*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.}``` ✏️ ____________(✪)______________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• SHAMEEKH B̶̶O̶O̶K1 Officially 𝘽𝙮 Harira Salihu Isah (Uwar batooler) 𝘔𝘈𝘙𝘜𝘉𝘜𝘊𝘐𝘠𝘈𝘙 '𝚈𝙰𝚁 𝚂𝙰𝚁𝙺𝙸 𝙲𝙴𝙴! Paid #300 '𝚈𝙰𝚁 𝙺𝙰𝚁𝚄𝚆𝙰! Free 𝙹𝙰𝙷𝙸𝙻𝙲𝙸 𝙺𝙾 𝙰𝙻'𝙰𝙳𝙰! Paid #500 𝙼𝙰𝙵𝙰𝚁𝙺𝙸 𝙽𝙰𝙷! Free ᴀɴᴅ ɴᴏᴡ 𝘚𝘏𝘈 𝘔𝘌𝘌𝘒 𝘏 PAID #500 𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠 ‫ اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله‬SAW 🖤🤍 Ina mai godiya ga Allah da ya bani iko da daman fara wannan sabon littafin nawa mai suna SHAMEEKH, Allah sa mu kammala lafiya, duk abinda ya ke ba dai-dai ba a ciki Allah ya yafemu duka, ni mai rubutawa da ku masu karatu, FAN'S ina matuƙar ƙamnarku, Uwar batoorl na mugun yinku irin sosai ɗin nan, masu daraja habibties. SADAUKARWA NE GARE KU Masoya alƙalamin Uwar batoorl. TUKUICI NE GARE KA SIR Abubakar Sadeeq CEO lafazi writer's association (gidan karamci) Da kuma ɗaukacin member's namu. GARGAƊI: masu YouTube channels, masu yin Audion littafi, kada wacce ta ɗaura mini littafi ba da yawu na ba, domin muddin na ci karo da haka to ko wacece/ wanene zan ɗau mummunan mataki a kai, hukuma za ta rabani da mutum, A KIYAYE!. ̶ ̶F̶r̶e̶e page Mareeyata wannan page naki ne kiyi yacce kike so da shi, Uwar batoorl na jinjina miki da sharhinki. Shafi Na Ɗaya. ⭐ DUBAI kwance yake a makeken haɗaɗɗen gadonsa wanda ya haɗu ya gaji da haɗuwa, lulluɓe yake da blanket mai shegen laushi ya rufe dukkan ilahirin jikinsa ko ɗan yastansa ba ka hangowa, ba abinda ke tashi a hamshaƙin haɗaɗɗen daƙin nasa sai wani arnen ƙamshi mai sanya nistuwa, da kuma sautin ac wanda ya taimaka wa ƙamshin wajan jefa duk wani halitta da ke cikin ɗakin a yanayi mai daɗin gaske. Wayansa dake saman bedside drawer ne ya fara ringing, waƙan jimmy na Colorado ne 𝙈𝙮 𝘾𝙤𝙡𝙤𝙧𝙖𝙙o! 𝙮𝙤𝙪'𝙧𝙚 𝙢𝙮 𝙩𝙤𝙣𝙮𝙞 𝙢𝙮 𝙩𝙤𝙢𝙖𝙩𝙤! 𝙢𝙚 𝙞 𝙜𝙤 𝙩𝙖𝙠𝙚 𝙮𝙤𝙪 𝙩𝙤 ke tashi yayinda wayan ke kan kukan neman agaji! 𝙨𝙬𝙚𝙚𝙩𝙤!𝙮𝙤𝙪'𝙧𝙚 𝙢𝙮 𝙨𝙚𝙫𝙚𝙣 𝙢𝙮 𝙧𝙤𝙣𝙖𝙡𝙙𝙤! 𝙚𝙝𝙝! 𝙚𝙝𝙝! 𝙢𝙮 𝙜𝙚𝙡𝙖𝙩𝙤𝙤!!! Ƙiran ne ya tsinke, ba jimawa wani ƙiran ya kuma shigowa, sai lokacin wanda ke cikin blanket ɗin ya ja siririn tsaki tare da mirginawa ya gyara kwanciyan sa hankali kwance ba ko alamun zai bi ta kan wayan balle mai ƙiran ya samu arziƙin a amsa masa. Bayan second's sai wayan ta kuma sanya kukan neman agaji, wannan karon wanda ke cikin blanket ɗin a yangance kaman ba ya so ya miƙo haɗaɗɗiyar hanunsa ya sanya wayan a silent, hannunsa ya maida cikin blanket nasa dan yasan yanzu kam zai yi bacci hankali kwance. Bayan kaman mintuna talatin har bacci ya fara awun gaba da shi, kaman a mafarki ya kuma jiyo kukan ɗayan wayansa dake kan gadon a kusa da shi, ringing tone ɗin tashi, (S𝙝𝙚'𝙨 𝙩𝙝𝙚 𝙖𝙣𝙜𝙚𝙡 𝙤𝙛 𝙢𝙮 𝙡𝙞𝙛𝙚, 𝙞 𝙙𝙚𝙮 𝙘𝙖𝙡𝙡 𝙝𝙚𝙧 𝙨𝙪𝙥𝙚𝙧 𝙬𝙤𝙢𝙖𝙣.....) kawai ya isa ya sanar da kai wanda ke ƙiransa, domin waƙan Simi na Maamaa ne ke Wannan karon tunda ko bai duba ba yasan mai ƙiransa, cikin nistuwa ya fito da hannunsa ya ɗau ƙiran tare da sanya wayan a hansakuwa (hands-free), ajiyewa yayi a gefen kansa dake cikin blanket har yanzu, daddaɗan sautin muryan sa na fara jiyowa, cikin ladabi yayi sallama tare da faɗin, "Ummiy naaa!" Ajiyahn zuciya wacce ya qira da Ummiy ta yi a ɗaya ɓangaren, sannan ta ce, "Allah Ubangijin kowa da komai ga yarona nan Rabbi ka shirya mini shi ka tsare mini shi kayi ma rayuwarsa gaba-ɗaya albarka." Ƙasa-ƙasa kaman wani mara gàskiya ya ce, "Ameen ya Hayyu ya Qayyum hajiyarmu." "SHAMEEKH wai yaushe za kaji maganata ne? Yaushe za kayi abunda ya kamata? Yaushe za ka girma ne kam?" "Ummiy kiyi haƙuri Allah ina sane kuma ina shirin zuwa." "Au! Ashe kana sane? Tom naji tunda kana sane yaushe ne?" "Ummiy zan zo a ƙarshen satin nan Insha Allahu." "Ashe dai baka sane tunda ba kasan yaushe bane kuma sai qarshen sati kayi niyan zuwa, zuwan naka ma nasan ba tabbas wataƙila ne, Allah ya shirya ka Shameekh." Shagwaɓe murya yayi kaman mace ya ce, "Ayya dai Ummeyh da gaske fa zanzo in Allah ya yarda." Ummiy ta ce, "Za kazo ne kake ƙin ɗaukan ƙiran mutane, to bari na faɗa maka za a ji mu akan maganar nan, kar kazo akan lokaci kuma kasan sauran wajan Hajiya za ku gamu ne ba ruwana tunda dama kai ba baƙon ta bane balle ka ce yanzu kake ji daga bakina." "Ummiy ayi haƙuri." "Shikkenan bakomi Allah maka albarka ya karemin kai ya kawo ka lafiya." "Ameen Ummiy na." "Ka kula sosai, ka daina ganin kai ɗa namiji ne ka kula da kanka ka kare mutuncin ka nasan matan wajen nan wasu sai a hankali." "To! Insha Allahu Ummiy, a cigaba da mana addu'a." Hira suka ɗan yi kaɗan ta masa faɗa kaman koda yaushe idan suka yi waya, sallama suka yi ta kashe wayanta, shi kuma Shameekh gyara kwanciya yayi da niyan cigaba da baccin sa, me ya tuna kuma sai ya fasa kwanciyan, yaye blanket ɗin yayi ya tashi ya zauna tare da jingina da kan gadon idanuwansa a lumshe. Zara-zaran yastun ƙafafuwansa na fara gani wanda suka sha gyara suna yalƙi ga su farare tass kaman na ƙafan jariri, sanye yake da farin pyajams da yayi mugun amsar fatansa kasancewan shi ɗin ma fari ne, daga yanayin yanda yake akan gadon kasan dogo ne shi ko ba'a faɗa ba, yana da ɗan jiki dan baza'a ce masa siriri ba, yana da faffaɗan ƙirji mai cike da haiba, gashin kansa kwance suke luf-luf duk da ba wai tara gashin yake yi ba, amma yayi wani irin aski na zamani ne wanda yayi mugun yi masa kyau. Fiskansa nabi da kallo wanda idanuwansa suke a lumshe, yana da dogon hanci ga kuma ƙaramin baki me dauke da jajayen lips nasa gashin giransa a cike yake kaman na mace wanda hakan ya qara masa kyau sosai, damatsan hannunsa ma kaɗai abun kallo ne, dan kana gani kasan kaga ingarman namiji jarumi kuma ƙaƙƙarfa. Hanunsa ya miƙa zuwa bedside drawer yana laluɓa wayansa, jin bai taɓa ba sai ya buɗe idanuwansa a hankali yana kallon wajan da hannunsa yake, idanuwansa madaidaita ne farare tas da su sai dai baƙin cikin yayi kaman brown-brown. Jawo wayan yayi tare da cire sa a key, call logs ya shiga dan ganin misscalls da aka masa, ganin number ba suna yayi misscall biyu sai ya taɓe baki, ɗayan kuma da yaga numbern Daddynsa ne sai ya bi ƙiran. Bayan wayan yayi ringing aka ɗauka, muryan babban mutum na jiyo saboda a hamsakuwa ya saka wayan, "Assalamu alaikum son." "Waalaikassalam, Na'am Daddy an tashi lafiya?" "Lafiya Alhamdulillahi! son ya ƙasan mutane ya al'amuran?" "Ga su nan fa Daddy duka babu daɗi." "Masha Allah! yaushe za ka shigo?" Ɗan sosa ƙeya yayi tare da kawar da wayan a kunnen sa, yana faɗin, "Allah nagode maka", ƙasa-ƙasa. Daddy ta ɗaya ɓangaren dariya yayi ya ce, "Wato mun dameka yaushe zaka dawo, hakan na nufin Umminku ta ƙira ka, to Allah shirya ka ya maka albarka." Da "Ameen" Shameekh ya amsa, waya suka yi ba jimawa suka yi sallama, yana cewa Insha Allahu zai shigo ba jimawa. Ɗayan layin ya ƙira, yana shiga ana ɗauka, "Hello Yaya Man ya akayi ya Dubai ɗin?" faɗin wanda ya ƙira ta ɗaya ɓangaren. "Lafiya komai normal." "Haka akeso, ya yaushe ne za ka shigo kuma?" "Ba zai jima ba Insha Allah, za ku ganni" faɗin Shameekh. "Ko dai kuna da wasa ne?" "No babu fa kai dai na kusa shigowan in Allah ya yarda." "To Allah ya amince, Allah ya kawo la lafiya, Yauwa na ƙiraka da wani number ma ba ka ɗauka ba, ko da yake ma ba ka ɗau layina ba balle wani layin." Shameekh shafa kansa yayi yana murmushi ya ce, "Kai ma dai ka so neman magana Sadeeq, kasan bana ɗaukan baƙon layi." "To sannu ɗan wasa" cewan Sadeeq a ɗaya ɓangaren yana dariya. Shameekh murmushi yayi wanda ya ƙara masa kyau sosai, sai ya ce, "Afuwan Sadeeq." "Ba mastala Man sai mun ganka." "To ka gaidamin su Abba su Baba duka." Sallama sukayi, ya kashe wayan ya ajiye a kan drawer dake gefen gadon, sauqa yayi a gadon yana miƙa wanda hakan ya bani daman ƙare masa kallo, zubinsa na jarumai ne jaruman ma jaruman gaske, jikinsa a mummurɗe ga ƙwanji mai ɗaukan hankali. Cikin takunsa na ƙasaita ya shige haɗaɗɗen toilet nasa, bayan shigansa da mintuna wata baturiya ta shigo ɗakin ta gyara shi tsaff ta gama komi cikin mintunan da basu haura ishirin ba, tana gamawa ta fice dan dama ta gyara palourn da sauran ɗakunan gidan. Bayan fitan baturiyan da kusan mintuna arba'in ya fito a toilet ɗin, sanye da rigan wanka a jikinsa, fari ne tass rigan wankan ma, gaban dressing mirror ya wuce direct, bayan ya share jikinsa da ƙaramin farin towel dake hanunsa, sai ya jawo mansa ya shafa, ƙamshin wannan mannasa yafi wani turare. Bushar da suman kansa da ba yawa yayi, ya ɗauko mayukan da sukafi kala biyar ya haɗa ya shafa a gashin kansa, sheƙi gashin ya keyi dan daman baƙi ne gashin, ya kuma taje kan nasa, sai da ya ɓata kusan 1 hour kamun ya wuce wajan ma'adanan kayansa wanda yake babba sosai wani waje kaman switch ya danna a take ma'ajin kayan ya buɗe, ganin kayan nasa sai ya yamusta fiska, dan har kaman zai juya ya fasa ɗaukan kayan sai kuma mai ya tuna ya juyo, ƙananun kaya ya ciro , farar riga da baƙin wando sai P-cap black. Kayan ya fesawa turaruka kusan guda shida, sannan ya ajiye kayan a wani waje wanda musamman na ajiye kaya ne a gefen dressing mirror, angogon maƙalwa a hanny ya ɗauko, baƙi designer mai stadan gaske, sannan ya ciro takalminsa baƙi sau ciki, ƙirar Dubai wanda kuɗinsa ya kai 750k. Sai da ya ciro komai da zai buƙata sannan ya fara warware rigan wankam da ke jikinsa, kwantattun gashi ne a jikinsa mai tafiya da hankali gami da imanin duk mai kallonsu, dan sosai gashin jikin yayi masa kyau kasancewan sa fari kuma farinsa mai yellow-yellow ne. Short da vest nasa duka farare ya saka, wannan baturiyan ce bayan ta gama gyara dinning tayi komai ta zo ta ƙwanƙwasa masa ƙofa, ya gama shiryawa