[2/3, 1:06 PM] El~Yaqoub: INSAAF Writing by:Amnah El~Yaqoub 1&2 MARUBUCIYAR : *DANA SANI* *BURINAH* *WAZAN ZABA?* *SHALELAN BABA* *NI DAKE* *DANGI DAYA* *INSAAF* Like my page on Facebook πŸ‘‡πŸ» https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 *Page Din farko nakane dan'uwa na,PRINCE ABBA BAKARYA, ubangiji Allah yabar zumunci, Amnah tana yinka sosaiπŸ˜‡* Dasunan Allah mai rahma mai jin qai, ya Allah yanda nafara wannan littafin lafiya, Allah kabani ikon gamawa lafiya, kuskuren da zan rubuta wanda nasani, da wanda bansaniba, Allah yayafe min, Allah ka haneni rubuta abinda zaiyi Sanadin tashin hankalin wani ko wata. Dan girman Allah, masu doramin littafi a channel dinsu su daina, wallahi tallahi tunda nafara rubuta littafi, bantaba shan wahala irin yanda Nasha wajan rubuta labarin DANGI DAYA ba, amma abin baqin ciki ina gamawa kuka sacemin kuka doramin a channel dinku, FARAR SAQA TV wallahi idan kuka sake doramin littafi a YouTube zanyi reporting dinku a lalata channel Din, kuntara views din banza , banyi littafin kudi ba banga dalilin dazaisa kunemi kudi da littafi naba, inada Damar dazan siyar dashi amma ban siyar ba,Bana saka number ta a littafi, amma acikin littafin littafin DANGI DAYA nasaka number brother na, idan kunyi masa magana zai sanar dani, yanzu de na roqeku kudaina, nagaba kuwa bazan roqeku ba. To wannan Karon alqalamina yatafi Lagos, kuyi hakuri wannan littafin zakuci Karo da kuka,😭 dakuma emogi d'an kadanπŸ‘ŒπŸ» Bazan ziga littafina ba, kakaranta kaji yanda yake da kanka 🀝🏻 *A taqaice* Labarin INSAAF labari ne da taurarin ciki suke fuskantar qalubale iri-iri, tauraron dakuma tauraruwar, kowa da irin nasa qalubalen, wanda daga qarshe zan warware muku komai insha Allah πŸ™πŸ» __________ Manyan motoci ne guda biyar suke sharara gudu a babban titin dazai kaika mubi local government, Cikin jihar Adamawa, sosai suke gudu kamar sun samu titin gidansu, duka motocin guda hudu farare ne, kuma kowacce daga cikin su number motor tana dauke da sunan INSAAF, guda dayace baqar qirar Range rover take dauke da number LSR Lagos Surulere, daya daga cikin local government dake Lagos state, sosai suke gudu Bana wasaba, motocin farare biyu agaba, biyu abaya, Sai kuma baqar motar datake tsakiyarsu Su biyu ne azaune a bayan motar shida yayansa, gaba dayansu suna sanye cikin suit wadda tayi bala'in yimusu kyau Babban Hankalinsa Yana kan computer dake kan cinyar sa Yana typing cikin sauri, computer na qarewa kallo launin brown, amma maimakon aga sunan company computer daya qerata sainaci Karo da sunan INSAAF Agogon dake daure a tsintsinyar hannunsa qirar Gucci ya kalla yasaki wani gajeren tsaki, sannan ya maida Hankalinsa kan abinda yake matashin saurayin dake gefensa kyakkyawan gaske, suna mutuqar kama da juna, saide shi bekai shi shekaru ba, window dake gefensa yagama kalla bayan sunzo wucewa ta wani qauye dake kusa da Mubi, sannan ya juyo ya fuskanci dayan yace "Yaya, kasan wannan qauyen fa mukazo nida Mamy last year munraba musu zakkah, wallahi Yaya nide qauyen Yamin , Shiru babu hayaniya, gashi lafiya muka Gama abinda yakawo mu muka tafi" Shiru yayi Yana jiran yayan nasa yabashi amsa, amma Shiru kamar da dutse yake magana, kawai typing dinsa yake Bata fuska yayi kalar shagwaba ya kalleshi sosai "Yaya magana fa nakema" Batare daya kalli qauyen ba Hankalinsa Yana kan abinda yake yace masa "naji" Shima da yaji irin amsar daya samu Sai yayi Shiru bai sake magana ba, ya rungume hannunsa a qirjinsa Yana Kallan window tare da tunanin Mamynsa, Yana fatan inama ace ta biyosu *** ***** *** "AMINA!" cikin sauri tafuto daga cikin dakinta tana daura dankwali a kanta, sanye take cikin atamfa wata kod'ad'd'iya, duk da ta daura dankwali hakan bai Hana gashin kanta mai tsawo da santsi futowa ba,Allah yayi mata baiwar gashi sosai me matuqar tsawo da sheqi,wani sillallan takalmi tasaka tace "Inna gani" "yauwa Aminatuwa 'yar albarka dauki tulun nan kisamo mana ruwa mudora abinci, Kinga yayanki baya nan, kuma wajan akwai Nisa, Dan Allah Karki tsaya shirme a hanya kinji ko" Ahankali cikin sanyinta tace "to Inna" Sannan ta dauki tulun tafice daga gidan batare data saka ko mayafi ba Tana cikin tafiya tana yar waqarsu ta dandali ta hangi wata majalissa duk maza ne sunata fira suna daria,Sai masu shan rake suma sunata nishadi, mutum daya ne daga cikinsu ya hango tahowarta ya fadawa sauran, lokaci daya majalissar ta watse, tuni wajan yakoma kamar ba'a halicci mutane, mamaki ya kamata, kawai saita girgiza kanta tawuce gidan qawarta lubabatu tashiga bakinta dauke da sallama,ta tarar dasu zaune a tsakar gida suna hira itada goggonta, lubabatu tana ganinta tace "Amina sannu da zuwa, kamar kinsan yanzu nake shirin biya miki kozakije Debo ruwa" Itama murmushi tayi, cikin sanyin muryarta mai zaqi tace "Tona hutar dake, tashi mutafi" Tamaida Kallan ta wajan goggo zata gaisheta, amma kafin ma tayi magana goggo tace "Ai Amina saide kije ke kadai, lubabatu tanamin aiki" Cikin tsananin mamaki ta kalli lubabatu taga azaune taganta babu abinda take, cikin sanyin jiki tace "to goggo" sannan tajuya zata fita daga gidan Lubabatu ta tashi zata bita, cikin tsawa goggo tace "ke!! Dawo ki zauna" Kamar zatai kuka tace "goggo rakata zanyi kofar gida" Cikin Kallan rashin mutunci goggo ta watsawa Amina harara, sannan tacewa lubabatu " Ai basai kin rakata Bama, da tare kuka shigo? Ba'ita kadai tashigo ba? To rakiyar ta'isa haka daga nan bakin kofa ma" Amina tana ganin haka, tasake girgiza kanta Akaro na biyu, wani irin abu yatare mata maqoshi, kuka takeso tayi amma tahana kanta, saide manyan idanuwanta sun kada sunyi jajir, cikin sauri tafice daga gidan Tafuto kenan daga gidan su lubabatu taga isyaku yayan lubabatu suna zaune shida abokansa kusan su biyar, isyaku Sai tsari yake, Sai zuba surutu yake suna dariya, kasancewar sa mutum mai yawan surutu, ta gabansu tazo ta wuce amma abin mamakin shine su basu guduba amma cikin sauri suka juya mata baya, ko kadan sunqi yarda su kalleta Ahankali ta daga kanta taga yanda mutane suke gudunta, lokaci daya taji hawaye masu dumi sun silalo daga idanuwanta, wannan Karon batayi kokarin Hana kanta kuka ba, sosai take hawaye tana tafiya cikin sauri, tun tana yin kuka na hawaye harta dawo tanayinsa da sheshsheka, in banda tanada karfin hali da tuni tayi wurgi da tulun Takoma gida, amma ahakan ta daure tanufi hanyar Rafi ita kadai *** ***** *** Cike da qwarewa motocin suka tsaya awajan taron Bude daya daga cikin Babban Companynsu dake Mubi local government An tsara sunan company asama mai taken.... INSAAF LTD (OIL&GAS SERVICES) anyiwa wajan kwalliya sosai yanda ya kamata,mutane sun taru danqam awajan, su kadai ake jiran zuwansu, cikin sauri daya daga cikin Escort dinsa yabude musu bayan motar suka futo shida qaninsa P.A dinsa Auwal ne yamatso da sauri yafara yimasa Bayani "Yallabai wannan sune takardun dazaka saka hannu bayan angama taro, sannan akwai wasu baqi da suke buqatar ganinka, akwai maganar kwangila data kawosu wajanka, dangane da wajan wannan taron kuma babu matsala, angama komai kamar yanda kabada umarni" Adede lokacin da PA yagama Bayani, adede lokacin suka qarasa ciki, ahankali yace "Okey" Bayan yagama jin Bayanin nasa Bayan anbude taro da Addu'ah kuma anyi Bayani sosai Akan wannan company, Sai aka Bawa mamallakin company dama yayi nasa jawabin, bedauki wani lokaci mai tsawo Yana Bayani ba, ya damqa amanar kula, dakuma riqe wannan company a hannun qaninsa, kuma dan'uwansa, ma'ana yabashi dama ya tsaya a matsayin shugaba na wannan company A take wajan ya dauki qaran tafi, kowa farin-ciki dauke Akan fuskar sa, mutane dayawa kuwa suna mamakin irin yanda yake qaunar wannan qanin nasa Lokaci daya hawayen farin-ciki suka zubo masa, yadaga kansa ya kalli yayan nasa, Ahankali yace "Yaya..." Cikin sauri yayan nasa ya dakatar dashi ta hanyar daga masa hannu, saida yagama ganawa daduk mutanan da PA dinsa yayi masa Bayani, sannan sukai shirin tafiya gida, kwata kwata zuwansu, dagama taron bedauki wani lokaci maai tsawo ba, mutane sunci sunsha sunyi hani'an, amma shi oga kwata kwata ko ruwan wajan baishaba Daga nan basu tsaya yin komai ba, aka Bude masa Mota suka shiga, Yana zama wayarsa tafara qara, be dauka ba, saida yabari ta katse dakanta, sannan ya kirata, yanaji andauka daga daya bangaren yace "ISHRAQA" Saida tayi murmushi sannan tace "dama kiranka nayi inji Yaya taro, dafatan komai lafiya" Ahankali kamar mai koyon magana yace "koh?" Dariya tayi, tace "Naga alama har yanzu fishi kake dani saboda naqi zuwa,akwai abinda yasa banzo ba" "yayi" shine kawai abinda yace Dan daga muryarta tayi cikin fishi tace "Wai kai Sai wani binka nake Ina baka hakuri Sai kace wani sarki Sai amsamin kake kamar bakaso d'an rainin hankali kawai, ni Sai anjima" tana fadar haka takashe wayarta Murmushin dabai shirya yi bane ya qwace masa, har dimple dinsa ya futo sosai, cikin ransa yace "yar rainin wayo kawai" sannan ya ajiye wayar agefensa yabude computer Yana Moving wasu documents zuwa wata folder Qanin nasa yayi sakare Yana kallansa, zai Iya cewa tunda Garin Allah ya waye babu wanda yaga murmushi afuskar yayan nasa, amma saboda Ishraqa tayi magana dashi har tayi Sanadin sakashi murmushi, shikam baisan shaquwar datake tsakanin suba, abinda yasa ni shine Ishraqa abokiyar shawarar yayan nasa ce, kuma baya boye mata komai, haka itama yasan sirrikanta dadama a matsayin su na Class Mate kawai Ajiyar zuciya yayi, yadubi yayan nasa "Yaya Naga Alama kana cikin farin ciki saboda Anty Ishraqa takiraka, kude kuna son junanku, inama ace Nima nasamu qawa wadda zamuyi qawance da'ita haka kamar ku" Juyowa yayi ya kalli qanin nasa, tsantsar Kallan yarinta da shirme yake masa, in banda shirme mezaisa yace suna son juna da matar datake da aure akanta, batare da yayi magana ba, ya maida Hankalinsa kan computer Haushi ya kama qanin nasa, Dan haka Shima yayi Shiru kawai Bayan wasu mintuna ya dago kansa tare da rufe laptop din,yasaka ta a cikin jaka sannan yarufe jakar, Ahankali yafara magana "Nagama Dora kowanne documents dawasu takardu daya danganci filaye,gidaje, gonaki, da takardun duka sauran companies na INSAAF dama sauran kadarori Akan laptop dinnan" in banda qanin nasa Yana kusa dashi da bazai jishi ba, cikin sauri ya kalli yayan nasa "Amma Yaya kana ganin babu kuskure kuwa Akan hakan?" Shima Kallan qanin nasa yayi cikin mamaki batare da yayi magana ba, wanne irin kuskure yake magana Akan Andora takardun komai Akan computer? Ai Yana ganin kamar hakan shine zaifi sauqi Kafin qanin nasa ya sake magana aka yiwa motar tasu wani irin duka, arazane suka d'ago kansu suka kalli gabansu, cikin sauri driver yataka birki, hakan dayayi shiya basu Damar dukan motar ta ko'ina, gaba daya sun faffasa glass dinta dak! dak!! gaban qanin nasa yafara faduwa,musanman dayaga gabza gabzan qartin dasuka zagaye motar tasu, lokaci daya tsoro yakamashi ya kama murdaddan dantsan hannun yayan nasa yariqe (🀣) Jikinsa Sai rawa yake, shikuma gogan ko kadan babu alamar tsoro a ransa, bare kagani Akan fuskarsa, shi dama yasan dole za'a rina, tunda yaga babu motocin gabansu da bayan su yasan cewa dole ansake shirya masa wata maqarqashiyar kamar yanda aka saba Jakar laptop dinsa ya dauka cikin sauri ya ratayata ajikin sa, sannan yabude kofar motar zai fita Qanin nasa ya sake qanqame hannunsa, tuni hawaye sun samu matsugunni Akan fuskarsa (🀣) Cikin kuka yafara girgiza kansa "Yaya ASIM.... karka fita, Allah zasu kasheka,Dan Allah Yaya karka fita suyima wani abu" Batare dayace komai ba ya qwace hannunsa yafice daga motar, suna ganin futowar sa kuwa suka hau kansa da duka,babu ji babu gani,Shima yafara ramawa, driver Yana ganin yanda suke fada Shima yafuto da sauri domin temakon ubangidansa amma kafin yaqaraso daya daga cikin su yasa bindiga ya harbeshi acikinsa, nan take yace ga garinku nan (😭) Wani irin karfi ne yazo masa, har yayi nasarar qwace makamin daya daga cikin su yafara yimusu wani irin mahaukacin duka dashi Shikuwa qanin nasa dake Mota qamewa yayi azaune, tunda yake baitaba ganin harbi a zahiri ba Sai yanzu, wani irin danshi yaji a Wandonsa, wanda ya tabbatar ko tantama babu fitsari ne (🀣) Yajuya ya kalli yayan sa yaga yanda yake fada kamar a filin Wrestling, gaba daya Jikinsa ya dauki mazari, daya daga cikin yaran ganin Yana dukansu kuma idan sukai wasa tsaf zai musu illah, Dan haka nan take babu Bata lokaci yazaro bindigar sa yaseta shi, ji kake taaaas ya harbeshi akafardarsa Wata irin gigitacciyar qara qanin nasa yasa, dakarfi yace "Yaya!!!" Shikuwa Asim cak ya tsaya, lokaci daya ganinsa yafara daukewa,ya tabbatar da cewa mutanan da suke neman rayuwar sa yau sunci galaba akansa, Ahankali labbansa suka furta "Amjad" Sannan yadaga hannunsa daqyar yayiwa qanin nasa daya Kira da suna Amjad alama yagudu, dif idanuwansa suka dauke, yazube Akan gwiwar sa, sannan yafadi awajan Idanun Ammar sunyi jajir saboda kuka, Akan idonsa yayansa yafadi, yasan cewa yanzu kuma saura shi, cikin sauri yabude motar yafuto, bai tsaya awajanba ya kama gudu, baisan ma inda yake dosa ba Suna ganinsa Yana gudun tsira, amma abin mamakin babu wanda yayi masa komai, asalima Dena kallansa sukai, ganin Asim a kwance kamar matattace yasa suka kwashe da wata irin dariya, su kayi kama-kama suka mai dashi cikin motar, hannunsa banda jini babu abinda yake zuba Babban cikin su yakira waya yace "oga mungama aikinmu, yariga ya sheqa saide labarinsa" Daga daya bangaren akai magana, sannan Yaron ya sake cewa "angama oga" daga nan yakashe wayar Babban tafkin ruwan dake tsallaken titin wajan nan suka tura motar, babu tunanin komai suka tura motar da Asim din yake ciki cikin wannan ruwa Suma suka hau motarsu suka tafi a dari da sittin, wajan yarage daga fassasun glass din motar, Sai jinin Asim daya zuba, dakuma gawar driver dake kwance male-male a cikin jini Shikuwa Amjad Yana cikin gudu kwata kwata baya Kallan gabansa, saiji yayi wata Mota tayi Sama dashi, nan take yafadi awajan sumanme *** ***** *** Hawayen Idonta ta share Akaro na ba a dadi, mutuqar gajiya ta gaji da wannan diban ruwan, gashi yayanta baya nan, idan ta zauna ma babu abinda zatayi, Gara ta debo musu ruwan ko hakan zaisa ta ragewa kanta dinbin damuwar datake damunta Tana qarasawa Rafin ta tsugunna da niyyar debo ruwan saitaga yayi ja, tasa hannu tana kawar dashi taga abu yaqi qarewa, tana juyawa hannun ta na dama taci Karo dashi, gabanta ne yayi mummunar faduwa, cikin sauri ta miqe tsaye ta callara wata irin qara wadda tasa cikin dajin amsawa, amma Shiru kakeji daga ita Sai kukan tsuntsaye, jikinta ne yadau ki rawa kakar-kakar, tafara ja da baya tana girgiza kanta, ganin cikakken mutum a kwance fari tass dashi tamkar bazaka masa hausa ya amsa ba, baya baya takeyi tana cewa "Ba mutum bane, wallahi aljanine" awajan tabar tulun ta kwasa aguje tayi gida, kasancewar tanada yalwar dukiyar fulani,Sai gudun datake yasa suma suke rawa Baram! Tabude kofar gidan su tashige, tana zuwa tsakar gidan tafadi akasa Babanta da yayanta dasuka dawo daga cin kasuwa atare suka ce "Subhanallahi..." Amma ko kallansu batayi ba, kokarin tashi take tashige cikin dakinta, Inna ce takamota tariqeta cikin tashin hankali tace "ke Amina, menene? Keda waye? Waye yabiyo ki haka?" Hannunta tadora Akan qirjinta datake numfashi Sama-Sama Sai haki take saboda gudun datasha, takasa basu amsa Sai Hannunta dayake rawa ta daga tana nuna musu hanyar kofar gidan Wacece Amina? Meyasa ake gudunta? Meyasa ake bibiyar rayuwar Asim? Fan's ya bayan kwana biyu? ✍🏻 Amnah El~Yaqoub [2/4, 11:22 AM] El~Yaqoub: INSAAF Writing by :Amnah El~Yaqoub 3&4 Like my page on Facebook πŸ‘‡πŸ» https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 Babane yaje Randa yadebo mata ruwa akofi, ya tsugunna agabanta tare da meqa mata "karbi wannan Kisha" Dasauri kuwa tashanye ruwan, amma duk da haka tana Haki, saide ba kamar nadaba, duk sun zuba mata ido suna Kallan ta, yayanta ma ya matso kusa yace "meyake faruwa qanwata? Kiyi mana Bayani mana" Numfashinta Yana Sama Sama kadan, tace "Yaya Ammar wallahi aljanine, aljani nagani a Rafi" Gaba dayansu su ukun suka hada baki suka ce " Aljani Amina!!" Babanta ta kalla tace "Eh wallahi baba, zan Debi ruwa kenan naganshi, nikam shikkenan nayi gamo" ta qarasa maganar tana Dora hannun ta a kanta ( ) Babanta ne ya kalli yayanta yace "Ammar muje mugani, wata qila akwai abinda yake faruwa" Cikin sauri tariqo baban "Baba karkuje, wallahi idan kukaje kuma zai Bude muku ido, karkuje baba" Murmushin manya kawai yayi, suka nufi hanyar fita shida Ammar, Inna ma dake tsaye tace "a a Malam, ai muma bamuga ta zama ba, ya za'ai yarinya tace taga aljani kutafi kubarmu mu biyu agida, idan wani shegen ne yayi mata ture fa" (πŸ˜‚) Baba yace "kumafa hakane larai, to kutashi mu tafi, idan magana tafi karfin mu Sai a fadawa mai Gari yakira masu ruqiyya ayi mata" Inna ta yafa mayafi tabisu, itama datayi tsuru agefe cikin sauri ta tashi takama hannun Inna tariqe gam, a haka suka tafi, a hanya duk wanda yaga Amina dauke kansa yake, idan yarane kuwa saide kawai kaga sun kwasa aguje sun gudu, Abin Yana mutuqar damunta, saide tashin hankalin data gani a Rafi yafi tsaya mata Arai Suna qarasawa kuwa tasake riqe hannun Inna,sukaja suka tsaya daga nesa, amma duk da haka saida ta buya a bayan Inna, Ahankali Ahankli take Dan leqo kanta Baba da Yaya Ammar kuwa cikin sauri suka qarasa,Yana Nan agefen ruwan a kwance kamar yanda ta ganshi itama, baba yace "subhanallah, duba duba Ammar, ai kamar mutum nake gani" Ammar yace "Wallahi mutum ne baba" Bismillah sukayi sannan suka janyo shi waje,hannunsa kuwa jini ne yake zirarowa mai kauri, baba ya kalli su Amina da suke can gefe, "Larai mutum nefa, wannan yarinya da shashanci take" ya qarasa maganar Yana Kallan Amina Inna tace "Auto, Bari mu qaraso" (πŸ˜ƒ) Wajan suka qarasa, Amina ta zuba masa ido tana Kallan tsantsar kyan da Allah yayiwa wannan bawan Allah, Yana kwance kamar babu rai ajikinsa, amma jakar laptop dinsa tana nan ajikinsa, gashin idonsa dogaye Zara-Zara,ga wani irin saje da yayi wa fuskar sa mutuqar kyau, bashida gemu saide saje daya qara masa kyau sosai, Inna ma data ganshi saida ta tsorata, cikin ranta kuwa cewa take wannan kyan nasa ai yayi yawa Baba yace "Ammar inaga daukansa zamuyi, mukai shi gidan maigari, duk abinda ya yanke shine daidai" Girgiza kansa yayi "haba baba, wanne irin maigari awannan halin da yake ciki, mukai shi asbiti kawai, idan muka dawo dashi Sai akai shi gidan maigarin muji ta bakinsa" Baba yace "to muje asbitin" kamashi sukai suka dagashi, baba yacire jakar laptop din yayarta anan, ya cacimeshi yariqo hannun, aikuwa jini nan yafara Bata hannun baba, shikuma Yaya Ammar yariqo qafafun, wucewa sukai dashi gefen titi suna tare Mota, suma su Inna sukabi bayan su, harsun tare Mota suna qoqarin sakashi Amina tajuya, ta kalli jakar da baba yacire ajikin wannan bawan Allah yayar, ta kallesu sun sakashi aciki suma suna kokarin shiga, da gudu tajuya taje ta dauko jakar ta ratayata a hannun ta, Inna kam ko lura da abinda Amina tayi batayi ba, sannan sukai sallama dasu baba, su suka dau hanyar komawa gida itada Inna, su kuma su baba suka wuce Asbiti Suna zuwa gida kuwa tawuce dakinta da wannan jaka, zama tayi har zata Bude taga menene aciki Sai kuma tafasa, haka tazauna tazubawa jakar ido cikin ranta tana so taga menene aciki, Ahankali tasa dogayen yatsun hannun ta tabude jakar, computer ce ta baiyana mai launin brown, ruwa yagama cikata harta gaji da cika, rubutun sunan INSAAF dake jikin computer tashafa ahankali, daga nan ko budeta batayi ba bare tayi tunanin shanyata arana, tamaidata cikin jakar tarufe, sannan tabude bakkon kayan ta tasakata acan qasa, qarqashin kayanta (πŸ˜–) Sukuwa su baba kai tsaye suka ce driver yakaisu Mubi General Hospital, sunje anyi musu duk abinda ya kamata amma basu ta'bashi ba, Kai tsaye daga nan suka turasu Adamawa State Specialist Hospital anan aka fara bashi temakon gaggawa,daqyar suka yarda Akan zasu fara yimasa aikin saboda basuzo da kudi ba, saida baba yayi musu alwaqarin cewa Gobe gobe za'a kawo musu kudin Daga nan aka shiga dashi Dakin tiyata har sukai nasarar cire masa harsashin, baba Yana zaune a waje shida Ammar, kawai tunanin yan shanunsa qwaya biyu yake yi, wanda yake kiwonsu saboda ranar Bikin Amina, yanzu dole saide yasiyar guda daya yanaji yanagani (πŸ˜‚) Hakan ce kuwa ta kasance, washe Gari Ammar yakoma gida yayiwa Inna Bayani, aka saida saniya guda daya yakoma asbiti da kudin, bayan sungama biyan kudin aka basu wani Rasit dakuma magungunan da'ake buqata, baba yazubawa wannan takardar Rasit din ido yayi Shiru Yana kallanta, kawai hoton saniyarsa yake gani ajikin takardar (🀣) Haka suka siyo magungunan ma, saide kuma fatan Allah yasa marar lafiya ya farfado lafiya Labarinsu : Gidan Malam buba kenan, cikakken bafulatanine da yake zaune aqauyen Mubi, Yayansu biyu shida matarsa larai, akwai Ammar da suke riqewa awajan su, shi Dan ruqo ne, Ammar shine kamar babba a gidan, Sai kuma yarsu Amina daga ita kuma babu qari, Amina yarinya ce qarama sosai, kwata kwata shekarunta goma Sha takwas , amma Allah yayi mata jiki dakuma sura irinta manya, kasancewar aqauye suke ba kowane zai gane hakan ba, Tanada qirji manya,hips dinta yan daidai misali, Ba qaramar kyakkyawa bace, chocolate Beauty ce sosai, kalar fatarta kamar ta Sudanese, tanada manyan idanuwa, gashinta dogo ne sosai, danma baya samun gyara Auren Amina biyar awannan qauyen nasu,duk wanda ta aura adarensu na farko yake mutuwa, muddin angon ta yazo karbar haqqinsa Tofa saide wani bashi ba, adaren zai mutu,aurenta nafarko auren soyaiyane da saurayinta datake mutuqar so Haruna d'an kande, d'an kande Yana bala'in son Amina, kamar yanda aka sani kowanne ango Yana murna ankawo masa amarya haaka ce ta kasance awajan d'an kande, duk da amaryar tana noqewa haka d'an kande yanemi haqqinsa, amma tun kafin yakaiga neman hanyar sa yaaji maqoshinsa yariqe, numfashinsa yafara yin Sama kamar me asma, awannan dare d'an kande yarasu, al'amarin yataba Amina sosai, saida aka hada da malamai masuyi mata roqon Allah Aurenta na biyu ta auri wani abokin Haruna, aminin d'an kande ne sosai, shikuma be mutu adaren auren su ba, Sai washe Gari, Yana tsaka da wasa da amarya yaji yawun bakinsa Yana tsinkewa, daga nan wani irin kumfa yake futo masa, kafin safiya Shima Allah yayi masa cikawa Daga nan Amina tafara Bawa kowa tausayi aqauyen, wasu suce kwanan su ne yaqare, wasu kuma sabanin haka Aurenta na ukuma hakace ta kasance Bata sauya zaniba Tofa daga nan aka fara gudun Amina, wasu har agabanta suke mata habaici cewa ita matsafiya ce, duk Iyayen dasuka San Amina tana qawance da yarsu saisu datse wannan alaqar, Abin Yana damun su Inna sosai, daga nan baba yafara karbo mata rubutu awajan liman tanasha Ana cikin wannan hali wani babban mutum mai mata uku yace zai aureta,alhaji ilu mai kudin qauye ne, kullum haka zaka ganshi azaune akofar gidansa Yana zare ido shi Ala dole gamai kudin qauye, haka yadage Akan zai auri Amina, inma itace take kashe mazajen auren to shi shine ajalinta,awannan lokacin su baba suna cikin tashin hankali kotakan Amina ba'abiba a kayi aure, ango yazo da kazarsa da daddare, Amina tana zaune adakin ita kadai, Yana zuwa kuwa yazubawa qirjinta ido Yana kallo kamar maye, ko alwala basuyi ba bare sallah ya afka mata, haka ya turmushe yar mutane ko qanqantar shekarunta be dubaba, babu wani wasa haka yafara neman hanya, ita tsoro ma yabata yanda taga duk ya rikice, gaba daya tsoro yahanata sakin jikinta bare yasamu hanyar shiga, haka yadinga neman hanya amma wajan qamas yake babu komai bare alamar danshi, ahakan yacire tausayi zai shiga, itade Amina batasan Yaya a kayi ba Sai hango alhaji ilu tayi a bakin kofa, anyi jifa dashi Yana fitar da numfashi daqyar,Kasa tashi yayi daga wajan saboda gaba daya ma jiyayi besan inda kansa yakeba, daga qarshe ma saiya miqe kafa yaci gaba da kwanciya anan (πŸ˜…) Itama Amina da sauri jikinta na rawa ta tashi tazauna tatakure kanta a cikin cinyar ta, awannan Rana yanda taga Rana haka taga dare, washe Gari kuwa daga wannan kwanciya ta barci alhaji ilu ya zarce, ita batasan ma yamutu ba, saida uwargidansa tazo taduba sannan tafasa ihu da kururuwa, yayansa da matansa suna kukan mutuwarsa suna dukan Amina, haka suka Koreta daga gidan jina-jina Al'amarin yabawa kowa tsoro, tundaga nan manya da Yara idan sukaga Amina kowa gudu yake, kowa ta kansa yake, gudunta suke sosai idan bakayi ban waje Ana tsaka da wannan hali Dan maigari yadawo daga wajan karatu, Laminu Yaro Dan qwalisa tunda ya qyalla idonsa Akan Amina yace Yagani yanaso, shi bashida wata mata bayan Amina Maigari yaso yaqi, amma Laminu ya nuna masa cewa duk wanda yamutu dama can kwanansa ne yaqare, bawai Amina ce take kashe su ba, haka a kayi wa Laminu auren gata, kasancewar sa Dan boko saiya raina shekarun Amina, Dan haka bai nemeta ba,Yana ganin kamar tayi qarama, itama dataga haka saita sake dashi, har shaquwa tafara shiga tsakanin su, saida auren su yayi sati daya, Laminu Yana nan ras da ransa, har Gari anfara gulmace gulmace Amina taga kudi shiyasa taqi kashe Laminu, ta ganshi Dan mai Gari gashi Dan boko, Laminu tun Yana daurewa harya Kasa, a kwana na takwas yanemi Amina, Shima a cikin ranar Allah yayi masa rasuwa Gari ya dauka Amina takashe Laminu, maigari kuwa yanke jiki yayi yafadi, daqyar aka samu yadawo haiyacinsa saboda Yana qaunar Laminu sosai a ransa, tundaga nan yatara mutanan Gari yace yakori Amina daga Garinsa( ) Al'amarin yadagawa baba da Inna larai hankali, daqyar suka hadu aka Bawa maigari hakuri, bai hakura ba saida yakafa musu sharadi muddin Amina tayi aure mijin ya sake mutuwa asanadinta,to kawai daga Dakin mijin tafice tabar masa garinsa, basai tabiya ta gidan iyayenta ba Dahaka su baba suka amince, kowa yaguji Amina, duk wanda ya ganta tsakanin su dauke kai kokuma gudu, saboda wannan abun kowa yaqi ta, babu mai sonta bayan Yaya Ammar, Inna, baba, Sai kuma lubabatu qawarta Back to story πŸ˜‰ *** ***** *** Lagos, Surulere local government "yanzu ranka yadade so kake kacemin Yaron nawa yamutu? In an'isa shege nake, wallahi tallahi bazai iyuba, banga gawar danaba danhaka dana bai mutu ba" Dan sandan ya kalli magidancin mutumin yace "Alhaji hakuri zakayi, har yanzu munakan bincike ne, dole abinda bincike ya nuna dashi zamuyi amfani" Yana Gama fadar haka yajuya ya maida kallansa ga Amjad da'akayi wa aiki a goshinsa saboda bugewa da yayi, sakamakon kadeshi da Mota tayi, idanunsa yayi jajir kasancewar sa fari, har yanzu hawaye sunqi tsayawa a'idonsa ya kalleshi da kyau yace "kayi hakuri kadena kuka, kaci gaba dayi mana Bayanin yanda abin ya faru" Cikin kuka yace "sun kashe shi fa..., agabana suka harbeshi yafadi" Gaba dayansu mutanan falon suka fashe da kuka, mamy tana zaune agefe tana Jan carbi, idanunta sun kumbura da alama Tasha kuka taqoshi, Amjad Yana jikin ta kamar Yaron goye, Sai kuma wata mata agefenta kana ganin ta kasan ba bahaushiya bace, balarabiya ce Magidancin nan yanajin furucin Amjad yafara Baza babbar rigarsa Yana fadin "shikkenan, innalillahi wa Inna ilaihirraji'un... Shikkenan Asim, wayyo niya Allah na" Sai jagwab yazauna aqasa Gaba daya yabawa 'yan sandan da suke tsaye tausayi, duk ya susuce kamar ma baya cikin haiyacinsa Miqewa Dan sandan yayi yadubesu "kuyi hakuri hajiya, muna nan munakan bincike har yanzu, saboda awajan da abin ya faru kwata kwata babu alamar gawar sa, saita driver kawai awajan, shikuma Amjad yace agabansa suka harbeshi, hakan yana nufin cewa kode be mutu ba yagudu da kansa, kokuma wanda suka harbeshi sun tafi dashi, amma insha Allah zamu tsaurara bincike Akan hakan, sannan Commissioner da kansa yabada cigiyar photonsa agidajen television's dakuma gidan redio duk wanda yaganshi yatemaka yasanar a police station din dake kusa dashi, insha Allah za'a bashi kyauta mai tsoka" Yajuya yabawa mutumin daya Kad'e Amjad da Mota hannu, yace"godia muke Yallabai, Haqiqah zuwansa yaqara taimaka mana wajan bincikenmu" Mutumin yace "babu damuwa" Kallansa yamai da ga Amjad yace"ko zaka iya binmu zuwa office domin sake amsa wasu tambayoyin? " Amjad yanajin haka ya sake shigewa jikin mamy ya rungume ta, hakan dayayi shiya sake nunawa d'an sandan cewa babu inda zashi, gaba daya tsoron mutane ma yake yanzu, ko nanda bakin gate bayajin zai Iya fita batare da mamynsa tana kusa dashi ba Dan sandan yayi murmushi kawai daga nan suka fita gaba dayansu *** ***** *** Amina da Inna suna zaune atsakar gida, Inna tana gyara daurin tsintsiyarta daya kunce, ita kuwa Amina tunanin wannan mutumin dasuka tsinta na cikin ruwa take, koya warke oho, amma gsky yanada kyau kam kamar bature, tarasa wazata Bawa labari ko zataji dadi (kunsan idan gulma tanacin mutumπŸ˜ƒ) Kamar an mintsineta ta tashi tace "inna zanje gidansu lubabatu yanzu zan dawo" "saikin dawo, Karki Dade akwai inda zamuje" Tace "to Inna" Tana zuwa gidansu lubabatu taga ancika falon nasu danqam dayara da manya anata kallo, saboda duk qauyen daga gidansu lubabatu Sai gidan maigari nan ne kawai suke da kayan kallo Yara yan kallo suna ganin shigowar Amina daya bayan daya suka watse, har bige juna suke wajan fita, jikinta ne yayi sanyi, duk saitaji ta muzanta, ita kuwa lubabatu da murmushi tatareta, tasa hannu zata janyota jikinta goggo ta daka mata wata uwar tsawa "ke Luba, koma daki kokuma yanzu inci mutuncin ki, sakara kawai wadda batasan ciwon kanta ba" Lubabatu sum sum tashige cikin daki ganin ran goggon nata yabaci yanda Bata taba zato ba Goggo tadubi Amina tace "kifita daga harkar 'yata Luba, ko'itama so kike ki lashe mata kurwa tabi sauran mazajen ki? To aniyarki tabiki, tsabar masifar naci irin naki yanzu Samari ko wajan Luba sun daina zuwa saboda Ana ganinku tare, to aniyarki ta kiyayi ramata...." Dagudu Amina tajuya tafice daga gidan, cikin kuka tafado gidansu ko sallama babu, Inna ta kalleta takasa binta tabata hakuri, tasan wannan kukan nata baya rasa nasaba da qaddarar rayuwarta, toya zasuyi? Ita kanta abar abawa hakuri ce yanzu bare kuma ita kanta Aminan(πŸ˜ƒ) Tashi tayi zata fara shara goggon lubabatu tashigo gidan, Inna tace "sannu da zuwa goggon Luba" Cikin fishi goggo tace "ba wannan ne yakawo niba, zuwa nayi inyi miki kashedi da gargadi Akan yarki Amina, tarabumin da yata, babu ita babu Luba, kowa yayi harkarsa, idan bahakaba kuwa wallahi hukuma ce zata rabamu" Tana fadar haka tajuya fuuuu tafice daga gidan, Inna tazauna Akan kujera da sauri tana ambaton sunan Allah, Sai yanzu ne tasan dalilin shigowar Amina tana kuka ✍🏻 Amnah El~Yaqoub [2/4, 11:52 PM] El~Yaqoub: INSAAF Writing by :Amnah El~Yaqoub 5&6 Dedicated to :Itz Sadeek, Alkhairin Allah yakai gareka πŸ€— Like my page on Facebook πŸ‘‡πŸ» https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 Toyaya zasuyi da rayuwar su? Qaddara ce Allah yariga daya dorawa Amina, su kansu basusan takamaimai abinda yake damunta ba, kuma Malam Yana karbo mata rubutu awajan Malam liman tanasha duk lokacin da abin ya faru Babu me'iya sauya Qaddara face Allah Ajiyar zuciya tasaki, tayi wulli da tsintsinyar hannunta sannan tafara hada abinci awani kwanon silva mai Dan kyau, shinkafa da wake ce amma duk ta caku6e,(πŸ˜–) Dakin Amina ta nufa, tana daga labulen taganta a kwance tayi kukanta harta qoshi "taso mutafi, wannan koke-koken babu inda zai kaiki, ki kaiwa Allah kukanki yafi miki wannan asarar hawayen" Ahankali ta tashi suka tafi, ko wanke fuska batayi ba, suna cikin tafiya sukazo wucewa ta majalissar su isyaku yayan Lubabatu , Ada isyaku Yana ganin Inna duk abinda yake zai Bari yazo ya gaisheta saboda qawancen dake tsakanin Amina da Luba, amma yanzu yana ganinsu yadauke kai kamar bai sansu ba, qarshe ma suna hada ido da Amina yasakar mata wata uwar harara, Inna tana ganinsa, Sukuwa sauran yan majalissar duk suka watse Abin yayiwa Inna ciwo sosai, ashe har yanzu haka Amina tana fuskantar wannan matsalar? Ashe har yanzu mutanan Garin basu saduda sunyi hakuri ba? Amma ahakan har take iya futowa aduk lokacin dataso? Inna Bata Gama tunanin taba suka hadu dawasu Yara sun dawo daga makarantar Allo, mutum daya daga cikin yaran tana ganin Amina tadaga murya tace "la'ila wallahi ga Amina nan" Atake yaran suka fara watsewa, kowa Yana gudu Inna batasan lokacin da hawaye suka zubo mata ba, Ahankali take share hawaye tana kuka, Amina tajuyo ta kalleta zatayi mata magana kawai Sai taga tana kuka, cikin sanyin murya tace "Inna meyasa kike kuka...? Bata Gama magana ba itama taji wani qullulun abu yatsaya mata awuya, lokaci daya tafashe da kuka itama, haka suke kuka itada Inna babu wanda yabawa kowa hakuri, har suka qarasa bakin titi suka shiga motar da zata kaisu Yola, anan Amina tasan inda zasuje Daqyar suka kawo kansu asbitin itada Inna, dasuka shiga ciki ne basusha wahala ba Allah ya nuna musu su baba Azaune a wata bishiya, bayan sun gaisa baba yace "Larai aida bakusha wahala kunzo da abinci ba" "yanzu Malam muda mukazo dubiya tayaya zamu taho haka hannu babu komai" Yace "Ai Ammar Yana siyo mana biredi, kuma akwai kayan shayi aciki" yadubi Amina yace "yanaga idonki sil haka ko kwalli babu 'yar baba? , kamar ma kinyi kuka" Inna tace "munyi kuka de baban Amina, al'amarin Amina yafara bani tsoro Malam, Anya kuwa ba zamuyi qaura mubar Garin nan ba?" Ammar dake tsaye yace "Inna Garin iyaye da kakanni idan muka barshi ina zamu? Duk suyi su Gama gulmarsu ai WATA RANA SAI LABARI {littafin takwarata miss suwaraπŸ˜ƒ} yaci gaba da cewa "wanda zai baka labarin ma wata Rana bazaka sameshi ba" Inna tana jinsa tayi Shiru,taga alama Ammar bashida hankali, Dan baiga abinda tagani bane yau shiyasa yake fadar haka, Inna ta kalleshi tace "kuje da'ita tadubashi, Nima gamu nan nida Malam" Ammar yadubi Amina yace "muje qanwata" Inna naganin tafiyarsu tadubi Malam tace "Malam al'amarin Amina fa yayi tsamari, yanzu futowar mu daga gida duk wanda yaganmu gudu yake, wallahi Malam bansan lokacin da nafara yiwa yarinyar nan hawaye ba, nikam Malam mezai hana muhada Ammar da Amina aure?inyaso daga nan mutattara yanamu yanamu mubar Garin? " "wacce irin magana kike wannan Larai, Amina fa ta dauki Ammar ne a matsayin yayanta" "hakane Malam, amma tasan cewa akwai aure atsakanin su, tunda munfada mata cewa shidin kamar d'an ruqo ne awajan mu" Saida baba yayi jimmm sannan yace "eto hakanma shawara ce mai kyau, saboda a cikin Garin nan namu de babu wanda zai qara futowa yace zai auri Amina, kuma Amina bazataci gaba da zama haka agabanmu babu aure ba, dole zata tafi Dakin mijinta, idan a kayi auren kawai saina saida gidanmu mubar Garin, Larai kin kawo shawara mai kyau, hakan za'ayi " Suna shiga Dakin tayi tozali da kyakkyawar fuskarsa data sake yin haske sosai, Yana kwance Yana bacci, ansaka masa robar qarin ruwa, zama tayi Akan kujera ta dubi yayan nata tace"Yaya ai kamar ma bacci yake " " bacci yake qanwata, tunda muka kawo shi sau daya yafarka, daga Naan kuma baisake farkawa ba, amma sunce zai Iya tashi daga nan zuwa Gobe ko jibi " Batace masa komai ba illa idanu data zuba masa, idan ta kalli farar fatarsa saita kalli Tata fatar, bakomai ne yake Bata mamaki akansa ba Sai gashin idonsa kamar na mace, haka taita kallansa ita kad'ai tana mamakin baiwar kyau da ubangiji yayi masa Su Inna ne suka shigo itada baba, kana ganin fuskar su zaka hango tsantsar farin cikin da suke ciki, Inna ma tadubashi tayi masa Addu'ah sannan sukai shirin tafiya gida Saida suka qara sati biyu a asbiti sannan aka sallamesu, ahakan ma shine ya matsa saboda yasan cewa tabbas 'yan gida suna nemansa, especially Mamy Amina tana share tsakar gidansu suka shigo shida baba da Yaya Ammar, Ammar ne yake riqe dashi duk da Yana d'an daurewa Akan sauran ciwon da wajan yake masa saida ya gaza, yadawo Yana rintse idonsa Tsintsiyar hannunta tayar tataresu da gudu tana musu sannu da zuwa, kallo daya ta yiwa baqon nasu, Yana sanye cikin suit dinsa wadda suka tsinceshi da'ita, amma jacket din nasa tana hannun Yaya Ammar , Sai ta cikin kawai white color tadubeshi cikin zazzakar muryarta tace "sannu" Batare daya kalleta ba ya daga mata kansa kawai, Sai runtse ido yake, daga wannan Bata sake yimasa magana ba tajuya, cikin ranta tana fadin wannan daga gani bashida juriya (🀣) Inna tace "Ammar qarasa dashi dakinka, akawo muku abinci" Yace "to Inna" ya kama hannun Asim yace "muje abokina" Ahankali yajuyo domin ganin mamallakiyar wannan zazza’kar muryar,Yana juyawa kuwa yayi tozali da dogon gashin kanta, tsananin mamaki ya kama shi, wannan qanqanuwar yarinyar ce harta mallaki wannan uban gashin? To Amma shi fuskarta yaso gani, dagowa tayi zata zubar da sharar data Gama, cikin sauri ya janye fuskar sa daga kallanta Suna shiga Dakin Ammar yanuna masa kan katifarsa yace "abokina ga wajan zama" Daga masa kai yayi batare da yayi magana ba, Ammar ya dauki buta ya futo zai shiga bandaki, cikin ransa Yana mamakin wannan bawan Allah, ace mutum babu magana saide Shiru haka da d'aga kai kamar qadangare (πŸ€”) Fillo yad'auka yakarashi ajikin bangon Dakin sannan yazauna ya jingina ahankali Yana qarewa d'akin kallo,Ahankali ya lumshe Idonsa Yana tunanin mahafiyarsa, ko a wanne hali take yanzu? Amjad.... Sunan Yana Fado masa ya runtse Idonsa saboda tuno yanda suka rabu da Yaron, koshi ma sun kashe shi? Dole yatafi gida, akwai matsala idan yaci gaba da zama anan, to Amma kuma Anya ba zaiyi hakuri yazauna anan garinba? Saboda mutanan da suke bibiyar rayuwar sa bazasu qyaleshi ba muddin su kasan yana Raye, to Amma Mamy fa? A wanne hali take ciki...?waye yake son ganin bayan sa? Waye? Waye shi? Babbar damuwar Sama itace laptop dinsa dabai san inda takeba, haqiqa Amjad yayi gaskiya dayace akwai kuskure wajan Dora komai a cikin wannan laptop din "Salamu Alaikum" Zazzaqar muryarta tadaki dodon kunnansa, batare daya Bude Idonsa ba, ya amsa mata, kallon ta takai gareshi taga Idonsa a lumshe, Sai gashin Idonsa dasuka kwanta wanda ya sake qawata masa kyakkyawar fuskarsa Ahankali ta dauke kanta daga gareshi tabude kwanon abincin data kawu musu tafara zubawa, taliya ce jalop, amma ta hausa, d'ago kanta tayi tanaso tace masa ga abinci amma kuma lokaci daya yayi mata kwarjini, shidin daga ganinsa kasan cewa babban mutum ne, sallama ma bata samu matsayin daya Bude ido ya amsa mata ba inaga maganar abinci? Duk yanda akai da alama Yana cikin dumbin damuwa, ashe a duniya akwai mutane masu damuwa kamar ita? Matsalarta babbar matsala ce, damuwar ta babbar damuwa ce da har tasa take ganin kamar tafi kowa shiga cikin damuwa "ga Abinci inji Inna" maganar ta tasake fadowa cikin kunnansa, Ahankali yake Bude Idonsa harya budesu fes a kanta, bece mata uffan ba yafara kokarin tashi zaune, Garin gyara zama yadan bige kafadarsa me ciwo da jikin bangon Dakin, cikin sauri yace "Washh" Kallansa tayi da sauri takai hannu zata taroshi Sai kuma tafasa ta tsaya cak, ta tashi ta sauri tafuto daga Dakin tana Kiran Inna Inna ta qaraso taga Yana runtse ido tace "Meyake faruwa ne bawan Allah ko jikinne?" Tana daga bayan Inna tace "Inna Fama ciwonsa yayi" Inna ta kalleshi cike da tausayi tace masa "sannu" Ahankali yace mata "yauwa" sannan yazauna ya dauki spoon zai fara cin abincin Inna ta karbi cokalin tace "kawo nabaka bawan Allah, idan Ammar bashida lafiya ninake bashi abinci dakaina" Beyi mata musu ba yasakar mata cokalin tafara bashi, Amina tana tsaye ta rungume hannun ta aqirji, tana kallonsu, bakinsa ta kalla d'an qarami kuma ja, gashi cokalin nasu irin me nauyin nan ne wani kwafd'ed'e me fad'i (🀣) Abincin datake bashi kadai shine yatuno masa da mahafiyarsa, Allah sarki mamy...., yasan cewa duk inda hankalin ta yake a yanzu yakai maqura wajan tashi Baba ne ya qwalawa Inna Kira, ta amsa masa sannan ta kalli Amina tace "zoki bashi abinci Amina, kiyi ahankali" "to Inna" cewar Amina data matso wajan ta zauna Inna tafita daga Dakin, Shima ya dauki ruwa yasha Yana mamakin wannan jaririyar da'akace tabashi abinci (🀣) Ita kuwa zuciyarta d'aya tadebo abincin zata bashi, amma saiya daga mata hannu, (βœ‹ 🏻) itama batace masa komai ba tamaida spoon din cikin kwanon, sannan tarufe abincin tatashi tafuto daga Dakin Acan Dakin baba kuwa su Inna sungama magana da Yaya Ammar Akan Akan zasu hadashi aure da qanwar sa, kasancewar yasan cewa akwai aure atsakanin su shiyasa koda wasa baiyi musu ba, ya amince da buqatar su Ita kuwa Amina Batasan abinda ake ba kawai daga Dakin Yaya Ammar data futo kai tsaye dakinta tawuce, suma suna Gama tasu maganar suka wuce Dakin Ammar din gaba dayansu Asim Yana ganin shigowarsu yaji dadi, bayan sun zauna baba yafara magana dashi "bawan Allah mude bamusan daga inda kakeba, kuma acan asbiti ma bamuyi wannan maganar dakai ba,nide sunana Abubakar amma Ana kirana da Buba awannan qauyen, wannan danane Ammar, dakuma matata larai, 'Yata Amina itace ta tsinceka a bakin Rafi taje Debo ruwa, tazo gida da gudu tasanar damu, d'ana Ammar shine yabani shawarar a kaika asbiti, kuma Alhamdulillahi yanzu kaji sauqi, muna so katashi muje gaban maigari kayi mana Bayanin daga inda kake " Ajiyar zuciya yasauke bayan yagama jin Bayanin su,Ahankali yafara magana"Baba sunana Asim...." Sai kuma yayi Shiru daga nan, su baba suka zuba masa ido suna kallansa, tabbas wannan daga ganinsa kasan Yana dauke da damuwa, to Amma babu Dadi bakasan mutum ba kawai kafara yimasa tambayar dabata daceba, danhaka baba yayi Shiru, Inna tace"muna jinka Hasim..." (🀣🀣) "bafa Hasim ba Inna, Asim,ake cewa" cewar Ammar Shide Yana jinsu bece dasu komai ba, Ahankali yaci gaba da cewa "Agarin Lagos nake, iyayena da 'yan'uwana duk suna can, Dan Allah baba kubar maganar zuwa wajan maigari, inaso kumin alfarma natafi gida gobe, nasan Hankalinsu atashe yake" Baba yayi murmushi yace "To madallah, haka akeso, amma bazaka tafi Gobe ba, kabari Sai jibi, Gobe zanyi auren 'Yata Amina tareda Ammar" Mamaki ya kama Asim, aure kuma? Wannan qanqanuwar yarinyar zasuyi wa aure? Bece da baba komai ba Sai "Allah yakaimu jibin" Washe Gari da sassafe aka daurawa Amina aure da yayan nata, akofar gidan maigari, wannan qauye kuwa Shiru kakeji anyi tsit kowa Yana jiran mummunan labari a cikin wannan satin, ango Ammar kuwa yasa sabon kaya Sai qyalli yake Yana walwali, baba yakira Amina har daki yayi mata Bayanin komai, lokaci daya ta rushe musu da kuka tace Bata yardaba, Bata so tarasa yayanta, Bata so yamutu yabarta, amma haka su baba suka daddage sukai mata nasiha mai ratsa jiki, musanman Inna ta mafi baba dagewa Akan Amina tayi hakuri ta rungumi aurenta Baba yace tatashi taje ta fitar da kayan dakinta za'a gyara musu shi su zauna aciki, kafin baqo yatafi su koma Dakin Ammar din Haka tafuto idanunta jajir Tasha kuka, dama d'akin bawani kayan kirki ne aciki ba, daga katifa Sai bakkon kayan ta, dakuma wani kwando Dan qarami na kayan kwalliya. Bakkon tafara dauka taji nauyi, sai tatuna da laptop din baqonsu datake ciki, tafitar da'ita tsakar gida, a lokacin Asim ya futo alwala tajuya ta kalleshi, Shima ya kalleta, idanunsu yahadu dana juna, cikin sauri kowa yadauke kansa, Yana alwala Yana d'an satar kallon ta, mamaki yake menene yasa ta kuka? Sake satar kallonta yayi Yana tunanin ina wani girma awajan wannan yarinyar dazasu yimata aure? Amina na ganinsa tayi sauri ta zuge zip din bakkonta zata dauko masa laptop dinsa, juyawa tayi zatayi masa magana saita kamashi Yana qare mata kallo Yana wanke qafafunsa (πŸ˜‚) Cikin sauri ya sake kawar da kansa, miqewa tsaye tayi tafasa dauko laptop din,tazuba masa ido qarara tana kallonsa, Tome yake gani ajikin ta?Shima ganin ta kamashi da satar kallonta yasa cikin sauri ya miqe yashige Dakin Ammar, yanata mamaki meyasa gidan aure amma kuma babu mutum kodaya dayazo musu? (πŸ€”)Da daddare baba yakira su yayi musu fada shida Inna, sannan baba yarakata har Dakinta dayasha gyara, sabuwar atamfar datasa tayi mata kyau sosai dawani uban mayafi mai girma data boye kanta aciki, fuskar nan taji kwalliya irinta su ta qauye, Addu'ah take cikin zuciyar ta Allah yasa Yaya Ammar karya nemi wani abu awajan ta, koda yake aitasan ma babu abinda zai nema tunda shima Yana mata Kallan qanwar sa ne, tunda gida d'aya suka tashi, koda ace yanemi haqqinsa ma bazata taba yarda ta bashi hadin kai ba, saboda tanaso yarayu, Gara su Inna suyi bacin rai ta Hana shi haqqinsa Akan ta bashi haqqin nasa daga qarshe yamutu yabarsu Sai can dare sannan ya shigo Dakin bakinsa dauke da sallama, Ahankali kuma cikin zaqin muryarta ta amsa masa, zama yayi agefenta ya ajiye ledar daya shigo da'ita mai dauke da kayan marmari, yace "qanwata yazaman kadaici" "lafiya Yaya" abinda tace dashi kenan "ya kamata ki tashi kiyi alwala muyi sallah koda raka'a biyuce" "inada alwala" Kallanta yayi, yaga taqi yaye mayafin nata, yace "toki Bude mayafin mana, ko Nima saina sayi bakin?" Ahankali tayaye mayafin nata, amma taqi yarda su hada ido dashi tace "aikai baka buqatar siyan baki Yaya Ammar, tunda gida daya muke rayuwa kanada Damar dazakamin magana na amsa akoda yaushe" Murmushi yayi, yasan saboda tatunatar dashi wani abu ne shiyasa tasako masa maganar suna rayuwa gida daya, to Dan suna rayuwa gida daya saiya Kasa neman haqqinsa awajan ta? Ya kalleta cikin wasa yace "tokidan Kalleni mana amarya, kina magana bakya Kallan angon naki" Tafukan hannunta tasa tarufe fuskarta cike da kunya , daga nan suka tashi, suka gabatar da sallah, yayi musu Addu'ah sosai, ya dauko musu fruit dinsu da yaji kankana sosai sukasha, sannan suka kwanta Bata cire kayan jikinta ba, Shima beyi mata magana Akan haka ba, Shiru Dakin yayi itade duk atsorace take, tana kuma Addu'ah Allah yasa ko yatsanta karya riqe bare ace ga neman haqqi Har bacci yafara fizgarta taji hannunsa Yana shafa wuyanta, gabanta yayi wani irin faduwa taji wani abu kamar yafada cikinta daga qirjinta, Addu'ah take a ranta tayi Shiru kamar tana bacci Shikuwa Ammar awannan halin da yake ciki ba yajin zai Iya hakura tunda ta riga tazama halalinsa Ahankali yajanyota jikinsa yarungumeta sosai Jiyayi yanda gabanta yake faduwa, yayi murmushi sannan yatura hannunsa cikin rigar ta yafara shafa cikinta yajishi ashafe kamar ba yanzu suka Gama cin kayan marmari ba, ta cikin rigar yafara shafar qirjinta, Yana goga mata hancinsa Akan wuyanta, yanda yake mata yazo mata awani irin yanayi, duk mazajen data taba aura babu wanda yake mata abubuwa haka ahankali cike da aji kamar baya so, Ahankali ahankali jikinta yafara saki, harta fara sakar masa jiki, Yana ganin haka yadage rigar Tata gaba daya yafara wasa da qirjinta sosai, ahankli tafara sakin wani irin numfashi, Shima gaba daya yafita haiyacinsa cikin rawar murya yace "Qan...qanwataaahhh kinajin abinda nakeji kuwa?" Idanunta a lumshe tadaga masa kai, Ahankali yaci gaba da abinda yake, al'amarin daya dauke su kusan awa daya Yana wasanni da'ita kafin yafara neman rabata da budurcinta yaji hannunsa yadauki wata irin rawa, haka ya daure yayi bismillah cikin ransa, yaci gaba da neman hanya Zafi da radadin da wajan yake mata ne yasa tasaki kuka tafara tureshi, amma inaaa! Gaba daya Ammar yasakar mata nauyin sa, ko tunanin saurararta beyiba awannan halin, yaci gaba da abinda yake, Jiyayi wuyansa kamar ansaka masa igiya an shaqeshi, lokaci daya yadena abinda yake, yasaka hannunsa a wuyansa yariqe, yaga d'akin nasu Yana wata irin juyawa, baisan lokacin da yafad'o qasan gadonba,har lokacin kuma hannunsa Yana kan wuyansa, qafafunsa ne suka fara rawa kamar mutumin da aka dannewa kai da fillo anaso yamutu, jiyayi wata irin murya marar Dadin ji tacika d'akin tana bashi umarni "Kasake ta!!!, Kasaketa zamu kasheka fa" Amina ta duro daga kan gadon tana kiransa "Yaya Ammar, menene?, Wuyanka ne yake ciwo?" Kwata kwata Ammar bayajin abinda Amina take fada masa, wannan babbar muryar datake bashi umarni ita yakeji, daqyar ya'iya yin magana cikin qarfin hali yace "bazan saketaba" Amina tasake kallonsa tana masa magana amma taga alama kamar ma baya jinta, shikuma Ammar sake shaqe masa wuya akai har yakasa numfashi idanunsa suka futo waje sosai Yana zare ido, baisan lokacin daya fara sakin Amina ba, kawai cewa yake "Nasaketa, nasaketa, wallahi nasaketa, lokaci daya kuma ansakeshi kamar ma babu wata murya data cika d'akin, numfashi yake maidawa sosai kamar wanda ya shekara Yana tseren gudu Amina tana jin abinda yafada tafashe da kuka, ''Yaya Ammar mekake fada haka? Kaida waye? " Cikin fitar numfashi na azaba ya kalleta cikin duhun d'akin yace "Amina, kiyi hakuri, babu yanda na'iya" Kuka tafashe dashi sosai takasa cemasa komai, Ahankali ya miqa hannunsa yajanyota jikinsa yayi mata wani irin ruqo, itade tajishi yayi mata wani riqo datayi tunanin ballata zaiyi, gaba d'aya kuma Sai jikinsa yasaki yafara Tari Daqyar tatureshi daga jikinta tadauki ruwa a cikin jug din roba ta bashi yasha, Ahankali tace "sannu Yaya" Kallanta yayi da Idonsa da sukai jajir ya d'aga mata kai, daga nan yajata jikinsa suka kwanta bacci anan qasan d'akin, cikin ransa kuwa tunani yake haqiqa Amina ba'ita kadai bace, akwai mutanan boye atare da'ita, dole dasafe ya fadawa su Inna aje anemo mata magani awajan Malam liman kokuma wasu malaman Dahaka sukai bacci, har Gari ya waye basu tashiba, saboda basu kwanta da wuri ba,Gari ya waye, jama'ah kowa yanata sabgoginsa Su Inna ma babu wanda ya qwanqwasa musu daki kawai de ta ajiye musu kwanon abincin su akofar Dakin, ta cigaba da harkokinta atsakar gidan. Dawani irin zazzabi Asim ya tashi yau, idanunsa har rufewa suke, ga ciwon kai da yake damunsa har yanaji kamar kansa zai rabe gida biyu, amma ahakan yayi sallama dasu Inna da baba Akan zai tafi gida, kuma Insha Allah zai dawo wajan su nanda 'yan Kwanaki shida Mamynsa Cikin baccinta tajiyo muryar Inna da baba sunayin sallama dashi, Ahankali tabude idanunta, tafiya zaiyi kenan? Basu yi sallama dashi ba kuma, kallonta takai wajan Yaya Ammar taga Yana bacci, gaba daya ta manta da batun laptop dinsa, saide aranta taji tanaso tasake kallansa koda sau daya ne kafin yatafi, cikin sauri ta daga labulen window taganshi shida baba, suna shirin fita, Ahankali tasaki labulen tadawo dakin tafara bubbuga gadon domin tashin Ammar "Yaya Ammar katashi, mun makara ko Salla bamuyi ba" Tana jiran taga ya tashi taji Shiru, da sauri ta kalleshi takirashi dad'an qarfi "Yaya Ammar!!!" Nanma taji Shiru, gabanta ne yabada wani irin dam! Lokaci daya jikinta yadauki rawa, hannunta Sai karkarwa yake ahaka ta Dora hannun Akan hancinsa taji kwata kwata baya numfashi, hannunta tadora aka ( ) tasaki wani irin qara, nan take tazube atsakar d'akin sumammiya Inna ce ta shigo d'akin da gudu, dakuma baba daya raka Asim bakin titi yadawo, ganin Amina sukai a kwance aqasa da alama ta suma, Ammar suka fara dubawa, jikin Inna har rawa yake tafara tattaba ko'ina na jikinsa, gaba daya duk ta rude Tama rasa gane yanada rai ko bashi darai, baba ne da yake cikin nutsuwa ya daga hannun Ammar yaga hannun ya silale yafad'i, daga nan jikin baba yayi sanyi, yasan shikkenan Ammar babu, rai yayi halinsa (😭😭) ahankali yazame yazauna da6as aqasan d'akin yafara hawaye kamar ba Malam buba ba Inna tana ganin haka ta futo daga d'akin tana ihu tana kururuwa, baba Yana "larai, Larai" amma Inaaaa! Inna ko kallonsa batayi ba, hannu ta Dora aka ( ) taci gaba da ihu "innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, nashiga ukuna ni larai, Ammar yatafi yabarni, Ammar shi kadai nake gani naji dadi yanzu babu, babu Ammar yatafi babu dawowa" Haka Inna tadinga ihun kuka wanda ya janyo hankalin maqota suka garzaya gidan maigari suka sanar dashi ai Ammar yamutu, nan da nan kuwa maigari yataho gidan shida tawagarsa (😳 ) Baba ne yataso yabiyo Inna tsakar gida anan yaga mutane sun taru Sai leqensu suke takatanga , ya tsugunna agabanta tare da dafa kafadarta "larai ki tashi Dan Allah kidena wannan ihun, Ammar Addu'ar ki yake buqata a yanzu, babu kyau a dinga yiwa mamaci kuka larai" Bige hannunsa dake kan kafadarta tayi, tace "Nika rabu dani Malam, wannan abun ya isheni, haqurina yaqare Malam, d'annawa guda daya tilo yamutu yabarni yazaka hanani kuka" "larai hakuri zamuyi, duba kiga yanda mutane suka taru suke Kallan ki, kiyi hakuri mana" "wanne irin hakuri kake magana Malam, Wai kai wacce irin zuciya ce dakai? Wallahi yau kam hakuri na yaqare" Tana fadar haka tamiqe tadauki bahon wanka ta cikata da ruwa tanufi cikin d'akin dasu Amina suke, tana zuwa batayi wata-wataba ta sheqawa Amina wannan ruwan (πŸ˜–) cikin masifa tace "tashi shegiya!, annamimiya, munafukar Allah" Jin saukar ruwa ajikin ta shi yayi Sanadin farkawarta cikin razana, tana goge fuskarta data Gama jiqewa Inna tayi mata wani irin kallon tsana, tace "kin kashemin dana Amina, burinki yacika, ashe dama maganar da mutane suke gaskiya ne, yau na gaskata maganar su, wallahi tallahi bazan taba yafe mikiba Amina, Allah Sai yayi mana sakayya" Baba ne yace "larai kiyi hakuri mubi komai a sannu Dan Allah" Inna Bata saurari baba ba, takamo hannun Amina data qame waje daya, tayi tsakar gida da'ita, Amina ta daga kai tana kallon mutane yanda sukai dandazo Akan katanga dakuma kofar gidansu, Inna Bata damu da mutanan da suke kallanta ba ta hankad'ata waje, sannan Takoma ciki tadauko mata bakkon kayan ta tabiyota da'ita Babane yafuto da sauri yariqe jakar, Inna tana Jan jaka baba yanaja, haka suka futo kofar gida, adede lokacin maigari yaqaraso shida tawagarsa Cikin tsananin fishi yace "Malam Buba dakai da larai, da wannan annobar ku tattara yanaku yanaku kubar min garina, Dan Naga alama d'aya bayan d'aya nema take saitaga bayan yan Garin nan" "Annobah" Kalmar ta daki dodon kunnan Asim daya dawo domin tambayarsu ko sunga laptop dinsa a lokacin da suka tsinceshi a ruwa, yamaida kallansa ga Amina datake zaune aqasa inda Inna ta wullar da'ita, kayan jikin ta duk ajiqe harkana iya hango shacin brezia d'in jikinta, da sauri yadauke Idonsa daga wajan, yamaida kallansa ga mutane yanda suka taru akofar gidan danqam kamar Ana kallon wani babban Abu Inna da baba da basu lura da dawowar Asim ba, suka fara Bawa maigari hakuri, Inna tasake cewa "kayi hakuri Yalla6ai, karufa mana asiri ayiwa d'ana sutura, karka rabamu da mahaifarmu" Maigari yadubi fadawan dayazo dasu yace "kushiga cikin gidannan kufuto musu da kayansu, shikuma Yaron ayi masa sutura, Ana gamawa azo ahada dasu da kayansu a kore su subarmin gidana" Baba yace "innalillahi wa Inna ilaihirraji'un,wannan masifa dame tayi kama?" Inna kuwa tana jin abinda maigari yace tajefawa Amina jakar kayanta, cikin kuka tace "Allah ya'isa tsakanin mu dake Amina, kinji dad'i ankoremu daga mahaifarmu, tokema kije babumu babu ke" Al'amarin ya d'aurewa Asim kai, ba yarsu bace ne? Meyasa suke jifanta da wannan kalaman? Yajuya ya kalli Amina yaga ta sunkuyar da kanta tana kuka kamar ranta zai fita, sosai ta bashi tausayi,yatsani kukan mace arayuwarsa,ko babu komai yarinyar nan ta dalilinta yazo wannan qauyen, awannan yanayin kam bazai yi Shiru yanaji Yana gani ayi mata irin wannan tozarcin ba, Ahankali ya kutsa kansa ta cikin mutanan dasukaiwa wajan dandazo yaqaraso wajansu Inna, nanfa kallo yakoma Sama, domin kuwa gaba d'aya 'yan wajan kallansa sukeyi, tambayar kansu suke shikuma wannan meya kawo shi nan? Isyaku yayan lubabatu kuwa Yana ganin Asim yagane shine wanda akasa kudi Ana nemansa,saida yaqara kallonsa sosai har wani karkatar dakai yake Yana yiwa Asim kallon qurulla domin ya tantance shid'inne dayaga photonsa atv ta gidansu koba shi bane? (πŸ€”πŸ€£) cikin sauri yabar wajan ya garzaya folice station domin sanar da 'yan sanda,bazaiyi sakaci wannan kudi ya wuceshi ba (🀣🀣) Cikin damuwa Asim yadubi baba yace "haba Baba, wannan yarinyar ba 'yarku bace? Meyasa kuke jifanta da wannan kalaman?" Baba yayi Shiru Yana kuka yakasa Bawa Asim amsa, inna ma cikin kuka tace "Amina ba 'yarmu bace, bamu San taba, bamu San tushenta ba, bamusan sunan taba, muma tsintarta mukai muka riqeta tsakani da Allah kamar yarmu ta cikin mu, munyi mata Rana mun rufa mata asiri ashe Bahaka bane a ranta, Gatanan azaune aurenta biyar duk mazajen data aura mutuwa suke, jiya jiya muka rufa mata asiri muka aura mata d'anmu, Toshima yau mun wayi Gari takashe shi, takashe Ammar, Ammar shine d'anmu na cikinmu, Amina ba 'yarmu bace " ( ) Gaban Amina yayi wata irin fad'uwa, cikin sauri tad'ago kanta ta kalli Inna, Inna ta kalli qwayar idonta tace"qwarai kuwa abinda kikaji shine gaskiya, kije can kinemi Iyayen ki, babu ni babu ke Amina tunda kikamin Sanadin rabani da d'ana " Asim kuwa qamewa yayi atsaye, aure biyar? gakuma Ammar Aure shidafa kenan, wannan qanqanuwar yarinyar? Tayaya? Wannan wanne irin tashin hankali take gani?to suwaye Iyayen ta? Begama tunanin saba yaga Amina ta tashi tazube gwiwoyinta qasa, tahade hannayenta biyu waje daya (πŸ™πŸ») cikin matsanancin kuka tace "Inna..... baba,Wallahi bani nakasheshi ba, Bana kashe mutane Inna, Yaya yariga yasakeni Inna, Dan girman Allah Karku rabu dani, Inna wanasani aduniyar nan bayan ku? Karku rabu dani Inna, idan kuka barni ina zanje? Nayarda kuyimin kowanne irin hukunci amma Karku rabu dani Inna, Ni kune iyayena, kuna sani tunda na tashi, bansan kowa ba bayanku, kuyi hakuri Dan girman Allah kuji qaina Inna....kada laifin danayi muku yasa kuce niba 'yarku bace Inna..." taqarasa maganar cikin sheshshekar kuka Inna ko kallonta batayi ba, baba kuwa yama Kasa d'ago kansa ya kalleta, larai ta riga tatona musu asiri, ta tonawa yarinya asiri a cikin wannan d'unbin jama'ah, da wanne ido zai kalli Amina? Inna tajuya cikin kayansu da maigari yasa aka futo musu dashi ta dauko wata baqar Leda tasake jefawa Amina ledar tace "ga tsiyar kinan,dasu muka tsinceki,Allah yahadamu a darussalam" Cikin bacin rai Asim ya qarasa wajanta tare da miqa mata fari kuma lallausan tafin hannunsa, fuska a d'aure yace "ke tashi mutafi" Cikin sauri tad'ago jajayen idanunta da suke cike da hawaye ta kalleshi Sorry fan's, kunji nace sunan labari INSAAF amma kuma inata maganar Amina Amina,πŸ€— to Masu wayo dakuma fahimta ne kadai zasu gane wacece INSAAF a cikin wannan page dinπŸ˜‰ ✍🏻 Amnah El~yaqoub [2/5, 10:53 PM] El~Yaqoub: INSAAF Writing by:Amnah El yaqoub 7&8 Like my page on Facebook πŸ‘‡πŸ» https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 Idonsa cikin nata ya d'aga mata kai alamun da gaske yake Hawaye masu zafi suka sake zubo mata, yayinda jama'ar wajan suka zama 'yan kallo suna ganin wani sabon salon iskanci, namiji Yana meqawa mace hannu a cikin bainar jama'ah (🀣) Kallansa take hawayen idonta sunqi tsayawa, waye shi? Bata sanshi bafa, tayaya zata bishi tabarsu Inna? idan tabishi tasan irin tashin hankalin da zata haddasa masa agidansu? Cikin ranta take wannan tambayoyin, ahankli ta girgiza masa kanta alamun bazatabishi ba Dago Idonsa yayi ahankali, asace yake kallon d'unbin mutanan da suke kallonsu amma yarinyar nan ta kunya tashi agabansu, saboda me zata zauna da mutanan da sukai mata irin wannan cin mutuncin,? Baiyi wata wataba yasa hannunsa ya fuzgota tare da bakkon kayan nata harma da ledar da Inna ta wullo mata Mutanan wajan kuwa suna ganin haka suka fara salati (🀣🀣) Hannunta takeson qwacewa amma yahana ta Damar hakan, janta yayi suka fara tafiya, Amma Amina sai kuka take sosai kamar ranta zai fita, juyowa tayi tana kallonsu Inna, cikin matsanancin kuka tace "Inna Karki barni, baba..." Haka Inna ta dauke kanta, shikuma baba har zuwa wannan lokacin ya Kasa kallon Amina Akan idon jama'ar wannan Gari, Asim yatafi da Amina babu wanda yahana shi, suna ganin kamar ma yatemakesu ne tunda yarabasu da masifa Tun suna tafiya tana turjewa har tayi hakuri taci gaba da binsa, cikin bacin rai da tsananin damuwa ta fizge hannunta daga riqon dayayi mata Cak! ya tsaya yadaina tafiya, juyowa yayi ya kalleta fuskar sa adaure, inbanda rashin hankali da kuma yarinta me zaisa wannan yarinyar tazabi zama a cikin mutanan da basa kaunar ta? Har sai yayi mata dole Akan rabuwa dasu? Afuto dakai waje ayima wannan tozarcin amma ahakan kake kuka kana kiransu? Haushi ya kamashi, jakar bakkon kayanta da d'aya ledar yazubar agabanta sannan yajuya yayi tafiyar sa (😠) Wani irin zazzafan zazzabi yakeji, ga kansa da yake ciwo, shi mema yasa yadawo ne? da yanzu ba zaiga wannan tashin hankali ba, wani bangare da zuciyarsa yace masa laptop dinka, itace dalilin dawowarka, yatuna yanda su Inna suka iya rufe Idonsu suka ciwa wannan yarinyar mutunci tayaya zai Iya tambyarsu wata laptop bayan radadin dasukeji na rashin dansu? Yasan cewa laptop kam yariga yarasata, yarasa komai, bai kuma san Yaya zai fuskanci Ishraqa da wannan maganar