Sai akace kada inzo sai kinyi arba,in ko banda wanan koda kikaga ban zama saboda mamace kuma aiki akai maki kina son hutu yasa nabarki ki huta don nasan innazo zaki wahal da kanki da aiyuka yasa na daure har wanan lokacin. Kamar ince yanzu ko kagaji da hakkuri da zamanta ka dawo ko karanta zakayi daga gidan iya dai tunda mukaje suna bata dawo ba tayi zamanta gida tace na samu sauki ai saidai. Banyi magana ba na shiga bandaki na hada mashi ruwan wanka amma saida na koma daki na dauko ruwa a cikin flask don ba ruwan zafi gashi ana sanyi a ranan balle ya watsa ruwan sanyi. Ya shiga wanka na koma dakina muka kwanta da Amir ban falka ba sai Asuba na tashi nayi sallah kitchen naje na hada muna ruwan zafi don yin wanka har lokacin ba wuta a garin gashi engine din gidan ya baci ba a gyara ba har lokacin duk da ban jona mashi kayan nauyi dama. Na juye ruwan na fara hada breakfast don bakin dayazo dasu mama najin motsina ta fito daga daki tana fada nace aina sa biba ta kwashe min ruwan takai min. Lafiyayyen breakfast na hada nayi wanka na gyara kaina lokacin mama ta fito tayiwa Amir wanka ta kimtsashi ta miko min shi in bashi nono Biba ta shigo tana fadin Anty naga wasu motoci a wajen gidan nan fa ? Da maisu a gidan ai motocin me kuma kinkan fara maganan ki ke nan mara ma,ana nace ta ganine mama yaya ya dawo jiya da dare kuna barci. Cikin mamaki mamake fadin lalai munyi barci jiya ban kayi dogon zance mai tsawo da ita saidai ita ta dinga min hira ina murmushi ba ita kadai ba kusan hakan dabi,atace rashin dogon magana mai tsayi da kowa hakan nake. Shine ya fito yana muna sallama mama ke fadin yanzun nan take fada muna ka dawo jiya da dare ina tunda iska ya taso aka fara hada hadari muka shige daki ai suka gaisa dashi tayi mai yaya hanya ? Bayan sun gama gaisawa ya juyo yana fadin mutanen nan zasu kama hanya yanzu gashi na makara ba ayi masu abin karyawa ba kuma ? Nayi na fada a sanyayye kinyi fa eeh na soya dankali da kwai sai dan ferfesun dana hada da sauran kayan cikin daya rage muna a fredge amma kin kyauta wai da nafitone in kaisu su karya su kama hanya. Biba ta fito da kayan zuwa wajensu ya jima a can din kafin ya dawo bayan ya saukesu inda zasu shiga mota na na hada mai ruwa yayi wanka sanan ya fito karyawa . Bayan ya zauna yake tambayan mama nake fada mai tana daki yace nayi mashi magana da ita nashiga na kira mama din tazo. Mama din tafito tana fadin ka dawo ashe bakin sun tafi ko yace sun tafi mama daga can nazo dasu sun jawo min motocine zuwa nan yan kamfanine aikinsu ke nan idan ka sayi mota a wajensu zasu jama sukai maka duk inda kake so. Tana mamaki tace su kuma ta haka sukeci da iyalinsu Allah ka rufawa bayin ka asiri ya amsa da amin tafiya ai tayi kyau sosai mama addu,anku yana aiki sosai a garemu kullum sai kara ganin haske a rayuwa mukeyi mama . Addu,an mu da alherin ka ga mutane malam da zamu samu irinka biyu zuwa ukku a cikin mu da yanzu an gama saninku a ko ina fadin kasan nan hannu daya akace baya daukan jinka. Anyi ma yawa akai malam dole jiki yayi tsami ko a hakan mama Alhamdullahi don tafiya anyita a sa,a sosai wana karo ban taba tafiya mai sa,a kamar wanan ba a rayuwana ba. Mama ta gyara zama tana fadin Alhamdullahi haka muke son ji ko yaushe gareku muji kuna samu karuwa tako ina shine addu,an mu gareku ai. In sha Allahu mama bana ina son ku taka arfa gaba dayan ku da yardan Allah cikin mamaki tace gaba dayan mufa kace yace insha Allahu hakan nake fata mama. Allah yace malam Allah yace daga gefe na amsa da amin a cikin murna tace dadina dake yar nan hankali yau da watace ya fadi hakan saita nuna bakin ciki a fili wasu matan basu da lissafi a rayuwa ko kadan wallahi ni dai nayi murmushi ina fadin mama aikoni keda hali haka zan iya kaiku insha Allahu. Haka shike yata nasam zaki iya hakan idan Allah ya hore aka kwashe da dariya suna ta hiransu yana karyawa har ta dauko mai zancen yadda saiba taje tayi hauka da kuma zancen zuwan saratu gida. Nan ya tsayar da cin abincin yake fadin me kuma saratu tazoyi gida yanzu ko haka akeyi kazo gida daga kaika gidan miji wai ? Towa zai sani malam uwarta ta boye zancen ga yan uwanku nasan kai ake jira ka dawo yanzu daka dawo ai dole a nemesu ai yaja tsuki da alama abincin ya fita mai rai yace Allah mama naje gida banji wani abu mai karfi ba yau din nan tana konawa dakin mijinta. Basu san ka dawo ba ke nan tace shigowa na gari na yo nan gidan don bakin nan dana zo dasu nasan idan na kaisu can karsheta inji kunya don haka nayo dasu nan gidan ai. Bai wani jima ba dai yabar gidan muka zauna hira