kenan yana taje sajensa da gemunsa da yake dai-dai da fiskansa, amsawa baturiyan yayi ta hanyar bata izinin shigowa, turo ƙofan tayi ta shigo ta ɗan rusuna ta ce, "Sir your breakfast is ready." "Ok" shi ne kawai abinda Shameekh ya faɗa, sai ta miƙe ta fice, turarukansa ya ɗauka ya feshe jikinsa ba abinda ke tashi a jikinsa ko ta ina sai ƙamshi kawai, keyn motansa da ke kan mirrow ya ɗauka, yaje wajan gadonsa wanda ke a gyare nit, kallon bedsheet ɗin da aka saka masa brown colour ne yasa shi jan tsaki ya ɗauki wayoyinsa ya juya ya fice a ɗakin fiskan nan a haɗe. Baturiyan ya samu tsaye a wajan dinning tana jiran zuwansa dan ta yi saving nasa, wucewa yayi ya zauna yana huci cikin harshen turanci ya ce, "Hey you!" Zuwa tayi da sauri ta staya daga gefe jikinta har yana ɗan rawa saboda yanayin da ya mata maganan, shi kuma kallon sama da ƙasa ya mata sannan ya ce, "Are you out of your sense or you are okay with the work you want to leave? Okay! then am paying you now so that you can leave cuz i can't take this nonsense for no reason." Jikin baturiyan na rawa tana faɗin, "Am sorry Sir³." Harara ya dalla mata ya ce, "Sorry for your self, if you want ur work again go and remove that useless bedsheet you use for my bed ,and this should be first and last don't you ever use this colour for my bed again, infact not even bedsheet anything in this house is either you use white, blue or black hope you get me?" "Am sorry Sir! Abinda kake so shi zan yi, yau ma stautsayi ne" faɗin baturiyan da turanci dan kana ganinta kasan hankalinta har ya tashi jin zai sallameta. A gadarance ba tare da ya ƙara kallon inda take tsaye ba ya ce, "Oyah! Go and take a look again to my rules for being a maid in this house" ya faɗa yana wucewa dinning ɗin ya ja kujera ya zauna. biyosa baturiyan tayi dan tayi saving nasa, kallon da ya mata ne ya sanya ta saurin juyawa, shi kuma staki yaja tare da mayar da kallonsa kan dinning ɗin ya ciro wayansa yana lastawa. Bedroom nasa ta wuce direct ta cire wannan bedsheet en tare da blanket ɗin duka, White bedsheet ta ɗauko ta shimfiɗa kaman yacce yake so, ta ɗauko black blanket me laushin gaske shima ta shumfiɗe sa, sannan ta ƙara gyara ɗakin, daman ya hanata shiga masa bathroom shiyasa ba ta bi ko hanyan ba, ba ta ma san inane bathroom ɗin ba, tana gama abinda ya kamata tayi ta fice ta samesa zaune yana danna wayansa, coffee ta haɗa masa dan shine abincin sa da safe sai dai sometimes yakan buƙaci chip's, ta buɗe baki za tayi magana kenan ya ɗaga mata hanu alaman baya son jin komai daga bakinta, shiru tayi abinta tare da juyawa tabar dinning ɗin tunda tasan baya son yana cin abu a staya a kansa. Shanye coffee ɗin yayi duka ya ɗau tissue ya goge bakinsa ya ɗauki keyn motansa ya fice a palourn, wajan haɗaɗɗiyar motansa mai shegen kuɗi ya nufa, yana shiga ya mata key, baturiyan kuma tana jin mostin sa ta fito da sauri ta bisa har wajan motansa ta ce, "Sir what should i cook for lunch?" Shameekh bai ko kalleta ba ya taɓe baki ya ce kar ma tayi girkin komai da shi, in za tayi to ta yi nata da gate man, yana gama magana ya ja motansa ya fice da mugun gudu, baturiyan jiki na rawa ta juya ta koma ciki, gyara dinning ɗin tayi ta kuma gyara palourn sannan ta tattara ta wuce kitchen, duk da ya ce banda shi amma za tayi ta ajiye ko dan visitor's tunda ya kan yi baƙi lokaci zuwa lokaci. ⭐ NIGERIA Damaturu-yobe State. Anguwan Shagari, anguwa ne na masu abin hannu, akwai gidajen masu rufin asiri amma akwai manya-manyan gidaje na masu kuɗin gaske, wani ɓari na anguwan kuwa wasu manyan gidaje ne wanda kusan duk yanayin ginin iri ɗaya ne, sai dai amma ko wani gida da gate nasa, gidajen suna jere kusan guda tara, ɗaya na kallon ɗaya, kuma duka gidajen ba ƙaramin girma ne da su ba, gidan da yake na uku a jeri shi na kusta kai ciki, gida ne haɗaɗɗe ya haɗu iya haɗuwa, dan tsayawa tsara irin haɗuwan gidan zai cinye mana page guda, cigaba da kusta kai na nayi har dai na tsaya dai-dai gefen wani ƙofa da na ke iya jiyo sautin mutane a ciki, ɗakin na tunkara, ina buɗe ƙofa nayi arba da wasu stala-tsalan kyawawan ƴammataye guda shida 6 zaune a cikin ɗakin. Guda uku na zaune a kan gado, ɗaya na zaune a kan mirrow sai kuma sauran biyun da ko wacce ke zaune akan stool nata daban, da alama duka ƴammatayen shekarunsu zai yi kusan dai-dai, kana ganinsu kasan sa'annin juna ne, ba za su wuce 22year's to 23year's ba, ko waccen su da waya a hanunta qirar i phone, ƴammatayen dukkansu farare ne tass kaman larabawa, sannan kyawawa ne dai-dai gwargwado Masha Allah! Ɗaya wacce ke zaune akan stool ne tayi magana ta ce, "Guys wallahi na mastu yaya Soffy ta dawo, nasan akwai show a gidan nan, wannan karon stoho zai yi shara." Ɗayar da ke zaune a ɗayan stool ɗinne ta ja siririn tsaki tare da aikawa wacce ta fara magana harara ta ce, "Amma dai Meelat da gangan da neman magana kika yi wannan maganar, kinsan dai ba wani shiri muke da yaya Soffy ba, duk idan ta zo sai tabi ta addabi rayuwan mutane akan wannan ɗan gidan masu ji da kai ɗin" matashiyar budurwan ta ƙarisa magana tana ɓata fiska. Wacce ke zaune a bakin mirrow ce tayi magana, kuma da alama ta ɗan fi su shekaru dan zata yi iya kai 25year's, wayan hanunta ma yafi nasu dan ita iphone 14pro ne a hanunta saɓanin su da yawancin su iphone X ne sai kuma 11pro a hanunsu, a zuciye da kuma tsawa-tsawa ta ce, "Subby can you plss close ur mouth, mai ya miki? mai ruwanki da shi? So karki kuma faɗa masa mai ji da kai, infact idan ba raini da ke damunku ba, ai ko Ya Sabeer ma ya girme shi, amma kina ƙanwar bayansa kina rena sa, so wannan ne last warning da zan muku akan sa, you guy's should watch your tongue's idan har kuna so mu shirya." Wacce da alama ita ce Subby sai ta tura baki tare da kawar da kai irin bata so faɗan da aka mata ba. Waɗanda suke zaune a kan gadon me za suyi idan ba dariya ba, duk dariyan Subby suke yi har dai suka stagaita, sannan ɗaya a cikinsu ta ce, "Ke ma Subby wa ya aike ki yin wannan magana? kinsani fa sarai yaya Jidderh ma tana ciki kuma dai ita ce sarauniyar" faɗin Deeyah tana murmushi. Wacce ke kan mirrown tashuwa tayi ta nufi hanyan ficewa a ɗakin tana danna wayanta tare da faɗin, "Zama a cikinku ya fara ja mini reni, tunda kun kalli kan mu ɗaya yanzu duk kun kamo ni tsayi", ta ƙarisa maganan tare da ficewa a ɗakin ta turo musu ƙofa. Meelat ce tayi fiskan tausayi tare da cewa "Dee, Leemah da Deeyah meyasa kukayi dariya bayan kunsan yaya Jidderh da saurin fushi, yanzu ga shi kun ja ta ɓata rai, kuma dai kunsan gwanda ita a kan yaya Soffy, ita ke zama a cikinmu ba ruwanta da mu ƙannenta ta yi wasa da dariya da mu, in dai hauka ne da a gaban yaya Soffy kuka yi wannan maganan ai da tuni kun gansa, da an bawa kowa sadakan bugu a baki." Meelat ta ƙara mai da idonta kan Subby ta ce, "Kinsan halin yaya Soffy sarai a kan shi, ni kuma duk ba dan komai nace na matsu ta dawo ba, wallahi nayi kewanta ne kawai, kunsan muna shiri da ita nikam." Subby taɓe baki tayi ta ce, "Ku kuka sani yanzu kuma" ta tashi ta shige toilet. Wacce aka ƙira da Dee ta ce, "Ai kuwa nikam anjima zan dangana da gidan stoho na bawa yaya Jidderh haƙuri dan nasan yanzu haka can ta wuce, bawa yaya Jidderh haƙuri ya zama mini farilla ni da nake dakon wayan hanunta, naji wai wancan wahalallen saurayin nata zai sauya mata kuma fa kunsan ba amsan na hanun nata zai yi ba." Leemah ta ce, "Nima zan biki mu bata haƙuri dan gaskiya banason fushin yaya Jidderh tamu." Deeyah jin abinda suka faɗa sai ta kwashe da dariya ta ce, "Ke ma Leemah nasan abu kika gani kike so tabaki, kunsan yaya Jidderh da kyauta, anyway ni banson komai amma nima zan bata haƙuri." Meelat murmushi tayi ta ce, "Da ya fi muku kam, kunsan dai yaya Jeeddeerh ita ce idonmu a gidan nan, serious bai kamata muna ɓata mata rai ba, Subby ce kawai da ba ta ji da ƙaton kan ta." Subby da fitowanta kenan daga toilet, jin abinda Meelat ta ce sai ta aika mata da harara." Meelat ta ce, "ki harareni da kyau, amma ko menene dai ke ce kika fara maganan da ya ɓata mata rai." Dee ta ce, "Yanzu dai a matsayina na Auntynku in absence of yaya Jeeddeerh ni yaya Fadeela na ce case close." Dukkansu biyar ɗin dariya suka saka har da ita Dee ɗin da tayi maganan, Deeyah ce ta fara hararanta ta ce, "Waye sa'anki a nan? dan kawai kin ga ba kya ce mana yaya shi ne har da reni, wai yaushe ma kika cika 21year's ne Dee?" Tura baki Dee tayi tare da faɗin, "To nidai naji ko nice ƙarama na ɗau matsayin manya na ce a rufe babin maganan ya wuce." Subby murmushi tayi ta ce, "Nikamma Deeyah kin tuna mini birthdayn mu ya kusa, akwai cin kuɗi, kaiii gaskiya dole ma na bawa yaya Jidderh haƙuri nima." Leemah ta ce, "za ma ki dawo hanya ai wallahi, indai yaya Jidderh ce ko wa ma yasan yana cin albarkacinta kuma tana yi wa kowa kirki." Meelat miƙewa tayi tare da buga stalle kaman ƙaramar yarinya ta ce, "kowa ya tuba dan wuya ba lada, sai da ke yaya Jidderh tamu." *** Juma'at Kareem. MASU DARAJA HABIBTIEES NA UWAR BATOORL AKWAI GARAƁASA GUDA, A YANZU KAMUN MU KAMMALA FREE PAGE'S TO KUƊIN LITTAFI DAI #300 NE, IDAN MUN KAMMALA KUWA #500 YAKE INSHA ALLAH. 