ba (Tofa! πŸ€”) Akan bakkon kayan nata tazube tana gunjin kuka, yanzu su Inna dama ba iyayenta bane? to suwaye iyayenta? Menene sunan ta? Babu wanda yasan amsar duka tambyoyinta Sai Allah Dago kanta tayi, can ta hangeshi Yana tafiya har yayi Nisa, awannan halin batada wani zabi bayan tabishi, idan tabarshi yatafi ma ina zata? Ina ta nufa? Wata ke dashi a duniya bayan Allah? Dasauri ta dauki kayanta tadora aka tabishi (🀣) Yanajin tafiyarta a bayansa amma ko kallon inda take Baiyi ba, suna tafiya babu wanda yake magana Sai kukanta da yake barazanar rabe masa kansa gida biyu wanda yake masa matsanancin ciwo, ita kuwa kuka take kamar hauka, barinma idan tatuna maganar su Inna, ita yar tsuntuwa ce, haka suka dinga tafiya har sukai nisa sosai daga qauyen suna shirin shiga wani qauyen nagaba Yagaji sosai da wannan tafiya, shikansa baima San ina sukeyi ba, ga zazzabi daya rufeshi, sanyi yakeji a jikinsa kamar Ana zuba masa ruwan qanqara, ya kamata subar tafiyar haka su qarasa titi su nemi Mota Har zuwa wannan lokacin Amina kuka take, har mamakin kukanta yake kwata kwata Bata gajiya, adede wata bishiya ya tsaya batare da tunanin komai ba yazube awajan tare da riqe kansa da yake masa mugun ciwo Tana ganin haka kukanta ya qaru, bakkonta dake kanta tasauke qasa, sannan ta tsugunna akusa dashi har jikinta Yana gogar nasa, cikin muryar kuka tace "meyake damunka?, kaima mutuwa zakayi ka barni ko?, nikam nashiga ukuna..." ta qarasa maganar cikin matsanancin kuka tana Dora hannunta a kanta ( ) Jinta akusa dashi,dakuma sanyin dayakeji yasa yafuzgota jikinsa kozaiji dama dama, al'amarin yabawa Amina tsoro, harta zaro manyan idonta tana kallansa ganin yanda ya rungume ta hartanajin yanda Boobs dinta suka kwanta Akan faffad'an qirjinsa, shi kansa ya karbi saqon yanda ya kamata dukda Yana cikin yanayin zazzabi (πŸ™ˆ) Rawar sanyi da taga yanayi anan tagane nufinsa, Ahankali tasa hannu tacire babban dankwalin atamfar da yake kanta, iskar bishiyar da suke zaune takad'a dogon gashinta zuwa fuskar Asim, idanunsa a lumshe suke, amma Sarai yaji saukar gashin nata, hannunta tasa tajanye gashinta sannan tarufe masa jikinsa da d'ankwalin *** ***** *** A bangaren isyaku kuwa, Yana zuwa police station jikinsa har rawa yake yace Yana so ahadashi da d.p.o kofur Shamsu yakalleshi "lafiya kake neman sa? Idan qara kakawo muzaka yiwa bayani" "Yallabai ba qara nakawo ba, abinda nakawo ai ya girmi qara Yallabai," Yayi qasa-qasa da muryarsa yace "kuma zaku samu naku kason, zanbaku wani abu daga ciki" Sunajin furucin isyaku suka fara washe baki, nan da nan suka kaishi har office din d.p.o, isyaku ya kalleshi da kyau yace "Yallabai ina mutumin nan da kwamishinan 'yan sanda yabada cigiyar sa? " D.p.o ya kalleshi da kyau yace "eh inajin ka meyafaru" Saida ya kalli gefe da gefensa kamar Yana tsoro Kar wani yaji shi (🀣) sannan yace "to yanzu haka Yana nan a cikin qauyenmu, inaso kabani yansanda Mota guda, muje ataho dashi" ( ) D.p.o ya kalli isyaku da kyau yace "ka tabbata abinda kake fadamin gaskiya ne?" Isyaku yasa ka hannunsa dede fuskarsa yanuna idanunsa duka biyun yace "ganin Idona naganshi Yallabai" (🀣) D.p.o yasake kallansa da kyau yanaso ya Gano gaskiyar abinda isyaku yake fada masa,Anya kuwa gaskiya ne? Tayaya mutum babba kamar Asim zai Iya zama a cikin wannan qauyen? Anya ba qarya Yaron nan yake musu ba? cikin zaquwa isyaku yace "haba Yallabai, me muke jirane? Kabasu umarni kawai mu tafi, ha'ah" Yaqarasa maganar tasa cikin gundura (πŸ˜ƒ) D.p.o yayi Ajiyar zuciya yace "tunda hakane, ainima banga ta zamaba, dani za'aje, tashi mutafi" (😳) Murna ta kama isyaku, nan da nan kuwa aka cika Mota da yansanda kamar yanda isyaku ya buqata, saide suna zuwa kofar gidan Malam Buba sukaga babu Asim babu dalilinsa, ( ) Sai sauran mutane dasuka Gama watsewa daga jana'izar Yaya Ammar, dakuma Inna da baba dasuka kwashi kayansu a amalanke da alama Garin zasu Bari Idanun isyaku yayi wiqi-wiqi ya raina fata (πŸ˜‚πŸ˜‚) D.p.o ya kalleshi cikin bacin rai yace "ina yake?" Isyaku yayi Shiru kamar andoka masa sanda yakasa d'ago kansa yakalli d.p.o bare su hada ido dashi (🀣🀣) D.p.o Yana ganin alamar qarya isyaku ya shimfida musu nan take ya kalli yaransa yace "ku saukeshi a motar nan kuyi masa dukan kawo wuqa" Isyaku yanajin haka yadora hannunsa aka ( ) yace "nashiga uku ni isyaku namutu na lalace, Yallabai shi dukan dama harda na kawo wuqa?" D.p.o yace "zaka ganshi yanzu-yanzu" yaqare maganar Yana Kallan yaransa Nan da nan kuwa suka gane ma'anar kallon nasa, suka jefo isyaku waje daga cikin motar suka hau dukansa kamar Allah ya aikosu, Sai ribd'arsa suke Yana ihun neman agaji (πŸ˜†) Basubar isyaku ba saida suka nuna masa jiki, nan take zazzabin wahala ya rufeshi *** ***** *** Tun dazu yake hangosu daga gonar sa, yaga alama kamar matafiya ne, gashi har yamma tayi yanaso Shima yatafi gida, dama gewaya yazoyi gonar tasa "bayin Allah lafiya kuwa kuke zaune awajan nan tun dazu?" Ahankali ta dago kanta ta kalleshi, babban mutum ne daya manyanta sosai, kansa Yana dauke da rawani irinna malamai, cikin sanyin murya tace "tafiya muke, bashida lafiya ne" Mutumin ya kalleta yaga idonta duk hawaye sun bushe, ya kalli Asim daya riqe Amina a jikinsa yaga bacci yake, yace "Ashsha, Aida kin nemi temako yarinya, ku taso mu qarasa gidana yasha magani,tasoshi" Duniyar tunani tafada, to ita dabatasan sunan saba tayaya zata kirashi harya tashi? Daga wa mutumin kai tayi alamun amsawa, Ahankali tafara zare jikinta daga nasa, cikin baccinsa yaji zatabar jikinsa yasaka hannu ya sake rungume ta Mutumin ya kallesu yayi murmushi da alama de ma'aurata ne, ya kalleta yace "tashi mijin naki mana" (miji) kalmar tadaki dodon kunnanta, Allah yakiyaye tasake yin waani auren a yanzu, idan tayi aure ma ai batayi wa kanta adalci ba, tunda tasan haqqin wanda ta aura zai rataya awuyanta ne idan ya mutu Hannunta takai kan muscles πŸ’ͺ🏻dinsa tafara tashinsa, Ahankali ya dago kansa tare da Bude lumsassun idanunsa da sukai ja saboda tsabar zazzabi ya kalleta, tace "Katashi mutafi" Mutumin dake tsaye ma yace "kuyi hakuri na tasheku, kuzo muje gidana ku huta gashinan babu Nisa" Ahankali yamiqe tsaye Yana runtse Idonsa, yadora hannunsa Akan goshinsa daya Sara masa kasancewar ya tashi tsaye,jiyayi kansa Yana juyawa yatafi luuu zai Fadi, cikin sauri Amina tatareshi yazube ajikinta, kansa ya sauka adede qirjinta, gabanta yayi mugun faduwa,meta aikata haka? Wannan mutumin gaba daya yagama jin komai na jikinta yau, Sai bayan ta riqeshi ne take tambayar kanta mema yakaita tareshi batabarshi yafadi ba? "subhanallah..." cewar wannan mutumin, yaci gaba da fadin "kamashi muje, sannu bawan Allah" Haka Amina tariqeshi ajikinta, Shima mutumin yariqe masa hannu suka tafi, basu yi wata tafiya mai nisaba suka qara so kofar gidansa da yake cikeda almajirai sunata karatun Allo Kai tsaye gidansa yakaisu, matarsa tayi musu tarba mai kyau, takaisu wani daki atsakar gidan dake gyare tsaf, harda shimfida, mutumin yadubi Asim yace "kwanta anan Yaro" ya sake Kallan matarsa yace "kawo musu abinci da ruwa, zanje nasiyo masa maganin zazzabi" Matar ta Amsa masa sannan tafuta daga d'akin, Amina ta dubeshi tace "ga katifa nan ka kwanta" Daga mata kai yayi alamun amsawa, sannan ya fara shirin kwanciya Akan katifar, tsugunnawa tayi asetin kansa tasaka hannu tana gyara masa fillon daya Dora kansa akai Yasaba duk lokacin dabayajin dadi Mamy ce take zama atare dashi, musanman idan Yana ciwon kai ta dinga yimasa massage akansa kenan harsai yadanji dama dama, Amina kuwa tana gyara masa fillon tafara kokarin miqewa ahankali yasaka hannunsa da yayi zafi sosai yariqeta, bin hannun nasa tayi da kallo fari tas dashi, hannunta tafara zarewa ya sake damqe hannun nata cikin nasa, babu yanda ta'iya haka tadawo wajan tazauna tayi Shiru tana kallon ikon Allah, shikuwa bargon dake kan shimfidar yaja yarufa dashi har kansa Sai gab da magrib maigidan yadawo, har lokacin tana nan zaune a d'akin tayi tagumi,saide ta qwace hannunta daga cikin nasa dataga yayi bacci, abincin da matar ta kawo musu ma cokali daya tayi tarufe abincin, maganin ya ajiye yace "tasheshi yaci abincin yasha magani" Fillon nasa tafara bugawa, daqyar ya tashi, maigidan yabashi abincin, daqyar yaci kadan, Ahankali yace "ya'isa" kallansa tayi cikin sauri, tun taho warsu daga qauyensus Sai yanzu taji yayi magana, ga fuskarsa a daure, mamaki ya kamata tsawon wannan lokacin suna tafiya Amma beyi mata magana ba Maganin yabashi,Asim ya kalli maganin ya yatsina fuska, sannan yace "banson magani" murmushi mutumin yayi, yace "haba dana Sai kace ba namiji ba kace bakason magani? Kokuma saboda baku sanni bane shiyasa? To sunana malam Ibrahim mai Allo, ni limamin Garin nan ne, ga mata ta can, nakawo ku gidanane kuhuta idan kaji sauqi bayan kwana biyu saiku tafi, bazan cutar daku ba Yaro" Murmushin qarfin hali Asim yayi jin wannan dogon Bayani da yayi musu, Ahankali kamar me koyon magana yace "A a... ni.. dama can banso" Malamin yayi murmushi ya ballo maganin yabawa Amina yace "toke yata karbi kibashi, wata qila ke kikasan Yanda kike bashi" (🀣) Cikin inda inda tace "a a Nima fa bansan..." Ganin zata tona musu asiri yasa Asim cikin sauri yabawa liman hannu, liman yabashi maganin, yaqyar ya'iya hadiye maganin har wani girgiza kansa yake kamar me iskokai (πŸ˜ƒ) Sannan yatashi yafuto domin yin alwala, Shima liman yafuto Yana tambayar sa menene sunan sune, basu fada masa ba, itade Amina bataji amsar daya bashi ba Wajan karfe Tara na dare ta futo daga d'akin tazauna a tsakar gidan, liman yashigo gidan ya ganta azaune yace"yata meyasa baki kwanta ba har yanzu? " Tace"yana cikine, shine na futo" Mamaki ya kama liman, yace "a a, ba mijin ki bane dama?" Tace "Eh baba" Liman yace "innalillahi wa Inna ilaihirraji'un" yayi Shiru kamar Yana nazarin wani abu, yadago ya kalleta yace "dazu yafadamin sunan ki Amina, 'yata Amina meyasa kuka Bari kuna cudanya da juna bayan kunsan bakuda aure?" Amina tayi Shiru takasa bashi amsa, Shima Shiru yayi Yana tuno yanda yasamesu a bishiya rungume da juna, dakuma inda zai Fadi tatareshi yafada jikinta" Kansa ya jinjina yace "taso kishiga d'akin talatu ku kwana tare" Babu musu tashige d'akin matarsa, shikuma yayi d'akin da Asim yake ciki Washe garima haka matar gidan tayi musu abubuwan daya dace, jikin Asim kuma da sauqi sosai ba kamar jiya ba,da yamma yasha magani ya kwanta daga Naan yayi bacci, d'akin ta leqa taga Yana bacci, tana juyowa zata koma wajan matar liman saiga liman dinma yashigo gidan, ya kalleta yace " 'yata zo zamuyi magana" Binsa tayi abaya, suka shiga d'akin matarsa, ya kalleta sannan yafara mata magana cikin fahimta yace, "Amina" Dago kanta tayi ta kalleshi, tunda suka hadu da mutumin yake mata kwarjini, tana ganinsa kamar mahaifinta, tace "Na'am baba" Yace "Amina a'ina kuka hadu da wannan bawan Allah?" "a garinmu, yajima acan" cewar Amina Liman yace "to ko made a'ina kuka hadu na temaka muku Amina, nafarko jiya yafadamin Lagos zaku tafi, daga nan bai fadamin komai naku ba, Nima ban tambayeshi ba, Amina tafiyar ku tare ni inaganin kamar akwai hatsari a cikinta, tafiya zakuyi doguwa, kuma a hanyar nan bakusan abinda zai faru atsakanin Kuba, ko babu komai akwai shaid'an, yanayin dana ganku jiya ni kaina nayi tunanin mata da miji ne, saboda haka na yanke hukunci dazu dazun nan natara almajirai na dakuma maqotana nadaura miki aure kedashi " (😳) Dam! Dam! Gaban Amina yahau luguden faduwa, meyasa hakane? Sai yaushe ne masifa zata Dena bibiyar rayuwarta? Batasan lokacin data fashe da kuka ba, cikinKuka tace "innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, nashiga uku na, Dan girman Allah karaba auren nan, wallahi Allah banaso, ni banason shi, qaddarar dana Bari abaya ba ta isheni, bazan sake auren kowa ba" "Amina banida ikon Raba muku aure, wannan Yana hannun mijin ki, bansan haka abin yake ba, da banyi gaggawar daura muku aure ba, amma inaso kisani, ni Allah baibani haihuwa ba, yanda kike kirana da suna baba Amina sainakeji kamar yata ce take kirana, ina jiye muku tsoron abinda zai Iya faruwa atsakanin kune shiyasa nayi muku auren, Amina tunda muka hadu daku naji kamar da yan'uwana nahadu, Dan Allah Karki watsamin qasa a'ido, shikuma dan'uwan tafiyar taki zan zauna dashi Gobe da safe in sanar dashi abinda nayi muku " Gefen dankwalinta taja tana share hawaye dashi, kuka take sosai harda Jan zuciya, liman ya kalleta yace" kiyi hakuri Amina " Ahankali ta daga kanta tace"to baba" Liman yace"Allah yayi miki albarka, wannan sadakinki ne danayi miki shi, nera dubu goma " Ya ajiye mata kudin agefenta sannan yafita daga d'akin, matarsa ce ta shigo d'akin tajanyota jikinta tana Bata hakuri, har dare yayi Amina Bata Dena zubar hawaye ba, idonta har zafi yake saboda kuka, kuma adaren matar liman ta rakata d'akin da Asim yake sannan tayi mata sallama, shikam baisan ma tashigo dakinba Yana bacci, ita kuwa zaune ta kwana Sai gab da sallar Asuba taji bacci me dadi yafara daukar ta, Akan kunnanta wasu masallatan suka fara Kiran sallar farko, ihun dataji ne yasa tazabura cikin sauri tamiqe tsaye, kamar muryar matar liman takeji tana kuka, cikin sauri tabude kofar d'akin tafuto, qaran Bude kofar da tayi ne yafarkar da Asim daga bacci, Shima yanajin wannan kukan ya futo Matar liman ta nufesu da gudu tana kuka kamar mahaukaciya, "Amina ku taimaka min, babu Malam yamutu" ( 😳) Amina tace "innalillahi wa Inna ilaihirraji'un" tafashe da kuka itama, yanzu liman yamutu?jiya jiya yazaunar da'ita yayi mata magana Akan aure amma yau harya mutu? Anya kuwa batada nasaba da mutuwarsa? Gabanta ya tsananta faduwa, idan kuwa hakan ya tabbata haqiqa data shiga ukunta, tazama masifa, tazama annoba kamar yanda su Inna suka fada, Asim kuwa qamewa yayi atsaye, mutuwar tatabashi sosai, Amina kuwa zama tayi a gaban gawar liman tana kuka, ga kukan jiya gana yau, hakan saiya haddasa mata ciwon kai, lokaci daya taji duniyar tafita daga ranta, fatanta daya shi ne Allah yasa itama ta mutu tahuta da wannan masifa, har a kayiwa liman sutura aka kaishi gidansa na gaskiya Amina Bata dawo normal ba Tundaga mutuwar liman saita dawo Shiru Shiru, saitayi awanni batare da tayi magana ba, Bata jin dadin komai, Bata tunanin tanada Rabon hutawa awannan duniyar, tunani yazama abokin hirarta, Bata damu da magana ba, babbar damuwar ta ma shine wannan auren da liman ya daura mata, batasan Yaya makomar sa zata kasance, tayaya zata tunkareshi da wannan maganar? Idan tafada masa ma qarshanta ya Musata, koba wannan Bama Bata fatan ace wani ya sake mutuwa Ata dalilin ta Haka gidan yacika da 'yan'uwa, kuma tunda akai mutuwar Bata sake sakashi a'idonta ba, har akai kwana uku, a kayiwa liman sadakar uku data bakwai, yan'uwan matar suka shirya tafiya da' ita garinsu, gida yafara watsewa, Ana cikin haka kuwa Asim yashigo gidan bayan sun gaisa da 'yan tsirarun mutanan ya kalleta batare daya Kira sunan taba yace "kishirya mu tafi" Itama batace masa komai ba haka tashige d'akin da'aka saukesu tahada kayanta waje daya tafuto dashi, lokacin da sukai sallama da matar liman saida kowa yazubar musu da qwalla,saboda kowa yayi tunanin yan'uwa ne, Amina tana kuka matar liman tana kuka sukai sallama suka tafi A hanya ma Yana gaba tana binsa abaya har suka qarasa bakin titi, shine da kansa yafara tare musu Mota zuwa kano, amma duk motar daya tare idan yayi musu Bayanin bashida kudi saisuja motar su suqara gaba, sun Bata lokaci awajan sannan wani bawan Allah yadaukesu suka tafi, suna cikin tafiyama babu wanda yake yiwa dan'uwansa magana (🀣) Amina kam idonta ta lumshe ma tana tunanin wannan baqar rayuwa Tata, abubuwa sun taru sunyi mata yawa, babu iyaye, babu asali, batasan ainashin takamaimai sunanta ba, ga wannan aure da liman ya daura musu, ta wacce hanya zata fada masa andaura musu aure? Tayaya zata fada masa?Sunyi Nisa cikin tafiya taji ya tambayi Aron wayar direban dayake jansu, itade Bata Bude idonta ba Amma duk abinda yake yi tanaji, number mahafiyarsa yasa ka sannan yakira, saida wayar tayi ringing harta katse ba'a dauka ba, a lokacin kuwa mamy tana zaune da niyya taqi daukar wayar, tasan cewa bazai wuce masu yi mata jaje ba, a kullum haka take amsa kiransu harta fara gajiya,sake Kira yayi a Karo na biyu, Shima saida takusa katsewa sannan ta dauka tare da cikakkiyar sallama abakinta, Shiru yayi yakasa magana duk da kasancewar sa namiji qwalla yaji tana shirin zubo masa, mamy tasake cewa "Salamu alaikum" Ahankali yace "Mamy" lokaci daya mamy ta tashi tsaye, tace "Asim,Alhamdulillahi, Allah abin godia, dama nasan baka mutu ba, inaji a jikina zaka dawo gareni Asim" Murmushin sa mai tsada yasaki yace "ban mutuba mamy, ina nan, mamy Amjad nasan sun kashe shi, kiyi hakuri mamy nakasa tseratar miki da danki" ya qarasa maganar Yana goge qwallar Idonsa Tuni hawaye yagama wankewa mamy fuska, cikin kuka tace "Amjad Yana nan, yanzu hakama Yana bacci adakinsa, kana ina?" "mamy kidena kuka mana, bagashi nadawo ba" Hawayen idonta ta share cikin kuka tace "Allah yakaremin kai dana, Allah yarabaka da sharrin maqiya, kafadamin kana ina saina taho" Ahankali yace "kano" Duk firar dayake Amina tana jinsa, da alama da mahaifiyarsa yake magana, wani malulun abu ya tsaya mata awuya, shida yake da maahaifiya har ya kirata, amma ita ba tasan ma ko wacece itaba, batasan me matar tafada masa ba kawai de taji yace "to" daga nan ya kashe wayar yabawa direban, haka taci gaba da tunanin mafita Har sukazo kano, Bata Dena tunanin mafitaba, tasaqa wannan ta kunce wannan Kai tsaye ya cewa me motar yakaisu Airport, suna zuwa kuwa yayi masa godia, sannan yace yabashi account number dinsa a takarda, me motar kuwa jikinsa na rawa yarubuta yabashi, Ahankali tabude motar tafuto hannunta dauke da jakar bakko ta kayan ta Kallanta Asim yayi, shida yake shirin tashin ta daga bacci ashe idonta biyu, me motar yaja abarsa yatafi, ahankli ta matsa kusa dashi ta kalleshi muryarta na rawa tace "Dan Allah... Ina... Inaso kakaini gidan Marayu" Kallan qwayar idonta yayi, tunda yake arayuwarsa bayan mamy wannan ne Karon farko da yaji tausayin wata macen (😳) Itama dago kanta tayi ta kalleshi tana jiran taji amsar sa, amma Sai taga kawai zuba mata ido yayi Yana kallonta, cikin sauri tayi qasa da kanta, saboda ba qaramin kwarjini yayi mata ba, gashi kuma babban mutum Dauke Idonsa yayi a kanta batare dayace mata uffan ba, Ajiyar zuciya yasaki shi kadai, tasake kallansa idonta na kawo ruwa tace "Dan Allah..." sai sharrr hawaye suka zubo mata Kallanta yasakeyi da tsananin mamaki, koda yaushe kuka kuka ko gajiya batayi? Kafin yabata amsa yaji anyi masa wata irin runguma daga bayansa Cikin tsananin murna Amjad yace "YAYA ASIM" Sai a lokacin Amina taji sunansa, ASIM ta maimaita sunan abakinta Murmushi yayi yace "Amjad yaushe zaka girma ne?" Mamy ma ta qaraso wajan sa tajashi jikinta ta rungume shi, Shima tsamm ya rungume ta a jikinsa kamar za'a qwace masa ita Ahankli ta zare jikinta tafara tattaba jikinsa, murdadden dantsan hannunsa ta riqe tace "babu de abinda yake damunka ko d'ana?" Yace "babu Mamy, inaso mutafi gida akwai maganganun danake so muyi, ina daddy na da Baby da sauran yan gidan?" "suna nan kalau Asim, basusan mun taho ba, nafiso kawai saide su ganka, amma kafin muje ya kamata kakira Maman INSAAF karkai laifi awajan ta, Dan nasan idan taji labari kadawo baka fada mataba har gida zatazo kuyi abinda kuka saba, kaima kasan sauran " Daga mata kai yayi sannan ya kalli Amina data zama 'yar kallo yace "muje" Sai a lokacin mamy da Amjad suka lura da'ita, Amjad yazuba mata ido Yana kallonta sannan yadubi yayan nasa yace "Wow.... Yaya Asim wacece wannan? She's Preety wallahi Yaya" Wacece maman INSAAF? shin mahaifiyar insaaf tanada alaqa da Asim ne? Yaya makomar auren Asim da Amina? ta wacce hanya zata fada masa wadda zai fahimceta cikin sauqi? Wanda suke tambayar wacece Insaaf ina fatan yanzu kun samu amsar tambayar ku? sharhi πŸ€—πŸ€— Amnah El~Yaqoub [2/6, 11:16 PM] El~Yaqoub: INSAAF Writing By:Amnah El~Yaqoub 9&10 Like my page on Facebook πŸ‘‡πŸ» https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 Dedicated to *FAUZIYA* *S* *MADAKI* My Admin sarkin gyara,πŸ˜‡ ina alfahari dake akoda yaushe πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» Sai a lokacin mamy ta lura da Amina, takai kallonta wajan Asim ko zataji yabawa Amjad amsar tambayar sa, amma saitaji baice dashi komai ba, asalima tafiya yafara yi, Ahankali mamy takai hannunta wajan Amina, takamota tace "taho baiwar Allah" Amina ta dauki bakkon kayanta suka tafi, mamy takama dantsen Asim tariqe gam kamar za'a sake qwace mata shi, Amjad Kuwa hannunsa yariqe Yana tambayarsa "Yaya babu abinda yasameka ko?Allah nagode ma dabasu kashe min kaiba" Mamy ta kallesu tayi murmushi, cikin ranta tana qara jinjina tsananin shaquwar datake tsakanin Asim da Amjad Duk mutanan dasuka ganshi inde dama sun sanshi to saisun tayashi murnar dawowarsa, idon Amina yayi tsilli-tsilli yau gata a Airport, saida suka kammala komai sannan sukahau jirgin dazai tashi zuwa Lagos Acan ma suna sauka motoci guda biyu suka gani na gidan sunzo suna juransu, already mamy tayi magana suzo tun kafin sutaho, rarraba idanunsa yake kozaiga daya daga cikin direbobin dasuka rakasu Yola, amma babu ko mutum daya daga cikin su, hakan yana nufin dama can sun shirya barin gidan kenan shiyasa aka hada baki dasu domin aga bayansa, to waye awaje dayake son ganin bayansa? Waye shi? Yasan cewa a cikin gidansu de babu, suna zaune lafiya cikin qaunar juna dukansu, family ne da suke da hadin kai sosai, to Amma tayaya wani a waje zaizo yahada baki da mutanan gidan domin a dauki ransa? Wannan tunanin da yayi ne yasa shi ciwon kai,lumshe Idonsa yayi tareda dafe kansa, mamy da Amjad har rige rigen tambayar sa suke "lafiya kuwa?" Bece dasu komai ba, kawai de ya d'aga musu kansa alamin babu komai tun kafin su qara so wajan motar duka drivers din suka zo suna masa sannu da zuwa cikin farin ciki ganin yadawo gida, Allah ya baiyana shi Awannan lokacin kam Amina tazama yar kallo, daga ganin yanda mamy take nan-nan dashi tasan cewa ba qaramin so suke masaba Suna zuwa unguwar kuwa tasake zama yar qauye tuburan, domin kuwa saida aka tantancesuma suka shiga, hakan yana nufin unguwar akwai tsaro, Karon farko data fara tunani Akan abinda yasamu Asim, abinda yafara zuwa ranta shine unguwa irin wannan me cike da matakan tsaro tayaya wani daban zai shigo har inda kake ya cutar dakai batare da an kamashi ba?harbi fa ba qaramin abu bane, idan abun yazo da qarar kwana shikkenan mutum yamutu, amma a harbeka ajefaka cikin ruwa wacce irin tsanace wannan? Gaskiya dole ya shiga cikin damuwa,tunanin ta yayi Nisa har suka qara so cikin gidan, gida ne tsararre daya amsa sunansa,bazakace a cikin Nigeria yake ba,ga motoci Kala Kala da suke adane agefe,Bude musu motar a kayi, sannan suka shiga cikin gidan, mutum uku ne a zaune cikin nashahurin falon nasu, mata biyu matasa dakuma yar qaramar yarinya, mamy tana yin sallama suka maida kallansu bakin kofar, Gaba dayansu suka miqe tsaye cike da mamaki, da gudu Lubna tataho ta rungumeshi, lokaci daya tasaki kuka tana shafa kansa, itama dayar tana qarasawa tahada dashi da Lubna ta rungume su tana kukan itama, yar qaramar yarinyar cede tataho ahankali, hankalinta a kwance tana wasa da teddy ta tsaya awajan, mamy kuwa murmushi take amma hawaye ne yake zuba daga idonta Amjad yayi Shiru yana kallon su, duk Sai kuka suke sun rungume shi, gyaran murya yayi sannan yace "to.., to to, Anty Amrah kukan ya'isa haka saiki cikashi" Wadda yakira da Amrah tadago ta watsa masa harara, kallanta nasake yi sosai, kana ganinta kaga yar qwalisa kuma zakayi tunanin Amjad din ya girmeta, amma kuma gashi yakira ta da Anty Amrah Shima dauke kansa yayi daga wajan ta Yana yatsina fuska, da alama basa shiri da juna (😏) Amrah ta kwantar da kanta akafadar mamy cikin shagwaba tace "mamy..." Mamy tashafa kanta,sannan tasa hannu tagoge mata hawayen idonta, takasa cemata komai Amjad ya sake kallon Anty Lubna data maqalqale Yaya Asim ko kunyar mamy bataji yace "to Laila majnun, ai gaisuwar ta'isa haka" Gaba dayansu sukasa dariya, sannan Lubna tacikashi, yar qaramar yarinyar ce ta kalli yaya Asim tace "Uncle ni nayi fishi dakai, shine katafi America kaqi dawowa ka manta Dani" Kallansa yakaai wajan yarinyar yayi murmushi, sannan yasa ka hannu yadagata Sama, hannu tasa taja hancinsa tace "Daddy kakawo min tsaraba? Mamy tace katafi America kuma zaka dawo, zaka tahomin da jirgin Sama mai tashi" Murmushi yayi yace "Am sorry my daughter...Daddy yayi laifi, gashi bankawo miki jirgin samah ba, amma zamu shiga jirgi muyi yawo, ki kalli ko'ina saimu dawo gida ko?" "eh Uncle, I miss you" tafadi haka sannan tayi kissing din kumatunsa, daganan suka qarasa cikin falon Amina de kallonsu kawai take, jikinta duk yayi sanyi, saida suka zauna sannan Anty Lubna ta lura da Amina, dammm!!! Gabanta yayi wata mummunar faduwa, haka kawai taji yarinyar Bata kwanta mata ba, wacece ita? Menene yahadata da mijinta har suka taho tare? Itafa Bata fatan kowacce mace ta ra6i mijinta, zata iya yin komai Akan mijinta, sosai take mutuwar sonsa, tsanar yarinyar ta darsu a cikin ranta, ta yatsina fuska tare dayin qaramin tsaki ta dauke kanta Amrah datake zaune kusa dashi tadubeshi tace "Yaya, yakamata kayi wanka kahuta, zanshiga kitchen da kaina in hadama girki me dadi, yau ranarmu ce, Bata Anty Lubna ba" taqarasa maganar tana kallon Anty Lubna, ahankli Lubna tayi mata dariyar yaqe kamar zata fashe da kuka (😟) Ajiye yarinyar datake hannunsa yayi, yashafa sukarta tace "My Widad, daddy zaiyi wanka OK?" Tace "eh Kayi wanka kazo kabani labarin America" Murmushi yayi ganin yarinyar da gaske ta yarda da maganar da Mamy ta shirya mata, sannan ya kalli Amrah yayi mata nuni da Amina "Amrah, kikaita d'akin ki tayi wanka, kiyi mata abinda ya dace" Yana fadar haka yafara tafiya zuwa dakinsa, Luban ta Mara masa baya, Amjad ya d'aga murya yace "Yaya baka fada mana Sunan taba" Cak yaja ya tsaya batare daya juyo ba Mamy ma ta kalli Amina da murmushi dauke a saman fuskar ta tace "Yata Yaya sunan ki?" Wasa take da yatsun hannunta, Ahankali tadago daradaran idanunta tace "Am.. Ami...." Kafin ta qarasa taji muryar Asim cikin kwanciyar hankali yace "MINAL" Amjad yace "gaskiya sunan Yamin dadi" yafadi hakan yana Dora hannunsa Akan setin zuciyar sa (🀣) Asim ya kalleshi yayi cikin dakinsa, itama Lubna tashiga sannan tarufo mana kofar (πŸ˜”) Amrah ta kalli Amina tace "Minal taso muje" Bakkon kayanta ta dauka tabi bayan Amrah, ita kuma mamy ta dauki wayarta domin Kiran Daddy suna zuwa d'akin taji waani qamshi ya dake ta,saida ta nuna mata komai sannan tafuto tabarta a d'akin Tana futowa daga wanka tasaka doguwar riga ta atamfa daya daga cikin kayanta Babu abinda tashafa ko mai babu bare powder, I fuskarta tayi fayau, sallah tafara ramawa sannan tazauna adakin tayi Shiru tana tunanin rayuwarta, har yau takasa Bude ledar da Inna ta Bata, wacece ita? Bata saniba, menene sunan ta? Bata saniba, Ahankali tabude jakar tafuto da ledar, sannan tafara kunce qullin dayake jikin ledar, gabanta yafara tsananta faduwa, hannunta ya dauki wata irin rawa, tana Gama kuncewa taci Karo da wata tsaleliyar riga ta Yara fara tas, doguwar riga ce amma taji adon net, hawaye ne suka fara tsiyaya daga idonta, muryarta narawa tafara girgiza kanta tana cewa "A a... A a... Bahaka bane, niba yar tsuntuwa bace, kune Iyayena Inna" Haka take kuka tana magana ita kadai kamar ta fita daga haiyacin ta, rigar ta daga ta rungume ta afuskarta tana matsanancin kuka cikin kuka tace "ya Allah ka baiyana min iyayena" qaran wani abu taji yafado daga qasan rigar, Ahankali tabude idonta takai kallanta gareshi Dan qaramin zobe ne na gold amma nayara, hannunta har rawa yake ta dauki zoben tana kallonsa, yayinda idanuwanta suke zubar da hawaye, zoben ta kalla sosai a yanzu kam yayi mata kadan ta sakashi a hannunta, bazai shiga ba, kwalliyar zoben ta kalla taga anyiwa harafin { i } wata irin kwalliya, idonta Akan wajan tace " i ?" tome yake nufi? Iman? Inaya? Intisar? Kokuma iklima? Girgiza kanta tayi ta hada rigar da zoben ta rungume taci gaba da kuka, adede lokacin Amrah tashigo d'akin taganta, jikinta ne yayi sanyi, Ahankali ta qaraso ta ajiye abinci agabanta tace "Minal meyafaru kike kuka? Ko wani abun aka miki?" Hannu tasa ta share hawayen sannan ta girgizawa Amrah kai Batare data yardaba tace "to kiyi hakuri, ga abincinki nakawo miki, idan kingama ki kwanta ki huta" Nanma Batayi mata magana ba kawai de tasake girgiza mata kai alamun to Amrah tatashi tafuta daga d'akin har tana waiwayenta Tana ganin fitar Amrah tamaida rigar da zoben cikin Jakarta, sannan tashige toilet ta wanke fuskarta, tadawo taci abincin Dan kadan, sannan tafara istigfari da yatsun hannunta, ahaka bacci yayi gaba da'ita a zaune *** ***** *** Da daddare suna zaune shida Mamy da Daddy afalon Daddy, kansa aqasa, ya sauya kaya zuwa qananu baqin jeans dakuma riga milk color, yayi masifar yin kyau, sumar kansa sai sheqi take, Daddy yace "Kaci gaba da Addu'ah my son, insha Allah nayima alqawarin Nima zan tsaya tsayin daka Inga an nemo wadannan mutanan da suke son ganin bayanka, ka kwantar da hankalin ka kaji, ai kunyi magana da commissioner of police ko?" Ahankali kansa aqasa yace "eh" Mamy ta kalleshi tana jiran taji qarin Bayani, saita ji Shiru, wannan hali na Asim Yana Bata mamaki, ace iyayenka ma suna ma magana amsa saide ta kasance ataqaice? Dago kansa yayi suna hada ido da'ita ya sunkuyar da kansa, Dan yasan zai samu Rabon harara ne kawai, to Yaya zaiyi? Kullum de haka ake masa, za'a kawo masa farmaki amma maganar de itace guda daya za'ayi bincike za'ayi bincike amma daga baya kuma saide aji Shiru, ahaka case din zai mutu Daddy ma da yaji Shiru yasan bazai sake samun wata amsar ba, Dan haka ya sake kallonsa yace "Toya kukai dasu?" Yanzun ma kamar bayason maganar yace "Sunce zasu tsaurara" (🀣) Mamy ta dafe kanta da hannunta ( ) Tace "me zasu tsaurara? Kayi Bayani mana" Kansa yadago ya kalleta yace "bincike" Kafin mamy tasake bashi amsa anty Lubna tayi sallama tashigo cikin d'akin tace "Mamy angama hada dinner" Tace "to Lubna gamunan futowa" Daddy ya dauki waya Yana Kira daga nan yayi compound Ahankali yadago kansa yace "mamy gameda yarinyar nan" Mamy tazuba masa ido tana kallansa, tanaso taga yanzu zai Bude baki yayi mata Bayani ne kokuwa Shima Bayanin bazai Bude baki yayi ba Cikin rashin damuwa tace "inajin ka" Saida yayi kalar tausayi da fuskar sa sannan cikin shagwaba yace "Mamy batada kowa" daganan kuma Sai yayi Shiru πŸ˜‚ Mamy ta jinjina wannan qarfin hali na Asim a cikin ranta, kallansa tayi cikin ranta tace zanyi ma ganinka, amma afili saitace "Allah sarki, to madallah" Cikin sauri ya kalleta, ganin ta dakatar da maganar tasu daga nan, yayi Shiru Shima Yana jira yaji ko akwai abinda zatace amma Sai yaji Shiru (😊) Ya kalleta yace "mamy inaso ta zauna tare damu kafin Allah yakawo iyayenta" Murmushi tasaki ganin yabude bakinsa yayi mata magana, tace "Asim, kaga kadena saka damuwa aranka, Sai kwanan ka yaqare zaka mutu, kuma Insha Allah maqiyanka bazasu ga bayanka ba, kadena saka wannan damuwar aranka har tasa kakasa sakewa damu muyi wasa da dariya kamar da, haba Asim Yaya kake so nayi ne?Kuma ni inde wannan yarinyar ce babu damuwa, Allah yabamu Zaman lafiya " Murmushin sa mai mutuqar tsada yayi mata, dimple dinsa suka futo sosai, yace" to mamy insha Allah zanyi yanda kikace " Sumar kansa ta shafa badan ta yarda da maganar tasaba tace" to Asim, Allah yayima albarka " Daga nan suka fita falo domin cin abincin dare Gaba dayansu family dinne a dinning suna cin lafiyayyen abincin da Lubna da Amrah suka hada, Daddy, mamy, Asim, Amjad, Lubna, Amrah, baby widad, dakuma Amina. Anty Lubna Sai yatsina fuska take, tana watsawa Amina wani Dan iskan kallo Shikuma Amjad Sai wani kallo yake mata cike da birgewa Daddy yagoge bakinsa da tissue ya kalli mamy "hajiya, baquwa mukayi ne? Dazu mun gaisa amma ban tambaya naji wacece ba" Shiru wajan yayi, kowa Yana jira yaji amsar da mamy zata bashi, kallonsa tayi tace "Alhaji ai Asim ne yazo tare da'ita, zata zauna damu nadan wani lokaci" "kinsan da cewa banason wannan kwashe-kwashen ko?" Gaban Amina yafadi, jin furucin daddy, dama tasan hakan zai Iya faruwa shiyasa tun farko tace masa yakai ta gidan marayu, itama dama tunda ta ganshi taji itama bai kwanta mata Arai ba, da alama bashida kirki, amma kuma gashi dansa yanada kirki sosai Asim ya ajiye spoon din hannunsa yazubawa daddy ido amma baice komai ba, Anty Lubna kuwa wani irin dadi ne ya mamaye mata zuciya, harta Kasa boye hakan a ranta, saida tafuto fili tace "hakane kam Daddy, idan batada galihu ne akaita gidan marayu mana" Daddy yace "Nima abinda nagani kenan" Tsananin bacin rai kam ya baiyana afuskar Asim, cikin tsawa yace "Lubna!!!" Kowa saida hantar cikinsa ta motsa musamman Amina, lokaci daya taji tsoron sa ya kamata, jikinta har rawa yake, Ahankali tamiqe cikin rawar murya tace "naqoshi" daga nan tayi d'akin Amrah Mamy tace "haba Alhaji, bansanka da wannan halinba, asalima da temakon naqasa dakai nasan ka" Cikin bacin rai Yatashi yayi dakinsa, saboda me daddy da Lubna zasu Fadi wannan maganar agaban wannan qanqanuwar yarinyar? Ko basusan hakan zai Iya haddasa mata damuwa ba? Daga nan kuma tunani yayi mata yawa tazo tasamu matsala tun tana qaramar ta (πŸ˜–) Haushi ya kama anty Lubna ganin Shima Asim din yatafi daki, hakan yana nufin ransa ne yabaci kenan har yabar abincin saboda waccan yarinyar ta tashi, gabanta ne yafadi, innalillahi... Allah yasa de ba sonta yake ba, data shiga ukunta, cikin sauri itama tatashi tabishi dakinsa har tana sassarfa (🀣) Daddy yayi Ajiyar zuciya yace "Naga alama saboda maganar danayi ran Asim yabaci, anyway kifada masa na amince tazauna din, but saboda farin-cikinsa nayi haka, saboda banason abinda zai sashi ya sake shiga damuwa" Amjad yasaki wani murmushi, mamy tace "to alhaji insha Allah zan fada masa" *** ***** *** Tundaga lokacin da Amina taji furucin Daddy akanta, dakuma matar Asim, saiya kasance takasa sakin jikinta dasu, koda yaushe tana waje daya ta ke6e kanta, ko kadan Bata so tayi magana, tafi so kawai ta zauna tayi Shiru ita kadai Tunani kuwa yace Salamu Alaikum, muddin tayi Shiru Tofa batada aiki Sai tunani, tunanin shine yake zame mata abokin fira Idan Bata daki, to tana can saman Benin gidan, tana kallon kyawawan gidajan unguwar, kamar yanda tasaba zuwa wajan haka yauma taje ta tsaya, ta rungume hannunta aqirjinta, tunani tafara tayaya zata fara neman iyayenta? Ta wacce hanya? Anya kuwa bazata nemi temakon Asim ba? "lala mafi ayyi mishikila ya hammude, natakallam ba'aden kuntu ma'a zaujaty Al'an" Larabcin dataji Yana tashi abayanta ne yasa tajuya cikin sauri, gidan dayake kallon gidansu Asim ne taga mata da miji suna shirin shiga Mota, amma mijin Sai waya yake Yana larabci, matar tana sanye cikin Baqar laffaya dataji Adon stone Sai walwali take, ta nad'e jikinta gaba daya, fara ce tass kana ganin ta kaga balarabiya ko tantama babu, sumar kanta tuli guda har kana hango tagaban goshinta, shikuma mijin yanada Dan duhu kadan, matar Sai murmushi take masa, da alama tanajin wayar dayake itama Lokaci daya taji bala'in qaunar ma'auratan tashiga ranta, sosai ta shagala wajan kallonsu ko kiftawa batayi, harma taso ta manta da wata aba damuwa datake damunta, Akan idonta mijin yabude wa matar tasa Mota tashiga gidan gaba, sannan Shima ya zagaya yashige, maigadi yabude musu get suka futo Wata irin nannauyar Ajiyar zuciya ta sauke "kinsan tane kiketa kallonta?" ta tsinci maganar Amrah daga bayan ta Cikin sauri ta juya tace "Anty Amrah" Dadi yakama Amrah, saboda tana son mutum ya girmama ta, Bata son raini ko kadan, qarasawa tayi kusa da'ita tace "waike bakya gajiya ne kizo nan ki tsaya kinata tunani ke kadai?, yanzu me kike gani a wancan gidan?" Girgiza kanta tayi tace "babu komai " Amrah tayi Ajiyar zuciya tace"Sunanta ISHRAQA,amma muna kiranta anty Ishraqa,idan kinaso ki birgeta, toki kirata da maman INSAAF, Nima naji mamy tana kiranta da sunan ne, bansaniba ko sunan 'yarta ne, bansan takamaimai wacce alaqa take da'ita da me sunan ba, amma kuma tunda a kace maman INSAAF aikinga may be 'yarta ce, amma bansani ba gaskiya, saboda babu wanda tafuto fili ta fadawa wacece insaaf din awajan ta, ciki kuwa harda aminin nata wato Yaya Asim, ranar da kukazo kina bacci tazo wajan Yaya Asim,qawarsa ce ta qut da qut,kuma class mate dinsa ce, duk yanda kike tunanin shaquwa tota Anty Ishraqa da Yaya Asim tawuce nan, qawancensu Yana birge kowa,tana fada masa damuwar ta, Shima Yana fada mata tasa, tun suna Yara tare sukai karatu har suka girma kowa yayi aure, daga nan ne suka rabu, tsawon wasu shekaru kuma Allah ya sake hadasu anan Lagos, Minal Anty Ishraqa tataka babbar gudunmawa a cikin family dinmu, kuma har yanzu ma tana kan takawa, labarin yanada tsawo sosai, watarana zaki sani,shikuma dayan mijinta ne EL HAMEED, larabawan Sudan ne,labarin su bazai qareba Minal, kizo mutafi ciki muyi kallo, yafi wannan tunanin" tana fadar haka takama hannunta suka yi ciki Afalo suka zauna Amrah ta kunna musu kallo sunayi, wayarta ce tayi qara ta amsa sannan tashige dakinsu Amrah na tafiya tazubawa TV ido tana kallo, ba kallon abinda akeyi din take ba, a a kawai tana tunanin Akan tayaya zata hadu da iyayenta? A'ina zata gansu? Harya shigo cikin falon Bata sanda zuwansa ba, yayi mutuqar kyau cikin suit, yariqe jacket din a dayan hannunsa, kallanta yayi batare dayace mata komai ba, yafada cikin kujerar ya lumshe Idonsa, bayason damuwa ko kadan, kuma yaga alama yarinyar nan tana son sakawa kanta damuwa, tun tana yar mitsitsiyarta zata haddasa wa kanta tunani daga nan kuma Sai hawan jini, yanzu me take so tarasa zata zauna ita kadai Afalo tana tunani? Wata zuciyar tace masa ka tambayeta mana, Girgiza kansa yayi cikin ransa yace "no.... Tayaya zan tambayeta? Mezance mata?" Amina tajuya ta kalleshi taga Yana Girgiza kai shi kadai (🀣) Magana tafara yi a ranta to kode bashida lafiya ne? Tunda suka zo gidan Bata taba kebewa ita dashi ba, wannan lokacin ne ya kamata ace tayi masa maganar datake damunta, idan tabarshi yatafi batason yaushe zasu sake ke6ewa ita dashi su biyu ba bare tayi masa magana akan sirrin ta daba kowane yasani ba Sai shi Ahankali ta tashi taqarasa wajan sa, kanta a qasa tana Jan hannunta kamar wanda suke mata ciwo ta nemi waje adede kafarsa ta zauna aqasan kafet din, muryarta ta rawa tace "YAYA" Zazzaqar muryarta tadaki dodon kunnansa, memakon yabude lumsassun idanuwansa saiya sake lumshe su (πŸ™Š) Sosai yaji Dadin yanda takirashi da wannan sunan, zaiso ace ko sau daya ne tasake fada, dago manyan idonta tayi ta kalleshi, muryarta tafara rawa, tasake cewa "Yaya" Nanma Shiru yayi mata kamar wanda yake bacci, hawayen da suke son zubo mata tana tare su, sune sukai nasarar sauka Akan kumatunta, Ahankali ta yunqura da niyyar tashi tabar masa wajan, yanajin haka yabude Idonsa yazube su Akan ta, karaf idonsa ya sauka Akan hawayen dayake zubo wa daga idonta Ahankali yabude bakinsa kamar me muryar rad'a yace "zonan" Hawayen tashare sannan tadawo tazauna aqasan sa Gyara zamansa yayi sosai yadora hannunsa Akan cinyar sa, ya rankwafo da kansa dede fuskarta,kamar Yana rad'a mata wani abu,inda Allah yakawo Lubna awannan lokaci data gamu da hawan ruwa(🀣) "Why are you crying?, ko maganar Daddy ce tasa kike kuka?" ta tsinkayi maganar sa cikin kunnanta Girgiza masa kai tayi tace "ba wannan ne yasani kuka ba, kawai ina tunanin rayuwa tane, duniya tana cike da mutane mabanbanta, masu halin qwarai da akasin haka, inda ace Allah bai hadani dakai ba, da bansan hannun wa zan fada ba, nagode sosai" tana fadar haka hawaye suka sake zubo mata, ta Dora kanta Akan kafafunta tana kuka harda sheshsheka Gabansa ne yafadi,Me wannan yarinyar take shirin yi bayan yayi niyyar taimaka mata? akano tace tanaso yakai ta gidan marayu, kode yanzu ma so take tatafi? Metakeson fada masa? "saboda....abin...da Daddy yayi miki ne zaki tafi?" yafadi maganar a rarrabe. Dago fuskarta me cike da hawaye tayi tace "a a Yaya, babu inda zanje, idan natafi wani wajan wanake dashi bayan kai? Kawai de inaso ka temaka min kamar yanda Allah ya temakeka, kanemo min iyayena afadin duniyar Nan, inaso naji dalilin dayasa suka rabu dani, meyasa zasu wofintar dani, ina tsoron ace niba yar halak bace, ka temakamin, Dan Allah" Taqarasa maganar tana hade hannayenta waje daya alamar roqo (πŸ™πŸ») Wata irin siririyar Ajiyar zuciya yasauke yace mata "shikkenan?" Batace dashi komai ba, ta daga masa kanta "ok zansa abincika miki" Cikin muryar kuka tace "nikai da kanka nakeso ka temaka min, inaso nasan asalina" Yatsani kukan mace, ita kuma yaga alama ta maida kukan kamar ba komai ba,tacika kuka dayawa saikace Ishraqa, cikin sauri ya d'aga mata hannu (βœ‹πŸ») yace "shikkenan...naji... Is Okey" Yadauki farin handkerchief dinsa dayake zuba uban qamshi ya miqa mata Yana mata nuni da idonta Aikuwa Karaf Akan idon Lubna data futo daga d'akin ta tanaso takirashi taji a'ina ya tsaya bai dawo gida da wuri ba? ( ) Cak taja ta Tsaya awajan tana kallonsu kamar an dasata Anya kuwa maganar Amrah gaskiya ne Asim baisan wacece INSAAF ba? Ishraqa Bata boye masa damuwar ta, Shima haka, idan bai Santa ba menene yasa hatta computer sa take dauke da sunan yarinyar? To kode akwai wata aqasa ne? πŸ€” Wannan familyn kuwa Anya babu wani abu aqasa? Mutane zasu so jin waye Asim, kuma menene takamaimai dalilin dayasa ake bibiyar sa? To duk kubiyoniπŸ€— SHARHI FA ✍🏻 Amnah El~Yaqoub [2/7, 11:38 PM] El~Yaqoub: INSAAF Writing By:Amnah El~Yaqoub 11&12 Like my page on Facebook πŸ‘‡πŸ» https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 Masoyana masoyan wannan labari ina godia sosai agareku, inajin Dadin yanda kuke tattaunawa Akan wannan labari tun kafin ma labarin yayi Nisa, ina godia sosai πŸ™πŸ» Amina da Asim kuwa basusan tashigo falonba, handkerchief din ta karba tagoge fuskarta dashi Baqin ciki kamar ya kashe Lubna, kishin mijinta ya kamata, ta tsani taga wata mace tana ra6ar Asim Ahankali take takowa harta qaraso inda suke, atsaye ta tsaya qerere ta kalleshi babu batun sannu da zuwa babu komai tace masa "ashe kadawo" Atare suka daga kai suka kalleta, riga da siket ne ajikin ta na les da yayi mata mutuqar kyau, gashin dokin datasa a kanta anyi mata qananun kalba dashi Amina ta miqe tabar musu wajan batare data bashi handkerchief dinba, Anty Lubna ta maka mata wata uwar harara tabi bayan ta da wani matsiyacin kallo, Asim yazuba mata ido Yana kallonta cike da mamaki Amina kuwa harta shige daki tana tunani, tarasa meyasa Anty Lubna Bata sonta, idan Yaya Asim ne anfada mata sonsa take ne? Ina ruwanta dashi? Abinda yake damunta ma kadai ya isheta, idan tayi hakuri ma Zamanta a gidan nad'an wani lokaci ne, tana samun iyayenta zata bar musu gidansu, tabar mata mijinta, auren da aka daura musu ma hanyar da zata rabu dashi take nema, tayaya zataso mutumin daya taimaka mata yamutu a Sanadin ta?babu soyaiyar Asim ko kadan a ranta, auren ma tana fatan arabashi tahuta Ajiyar zuciya Lubna ta sauke ta kalleshi, "inama magana kayi Shiru, nace ashe kadawo" "nadawo" Shima yabata amsa a taqaice "Wai Dan Allah My dear menene hadinka da wannan yarinyar? Tunda kuka dawo ina lura dakai Sai nan-nan kake da'ita, ita 'yar gidan uban waye da zata dinga kuka ka zauna kana lallashinta Sai kace zaka maidata jikinka?" ( ) Tsananin mamaki ya kama Asim, kamar hoto haka yake kallonta, 'yar gidan uban waye? shita zaga kenan? Ransa abace yace"tambaya kike?" Cikin fishi itama tace "eh, yar gidan uban waye?" " 'yar gidan ubanki ce Lubna" (😳) Yana fadar haka ya dauki brief case dinsa yayi dakinsa Juyawa tayi tana kallon sa, hawaye yazubo Akan fuskarta, tadora hannunta Akan qirjinta tace "nizaka zaga Akan wannan yar iskar yarinyar?" Tsugunnawa tayi awajan hannunta a kanta tana gunjin kuka, babu me Bata amsa, domin kuwa shide Asim baya nan, baqin ciki kamar yakashe ta, ada damuwar ta daya itace INSAAF, laptop dinsa insaaf, takardun komai insaaf, insaaf, tarasa gane wacece wannan tsinanniyar insaaf din (🀣) Sotake taganta ido da ido ayita ta qare, to yanzu bayan insaaf din ga wata jarabar tasake samunta, bazata juri ganinsa da kowa ba, wallahi saide duk abinda zai faru ya faru a cikin gidan, cike da masifa ta tashi tabishi cikin d'akin Labarin su : Alhaji Abbas da Alhaji Abdullah iyayensu daya, su biyu iyayensu suka Haifa, Abdullah ne babba, Allah yahore masa kadarori dayawa, tun kafin suyi aure yasan zafin nema, har suka kai minzalin aure, da hankalin su iyayensu suka rasu, inda suka damqa amanar Abbas a hannun Abdallah, kuma Alhamdulillahi Abdullah yariqe dan'uwansa amana, raana daya sukai aure Allah ya azurta Abdullah da samun d'a namiji, suka samasa suna ASIM, sun Dade basu sake samun haihuwa ba, Sai bayan wasu shekaru masu yawa Allah ya sake azurta Abdullah da matarsa Hussaina haihuwar 'ya mace suka saka mata sunan mahaifiyar su, amma suna kiranta AMRAH. har zuwa wannan lokacin Abbas bai samu haihuwa ba, Sai bayan shekara daya Allah yabashi d'a namiji ya sanya masa suna AMJAD Bayan shekara daya Allah yayiwa matar Abbas Rasuwa, haka mamy tahada Amjad da Asim da Amrah duk ta riqesu, ta riqe Amjad tsakani da Allah, babu wanda zaice ba mamy ce ta haifeshi ba, Shima yashaqu da mamy sosai, kasancewar bai tashi tare da mahafiyarsa ba, Amrah tun tanajin haushi ya qwace mata fada awajan mamy harta zo ta daina, haka mamy zatayi ta rarrashinta tace ai qaninta ne, wannan rashin jituwar shine yake wanzuwa atsakanin su har yanzu,dayake mamy Bata son raini, Bata duba shekara daya Amrah ta bashi ba haka ta koya masa kiranta da Anty Amrah Tundaga lokacin da matar Abbas ta rasu wato daddy bai sake aure ba, Sai bayan wasu shekaru yayi aure, Zaman nasu babu dadi da matar daga nan suka rabu, Rana daya Allah yayiwa Alhaji Abdullah rasuwa, wato mahaifin su Asim, mutuwar ta jijjigasu sosai, alokacin Asim yanada hankali sosai, yasan komai, suna zuwa makarantar kudi shida qannansa, alokacin ne yahadu da ISHRAQA,a jinsu daya ita dashi, suyi wasa tare, suje suyi lilo tare, hatta toilet din makaranta Asim ne yake raka Ishraqa 🀣🀣 Yanda suka shaqu ne yasa yan a jinsu suke tunanin soyaiya suke, su kuma kwata kwata babu wannan a tsakanin su yanda ake nuna wa su Asim gata Tona Ishraqa yawuce nan, babanta da kansa yake kawo ta makaranta, Sukuwa direban gidansu ne yake kawo su Kusancinsu da Ishraqa ne yasa iyayenta suka San Iyayen sa, musanman mamy, tasan baban Ishraqa, suna mutunci sosai saboda alaqa dakuma shaquwar datake tsakanin yaransu, wani lokacin suna gaisawa idan tazo daukar su Asim in direban gidan baya Nan Rana daya su Ishraqa suka koma Sudan wajan danginsu, wannan ne Sanadin rabuwarta da Asim, bayan yayi candy yanunawa Qanin baban sa wato daddy mahaifin Amjad ya nuna masa yanaso a saida kadarorin babansa ko kasuwanci ne yafara, mamy ma tagoyi bayansa, dasukaje wajan daddy da maganar saiyace za'a duba agani, daga nan bai sake tada maganar ba, lokacin jamb yayi, yaje yazana yasamu sakamako mai kyau, nanma yaje masa da maganar karatu, Sai daddy yace yayi hakuri zuwa wata shekarar saiya tafi, saboda yanzu yana harhada kudin gadon mahaifinsa ne Suna jin haka basu yi masa musu ba, haka yayi hakuri da wannan jamb din, wata shekarar ya sake yin wata nanma yasamu sakamako mai kyau, alokacin dasukaiwa daddy maganar yace su saurareshi, mamy tana jin haka tasaida sarqarta tanema masa makarantar, Sai bayan yafara karatun ne sannan daddy yazo musu dawasu takardu daga cikin takardun mahaifin su Asim da Amrah, Bayan yatafi Asim yanunawa mamy takardun yace ai basu cikaba, mamaki ya kama mamy ganin yanda Allah ya horewa danta basira tun ba'aje ko'ina ba, ita kanta tasan takardun Bahaka sukeba,yariqe kaso mafi yawa aciki, takardun daya basu ko kwatar kudin mahaifin Asim basu yi ba, amma Sai tayi Shiru saboda gudun bacin rai Rana daya daddy yacire Amrah da Amjad daga makarantar kudi yamai dasu ta government, Abin yayiwa mamy ciwo sosai, amma dataga ba Amrah kadai yayiwa manaqisa ba harda Dansa Amjad Saita share batun,kuma duk wannan abun dayake faruwa mamy bata taba nunawa Amjad komai ba, asalima ko kadan Amjad bai shaqu da mahaifinsa ba kamar yanda ya shaqu da mamy, ita kanta Amrah tun tana kishi dashi harta daina ta saduda πŸ˜‚ Tundaga lokacin Asim yafara janye jikinsa daga Daddy, ko shawara zaiyi saide yayi da mahaifiyarsa kawai,mamy dataga alamun haka awajan danta, saita nemi shawara awajan qawarta, kuma ta Bata shawara mai kyau, tundaga lokacin da qawarta tabata wannan shawarar tafara nunawa Asim yadena janye jikinsa daga na Daddy, shidin kamar uba yake awajan sa, qanin mahaifinsa ne, shikuma Yaro ne mai jin maganar mahaifiyar sa,tundaga lokacin bai sake nunawa Daddy komai ba, saide tun daga lokacin ya kasance Shiru Shiru,bashida buri illa ya taimaki Amrah dakuma Amjad da Allah yasa ka masa son Yaron a cikin zuciyarsa, kwatsam wata Rana Daddy ya nuna yanason auren mamy, alokacin tasake zuwa wajan qawarta neman shawara, qawarta tabata shawara ta Aureshi kodan saboda yaransu, alokacin da Asim yaji zancen auren qin amincewa yayi, saida tayi da gaske sannan ya yarda, cikin satin aka musu aure, lokacin tafiyar sa University tayi, wannan Karon Shima Daddy baiyi qasa a gwiwa ba ya taimaka wa Asim, kuma har lokacin daga mamy har Asim babu wanda yayiwa Daddy maganar kudin gadon su dayake hannunsa, Shima kuma bai basu ba, saide kuma duk wani haqqi dayake kansa na aure dakuma haqqin Yara Yana Sauke musu shi, tunda Asim ya shiga makaranta Lubna ta Dora ido akansa taji tana sonsa, ita irin matan nan ne masu budaddan ido, Kai tsaye qanin mahaifinta tayiwa maganar, kasancewarsa abokin Daddy , shikuma yasamu Daddy da batun, Kokadan Asim baya qaunar Lubna alokacin, amma haka yayiwa su Daddy biyaiya ya amince, kuma alokacin ne daddy ya basu mamaki, domin kuwa duka kadarorin maahaifinsu daya rage awajan sa ya dauko ya nuna musu, sannan yace tunda Asim ya girma ya karba yaci gaba da ajiyesu a hannun sa, mamy babu wanda yakai ta farin- ciki awannan lokacin, Asim Yana karbar takardun yaga ba original bane, haka yayi Shiru baice da mamy komai ba, saboda bayaso farin cikin datake ciki yayanke. Bayan yagama makaranta a kayi bikinsu da Lubna, saide abin baqin cikin shine kamar yanda yake ganin ta mai budaddan ido hakane ta tabbata, budewar ta tayi yawan dayasa yagane cewa bai sameta a matsayin budurwa ba, wani yariga shi πŸ™πŸ™ Sarai yagane, itama Tayi tunanin daya gane zaiyi mata magana, amma abin mamakin baice da'ita komai ba, tun tana dari dari harta sake,amma abinda Bata saniba shine abin Yana nan a cikin ransa, har yau Yana kallonta da wannan abun. Asim yafara fafutukar neman aiki amma babu aiki, mamy ta sashi agaba tace ya saida filayensa dana Amrah yafara kasuwanci da kudin, bai nuna mata takardun wajan nasa fake bane haka ya amsa mata zai saida din, alokacin cikin ikon Allah yasamu aiki awani company suna biyansa albashi mai kyau, tundaga nan kuma yake ganin abubuwa arayuwarsa, sosai wasu mutanan suke neman rayuwar sa daga gefe, muddin yayi dare awajan aiki baidawo gida ba, to haka zaiga mutane suna bin bayansa, tun Yana waiwaye Yana qara sauri harya dawo guduπŸ˜‚ Tun Ana masa abu a boye har ya kasance a nayi masa afili, kuma har yau baisan suwaye ba Daddy ma dayaga abin yayi yawa, shida kansa Ya hanashi fita ko'ina, kuma hukuncin daya yanke din yayi wa kowa dadi Haka ya hakura da aikinsa domin ceton ransa, adede lokacin su Ishraqa suka dawo Nigeria itada mijinta, Asim yayi murna sosai da ganin ta, itama haka, haka Suka zauna Yana Bata labari Kala Kala itama tana bashi,cikin labarin data bashi harda na aurenta bayan sunyi candy, saide abinda ya lura dashi shine kamar tana cikin damuwa amma kuma Bata sanar dashi ba, Shima bai takura mata da wannan tambayar ba, su Ishraqa sun dauki tsawon lokaci a Nigeria kafin suyi shiri zasu koma Sudan, alokacin ne suka dauki dukiya mai mutuqar Tarun yawa itada mijinta El Hameed suka damqawa Asim yaci gaba da juyata tunda Yana zaune agida babu aikin dayake Alokcin dasuka Bawa Asim wannan dukiyar tsorata yayi, ganin kudin sunyi yawa, mamy da tayi Shiru tana kallon Ishraqa saita nuna musu cewa ai kudin yayi yawa, alokacin mijin Ishraqa yace musu susai kadarori dashi su ajiye, suma ba kudinsu bane kudin INSAAF ne 😳 Daddy ma da yaji haka duk Sai suka bashi goyon baya, Alokcin Amrah da Amjad suma suna da hankali duk sunsan komaai, Asim ya karbi kudi yasiyo gidaje, filaye, daduk wasu abubuwan kadarori sannan yabude company dawani anan Lagos, bayan wasu shekaru Sai su Ishraqa suka dawo Lagos da zama gaba daya itada mijinta, Asim yanema musu gida mai mutuqar kyau kusa danasu gidan, kuma tsawon wannan lokacin Asim bai taba tambayar Ishraqa wacece INSAAF ba, abinda ya sani shine duk wani kudi dayasan na INSAAF ne Yana kiyayeshi, koda wasa baya taba kudinta, saide ribar dayake samu yake amfani da'ita, saboda kada ya shagala ne yasa hatta laptop dayake amfani da'ita ma wadda da kudinta aka siya bada riba ba yaje aka saka masa sunanta a jiki domin tadinga tuna tar dashi Shi kansa baisan Yaya akai mamy take Kiran Ishraqa da maman INSAAF ba, kawai de yaji tana fada, yasan kuma bazai wuce a cikin hirarsu ta mata tasani ba, shide abinda ya sani shine Ishraqa bazata haifi wata yarinya ba kuma ace takasa sanar dashi, saide in ko yar dan'uwanta kokuma yar mijinta, amma cikin ransa shi kansa yanason sanin wacece insaaf, domin kuwa tun kafin ya ganta yaji a ransa cewa ita din tabbas ta daban ce. 