da mama tana kara ban tarihin rayuwansu lokacin mijinsu yana raye kafin ya rasu. Gidan Asmau ya fara biyawa a lokacin ya samu suna karyawa ta dan fara kame kame tana fasin ta zubo mashine tace wani ai tun jiya na dawo garin ina gidan Rahama can na sauka. Tayiwa bakina abin kari sun karya har sun kama hanya sunce sun wuce kaduna tun dazun nasan kona kasu nan takaici kawai zaki barni dashi ace yara kananu sai wajajen sha dayan rana suke karyawa kina kwance kina barci don baki damu dasu ba ? Yaya ban damu dasu bafa kace ko nayi abin karyawa tun dazun karshenta baci zasuyi ba cikin tsawa ya hauta da fada yana fadin nasan maganin ki yaya Auwal zan fadawa shi zai dauki mataki a kanki. Da sauri tace yanzu dai ai na dinga tashi da safe ina hada masu bashike nan ba ka kaini kara wajen yaya Auwal kasa yazo har gida taci min mutunci ga banza. Fita yayi ya kama hanyar gidansu mama da ita ya fara cin karo zata unguwa ganinshi yasa ta dakata tana tambayan yaushe ya dawo yace jiya da dare. Tare suka shiga wajen iya suka gaisa da ita Salima ta fito suka gaisa har tabada baya zata koma daki tayi brush ya dakatar da ita yana fadin yaron nan kabir yana gari ko yayi tafiya ? Yana nan yaya kice yazo karfe hudu ina nemanshi yakira layina yaji inda nake lokacin ta amsa da to yaya tashige don kimtsawa ya dubi iya yace zaman salima da Nafisa a gida yana damuna iya ? Ina son ayi aurensu a huta aji da wa yanda ke tasowa yanzu kuma ita Nafisan tana da mijine yarinyar da uwarta ta koya mata kitihi iri iri wa zai aureta ? Haba dubu kikan fara maganan ki ke nan nafisa dince da kitihi har kala kala haka ita wace ba a koyawa ba tayi auren ne ina mamaki gaka da abin zagi a gindinka kaje zagin nawani ? Irin abubuwan nan tambayan bawa sukeyi a rayuwa ke da girmanki meye na fadan hakan akan dan wani don Allah kinsan nufin yaron nan akan auren nan akan yaran nan daya fada ? To iya nidai bada wata manufa ba fada ba din Allah dukkansu aure zasuyi kwanan nan ita saratu bagata can gidan mijinta ba yanzu an huta da ita. Wace saratu saratu saratu kan na dakin uwarta yanzu ka ganta tashigo gidan nan tace zata gidan kawarta a kwashe mata kai. Saratu fa iya garin yaya ta dawo gida kuma iyan tace ka tambayi uwarta ita tasab dalili nayi magana tunda mijinta ya bugo ta koma ance ina nafito. Ya kuma turo abokinshi uwarta tace bata komawa sai yazo ya juya wajen mama din yana fadin mama yaya akai haka kuma ban sani ba ? Ta yaya zaka sani tunda baka nan yau kwananta goma sha daya da zuwa miji ya dauketa ya kaita kauye ya aje cikin matanshi ina saratu zata iya aikin yawa da sukeyi ? Mama ba aure taje yi ba su wa yanda ta sama ba haka suke zaune dashi ba tunda suna son mijinsu ta tareshi da fadin sai ta zauna wahala ya kasheta ke nan ko ? Mama dakata don Allah kin taba jin inda wuya ya kashe mutum don Allah ita mace fa da hakkuri akasanta ita dabance a cikinsu daba zata iya hakkuri da mijinta ba ta zauna yadda kowa ya zauna yana hakkuri ko tafi sauran matan nashune da suka zauna su ? Ina an fada mata tace tana iyawa karya ake mashi saida na zauna daku kafin duk su yaya su saka baki cikin maganan tana iyawa tace min tana son shi san nan yanzu zata dawowa mutane gida don tana yar iska uba me tadawo yanzu ayi mata to nan ? Kana magana kamar baka fahinci mutane ba ina saratu zata iya girkin mutum kusan dari don Allah ? Amma mama ita tace tana sonshi ai yau din nan zata koma ai tasan yana da iyayye yana da mata da yara tace ta amince ta aureshi mu zata dawo ta rainawa wayau yanzu ? Irin rainin wayau da na guda ke nan gun Asmau don nasan sakarauce ta mayar da kanta sha,shasha saboda son jiki nazo da baki dole gidan Rahama naje na sauka jiyan. Ina zakazo da boka a barshi da yunwa yanzu dana biya gidan sai yanzu na samu wai tayiwa yara abin kari zasu karya yaro za a bari da yunw har wanan lokacin saboda sha,shancin banza da suka dorawa kansu. Dama nasan za a rina wanan daban tsiyan da suke taruwa sunayi a wuni ba mai iya yiwa kansa abin kwarai yanzu gashi duk ta dauka in anyi magana mama kice an matsa mata ba a kaunarta ina tsiya ina girki ga mace girkifa za ace ya koro mace gidan miji idan ba tsiya da samun waje ba. Naki bai hadaki da mijinki ba sai zancen girki din Allah mama ta amsa da fadin ai shima ya shafi mijin tunda yasan inda ya dauketa da zai kaita kauye yace sai tayi kalan aiyukansu. A ina ya dauketa gidan attajirai ko gidan sarakuna naga dai har gobe gidanku suna aiyukan hannu na hausawa iya ta fada yanzu inane yar nan Nafisan da kike zagi ba zata iya shiga ba ?. To taje kauyen ita amma