9161720046 Harira salihu isah Opay & 2220553988 Harira salihu isah Uba Shedar biya ta wannan layi 07015870735. Mutanen Nijar ku ma ku yiwa wannan layi magana dan yin payment naku 07015870735. # Hareeyh # 09161720046 # 07015870735 # 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩 # 𝙇𝙞𝙠𝙚 & # 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚 SHAMEEKH B̶̶O̶O̶K1 Officially 𝘽𝙮 Harira Salihu Isah (Uwar batooler) ‫ اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله‬SAW 🖤🤍 GARGAƊI: masu YouTube channels, masu yin Audion littafi, kada wacce ta ɗaura mini littafi ba da yawu na ba, domin muddin na ci karo da haka to ko wacece/ wanene zan ɗau mummunan mataki a kai, hukuma za ta rabani da mutum, A KIYAYE. SHAMEEKH or SHAMIKH : is an Arabic name that is use interm of naming a muslim baby boy, the name Shamikh is drive from the holy Qur'an chapter 77 verse 27, Shameekh mean's HIGH, LOFTY and ABOVE ALL OTHER'S. Yauwa waɗanda ke da mastala akan basu iya faɗan sunan ba, idan suka karanta ayar za su fahimci yanayin yacce ake ƙiran sunan, a cikin suratul MURSALAT aya ta ashirin da bakwai. ̶ ̶F̶r̶e̶e page Page naku ne Surryta Habiba Muhammad Yusuf PAID #500 Shafi Na Biyu. ⭐ ADAMAWA STATE. FEDERAL MEDICAL CENTER YOLA. Wata farar mata ce ta fito a ɗaya daga cikin ɗaƙunan malaman asibiti da ke jere a floor ɗaya, office ne wanda yake a jerin na manyan likitoci masu duba mastalan da ya shafi mata, dattijuwar matar da kana ganinta kasan ta manyanta, sanye take da leshi baƙi ɗinkin dogon riga wanda yayi mugun amsarta, hijab nata fari tass ɗan dai-dai, idanuwanta ta maƙala musu glasses fari, amma kana gani kasan medicated glass ne ba na gayu ba, hanunta riƙe da labcoat, tafiya take cikin nistuwa fiskanta yalwace yake da murmushi, jama'a sai ɗaga mata gaisuwa suke tana amsawa tun fitowanta office nata har ta iso inda drivernta ke jiranta, tana isowa wajan motan sai drivern yayi sauri zai buɗe mata ƙofa, amma sai ta dakatar da shi, fiskanta da fara'a ta buƙaci ya bari za ta buɗe da kanta, drivern ba dan ya so ba ya masta ta buɗe ta shiga tare da karanto addu'an hawa ƙarfe, ajiye abubuwan hannunta tayi a gefenta tare da gyara zamanta tana hamdala ga Allah. Driver ne ya ce, "Sannu da aiki Hajiya." Tana murmushi ta amsa masa, tare da tambayansa nasa aikin, shi ma ya amsa mata, counter(carbin irge) da ke maƙale a yastunta ta gyara tare da cigaba da yin tasbihin da take yi, ƙira ne ya shigo wayanta dake cikin jaka, Jawo jakan ta yi ta buɗe ta ciro wayan, sautin qira'a na Amanar-rasulu yana tashi, amma kamun ta gama ciro wayan har ƙiran ya yanke, tana cirowa ta duba ta ga layin Alhaji ne, murmushi kawai ta kuma yi tare da bin ƙiran, yana shiga ringing ɗaya kawai yayi aka ɗauka, ita ta fara yin sallama cikin nistuwa da girmamawa ga wanda ta ƙira ɗin. "Assalamu Alaikum Baba an wuni lafiya?" "Lafiya ƙalau Alhamdulillahi Fatima, ya kike? ya aiki?" Faɗin muryan wani stoho a ɗaya ɓangaren. Matar ta ce, "Lafiya Alhamdulillahi Baba, yanzu haka ma tasowana daga asibitin kenan ko gida ban ƙarisa ba." Gaisawa suka yi ta tambayi stohon ƙarfin jikinsa, ya amsa mata da sauƙi sannan ya ce, "Fatima wai ina labarin abokinane kam?" Matar murmushi ta yi ta ce, "Ya na can lafiya baba, munyi waya ɗazu ma ya ce yana gaisheku kuma in Allah ya yarda yana shigowa." "To! To! Madallah, Allah kawo sa lafiya, Allah muku albarka duka ku da zuria'anku." Da "Ameen" matar ta amsa, sannan stohon ya faɗa mata ga Hajiya ya miƙa mata wayan suka gaisa, Hajiyan ta ce, "Faɗimatu wai yaushe za ki shigo ne?" Matar na murmushin jin tambayan mahaifiyarta ta ce, "Mama wai daman ina jiran mai-gidanki ne, idan ya zo sai mu taho tare." Hajiya a ɗaya ɓangaren ta ce, "Me haɗin Dubai da Adamawa?" "Babu mama" faɗin matar tana murmushi dan tasan za'a yi haka daman. "To idan har kin yi niyan zuwa kawai ki zo, shi kuma idan ya ga dama kar ya zo za mu haɗu ne, ni da shi ɗin" Hajiya ta ƙarishe maganan da ƙwafa. "To shikkenan Mama, Insha Allah za mu taho ranan asabar tare da kishiyanki." "Allah kai mu, Allah miki albarka, Allah kawo ku lafiya dukanku." "Ameen Mama." Suna gama magana suka yi sallama ta kashe wayanta, dai-dai lokacin sun iso gidan su dake anguwan Abuja road, buɗe musu gate aka yi suka shige, bayan driver yayi parking ta fito dan shigewa cikin gidan, sai ga wata kyakkyawar yarinya budurwa, yar kimanin shekara sha takwas ta zo da gudu, tana faɗin, "ayoyoo Ummiy sannu da dawowa", ta rungume ta. Ummiy na murmushi ta ce, "sannu babyn Ummiy, ɗauko jaka na da labcoat a mota", ta faɗa tare da raba yarinyar da jikinta. Yarinyar ta ce, "To Ummiy na." Shigewa cikin gidan Ummiy tayi da sallama, Talatu yar aikin su dake goge palourn ne ta amsa, stugunnawa tayi har ƙasa ta ce, "Sannu da dawowa Hajiya." "Yauwa Talatu sannunki kema da aiki", Ummiy na gama faɗan haka ta wuce ta haura matakalan da zai kai ta sashinta da ke sama, sannan ta nufi ɗakinta. Shiga ɗakin tayi da sallama duk da ba kowa a ciki,(Ku zama masu yaɗa sallama ko da kuwa babu mutane a wajan, domin akwai salihan bayi mala'ikun da ke amsawa, kuma suke jira ka yi sallama dan su rubuta maka ladanka), hijab nata ta cire ta wuce banɗaki direct. Yarinyar da Ummiy ta ƙira da Baby ce ta shigo ɗakin da sallama ita ma, jin shiru ba wan da ya amsa mata sai ta turo ƙofan ta shigo, jin ƙaran sauƙan ruwa a banɗaki, shi ya tabbatar mata da Ummiy na ciki, ajiye mata jakan tayi da labcoat nata a ma'ajiyarsu, sannan ta nemi waje ta kwanta a kujeran dake cikin ɗakin daga gefe, tana jiran Ummiyn nata, bayan mintuna Ummiy ta fito. Wucewa tayi wajan dressing mirrow ta shafa mai da turaruka masu qamshin gaske ( lallai anan Shamikh yayi gadon stafta, son ƙsmshi da komai ma). Bayan ta gama shiryawa dogon riga mara nauyi ta ɗauko ta saka, sannan ta zauna a bakin gadon nata, sai da tayi hamdala na daɗin jikinta da ta ji, sannan ta ce, "Baby ina ga dai bakinki akwai magana." Baby tashuwa tayi tana murmushi ta ce, "Ummiy nayi missing na big bro ne wallahi." Ummiy ta ce, "Ikon Allah! Baby anya magananki akwai gaskiya?" Turo baki tayi ta ce, "Da gaske fa Ummiynmu, yauwa Ummiy yaushe za mu je Maiduguri ne nikam?" "Yauwa kin tuna mini ɗazu mun yi waya da Hajiya Mama na faɗa mata za mu shigo ranan Asabar in Allah ya yarda." "Wayyooooo! Allah bar mana ke Ummiy, Allah nayi missing na Maiduguri barin ma aunty Jidderh ta, shiyasa nake son wannan family meeting ɗin, saboda lokaci nayi za ka kalli kowa, gaskiya Allah sambaɗawa stoho albarka, da ya kawo wannan ingantacciyar shawara." Murmushi Ummiy tayi tare da amsawa da Ameen, an ce Allah ya yiwa stohonta albarka, sannan ta ce, "Ki tabbatar dai kin shirya kamun ranan idan ba haka ba kuma tafiya zan yi na barki dan ina son mu tafi da sassafe ne." Zaro ido baby tayi ta ce, "Ummiy dan Allah mu bi Flight wallahi nikam bazan iya zaman mota ba." Kallonta Ummiy tayi, tare da yin murmushi ta ce, "Daman so nake naji me za ki ce baby, kekam ko stunstu ya ganki ya barki da son firewa, ke da jirgi kam inaga pilot zan bai wa aurenki." Cunna baki tayi ta ce, "Ni dai Ummiy koma me in dai Flight za mu bi shikkenan komai dai-dai ba mastala, kuma maganan big bro ma nafasa sai ya zo", daman har ta miƙe tsaye sai ta koma ta zauna kusa da Ummiy ta ce, "Ayya Ummiynmu, dan Allah idan big bro ya zo ki faɗa masa ya sauya mini waya, dan Allah dai kin ji Ummiyna." Ummi cewa tayi, "Ai daman nasan kwanar zancen, ba zai wuce wani abun kike so ba, ban da dai haka kawai baby ki ce kina kewan Shamikh, amma dai baby duk yaushe ya sanja miki wayan? ki din ga jin tausayin yayanki fa baby, akwai mutuwa, akwai jarabawar ubangiji, yau kana da shi gobe ba ka da shi, bana so ki saba da irin rayuwar nan, domin Allah na jarabtar bawansa a ko da yaushe, idan babu mu wa zai jure miki haka?" Sunkuyar da kan ta tayi ta ce, "Insha Allah Ummiy zan zama mai yarda da ƙaddara a duk lokacin da hakan ya samemu sannan zan kasance mai haƙuri da akwai ko babu." Murmushi Ummiy tayi ta ce, "To Allah ya miki albarka, ki shirya da wuri ko, insha Allahu kuma idan ya dawo zan saka shi ya sanya miki, ai ya zama dole a sauyawa autar Ummiy abin da take so, kuma autar Ummiy ma tasan yayanta yana ƙaunarta, mai mata komai ne ko babu Ummiy, muddin yana da halin mata." Murmushi mai kyau baby tayi tare da cewa, "Ameen Ummiy, Allah ya ja kwana ya barki da Daddy." Murmushi kawai Ummiy tayi, tare da faɗin Ameen ɗin a zuciyanta. "Ummiy bari na je nayi assignment da wani lecturer ya bamu tun jiya, amma fa Ummiy ki fito ki ci abinci kamun ki kwanta, kin ji Ummiyna" ta faɗa tare da tashuwa ta nufi ƙofa. Tashuwa Ummiy tayi ta bi bayanta, suka fito tare, dinning Ummiy ta wuce, ita Baby kuma tayi ɗaki ta ɗauko system nata, ta ajiye a kujera a palourn ta wuce dinning, samun Ummiy tayi tana shan kunun gyaɗa da ya ji haɗi. langwaɓar da kai baby tayi ta ce, "Yanzu Ummiy kunun kawai za ki sha fa na sani, ba za ki ƙara komai ba, bayan kinsan big bro baya son hakan Ummiy." Ummiy ta ce, "Sarkin surutu Ummiy bata jin yunwa, sai zuwa anjima." Ɗiban kunun tayi ita ma ta ce, "to Ummiy Allah ya kai mu anjiman, kamun na gama assignment ɗin sai mu miki favorite food naki." "To a gama lafiya, daman dai shi nake sha'awan ci." Baby cikin Palourn ta wuce riƙe da kofin kununta, system nata ta jawo ta buɗe tana assignment tana kurɓan kunun. Ummiy dake dinning ɗin ƙira ne ya shigo wayanta, ɗauka tayi tana amsa sallaman da aka mata a ɗaya ɓangaren tana faɗin, "Mamana kuna lafiya?" Shiru tayi da alama magana ake a ɗayan bangaren, can kuma ta kuma cewa, "Duk muna lafiya muma mamana, ga ƙanwarki lafiyarta lau ko ɗazu sai da tayi magananki." Murmusawa wa ummeyh tayi ta kuma faɗin, "Allah ya miki albarka Mamana, Insha Allahu muma muna zuwa ba jimawa." Juyawan da Ummiy za ta yi ba sai ta ga baby a gefenta ba tana faɗin, "Please Ummiy ki bani mu gaisa nasan Aunty Jidderh ce." "Mai anguwan garinku baby, ba dai kina da wayarki ba, to ƙira ta da naki ba zan ba da nawa ba." Jidderh ce tayi