😳 Asim hadaddan Gaye ne, ya'iya daukar wanka me daukar hankali, halinsa nede Sai ahankali kawai, miskilancin sa yayi yawa, kuma haka yasamo asali ne daga lokacin da yasan yanada maqiya daga gefe, koda yaushe idan yazauna yayi Shiru baida aiki Sai tunanin waye yake son ganin bayansa?, kalar fatar jikinsa fari ne sosai, bashida gemu saide saje daya zagaye bakinsa dashi wanda yaqara qawata fuskarsa, wani lokacin ko magana yake haka zakaga dimple dinsa suna futowa, bare kuma idan yayi murmushi anan ne zaka san daure fuskar dayake ba yayi masa kyau ko kadan Shekarunsa 38, amma idan ka ganshi bazakace yanada wannan shekarun ba, saboda abinci dayake ci mai kyau da wajan zama mai kyau, uwa uba yawan motsa jiki dayake, wanda yazame masa dabi'a har hakan yasa hannunsa jikinsa ya murde musanman hannunsa, amma kallo daya zaka masa kasan cewa gwarzo ne kuma jarumin namiji, haka kuma dole ajinjinawa matar datake iya daukan larurarsa wato Lubna πŸ˜‚ Bayan yayi aure yadade bai samu haihuwa ba, Sai kwanan nan Allah yabashi yarinya mace, ya saka mata suna Hussaina wato sunan mamy, suke kiranta da Widad, kwata kwata yarinyar shekarar ta uku da rabi Haka Amjad Shima fari ne sosai, idan ka ganshi shida Asim Sai kace iyayensu daya, saboda kwata kwata Amrah ita Bata iyo farin su ba, tanada Dan duhun fuska kadan, Sukuwa duk farare ne har mamy Shekarunta 30 shikuma Amjad 29 Mace ce ita maison ado, dakuma son girma, batason raini, shiyasa tasu ba tazo daya itada Amjad ba, tun suna Yara har yanzu idan suka fara fada itadashi saika dauka qananun Yara ne, musanman idan suka fita unguwa wani yace ita qanwar sace, anan za'a dinga fada, wannan shekara dayan data bashi ganinta take kamar ta bashi shekara dari πŸ˜‚πŸ˜‚ Da kudin INSAAF dayake wajan Asim yasake Bude wani reshen kamfanin nasu a Yola, shine ya yanke shawarar zai Dora Amjad akai, wannan dalilin ne yasa suka shirya sukaje Yola domin Bude wannan company, kuma daga wannan ranar yasan cewa har yanzu akwai sauran masu bibiyar sa domin kashe shi, dama yadade Yana nazarin dauke duk wasu takardu dayasan banashi bane na INSAAF ne, domin ya dorasu Akan laptop, kuma yayi nasarar hakan, daga qarshe kuma ya nemi computar yarasa,(πŸ€—) Hajiya Amina ta dauke mana kuma Naga alama batada niyyar bamu πŸ€” ✍🏻 Back to story To masu son jin labarin Asim, gashinan, yanzu kunji alaqar sa da Ishraqa, qawarsa ce, class mate dinsa, aminiyar sa Comments pls ✍🏻 El~Yaqoub [2/8, 10:21 PM] El~Yaqoub: INSAAF Writing By:Amnah El~Yaqoub 13&14 Like my page on Facebook πŸ‘‡πŸ» https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493/ Har Asim yafuto daga wanka Lubna tana kuka, kallanta yayi yadauke kansa, gaban mirror ya qarasa Yana shafa mayuka masu Dadin qamshi a jikinsa, fatar nan Sai shining take, murdaddan jikinsa ya baiyana, faffadan qirjinsa ya sake futowa sosai, itama dataga tayi kukan tayi,amma ko kula ta baiyiba Sai tayi qwafa tafice daga d'akin Bin bayan ta yayi da kallo, yaje yarufe kofar d'akin sannan yacire towel din yajefa shi kan gado ( πŸ™ˆ) yarasa meyasa Lubna ta raina shi, kokuma saboda tana ganin baya daukar mataki a kanta ne oho. tsaf ya shirya a tsinake cikin manyan Kaya, riga da Wando na farin yadi, Ana iya hango farar Singlet din jikinsa, bazai taba iyuwa ka kalleshi ka dauke kanka ba, Sai zuba qamshi yake, yafuto fuskar nan tasa amurtuke, Lubna tana zaune afalo tana danna waya, qamshinsa dataji ne yasa ta daga kai ta kalleshi, Kasa dauke idonta tayi akansa, ita kanta tasan cewa tayi sa'ar miji, amma har yanzu yakasa ganewa cewa saboda kishin sa take wani abun Maimakon tatashi ta bashi abincin saita dauke kanta, Shima bai nemeta ba yaci abincin sa yawuce d'akin mamy,alokacin mamy tagama yin sallah kenan itama futowa zatayi, Yana ganin haka Shima saiya biyota suka dawo falon Lubna tana ganinsu tatashi tashige dakinta, mamy tana ganin yanayin fuskarta tasan cewa akwai damuwa, saboda Lubna Bata iya boye bacin ranta ba Akan kujera ta zauna Shima Asim dayake binta kamar jela ya kwanta Akan kujerar sannan yayi fillo da cinyar mamy ya lumshe Idonsa baice da'ita komai ba Mamy tayi murmushi, tana shafa sumar kansa datake sheqi, inde wajan kwanciya akan cinyar ta ne taga alama da Amjad da Asim dakuma 'yar Asim din sune zasu qarasa mata 'yar cinyar Tata (πŸ˜‚) Shi Asim saide kawai yayi fillo da cinyar Tata ya lumshe ido yayi shiru, har Gara Amjad surutu zaiyi ta mata, ta wannan Fannin kam Amrah ta qwace girman, domin kuwa duk cikin su itace Bata wannan son jikin Ajiyar zuciya tayi tace "meya hadaka da matarka Asim?" Idanunsa a lumshe yace "babu komai mamy" Mamy najin haka tayi Shiru, tsakanin mata da miji Sai Allah, kartaje Garin tambaye tambaye ta tambayowa kanta abinda yafi qarfin kunnanta Dayaji tayi Shiru batace komai ba saiya bude Idonsa yace "Mamy inason Minal Takoma School" Tace "eh kayi tunani mai kyau, kafin muga abinda hali zaiyi Itama nasan karatun nata yayi Nisa, yarinyar nan tana bani tausayi Asim" "abinda takasa ganewa kenan" ya Fadi hakan a baiyane, shi yayi tunanin a zuciyarsa yafadi maganar Yana nufin Lubna takasa gane Amina abar tausayi ce, ashe afili yafada Mamy tace "wacece takasa gane hakan?" Kansa ya Sosa yace "ahh babu komai mamy" Jinjina kanta tayi batare da tayi magana ba, ta riga tagano bakin zaren, tasan da Lubna yake, kowa yasan kishin Lubna Akan Asim, kuma yanzu ma tasan Akan kishin ne suka samu wannan Dan sabanin, duk da yaqi fada mata ko menene ya hadasu Amina tafuto daga d'akin su zata kawo masa handkerchief dinsa tayi tozali dashi a kwance Akan cinyar mamy,taqame awajan cikin tsananin mamaki, yanzu wannan qaton ne mamy tabari ya kwanta Akan cin yarta? πŸ€”πŸ€£ Kuma itama Sai shafa kansa take yawani lumshe Idonsa Sai kace d'an jariri, Ahankali tajuya Takoma cikin daki batare da sun ganta ba *** ***** *** Kamar kullum yauma sassafe tabi ta Corridor tahau saman beni tana Kallan gidan wannan matar da Anty Amrah takirata da Ishraqa, ba tasan dalili ba tun lokacin data ganta taji tanason sake Sakata a'idonta, matar tana birgeta, gata yar gayu,komai nata abin birgewa, bataqi ace ta zauna tanata kallonta ba Yau sosai take fuskantar gidan ma, ko tsoron su gantabataji, har wani karkata kanta take tana hango lungu da saqo na gidan (🀣) Zagaya wajan tafara yi,tana miqa wuya saikace wanda a kace mata Ishraqan tana zaune ne a compound "ke kam Narasa meyasa kika liqewa wajan nan Minal" Juyawa tayi ta kalli anty Amrah tayi murmushi tace "Anty Amrah inason nasake ganin wannan matar dakikamin Bayanin tane ranan nan" Cikin mamaki Amrah tace "wacce mata kenan?" Hankalinta Yana kan gidan batare data kalleta ba kai tsaye tace "ANTY ISHRAQA" Amrah tayi murmushi tace "tana birgeki kenan" Itama cikin murna ta juyo tana kallon Amrah, har Hakan yabawa Amrah mamaki ganin ita ba gwanar Fara'ah bace, babu wanda zaice yaga Minal tana dariya tunda sukazo gidan Cikin farin ciki tace "eh Anty Amrah, tana birgeni sosai, inama ace zata rungume ni aqirjinta ko sau daya ne" Amrah ta zaro ido tace "ta rungume ki Minal?" (😳) Hankali kwance tace "eh wallahi" Amrah ta jinjina kai tace "Eh lalle Minal bakida hankali" (πŸ˜‚) Daga nan tajuya tayi cikin gida tabarta awajan Ko kadan bataji haushin maganar da Amrah tafada mata ba, saima cigaba da Kallan gidan datayi, tana jira taga futowar Ishraqa amma Shiru Bata ganta ba, haka tayi ta zama harta gaji da jira tajuyo cikin gidan itama Tazo wucewa ta saitin window din d'akin Anty Lubna taji tana waya, kuma batayi qasa da muryar taba, Ana iya jiyo abinda take fada Haka kawai ta tsinci kanta da tsayawa awajan, gabanta ne yayi mummunar faduwa yayinda taji Anty Lubna tana cewa "Zansaka masa maganin a cikin abincin sa, insha Allah wannan Karon zamuyi nasara akansa, Yana can yanata fishi, aini inde Akan wannan shegiyar insaaf dinne zan'iyayin komai, natsaneta tun kafin nasan ko wacece, suma layun duk zan binnesu yau, kuma Insha Allah baza'a samu wata matsala b.... " Bata gamajin wayar ba jikinta ya dauki rawa, gabanta yaci gaba da faduwa, har wani duhu duhu take gani, Ahankali tajuya zata koma baya, amma inaaaa! Kafafunta sun gaza daukar ta, dole Sai awajan ta zube, yanda kasan yar bori haka ta Zauna, Sai numfashi take saukewa yayinda idonta yake kan windon d'akin Anty Lubna, kanta tacusa cikin Kafafunta tana furta kalmar "innalillahi wa Inna ilaihirraji'un" Yaya Asim zata binnewa laya? Tome zata saka masa a cikin abincin? Karfa ta kasheshi, wata zuciyar tace toke ina ruwan ki? ba'a haka kikazo kika samesu ba? Wata zuciyar tasake cewa aikuwa tana kasheshi kanki zata dawo, (🀣) Idan Bata kasheki ba kece mace ta farko da zata sa akoreki daga gidan Cikin sauri ta tashi tabi ta wata hanyar Takoma falon, ya kamata ace ta taimaka masa, ko banza shine mutum nafarko daya taimaka mata alokacin da mutanan qauyensu suka gujeta, Alokacin da wanda take ganinsu kamar iyayenta suma suka gujeta Afalon tazauna tayi tagumi hannu bibbiyu, dole zata Sawa Anty Lubna ido taga inda zata binne layun, abinda takasa ganewa shine dama Anty Lubna tana da sa hannu wajan son kashe Yaya Asim? Kokuma saboda insaaf dinne zatayi haka kamar yanda taji tana fada? To Wai wacece INSAAF dinne? Kuma dawa take wannan wayar? Duk wanda ya ganta awannan lokacin yasan kawai de tana zaune ne, amma kana ganin ta zaka san cewa hankalinta baya jikinta Anty Amrah tafuto falon itama, ganin Amina yau azaune afalo tana kallo Sai tayi mamaki, tazauna ta dauki wayarta tana danne danne Widad ce tafuto daga d'akin mamy kai tsaye wajan Amina ta nufa tazauna akusa da'ita tace "Kema kinayin kallo?" Kafin Amina tabata amsa Anty Amrah Tace "fada mata dai widad, kema dole kiyi tambaya tunda Kinga yau tabamu mamaki ta zauna afalo tana kallo" Murmushi Tayi takama hannun widad tace "inayin kallo mana Widad" Zaro ido yarinyar tayi tace "laaaa dama kema kinsan sunana? Toke ma ya sunan ki?" Amina ta dauki yarinyar ta dorata Akan cinyar ta tace "Sunana Amina" Dariya widad tayi tace "to Amina zakizo kina tayani wasa a dakina? Kinga momy Bata zuwa munayin wasa da baby ta, shikuma Daddy na kullum kullum baya dawowa da wuri" Amrah tace "Widad I will slap you idan kika sake cewa Amina, Anty Minal sunan ta" "to uwar 'yan tsari, sarkin azar6a6i, taso mutafi dan uban ki" suka tsinci muryar Lubna tana zagin widad, tana qarasowa kuwa ta fizgi hannun widad tare da makawa Amina harara, suka tafi, Amrah tabi bayan Lubna da kallo tare da girgiza kanta ta tashi takoma cikin daki Jikin Amina yayi sanyi, amma haka ta daure taci gaba da zaman dole Afalon, tanaso taga gudun ruwan Anty Lubna Har gab da magrib tana Zaune Afalon, bataga Anty Lubna tashiga kitchen ba, kuma tun shigar su daki da widad har yanzu Bata futo ba, Sai da aka fara Kiran sallar magrib sannan tafuto ita kadai ko lura da Amina datake falon batayi ba, Sai sauri take tana gyara gefen zaninta Ahankali Amina ta tashi tabi bayan ta, a bayan labule ta 6uya, tsaf tagama Kallan Anty Lubna data tsugunna a bayan d'akin Asim tana tone qasar wajan, Sai waige waige take Dan Kar a ganta, Amina tana ganin wajan tasaki labule n data 6uya aciki , tajuya cikin daki da sauri tana tabbatar da hasashen ta Tunda tashiga d'akin Bata sake futowa ba, ba tasan wainar da suke toyaba, abincin dare ma Kasa fita ci tayi, dama batason Zaman dinning dinnan, duk Bata sakewa Lokaci yanaja, ta kwanta amma idonta biyu batayi bacci ba, tana jin Anty Amrah ta shigo d'akin amma Sai tayi Shiru kamar me bacci, itama Amrah batayi mata magana ba ta kwanta tafara bacci, tayi tunanin tana bacci Amina dai Sai juyi take ita kadai, har dare ya tsala, Agogon d'akin ta kalla taga karfe biyu da rabi, Ahankali tatashi tabude kofar d'akin ahankali tafuto, falon ta kalla taga duhu duk an kashe komai ankwanta, babu alamun tsoro ko kadan a ranta, haka tabude kofar falon tafuto, Gari yayi Shiru musamman ma unguwar su daba kowa ne yake zama a cikin taba, bakajin motsin kowa, Shima mai gadi ya kashe wutar d'akin sa, babu qaran komai saina gyare, wajanda Anty Lubna tabinne Laya can ta nufa, Ahankali tafara tonewa saboda Kar tayi qwaqwqwaran motsi Asim yajiyo ta saboda bayan d'akin sa ne, duk wanda zaiyi abinda Amina tayi to tabbas saiyaji tsoro, amma ita abun mamakin ko kadan babu tsoro atare da'ita, hankalinta kwance tacire duka abinda Anty Lubna ta binne, sannan ta daddage ta wullashi bayan katangar gidan, sannan tarufe wajan kamar yanda yake, Takoma cikin falon, kofar falon tarufe ta jingina a jiki tasaki wata irin Ajiyar zuciya tare da lumshe idonta Wani irin haske ne ya baiyana a cikin falon, duk da idonta a lumshe suke saida taga hasken, Ahankali tafara Bude idonta harta budesu gaba daya, dashi tayi tozali yafuto daga d'akin sa hannunsa dauke da ruwan gora, daga shi Sai gajeren Wando, murdaddan jikinsa ya sake futowa sosai, ga gashi ya kwanta Akan qirjinsa, Bata taba ganin qirar namiji a baiyane hakaba, shiyasa tana ganinsa haka ya tsorata ta sosai, gabanta yafara dukan Tara-Tara, cikin ranta tace Yaya Asim... dama haka jikinsa yake? πŸ€” Kuma yafuto falo babu komai a jikinsa dagashi Sai gajeren Wando? Sunkuyar dakanta tayi, tafara tafiya sum sum zata shige dakinsu Takun da yaji ne yasa yajuya da sauri, yayi mamakin ganin ta, metake yi afalo a'irin wannan yanayin? Gaba daya Sai kunya ta kamashi, karfa yarinyar nan ta raina shi, ya sunkuya ya kalli jikinsa cikin sauri yahade qafafunsa waje daya (πŸ™ˆπŸ™Š) Yana dagowa ya ganta zata shige daki, nan take ya daure fuskarsa yace "ke zonan" gabanta ne ya tsananta faduwa ahankali ta juyo tazo gabansa ta taugunna batare data kalleshi ba, tace "gani Yaya" Duk da yaji Dadin muryarta dakuma yanda takirashi da sunan hakan bai Hana shi daure fuska ba, bayason tagama kallansa ta raina shi "me kikeyi afalo bakiyi bacci ba?" Tambayar tashi tazo mata a bazata, tarasa wacce amsa zata bashi, cikin inda inda tace "dama... dama... am kallo nazo zanyi.... Shine naleqa waje nadawo" Zuba mata ido yayi Yana kallanta batare da yayi magana ba, dataji Shiru saita dago kanta ta kalleshi karaf idonta yasauka a cikin nasa, cikin sauri ta maida kanta qasa, Shima kallanta yayi ya sake tsuke qafafunsa Yana hadesu waje daya (πŸ€£πŸ™ˆ) Sannan yace "kawomin cup a kitchen" Cikin sauri tatashi tayi kitchen din dama Zaman ya gundureta, tana kawo masa cup din tasake taugunna wa tabashi, karba yayi ya ajiye shi aqasa sannan yabude gorar ruwan yafara zubawa a cup din, saida yazuba sannan yasa hannu zai dauka cup din ya qwace daga hannunsa zai Fadi awajan, cikin sauri tasa hannunta zata tare cup din Shima yasa ka nasa hannun, hannunsa bai sauka ko'ina ba Sai Akan nata hannun, dago kanta tayi tana kallonsa Shima yazuba mata ido Yana Kallan manyan idanuwanta batare da sun janye hannayensu ba Adede lokacin Lubna tabude kofar d'akin nasu tafuto taana zuba hamma, ( ) tashafa wajan baccinsa taji baya nan, kuma ta duba toilet ma baya nan, bakin data Bude tana hamma saita Kasa rufe shi tazuba ido tana kallon su baki bude(🀣) Lokaci daya ta nemi baccin dayake idonta tarasa, huci tafara yi kamar zakanya ta nufesu, batayi wata wataba ta hankade Amina daga kusa dashi tafadi can gefe Har hakan yayi sanadiyar faduwar cup din qasa, cikin fishi tace "annamimiya, uban me kikeyi anan Keda mijina? Ki tashi kibar nan wajan tun kafin nazama ajalinki" Ahankali ta miqe tsaye tace "Anty Lubna bafa komai nake...." "banason jin komai kibace kibar nan wajan nafada miki" Girgiza kanta tayi tajuya tayi cikin dakinsu, Lubna ta juya ta kalli Asim daya zuba mata ido Yana kallonta Idonsa yayi jajir, tasan idan tayi magana tsaf zai Iya wanka mata Mari, Dan haka batace masa komai ba tashige daki tana sakin tsaki, sake kallonta yayi Yana jinjina rashin taarbiya irinna Lubna, yanzu shi takewa tsaki? Haqiqa tafara kawo shi wuya, Idan ya tashi yimata hukunci ba zataji dadi ba, in banda shirme metake tunani zai aikata da wannan yarinyar dayasan cewa idan yayi aure da wuri zai haifi kamarta? Amina kuwa bataji Dadin abinda Lubna tayi mata ba, to Naga itama din mijinta ne, meyasa zatake mata haka? Cikin ranta tace wallahi Allah saiya saka min, kuma niba annamimiya bace, saide ke Washe Gari da safe weekend ne kowa Yana gida, Amina Bata tashi da wuri ba kasancewar ta Dade batayi bacci ba, Sai wajan karfe goma tafarka, azabure tatashi kasancewar tatuna da maganar Lubna, idanunta tahau murtsikawa ta diro daga kan gadon tashiga toilet ta wanke bakinta da idonta tafuto falon, duk mutanan gidan suna nan banda Daddy Anty Amrah tashige daki tana amsa wayar Amjad "kakusa zuwa ne? Kaga niba wani kitchen dazan shiga, Kai inde baka takurani ba bakajin dadi kwata kwata rayuwarka" (🀣) hamdala Amina tayi dataga Asim baya nan, qila baici abinci Bama kwata kwata Qamshin girki taji Yana tashi a kitchen, tadan leqa saita hango Anty Lubna tana girki, haka nan taji zuciyarta takasa samun nutsuwa da wannan abincin, Bata saniba ko acikinsa tazubawa Asim maganin, idaanma tazuba idan ma Bata zubaba insha Allah bazata Bari yaci abincin Nan ba Zama tayi akujera tana tunanin dabara, agabanta Anty Lubna tagama jera abincin akan tire, ta qwalawa Amrah Kira "Amrah!, nagama ki futo kikai sauran kan dinning, gana yayanku nazuba masa nasa daban zan kai masa daki" Tazo wucewa tagaban Amina ta kalleta ta watsa mata harara, Amina ta yunqura ta tashi kamar zatayi cikin d'akin su da niyya tabangaje Anty Lubna, aikuwa abinci ya 6are (πŸ˜‚ ) Tana ganin abincin ya zube tayi hamdala a ranta Anty Lubna kuwa baqin ciki ne ya kamata kamar ta mutu, maganin da suka dauki tsawon lokaci suna so su sakawa Asim a abinci yau tasamu tasaka masa shine wannan yarinyar zata zubar da abincin? Ta daga kai ta kalli Amina, tasaka yatsanta abakinta Tama rasa me zata mata taji sanyi, Amina ta sunkuya tahada mata kayan daya zube ta dago tace "Anty Lubna Dan Allah kiyi haku...." Bata qarasa ba Lubna ta zabge ta da wani irin gigitaccen Mari ( ) Akan Idonsa yaga Marin da Lubna ta zabga mata, ya tsaya a bakin kofar falon nasu yanaso yaga gudun ruwan ta Ihun kukan datasa ne yasa Amrah futowa daga d'akin su da gudu, tana ganin Yaya Asim a bakin kofar falon ransa a mutuqar 6ace, Sai tayi Shiru Anty Lubna tasake kallon Amina cikin haushi, saboda tayi mata wannan Dan Marin ne yasa tabude baki take mata wannan uban ihun? Aidama haushinta takeji, da baqin cikinta ta kwanta cikin dare saboda ta ganta da mijinta, cikin bacin rai tace "Dan uban ki Nasha wahala na yi girkin zaki zubar min dashi? Tsugunna ki tas ki debeshi" Tana kokarin tsugunna wa tasake dauke ta da wani Marin wanda ya gagata Amina, cikin tsawa yace "Lubna!!!" Atare suka kai kallonsu wajan kofar, Amina tashige cikin dakinsu da gudu tana kuka, cikin falon ya qara so cikin fishi yace "waike Lubna wacce irin mahaukaciya ce ne?" Amrah tana ganin haka tayi d'akin mamy tadugu zata sanar mata, saboda Bata taba ganin ran yayan nata yabaci haka ba Cikin bacin rai itama tace "nikake cewa mahaukaciya saboda wannan yarinyar marar asali?, kasan wahalar danasha wajan wannan girkin zatazo tazubar min dashi?" Nunata yayi da hannu yace "to waye zaiyi abinda kikayi yanzu inba mahaukaci ba? Yarinyar dabatafi ki zaneta da tsinken tsintsinya ba shine zaki kamata kina duka kamar Kin samu baiwa? Dududu nawa yarinyar take dazaki mata irin wannan dukan? Kokuma bakya tunanin irin wannan dukan zaisata ta kangare? Duka lalata Yaro yake, idan kika kuskura kika sake dukanta wallahi Sai ranki yabaci " Yana fadar haka yabi bayan Amina cikin d'akin su Mamaki, taraddadi, dakuma faduwar gaba duk suka taru sukayiwa Lubna yawa, Anya kuwa Asim bai fara samun matsala Akan yarinyar nan ba? Kode ba kalau tabarshi ba? πŸ€” Yanzu wannan yarinyar zai Dubi idonta yace mata tadaketa da tsinken tsintsiya? Saikace Widad? Yana shiga d'akin ya ganta ta kifa kanta Akan gado tana rusgar kuka, tausayi tabashi sosai, shide Yana tausayin yarinyar Ahankali ya zauna agefen gadon dab da'ita, so yake yabata hakuri, amma yarasa mezai ce mata, shide ba lallashin matarsa yake ba bare ya qware wajan lallashi, komaai saide ayi masa, kamar bakinsa Yana masa nauyi yace "kiyi Shiru" Dago kanta tayi ta kalleshi, batare da tunanin komai ba tafada kan faffadan qirjinsa ta rungume shi sosai tana cigaba da kuka Mamaki ya kama shi, yarinyar nan kuwa kalau take? Meyasa zata rungume shi,sake kallanta yayi yaga yanda ta kwantar da kanta Akan qirjinsa,Kasa rungumeta yayi da hannayensa, kukan datake dakuma yanda yake jin tudun nashanunta Akan qirjinsa shine ya haddasa Masa shiga cikin wani yanayi, gakuma tsikar jikinsa Sai tashi take, Ahankali kamar mai tsoron wani abu yasa ka hannunsa ya rungumeta sosai,Yana bubbuga bayan ta alamar lallashi, ita datake kuka maimakon ace itace take sauke Ajiyar a zuciya Sai abin yazo a bazata, domin kuwa wata irin wawuyar Ajiyar zuciya Asim yake saukewa Ajere (πŸ˜‚) Lubna tabiyosu cikin d'akin cike da masifa, amma saide me? A halin data gansu ne yasa tajuya cikin tashin hankali ta Dora hannu aka, tasaki ihun kuka "nashiga uku na,nashiga uku shikkenan ta qwacemin mijina" Asim yanajin kukanta yajanye jikinsa daga na Amina ahankali, ya tashi yakulle kofar d'akin,(😳) sannan yadawo yazauna aqasan gadon, yakamo hannyen Amina datake zaune Akan gado yariqe hannayen nata cikin nasa,yazubawa fuskarta ido Yana kallon yanda gashin idonta suka jiqe, saboda kuka Ita kuwa Amina Kasa dago kanta ta kalleshi tayi, hawaye Yana silalowa daga idanuwanta zuwa kan kumatunta, gashi babu Damar gogewa ya kama hannayen nata duka biyun yariqesu cikin tattausan hannunsa Mamy da Amrah ne suka qara so wajan, futowar ta kenan daga wanka Amrah tace mata gidan nasu ba qalau ba tazo tayi musu magana Lubna tayi wani irin zama a falon tana ihun kuka Minal ta qwace mata miji Mamy ta qarasa bakin kofar d'akin tafara nocking Tofa, wata dramar Sai a gidan Asim, 🀣🀣🀣 Sharhi pls ✍🏻 Amnah El~Yaqoub [2/9, 11:07 PM] El~Yaqoub: INSAAF Writing by:Amnah El yaqoub Like my page on Facebook πŸ‘‡πŸ» https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 15&16 Yana jinsu suna nocking amma ko alamun tashi baiyi ba, asalima hannunta dayake cikin nasa yafara murzawa ahankali,shikansa baisan dalilin dayasa yake murza mata hannun ba, amma bazai iya daina wa ba saboda sabon al'amarin dayake shigar sa, Kasa dagowa tayi ta kalleshi, gaba daya yayi mata wani irin kwarjini, shidin babban mutum ne ba qananun Samari ba irinsu Amjad..., muryarsa ya sassauta cikin sigar rad'a yakirata "Minal" Dago idonta tayi ta kalleshi, idonta har yayi ja, hawaye ya zubo daga cikin idonta guda daya, cikin ransa yace "yasalam..." Tunda take dashi yau ne Karon farko daya taba Kiran sunan ta, saita ji abun wani iri, saboda bai sababa, saide koda yaushe yace mata "ke", kokuma Ke zonan, ke tashi mutafi, ke dauko min abu kaza, yanda yake murza hannunta saiya hakan yafara haddasa mata shiga cikin yanayi, Ahankali tace "na'am" Tashi yayi daga qasan gadon yadawo dab da'ita ya zauna batare daya Raba hannunsa danata ba Cikin rad'a yasake ambaton sunanta akaro biyu "Minal" Muryarta na rawa ta amsa masa, hannunta yasaki yasake matsowa dab da'ita har suna jin numfashin juna, hannayensa yasaka yariqe fuskarta dashi, sannan yazuba mata ido Yana kallanta batare dayace komai ba,d'an qaramin lips dinta yake kallo,wanda yake ji kamar yadora nasa akai, Ahankali tadago kanta tazuba masa manyan idonta, idonsu ya sarqe dana juna, wannan Karon Bata janye idonta daga cikin nasaba, haka Shima baice mata komai ba, yade riqe fuskartata da hannunsa Yana kallonta kamar yasamu sabuwar halitta, idonta ne yayi raurau yafara kawo qwalla, Ahankali ya Matso da fuskarsa kusa da Tata kamar mai shirin yimata kiss, cikin rad'a yace "ki.... kiyi... hakuri..." Kallansa tayi, sauran qwallar datake riqewa suka zubo mata, ba kukan komai takeba saina tausayin sa, Yana tare da mata amma baisan tana masa zagon qasa ba. Sake sassauta Muryarsa yayi yace "kinji..." Hannunta tasa ta share hawayen tace "babu komai Yaya, na haqura" Kallanta yasake yi yace "are you serious?" Jijjiga masa kai tayi kawai. Mummunan bugon da a kayi wa kofar ne yasa yasaki fuskar Tata ahankali sannan ya tashi ya nufi kofar yabude Gaba dayansu ne suka Danno kansu cikin d'akin (πŸ˜‚) Mamy, Amrah, da Anty Lubna wadda fuskarta tayi sha6e-sha6e da hawaye, Kallan Asim tayi dayake tsaye sannan ta kalli mamy cikin kuka tace "gashinan mamy ki tambayeshi, wallahi rungume ta yayi, male-male naganta a qirjinsa" ( ) Gaban Amina yayi wata irin faduwa, idanunta yayi tsilli-tsilli tana kallon mamy Shikuwa gogan babu alamun damuwa afuskar sa yara6a ta gefensu yafice daga d'akin Anty Amrah tafice daga d'akin tana girgiza kanta, tayaya Yaya Asim zai rungume Minal? Mamy ta kalli Lubna tace "kiyi hakuri Lubna, zanyi magana dashi" Daga nan taja hannunta suka fice daga d'akin, Anty Lubna tadawo d'akin hannunta dauke da ruwa a cup, miqawa Amina tayi tace "ki karba Kisha Minal" Babu musu tasa hannu ta karbi cup din tashanye duka ruwan, sannan tasaki Ajiyar zuciya, Anty Amrah tayi qasa da murya ta kalli Amina tace "Minal waida gaske ne yaya ya rungume ki?" (πŸ˜‰) tafadi maganar cikin sigar son jin gulma Cikin sauri ta girgiza kanta "a a Anty Amrah, ni be rungume niba" Murmushi Amrah tayi tasake kallanta da kyau "to kuma nida nake qawar takima boyemin zakiyi? Dan Allah ya rungume ki?" Sake girgiza kanta tayi "Anty Amrah bafa haka bane" "bawani nan, kede kawai kice yau Yaya yarage zafi" (🀣) Amina takalleta tace "Anty Amrah kifahimce ni..." Katseta Amrah tayi "bawani fahimta yarinya, tome yake fada miki dakuka kulle d'akin?" Kai tsaye tace "hakuri yabani" Cikin sauri Amrah tace "Dan Allah da gaske kike? Yaya Asim ne yabaki hakuri da kansa?" Cikin mamaki tace "baya bayarwa ne?" Amrah ta jinjina kanta tace "lalle bansan wacce irin sa'ah gareki ba, nida zai aure ki ma danaji dadi wallahi, Anty Lubna kishin ta yayi yawa wallahi, kuma yawanci masu zafafa kishin nan Allah yafi jarabtar su dayi musu kishiya, domin ya gwada imaninsu" Tana Gama maganar ta tashi tsaye yace "qanina yakusa dawowa daga Yola, Bari naje bakin gate na taro shi" Amina ta daga mata kai, Wai qaninta, dama Anty Amrah tanada qanine? Amrah nafita falo taci Karo da Amjad harma ya shigo gidan, hannunta tabude tatafi da sauri kamar zata rungume shi tace "oyoyo d'an qanina" (🀣) Amjad ya kalleta, ya sake kallonta daga Sama har qasa, yadaga murya yace "Wai ke Anty Amrah meyake damunki ne Dan Allah?,yanzu inda tare muke da wasu haka zaki dizgani, Wai qaninki" Bacin rai sosai a saman fuskar sa, ya nemi waje yazauna a daya daga cikin kujerun falon Itama zama tayi tace "Dan rainin hankali, danma kasamu inama oyoyo, waye yazo yayima haka a gidan?" Cikin fada yace "eh Karki qarayi inde saikin cemin qaninki, harda wani god'ai god'ai dani Saina zauna kina cemin qaninki" "toba qanin nawa bane? Nawa kake? Fina kayi?dakaqi dakaso Anty Amrah dole, kuma nice de gaba dakai, babu yanda zakayi dani" Cikin bacin rai yace "OK haka kikace?" Itama cikin dakewa tace "yes" Yace "OK, to wallahi kinemi abokin shawararki, bade niba, samarin ki kowa kika kwaso saikinzo kin nemi shawara ta, todaga yau ta qare, kinemi yayanki, wanda yafi ki, saiya baki shawara" (😠) Tace "inde Akan nace qaninane kake wannan ihun, wallahi Amjad bazan daina ba, qilama har goyaka nayi lokacin dakake Yaro, wayasani ma ko harda wanka nama (😳) Kawai daga zuwan ka kamar wani jarababbe kazo kahau ni da masifa" Amjad yayi Shiru Yama rasa mezai ce mata (🀣) Da Hankalinsa mamy take musu wanka gaba dayansu, amma saboda tsabar rainin hankali shi zata kalla tace tayiwa wanka, harda cewa kamar jarababbe, kallanta yayi Shima yace "aini kamar jarababben ne, ke kuwa jarabar Cema gaba dayanta" (🀣) Kallansa tayi tace "yayi kyau, ka gwadamin hankali, gobe ma idan zaka dawo zan futo ina rawar jiki, na tarbeka" daga nan tafara yunqurin tashi Hannunsa yasa ya fuzgota saigata azaune Akan kujera, Kallan mamaki tayi masa, yanzu Amjad ne yake da wannan qarfin har ya fuzgota haka? Shikuma baima lura da irin kallon datake masa ba, yayi qasa da murya yace "haba Anty Amrah, ai Bama 'yar haka dake, menene kuma rayuwar?" Cikin fishi tace "to ai Kaine kake neman rainani Amjad, saboda kaga kafara ajiye gemu" Cikin qasa da murya kamar bashi ba yace "kifadi komai ma baji, inde babu mutane awajan (πŸ˜ƒ) ina jama'ar gidan suke ne?" Ajiyar zuciya tayi tace "kowa Yana d'akin sa, ai yau baram baram akayi in fadama" Zamansa ya gyara yace "haba? dawa akayi?" "Yaya Asim da Anty Lubna, Akan Minal ne fadan, saura kadan ya Mari Anty Lubna, aikuwa nabar wajan ban tsaya ba, Anty Lubna Sai ihu take Wai Minal zata qwace mata miji, Wai ta gansu itada Yaya Asim harma ya rungume ta" Gaban Amjad yafadi yace "waida gaske kike?" Amrah tace "haka de Anty Lubna tace" Cikin sauri ya miqe zai tafi d'akin mamy, hannunsa ta ruqo tace "ina zaka?" "zuwa zanyi wajan mamy, wallahi inason yarinyar nan, tun lokacin dana fara ganin ta" ( ) Tace "aikuwa karka shiga yanzu, Dan naji maganar Yaya acikin d'akin, kabari sugama magana shida mamy Sai kaje" Cikin damuwa yakoma kan kujerar ya zauna, yace mata "ina abinci na?" Nuni tayi masa da dining tace "gashi can a dining, Anty Lubna ce tayi" Girgiza mata kansa yayi, sannan ya nufi dining din *** ***** *** "Asim, kafadamin gaskiya, wacce irin magana naji Lubna ta nayi? Da gaske ne ka rungume Minal?" Karon farko daya fara yiwa mahaifiyarsa qarya, koda yaushe baya boye mata komai, kullum cikin fada mata gaskiya yake, qeyarsa ya Sosa sannan yakalleta yace "mamy...runguma kuma?" Tace "Asim matarka zatama qarya ne? Baka rungume Minal dinba?" Shima cikin dakiya yace "to mamy saboda me? Niban rungume taba" "to koma de menene banason naqara jin hakan, kadena biyewa shirman Lubna" Wata irin Ajiyar zuciya yasaki a6oye, sannan yayi hamdala a ransa da mamy Bata ganoshi ba, kansa aqasa yace "insha Allah mamy" Tace "Allah yayi maka albarka, tashi katafi" Babu musu ya tashi yafuto daga d'akin, mamy tabishi da kallo, itade tasan Asim baya mata qarya, amma wannan Sosa qeyar da yayi alamu ne na rashin gaskiya, kuma tunda take da Asim baitaba kawo mata yarinya yace yanaso ba, ita kanta Lubna tasan cewa bayaso amma ahaka ya aureta, to kode son Minal din yake? Tayaya zata yarda cewa bai rungume taba? Bayan kulle d'akin sukayi? (🀣) Kuma sunaji Ana nocking sukaqi budewa, idan ba rungume ta yayi ba to nasiha yake mata?πŸ€” Ajiyar zuciya tasaki tana fatan ace Bahaka bane, Dan batasan tashin hankalin da Lubna zata shiga ba Akan haka, kuma kowa Sai hankalin sa ya tashi Akan haukan kishinta Amjad ne ya shigo d'akin, Yana zuwa yafada jikinta, cikin shagwaba yace "mamy I miss you sosai wallahi" Kansa ta shafa tace "Anya kuwa Amjad wannan aikin naka baka saka shiririta acikinsa? Daga zuwa wajan aiki yan Kwanaki harka dawo gida?" Cikin shagwaba yace "uhm... Allah mamy ni bazan iya irinna Yaya ba, bazan iya wata daya batare dana ganki ba" Taji Dadin furucinsa sosai, tace "Allah yayi muku albarka autana, Allah yaraya minku" Sake shigewa jikinta yayi yace "Amin, mamy wata magana zamuyi" Dagoshi tayi daga jikinta, sannan tayi masa kallon fahimta tace "inajin ka, wacce irin magana?" Kallanta yayi yace " mamy dama zan fada miki ne, inason Minal, inason in aureta idan kun amince Keda Yaya" Murmushin manya mamy tayi, cikin ranta taji dadi sosai, ko banza Amjad yakawo musu maslaha Akan rikicin Lubna da Asim, tace "to Allah ya tabbatar mana da Alkhairi, zan sameshi muyi maganar dashi insha Allah" Cikin murna Amjad yace "yes...shiyasa nake sonki mamy na, Allah yabar mana ke" yakama hannunta yayi kissing hannun, sannan yafuto daga d'akin cikin murna *** ****** *** Zaune suke a d'akin su washe Gari, itada Amrah Amrah ta kalleta taga tayi Shiru tana tunani, ta matsa kusa da'ita tace "Minal, in baki wata shawara mana" Kallonta tayi tace "menene Anty Amrah?" Amrah takama hannunta tariqe tace "Bari kiji in fada Maki, Kinga idan zaki sake acikin gidannan ki dinga harkokin ki toki sake, wallahi idan kika tsaya Anty Lubna tana marinki, bakya ramawa, rainaki zatayi, kisaki jikinka, kema gidanku ne, ki dinga daukan wanka kina kwalliya, kisaki ranki, kiyi walwala, kiyi Fara'ah da dariya kamar kowa, babu wanda yataba ganin dariyarki a gidan nan Minal, kullum fuska babu Fara'ah kamar fuskar Yaya Asim "(πŸ˜‚) Murmushi tayi mai ciwo, tatuno asalinta, ba tasan wacece itaba,ba tasan iyayenta taba, waya sani ma ko shegiya ce shiyasa aka wullarta, idanunta yayi raurau kamar zatayi kuka tace"wacce irin walwala Anty Amrah,banda kowa, bansan tushenaba, bansan ta Yaya aka haifeni ba, ina Naga wani Damar da zanyi kwalliya?Kuma ni ban'iya Bama " Amrah tasake matsowa tace" Minal, kowa baya wuce qaddarar sa, ni kinsan tawa kaddarar ne? Nayi soyaiya da Al'amin, munshaqu da juna, kowa Yana farin-ciki da hakan, saida nagabatar dashi awajan Daddy da Mamy suma suka ce yayi, bashida matsala, Rana daya yazo wajena Yana kuka yacemin anyi masa mata agida, auren dole za'ayi masa, nashiga cikin damuwa,Yana kuka ina kuka, alokacin yace muyi alqawari bazamu taba rabuwa da juna ba, komin Daren dadewa injirashi zaizo muyi aure,lokacin ina shekara a shirin da biyar,Minal shekara daya tawuce, biyu ta wuce, Shiru babu labarin Al'amin, ni kuma abin baqin cikin shine yanda na yarda dashi, duk abinda yafadamin ina yarda dashi, saida abin ya ishi Yaya Asim yaje neman Al'amin da kansa, domin yaji meyake faruwa ne, lokacin dayaje bai samu Al'amin ba, amma yahadu dawani maqocinsu, anan aka sanar dashi cewa Al'amin ba auren dole aka masa ba, kawai yaudara ta yake, yarinyar daya aura ma yar unguwar suce,kuma kowa yasan Al'amin Yana son yarinyar, a ranar da Yaya Asim yazaunar dani yayimin fada na hakura da Al'amin, kwana nayi banyi bacci ba, Minal niban taba zaluntar kowa ba, ina zaune da kowa lafiya, amma ga abinda wanda nayarda dashi yayi min, har gobe idan nayi sallah ina roqon Allah, idan nice na zalunceshi, Allah yasa ka masa, idan shine ya zalunceni Allah yasa ka min, Minal shekaru na talatin yanzu babu aure, Abin Yana damuna sosai, amma babu yanda zanyi da qaddarar ubangiji, gashi ina walwala ta, ina harkokina kamar kowa, duk abinda yasamu Bawa yamiqa lamuransa ga Allah Minal, da wannan tunanin da kike da Addu'ah kika Dage da'ita, zaifi, amma Dan Allah ki saki ranki mu dinga abinda mukeso a gidan nan, ni tunda naganki sainaji kamar nasami 'yar'uwa, tunda dukansu yan'uwan nawa maza ne, ba kamar mace ba" Minal tasaki Ajiyar zuciya ta kalli Amrah tace" yanzu Anty Amrah kedin har kinyi shekara talatin? Naga jikinki bai nuna hakan ba" Amrah tayi murmushi tace "inda nasake godewa ubangiji na kenan, yanzu babu wanda zai ganni nida Amjad yace nagirmeshi" Zaro ido Amina tayi tace "waida gaske kinfi Yaya Amjad?, dama shiyasa yake cemiki Anty Amrah?" Murmushi Amrah tayi tace "na fishi Minal, shekara daya nabashi, inde Kasa Allah acikin lamuranka ai zai taimakeka Minal, kema kisaki jikinki, kiyi gayu, ki daina yin Shiru, kuma inde kwalliya ce Karki damu zan koya miki" Cikin mamaki tace "gaskiya hakane Anty Amrah, insha Allah Nima zan kamanta kamar yanda kika bani shawara, kuma dama Yaya Asim yace zai tayani duba iyayena" Amrah ta kama ha6arta tana kallon Minal tace "Wai yaushe har kuke haduwa ne kuke fira ke dashi?, nifa mamaki nake, ganinake kamar ba Yaya Asim dinmu ba, Anya kuwa Minal babu wata aqasa?" Rabonta da shagwaba harta manta, amma yau saita tsinci kanta dayin shagwabar, tace "Allah Anty Amrah babu komai" Amrah tace "ai shikkenan, idan tayi tsami maji" (πŸ˜‰) Daga nan tafuto daga d'akin tana tunani a ranta, Amjad dinne zai samu kokuma Yaya Asim? πŸ˜‚ *** ****** *** Dawowarsa kenan daga wajan aiki, fuskarsa babu wata Fara'ah kamar kullum, Yana sanye cikin suit da tayi masa kyau sosai, Kai tsaye d'akin Mamy yawuce, Yana zuwa ya ganta tana sakawa d'akin nata turaren wuta, brief case dinsa ya ajiye Akan gadon, sannan yacire jacket dinsa, itama ya wullata kan gadon, sannan yafada gadon Shima ya kwanta, tare da fadin,"Wash! sannu mamy" sannan ya lumshe Idonsa, inda ace zai samu maiyi masa tausa yanzu daya so hakan Murmushi tayi tace "kaje wajan matarka ne?" "no, ban shiga ba, sonake nafara ganinki mamy" Tace "naji, to ai kaganni, kaje kaga matarka, Kaci abinci saika kwanta acan kahuta, cinyata Bata hutaba, gadona ma bazaku barshi yahuta ba Asim" Murmushi yayi yabude Idonsa batare da yayi magana ba Turo kofar d'akin tayi ta shigo bakinta dauke da sallama, jin zazzakar muryar ta ne yasa yakai Idonsa ahankali ya kalli kofar Idonsu ne yahadu dana juna,Yana daga kwancan yazuba mata ido, Idonsa ne yasauka Akan qirjinta, yatuno lokacin data rungume shi, yaji wani irin laushi, cikin sauri ta dauke idonta itama, tana tuno ranar data fada jikinsa ta rungumeshi, da yanda ya sake matseta a jikinsa Yana sakin Ajiyar zuciya , shi kuwa Kasa dauke Idonsa yayi a kanta, yanajin wani irin yanayi na shigarsa Gaba daya saita diririce tarasa mema zatace, amma data tuno shawarar Anty Amrah, saita ji qwarin gwiwa yazo mata Wani irin murmushi tasaki tace "mamy sannu da aiki" Sake Bude Idonsa yayi ya kalleta da tsananin mamaki, dama yarinyar nan tana murmushi? Mamy kuwa kallonta tayi tace "sannu Minal, yau kece adakin nawa?" Gabanta ne yafara faduwa ganin yanda yazuba mata ido Yana aikin kallonta, tace "eh mamy, dama nazo neman Anty Amrah ne" "Amrah Bata nan inaga tana wajan Lubna, kije d'akin Lubna may be suna tare" (🀣) Cikin ladabi tace "to mamy kawo na qarasa miki aikin" Mamy tayi murmushi tace "a a Minal, jeki hutawarki, Aina gama ma" Tace "to mamy afuto lafiya" Sannan ta kalleshi, cikin sauri yadauke kansa, itama cikin ranta tace bayan nakama din, amma afili saitace "Yaya ina wuni" "lafiya" Abinda yafada kenan ya lumshe Idonsa, can qasan ransa yanajin Dadin yanda tafara sakin jikinta da 'yan gidan, laptop dinsace tafado masa, lokaci daya yanayin sa ya sauya Tashi yayi, yafara daukan jacket dinsa zai fita, mamy ta dubeshi tace "Asim qaninka fa yabani saqo wajanka" Kallanta yayi sannan yadawo kan gadon ya zauna yace "to mamy" Itama zama tayi sannan tace "yace afada maka yanason auren Minal, ni kuma na amince masa" Wata irin faduwar gaba ce ta ziyarci Asim, harya Kasa 6oye hakan saida yadora hannunsa Akan qirjinsa, mamy tana ganin yanayin sa mamaki ya kamata, Anya kalau Asim yake kuwa? Hannunta ta Dora Akan kafadarsa tace "lafiya kuwa?" Kansa ya jinjina yace "lafiya mamy" Bakomai ne yasa gabansa faduwa ba Sai tinawa da yayi yanda mazajen da Amina ta aura suke mutuwa, aure shida kowa Yana mutuwa, hakan yana nufin Shima Amjad kenan idan ya aureta mutuwa zaiyi? πŸ€” Anya kuwa zai yarda da wannan maganar? To ai kuma mamy zata tambayeshi menene dalilinsa naqin yarda? Mamy ta kalleshi da kyau tace "kayi Shiru Asim, ko baka amince bane?" Fuskarsa babu yabo babu fallasa yace "a a mamy, Allah ya tabbatar da Alkhairi" Daga nan ya tashi ya dauki kayansa yafita daga d'akin cikin tashin hankali, da kallo mamy ta bishi, taga gaba daya yanayin sa ya sauya, Anya kuwa Asim bayason Minal? Meyasa yanayin sa ya sauya lokaci daya haka? Yana futowa daga d'akin yafara furta kalmar innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, tayaya zai Iya futowa fili ya fadawa mamy cewa Amina duk mazajen data aura mutuwa suke? Hakan kamar tonon Asirin yarinyar ne Dakinsa yashige, yaga Lubna da Amrah suna ciki, brief case dinsa kawai ya ajiye yafuto, Amrah tana masa sannu da zuwa ya amsa batare daya Kalle taba, daga nan yafi ce daga gidan, bai zarce ko'ina ba Sai wajan babban abokin sa Muhsin Wanda Shima acikin unguwar yake, a compound din gidan Muhsin ya tsaya Yana zagaye wajan cikin tashin hankali bayan yakira shi awaya Muhsin yafuto daga gidansa yace "abokina mu qarasa ciki mana" "no Muhsin nanma ya'isa" Kallansa yayi da mamaki yace "amma lafiya kuwa?" "lafiya, amma ba qalau ba" (🀣) Muhsin yace "tooo, to bari nasa a kawo mana abin Zama, amma ya zakazo gidana kuma mu tsaya atsaye" "ai maganar danazo da'ita Muhsin Bata zama bace" (🀣) "ikon Allah" cewar Muhsin, sannan ya sake cewa "to inajin ka, meyake faruwa?" "ina yarinyar nan dana baka labari nazo da'ita?" Muhsin yace "eh nagane, koba Amina ba?" Girgiza kansa yayi yace "no, call her Minal" Mamaki ya kama Muhsin, yace "tonaji, meyake faruwa ne?" "Muhsin komai ma yafaru, Amjad ne yake son aurenta" "to menene a ciki? Ai wannan abun murna ne" "awajan ka kenan, Muhsin yarinyar nanfa duk wanda ya aureta mutuwa yake, maganar gaskiya ina tsoron Amjad ya aureta Shima yamutu, aurenta shida, duk mazan basa wuce sati daya sun mutu, tayaya zan Bari ya aureta? Idan kuma Shima yamutu fa?" Muhsin ya kalleshi sosai, bayan tashin hankalin daya hango a fuskarsa harda tsananin kishi ma, kafadarsa ya dafa yace "to menene aciki? Asim kowa fa yamutu kwanansa ne yaqare, idan Amjad bai aureta ba Kaine zaka aure ta?" Cikin sauri yace "wa? ni? Wannan qanqanuwar yarinyar?to tamin me?" Muhsin yayi dariya yace "tamaka abinda zaisaka kuka da ihu wallahi, d'an renin wayo, to idan ba kishi kakeba menene nashiga damuwa haka?" Cikin zafi yafara yiwa Muhsin magana "saboda inason dan'uwana, kuma bazan Bari inaji ina gani yaje yamutu ba, tayaya zanyi kishi Akan hakan, kawai banaso Amjad yamutu ne, kuma ni Bana kishinta" Muhsin yayi murmushi yace "to shikkenan, muyi musu Addu'ah kawai, shi ne mafita" Kallan Muhsin yayi, wato har abinma ya tabbata kenan daza'aje ga yin Addu'ah? πŸ€” kasa cewa komai yayi, daga qarshe ma saiyace "Sai anjima Muhsin" Muhsin yayi murmushi yace "to saimun hadu" Shima yajuya cikin gida cike da mamakin abokin nasan, haqiqa Asim Yana kishin yarinyar nan, gaskiya zaiso ace yaga wannan yarinya kosau daya ne, yaga yarinyar da tayi nasarar sace zuciyar abokin nasa, dukda da alamu shi Asim din baisan cewa yafara kamuwa ba Yana futowa daga gidan ya tsaya a waje, shida yazo wajan Muhsin ko zaisamu wata shawarar wadda zaisa afasa wannan auren, shine zaice masa ayi musu Addu'ah? To yanzu Yaya zaiyi? Kode wajan Ishraqa zaije? Nan take ya yarda da shawarar zuciyarsa, Yana zuwa gidan Ishraqa maigadi ya rissina ya gaidashi kasancewar ba boyaiye bane, har falon nata ya shiga, yazauna Akan kujera Gidan yatsaru sosai, an narka masa dukiya kamar baza'a mutu ba 'yar aikinta tazo da sauri ta kawo masa abin motsa baki, baima kalli abinda ta ajiye masa ba, yace "ina Antynki?" Saida ta rissina sannan tace "tana ciki Yallabai, Bari a kirata" Daga mata kai yayi, tare da jingina da kujerar yarufe Idonsa Dawowa tayi tace "Yallabai tace kashiga" Bude Idonsa yayi, sannan ya tashi ya nufi d'akin dayaga tashiga, wanda Bana Ishraqa bane, shi kansa duk zuwan dayake gidan, bai taba shiga cikin dakinba Yana shiga d'akin yaga wasu hadaddun photuna na yarinya dabata wuce shekara biyu ba, chocolate beauty ce yarinyar, babu ta inda take kama da Ishraqa, ga wani gado na Yara agefe harda matakalar da zata kaika saman gadon, banda uban kayan wasa dayake zube acikin d'akin, Ishraqa Yagani tana ta faman mopping din d'akin (🀣) Ahankali yazauna tare da dafe Kansa ( ) Tanaganin haka, tasan cewa ba kalau ba, tadawo gefensa ta zauna tace "Asim lafiya kuwa?, waye yamutu?" (πŸ˜†) "lafiya Ishraqa, ke kinji ki da wata magana, kawai kuma daga ganin yanayin mutum Sai maganar mutuwa? banjin Dadin jikina ne" Tace "sannu, amma ka fadawa Lubna ne?" Kansa ya Girgiza yace "ba tasan ma nataho nan ba" Tausayin sa ya kama Ishraqa, kullum inde Yana cikin damuwa tarasa meyasa Lubna Bata kwantar masa da hankali, tace "a a Asim, kafadamin mana, menene yake faruwa?" Ahankali yadago kansa yace "akwai yarinyar danazo da'ita rannan, saboda ita ne" Ajiyar zuciya TASAKI tace "menene damuwar?" "kawai de Akan maganar aure ne, Amjad yanason auren ta, ni kuma banso" Tace "tokai sonta Kakeyi ne?" Baqin ciki ya kama Asim, Wai meyasa kowa yake masa Kallan yanason Minal ne? Fisabilillah me wannan yarinyar zata iya Masa? Yarinya kullum kuka, tayaya zata iya tarairayarsa? Memakon ta bashi kulawa ma ai saide yaqare a rainonta (πŸ˜‚) Danhaka yayi Shiru baice da Ishraqa komai ba, yaga alama itama bazasu daidai ta ba, yadaga kansa ya kalli d'akin, dakuma uwar dukiyar da aka narkawa d'akin, yace "me kike yi anan d'akin? D'akin waye?" Jikinta ne yayi sanyi kalau, tayi Shiru takasa ce masa komai, Shima yasake kallanta yace "gaba daya kin maida d'akin kamar d'akin rainon Yara, ko 'yarki ce aciki ai Sai haka" Kallansa tayi, wannan Karon hawaye ne suka zubo mata, yajuya ya kalleta yace "subhanallah... Meyafaru Ishraqa?" Hawayen idonta ta share tace " d'akin tane" Cikin sauri yace "Wai wa?" Kai tsaye tace "INSAAF" mamaki ya kamashi sosai, yace "Ishraqa Wai wacece insaaf ne? Menene hadinki da'ita? tsawon shekarun nan ya kamata ace nasan ko wacece" Hawaye ne yasake zubo mata, Ahankali ta kalleshi fuska cike da hawaye tace " 'yatace Asim" Cikin sauri ya kalleta yace"what?" Girgiza masa kai tayi alamun hakane, sannan tasa hannu ta share Hawayen idonta tace" 'ya tace da qaddara tarabani da'ita tun tana shekara biyu a duniya, kayi hakuri Asim, bantaba boyema komai nawaba Sai wannan, Asim inada 'ya Nima, wadda muke qaunarta kamar hauka nida EL HAMEED, ita kadai muka Haifa alokacin danayi shekara daya da auren sa, kuma har yanzu bansake haihuwa ba, wayasani. ma ko banda Rabon ganinta harna koma ga mahalicccina, amma ina fatan ace duk inda insaaf take ta kasance mai taimakon naqasa da'ita, mutane su sota, tayi farin jini awajan kowa, tun lokacin da muka dawo Lagos muka ware mata wannan d'akin, muka zuba mata komai acikinsa, har yau gani nake kamar zata dawo gareni, shiyasa kullum babu ranar fashi sainazo nagyara mata dakinta " Asim yayi Shiru kamar ruwa ya cinye shi, shida yazo da matsala gashi ya tadda wadda ta take tasa (😟) Sai da aka jima caaan, sannan yace" yanzu Ishraqa kinada yarinya amma kikasa sanar dani? " " Asim banason tuna labarin ne, da gani har El Hameed babu wanda bashida hawan jini saboda rashin insaaf "( ) Cikin damuwa ya kalleta yace" to yanzu tana ina? Yaya akai kuka rabu? " " labarin yanada tsawo Asim, amma zan samu lokacin saina fadama abinda yayi silar rabani da yarinya ta, dakuma yanda akai ta mallaki dukiya mai tarin yawa " Tana kaiwa nan, wani Hawayen yazubo mata, kallanta yayi cikin tausayi, a ransa yace "like Minal, abu kadan kuka" (πŸ˜”) Yace "kiyi hakuri Ishraqa, amma why not kije ki dauki widad, na baki ita" Murmushi tayi tace "kuma mamanta fa? Lubna bazata bani 'yarta ba, Dade nice inda ace insaaf tana nan da saina baka ita ka aureta, harka samu kulawa sosai irinta larabawa" Cikin sauri Asim ya katseta "haba haba Dan Allah Ishraqa, menene hakan? Kuma kirasa da wadda zaki hadani Sai 'yarki? da girmana da komai saina tsaya atsaye yarki ta shiryani, ai kema kinsan bazai iyu ba, in auri 'Yata, tacikina" Yanda ya daddage Yana fada kaikace auren aka daura masa da yarinyar,harda wani 'yarsa tacikinsa kamar shine ya haifeta, Sai abinma yabata dariya, tace "Asim, Wai me ka daukeni ne? Bazan haifi yarinya in baka aurentaba? Wai tukunna ma wata nawa kabani ne? Sai wani abu kake kamar kai kafi kowa shekaru a duniya, to wallahi Kar insaaf tadawo kazo kanamin qaramar murya ehe" (πŸ˜‚) masu son Insaaf complete kuyi hakuri babu masu son complete dinsa zasu siya suma ina basu hakuri a kan haka masu cewa a dinga turowa sau uku arana suyi hakuri ina zuwa makaranta masu cewa a dinga yi safe da yamma suma suyi hakuri dasafe ina makaranta da yamma ina aikin gidaπŸ€— Duk soyaiyar wannan novel dince tasaku fadar haka, naji dadi kuma nagode,insha Allah zanyi kokari a dinga turo muku kullum Amnah tana yinku sosai kamar yanda kuke yinta πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» Sharhi pls ✍🏻 Amnah El~Yaqoub [2/10, 11:17 PM] El~Yaqoub: INSAAF Writing by :Amnah El~Yaqoub 17&18 Like my page on Facebook πŸ‘‡πŸ» https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 Anty Amnah yaushe zaki fara novel, yaushe zaki fara posting INSAAF,saide kiyi typing ki ajiye kinqi kifara posting, ta gashinan nafara magana ta qare πŸ€—wannan page Din nakane kacokam *Unique* *Jamal*, Allah yabaku sa'ar jarabawa yasa ku gama lafiya πŸ‘πŸ» ________ kallanta yayi, ya Girgiza kansa yace "wannan shirme ne irin naki Ishraqa, impossible" ya qarasa maganar Yana yatsina fuska Tace "to shikkenan, Yaya maganar computer?" "babu labari, kawai saide Addu'ah" Murmushi tayi tace "ka kwantar da hankalinka, insha Allah babu abinda zai faru, Sai Alkhairi" Wani irin kallo yayi mata, wacce irin matace wannan? Ana fada miki kadarar wadda kika Kira da 'yarki tabata, bayan abubuwa na company dasuke ciki, amma kina murmushi kamar babu abinda yake damunki Ajiyar zuciya yasaki "Ishraqa, nawuce gida" "to abinci fa? Kona zubama katafi dashi?" "matata tamin girki" Daria tayi "Dade bansan halin Lubna ba shine zaka fadamin haka, harda wani kare ta, kullum saide taita ihu tana sonsa, amma munqi gani aqasa, Sai anjima to" Shima ya kalleta yace "eh na ji Sai anjima" Yana fita taji kanta yawani irin sarawa, tasa hannu ta dafe kanta, lokaci daya jira yafara dibanta tatafi zata fad'i, Allah ne yakawo mijinta El Hameed cikin sauri yataro ta tafada jikinsa, kan gadon ya kwantar da'ita yafara jera mata sannu, sannan yajuya cikin sauri yabude fridge din d'akin, babu komai acikinsa Sai ruwa, saboda ba kowa ne yake zama acikin d'akin ba, ruwan yabata Tasha sannan yasake kwantar da'ita yariqe hannunta"yaya kikeji yanzu? kokuma mutafi asbiti? " " A a Habibiy, dama saramin naji yanayi, yanzu yadena " "Habibty, ya kamata ki rage sa damuwa aranki, kina yawan tinani idan Bana nan ko?" "dole ce tasa hakan, Asim ne yazo, shine nabashi labarin Insaaf, I think wannan ne dalili" "nahadu dashi a waje, yanzu de ki tashi muje asbiti ko?" "A a Habibiy, naji sauqi fa, saide muje wajan doctor din damukai magana dashi zai dubamu" "to shikkenan, kibari gobe saimu tafi, but are you sure kinji sauqi dangane da ciwon kan?" Ahankali ta lumshe masa idonta tabude, murmushi yayi, sannan yayi kissing goshinta, daganan suka futo daga d'akin *** ****** *** Washe Gari dasafe bayan sun Gama break fast zama sukai afalo itada Amrah, Amrah ta qarewa kayan jikinta kallo taga duk sun mutu, kuma koda wasa Bata taba nuna musu komai ba a haka take saka abinta, shikuma Yaya Asim irin yad'an dauke ta suje shopping dinnan ma beyi ba, wani lokacin har Gara Amjad ma zai dan kai mutum shan Ice cream(πŸ™) Amma Yaya Asim, idan kudin tambayeshi ma yanzu zai fara jero ma tambaya mezakai da kudi, taqarqari yabaka dubu hamsin kaje ka qarata,kokuma yahau fada shi bayason almubazzaran Ci da kudi saboda bakasan zafin nema ba (🀣) yanzu ta wacce hanya ya kamata tayi masa magana Akan suna so Yabasu kudi suje shopping? Minal batada komai, kamata yayi Yabasu ko dubu dari ne, asiyo mata komai da komai tafuto gari ta dinga shiga mai kyau, wata zuciyar tace mata to kode mamy zata fadawa? To ai kuma mamy ma idan taji cewa zatayi Asim din baqonsu ne da bazasu fada masa ba? (πŸ€”) To'ita yanzu Wai ya yazasu yine? Amjad har code din Atm dinsa tasani saboda tsabar yanda yake Bata kudi komai Baja Baja, amma Yaya Asim, hmm inajin ma saudaya tataba ganin nasa Atm card din, Shima ganine daga nesa (πŸ˜‚) Shi Ala dole Yana tattalin dukiyar insaaf, kuma dacan Bahaka yakeba, tunda aka dauki wannan kudi na insaaf aka bashi, Tofa daganan komai ya canja Sake Kallan Amina tayi, tayi gyaran murya tace "Am...Minal, ko zaki fadawa Yaya Asim yabamu kudi mutafi shopping ? Tunda Kinga babu abinda mukeyi yanzu, ni wallahi Kinga har fargabar magana nake masa" Cikin mamaki ta kalli Amrah "to Anty Amrah kema kina fargabar yimasa magana ni kuma dayake bani tsoro mezan iya fada masa?" Amrah tazaro ido waje tace "tsoro kuma? Tsoron sa kikeyi dama?" "ni wallahi tsoro yake bani Anty Amrah, tayaya zan'iya tambayar sa kudi? Idan naganshi agabana tsoro yake bani" Amrah ba tasan lokacin data kwashe da dariya ba, ta kalleta "to ai danaga ke har fira kukeyi Keda shi, shiyasa nafadi haka, amma Bari yafuto Sai na gwada, amma tare zamuje dake" Ahankali tace "to" Basu Dade da Gama magana ba yafuto daga dakinsa cikin shirin tafiya wajan aiki,yau shigar manyan Kaya yayi, harda babbar riga,yadine me mutuqar tsada launin Light blue, hular daya Dora akansa tayi masa mutuqar kyau, sajen daya zagaye masa bakinsa yaqara futowa, Hankalinsa Yana kan waya yayi hanyar fita daga falon Cikin sauri Amrah tace "Yaya ina kwana" Kallo daya yayi musu yadauke kansa "lafiya" abinda yafada kenan, daga nan bai qara sauraron suba yafita daga falon Amrah ta kalli Amina tace "Kinga mutumin damuke jira yayi gaba yabarmu" πŸ™ Tace "Tomu hakura kawai Anty Amrah idan yadawo kokuma wata Rana...." "wacce irin wata Rana?, Toni in banda wajan cin abinci ma bakoda yaushe nake ganinsa ba, kullum Yana aiki kamar computer, tashi mu bishi" Cikin sanyin jiki tace "to" Suna fita compound din gidan suka hangeshi yana danna waya kusa motarsa, ga driver nan Yana qarasa goge motar, Sai sheqi take tana daukan ido Dago kansa yayi ya hangesu suna qarasowa wajansa, shigar jikin Amina ya kalla yaga wannan de atamfar tatace datasa ranar aurenta,daurin dankwalin kanta ya kalla anan ya hango tulun gashin kanta daga gefe, duk yayi wani iri saboda babu gyara, tsaki yasaki cikin ransa, yarinyar nan batason gyara gashin ta, kuma gashin nata yanada tsawo sosai, may be ma tsawon nasa ne yasa yayi mata yawa wajan gyara, yarinya qanqanuwa da wannan uban gashi dama tayaya zata iya gyarawa? dududu batafi a zaunar da'ita ayi mata kwalliya ba πŸ˜† Qarasowa wajan sukayi itade ta sunkuyar da kanta qasa taqi dagowa su hada ido Driver ya dubeshi yace "Yallabai zamu iya tafiya, nagama" Amrah tayi sauri tace "Yaya..., Dan Allah Yaya ko zaka bamu kudi munaso muje shopping nida Minal" Qura mata ido yayi Yana kallonta, Yana jira tagama magana Amrah kuwa tana ganin haka cikin ranta tace shikkenan, dama nasani, yanzu haka dubu hamsin din daya saba zai wullo mana mutafi, danya qara musu wani abun saita cigaba da cewa "kuma Yaya kaga Bata da abubuwa dayawa, duk muna so musiyo, dasu takalma da jaka" Asim ya sake kallanta yaga Sai abubuwa take jerowa, itama dataga haka saita sake cewa "dasu mayafai, da riga da Wando" Dauke kansa yayi daga kallonta, yaga alama bazata Dena yimasa lissafi ba, ya maida kallonsa ga Minal yaga kanta Yana qasa tana Jan yatsun hannunta, itada ake maganar saboda ita amma takasa cewa komai, yanzu haka Yana sata yin magana zata fashe masa da wannan shegen kukan nata Hannunsa yasa ka cikin aljihun wandonsa, Amrah tayi tunanin kudin zai basu harta fara Addu'ah Allah yasa yadebo dayawa (πŸ˜‚) Saitaga ya miqo mata ATM card dinsa yace "gashinan,7788 ne cord din, kuciri yanda zai isheku" Amrah ta hangame baki hannunta riqe da atm card, lokaci daya ta Lula duniyar tunani, eh lalle Sai yau taqara tabbatar wa Yaya Asim Yana ciki (πŸ˜‚) Shikuma Yana Bata card din yashige Mota, driver Yaja suka tafi, sun danyi tafiya kadan yasa driver ya tsaya, sannan ya sauke glass din motar qasa ya qwala mata Kira "Amrah!!" Sai alokacin tayi firgigit tadawo daga duniyar tunanin data tafi, cikin sauri ta kalleshi "Na'am Yaya" "please kubiya ta saloon awanke mata kanta" Cikin sauri Amrah tace "to Yaya, zamuje ko'ina" πŸ˜ƒ Tajuyo ta kalli Amina "muje mu shirya mutafi Minal, ba zamuje da motar gidaba, taxi zamu hau tunda ba waje daya zamuje ba, idan mukaje da Mota itama kaya zata zame mana" Tace "to Anty Amrah" Ko awaya daya basu qara agida ba, suka tafi, Kai tsaye Barack sukaje, suka shiga ERENA, Amrah kawai kwasar kaya take tana miqa ATM 🀣 ta lodo mata riga da Wando masu masifar kyau, banda dogayen riguna masu mutuqar kyau da tsada, takalma, jaka, Dan kunne, sarqa, kayan kwalliya, dakuma less daban daban Kala Kala masu kyau da shadda, atamfa ce batada yawa, itade Amina kallonta kawai take, kayan sunyi yawa kamar wanda za'a hada wa wata lefe, ita tsoro ma kasuwar tabata da farko, yanda taga jirgin sama Yana yawo a saman kasuwar Daga nan sukaje wajan saloon, tsananin mamaki ya kama Amrah dataga yawan gashin da Minal take dashi, tana ganin gashin babu wanda yafado a ranta Sai Anty Ishraqa, har so take wataran tazo gidansu idan zatayi sallah tabude kanta taita kallon gashin Harta Bude baki zatace amma Minal kede ba bahaushiya bace kawai kuma Sai tayi Shiru, saita ga idan tayi mata maganar kamar cin fuska nema agareta tunda kowa yasan cewa ita din batasan asalinta ba Harda wankin qafa saida akayi mata, lokaci daya kuwa tafuto fess, Wai ahakan ma Bata fara amfani da mayukan dasuka siya ba Saida suka kai kayan daya kamata adinka wajan dinqi, sannan suka bashi kudinsa, suka dauki taxi suka tafi gida Amrah Sai daria take a ranta, kawai hango Yaya Asim take a office yanajin alert, Suda daukan kudi shida karbar alert πŸ˜‚ *** ****** *** "kamar de yanda bincikenmu ya nuna Alhaji, kaida Hajiya bakuda wata matsala dangane da rashin haihuwa, lafiyarku kalau, kawai Allah ne bai kawo samun Rabon ba, may be Sai zuwa nan gaba, saide kuci gaba da Addu'ah Allah yakawo masu albarka" El Hameed yamiqawa doctor din hannu tare da yimasa godia, yakai kallonsa ga Ishraqa yaga har idanuwanta sun kawo ruwa Yace "Habibty tashi muje" Bata'iya ce masa komai ba ta tashi tafuto daga office din, motar yabude mata ta shige, tana zama kuwa takifa kanta acinyarta tafashe da kuka Shima zagayawa yayi ya shiga Yaja motar suka dau hanyar gida, kallanta yayi ya maida dubansa kan titi "yanzu Habibty ashe bazaki godewa Allah Akan kyautar da yayi mana abaya ba?, lokacin daya bamu Insaaf roqarsa mukayi? Karki manta wasu mutanan dayawa neman guda d'ayan ma suke amma basu samu ba" Cikin kuka tace "tomu damuka samu d'in ina take? Ina 'yata take?" tasake rushewa da kuka Kansa ya Girgiza yace "Ishraqa bake kadai fa kike son Insaaf ba, Nima Ina qaunarta, inaso kisani banida kowa a duniyar nan saiku, bayan ke banida kamarta, muyi Addu'ah idan tana Raye, Allah ya baiyana mana ita, idan kuma Bata Raye Allah yabamu hakurin rashin ta" "nide 'yata Bata mutu ba, karka sake cemin 'yata ta mutu, zata dawo wajena" (πŸ˜‚) Shiru yayi bece da'ita komai ba ganin sun qaraso gida, Hon yayi Yana jira megadi yabude musu get amma Shiru da alama baya kusa ne Adede wannan lokacin aka kawo mutanan kasuwa, d'an taxi ya saukesu da kayansu niqi niqi a hannu Ishraqa acikin Mota tana kuka taga maigadi bashida niyyar budewa kawai saita Bude murfin motar tafuto, idanunta sunyi jajir kasancewar ta farar balarabiya Amina tana ganinta tasaki ledar hannunta qasa, faduwar abun da Ishraqa taji ne yasa tajuya ta kalli wajan, idanunta yahadu dana Amina, lokaci daya faduwar gaba ta ziyarcesu Junansu suka zubawa ido suna Kallan kallo amma babu wanda yayiwa wani magana acikinsu, jikin Ishraqa yayi sanyi, kallon yarinyar take sosai tanaso tasan meyasa gabanta yake faduwa kawai daga haduwar su? Amina hamdala kawai take a ranta, batasan meyasa ba haka nan taji Allah ya d'ora mata son matar, komai nata birgeta yake, musanman yanda take kwalliya,Anya bazata koyi irin kwalliyar matar nan ba? Ahankali tafara takawa zuwa gare ta, Ishraqa tazuba mata ido, haka itama Amina idonta cikin na Ishqara, ganin da gaske kamar wajan ta zatazo kawai saita Girgiza kanta tawuce cikin gida Cikin sauri Amina ta miqa hannunta tanaso takira sunan ta amma kuma saide tuni tashige cikin gida, jitayi wani irin baqin ciki ya kamata, ta d'ade tana son ganin matar gashi yau Allah ya had'asu amma kuma batayi mata magana ba, dama hakane, Saikaga Allah yadora ma kaunar mutum aranka, amma shi awajan sa ba Bahaka bane, wata zuciyar tace da'ita, meyasa zakiyi mata magana?inake ina wannan matar? Gwalgwalan da suke hannunta kad'ai ya'isa kasan cewa ba qaramar mace bace, girgiza kanta tayi, afili ta furta "bazai iyu ba" Daganan tanufi get din gidan, Sai alokacin maigadi yabudewa El Hameed get, kafin yarufe tuni Amina ta fad'a cikin gidan (πŸ˜‚) Amrah tayi sauri ta kwashi ledojin kayansu tabawa maigadinsu itama tabiyo bayan Amina cikin sauri Tun kafin El Hameed yafuto daga Mota Amina ta qwalawa Ishraqa Kira "ANTY ISHRAQA" Cak ta tsaya awajan datake batare data juyo ba, me kuma wannan yarinyar take nema awajan ta? Kawai daga haduwa saita shigo mata gida? da waye ma yafada mata sunan ta? Shareta tayi, taci gaba da tafiyar ta batare data juyo ba bare Amina tayi tunanin samun kyakkyawan kallo Ganin zata shige ta qyaleta ne yasa ta daga muryarta tace "MAMAN INSAAF !!" Cikin sauri Ishraqa ta juyo, saboda an kirata da sunan datake mutuqar so, d'an sauran kukan data riqe ya qwace mata, Ahankali hawaye ya silalo daga idonta Amina tana ganin tajuyo ta qarasa wajan ta da sauri, duk da gabanta Yana faduwa bataji tsoron taba, kawai saita bar faduwar gaban nata a matsayin kwarjini da matar tayi mata, dakuma rashin sabo Kallon idonta tayi cikin in-ina tafara magana "dama.. Nace... Dan Allah... Ko zaki iya rungume ni?" Amrah tashigo gidan, tana ganin Amina awajan Ishraqa tace "yau Naga takaina" Tadaga murya takirata "Minal !!" Amina tana jinta ta qyaleta El Hameed yana daga gefe Yana kallon ikon Allah, yasan Ishraqa ba zatayi abinda yarinyar tafada ba, musanman yanzu datake cikin bacin rai tsaf zata huce akan yarinyar, amma abinda yaqara bashi mamaki harya Kasa boyewa shine ganin Ishraqa ta meqawa yarinyar hannu Amina na ganin haka tafada jikinta ta rungume ta sosai, itama Ishraqa jin yarinyar a jikinta saitaji wata irin nutsuwa tana shigar ta, hawaye ya sakko daga idonta, Ahankali tasaka hannu ta rungume Amina, lokaci daya Amina ta lumshe idonta, tana sauke wata irin Ajiyar zuciya Pls kuyi hakuri da wannan ba yawa Sharhi please ✍🏻 Amnah El~Yaqoub [2/11, 10:41 PM] El~Yaqoub: INSAAF writing by:Amnah El~ 19&20 Like my page on Facebook πŸ‘‡πŸ» https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 Tsawon minti uku suka dauka a haka, El Hameed dai yayi Shiru Yana kallansu, ita kanta Ishraqa bazata ce ga dalilin dayasa ta rungume yarinyar ba, Amrah ta qaraso ta janyeta daga jikin Ishraqa, tace "Anty Ishraqa Dan Allah kiyi hakuri" Ko sake kallon fuskar Amina batayi ba, cikin sanyin jiki ta dagawa Amrah kai, hannun Amina cikin na Amrah suka futo daga gidan, Amma Sai waigowa take tana Kallan Ishraqa, wani dadi yana qaruwa acikin zuciyar ta El Hameed ya qaraso wajanta Yana mamakin yanda fuskarta tasaki kamar ba'ita ce take kuka ba,yayi Ajiyar zuciya Yana kallon get din nasu bayan fitarsu Amrah "yanzu fa inda ace Insaaf tana nan zata iya kaiwa kamar wannan yarinyar" Hararar wasa tayi masa "Habibiy yaushe zan iya haifar kamar wannan?, kaduba kaga yarinya budurwa kace zan haifi kamarta?" "Habibty koda yaushe maida Insaaf baya kike, karfa ki manta last month mukayi mata birthday party na 18 years, saboda haka yarinya de ta girma, ke kuma kin zama tsohuwa" ya qarasa maganar cikin sigar tsokana Ahankali tad'an daki qirjinsa sannan tad'ora kanta akai, murmushi yayi yasa hannu Yana shafa gadon bayan ta *** ****** *** Da daddare gaba dayansu zaune suke afalo, Widad tana cinyar Mamy, Asim yana daga can gefe azaune Yana kallonsu, waya ce a hannunsa Yana dannawa, amma hankalinsa yanakan su, Amrah da Amina suna zaune aqasa kowa Hankalinsa Yana kan kallo, Amrah tana Bawa mamy labarin inda sukaje d'azu dasuka fita kasuwa, saida tayi maganar kasuwa sannan ya tuna da maganar gyaran gashin dayace ayi mata, kallon gashin nata yayi yaga Sai sheqi yake, yakai dubansa zuwaga rigar jikinta, idanunsa sukai arba da nashanunta wanda rigar tabasu haqqinsu na futowa sosai, fuskarta de babu kwalliya, amma tayi kyau sosai, kayan ya karbi jikinta Widad ta tashi daga cinyar mamy tadawo wajan Amina takama dogon gashinta, tace "laaa kema Ana saka miki gashi irin wanda ake Sawa momy na?" Mamy tayi dariya tace "Widad Bari mana, kidena ja mata gashi, wannan ba irin na momynki bane" Sake dago kansa yayi yaga yanda widad take wasa da gashin, Sai hakan yabashi sha'awa yakasa dauke Idonsa akansu, Yana qaunar gashi arayuwarsa, shiyasa ma da Lubna take saka attachment beta6a Hana ta ba Amrah tace "Ai mamy awajan saloon dinma bakiga yanda ake kallonta ba, saikace gashin Anty Ishraqa" Mamy tace "eh maman Insaaf ma irinsa ne da'ita, ko anyi mata kitson baya iyuwa, shiyasa kullum take hanyar wajan masu saloon" Amina tana jinsu batace komai ba saide Dan qaramin murmushi da tayi kawai Amjad ne ya shigo d'akin bakinsa dauke da sallama, yayi kyau sosai acikin qananun kaya,wasu takardu yabawa Asim sannan yayi wajan mamy yazauna akusa da'ita tare da d'ora kansa Akan kafadarta yace "Mamy nadawo" Kansa tashafa tace "Sannu Autana, kunyi waya da Daddynku kuwa?" "eh nakira shi dazu, mun gaisa, yacemin ma yakusa dawowa, mamy Wai kinyi masa maganar sa ranar ne?" Amina da Amrah da Asim duk suna jinsu, kowa yasan Akan abinda suke magana, amma ita ko kadan ba tasan a kanta ake maganar saka ranar ba Mamy tace "nayi masa magana, yace abari yadawo tukunna, amma nasan babu wata matsala zai amince, saboda haka kawai kufara shirye shirye kaida yayanku" Lokaci daya yaji wani irin farin ciki ya lullu6eshi, Wai shine zai auri Minal, shide Allah yadora masa qaunar yarinyar acikin ransa, kallonsa yakai gareta yaga hankalinta Yana kan kallo, haka yadinga jifanta dawani irin kallon soyaiya mai tsayawa a zuciya Asim ya kallesu shida mamy, ya sake kallon Amjad yaga yanata farin-ciki Sai wani kallo yake mata, girgiza kansa yayi cike da taqaici,maganar zuci yafara, Sai wani rawar jiki yake saboda zai auri bazawara, besan tayi aure harsau shida bane shiyasa yake wannan yarintar, uwa uba ma da yaji cewa duk mazan data aura mutuwa suke dabai fara wannan rawar kafar ba, 🀣 yasan cewa yarinta ce kawai take damun Amjad, shi kam yanason ransa, bazai iya auren mutuwarsa ba, to yarinyar datayi aure shida ma ai ba qaramin namiji ne zai Iya Mata ba, tunda tashiga hannun maza Kala-Kala Tsintar maganar mamy yayi tana cewa Amjad "kunyi maganar kaida itane, babu wata matsala daga nata bangaren?" Asim yaqurawa Amjad ido yanaso yaji amsar dazai bayar,Minal d'in ta amince kokuwa Amjad ya shafa kansa cike da kunya yace "bamuyi magana ba mamy, amma nide a nawa 6angaren babu wata matsala, ko a Yaya take zan'iya auren ta" Asim yanajin haka ya tashi yabar falon, ya nufi nasa falon, cikin ransa Yana cewa ai shikkenan tunda yaga zai Iya karbar mutuwar 🀣 Wannan ai babu amfanin ma afad'a masa mutuwa ake kokuma bazawara ce, idan sukai auren shida kansa saiya tabbatar waya aura Mamy tabishi da kallo cike da mamaki, me hakan yake nufi? πŸ€” Amrah kuwa bayansa tabi da kallo tana dariya qasa-qasa Mamy ta kalleta tace "Amrah kawowa Amjad abinci" Saida tad'anyi jimm sannan ta nufi kitchen tana gunguni, saikace wani Babba mamy zata sata ta tashi, bayan itace ya kamata ace ta aikeshi, tana cikin tafiya taji muryarsa yace "AMRAH" Cikin mamaki ta juyo ta kalleshi, Rabon dataji Amjad yakirata kai tsaye harta manta, zata iya cewa tun suna Yara, cikin masifa tajuyo tana kallonsa, shikuwa wani irin murmushi yasaki Yana shafa sumar kansa sannna yace "ki zuba min d'an kadan" Abincin ta kawo masa ta dangwarar a gabansa ko zuba masa batayi ba, tawuce dakinsu Yana zuwa dakinsa abokin sa Muhsin yakira shi, dauka yayi tare da lumshe Idonsa yace "ina jinka" Daga d'aya bangaren Muhsin yace "Abokina munyi magana da principal din wannan makarantar , yace zata fara zuwa ranar Monday" Dasauri yabude Idonsa yace "Monday... Jibi kenan fa" Muhsin yace "akwai damuwa ne?" "no, da'inaso nayi mata lesson ne kona one week ne kafin tafara zuwa, to bansamu lokaci ba" "tokai da ina kaga lokaci? da Amjad Kasa ma Aida tuni sunyi Nisa" "Amjad kuma?" "to menene dan