saratu bata komawa kauyen nan sai dai asan abin yi gaskiya kauye kan ta fito ke nan cikinsa in sha Allahu. To shike nan mama tunda haka kikace saidai ku sani duk wani zance na saratu daga yau bani ba ita wallahi ta zauna gida tunda kunga hakan yafi maku. Ya mike iya ke fadin kai Alh dawo mana ya juyo yayi dan murmushi yake yana fadin ke kuma matar Alh ba don bana in sha Allahu ga kujeranki ga tawa iya muna gaban jirgi da yardan Allah ni dake. Kai kai kai kar kasa in fara shiri don Allah wanan ai ba karamun fata bane kayi min Allah dai ya nufa yasa hakan abakin yan amin. In sha Allahu iya haka nake da niyan dake da uwayena dukansu hudu in Allah ya yarda zamu keta hazo muje dakin Allah mu ziyarci kabadin Annabi mu sauke nauyin da baba yayi niya Allah bai nufa ba. Kace in fara shiri ke nan dai Jafaru yace iya fara insha Allahu makkan bana dake ciki da yardan ubangiji kuwa iya in ranmu yakai. Ranmu yakai jafaru ranmu yakai Allah yasa muna da rabon ganin hakan da rayuwan kai naji dadun wanan fatan ko ince albishir din Albishir dai iya. Su kishiyoyinki na sayowa ko wacensu mota ita Asmau daya ita kuma Rahama daya na tausan gaba uwargida zata makka a taushi kirjinsu ta kwashe da dariya tana fadin aiko uwargida ta kosa tunda motace tausan gaban kishiyoyin ta. Mama na gefe sai dan murmushin take takeyi saida raga alaman fita zaiyi daga falon race wai da gaakiya kakeyi ne yace insha Allahu mama haka nake fata ku sauke farali a banan nan kedasu mama da su yaya Auwal inda hali zan hadaku da barakha din iya kuje. Allahu Akbar lalai dan nan arzikine iliya dan mai karfi ke nan yaro ya zo da arzikinsa da kardin Allah ,,,, ji iya kuma ana zance wani dan kike magana tace mai babban suna mana wani dan ai haihuwansa alherine a waje dubama ga yadda aka samu yaron nan koshi ya isa yasa mutum ya fahinci hakan . Fita yayi ya barsu bai kara zancen saratu ba fitan da mama batayi ba ke nan a ranan ta kira yaya barakha tana sheda mata abunda ya faru barakha din tace kai amma jafar ba abunda za ace mashi. A yanzu jafar din ya juye mata kamar bashi ba tana jin shakkunsa da nauyi ba kamar jafar dun baya data sani ba da rake iya tankwasawa kota umurceshi yabi. Tasan yasan abunda ke nan akan kawu amma ya share ya nuna bai san da hakan ba ko zancen bai dauko mata ba amma zata kyaleshi taga gudunsa. Tasan ba zai taba kyale kawu di yazid ya wullakantashi ba ai tunda daga yazid har habu sam basu jin zamcenta yanzu jafar din ne mai dan dama dama a cikinsu. Yanzu kuma shima ya juye har yana son ya fisu gashi ta kasa gane matsalan daga wajenrta yake balle ta gyara Allah yasa mu dace amin. Sai washe gari yabawa kowa motarta ya fadi kalan tace Asmau ta zaba tace baka take so tabar min farar munyi mai godiya dani da ummah har da mariya ta kirashi tayi mai godiya ya kuma ji dadin hakan sosai nagane hakane da yake cewa ke kina ta wahal da mutane da kira halal zaki saya masu credit ne ? Zancen makkasu ya tabbata wurin mutum goma ya biyawa makkah da zasu tafi har labarin irin tarin dukiyan dayasamu a yanzu yakaiwa saiba sai gashi ta fara bugo mashi waya tana ban hakkuri. Kashedi yayi mata yace kada ta sake kiranshi idan ba haka ba zai kaita ga hukuma ayi masu tsakani da ita amma hakan baisa ta daddara ba. Don sai ta fito da sallon kiran wayan taba yarta idan ya dauka tace daddy yaushe zakazo ka daukemu bata san tsiya ta kullawa kanta ba a wanan sallon . Haka yasa ya tura su yaya Auwal su karbo yarinyar a hannunta nan kuma tace bata isa ba shima yaya Auwal yace bata kai mashi can ba dole tabada da yarinya don bai yarda da tarbiyanta ba. Dole mahaifita yasata gaba ta mika masu yarsu suka dawo da ita kaduna can gidan Asmau aka aje yar don yaso yace a wajena zata zauna mama tudu tace dashi ko kusa zaman yar nan yana iya kawo matsala tsakaninka da yarinyar nan kaga ba shiri take da uwarta ba. Ka barta can ta zauna tare da yan uwanta tunda dasu ta saba dama ita yar hakan zaifi mata dadi yace mama niba ra,ayinta naso ba don ta samu tarbiyan da nakesone ai tace barta dai can tukun na hakan yasa dole da akazo da ita ya barta gidan Asmau din. ZAINAB IDRIS MAKAWA [6/14, 22:19] Aisha Srtr Mt: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,, 1️⃣0️⃣0️⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,, GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , , YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , , HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,, Zance dai tun ana ji kamar karya saiga abu ya tabbata Alhazai sunata shirin tafiya saudiya don yin ibada wa yanda