murmushi ta ɗaya ɓangaren ta ce, "Ayi haƙuri Ummiynmu a bata naji muryan ƙanwata." Ummiy miƙawa baby wayan tayi ta ce, "Karɓa ba dan halinki ba, kin ci albarkacin Mamana." Baby amsa tayi tana murmushi ta shagwaɓe murya kaman tana gaban Jidderh ɗin ta ce, "Yaya Jidderh ni fushi nake dake kwana biyu ba ki ƙirana shi kuma yaya inaji ya manta da ni ma kwana biyu shi ma bai mini recharging ba balle na ƙira ki." Jidderh ta ce, "Amana afuwa babynmu.' Ƙara tura bakin tayi ta ce, "Ni dai naƙi yaya Jidderh." "Haba dai in-law ta kuma ƙanwata." murmushi ne ya kuɓuce wa baby har da gyaɗa kai irin ta ji daɗin sunan, ta ce, "Insha Allah kuwa yaya Jeeddeerh ta, daga ke ba wata bayan ke ba ƙarii Allah bar mana ku." Jidderh ta ce, "Ameen ƙanwar kirki, yaushe za ku shigo?" "Ranar Saturday yaya Jeeddeerh, kuma ni awajanki zan sauƙa, bro Yusuf yana nan ai?" "Eh baby yana nan, Allah ya kawo mana ku lafiya." "Ameen yaya jeeddeerh", baby ta faɗa tana murmushi. Wayansu suka yi tana faɗin a gaida mata kowa da kowa, sannan suka yi sallama ta kashe wayan. Ummiy da already taga call nasu bame ƙarewa bane wucewa tayi sama dan ta huta kamun lokacin sallah yayi. Baby da ta juya taga ba Ummiy a dinning kuma bata palourn, ajiye wayan tayi a gefenta bata je kai mata ba dan ta san hutawa Ummiy taje yi, assignment nata ta ci gaba da yi. ⭐ Jeedderh ce a ɗakin da yake mallakinta, komai na ɗakin blue colour ne sai white, kwance take akan haɗaɗɗen gadonta, tana riƙe da wayanta ta zuba masa idanuwanta gaba ɗaya, da alama wani abu mai muhimmanci take yi duba da yacce hankalinta duka ke kan wayan. Wani sihirtaccen murmushin da jeedderh ke saki, wan da ya ƙara mata kyau, shi ya sanya ni leƙa wayan dan ganin abin da ke sanya ta, irin wannan sansanyar murmushin. Message Jidderh ke rubutawa, wan da na tabbata santin message ɗin ke sanya ta wannan haɗaɗɗen murmushin. Tana gamawa ta tura wa mallakin saƙon ba ɓata lokaci, turawanta kuma yayi dai-dai da shigowan ƙira a wayan nata, "SAFWAN" shi ne sunan da ya bayyana ɓaro-ɓaro, akan layin da ya ƙirata, Jidderh tura baki tayi kaman ba za ta amsa ƙiran ba, tana ji yana ringing amma sai da ta tabbatar ya kusa stinkewa, sannan ta ɗauka a hankali cikin nistuwa ta kai wayan kunnenta, muryanshi ta jiyo yana faɗin, "Hello baby ya kike?" Cunna baki tayi kaman yana gabanta ta ce, "Uhmn lafiya." "Masha Allah babyna ya labari?" Jidderh da ke jin kaman ta shaƙesa, a hankali ta ce, "Please Safwan zan yi sallah, idan na idar zan ƙiraka." "Okay baby am waiting a saka mu a addu'a, Allah kuma ya mallaka mini ke." Sai da Jidderh ta harari wayan, dan jin ya ce wani Allah sa ya mallaketa, sannan ta ce, "Okay byee", tana faɗan haka a taƙaice ta kashe wayanta. Sai da ta daste ƙiran sannan ta tura baki tana ƙun-ƙuni, can kuma ta tuno da maganan da suka yi da baby na katin waya, dafe kai tayi a hankali cikin sanyin muryanta ta ce, "Bari nayi sallah tukunna, zan tura miki babynmu ƙanwar miji", ta ƙarishe faɗa tana murmushi ita kaɗai. Sai da tayi dialling wani number da ta rubuta "ZAWJ", amma har sau uku tana ƙira ba'a ɗauka ba, haushi taji ta jefa wayan kan gado, tana tura baki har da bubbuga ƙafa ta yi hanyan toilet. Jidderh alwala ta ɗauro ta zo ta saka hijab tayi sallah, ta jima tana addu'ointa sannan ta shafa, tare da mayar da darduman da hijab ɗin mazauninsu. Banɗakin ta koma tayi wanka ta fito ɗaure da towel mai madedecin girma, fari tasss da shi, sai da ta shafa wani ruwan turare mai haɗi, ta zauna a haka jikinta ya bushe, sannan ta zo ta bi da man ta mai ƙamshi da Humra da kuma turaruka, iya abin da tayi kenan bata tsaya wani kwalliya ba, domin Jidderh ba ma'abociyar ɗige-ɗige ba ce. A iya shafe-shafen turaren da Jidderh tayi kawai, kar ku ga haɗuwan da tayi na kyau da baiwan da Allah ya mata, don jidderh kyakkyawa ce ta gaske, ita ba fara ce sol ba har can, sannan kuma ba za'a ce mata baƙa ba, ba ta da jiki sannan ba siririya ce sosai ba, tana da dirinta dai-dai wan da ya tafi da yanayin aukin jikinta, ƙirjinta madaidaita Masha Allah, ƙugunta ma duka Masha Allah son kowa ƙin wanda ya rasa, tana da dogon gashi har bayanta baƙi wuluk gwanin sha'awa, dogon hanci Masha Allah, ga bakinta ɗan dai-dai kaman ramin asusu, idanuwanta manya-manya waɗanda ake kira da golden eye's, a taƙaice dai jidderh kyakkyawa ce ta ƙarshe ma, duk iya yacce ake buƙatan mace to ta kai wajan, dan Allah ya wadata da komi Alhamdulillahi Masha Allah. Shiryawa tayi cikin pink sleeping dress mai kauri sosai, amma kayan akwai laushi da stansti, ga shi har ƙasa wandon ya kai mata, rigan kuma iya guiwa amma abuɗe gaban rigan yake sai igiya kawai, kayan sosai ya amshi Jidderh kaman ka sace ta ka gudu da ita. Wani ƙaton zumbulelen hijab ta saka black color, wayanta ta ɗauka da duk abin da za ta buƙata, sannan ta fice a ɗakin nata ta ja ƙofa ta rufe. Ɗakin mummy ta shiga ta sameta tana ninke hijabi ta idar da sallah kenan, tana kallonta ta murmusa tare da cewa, "Uwar masu gida sai ina haka da wannan hijabi kaman matar limami?" Murmushi Jidderh tayi ta ce, "Mummy za ni wajan takwarata na gaishe su da stoho, wataƙila ma na kwana a can." "Tom ki kula sosai-sosai, Allah ya tsare ki gaishe da baba Alhaji." Sai da jidderh ta juya tana ƙoƙarin ficewa ta ce, "Insha Allah mummy za su ji, yau zan je na ƙwace mijina." Mummy murmushi tayi tare da ɗaga murya yacce jidderh za ta ji, ta ce, "Za ku yi ku bari duk ku gama baba alhaji na hajiya mama ita kaɗai ce." Jidderh Ficewa tayi a gidan nasu tana tare da jan ƙofan palourn ta rufe, hanyan ficewa a gate na gidan nasu ta nufa, kusan cin karo suka yi da wani matashin saurayi kyakkyawa da shi, murmushi ya saki yana kallonta ya ce, "Ke kuwa stohuwa lafiya haka da ƙaton hijabi kaman mai zuwa ɗaukan darasi, ga shi sai sauri kike kaman mai shirin tafiya sama, sai ina haka?" Cunno baki jidderh tayi ta ce, "Allah yaya Faisal banaso nikam, ni ba stohuwa ba." Murmushi saurayin da ta ƙira da yaya Faisal yayi ya ce, "To naji Hajiya jidderh an daina, sai ina da daren nan?" "Yaya faisal gidan takwara zan je." "Au ki ce soyayyan stoho ta mosta za ki je ganinsa." "Ai kuwa kam kai da ka sani, idan ban ga wannan storhon ba ai babu bacci hankali kwance, balle kuma cikin nishaɗi." Murmushi Ya Faisal yayi tare da girgiza kai ya ce, "Faɗa ɗayan gaskiyan kada ki yaudari stoho, dan munsan ba shi kike nufi ba, wancan na Dubai ɗin kike nufi." Jidderh murmushi tayi kawai tare da kulle fiskanta wai taji kunya. Ya Faisal ya ce, "Ga shi na zo gaishe da mummy ne da na raka ki." "Lahh! Ya Faisal kar ka wani damu zan je ni kaɗai, kuma may be zan tafi da motana idan ƙuya ya bai hanani ba." "Okay sis Allah ya stare hanya ki gaishe da su nikam basu ganina sai ɗan Dubai ya shigo." Murmushi jidderh tayi kawai dan tasan stokana irin na ya Faisal, ta ce, "Byee Yaya Faisal." Wucewa jidderh tayi, tana isa bakin ƙofan, sai mai gadi ya taso zai ya buɗe mata ƙofa, ita kuwa tana murmushi ta ce, "lah! a'a baba wallahi ka bari zan buɗe da kai na, ka huta abinka." Baba mai gadi yana murmushi ya ce, "Hajiya Uwar masu gida ina za ki je da daren nan haka kinsan Alhaji ya hana fitanku, muddin aka yi Magriba." "Gidan takwara zan je baba, zan kwana a can ma." "To amma ai ke ɗaya bai yi ba kuma ga shi da ƙafa, ai ya kamata ki ɗau mota uwar masu gida, tun da dai kin iya", baba mai gadi ya faɗa yana murmushi, dan duk cikin jikokin wannan family a mata dai babu ya Uwar masu gida(sunan da ake ƙiranta da shi kenan), jidderh tana da hali mai kyau, ga kirki ga haƙuri, ga girmama manya, da sanin ya kamata, ba ruwanta da rena mutum dan yana aiki a gidansu, ba za ka taɓa jin ga jidderh tayi faɗa da wani ba tun tasowanta, shiyasa manya da yara ba wan da baya son ta a familyn, dan ta fita Zakka, kirkinta na daban ne(Wannan kuma hali ne na masu suna Hauwa'u kulu mai jidda). jidderh ta ce, "Bakomai baba, insha Allah zan je lafiya", suna cikin magana sai ga Faisal har ya fito daga wajan mummy, yana murmushi ya ƙariso wajansu tare da cewa, "Stohuwa har yanzu baki tafi ba?" "Eh Ya Faisal, inji baba mai gadi ne sai na ɗau mota ni kuma ƙuyan driving nake ji, daga nan zuwa gidan takwara kam." "Ai da gaskiyan Baba, uwar masu gida ba abar wasa ba, amma tun da har na fito sai muje na ajiyeki ba." "To Yaya Faisal." Baba mai gadi murmushi yayi tare da faɗin, "Alhaji Faisal ai zuwanka ya fi zuwan gomna, dan gwanda a kai ta, da daren nan gari ya kusa fara duhu tafiyanta ita ɗaya kuma a ƙafa bai yi ba, Allah ya kai ku lafiya, a gaishe da su Baba Alhaji." Amsawa Ya Faisal yayi yana murmushi, suka shiga motan nasa da jidderh, Baba mai gadi ya buɗe musu wangamemen gate ɗin suka fice, suna fita Ya Faisal na driving ba tare da ya kalli jidderh ba ya ce, "A gaskiya baba mai gadi ɗan amana ne sis, kalli fa ai irin wannan kulawan ko ƴar cikin ka iya haka za ka kula da ita, Allah dai ya kare masa zuri'ansa shi ma." "Ameen Ya faisal, Baba mai gadi kam ai ɗan aljanna ne, da amana da gaskiys yake aikinsa, amma meyasa naga ka fito da wuri?" "Daddy bayanan Mummy ce kawai kuma mun gaisa", faɗin Faisal da ke driving nasa. Suna zuwa ƙofan gate na gidan baba alhaji ya tsaya ya ce, "Ni ba shiga zan yi ba sis, ki sauƙa anan zan juya gida lokacin zuwa masallaci ma yayi." Murmushi jidderh tayi ta ce, "Nikam ai nagode hakan ma ya Faisal, Allah ba da ladan rage mini hanya", ta faɗa tare da ficewa a motan, suka yi sallama ta wuce ƙofan gidan, Faisal yana tsaye ta ƙwan-ƙwasa ƙofa, mai gadin ya tambayi waye? Ta faɗa kamun ya buɗe ta shiga bayan ta ɗagawa ya Faisal hannu, murmushi shi kuma ya sakar