Amjad din yakoya mata?ko kana kishi ne?" "A a.... Allah yasawaqe" Muhsin yayi murmushi yace "Amin, Nima Ina hanya ganinan zuwa gidan naka, ya kamata kayi mata karatun de kafin Monday din ko Yaya ne, Saikaga qoqarinta, kaga daga nan Sai kasan abinda zaka yanke" "da sonake kawai tazana jarabawan ssce, saina nema mata Admission tatafi University, madecine nakeso tayi, tunda yarinya ce qarama saitai tayin karatun, nasan karatun nata bazai wuce 6 years ba" Muhsin yanajin wannan qarfin hali na Asim yayi daria, kaiba auren yarinya zakayi ba amma Kaine da tsara mata yanda kakeso, afili yace "kaga gashinan naqaraso gidan, Bari nashigo" Katse wayar yayi, yakira Amrah, tana dauka yace "turomin yarinyar nan, tataho da littafi da biro" "yarinya kuma Yaya...? Wacce yarinya?" Dan qaramin tsaki yayi yace "Minal" Amrah tadauki littafi da biro takaiwa Minal da suke falo itada mamy da widad, Amjad baya nan, tafada mata saqon Yaya Asim, sannan tajuya Takoma cikin daki Gabanta ne yafara faduwa haka de ta nufi hanyar d'akin nasa duk jikinta yayi sanyi Muhsin yadubi Asim bayan ya zauna acikin kujerun falon nasa launin Ash, yace "baban widad yagida ya ayyuka" "Alhamdulillahi, ya iyali" "normal, ina hajiya Lubna" "taje gida, Bata nan" "kace yau gwauro ne" Kafin Asim yabashi amsa ta shigo falon, bakinta dauke da sallama, Muhsin ne ya amsa mata, tazauna a qasan kafet din falon tare bashi littafin tace "Yaya gashi" Karba yayi ya ajiye a gabansa, sannna yafara yimata yan tambayoyi dangane da science,dakuma wasu na English tana bashi amsa kadan kadan, Muhsin Yana gefe Yana kallonsu Da karatu yayi Nisa saita saita fara yin Shiru, yayi tambaya yayi tambaya yaji Shiru, gaba ya lura Bata fahimtar komai, haka yayi Shiru yaci gaba dayi mata Bayani, saida yagama tass sannan yafara jefo mata tambayoyi,da farko yace ta karanto masa part of speech, takawo guda bakwai kalau, Sai Ana qarshan ne maimakon tace interjection saitace injection, dariya takama Muhsin amma saiya danne beyiba, kawai qarfin hali yake gani irinna Asim, karatun yayi mata yawa a matsayin ta na wadda tayi karatu a qauye, kamata yayi yafara yimata da kadan kadan ahankali harta saba Zuba mata ido yayi Yana kallonta, jiyake kamar ya ranqwashe mata kai, yace "gyara na qarshen dakika fada" Amina tayi Shiru, gashi gabanta Sai faduwa yake, taqaici yakama Asim, ya kalli Muhsin yace "see, yarinyar danake cewa medicine zatayi itace takasa bani amsa" Kafin Muhsin yabashi amsa yadaka mata tsawa "badake nake ba!!" Zabura tayi Takoma gefe, jitake dukanta zaiyi, Ahankali murya na rawa tamkar mai shirin yin kuka tace "Yaya ni.... ni nafison... Arabic" Cikin sauri yace "what? To bazaki Arabic dinba, boko zakiyi, kuma bokonma medicine" Hawaye ne ya zubo daga idanuwanta, cikin kukan shagwaba tace "Allah nide Arabic nakeso" Littafin ya wulla mata yace "Kinga tashi, tashi tashi kibani waje tun kafin na zaneki anan, ina fad'ar abinda nakeso kema kina fada, now.... band'ora hannu na ajikin kiba kin zauna kina min kuka, oya tashi kiban waje" πŸ˜‚πŸ˜‚ Hawayen idonta ta share, babu musu ta yunqura tatashi, ta dauki littafinta tafice daga falon Kansa ya dafe da hannunsa ,ya tuna yanzu wannan takaicin Amjad zai dauka yakai gidansa, cikin damuwa yace "ka auri qaramar yarinya ma koka auri wahala" Muhsin ya kwashe da dariya harda sunkuya wa, cikin haushi yajuya Yana kallonsa Sharhi ✍🏻 Amnah El~Yaqoub [2/13, 12:02 AM] El~Yaqoub: INSAAF Writing by:Amnah El~Yaqoub 21&22 Like my page on Facebook πŸ‘‡πŸ» https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 "menene abin dariya anan?" Muhsin ya qyaleshi saida yagama cin dariyarsa sannan ya kalleshi "nifa Ina ganin al'amarin ta kamar akwai aljannu aciki, why not kakaita wajan malamai, ayi mata ruqiyya ko za'a dace?" "aljannu kuma Muhsin?" "of course Asim, saboda babu yanda za'ayi ace dazaran yarinya tayi aure Sai miji yamutu, ai kaima kasan akwai alamar tambaya" Jinjina kansa yayi "amma tayaya zan kaita wajan malamai Muhsin? Kamar da cin fuska aciki..." "bawani cin fuska Malam, ka taambayeta mana, ai zata iya sani, bazai iyu ace tanada aljannu amma Bata sani ba" "OK, zanyi mata" "yawwa ni ina ganin hakan zaifi" *** ****** *** Daga d'akin tafuto tana goge guntun hawayenta, Amrah tana falo tana kallo ita kadai. Tadubeta "har kun gama karatun?" "eh mungama Anty Amrah" "to yanaga kina goge ido? kode dukanki yayi?" Kafin tabata amsa Amjad ya shigo falon, ya kallesu yace "Amrah, kushirya muje musha ice cream" Banza tayi ta rabu dashi, ya kalli yanda ta6ata fuskarta, shi kam mamy ta hadashi da aiki, takowa yayi yadawo dab'da'ita yazauna, ya kalleta yace " ai yanzu nadena cemiki Anty, tunda na kusa aure" Amina ta kalleshi, ashe aure zaiyi shiyasa dazu suke maganar aure shida mamy, Amrah tace "to Ina ruwana kuma, saide kuje, nikam babu inda zani" Murmushi yayi "haba Anty Amrah tah, Anty na takaina, aini dake kinsan Bama haka ko, nadena, I am sorry nadena" Murmushi tasaki "to naji, tashi muje" Tashi sukai, ta kalli Amina, " idan kin shirya muna jiranki amota " Daga mata kai tayi, sannan tashige dakinsu tana tunanin wanne irin shiri kuma bayan na jikinta? Haka de ta sauya shiga zuwa doguwar riga, takama gashin kanta ta daure, amma duk da haka bai dauru sosai ba,tashiga toilet Dasauri ta wanke fuskarta, Bata shafa komai ba, tayafa mayafin rigar tafuto daga d'akin Tana futowa taga Widad a falon tace "Widad yaushe kuka dawo?Ina Momynki?" Dariya Widad tayi, batare data Bata amsa ba, tazari mayafinta tafice daga falon da gudu Amina ta dafe kanta tace "kai! yau nashigesu" Cikin sauri tabita da gudu, gudun datake yasa gashin kanta dabai Gama dauruwa ba yake tsalle Yana kad'awa, alokacin su Asim suka futo daga d'akin sa shida Muhsin,suna kallonta tafita da gudu kai babu dankwali, Amina batama San sun futo ba, tana zuwa harabar gidan taga babu Widad, tajuya tana Zagaya gidan anan taci Karo da Anty Lubna tajuya bayan ta tana waya qasa-qasa, cak taja ta tsaya awajan gabanta yafara lugudan faduwa, Ahankali tajuya zata tafi saboda kada tajuyo ta ganta, saita tsinci muryarta tana cewa "Kayi hakuri, karka tonamin Asiri, zanyi abinda kasani, amma karkazo gidan aure na ka tonamin asiri, wallahi zanyi duk abinda ka Umar Eni dashi, to Amma fa matsalar Shima computer yake nema, bai ganta ba, bai San inda take ba, amma insha Allah inde ya ganta, zansa flash na dauke komai dayake ciki, duk takardun da suke ciki da komai da komai zanturo su zuwa flash din, Nima fa Abin Yana batamin rai, komai Insaaf komai Insaaf, nida nake matarsa baisa sunana kodaya acikin harkar dukiyar sa ba " Kan Amina yayi dummm haka, saita fara jin kunnanta yanason daina aiki, Ahankali ta d'ora hannunta tadafe kanta computer? to ai shaf ta manta computer tana wajan ta, dama nema yake? Innalillah...... Yanzu Yaya zatayi? Ta zalunceshi, ta sashi a halin tashin hankali Yana neman abunsa ta hanashi, to Amma ita Insaaf din ba'ita ce Anty Amrah tace mata yar gidan Anty Ishraqa bace? To inhakane menene hadinta da Yaya Asim dazaisa sunan ta Akan komai, gashi har matarsa tana kishi akaan haka, yanzu daama Anty Lubna saboda kudi take zaune da Yaya Asim? Kokuma saboda taga bayansa ne? To ita da waye suke shirya wannan maqarqashiyar? Dole tanada wanda yake Bata umarni, tunda koda yaushe awaya take jinta tana maganar, wani bala'in tausayin sa ya kama Amina, Anty Lubna kuwa sake gyara mayafin kanta tayi taci gaba da wayarta hankalinta kwance "wallahi Allah nasaka masa wannan maganin, wannan shegiyar yarinyar dayazo da'ita ne tamin Sanadin sa, amma da yanzu yaci, yanzu haka saboda ita nafasa kwana nadawo, Dan bansan meze faru ba, idan Bana nan,Kwanaki kamasu nayi cikin dare ita dashi, amma babu matsala kuwa idan nasaka masa gubar wadda zata karya garkuwar jikinsa? bazata kashe shi ba? " Amina na jin haka tajuya tabar wajan, wannan al'amarin yafi qarfin ta, Gara tafada masa kawai ya dauki mataki da kansa, Abin yafi karfin ta, yafi karfin tunanin ta, bazata iya ita kadai ba, dole ne tasameshi tafada masa gaskiyar abinda take ji awajan matarsa Compound din gidan tadawo, anan taga Widad, tare dasu Asim da Muhsin, Sai wasa take da mayafinta Qarasawa tayi duk hankalinta atashe, sakamakon maganar dataji su Lubna sunayi, banda gabanta dayake faduwa, ko sallama bata musu ba ta miqawa Widad hannu tace "Bani mayafin" Widad tasaki murmushi takama qafar Asim tariqe shi gam tana buya tace "nide wasa zanyi dashi, bazan baki ba" Asim da Muhsin duk suna kallonsu, haushi yaci zuciyar Asim, danme zata futo haka kanta babu dankwali, kowanne kare da doki suna kallonta πŸ˜‚ Amina kuwa bataga bacin ran nasa ba, saboda tashin hankalin datake ciki ma ya'isheta, hannu tasa zata kamo widad a jikinsa, yarinyar tasake komawa daya bangaren, itama tabita suka fara zagaye jikin Asim, yanda take kokarin kama yarinyar ne yasa jikinta Sai haduwa yake da nasa, yanajin yanda take goga masa abubuwanta a jikinsa, tana nema ta haddasa masa fitina kuma Yaga alama ita ko kadan kamar babu abinda hakan yake haifar mata, yarasa meyasa wani lokacin Bata tsoron ta'bashi kamar wata matarsa, ko tana tunanin shidin Amjad ne dayake shirin aurenta? kokuma saboda tayi mu'amular aure da mazaje dayawa ne? Wata irin tsawa ya daka musu "Wai miye hakane?!!" Cikin shagwaba tace "to Yaya kace ta bani mayafi na, su Anty Amrah jirana suke" Kallonta yayi yace "ohhh itama Widad din kukan zaki mata?" ya qarasa maganar Yana nuna mata Widad, aikuwa Widad tana jin haka tasaki dariya Yajuya yace "ke Bata abunta" Babu musu Widad tabata, sannan tayi mata gwalo, hararar widad tayi tace "zan kamaki ne yarinya" πŸ˜‚ Sannan tawuce tabarsu awajan, ko sake kallonsu batayi ba, Asim yabi bayanta da kallo yace "gaskiya na yarda da maganar ka Muhsin, yarinyar nan tanada aljannu, kaduba kaga fa da widad take fada" Muhsin yayi murmushi "wannan aiba aljannu bane Asim, harda yarinta ma, yarinta ce kawai, shiyasa tabiyewa yarinyar suke wata yarintar" πŸ˜ƒ Widad ta hango Anty Lubna, tatafi da gudu zuwa wajan ta *** ****** *** Washe Gari lahdi, kowa Yana gida, haka ta tashi sukuku tana tunanin hanyar zata da fada masa maganar dataji Anty Lubna ta nayi awaya, tarasa yanda zatayi ta ganshi bare suyi maganar, Amrah ta kalleta "kalau kike kuwa Minal?" "lafiya kalau Anty Amrah, mekika gani?" "Naga kina ta tunani ne" Murmushi ta qirqiro tace "a a, babu damuwa" Wayar Amrah tahau qara, tana dubawa taga Yaya Asim ne yake Kira, dauka tayi tana sauraronsa, daga baya tace "to Yaya" Ajiye wayar tayi tadubi Amina, tace "kije falo, Yaya yana kiranki" Hamdala tayi a ranta, cikin sauri ta miqe tatafi, har hakan yabawa Amrah mamaki Tana zuwa falon ta ganshi Yana karanta jarida, sallama tayi masa sannan ta zauna aqasa, jaridar ya ajiye sannan ya nuna mata gefensa "tashi ki zauna" Ahankali tadago idanuwanta ta kalleshi tayaya zata zauna agefensa? Idan matarsa tazo ta gansu kuma tahau dukanta, Ahankali tace "a a Yaya, nanma yayi" "ki tashi nace" Cikin sauri ta tashi tazauna a'inda ya nuna matan, Ahankali yajuyo Yana fuskantar ta,yanda yajuyo yake kallonta saika dauka wasu shahararrun masoyane, yanaso yayi mata maganar Amjad, ya kamata a matsayin sa na wanda yakawo ta gidan ace sun tattauna Akan maganar, ko yaya ne abata haqqinta, idan ta amince da auren shikkenan, idan Bata amince ba Sai tayi karatu, amma Yana fatan ace bazata amince ba, saboda a halin datake ciki yanzu karatu shine gatan ta, zai so ace tayi karatu me Nisa domin ta in ganta rayuwarta har zuwa lokacin da iyayenta zasu baiyana idan Allah yayi suna Raye Ajiyar zuciya yayi "inaso zamuyi magana ne..." Gabanta ne yake faduwa, ganinsa agabanta sosai yayi mata kwarjini,gashi yajuyo Yana fuskantar ta, Ahankali ta daga masa kanta Yace "Akan maganar Amjad ne, kina ganin kamar...babu wata damuwa ne zaki iya..." Amina tadago kanta ta kalleshi, meyasa yaqi yayi mata maganar kai tsaye? Meyasa yake wata irin hanya-hanya kamar bayason yin maganar? Da alamu duk abinda zai fada mata me wahalar fada ne awajan sa Dan haka ta katse shi tace"Yaya, Nima akwai maganar danakeso muyi " Shiru yayi Yana kallonta, kode itama ta ganene bayason yimata maganar shiyasa zatayi abinda zai fishsheta? πŸ€” To bari yaji dame tazo kuma, yace "inajin ki" "dama.... am dama fa.... Kwanaki ne..." Daga nan tayi Shiru takasa qarasawa, tunani take a ranta tayaya zai karbi abun? ta wacce hanya zata fahimtar dashi abinda matarsa take qulla masa? Anya kuwa zai yarda? Karfa yace sharri take yiwa matarsa... Dago kanta tayi ta kalleshi, taga yazuba mata ido Yana kallonta, gaba daya ya tattara Hankalinsa waje daya yabata, daga kansa yayi, alamun yanajinta taci gaba, Ahankali tafara wasa da yatsun hannunta tace "Yaya, kwanaki naji Anty Lubna tana waya... wai, wai zata saka maka magani acikin abinci, idan Kaci zaka mutu...." Gabansa ne yayi wata irin faduwa, lokaci daya yanayin sa ya sauya, idanunsa suka furfuto, ya sake kallonta yace "Lubna kuma? Kinsan abinda kike fada kuwa?" Cikin ranta tace dama nasani, nasan bazai taba yarda ba,to wannan na kwanakin bayan ma kenan yaqi yarda inaga tafada masa abinda taji jiya? gabanta yaci gaba da faduwa, idanunta ya raina fata, Ahankali tace "Eh Yaya, kuma tasaka maganin a abincin, shine nazubar dashi, alokacin sau biyu tana marina" Lokaci daya yatafi duniyar tunani, ya tuna lokacin daya shigo gidan yaga tana marinta saboda tazubar da abinci, Anya kuwa yarinyar nan da gaske take? Tayaya Lubna zatayi masa haka? Ita da kanta ta nuna tana sonsa aka hadasu aure to tayaya zataso yamutu? To idan tanaso yamutu su kuma wanda suke son ganin bayansa waye yake turosu? Ahankali yakamo hannayenta duka biyun yariqe, ya hada idonsu waje daya, gabansa Sai faduwa yake, mamaki tattare saman fuskarsa yace "fadamin....,ki fadamin komai" Lokaci daya tsoro ya kamata, ganin irin yanayin dayake ciki,to idan yaji harda computer sa take nema Yaya zaiyi? Ahankali tafara kokarin cire hannunta daga nasa, tana tsoron ace wani daga cikin yan gidan ya shigo falon ya gansu a haka, uwa uba Anty Lubna, idan ita tana had'a jikinta danasa tasan cewa akwai aure atsakanin su, amma shifa? Bai saniba, sannan duk gidan babu wanda ya sani Yanajin yanda take kokarin janye hannunta daga cikin nasa ya sake ruqo hannun, yaqi Bata Damar qwace hannun, domin ta taqaita maganar tasu Sai tace "Dan Allah Yaya karka sakecin abincin da Anty Lubna zata baka, wannan shine abinda nakeso nafadama, Amma fa Amana" (😊) Da babu Gara dinga ragewa ko kadaanne πŸ€—πŸ€— Sharhi ✍🏻 Amnah El~Yaqoub [2/14, 12:43 AM] El~Yaqoub: INSAAF Writing by:Amnah El yaqoub 23&24 Like my page on Facebook πŸ‘‡πŸ» https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 "Amana" Yamaimaita kalmar a ransa, Ana cikin magana ta hankali tasako masa wata yarinta Wai amana,wannan maganar ake kira da amana, yazuba mata ido Yana kallonta yaga idonta yayi wani tsuru tsuru, tsananin tsoro yataru yayi mata yawa, kamar ace mata kyattt tafita aguje, tsananin tashin hankalin data hango a saman fuskarsa ne yasa tasake tsorata, har tana dana sanin fadar maganar da tayi, hannunta dake cikin nasa ya sake riqewa kamar zai 6allata yace "waye yafada miki?" Girgiza kanta tafara yi tana kokarin qwace hannunta tun kafin ya karyata, kafin tabude baki tayi magana ya daka mata wata irin tsawa "nace waye yafada miki?!!!" "Babu kowa Yaya, amma...." "dakata" βœ‹πŸ» Ya dakatar da'ita ta hanyar daga mata hannu Sannan yasaki hannun ta dake cikin nasa yace "tashi kibar nan wajan" Cikin sauri ta tashi tawuce daki, Dan dama atsorace take dashi, tana zuwa daki kuwa taji motsin ruwa a toilet alamar Amrah na wanka, kayanta na qauye tabude, ta dauko laptop din ta nadeta acikin wasu kayan, sannan tasake 6oyeta da kyau Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un kawai yake maimaitawa acikin ransa, ya saka hannu ya hargitsa sumar kansa kamar sabon kamu, tayaya haka zata faru? A'ina Yarinyar nan taji wannan maganar? Anya kuwa da gaske ne? To tayaya za'a ce Lubna tanason ganin bayansa? Gaba daya kansa ya kulle, yama rasa wanne irin tunani zaiyi,mutum dayace ta Fado masa, yasan cewa kuma zata kamo masa bakin zaren, Dan haka kai tsaye ya nufi gidan Ishraqa, anan ya sake tadda wani abun mamakin, wannan d'akin daya sameta rannan yauma aciki ya ganta, shide yasan cewa Ishraqa Bata aiki da kanta, saide tasa me aiki tayi mata, saide abinda ya danganci mijinta ne kam Bata wasa dashi, tana kiyaye wannan bangaren, amma Sai gashi yauma yazo ya ganta tana gyaran gado tuquru, zama yayi tare da dafe kansa dayake masa mugun ciwo, yace "Ishraqa akwai matsala" *** ****** *** Tunda sukai waya da oga har yau takasa samun sukuni, yanzu tayaya zata zubawa Asim guba, wadda zata karya masa garkuwar jiki? Laptop din de tayi wannan alqawarin, amma guba kam, Sam Sam bazata iya zuba masa ba, to ai idan tazuba masa ma itace a wahale, hatta wankansa kanta zai dawo, komai itace zata masa, Gara ta haqura kawai, to Amma kuma idan batayi ba mutumin nanfa zai'iya zuwa gida yatona mata asiri awajan Asim, ita kuma Bata fatan Hakan, idan mutanan gidan sukaji abinda ta aikata kafin ta shigo gidan haqiqa kowa saiya tsaneta Tashi tayi tana Zagaya d'akin, Ahankali tafara magana "gaskiya bazan saka masa ba, nahaqura kawai, idan nasaka masa ma nice a wahale, computer de idan naganta dole zan kwashe komai na basu, kodan wannan shegiyar Insaaf din" "momy ba kince babu kyau Ana cewa mutum shegiya ba" Ta tsinci muryar Widad tana doko mata tambaya, cikin sauri ta kalli yarinyar taga tana wasa da babyn roba, batasan ma tashi go dakinba Ajiyar zuciya tayi tace "mekike yi anan? Tashi muje muyi lesson" Widad ta daga mata hannu, babu musu Lubna ta dauke ta, tayi kissing kumatun yarinyar sannan suka fice daga d'akin *** ****** *** Ishraqa tayi Ajiyar zuciya bayan tagama sauraron Asim wanda yake mata Bayani idanunsa yayi jajir, tace "Nifa Asim kwata kwata ban yarda da maganar yarinyar nan ba, tayaya Lubna yanda idonta yarufe a kanka, matarda taqi jinin ace wata mace ta rabe ka itace zata kasheka, to inasu Mamy da kowa da kowa na gidan? Kisan kai aiba qaramin abu bane, kaima daka tsaya ka saurareta kafi 6atamin rai,haka kawai baka Santa ba, bakasan tushen taba, yarinya taga kakawo ta gida, tasamu waje ta wanke, ba dole tayi tunanin rabaka da matarka ba?, ni ranar nan naganta tare da Amrah, inda nasan haka halinta yake dana wanka mata Mari tafice tabarmin gidana, tun tuni kayi gaggawar sallamarta, inma gidan marayu ne kakaita, kokuma kasan inda zaka kaita, inba hakaba kanaji kana gani zata rabaka da danginka " Dago kansa yayi ya kalleta "gidanki kuma?" Cikin yatsina fuska Ishraqa tace "Um Wai na rungume ta, bansan meya sanyayamin raina ba harna kulata, nide na fadama, inma baka sallameta ba wallahi da kaina zanzo nafitar da shegiya daga gidan" (😣) Ajiyar zuciya yayi, wannan furucin na Ishraqa shine yad'an kwantar masa da hankali, kuma saiya sake tuna irin soyaiyar da Lubna take masa, komai yimasa takeyi, tagama shagwaba shi, Ahankali yace "hakane, nima nafi tunanin shirmanta ne kawai, Amma I am sorry Ishraqa, bazan iya korarta ba, ina tausayin ta" Wannan kalmar tausayin da yayi ne ya sanyaya mata jiki, lokaci daya 'yarta mafi soyuwa a ranta tafado mata, batasan inda take rayuwa ba, tanacin abinci ko bataci, atiti take ko agida, a mace take ko araye, Sai tayi Shiru kawai batace masa komai ba, amma bacin rai kam yarinyar ta6ata mata rai, Wai Kisan kai 😠 Kallan bedsheet din d'akin yayi yaga ta sauya, yace "mekike yi adakin nan ne?" Ranta ad'an 6ace tace "Insaaf na gyarawa" πŸ˜‚ Kallanta yayi cikin mamaki "kinganta ne?" "a a, kuma Naga Insaaf din kakasa sani?kakasa ganinta a jikina? ni dama Ina gyara mata kullum" Mamaki yaqara kama Asim, "Ishraqa soyaiyar nan tayi yawa,waiku larabawa meyasa kuka cika son Yara dayawa ne? yanzu kina nufin inda tana nanma kece zaki mata aikin?" "to menene Asim? 'yartawa qwalli daya jal idan bansota ba wazan so? Wallahi idan tana nanma yimata zanyi, muyi wasa tare, muyi fira tare, mu shirya muyi kwalliya muje unguwa mudawo, idan tahadu da saurayi injirata tagama tazo mutafi, mudawo gida in sata agaba muyi bacci, nifa kaga Asim iyayena basu tsananta minba, Nima bazan matsawa yata ba, wani matsin Idan yayiwa Yaro yawa masifa yake janyowa, Saikaga qawayenta suna hure mata kunne daga gefe, a lalata ma tarbiyar daka Dade kana dora yaronka akai, bansan me zatai a bayan Idona ba, Gara najata a jikina tazama qawata, zatafi sakewa dani ta dinga sanar dani damuwar ta fiyeda qawayenta" "zaki sata agaba ki kwanta tare da'ita, toshi kuma mijin naki fa?" "shima ban Hana shi ba Asim, yazo mu kwanta wallahi" πŸ˜‚ Kansa ya Girgiza "Lalle Ishraqa soyaiyar taki kuma tazama tafitar haiyaci, idan kun fita saurayi yatareta zaki tsaya agefe kijirata, kundawo gidan ma bazaki bar yarinya tasake tahuta ba, saurayinta ya kirata awaya suyi waya, bazaki Bata Damar hakan ba Shima kina tare da'ita, no, kibar yarinya tasake mana " " eh lalle Asim na lura idan Insaaf tana nanma Kaine zaka dinga hure mata kunne takula Samari πŸ˜‚ Koda yake ai babu damuwa ma tunda Kaine saurayin " Annurin fuskarsa ne ya sauya lokaci daya, Dan qaramin tsaki yaja ya miqe tsaye zai tafi, wayar sa ce tafara qara yad'auka "Amjad" Daga dayan bangaren Amjad yace "na'am Yaya, Yaya akwai matsala fa, baqin nan dazasu zo daga Singapore sunyo waya, kuma idan sukazo zasu tafi da wannan takardar dakukai zama dasu Akan ta ne, Allah yasa de kayi printing dinta" Kansa ne yasara, Ahankali yasamu gefen gadon yazauna, Ishraqa na ganin haka itama ta zauna tana fuskantar sa, cikin tsananin damuwa yace "wallahi Amjad takardar nan Bata nan, bancireta daga cikin computer ba" Amjad yace "yasalam, yanzu Yaya ya zamuyi?" "wallahi bansaniba Amjad" Yana fadar haka ya kashe wayar Yana furta kalmar innalillahi wa Inna ilaihirraji'un "meyake faruwa Asim?" "Ishraqa abubuwa sunyi min yawa,bansan... bansan... Yaya zanyi ba" ya qarasa maganar ararrabe cikin damuwa Wani irin tausayinsa ya kama Ishraqa, jikinta yayi sanyi tace "meyake faruwa ne?" "akwai mutanan dazasu zo daga Singapore ne, zasu karbi takarda awajan Amjad, zasuyi sign, to tana cikin computer nan data 6ata" Cikin nutsuwa tace "Asim" Kasa amsawa yayi,kawai juyo wa yayi ya kalleta batare dayace komai ba, cikin sanyin murya tace "Insha Allah, Allah Yana tare dakai, ka kwantar da hankalinka, muyi Addu'ah komai zaizo cikin sauqi insha Allah" Daga kansa yayi cike da damuwa yace "nagode" daga nan ya tashi yafi ce cikin tashin hankali Tsawon kwana biyu Asim ya dauka Yana cikin tashin hankali, yarasa wazai fadawa, jiyake dazai tariyo baya da yayi, jiyake inama ace bai tafi da wannan computer ba, inama ace yabi shawarar Amjad bai dora komai akai ba, tashin hankalin dayake ciki ne yasa ya manta da maganar makarantar Amina, abinci ma baya'iyaci sosai, idan yazauna saide yayi Shiru Yana tunani, babu wanda yayi tunanin Yana cikin damuwa ne saboda dama haka yake ba magana yake ba,acan 6angaren Amjad ma Yana can Yana nasa tunanin yanda za'ai su samu mafita Zaune suke adaki Amrah tana koya mata daurin dankwali, bayan sun Gama tace "nikam Minal Yaya maganar school dinki ne?" "har yanzu Yaya bece komai ba Anty Amrah" "toke meyasa bazaki masa magana ba? Kije ki sameshi yayi miki lesson dinki, idan kun Gama saikiyi masa maganar karatun" Littafin ta tadauka tace "tona tafi" Wannan Karon babu alamun tsoro a tattare da'ita tanufi falonsa, Addu'arta daya Allah yasa baya tare da wannan jarababbiyar matar tasa Tana budewa kuwa ta ganshi azaune a falon yariqe kansa da hannayensa duka biyu kamar me ciwon kai Shikuwa Asim tunani yake sosai, baisanma ta shigo falonba, tunani yake kode zaibi jirgi ne yakoma qauyensu Minal ya tambayi su baba ko sunga computer dinsa? Wata zuciyar tace masa to ai kuma suma sun bar Garin, maigari ya koresu "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un" , ya maimaita hakan a ransa Ahankali ta qaraso wajansa ta tsugunna, tace "Yaya" Amma bai dago ba,hannunta ta daga ahankali zata ta6ashi, a Karo na biyu tasake cewa "bakada lafiya ne?" Cikin sauri ya dago kansa sukai ido biyu, ganin hannunta yayi dab dashi kamar tanason tabashi, yabi hannun nata da kallo Yana mamakin meyasa Bata tsoron ta6ashi wani lokacin? Sai kuma yayi tunanin cewa ai yarinya ce, sannan Kuma babu wanda yake kusa da'ita a gidan Sama dashi, may be tana ganinsa ne kamar yayanta Itace tafara dauke idonta daga cikin nasa, tace "Yaya lesson nazo" Girgiza kansa yayi, cikin damuwa yace " ba yanzu ba,kitashi kitafi" Furucinsa ne ya tabbatar mata da Yana cikin damuwa, kokuma ba kalau yake ba, duk da dama amsar tasa haka take ba yawa ba dadi Gabanta ne yafara faduwa ahankali tace "bakada lafiya ne?" Bebata amsa ba, kansa kawai ya Girgiza mata,kallonsa tayi tasake cewa "kayi hakuri" sannan ta tashi tafice, bayan ta yabi da kallo, saida yaga fitar ta sannan ya maida kansa cikin tafukan hannunsa Batafi minti goma da fitaba Lubna ta shigo falon nasa da wata takarda a hannunta, akan hannunta kujerar dayake zaune ta zauna, fuskarta fal take da kwalliya, tace "Daddyn Widad inaso zanyi oder wasu kayan kwalliya ne daga Dubai, shine nakesan dubu dari biyu" Dago kansa yayi ya kalleta, tunda safe yake cikin wannan halin amma Bata tambayeshi menene yake damunsa ba, yarinya qarama yanzu ta tashi daga wajan amma saida tayi masa wannan tambayar, Anya kuwa har yanzu Lubna tana sonsa kamar da? To kode gaskiyar Minal dinne da tace Lubna tanaso ta kashe shi? πŸ€” Kai tsaye yace mata "Bandashi" Bude baki tayi cike da mamaki "bakada shifa kace? Kawai de kace bakada niyyar bani, amma bawai bakada shi ba" Cikin bacin rai yace "Wai Lubna meyake damunki ne? Meyasa bakida hankali da tunani wani lokacin?" "dakata Asim, Dan nazo wajanka neman kudi ba shine zai baka Damar dazaka dinga cimin mutunci ba" "OK, haka kikace? Yanzu ke bakiga halinda nake ciki ba zakizo haka ko ladabi babu kimin maganar kudi?" "kawai kace Lubna banda niyyar baki kudi, bazan bayarba, amma ba maganar wani hali dakake ciki ba, ni bakaga halin danake ciki ba?" "fice kibarmin falon nan please" "basai ka fadaba" tana fadin haka tafice daga falon, Kai tsaye dakinta tashige tana cizon yatsa,bacin rai fal ranta, magana tafara afili, "ni Asim zaiwa haka akan dubu dari biyu? Zaiga abinda zai biyo baya kuwa" Tana fadar haka tatashi ta dauko maganin datace tafasa saka masa a abinci, ta kalli maganin tace "Gara ayita ta qare, inma ka kwanta jinyar zan iya qarawa gaba, Lubnan da kasani Bata yanzu ba" kitchen tashiga tahada masa jallop din taliya, girkin ya tsaru, yaji nama manya manya aciki, saida tazuba maganin aciki, sannan tajuya tasake Juyawa yanda zai hade jikin abincin, ta dauko flet mai kyau, tajuye abinci duka aciki, sannan tawuce tafuto falo, anan taci Karo dashi da mamy azaune a falon, da alama akwai maganar dayake mata,falonsa takai abincin sannan tadawo wajan su, tsugunnawa tayi aqasa, cikin ladabi tayi masa magana "Daddyn Widad na kaima abinci, nasan kana jin yunwa" Kallanta yayi, yaga kamar ba'ita ce tagama yimasa rashin kunya ba, amma yanzu harda tsugunnawa a gabansa, yace "no, kibarshi" Mamy tace "a a, haba Asim, yazatasha wahala tayi ma girki kaqi Ci? Kaje Kaci, Nima zanje daki nayi wanka" Daga kansa yayi, sannan ya nufi dakinsa, Lubna tasaki wani matsiyacin murmushi tawuce nata d'akin Yana shiga falon ya kalli abincin, gaba daya shaf ya manta da maganar Amina, uwa uba abokiyar shawarar sa Ishraqa tabashi shawara cewa Minal qarya take, hakan yasa ya shiga dakinsa zai wanke hannunsa Yana shiga d'akin widad tafado cikin falon tana qwala masa Kira, "Daddy yau ni a wajanka zan zauna muyi wasa" Ko sauraren amsar sa bayiba, tasaka hannu acikin jallop din taliyar nan tafara Ci 😭 Sosai takecin abincin,tashi tayi ta kunna kayan kallon falon, tadawo ta zauna tanaci tana kallo, yatsina fuska tayi, saboda yanda taji cikinta ya murda, lokaci daya ta qwalla qarar dayaja hankalin 'yan gidan gaba daya, aguje Asim yafuto daga cikin d'akin, Yana zuwa falon yaga Widad a kwance wani irin kumfa Yana fita daga bakinta Gabansa ne yayi mugun faduwa,lokaci daya maganar Amina ta Fado masa ((Dan Allah Yaya karka sakecin abincin da Anty Lubna zata baka, wannan shine abinda nakeso nafadama, amma fa Amana)) Amrah da Amina gaba daya jikinsu rawa yake, tuni hawaye ya wankewa Amina fuska Cikin sauri yayi kanta Yana jijjigata, kamar wani zararre haka yakoma "Widad! Widad!!" Dayqar tabude bakinta tace "Da... ddy..." Lubna ce ta shigo d'akin da gudu, tana ganin halinda Widad take ciki, ta yanke jiki ta Fadi sumanmiya Mamy ce kawai mai qarfin halin Kiran driver, cikin sauri kuwa Asim yashiga suka nufi asbiti, Amrah da Amina kuma suka kinkimo Anty Lubna suma suka bisu abaya Gaba dayansu atsaye suke sunyi cirko cirko suna jiraan futowar likitocin da suke duba Widad, tsawon minti talatin aka dauka, suna tunanin zasu futo amma shiru, har Anty Lubna ta farfado anyi mata qarin ruwa ta fixgeshi tafuto, Sai kuka take kamar ranta zai fita Mamy tana gefe daya atsaye tana salati, Amina da Amrah kuwa kowa hawaye yake, Asim kuwa ko kallon inda Lubna take baiyi ba Kusan awarsu daya da wani abu suka futo, doctor ya kallesu yace "saide kuyi hakuri Yallabai, munyi iya bakin kokarin mu, amma hakan Bata samu ba, Allah yayi mata rasuwa" Wani irin sarawa kansa yayi kamar an Doka masa guduma, lokaci daya ya sulale yazauna awajan Yana ambaton kalmar "innalillahi wa inna ilaihirraji'un" Amina da Amrah suka saki wani irin kuka, kowa Sai Kiran sunan yarinyar suke, mamy ma hawaye ne yake zubo mata, tasa hannu tana sharewa, me Widad taci? Anty Lubna tadora hannu aka "nashiga uku na, nide 'yata Bata mutu ba, nashiga uku widad Karki tafi ki barni, karkimin haka widad, Asim ka kashe min yata, meyasa zaka Barta taci?" Cikin tsananin bacin rai ya nufeta ya sharara mata wani kyakkyawan Mari, su mamy sukai kansa, amma kafin su riqeshi ma yadamqi wuyan Lubna ya shaqeta," Mena miki? Meyasa kikeson kasheni? Kifadamin waye yasaki? Saina kasheki yanzu yanzun nan, tunda kika kashe min 'yata " Gaba daya Sai waje ya kaure da kuka, mamy tana kuka tana dukan hannun Asim yacika Lubna amma Asim ya kama wuyanta yariqe, daga mamy har Amrah babu wanda ya Fahimci komai, ita Lubna tana cewa Asim ya kashe mata yarinya, Shima Yana cewa Lubna ta kashe masa yarinya, Daqyar da taimakon likitocin asbitin aka qwaci Lubna daga hannun Asim, idanunsa yayi jajir, amma baiyi hawaye ko daya ba, tarin wahala Lubna take saki, numfashinta Sai Sama yake, cikin kuka mamy tace "haba Asim....,da hankalinka da komai, so kake ka kashet....." Kafin ta qarasa yatareta, "mamy ku dauke ta daga gabana nadena ganinta, babu ni babu ita, taje na saketa" To jama'ah, karkuji ni Shiru zan Dan huta insha Allah, tunda muka fara bamu hutaba πŸ€— Insaaf tana gaisuwa gareku Wanne irin sirri Lubna take tsoron atona mata? masu maganar yaakamata Ishraqa ta hadu da yarta, da masu cewa ya kamata ta bashi laptop dinsa duk najiku, babu yanda za'ai an rubuta labari a banje shi adawo da gaba baya, idan kukai hakuri zamuzo wannan ga6ar insha Allah, nagode πŸ™πŸ» ✍🏻 Amnah El~Yaqoub [2/15, 10:19 PM] El~Yaqoub: INSAAF Writing by:Amnah El yaqoub Like my page on Facebook πŸ‘‡πŸ» https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 25&26 Cikin kuka mamy tace "Asim.... saki Asim?" Cikeda 6acin rai yace "Mamy na tsaneta, ta cutar da rayuwata, kuma Sai taga abinda zai biyo baya" Wannan furucin nasa da yayi na sakine yasa su Amina da Amrah cigaba dakuka, ita kanta Lubna kalmar sakin daya fada tasata acikin wani tashin hankalin, jitayi numfashinta Yana Sama-Sama, tasa hannunta aqirjinta, likitocin dasuka qwace ta ne suka fara kokarin temaka mata. Adede lokacin tashigo asbitin hankalinta atashe,yauma kamar kullum laffaya ce a jikinta, tana zuwa ta nufi wajan mamy datake kuka sosai, shikuma Asim kansa Yana qasa yamaqi kallon kowa. "mamy meyake faruwa? Megadi ya shiga gidana yacemin kun kawo Widad Asbiti, meya sameta?" Kafin mamy tabata amsa yadago kansa yana mata nuni da Lubna "Gatanan...ki tambayeta" Juyawa tayi wajan Lubna wadda gaba daya Bata haiyacinta, likitocin dasuka riqeta ne suka maidata wani daki, tajuya ta kalli Amrah da Amina, suma taga suna tsaye suna kuka, tasake kallon mamy itama kukan take, cikin tashin hankali tace "Dan Allah Ku fadamin, meyake faruwa ne? '' Mamy ce ta share hawayen idonta tace"Ishraqa Widad tarasu yanzu " " innalillahi wa Inna ilaihirraji'un.... " Shine abinda Ishraqa tafada tazauna awajan jagwab, hawaye ne yafara ambaliya Akan kuncinta, ta kalli Asim da kansa yake qasa"meyasame ta? Batada lafiya ne?" Sai alokacin yad'ago kansa, idanunsa sunyi jajir, har gara ace yayi kuka zaifi wannan tsananin bacin ran dayake ciki Yace"lafiyarta kalau Ishraqa, ni tayi niyyar kwashewa ba widad ba, dama nafada miki ai " Ishraqa tasake fashewa da kuka tana fadin" hasbinallahu wa ni'imal wakeel " Mamy ta kallesu cikin sauri, akwai wata aqasa kenan, da alama dama can shida Ishraqa sun san da wata maganar Doctor ne ya shigo yace" zasu iya zuwa police station suyi report daga nan saisu dauki yarinyar, tashi yayi cikin qarfin hali yace "Bama buqatar hakan doctor, already munsan wanda ya aikata hakan, Bari mu dauke ta muje gida kawai" Doctor ya jinjina kansa sannan sukai cikin d'akin da yarinyar take Bayan shigar su d'akin Sai kowa yayi kanta, Gatanan a kwance kamar zaka kirata ta tashi Abubuwa da dama suka dinga dawo wa Amina a ranta tatuna ranar da ta dauke mata mayafi, da ranar datake cewa tanaso su dinga wasa tare,wani irin abu ya tare mata maqoshi, Sai kuka take, Amrah kuwa kawai kallon gawar yarinyar take, Wai widad ce ta mutu Ishraqa kuka kamar 'yarta ce tarasu, bakomai ne yafado mata a ranta ba Sai 'yarta, inama ace itama zataga koda gawar 'yarta ne? dataji dadi a ranta, kuma hankalinta zaifi kwanciya, tasan Insaaf ta riga ta mutu, amma yanzu batasan ma ina take ba Ahankali ya tsugunna ya shafa fuskar yarinyar, (Daddy yauni a wajanka zan zauna muyi wasa) Yatuna maganar yarinyar ta qarshe, Sai alokacin yaji qwalla tacika Idonsa, yasa hannu zai share Yana kokarin maida kukan, mamy ta dubeshi "kayi kuka Asim..., Kar hakan yajama matsala please kayi kuka ko yaya ne..." Girgiza kansa yayi "a a mamy, Allah yaji qanta, Allah yayi mata rahma yasa mai cetonmu ce" Gaba dayansu suka amsa da amin, bai qara cewa komai ba, daga haka yadauke ta suka tafi gida Tunda a kayiwa Widad sutura aka kaita makwancinta gidan yayi Shiru, Daddy da Amjad dakuma wasu daga cikin dangin Lubna duk sunzo, saide har yanzu duk wanda yazo idan ya tambayi ina take, aka fada masa tana asbiti Tofa idan yatafi baya dawowa πŸ˜‚ Ishraqa kuwa tana gefen mamy tsoron duniya ya shigeta πŸ˜ƒ Kawai tuna lokacin da Asim yaje mata da maganar take, gaskiya mutum ba'a bakin komai yake ba, haka kuma mutum ba abin yarda bane, to Amma Yaya akai ita wannan yarinyar tasan da wannan maganar? Mamy kuwa tana amsar gaisuwa ba tayiwa Asim maganar Lubna ba, kuma batayi wa Ishraqa magana Akan maganar dataji sunayi itada Asim ba Gaba daya hankalinta Yana wajan Asim din, tunda yamma daya shige dakinsa bataga yafuto ba, gaisuwar ma su Daddy ne da Amjad suke karba a compound, gashi beci komai ba, haqiqa yau taga amfanin Lubna, ko yaya inde mutum yanada mata yafi ace bashida ita, tasan dayana da wata matar dole zata sashi yaci abinci,zata jashi a jiki ta rungume shi ta lallasheshi,ta Fahimci halin dayake ciki, to Amma menene yake faruwa atsakanin Asim da Lubna? Ita Lubna tace ya kashe mata yarinya, meyasa zai Barta taci abinci?Hakan yana nufin itadashi sunsan akwai guba acikin abincin kenan kome? Toshima kuma Yana cewa takashe masa yarinya, dole zata nemi qarin Bayani awajan Asim, Amrah ta kalla tace "tashi kikaiwa yayanki abinci" Amrah tatashi zata kitchen din, jiri ya debeta, tazauna cikin sauri, sauran jama'ar falon suka hau yimata sannu Ta kalli Amina tace "jeki kai masa Minal" Ahankali tatashi daga gefen Ishraqa 😊 Dan dama tunda ta ganta a falon saida tasan yanda tayi ta mamuqa tashiga tazauna agefenta, wani ma tsaf zaice tare sukazo gidan Kitchen din tashiga tahada masa komai kamar yanda taga sunayi, sannan ta nufi dakinsa Afalonsa ta ganshi, Yana kwance Akan doguwar kujera ya lumshe Idonsa, ga TV nan tana yi Yana sauraron karatun alqur'ani Ahankali ta tsugunna, tazuba masa abincin d'an kad'an, batayi karanbanin zubawa da yawa ba, tasan cewa Kota zuba dayawama ba lalle ya'iya ciba Kallonsa tayi, tarasa tayaya zatayi masa magana,ba tasan Yaya zatayi ba, amma tabbas shidin abin tausayi ne, ba tasan hanyar da matarsa takebi wajan kwantar masa da hankali ba, wata zuciyar tace, ya kamata ki bashi kulawa, akwai auren sa a kanki, haqqinsa ne ki kula dashi, ki saurareshi, ki lallasheshi koda hakan shine abinda zaki masa na qarshe a rayuwarki, matsawa tayi gab da inda kansa yake ahankali tace "Yaya..." Yana jinta, amma bai Bude Idonsa ba, da farko ma yayi tunanin Amrah ce, kansa ne yake masa mugun ciwo, bayason damuwa ko kadan Ita kuma dataji yayi Shiru, tayi tunanin ko Yasamu bacci ne, tannunta tadora Akan goshinsa taji da zafi sosai, cikin sauri ta dauke tace "subhanallah..." Ahankali yabude Idonsa yazubesu a kanta, kallonsa tayi damuwa ta baiyana Akan fuskarta qarara "bakada lafiya ne? tashi Kaci abinci saina kawoma magani, tashi Yaya" Beyi niyyar cin abincin ba, saboda jin cikin sa yake duk acunkushe, amma ganin yanda duk ta rikice, shine yasa ya tashi ahankali yazauna, abincin ta dauko tadawo gefensa tazauna Akan kujerar itama, kusancin nasu yayi kusanci har tana jin yanda jikinsa yake gogar nata Spoon din ta dauko, tadebo abincin takai bakinsa, cike da yarinta tace "haa, Bude bakin Kaci abinci" Mamaki ya kama Asim, yanda ta Dage zata bashi abincin saikace irin mamansa d'innan kokuma wata babbar mace, wannan yarinyar haqiqa Amjad zai samu kulawa sosai idan sukai aure, shida yake ganin Lubna tana kulawa dashi ashe wasan Yara take.... Amina tayi saqare da cokali a hannu, gabanta ne yafara luguden faduwa saboda wata shawara da zuciyarta tabata, Anya kuwa zata iya? Sai kuma wata zuciyar tace to ai mijin ki ne, ba haramun bane, kwarjinin da yayi mata ne yasa hannunta yad'an fara rawa kadan, Ahankali takai dayan hannunta kan lallausan lips dinsa, tabude masa bakin nasa,saita ji laushi saikace bakin Yara, jin hannunta Akan lips dinsa yasa ya lumshe Idonsa babu Shiri πŸ™ˆ Saida yaji tana kokarin saka masa spoon din abakinsa ne sannan yabude Idonsa, beyi musu ba kuwa ya qarasa Bude mata bakin tafara bashi abincin, cikin zuciyarsa Yana tunanin dole zai dauki kyakkyawan mataki Akan Minal, yanda take masa d'innan wata Rana Sai Asamu matsala, duk tabi ta maidashi wani Dan jariri cikin mintunan dabasu fi goma ba, zata iya yiyuwa anata bangaren tana ganin hakan ba komai bane, zata iya yiwa kowa, but anasa bangaren akwai matsala gaskiya Ko cokali biyar beyi ba, yaji wani irin amai yataso masa, kafin yayi yunqurin tashi harya fara yi ajikin hijabinta, duk ya 6ata mata gaban hijab din, lokaci daya ta rude, tafara jera masa sannu, sannan tatashi taja hannunsa tarakashi toilet ya wanke bakinsa, hijabin jikinta tacire, tasake kamoshi suka dawo falon, Akan kujerar ta zaunar dashi tana masa sannu Kansa kawai ya d'aga mata, Idonsa a lumshe, tace "Bari naje nakawo ma magani awajan mamy" Cikin sauri yariqe hannunta, dayan hannun nasa Yana dafe da goshinsa yace "karkije, ciwon Kaine kawai, zai daina anjima" Dawowa tayi tazauna tasaka hannunta duka biyun ta janye nasa hannun daga kan goshinsa tace "to sannu, Allah yasawaqe" Baisan lokacin da yaji hawaye sun zubo daga idanunsa ba, tunda widad ta mutu har suka kaita makwancinta beyi kukaba Sai yanzu Amina ta rikice ganin hawaye a'idon babban mutum kamar wannan, tarasa Yaya zatayi masa, duk saita daburce, itama kukan taji Yana kokarin zuwa mata, Bata yi kokarin Hana kanta ba tabar hawayen suka fara sintiri a kumatunta, cikin kuka tace "Dan Allah kayi hakuri kaji...." Lokaci daya ya fuzgota jikinsa yasaki wani irin kuka, sosai yake kuka kamar mace, baqin ciki sa daya me yayiwa Lubna? Yanzu badon Allah yakawo Minal gidan ba kenan da yanzu shine yamutu, meyasa takeson kashe shi? Dama tanada wata manufa ne akansa? Cikin sheshshekar kuka yace "thank you Minal..... Nagode... Nagode... ta dalilin ki.... Yauma na rayu...., akaro na biyu" Kukan yaci gaba dayi sosai, kansa Yana kan Boobs dinta, yayinda hawayen Idonsa suke silalowa zuwa cikin rigarta suna sauka a saman breast dinta Numfashin tane yake wani irin gudu, gaba daya ya d'aure mata kai, babba dashi Yana kuka, saita ji ta nemi nata hawayen tarasa πŸ˜ƒ Ahankali tadora hannunta akansa, tanaso ta janye masa kansa dake kan qirjinta, amma yaqi Bata Damar hakan, domin kuwa sake riqeta yayi Yana kuka kamar Dan qaramin Yaro Batada zabin daya wuce taqara bashi hakuri kozai daina wannan kukan, Ahankali tace "Dan Allah kayi hakuri" Saida yasha kukansa, sannan yayi Shiru, amma kansa Yana nan inda yake πŸ™ˆ Turo kofar d'akin akayi aka shigo, cikin sauri takai kallonta ga wajan, gabanta ne yafadi ganin Muhsin abokin sa ya shigo, cikin sauri tafara qwace jikinta daga nasa, Saide kuma ta makara, domin kuwa Muhsin yariga ya gansu Asim kuwa ko a jikinsa, Ahankali ya d'aga, ta cikin sauri kuwa tafice daga d'akin hijabin ta a hannu Muhsin ne yazauna tare dashi har can dare, sannan yatafi gida, Yana tafiya kuwa Daddy da mamy suka shigo d'akin nasa, alokacin harya sauya kaya zuwa jallabiya zai kwanta, adakin nasa suka zauna gefen gado, shikuma yazauna kansa aqasa, Daddy yace "Asim Iyayen Lubna sunzo sun sameni sunata bani hakuri, meyake faruwa ne kayi mana Bayani" Be 6oye musu komai ba yafada musu abinda Amina tafada masa, da kuma shawarar da Ishraqa ta bashi, da yanda tasa masa maganin har Widad taci, sannan yaqara da cewa "Daddy saide kuyi hakuri, amma dole zankai Lubna wajan hukuma, dole zatayi musu Bayanin wanda ya sata yin wannan aikin" Mamy tace "innalillahi wa Inna ilaihirraji'un.... wannan masifa dame tayi kama? bazan hanaka ba Asim, may be ma dasa hannunta acikin mutanan da suke bibiyar rayuwarka, tunda zata iya Sama guba a abinci ai zata hada baki dasu, kakaita koma inane, nayarde maka" Daddy yace "gaskiya Lubna ta aikata babban kuskure, amma ni a ganina idan aka kaita wajan hukuma ma kamar zubarwa kanmu mutunci ne, ai abun kunya ne ace Asamu irinta acikin zuri'armu, abarta da Allah kawai, zataga yanda makomarta zai kasance, gashi yanzu tayi niyyar kashemin dana, amma al'amarin yajuye yakoma kan 'yarta, kayi hakuri my son, insha Allah zaka samu Yara masu albarka, wanda zasu futo daga tsatson uwa tagari " Mamy tace"Eto kuma hakane gaskiya, to kayi hakuri Asim" Shide Asim yarasa gane wanne irin hakuri ne da Daddy, duk lokacin da abu ya sameshi saiyace zai kula da bangaren, kuma daga baya saide abashi hakuri, yanzu wannan dinma gashinan yace yayi hakuri Daga musu kai yayi kawai, yace "zan kwanta" πŸ˜‚ Basu qara ce masa komai ba,mamy takashe masa wutar d'akin suka futo Haka gidan sukaci gaba da zama Shiru, har akai sadakar ukun Widad Alokacin ne kuma masu buqatar takardar nan turawan Singapore sukai waya zasu zo washe Gari, tashin hankalin da Asim ya shiga, yawuce misali, haka Shima Amjad, Amina da Amrah suna d'akin mamy suna gyara mata,Sai lailaye gadon nan suke, mamy tana kan sallaya tana waya da Daddy daya fita unguwa, Amjad ne yashigo, duk ya Rame yayi wani iri, kwanciya yayi agefen gadon, Amrah ta daka masa wata uwar harara, ta tsani tana gyaran gado azo a kwanta wallahi πŸ˜– Mamy ta Gama wayar ta kalleshi, "Autan mamy, jeka kiramin yayanka" "magana kuma mamy?" "Eh jeka turomin shi" "mamy, yayafa baya cikin nutsuwar sa yanzu, Nima daga wajansa nake, ko magana ma bayason yi, kibari Hankalinsa yad'an dawo saikuyi maganar cikin nutsuwa, may be danyarabu da matarsa ne shiyasa, kuma taqi dawowa, Aida yanzu andawo da'ita, ni dama nagaji da jarabar kishin ta wallahi 😳, Gara daya saketa, idan besaketa Bama wataran saide kiji na saketa " Amrah tace"to sannu Daddy" Mamy ta jinjina kanta "meyasameshi yanzun?" "mamy akwai wata takarda da mukai missed, kuma mutanan da suke buqatar takardar zasuzo su karba ne, bamu San abinda zamu ce musu ba" Mamy tace "wacce irin takarda ce wannan? To kuyi wata mana, da a'ina kuka Barta harta Fadi?" "mamy wanda yafara rubutawa baya qasar, kuma da tawadar qasaar Germany akayi rubutun, idan muka sauya da namu zasu gane, takardar yaboyeta tare da sauran document dinsa acikin laptop dinsa, kuma yace computer ta 6ata" Gaban Amina nane ya yanke yafadi, cikin tashin hankali tace "innalillahi..." Daga nan tafice daga d'akin cikin sauri, gaba dayansu suka bita da kallo Afalo ta wuce Asim daya shigo gidan yazauna cikin damuwa Da gudu tashiga dakinsu, a haukace tabude kayanta ta dauko masa computer sa, innalillah kawai take maimaitawa cikin ranta, da yanzu ta cucesu, bayin Allah ashe neman computer suke Bata sani ba Tana futowa daga d'akin ta ganshi afalon azaune, cikin sauri ta qarasa wajansa tace "Yaya..." Yana dago kansa, ta miqa masa laptop din, mamaki, faduwar gaba, tsananin murna suka kama Asim, cikin sauri ya karba dawani irin farin ciki Akan fuskar sa yace "Minal... a'ina kika ganta?" Itama murmushi tayi masa, tace "kayi hakuri Yaya, dama tana wajena, na manta ne ban bakaba, Sai yanzu naji Yaya Amjad yace ita kuke nema" Shiru yayi Yana kallonta, murmushin yayi mata kyau sosai, zai Iya cewa wannan ne Karo na biyu dayaga murmushi Akan fuskarta,amma dariya kam bai taba ganin Amina tayi dariya ba, amma farin cikin data sashi yau, Shima yayi alqawarin zaisa ta, saiya nemo mata iyayenta, sannan dole zai ware mata Rana guda yakai ta wajan wasan Yara tayi abinda ranta yakeso (😟😒 πŸ˜”) Afili yace "kiramin shi, jeki turomin Amjad din" Juyawa tayi, ta koma d'akin mamy tana basu labari, ai suna jin abinda take fada musu duk suka dawo falon gaba dayansu, Rabon da mamy taga Asim yadanyi walwala tun mutuwar Widad, amma yau gashi Minal tasa shi, lalle taqara yarda minaal itace farin cikin Asim Kunna computer yayi, ta kawo komai Yana nan yanda yake kawai keyboard dinta ne suka lalace, Amjad yabawa, yace yaje yadauke musu duk wani abu dayake kanta, yadena ajiye komai da komai Akan computer daga yau πŸ˜ƒ Saide In abun yazama dole *** ****** *** Washe Gari Amjad yahau jirgi yakoma Yola,aranar kuwa baqin sukazo suka karbi takarda, hankalin kowa ya kwanta Asatin Amjad yadawo Lagos, yayiwa mamy maganar auren sa da Minal, tace masa kawai yaje yaci gaba da shirin biki, aikuwa nan da nan gida ya rikice, Sai siyaiyar kaya mamy take dan'autanta zaiyi aure *** ****** *** Muhsin ne ya shigo falon nasa, ganinsa da computer agaba yasa ya jinjina kansa "sannu da aiki abokina" Saudaya ya kalleshi "sannu da zuwa Muhsin, Bari nasa a kawo ma ruwa" "a a barshi, gani ga fridge din idan zansha zan dauka" Asim yace "OK" Muhsin yayi Shiru Yana saurarensa, yayi tunanin zai ajiye abinda yake yabashi lokaci sudanyi fira ko kadan ce, amma Sai yaga babu alamar hakan Ajiyar zuciya yayi "amma Asim duk matar da zata aureka Sai tayi hakuri dakai, kullum aiki, Kai baka gajiya da wannan aikin ne? Office aiki gida aiki, haba, ya kamata ka ragewa kanka wannan aikin" Murmushi yayi "Muhsin kenan, wanne irin hakuri kuma? Bagani azaune agida ba, tana ganina" "to tana ganinka tana ganin photo, kaida photo ai duk daya Asim, yauwa Asim ina wannan yarinyar me manyan idanun nan?"ya qarasa maganar Yana kallon yanayin Asim "wacce yarinya kenan?" "wannan qanwar taka, kyakkyawan nan, Yama sunan ta.... Amina ko... Yawwa Minal" Annurin fuskarsa ne yadauke, tuni ya kawar da computer tasa gefe guda, ya kalleshi yace "tambayarta kake?" Muhsin yace "yes, saboda ai Nima kamar qanwa tace, tunda kaima qanwar ka ce" Jinjina kansa yayi, sannan yace "ta'ina? Lalle Muhsin kanada kalan dangi dakuma cusa kai, ita Minal dinne harta zama qanwar ka?, to kashiga cikin gidan ka tambayesu, may be tana ciki" Muhsin yayi murmushi ganin ya kunno abokin nasa, yace "tokai Asim menene na daukar zafi dannace qanwata? Koka fara Santa ne dakake kishi" "inrasa dawa zanyi kishi Sai Minal? Karka manta bayan alaqar datasa na kawota gidannan, ina ganinta yarinya qarama, wadda inda ace nayi aure da wuri zan haifi kamarta" πŸ˜‚ Zaro ido Muhsin yayi, "yanzu Asim Minal din zaka Haifa? Lalle bakada mutunci, kuma Kai qaramin Dan renin hankali ne, Malam dama na tambayeka ne domin na gwada ka Akaro na biyu Inga kana sonta ko baka sonta, kasan ita yarinya qarama ce wadda zaka haifi kamarta amma ahakan kake liqe mata, kana yiwa yarinyar mutane wayo kana jin dumin qirjinta, πŸ™ˆ Nan nazo nasameka d'ame d'ame Akan qirjinta kana wani kuka saikace qaramin Yaro, kagama jin tudun qirjin yarinya kazo kana huramin hanci kai baka sonta, to qinta kake? " Wani malalacin murmushi yayi" Muhsin kenan, wato kana bani mamaki wani lokacin, daka ganni Akan qirjin nata saime? Dama de kawai kacemin zuwa kayi Kamin hayaniya saboda rannan kazo kaganmu a haka, todana kwanta Akan qirjin nata cemaka akai wani abu naji? " Muhsin ya Girgiza kansa" a a, ina zakaji wani abu kuwa, kaida kake waliyi, Nima bance kaji komai ba, amma ina baka shawara, ka gaggauta auren yarinyar nan, idan Bahaka ba duk lokacin da Amjad ya aureta wataran zaka aikata wa matar qaninka abun kunya " Ransa ne yabaci sosai, ya saka hannu ya dafe kansa " Muhsin waye yafada ma zan iya auren Minal? Tayaya zankai kaina ga mutuwa? Bayan rasuwar mahaifina banqara jin tsoron mutuwa ba Sai da widad tatafi, da hankali na da komai tayaya zankai kaina cikin rijiya? Inason raina, saboda haka dan Allah katashi katafi Nina gode da wannan ziyarar " Muhsin yayi murmushi yace"to Allah de yatsare gaba Asim, danna baya kam yariga ya faru" πŸ˜‚ Daga nan yafi ce daga falon, shikuma yaja computer sa yanaci gaba da aikinsa *** ****** *** Ganin shirin da ake yi a gidan, yasa Asim Kiran Amina falonsa Taje tazauna a qasan kafet din d'akin,tana kallonsa, cikin ranta tace shide kullum aiki, inama inada dama wallahi dasai na qwace, mutum kullum babu hutu, daga aiki Sai aiki πŸ™ Hankalinsa Yana kan computer daya sake Yana wani aiki, yace mata "akwai maganar danake so muyi" Tace "to Yaya" "kishirya anjima akwai inda zamu fita" Tasake cewa "to Allah yakaimu, zan shirya" Jinjina kansa yayi, wannan Karon ma be kalleta ba Yana aikinsa yace "medame kike shiryawa, me kike buqata wanda za'a siyo miki?" Dago kanta tayi ta kalleshi, kamar bada ita yake magana ba, Hankalinsa Yana kan laptop din gabansa, tace "Yaya shirin me kuma?" Kai tsaye yace "na aurenku mana, Keda Amjad" Dam! Dam!! Gabanta yayi wata irin faduwa, cikin sauri tace "Aure kuma? Wanne irin aure Yaya?ni bamuyi maganar dashi ba, be fadamin ba" ta qarasa maganar cikin rikici, kana ganinta zaka san cewa a rikice take Batare daya Kalleta ba yace "yanzu kinsani" Idanun tane sukai rau rau, ta kalleshi "nifa inada aure" Computer gabansa ya ture, yajuyo yazubawa manyan Idonta wani kallo, shide yasan cewa a gabansa aka koreta, kuma da bakin ta tace kafin Ammar yarasu yasaketa, idan ma bai saketa ba to ai yariga yarasu, yaushe tayi wani auren? Tanaso tace masa tasake auren wani mutumin na bakwai kenan ko me? Kode batasan girma da darajar aure ba ne shiyasa zata fara wasa dashi? Sake kallon qwayar idonta yayi yace "yaushe kikai auren? Waye mijin naki?" Gabanta ne yafara faduwa, cikin alamun tsoro ta dago kanta ta kalleshi sannan tace "Gaka" Group d'inda basa sharhi insha Allah nadena yimusu posting Masoyan littafin INSAAF nagode πŸ™πŸ» Comments Sharhi πŸ™πŸ» ✍🏻 Amnah El~Yaqoub [2/17, 12:07 AM] El~Yaqoub: INSAAF Writing by:Amnah El~Yaqoub 27&28 Like my page on Facebook πŸ‘‡πŸ» https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 Akwai abubuwa dayawa wanda ya kamata ace na rubuta saboda aso Widad, amma haka na ciresu saboda karma yarinyar tashiga ran mutane dayawa, saina rubuta page daya biyu amma ko sako yarinyar banyi aciki ba, ashe gudun Gara nayi 😟, duk da haka ban tsira ba, ya kamata fa ace muna tunawa da mutuwa, bazai iyu a rubuta littafi haka babu wani wanda zai ta6a ran mai karatu ba, kenan ma soyaiya kadai zamu rubuta πŸ˜ƒ, mutuwa tana kan kowa, wanda basuji Dadin mutuwar Widad ba suyi hakuri please πŸ™πŸ» Ina masoyan Daddy? Toku matso kusa😊 __________ Gabansa ne yayi wata irin faduwa, yanayin fuskarsa ya sauya, yayi quri da ido Yana kallonta cike da mamaki, yace "what? Kinsan me kike fada kuwa?" Ahankali tadago idonta tana kallonsa, amma takasa ce masa komai, dama tasan cewa hakan zata iya faruwa koma fiyeda haka, daqyar ta'iya daga masa kanta, muryarta na rawa tace "E...eh wallahi, Allah da gaske nake" Gaskiyar daya hango Akan fuskar yarinyar ne yasa yagane gaskiya take fada masa, but tayaya?, yaushe hakan tafaru? Shida yake gudun Amjad ya aureta ashe shine rikicin yake kansa?Ahankali Ahankali yafara maimaita kalmar innalillahi wa Inna ilaihirraji'un.... Cikin ransa πŸ˜‚ To inhakane menene ma amfanin daga Hankalinsa Akan neman computer? Shida yakusa mutuwa bai saniba? Yana yiwa Amjad kallon gawa ashe shine gawar, 😟 Yana yiwa Amjad kallon zai auri bazawara ashe shine yake auren ta bai saniba Hannunsa yasa ka cikin sumar kansa, yakasa furta komai, yanzu shikkenan Shima bin Widad zaiyi? Kallonsa tayi, taga yakasa magana, Ahankali cikin nutsuwa tafara magana "tun muna qauyensu Malam mai Allo, shine wanda ya daura mana aure, lokacin bakajin dadi, yafadamin washe Gari zai sanar da kai amma Allah bai nufa ba washe Garin yarasu, idan baka yarda ba zan nunama sadakin daya bani yace shine sadakin aure na, matarsa ma sheda ce, tasan komai, tasan da auren, amma ni banason in qara yin wani aure a rayuwata, Bana fatan ace haqqin mutune yadinga taruwa akaina, Bana fatan ace tasanadina wani ya sake mutuwa, nasan cewa wata qila da haqqin rayukan mutanan da suka mutu ta Sanadina ne yasa har yanzu ban samu iyayena ba, Dan Allah karku min aure Akan aure, inaso ka sauwaqe min, ni bazan sake aure ba har abada.... "tana qarasa maganar hawaye ya silalo daga cikin idanuwanta, ahankli tatashi tafice daga falon, tanaso ta tambayeshi karfe nawa zasu fita? Amma babu Damar hakan Dan taga fuskarsa tayi wani iri kamar zaiyi kuka πŸ˜‚πŸ˜‚ *** ****** *** Tunda ya zauna a falon yake sakin tsaki shi kadai, ga waya a hannunsa Yana danne danne, Amrah ta kalleshi "Amjad lafiya kuwa?" Saida yayi Dan qaramin tsaki sannan yace "nida wani Gaye ne muke tafka fada a Facebook, Sai batamin rai yake, shine Nima nace masa inda zan ganshi Sai an qwace shi a hannu na" 😳 Amrah batasaan lokacin data saki wata irin dariya ba, tace "Kaine zaka daki mutum har a qwace shi a hannunka?" Shima dariyar yayi "ke duk kurin banza nefa nakeyi, Kinga mutane Sai hakuri suke bani, jisuke wani babba ne, Nima kuma Sai da naduba profile pic dinsa naganshi wani gabjeje, tayaya da hankalina zan yarda nahada hanya dashi? Hauka nake? Saide in bashi hakurima ince ya kamata mubar fadannan haka "🀣🀣 Me Amrah zatayi inba dariya ba, sosai takecin dariya sannan tace "yawwa Amjad, Nika tunamin ma,kaga pic din wannan gayen, last month nahadu dashi" Wayar datake bashi ya karba, ya kalli gayen sosai, babu qarya ya'iya dressing daga ganinsa Dan wanka ne, yace "A'ina kuka hadu?" "Facebook" "to inde Yana sonki da gaske yafuto mana" Murmushi tayi "Yana sona gaskiya, kuma Nima Ina ganinsa Naga Yamin, amma nace yaushe zaizo, saiyace min Wai bayaso yazo gida da farko, yafuso mufara haduwa awani wajan, Sai kuma yasa time yazo gida" Amjad ya Girgiza kansa Yana kallon Amrah cike da mamaki "yanzu Amrah idan ance miki yarinya kihau mutum da bala'i, tayaya zaki Ci gaba da kula shi, bayan daga jin wannan furucin nasa kinsan mayaudari ne, kirabu Dashi kawai, ba mijin aure bane, idan mutum yanason aurenki da kansa zai fara miki maganar aure, idan beyi miki ba dazaran kince yafuto zai futo, saboda shirme kin tsaya kina kula wannan gaulan, Karki sake kula shi nafada miki " Amrah tasaki baki da hanci tana kallon Amjad yanda yadage Yana mata fada saikace wani Yaya Asim, cikin masifa tace"to Daddy" Kallanta yayi shi ma cikin fishi yace"Daddy kuma? Namiki kama da Daddy ne?" " to waye zaiyi abinda kayi inba Daddy ba?, kawai daga nunama pic din mutum saika hau yin fada kamar kasamu wata qanwar ka kokuma sa'ar ka?,harda kallon qwayar Idona kana cemin yarinya, ban girmeka ba? " " to naji, karkuma abin naki yawuce gona da iri, ya'isa haka Karki kuskura kisake cewa kin girmeni " " nafadama angirmeka Amjad kayi abinda zakayi, Dan renin hankali kawai, marar kunya " " OK haka kikace ko? To nan gaba Karki sake kawomin shawararki, kije ki qarata da samarin ki masu qaton ciki " " Nima karka sake kawomin labarin yanmatan ka, itama Minal din dakake shirin aura karka sake kawomin maganar ta daga yau, komai yazo qarshe tsakanina dakai " Suna wannan fadan nasu Minal tazo tawuce su,gashin idonta duk sun hadu, alamun Tasha kuka, tashige dakinsu tareda rufewa *** ****** *** Hannuwansa zube cikin aljihun wandon suit din dake jikinsa, tunda tafita daga d'akin yakasa zaune yakasa tsaye, Sai Zagaya d'akin yake, gaba daya kansa ya kulle yama rasa Yaya zaiyi? Wazai fara tunkara da wannan maganar? Anya kuwa Amjad bazai shiga cikin wani hali ba idan yaji wannan maganar? Wata iska me zafi ya furzar, ya qarasa kusa da computer sa da yayi gefe da'ita tun dazu, wayar sa ya dauka yakira Muhsin "Muhsin akwai matsala" "matsala kuma Asim? Meyake faruwa?" "kazo ka sameni please, ina cikin bala'in tashin hankali Muhsin"πŸ˜ƒ "subhanallah... to gani nan zuwa" cewar Muhsin Duk'da yakira Muhsin har yanzu yana tsaye yana zagaye qayataccen falon nasa, shaf ya Dade da mantawa da aikin dayake a computer Muhsin ya shigo falon Hankalinsa atashe "Asim meyake faruwa? Gabana faduwa yake wallahi tunda Kamin waya" "Muhsin dangane da yarinyar nan ne" yafadi maganar kamar zai fashe da kuka 😒 Murmushi Muhsin yayi "Alhamdulillahi, tafada ma ne?" Cikin sauri Asim yaruqo hannunsa, "mekake nufi tafadamin? Kaima kanada labarin abinda tafada min ne?mekake nufi da tafadamin?" Muhsin yadafa kafadarsa "nifa ba komai nake nufi ba, ina nufin ta fadama ne tana sonka ne itama?" "Muhsin kadena maganar wasa, yarinyar nan fa tafadamin akwai aure na a kanta, bansan... bansan Yaya zanyi ba" Muhsin yace "Alhamdulillahi, Asim kace komai yazo mana cikin sauqi, kawai yanzu muyi kokari mujanyo hankalin yarinyar nan" Kansa ya dafe da hannunsa sannan yace "Muhsin fice daga gidannan Dan Allah kafin na Bude Idona" Muhsin yasaki dariya, babu musu yafi ce Yanajin fitar Muhsin zuciyarsa tagama yanke masa abinda ya dace, Dan haka cikin sauri ya nufi d'akin mamy. Turare take fesawa a jikinta, tagama shiryawa kenan zata futo falo, ta ganshi ya shigo d'akin nata, yanayin fuskarsa ta kalla kawai tasan ba kalau ba, zama yayi a gefen gadon yace "mamy akwai damuwa" Takowa tayi tazauna agefensa, "meyake faruwa? Ko bakada lafiya ne?" "lafiyata kalau mamy, munyi magana da Minal ne... shi ne... shine..." Daga nan yayi Shiru yakasa qarasawa, jansa tayi jikinta, ta sassauta muryarta "Asim, fadamin menene?" "Mamy munyi magana da'ita, ina tambayarta metake buqata ne lokacin bikinsu, shine tacemin tanada aure" Cikin sauri mamy tace "aure kuma? Dama ba budurwa bace? To Ina mijin nata yake kadauko ta kataho da'ita nan?" Jikinsa ne yayi sanyi, ya kalli mahaifiyar tasa "cewa tayi nine" Dasauri mamy tace "Kaine mijinta? Ina Minal din take?Bari nakirata naji daga bakinta" Tana fadar haka tafara kokarin tashi, sake riqeta yayi sosai a jikinsa "A a mamy karkije, zan saketa!" Dasauri ta kalleshi, taga alama kuma yanda yafada din zai Iya sakin nata, to meke faruwa ne? Dama baya sonta ne amma yake nuna kishi a kanta? To kode Shima besan yakamu da sonta ba? Rabuwa tayi dashi ta dauki wayarta takira Amrah tace taturo mata Minal da Amjad Amjad ne yafara shigowa, Yana ganin Asim yakoma kusa dashi yazauna,tana shigowa d'akin ta gansu shida Amjad duk sun mamiqe ajikin mamy kamar wasu yan yaye, musanman Asim ma yawani rirriqeta kamar zata gudu ta barshi Ahankali tazauna aqasa tace "mamy gani" Mamy tace "Minal yanzu Asim yake fadamin wata magana, menene gaskiyar al'amari ne?" Gabanta yafara faduwa, yau kam taga ta kanta, Ahankali tace "hakane Mamy, kafin muzo nan wani malami yayi mana aure ni dashi" Amjad najin haka yazaro Idonsa waje 😳😳 Cikin sauri yace "Aure kuma? Keda Yaya Asim din?" Cikin sauri ta daga kanta sannan tace "Amma... Ni banaso, nafison na zauna haka, banason nasake yin wani auren" Amjad yace "subhanallah... Minal meyasa zakice haka? Innalillah..., meyasa baki fada mana tunda wuri ba? Da yanzu alhaki Yana kaina" yajuya ya kalli Asim yace "Yaya Dan Allah kayi hakuri" Fuskarsa cike da bacin rai ya tashi daga jikin mamy ya kama kunnansa yariqe "meyasa zaka ban hakuri? Kaine baka sanar da'ita shirin dakake yi ba, shiyasa, but Duk abinda kakeso inde baifi karfina ba zan mallaka mashi Amjad,saboda haka zan saketa ka aureta" Cikin sauri Amjad ya manta da zafin da kunnansa yake masa, ya kalli Asim "A a Yaya, na hakura wallahi, Nima nabarma ita" Asim ya Girgiza kansa yace "banason musu" Mamy tace "ya'isa haka dan Allah, Minal tashi kije idan alhaji yazo zanyi masa Bayanin komai" Tashi tayi, su kai ido hudu da Asim cikin sauri yadauke Idonsa daga kanta, idan tunanin ta yazama gaskiya saitaga kamar tsoron ta yake ji πŸ˜†πŸ˜‚ Tana fita, Shima Amjad ya kalli mamy "Zanje nahuta mamy, kaina yanamin ciwo" Mamy tace "to saida safe" daga nan bai sake magana ba yafuto daga d'akin, jiyake kansa kamar zai rabe gida biyu, mamy kuwa kawai de tace masa saida safen ne, amma dole zata bishi dakinsa taga halin dayake ciki, bazata iya barin autan ta cikin wani hali ba Yana zuwa tsakiyar falon nasu yadora hannunsa aka, jiyake kamar yafashe da ihu, hanyar dakinsa yanufa, Sai kuma yajuyo ya nufi d'akin Amrah, budewa yayi yashiga, Sai kuma ya tuna dazu sunyi fada πŸ˜‚ Saiya dawo baya, yarufe musu d'akin, Amrah tana kwance Akan gado ta hango shi, tayi tunanin zai shigo Sai kuma taga yakoma,Ahankali tatashi tabi bayansa Tana zuwa dakinsa ta hango shi acan qarshan gado yana kuka, cikin sauri ta qarasa wajansa tazauna kusa dashi tace "nashiga uku Amjad meyasameka kake kuka?" Yana ganinta kusa dashi yafada jikinta Yana kuka wiwi kamar mace, mamaki ya kama Amrah, ta kalli yanda yafado jikinta abinda bai taba yiba tunda suka tashi gida daya, janye shi tafara yi daga jikinta tace "Amjad, kayi magana mana menene?" Cikin kuka yace "Narasa ta Anty Amrah, Narasa Minal, ashe anyi musu aure itada Yaya Asim" "ohhh, saboda kaji Minal tana auren Yaya Asim shiyasa kadawo kacemin Anty Amrah kenan ko..."