sukai nasaran zuwa sune yaya Auwal da ya Isah yaya barakha da Asmau matarshi su mama su hudu sai iya da yaya Rukkaiya. Kamar yadda ake samun kalubali idan haka ya faru dole sai anyi tsegumi shima ya samu a wajen mahaifiyarshi don ta nuna rashin jin dadinta tayi fada don me zaikai har mutum uku maka dakin mama lokaci daya ga dan uwanta da suke uwa daya uba daya bai kaishi ba ? Kome kawu yayi mashi dai jininsune don shiyasha nono ya sake mata baiyi magana ba a lokacin don sai ana gab da tafiya aka san masu sauke faralin ya hana kowa ya fito fili ya fadi donshi kowa ya kama bakinsa da zancen. Saida ta kara tayar da zancen a gaban yan uwansa gashi ga habu ga yazid ga iya dasu salima ta soma korafi akan ya nuna mata yanzu yakai tunda har dan uwanta badai daraja a idonsu ya biyawa kowa nasa makka yaki biyawa dan uwanta don ya tozartasu . Ace dakin mama harsu ukku zai biyawa makka mama tudu ta fitane gareshi ko takaita daraja a wajenta a,a mama kada kice haka don Allah ? J da kike gani ni yanzu ban iya cewa komai akanshi yasan dalilin da yayi hakan a garesu ba wani magani ko munafuncinsu daya cishi. Mutanen nan suna nunawa a gaban kowa shi dan dakinsu abinsa idan ya taso tun baikai haka ba sai idan karfinsu ya kare akanshi da baida lafiya nan gaban kowa yaya Ai take kuka tana fadin dama ita aka dorawa ciwon bashi ba. Akwai soyayyan dayafi wanan har dan uwanka zai sadaukar da ransa akanka ka kasa mashi komai matar nan tana iya kokarinta damu tun muna kanana yanzu haka yadda yaran mu suka saba da maman tudu mama basu saba dake ba hakana don hattaransu da kikeyi akan uwayensu mama kikan manta da yayan mu jininkine su ?. Shi kuma kawun da kike magana a kai kowan mu nan yasan irin ta,asan da kawu yaiwa rayuwanki ya haniki zaman lafiya damu yayan ki haka kuma bai son ganin cigaban mu wanan a baiyane yake kowa ya san hakan mama don haka kada ki matsa muna kan kawu don Allah kawu dan uwankine ba dan uwanmu ba . Kai habu ka shiga hankalinka kafin na fyatoka daga hancina ba yau ba na kula dakai da tsatsauran ra,ayinka akan yaya idan kai ba zaka taimaka mashi ba ka bari wanda yayi niyar hakan yayi. Tunda shi Yazid yace ba zai taba yafe kudinsa dake hannun yaya ba ga kuma Saratu yanzu ta taso da zance kudinta take so ta koma gidan mijinta tunda kunki taimaka mata ku . Yaya J yana zaune yanata charting bai dago kai ya dubesu ba amma hankalinsa na kan abinda kowa ke fadi wurin a lokacin saida yaji yazid yace mama kudin nan kudinane fa ? Ubana ya mutu yabar min gadon su kuma banyi da kowa nace abashi kudina ba wanda yai fushi da matakin dana dauka ya biya mashi man in rabu dashi matukar bai biyani ba wallahi sai yayi fursuna akan kudin nan haka kawai zaiyi na iya kyaleshi koshi sai ya biyani a lahira don ban yafe mashi ba. Nasan zaka aika donshi nake son dan uwaka ya biya kudin tunda na fahince kai abin kunya baya gabanka yazid nemansa ma kakeyi ka yafa. Aban kudina in rika mama yadda kowa ya rike nasa nima in rike abina nagaidai babu ruwanki cikin zancen idan kuma za a biya mashine a ban kudin yanzu. Shirun da yaji anyi a falon yasa ya dago kai kallonshi sukeyi a lokacin yasa yace wa wai dani ake maganane banji ba ? Ka daiji abinda yake fada game da kawunku idan ya matsa zankai ga mashi baki yasa nake kyale yazid da iya shegenshi. Baki kuma mama akan kawu zakiyi mai baki har idan kinyi muna hakan ai kamar kin cutar da rayuwankine mama ka bashi kudinsa tunda tozarci yake neman muna. Ni mama a,a ba wanan akawarin a waje ko kin manta daga ina kudin suka fito suka koma hannun kawu da har yanzu kudin suna hannuna da sunfi abinda ake nema yanzu a kawu. Kawu da munafuka din nan saratu nan suka tasaki gaba da sunan cewa kudin nake wandaka dasu har naje na auro Rahama. Ni auren Rahama gareni alherine ba tsiya ba tunda ina ganin haske ga taraiyana da ita akan me zan dauki kudina ince na biyawa kawu kudin yazid . Ai gara in nayi niyar taimakawa yazid din insan kyauta na bashi kudin da biyan bashi ba mutumin da bai kaunar ya ganni da rai zan biyawa bashi mama ba wanan zancen kuma tsakanina dashi gaskiya inda yakai mashi kudinsa ya fito dasu don sunan a boye tunda ba abinda yayi dasu. Barakha dai tunda ta rokeni gafara ta kuma fada min dalilinta na goyon bayan haka ita kan bance ban taimaka mata ba yanzu. Auren Rahama bani kadai ba duk wani wanda yake tare dani ya karu dashi amma aka rufe ido akaso tozartani cikin duniya saida Allah ya rufa min asiri ban taba taba wanan kudin ba da sunan wani abu a rayuwana don nasan irin azabab da Allah ya tanadar akansu. Ya basu kudinsu