mata sai sannan yaja motansa yayi gidansu shi ma. Mai gadin ne ya gaidata da fara'a, dan kowa yasan kirkin jidderh ta kyawun halinta, yana murmushi ya ce, "Uwar masu gida sannu da shigowa." Murmushi jidderh tayi ta ce, "Yauwa baba nagode, sannu da aiki", ta faɗa ta wuce cikin gidan har ranta tana jin daɗin wannan suna, da suke ƙiranta da shi manya da yara, musamman ma'aikatan familyn nasa, jidderh Uwar masu gida. Ƙatoton gida ne wan da faɗan yacce yake ma ɓata baki ne, domin har kaman ya fi gidansu jidderh girma, da sallama ta shiga cikin gidan, bata bi hanyan da zai sada ta da babban palourn ba, ta ɓj hanyan da zai kai ta palourn takwarar tata, ta shiga bakinta ɗauke da sallama. Amsa mata dattijuwar yar aikin da ke jera abinci a dinning tayi, tana sakin fara'a ta ce, "Maraba lale da uwar masu gida." murmushi jidderhnma tayi ta ce, "Barka Baabaa larai." Wucewa tayi ɗakin Hajiya mama direct, ta sameta tana kan sallah, cire hijab ɗin jikinta tayi ta faɗa kan gadon kamn yarinya ƙarama, wayanta ta bude ta shiga ta turawa baby recharge card na 5k, sannan ta tashi ta ɗauro alwala ta mayar da hijabinta ta tada sallah. Baabaa larai ce tayi sallama a ƙofan ɗakin, gyaran murya Hajiya mama tayi alamun tana lazumi, jin haka sai baabaa larai ta juya. Jidderh bayan ta idar da Sallan ta ja carbi, ita ma tayi nata addu'an ta shafa, sannan ta cire hijabin ta ɗaure igiyan gaban riganta ta rufe. Komawa kan gadon tayi ta kwanta, tare da ƙara yin dialing numbern ɗazu, yanzun ma dai kaman ɗazu ne har ƙira uku tayi amma ba a ɗauka ba, ƙaramin tsaki ta ja tare da dialing numbern Safwan, yana shiga aka kashe aka ƙirata. "Wahalalle", haka ta faɗa kamun ta ɗau ƙiran, ba laifi yanzu dai ta sauraresa, sun yi hira amma sama-sama take amsa masa, shi kam Safwan da alama ko a jikinsa. "Babe yaushe za ki barni na zo na ganki? seriously am eager to see you, and ina so na turo magabatana ayi maganan auran mu, i can't wait to see dis beautiful diamond lady a gidana a matsayin halal wife tawa, kullum ki ce ba yanzu ba, dan Allah babe ki yanke rana." Jidderh tana jinsa har ya gama zancensa, ta taɓe baki ta ce, "Allah ya tabbatar da alkairi Safwan." Addu'ar da tayi ba ƙaramin daɗi ya masa ba saboda ƙaunarta da yake yi, wanda hakan ya sanya shi cewa, "Babe guess what!" Cike da zaƙuwa da kuma gajiya da wayan ta ce, "Yes am getting you." "Wayanki ya iso Insha Allahu, zan iya yin komai dan farincikinki, duk lokacin da kika ce a kawo ba ɓata lokaci zai iso gare ki." Taɓe baki jidderh tayi ta ce, "An gode Allah ya ƙara budi." Safwan na murmushi ya ce, "Ameen wife material, mace mai godiya da iya addu'a ai ita ce macen da ko wani namiji ke fatan samu, Allah ya miki albarka." "Ameen, am please Safwan ina jin bacci", faɗin Jidderh da ke jin kaman ta saka kuka. "Okay Babe Allah ya tashe mu lafiya, ki kula mini da kanki sosai kin ji." "Insha Allah." Safwan ya ce, "To Allah ya tashe mu lafiya, ina matuƙar sonki." Kittt! haka Jidderh ta kashe wayanta, tana taɓe baki tana faɗin, "Yen yen yen! ka bi ka dame ni, sai ka ce an ce maka ko ina sonka ne, mutum shegen naci kai ba zaka fahimci ba'a sonka bane, ba abin da ban faɗa ba amma ka maƙale kaman chewing-gum, idan kuka ka ji wani labari nan gaba sai ka ce yaudararka nayi." Hajiya Mama da ta idar da addu'anta ta shafa ne, ta aiko wa jidderh dan-ƙwalo ta ce, "Gidanku cubulle, na faɗa miki ba a yiwa namiji haka amma sam ke bakya ji, wulaƙanta mutum ba abu ne mai kyau ba, tun da kin faɗa masa gaskiya ya ƙi ji, ai sai ki kiyaye kawai ki bisa yanda yake so ku rabu lafiya, maza fa sai a hankali, a wannan zamani ba iya mata ke shige-shige ba, har namiji ya iya bin malamai dan haka ki bi a sannu a rabu lafiya bana son damuwa." Abin da wasu matan ba sa ganewa kenan, maganan wulaƙanta najimi amma sam basa ji, kuma wannan na ɗaya daga cikin abin da ke damun yaranmu mata a yanzu, sai ka ga yarinya ta kwana biyu ba aure, tun tauraronta na haskawa har ya disashe, tabbas an sani komai sai Allah ya nufa ya kuma ƙaddara idan lokacinsa yayi, amma wasu da yawa makamancin iriyar wannan dalili ita ce mastalarsu, mu kiyaye, Allah kuma ya bai wa kowa miji nagari, masu aure Allah ya karo zaman lafiya da haƙuri da juna ya kuma raya zuri'a ya shirya mana su. Turo baki Jidderh tayi ta ce, "To Hajiya na jiiiiiii." *** MASU DARAJA HABIBTIEES NA UWAR BATOORL AKWAI GARAƁASA GUDA, A YANZU KAMUN MU KAMMALA FREE PAGE'S TO KUƊIN LITTAFI DAI #300 NE, IDAN MUN KAMMALA KUWA #500 YAKE INSHA ALLAH. 9161720046 Harira salihu isah Opay & 2220553988 Harira salihu isah Uba Shedar biya ta wannan layi 07015870735. Mutanen Nijar ku ma ku yiwa wannan layi magana dan yin payment naku 07015870735. # Hareeyh # 09161720046 # 07015870735 # 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩 # 𝙇𝙞𝙠𝙚 & # 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚, SHAAMEEKH , B̶̶O̶O̶K1 Officially 𝘽𝙮 Harira Salihu Isah (Uwar batooler) ‫ اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله‬SAW 🖤🤍 GARGAƊI: masu YouTube channels, masu yin Audion littafi, kada wacce ta ɗaura mini littafi ba da yawu na ba, domin muddin na ci karo da haka to ko wacece/ wanene zan ɗau mummunan mataki a kai, hukuma za ta rabani da mutum, A KIYAYE. ̶ ̶F̶r̶e̶e page Billy Ammin Safwan, masoyiya bealkysou Allah Ubangiji ya miki albarka ya nuna mana bikin nan da rai da lafiya, ƙanwar aunty Ummi kiyi yacce kike so da page ɗin nan. PAID #500 Shafi Na Uku. ⭐ Ƙwafa Hajiya Mama tayi ta ce, "Ni ban ma san me ya kawo ki ba takwara, kin zo dare-dare kaman mara gaskiya za ki addabi rayuwan mutane." Jidderh na daga kwance ta ce, "Ni bansan ma me yake kawo ni gidan stohuwar nan ba, bana iya haƙuri sai na zo, idan nazo kuma ki ta mini gori kaman ɗauke mijin zan yi na tafi da shi, laifi nane ma da nake zuwa ma gidanki ai", ta ƙarishe zancen muryanta na rawa, kaman mai shirin kuka dan har idanuwanta yayi ƙwalla. Hajiya Mama haɓa ta kama ganin ikon Allah, ta ce, "Eh samun waje kare da rawa a bakin ramin kura, mai arahan hawaye, yanzu me abin kuka anan? To Allah ya azurtaki da Manzon sauƙi takwara, mutum sai son hawaye da kuka kaman wacce mijinta ya mutu, wai haka za ki dinga yi wa mijin ko nice da kike ganin damana kike min wannan taɓaran? Sai ka ce daman ni na ce ki zo." Tura baki tayi ta ce, "Ni dai Hajiya banaso, zan tashi na koma gidanmu, alhamdulillah muma muna da gida." Hajiya tana ƙoƙarin miƙewa ta ce, "Na kan ga rasulu idan nayi hali na gari, yanzu ke takwara ni kike faɗa wa kuna da gida? To naji daman nasan kuna da shi ai ba a daji kuke kwana ba, amma a haka kika zo mini gida dan ki takura wa mijina, to kin zo kenan ba in da za ki koma, ke da barin gidan nan ai kuma ba yau ba, abin da ya sanya ki zuwa dare-dare, shi zai zaunar da ke ki kwana dole, dan ƙafan gwoggonki Fatu." Jidderh tura baki ta kuma yi, kaman mai shirin yin kuka ta ce, "Nidai ba ruwan gwoggona." Murmushi Hajiya Mama tayi ta ce, "To naji masu gwaggo, mu da bamu da su a raye Allah bamu haƙuri, kuma na kowa ma zai tafi indai mutuwar yanzu ne, taso muje mu ci tuwo dan nasan daman kwaɗayi ya kawo ki gidana." Jidderh ƴar dariya tayi jin wai kwaɗayi ne ya kawo ta, miƙewa tayi daga kwancen da take tana faɗin, "Eh koma menene dai na zo ne dan na ci tuwo da sakwarata." "Sai dai sakwara kam, ni rabani da halinki, bansan abin da ya kai Sama'ila saka miki sunana ba, dan ni ba haka halina yake ba", Hajiya Mama ta faɗa tana ƙoƙarin ficewa a ɗakin. Jidderh sauƙowa tayi ta naɗe wa Hajiya Mama sallaya da hijabinta, sannan ta ɗauki wayanta ta bi bayanta a niste, suka fice a ɗakin, palour suka nufa dai-dai Baba Alhaji na shigowa shi da wani matashin saurayi. Stohon da suke cewa Baba Alhaji murmushi ya saki ganin jidderh, ya ce, "Ah! Amaryata ce da daren nan." Jidderh na murmusawa ta ce, "Nice dai angona mai ran ƙarfe, ka ƙi zuwa hatta ɗaukan amaryan shiyasa na taho abina da naga dare tayi." Baba Alhaji ya ce, "To Masha Allah! Amaryata ta kyauta, Allah ya miki albarka." Amsawa da "Ameen", jidderh tayi, sannan ta ce, "Yaya Sabeer an wuni lafiya?" Matashi mai suna ya Sabeer murmushi yayi ya ce, "Lafiya alhamdulillah stohuwa amaryan stoho." Jidderh kallon Hajiya Mama tayi, tare da turo baki ta ce, "Allah kuwa sakwara ki ce musu su daina ce mini stohuwa, ƴar gangariyan budurwa da ni haka kawai a rage mini farashi." Hajiya Mama haɗe fiska tayi tare da kallon Ya Sabeer ta ce, "A daina faɗa wa takwarata stohuwa, ita ba stohuwa ba kuna ganin yarinya ƴar jinjira da ita, kuna stofar da ita." Ya Sabeer dariya yayi tare da riƙe bakinsa, da kunnensa alaman yaji ya daina, ita kuma jidderh murmushi tayi ta ce, "Yauwa Hajiya Mama ta." Baba Alhaji ne ya ce, "To azo aci tuwo kubar shirmen nan, dan Hauwa'u rigimanta ya mata yawa." Duk akan centre carpet suka zauna, Jidderh ce tayi serving nasu, ta saka wa baba alhaji tuwon biski da miyar zogale da ya ji kifi kasancewan yana da ciwon sugar, Hajiya Mama kuma ta saka mata tuwon shinkafa da miyar zogale da kifin ita ma, ta saka wa Ya Sabeer tuwon shinkafa da miyar kuɓewan da yaji man shanu ga namomi, sannan ta saka wa kanta tuwon doya(sakwara) da miyar egusi shi ma ya ji bushashshen nama. Abincin suke ci wajan shiru ba ka jin ƙaran komai, sai na taunan abincin nasu, jidderh bata wani ci sosai ba ta cire hanunta, ɗiban ruwan zafi tayi ta haɗa black tea ta sha, gefe ta matsa tana duba wayanta hankali kwance ciki ya ɗauka. Hajiya Mama kallon jidderh tayi tare da girgiza kai, ta ce, "Ke dai takwara Allah ya yaye miki rashin cin abincin nan, watarana har gwanda mai sunan Alhaji da ke kam." Murmushi