🀣 Girgiza kansa yayi dake jikinta, cikin shagwaba yace "Niki daina yimin wasa" Wani irin abu taji a jikinta, tafara kokarin janye jikinta, amma Amjad saiya dora kansa Akan cin yarta, ya Zagayo da hannunsa ta baya yariqe cikekken hips dinta Lokaci daya taji wani yarrrr! Hannunta tadora Akan hannunsa dayake kan qugunta tace "kai cikani, saikace kasamu mamy duk ka riqeni, kayi hakuri mana to, Kai saika dinga kuka saikace mace" Hannunsa yadauke daga kan hips dinta ya share hawayen, cike da shagwaba yace "Toba ke ce kikaqi lallashi naba" πŸ˜” Gaban Amrah yafadi, tambayar kanta tafara yi, Anya kuwa kalau Amjad yake, menene hakan yake mata? Cikin sauri tamiqe tsaye har Yana dago kansa Yana kallonta cikin mamaki, jitayi yanayin ta Yana sauyawa, wacce irin masifa ce wannan tarasa Akan wanda zataji feeling Sai qaninta? "Anty Amrah tafiya zakiyi?" yadoko mata tambaya Tace "Amjad banson shirman banza, nabaka hakuri kaqi hakura Sai rirriqeni kake kamar kasamu wata sa'arka, kuka kakeso na zauna na tayaka?" Shima cikin fishi yace "to Kar Allah yasa ki tsaya din, kitafi mana, kifi ruwa gudu"πŸ˜… Mamy ce tashigo d'akin tace "kai innalillah... Wai yaushe zakuyi hankali ne? Amrah da girman ki ban hanaki kula Amjad ba? Miye ya shigo dake dakinsa?" Baqin ciki ya kama Amjad, Wai da girman ta, to ba dole ma ta raina shi ba, tayaya za'ai mamy ta dinga fadar haka agabanta? Haushi yasa ya maida kansa cikin fillo yaqi kallon mamyn πŸ˜ƒ Amrah kuwa fuska babu walwala tafice daga d'akin, kullum mamy saita dinga cewa itace babba ta qyale Amjad, koda yaushe ita ce me daukar laifi, wallahi yasake yimata rashin kunya qararsa zata kai wajan Yaya Asim Washe Gari suna zaune afalo bayan Break,Amrah tana danna wayarta, Amina kuwa kallo take, mamy na karanta Hisnul Muslim Futowa yayi cikin qananun kaya, riga da Wandon jeans, amma rigar yadora mata jacket asama, kayan sunyi masa kyau sosai kasancewar ba sakawa yake ba, daga suit Sai manyan Kaya, sune kawai kayan sakawarsa Qamshin turaren dayasa yacika falon nasu Babu wanda bai daga kai ya kalleshi ba, idanun sane yahadu da nata, cikin sauri ya janye Idonsa daga cikin nata Mamy tana lura dashi, Amina kuwa shaf tama manta da maganar auren da tayi masa jiya, saboda abin be dameta ba, ba auren ne agabanta ba, Bata fatan ace wani mutum yasake mutuwa adalilinta, haka babu abinda takeji a ranta game dashi, tasan de tana hashi girmansa a matsayin sa na babban mutum, tsoron data hango acikin qwayar Idonsa jiya, yauma shita gani πŸ˜ƒ Sai abin ma yabata dariya, Ahankali tayi murmushi ta dauke kanta daga kallonsa Amrah ta rissina tace "good morning Yaya" Daga mata kai yayi kawai, yanemi waje yazauna, already sun gaisa da mamy tun bayan asuba, amma duk da haka saida ya dubeta yace "mamy Barka da safiya" Kallansa tayi taga yanda yake wani dauke kansa, tarasa gane wanne irin karfin hali Asim yake dashi, kanason yarinya amma bazaka nunaba, koda yake may be tunanin ta ne yazama gaskiya, Shima ba lalle yasan yanason Minal dinba Ataqaice tace masa "yauuwa" Tamaida dubanta ga Amina tace "Minal, tashi ki kawo wa Asim break fast dinsa" Cikin sauri ya kalleta, Minal kuma, Wai meyasa mamy take masa hakane? Bayan da itace take kawo masa da kanta, haka yayi Shiru yasake dauke kansa Ahankali tatashi ta dubeshi tace "Yaya ina kwana?" Batare daya dago kansa ya kalleta ba yace "lafiya" Dan tabe bakin ta tayi tawuce kitchen din tana magana a ranta, idan auren ne bayaso ai komai yazo cikin sauqi, tunda itama bataso kawai saiya saketa Kawo masa abincin tayi ta ajiye, ko zuba masa batayi ba Takoma wajan zamanta tazauna, ransa yaqara baci, Tome yarinyar nan take nufi? Shine zai zuba abincin da kansa kenan? Mamy tana kallonsu ta gefen idonta, tanaso taga Yaya zasu qare Bude abincin yayi, yayi Dan qaramin tsaki sannan ya kalli Amrah "ke taso kizuba min abinci" 😠 Kafin Amrah tatashi mamy tace "Minal tashi kizuba masa" Yanzun ma cikin sauri ya kalleta, mamy Sai saka yarinyar nan take tana kulawa dashi ba tasan gawa ake Bawa kulawa ba, shi kam yasan cewa yanzu tasa ta qare 😒 Babu musu tatashi tazuba masa, tazauna kenan Amjad ya shigo falon cikin shirin fita Kallan Amrah yayi, suka sakarwa juna harara, sannna yazauna kusa da mamy, Amina ta gaida shi ya amsa cikin mutunci Yace "mamy zanbi Yaya office, yau tare zamuyi aikin" "Autan mamy kabar naka aikin kadawo nan ka zauna ko?" "mamy bazan iya missing dinki dayawa ba, amma zan koma insha Allah" Tace "yawwa Autana, Allah yayi muku albarka, Daddynku fa Yana hanya, around 11 zai qaraso" "Allah yakaimu mamy, idan mundawo daga office saimu gaisa" Wayarsa ce tayi qara, yad'auka tare da amsawa "Yallabai gobe kanada meeting din gaggawa a malesia, ticket dinka yazama ready, zaka iya tafiya yau ko gobe" Tace "babu damuwa, zan tafi yau din" daga nan yakashe wayar ya miqe tare da kallon Amjad Amjad ya tashi yafice Yana yiwa mamy sallama Ta kalli Asim tace "to saika dawo, idan alhaji yazo zanyi masa magana Akan maganar ka data Amina" "babu damuwa, zanje Malesia yau, zuwa jibi zan dawo insha Allah, kimin Addu'ah" "Allah yakaika lafiya" cewar mamy, takalleshi taga babu wani abun daya dauko, ko brief case dinsa ma yau bai dauka ba, idonta ya sauka Akan wayoyinsa guda biyu, ta kalli Amina tace "Minal dauki wayoyinsa ki rakashi compound" Al'amarin mamy kuma yafara Bawa Asim tsoro, kallanta yayi yadauke kansa, cikin sauri yafice daga falon Mamy ta sake kallon Amina tace "tashi mana" Ahankali tatashi ta dauki wayoyin nasa akaron farko, tabi bayansa dasu, Amrah sai dariya take qasa qasa Tana futowa ta ganshi atsaye a bakin kofar falon, hannunsa ya miqa mata batare dayace komai ba Babu musu ta saka masa wayoyinsa akai tajuya zata koma ciki Mamaki yakama Asim, wato idan ya matsu yaje lafiya ko karyaje duk shiya sani,duk da mamy tayi masa Addu'ah ai malamai sunce Addu'ar mata Akan mijinta batada hijabi awajan ubangiji, kawai zata bashi wayoyi ta juya ko Addu'ah babu 🀣 Ajiyar zuciya yayi yabi dogon gashin ta da kallo sannan yace " ke baki iya Addu'ah ba ko?" Cikin sauri ta juyo ta kalleshi "Yaya ai danaga mamy tayi ma, amma kayi hakuri" taqarasa maganar idonta na ciko da qwalla Cikin ransa yace yarinyar nan tacika shagwaba dayawa, afili yace "kina Jina, zanyi waya da Muhsin yazo yakaiki school, har yanzu ke qaramar yarinya ce, kicire tunanin aure aranki kiyi karatu,kuma banson kula qawaye da Samari kinjini?" Cikin sauri tace "eh Yaya, Allah yadawo dakai lafiya" "Amin" abinda yace kenan yajuya zuwa wajan motarsa da Amjad yashige tun dazu Tunani yafara, ya kamata ace Yana dawowa ya tsaya ya nutsu yanemo Iyayen ta, ko hakan zaisa ta dinga dariya kamar kowa Sai wajan 11:47 Daddy yadawo, bayan yaci abinci yahuta mamy ta kalleshi tace "Alhaji auren Amjad da Minal fa bazai iyuba" "inajin ki, saboda me? Ko akwai abinda ya faru?" "akwai Alhaji, babba ma kuwa, Asim ne yayiwa yarinyar maganar auren, saitake fada masa ai tun kafin suzo nan akwai Malamin daya daura musu aure" Cikin sauri ya kalleta yace "tanan ta 6ullo kenan" "bangane ba Alhaji kamar Yaya tanan ta 6ullo?" Gyara zamansa yayi yace "Hajiya, kifita daga sabgar yarinyar nan, nagama lura da'ita kawai kwadayin kudi da son abun duniya ne yakawo ta gidan nan, da zata auri Amjad, tadawo tace Asim mijinta ne bayan tagama gane sirrin gidan tagano Asim ne me kudi, toni ban yarda da wannan batu ba, tayaya babu sheda babu komai haka kawai zan dauki Yarona inbata? Taje ta kawo min mutumin daya daura auren, idan naji daga bakinsa zan iya yarda, idan hakan ne zansa Asim din yasaketa ta tattara kayanta tabar mana gida " Mamy ta kalleshi cikin damuwa tace"Alhaji kayi hakuri mana, nifa na yarda da maganar Minal, alhaji ba zatayi qarya ba, tanada hankali" "Mezai Hana kice haka tunda kece kika haifeta? Nace mezai Hana kice haka? Tunda itada Amrah duk daya kike ganinsu, Toni nagama magana, tashi kifice kibar min nan" Babu musu mamy tatashi tafuto, falo ta zauna tarasa yanda zatayi, tayaya Alhaji zaice araba aure? Asim yanason yarinyar nan, ita uwa ce tanason farin cikin danta, tasan cewa Minal itace farin cikin Asim, agaba zasuji Dadin zama da juna bayan soyaiya tagama wanzuwa atsakanin su, Kanta ne ya kulle, takira Aminiyarta, tafada mata komai, nan da nan qawarta tabata shawara takira Babban abokin Daddy tasanar dashi, insha Allah zaisashi ya janye wannan maganar Suna kashe waya mamy takira Alhaji Umar babban abokin Daddy, Alhaji Umar ransa yabaci sosai, yace taje ta kaiwa Daddy wayar, zaiyi magana dashi, idan yaqi karba kuma tarabu dashi zaizo gidan da kansa anjima Mamy tayi masa godia ta kashe wayar, sannan ta nufi d'akin Daddy Kasancewar abude tabar kofar lokacin da zata futo baiji alamun shigowarta ba, Yana tsaye yajuya bayansa, yabawa kofar baya, yayinda yake kallon window din d'akin Magana yake yi cikin fishi, gaba daya Idonsa yarufe, cike da tsananin bacin rai yake fadin "Zan koreta yanzu yanzun nan, ni yarinyar nan tun lokacin dana ganta naji na tsaneta, kuzama cikin shiri zan koreta daga gidana yanzu tana futowa ku kashe ta , duk itace Sanadin lalacewar komai, karka manta itace Sanadin barin Lubna daga cikin gidan nan, tayaya nida nakeso dukiyar sa data Insaaf duk sudawo hannu na zatazo ta hargitsa min komai?Akan kudi zan iya yin komai, sauran dukiyar gadonsu ina sane nahanasu,Dan haka sauran wadda take hannunsa ma zanyi kokari na qwace ta, Yaron ne akwai shegiyar basira shiyasa abin ya gagara, shikuma Amjad ta riga ta shanye shi bare nahada baki dashi, saboda haka ku kula, tana futowa agama da'ita, Shima Asim din Yana dawowa babu abinda zan jira, zan kashe shi..... Yauwa saboda..... " Bata iya tsayawa tagama jin komai ba, jiri yafara daukan ta, haka tafara ganinsa bibbiyu, daga nan komaai na d'akin yafara rabewa a'idonta Yana zama guda biyu Daqyar ta'iya daga qafarta tafuto daga cikin d'akin batare daya lura da'itaba Ikon Allah ne kawai ya kaita dakinta lafiya, tana zuwa kuwa duhu ya mamaye idonta, tafadi a qasan tiles din d'akin Amrah datake zaune tana kallo a system dinta cikin sauri ta diro daga kan gadon ta cicimeta tana kiran sunan ta "mamy...., mamy meyake faruwa?" Kuka tafara tana jijjigata, ganin kamar mamy ta suma ne yasa tatashi Dasauri ta kawo ruwa ta yayyafa mata, cikin ikon Allah kuwa tafarka, tana Bude idonta tace "Amrah, tashi kikira Minal ku hada mana kayan mu, zamu bar gidan nan" Gaban Amrah yafadi,kuka ne ya qwace mata, koma menene tasan cewa akwai damuwa mai girma, tace "mamy meyake faruwa? Meya sameki Dan Allah, kifadamin" Jikinta ne ya dauki rawa, tace "nace ki tashi kikirata" Amrah tatashi tayi dakinsu cikin sauri domin kiran Amina, mamy tana ganin fitar Amrah tafashe dawani irin kuka mai cin rai, sosai take kuka banda kanta dake mata wani irin ciwo, afili tafara furta kalmar "innalillahi wa Inna ilaihirraji'un" Wayarta ta dauka takirashi, bugun farko ya amsa yace "Mamy nah" Cikin dauriya Dan kada ya gane halin datake ciki tace "Asim kana ina?" "ina Airport mamy, mungama komai, Ana sanarwa ma a shiga ciki" Kasa riqe kukanta tayi, cikin gunjin kuka tace "Asim kadawo...." "innalillahi..., mamy kuka kuma? Meya sameki? Meyasa kike kuka kifadamin waye ya6ata miki rai?" Tausayinsa ya kama mamy, cikin kuka tace "Asim nacema kadawo gida yanzu yanzu, akwai matsala" Sharhi Sharhi SharhiπŸ€— ✍🏻 Amnah El yaqoub [2/17, 10:45 PM] El~Yaqoub: INSAAF Writing by:Amnah El~Yaqoub 29&30 Like my page on Facebook πŸ‘‡πŸ» https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 Wayar yakashe cike da tashin hankali, direban daya kawo shi Airport din yayiwa magana kawai suka juya Gaba daya hankalin sa ya tashi, menene zaisa mamy kuka? Tabbas akwai abinda yake faruwa agida, koma menene ya tabbatar ba qaramin abu bane, tunda har ta'iya cewa yafasa wannan tafiyar yadawo gida. Suna hanyar komawa gidan yadubi direban yace "kayi sauri mana" Cikeda ladabi yace "to Yallabai" Gudu yaqara amma Asim Sai yake ganin kamar ma basa tafiya, wayar sa yad'auka yakira Amjad, bugun farko yad'auka tare da sallama "Amjad kaje gida yanzu yanzu, ina tunanin akwai abinda yake damun mamy" Cikin mamaki yace "Mamy kuma? Naga lafiya muka Barta agida, meyasa meta?" "nacema kaje gida, Nima gani nan zuwa" Yana fada masa haka yakashe wayar yanajan qaramin tsaki Sun kusa zuwa gidan kenan, Ishraqa ta ki rashi "Asim baku tashi bane har yanzu?" "bamu tashi ba Ishraqa, Aina fasa ma nadawo gida, zanyi waya office sutura wani ya wakilceni" "Meyake faruwa kadawo, lafiya kake deko?" "no, Ishraqa mamy ta kirani tana kuka tace nadawo gida bansan menene yake faruwa ba, bansani ba ko wani abun ne ya faru da Minal ko Amrah" "kagani ko, aikaga abinda nake fad'ama ko, Asim nafadama kakori yarinyar nan daga gidan ka, zata rusa muku gida, na tabbatar yanzu ma itace Sanadin komai, idan an tabaka kace ai tausayinta kake, to akwai lokacin da za'azo Kaine zaka zama abin tausayi ba'ita ba, tayaya zaka dauko yarinyar da zata zo ta rusa muku farin cikinku...?" Dan qaramin tsaki kawai taja, takashe wayar Tata Cikeda bacin rai El-Hameed yadubeta yace"meyake faruwa ne Habibty?" "Nida Asim ne, Wai yafasa tafiya malesia, mamy takirashi tana kuka Wai yadawo gida akwai matsala" El-Hameed yace "subhanallah kuka kuma? Kinga tashi, tashi kishirya muje gidan, ai bekamata mu zauna ba" Tashi tayi tashige dakinta domin shiryawa, baqar abaya ta sanya, Sai dankwalin abayar data Yafa , saita koma kamar wata yar shekara talatin πŸ‘ŒπŸ» *** ****** *** Tana gama waya da Asim tanemi 'yan sanda, cikin tsananin damuwa tace su hanzarta suzo gidan Nan da nan kuwa 'yan sanda suka shigo Mota suka nufo gidan Direban Yana tsayawa a compound yabude motar yafuto, ko rufe motar beyiba yashiga cikin gidan dad'an saurin sa Kai tsaye dakinta yashiga yaga tana janyo kayanta daga cikin wardrobe tana lodasu Akan gado Har zuwa lokacin kuka take saide bame qara ba, kawai share hawaye take kamar ba'ita ba Yanda ya banko kofar ya shigo d'akin ko sallama babu hakan ne zai nunama cewa Hankalinsa atashe yake Wajanta ya nufa yariqe kafadunta, cike da tashin hankali yace "Mamy..., meyake faruwa ne?menene yasamu yaran? Ko kece akayi miki wani abu, mamy kifadamin mana" Kukanta ne ya tsananta, sosai take kuka harda shashsheka, tasa tafukan hannunta biyu ta rufe fuskarta, hannunsa yasa ya janye nata hannun, gabansa Yana faduwa sosai, yanzu kam ya tabbatar wanine yamutu kawai, jikinsa ne yayi sanyi yace "Mamy...." Dago kanta tayi ta kalleshi, tsananin tausayinsa ya kamata,tsawon wannan shekarun Yana Fama da tashin hankali, kullum Yana cikin fargabar fita, idan yayi tafiya me Nisa Sai ansan yanda akai aka shirya masa wata maqarqashiyar, ashe Daddy ne, wacce irin rayuwa ce wannan ace qanin ubanka uwa daya uba daya shine yake nema ya kasheka da hannunsa saboda son abin duniya? Ahankali tasa hannunta tarike fuskar sa dashi, Allah abin godia, Allah yaqara Kare mata danta jikinsa tafada tana cigaba da kuka,bayan ta yafara bubbugawa yace "kiyi Shiru mamy" Ahankali tasa hannu ta share hawayen nata, sannan ta janye jikinta daga nasa Tana cewa "kadawo?" Bebata amsa ba Sai wata tambayar daya sake jefo mata "meyake faruwa mamy, waye yamutu?" "babu komai Asim, kaje ka hada kayanka gidannan zamu Bari" Cikin sauri yace "barin gida kuma mamy? Meyake faruwa ne Wai?" "nacema kaje ka hada kayanka, bazamu Ci gaba da zama anan ba, inason rayuwarka, inaso ka rayu tare dani" Zama yayi a gefen gadon Yana cewa "hasbunallahu wa ni'imal wakeel Amjad ne yashigo d'akin cike da damuwa, Yana zuwa ko kula Asim beyi ba yanufeta,gabansa banda faduwa babu abinda yake, tsawon rayuwar sa da mamy shide ze'iya cewa betaba ganinta tana kuka ba, saide in suna Yara, amma da hankalin su de betaba ganiba, hannunta ya kama yariqe yace "mamy meyake damunki? Yaya yacemin kina kuka, mamy waye yasaki kuka?" Hannunta ta fizge daga cikin nasa, tayi banza da qyaleshi, be daddara ba yasake kamo hannunta, kafin yayi mata magana ta daka masa wata irin tsawa "banason nacin banza da wofi ka qyaleni dallah!!!" Cikin sauri Asim dayake zaune agefe gado ya kalleta Meyake damun mamy ne? Yau mamy ce takewa Amjad tsawa? Yaron da ko kadan batason ganin damuwar sa? Ahankali yafara ja da baya haryazo jikin bangon Dakin ya tsaya Yana kallonta cike da mamaki, zuciyarsa banda bugawa babu abinda take, gaba daya jikinsa yayi sanyi, me yayiwa mamy tayi masa irin wannan tsawar? Kode shine yabata mata ranta? Qwalla ce takawo cikin idanunsa, Ahankali yasa ka hannu ya share, Yana kallonta, amma kwata kwata mamy taqi ta kalli inda yake ma Asim yatashi ya qarasa wajansa zai lallasheshi, cikin sauri tace "Asim idan kaje wajan Yaron nan sai ranka yabaci" Gaban Asim yayi mugun faduwa, idanunsa harya fara sauya kala cikin tsananin damuwa yace "mamy Wai meyake faruwa ne? Kiyi mana Bayani mana, mamy ko Amjad ne ya6ata miki ranki?, Dan Allah kiyi hakuri, mamy Karki hukuntashi shi kadai, kiyi mana tare, Amjad Yaro ne zai iyayin kuskure" Cikin kuka tace "kanaso ka nunamin abinda yake daidai ne Asim?, toka ta6ashi kagani, wallahi Sai ranka ya6aci" Su Ishraqa da El Hameed ne suka shigo cikin d'akin nata, ganin yanda take kuka tana hada kaya ne yasa duk Sai mamaki ya kamasu Asim yace "innalillahi wa Inna ilaihirraji'un" Yakoma bakin gadon yazauna, Amjad kuwa kawai kallon mamy yake, har yanzu gani yake kamar ba mamyn sa ba, mai sonsa mai qaunarsa, wadda take fifita soyaiyar sa Akan ta 'ya'yanta El-Hameed yace "Hajiya meyake faruwa ne? Duk hankalin mu ya tashi, kiyi hakuri kiyi mana Bayani" Ishraqa ma tace "Mamy meyake faruwa Dan Allah?" Kafin tabasu amsa Amrah tashigo d'akin hannunta janye da jakar kayanta, cikin sanyin jiki ta kalli mamy tace "mamy nad'auko kayan" Ishraqa tace "kayan me kuma? Ina zaku da kaya?" Asim yad'ago kansa yace "Nima abinda tafada min kenan, inje inhado kayana zamubar gida" Sai lokacin Amina tashigo d'akin itama, hannunta dauke da kayanta, amma Bata dauki masu yawa ba, dan batasan abinda yake faruwa ba, kawai de Anty Amrah tace mata tahad'o kayanta Dan haka kala uku ta dauka kawai, Sai kuma kayanta da Inna tabata wanda suka tsinceta dashi, doguwar riga dakuma zoben gold dinta Gani tayi mamy tana kuka, Asim azaune agefen gado ya dafe kansa Tunani tafara, dama ba dazu yace mata yayi tafiya ba? Fasawa yayi kenan? ta kalli Amjad shikuma Yana tsaye agefe kamar me laifi, gakuma El-Hameed mijin Anty Ishraqa atsaye, dakuma ita kanta Ishraqan ta harde hannunta a qirjinta. gabanta ne yafara faduwa sakamakon ganin matar, ba tasan meyasa ba duk lokacin dataga Anty Ishraqa gabanta yake faduwa,saitaja ta tsaya a bakin kofar d'akin Bata qarasa shigowa ba Cikin 6acin rai Ishraqa ta kalli Asim "ku zakubar gida kokuma yarinya ce zata bar gida? Ai mamy banga amfanin barinku gida da wannan yarinyar ba, domin kuwa duk inda kukaje tana tare daku, kun kashe maciji ne Baku sare kansa ba, idan lokacin mutuwar Widad anyi dace tafadi gaskiya yanzun kuna tunanin ba'ita ce silar kukan mamy ba?" Asim yadago kansa ya kalleta yace "Ishraqa miye haka ne?" Cikin fishi tace "wanne irin miye haka? Ita Minal din ina iyayenta suke da zata barsu tazo nan tana haddasa muku damuwa acikin gida?" Daddy ne yashigo d'akin ko kula da Amina datake kofar d'akin beyi ba,Idonsa yariga yarufe, kawai so yake yaganta ya koreta tabar gidan domin flan dinsa yatafi daidai yanda ya tsara. ya kalli Ishraqa yace "abinda nace kenan Ishraqa, tafice tabar min gidana, taje ta nemo waliyin daya daura mata aure itada Asim, saina yarda da wannan maganar, idan bata kawo waliyin ba kuwa ni babu ruwana, babu auren d'ana a kanta" Baqin ciki ya kama mamy, ta juyo tana kallonsa wani irin hawayen taqaici Yana zubo mata, wata irin tsanarsa tana qaruwa acikin ranta Hawaye masu d'umi suka zubowa Amina, tasa hannu ta share, idonta Akan Ishraqa, haqiqa Sai yau tasake tabbatar da cewa ba kowa zaka so yasoka ba, yanda take jinta a ranta, Bata cancanci hakaba, yanda Allah yadora mata soyaiyar ta be kamata tayi mata irin wannan cin mutuncin ba, Bata taba jin ta tsani ganin iyayenta ba Sai yau, meyasa zasu wofintar da'ita har Ana yimata cin mutunci Akan abinda tasan cewa gaskiya ne, saboda dukiyar Asim zata dorawa kanta auren qarya ne? Kuka tafashe dashi, sosai take kuka harda sheshsheka Ishraqa ta kalli Asim tace "Aure kuma? dama aurenta kake shiyasa kacemin bazaka iya korar taba?" Asim yayi Shiru bece da'ita komai ba, yarasa meyasa Ishraqa takasa fahimtar Minal a wannan lokacin, yarinyar tanada nagartar daba kowacce mace ce Takeda itaba Ishraqa kuwa dataga bebata amsa ba saita juya Inda take juyo kukan Minal a bakin kofar daki ta kalleta tace " Hankalinki ya kwanta, kinzo kin hargitsa musu gida, kina murna ke kin auri Asim? To bari kiji, akwai yarinyar danayi masa, Karki miqe kafa " Cikin tsawa mamy tace "Ishraqa!!!" Ishraqa tajuya ta kalli mamy, bataso ta dakatar da'itaba, cikin bacin rai tajuya takamo hannun El-Hameed suka futo daga d'akin, saida tazo setin Minal ta kalleta ta wurga mata wata irin harara, sannan ta bangajeta gefe guda, har hakan yayi sanadiyar zubewar kayan dayake hannun Amina 😒 Haushi ne ya kamata, a Karon farko taji bazata qyale wannan Anty Ishraqan ba😳 Abin yayi yawa, jitake kamar tarama abinda Tama, amma kuma babu hali tunda ta girmeta,kuma Bata tashi da tarbiyar yiwa nagaba da'ita rashin kunya ba,amma duk da haka saida ta d'aga idonta, ta kalleta ido cikin ido ta Rama hararar da tayi mata, sannan ta tsugunna tafara tattara kayanta daya watse, mamaki ya kamata Ishraqa, ita wannan yarinyar zatayiwa harara? Daga ita har El Hameed binta sukai da kallo, saide Idonsu Yana sauka Akan kayan datake d'ebewa gabansu yayi wata irin fad'uwa Idon El-Hameed Akan rigar da Amina ta d'auke dakuma Dan qaramin zoben da bazai taba mantawa dashiba, da lokacin daya siyoshi a Sudan Cikin faduwar gaba yace "la'ilaha illallah, muhammadur rasulullah...." 😒(s.a.w) Sai kuka. Cikin sauri Ishraqa tafara yiwa Amina wani irin kallo idanunta duk sun furfuto waje, kamar ta6a66iya haka tafara dudduba jikinta, takama kanta tana dube dube har zuwa bayan kunnanta, lokaci daya tafashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya Gaba daya kuma sai kallo yakoma kansu πŸ˜ƒ Mamy, Daddy, Amjad, Asim, Amrah, kowa saiya zuba musu ido suna kallonsu cike da mamaki Yanzu fa suka gama fadawa yarinyar magana, tomenene kuma yasa su kuka? Ishraqa takama hannun Amina ta riqe gam, tana kuka nafitar hankali,Allah abin godia, yau Allah ya nuna mata 'yarta, Allah ya baiyana mata Insaaf dinta, gudan jininta sosai take kuka amma kuma kwata kwata takasa dago kanta ta hada ido da yarinyar 🀣 Shikuwa El-Hameed har zuwa wannan lokacin salati kawai yake maimaitawa, me suka aikata? Me suka aikata wa 'yarsu? Yanzu dama irin rayuwar da Insaaf take fuskanta kenan? Kafin daya daga cikin su ya tambayesu dalilin kukan su, 'yan sanda suka qaraso Daddy Yana ganinsu ya nuna musu Amina "Gatanan, ku tafi da'ita, ta auri dana ne saboda taci dukiya, ku kamata inspector kutafi da'ita" Gaban Ishraqa ne yayi wata irin muguwar faduwa, aure? Meyake shirin faruwa ne? Hakan yana nufin Insaaf dinta ce ta auri Asim?karfa ace game dinta da Asim ne yake shirin tabbata πŸ€” Ashe kuwa za'ayi tashin hankali duk d'an sandan daya kuskura yata6a mata yarinya πŸ˜‚ Daya daga cikin 'yan sanda mace ta qaraso zata kama hannun Amina tasaka mana ankwa, cikin sauri mamy tace "inspector" Dan sandan yajuya ya kalleta, tace "ba'ita zaku kamaba, shi zaku kama" Tofa anan kallo yakoma wajan Mamy, mamaki ya kama kowa, Amina kuwa baqin ciki ne yataru yayi mata yawa, Ishraqa tagama cimata mutunci kuma tazo tawani riqe hannun ta tana kuka,menene yayi saura kuma? Dama saboda Asim ne tazauna agidan, yanzu gashi Ana cimata mutunci Akan haka,saitaji rayuwar duniyar duk ta isheta, gidan duk yafita a ranta, neman Iyayen nata ma taji a ranta bazata sake yunqurin neman su ba, inda basu rabu da itaba dabata shiga cikin wannan halin ba, ya kamata ace tayi nesa dasu, fizge hannunta tayi taqarasa wajan Dan sandan, cikin kuka tace "nice me laifin, please katafi dani" Cikin sauri Asim ya kalleta, meyasa koda yaushe takesan sakashi a damuwa ne? Tayaya zata tafi ta barshi bayan tafada masa shi kadai gareta? πŸ™Š Mamy tace "inspector kukama alhaji kutafi dashi" Sai alokacin Amjad yasake yimata magana, yace "Mamy! Daddy nefa" βœ‹πŸ»Daga masa hannu tayi batare data kalleshi ba, kuka ne ya qwace mata tace "Alhaji na zauna dakai tsakani da Allah, nasan cewa ka zaluncemu amma ahakan na aureka, yau alhaji Kaine kake neman rayuwar Asim...? Alhaji Asim danka ne, wanne irin laifi yayi ma wanda zaisa ka kashe min dana,? wallahi saika fadawa hukuma kaida waye kukesan ganin bayan d'ana " Gaba daya d'akin ya kaure da kuka, lokaci daya kaan Amjad yasara, mamy Bata lura da kukan datake ba ta kallesu tace"saboda nasamu naqwato muku dukiyar ku dake hannunsa yasa na yarda na Aureshi tare da shawarar qawata, ashe shirme nake, nayi tunanin da Asim ya nemi haqqin mahaifinsa awajansa zai bashi, ashe bai bashiba yahada duk yariqe, na riqe masa Dansa batare da cutar wa ba, Amma shi Yana neman ganin bayan nawa 'Ya'yan " Sai yanzu ne suka Fahimci inda zancen ta ya dosa Asim de ya sunkuyar da kansa yama Kasa cewa komai, amma bayan El Hameed babu wand baya kuka acikin d'akin, Ana cikin wannan halin Amina ta silale tabar gidan batare da kowa ya lura ba Yan sanda suka kama daddy suka futo dashi "kai, ku dakata, wallahi wallahi..... , banida laifi inspector, bani kadai bane, wallahi banida laifi, sharrin shaidan ne kawai " Haka yake ta fada, amma yan sanda basu lura dashi ba suka tusa qeyarsa suka tafi dashi Ishraqa takai dubanta zuwa bakin kofa taga Wayam! babu Amina babu dalilinta πŸ€— Wata sabuwa, ko yaya Asim zaiji a page Din gaba idan yagane abinda yake gudu ne ya sameshi na auran 'yar qawarsa? Takawarku lafiya masoyan Insaaf, sharhi please πŸ™πŸ» ✍🏻 Amnah [2/20, 10:32 PM] El~Yaqoub: INSAAF Writing by:Amnah El~Yaqoub 31&32 Like my page on Facebook πŸ‘‡πŸ» https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 Ina qara Bawa masoyan wannan littafi hakuri sakamakon Jina Shiru da sukayi kwana biyu πŸ™πŸ» Banajin dadi ne wallahi, Mura ce take damuna dakuma ciwon kai sosai πŸ˜–, amma Alhamdulillahi yanzu dad'an sauqi, wanda suka sanni abaya nasan zasumin uzuri saboda inde nafara littafi kullum sainayi update, wanda suka kirani sukamin yajiki nagode sosai, Allah yasaka da Alkhairi yabar zumunci, nagode πŸ™πŸ» ________ Sai alokacin Amjad yagane abinda yasa mamy tayi masa haka, cikin kuka yafice daga gidan, yabi bayansu Daddy 😒 Ishraqa kuwa Cikin sauri tafuto daga d'akin tana dube dube, amma inaaa! babu ko alamar Amina, da gudu tadawo wajan El Hameed, Shima gaba daya ya rikice, cikin tashin hankali yace "ina take?" Hawaye sha6e-sha6e Akan fuskarta tace "bangantaba Hameed, nashiga uku na, Hameed Insaaf ta gudu wallahi, Bata sona" Cikin mamaki Mamy tace "Insaaf kuma?, me kike nufi Ishraqa?" Wajansu ta nufa cike da tashin hankali tace "Mamy wallahi itace, 'yatace Insaaf, mamy Minal itace Insaaf d'ina, nashiga uku na Yarinya ta nake Kora daga gidanan" gaban gogan namu yayi wata irin faduwa, Minal itace Insaaf? Tayaya? Meyake shirin faruwa ne yau?Wai Ishraqa Tana nufin 'yarta ya aura? Innalillah.... wannan abun kunya dame yayi kama? Shikkenan kuma, girmansa yariga yafadi, Ishraqa tayi nasara akansa Ahankali yasa ka hannayensa biyu ya dafe kansa Mamy tace "yau munga ta kanmu, Ishraqa maganar dakike fada kuwa da gaske ne?" Ishraqa tayi Shiru tana kuka Bata Bawa mamy Amsa ba, El-Hameed ne yagoge hawayen Idonsa yace "Ba sunan ta Minal ba Hajiya, sunan ta Insaaf, shine sunan dana saka mata da kaina, sunan mahaifiyata taci" Mamy tace "amma Yaya akai kuka ganeta? Tsawon lokacin tana tare damu amma Baku ganeta ba" Kai tsaye yace "ta kayanta hajiya, wanda yake jikinta lokacin da muka rabu da'ita, dakuma zoben dana siya mata da kaina" Duk wannan Bayanin da ake Asim bai dago kansa ba πŸ˜‚ Abin duniya yataru yayi masa yawa, kwata kwata yaqi kallon su, amma Yana jinsu Sarai Ishraqa ce tataso takama hannunsa, cikin kuka tace "Asim katashi muje ka nemomin yarinya ta,Insaaf tayi fishi dani tabarni, Dan Allah Asim katashi" taqarasa maganar Tana kuka sosai Dago kansa yayi ya kalleta, yakai dubansa zuwa hannunta, duk ta kamashi ta rirriqe kamar tana tsoron a qwace shi,inda ace Dane, babu abinda zai Hana ya riqeta suje, saboda amintarsu tazama 'yan'uwan taka, amma yanzu, bazai iyuba, matsayin ta ya sauya da yanda ya santa abaya, Ahankali yazare hannunsa daga cikin nata Kuma har lokacin bece da'ita uffan ba Amrah kam mamaki yagama kashe ta, ashe duk abin nan dayake faruwa da dukiyar Minal suke taqama? Ashe kudinta ne yarufa musu asiri? Mamy ta kalleshi tace "Asim ai bamu gata zama ba, tashi zakayi mubi bayan yarinyar nan, duk abinda ya faru ai acikin rashin sanine" "wanne irin rashin sani Mamy? Ishraqa yarinya ce? kina gani tana yimata fada Nima da kaina nayi mata magana, amma taqi saurare na, yanzu ne hakan ya janyo?" Cikin kuka itama tace "Allah katashi ka nemomin yarinyata" Kallanta yayi, shi Sai yanzu nema yake ganin wasu abubuwa wanda Minal takeyi kamar Ishraqa, komai kuka, abu kadan kuka, yanzu duba yanda take kuka saikace wanda aka yankata Ajiyar zuciya yayi, ya tashi, gaba dayansu suka dunguma suka bar gidan *** ****** *** Ko kallon gabanta batayi, haka take tafiya tana share hawaye, ba tasan inda zataba, ba tasan ina ta nufa ba, ko'ina ma jefa kafarta takeyi, saida tayi tafiya me Nisa sannan tanemi waje ta zauna, ta kifa kanta Akan cin yarta tana kuka mai cin rai, haqiqa rashin iyaye bashida dadi, amma ayau kam ta haqura danata Iyayen, Gara tatafi wata duniyar daban ta shimfida sabuwar rayuwa, to Amma ina zata? Su Inna sun koreta, maigari yace suma subar masa garinsa, idan Takoma Garin ma, haka zata zama kamar wata mujiya acikinsu, dole tabar Garin nan Takoma wani Garin inda ba'asanta ba, ba'asan wacece itaba, to Amma akwai auren Asim a kanta, Yaya zatayi dashi, lokaci daya zuciyarta ta ambata mata sunan kotu Cikin sauri tatashi tsaye ta goge hawayen idonta, afili tace "Gara inje kotu ta rabani da wannan auren" Hannunta ta kalla batada kudi ko sisi, kayanta da suke hannunta taduba ko zataga kudin sadakinta data ajiye, nanma taga bayanan, kenan ta barshi agidan, to Yaya zatayi? Dan qaramin zoben gold dinta ta kalla, kode shi zataje ta siyar tayi kudin Mota? Girgiza kanta tayi,tasake kallon zoben, afili ta furta "to amfanin me zakamin? Suma wanda suka sakamin zoben sun rabu dani, tayaya Nikuma zanci gaba da zama dakai" tana fadar haka tayi jifa da zoben, rigar ma ta wullar da'ita 😳 Tundaga nesa yake hangota tana jifa da kaya, mamaki ya kamashi, kamar Minal yake hangowa, to meyake faruwa ya ganta anan? Ita daya kamata ya ganta agida yadauke ta su tafi makaranta? πŸ€” Gudun motarsa yaqara, Yana zuwa dede inda take ya tsaya, yafuto da sauri ya qarasa wajan ta yace "Minal, mekike anan?" Kallansa tayi tace "Yaya Muhsin" "na'am Minal, ina zakije? Asim Yamin waya dasafe inzo na daukeki zan kaiki makaranta" Girgiza kanta tayi tace "babu komai Yaya Muhsin, ka kaini kotu Dan Allah" "kotu kuma? Meza kiyi a kotu?" "Yaya Muhsin inaso alqali yaraba aurena da Yaya Asim" Kallan mamaki yake jifanta dashi, yarinyar nan kuwa tasan yanda Asim yake kishinta? Saboda me zatace Araba musu aure? Anya kuwa babu abinda yake faruwa?, Ajiyar zuciya yayi sannan yace "Kinga shigo Mota mu tafi" Babu musu tashiga motar, shikuma ya tattara mata kayan data zubar awajan, suka dauki hanyar zuwa gidansa *** ****** *** Duk gaba dayansu kowa Hankalinsa atashe yake, musanman Ishraqa da El-Hameed, Dan kwalin abayar datayi rolling dashi tuni gefensa yajiqe da hawaye πŸ˜‚ El-Hameed dinne ma me dauria, Asim kuwa abu ne yataru yazame masa goma da a shirin, ga 6atan wannan yarinyar, ga kuma Amjad, duk Hankalinsa ya tashi,gashi wajan ba wajene dazaka dinga ganin mutane sosai ba bare ka tambayesu kosun ganta Wayar sace tayi qara, amma be kula ta ba bare yadauka, Sai a Karo na biyu ne yad'auka tare da fadin "Muhsin" Daga daya bangaren Muhsin yace "Abokina meyake faruwa ne? Naga matarka a hanya tana watsi da kaya" πŸ˜‚ "tana ina Muhsin? Ne manta mukeyi" "tana gidana, suna tare da Nabila" "Okey, gamu nan zuwa" Yana kashe waya Ishraqa tazuba masa ido tana jira taji abinda zai fada musu, mamy tace "ya'akayi ne Asim?" Cikeda aji yace "tana gidan Muhsin" El-Hameed yace "Alhamdulillahi, Allah abin godia Bari nakira Hammudi" πŸ˜‚ Ishraqa kuwa murmushi take, yayinda wani hawayen farin ciki yake zubo mata, juyawa sukai suka koma daya layin, inda gidan Muhsin yake, El-Hameed Sai dariya yake, yakira Hammudi. Hammudi Yana dauka yace "Wajadnaha ya Hammudi, Wajadnaha allailah, kuntu masrur wallahi" Daga daya bangaren Hammudi yake tambayar sa "wa suka samu?" Ishraqa ta qwace wayar tace "Insaaf" Haka suka dinga waya da Hammudi har suka qaraso gidan Muhsin, su mamy da Asim de kawai kallonsu suke πŸ˜‚ Yanda suke farin-ciki abin tausayi Har rige-rigen shiga falon Muhsin suke, Suna shiga kuwa suka ganta azaune itada Nabila matar Muhsin, duk yanda Muhsin yake Bata labarin amaryar Asim yarinya ce batayi tunanin takai hakaba, a ganinta tsaf Minal din zata iya dauke Asim πŸ™Š El-Hameed Yana qarasawa cikin falon Dasauri yaje ya rungume ta, Ishraqa kuwa tana zuwa Sai tayi turus jikinta duk yayi sanyi, amma haka ta zauna tana kallonsu itada El Hameed tana murmushi, yayinda hawayen farin-ciki yake zubo mata Mamaki ne ya kama Amina, takai kallonta zuwa ga mamy taga itama Sai Fara'ah take, hakama Amrah, sai alokacin yashigo falon shida Muhsin, hannunsa Yana zube cikin aljihun Wandon Suit din dake jikinsa, saide babu jacket din yacire ta, kana iya ganin yanda murdaddan hannunsa yake ta cikin rigar, kallo daya sukai wa juna kowa ya dauke kansa, Muhsin Yana kallonsu gaba dayansu Mamy ta kalli Amina tace "Minal 'yata, kigodewa Allah, yau Allah ya baiyana miki Iyayen ki" Dasauri tatashi tsaye tana yiwa mamy wani irin kallo, mamy tasake jinjina mata kanta tace "hakane Minal, Ishraqa da El-Hameed sune Iyayen ki, yau Allah ya karbi Addu'ar ki" Girgiza kanta tayi, idanunta qamas babu kuka, tace "mamy aini banida wasu iyaye, niba iyayena bane, suje su nemi 'yarsu" Gaba daya falon babu wanda Bata Bawa mamaki ba, jikin El-Hameed yayi sanyi, ya kalli Ishraqa, itama kallansa tayi, wani irin kuka me ciwo yazo mata Takai hannunta takamo na Minal sannan tace "Insaaf... Karki min haka 'yata, nice mahaifiyar ki, Kinga mahaifin ki Insaaf" Taqarasa maganar tana nuna mata El-Hameed, fizge hannunta tayi daga cikin na Ishraqa, tafada jikin mamy tana kuka sosai Dasauri Ishraqa da El-Hameed suka taso zasuzo wajan ta, mamy ta daga musu hannu batare datace komai ba, sannan takama hannun Minal din suka futo daga gidan Har sukazo harabar gidan mamy Bata saketa ba, daga Ishraqa har El-Hameed jikinsu yayi bala'in yin sanyi Saida suka shiga gidan Asim ya kalli Muhsin yace "yarinyar nan tanada damuwa wallahi, duk Sai wahalar damu take, Sai shagwaba takewa mutane sukuma su mamy suna biye mata" Muhsin yace "a a Asim, ya kamata kuyi mata uzuri, damuwar datake ciki ai tanada yawa, kuma gashi kaima kace ba sonta kake ba, aikuwa kaga ni banga laifin taba" ya qarasa maganar yanaso yaga yanayin Asim din Shikuma Asim kafadarsa ya d'aga yace "tokai yanzu kana ganin ya dace ace na auri 'yar Ishraqa? Da girmana da komai Sai a tambayeni wanake aure ince 'yar qawata, πŸ˜– Abin da kunya Muhsin, ita kanta yarinyar ba tafi karfin in raineta ba" Muhsin yayi wani qaramin murmushi yace "Asim bafa haram bane, ni banga abin damuwa Akan haka ba, koda yake, ai itama yarinyar baso take ba, shikkenan saika sauwaqe mata ta auri wanda ra'ayinsu yazo daya, saboda kaga dazu ma Dana hadu da'ita roqona take yi Dan Allah nakaita kotu Araba aurenka danata " Cikin sauri ya kalli Muhsin tare da zaro manyan idanuwansa yace"kotu fa kace Muhsin"😳 Dariya takama Muhsin, amma saiya danne yace "Of course, abinda tafadamin kenan, shine nace tayi hakuri muje gida" "yanzu ita har tasan a kaita kotu Araba aure? Auren da Allah ne yahad'a abinsa?" πŸ˜‚ Muhsin yasaki dariya yace "to abokina me amfanin auren da babu kulawa, may be abinda tagani kenan, babu kulawa, gashi bataso kaima baka so" "kaga Muhsin, Dan Allah kadena wannan maganar kotu kotun, tayaya zan saki yarinyar Ishraqa? Da wanne idon zan kalleta?inajin tausayin yarinyar, Gara na tausaya mata mu zauna ahaka" Muhsin yace "tab! Tausayi manya, yanzu Yaya maganar Daddy?" "bansani ba Muhsin, yanzu nakeso Nabi bayansu" Muhsin yace "eh ya kamata muje, amma mu shiga gidan mu fadawa mamy, saimu wuce" Asim yace "OK,no problem" Daga nan suka shiga cikin gidan. Suna shiga falon suka zauna, har lokacin Amina tana wajan mamy,Ishraqa jitake kamar taje ta janyota jikinta su dauwama ahaka, amma tasan ta6a tawa yarinyar rai, dole hakan zai Iya faruwa, Asim ya kalli mamy yace "Mamy kiyi hakuri, inaso naje wajan Amjad, Yana cikin damuwa mamy" Amrah ma tace "eh mamy Dan Allah, kinji mamy, Nima zan bisu, Dan Allah mamy karmu tafi mubarshi" "Dan Allah kudena min wannan maganar haba!" Muhsin yace "Mamy kiyi hakuri, amma idan kuka tashi daga nan muma ba zamuji dadi ba" Ishraqa ma da idanunta sukai jajir tace "kiyi hakuri mamy, tunda Allah bai bashi nasara ba, Allah ma gafurun rahimu ne" Kanta ta sunkuyar qasa tace "Hakane, to shikkenan, zamu zauna insha Allah" Turo kofar falon akayi, gaba dayansu suka kai dubansu zuwa ga kofar, Amjad ne yashigo duk Hankalinsa atashe, kana ganin idanunsa zaka san yasha kuka Bana wasa ba, mamy tana ganinsa tatashi tashige dakinta, Asim ya Girgiza kansa cike da damuwa yamiqe zaibi bayan ta Ahankali yace "Yaya" Asim ya tsaya cak awajan Ahankali yataka zuwa wajansa yace "karka bita Yaya, na cancanci fiye da haka Yaya, kakoma ka zauna zan bita da kaina" Yana fadar haka yasa ka kansa zuwa d'akin nata, batare daya jira amsar Asim dinba Ajiyar zuciya Asim yasaki yadawo falon yazauna kusa da Muhsin, ya kalli Amina suna hada ido ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsun hannunta Yasake daga kai ya kalli Ishraqa suka hada ido,take maganganun datake fada masa Akan auren yarta yafara dawo masa, cikin sauri ya sunkuyar da kansa qasa πŸ˜‚ Cikin ransa Yana fadin shikkenan burin Ishraqa yacika,girma nade yariga yafadi ✍🏻 Mrs Usman ce [2/21, 10:14 PM] El~Yaqoub: INSAAF Writing by:Amnah El yaqoub 33&34 Ina qara miqa saqon ta'aziyya ta ga dan'uwana Wato Its Saddik, Allah yaji qanta, Allah yayi mata rahma, Allah yasa tahuta πŸ‘πŸ» Idan Tamu tazo ya Allah Kasa mucika da Imani Like my page on Facebook πŸ‘‡πŸ» https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 _________ Tabbas idan yaci gaba da zama awajan, babu abinda zai hana Ishraqa tayi masa wankin babban Bargo 😟 Danhaka yayi qasa da muryarsa yace "Muhsin, ya kamata mubar wajan nan" 🀣 Cikin mamaki Muhsin yace "saboda me?" Da idanunsa yayi masa nuni da 6angaren da Ishraqa take Nan take Muhsin ya fahimta, yayi murmushi sannan yace "muje" Ko inda Ishraqa take bai iya kalla ba suka fice daga falon, suna compound din gidan Muhsin yasaki dariya yace "wai saboda kaga Ishraqa a falon ga kuma Minal shine kace mu futo?" "Muhsin idan ganine Aida sauqi, kawai yanda nagama cikawa Ishraqa baki bazan auri yarta ba, shi nake tunawa, kuma nasan bazatayi fuska ta share ba" Muhsin ya kwashe da dariya yace "lalle Asim, toba Gara ka tsaya ba, ayi wacce za'ayi?, yanzu dakasa muka futo ina zamuje?" Kai tsaye yace "Wajan Daddy" "Wajan Daddy kuma? Kasan abinda kake fada kuwa Asim?" "nasani Muhsin, Saboda Amjad, muje" Muhsin ya kalleshi ya Girgiza kansa, besan wacce irin zuciya abokin nasa yake dashi ba, koma menene yasan cewa haqiqa Minal tayi sa'ar miji, bece dashi komai ba suka tafi *** ****** *** Bayan tashiga d'akin Kasa jurewa tayi tafashe da kuka, Ahankali yaturo kofar d'akin nata yashigo jikinsa a sanyaye Kallanta yayi yaga tabawa kofar baya, hakan yana nufin koma waye yashigo batason ganinsa kenan, gwiwo yinsa yazube aqasa, yace "mamy..." Tana jinsa tayi Shiru, hawaye take amma takasa juyowa ta kalleshi Yace "mamy Ashe zaki iya yin fishi dani?, zaki iyayin fishi da Amjad dinki? Autanki?" Wannan maganar daya fada saita sa jikinta yayi sanyi, kukan ta ya tsananta Shima ganin tana kuka Sai hakan ya sashi zubda hawaye yace "Mamy uwa Bata fishi da yaranta, tunda na tashi bansan kowa ba, bansan mahaifiyata ba kena sani a maimakon ta Mamy, kuma kin hadani da yaranki kinyi kana tarbiyar da kowacce uwa tagari take yiwa yaranta, mamy bantaba sanin wani abu waishi zalunci ba bare nayi, kuma Narasa wanda zan zalunta Sai Yaya Asim...., mamy meyasa laifin mahaifina zai shafeni? Kiyi hakuri Dan Allah na roqeki " Yaqarasa maganar Yana hade hannunsa waje daya πŸ™πŸ» kuka yake sosai, kuma har lokacin Bata juyo ta kalleshi ba, cikin kuka yace" Mamy tun muna Yara kece kike fada mana mu daina ruqo, mu dinga hakuri da juna, ubangijin daya haliccemu ma muna aikata masa laifi kuma yayafe mana, meyasa ba zakiyi hakuri kiyafewa mahaifina ba? " Hannu tasa ta share hawayen idonta, bazata iya fishi da Amjad ba, tana kaunar Yaron acikin ranta, amma mahaifinsa ya yaudaresu, kudi da Rudin duniya sun Gama dibansa. Ahankali ya tashi zai futo daga d'akin, saboda mamy de ko kallansa taqi yi. Tanajin alamun tashinsa ta juyo tace "toda katashin inane zakaje?" πŸ˜ƒ Cikin sauri ya juyo ya kalleta, amma Yana tsoro yakasa qarasa wa wajan ta, Sai tausayin sa ya kamata, tace "kaje kanemi abinci Kaci" "banajin yunwa mamy...." Batace masa komai ba tanemi gefen gadonta tazauna, Ahankali yatako wajan ta, tare da riqe hannunta yace "mamy ki yafe mana nida Daddy please" "Amjad me mahaifinka Yamin dazaka ce nayafe Mas....." Bata qarasa ba taji wani irin taqaici ya kamata, har yanzu idan tatuna abinda alhaji yayi jitake ta tsaneshi, wani irin sabon kuka yazo mata, Bata Hana kanta ba, haka tafara hawaye tana sharewa, Shima kukan yasaka mata, tana ganin haka tajashi jikinta ta rungume shi, kowa kuka yake acikinsu, ita kuka shi kuka babu wanda yabawa dan'uwansa hakuri, da kansu suka gaji suka daina Tashi tayi takamo hannunsa tace "muje nabaka abinci" Haka suka futo falon inda suka Bawa kowa mamaki, ta kalli Ishraqa da ido ya kumbura saboda kuka, ta kalli El-Hameed shikuma yazubawa Amina ido Yana kallonta, takai kallonta wajan Aminan taga tana nan zaune inda ta Barta, amma ta lumshe idonta kamar me bacci Murmushi tasaki, saboda Iyayen da yarinyar duk sun Bata dariya, kuda yarku amma kuna tsoron tunkararta? Haqiqa yau Minal tazama boss, kuma da alama Sai daya Actor din yazo sannan ne zasu daidaita Zama tayi, sannan tazaunar da Amjad agefenta, ta kalli Amrah tace "Amrah kawowa Amjad abinci" Amrah tatashi tayi kitchen tana mamakin wannan shaquwa ta Amjad da mamy, kome yafada mata harta sauko cikin sauri haka? Bayan yagama cin abincin Yana shirin tashi Asim yashigo, yayi mamaki dayaga har lokacin su Ishraqa suna gidan, yanayin Zaman nasu ya kalla yasan akwai sauran waani abun kuma, Allah Allah yake Kar Ishraqa ta kunya tashi a gaban Minal dakuma su mamy, shiyasa yaqi kallon inda take ma 🀣 Fuskarsa yad'an daure sannan ya zauna yakalli mamy yace "Munje wajan Daddy nida Muhsin, basu bamu damar ganinsa ba, sunce Sai kinje, Mamy kiyi hakuri Dan Allah" Amjad dake zaune kansa ya Sara, Shima Hakan ce tafaru dashi bayan yabisu abaya, kwata kwata basu bashi Damar ganin Daddyn ba Ahankali yamiqe ya kalleta yace "Mamy saida safe" Daga nan yawuce dakinsa Itama Amina kokuma nace Insaaf, tashi tayi ta nufi hanyar dakinsu, ciki-ciki tace musu "saida safe" Asim ya kalli Amjad, yasake dawo da Idonsa ya kalli Minal, Ahankali yace "ikon Allah" πŸ€” Yau kuma anta6o shagwa6a66e da wata shagwa6a66iyar babu Zaman lafiya Amrah ce tatashi tabi bayan Amjad, saide tana kama handle din d'akin da nufin budewa taji shi a kulle, haka tadawo falon ta zauna jikinta a sanyaye Ishraqa da sauqi tamiqe zatabi bayan Amina, mamy tayi sauri tace "karkije Ishraqa, kibata lokaci ta huce, zatafi saurareku" Dawowa tayi ta zauna Akan kujerar tadafe kanta da hannunta , idanunta nakawo ruwa 😒 Kallanta Asim yayi yace "kuma wa zakiyi wa kukan?" El-Hameed yayi murmushi, Amrah ma ta kalleshi tayi murmushi, mamy tace "Asim kabarta da abinda yake gabanta mana, idan bazaka lallashi Minal ba ai bazaka zo ka tunzura Ishraqa ba" Shiru yayi bece komai ba, Ishraqa ta kalleshi takawar dakai batace dashi komai ba, besan cewa dama aciki take dashi ba, jira take tagama da matsalar gabanta sannan tadawo kansa Amina kuwa tana shiga d'akin ta jingina ajikin kofar d'akin tana tunani, rayuwa kenan, yanzu ashe Anty Ishraqa itace mahaifiyar ta? Qwalla ce ta cika idonta,tatuno lokacin da Ishraqa take zazzaga mata masifa harda cewa inde Asim ne to tayi masa mata, ko waye yace mata ita din sonsa take? Harda cewa Wai karta miqe kafa, to mezatai dashi itama tunda shima ba sonta yake ba, hawaye ne yazubo mata tasa hannu ta share Tana shirin barin jikin kofar tajiyo mamy tana cewa "Ishraqa, ya kamata kifada mana dalilin dayasa yarki ta6ace daga hannun ki, nide nasan kintaba cemin Insaaf yarki ce, kuma kinaso na dinga kiranki maman Insaaf, amma duk cikin mu nan babu wanda kuka taba fadawa dalilin dayasa kuka rabu Kuda yarku" Hawaye ne yazubo mata, ta kalli El-Hameed tace "ka basu labari" Shima kallanta yayi yace "A a kibasu labari Ishraqa" Asim yayi murmushi,cikin ransa yace yau Habibty Takoma Ishraqa πŸ˜ƒ Ahankali tafara basu labari tace "kamar yanda na fadawa Asim, Insaaf Bata wuce yar shekara biyu ba, muka nemeta muka rasa,kafin muyi Candy muka koma Sudan nida iyayena, bayan nayi Candy aka daura mana aure nida El Hameed, iyayensa suna da hali kamar yanda nawa suke dashi, shekarar aurenmu daya Allah ya azurtamu da samun Insaaf,Iyayen El Hameed sun nuna mata gata sosai, sunyi mata kyautuka masu yawa, haka Nima nawa Iyayen, lokaci daya mahaifiyar El Hameed tarasu, daga baya Shima mahaifinsa ya kwanta ciwo, anan ne ya mallakawa Insaaf kadarori masu yawa, kuma aka saka sunan ta Akan komai, daga baya Shima Allah yayi masa rasu. Insaaf nada shekara biyu muka zauna nida iyayena da Hameed cewa mezai Hana muzo Nigeria mujuya wa insaaf kudinta kafin ta girma tayi hankali, tayi ilmi me zurfi, taci gaba da kula da abinta, tunda abaya mun zauna a qasar munji Dadin haka, haka kuwa akayi, alokacin Hameed yace muje, shi akwai abinda zaiyi, haka muka taho nida iyayena, bana mantawa alokacin tana sanye da rigar dana ganta da'ita dazu, dakuma zoben da El Hameed yasiya mata shi, mun sauka a Nigeria cikin Garin Abuja, kai tsaye babanmu yace muje kano anan ya kamata muyi komai, ahanyarmu ta tafiya ne mukai hatsari, Allah yayiwa iyayena duka su biyun rasuwa, ni kuma nasamu raunuka daga qarshe ma na suma, nide Sai a gadon asbiti naganni, nafarka na dinga tambayar yata insaaf amma wanda suka kawo mu asbiti sunce su basu ga wata yarinya ba, mutum uku kawai suka gani acikin motar nashiga tashin hankali matsananci, babu iyaye babu yarinya ta,nakira El Hameed awaya nasanar dashi, alokacin yazo, munfi kwana da Kwanaki muna cigiyar Insaaf amma babu wani labari, haka muka hakura muka koma Sudan Bayan munkoma hankali na yaqi kwanciya, koda yaushe ina kuka ina tunanin yarinya ta, haka muka Kasa hakuri saida muka dawo nida El Hameed, alokacin ne Naga Asim baya aikin komai, shine muka yanke shawarar mu bashi kudin Insaaf yadinga Juyawa, bayan mun bashi haka muka sake komawa Sudan, ahakan ma hankalin mu bai kwanta ba, koda yaushe gani muke kamar idan muka dawo Nigeria zamu sameta, haka muka tattaro, muka rabu da danginmu muka dawo Nigeria da zama, bayan mundawo shine muka sauka a Lagos, muka nemi gida kusa da naku " Tana gama jin wannan labarin nata tafashe da kuka, ashe haka iyayenta su kasha wahala a kanta? Wacce irin qauna ce wannan? Hannunta ta daga Sama tana qara yiwa Allah godia, taga iyayenta, menene kuma yayi saura yanzu? Saide su Innah, sune kuma take fatan ace tasake haduwa dasu a rayuwarta koda sau daya ne Hawayen idonta tashare, bayan tatuno gagarumar matsalar datake tare da'ita Ta mutuwar mazajen datake aura, dole Yaya Asim yayi hakuri ya saketa, bazata so yamutu saboda itaba Gaba daya falon yayi tsit, bayan sungama sauraren Ishraqa, mamy tace "Amma kuma Ishraqa kince a ahanyarku ta zuwa kano kukai Accident, shikuma Asim yafada min Ayola yahadu da'ita" Girgiza kanta tayi tace"bansan Yaya akai taje Yola ba, wannan shine iyakar abinda nasani mamy" Mamy ta kalli Asim tace "Asim Yaya akai Minal taje Yola ne?" Cikeda aji yace "mamy wallahi bansani ba, itama fa tayi tunanin wadancan mutanan sune suka haifeta, tayaya zatayi bincike Akan Sanadin daya kawo ta Yola? Sannan Bata dadi muka rabu dasu ba, dama da saina tambayesu" Dasauri El Hameed yace "mekake nufi Asim? Menene yahadata dasu har suka rabu Bata dadi ba?" Asim yayi Shiru yarasa amsar dazai basu, Ishraqa tace "kafada mana man Asim, gudunta sukai ko? Suma sum qyamaci yata kamar yanda nayi acikin rashin sani? Sun gujeta bayan sun gaji da ruqonta ko?" Dago manyan Idonsa yayi ya kalleta yaga duk ta rikice, tayaya zai Iya fada mata cewa yarta tayi aure kusan mutum shida? Tayaya zai futo fili ya fadawa Ishraqa cewa duk mijin da Minal ta aura mutuwa yake? Tayaya? Ajiyar zuciya yayi yace"idan kina jin ciwo wasu sun guji 'yar ki ba gashi Sanadin haka kin hadu da'itaba? " Gaba daya falon suka ce hakane, Ahankali ya miqe yabawa El Hameed hannu yace" Congratulations" Shima cikin farin ciki yayi masa godia, Ishraqa tafara yimasa wani irin kallo, kallon saika raina kanka, sannan ta dauke kai, Shima bece da'ita komai ba yadauke kansa 🀣 Saida safe yayi musu, ya kalli Amrah yace takai masa tea dakinsa, shikuma yawuce d'akin Amjad, daya tura yaji arufe, saiya fara neman wayar sa Ishraqa ta dubi mamy cikin zaquwa tace "Bari mu dubata" 🀣 Mamy tayi dariya tace "tomuje mana" Dakin suka nufa duk su ukun, mamy, Ishraqa, El Hameed. Har lokacin tana nan tsaye awajan tanajin duk irin firarrakin da suke yi, tanajin alamun tahowarsu tayi sauri tafada kan gadon, taja blanket tarufa, sannan ta lumshe idonta kamar me bacci Haka kawai takejin wani irin dadi na musamman Yana ratsata, ga wani 6angare na zuciyarta Yana qara girmama Asim da yayi Sanadin haduwarta da iyayenta Dakin suka shigo, Ishraqa tahau gadon ta zauna asetin inda kanta yake, Ahankali tadora hannunta a kanta, ta dauke mata kanta dake kan fillo tadawo dashi kan cinyar ta, dankwalin dake kanta ta janye, dogon gashin ta mai santsi ya baiyana, gashin tafara shafawa ahankali El-Hameed dayake tsaye Shima ya qaraso daga daya bangaren ya zauna Yana kallonsu Cikeda so da qauna Mamy dake tsaye a bakin kofar d'akin tayi murmushi tana ganin irin wannan soyaiya Duk abinda suke Amina tana jinsu, amma tayi Shiru El-Hameed yace "Habibty kode Anan zamu kwana ne?" πŸ™Š Daga masa kai tayi, Cikeda farin-ciki tace "Emana, anan zamu kwana tare da Insaaf Habiby" Mamy tayi dariya cikin ranta tace yau nagamu da mutane, afili tace "haba Ishraqa, kuyi hakuri mana zuwa gobe" πŸ˜ƒ Pls kuyi hakuri da wannan nasan ba yawa Mutara zuwa gobe πŸ™πŸ» ✍🏻 Amnah El~yaqoub [2/23, 3:11 PM] El~Yaqoub: INSAAF Writing by:Amnah El yaqoub 35&36 Like my page on Facebook πŸ‘‡πŸ» https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 Yau kunjini Shiru banyi posting da wuri ba, 😜😜Wai bari nayi muka tashi daga mkrnta sannan nayi muku medan tsawo πŸ™„πŸ™„ Murmushi sukai gaba dayansu πŸ˜ƒ Daqyar suka iya barin d'akin, bayan tsawon lokaci da suka dauka suna aikin kallon 'yar tasu, sai da dare yayi sosoa sannan suka tafi gida Awannan dare kam, wadannan ma'auratan basu runtsa ba Itama anata bangaren suna tafiya tatashi ta dauro alwala tana qara yiwa Allah godia da yakawo qarshan matsalar ta ta farko Washe Gari da sassafe suka tashi, break suke jerawa a dinning itada Amrah, bayan sun Gama suka zauna awajan itada Amrah kafin yan gidan su futo Amrah ta kalleta tace "Insaaf matar Yaya Asim, tokefa zama be ganki ba, ya kamata kidage kibawa yayan mu kulawa, Dan Yaya Asim yanason kulawa, kawai samu ne baiyi ba" Amina tace "Hmm, Anty Amrah kenan,Toni mezan masa? Ba gashinan yanzu ma Ana masa komai ba" "to cemiki akai a haka za'a Dore? Ai komai wajanki zai dawo, bashi abinci abaki,bashi kayan sakawa, ki shirya shi, kigyara masa sumar nan tasa" Cikin sauri tace "in bashi abinci abaki? Sai kace wani jariri?" Amrah tayi dariya tace "lalle ma Minal da sauran ki, waye yafada miki Ana sake da irinsu Yaya Asim? To bari kiji kibashi mamaki wallahi, kinuna masa kinfi tsohuwar matarsa iya kula da miji, ai shi kamar jaririn ne a wajanki, yanda zaki saka Babyn ki acinya ki shayar dashi, Shima haka zaki masa " " nashiga uku Anty Amrah, yayanki nefa " " to Dan Yaya nane Sai nayi Shiru bazan koya miki yanda zaki rikita shi ba? Ai taimakon sa nayi, ina wannan qananun kayan damuka siyo a kasuwa? " Ahankali ta daga mata kai alamun eh, gabanta Sai faduwa yake Amrah tace"Yauwa, su zaki dinga sakawa, Kinga Anty Lubna Bata sakawa, to ke saiki saka abinki, Shima ki dauko masa qananun kaya kibashi kice shi kikeso yasaka yau Ball kikeso kuyi, idan kungama kijashi toilet kiyi masa wanka "πŸ˜‚ Hannunta ta dora Akan bakinta πŸ™Š Tace" Anty wanka kuma? Nashiga uku " Adede lokacin yashigo falon yayi mutuqar kyau cikin blue din yadi, kayan ya karbi farar fatarsa, Sai zuba qamshi yake, kallo daya Amina tayi masa maganar Amrah ta Fado mata, cikin sauri ta kawar da kanta Fuskarsa babu digon Fara'ah yanemi waje ya zauna, Dasauri Amrah tace "Yaya ina kwana" "lafiya" yabata amsa a taqaice Kallansa tayi qasa qasa tace "ina kwana?" Kallanta yayi yadauke kansa sannan yace "Lafiya" yafara kokarin janyo flaks zai hada tea Amrah ta kalli Minal tayi mata wani irin sign da'ido, tana nuna mata Asim Duk saita rikice tarasa Yaya zatayi, flaks din daya dauka zai zuba shayi ta nuna mata Anan tadau haske, tashi tayi takai hannu zata karbi flaks din tace "Kawo" kallanta yayi yanda ta sunkuyo zata karbi flaks din Sai hakan ya haifar da kusanci atsakanin su,uwa uba kayan data saka na less saiya Bawa Asim Damar ganin boobs dinta daga saman rigar Amrah tana kallansu qasa qasa amma Bata nuna musu taga a halin da suke ciki ba Mamy ce tafuto, Sarai taga a yanayin da suke ciki amma saitayi fuska 😎 Tanemi waje ta zauna Babu musu yasakar mata flaks din, ita kuma ta hada masa Abincin suka fara Ci cikin nutsuwa bayan sun gaisa da mamy Saida suka gama mamy ta kalli Amrah tace "Amrah, Naga alama har yanzu Autana bai huceba, kije kikai masa abinci ki kula dashi kafin nashigo" Amrah ta amsa tatashi tahada abincin sannan ta nufi d'akin Amjad, wajan saiya rage daga ita Sai mamy Sai Asim daya dauki wayar sa Yana danne-danne Mamy ta kalli Minal tace "Insaaf!" Jitayi sunan yayi mata wani iri, saitaga kamar ba'ita ake kiraba, dago kanta tayi ta kalli mamy tace "Na'am mamy" "kiyi hakuri ki saurari iyayenki, bakida kamar su a duniyar nan, iyayenki suna qaunarki, Allah yanason mutum mai hakuri, kuma duk abinda tayi miki ma acikin rashin sani ne, ya kamata kiyi hakuri ki fahimcesu" Asim yadago kansa ya Kalle su, Wai yarinyar nan tun jiya adinga bin kanta? Gyaran murya yayi yace "ko yanzun ma bakya sonsu na kaiki gidan marayun?" Mamy tayi murmushi, Ahankali tatashi tashige dakinta zata dauko wayarta tatafi wajan Amjad Wani irin kallon shagwaba tayi masa, tace "toba kafin na gansu ne nafada ba" Besan meyasa ba, haka kawai ya tsinci kansa dajin Dadin yanda take masa shagwa6ar,kallanta yasake yi yace "kuma kin samesu kike musu haka?" "to ai nadena" "Ok, congrats" Murmushi tayi tace "Nima nagode Yaya, bansan dame zan saka maba, kayimin komai a rayuwa, Kaine silar haduwata da iyayena, Yaya dame zan sakama?" Gaba daya Asim ya shagala wajan kallon Dan qaramin lips dinta, bemasan tagama magana ba, tunanin sa da nutsuwar sa gaba daya sun tattara sun koma bakinta Murya tad'an daga tace "Yaya!! " Kallanta yayi yace"mekike buqata?" "ni babu abinda nake buqata, buqata ta daya sune iyaye na, kuma na gansu, Kai nake tambaya bansan dame zan saka maba" Kallanta yasake yi,cikin ransa yace "your lips" πŸ™ˆ Afili kuwa saiya daga kafadunsa biyu, yace "kisaki jikinki da Iyayen ki, bakida kamar su a rayuwa" Mamy tafuto daga dakinta ta gansu azaune awajan har yanzu, tayi murmushi ta nufi hanyar d'akin Amjad. Sallama suka doko atare duk su biyun, Ishraqa da El-Hameed, Asim yayi Shiru yayi Suman zaune, ya kalli Minal yaga kujerar datake zaune tana fuskantar tasa kujerar, idanunsa ya runtse πŸ˜– Karfa Ishraqa tayi tunanin wani abu, gaba daya Sai kunya ta kamashi, Abin yabashi mamaki Wai shine dajin kunyar Ishraqa, wannan al'amari dame yayi kama? Ishraqa kuwa wajan mamy ta nufa suka fara gaisawa harda El Hameed din, Kallon El Hameed tayi, sannan tayi masa sign da idonta zuwa wajan su Asim da Amina Asim yayi Shiru kamar baiji shigowar Suba, yanaji mamy tace "Ishraqa ku zauna mana, Bari indubo Amjad nadawo" Cikin sauri Shima ya tashi, yad'an hade fuskarsa saboda Karma Ishraqa taga fuska tayi masa magana πŸ˜‚ Bayan mamy yabi, aikuwa tana ganin tasowarsa tace "Asim, baka ganmu bane?" Amina tayi murmushi itama tataso ahankali ta nufi wajan Iyayen nata, atare kuwa suka sauke Ajiyar zuciya ganin ta saukko daga fishin nata El-Hameed ya tashi ya ruqo hannunta yazaunar da'ita a tsakiyar su Asim kuwa bai saki fuskarsa ba yadawo da baya yamiqawa El Hameed hannu suka gaisa, yasake yin hanyar d'akin Amjad πŸ˜‚ Ishraqa tayi murmushi tace "Asim jiya baka shigo minba bayan mun tafi gida, yauma nayi tunanin zaka shigo amma banganka ba" Batare daya kalleta ba yace "Eh wallahi" Yana fadar haka yayi d'akin Amjad Fashewa tayi da dariya,El Hameed yace "Habibty Sirikinki nefa" Tace "ka qyale Asim Habiby, borin kunya kawai yake, kasan kafin muga Insaaf nafada masa zan bashi auren ta, amma Asim saiya nunamin kwata kwata shifa bazai auri yarinya taba, harda cewa Wai tayaya zai auri yarsa ta cikin sa, kajifa wani rikici, shiyasa yanzu nakeso na tuna masa maganar amma kaga yaqi tsaya wa awajena " Minal tayi murmushi, tatuna lokacin da Ishraqa take cewa karta miqe kafa agidan Asim, ta riga tayi masa mata, ashe ma itace matar *** ****** *** Tana zaune agefen gadon sa, ta ajiye abincin a qasan d'akin, shi kuwa Yana kwance Akan gadon yakifa kansa acikin fillo Cikin shagwaba yace "Anty Amrah Niki qyaleni, nace miki banjin Dadin bakina bazan iyacin komai ba" "to inkoma in fada mata kace bazakaci abincin ba?" Dago kansa yayi daga cikin fillo ya kalleta yace "wacece?" "mamy ce ta turo ni" Bata fuskarsa yayi 😣 "auke bazaki iya zuwa a matsayin ki na yar'uwata kibani kulawa ba Sai mamy tasaki?" Amrah ta kalleshi