ko kuma yaje gidan yari akansu ni wanan ba zancena bane gaskiya don ban cikin maganan tun farko an tsameni a zancen yanzu ko idan nasa kaina ninaso hakan . Duk abin da kowa yayi min ina sane ina dai hakkurine a zauna lafiya amma kada mutum ya daukan ban fahinceshi ba kai Habu kwanan nan bada jimawan nan ba na kiraka akan ka taimaka min da kudi muna asibiti da Rahama za ayi mata aiki kememe kaki kulani balle ka taimaka min. Shiko yazid dana kirashi cewa dani yayi shi ina yaga kudi zai dai turo min dan abinda yake dashi ya turo min da dubu hamsin sai bare wanda ban hada komai dashi ba ya iya ban dubu dari hudu lokaci guda ga barakha da bata aikin komai sai sana,an hannu ta iya turo min da dubu dari. Kai ammako anji kunya haka akayi baka fada ba iya kona fada maganin me fadin zai min a lokacin tunda badashi banda wanda zai ban . A tunane shi dan uwa Allah kan baka sune don rufin asirin juna sai yanzu na fahinci abin a yanzu ba haka yake ba don kowa kanshi ya sani a yanzu. Wanan zance kamar almara fa Jafaru daga habu har shi yazid da bazarwa suke rawa a yanzu bada taka ba da har zaka shiga hali haka su kasa taimaka maka ? Gasu ai shiyasa na fada a gabansu yanzu ba kawune kadai yayi min abinda ba zan manta ba har dasu da nake gani rabin rayuwatace su don na shiga jerabawa suka iya min hakan. Dubu kingani ko kinga irin abinda nake fada maki ko kinga abinda matsalolinki suka jawowa rayuwan ki tun kina raye kin daiji irin abin ko ? Na fada maki irin halaiyan nan na banza bi mutum suke su nadeshi su shafi har wanda baiji bai gani ba yau ina laifin yaron nan a wajen ku ? Kai Habu ya dago da idonsa da sukai ja yace ni nasan anyi hakan amma ban dauka cewa abin serious bane sosai a lokacin yasa ban turo kudin ba amma yayi hakkuri don Allah ? Ba dole ba dole yayi hakkuri idan baiyi hakkuri ba kasheku zaiyi tunda hamnuka bai rubewa ka yarda. Wai iya baki bari ayi magana kin hana sai kace kece mama dakuwa tayiwa salima din tana fadin daga uwar naku harku waye silan zuwanku duniyan nan. Iya munzo akan zancen auren salima ina son kafin tafiyan ku insha Allahu za ai aurensu jin hakan yasa mama dagowa da sauri tana fadin sati biyu kamar hauka ? Aure haka ba shiri komai a dai bari har Allah ya dawo damu lafiya zaifi yace wani shiri mama ki dai sakawa yarki albarka amma duk wani shiri ai an gama komai ina ganin yanzu abinda ya saura sai wanan cincin din da kukeyi din nan ai koshi na gama da wanan bangaren ko insha Allahu komai na saya. Shine zuwa kanon da mukayi kwanaki dasu zaman su gida haka yana damuna saida ta nisa tace angama komai kace fa a bangaren ka ko shi ya gama ginansane ? Ya gama ina ganin yaushe sukace zasu kawo kayan akwatunama yana tambayan kanwar tashi tace yace a cikin satin nan dai zasu kawo. Allah dai ya saka maka da alherinsa yasa kafi hakan a rayuwanka jafar kayi yadda duk akeso ayi Allah ya baka zuria masu rama maka ya amsa da amin . Itama mama ta amsa tare da fadin har ita Nafisan ke nan yace insha Allahu wanan dan uwan mahaufiyarta dayaje karatu waje ya dawo dashi za ayi a nan kaduna zai ajeta. Wani nisawa mama tayi ta shiga dogon tunane can ta dago tana fadin amma wanan duk tsarinkane ko tunda ka gaji da ganinsu gida ? In ma tsarinsane aina alherine tunda aure ya hada Allah kadai yasan ladan da zai samu a wanan abinda kayi Jafaru Allah ya biyaka da alherinsa kaji. Mikewa J yayi yana fadin to mama mu zamu tafi wa yan nan dana lissafa maku sune zaku tafi tare bana saudiya insha Allahu badi kuma idan ranmu yakai sai a duba wa yanda ya dace suje. Mama bata iya magana a lokacin don yadda zuciyarta yayi mata nauyi da zantukan da sukayi dasu na kawu yafi tsaya mata a rai yadda har suka tashi yaran gaba daya suka tsani dan uwanta a yanzu. Yadda yace hakan ya faru ansha buki ankai amare komai nasu iri daya saidai kala daya bambamta da kuma abinda kowa ya sayawa kanshi anyi lafiya an kare lafiya amare sun tare dakinsu abin gwanin ban sha,awa dasu. Saratu kuma tasha zunde hakan yasata zama daki don ta zama mujiya a cikin mutane yawan zunde yasata boyewa don wanda ma bai sani ba sanadin bukin nan yasan abinda ya dawo da ita gida. Bayan an gamane dama mama tun kafin bukin ta koma gida don tafiyansu daya gabato munji kewanta sosai a lokacin. Ina kitchen girkin rana nakeyi dan aiki nawa yakaini rana naji wayata tana ta ringing bibace ta dauko wayan ta kawo min na fito ina amsawa don ganin wace ke kirana din a lokacin. Yandace na daga da sallama ina gasheta ta amsa a gurguje take fada min wai nasan me su yan uwan mu suna cikin garin nan kwana biyu