kawai jidderh tayi ba ta ce komai ba. Ya Sabeer ya ce, "Ai Hajiya Mama dai-dai kenan, kin ga an haɗa su perfect match, amma dai nikam ina namiji ban ci ba wa zai ci? Ni fa na nemo abincin, ai gwanda ace mace bata ci sosai akan a ce namiji ne baya ci sosai, don ita mace hakan ma ado ne gare ta." "Kubar damar mini amarya da surutu, tun da ta ƙoshi to a ƙyale ta", faɗin baba alhaji. Jidderh murmushi tayi tare da cewa, "Yauwa mijin ka gama ci kai ma sai muyi fira", ta faɗa tana komawa kan kujera ta zauna. Alhaji baba ne ya mayar da dubansa kan Ya Sabeer ya ce, "Nikam yaushe ƙanwarka za ta dawo ne? Ko ita ma ta fara ɗaukan huɗuban wancan mara jin maganan ne eyye?" Ya Sabeer ya ce, "Baba Alhaji wannan yarinya kam me mutum ma zai ce ne, su Mom sun jima da sakalta ta, kawai ka ƙira Dad ka tambayesa, dan nikam ban san ko tana hanya ko bata hanya ba, ba ma magana take mini ba tana jin yanzu ta girma ta fistare." Ƙwafa Hajiya Mama tayi kawai, amma ba ta ce komai ba, shi ma baba Alhaji bai kuma cewa komai ba, har suka kammala cin abincin, baba larai ta zo ta gyara wajan tass. Alhaji baba sai da ya gyara zamansa har da kishingiɗa, sannan ya ce, "Amaryata ɗauko mini ƴar salulata (waya) a ɗaki, ki zo ki mini ƙira dan naga iyayennaku sai an saɓa musu za su yi abin da ya kamata, su kuma kula da tarbiyyanku, idan ba ma lalacewan zamani ba duk cikin yaran nan akwai mai yara irin yacce na haife su ne, ni ban kasa tarbiyyansu su kusan goma sha ba, amma ni za su wasta mini kasa a ido su kasa yi wa jikokina tarbiya, daga mai uku sai mai huɗu, ba mai yaran da suka wuce biyar, sun ɗau rayuwan yahudawa sun ɗaura wa kan su, basu san yahudawan la'ana ce ke bin su ba, da akwai wan da ya kai yahudu auran mata da yawa da haihuwa ne, addu'an Annabi ne ya sa yanzu suke zama da mata ɗaya kuma yara biyu mace da namiji, ai Annabi Dawuda yahudu ne kuma matansa sun kai ɗari, Annabi sulaiman ma yahudu ne matansa sun bai wa ɗari baya, yanzu Allah ya rahamce mu muke auren mata har huɗu sannan mu hayayyafa, yacce Annabi SAW zai yi alfahari da mu ranan ƙiyama, kuma sai ga shi mun ɗauko al'adan yahudu mun iza a kawunanmu, to zan kuwa saɓawa iyayenku." Jidderh tashuwa tayi ta tafi ɗauko wayan da sauri, dan kowa yasan Baba Alhaji bai da mastala amma idan aka taɓo sa, ransa ya ɓaci to fa jam'i yake haɗawa, stoho mai ran ƙarfe. Ya Sabeer ma tuni ya miƙe ya musu sallama, yayi gaba abinsa kamun Baba Alhaji ya haɗa da shi, a basa kasonsa, gidansu ya wuce a ƙafa kasancewan gidansu yafi kusa da na su Baba Alhaji. Jidderh ta ɗauko waya tana ƙoƙarin zama, sai ƙira ya shigo wayanta ita ɗin ma. ⭐ Baby ce zaune a dinning area ita da Ummiy suna cin tuwo, kuma tuwon da Ummiy ta fi so, tuwon shinkafa da miyar kuka da man shanu. Da Ummiy ta gaji da surutun baby, sai ta ƙwalawa Talatu mai aiki ƙira, zuwa tayi cikin ladabi ta ɗan durƙusa ta ce, "Hajiya gani nan." Ummiy na murmushi ta ce, "Yauwa Talatu yarinyar nan ta dameni, tun ɗazu yarinya taƙi barina na ci tuwo, cikin kwanciyan hankali sai fitinata take, wai sam ita ce tayi miyan ba ke ba, dan taji na ce yayi daɗi, gaskiya ne ita tayi ko kuwa fitinane irin na baby?" Talatu murmusawa tayi ta ce, "Hajiya ai wallahi dai ita ce tayi, dan taƙi ƙyaleni na saka ko hannu na taya ta, ita tayi har da tuwon ma." Ummiy na washe baki cikin jin daɗi ta ce, "Inyee ki ce mini babyn Ummiy ta girma saura aure, amma wannan iya girkin dai kyawunsa na aurar da ita a ƙauye, dan ta wuce auren birni da wannan girkin." Talatu dariya ta fara yi, da yake daman sun saba raha da Ummiy, ba ruwan Ummiy da kana mata aiki ko wani abu, bata wulaƙanta ɗan Adam sam-sam, wasa da raha duk idan ta kama tana yi da masu aikinta, kuma ita ɗin ce ta ce su dinga shiga kitchen da baby dan ta koya aiki, tun da ita asibiti na cinye mata lokaci, kuma kada ta ɗau alhaƙin yarinya irin tarbiyan yaran masu kuɗi a yau, yarinya ta girma ta kai aure amma ba abin da ta iya, komai sai mai aiki ta mata, idan tayi aure to ita kawai kwanciya da miji ta sani, masu kuɗi ku gyara tarbiyan yaranku saboda halin rayuwa shawara ce. Talatu tana dariya ta ce, "Haba dai Hajiya wannan ai matar drivern jirgi ce, ba in da aure ba ya kai mutum, amma Insha Allah ko a ƙauye Saudiyya ba za ta zauna ba." Baby murmushi tayi ta ce, "Yauwa aunty Talatu na, faɗa wa Ummiy ko a Makka ne to a babban birnin zan zauna in Allah ya yarda, shiyasa nake yin ki auntyna." Ummiy ta buɗe baki za ta yi magana sai wayan baby ya fara ihun neman agaji, Ummiy da yake wayan na kusa da ita, ɗauka tayi ta miƙawa baby tana faɗin, "Duba mana ko ƙiran kuɗaɗe ne za su shigo Mu fara shiri, amaryan ɗan ƙauye." Baby amsan wayan tayi tana tura baki wai bata so, ganin saƙo ne ba ƙira ba buɗewa tayi, ai ba shiri ta waro ido akan wayan tana gani da kyau, ai miƙewa tayi ta ɗan yi tsalle har da juyi tana faɗin, "Wayyo Allah na! Ina son ki yaya jidderh, Allah ya bar mini ke, Allah ya mallaka miki Yaya ke kaɗai ba kishiya, Ummiy ga shi ki gani yaya jidderh ta saka mini card." Karɓan wayan Ummiy tayi ta duba, ganin yawan katin sai ta murmusa ta ce, "Allah ya mata albarka ya ƙara buɗi, Allah bata miji nagari", ta faɗs tare da miƙa wa baby wayanta. Baby ya amsa wayan tana cewa, "Ai Insha Allah Yaya ne mijin, shi ne nagari kuma na alkairi, kai idan yaya ya kuskura zai yi wa yaya jidderh kishiya ko yaudara, to ni kaɗai na ishe sa tuwo da miya dan ba zan bari ba ma hakan ta faru." Ummiy haɗe fiska tayi ta ce, "Sannu addarsa, Allah zan saɓa miki akan manyancenki baby, shi shameekh ɗin sa'anki ne, to ki yarda ya ji abin da kike cewa, addu'an alkairi kawai shi za ki yi ba surutu ba, kuma maza ki ƙirata yanzu ki gode mata, bana son surutunkin nan mara kai." Cunna baki baby tayi wai dan Ummiy ta mata faɗa, Ummiy kuwa ko kallonta ma bata yi ba ta ci-gaba da abin da take yi, sai da Talatu ta bai wa Ummiy haƙuri Allah ya huci zuciyanta, sannan ta bar dinning ɗin, baby kuma layin yaya jidderh ta laluɓo tayi dialing kaman yan da Ummiy ta faɗa. ⭐ Wani haɗaɗɗen club ne a ƙasar Dubai, club ɗin da sai wane da wane ke zuwa, don classic club ne, Shameekh ne zaune a wani table da wani matashin saurayi wan da za su yi sa'an juna a shekaru, matashin kyakkyawa ne Masha Allah, amma fa bai kama ƙafan Shameekh ba, duba da yacce suka mai da hankalinsu akan juna, to kasan tabbas abu mai muhimmanci suke tattaunawa a kai, wannan matashin ne ya ce, "Man yanzu to ya za'a ɓullowa abun?" Shameekh ya buɗe baki zai yi magana sai haɗaɗɗiyan stadaddiyar wayansa, tayi flash ta kawo haske da vibrating alaman ƙira ne ya shigo, fasa maganan yayi tare da saka wayan a silent, yana gani har ƙiran ya kaste. Wannan matashin ƙwafa yayi ya ce, "Gaskiya idan aka ce maka kana kyautawa to ƙarya aka maka Man, kai fa ka laƙantu da wulaƙanci da iyayi kaman wani Garage gare ka ba dick ba, haba mata masu Garage su ya kamata su yi wannan iyayin, ba gardi irinka mai Banana ba, tun ɗazu wannan baiwar Allah sai ƙiranka take yi, amma ka ƙi ɗauka, wai meyasa ne kake mata haka?" Shameekh haɗe fiska yayi tare da aikawa matashin da wani kallo ya ce, "Manseer please let's talk about what brought us here, kabar maganan wani dick wani Garage ne ko me, kasan ba son maganan banza nake ba, dan ba shi bane a gabana." Manseer dariya yayi ya ce, "A faɗawa kaji da agwagi mu zabbi firewa muke yi, magana kake nema wai an ce da gauro ya iyali, kai ɗin ne baka son maganan banza? Hhhhh ko da yake daman ai nasan ba shi ne a gabanka ba cucumbern jidderh ne a gabanka, so please idan za ka bar wulaƙanta ƴar mutane ka bari idan ba haka ba za ka sha mamaki." Wani kallo Shameekh ya yiwa Manseer tare da haɗe fiska ya ce, "Yanzu idan da yara a nan ba sai ka ja su renamu ba, ni na faɗa maka ina da issue da mace balle wani ka ɗosana mini wani shirme." Murmushi Manseer yayi ya ce, "Eh lallai a yanzu kam ba ka issue da mace, amma ka guji haɗuwanka da ita, Allah ya sa ta dinga ƙarar maka da ruwan jiki za ka dawo hanya." "Abar wannan magana", faɗin Shameekh rai a haɗe. Manseer ya ce, "Ai dole ka ce abar maganan tun da kasan kwanan zancen, Man nifa idan ba ka yi ka bani waje, ka masta na shige layin masu nema ayi da ni, wannan haɗaɗɗiyar wa zai so ta wuce sa, irin su idan ka ajiye su a gida ko ba komai ka dinga farinciki idan ka kallesu, mace har mace ga....", wani irin kallon da Shameekh ya yiwa Manseer, shi ya sanya shi haɗiye sauran maganan da zai yi yana dariya, dan Shameekh ɗin ya san dole maganan banza zai faɗa. Tsaki Shameekh ya ja rai a ɓace ya miƙe ya kama hanyan ficewa a club ɗin, dan daman a takure yake da kallon da ƴammatan club ɗin ke masa. Yana ficewa waje yayi wajan motansa, fiskan nan a haɗe rai a ɓace ya buɗe motan ya shiga, yana ƙoƙarin tayar da motan sai Manseer ya fito daga club ɗin shi ma dan dama bayansa ya biyo tun fitowansu, kallonsa ya sashi saurin tayar da motan yayi gaba, yana driving ya ja wayansa ya duba lokaci, ganin mid-night ne yanzu a wajensu suna fin agogon Nigeria da 4 to 6 hours, wanda hakan ke nufin yanzu bai wuce 9 zuwa 10 na dare ba. Yana isowa gidan nasa yayi horn, mai gadi ne ya taso ya leƙa duk da dare ne amma ya gane mai gidannasa ne, tun da daman ya sani yana iya kai ire-iren wannan lokacin a waje, buɗe masa gate yayi ya shigo da motan, parking yayi ya fito mai gadi ya masa sannu da dawowa, hannu kawai Shameekh ya ɗaga masa alaman ya amsa, ya shige cikin gidansa. Bai staya yin komai ba a palourn ya wuce ɗakinsa, yana shiga ya cire kayan jikinsa ya rage daga shi sai white short nasa, sanin idan ya shiga toilet ɗin zai iya jimawa, shiyasa