ta girgiza kanta, "me hali de baya fasa halinsa, Amjad Wai meyasa ka rainani ne Dan Allah? Kokuma saboda kaga kanmu daya?" Cikin sauri yace "kanki daya dawa? Haba Amrah, kema kinsan Aina fiki wallahi" Dan qaramin tsaki taja, tatashi tsaye tace "ga abincinka nan, idan kayi niyya saika dauka Kac...." Bata rufe bakinta ba yawani fusgota ta'iyo baya Sai ganinta tayi azaune kan cinyar sa πŸ™ŠπŸ™ˆ Ranta yayi masifar 6aci, ta kalleshi zata fara zazzaga masa masifa taga Shima Hakan take, domin kuwa idanun Sama sun rufe saboda 6acin rai, nunata yayi da hannunsa yace "Karki sake min tsaki Amrah" Haushi yasake kamata, ta kalli yanda tazauna a jikinsa kamar wani muharramin ta, tace "Amjad, cikani kokuma na wanka ma Mari yanzu nan" 😳 "bazan sakeki ba Amrah kiyi abinda zakiyi, kinfara isata Amrah, ina dalili koda yaushe bakida wanda zaki raina acikin gidannan saini, wallahi idan naqara jin kinmin tsaki da gani harke Sai ran kowa yabaci a gidannan" Muryarta ce tafara rawa alamun tana gab da sakin kuka tace "anyi Tsakin, Kai waye da bazan ma tsaki ma,?" "Mtsww!" Tasake yin wani tsakin,kallanta yayi cike da mamaki, babu shakka saiya yi maganin Amrah sannan zata fara ki yaye bacin ransa batayi aune ba taji lips dinsa Akan nata 😳 Iya hakan yaso ya tsaya, danya tsoratar da'ita, amma yanayin da yaji yafara fisgarsa ne yasa da zafi-zafi yafara tsotsar bakinta, hannunta duka biyun tasa tafara dukansa, wani irin hawayen baqin ciki yafara silalowa daga idanuwanta Cike da mugunta yagama kissing dinta sannan Dan kansa yasaketa, cikin sauri tatashi tafashe da kuka, ta dauki flate din data rufe masa abinci ta kwad'a masa, cikin sauri yasa hannu ya tare, tasake daukar fillon gefensa ta doka masa. Mamy ce taturo kofar tashigo taga abinda suke, Asim ma Yana bayan ta, cikin kuka tace "Azzalumi" Mamy tace "Waiku yaushe zaku San kun girma ne? Ku kenan koda yaushe kullum cikin fada? Yanzu abin naku har ya wuce cacar baki yakoma doke-doke?" Amrah ta share hawayen idonta tawuce su mamy batare data tanka ba, Asim yabita da kallo Mamy tanemi waje ta zauna ta kalli Amjad"menene yasamu idonka haka?" "babu komai mamy, kawai de bansamu bacci bane" Kanta ta jinjina tace "katashi Kaci abinci" Cikin sanyin jiki yace "to mamy" Daga nan tajuya tafice daga d'akin Asim yasaki Ajiyar zuciya yazauna Shima a gadon batare dayace masa komai ba, Amjad dinne ya kalleshi yace "Yaya kayi hakuri Akan abinda Daddy na yayima, Dan Allah kayi hakuri Yaya" ya qarasa maganar Idonsa na kawo ruwa Asim ya kalleshi yace "Daddynka ne kai kadai kenan?" Fadawa yayi jikin Asim yasaki kuka, Asim ya Girgiza kansa yace "Wai kai Yaro ne?" Girgiza kansa yayi yace "kayi hakuri Dan Allah Yaya" "naji, nahaqura ni, katashi Kaci abinci mukoma police station, insha Allah komai yazo qarshe" Daga masa kai yayi sannan ya tashi daga jikin Asim din, yasakko qasa zaici abincin yaji mararsa ta riqe, cikin sauri ya dafe cikin sa yace "Wayyo Allah na Yaya" Asim yace "miye kuma?" "Yaya cikina ciwo" Kallansa Asim yayi, yayi Kasa da murya yace "kai, meka yiwa yarinyar can?" "to Yaya kullum saita dinga min fada, ita mamy ce da zata sani agaba tana min fada? Yaya cewafa tayi zata mareni, ni kuma na koya mata hankali" "yayi kyau, ai yanzu itama ta koya ma hankalin ko?" Kallansa yayi kamar zaiyi kuka, yace "Yaya wai dama haka akeji?" Asim ya girgiza kansa ya tashi yafice daga d'akin batare dayace masa komai ba Yana futowa falon yagansu Sai Fara'ah suke, besan Akan me suke tattaunawa ba, kawai ganinta yayi Sai dariya take, tsananin mamaki ya kamashi, dama yarinyar nan tana dariya amma shine batayi? Tsayawa yayi awajan Yana kallon su cike da birgewa, El Hameed Sai waya yake amsawa Yana Bata tana gaishe su, sauqinta daya suna jin English, da Dan wanda tasamu a qauye tayi amfani suka gaisa dasu El-Hameed yace "yata, saiki shirya muje gida kiga kayaiyakin ki, da dakinki, photunanki nada wanda kike yarinya, bakyajin magana, amma dazaran mamanki tayi miki tsawa saiki fara kuka idan ta lallashe ki kikaqi yin Shiru itama saita fara kuka, ko nono tabaki kikaqi karba yanzu zata shiga damuwa " Ishraqa tayi masa wata harara ta masoya Duk falon Sai suka sa dariya, amma banda Asim dayake tsaye Ishraqa ta kalleta tace "Yaya a kai kuka rabu da mutanan dasuka riqeki Insaaf? Yanzu suna ina muje muyi musu godia?" Hannunta ta wara alamun Bata saniba, tace "Nima bansaniba, bansan inda suke ba" "to meyasa kuka rabu?" Asim yazuba mata ido Yana jiran amsar da zata basu, saiyaji tace "megari ne ya koremu,su suka tafi, ni kuma sainabi Yaya" Ishraqa ta daga kai ta kalli Asim, suna hada ido yadauke kansa Takalli Minal, cike da tsokana tace "wanne Yaya?" Bata San Yana tsaye a bayan su ba, Danhaka kai tsaye tace "Yaya Asim..." Sai yaji muryar Tata taqara gyara masa sunan nasa, Bata taba kiran sunan saba, amma yau daya Sai yaji kamar tafi kowa iya ambaton sunan Ishraqa tayi dariya tace "to ai bangane bane danaji kince Yaya, dakin cemin dasu Inna suka tafi nikuma sainabi mijina" Nanma taqarasa maganar tana kallon Asim 🀣 El-Hameed yayi dariya ya girgiza kansa, Asim kuwa kawar da kansa yayi gefe, yaga alama Ishraqa nema take de saita Tona masa asiri hankalinta zai kwanta Minal tayi murmushi, ita ba tasan duk wannan tambayoyin da Ishraqa take mata saboda Asim neba Ahankali yatako yazauna a daya daga cikin kujerun falon, ya kalli cikin idon Ishraqa yace "toba shikkenan magana ta qare ba?" Babu wanda bai Bawa dariya ba, sosai Amina take dariya, yadago kansa Yana satar kallonta, itama anata bangaren satar kallonsa tayi, aikuwa Idonsa yahadu dana juna, cikin ransa yace kai,ya Allah! Ya kalli mamy yace "Mamy Yaya maganar Daddy?" Daure fuska tayi tace "nayi waya dasu dazu, nace sutura case din zuwa court, acan Sai suyi masa hukuncin daya dace dashi" "mamy kiyi hakuri, Nima dayake son yakashe ni nabarshi da mahaliccinsa" "Asim bazan rabu dashi ba saiya yiwa kotu Bayanin duk abinda ya shuka, Sai yafadi mutanan daya hada baki dasu suke son kasheka, dukiyar ku kuma idan yabayar kansa, idan bai bakuba zai Baku ranar lahira, ranar da bashida kudin biya saide abiyaku da ladansa, Shima ladan idan babu Sai a rage naku zunubin aqara masa, saboda Amjad yasa na jinkirta maganar, saboda inajin nauyin Yaron, amma babu yanda zanyi, idan bai Fadi da wanda yake waya Akan akashe kaba, to koda shi anyi masa hukunci sauran suna nan, saboda haka dole yafada su waye, a yanke wa kowa hukuncin daya dace " Duk falon Sai sukai Shiru suna sauraron mamy, gaskiya tafada, Daddy bai kyauta musu ba, Amina ta kalli Asim, saiya Bata tausayi, koda yake a yanzu kam shidin ba abin tausayi bane, itace abar tausayi tunda shide yagama da tasa matsalar, itace de duk lokacin data tuno mutuwar da mazajen ta sukeyi, Sai gabanta yayi mugun faduwa Asim ya kalli mamy yace "hakane Mamy, amma Sai yaushe zamuje? Amjad yana cikin damuwa" "idan kungama abinda kuke anjima Sai muje" Amjad ne yafuto daga dakinsa, yagama cin abinci yayi wanka ya sauya shiga zuwa manyan Kaya kamar yanda yayansa yasa ka, wani irin kyau yayi kamar baya tattare da damuwa Su Ishraqa ya kalla yace "Anty ina kwanan ku" Suka amsa masa cike da kulawa, ya kalli mamy yace "Mamy ina Anty Amrah?" "Amrah tana daki, mekuma zakaje kayi mata? Ba yanzun nan kuka Gama doke doke ba?" Kansa ya shafa yace "mamy hakuri zan Bata fa" Tace "naji, Allah ya shirya minku gaba dayanku" Murmushi yayi ya kalli Yaya Asim, sannan yashige Dakinsu Amrah, Asim ya girgiza kansa, wadannan yaran basaji, wato bai daddara da abinda yaji dazu ba shine yanzu yakoma Yana shiga d'akin yaganta a kwance agado idanunta a lumshe, zama yayi agefenta Yana qare mata kallo, Amrah fa mace ce har mace, duk wanda ya aure ta dole ayi masa murna saboda zai huta sosai, yakai dubansa zuwa hips dinta ya ganshi abaje kamar na wata matar aure, Ajiyar zuciya yasaki yayi Kasa da murya yace "Amrah!!" Gabanta ne yafadi, mekuma yakawo shi wajan ta?, Shiru tayi masa kamar me bacci Sake matsawa yayi kusa da ita ya kalli tafin kafarta fari tas dashi babu digon datti, Ahankali yadora hannunsa akai Yana shafawa, cikin shagwaba yace "Anty Amrah..." Doke masa hannunsa tayi da kafarta, cikin masifa tatashi zaune tace "miye yakawo ka dakina? Amjad bansan ganin fuskarka katashi kafice" "naji zan fita, amma kiyi hakuri, Nima.... nima dazun bansan hakan zata faru ba,kiyi hakuri kinji...." Banza tayi ta qyaleshi, yasake sassauta murya yace "kinji please" "naji, Dan Allah katashi kafice" Ahankali ya tashi daga kan gadon yafuto, tabi bayansa da wata irin harara cikin ranta tana fadin d'an iska kawai, marar kunyar banza Yana futowa daga d'akin nata basu 6ata lokaci ba suka nufi wajan Daddy, suna tafiya Ahanya Amjad yayi Shiru Yana kallon hanya, shide yasan cewa ba soyaiya yake da Amrah ba, amma besan dalili ba idan tayi fishi dashi yake Jin babu dadi a ransa, gashi koda yaushe cikin fada suke, amma idan tayi fishi taqi kula shi yana shiga cikin damuwa Dan qaramin tsaki yaja a ransa, to mema ya kaishi kissing dinta? Wacce masifar ce ta kaishi? Karma tafara tunanin da niyya yayi mata hakan Dan yaji dadi kokuma wani abu makamancin haka, bayan Shima ba hakan ya soba, to Amma tayaya zai Hana ransa abinda yake so? 😳 Yana wannan tunanin har suka qarasa, basu Sha wata wahala ba tunda tare suke da mamy aka bar Daddy yafuto, mamaki ya kama su ganinsa tare da Alhaji Umar, qanin mahaifin Lubna, wanda shi din abokin Daddy ne qut da qut Jikin Amjad yayi sanyi, yakoma gefe daya Yatsaya kansa agefe, kwana daya kawai amma har kamar Daddy tafara sauyawa Yana qaraso wa wajan su ya tsugunna yace "Hajiya Ussaina, kinmin komai a rayuwata, yanda kika riqemin dana ba kowacce macece zatayi hakan ba, Amma son abin duniya yarufemin ido naci amanar dan'uwana da muka futo ciki daya, naci amanar yaransa, haqiqa nabiyewa Rudin duniya, Amma inaso kisani ba laifi na bane hakan, asalima Alhaji Umar shine silar lalace war komai, shine mutumin dayake zigani daga gefe ina aikata komai, yasa na dauko takardun kadarorin ku nabashi a jiya, ashe yariga yagama siyar da komai yayi amfani da kudin, yar dan'uwansa taga Asim a makaranta ta nuna tana sonsa, yazo min da maganar auren banyi tunanin komai ba na amince, bayan yariga yasan yarinyar ba mutuniyar kirki bace, asali ma shida kansa yafadamin yasha neman yarinyar, amma rashin hankali yarufemin ido nayarda aka hadata da dan d'an'uwana, bayan zaluncin da yayiwa yarinyar yake ne manta a matsayin ta na yar dan'uwansa, hakan bai isa ba saida yafara yimata barazana Akan inde Bata kashe Asim ba, zaizo har gida yatona mata asiri, ita kuma hakan ne yasa take aikata komai , abinda nasani shine na zalunci kaina da kaina, saboda nida kaina na aikowa da Lubna guba tazubawa Asim, amma Sai Allah ya kare shi Widad taci, saboda alokacin gani nake kin riga kin janye min dana Amjad daga jikina, kin rabani dashi, shiyasa Nima naso na rabaki da naki Yaron, amma banda wannan sauran kashe kashe da komai alhaji Umar ne yake kiran Lubna yake Bata umarni Akan komai, nariga na amshi laifi na tun a Daren jiya nayiwa hukuma Bayanin komai, ina fata hukuncin da za'a yanke min yazama Shine Sanadin shiryuwata, inaso Keda Asim da Amrah ku yafemin " Yana gama wannan maganar yafara hawaye sosai, ita kanta mamy jikinta yayi wani iri, hawaye ya zubo mata tasa hannu ta share Amjad kuwa yarufe Idonsa da tafukan hannunsa yana kuka wiwi, Asim ya goge kwallar Idonsa ya dubi d.p.o yace "babu yanda za'ai muyi belinsa yanzu?" "mun riga mun tura case dinsu zuwa kotu Yallabai, laifin dasuka aikata ba qarami bane dazamu iya badashi yanzu, anrasa rayukan mutane ta sanadinsu, yanzu haka mun tura ataho da Lubna, zamu tattarasu mu turasu court gobe, amma idan bai Bawa kotu wahala ba kamar yanda muma yabamu hadin kai yafada mana komai tun kafin kuzo, to itama kotu zata iya masa sassauci Akan haka " Al'amarin yawuce inda Asim yake tunani, haka suka dawo gida cike da damuwa, washe Gari kuwa kotu ta yanke musu hukunci, Alhaji Umar hukuncin kisa ta hanyar rataya,sannan kotu zata saida kadarorinsa abawa su Asim haqqinsu daya cinye, Daddy kuma an turashi Gidan kaso na tsawon shekara biyar, Lubna kuma Shekara biyu tare da aiki mai tsanani Sosai take kuka tana kallon Asim, tanaso ta roqeshi yayafe mata amma babu hali Bayan sun dawo daga katun Kasa gane kan Amjad sukayi, saida suka hadu gaba dayansu suka bashi hakuri tare da kalamai masu dadi sannan ne yad'an saaki ransa Su Ishraqa ganin gidan babu lafiya suma basu nunawa Mamy suna son Insaaf tadawo wajan su ba kafin ayi maganar yanda zata tare agidan mijinta Sai bayan sati daya suka shirya duk su ukun suka tafi Sudan domin taga dangi suma su ganta Bayan sun sauka a qasar anan ne taga soyaiya sosai awajan dan'uwan mahaifinta Hammudi, Sai kuma wata cousin din Ishraqa mai suna Malaz, tunda sukaje awajan ta take zama, Ishraqa kam Bata zauna ba, kasuwa take shiga itada wata qawarta suna hado abubuwan gyaran jiki , kwanan su hudu amma saboda yanayin Garin harta fara haske, kowacce Rana da abinda Malaz take koyawa Amina na kula da miji,kwanansu biyar Ishraqa ta turata wajan qawarta dake Shari Moya, acan ake mata gyaran jiki, turaren tsugunno kuwa wato (dukkan) tsallaken kwana daya sukeyi, yau idan akayi, gobe ba za'ayi ba, lokaci daya jiki ya murje, fata tafara sheqi, lungu da saqo nata ya dauki qamshi Dazasu taho Nigeria sunje kasuwa, taga wani agogo mai kyau ta kalli mamanta tace "Anty Kinga wannan kamar zai yiwa Yaya Asim kyau" Ishraqa tayi murmushi tace "zaiyi masa mana, ki dauka masa kihada masa da zobe ma, idan mun koma saiki saka masa" Kunya ce ta kamata, tasa hannu tarufe idonta, Haka suka bari qasar cikeda kewar yan'uwa washe Gari suka dawo Nigeria, Kai tsaye agidan Ishraqa suka sauka, anan Amina taga wata sabuwar duniyar, kasancewar da daddare suka sauka basu nuna mata komai ba, bayan sun Gama cin abinci, tayi wanka tana saka kayan bacci Ishraqa tashigo d'akin Zama tayi a gefen gadon ta tana kallon yar Tata, Amina ta juya ta kalleta tayi murmushi, turare ta fesa sannan tadawo kusa da ita zauna tace "Anty ina Abba na" "Yana kwance adaki, yanzu zan tafi Nima, karbi ma ganinki Kisha, Antynki Malaz tace Karki yi wasa dashi" Yatsina fuska tayi, idonta yayi rau rau Yana kawo ruwa tace "nifa Anty dama Dena bani wannan abun kukai" Ishraqa ta kalleta da mamaki tace "saboda me?" "Anty ni banaso Shima narasashi" "waye bakya so ki rasa?me kike nufi?" "shi Yaya Asim din,Kinga shine ya taimaka min, kuma ni...ni inajin tausayin sa" Ishraqa tayi murmushi tace "Kinga Insaaf, kifadamin menene matsalar? Ba'iya uwa zaki daukeni ba, harda qawarki, kifadamin komai, kince kina Jin tausayin sa, hakan yana nufin kina sonsa ne?" Cikin sauri tace "a a Anty, ni Bana sonsa, nide kawai inajin tausayin sa, kuma banaso narabu dashi" Ajiyar zuciya ta sauke, takamo hannun yarinyar Tata tariqe, tace "Insaaf kinason Asim, wannan shine maganar gaskiya" "A a Anty, ni tausayinsa nakeji kawai, sannan Kuma Ina tsoron wani abu yafaru atsakanin mu, zai mutu,kamar yanda sauran mazajan dana aura suke mutuwa, ni kuma Bazan iya jure rashin sa ba" Mamaki yakama Ishraqa, tace "mazaje kuma?" Idonta ne yacika da qwalla, tabbas akwai abinda yake damun yar tasu, wacce irin damuwa ce wannan? Muryarta na rawa tace "kintaba yin aure ne Insaaf?" Kanta ta daga mata, sannan tace "Aurena shida Anty" Hawaye ya sakko wa Ishraqa, akwai wata aqasa kenan, tasa hannu ta share tace "meyasa baki fadamin ba? Haba Insaaf? Nifa mahaifiyar kice, ta wani Fannin kuma qawarki, tunda kina auren abokina ai kema kinzama qawata, meyasa tun kafin muje Sudan baki sanar dani ba, Dan nasan irin gyaran dazasu miki? Wacce irin rayuwa kikai Abaya Insaaf? " Kallan mahaifiyar Tata tayi tace" Anty nifa... ni... ni babu abinda yake hadani dasu, kowa na aura mutuwa yake, inde sunzo wajena da daddare to shikkenan saisu mutu, bansan meyasa ba Nima, Yaya Ammar ma Dana aure shi kwanan sa daya yarasu, shine su Inna suka koreni daga wajan su, Shima me garin yace dama yafadamin inde wani yasake mutuwa ta dalilina to zan bar masa garinsa, shine Yaya Asim yace nazo mutafi, dana biyoshi wani malami yayi mana aure dashi, Shima washegarin daya daura mana aure yamutu, Kinga Shima Yaya Asim zai mutu ko? Shima tafiya zaiyi yabarni, shiyasa nakeso Shima yasake ni, banaso yamutu Anty...." Sharhi,Anda Share please πŸ™πŸ» ✍🏻 Amnah El yaqoub [2/24, 1:08 PM] El~Yaqoub: INSAAF Writing by:Amnah El yaqoub 37&38 Like my page on Facebook πŸ‘‡πŸ» https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 Kasa magana Ishraqa tayi, Sai kuka data fashe dashi, kawai Girgiza kanta take takasa cewa komai, itama 'yar dataga haka saita fara hawaye, cikin kuka tace "Anty kiyi Shiru" Cikeda kuka tace "saboda me zanyi Shiru Insaaf?, nadade na sanin akwai abinda kika boyemin, ina nan ina Addu'ah Allah yasa kinfada cikin hannu nagari, ina tunanin mutane zasu soki ashe gudunki suke, hasbinallahu wa ni'imal wakeel, wacce irin masifa ce wannan? Aurenki bakwai Insaaf meyasa kikeso kiyi na takwas? Idan Asim ya sakeki wakike tunanin zai aureki ya 6oye miki sirrin ki kamar yanda Asim yayi? Duk yanda nake dashi betaba fadamin labarinki ba tun kafin nasan ke 'yata ce, Insaaf Ada kenan ma dabaisan akwai wata alaqa a tsakanin muba, tayaya kike tunanin yanzu zai fadamin wannan matsalar? Asim mutum ne Insaaf, abun so awajan kowa, bazan taba yarda kirabu da Asim ba, Insaaf tun kafin na haifeki nake tare da Asim, tun kafin yasan ke wacece yake kula da dukiyar ki, idan kika rabu dashi kwata kwata ni baki kyauta minba, zan samu babanki nayi masa magana gobe, amma kidena cewa kinaso yasakeki kinji, Allah bayason haka " Ahankali ta daga mata kai, sannan tace"to Anty" "yauwa karbi maganin ki Kisha, ki kwanta kihuta" Babu musu ta karba ta shanye Sannan ta kwanta, Ishraqa taja mata Bargo sannan takashe mata wutar d'akin tatafi d'akin El Hameed itama ta kwanta Qasa qasa yake jin kukan ta Yana ratso cikin kunnansa Ahankali ya karanta Addu'ar tashi daga bacci, ya kalleta yace "Habibty lafiya kuwa?" "Habiby nayi magana da Insaaf ne yanzu" "magana kuma? Dama baki Barta ta kwanta tahuta ba?" "A a Habiby, maganar tanada muhimnci sosai, Insaaf tana tare da matsala Habiby, tacemin tanaso Asim ya saketa" Yanajin haka ya tashi zaune da sauri "saki kuma? Meyake faruwa to?" "Habiby Insaaf fa aurenta shida kafin Asim...." tsaf ta zayyana masa komai kamar yanda Minal ta sanar da'ita "innalillahi...yanzu Ina Insaaf din take?" "ta kwanta, tana dakinta" "wanne irin tana dakinta Ishraqa, tayaya yarinya zata fada miki wannan maganar kitaso ki Barta cikin damuwa?" 😟 "to ai Naga dare yayi, kuma daga tafiya me nisa muke, kaima bansan dagama hankali" Dan qaramin tsaki yaja yace "Kinga, tashi muje dan Allah, to Ishraqa kodaga bangon duniya muke ya dace mubar ta cikin damuwa ne? Muje idan na tabbatar tayi bacci saimu dawo" Daga masa kai tayi, sannan suka nufi d'akin Minal, suna zuwa ya kunna wutar d'akin, harta fara bacci Alokacin, wutar dasuka kunna ne yasa tatashi, zama Sukai Akan gadon, El Hameed ya shafa dogon gashin ta yace "bakya tare da damuwa Insaaf?" Cikin mamaki tace "Abba damuwa kuma?" "mamanki tayi min Bayani yanzu, kiyi hakuri karkisa damuwa aranki harta ta6a lafiyarki" Murmushi tayi tace "babu komai, ai harna fara bacci ma" "to Allah ya yi miki albarka yata, kwanta kiyi baccinki" Komawa tayi ta kwanta, ya sunkuya yadora ba kinsa a kanta yayi kissing sannan yaja mata bargon Fira suka fara yi shida Ishraqa kadan kadan, basusan yaushe bacci ya dauke suba, haka suka kwana duka su ukun a dakinta *** ****** *** Zaune yake a falon su, yayi kyau sosai cikin shigar sa ta kullum wato suit, breakfast yagama amma yana zaune afalon baitafi wajan aiki ba, mamy tana gefensa da Carbi a hannun ta,idan bai manta ba rabonsa da Insaaf tun kafin sutafi Sudan, ta nemeshi awaya ma ya gagara, wajan contact din kan wayar sa yashiga yafara duba numbers din ciki, saida yagama gani sannan ya yatsina fuskarsa, Sai yanzu yatuna batada waya , ya kamata ace yakira ta ya nuna mata kuskuren ta Akan rashin kiranshi, to Amma kuma ta'ina zai kirata? Ishraqa zai Kira ko El Hameed? πŸ€” Amrah ce tafuto daga d'akin su kai tsaye wajansa ta nufa ta zauna aqasansa ta gaida shi A taqaice ya amsa mata,zuciyarsa ce ta bashi shawara yanemo number Ishraqa. Number yakamo yayi dialling saiya katse, yasake yi a Karo na biyu nanma ya katse Wayar ya ajiye agefe, to yanzu idan ya Kira Ishraqa ma meze cemata? Wata zuciyar ce tace dashi kakirata, kasan Yara da San wasa da waya, yanzu haka wayar tana hannun Minal din tana yin game da'ita Haka yasake dialling number, tana shiga kuwa aka daga, muryar Ishraqa yaji tace "Salamu Alaikum Asim katashi lafiya?" Wayar ya kalla, cikin sauri ya kashe, anata bangaren tace "kode network ne?, Bari nasake Kira" Tana Kira yad'auka yace "Sorry akwai number dazan Kira ne sainayi mistek" 😎 Tace "to shikkenan, jiya mun sauka da daddare, ko zaka shigo ne kafin kawuce office?" "no, akwai ayyukan da zanyi" Mamy dake gefe ta daga kai ta kalleshi, Yana cewa akwai ayyukan da zaiyi amma kuma Yana zaune bashida alamar tafiya office dinma, tarasa meyake jira? Daga dayan bangaren Ishraqa tace "Ok, Allah yakiyaye hanya" Shima yace "Amin" sannan yakashe wayar Ishraqa tayi Murmushi, kode Asim yana neman Insaaf ne? Ikon Allah, aure me Hana wani abun,aure mesa ayi wani abun, jidai yanda Asim yake magana da'ita kamar ba Ishraqa tasa ba, kamar ba aminiyarsa Ishraqa ba, Ahankali tatashi tashiga d'akin Insaaf, tana zaune da breakfast agabanta, El Hameed Yana karanta mata Jarida, zama tayi ta kalleta tace "idan kingama break din kishirya muje kizabi wayar da kikeso, yanzu mijin ki yanason magana dake, kikirashi" Ta ajiye mata wayar agefenta El-Hameed yace "saide kuje Keda ita, ni akwai inda zani, nayi waya da wani malami Akan issue dinta, zanje musan abinda ya kamata ayi" Tace "to zamuje insha Allah" Kallan Minal yayi yace "Insaaf idan kingama wayar, ki same mu adaki" Ahankali tace "to Abba" Suna fita takirashi, yayi mamakin ganin kiran Ishraqa bayan sunyi sallama ita dashi, dauka yayi tare da sallama, itama anata bangaren ta amsa masa, tace "Yaya ina kwana" Wata irin Ajiyar zuciya yasauke, har ita kanta Minal din taji shi, Kallan gefen mamy yayi, ya kalli Amrah data zauna agabansa, lokaci daya ya tsinci kansa da qaramar murya πŸ™Š Cikin qasa-qasa da murya yace "bakya kira kiji lafiyar mutane ko?" Cikin shagwaba tace "to Yaya ni banda waya fa..." Yasalam! Yafurta hakan a ransa "Alright, kishirya Amjad yakaiki saiki za6i wadda ta miki, Amrah tanason magana Dake" "Yaya Anty tace zasu siyamin, ka cewa Anty Amrah ina missing dinta" Idanunsa ya runtse 😣 Iya Amrah take missing, Ahankali yace "Bye" qit yakashe wayar Mamaki ya kamata, Ana magana rimi-rimi kuma Sai abun yaqare a haka? Tashi tayi ta nufi wajan Iyayen nata, anan suka fara nuna mata kayaiyakin ta, da wasu daga cikin kadarorinta,da kayanta tana qarama, Abin saiya dinga Bata mamaki yanda suka iya Adana kayan har zuwa wannan lokacin, anan El Hameed yabar su, yafice zuwa wajan Malamin da sukai magana *** ****** *** Amjad ne yafuto daga dakinsa, kana ganin fuskarsa zaka tabbatar Yana cikin damuwa, bayan ya gaisa da Mamy yazauna kusa da Asim, yace "Yaya ina kwana" Kallansa yayi yace "lafiya, yaushe zaka tafi Adamawa ne?" "inata shiri Yaya, zan koma insha Allah, Bana Jina yanda ya kamata ne shiyasa" Asim ya jinjina kansa, yasan cewa damuwar Amjad Bata wuce Akan Daddy bane. Amjad ya kalli Amrah yace "Anty Amrah ina kwana" Tanaji tayi banza dashi, yayi Dan qaramin murmushi yace "bazaki amsa ba?" Nanma batace masa komai ba tayi Shiru, Asim ya kalleta, yaga alama kamar Amjad Yana son Amrah, amma ba zaice komai ba tunda Shima Amjad din be furta ba, inda hakan ta kasance kuwa zaifi kowa farin-ciki, ko banza Amjad dinsa zai zama cikakken namiji, yadena wannan shagwa6ar,yanda yakejin Amjad a ransa zai Iya bashi kowanne irin goyon baya Akan hakan, ajiyar zuciya yayi yace "ba dake yake magana bane?" Kallan Asim din tayi tace "naji shi Yaya, kafada masa ni yafita harkata, kowa yayi abinda ya shafeshi" 😠 Asim ya dafe kansa da hannunsa yace "meyake damun kune? Ku qananun Yara ne? Koda yaushe bakuda aiki daga fada Sai fada?" Mamy dake gefe ta kalli yaran nata "doke-doke zaka ce Asim,Abin ai yafi qarfin fada, ninariga na zare hannu na daga Al'amarin su, saide Kai in zaka iya" Amjad ya shafa sumar kansa yayi murmushi, ya tashi yace "Bari in dauko wayata akwai inda zani, Anty Amrah ko zakije?" Yaqarasa maganar Yana kallonta 😊 Kanta ta girgiza tace "A a" Daga nanma tatashi tashige dakinsu, tunani take a ranta tayaya ma zata bishi? Agidama ya matse ta yayi kissing dinta idan tabishi waje tasan mezai faru? Shima murmushi yayi kawai yawuce dakinsa, Asim yabishi da kallon mamaki, baiyi tunanin Amjad zai share Amrah ba,yayi tunanin zai biyeta suyi cacar baki ne kamar yanda suka saba, amma abin mamakin saiyaga murmushi ma yayi, kode tunanin sane yake shirin tabbata? Ajiyar zuciya ya sauke ya kalli Mamy "zantafi office mamy, saina dawo" "inason magana dakai" Dawowa yayi ya zauna, ta kalleshi da kyau, tanaso ta tambayeshi menene damuwar sa? dawa yake waya haka Sai kashe murya yake kamar yasamu budurwar sa, duk da tasan ba lalle ne yabata amsa ba, ya kamata ace taji da wadda yake wannan maganar, kartaje haqilon banza kawai take akansa tace "dawa kake waya ne?" Kai tsaye yace "Mami Minal ce..." Murmushi tayi tace "lafiya dai ko?" "gashinan de" πŸ˜‚ "meyake faruwa to?" "mamy tunda sukai tafiyar nan Bata ta6a nemana ba, sannan memakon ta sauka anan shine tabisu Takoma can gidan, nakirata ina mata maganar Bata kirana, shine tacemin tayi missed din Amrah" yaqarasa maganar Yana hade rai Mamy tayi Shiru tana Kallan tsantsan karfin hali dakuma rashin gaskiya irin na Asim, da kunnanta taji yana cewa Amrah tana son magana da ita, amma yanzu Wai qiri- qiri yake cewa yayi mata magana Bata kiransa Kallansa tasake tace "Asim" "na'am mamy" Tace " kafita daga cikin Idona na rufe Asim,kafadamin kana son wannan yarinyar kokuma baka sonta?" Cikin sauri ya kalleta yace "Mamy daga maganar kiran waya meya kawo zancen soyaiya kuma?" Mamy tace "ikon Allah,toka sauwaqe mata, ina amfanin zama da mutumin da baya qaunarka?" "to mamy waye yace Bana qaunarta?, itace Bata sona, Nima shiyasa ban nuna mata ba"πŸ˜œπŸ˜‚ "waye yafadama Insaaf Bata qaunarka?" "mamy Muhsin ne yacemin ranar dasuka hadu a hanya yadauke ta suka tafi gidansa ita da kanta take roqonsa yakai ta court Araba auren mu" "Subhanallah..., to Amma kasan yarinya ce, sannan may be da rashin kulawar da kuke Bawa juna shiyasa tafadi haka, Asim baka kula ta, itama Bata kulaka, tayaya zaku Fahimci juna?" "Nima bansan ina sonta ba, saida Muhsin ya fadamin, daga baya sainayi tunani Naga hakanne, sannan mamy akwai abinda nake tsoro, duk mazajen da Minal ta aura mutuwa suke mamy, inajin yanzu saura ni, saboda banajin zan iya rayuwa batare da'itaba Mamy" 😒 Mamy tayi murmushin jin dadi, lalle fa a kace soyaiya mai sauya Bawa, Wai yanzu Asim ne yazauna yake fada mata yanda yake son wata yarinya, inda Ishraqa taji wannan maganar ai Zaman unguwar saiya gagareshi, Dan tasamu abinyi kenan Tace "Asim maganar mutuwa kowa kaga yamutu, kwanan sa ne yaqare, Amma dama kasan tataba yin aure amma baka fada mana ba Asim?" Kansa aqasa yace "Aurenta shida mamy, nine ba bakwai, kuma dukansu mutuwa suke, shine dalilin dayasa mutanan da suka raineta suka gujeta, ni kuma nataho da'ita" "innalillah...., Asim aure shida fa kace? To menene yake damunta? Menene Sanadin mutuwar tasu?, aini nayi tunanin befi aure biyu ba kake nufi" "A a shida ne, sannan Nima banyi mata wannan tambayar ba, saboda kartaga kamar cin fuska nake mata" "tabdi, lalle akwai abinda yake faruwa, a 'yan qananun shekaru irin nata tayi wannan auren kuma ace duk suna mutuwa Asim akwai alamar tambaya, amma katashi kaje zanyi magana da Ishraqa, idan ma Addu'ah za'a mata da roqon Allah duk Sai ayi, amma kadena tsoro kaji? " ta qarasa maganar cikin sigar lallashi Kansa ya d'aga mata sannan yace"to Mamy yaushe zata dawo?" Mamaki de yaqara kama Mamy, tace "Asim kaida Ishraqa ai kunfi kusa, kaje ka dauko matarka" Nayau ba yawa, kuyi hakuri please ✍🏻 Amnah El yaqoub [2/25, 5:48 PM] El~Yaqoub: INSAAF Writing by:Amnah El yaqoub 39&40 Like my page on Facebook πŸ‘‡πŸ» https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 Cikin sauri yace "A a mamy, duk yanda kukai babu damuwa, Nina tafi office" Mamy tayi murmushi tace "to Allah yadawo min dakai lafiya Asim" *** ****** *** Acan gidansu Ishraqa kuwa zaune suke afalo su biyu, mai ne a hannun ta tana shafawa Minal a kanta,wayar Ishraqa tayi qara, tana dubawa taga mamy ce, ta dauka suka gaisa cike da kulawa, mamy tace "Ishraqa kin dauke min yata, yaushe zata dawo ne? Shima dan'uwan naki yanzu yagama mita Wai taqi tadawo, nace masa yazo yayi miki maganar shine yace duk yanda mukai daidai ne" Dariya tayi tace "Mamy Aida kin turo shi yazo da kansa" "a a, ai yanzu kin zama dodon Asim tunda yagane komai" "babu wani dodo mamy, ai anzama daya, wallahi Nima inaso ta tare to jiya Sai muka tattauna Akan matsalarta nida Abbanta, yace zaije wajan wani malami yayi masa Bayanin komai, to shiyasa muka jinkirta, ashe Wai yarinyar nan tana tare da matsala amma daga ita har Asim din sukai Shiru mamy " Mamy tace"kemade kya fada Ishraqa, ni Sai yanzu yake fadamin, shine nace zan sameki muji ta inda zamu 6ullowa matsalar, to ashe itama tafada muku" "tafada wallahi, kibashi hakuri, idan Abbanta yadawo zanyi masa magana insha Allah" "to shikkenan Ishraqa babu damuwa, amma babu wani taro da za'ayi Ishraqa? Ina nufin na tarewar Tata, tunda Kinga dakuka ganta ma babu wani abu da mukai" "to aini mamy duk jikina ne yayi sanyi, wannan matsalar Tata tafi komai dagamin hankali wallahi, a barshi kawai, muyi musu Addu'ah" "toshknn Ishraqa hakanma yayi, Allah ya tabbatar da Alkhairi a gaida yartawa". Suna gama waya ta kalli Minal tace "Insaaf, tashi kije ki dauko maganin ki Kisha, mijin ki Yana maganar tarewarki" Bakinta taturo gaba, cikin shagwaba "Anty nifa tsoron sa nakeji,tayaya zamu zauna tare ni dashi, kuma ni gara mu haqura, banaso ya mutu" "banason shirme Insaaf, cemiki akai shi din sonki yake? To bari kiji da bakina da nasa anan wajan yafadamin tausayinki yake ba sonki yake ba, rannan daga ke saishi naganku afalo kuna zance, zaki kawomin maganar tsoro? Kinga tashi ki dauko Kisha,idan baki shaba Yaya zanyi dasu?" Haka taje ta dauki maganin Tasha, sannan tafuto, anan taga Abbanta harya dawo tare da wani malami, Allah ya Sota ta sanya hijabi babba, cikin nutsuwa ta gaida baqon, sannan ta zauna aqasa, Ishraqa ta futo da ruwa da lemo ahannuta ta ajiye musu, sannan tanemi waje ta zauna Malamin ya dauki iya ruwa yasha, sannan ya qurawa Amina ido Yana kallanta, dago kanta tayi ta kalleshi, cikin sauri ta maida kanta qasa Saida ya dauki lokaci yana kallonta sannan yace "ke!" Batare data kalleshi ba tace "Na'am" "kinada Aljannu ne?" Cikin sauri ta kalleshi tana girgiza kanta "Aljannu, a a, ni banida aljannu, banida komai" Murmushi Malamin yayi yace "shikkenan tashi kije" Babu musu tatashi tashige dakinta, Malamin ya kalli El-Hameed da Ishraqa yace "Alhaji yarinyar ku tanada aljannu, kallo daya nayi mata nagane hakan, akwai baqaqen aljannu atareda ita, sannan jinnul Ashiq ya aure ta, bazai Bari tayi aure cikin kwanciyar hankali ba" Hawaye ya zubowa Ishraqa, tasa bayan hannunta ta share, to a'ina Insaaf ta hadu da aljannu kuma? El-Hameed yace "Subhanallah, yanzu Malam Yaya za'ayi?" "akwai magungunan dazan aiko muku dashi , saita dinga amfani dashi, insha Allah komai zai wuce,saboda magungunane masu qarfi, idan akwai abinda ya faru kuma saiku sake sanar dani" Godia suka sake yi masa, sannan suka rakashi yatafi Suna dawowa El-Hameed yace " bansan yanda akai tasamu wannan matsalar ba, amma insha Allah komai yazo qarshe" "abinda nagama tunani kenan Habiby, shiyasa itama tace tanaso tarabu da Asim, Kar Shima yamutu" "a a maganar rabuwa da Asim ma ai Bata taso ba, idan tarabu dashi tayaya ne zamu gane aljanin yabar ta kobai Barta ba?" "saida na6ata raina na nuna mata babu ita babu rabuwa da Asim, sannan ne tayi Shiru, kuma mamy tamin waya tanaso Insaaf Takoma Dakin mijinta" "Allah yaqara kiyaye wa, insha Allah idan tafara amfani da maganin nata, saita koma" *** ****** *** Da yamma ya aiko musu da magungunan Kala-Kala, saida suka Bata maganin ne tasan cewa Kallon me aljannu suke mata, haka ta hakura ta karba, amma itade tasan cewa batada komai, sati daya suka dauka suna Kallan yanda take amfani da maganin, itade babu ranar fashi kullum saita Sha, amma duk lokacin da zatayi na hayaqi daqyar take yi, Sai Ishraqa ta tsaya a kanta Saida tayi kwana goma tana amfani da maganin sannan suka fara shirin maida ta gidansu Asim Ranar Yana wajan aiki, baisan a ranar za'a dawo da'itaba, Ishraqa kuwa da yamma ta rakata, bayan huduba datayi Mata, saita tagama hure mata kunne Akan kula da Asim sannan tabaro gidan Dakin Amrah tayi Zaman ta, mamy tashigo d'akin da sallama abakinta, cikin ranta tace masha Allah, saboda yanda taga jikin Minal din Sai wani irin sheqi yake, dama tasan zata samu gyara mai kyau inde sukaje Sudan, bare ma yanda Ishraqa take yar gayu takame El Hameed gaba da baya babu yanda za'ai tabar 'yarta haka, zama tayi agefenta tace "Insaaf yakika zauna ke kadai? Kikirashi mana" Sarai tasan inda zancen mamy ya dosa, Sai tayi fuska tace "mamy ina Anty Amrah" "Amrah taje unguwa, amma nasan kafin magrib zata dawo, kikira Asim yadawo da wuri, shida yake tambaya kinje kin zauna yaushe zaki dawo ai gashi kin dawo Shima saiya dawo" Murmushi tayi batare datayi magana ba, mamy tace "zaman Aure Sai kinyi hakuri Minal... zomu zauna ne, zomu sa6a Idan wani abu yashiga tsakanin ku mijin ki ne, kiyi kokari ki zaunar dashi ku sasanta kanku, sannan zan fada miki wani sirrin Asim guda daya, Yana son kulawa, shi mutum ne maison akulashi, ko rai ya6ata miki kikai fishi toki shareshi kidena kula shi anan Hankalinsa zai tashi, da haka Lubna ta samu kansa, amma ina fatan yasamu kulawa awajan ki fiye da wadda yasamu awajan Lubna, Kada kiji kunya ta, Nima kamar mahaifiyar kice" Ahankali ta daga kanta tace "to mamy insha Allah" Haka mamy ta zauna suna fira kadan kadan har aka Kira sallar magrib Amrah tadawo sannan mamy tabar d'akin Amrah ta kalleta tace "Amarya Amarya, gaskiya ne, irin wannan kyau haka kamar an miki wankan inji?" "kai Anty Amrah, ahakan?" "Emana, kinganki kuwa? Kinyi wani fresh,Wai Yaya Asim ya ganki kuwa?" "A a baidawo ba" Amrah ta riqe ha6arta tace "Tabdi, injin bazai ganeki ba" Murmushi tayi maimakon tabata amsa saitace "tunda yamma fa nazo, ashe ke bakya gidanma Sai mamy ce take fadamin" Zama tayi akusa da'ita tacire mayafin kanta tace "Eh wallahi naje Agege suna, wata qawata ce ta haihu" Tace "To Allah yaraya" "Amin Minal, Bari inyi sallah" Tafadi haka tare da shigewa toilet Da daddare mamy ce tarakata d'akin Asim din, sannan tayi mata sallama tafuto Haka ta zauna shiru ita kadai, Bata taba shiga cikin dakinsa ba Sai yau, koda yaushe iyakarta falon sa,amma tsarin d'akin nasa yayi mata sosai, babu tarkace dayawa, kayan furnitures din brown ne and milk color, mayafin jikinta tacire tashiga toilet tayi alwala tazo tayi sallar Ishsha'i, harta idar baidawo ba Ta kalli agogo taga bakwai da kwata, afili tace "bari intashi inyi wanka na kwanta" Kayan jikinta tafara ragewa, saida tacire komai ta zubasu Akan gadon, daga ita Sai d'an qaramin pant yaturo kofar d'akin yashigo Gabansa ne yayi mugun faduwa saboda ganin abinda bai taba zato ba, qyam yaqame akofar d'akin Yana kare mata kallo, shi Yana tunanin yarinya ce qarama ashe Bahaka bane? πŸ€” Lokaci daya yaji yanayin sa Yana sauyawa, Addu'ah yafara yi a ransa Allah yasa karta juyo ta ganshi, ta tsaya ahakan yayita kallonta Hannu tasa zata janye pant din amma saitaji a jikinta kamar Ana kallonta Juyawar da zatayi kuwa Sai ganin Asim tayi yazuba mata ido Yana kare mata kallo Wani irin ihu tasa tashige cikin toilet din d'akin da gudu Sai a sannan yayi wata irin Ajiyar zuciya, sannan yashigo d'akin yazauna a bakin gado, yaushe tadawo ne? Amma mamy Bata fada masa ba Murmushi yayi ya kalli kofar toilet din, cikin ransa yace matsoraciya, ji yanda ta tsorata kamar Bata taba aure ba Lumshe Idonsa yayi Yana shafa sumar kansa Tun dazu tagama wankan, amma ba tasan Yaya za'ai tafuto a haka ba, idonta ne ya sauka Akan towel dinsa na wanka, tadauka tadaura sannan tafuto, Sai Jan towel din take qasa Yanajin alamun futowar ta yabude lumsassun idanunsa yazubasu a kanta, fatarta Sai qyalli take tana wani irin sheqi, jiyake kamar ya fuzgota jikinsa amma kuma hakan bazai iyuba dole saita saki jikinta dashi Juyawa tayi ka kalleshi cikin sauri yadauke kansa, itama idonta ta dauke tana tuno yanda yaganta babu komai dazu, itakam wannan mutumi Yana samun nasara a kanta Wajan mayukansa tanufa duk saita rasa abinda zatayi, kayan mayukanta dasu turaruka wanda aka hado mata Asudan duk suna cikin Jakarta Yana daga kwancen yace mata "baki iya sannu da zuwa ba Sai ihu ko?" Kanta ta sunkuyar qasa tace "sannu da zuwa Yaya" "yawwa, bakiga man shafawar bane nazo na dauko miki?" Mamaki ya kamata, Yaya Asim ne mai cewa zai dauko abu? πŸ€” girgiza masa kai tayi tace "a a" Ahankali yataso daga kan gadon yaqara so wajan ta, tsoro ya kamata, gaban ta yafara faduwa, tasake yin qasa da kanta taqi kallonsa, shi kuwa mansa dayake shafawa ya dauka ya zauna a qasan kujerar datake zaune, sannan ya lakuto man a hannunsa, ya dauki kafarta yadora Akan cinyar sa yafara shafa mata Lokaci daya taji wani irin yanayi Yana shigar ta, shi kansa laushin da yaji fatar jikinta nayi shiyasa yaci gaba da shafa mata man, Yana shafawa Ahankali baisan lokacin dayazo cinyar ta ba, Sai alokacin ya kalleta, cikin sigar rad'a yace "Sannu da zuwa" Daga masa kai tayi, mamakin sa duk ya cikata Yasake yin qasa da murya yace "meyasa baki fadamin zaki dawo yau ba?" Hannunsa dayake murza mata cinya tafara janyewa, maimakon yajanye hannunsa, saiya hada hannun nata yariqeshi cikin nasa Ahankali tace "babu komai" "saboda bakya missing Dina ko?" Ya jefo mata wannan tambayar Kallansa tayi cikin sauri, murmushi yasakar mata, dimple dinsa ya lotsa, saita ga yaqara yin kyau, kuma ya birgeta kamar ta dora hannunta awajan "kishirya zanje wajan Mamy" Wata irin Ajiyar zuciya tasaki lokacin da yafita daga d'akin Kai tsaye d'akin mamy yashiga, tace "Ashe kadawo?" "nadawo mamy, ashe Minal tadawo" "Ishraqa ta rakota da yamma, nayi tunanin zaka dawo da wuri ma" "wallahi mamy aiki ne ya tsaida ni, kuma... kuma bansan... bansan cewa zata dawo ba" ya qarasa maganar a rarrabe Mamy tayi murmushi tace "to saura lefe dakuma tare wa ko?" Kallanta yayi yace "lefe?" "au kama manta da lefe kenan ko? Haba Asim, ai yanda akewa kowacce yarinya itama ya kamata ayi mata, Sai kuma kutashi daga nan kukoma naku gidan" "Za'ayi mata mamy, amma maganar tashi mamy ina zamuje mu barki?" "A a,Lubna ma Dan dole ne shiyasa nayarda kuka zauna anan, saboda koda yaushe neman ganin bayan ka ake, amma yanzu Alhamdulillahi babu wannan matsalar, kaga saiku tashi" "A a mamy, zamu zauna anan din tare daku, nasan itama zataso hakan" "to shikkenan, Allah yasanya Alkhairi, Allah yabaku Zaman lafiya, Dan Allah kadinga Jan yarinyar nan a jiki Asim, kadinga Bata kulawa ko zata saki jiki dakai, Kaine zaka koya mata Yanda zata Soka" Sumar kansa ya shafa yace "insha Allah Mamy" Daga nan yayi mata sallama yatafi dakinsa Yana zuwa yaga harta kashe wuta ta kwanta, murmushi yayi yawuce toilet ya watsa ruwa, sannan yasha coffee yayi shirin bacci Kwanciya yayi a gadon, yasaka hannu ya janyota jikinsa, Ahankali tabude idonta dake cike da bacci ta kalleshi, iska ya hura mata a'idon yace "Daga yau inde ina nan Karki sake kwanciya ke kadai" Kallansa take kwata kwata Bata Fahimci abinda yake nufi ba, Shima kamar yasan Bata ganeba, cimak ya dauke ta yadora ta a jikinsa Sannan yace "Nan ne wajan baccinki" Ahankali ta daga masa kanta, hular kanta yacire yafara shafa dogon gashin ta, Sai cusa hannunsa yake ciki, hakanne yasa ta lumshe idonta tayi luf Akan faffadan qirjinsa Batasan lokacin da bacci ya dauke ta ba, hannunsa yasa ya rungume ta sosai a jikinsa, yanajin yanda albarkatun qirjinta suke ta6ashi, amma beyi mata komai ba, ya Dade Yana zuba murmushi shi kadai, sannan Shima yasamu bacci ya dauke shi Asuba tagari😡 ✍🏻 Mrs.Usman ce [2/26, 2:01 PM] El~Yaqoub: INSAAF Writing by:Amnah El yaqoub 41&42 Like my page on Facebook πŸ‘‡πŸ» https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 Shine yafara tashi da asuba, har zuwa lokacin tana jikinsa a kwance, Ahankali yasaka hannunsa ya janye gashin kanta, sannan yayi kissing wuyanta yashiga toilet. Saida yayi wanka sannan yayi alwala ya shirya cikin jallabiya,kan gadon yazauna ya sunkuya daidai fuskarta, yadora lips dinsa Akan idonta yayi kissing, Ahankali tabude idonta Sai ganinsa tayi kamar zai hade fuskar tasu waje daya,hannunsa yadora Akan lips dinta ya shafa, sannan yace "ki tashi lokacin sallah yayi" Batace dashi komai ba tafara kokarin tashi, yace "natafi masallaci" Wani irin juyi tayi, tasaki hamma, tafara salati, cikin sauri yafice daga d'akin, idan baiyi da gaske ba Insaaf zata iya karya masa alwala Har Gari yayi haske baidawo ba, itama tana idarwa tagudu d'akin Amrah, ta kwanta anan taci gaba da baccinta, Ita Amrah tana bacci batasan ma tashigo ba Sosai su kasha bacci itada Amrah, Sai wajan karfe goma suka tashi, Amrah ce tafara farkawa tana ganin Minal abayanta mamaki ya kamata, dukanta tayi abayanta tace "Insaaf... Yana ganki adakina? Ina kika bar mijin naki?" Cikin muryar bacci tace "miji...?" Zaro ido tayi 😳 data tuna da Yaya Asim... Tace "kaiiii, qarfe nawa yanzu?" Amrah ta kalli agogo tace "Karfe goma, meyasa kika taho nan?" "toshi mafa baya nan, masallaci yatafi" "kuma memakon ki zauna acan harya dawo idan akwai abinda zaki masa kiyi masa shine kika gudo d'akin nan?" Kallan Amrah tayi tace "yanzu yatafi ne?" "a a nikam Ina zan sani? Amma baya kaiwa goma agida kema kin sani" Tashi tayi tafuto daga d'akin, tana zuwa falo taci Karo da Ishraqa da wasu kayaiyakin nata data biyota dasu Tsananin mamaki ya kamata, waje tanema ta zauna,tana kallon Minal din, mamy ce tafuto daga dakinta ta kalli Minal tace "Insaaf har an tashi ne?" "mun tashi mamy ina kwana?" "lafiya kalau, jeki hadowa Umman naki abinci" Cikin sauri Ishraqa tace "a a mamy, aqoshe nake, sauran kayanta ne nabiyota dashi yanzu zan koma gida Nima" Kallan ta yayi, cikin shagwaba tace "Anty Naga ko zama bakiyi ba" "bagani azaune kinganni ba, kwanciya kikeso nayi kuma?" Mamy tace "Insaaf dauki kayan kuje d'akin, Bari naduba Amrah" Tana fadar haka tashige d'akin Amrah, dama tayi hakane danta basu waje ko akwai abinda zasu tattauna, tsakanin 'Yada uwa Mamy tana tafiya Ishraqa ta kalli Minal tace"dauki kayan muje" Babu musu ta dauki kayaiyakin tayi cikin d'akin Asim, itama Ishraqa tabi bayan ta Suna shiga Ishraqa ta qarewa d'akin nasa kallo, tanemi waje ta zauna a gefen gadon, itama Insaaf din zama tayi agefenta tana sakin hamma Ishraqa takama kunnanta tariqe tace "ke!" Cikin sauri tasa hannunta awajan tace "Anty akwai zafi Allah" Bata saki kunnan nataba tace "inake ina bacci mijin ki yana fita aiki sassafe?" "Anty wallahi nadena" Sakin kunnan tayi ta kalleta tace "Haba Insaaf, kirufamin asiri mana Karki bani kunya awajan Asim, nagama cika masa baki zai samu kulawa awajan ki amma gashi tun ba'aje ko'inaba Harkin fara rabuwa dashi, to Asim daban yake da sauran mazajen ki, da ilminsa, kuma kullum fita yake Yana haduwa da wasu matan, in kuma kofa kika budewa kishiyar ki to.... " Cikin sauri ta katse ta tace"Anty wacce irin kishiya kuma?" "Insaaf kishiya de dakika sani, bakya son kishiya zaki kwanta kina bacci?, haba Insaaf, ina abubuwan dana fada miki? To inzaki ware ki ware, kinji nafada miki" "to Anty inde share share ne zanyi" "ba share share kadai ba Insaaf, kidinga Jan mijin ki ajikin ki, kina bashi kulawa, ta hakane zai manta da kowacce mace ai" "nifa kunyar sa nakeji Anty, yanamin kwarjini, kuma harga Allah banaso yamutu, Allah idan yamutu bansan Yaya zanyi ba" Hannunta taruqo tace "Insaaf...., ai mungama da wannan matsalar insha Allah, menene amfanin magungunan da baban ki yakarbo miki? Kidena jin tsoron sa, kiyi masa duk abinda ki kasan zaki samu Lada, ga qananun kayan ki nan, jiya nasiyo miki su, dakuma sauran kayaiyakin ki" Kayan tajanyo tafara dubawa, kaya ne qananu masu nuna surar jikin mutum tace "Anty wannan kayan ai sunyi qananu dayawa kuma....." "to 'yar qauye, Karki saka, ki ajiyesu adaki, wannan wayar dayake yawan danne danne aciki,daya hadu da wata inta liqe masa shikkenan, idan kika masa magana saide kiji Yana cewa ya ina lissafi kina dawo dani baya?" "a a wallahi....Allah idan ya kula wata sainayi fishi dashi" Ishraqa ta kalleta, tana ihu batason Asim amma kuma Sai kishin sa take, to bazata qara magana ba, tsakanin mata da miji Sai Allah, tunda tace fishi ba tasan me zatayi masa ba, su suka sani Tashi tayi tace "to nikam natafi gidana, amma Dan Allah inga sauyi daga yau Insaaf" "to Anty, muje narakaki" "a a, yi zamanki, nagode Sai anjima" Daga nan tafita daga d'akin tajawa Minal kofar Dawowa tayi tazauna tafara tunani, to yanzu ta ina zata fara? Yanzu Anty data kawo mata wannan kayan tayaya zata sakasu a gidannan ta zauna dasu? Ajiyar zuciya tayi, tatashi taduba cikin kayanta ta dauko wani dogon hijabi, ta ajiye agefe, kayan nata tafara dubawa duk qananu ne, yanzu wannan kayan zata saka kuma ta zauna Yaya Yaganta ahaka? Anya? Mayardasu tayi ta ajiye sannan tafara gyara d'akin, tashiga toilet nanma ta gyara shi Tafuto tasaka turaren wuta ko'ina ya dauki qamshi, sannan tashiga tayi wanka, ta shirya cikin riga da sket, kayan sunyi mata kyau sosai, tafuto falo tazuba abinci taci Dakin Amrah Takoma, suna fira, Amrah ta karbi wayarta taga duk babu wasu abubuwan na amfani aciki, tace "Minal yanaga ko Dan whtaspp dinnan bakya yi?" "to dawa zanyi Anty Amrah? Nida ba qawaye ba? Kece kuma gakinan agida ina ganinki" "kamarya ni? Mijin naki fa?kawo kiga na Bude miki, zan turawa qawaye na number ki suyi adding dinki a group na matan aure,zaki sake sanin wasu abubuwan" "to Anty Amrah gashi'' Amrah ta karba tabude mata, number Yaya Asim taduba taga tasa Yaya, ta kalleta tace" lalle ma, harda wani Yaya, ina laifin ma kisa masa wani sunan, haba Minal kamar ba 'yar zamani ba? " " to ai Gara ni inada number tasa, may be ma shi bashida tawa " " to baki ki rashi ba tayaya zai samu number ki? Kinga gashinan online karbi kitura masa txt kice kina missing dinsa yadawo gida da wuri " Dariya tayi tace"tab, Yaya Asim din? Kawai saboda nace ina missing dinsa saiya bar aikinsa yataho wajena? Shida yakeda jarabar aikin nan" "kina mamaki kenan? Minal yayafa Yana sonki, amma ki gwada kigani" Wayar ta karba tatura masa sallama, sannan tafara typing "Yaya ya aiki, yaushe zaka dawo..." Amrah ta kalli wayar tace "goge wannan, ba gwada shi zakiyi ba? Ai kalamai zaki tura masa" Tace "wahalar banza kawai zansha Anty Amrah" "bawani wahala gwada, Dan gulma kunason juna kun tsaya Sai wani abu kuke kamar 'ya'yan fari, koda yake ashefa 'yan farinne dagake harshi" πŸ˜‚ Murmushi tayi tace "yayan ki nefa" "to ganina yake?, idan a gabansa ne na'isa nayi?, kutura masa Dan Allah, yanzu haka dawasu yake magana kintsaya kina wasa da damarki" Cikin sauri tace "haba?" Amrah ta kalli idonta tayi murmushi tace "kitura masa cewa Yaya kewarka tamin yawa tunda katafi dasafe nake tinaninka yaushe zaka dawo naganka?" Zaro idonta tayi tace "kaiiii Anty Amrah, nida yafita yabar ni inata bacci, wallahi babu ruwana nikam" Amrah ce ta qwace wayar tatura masa Alokacin Yana office dinsa kishingide acikin kujera, datar ce abude, amma baya kan whtaspp, text din daya shigo masa da wata number ne yadauki Hankalinsa, ya karanta yasake karanta wa, cikin sauri ya hau kan whatsapp dinsa, tunani yafara waye zai turo masa wannan txt din? Wata zuciyar ta bashi amsa da Insaaf Murmushi yasaki har dimple dinsa Yana lotsawa, yasaka hannu yashafi sumar kansa, kode itama tafara sonsa ne? Wayar yasaka cikin aljihun Wandon sa ya tashi yafara tattara kayan sa zaibar office din Agogon office din ya kalla yaga shabiyu saura, ya dafe kansa da hannunsa, karfa yarinyar nan ta zautar dashi, daga turo masa txt ya tashi yabita, afili yace "tunda tanason ganina menene amfanin zama na anan?" Hanyar fita daga office din yanufa saiya tuno da mamy, jinjina kansa yayi yace "Kar mamy tace saboda Insaaf nadawo gida" Cikin zuciyarsa yace to ai kuma tasan ina son matata Dawowa yayi yazauna afili yace "bari de ayi sallar azahar saina tafi" Acan gidansu kuwa daga ita har Amrah dasuka ji Shiru kawai Sai suka haqura, ta kalli Amrah tace "kingani ai" "Mena gani? Kin tsaya Kinga bezo bane?" Tace "to, nikam bari natafi daki akwai kayan dazan qara shiryawa" "to saikin dawo" cewar Amrah Harta gama qarasa shirya kayanta, tayi sallar azahar, har biyu da wani abu tana zaune da carbi ahannuta tana ja, Addu'ah tayi tatashi taje tasake wanka, tabade jikinta da turare,taduba kayan da Ishraqa ta kawo mata ta dauki wani riga da sket masu kyau tasaka, siket din saura kadan ya qaraso mata gwiwa, rigar kuma Normal riga ce amma an yanke gaban rigar anyi wani round agabanta, kana ganin komai Dan kunneta tasaka, sannan ta dauki qaton hijabinta zata saka taji an turo kofar d'akin, mamaki ya kamata, amma saitayi tunanin Amrah ce, ganinsa acikin d'akin ne yasa gabanta yafadi, shaf Tama manta da batun text data tura masa, saita fara tambayar kanta menene yakawo shi gida yanzu? Shikuwa Asim mutuwar tsaye yayi a bakin kofar, gaba daya yarinyar tagama tafiya da tunanin sa Hijabin tafara dagawa zata saka amma data tuno yanda Ishraqa tabata shawara saita ajiye shi Akan gadon ta nufeshi tace "sannu da zuwa Yaya" Hannunsa ya miqa mata, babu Musa tasaka nata hannun, cikin sauri ya fuzgota jikinsa tare da sakin wata irin Ajiyar zuciya, hancinsa ne yake yawo a jikinta, duk wani waje dayaji Yana tashin qamshi a jikinta saida yakai hancinsa wajan, yadawo da hancinsa dede wuyanta yasakar mata wani irin kiss, sannan yace "miss you too Baby...." Wani iri taji, bayan mamaki daya kamata, kenan dawowarsa tanada nasaba da tetx din dasuka tura masa?kode da gaske Amrah take Yaya Asim Yana sonta? Bata San dalili ba, haka nan taji wani irin farin-ciki ya kamata, cikin sigar shagwaba tace"yaya wajan mamy fa zanje " Daukarta yayi cimak, yazauna Akan gado ita kuma yadora ta Akan cinyar sa, kansa yadora a wuyanta yace" wacce Mamy? Bayan kince kina missing Dina nadawo gida? " " Yaya nifa dama.... Dama...." " shiiiii"🀫ya katse ta Sannan yace "wato bakya kewata ko?" Girgiza kanta tayi, tace "ina...yi " "to nunamin" Kallansa tayi tace "me?" "kewata mana, ba gashi kinsa nabar aikina nadawo wajanki ba?" Shiru tayi, tadago kanta ta kalleshi ma takasa, kwarjini yake mata sosai, gashi Yana tayi mata abubuwa kamar ba Shiba Tunanin tane ya tsaya cak, samakon jin hannunsa a inda Bata zata ba, budaddiyar rigarta ya qarasa zuge mata zip din rigar, lokaci daya rigar tayi qasa, wata irin kunya ta kamata, cikin sauri tarufe idonta da tafin hannunta, tasake fadawa cikin jikinsa Murmushi yayi, yadora fuskarsa Akan Tata, yayinda hannunsa yake yawo Akan qirjinta, wani irin yanayi ya tsinci kansa aciki, kwata kwata ya manta da yarinyar dayake rainawa yake tare, al'amarin nasa bai tsaya iya nanba, saida yasamu nasarar hade bakin su waje daya, yanda yake shan bakinta da zafi zafi shine ya tabbatar mata cewa haqiqa yayi kewar matarsa, kokarin janye jikinta tafara, yayi sauri yasake ruqota, yaci gaba da abinda yake, yarasa meyasa take masa noqe-noqe kamar ba tasan komai ba, kunyarta tayi yawa, tayaya kin auri maza kusan shida amma kikasa bada hadin kai lokaci daya? Kwata kwata tunanin sa ya gushe, baisan Yaya akai ba,shide ya tsincesu Akan gado,lafiyarsa kalau yashigo gidan, amma Sai yaji lokaci daya kansa yasara kamar wanda aka buga masa wani abu, amma bai kawo komai a ransa ba,boobs dinta dake cikin hannunsa ya matsa, cikin wata irin murya yace "Baby nawane ko?" "uhmm... Yaya ni Dan Allah kabari" Zuciyarta daya tafadi wannan maganar, ba tasan shagwa6ar datayi masa sake tunzurashi tayi ba Murmushi yayi, yayi kissing goshin ta, da idanunsa dake cike da buqata ya kalleta yace "bansan meyasa ba, inaji kaina yanamin wani irin ciwo" Tace "Yaya ai akwai magani" tafadi haka batare data kalleshi ba "ai kece maganin" Murmushi tayi takauda kanta gefe, yace "inaso inyi wanka,ko zaki rakani?" Idanunta tarufe cike da kunya tace "a a" Hancinta ya lakace mata, sannan yafara gyara mata rigar Tata, amma yaqi yarufe mata bayan, daqyar ya'iya Raba hannunsa da qirjinta da suke mata wani irin zafi, sannan yashige toilet domin watsa ruwa Washe Gari cewa yayi bazai je office ba, haka tazauna adakin nasa tana kokarin sakin jikinta dashi, kamar yanda yafada mata batada wajan zama Sai jikinsa hakan ce ta kasance, saide wuni guda yad'auka Yana sake alwala, da yayi sabuwa zata karye, tashiga wanka kenan ya dauki waya yakira Muhsin, bayan sun gaisa Muhsin yace "Ango mijin Amarya, ya aiki?" "banje office ba yau, ina gida ne" Dariya Muhsin yayi yace "tab, amma Insaaf tanada sa'ah, gaskiya kana kokarin tausayin yarinyar nan" Murmushi yayi "Muhsin ai wannan yawuce tausayi, saide so" "Okey, yanzu kadawo kan hanya kenan?" "dama na Dade da dawowa" "Alhamdulillahi, gaskiya naji dadi Asim, Allah kuma yakawo qannan widad da wuri" "qanne kuma tun yanzu?" "tome zaka jira? Ai lokacin abu ayishi" Dariya yayi yace "kaide bakada dama" Muhsin yace "gaskiya ne, gobe idan kafuto office akwai wani laqani dazan baka, zakasha mamaki na" "wanne irin laqani kuma Muhsin?" "kaida muhadu goben" "no, bawani gobe Malam, kazo ina gida ka kawo min yanzu, kuma ka fadamin na menene" "to shikkenan ganinan zuwa" Ko 30 mint basu yi ba, yazo gidan,Asim yafuto compound din gidan yace "wanne irin laqani ne zaka Bani? Kona soyaiya ne? Kasan har yanzu fa ban tabbatar tana sona ba" Muhsin yayi murmushi yace "bawani laqanin soyaiya, Kaine zaka koya mata soyaiyar, wannan maganin, idan kasha, Kaine zaka ban labari, maganin maza ne, kasan de yarinyar nan kaida kanka kace aurenta shida, kasan kuwa me iya mata Sai Allah"😳 Girgiza kansa yayi yace "A a Muhsin, yanzu a yanda nake sainasha wani magani? ai banda matsalar komai, ni ahakan ma ina tausayin tane" "tausayi kuma? To Kar take kallon ka, tasan komai kamar yanda kaima kasani, wallahi idan kaje mata, taji Bata gamsu ba, raina ka zatayi, qarshe ma tace tsohuwar matarka tagama janye ka, kuma kasan Ana musu Dan gyare-gyaren jiki, kawai Malam kafuto a mutum musamu qananun Yara " Shiru yayi, Sai can yace" kuma fa hakane, maganar ka tana kan gaskiya Muhsin, bani maganin " Muhsin yabashi, ya karba yace" godia nake abokina " Suka tafa, Sai dariya suke kamar basu ba, sannan yayi masa sallama yakoma ciki Yana zuwa falon sa yabude fridge ya dauki ruwa yasha magani,πŸ˜‚ sannan yawuce cikin daki, alokacin harta futo daga wanka tana shiryawa Kai tsaye toilet din yashige domin ya watsa ruwa, yakusa gama wankan yaji yanayin sa Yana sauyawa, cikin ransa yace ashe maganin nan Yanada kyau sosai Futowa yayi qugunsa daure da Towel Tana ganin futowar sa tatashi ta dauko masa kayan sakawa, kawo masa tayi ta ajiye agefen gadon Binta yayi dawani irin mayen kallo, wata irin sha'awa tana taso masa, wadda tunda yake, baitaba jin makamanciyar taba, lips dinsa yasa a baki ya ciza, sannan ya sunkuya yariqe gwiwar sa kamar mai ruku'u Kallansa tayi da mamaki tace "Yaya lafiya?" Girgiza kansa yayi yace "ba kalau ba.... Bazaki gane bane...." Matsowa tayi kusa dashi tace "bakada lafiya ko?" Yace "sosai....inaji kamar.... Kamar na mutu..." Gabanta ne yafadi, tace "mutuwa Yaya?"😳 Wani irin kallo yabita dashi, Sai lashe lips dinsa yake, yasaka hannu ya fusgota jikinsa, tana jin yanda Towel din jikinsa ya kunce tayi sauri ya rufe idonta Gaba daya jikinsa rawa yake, sosai ta tsorata da yanayin sa, mutum yashigo kalau amma lokaci daya yafita a hayyacinsa? Bai iya cire mata rigar jikinta ba, hannu kawai yasa ya yagata, soyaiya yafara nuna mata a zafafe, yanajin yanda take ture hannunsa daga jikinta, yahada gaba daya hannayen nata yariqe Cikin fitar hayyaci yace "meyasa kike min haka ne?" Kallansa take cike da tsoro, duk abinda yake yi faruwa taqi yarda ta kalli jikinsa, Girgiza kanta tayi tace "Yaya....wai meyake damunka?" Kallanta yayi da rinannun idanunsa,jiyake lokaci daya kansa yana ciwo, tsakiyar kansa kamar Ana doka masa guduma haka yake ji, amma bala'in dayake ji a jikinsa yahana ya qyaleta tsoro yasake kamata, cikin fitar hayyaci yae"kece....kibani haqqi na " Gabantane yayi wata irin muguwar faduwa, lokaci daya mutuwar mazajen ta tafado mata, tsoro ya kamata, duk da tanashan magani tana jin tsoro, gani take kamar Shima zai tafi yabarta, koba wannan Bama ai bazai iyu ba, saboda yanayin datake ciki, gakuma su Mami Cikin wani irin zulumi tace masa "Yaya ai inada period..." ✍🏻 Mrs. Usman [2/27, 7:24 AM] El~Yaqoub: INSAAF Writing by:Amnah El yaqoub 43&44 Like my page on Facebook πŸ‘‡πŸ» https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 Zaro Idonsa yayi 😳😳 Ya kalleta yace "innalillahi, Muhsin kakashe ni" Sai yanzu ne tasake tabbatar wa akwai abinda suka qulla shida abokin nasa, tace "Muhsin kuma? Meya yi ma Yaya...?" Kafin ta qarasa magana yasake fuzgota jikinsa, lokaci daya yahade bakin su waje daya, ganin tsayuwar bazata musu ba yasa yadauke ta cak suka fada kan gado Yanda yake bida'ita cikin zafi-zafi yasa tafara jin dadin abinda yake mata, amma da akai Nisa taga abin nasa yawuce na hankali anan idonta yafara raina fata Tafada masa tana period amma taga kamar ma baiji abinda tafada masa ba,gaba daya yafice daga haiyacinsa, hannu biyu tafara dukansa amma ko kadan Asim bai jinta,ciwon da kansa yake masa ma yanaji amma a halin dayake ciki yanzu bazai iya hakura ba, gashi yahade bakin su waje daya, Sai mutsu mutsu take tana neman agaji Bai qyale taba saida ya tabbatar yabiya wa kansa buqata ta cinyar ta, amma abin mamakin jiyayi kamar ma yanzu yafara, wani irin Karfi ne yasake zuwa masa, baisan lokacin daya fashe dawani irin kuka ba, ya kamata ya qanqame ta, cikin ransa kuwa Allah ya'isa kawai yake aikawa Muhsin Idanunta sha6e-sha6e da hawaye tace "Yaya Dan Allah kayi hakuri..." Kallanta yayi amma yakasa magana, yarasa hakurin me take bashi, tanaso tace masa batasan komai bane kome? Tayaya za'ai mace bazawara tazauna tana masa wannan kukan? Meyake damun tane? Cikin wata irin murya yace "kiramun Amjad" Kamar dama jira take cikin sauri tatashi daga jikinsa, saida ta tsaya taga yanda jikinta yake, babu kaya ko daya, takai dubanta gare shi taga ya zuba mata ido kamar tsohon maye, wardrobe tabude ta dauki dogon zani ta daura, sannan ta saka qaton hijab tafi ta daga d'akin Tana fita taga Amrah zaune afalo, cikin tashin hankali tace "Lafiya Minal? Meya sameki kike kuka?" Ahankali ta girgiza kanta tace "Wai Yaya Amjad yazo injishi" 😭 Dariya ce takama Amrah, amma batayi ba, saboda babu dadi yanda take kukan nan kuma kakama yiwa mutum dariya, dafa kafadarta tayi tace "toki koma bari in turo muku shi" Babu musu tajuya zuwa ciki, Amrah kuma tashige d'akin Amjad, tana shiga ta ganshi daure da towel yafuto daga wanka, saita ga kamar ba Amjad ba kullum qara girma yake, suna hada Ido tace "kaje inji Yaya" Tayi sauri taja masa kofar tabar wajan Minal kuwa tana zuwa d'akin taga yasaka jallabiya, yana zaune agefen gadon, amma kansa Yana qasa, wajansa ta qarasa tace "Yaya Wai gashinan" Baibata amsa ba Sai hannunsa,daya miqa mata, babu musu ta qarasa wajansa,janyota yayi yasaka ta a jikinsa, yasaka hannunsa duka biyun ya qanqameta, Sai wani irin numfashi yake saukewa, ta cikin hijabin nata ya zura hannunsa Yana wasa da qirjinta, ita kuma zafi take ji, Sai runtse ido takeyi, mamakin sa take yanda baya gajiya da wannan abun, qwanqwasa d'akin akayi, cikin sauri tafara janye hannunsa dake kan qirjinta, amma saiya sake riqewa, Sai tura kansa yake cikin wuyanta, cikin rawar murya tace "Yaya Ana nocking.... fa" Cikin wata irin murya yace "Insaaf....ki barni.... Ki naso na mutu ko? " Cikin sauri tafara girgiza kanta "a a Yaya, banaso ka mutu, idan ka mutu zanshiga cikin wani hali" Kallanta yayi furucin ta yabashi mamaki, kokarin hade bakin su yake yi amma Sai aka sake wani nocking din Maimakon ya tashi saiya fara kokarin shigewa cikin hijab din nata, kuka tasaka masa, Ahankali yace mata "sorry..." Sannan ya tashi tsaye, tana Kallan yanayin dayake ciki tayi sauri ta sunkuyar da kanta, shi kansa jiyayi mararsa tana masa wani irin ciwo, cikin sauri ya sunkuya, adaddafe yabude kofar, Yana ganin Amjad yace "mutafi Asbiti Amjad" Cikin tashin hankali yace "innalillahi... Yaya Asim? Meyasameka kake tafiya a sunkuye?" 