ke nan suna neman gidan basu gane ba ? Suna ina nace mata cikin zakuwa tace gasu suna cin abinci nace dasu in sunga nikan zan basu kudin mota su koma ko suje wajen mama aji yadda za ayi amma ban yarda yaya habu yazo ya samesu a nan ko mama taji ta soma fadan nan nata. A cikin wani murya mai kama da tsawa nace da ita kada ki soma turo min su nan gidana koda yake bari Aminu yazo ya dauki min su. A,a Rahama kinsan halin mutanen gidan nan yanzu da angansu kuma sai ace munji dadin waje muna kwaso yan uwan mu yaya muka kare dasu balle kuma mun dauko wasu ? Maria su kore mu udan sunce basu zama da yan uwan mu saidai mijinki ba amma ni na jima da aje magana a kansu da yaya Jafar. Allah ya yanke muna wahala ya turo muna su nan likacin daya kamata su din a,a Rahama ki bari na basu kudi su koma gida din Allah ? Gida wajen wa suje suyi ta aikin bauta mu muna nan cikin daula suna can suna bautawa kawu ga Aminu nan zuwa yazo min dasu na fada ina katse wayan. Sam banji dadin wanan zance nata ba ba a dauki lokaci ba Aminu ya dawo min dasu zabar tausayi saida nasha kuka dana gansu lokacin. Aminune ya duko gefena yana fadin anty bari na kaisu dakina suyi wanka in basu kaya su muje suyi aski sai mu dawo ina jan majina a hancina saboda kukan da nayi nace dashi bari na dauki maku kudi kaje dasu ka sayo masu kaya yace to anty don dai kince da kayane dan aski kawai ai ban rasa kudin da zasuyi aski a wajena. A,a tsaya in dauko kudi ku dan sayo kaya su samu na canzawa nashiga na dauko kudin na mika mai suka fita kuka nacigaba dayi ina waya da mama da hankalinta ya tashi. Take fada min mijinta bai yadda da yaya mazan ba ya daifi yadda damu matan ita bata san abinda yasa baison ayi zancen su ba ? Ni da kaina na kira yaya ina kuka na labarta mashi zuwansu din da yadda abin ya faru cikin karaji naji tace yanzu suna ina ? Aminu ya kaisu suyi aski ya dan sayo masu kayan sauyawa yace barin nemi Aminu din ajiyan zuciya na sauke dama nasan yaya ba zai taba kinsu ba. Don sauda yawa yana min hiransu lokaci lokaci yakance dani yakamata a dubu su ko ya kira hardo ya tura masu sako duk da nasan hardo zai basu amma baffa amshewa zaiyi. Tare suka dawo gidan dashi sayayya sosai yayi masu suka shigo yanawa musa sheri da ke ashe kanin naki aure yayiwa gudu yazo nan saida yaga za ayi mashi auren dolene ya tuna damu. Harshe na juya ina tambayanshi yake fada min yadda akayi raina ya baci sosai da kawu abinci na mike na kawo masu sukaci suka dasa wani hiran dashi. Dakunan daba kowa a ciki na boys quarters yasa Aminu ya bude ya saukesu a ciki da yake ba nan gidan mu yake ba saida zai tafine yakecewa dani ina ganin fa nan za a kawo yaran nan idan uwarsu zata saudiya. Su basma yace eeh don ban yarda da cewa da tayi wai akaisu gidansu ba Allah ya kaimu nace ban yarda na nuna komai ba ga hakan. Amma nasan akwai ta don yadda yaran suke basu jin magana kuma ba a tsawata masu amma ba komai zanyi iya kokarina dasu insha Allahu. Aikuwa hakan ya tabbata don kuwa tun ana saura kwana ukku su bar kasan sai gashi da yaran yazo min ban ko san da zuwansu ba ya kwasosu zuwa gidana ba yadda zanyi dole na rugumesu . Irin wasan da sukeyi ya fara daga min hankali wasane na alaman ba kwabo din nan ga yaro nan muka fara kwasa dasu nayi masu serious warning akan hakan. Ban yarda na sake masu ba sam da safe kuma zan tayar dasu suyi sallah akan lokaci idan angama kuma nasa suyi brush biba tayi masu wankan safe. Gaida mutane akan Aminu na fara koya masu hakan ya shigo suka bishi da kallo na daka masu tsawa su gaidashi daga zaune inda suke sukace ina kwana nace ba zaku tashi ku gaidashi ba bakuga yadda biba ta gaisheshi bane hakan yasa suka mike daya bayan daya suna gaida shi. Nace duk wanda yazo baku tashi kun duka kun gaidashi ba saina tsunkewa mutum kunnensa da yuka . Haka sunso su dinga irin barnan nan da sukeyi su halaka abu ana kallonsu ba kwabo su barnatashi ana kallo haka zasu barna abu. Shima cikin nasiha da fada na hana wanan da mamansu tazo gidana muyi ban kwana wai daga gidansu take shi yaya ya kawota yadda suka gaida ita ya bata mamaki. Har take fadin wai basmace nan kuwa a,a yan matan anty kece nan harda su makeup a fuska koba kwali kika shafa a indonki ba. Ina jin mijin tace mata waye anty ita ba zasu iya kiranta da mummy ba ko mama karna kara jin wani anty can daga yau nace dashi ai haka suke kirana tunda sunji biba na fadan hakan. Tana dan murmushin yake a fuskanta yace ki duba don Allah dan kwana biyun da yaran nan sukayi a nan yadda suka koma keda suka gaidake da zuwa bakiji dadin hakan ba yanzu ? Toni yaya me zance kai kome nayi ai banyi daidai bane a wajen ka kasan halinsu baji sukeyi ba nan ma dai don suna shakatane ai to kada ki koya masu din ni ai nasan matakin da zan dauka don ba zan yarda ba gaskiya. Basu jima ba yace su tashi suje nasan don ganin da yayi yaran sun narke a jikintane saida ya mike yake cewa dani ki shiryasu idan na dawo zamuje can gida ku sallami su mama. Hakan ya faru don kafin ya dawo munyi wanka mun shirya tsaba duk da kayan yaran ga kaya na kwarai sabbi amma duk sun nakashe daga wanda ya yage a tsakiya sai wanda zip dinsa ya lalace hakana dai muka samu aka saka aka fita ina yaba sakaci irin na wanan matar a raina wai kuma harta iya hado wanan kayan haka azo dashi. Munje gidan ba laifi don mama har daukan Amir tayi tanawa mashi wasa da wakan yabo na mai sunan, baban nasu yana murmushi ta dubi yaran tace indai ba idona ke gizau ba sai ince yaran nan sun sauya a dan kwana biyun nan da sukayi. Tunba Siyama ba ni dai har kiba naga tayi ai dole yanzu ta rage wanan alaulayin nata Saratu dake neman shiri da dan uwan nata ke fadin hakan . Yawan cuwon nan da kwanciya naga duk ta dainashi yanzu uban ya fada mama tace dashi aiko yunwa ya isheta yaushe suke tsayawa su kula yara? Jiyama nake ji ance anga uwar wai a nan garin na dauka ai duban tar tazo ko tazo ina zata ganta nayiwa maigadi kashedi idan ya bari tazo min gida bakin aikinshi ranan. Ni dai banyi magana ba ina zaune ina jinsu aka gama yace mu tashi muje da zan fito na mikawa mama dubu biyar iyama dubu biyar muka fito. Naso na rakasu har kaduna amma yaya Auwal yace kowa ya zauna gida sun gode sai mazan su suka rakasu zuwa kaduna a ranan kuma akace sun tashi da dare don saida suka daga suka dawo gida. Gaskiya munji kewa sosai gidansu mama Saratu aka bari da matar Yazid duk ita da ita da babu dukka dayane tunda bata fitowa kullum suna ciki rufe. Sai su Aminune isah yaya yace zasu dinga kwana gidanshi shi kuma musa a gidan su mama haka ya rabasu ni dai najawa yaran kunne sosai a lokacin. Nayi ta jira inji wani korafi daga mama game da yan uwana din sai baniji ba yasa na saki zancen a raina suma basu da rugima sai hakan yayi min dadi. Sana,anmu da Nafisa a yanzu ya bunkasa sosai don ba zannuwan gado kawai muke daukowa ba har da kayan kitchen masu kyau sabbin yayi muke daukowa hakan yasa muka fara shawaran bude shago a asirce ba tare da kowa yasani ba. Ni da wata kawata da muke unguwa daya zata bude shagon kayan mata ni kuma nace na kayan kitchen din da sauran abubuwan mata. Na nemi shawaran yaya na fada mai ya yarda da yace zaiyi magana abokinsa ya nema muna shago a bakin tiri inda za afi samun kasuwa. Ni dai nasan baiyi niyar zuwa saudiya ba sai gashi kwatsam yazo min da zancen zaibi jirgin yawo ya cin masu don hankalinshi bai kwanta ba tunda suka tafi. Duka duka cikin kwana ukku ya daga yabi bayansu duk wanda aka fadawa ya tafi makka sai yayi namaki tunda yace sai wani shekara zai tafi. Ashe gara da Allah ya kaishi don kuwa mama tun zuwansu ta fadi ciwo yau ciwo gobe lafiya har suka bar madina zuwa makka ana fama da ita hankalinsu yaya duk ya tashi sai ganinsa sukayi kwatsam yace hankalinshine bai kwanta ba. Zuwan shi ne dan dama dama don dole aka samu keke yana garata ta samu tayi aiki a lokacin ganin ta dan samu sauki ya koma da ita madina sukai ziyara ya rigasu dawowa Nageria tunda shi jirgin yawone. Saida ya dawo muke jin cewa ga abinda ya faru a can din da mama ai taji jiki sosai badon zuwanshi ba zata samu aiki ba sosai amma bai dawo ba saida ta tabbatar da tayi ibadan daya dace tayi. Yaji dadin yadda ya samemu da yaran don gaskiya ba yabo ba yaran sunyi kyau sosai duk da ba komai nake masu ba amma tarbiya ba guda ba kowa na fadi. Dan matsalan da aka samu shine fadan da akayi da Saratu yaya Habu kuma yaci mata mutuncu tun ranan akan naman laiyane datace wai naman da aka bata bai mata ba tazo har gida taci min mutunci ina fada mata ni banda labarin komai akai su yaya suka raba aka aiko min tace attabau laifinane tunda yaya ya bar muna shanu da raguna shine don an raunata za a kawo mata nama kadan. Karshe dai na biye mata mukayi cacan baki da ita Aminu ya kira yaya Habu yazo gidan ya sameta yaci mata mutunci sosai tabi hanya tana kuka. Da yaya ya dawo yaji abinda ya faru yaje nemanta ashe tana jin ya dawo ta gudu ta boye bata yarda sun hadu ba dashi. Labarin abinda ya faru da mama suna dawowa yabi gari nasan kuwa yan gidane ke fada akaji aka sauya zancen kawu yazo taron ta don anyi belinshi shi yake tambaya ashe haka tasha matsala a can tace eeh nasan