ya fasa shigan ya koma ya zauna a kujeran da ke cikin ɗakin nasa, wayansa ya ɗauka ya kalli misscall's da aka masa, scrolling na number's ɗin yayi, da ya zo dai-dai layinta sai ya tsaya kaman ya ƙira kaman kar ya ƙira, sai ga wani ƙiran ya shigo wayansa kuma new number ba suna, kasancewan ya gane numbern sai ya ɗauka dan misscall na numbern da yawa, yana ɗauka yayi shiru bai ce komai ba, a ɗaya ɓangaren kuma cewa aka yi, "Hello! Ya Shameekh ya kake?" A taƙaice ya ce, "Lafiya, ƙira da daren nan lafiya? Wacece?" Wani numfashi aka sauƙe a ɗayan bangaren wan da zai tabbatar maka da na haushi ne, amma ba'a ce komai ba. Shameekh kuwa jin shiru ba a ce masa komai ba, sai kawai ya kashe wayansa yana taɓe baki, amma fa ya gane wacce ta ƙira ɗin dan true caller ya nuna sunanta ɓaro-ɓaro, kuma daman ya gane layin da take addabansa da shi, damuwane baya so shiyasa yayi hakan kawai, guntun staki ya ja a fili ya ce, "Ke kika sani." Shameekh bai gama rufe baki ba wani ƙiran ya kuma shigowa, kuma da wannan numbern ne na ɗazu, yanzu kam ransa a ɓace yayi picking, dan ba abin da Shameekh ya stana kaman yawan ƙira kuma da number mara suna ko ɓoyayyen layi, a harzuƙe ya kara wayan a kunnensa tare da cewa.. ⭐ Jidderh ganin ƙira ya shigo wayanta fasa miƙawa Baba Alhaji wayansa tayi, cikin zaƙuwa ta duba dan duk a tunaninta shi ne ya ƙirata, amma sai ganin layin baby tayi wan da tayi saving da "Lil Sis", ɗauka tayi tana murmushi ta ce, "Assalamu alaikum babyn aunty jidderh ya aka yi?" Baby a ɗaya ɓangaren cewa tayi, "Na'am yaya jidderhta, lafiya lau naga kati nagode sosai, Allah ya ƙara buɗi, Allah ya bar mana ke yayarmu." San-sanyar murmushi jidderh tayi ta ce, "Ameen ya Rabbi babynmu, ki gaishe da Ummiy ko sai da safe." "To Yaya jidderh Insha Allah Ummiy ta ji gaisuwa", baby ta faɗa suka yi sallama sannan jidderh ta kashe wayanta. Jidderh ta ce, "Mijin ga wayan naka wa za'a ƙira maka?" "Yauwa Hauwa'u dubo mini layin babanku Sulaiman." Jidderh amsawa tayi tare da shiga numbonin wayan, ta laluɓo layin big Dad ta aika da ƙira, yana shiga ringing ɗaya yayi aka ɗauka, ana ɗaukan ƙiran ta miƙa wa baba alhaji wayan ta ce, "Ga shi nan an ɗauka stoho." Amsan wayan yayi tare da karawa a kunnensa, ya amsa sallaman da big Dad ke masa a ɗaya ɓangaren, gaisawa suka yi big Dad ya ce, "Baba ya jiki ya kuma su hajiya?" "Duk muna lafiya sulaimanu, na ce yaushe Safiya za ta dawo?" Faɗin Baba Alhaji fiska a haɗe. Big Dad a ɓangarensa sai da ya ƙai-ƙaya kan sa sannan ya ce, "Ammmm baba tana dawowa Insha Allahu." Alhaji da faɗa ya ce, "Kai Sulaimanu ungo naka, na ce ungo naka ɗan ƙaniya, daman na ce maka ba ta dawowa ne? Ka fa shiga hankalinka Sulaimanu, ita Safiya fa yarinya macece kar ka ɗaure mata baya ka lalata mini jika, dan bazan yafe maka ba muddin tarbiyan jikata ya lalace, maza-maza indai na isa da kai ka ce ta dawo goben nan, ba zai yiwu ƴa mace da ita ta zauna a ƙasar marassa ishashshen tarbiya ba, tun da rai na ba za ku ƙonani ba, yarana basu yi wannan abun ba to jikoki na baku isa ku ce za ku sanya su a wata bidi'ar rayuwan ba." Hajiya Mama rai a ɓace ta ce, "Alhaji ka bani wayan." Baba Alhaji miƙa mata wayan yayi, big Dad na ƙoƙarin gaisheta ta ce, "Sulaimanu ka riƙe gaisuwanka, ina fatan ka ji abin da babanku ya ce ko? To sayfiya ta dawo goben nan kuma duka zan haɗu da ku ne mutanen banza mutanen wofi kawai." Haƙuri big Dad yake bayarwa amma ba wan da ya saurare sa, dan baba alhaji ma karɓan wayansa yayi ya kashe. Jidderh cikin girmamawa ta ce, "Ayi haƙuri mijin, a dinga mana addu'a Allah ya shiryamu, ke ma kinji Hajiya sakwaralle ta, Insha Allah ba abin da zai samu tarbiyanmu duka." Baba Alhaji murmushi yayi ya ce, "Allah ya sa, Allah kuma ya kare ku a duk in da kuke, Allah ya muki albarka Hauwa'u." Jidderh ta ce, "Ameen mijin, saura ke ma sakwaralle ki saka mana albarka indai ba kishi kike ba", ta faɗa tana yiwa Hajiya Mama dariya. Dan-ƙwalo Hajiya Mama ta yi wa jidderh ta ce, "Ungo naki ke da ƴan uwan naki, Allah ya shiryaku." Jidderh na dariya ta amsa da Ameen, ta miƙe ta nufi ɗakin Hajiya Mama tana faɗin, "To abar mini kallon kishi sakwaralle dan yau da ni ke da miji", ta faɗa dai-dai tana shigewa ɗakin. Hajiya Mama girgiza kai kawai tayi ta ce, "Wannan takwara tawa sai addu'an shiriya." Baba Alhaji murmushi yayi ya ce, "Allah ya shirya mana su duka, amma da ace duka yaran nan irin halin Hauwa'u gare su, ai da hankalin kowa a kwance, wannan yarinya dai Allah ya mata albarka, Allah ya nuna mana ƙarshen watan nan lafiya, kowa ya halarta nasan hukuncin da zan zantar, dan dole na yiwa abin tufkar hanci." Hajiya Mama ta ce, "Ameen, Allah ya kai mu da rai da lafiya ya kuma tabbatar da alkairi." *** MASU DARAJA HABIBTIEES KADA KU MANTA DAI WANNAN TAFIYA TA DABAN CE, MASU SHARHI KUNA GIGITANI ALLAH BAR ƘAMNA🤝💜, ANA FARA PAID PAGE'S INSHA ALLAH ZAN ƘARA YAWAN PAGE KU DAI A CI-GABA DA SHARHI. # Hareeyh # 09161720046 # 07015870735 # 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩 # 𝙇𝙞𝙠𝙚 & # 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚, SHAAMEEKH , B̶̶O̶O̶K1 Officially 𝘽𝙮 Harira Salihu Isah (Uwar batooler) ‫ اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله‬SAW 🖤🤍 GARGAƊI: masu YouTube channels, masu yin Audion littafi, kada wacce ta ɗaura mini littafi ba da yawu na ba, domin muddin na ci karo da haka to ko wacece/ wanene zan ɗau mummunan mataki a kai, hukuma za ta rabani da mutum, A KIYAYE. PAID #500 Shafi Na Huɗu. ⭐ Shaameekh a harzuƙe ya ɗau ƙiran, wanda da alama har yanzu ɓacin ran maganan da Manseer ya masa bai wartsake ba, "Wai ke kam wace kalan mayya ce? Sau nawa ina gargaɗanki da ƙira na, na hana ki ƙira na amma sam bakya ji, sannan kina ƙira na da wani number daban, wai ke baki da aji ne? Ko baki iya kama mutuncinki irin na ƴa mace bane?", ya ƙarishe faɗa yana mai jin, kaman ya shaƙeta ya huta. A ɗaya ɓangaren kuwa mai ƙiran nasa fashewa tayi da kuka, cikin kuka ta tausasa muryanta ta ce, " Haba Ya Shaameekh dan kawai ina sonka, ai kai ma kasan ba laifina bane, dan ba nice na ɗaurawa kai na ba, kuma mai son ka ai yafi mai ƙin ka, idan kana wulaƙanta ni kuma kai ma kada ka manta za ka haifa, idan aka yiwa taka ƴar ai ba daɗi za ka ji ba." A hasale Shaameekh ya ce, "Nace miki bana son ki, ki riƙe kan ki kada ki bari na ɗau mataki a kan ki, ni ba sa'anki bane da za ki dinga faɗa mini ko wani maganan da ya fito a bakinki." "Wallahi kana so na Ya Shaameekh, kuma sai ka aureni, wannan karon zan koma gida, kuma za a yi duk abinda za a yi, wallahi ina a shirye tsaf a kan ka ba wan da ba zan iya ja da shi ba, har Mom and Dad, kuma idan ma akan wancan figaggiyar kake mini wulaƙanci, to za ka sa na kasheta ne a banza, idan ya so daga baya nima a kashe ni kowa ma ya rasa, dan a kanka ba wan da ba zan iya yiwa illa ba, ko waye kaji na faɗa", ta faɗa a ɗaya ɓangaren a yanayin kaman wacce ke cacar baki da abokiyar faɗanta. Wani killer smile Shaameekh yayi, domin shi baya son hayaniya, amma duk yacce ya kai da rashin son magana, wannan yarinyar sai ta ingiza sa yayi, ga shi ko yana faɗan ma ba za ka ce faɗa bane, kawai dai maganan nasa na zaratan maza ne amma a niste yake yi, cewa yayi, "Idan kika gwada aikata wannan kuskuren to lallai za ki yi danasani a rayuwanki na da baki zo duniyar ba ma, nothing concern me with our blood relationship, dan zan ɗau mummunan mataki a kan ki ne ko da kuwa zai raba kan family ne i don't care, duk randa tayi ko da ciwon kai ne, kuma ke kika zama sanadi to za ki sha mamaki, stupid girl marar aji kawai, ba ta in da za ki haɗa kan ki da precious diamond mace mai aji da sanin ya kamata, kina ballagaza wawiya", yana gama faɗa ya kashe wayansa yana huci, ga ɓacin ran Manseer ga wan da ta ƙara masa, a ce ayi mace a duniya bata san inda ke mata ciwo ba, dole ne sai ka so wanda baya son ka. Tsaki ya kuma ja ya ce, "Mutane sai ka ce dabbobi mai zan yi da ke? useless girl kina zaune cikin ƴan iska kina abin da ranki yake so, bazan auri sauran wasu ba no matter how." Sai da ya ɗan saita zuciyarsa da yake ji a ɓace, sannan yayi dialing layinta, ringing ɗaya yana shiga ta ɗauka kaman wacce ke jira daman, cikin zazzaƙar sassanyar muryanta mai daɗin sauroro ga sanyi ta ce, "Assalamu'alaikum wa rahmatullahi wa barkatuhu abun ƙaunan Jidderh." Jin muryanta kaɗai ya saka shi samun wani ni'imtaccen nistuwa, idan ana neman mace tagari jin daɗin duniya to jidderh ta wuce in da ake nema ma, shiyasa maganan Manseer yayi mugun ɓata masa rai, dan nunawa yake kaman bai wani damu ba, amma a can ƙasan zuciyarsa yan da yake jin ta daban ne, duk cikin ƙannensa babu ya ita, dan ita ɗin kyauta ce daga Allah, ga duk wan da ke tare da ita. Lumshe ido yayi yana busar da iska mai zafi a bakin sa, amma bai ce mata komai ba, sallaman ma a zuciya ya amsa, ita ma jidderh a nata ɓangaren lumshe idon tayi, tana jin ta cikin wani irin yanayi, Allah ne kaɗai yasan irin ƙaunar da take wa wannan bawan nasa, ji take rashinsa zai iya kawo ƙarshen rayuwanta, tana masa son da bata yi wa kanta ko kwatansa, juyi tayi tare da ƙanƙame pillow a jikinta tana jin fitar ko wani sauti na numfashinsa a cikin wayan, kaman a fiskanta yake sauƙe numfashin, wani irin yanayin ƙaunarsa take ƙara stunduma, kuma shirunsa daɗi ya mata bai dameta ba, dan tasan daman ba lallai ya amsa mata ba muddin ta faɗi hakan. A hankali ta raba laɓɓanta da junansu ta fitar da sautin, "Yayana abun ƙaunata fatan ka wuni lafiya cikin aminci? Ya gida? ya aiki?" "Alhamdulillahi", haka kawai Shaameekh ya faɗa a taƙaice. "Masha Allah! Yayana