🀣 Bai iya Bawa Amjad amsa ba, Sai wucewa da yayi,suna zuwa main falo Amjad yajuya yace "bari nakira mamy" Cikin sauri yayi caraf yaruqo hannunsa, ya girgiza masa kai alamun a a, Amjad de yayi Shiru mamaki duk yagama kashe shi, haka yasa hannu yaruqo kafadar yayan nasa, suka futo daga falon acikin wannan halin yafita compound, maigadi damai wanke motocin gidan suna ganinsu suka qaraso suna tambaya "Yallabai lafiya kuwa?" Amjad ne yasamu sukunin basu amsa, daga nan suka musu Addu'ah, suka juya, shikuma Amjad yayi sauri ya6ude masa Mota yashiga, sannan Shima ya Zagaya yatada motar suka bar gidan Acikin motar ma Sai hada uban gumi yake, yadora kansa ajikin glass din window, Ajima kadan Amjad yadubeshi yayi masa sannu, da haka suka qarasa wani private hospital Acan asbitin ma Asim qin dagowa yayi, haka yake tafiya a sunkunye Yana runste ido, duk taku daya da zaiyi zagin Muhsin yake acikin ransa πŸ˜‚ Kai tsaye wajan likita suka nufa, saida yabawa Amjad baya sannan ya'iya miqewa, likita kuwa Yana ganin yanayin sa yafara salati, anan ya hada allurai masu qarfi yayi masa, ciki harda na bacci, yabashi gado ya kwanta, ya dauki babban blanket yarufe shi saboda yaga kamar Yana 6oyewa qanin nasa halin dayake ciki Ko minti goma bai qara ba, bacci yayi awun gaba dashi, kusan awarsa uku Yana bacci, sannan yafarka, cikin ikon Allah kuwa saiya jishi kalau, yasaka hannu ya shafa jikinsa yaji komai normal, sannan yayi hamdala ga Allah Yana Juyawa gefensa yaga Amjad a zaune, yazuba ido Yana kallon saman d'akin Mamaki ya kama Asim, toshi wannan Yaron menene yake damunsa haka Gyaran murya yayi yace "Amjad" Firgigit yayi yadawo daga duniyar tunanin dayake ciki yace "na'am Yaya" Kai tsaye yace "kiramin Muhsin da wayar ka" πŸ˜‚πŸ˜‚ Amjad ya kalleshi, Yana mamaki, daga tashin sa daga jinya Yana neman abokin sa, beyi musu ba yakira shi, tana shiga kuwa Muhsin yad'auka, Asim yace "Ashe bakada mutunci Muhsin?" Muhsin yayi dariya yace "A a, ango, ashe Kaine, Toya Bayani? dafatan de an wuce wajan kaji Dadin maganin" "dalla Malam wanne irin jin dadi, Kasa ni acikin halin ha'ula'i, yanzu haka ina Asbiti" "subhanallah... Asbiti Asim? to magani beyi aiki ba, tunda itace takai ka asbiti ba Kaine kakaita ba" "Muhsin ka cuceni, yanzu inda ace yarinyar nan kalau take haka kakeso naje? Kashe yar mutane kakeso nayi?" Amjad ya kalli yayan nasa ta qasan ido, Sai yanzu yagane inda jinyar Yaya Asim din ta dosa,dariya ce ta kamashi, ya kawar da kansa gefe ya Dara πŸ˜ƒ Muhsin yace"tooo, yanzu kam na Fahimci inda zancen ka yadosa,...." ya kwashe da dariya, sannan yaci gaba da cewa" tabdi, kace akwai qura, kuma ya kayi Asim? " " bansani ba "qit yakashe wayar sa, yajuya zai Bawa Amjad wayar Sai yaga fuskar Amjad agefe da alamu ma dariya yake masa, daure fuska yayi yace" kai miye haka?"😠 Amjad ya nutsu, Ahankali yace"sorry Yaya" "kiramin likita, yazo ya sallame ni gida zamu tafi" Bayan yakira likitan ko awa daya basu qara ba suka bar asbitin, suna tafiya a hanya Amjad ya kalleshi yace "Yaya, dama inaso zamuyi wata magana" Asim yayi tunanin maganar ta shafi jinyar tasa, saiya sake dauke kansa yace "ina jinka" "Akan Anty Amrah ne" Sai alokacin ya kalleshi yace "meyake faruwa?" "Yaya wallahi I love her so much...." Asim ya d'aga girarsa guda daya Yana kallon Amjad, Shima Amjad din daya kalleshi saiya sake samun qwarin gwiwar Ci gaba da magana "Yaya inajin tsoron tane, bansan Yaya zata kalli al'amarin ba, amma nide gaskiya ina sonta" Asim yace "babu damuwa, Bari muje gidan" Cikin sanyin jiki yace "to Yaya" Suna qarasawa gida maigadi da suke zaune a bakin gate suna Dan taba hira, suka taso da gudu suna masa sannu, cikin kwanciyar hankali ya amsa musu sannan suka shige ciki, Kai tsaye d'akin mamy sukaje Mamy na ganinsu tace "Daga ina kuke?" Asim ya shafa sumar kansa, Amjad na ganin haka yayi sauri yace "daga unguwa mamy" Ta kalli Asim daga Sama har qasa tace "kuma unguwa da jallabiya?" Murmushi sukai gaba dayansu, sannan suka nemi waje suka zauna, tace "kode akwai wani abu ne?" Asim yace "mamy Autanki ne yasamu matar aure" Lokaci daya farin ciki ya kama mamy tace "Alhamdulillahi, Allah abun godia, wacece?" Kai tsaye Asim yace "Amrah" πŸ˜… Fuskar mamy saita tashi daga yanayin farin-ciki zuwa yanayin mamaki tace "wakace?" Asim kuwa yasake cewa "Amrah, Amrah de taki ta gidan nan" Mamy tasaki Ajiyar zuciya tace "tooo..... Ikon Allah, to Asim da'ace wanine yafadamin wannan maganar bazan yarda ba, amma dayake Kaine da kanka, yanzu na yarda, yanzu kai Asim da hankalinka da komai shine Amjad zai sakoka agaba kazo kanamin wannan maganar? Asim harka manta da yaqin da sukeyi? Saboda masifar Amjad da Amrah tafi qarfin fad'a saide muce yaqi, wataran gidansu kamawa zaiyi da wuta, Dan haka bada niba " Asim yayi murmushi, Amjad kuwa yanayin fuskar sane ya sauya zuwa shagwaba, yace" mamy Allah nide nadena, dama ai komai ma duk laifin tane, saita dinga cemin yaro " "to Kaine kullum saika dinga nuna mata kai Yaron ne, komai shagwaba, komai shagwa6a badole tacema Yaro ba" cewar Asim Mamy tasaki baki tana kallonsu tace "Okey dama Kaine kake zigashi kenan, to Yana Dan autana idan beyi shagwaba ba qarfe kakeso yakoma dagawa kamar kai?" Asim yace "to yaci gaba mamy, wataran idan yaje zance wajan wata ya kama yimata wannan shagwa6ar wallahi saita kifa masa mari" Mamy tace "naji, yayi abarsa, lokaci be, wataran ai bazai yiba" Kallanta yayi Shima cikin shagwa6ar de yace "A a mamy nikam nadena" πŸ˜‚ Tace "Okey kunyatani zakayi kenan? To ai shikkenan, inde nice na haifi Amrah, nabaka ita Amjad, amma da sharadi daya, idan ta amince, kaje ka sameta duk yanda kukai inde ta amince din, Toni banida damuwa" Yanajin haka yasaki wani irin ihun murna ya rungume Asim, sannan yace "Angama mamy" yafice da gudu daga d'akin Asim yabishi da kallo ya nuna shi da hannu yace "kingani ai, Kinga irinta ko?" Mamy tayi dariya tace "kai jama'ah, Dan Allah Asim kabarmin yaronnan ya wataya, haba" Kansa ya shafa yace "to shikkenan mamy, Allah ya tabbatar da Alkhairi" Murmushi tayi tace "Amin" Daga nan yafuto daga d'akin nata Falon nasu yashigo hannunsa dauke da ledoji niqi-niqi, Kai tsaye d'akin ta yashiga, tana karatun novel Sai ganinsa tayi yashigo d'akin nata,ledojin ya ajiye mata agabanta, sannan ya zauna Akan gadon Yana fuskantar ta, tafin kafarta ya kalla, Ahankali yakai hannunsa ya shafa, 6ata fuska tayi tace "miye hakan kuma?" Wani irin kallo yazuba mata mai karya garkuwar jikin yanmata, sannan yace "naganta ne fes kamar yanda kike komai naki fes fes" Idanuwanta tajuya πŸ™„tace "too yau kuma da salon da kazo kenan" Murmushi yayi yace "A a, tana birgeni ne, ko zaki shirya muje ayi miki qunshi, zaiyi miki kyau wallahi tunda bakyayi sosai, Kinga yatsun kafarki ma idan aka miki wani irin kyau suke" ya qarasa maganar Yana dora hannunsa Akan yatsun kafarta Tsaki taja ta qwace qafarta tace "Amjad, menene yakawo ka? Banason wannan kwane kwanen dakake" "nikuwa Anty Amrah menene zai kawoni wajanki banda zumunci? Kinga kaza ce nasiyo miki da ice-cream, nasan zakiji da dinsu" ya qarasa maganar yana turo mata ledar gabanta Cikin sauri tafara Bude ledar tace "Allah Amjad? Allah sarki dan'uwa Rabin jiki, kace yau bazanci abincin gidannan ba" Yace "koh?" Tace "eh mana" "idan kina so ai kullum zan dinga siyomiki nikam" Kallansa tayi tace "Amjad Anya kuwa Kaine?" "nine mana, mekika gani?" "kawai gani nayi kamar bakai ba" "toki daina wannan tunanin, kinsan kuwa yanda nake bala'in qaunarki?" Naman kazar ta dauka takai bakinta tace "Allah sarki Amjad, toka sa hannu mana muci" πŸ˜‚ "saide... Ki bani.... A baki.. na..." Ya qarasa maganar a rarrabe Harararsa tayi tace "karkaci" Cikin shagwaba yace "uhm.. Allah kibani, toba nine nasiyo ba" Kallan sa tayi tace "nace gashinan Kaci, ka tsaya kanamin wani fi'ili, toka zauna kajira Dan Allah" Tana gama fada masa haka tasaki Jan kazar gabanta tanaci hankali kwance, kallonta yayi, ya yi qasa sa murya yace "Anty Amrah" "ina jinka Amjad" "zaki iya auren qaninki?" Wani irin murmushi tayi tace "abin dariya wallahi, Wai Yaro ya tsinci haqori, to Amjad kaida kanka mafa cewa kayi qanina, to ta Yaya zan iya auren sa? In rasa wazan aura Sai qanina? To ai bari kaji, ko Kaine dakayi tsawon qafa harka Fini tsawo, bazan iya auren kaba, saboda auren yarannan yan Ashirin da biyar da shida duk shirme ne, dayawa daga cikin su mafa ba'a gama musu tsawa ba, tayaya zasu tsawatar dani? " Wani irin baqin ciki ya kama Amjad, babu maganar da tafi masa ciwo irin yanda tace dayawa daga cikin su ba'a gama musu tsawa ba, Wai me Amrah ta dauki kanta ne? Ajiyar zuciya yayi, ya kalleta Sai cin namanta take tana gasa masa magana hankalin ta kwance, yace"mudena maganar wasa Amrah, da gaske, inason ki, inaso kibani dama na aure ki " Wani naman ta dauko zataci, amma jin wannan furucin nasa yasa ta tsaya cak, saita yi wani saroro tana kallonsa, aduniya Amjad bai taba cimata mutunci irin na yauba, wato ya matse ta yayi kissing dinta, shine yanzu zaizo mata da wannan maganar, kawai saita zuba masa ido tana kallonsa, gaba daya mamakin sa yagama kamata, tarasa mema zata masa tahuce, kawai Sai tayi jifa da naman tafashe dawani irin kuka, sosai take kuka, ta kifa kanta Akan cinyar ta, haqiqa yau Amjad ya cuceta, yagama ganin gadon baccinta Ganin yanda take kuka sosai Sai jikinsa yayi sanyi, ahankli ya tashi tsaye yace "kiyi hakuri idan magana ta ta 6ata miki rai, amma Ban taba tunanin zaki iya gudunaba Amrah, hakan yana nufin karnaji haushi idan wata bare ta nuna Bata sona, tunda kema yar'uwa ta kin qini, but I am sorry, bazan iya Hana zuciyata kaunar ki ba Amrah" Yana fadar haka yafice daga d'akin Yau bai fita wajan aiki ba, Yana kwance agado amma computer ce agabansa Yana search, futowa tayi daga toilet, tana sanye cikin riga da wando, kayan sun kamata sosai, amma ba qaramin kyau sukai mata ba, wuce shi tazo tayi ta qarasa gaban mirror takama gashin kanta tana daurewa, da kallo yabita, shaf ya manta akwai abinda yake yi a computer Wata doguwar riga ta dora sannan ta zura hijab dinta tatada kabbarar sallah Wani irin farin-ciki ya kama zuciyar Asim, hakan yana nufin tayi wankan tsarki kenan, Yana aikin kallonta harta idar, sannan yace "Baby na zokiga wani abu" Murmushi tayi tace "to Yaya" ta qaraso wajansa Cikin sauri yace "Dan cire wannan hijabin please" Babu musu ta cireshi, tana qaraso wa yajanyota jikinsa, sannan ya tura mata computer gabanta, tana gani tace "Wow, gaskiya akwatunan nan sunyi kyau sosai Yaya" Lips dinta ya kalla, Ahankali yakai hannunsa yafara shafawa yace "da gaske?" Bata iya bashi amsa ba, kawai kanta ta daga masa Murmushi yayi, yamatso da fuskar sa kan Tata fuskar yace "ai naki ne" Cikin sauri tace "haba?" Murmushi yayi, yarintar yarinyar tana birgeshi, ya Dage ya nuna mata kayanta amma ahakan sake tabbatar wa takeson yi, shine saita sashi ya rantse Yace "nakine, sun kusa qaraso wa wajanki insha Allah" "nagode Yaya" Kallanta idonta yayi, yayi qasa da murya yace "wannan ne kawai tukwici na?" Dago manyan idonta tayi ta kalleshi, suna hada ido tayi sauri tayi qasa sa idonta tace "tome kakeso?" Acikin kunnanta ya rada mata "your lips" Cikin kunya ta rufe idonta, yayi murmushi yace "shikkenan, bani labarin samarinki" "ni banda Samari ai, Sai mutum daya, Haruna Dan kande, shine yake sona sosai, kuma yarasu" "sorry, Allah yaji qansa, amma meyasa zakice shine sonki sosai? Bakisan akwai wanda ya fishi sonki ba?" Cikin mamaki tace "waye?" Kai tsaye yace "gani, I luv you so much Insaaf, kifada wa Mamanki tayi nasara akaina, wannan manyan idanun naki, da wannan dogon gashin naki, sunsa nafada cikin soyaiyarki, wadda ban shirya mata ba" Yaqarasa maganar Yana shafa saman idonta, wani irin dadi taji ya ratsa cikin zuciyarta, ahankli ta lumshe idonta, hakanne yabashi Damar cigaba da shafa saman fuskarta, daga qarshe yadora bakinsa Akan nata Yayi mamakin yanda ta bashi hadin kai wajan kissing dinta, cikin nutsuwa yake aiwatar da komai Itama anata bangaren tanajin Dadin yanda yake kissing din nata Ahankali, ba tasan lokacin data ruqo kansa ba, hakan data masa yayi masa dadi sosai, hannunsa ne yafara yawo a jikinta, al'amarin daya dauke su kusan minti talatin suna abu daya, awannan lokacin da gashi har ita, sunyi sallama da kayan jikinsu, shine yayi kokarin jan blanket ya rufesu dashi, cikin bargon yasaka kansa Yana yi mata wani irin wasa mai wuyar fassarawa, lokaci daya yaji kansa yasara, irin ciwon kan da yaji rannan shine yanzunma yasake ji, Abin yabashi mamaki sosai, amma saiya fara Addu'ah acikin zuciyarsa Bakinsa yadora Akan boobs dinta yanasha, yayinda Hankalinsa yayi gaba, tunanin sa yabar jikinsa, baya fata da burin samun komai Sai Raya sunnar ma'aiki tare da matarsa, acikin wannan halin yafara neman hanya, amma abinda yabashi mamaki Sai yaji kofa arufe, salati yafara yi acikinsa ransa, dama Insaaf budurwa ce kome? Yanaso ya tabbatar, yanaso yau yasan komai dangane da yarinyar, wani irin qarfi yaji yazo masa, babu alamun tausayi yasake cigaba da neman hanya, lokaci daya yaji anyi wani irin wulli dashi har saida yaje qarshan gadon 😳 Gabansa yayi wata irin faduwa, amma bai saka tsoro acikin ransa ba, ya kalleta yaga de tabbas ita kadai ce, cikin karfin hali yasake fuzgota jikinsa, wannan Karon tun kafin yafara neman hanya yaji an shaqe masa wuyansa, tuni yasake ta yasaka hannunsa duka biyun Akan wuyansa, Yana daga kansa Sama yaga d'akin nasu Yana wani irin Juyawa, daqyar yasamu numfashinsa yadawo daidai, lokaci daya yafara Tari, numfashinsa Yana Sama Sama kamar wanda yayi tseren gudu Haqiqa yau yasake tabbatar wa Insaaf tanada aljannu, domin kuwa wannan abun da yaji, yafi qarfin ace karfin mace ne Saida yagama Tari, sannan yafara ambaton sunayen Allah, tana ganin halin dayake ciki tatashi ta dauki bargon kan gadon tarufe masa jikinsa dashi, Ahankali yasaka hannunsa ya janyota jikinsa ya rungume ta, hawaye ne ya silalo daga idanuwanta, cikin kuka tace "Yaya kaima anyima abinda akewa sauran wanda na aura ko? Haka ake musu Yaya shikkenan daga nan Bana sanin komai saide Naga sun mutu, Dan Allah karka tafi kabarni, Yaya Asim ina sonka, please karka barni kaima" Ahankali yasaka hannunsa Yana shafa gadon bayan ta, haduwar fatar jikinsu babu kaya ba qaramin tada masa hankali take ba, yanda boobs dinta suke mintsininsa jiyake kamar yayi wasa dasu, amma daya tuna irin shaqar da akayi masa awuya, Sai yasa hannu yashafi wuyan nasaπŸ˜‚ Kenan yarinyar nan budurwa ce, idan miji Sai sadu da itane ake samun wannan matsalar, cikin muryar datasha wahala yace "suma irin haka ake musu suna mutuwa kafin su shiga ciki?" Kanta Yana kan qirjinsa ta gyada masa kai, wata irin Ajiyar zuciya yayi mai sanyi πŸ™ˆ Yasake rungume ta sosai a jikinsa, wata zuciyar tace dashi to qila saura kai, babu makawa kaima zaka iya mutuwa yanzu, tunda gashi tafada da bakinta suma sauran hakan ce take faruwa dasu, Sai yanzu wani irin tsoro ya kamashi πŸ˜‚ Amma daya tuna da Allah, saiya yi qarfin hali yace mata "kiyi Shiru, insha Allah babu abinda zai faru, ina tare dake akoda yaushe" Yanzunma daga masa kai tayi, Ahankali ya tashi yashige toilet yayi wanka a gurguje, sannan yazo yatada kabbarar sallah, sosai ya kaiwa Allah kukansa dangane da wannan matsalar, bayan ya idar ya dauki alqur'ani yafara karanta wa Itama hakan tayi, tazo gefensa suna karatun tare, saida yamma liss sannan sukai Addu'ah suka shafa, har lokacin gaban Asim bai daina faduwa ba, amma idan ya tuna yariqe Allah da manzonsa Sai yaji nutsuwa ta shigeki Tare suka futo daga d'akin shida ita, yasaka hannu yarufe kofar harda saka key, ta kalleshi tace "Yaya ina zamuje Naga kana rufewa?" Girgiza kansa yayi yace "bazamu sake kwana adakin nanba, Sai mun nemi mafita" Cikin sauri tace "to adakin Anty Amrah zan dinga kwana? Kai kuma d'akin Yaya Amjad?" Shiru yayi Yana kallonta, Sai can yace "kuma fa hakane, Kinga babu inda zaki tafi kibarni, insha Allah ayau zansan abinyi, kije d'akin Amrah, zanje wajan mamy yanzu" Tace "to" sannan tawuce d'akin Amrah, shi kuwa Yana zuwa d'akin mamy yazauna akusa da ita Ta kalleshi tace "Asim lafiya ko?" "lafiya, amma ba kalau ba mami, ina zan samu manya manyan masu Ruqiyya ne yanzu?" Cikin mamaki tace "Ruqiyya? Waza'ayiwa Ruqiyya?" Sharhi ✍🏻 Mrs Usman ce [2/28, 8:40 AM] El~Yaqoub: INSAAF Writing by:Amnah El yaqoub 45&46 https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 Dole na jinjina muku saboda yanda kuke qoqarin bin wannan labari, koda yaushe sharhin ku Yana birgeni πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ», banda bakin da zanyi muku godia, Amnah tana tare daku akoda yaushe, ina qaunarku har cikin raina πŸ˜… Alkhairin Allah yakai gareku : 🌸Ayusher🌸 Zeee jhnπŸ’– Fatyn Kaihaf πŸ’–πŸ’πŸ’‹ Ayusher Abdallah Fidos Yar mama ❀️ Alhusna Mrs Idris Zainab S muhd ZeeMusty Na sadaukar da wannan page agareku, Amnah tana yinku sosai wallahi πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» _____ Shiru yayi yakasa Bata amsa, mamy tace "Asim, maganar ruqiyya kake, nace waza'ayiwa Ruqiyya?" Kansa aqasa yace "Insaaf" "innalillahi... Wani abunne yasake faruwa kuma? Ko Aljannun tane suka tashi?" Asim ya kalli mamy yayi Shiru, to yanzu ta ina zai fara yimata Bayani? Tayaya zai kalli idon mahaifiyar sa yace neman haqqinsa yaje yi yaji an shaqe masa wuya? Girgiza kansa yayi yace "akwai de matsala mamy" "to Asim cemin kake akwai matsala akwai matsala, kuma kaqi sanar dani komai" Wayarta ta dauka takira Insaaf, bugu daya ta dauka, mamy tace "kizo inasan ganinki" Tana zuwa d'akin taga Asim azaune, tanemi waje tazauna agefensa Mamy ta kallesu tace "ku fadamin menene yake faruwa har ake nema Akira masu ruqiyya?" Cikin sauri ta daga kanta ta kalleshi tace "Yaya masu ruqiyya za'a Kira?" Cikin damuwa yadaga kansa yace "abinda nake tunani kenan, sannan daga baya Sai a hada har gidan ayi karatun Qur'ani" Shiru tayi tana nazari Akan maganar sa, tarasa meyasa ake mata kallon me aljannu, ita Bata taba tashin aljannu ba, babu wata wadda ta taba cewa tanada aljannu, amma zataga gudun ruwan su, Ahankali tace "to akirasun" Mamy ta kallesu tace "toku tashi kuje, tunda kungama yanke shawarar komai" πŸ˜ƒ Insaaf ta kalli mamy tace "mamy dazu nefa...." "Bari muje mamy, zamu dawo anjima" Asim ya katse Insaaf din cikin sauri 🀣 Mamy tayi Ajiyar zuciya tace "to Allah yakaimu" Suna futowa daga d'akin nata, yace zaije wajan Muhsin, zasu dawo anjima, tayi masa fatan Allah yakiyaye sannan Takoma d'akin Amrah tana fatan ace matsalar ta tazo qarshe *** ****** *** Zaune suke a gaban wani malami da Muhsin yayi musu jagora zuwa wajansa Malamin yayi Ajiyar zuciya bayan yagama jin duk abinda yake tafe dasu yace "subhanallah...., dagaji ta hadu da mugayen aljannu ne, Bari nakira wani abokina, saina hadaku dashi, kuyi hakuri insha Allah, zaku samu mafita" Wayar sa ya dauko yakira wani Malamin daban yayi masa Bayanin komai, Malamin yace ataho masa da yarinyar, yanaso yaganta Sallama sukai, ya dubi su Asim yace "munyi magana dashi, amma dole saikun tafi da yarinyar, yanaso yaganta" Muhsin yace "Okey, to shikkenan Malam, mungode, zamuje insha Allah" Malamin yace "babu damuwa, kuje waje, zanturo muku wanda zai muku jagora zuwa wajansa" Godia suka sake yimasa, sannan suka futo daga falon nasa Kai tsaye gida suka wuce duka su ukun, a lokacin duk suna zaune afalo, Amjad yajuya Sai kallon Amrah yake, tana dago idon ta saita ga sun hada ido dashi, harara take sakar masa taci gaba da kallo Insaaf da mamy kuwa kallo suke, basusan abinda yake wakana atsakanin su Amrah ba πŸ˜‚ Asim ne yashigo falon, gaba dayansu sukai masa sannu da zuwa,Insaaf ta miqe zuwa kitchen ta kawo masa ruwa ta ajiye agabansa, sannan ta zuba masa a cup tabashi, Takoma kusa da mamy itama ta zauna Da wani irin kallon soyayya yabita, kwata kwata ya manta su mamy na wajan mamy ta kalleshi tasaki gyaran murya tace "ya akayi Asim?" Cikin sauri yajuyo ya kalleta, sumar kansa ya shafa yace "Mamy mun dawo, but yanzu zamu juya, Malamin yace muzo mu tafi da'ita" "ku tafi da'ita ina? Ai bazata biku ita kadai ba, Gara mutafi gaba dayanmu" Tajuya ta kalli Amjad taga yatusa Amrah agaba Yana aikin kallo, ta Girgiza kanta, wanna yaran kuwa lafiyar su kalau? πŸ€” Gaba daya Yara sun susuce Akan mata? πŸ€” Daga murya tayi tace "Auta kutashi mutafi, Amrah jeki kiramin Ishraqa kice tazo akwai inda zamuje" tasake duban Insaaf tace "dauko hijabin ki mutafi" Babu musu tashiga daki ta dauko hijab dinta suka futo daga gidan gaba daya, a compound suka hadu da Ishraqa da El-Hameed, mamy tasake yimusu Bayanin komai, El Hameed yace "to hajiya ko zamuje wajan Malamin daya Bata magungunan nan ne?" Mamy tace "A a Hameed, muje wajan wannan din de agani, Fatanmu de Allah yasa mudace" Gaba dayansu suka amsa da Amin, sannan Amjad ya dauko wata motar suka tafi gaba dayansu Bayan sunje gidan Malamin sosai ya karbesu hannu bibbiyu, acikin babban falon sa suke azaune gaba dayansu, kowa yayi Shiru Yana jiran Malam Saida yagama sallamar wasu mutanan sannan yadawo kansu, yasake basu hakuri suka sake gaisawa ya kalli Asim yace "ina yarinyar take?" Asim ya kalli Insaaf ya nuna ta, Malamin ya kalleta yace "taso nan yata" Wani irin d'an iskan kallo tayi masa tasaki wani irin tsaki mai qarfi Lokaci daya su mamy suka saki baki suna kallonta cike da mamaki, Malamin yayi murmushi yasake kallonta yace "bazaki zo ba?" Kai tsaye tace "bazan zoba, duk abinda kakeji dashi Nima inaji dashi" Wannan Karon kam, tabawa kowa mamaki, shide Malamin baice da'ita komai ba, yayi wata irin dariya yace "to bari mugwada muga abinda kikeji dashi din" yajuya ya kalli su Asim yace "Waye yayanta anan? Ina nufin muharraminta" Mamy ta nuna Asim da El-Hameed tace "wannan shine mijinta, wannan kuma mahaifinta ne" Yace "Okey, ku dauko min ita" Asim ya tashi yanufeta, Shima El Hameed ya qaraso, hannu Asim yasa zai kamo ta ta watsa masa wata irin harara, manyan idanunta har wani komawa gefe daya suke saboda masifa tace "karka tabani" Lokaci daya annurin fuskarsa ya dauke, wannan ba Insaaf dinsa bace, Insaaf dinsa tanada tarbiya, bazata aikata haka ba, yasan cewa kawai aljannu ne, cikin bacin rai ya damqo hannunta, Shima El Hameed ya kama daya hannun nata, suka fara kokarin dagata, amma tana yin wata irin Girgiza takusa watsar dasu awajan Amjad dake gefe azaune Ahankali ya matsa kusa da mamy ya kama hannunta yariqe πŸ€£πŸ™ˆπŸ™Š Malamin Yana ganin yanda ake kokawa da'ita ya tashi ya dauko wani ruwa acikin gora, yabude shi ya tuttula mata a jikinta, lokaci daya jikinta yasaki, tazube a tsakiyar falon, wani irin kuka tafashe dashi irin me gunjin nan, ga wani irin numfashi datake yi kai bazakace macece take wannan numfashin ba, kamar muryar gardi Ishraqa ta dora kanta Akan qafafunta tafashe da kuka, kuka take sosai harda shashsheka, Amrah ta matsa jikinta tana Bata hakuri da muryarta datayi rauni alamun itama tana gab da Fashewa da kukan Malamin Yana daga tsaye ya kalli Insaaf dake kwance tana wani irin gunji marar Dadin ji, yace "ba zakuyi magana ba?" Tayi Shiru ta qyaleshi, yajuya ya kalli ya ransa yace "kufara" Matasan yaran kusan su biyar suka matso kusa da ita suka fara karatun alqur'ani, Kowa da inda yake karanta wa,sunkusa minti talatin suna karatu amma Insaaf ko uhm batace ba, tana kwance tana wannan gunjin kukan Ran Malamin ya6aci, cikin fishi ya tashi ya dauko wannan ruwan daya zuba mata dazu, ya kwara mata shi a fuska, wani irin qara tasaki wanda yasa mutanan falon suka fara toshe kunnuwansu Har zuwa wannan lokacin Ishraqa taqi dago kanta ta kalli Insaaf, kuka kawai take tana tausayin yar Tata Cikin tsananin azaba ta daga hannunta, cikin wata irin murya me girma tace "zan fada...., karka sake qonani, zan fadaaaa!...." Amjad ya zaro Idonsa waje 😳, yasaki hannun mamy yakamo dantsen hannunta yariqe sosai 🀣 mamy tana jin yanda jikinsa yake rawa, haka tayi fuska ta qyaleshi Malam yace "mezaku fada? Suwaye ku?" Cikin gunjin kuka tace "Auranta nayiiiii...., nine mijinta manub.... Nine nake kashe duk wanda ta aura, nine nashiga jikin mutanen dasuka Santa nasanya musu tsoron ta acikin zuciyar su, banaso kowa ya ra6eta, matata ce" Gaba daya falon Sai suka fara salati, Asim yayi Shiru Yana kallon ikon Allah, shida matarsa wani shege agefe Shima Yana iqirari matarsa ce Malam yace "to Manub danme zaka aure ta?bayan kasan babu aure atsakanin mu? Meyasa kake cutar da ita kana daukan ran mutane wanda basujiba basu gani ba?" Shiru tayi batayi magana ba, ruwan hannunsa yasake watsa mata cikin sauri tace "tun tana qara ma na aure ta, meyasa saida ta girma zasu aure ta bayan nadade da auren ta, lokacin da motar su tayi hatsari a gefen gidanmu ita kadai ce tafuto tana kuka, ni kuma tundaga nan naji ina sonta na aure ta, na dauke ta daga Garin na kaita tsakanin kano da Adamawa na ajiye ta,tundaga nan nake bibiyar rayuwar ta, suma wanda suka tsinceta sukaci amanata suka aura mata dansu Ammar, Shima na kashe shi sannan nashiga jikin uwar Yaron nasaka mata tsanar Insaaf acikin ranta har saida suka koreta daga gare su " Asim ya tuna irin rashin mutuncin da Inna tayiwa Insaaf ranar dasuka koreta, dama abin yayi yawa, ashe ba'ita kadai bace da sharrin aljannu Malam ma yayi Shiru yanajin wannan rashin Imani, yace" yanzu zaka rabu da'ita kokuma saina konaka? " "bazan Barta ba, matata ce ita " Malam yanajin haka yayiwa yaransa alama suci gaba da karatu, suna farawa tafara ihu tana cewa"zan fita, wallahi zan fita" Malam yace "ta'ina zaku fita?" "tabaki, wallahi zan Barta har abada" Malam yace "Bata baki zaku fita ba, ta hanci zaku tafi, sannan muddin kasake dawowa jikinta saina qonaka gaba daya" "zan tafi, zan tafi, wallahi natuba bazan dawo ba" Yana fadar haka Insaaf tafara jera atishawa, saida tayi guda uku qwarara sannan wani irin bacci mai nauyi yayi awon gaba da'ita Malam ya tashi ya hada musu magungunan da zatayi amfani dashi, ya basu sannan yace "insha Allah tabarsu kenan, bazasu dawo ba, ni Nasha ganin irin wannan case din dayawa, yanzu wannan maganin zatana amfani dashi kullum, daya mai ne ta dinga shafe jikinta dashi idan zata kwanta, sauran kuma Nasha ne, dana turare" El-Hameed yace "mungode Malam, Allah yasaka da Alkhairi, yanzu Malam menene abin sadakar?" Murmushi yayi "dubu arba'in ne, amma kukawo abinda yasamu" Asim yayi gyaran murya yace "Mungode Malam, insha Allah zan aikoma da check na nera million daya, kuma dan Allah Kaci gaba da saka matata acikin Addu'ah Allah yaqara kare min ita" πŸ₯° Muhsin yayi murmushi ya jinjina kansa Ishraqa tadago kanta tace "mungode Malam, Allah yasaka da Alkhairi,haqiqa ka ceci rayuwar yata, bamuda bakin da zamu gode ma, ka shirya next week dakai za'ai Umara insha Allah" El-Hameed ma yace "sannan idan Malam yadawo daga Umara akwai sabuwar Mota tasa ce halak Malak" Yaran Malam suna jin haka suka saki kabbara, dama ko ba'a fada maba kana ganin yarinyar kasan yar gata ce ta gaske, yanda suka taho yuya guda haka duk Akan mutum daya, 🀣 Malam yace "haba bayin Allah, ya zaku min haka?, ai wahalar tayi yawa" Mamy tace "babu komai Malam, qalubale dakuma halin kadaici da tsananin tashin hankali da yarinyar nan ta fuskanta Sanadin wannan matsalar bazai fadu ba, mune da godia wallahi" Malam yace "to hajiya, nagode, Allah yabata lafiya, sannan insha Allah zan dinga aiko mata da magungunan dazaran sun qare, saitaci gaba da amfani dasu" Gaba dayansu suka sake yimasa godia, Asim yasaka hannu ya dauki Insaaf, Sai yaji ta shafal, ba kamar dazu ba, har lokacin tana bacci ba tasan abinda yake faruwa ba Muhsin ne yayi driving dinsu suka koma gida, Amjad kuwa Kasa driving din yayi, Sai El Hameed ne yamai dasu gida 🀣 Gaba dayansu gidan mamy suka wuce, Amjad saida ya ganshi azaune a falon gidan, sannan yasaki wata irin Ajiyar zuciya 😊 Mamy ta kalleshi tayi murmushi Kai tsaye Asim yawuce da'ita dakinsu, Akan gadon ya kwantar da'ita Shima ya kwanta, sannan ya janyota jikinsa ya rungume tsam Akan qirjinsa Yana shafa dogon gashin kanta. Su kuwa gaba dayansu a falon mamy suka zauna aka sake jajantawa juna,Ishraqa de fata take Allah yasake hada fuskarta da mutanan da suka riqe Insaaf tsawon rayuwar su, sun san cewa ita ba yarsu bace amma suka riqeta ruqo na gaskiya. har aka Kira la'sar Asim bai futo ba, mamy taji Shiru ta kalli Amrah tace "ke jeki Gano ko tatashi, naji su Shiru" Ishraqa tace "a a mamy, barsu su huta, anjima da daddare Sai mu dawo" Mamy tace "a a, muje ku ganta kafin kutafi Ishraqa" Amrah ce tatafi d'akin nasu, tayi nocking taji Shiru, Ahankali tatura kofar tashiga, anan ta gansu kwance Akan gadon ya rungume ta a jikinsa kamar zai mai data ciki, Bude kofar da yaji anyi ne yasa yabude Idonsa dake cikeda bacci ya kalli kofar, Yana ganin Amrah yace "ke lafiya?" Kansa ta sunkuyar tace "Yaya waisu Anty Ishraqa ne zasu tafi gida, shine zasu ganta" "kice su shigo" abinda yace kenan, ya maida kansa kan fillo πŸ™Š Dawowa falon tayi tafada musu, gaba dayansu suka shiga d'akin, alokacin ya tashi yashiga toilet Yana alwala, saida yafuto ya gansu duk sun kewaye ta, itama tana zaune a tsakiyar su kamar ba'ita ba, cikin mamaki yasake kallonta, Agogon hannunsa yake daurawa ya qaraso gaban gadon yace "babu abinda yake damunki ko?" Tace "babu komai Yaya, Wai yanaga duk jikinku yayi sanyi? Menene yake faruwa?" Mamy tace "babu komai Insaaf, tunda kina jinki lafiya to Alhamdulillahi , Allah ne yarabaki da masifar datake damunki, insha Allah saide atada labari, aljannu ne ajikin ki kuma an cire miki su" 🀣 Tace "aljannu?" Duniyar tunani tatafi.... Sai alokacin tatuna ashefa ance ta shirya zasu tafi wajan ruqiyya, to ai daga nan ba tasan ma menene yasake faruwa ba Asim ya matsa yariqe hannunta yace "zanje masallaci, ko akwai abinda kike buqata?" Kanta ta girgiza tace "babu komai Yaya, Allah yadawo dakai lafiya" Kansa ya d'aga mata kawai, daga nan yafice daga d'akin Suma su Ishraqa sunaji an idar da Salla a masallaci suka tafi, saboda sunsan Asim din zai Iya dawowa Ana idar da sallah kuwa yadawo, mamy Yagani zaune afalon,itada Amrah da Amjad, Shima zama yayi Yana duba saqonni acikin wayar sa Har dare suna zaune afalo kadan kadan suna fira, amma Asim kam Hankalinsa Yana wajan Insaaf, dama kawai yake nema yagudu wajan ta πŸ˜‚ Mamy tatashi tashige d'akin tana fadin "bari naje nayi wanka nahuta" Cikin sauri kuwa Shima ya tashi yashige cikin d'akin nasu. Amjad Yana ganin tashin mamy da Yaya Asim yayi sauri yadawo wajan Amrah , qasan kujerar datake zaune ya zauna kamar me neman gafara yace "Anty Amrah har yanzu baki cemin komai ba" Wani irin haushi ne ya kamata, ta tsani taji Amjad Yana mata wannan magana, takaici hanata magana yake, shikuma taga alama baya gane hakan, tashi tayi tashige dakinta, Shima dafe kansa yayi, yarasa ta ina zai 6ullo mata, wata dabara ce tafado masa, ya tashi yaje dakinsa ya dauko biro da takarda yabi bayan ta zuwa dakinta, tana ganinsa ta kawar da kanta, zama yayi agefenta, ya marairaice mata murya cike da salon wayo da yaudara yace "Anty Amrah, idan natuna magana ta ta qarshe tsakanina da Daddy Sai inji jikina yayi sanyi" 😊 Tace "Umm... yayi kyau" Yasake kallonta yaci gaba da cewa "maganar sa ta qarshe daya min, Amjad ya kamata kayi aure, karna mutu banga 'ya'yanka ba, Amjad burina kayi aure kafin na mutu nabar duniya" πŸ˜‚ Cikin sauri ta kalleshi, shima kallonta yayi,idanunta kadai ya kalla yagane maganar tasa kamar ta shigeta, dayaga zancen sa yayi tasiri a kanta saiyaci gaba da cewa "yanzu gashi baya nan, Bama lalle kafin yafuto nanda shekara biyar yaganni ba, qila mutuwa ta rabani dashi, wannan ne dalilin dayasa nakeso muyi aure Amrah, Daddy yayi muku laifi, amma idan kika aure ni zaiji dadi Shima, zaiji dadi ace yau na auri yarinyar Mami, muje mukai masa ziyara a matsayin ma'aurata, amma idan baki yarda da magana ta ba, ga wannan takardar muyi a rubuce, ki yarda ayi auren, idan Daddy yaga nayi auren bai mutuba, Hankalinsa ya kwanta, shikkenan saina sakeki daga baya " Kallansa tayi tace"in hakane meyasa bazaka nemi wata ba? Dole saini? Saboda Nika raina nikake gani kullum?" Sake marairaice wa yayi yace "to Anty na wajan wa zanje? Wace zata yarda ta aure ni da wuri bayan ko halin juna bamu sani ba? Kece de yar'uwa ta kuma yayata, kece me rufamin Asiri" πŸ˜‚ Ajiyar zuciya tayi tace "to zan tonama asiri kuwa duk lokacin da yarjejeniya ta qare kaki sakina" "babu maganar tone tonen asiri ma, kalau zamu rabu insha Allah, saka hannu yanxu de" Babu musu ta karbi takarda ta rattaba hannu **** Da daddare shida kansa yadinga Bata abinci a baki, saida ta qoshi sannan ya ajiye sauran, shirin kwanciya sukayi, kayan jikinta ya rage mata, itade tana zaune tana ganin ikon Allah, yanda yake Bata kulawa Yana lallaba ta kamar ba Yaya Asim ba Kwanciya sukai yasaka ta cikin jikinsa, basu dadeba bacci ya dauke su Kusan karfe daya saura yafarka azabure, har hakan yayi sanadiyar farkawarta, tace "Yaya lafiya?" Kansa ya Girgiza yace "wallahi shaf na namanta, ban baki maganin ki,ya kamata ace kinfara amfani dasu tun yau din, dakuma wanda zaki shafa" Turo bakinta tayi gaba, cikin shagwaba tafara magana "Yaya to...toka barshi gobe sainayi, yanzunfa inajin bacci, kuma ni Allah banajin ciwon komai" Kallanta yayi yasakar mata wani irin kallon soyaiya, yanayin yanda take masa shagwa6ar Yana birgeshi, saqon Yana zuwa inda ya dace, qasa yayi da muryarsa yace "A a fa Baby.....kina wasa da lafiyarki Kenan ko?" Sake turo masa baki tayi tace "uhm.... uhm...Allah ni...." girgiza kansa yayi, ya tashi ya dauko mata maganin, wanda zata sha yabata Tasha, sannan yabata wanda zata shafa, karba tayi tafara shafawa a hannunta da kafafunta, qwacewa yayi yace "hakan shafawa kike?" Kafin ta bashi amsa yafara murza mata man, batayi masa musu ba ko kadan tunda tasan magani ne, tundaga tafin kafarta yafara shafa mata har zuwa cinyar ta,sosai yake murza mata man, laushi jikinta dakuma gyaran datasha yasa yama fara mantawa magani yake shafa mataπŸ™Š salon yanda yake shafa mata ne ya sauya, shi kansa baisan laushin fatar ta dana man ya d'ebeshi ba saijin kansa yayi Yana shafa ko'ina na jikinta, jikinsa ne yafara rawa Yana fitar da wani irin numfashi Dasauri Dasauri. man yasake lakutowa yafara shafawa a qirjinta, da farko tayi tunanin shafar magani ce, amma dataga abin nasa Bana qare bane, Ahankali yace "Yaya.....Yaya Wai iya nan za'aci gaba da shafa wa ne?" Kallanta yayi yace "me kikace?" Bakinta tatura tace masa "babu komai" Sbd taga baya cikin Hankalinsa,tarasa meyasa yake son taba kirjinta, saikace baitaba aure ba Shikuma Asim qirjinta yaci gaba da shafawa baisan lokacin daya Fado kanta ba, cikin wata irin murya yace "Insaaf...." Kallansa tayi takasa magana, yace "please in gwada mugani?" Daga masa kai tayi tace "amma.... Ahankali Yaya" Bai iya cemata komai ba, Sai wasu irin zafafan wasa daya fara aika mata, tun tana jinsa tana share shi batasan lokacin data bashi hadin kai ba, Abin mamaki wannan Yaron kalau yaji shi babu wani ciwon kai, Kai tsaye ya nufi hanyar sa, cikin ransa ya karanta Addu'ar saduwa da iyali, Insaaf batasan meyake faruwa ba, tunanin ta yayi gaba, Dadin da Asim din yake jiyar da ita ta hanyar wasa yasa ta manta dacewa ta bashi dama ya karbi haqqin sa. lokaci d'aya taji wata irin azaba ta shigeta Batasan lokacin data saki wata irin gigitacciyar qara ba, a firgice mamy tafarka daga baccin datake Sanadin jin wannan qaran Insaaf kuwa hannu biyu tasa tana dukansa, cikin kuka tace "Yaya! zan mutu, Yaya Asim please kayi hakuri, kabari zan mutu, wallahi zaka kasheni" Asim kuwa baisan ta nayi ba, Yana cikin wata irin duniya wadda bai taba tsintar kansa aciki ba, kuka yafara yimata wiwi Yana kiran sunan MamyπŸ™ˆ "mamy.... nashiga uku na, mamy...dadi, Insaaf zata kasheni" Tun Insaaf tana jin kukansa Sama-Sama harta daina jin komai, daga nan Bata sake sanin inda kanta yake ba shi kuwa Asim baisan abinda yake faruwa ba, saboda bai tashi dawowa hanyacin saba Sai wajan karfe uku nadare Sai alokacin yaga halinda take ciki, gabansa yayi wata irin faduwa,dudduba jikinta yayi yaga yarinya Bata motsi kamar macacciya, hannunsa yadora akansa yace "innalillahi...." Jikinta yasake ta6awa yaga kwata kwata Bata numfashi Daga kan gadon yasauko yayi sauri yashiga toilet yayi wanka, ya nemi rigarta doguwar yasaka mata, yadauke ta cak, suka futo daga d'akin, mamy data Kasa komawa bacci tun lokacin dataji wannan qara saita sake jin qaran Bude kofa Futowa tayi anan ta ganshi dauke da Minal, cikin tashin hankali tace "meyasa me ta?" Kasa magana yayi, gabansa Sai faduwa yake,Idonsa yayi tsilli tsilli kamar 6arawo πŸ˜‚ jikin Insaaf din ta kalla anan taga jini duk ya 6ata mata jiki, nan take ta Fahimci komai, cikin tashin hankali tace "nashiga uku ni Usaina Asim kanka daya kuwa?" Shiru yayi yakasa Bata amsa, tace "ka tsaya kana kallo na Muje, muje a kaita asbiti" Suna zuwa asbitin dayake na kudi ne anaan suka karbeta suka fara dubata Shida mamy suna zaune har zuwa lokacin yakasa daga kai ya kalleta, wata irin kunyar ta yake ji Har Gari ya waye, ba'a basu Damar ganinta ba, Amrah da Amjad suka tashi suka ga gida Shiru babu kowa, saida suka Kira mamy sannan tace su zauna sunje unguwa ne, yanzu zasu dawo Ishraqa da El-Hameed ne suka zo ganin jikin Insaaf, Amrah tace ai sun tafi unguwa inji mamy Haka suka juya, El Hameed yawuce wajan aiki, ita kuma takira wayar mamy, anan mamy take fada mata suna Asbiti, Ishraqa Bata tambayi ba'asin komai ba tashigo Mota tabiyo su Asbiti Alokacin anbasu damar ganinta, suna zaune adakin shida mamy, ita kuma Insaaf an saka mata qarin ruwa Tana kwance tana bacci fuskarta tayi wani irin fayau, Ishraqa ce tayi sallama tashigo d'akin da taimakon wata likita data rakota, Asim yanajiyo muryar ta a bakin kofar d'akin yayi sauri yashige cikin toilet din d'akin 🀣 Ishraqa Bata ma lura dashi ba,tashigo d'akin ta tazauna jikinta a sanyaye tana kallon Insaaf dake bacci Tace "mamy lafiya? Meyasa meta?" Kafin mamy tabata amsa likitar data duba Insaaf tashigo d'akin tadubi mamy tabata wata takarda tace "yawwa hajiya gashi, Za'a siyo mata wannan magungunan, sannan anyi mata dinki dazu, Dan Allah afada masa yad'an d'aga mata qafa kafin wajan ya warke" Lokaci daya Ishraqa ta Fahimci komai, wani irin farin-ciki ya kamata, hakan yana nufin 'yarta tasamu lafiya kenan?, Aljanin daya aureta yabarta kenan, godia tafara yiwa Allah acikin ranta Asim Kuwa dayake cikin toilet yanajin Bayanin da likita tayi yadafe kansa da hannunsa Cikin ransa yace yau nata6owa kaina, tayaya zan fita daga Toilet dinnan in kalli Ishraqa? Tab yau akwai wunin toilet awajan wasu πŸ˜‚πŸ˜‚ ✍🏻 Amnah El yaqoub Like my page on Facebook πŸ‘‡πŸ»[3/2, 5:47 PM] El~Yaqoub: INSAAF Writing by:Amnah El yaqoub 47&48 Like my page on Facebook πŸ‘‡πŸ» https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 Ina miqa Godiya ta agareku, fan's dina da suke cikin page dina na Facebook, musanman Ummu Nihla Junaid, inajin Dadin sharhin ki, naji Dadin maganar ki Akan littafin INSAAF, nagode sosai πŸ™πŸ» _____ Sunkuya wa yayi yadora hannunsa Akan gwiwar sa Yana qarewa toilet din kallo Yana neman wajan zama, Dan maganar gaskiya bazai iya fita ba Acikin daki kuwa Ishraqa ta kalli mamy tace "ai Amjad da Amrah cemin sukai kunfita, da alama basusan Bata da lafiya ba ko?" Mamy tace "basu saniba, Nima kaina bansani ba, qara najiyo a falon na futo shine naganshi zai kawota asbitin, in banda jaraba ma irinta maza yarinya daga yin magani amma akasa yin hakuri?" πŸ€” Cikin sauri Asim ya rufe Idonsa Yana girgiza kai πŸ™ˆ, fisabilillah mamy tun cikin dare suke tare amma takasa yimasa fada saida Ishraqa tazo? Yanzu inda Ishraqan tasan Yana cikin toilet din Yaya zaiyi kenan? Ishraqa tayiwa mamy murmushi tace"to ya za'ai mamy ai lokaci ne, duk Daren dadewa dama haka zata faru, Sai hakuri " "A a, ba irin wannan yanayin ake cewa Sai hakuri ba Ishraqa, har wanne irin naci ne zaisa ka haikewa yarinya qarama irin wannan har dasu dinki, yaran zamani bazasu taba saura rawa mata adaren farko, kowa kansa rawa yake Yana jin karfi a jikinsa kamar doki" "nashiga ukuna" πŸ˜–cewar Asim dayake toilet Ishraqa tayi murmushi tace "to Allah yabata lafiya, tunda tarabu da wannan masifa ai Alhamdulillahi, Mamy kije gida ki huta, saina zauna tare da ita" Mamy tace "Dama basai kinfada ba Ishraqa, tafiya zanyi, kema tashi zakiyi mu tafi" 🀣 Cikin sauri Ishraqa tace "to mamy waye zai zauna anan? Ko shikkenan angama komai harda ita zamu tafi?" Mamy tace "a a, mu kadai zamu tafi, shida ya aikata mata hakan ai zai taho da'ita" Ishraqa tace "Wai Asim? To Yana inane? Kona Kira shi awaya nafada masa yazo mu zamu tafi?" Mamy tace "A a, a a, Karki ki rashi Sarai Yana jinki, tare muke dashi" πŸ˜‚ Ishraqa tace "A a, to Yana ina? Ai ban ganshi ba" Mamy tace "Yana cikin toilet, yanajin tahowarki yashige yarufo" Ishraqa tayi yar qaramar dariya , cikin ranta tace rayuwa kenan, Wai yau Asim ni yake kunya Mamy tadaga murya tace "kafuto mu zamu tafi gida!!" Yana jinta yayi Shiru yaqi amsawa, tasake daga murya tace "Asim!!!" Nanma yanajin ta yayi Shiru, Ishraqa tayi murmushi tace "muje mamy, Allah yabata lafiya" Mamy tace "to ai shikkenan muje, shiya sani" Daga nan suka fita daga d'akin, mamy Sai mita take, shi kuwa yanajin fitarsu ya tashi tsaye ya lumshe Idonsa, yasaki wata irin Ajiyar zuciya tare da hamdala acikin ransa 😊 Ahankali yabude kofar toilet din yafuto, kujeran da mamy tatashi yazauna, ya kama hannunta yariqe Yana kallonta Ahankali ahankali tafara Bude idonta, harta gama budesu gaba daya, cikin sauri yace "my wife...." Cikin qaramar murya tace "Yaya..." "na'am Baby na, sannu, sannu kinji" Daga masa kai tayi tace "yaya kakusa kasheni" "bazan kashe Kiba Insaaf, idan na kashe ki dawa zan rayu bayan kece rayuwata gaba daya?" Wata irin shagwaba tayi masa tace "to ba Kaine ba..." "Insaaf kidena min wannan shagwa6ar mana, ko ki naso a samu matsala?" Daga masa kai tayi alamun eh πŸ˜… Murmushi yayi yace "Ok kinaso ko? Saboda kinsan bazaki bani ba, to kiyi hakuri, Yaya yayi laifi, amma bazan sake ba kinji?" Yatsina fuska tayi tace "ni saika siyomin kaza" Murmushi yayi, dimple dinsa ya futo, yaga alama de rigima kawai take ji yace "inde kazace zan siyo miki, data siyan baki ranar da aka kawo ki, data Daren jiya, data Daren gobe" Yana qarasa wa sukasa dariya gaba dayansu, Sai wajan Sha biyu na Rana aka sallamesu, koda wasa bai bari tataka kafarta ba daukar ta yayi suka tafi gida Suna zuwa gida Yagansu gaba dayansu afalo, da Ishraqa da mamy da Amrah da Amjad dayasa mamy agaba da alama akwai abinda yake nema Jiyayi inama qasa ta tsage yashige saboda kunya, zuwa yanzu kam Amrah da Amjad ma da ake 6oye musu suma sun gane komai Insaaf tana hada ido da mamy tayi sauri ta6oye fuskar ta acikin qirjinsa, shi kuwa kallo daya yayiwa Ishraqa yayi saurin kawar da kansa Murmushi tayi tace"Asim sannu da zuwa "πŸ˜… Yasan da biyu tayi masa maganar, to Wai dan Allah shi Yaya zaiyi ne? Ga Insaaf a hannunsa gaba daya saiya rikice, ina zaikai wannan kunyar? Cikin sauri yayi fuska yashige d'akin sa tare da rufowa Suna zuwa ya ajiye ta Akan gado tace "Yaya naji kunyar mamy, kaga Kasa tasan abinda mukai ko" Zama yayi akusa da ita yadora kansa Akan fillon datake kwance yace "idan mamy ce Aida sauqi, bakiga Antynki a falon ba?" "naganta mana Yaya, to menene? Kai ita kakejin kunya?" Yace "sosai wallahi, bazaki gane bane" Murmushi tayi tace "Yaya ka kaini toilet nayi wanka inaso nayi sallah" Cikin sauri ya tashi ya kaita toilet din, bai futo ba saida yayi mata wankan yasake gasa mata jikinta, suna futowa sukaga abinci adakin, anan suka zauna yafara Bata itama tana bashi, ahaka suka wuni adaki babu wanda yafita acikinsu Tsawon sati daya Asim yad'auka Yana kula da Insaaf, ko kadan bai sake neman taba, duk da ya naji a jikinsa kamar ya hadiyeta saboda sha'awa, ita kanta atsorace take dashi, muddin tatuno ranar data shiga hannunsa gabanta har faduwa yake idan tatuna ranar dazai sake cewa ta bashi Yau tana d'akin mamy fruit ne agabanta tanasha, Mamy Bata d'akin Turo d'akin yayi yashigo, cikin sauri ta kalli agogo tace "Yaya, yanaga kadawo da wuri yau?" Zama yayi yajanyota jikinsa, yadora ta Akan cinyar sa yace "Nima zansha" Daukowa tayi takai masa bakin sa, babu musu yabude bakin tasaka masa, Shima saiya karba yafara Bata yace "kece kikasa nadawo ai" Bakinsa ta goge masa tace "ni kuma?" "emana, kayan ki sunzo fa, suna dakinmu, su mamy suna can suna gani, kitashi muje kema ki kalla" "na kalli me Yaya? A a, zan gani Ahankali, amma yanzu de bazanjeba" Yace "shikkenan, yanda kikace" ya ajiye fruit din hannunsa ya jata suka zube Akan gadon Cikin sauri tafara tashi tace "Yaya d'akin mamy nefa, ya zamu kwanta mata agado" Zip din rigarta yaja yace "waike bakya tausayi nane?" Kukan shagwa6a tafara yimasa, shi kuwa Yana cin Karo da nashanunta Hankalinsa yakasa kwanciya saida yafara wasa dasu, cikin ranta tace mayen nono kawai Ganin taki saki ranta yasa yafara tsokanarta Yana Jan hancin ta harta sake dashi suna dariya, mamy taturo dakinta tashigo, tana ganinsu tayi sauri taja kofar tarufe sannan ta daga murya tace "Asim!" Kallan Insaaf yayi yakasa magana, itama shi take kallo idonta ya firfito, mamy datake bakin kofa taqara cewa "Asim baka jinane?" Rigarta yafara maida mata, kafin yarufe saida yayi kissing boobs din sannan yayi sauri yafuto,kansa aqasa, yayi tunanin magana zata masa Akan abinda tagani saiyaji tace "magana zamuyi kazo inason ganinka, muje falo" Kansa aqasa yace "to mamy" Sannan yawuce zuwa falo Mamy ta leqa cikin d'akin tace "Insaaf mekike bakije Kinga kayan naki ba? Kije kigani mana" Itama cikin kunya tace "to mamy" sannan tafuto Mamy tawuce wajan Asim tace "munyi magana da abokin Daddyn ku, Akan maganar Amjad da Amrah, Amjad yafadamin sun Gama daidai ta kansu, ina ganin kaje ka sameshi saiku San ranar daya kamata Asa ayi bikin nan" Mamaki yakama Asim, Anya kuwa Amjad da gaske yake? Amrah ce ta amince haka cikin sauri? Kokuma de wani abun ya shirya, kafada ya d'aga yace "shikkenan mamy, amma kina ganin idan akasa wata daya yayi?" "haba Asim wata daya yayi kadan, nifa auren nan dande yazama dole nema amma banaso Amrah ta barni wallahi" Asim yayi murmushi yace "Mamy yau kece kike fadar haka? to ai tare dake take akoda yaushe, meyasa zaki damu?" "tare dawa?bazasu zauna daniba wallahi, kuma in aurar da 'yar tawa in zauna gida daya da'ita?" "to menene mamy, muma bagamu ba?" "ku daban Asim, suma daban, Kai Kaine ka auro, zaku iya zama agida, amma Amjad shine ya aure ta, dole gidan zasu bari" Murmushi yayi yace "to shi Amjad din badan gidannan ne ba?" "kai Asim kome zaka ce fa saide kafada, amma bazasu zauna daniba, Yara kullum suna fada suna cacar baki suna doke doke tayaya zan zauna dasu, suje can su qarata, idan sun Gama doke doken saisu Bawa kansu hakuri, ni har yanzu ma nakasa yarda Amrah ce ta amince da auren, amma bansani musu ba " Asim yace" to shikkenan mamy, zanje nasame shi yanzu " Yana fita yawuce gidan Muhsin ya dauke shi, suka dauki El-Hameed, daga nan suka wuce gidan Abokin Daddy, inda aka yanke ranar bikin Amrah da Amjad tsawon wata biyu Da kayan sa Rana yadawo gida yabawa mamy Pls kuyi hakuri Dan Allah πŸ™πŸ»jiya kunjini Shiru banda data ne kuma Asim bai samin ba 😏 Yanzunma Ishraqa ce ta taimaka ta samin ☹️ Gashinan babu yawa, amma insha Allah gobe saikun gaji da karatu, nagode πŸ™πŸ» ✍🏻 Mrs. Usman ce [3/3, 8:46 AM] El~Yaqoub: INSAAF Writing by:Amnah El yaqoub 49&50 Like my page on Facebook πŸ‘‡πŸ» https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 Lokaci daya aka fara shirin biki, mamy tahana kanta sakat, Bata zama yau itace nan gobe itace can, idan tatuna yau itace zata aurar da Amrah saitaji hankalinta yasake kwanciya, uwa uba idan tatuna autanta ne mijin Zaune suke a dakinsu da gashi Sai ita, kayan lefen da yayi mata take dubawa akwatuna goma Sha biyu, tun ranar da aka kawo taga akwatunan ko budesu batayi ba, Ahankali take daga kayan tana gani kayane masu tsada daga gani wanda ya hada yaji a jikinsa πŸ˜… Kallonta yayi Yana shan coffee "Sai yau kika duba kayan nan, kwanan su uku kenan acikin d'akin mijin ki, ko basu yi miki bane a sauya?" Wata irin hararar wasa tayi masa tace "sunyi kyau sosai, amma basu kaika kyau ba" Wani irin dadi yaji, yau shine Insaaf tasake dashi har take fada masa wannan maganar,jiyake kamar karta daina yabon nasa,wani kallon soyaiya yazuba mata, sannan yayi sipping coffee yace "nidin har wani kyau ne dani?" Ita ba tasan danta fada masa komai yayi mata wannan tambayar ba, ba tasan wayo yayi mata ba, zuciyarta daya tace "kaii emana, nida nafara ganinka ma jinake aljanine" Cup din hannunsa ya ajiye yafara wata irin dariya, tadena duba kayan ta kalleshi, ashe Yana wannan uwar dariyar Shima? πŸ€” Cikin dariya yace "Aljani kuma?" "emana, nida naje diban ruwa naganka a kwance natsorata, natafi da gudu na fadawa su Inna, Allah sarki rayuwa, ina fatan ace Allah yabada fuskata datasu Inna kafin na mutu nabar duniyar nan" Cup din hannunsa ya ajiye yataso yadawo wajan ta ya kama hannunta, "Nima inaso na gansu, Ada banyi tunanin Aljani ne yasa suka miki haka ba, shiyasa naji basu kyauta ba, amma yanzu dana gane sainaji ya kamata ace ko sau daya ne mungansu, tare da matar Malamin nan" "Aljani kuma Yaya? Kana nufin aljanin da mamy tacemin ancire min sune sukasa Inna tayi min haka?" "sune, haka suka fada da kansu, sannan ina tunanin Shima Malamin da muka sauka agidansu dasa hannun wannan aljanin, but lokacin da ake miki ruqiyya aljanin beyi magana Akan Malamin ba, amma koma menene idan Aljani ne, idan ma bashi bane, ina qara yiwa Allah godia daya azurta ni da mace kamar ki, kuma dole musan yanda zamuyi mu nemo matarsa musake yimata godia, hakan ya miki? " Jikinta a sanyaye tace" yayi Yaya, yawwa Yaya, namanta ban baka abinka ba " " abun me? " " toka tsaya kagani mana"tatashi ta dauko masa saqonsa tadawo wajansa tace "rufe idonka" Babu musu yarufe idon nasa, tasaka masa Agogon data siyo masa a Sudan da zobe sannan tace "to Bude" Yana budewa Yagani yace "wow, I luv you so much Wife, yaushe kika siyomin?" "lokacin da mukaje Sudan" Agogon yadinga shafawa, ya kaishi bakinsa yayi kissing,sannan yace "yayi kyau sosai,bazan taba mantawa da wannan kyautar ba, tana daya daga cikin abubuwa masu muhinmanci dakika bani, amma wanda yafi kowanne muhinmanci acikinsu shine yanda na sameki a matsayin cikakkiyar budurwa, nayi tunanin Narasa wannan Damar a rayuwata" Kallansa tayi tana nazarinsa, acikin maganarsa kamar yanaso yace bai taba samun mace budurwa ba, to inhakane Anty Lubna fa? Bata tambayeshi ba Sai tayi Shiru kawai, tunda Shima bai futo fili yafada mata ba, under wear tafara dubawa ta dauko brezia tace" Yaya wannan ai sunmin yawa, saide Anty Amrah tayi amfani dasu " Sake matsowa yayi jikinta yace" bawani yawa, hakanne ta miki yawa? Dede size dinki nace su saka miki" "to kai waye ya fadama size Dina? Sunmin yawa nikam" Wani irin kallo yayi mata yace "size din naki Sai an fadama min? Kawo kiga nasa miki kigani, zata miki daidai" Dariya tafara tace "a a, barshi, idan zan saka saina gani da kaina" "Allah baki isaba Sai an gwada rigar nan" Dariya yabata ganin yanda yadage saiya gwada mata riga, tasan da biyu, inba hakaba mutum yadage Sai yayi abu bayan kace bakaso Tana dariya Shima yanayi ahaka yacire mata rigarta, sannan yafara saka mata brezia, aikuwa tayi mata daidai Kallanta yayi yace "tobagashi nan ba, amma da kikace tayi yawa" Shafa gefen breast dinta yayi yace "Kinga nan dama basai yashiga duka ba, haka ma yayi min" Maimakon yacire hannunsa tunda ya nuna mata wajan saiyaci gaba da shafawa, lumshe idanunta yayi, cikin wata irin murya tace "ya....ya,kabari please" Matso da fuskar sa yayi kusa da Tata, "mezan bari?" "abinda kakemin kabari pls" Muryarsa ashaqe yace "bazan iyaba, nayi hakuri fa baby, yau kwana nawa? Kusan kwana goma fa, ke bakya tausayina? Ko so kike nayi miki kuka?" Shiru tayi tarabu dashi tana tuno ranar daya mata filla filla, Ahankali tasa hannunta ta janye nasa hannun, gaban ta Yana tsananta faduwa, cigaba yayi da abinda yake, lokaci daya hawaye yafara zubo mata, bakinsa yadora a face dinta ya lashe hawayen, sannan yahade bakin su waje daya, sosai yafara nuna mata zazzafar soyaiya, lokacin daya jishi acikin wata duniyar daban kuka yafara Yana kiran sunan Mamy, πŸ™ˆ Haka itama kukan take tana kiran sunan Anty Ishraqa saboda azaba, amma ahaka tasa hannu tarufe masa baki, kartaje Garin kiran dayake mamy tajiyo shi tazo tana bugs musu kofa πŸ˜‚ can Sama Sama kamar a mafarki yake jin kukan nata, amma bai saurare taba saida yasamu abinda yake so, taji jiki sosai, haka Tasha kuka harda na banza, kwata kwata bataji banbanci dana farkon ba, hatta tafiyar ta saida ta Dan sauya,lalla6ata yadinga yi bayan komai ya lafa, aikuwa Sai shagwaba take yimasa, shikuma duk saiya gigice yarasa ina zai sata, rungume ta yayi a qirjinsa bayan sunyi wanka, sumar kansa tashafa tace "Yaya" "na'am baby na ya akayi" "Wai meyasa kake kiran sunan mamy ne, wataran fa zata iya jinmu" Sake matseta yayi a jikinsa yace "wallahi bansan ina kiranta ba, idan ina tare dake rasa nutsuwa ta nake gaba daya, da dinki yayi yawa Insaaf, Allah yasaka wa mamanki da Alkhairi" πŸ™ŠπŸ€£ Murmushi tayi "Amin yaya" haka ya hanata futowa falon ranar, har dare suna dakinsu, kuma babu wanda ya nemesu *** ****** *** Ahankali lokaci yana tafiya har bikinsu Amrah ya qaraso, zuwa yanzu Insaaf harta fara sabawa da jarabar Asim, saide babu wani dadi datake ji, saide wahala kawai, wani lokacin tafi son yayi wasa da'ita ma biki yarage saura sati daya Ishraqa tahadasu duka takai su wajan gyaran jiki, amma na Amrah yafi yawa, idan Insaaf taga Amrah tana shan maganin mata har tausayi take Bata, to Amma idan tatuna cewa Amjad ne Angon saitaji da Dan sauqi, ba lalle yakai Yaya Asim mugunta ba , biki yazo yan'uwa da abokan arziqi na nesa dana kusa duk sunzo, gida yafara taruwa da jama'ah, tun kafin ma mutane suyi yawa Insaaf tafara jin kanta Yana mata ciwo, ga tashin zuciya datake ji, haka ta silale tabar gidan babu ma wanda ya lura, ta tafi gidansu, itama Ishraqa tana gidan bikin anata abubuwa, qawaye mamy kuwa kowa Sai murna yake tayata saboda yaude Amrah zatayi aure cikin hukuncin ubangiji Insaaf kuwa saida yamma dataji dama dama sannan tadawo gidan, Yaya Asim baya nan, suna tare da Amjad suna sake shirya gidan da zasu zauna tunda mamy ta Dage basu zauna mata agida baπŸ˜‚ Washe Gari daurin aure, tunda safe data Daukowa Asim manyan kayansa ya shirya yaga tana yatsina fuska, fuskarta ya kama da hannunsa yace "Baby meyafaru? Kalau kike kuwa?" Cikin dauriya tace "lafiya ta kalau Yaya, Sai yaushe zaka dawo?" "kinason ganina ne?" "inason Jin qamshin jikinka, banaso kayi nesa Dani" Mamaki ya kama shi, janyota yayi jikinsa ya rungume ta, babu musu ta cusa kanta acikin qirjinsa ta lumshe idonta Daukarta yayi cak, suka koma kan gadon yace "Baby, kona cire kayan muyi Zaman mu kina buqatata?" Daga masa kai tayi tace "eh ka zauna, ni kawai qamshinka nakeso naji" Wayarsa ce tayi qara, Yana dubawa yaga El Hameed ne, yad'auka cike da ladabi, ba tasan me aka fada masa ba taji yace "Ok, toshknn" Ya kalleta yace "Insaaf, Abban ki ne ya kirani, zamu tafi wajan daurin aure, kuma Kinga nine waliyin Amjad, suna jirana" Shagwa6ar Tata sakar masa, Sai yatsina fuska take tace "uhm... uhm Yaya... nide banaso katafi" Rikicewa yayi yace "A a haba baby na, Kinga to kiyi hakuri kiyi Shiru, shikkenan mu zauna kawai" πŸ˜ƒ Kallansa tayi tace "to kaje, amma kadawo da wuri" "Ana daurawa zan dawo, ko zama bazan yi ba" Tashi tayi daga jikinsa tace "toka kulamin da kanka " Kissing dinta yayi yace "to wife" Daga nan yafice cikin sauri Itama shiryawa tayi ta fita wajan su Amrah da sauran qawayenta, bayan sallar Azahar Ana ta shirye shiryen kamu taji wani irin jiri Yana dibanta, haka ta daure Bata fadawa kowa ba, Asim daga wajan daurin aure mutane suka riqeshi, amma komai cikin sauri yake yinsa saboda jikinsa ne kawai awajan su tunanin sa da zuciyar gaba daya Yana wajan Insaaf Da yamma tasake shiryawa cikin less da yayi mata masifar kyau, ankai amarya wajan kamu itama tafuto da sauri zata shige Mota driver yakaisu, tana cikin sauri taji jiri ya debeta, ga ciwon kai, cikin sauri ta dafe kanta tana Kallan sararin samaniya Sai gata tazube aqasa Ishraqa tana can tanata kokarin saka mutane Amota ta hango kamar Insaaf ce mutane suke kokarin daga ta, gaban ta ne yafadi cikin sauri tadawo gidan, tattaba fuskarta tafara yi taga yarinya Bata motsi, tadubi driver tace "muje asbiti kawai" Cikin sauri ya daukesu suka tafi, suna hanya Ishraqa ta Kira wayar mamy tafada mata, mamy tace zata taho amma Sai Ishraqa ta hanata tace takula da mutanan kawai tunda ita tana tare da Insaaf din Bayan an kar6eta gado suka Bata, akayi mata txt likita tazo tayi allurai, sannan tasaka mata qarin ruwa Har bayan la'asar Ishraqa tana zaune Shiru, ledar ruwa biyu ta qare aka saka mata ta uku, itama ta qare aka saka mata tahudu, itama data qare aka saka mata Leda ta biyar To daga nanfa jikinta yafara sanyi πŸ˜₯ Batayi wata wata ba ta dokowa Asim Kira, alokacin sun Gama komai Yana hanyar tafiya gida Sai tsaki yake, yaji wayar sa tana qara, Yana dubawa yaga Ishraqa ce mai kiran, dauka yayi yace "Maman Insaaf ina wuni" πŸ˜ƒ "lafiya Asim, gamu a asbitin doctor Ilyas fa, Insaaf Bata jin dadi, nayi tunanin qaramar jinya ce, to yanzu an saka mata ledar ruwa ta biyar kenan" "innalillahi...., gani nan, gani nan zuwa" daga nan yakashe wayar yajuyo zuwa asbitin Yana qaraso wa yaga har ruwan yakusa qarewa, ya kalli Ishraqa yace "meyake damun tane?" "bansani ba wallahi, dazu de sunyi mata txt da allurai Sai kuma qarin ruwan dasuka saka mata" Zama yayi a gefen gadon yafara tattaba fuskarta, Ahankali tabude idonta ta kalleshi yace "sannu" Tace "yawwa Yaya" Ishraqa ta matso tace "kintashi? Yajikin naki?" "lafiya kalau Anty, banajin komai yanzu, dama kawai jiri nakeji" Likita ne yashigo yasake dubata yace "zaku iya tafiya, babu abinda yake damunta kawai maleria ne da ciwon kai" Katin Asim ya karba sukaje akayi discharge dinsu sannan suka wuce gida Suna zuwa gida taci gaba da harkokin ta, saida Asim din yahana ta yin komai, amma tanajin jikin nata dadan sauqi, batajin jirin komai,lafiya kalau suka kwanta, amma tana manne a jikinsa tana shaqar qamshin jikinsa Cikin dare tatashi ta wata irin mahaukaciyar yunwa, Ahankali ta zare jikinta daga nasa tatafi kitchen, yan gidan da sauran yan biki duk suna bacci, indomie tadafa guda biyu tazauna a kitchen din tafara ci, zuciyarta ce tafara tashi, kafin tayi yunqurin tashi tafara sheqa amai awajan, Asim kuwa Yana juyi da yaji Bata kusa ya tashi ya duba toilet bai ganta ba, yafuto falo anan yaji motsinta a kitchen, Yana shiga yaganta ta dafe kanta da hannunta, cikin sauri ya qarasa wajan ta ya tare ta, mamy yakira ya sanar mata, cikin sauri tafuto tabiyosu zuwa d'akin, bayan ya kwantar da'ita mamy tace "Sannu Insaaf" Bata iya amsawa ba Sai kanta data daga kawai Mamy ta dubi Asim tace "meyake daamuntane?" "mamy likita yace maleria ne, har qarin ruwa fa yayi mata, amma kuma yanzu ma Kinga jikin nata" Tasake duban Insaaf tace "menene yake miki ciwo ne?" Tace "mamy inaji kamar na mutu, ga jiri dayake dibana, kuma yunwa nakeji sosai, kuma amai nakeji gaba daya" Mamy ta zaro idonta 😳tace "Amai? A a, ba muga ta zama ba, Asim dauke ta mukoma asbitin nan" Babu musu yace "to mamy" Kayanta ya sauya mata, suka koma asbiti, wannan Karon likitan Yana ganinsu yace kawai ta'iyo fitsari a kawo masa, Asim ya sata tayi fitsari yakai musu, wani qarin ruwan suka saka mata, kafin Gari ya waye saida Tasha Leda hudu, daga nan fa Asim yakoma abin tausayi, gaba daya yashiga damuwa musanman idan ya kalleta yaga tasake yin wani irin fari, shi dama tun jiya dayaga yanayin ta yasan ba kalau take ba, amma saitace masa ita lafiyarta kalau, yanzu gashi daga jiya zuwa yau Tasha ledar ruwa har Tara, mamy ta kalleshi taji yabata tausayi, gakuma yarinya a kwance itama ba tasan inda kanta yake ba Likitan ne yadawo zai dubata Asim yace "doctor result