ba komai bane Allah yati min haka in gane gaskiya. Yaron nan Jafaru Allah ya kara mashi albarka dashi da zurianshi jafar yayi min komai duk da Jafaru danane dole in nemi gafaranshi ko alhakinsa da ake sa inci yana hanani ganin rahama a rayuwana. Baidai ji dadinta ba ranan har ya tafi zance zuwa makkan nan ya kawowa mama sauyi sosai a rayuwanta dkn naga zuwata biyu gidan mu ko tsaraba ita da kanta ta kawo muna har gida ta kuma wuni a nan ita da anty barakha sai dare suka koma gida. Asmau ta dawo makka ta samu nasa yara makaranta inda na koya masu abubuwa da dama dole tasan yaran sun samu natsuwa a yanzu abinda banji dadi ba shine da taso ta nuna min wai tafi a yanzu. Ko don tana ganin taje makka ni bai kaini bane oho sai taso idan an hadu tayi min irin sakin maganan nan na gugar zana na daiyi gaba na baya sai hange a raina nace taji dashi nasan abin da nakeyi ni. Mama bata ragawa sararu ba kan abinda tayi min gashi taji ga Aminu mijinta tazo kwanashi ukku a gidan lokacin da basu nan hakan ya batawa mama rai tace sai ta koma dakinta. Ta kira kawo tace ta gaji yaba yara kudinsu ita ta gaji da abin kunyar dake faruwa hakana yayi mamaki sosai da mama ta iya budan baki ta tambayeshi kudin . Gaba daya yasan komai ya lalace mashi a yanzu gareshi wai ashe dama akwai kaddara da mutymin nan ya boye yana jiran abu ya lafa ya fito dasu yaci bulus duk da dai ba duka aka samu kudin ba sun dai samu abinda suka samu a wurunshi yazid yace ya hada da gidan iya ta mara mashi baya ya karbe gidan. Ashe ya biya muna makka ni da salima nafisa lawisa kanwarsu yar wajen ummah sai matar yazid da maria sai kannisa maza su ukku da zamu dasu dashi kanshi. Kiri kiri yaki biyawa saratu makka kamar zatayi hauka yace bai biya tunda bai isa da ita ba ga auren yayan yaya barakha da za ayi kafin tafiyan mu makka din Ni ba abinda yai min dadi sai yan uwana maza da karatun su yanzu yaci gaba a nan da dawowansu a kusa dani yayi muna dadi sosai yaso ya hada da ummah muje mijinta yace shi zai biya mata ta bangareshi tunda yana dashi. Anyu buki da sati ukku muka fara shirin tafiya mama taso Amir ya zauna hannuta amma yaya yaya yace mama zata zo ta zauna dasu a gida da yar wajen yaya Ai babba. Haka Asmau tace akawoshi gidansu yace a,a shine hakam ya dan hadasu hatsaniya tace yaki ya kawo mata dana amma ita ya kwashi nata takai min na zauna dasu. Yace yakai daya kai din bashi ba har ita taji dadin ganin yaran yadda suka dawo suka samesu ai don haka ba zai kawo Amir ba ta kashemashi shida yunwa nata ma ya kwashesu yakai ma mama dubu yace har ya dawo. Dole ta kyale muka tafi muka sauke farali munyi aiki sosai muna can labari yazo muna dan wajen Asmau ya fada tankin ruwa ya mutu. Hankalinmu ya tashi sosai da jin hakan shiya fara tambaya ai gidan ba tankin ruwa wai ashe bayan rafiyan mu uwar tazo ta kwashesu taje dasu gidanta wai zasuyi sallah a can shine wanan abun ya faru dashi. Haka muka dawo cikin bacin rai saidai nikuma muna dawowa ciki ya baiya a gareni ciki na biyu ke nan haka nayi ta fama lauyi ga tajiigindin duniya wanda ba a rasawa a kullum dake faruwa na haihu lafiya na kara samun namiji again nan kishin Asmau ya tashi saida yaya yayi mata iyaka dani ta shiga hankalinta. Na kusa haihuwa kuma ciwon yar wajen Saiba ya tashi itama ta rasu nan hankalina ya tashi sosai Allah dai ya taimakeni na haihu a lokacin. Na dan huta da haihuwa don tazaran shekara ukku ban haihu ba nasake samun wani cikin na haifi wani dan yanzu haihuwana biyar da nake maki labarin nan shagunana biyu manyan store daya a nan zaria daya a kaduna. Sau daya muka hadu da saiba ba don farin sani ba ba zan shedata ba muna dakin yaya kubura wajen buki suka shigo wai suna tallan kayan mata tunda tayi arba ta gan mu nuda Yanda da matar yazid da yanzu muke aminai ta saka kafa ta fita falin bamu kara ganinta ba. Sai dai ince Alhamdullahi don muna zaune lafiya da Asamau Allah kuma yana ta budawa mazajen mu Saratu daice a gida itama auren yaki ta koma tafito har sau ukku a karshe dai auren ya mutu iya kuma ta amsa kiran mahalincin mu muna da shekara biyu da dawowa makka lokacin. Alhamdullahi da fatan an dauki wani darasi a cikin dan takaitattacen labarina na fahinci rayuwa bai tafiya ga mutum daidai sai tare da dan uwansa da duk maison ya ga haske a rayuwa ya rike zumunci in mace ko namiji don naga hakan a rayuwan gidan mazajen Alhamdullahi muna cikin rufin Asirin Allah sosai a yanzu fiye da lissafinki mai karatu da fatan zaki yafeni inda nayi kuskure Allah ya bamu ikon cikawa da imani amin ya Allahu. ZAINAB IDRIS MAKAWA.