abun ƙaunata ina matuƙar kewanka", faɗin jidderh cikin shagwaɓa kaman ƴar jinjiran kule. Shaameekh da shi kaɗai yasan abin da yake ji, da kuma yanayin da yake shiga musamman idan tayi wannan shagwaɓan nata, ajiyan zuciya kawai ya sauƙe yayi shiru bai ce komai ba, amma dai yasan yanayinsa a yanzu ya koma dai-dai, ya ma mance da ɓacin ran da yake ciki. "Yayana yaushe za ka dawo? ka ga su Hajiya Mama sun fara surutu." "Soon Insha Allah", yanzun ma a taƙaice ya faɗa hakan. "To Allah ya sa, Allah ya dawo mini da kai lafiya, ya tsare mini kai, Allah ya hana ko wacce mace kallonka." "Ameen nagode da addu'a", ya faɗa yana mai shafa sajensa. "Bakomai Mijin Jidderh in Allah ya yarda." "Ki kwanta dare nayi, ki gaishe da kowa da kowa, gudnyt." Jidderh a ɓangarenta shagwaɓe fiska tayi kaman tana gabansa, amma ba yacce ta iya dole ta ce, "Allah ya tashe mu lafiya." "Ameen take care byee." "Byeee Yayana kuma mijin jidderh", ta faɗa tana sakin murmushi. Shaameekh ma murmushin gefen baki yayi wan da ya matuƙar fito da kyawunsa, sannan ya kashe wayan, ba ɓata lokaci kuma ya miƙe ya shige toilet, sai da ya staya ya wanke toilet nasa tsaff da shi kaman ka zuba abinci ka ci a ciki, sannan ya fara wankansa. Jidderh kuwa bayan ya kashe wayansa, rungume wayan tayi a ƙirjinta stam (kaman Shaameekh ɗin ta samu), tana sakin murmushi mai sanyaya zuciya, duk da ba hakan ta so ba ƙanin miji ya fi mijin kyau, bata so ya kashe yanzu ba dan jin muryansa bai ishe ta ba, a hankali ta ce, "Yayana ina ƙaunarka, Allah barmun kai, Allah ya kulamun da kai a ko ina kake, Allah ɗaura ka a kan maƙiyanka." Tashuwa jidderh tayi ta kashe wutan ɗakin, sannan ta koma ta kwanta da niyan bacci, sai dai dirin neman agaji wayanta ya shigo wayanta, tura baki tayi kaman mai ƙiran na kallonta, dan tasan babu mai ƙiranta yanzu idan ba maye Safwan uban ƴan naci ba, har kaman ba za ta ɗauka ba, sai ta fasa ta ɗauka tare da yin sallama, shi kuma ya amsa a nasa ɓangaren, tare da cewa, "Babe ya kike ya daren?" "Alhamdulillahi!" Ta faɗa a taƙaice. "Gud haka nake so, babe nasan yacce naji muryan kinnan bacci kike ji so, nima daman muryanki kawai nake buƙatan ji dan na samu yin bacci, so take care ko." "Nagode Allah ya tashe mu lafiya", jidderh ta faɗa bakin nan a ture. "U are welcome babe I love you soo much byee", yana faɗa ya kashe wayansa. Jidderh harara ta bankawa wayan sannan ta ce, "Ka taimaki kan ka da ka kashe", tana faɗa ta ja blanket ta rufu sai bacci kuma, safiyar alkhairy jidderh. A gidan big Dad kuwa, Hajiya Kubra matar big Dad wacce suke ƙira da Mom, zaune take a gefen Alhaji Sulaiman(Big Dad), da ke waya da su baba alhaji ta haɗa rai, duk abinda suke cewa tana ji, bayan Alhaji ya gama wayanne ya juyo tare da kallonta ya ce, "Hajiya ya aka yi?" "Hmmn! wani irin yaya aka yi kake tambaya na, wai nikam du-du-du yarinyar nan a nawa take? kuma fa nasan tana dawowa ita ma soon." Big Dad murmushi yayi ya ce, "Kar ki damu kan ki da maganan su baba alhaji, soyayyan da yake yiwa jikokin nasa ne ya ja haka, kar ya dame ki dan Baba na son jikokinsa fiye da tunani, mu dai mu mata addu'an Allah ya dawo da ita lafiya shi ne kawai, duk wannan ba wani abun dogon magana bane." "Uhmn! Ameen to Daddyn Soffy." Shikkenan big Dad da Mom suka ci-gaba da hiransu kaman ba komai. ⭐ Shameekh bayan ya gama wankan ne ya fito ɗaure da farin towel nasa, ɗaure a ƙugunsa jikinsa duk ruwa, wannan lema-leman ruwan sai ya tafi da gashin jikinsa hakan ya ƙara masa kyau. Ba tare da ya kunce towel ɗin ba balle saka kayan bacci, haka ya wuce direct kan gado ya faɗa ya kwanta haka, yayi addu'a ba jimawa bacci yayi gaba da shi mai daɗin gaske. Ƙarfe huɗu 4am na dare na bugawa Shaameekh ya tashi, sai lokacin ya cire towel ɗin, ya sanya armless da 3quater ya saka duka baƙaƙe, ficewa yayi a ɗakin da tafiyansa ta burgewa, wani hanya ya ɗauka daga palourn wan da ya sada shi da, haɗaɗɗen wajan mosta jikinsa. Tun ƙarfe huɗu yana abu guda sai zufa yake haɗawa, kaman wan da ya yiwa sarki ƙarya, shi ne bai sarara ba sai da lokacin sallah yayi. Yana fitowa a wajan ya ɗau goran ruwa a fridge ya kwankwaɗa tass, sannan ya wuce haɗaɗɗen ɗakinsa ya watsa ruwa sama sama bai staya ɓata lokaci ba, yayi alwala ya fito, jallabiyansa ya saka fari mai kyau ya ɗau keyn motansa ya fice a gidan. Masallaci ya je yayi sallah, ko da aka idar bai baro masallacin da wuri ba, dan sai da yayi lazuminsa da azkar nasa, sannan ya juyo gida, nan ma bai yi komai ba ya zauna karatun Alqur'ani, shi ne bai rufe Qur'anin ba sai da ƙarfe bakwai tayi, yana rufewa ya jero addu'oensa ya shafa, sannan ya cire jallabiyan ya bi lafiyan gadonsa ya kwanta. Ɓangaren jidderh ma da asussuba ta farka wajan ƙarfe biyar, da addu'an bacci da kuma salati ta fara buɗe bakinta, sannan ta miƙe ta wara idanuwanta a hankali, miƙa tayi ta sauƙo daga makwancin nata, ta wuce banɗaki, sai da ta wasta ruwa sannan tayi alwala ta fito, raka'atainil fijir tayi ta zauna yin istigfari har sai da aka shiga salla, sannan ta miƙe ta bi masallaci, ana idarwa ta taɓa karatun Alkur'ani, sannan ta miƙe ta mayar da komai mazauninsa, a cikin kayakinta da ke ɗakin Hajiya Mama ta sanya riga da wando ta yadi mara nauyi, sannan ta fice a ɗakin ta nufi kitchen, dan taya su baabaa Larai aiki, kasancewan ita ba mai son jiki bane, sannan tana son ta iya ko wanne irin girki ko dan ta burge masoyinta. INDIA Misalin ƙarfe shida na safe a agogon ƙasar India, yanayin garin yayi kyau da daɗi kaman hadari-hadari, wata rantsaststiyar haɗaɗɗiyar mota ce tayi parking, a harabar wani arnen hotel da ke babban birnin Delhi. Wata matashiyar budurwa ce ta buɗe ƙofan motan ta sauƙo, fiska ba yabo ba fallasa tana tauna chewing-gum, sanye take da dogon wando wan da ya kama jikinta sosai, ya ɗameta har kana hango shatin inners nata, dan dai kawai ba mai jiki sosai ba ce, da sam-sam ba za ta ganu ba, sai dai dogo ne har ƙasa da rigansa, wan da bai gama rufe ko cibiyanta ba, ga ƴar ficilan jakanta fashion na ratayawa, kan ta cike da attach (wig), tana taunan chewing-gum nata ta ce, "Guy's see you letter", ta ƙarisa faɗa tana ɗaga musu hannu har suka ja motansu suka yi gaba. Sannu a hankali take taku irin na cikakkun wayayyun matasan ƴan duniya, a haka ta yi cikin hotel ɗin, lifter ta shiga ya kai ta har floor da ɗakin da ta kama yake, tana shiga ta fara cire gashin dokin da ke kan ta(wig) (Ranƙwal kenan fan's, an ce da wata wai acici ƙwalloji, kan ta ba gashi kaman an ci giginya da wuƙa🫣). tana cire wig ɗin ta koma kan kayan jikinta, sai da ta kwaɓe kayanta tass tayi stirara haihuwan uwarta, sannan ta nufi toilet a haka, ta shige ba addu'a balle salati, bata wani jima a toilet ɗin ba bayan mintuna ta fito ɗaure da guntun towel, ba sallah bare salati ta baje a kan gadonta sai bacci. Wannan matashiya kwance take tana sharar baccinta hankali kwance, ba batun tashuwa tayi sallah ko wani abu sai gwarti take yi, kukan neman agaji da wayanta ke yi, shi ya zama silar tashuwanta daga daddaɗan baccin da take kwasa. Tana buɗe idanuwanta ta jawo wayan ba salati balle salallami, tana kallon numbern da aka ƙira ta da shi ta ja guntun staki, tare da ɗaukan ƙiran ta sanya a hands- free, ta na tura baki ta ce, "Hello!" Muryan wata dattijuwan mata ce ta amsa a ɗaya ɓangaren ta ce, "daughter ya kike?" "Ina lafiya Mom, please bacci nake yi kuma kunsan ba so nake ina bacci ana tashi na ba, ki bari zuwa anjima idan na tashi sai ki ƙira ni", budurwan tayi magana cike da gadara, kaman wacce ki yi wa ƴar cikinta magana ba uwarta ba. "Sorry lovely daughter, zan ƙira anjiman amma dai yanzu daman zan tambayeki ne yaushe za ki shigo ne?" Tana tura baki ta ce, "Mom zan shigo zuwa gobe, i my self am very eager to be at home, akwai abin da nake son yi, a serious mission Mom." "No daughter, kiyi haƙuri ki taimaka ki dawo yau kin ji." Sai da yastine fiska sannan ta ce, "Anyway shikkenan dai Mom zan duba na gani, amma gaskiya sai na gama baccina, kuma zan dawo ne dan abin da nake so nayi." "Tun da za ki dawo ai shikkenan daughter, ba komai huta abinki Allah ya miki albarka ya dawo da ke lafiya, Allah kuma ya baki sa'a." Ba tare da ta amsawa Mom ɗin ta ba ko kuwa ta mata sallama, ba ko ɗaya ta kashe wayanta kitt, ta ajiye sa tare da jan tsaki ta ce, "Mutane sai takura, ni gaskiya ba don ina da mission na da zai kai ni gida ba, da ba zan koma ba dan nasan aikin masifaffen stohon nan ne, da ya ƙi mutuwa ya addabi rayuwan mutane kaman muna oldest day's, mtswww to be in a family such like my family is a biggest problem, family ga girma ga girman maganganun", ta ƙarishe mitanta tare da komar da kan ta kam pillow, ta ci-gaba daga in da ta dasa aya a baccin, domin bai ishe ta ba jiya kwanan club suka yi da freind's nata (Allah ya kyauta Allah shirya mu.) ⭐ Washegari Ummiy bayan ta yi sallahn asuba ta yi azkar nata da komai, bacci ta koma sai zuwa ƙarfe tara ta tashi, da mamaki take kallon agogon da ke maƙale a bangon ɗakin nata, bacci tayi har haka ana neman ƙarfe goma, amma baby bata shigo ta tashe ta ba kam me kenan, hakan na nufin bata tafi makaranta ba tana can tana bacci, girgiza kai kawai Ummiy tayi, tare da ƙiran sunan Allah tana mai miƙewa staye, fitowa tayi ta nufi ɗakin da yake mallakin baby. Tana isa ta buɗe ƙofan dakin tare da yin sallama, ai kuwa hangota tayi ta baje abin ta tayi ɗaɗɗaya akan madedecin gadonta, girgiza kai tayi ta ce, "Wai ke kam lafiyanki ƙalau kuwa da maganan bacci? Kina kwance har ƙarfe tara baki shirya kin tafi makaranta ba, baby zan haɗa ki da yayanki ya saɓa miki fa."