din bai futo bane?" Kallansa yayi yace "yafuto, zamuyi mata scanning yanzu, sannan batada jini a jikinta, dole za'a qara mata" "toku duba nawa idan yayi saiku saka mata" "a a, akwai a asbitin ma, zamu saka mata yanzu, karku damu Yallabai" ya qarasa maganar murmushi Akan fuskarsa Asim ya kalleshi wani irin haushi ya kamashi, su suna wannan halin amma dubi yanda doctor yake musu murmushi Wata nurse ce tazo taturata sukaje akayi mata scanning, sannan suka dawo da ita suka daura mata qarin jini, idanun Asim yayi jajir damuwa tataru tayi masa yawa, Ajima ya kalleta yasake kallanta, gaba daya tausayin yarinyar yagama kamashi, ko menene yake damunta haka? Likitan daya shigo dazu ne yadawo d'akin ya kalli Asim, ya miqa masa results din txt din yace "congratulations Yallabai, madam tana dauke da juna biyu na tsawon wata biyu, munyi mata scanning mungano 'yan biyu ne, shiyasa take wannan wahalar, but saide kuyi hakuri da wannan laulayin insha Allah Ahankali zata dinga Jin sauqi" Zaro Idonsa yayi😳 yace "yan biyu doctor" Cikin murmushi likita yace "to, abinda muka gani kenan, bamu saniba mata ne ko maza ne, akwai magungunan cin abinci damuka rubuta mata dashi zata rage yawan amai tanacin abinci ko yaya ne, amma rashin lafiya saide Ahankali shine zata warke" Mamy ta lumshe idonta tana yiwa Allah godia, cikin farin ciki tace "Alhamdulillahi, Asim kaga ikon Allah ko? Nida nake yan biyu ban haifi yan biyun ba, amma gashi kai Allah yabaka" Wani irin farin-ciki yake ji sosai, ya kalli mahaifiyar tasa yace "mamy yan biyu fa" Sai hawaye 😭 Murmushi tayi tace "godia zaka yiwa Allah Asim ba kuka ba, shine yabaka su alokacin daka rasa yarka qwaya daya jal, amfanin yarda da qaddara kenan" Hawayen Idonsa yagoge ya kalli Insaaf datake kwance Ana mata qarin jini, cikin ransa yace I luv you so much Insaaf Mamy ta kalli likita tace "doctor ai wannan albishir dole zan aikoma da goronsa" Murmushi yayi yace "to hajiya godia nake" daga nan yafice daga d'akin Mamy tace "To Asim, Bari inje gida na aiko muku da abinci, sannan in fadawa Ishraqa abinda yake faruwa, ga kuma Amrah anjima za'a kaita, ka zauna ka kula da'ita" "to mamy, Allah yakiyaye" Mamy na fita yakoma kan gadon ya rungume ta Yana kissing dinta ta ko'ina πŸ™Š Mamy tana zuwa gida taga Ishraqa ta tsaya Akan komai, komai Yana tafiya yanda ya kamata, lokacin data fada mata Insaaf tasamu ciki Sai tayi murmushi kawai, tana yiwa Allah godia, alokacin tayi gefe ta Kira El Hameed ta sanar dashi, cikin farin ciki yace "Alhamdulillahi, Habibty saiki shirya muje shopping a fara siyo mata kayaiyakin baby" πŸ˜‚ Ishraqa tace "Habiby mene?cikin wata biyu zamu fara yiwa siyaiyar kaya?" Fada yafara yi mata "to zama zamuyi Sai haihuwar tazo sannan zamu siya? Wacce irin magana kike yi hakane? Yarinya zata haifi yan biyu idan Allah yabata dama, a a, jikokina ne fa nafarko, saina tsaya jira Sai ciki ya tsufa sannan zan siyo musu kaya? Toke idan bazaki ba, nikam zanje nasiyo musu " Ishraqa tayi murmushi tace"to maida wuqar Yallabai, shikkenan Allah ya sauketa lafiya" Da daddare su mamy suka hadu, aka yiwa Amrah fada tare da nasiha, Ishraqa takama hannunta suka shiga Mota Sai gidan Amjad, gidan ma babu Nisa sosai, acan suka Barta tare da qawayenta, bayan qawaye sun tafi, Amjad yashigo d'akin da sallama, Ahankali ta amsa masa, zama yayi agefenta tare da cire babbar rigarsa ya ajiye Kallanta yayi yaga tayi wani mugun kyau, jikinta yayi wani irin fresh, qirjinta ya kalla yaga masha Allah komai acike, Ajiyar zuciya yayi yace "Anty Amrah kinyi kyau sosai" Ahankali tace "thank you" Tashi yayi yace "ki tashi muyi Sallah mana ko, saikici abinci ki kwanta ki huta" Kallansa tayi, itade tasan cewa wannan aure dama yarjejeniya sukai, menene yakawo zancen sallah kuma? Ba amaren da sukai auren gaskiya ne suke wannan abun ba?, wata zuciyar tace to ai ba neman ki yayi ba, ibada ce zakuyi, Ahankali tasauko daga gadon, yanda ta sunkuya wajan saukowar shiya Bawa Amjad Damar ganin qirjinta sosai, wani irin murmushi yayi wanda ake Kira zaki raina kanki yarinya Bayan sun idar da sallar saita ga Yana kokarin cire mata hijabi, tace "bari mana Amjad, zan cire idan zan kwanta" Ledar kazar daya shigo da'ita ya dauko yace "to kici kazarki saiki kwanta ki huta, kinsan akwai gajiya" Cikin sauri tace "ka zata kuma?" "emana, ta kice, siyo miki nayi, saboda nasan kina sonta" Jikinta ne yayi sanyi, cikin ranta tace Allah sarki Amjad, yayi kokari, to Amma kuma menene abin siyo mata wata kaza? Kaza ai ta amare ce kuma duk amaryar dataci saita biya afili saitace "a a, Kaci abarka kawai, meyakaini cin wata kaza nida ba za mane yakawo ni ba?" "a a, kici wallahi, menene aciki?" Qinci tayi, duk da ranta yanason kazar, shi kuwa saiya dauko guda daya yabata a baki, babu musu tabude bakin tafara Ci, wasa wasa saida sukaci sosai shida ita, kayan wajan ya dauke bayan sun Gama, yadawo yazauna agefenta yazauna, cikin shagwaba yace" Anty Amrah.... tah " Kallansa tayi ta kawar da kanta, jikinta ya matso yacire mata hijabin, batayi aune ba taji ya kwanta agadon bayan ta, yazubo hannunsa saman qirjinta ya matse ta a jikinsa, hancinsa yafara gogawa a saman wuyanta, cikin muryar rada yace" Antyyynaaaah...... " Wani irin abu taji yafara yawo a jikinta,Amjad kuwa hannunsa daya dora aqirjinta yafara yawo dashi Sai qamshin datake ne yake sake fizgar jikinsa Wani irin haushi ya kamata, cikin sauri takwace jikinta tatashi tsaye tace"Amjad pls tashi kafita" "tayaya zan barki ke kadai Anty Amrah" Hannunta ta hade waje daya πŸ™πŸ»tace "pls, Dan Allah katashi kafi ce kabar min d'akin nan" Yace "Ok" yafuto yaja mata kofar d'akin, compound din gidan yaje ya tsaya yakira wayar Yaya Asim Bayan ya a dauka yace "Yaya" Asim yace "ya akayi Amjad?" Muryarsa ce take rawa kamar zaiyi kuka yace "Yaya Anty Amrah ce, kaga yanzu ma daga d'akin ta koroni" Asim yayi Shiru, takaici yataru yayi masa yawa, yanzu dare ne, idan yace zaizo gidan nasu zai Iya kwakwkwada mata mari ne, tayaya zata bar masa dan'uwa a waje ita tazauna adakin? Tanaso tace ita yarinya ce ba tasan me ake nufi da aure ba? To yanzu bazaije gidan ba, idan yaje a kanta zai huce dama akusa yake matarsa babu lafiya πŸ˜‚πŸ˜‚ Ajiyar zuciya yayi yace " "Kora kuma? Kai kuma shine kafuto kabar mata d'akin? Amjad kana Jina ko? Babu wata Anty Amrah, Amrah zaka ce, itace aqasanka yanzu, kadena mata shagwaba kafuto mata a namiji, karka sake tsaya wa ta rainaka kana Jina ko?" Shima Amjad din Ajiyar zuciya yayi yace"nagane, angama yaya" Daga nan yakashe wayar yajuya cikin gida Washe Gari dasafe likita ya sallamesu, jikin nata dadan dama dama, tana zaune a gaban motar Asim Yana ja, tafiya kadan Saiya kalleta yace "baby babu komai de ko?" Tace "babu komai Yaya" Sunci gaba da tafiya taga wata mata a gefen hanya tana saida dambu, cikin sauri tace "tsaya Yaya, tsaya tsaya kasiya min dambu, yaban sha'awa" Kallanta yayi cikin mamaki yace "dambu kuma baby?" Batare data kalleshi ba tace "Eh, shi nake so" Kansa ya Girgiza yace "yanzu baby kirasa abinda zakici Sai abincin bakin hanya? kan titi?" Cikin shagwaba ta daga masa kanta alamun eh Jinjina kansa yayi, yafita yasiyo mata, yabata sannan yaja motar suka tafi, suna zuwa gida tabaje a falon tasa dambu agaba tana Ci, sosai take wata irin Loma kamar mayunwaciya, Asim yayi Shiru Yana kallanta Mamy kuwa da tasan halin mace mai ciki murmushi kawai tayi Saida taci dayawa sannan tafara jin amai, cikin gudu tayi daki tashige toilet tana amai, Dasauri ya tashi zai bita mamy tace "ina zaka?" "mamy Kinga gudu takefa, kuma likita yace ta dinga tafiya ma Ahankali, saboda lafiyar abinda yake cikinta" Mamy tace "oh ni Hussaina, Dan Allah Asim ka sararawa ranka" πŸ˜‚ Dawowa yayi yazauna badan yaso ba, itama Insaaf din Bata Dade ba tafuto tana goge bakinta, ta kalli mamy tace "mamy zo6o nakeso Nasha" Mamy tace "to Insaaf, zauna ki huta zan hada miki shi yanzu yanzu" Tace "to mamy" sannan ta maida kan TV Acikin TV din ne aka nuno wata mata tana cin alale da manja, lokaci daya taji a duniya babu abinda takeso inba alale ba, Asim Yana kallonta qasa-qasa, Yana jira yaji me kuma zata tace tanaso ☹️ itama Juyawa tayi ta kalleshi tace "Yaya" Cikin sauri ya kawar da kansa Yana Addu'ah Allah yasa ba alalen siyarwa zata sake cewa tanaso ba πŸ˜‚ Mamy ta kalleshi taga yanda yake kawar da kai, dariya ta kamata, ta zuba musu ido tana kallon ikon Allah, Insaaf tasake juyowa ta kalleshi da kyau tace" Yaya kaje ka samomin Alale irin wannan, shi nakeso naci" ✍🏻 Amnah El yaqoub [3/3, 11:02 PM] El~Yaqoub: INSAAF Writing by:Amnah El yaqoub 51&52 Like my page on Facebook πŸ‘‡πŸ» https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 Sarai yaji abinda tace, amma saiya sake kallanta yace "mekikace? Mekikeso kici?" Cikin shagwaba tace "Bana fadama ba" Qeyarsa ya Sosa ya tashi yace "to bari naje na nemo miki" Mamy tace "A a, kayi zamanka, Bari naje nayi mata saina hado mata zo6on ma" Komawa yayi yazauna Yana Kallan Insaaf, tosu masu cikin dama haka suke? daga wannan abu Sai wannan? Lokacin da Lubna Takeda ciki babu abinda Yasani, saide ya Kade rigarsa yafice office πŸ˜‚ Bazai dawo gidanba Sai dare, yanzu kuma gashi yanayi Dan dolensa mamy tatashi tawuce kitchen, ta hada mata komai yanda ya dace, sannan tadawo falon, har zuwa lokacin suna nan zaune yanda ta barsu,abincin ta dauka tafara Ci amma ko guda daya bataci ba taji amai, haka, da gudu tasake tafiya taje tadawo, Asim ya runtse Idonsa πŸ˜–gaba daya abin duniya yataru yayi masa yawa Bayan tadawo mamy tayi mata sannu, ta kalli mamy tace "nagaji da Aman nan mamy, kuma yunwa nakeji, na gaji wallahi, bansan meyake damu naba" Mamy tayi murmushi ta kalli Asim tace "baka fada mata ba?" "ban fada mata ba mamy, naga Bata gama warwarewa bane" Mamy tace "A a Asim" Ta kalli Insaaf tace "Insaaf Allah ne ya azurta ku da samun baby, ciki ne dake, laulayi ne yasa bakya iya cin abinci dayawa, Sai kiyiwa Allah godia da kyautar daya miki" Maganar taji wani iri, cikin ranta tace ciki kuma? Haka ake cikin? Yanzu ahakan itace zata haihu? Kallan mamy tayi tace "mamy ciki kuma? Ina tsoron haihuwa zan'iya mutuwa" Cikin sauri Asim yajuyo ya kalleta, yace "wacce irin magana kike hakane?" Kafin ta bashi amsa ya dauko zo6on da mamy ta hada mata yakai mata gaban ta yace "Kinga, ba zaki mutu ba, Sha abinki, ga zo6on Kisha" Kanta ta daga masa sannan ta karba tafara Sha, yayi mata dadi sosai kuwa, cikin ikon Allah datasha batayi Aman ba, tana gama Sha ta kwanta Akan kujera Mamy tace "to ai bakici komai ba zaki kwanta, me kike so sai adafa miki" Kallan mamy tayi tace "mamy alale kawai nakeso, amma bazan iya cin wannan dinba" Mamy tace "Ok bari na fadawa Ishraqa tayi miki ko zaki iyacin nata" Wayarta ta dauko adaki takira Ishraqa, ta nayi mata Bayani Ishraqa tace zatayi, aikuwa ko awa biyu ba'ayi ba tabawa maigadinta yakawo, zama tayi tafaraci amma daya Kasa zaune yakasa tsaye Addu'ah yake a ransa Allah yasa ta'iya Ci, kalau kuwa taci, ta tura masa flaks din tace "Yaya ajiye min sauran, anjima shi zan qaraci" Babu musu yace "to" sannan ya tashi yayi kitchen da sauran abincin, Yana tafiya Yana waigenta, wacce irin fitina ce wannan ace bazaka iya cin abincin gidanku ba saina maqota ☹️ Da daddare suna cikin bacci tafarka, wata irin hamma tayi tashafa cikinta taji babu komai kamar anyi mata yasa, kallan Asim taga Yana bacci, Ahankali takai hannunta tashafa sajensa, Bude Idonsa yayi ya kalleta "Baby lafiya? Meyafaru?" Shiru tayi tana darurar fada masa yunwa takeji Janyota yayi jikinsa yace "fadamin, meyake faruwa?" "Yaya yunwa nakeji" "tome zakici? Sai naje kitchen din da kaina nagani ko zan iya hada miki" πŸ™Š "Yaya nifa dabino nakeso" Zaro Idonsa yayi 😳yace "Dabino baby? Dare yayi fa" Tace "ai Yaya idan banci dabinon nan ba akwai matsala, bazan iya bacci ba" Tashi yayi zaune yace "Subhanallah...meyakawo wannan maganar kuma?" Tsaye ya miqe yazura jallabiya, sannan yasake Kallan agogo, ya dauki key din Mota yafuto, Dasauri tabiyoshi tace "Yaya muje" Babu musu yace "to sako hijabi mutafi" Maigadi ma yariga yayi bacci, saida suka tasoshi yabude musu get din sannan suka futo, haka suka dinga bulayi suna neman dabino amma basu samu ba, wani mai kayan fruit suka gani Yana tattare kayansa da alama Shima yayi dare ne bai tafi gida ba, tambayar sa sukayi yace maqocinsa dai Yana siyarwa, haka suka daukeshi Amota suka tafi gidan, aka taso maqoci, yakawo musu dabinon kusan Rabin kwano Asim ya kalleshi yace "Bata kwano biyar, idan yaqare saina dawo aqara mata wani" Jikin me dabino na rawa ya auna musu sannan suka tafi gida, suna zuwa yacire rigarsa ya kwanta, ita kuwa zama tayi Akan gadon tafara cin danon, saida taci yakai Rabin kwano Sanna tature sauran, Shima gajiya tayi taci, amma ba qoshi tayi ba, juyi yayi yaganta azaune tana hada qwallon dabino waje daya, cikin muryar bacci yace "Wai baki kwanta ba?" Tace "yanzu de zan kwanta Yaya" Murmushi yayi yakoma yaci gaba da bacci *** ****** *** Tunda safe dasuka tashi yake da daure fuska, Yana kallanta tanata zirga-zirga saide ya kalleta ya dauke kansa, babu alamun wasa ko kadan a fuskarsa, singlet ce a jikinsa Sai dogon wando na jeans, tunani yake ina zaije yahuta tunda ya dauki hutu awajan aikinsa? Yasake kallanta Sai abin gaban ta takeyi ko kallo ma be ishetaba, mezai sa yazauna ma a gidan suna wannan Zaman ko in kula din?πŸ€” Kallanta yayi yahadiye wani irin saliva saboda yanda kayan jikinta suka gama tafiya da Imaninsa, yace "Amrah dauko min rigata adaki inaso nafita" Kallansa tayi, cikin ranta tace Amrah! Ta kalli jikinsa Sai wani shining yake kasancewar sa fari tas, tasake Kallan dantsan hannunsa taga kamar bashi ba, tunani take kode taje ta dauko masa? Gida da gashi Sai ita Gara ta lallaba shi surabu lafiya πŸ˜‚ Afili tace "da meyasa kafuto babu rigar" Fuskarsa a daure yace "to ko bazan samu bane inyi abinda Naga ya dace?" Dasauri tace "menene abinda ya dace din?" Tashi yayi yafara nufarta yace "bari inzo in nuna miki" Tana ganin ya nufota tayi sauri tashige dakinsa ta dauko rigar ta kawo masa Murmushi yayi yace "thank you, sweet Anty" Itade Amrah tayi Shiru ta qyaleshi, rigar yagama sakawa Idonsa ya sauka Akan qirjinta yayi wani irin murmushi yace "Suger Anty...." Juyawa tayi zata bar wajan, taga alama Jan magana kawai yakeji, tana tafiya taji ya rungumota tabaya, tace "Amjad bari mana" Kafin yayi magana sukaji wani irin qara mai firgitarwa sakamakon tayar wata babbar Mota data fashe, gaba dayansu suka kwasa aguje zuwa daki, Amrah gudu Amjad gudu πŸ˜‚ Suna shiga daki suka Amjad yafara kokarin rufe wa, Amrah kuwa jikinta ne yake rawa takama hannunsa Tariqe tana fadin "Amjad yi sauri karufe kofar" Yana rufewa tashige cikin jikinsa, tana jiyo yanda bugun zuciyarsa ya sauya, kallanta yayi yaga tashige cikin jikinsa gaba daya Sai yanzu ne yaji wata irin kunya ta kamashi, Yaya akai wannan qaran yasa shi ya tsorata harya biye mata suka shigo daki aguje? Anya kuwa wannan abun ba zaisa Amrah tasake raina shi ba? Murmushi yayi yasaka hannu yasake rungume ta sosai a jikinsa, yayi qasa da kansa cikin muryar rada yace "Amrah abin yatafi fa" Qin dago fuskarta tayi daga qirjinsa tace "tsoro nakeji Amjad" Wani irin dadi yaji, yasake rungume ta,yayi qasa da kansa dede fuskarta, cikin shagwa6ar daya saba yace "Allah yatafi fa" Bakinta tabude zatayi magana yayi sauri yahade bakin su, zaro idonta tayi ka kalleshi, suna hada ido ya lumshe mata Idonsa, yasaka hannu yariqe kanta Yana yi mata wani irin kiss, kokarin tureshi take amma yayi mata wani irin ruqo, dukansa tafara amma maimakon yasake ta saiya sake riqeta yakai hannunsa bayan rigarta yayi qasa da zip din Lokacin da yayi arba da qirjinta rasa nutsuwar sa yayi, Amrah tafashe dawani irin kuka, takaici ya kamata, cikin kuka ta qwace bakinta tace "haka mukai dakai?, dama bakada alqawari?" Idanunsa sunyi jajir yadago kansa ya kalleta "me mukai dake? Wai kina nufin na aureki ne saboda na sakeki? You know I love you ko? To bazan iya sakin ki ba, and kisa aranki auren mu mutukaraba ne" Wani irin kuka tasaki tana dukansa hannu bibbiyu, bai saurareta ba yaci gaba da wasa da qirjinta, ita kuma takaici ne yake kamata duk lokacin data tuna Amjad ne yake taba mata breast, haka ta rabu dashi taci gaba da kuka, bai Barta ba saida yayi abinda yake so dashi, sannan ya tashi yafice daga d'akin Yana fita takira wayar Insaaf, alokacin tana zaune afalo ita kadai da apples a hannunta tanata faman ci, tana dauka Amrah tafashe da kuka tace "Insaaf Amjad ya cuceni, dama qarya ya shirya min ya aure ni, Wai yanzu bazai sakeni ba, wallahi gida zan taho, bazan Bari qanin bayana Yana lalubemin qirji ba" πŸ™ˆ Insaaf tayi murmushi cikin ranta tace to anzo wajan πŸ˜‚ Afili tace "Anty Amrah idan kin dawo gida ma Amjad ba sakin ki zaiyi ba, mutumin daya shirya qarya ya aureki tayaya kike tunanin zai sakeki? Ni banga laifin Yaya Amjad ba, Yana sonki, kuma auren qaninki aiba haramun bane, Anty Amrah manzon Allah s.a.w matarsa ta farko ta girmeshi, meyasa bazaki so kiyi koyi da Nana khadija ba? Kiyi hakuri Dan Allah, wannan de bada abincin da kikace ina yiwa Yaya Asim da wanka da shirya shi,haka zakiyi hakuri kema kifara yiwa Amjad"πŸ˜‚ Hawayen idonta ta share tace "ainima nasan ba haram din bane, amma Insaaf saboda tsabar rashin kunya Amjad zai kalleni Yana lalubeni, ko kunya ta ba zaiji ba" "to wacce irin kunya zaiji Anty Amrah? dama kece kike ganinsa a matsayin qani, amma shi baya daukar ki yayarsa, mamy da kowa da kowa yayi farin-ciki Akan aurenku, Dan Allah karki Bawa kowa kunya, gashi Yaro Dan saurayi, da kudinsa, Keda ya kamata kici gaba da lallaba abinki karya kula kowacce mace, yanda yake qaunarki wallahi Sai yanda kikai da abinki, amma kiyi tunani akai " Jikin Amrah yayi sanyi,Ahankali tace"to shikkenan Insaaf nagode" daga nan suka ajiye wayar, Insaaf ta ajiye wayarta tana murmushi, da niyya ta yabi Amjad, ta zigashi, saboda yasake samun karbuwa awajan Amrah, fatanta daya Allah yasa shawarar data Bata zatayi amfani da ita Mamy tayi murmushi tafuto daga dakinta bayan tagama jin duk maganganun da Insaaf takeyi awaya, tasan Sarai da Amrah take waya, godia tayiwa Allah acikin ranta daya Bata sirika ta Gari, dama tasan Amrah da Amjad akwai wani abu aqasa, bakomai ne yabata murmushi ba Sai lokacin data ce yanda Amjad yake sonta Sai yanda tayi dashi πŸ˜‚hakan yana nufin Shima Asim din da yake sonta Sai yanda tayi dashi kenan acikin daki πŸ€” Falon ta qaraso tace "sannu Insaaf, jeki turomin Asim" Apple din hannunta ta ajiye tace "to mamy" Dakinsu tashiga taga yagama shiryawa Yana fesa turare, qananun kayane a jikinsa da sukai masa kyau sosai, tsayawa tayi a bakin kofar tana kallonsa tace "kayan yayima kyau Yaya, saika zama kamar saurayi , please kadinga sakamin su, inaso" Murmushi yayi yace "aikece mai shirya ni,komai Yana hannunki Baby, amma nida ba Yaro ba ina zan dinga saka qananun kaya" Kafafunta tafara bubbugawa aqasa, cikin shagwaba tace "ni.... ni.... Allah nide saika sakamin" Cikin sauri ya qaraso wajan ta ya riqeta, "haba Baby, bafa ke kadai bace, kidena wannan bige bigen qafar Dan Allah, naji zansa, zan saka miki" πŸ˜‚ Murmushi tayi tace "to kaje inji mamy" Daga nan tashige toilet Murmushi yayi yafice daga d'akin Shima, yanason shagwa6ar Insaaf, duk lokacin data fara yimasa shagwaba rasa nutsuwarsa yake Zaune yake a gaban mamy, ta kalleshi tace "Asim zuwa yanzu ya kamata ace kadauki dukiyar Insaaf kabata, tun yarinya batafi shekara uku ba kake kula da komai na dukiyar ta, mutanan nan basu taba yima maganar kudinsu ba, babu wanda yasan ba naka bane Sai iya mu yamu, ya kamata yanzu kamaidata makaranta, idan tagama tafara aiki itama saitaci gaba da kula da dukiyar ta, amma Yaya kagani? " "mamy wanne irin aiki kuma? Nifa school dinma nafasa, ba zataje ba" "aikuwa baka isaba Asim, wacce irin magana ce wannan yarinya ba zatayi karatu ba, waini kam dakata ma, haka zata zauna babu ilmi tsawon rayuwar ta?" Cikin tsananin kishi yace "mamy to idan tatafi makarantar waye zai dinga kula da gidan? Haka za'a bar gida babu kowa?" Mamy tace "menene amfani na?" "to mamy idan kina nanma ita saita dinga fita kullum, sannan idan tagama makaranta ma kince zata fara aiki, waye zai kula girkin gida, da Yara, ni kwata kwata ba'a magana tama, dukiyar ta de zan Bata, amma tayaya zata bar Yara babu kulawa" ☹️ Mamy tayi Shiru tana ganin wannan tsananin kishi irinna Asim, ta kalleshi tace "ni Narasa wanne Yara kake magana Asim? Yaran da ko duniya basuzo ba kake maganar za'a barsu babu kulawa?" πŸ€” ✍🏻 Amnah El yaqoub [3/5, 11:15 AM] El~Yaqoub: INSAAF Writing by:Amnah El yaqoub 53&54 Like my page on Facebook πŸ‘‡πŸ» https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 Kansa ya sunkuyar qasa cike da kunya yace "Wai dama Ina nufin idan sunzo" "a a Asim, ya kamata abata haqqin ta itama kamar kowa, tunda dama can kaima kayi mata sha'awar karatun, idan tafara kamar yaune zakaga tagama" Badan yasoba yace "hakane mamy, to zan duba nagani" πŸ˜‚ Tace "to aduba da kyau" *** ****** *** Tunda yaje office dinsa bai zaunaba, kaya kawai yake harhadawa wanda yasan ya shafi Insaaf, duk wani documents dayasan natane da takardun gidaje da filayenta saida ya hada su waje daya, wayar sa yad'auka yakira Amjad, alokacin yana dakinsa a kwance, Yana tunanin irin takun dazai sakewa Amrah, idan ba daure mata fuska yake ba, bazasu taba daidai tawaba, tsaki yaja da yaji qaran wayar, Yana ganin wanda yakira shi ya tashi Dasauri yace "hello Yaya" "Amjad ina office kazo ka sameni yanzu" "Ok Yaya, gani nan zuwa" Amjad Yana zuwa Asim yayi masa Bayanin komai, Amjad yace "Toshikkenan Yaya," Tare suka zauna sukaci gaba da harhadawa, Shima Amjad yakawo na wajansa, babu abinda yarage ahannunsu Sai ribarsu dasuke riqewa, ya kasance yanzu itace zasuci gaba da Juyawa kafin court tabasu nasu, wanda zata karbo musu awajan alhaji Umar Saida suka gama sannan Asim yayi waya a shirya masa hall babba, wanda zai dauki mutane dayawa, nan da nan kuwa suka bashi tabbacin zasu hada komai, kawai date suke buqata yafada musu Shiru yayi yana nazarin wacce Rana ce ta dace, kawai saiyace su shirya masa zuwa jibi Bayan yakashe wayar Amjad ya kalleshi yace "Yaya jibi jibin nan baiyi sauri ba?" "a a, beyi sauri ba Amjad, ai lokacin abu ayishi, kasanar da mutane kawai, akwai babban taro jibi" "Ok Yaya, Allah yakaimu" Amjad yajuya yafita, yafara kiran mutane Yana fada musu, bai koma gida ba saida yamma, Yana zuwa kuwa yafada kan kujera ya lumshe Idonsa, dama agajiye yake sosai, wani irin qamshi yaji yadaki hancinsa, yasan Amrah ce tashigo falon, amma saiya share ta ko Bude Idonsa baiyi ba bare ya kalleta Kallansa tayi, tatuna shawarar da Insaaf tabata Tace "Sannu da zuwa" Daga mata kai yayi, batare daya Bude Idonsa ba yace "bani ruwa" Babu musu taje ta dauko ta kawo masa "gashi" Mamaki ne ya kamashi,yayi tunanin bazata kawo ba, wata zuciyar tace kasani Kota shiryu ne? Wata dabara ce tafado masa, yayi Dan qaramin tsaki, yace "kaina yana min ciwo sosai" Zama tayi Akan kujerar tace "Sannu, kona kawoma magani?" Mamaki yaqara kama Amjad, cikin ransa yace Alhamdulillahi nasamu mafaka πŸ˜‚ Fuskarsa ahade Cikin sauri yace "A a, basai Nasha magani ba, idan na kwanta nahuta zai daina" "Allah yasawaqe" abinda tace dashi kenan, ya amsa mata, ya dauki ruwan data kawo masa yasha, sannan yawuce dakinsa ya kwanta, har magrib Yana daki yaqi futowa, kuma yayi hakane da niyya danyaga tadamu dashi ne kokuwa haukansa kawai yake Amma abin mamakin da daddare ma har daki ta kawo masa abinci da magani, tayi masa sannu sannan tatafi nata d'akin ta kwanta Maganin ya riqe Yana murmushi, ya ajiye shi ya tashi yarufe dakinsa yaci abinsa sosai ya qoshi, sannan ya kwanta, dasafe motsinta da yaji a kitchen ne ya tasheshi,zuwa yayi ya ganta tana kokarin hada breakfast, bataji shigowarsa ba saiji tayi ya rungume ta taba ya, babu wata shagwaba ko alamun wasa yace "good morning" Daga masa kai tayi jikinta duk yayi sanyi, shi kuwa kissing din wuyanta yayi yace "bakya gajiya da aiki ne?" "yajikin?" Murmushi yayi yace "Alhamdulillahi, da d'an sauqi, saide jinyar rashin matata akusa dani" "uhm..." abinda tace kenan Yace "bari in tayaki, aikin" yasaketa yasaka hannu suka qarasa, sun Gama kawai dinning kenan ya kalleta yace "gobe fa akwai taro, Yaya Asim ya shirya taro, amma gaskiya ba lalle kije ba" Kallansa tayi tace "saboda me?" "to yaushe mukai auren da zaki fara fita?bayan ko amarcin ma baki tsaya munyi ba" Maganarsa ce tasata kunya, Wai Amarci, kuma amarcin ma da Amjad, har yau gani take kamar almara, zata iya zama dashi tayi kowacce irin biyaiya, amma banda wannan abin kunyar, tayaya haka zata faru? Babu musu tace "to shikkenan, taron menene?" "babu ruwana, idan naje sainayi miki video inzo in nuna miki, hakan ya miki?" Tace "to" Tafara zuba musu abincin, cikin sauri ya tashi ya karba yace "zauna ki huta, zan zuba" Tace "kaida bakada lafiya?" "babu damuwa" Shida kansa yazuba mata abincin, sukaci suna fira kadan kadan, bayan sun Gama yashige daki ya shirya, sannan yadawo falon yazauna, haka kawai yake jin kansa cikin farin ciki kasancewar yau Amrah tayi hakuri tasake dashi tanayi masa biyaiya Acan gidansu Asim kuwa Shima ya fadawa su mamy da Insaaf dasu Ishraqa duk su shirya zasuje wajan taro gobe dasafe, mamy ta tambayeshi taron menene saiyace ya shirya wa Insaaf yar qaramar walima ne, bayaso kowa yasan abinda ya shirya Yauma saida dare yayi Amjad yasake langa6ewa kansa Yana masa ciwo,Amrah ta kalleshi tace "Sannu, Allah yasawaqe" Yace "Amin, idan kingama kallon kikai min magani da ruwa, zansha in kwanta" Bata kawo komai a ranta ba tace "to" sannan ta dauki remote tana sauya Channel Shikuma Yana zuwa d'akin yafada kan gadon sa yasaki wata irin dariya yace "yau nake ango insha Allah" Har wajan 11 Bata kawo masa ba, harya hakura yayi shirin kwanciya, yakashe wutar d'akin sannan yaji anbude kofar, cup ne a hannunta da ruwa Sai magani, ganin d'akin babu haske yasa ta kunna, cikin sauri yace "kashe kashe, banson hasken nan Amrah" Yanda yayi mata magana da sauri sauri Sai yasa ta tsorata cikin sauri takashe wutar, kusa dashi ta zauna tace "ga maganin" Kallan maganin yayi cikin duhu, yanzu tayaya zaisa paracetamol bayan lafiyarsa kalau? haka ya karba Dan dole yasha, tatashi zata fice yayi saurin riqo hannunta yace "ki ajiye sauran maganin anan, may be anjima zaiyi amfani" πŸ˜‚ Tace "kamarya? Ban fahimta ba, ko zaka sake Sha ne anjima?" Murmushi yayi yace "eh, tun dazu kannawa yake ciwo, nasan zuwa anjima ma zan buqace shi, pls kidan matsa min kaina kadan kozai rage wannan ciwon" "amma Amjad Naga wani lokacin agida idan kana ciwon kai dazaran kayi bacci shikkenan, meyasa yanzu bazaka kwanta kayi bacci ba?" "Amrah, wannan ciwon kan daban yake, nayi tunanin idan nace kimin abu bazaki min musu ba a matsayina na dan'uwanki" Tace "to shikkenan" tasa hannunta Akan goshinsa tana danna wa, Ahankali ya lumshe Idonsa, yadora hannunsa Akan nata, batare daya Bude Idonsa ba yace "kaina ciwo Amrah" Tace "Sannu" Tashi yayi daga kan fillo ya maida kansa kan cinyar ta, cikin sauri ta kalleshi tace "kwanciya nakeso naje nayi Amjad, please ka dagani" Wata irin fuzga yayi mata tuni tasamu wajan kwanciya a gefensa, yayi juyi, yariqe hannayenta duka biyun yace "ki yimin abinda na saki malama" Gabanta ne yafadi, tafara zare ido tace "to... to zanyi" Hannunta yasaki yace"cigaba " Cikin rawar tace" toka dagani mana " Daga ta yayi, tasa hannunta akansa taci gaba da abinda take, tun tana yi na nutsuwa harta fara gajiya, shi kam Amjad Dadin yanda take masa yake ji,cikeda qosawa tace"ninagaji, d'akina zan tafi" tasaki kansa tafara kokarin tashi, cikin wata irin murya yace "Dan Allah Karki tafi please" Tsaki taja, cike da tsiwa tace "Dan Allah Malam karabu dani haba!, wannan wacce irin jaraba ce....." Kafin ta qarasa magana yahade bakin su waje daya, cikin fitar hayyaci yake nuna mata tsantsar yanda yake sonta, gaban Amrah banda faduwa babu abinda yake, gashi yasakar mata nauyi tarasa yanda zatayi dashi, ahakan take kokarin tureshi amma takasa, Amjad kuwa abinda yasa a ransa shine sai Amrah ta gane kurenta,cikeda mugunta yafara tafiyar da'ita,lokaci daya Amrah tafashe da kuka tayi masa wani irin cizo akafadarsa, Sarai yaji ta cijeshi, amma kwata kwata yakasa yimata magana ba sakamakon tsintar kansa dayayi acikin wani irin yanayi wanda bai taba tunanin akwaishi ba, da nufin mugunta yaje mata, amma rasa nutsuwarsa dayayi yasa ya aikata mata abinda koda a muguntar ne ba lalle yayi mata hakan ba Cikin kuka take neman taimako "Amjad zaka kashe ni, kabari Amjad Dan girman Allah kayi hakuri, wallahi bazan sake ba, zanma duk abinda kakeso" Amjad kuwa baisan ma tana yi ba, saboda Hankalinsa baya tare dashi, hannunta yasake riqewa cikin fitar haiyaci yace "Bazaki bari... bako... Allah zan dakeki" Tasan cewa yafadi hakanne cikin fitar haiyaci, saboda a zahiri Amjad bai taba nuna mata cewa Wai zai Iya dukanta ba, Cikin kuka tace "Amjad abinda kakemin yafi duka, Gara ka daukeni, pls kayi hakuri" Amjad kam Shiru yayi bai sake sauraron taba, saida ya dauki lokaci mai tsawo Yana abu daya, kafin yadawo cikin Hankalinsa, yanda yaga tana kuka harda majina saita bashi tausayi, amma saiya saki wani irin munafikin murmushi yace "Allah yayi miki albarka Amrah, Gara da Allah ya qaddara kece matata, idan da ace ba nine mijin ki ba haqiqa dana tafka babban rashi" Kuka take sosai, haka haka take jin maganar tasa, ko fahimtar Sama batayi saboda yanda take jin wata irin azaba, kamar qafafunta Baza jikinta haka takeji Tashi yayi ya gyara jikinsa yazo ya kamata "tashi muje kiyi wanka, sorry sorry nadena bazan sakeba kinji" Kanta ta girgiza tace "bazan iya ba Amjad, nashiga uku na" tasake fashewa da kuka Murmushi yayi ya dauke ta zuwa toilet din, batayi mamakin yanda ya d'aga ta ba, mutumin da ya'iya yimata wannan aika aikar ai bafi qarfin ace ta yi mamakin daga ta dayayi Bayan sunyi wanka kwanciya sukai, har zuwa lokacin hawaye Amrah take, saita tuna lokacin da Yaya Asim ya dauko Insaaf daga Asbiti, idan hakane lalle dole aji tsoron maza Hannunsa taji Yana share mata hawaye, yace "Kiyi Shiru mana, ko saina qara zaki daina kukan?" Cikin sauri ta girgiza kanta tace "nayi Shiru fa" Murmushi yasaki ya rungume ta Yana shafa bayan ta, daga nan wani irin bacci mai dadi yadauke shi, Amrah kuwa daqyar tasamu ta rintsa 🀣 Da asuba ma kukan taci gaba dayi, tun tana bashi dariya harta dawo tana bashi tausayi, bata sake fashewa da kuka ba saida ya kaita toilet din zatayi alwala taga wani jinin a jikinta, lokaci daya tsoron Amjad yasake kamata, mamaki take Wai Amjad ne me wannan uban qarfin,Bata iya yin sallah ba Sai azaune, bayan ta idar komawa sukai suka kwanta, tana jinsa yajata jikinsa batayi masa musu ba. Karfe goma na safe kiran wayar mamy ne ya tashe su, cikin bacci Amjad ya dauki wayar, mamy tace "Amjad har yanzu baku futo ba, ko muwuce kawai saiku taho daga baya?" Kansa yadan Sosa yace "mamy zanzo, amma kuje din kawai, zan shirya nataho" Sallama sukai, duk wayar da suke Amrah tana jinsu, Ada kam tace bazata ba, amma a yanzu kam dole ne ta shirya tabishi, ai saiya sake ganinta a gidan bare yanemi ya kashe ta, inde tabar gidan nan bataga me dawo da'ita ba Tare suka sake wanka,ya hada mata ruwan dumi tashiga ciki, Sai taji jikin nata dadan dama dama ba kamar cikin Daren ba, gani yayi tana shiryawa yace "ina zakije?" Idanunta ne sukai qwalqwal suna kawo ruwa tace "inaso na bika" Hularsa yasaka yajuyo ya kama hannunta yace "mezakije kiyi? Yaushe mukai auren da zaki fara fita? Bahaka Bama ki kalli yanda kike tafiya , kiyi hakuri kawai" Hawaye ne suka sakko mata, taga alama kamar bazai Barta tabishi ba, kuma idan ta zauna a gidan nan inde wannan abun zai dinga mata watarana saide azo a dauki gawarta Hawayen ta share tace "Dan Allah" Yace "to shikkenan, amma idan munje karkiyi nesa Dani, kizauna akusa dani idan kingaji da tafiya saina daukeki" Ahankali tace masa "to" Daga nan ya taimaka mata ta shirya suka tafi *Federal Place Hotel & Events* ya qawatu iya Kar qawatuwa, babban hall din an tsara shi yanda ya kamata, da wajan Zaman baqi da abokan cinikayya dakuma 'yan'uwa, su mamy suna tare gaba dayansu, da ita da Insaaf da Ishraqa da El-Hameed, Asim kam Yana tare da baqi Sai gaisawa yake dasu Yana musu Barka da zuwa,baya cikakken minti biyu bai juyo ya kalli Insaaf ba, Ishraqa dai kawar da fuskarta kawai take, mamy kam ajiyar zuciya tayi Dan ta riga ta saba πŸ˜‚ Ahankali suka shigo wajan hannunsa Yana cikin nata, kayan dasuka saka iri daya ne, adon shadda sukayi, duk wanda ya gansu zai Iya rantse wa cikakkun masoyane, mamy ta daga kai ta hango su tayi murmushi, taji Dadin ganinsu hakan, saide tana ganin tafiyar Amrah, ta gane cewa Autan nata ya girma, itama Ishraqa tana ganin yanda take tafiya tana Dan Buda kafa saita gane, cikin sauri tatashi taje taruqo hannunta tace "amarya da kanta, sannu da zuwa" tasake yin qasa da murya tace "kedan gidanku gyara tafiyar ki" Wani irin kuka ne yataho mata, Ishraqa tace "mene hakan kuma Amrah?" Amjad Yana ganin haka ya Sosa Qeyarsa yayi wajan Yaya Asim πŸ™ˆ Amrah ta dora kanta ajikin Ishraqa tace "Allah Anty bazan koma gidansa ba, Amjad mugu ne" πŸ™Š Mamy tana ganinsu ta kawar da kanta Bata nuna ma tasan akwai abinda yake faruwa ba,tunda ga Ishraqa nan tasan babu damuwa Ishraqa ta lallasheta tayi Shiru, sannan suka zauna, anan tagaidasu mamy da El- Hameed Taro aka Bude da Addu'ah, sannan Asim ya tashi yafara magana "tsawon rayuwata, bansan da wacce irin kalma zanyi amfani wajan gode muku ba" Kowa yanajin wannan furucin nasa Sai hall din yasake yin shiru, Ana sauraronsa Yaci gaba da fadin "kunyi min komai, ba'iya nikadai ba harda dangi na, irinku ne wani lokacin ake Kira da Bare yafi dan'uwa, rayuwar makaranta ba'a bar mantawa bace, koda zan manta rayuwar danayi a'iya makarantun danayi haqiqa bazan taba mantawa da makarantar data hadani dake ba " ya qarasa maganar Yana kallon Ishraqa Yayinda hall kacokam ya nutsu, kowa Yana kallonsa Yaci gaba Dacewa"Alokacin dana rasa komai, Narasa mai tallafa min, Allah ya jefoki acikin rayuwata, kika tallafamin tare da sauran yan'uwana kika hanamu furta kalmar DANA SANI, kun dauki yarda kun bani, kun bani kudi alokacin danake tsananin buqatar su, idan kanaso mutum yaji dadi to ka kyautata masa adede lokacin da bashi dashi, Ishraqa!! BURINAH a rayuwa shine nariqe amanar 'yarku a gareni kamar yanda nariqe amanar dukiyar ta,Bana fatan wata macen daban tashigo cikin rayuwata harta sanya min wasiwasi acikin zuciyata ta yanda zanzo ina tunanin WAZAN ZABA atsakanin su biyu, duk da yar gata ce awajan iyayenta banaso gatanta yasa wataran iyayenta su kirata da SHALELAN BABA, saide shalelan Asim" Yajuya ya kalli Insaaf data zuba masa ido tanajin wannan dogon Jaws jawabin nasa, suna hada ido yace "NI DAKE har abada zamu rayu tare, mu kasance mun zama DANGI DAYA, ina alfahari dake INSAAF, kuma ayau ne nakeson sauke nauyin dake kaina, na dukiyar matata, inayi mata albishir da komawa makaranta, dakuma fara aiki aduk lokacinda taso" Yana kaiwa nan hall din ya dauki tafi, yayinda jikin Ishraqa yayi mugun sanyi, El Hameed ya kalleta yace "Wai saboda wannan dama Asim ya kiramu wajan nan?" Ishraqa ta kalli mamy tace "haba mamy? Meyasa hakan Dan Allah?" Mamy tayi murmushi tace "Ishraqa ai kunyi kokari, bamuda bakin da zamu gode muku, Dan Allah mubar maganar nan" Kafin Ishraqa da El-Hameed suyi magana sukaji Ana kiran sunan Insaaf Akan step, kallan Iyayen nata tayi, El Hameed yayi mata alama taje, cikin sanyin jiki tatashi aikuwa Sai kallo yakoma kanta, bakajin qaran komai saina camera qyas qyas qyas, tana zuwa tayi masa wani irin kallo, ta kalli hannunsa taga documents ne yake miqo mata, hannu tasa ta karba, microphone ta dauka tayi sallama, tareda yiwa baqi Barka da zuwa kamar yanda taji Asim yayi, muryarta ce tafara rawa, gab take da sakin kuka tace "bansan mezance ba, abinda nasani shine mijina yagama min komai a rayuwata, alokacin dana rasa kowa nawa, babu dangin iya babu na baba, shine yayi sanadiyar hadani da iyayena...."tana kawowa nan tasaki kuka, taci gaba da fadin" shine abinda nake so ba dukiya ba, dag yau nabashi wannan dukiyar halak Malak, shine fatana, burina, muradina, shi nake so ba dukiya ba "ta ajiye masa duka documents din daya Bata, ta sakko tana share hawayen idonta, hall ya kaure da tafi da hayaniya, Shima Asim din yanda ta ajiye documunts din bai dauka ba,Amjad ne yayi murmushi yafara tattara komai daga wajan Asim kuwa biyota yayi har inda take zaune, babu kunya ya sunkuya yayi qasa da muryarsa, yanayi mata rada akunne , amma taqi dago kanta ta kalleshi, ita kanta Ishraqa kin kallonsa tayi Mutanan dake cikin hall kowa yafara cin abinda yake so, masu selfie nayi, masu video nayi, kowa Yana harkarsa, masu tafiya kuma suna tafiya, Insaaf tasa hannu ta goge hawayen idonta, kamar wasa tadago kanta zuwa window saita hango su dubiyu atsaye, gaban ta yayi mugun faduwa Cikin sauri tatashi tsaye tana qare musu kallo, tanaso ta tabbatar su dinne kokuwa basu bane? Suma anasu bangaren suna ganin yanda take kallonsu cikin sauri Inna tace "Malam mutafi, Kar Amina tasa akamamu, muje, muje, Naga kamar ta gane mu" Baba ya sunkuya ya dauki wani tsohon buhunsu na kaya ya kama hannun Inna zasu tafi Asim yajuya ya kalli inda Insaaf take kallo, lokaci daya ya ganesu, menene yakawo su Lagos Suda aka kore su daga Yola? Jikin Ishraqa ta taba tace "Anty, wallahi sune, su Inna ne, kin gansu can" Kafin Ishraqa tayi mata magana tatafi da gudu tabi bayansu tare da rungumesu duka su biyun Asim ya rintse Idonsa, πŸ˜–πŸ˜£jiyake kamar Akan qaya take gudun nan saboda lafiyar Baby's dinsa 🀣 ✍🏻 Amnah El yaqoub [3/6, 1:56 PM] El~Yaqoub: INSAAF Writing by:Amnah El yaqoub 55&56 Like my page on Facebook πŸ‘‡πŸ» https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 Kasa juyowa sukai su kalleta, suna jin yanda ta rungume su ko qyamatar su batayi ba, Inna tafashe da kuka ta tsaya cak, amma takasa daga ido ta kalleta, baba ne yadago kansa ya kalleta yace "Amina... ashe da Rabon zamu sake ganinki?Dan Allah kiyi hakuri Karki sa ayi mana wani abu, ba komai ne yakawo mu wajan nanba Sai Bara, Shima saida nacewa larai karmu zo ta Dage Sai munzo" Insaaf tana jin furucin baba tafashe da kuka, tadago kanta daga jikin su tace "baba Bara kuma? Menene yake faruwa ne?" Su Ishraqa ne suka qaraso wajan,tare dasu mamy Sai alokacin Inna ta kalli Insaaf tace "kiyi hakuri Amina, Dan Allah ki yafe mana, saida na aikata miki wannan butulci nagane nayi kuskure, nasoki kamar yata taci kina, bansan wacce irin zuciya gareni ba dana aikata hakan, kiyi hakuri kiyafemin Amina" Hawaye ne yazubo mata, tasa hannu ta share, tace "Inna nayafe muku, dama ban riqeku ba, kun riqeni kamar yarku, Baku qyamace niba, kun dauki danku kunbani Inna duk da kunsan larurar datake tare dani, babu komai Inna,baba, kudena neman yafi yata, nayafe muku wallahi" Asim ya sunkuyar da kansa Yana shafa goshinsa, yayinda hannunsa daya yake cikin aljihun Wandon jeans dinsa Wani irin kallo yayiwa Insaaf, ko menene nacewa sun dauki dansu sun Bata? Menene ma natada maganar auren? Tun kafin tasake cewa ta auri maza shida Gara subar wajan, dan zuciyarsa zafi take masa yanzu haka datayi maganar ta auri wani πŸ˜– Ya kallesu yaqaqalo wani murmushi yace "mu qarasa gida mana ko" Su Inna suka kalleshi, Malam yace "ikon Allah, bawan Allah Kaine?" Asim yayi murmushi, El-Hameed Hameed yace "Insaaf, muje gida su huta" Inna tace "Insaaf kuma? Bawan Allah kasan Amina ne?" Murmushi sukai, mamy da Ishraqa suka jasu zuwa Mota, Asim kam budewa Insaaf gaban motarsa yayi, Amrah tashiga baya tarufo Dasauri danma Kar Amjad yabiyota πŸ˜‚ Ishraqa tayi murmushi tasa Amjad ya dauki su Inna, sannan suka wuce gida. Suna tafiya a hanya taga gyada dafaffiya, tace "Yaya kasiya min gyada" Parking yayi yace "to Baby" Amrah tayi fari da idonta cikin ranta tace tab inaga Yaya Asim ya manta ina cikin motar πŸ™„πŸ™„πŸ™„ Gyadar yasiyo mata, yabata, budewa tayi zata fara Ci, yace "kibari muje Gida saina 6are miki" Insaaf tayi murmushi tace "to Yaya" Kai tsaye gidan mamy suka je, gaba dayansu zama sukai afalo, Ishraqa da mamy suka gabatar musu da abinci da kuma abin Sha, Inna da baba de Sai kallon falon suke yanda aka tsara shi, duniya kamar baza'a mutu ba Asim Yana kusa da Insaaf Yana 6are mata gyada tanaci πŸ™ˆ Mamy ta zauna tace "sannunku bayin Allah, mungode sosai, ai Insaaf tabamu labarin ku, kuma munji Dadin irin ruqon da kuka yi mata" Baba yace "hajiya Amina ce kike Kira Insaaf kokuma watace?" Mamy tayi murmushi tace "itace, Aminanku dakuka sani mu anan itace Insaaf" Ta nuna Ishraqa da El-Hameed da Asim tace "wannan shine mahaifinta, ga maman ta, wannan kuma dana ne Asim, wanda kuka taimaka wa daga baya ya aureta" Inna tace "Allahu akbar, Allah mai iko, Amina ashe kinsamu Iyayen ki" Insaaf tayi murmushi cikeda jin dadi, har yanzu gani take kamar Inna ce namanta, suntashi tare, sunyi rayuwa tare, ka wayi Gari bakasan kowa ba saisu, sune kake gani a matsayin iyayenka Mamy tace "hakane, dama haka Allah yake ikonsa, tahadu dasu ne bayan sunzo Lagos itada Asim......" daga nan mamy ta basu labarin komai Jikinsu yayi sanyi gaba dayansu, ashe attajira suke riqewa basu saniba,sun koreta gashi ita ta gansu amma Bata gujesu ba, Ishraqa tadubesu cikeda kulawa tace" Inna ya kamata kubamu labarin yanda akai kuka samu insaaf" Baba yace "lokacin akwai Yaya na dayake zaune akano, munkai masa ziyara a hanyar mu ta tafiya gida motar mu ta lalace, Sai muka fara tattaki, anan muka ganta azaune a wata bishiya, mu kayi mata magana amma kwata kwata saimukaga Bata fahimtar yaren damuke mata, larai tasa hannu ta dauke ta, muka shiga cikin garuruwan da suke a hanya mukai cigiyar ta, amma babu wanda ya nuna ya santa, haka muka tafi da'ita garinmu, bayan munje gida yin duniya larai tayi da ita tana tambayarta Yaya sunan ta, amma saide kallo, bamuyi dabarar gwada mata kowanne yare ba kamar fillanci ko zamuji ta amsa, haka muka hakura muke kiranta da suna Amina, saida ta girma tayi hankali muka aurar da'ita daga nan muka Gano cewa tanada matsala duk wanda ta aura Yana mutuwa, haka naje wajan limamin garinmu nake karbo mata rubutu, daga qarshe de har muka aura mata danmu Ammar,Shima Allah yayi masa cikawa " Kuka ne ya kamashi, yasa hannu ya goge hawayen Idonsa sannan yaci gaba da cewa "daga nan ne mai Gari ya koremu, larai tarasa nutsuwarta har saida ta kori Amina saboda mutuwar Ammar, mu kuma muka tafi gombe, nafara neman kudi ina ciyar damu, daga baya komai nawa yaqare, wani bawan Allah a gombe yabamu shawara mu tafi Lagos mu nemi kudi, ance Garin ba'a zama haka, Ana neman kudi sosai, shine muka taho nan muka fara Bara " Babu wanda bai tausaya musu ba, Insaaf de tun dazu take goge qwalla, El Hameed yace" kayi hakuri baba, kadena kuka, Baku aikata abinda zakuyi kuka ga, bakomai ne yake kashe mazajen da Insaaf ta aura ba Sai aljani, kuma shine yashiga jikin matarka yasa ta kori Insaaf, kuyi hakuri muma mun Fahimci komai, Allah yayafe mana baki daya, kuma Insha Allah kunzo gida, babu inda zaku tafi, zaku zauna agidana tare dani, mungode Allah yasaka da Alkhairi " Asim yadago kansa ya kalli El-Hameed yace"sai baba yafara zuwa company, akwai aikin dazan do rashi akai, sannan nayi masa alqawarin gida insha Allah, saisu zabi inda suke so su zauna " Amrah tayi murmushi tace "shikkenan Insaaf tazama me gida biyu, ga gidan Anty ga gidan inna" Dariya suka yi gaba dayansu, Ahankali tatashi tashige dakinta nada, Sai runtse idonta take sabd yanda take Fama wajan Amjad ya yunqura zai bita suka hada ido da mamy, wannan shine Karon farko da yaji kunyar mamy, kuma yasan kowa ya kalli tafiyar Amrah dole zai gane abinda ya wakana a tsakanin su, Ahankali ya tashi yafice daga falon πŸ˜‚ Har dare duk suna zaune afalon sunata fira, babu wanda yakai Insaaf farin-ciki, Sai wajan qarfe Tara Amjad yashigo gidan kansa aqasa, ya kalli mamy yace "mamy zamu tafi" Mamy ta kalleshi taga Sai sunkuyar dakai yake πŸ˜‚tayi murmushi ta kalli Ishraqa tace "maman Insaaf turo masa Amrah su wuce, dare yayi" Ishraqa tasan dalilin dayasa mamy tayi mata magana, babu musu kuwa tabi bayan Amrah, tana zuwa ta ganta a kwance adakin, zama tayi akusa da'ita tace "Amrah, kitashi Amjad yazo, zaku wuce gida" "Anty nifa babu inda zani, kawai kifada masa yatafi shi kadai" "Amrah, kunzo tare tayaya zakice yatafi shi kadai?" Wani irin kuka ne yazo mata tace "Anty wallahi Dan nakoma kashe ni zaiyi, Amjad bashida tausayi, ni ko kallansa nayi gabana faduwa yake, dan Allah kice masa yatafi kawai" "haba Amrah, kamar qaramar yarinya? Kowa kika gani da haka yasa ba Amrah, kicire tsoron sa aranki, inba hakaba ramewa zaki dinga yi, kiyi hakuri kinji, kuma ki dinga shiga ruwan dumi kina zama" Hawaye ta share tace "to Anty" Ishraqa ta kamo hannunta suka futo, murya qasa qasa tayiwa mamy sallama sannan suka tafi Tsawon wata biyu kenan suka dauka suna gudanar da rayuwar su cikin farin ciki, yanzu kam Amrah harta saba da Amjad, tasaki jikinta tana zaune lafiya dashi, Insaaf yanzu ta Dan rage yawan kwadayi tana rainon cikinta itada Asim batada wata damuwar komai, gasu Inna atare da'ita, ga iyayenta gakuma mamy da mijinta, haka rayuwar su taci gaba da Juyawa cikeda farin-ciki babu abinda ya sauya har watan haihuwar ta ya kama, gaba daya kafafunta sun kumbura, idan tazauna daqyar take tashi, tana Hawa Asim tausayi sosai, ga yarinta, shiyasa koda yaushe yake zaune agefenta koda akwai abinda take buqata, Ishraqa tanaso idan Insaaf ta haihu tadan sake gyara ta tunda haihuwa ce har yan biyu, shiyasa tacewa mamy ko zata Bata Insaaf bayan ta haihu tayi wanka saita dawo dakinta, babu musu mamy ta amince, saboda tasan tsakanin ya da uwa dole akwai wasu abubuwan daya kamata ace sun shirya, kuma koba haka Bama yawanci a al'adance a nayi Asim nede yaji babu dadi duk da ba Nisa zatayi dashi ba ga-gida ga-gida, kwanan ta biyu da tafiya amma Sai yaji kamar tayi shekara Bata tare dashi, yau da wuri ya shirya ko break fast beyi ba yayi wa mamy sallama, ta kalleshi tace "bazakayi break fast bane?" "ina sauri mamy, zanje office ne akwai abinda zanyi" "to Allah yadawo dakai lafiya" Amsawa yayi sannan yafice daga gidan, suna futowa daga gida ya kalli direbansa yace "muje gidan Ishraqa" πŸ˜‚ Babu musu direban yajuya, suka qarasa gidan, Ishraqa tana break afalo taga Asim yashigo, mamaki ya kamata yaushe Rabon ta dataga Asim a gidanta, Sai yau Sanadin Insaaf πŸ˜‚ Tace "Asim sannu da zuwa" Zama yayi Akan kujera yace "yawwa Maman Insaaf, yagida yame jiki?" Bread ta karya tanaci tace "Insaaf, inajin tana dakinta, uwar raki, komai raki, duk kagama sangartata, haihuwa cede a gaban ku" Kallon ta yayi yaga tana magana hankalinta kwance, bread ma takeci amma tabar masa mata adaki yace "yanzu tayi break fast ne?" "nakai mata abincin ta, inajin taci, Kai zataci ma, waya fada mata Yara biyu wasa ne, cikin ma kadai zaisa ta jin yunwa" Ajiyar zuciya yayi ya tashi yashige d'akin Insaaf, Ishraqa ta kalleshi tace kukuka sani ☹️ Yana shiga d'akin yaganta azaune da uban ciki, wanka tayi tana shiryawa, tana ganinsa tace "Sannu da zuwa Yaya" "Sannu baby, ina missing dinki da yawa" ya qarasa maganar Yana shafa cikinta Rigarta ta daga sata saka, ya taimaka mata tasaka amma Sai taqi saukowa qasa, cikin shagwaba tace "Yaya kagani fa, Allah duk kayana sunmin kadan" tana qarasa maganar hawaye ya silalo daga idonta Lokaci daya ya rikice "kiyi hakuri baby, sorry sorry, ai kin kusa haihuwa insha Allah tunda edd dinki yacika, yi hakuri kinji" yajanyota jikinsa ya rungume ta sosai, itama jin qamshin turaren sa yasa ta gyara kwanciyar ta a qirjinsa tare da lumshe idonta ✍🏻 Amnah El yaqoub [3/7, 4:05 PM] El~Yaqoub: INSAAF Writing by:Amnah El yaqoub 57&58 Like my page on Facebook πŸ‘‡πŸ» https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 *Dedicated to:* Fati Ahmad(fatyn yalleman) Anty mama Hafnah El Yaqoub Hudancy luv Fatyn Kaihaf *Special gift to:* Its Sadeek Fauziya s madaki Unique Jamaal Prince Abba bakarya Ayusher Abdallah Alhusna Mrs Idris Maman Musa Hannunsa yadora abayanta Yana shafawa, sun dauki lokaci ahaka sannan yatashi yaduba mata doguwar riga acikin kayanta, yasaka mata Ishraqa ta jisu Shiru babu wanda yafuto acikinsu, afili tace "ku kuka sani" daga nan tatashi tayi dakinta Shikuma Asim abincin ta na break yaja yafara Bata, Shima ba abincin yaci ba, Danhaka yayi zamansa Yana Bata Shima yanaci, saida yaga taqoshi sannan yatashi zai tafi office, tace "Yaya idan katashi zaka biyo tanan?" Kansa ya Sosa yace "A a baby, ba lalle ba, Kar mamanki tace ina damunki" "babu abinda zata fada wallahi, nide ka shigo Dan Allah, inaso naganka" "angama baby, idan na tashi zanzo kiganni saina wuce gida" Kokarin tashi take tace masa "muje na rakaka" "a a a a baby, kinyi nauyi dayawa ai, kiyi zamanki ki huta" Zama tayi tace "Allah yadawo min dakai lafiya" Murmushi yasaki, yaji Dadin Addu'ar Tata, saida ya sunkuya yayi kissing lips dinta, sannan ya amsa da Amin, yafice daga d'akin, yayi tunanin zaiga Ishraqa afalo Sai yaga Bata nan, bai nemeta ba Shima yafice daga nan suka wuce office *** ****** *** Bayan sati biyu Tana jikinsa a kwance Sai zance yake mata murya qasa-qasa, riqon ta yake Akan ta shirya tabi shi sutafi Tace "yanzu Amjad idan nabika kuma su mamy fa" "yanzu tare kike dasu? Idan naje Yola ma bazan Dade ba zan dawo tunda na barki anan, amma idan kika shirya muka tafi nasan bnda wata damuwa, kina tare dani" "toka bari idan naji sauqi saimu tafi, yanzun banajina normal kamar da" Kallanta yayi Dasauri yace "kede kifadamin kode qwallo na tashiga raga" Kukan shagwaba tafara masa tana masa wani irin dukan soyaiya a qirjinsa, murmushi yayi yana qara godewa Allah Wai shine Amrah tasake dashi haka har dasu shagwaba Kanta ya shafa yace "Anty Amrah kifadamin gaskiya bahaka bane?" Cikin shagwaba tace "to ba gashi kasani yanzu ba" Wata irin runguma yayi mata Yana fadin "Alhamdulillahi, Nima na kusa zama Daddy Anty na zata Haifa mun Baby" Tanajinsa tayi Shiru, ita kunya takeji ace Wai cikin Amjad ne a jikinta, yanda ta botsare afarko harda cewa bazata dawo gidansa ba, gashi yanzu tadawo anjita shiruuuu harda tsarabar Baby, shi kuwa Amjad wayar sa yad'auka yakira mamy, amma Bata kusa Bata dauka ba, saiya tura mata text yafada mata, yakira Asim Shima yafada masa, bayan sunyi sallama Asim ya Girgiza kansa, Amjad kenan, wayaga Amjad da BabyπŸ˜‚ *** ****** *** Yau tunda tatashi take jin jikinta babu dadi,ga wani irin ruwa datake zubarwa, ko awa daya Bata qaraba cikinta yafara ciwo, Ishraqa na ganin haka, suka wuce asbiti cikin sauri, saida likitoci suka karbeta sannan tasamu takira mamy da Asim ta sanar dasu, Hankalinsa atashe sukazo Asbitin, tunda safe take labour har azahar, Asim yarufe fuskarsa da hannayensa Yana Addu'ah Allah yasauketa lafiya Sai bayan sallar la'asar sannan suka jiyo kukan baby, gaba daya su ukun atare suka miqe tsaye, wannan ya kalli wannan, wannan ya kalli wannan, mamy ta daga hannunta Sama tace "Alhamdulillahi...." Asim kuwa wata irin qwalla ce tafuto masa, Ahankali yasa hannu ya goge Yana qara yiwa Allah godia a ransa, Insaaf kuwa ba tasan ma meta Haifa ba, tana haihuwar ta suma, saida aka dauki lokaci ta farfado sannan taji wani irin ciwon daya take nada, lokaci daya ta gagace tana kuka da Addu'ah Daya daga cikin nurse din ce tafuto musu da babyn da aka Haifa, cikin sauri suka qarasa wajanta, Cikin murmushi ta miqawa Asim babyn tace "Yallabai ina tayaka murna ansamu Baby boy, amma madam tana wata naqudar" Jikinsa a sanyaye yakarbi Yaron, Allah abin godia, gaba daya Yaron kamar Asim ne, babu inda yabar Asim, mamy ta qaraso ta karbe shi daga hannunsa tace "kayi mata Addu'ah Asim, insha Allah zata sauka lafiya" Sai alokacin yadanji nutsuwa a ransa Saida ta qara awa uku atsakani, sannan ta haihu, daganan kam baccin wahala ne yadauke ta, ba tasan inda kanta yake ba, wata nurse din tasake futowa da wani babyn a hannunta tace "Tasauka hajiya, ansamu wani na mijin, zamu kaita d'akin hutu zuwa anjima zaku iya ganinta" Asim baisan lokacin da yaji hawaye yazubo masa ba, Ishraqa ta kalleshi tsananin tausayin sa ya kamata Yara masha Allah lafiyaiyu dasu masu kama daya Sak babu banbanci, kuka daya yafara, Shima dayan yanaji yafara nasa, gaba daya Sai suka kaure wajan da kuka Asim ya kallesu ya kalli mamy "mamy kuka sukeyi, ko mamansu suke so?" Mamy tayi murmushi tace "Suda ko ganinta ma basu yi ba Asim, yunwa ce kawai" Ishraqa tace "ko abasu dabino da zamzam? Mun taho dashi" Asim ya kalleta yace "Abasu mana, zoki basu" Matsowa tayi ta karbe su daya bayan daya ta basu, yaran take qarewa kallo farare kamar ba hausawa ba, Wai Insaaf dinta ce ta haifesu, Allah ya basu ita ita kadai, gashi yanzu ita yabata biyu alokaci daya, wayarta ta dauko ajaka takira El Hameed dayake wajan aiki tace "to Habiby Insaaf tasauka, kasamu abokai biyu" Cikin farin ciki yace "kaiiiii Alhamdulillahi, ganinan zuwa, Karki bari adamesu ganinan zuwa" πŸ˜ƒ Wayar takashe tana mamakin wannan soyaiya ta El Hameed Akan jikokinsa, aiko Asim din Sai haka 🀣 Mamy takira Amrah da Amjad duk tafada musu, lokaci daya asbitin ya karbi baquncin su Sai dare sannan Insaaf tafarka, cikinta tafara shafawa taji kwalaf babu komai, Sai wata yunwa datake cinta, likitan ya basu Damar ganinta, aikuwa gaba dayansu suka shiga, yaran farko Yana hannun Amjad, dayan kuma Yana hannun El Hameed πŸ˜ƒ Kawai tana ganinsu ta rufe fuskarta da hannunta, gaba daya saita basu dariya Yaran suka ajiye mata amma firr Insaaf taqi dago kanta ta kallesu, mamy tace subar d'akin ko zata sake da yaran Asim kam qin fita yayi daga d'akin, Yana ganin fitar kowa yataho wajan ta cikin sauri ya rungume ta, atare suka saki Ajiyar zuciya, bai iya hakuri ba saida ya lalubo bakinta yadinga kissing, dan kansa yazare bakinsa anata, Sannan yace "I luv you my dear, Allah yayi miki albarka, kingama min komai a rayuwata, kalli yaran da kika Haifa mana, suna kama dani Insaaf, Allah yaraya min ku gaba dayanku, Allah yasa ki sake Haifa min wasu yan biyun" "Yaya haihuwa da wahala fa, jinayi kamar zan mutu, Bazan sake haihuwa yanzu ba, Gara muyi planning" "bazaki mutu ba baby, amma Dan Allah kidena maganar planning dinnan, shekara kusan arba'in nake shirin yi Insaaf, amma Kinga Sai yanzu Allah yabani haihuwa, ta Yaya zan dakatar da baiwar da Allah yayi min? Dan Allah kidena wannan maganar, ku kadai zan kalla naji dadi, tunda Allah yahore mana abinda zamuci musha, muyi musu tarbiya ai Alhamdulillahi " Cikin sanyin jiki tace" to Yaya,Allah yaraya mana su" "yauwa wife, kokefa" ya qarasa maganar Yana Jan hancinta, atare suka sanya dariya Ranar suna Yara sukaci sunan El Hameed dakuma Abban Asim, El Hameed ne da kansa ya hada walimar da aka gabatar da gidansa ta sunan yan biyu, Yara sunga gata kamar ba'a taba haihuwa a familyn ba Haka kawai El Hameed zaisa a dauko masa yaran yasa su agaba Yana karatun jarida, haka kawai Allah yadora masa qaunar jikokin nasa a ransa Ishraqa ta Dage Sai gyara yarta take, tana kula da abincin datake Ci, dakuma na yaran, kasancewar Ana qara musu da madara sai sukai qiba bulbul dasu gwanin sha'awa Watarana Asim yazo gidan yaga yanda ake dura musu madara, Kota ido babu haka yafuto qiri qiri yace a daina basu, su dinga shan nono, saboda zaisa qwaqwalwarsu ta Bude, Ishraqa tace ai madarar tana taimaka wa yaran, saboda nonon baya isarsu sosai Amma haka Asim ya qeqasa qasa yace shifa abasu nono Ita kuwa Ishraqa duk lokacin da yaran suke hannunta haka take dura musu madara🀣 Idan suna hannun Insaaf din kuma Sai Insaaf din ta dinga basu nono Zaune suke afalo itada Ishraqa, tana Bawa yaran nono Sai tsaki take ja, Ishraqa ta kalleta tace "Keda waye?" "Anty yaran nan ne mana, basa qoshi wallahi, ko fitsari sukai yanzu zakiji sun fara kukan yunwa" "ki dauko madara kibasu, tunda suna shan madarar Aida sauqi" Cikin wani irin Salo tace "to Anty ai Yaya yace bayason Ana basu madara" πŸ™„πŸ™„ Ishraqa ta riqe ha6arta tace "to Laila majnun, ai jiki magayi, shi yayan daya Fadi haka a qirjinsa suke shan nonon?" Insaaf takasa Bata amsa tayi Shiru, Yaron ta ajiye ta dauki dayan tafara bashi, Ishraqa tace "nikam bari naje daki, idan kingama basu nonon kikawo minsu ki huta" Tana shiga daki Insaaf tacire Yaron tafara matsar qwalla πŸ₯Ί Adede lokacin yashigo falon Shima, cikin sauri yace "subhanallah baby lafiya?" Kuka tafashe dashi tace "Yaya basa qoshi, Allah ni nono na zafi yake min" Rikicewa yayi lokaci daya yace "Sannu, sannu baby, Kinga tashi muje daki ki kwanta ki huta, idan kin huta saiki basu, barsu haka yanzun" 🀣 Yaron ta dauka guda daya, Shima ya dauki guda dayan suka shige dakinta Saida tahuta kamar yanda yafada, sannan ta qarasa Bawa yaran nonon, kamar dole Sai sannu yake mata tana runtse ido πŸ˜ƒ Suna gama Sha ya daukesu duka su biyun yace "ina Antynki?" Kamar zatayi kuka tace "tana dakinta" Kallanta yayi cikeda tausaya wa yace "sorry, ina zuwa, Bari nakai mata su" πŸ™Š Dakin Ishraqa yatura yashiga, tana zaune tana linkewa yaran kayansu, Sai ganin Asim tayi yashigo tace "har sun Gama shan nonon kenan" "sunga ma, dama aiki zan tayata, shine tace nakawo su wajanki" 😊 Ishraqa tace "eh nace ta kawo min su, kwantar dasu kawai" Babu musu ya kwantar da yaran yafice daga d'akin Yana komawa d'akin ya Janyota jikinsa yadora ta Akan cinyar sa, cikin rada yafara lallashin ta "baby suna damunki ko? Kiyi hakuri idan suka sake girma Sai adinga basu madarar, Nima inaso ki huta baby" Kanta ta daga masa, yakai hancinsa wuyanta yafara kissing, cikin wata irin kasalalliyar murya yace "kin haqura ko?" Nanma batayi magana ba Sai daga masa kai datayi, murmushi yayi yace "baby ni bakiyi missed Dina Bako?" hararar wasa tayi masa, sannan ahankli tadora lips dinta Akan kumatunsa tayi kissing, cikin sauri yahade bakin su waje daya Babu musu ta bashi hadin kai, tun suna numfashi kadan kadan har suka dawo suna fidda numfashi mai sauti, Asim yayi Nisa sosai saboda yayi kewar matarsa ba kadan ba, jikinta yafara shafawa lokaci daya tajiyo ihun kukan yaran nasu πŸ˜‚ Ahankali taraba jikinsu tace "Yaya yaran can suna kuka, Bari na karbo su nabasu nono" Da jajayen Idonsa ya kalleta yace "ki dauki wayata kikira Antynki kice mata nace abasu madara" πŸ˜‚ Mamaki ya kama Insaaf, tace "Yaya madara kuma? Ba yanzu kagama bani hakuri Akan na dinga basu nono ba?" "baby ai banyi zaton haka suke da shan nono ba, shiyasa na Fadi haka, gaskiya kina kokari, shikkenan Yara Dan fitina daga nono Sai nono, Toni ina zanje naji sauqin abinda yake damuna kenan?kirata Dan Allah, kifada mata abasu madara" πŸ˜‚ Insaaf tayi murmushi, taga alama Yaya Asim a hannu yake, kiran Ishraqa tayi awaya, tana dauka tace "Anty Wai yace abasu madara" πŸ˜‚ Ishraqa ta kwashe da dariya kawai takashe wayar, afili tace "kai ya Allah Asim, Asim kenan," Tana kashe wayar suka dora daga inda suka tsaya πŸ™ˆ *After 4 years* Yara ne su biyu afalo suna fada harda dambe Akan safa, ☹️ Kwata kwata bazaka banbance suba saboda yanda suke tsananin kama da juna, komai nasu iri daya Hassan mai sunan baban Asim shine ya riqe safar yace "wallahi bazan baka ba, kullum saina nemo safata zaka ce takace" Hussain mai sunan El Hameed yace "Momy! Kinga Hassan ya hanani safa ta, Allah zanji wa Yaron nan ciwo" Insaaf tafuto da gudu taji Ana zancen ciwo, taqara girma da wayewa tazama cikakkiyar mace, jikinta luwai luwai kamar ka latsa jini yafuto, takama hannun Hassan tace "babana, ka bashi safarsa, banason rigima, kasan taka safar tafadi, kabari zan nemo ma wata adaki, ka bashi abarsa" Maimakon yabata safar saiya wullar da'ita aqasa, tasa hannu tadauka tabawa Hussain safarsa Takama kunnasa tace "duk lokacin danaji kasake cewa Hassan Yaro, har kayi masa maganar Jim ciwo saina zaneka a gidannan kajini?" Cikin sauri ya d'aga kansa, tace "oya tell him sorry Hassan" Kallan Hassan din yayi yace "I'm sorry Hassan" Sallama akayi afalon,gaba dayansu suka saki murmushi daga ita har yaran nata, Amrah ce tashigo falon hannunta dauke da Baby boy Ta kalli Hussain tace "Hassan, yabaku tafi school ba har yanzu?" Hussain yace "good morning Anty" Insaaf ta kalleshi tace "Hussain Kaine Hassan din?" Dariya Hassan yayi yace "Anty kinganni fa, shine Hussain ya amsa miki" Amrah tace "oho, nikam har yanzu Bana gane yaran nan" Insaaf ta karbi Yaron hannun Amrah tace "taho Yaya Asim Dina, ina kika bar widad kuma?" "widad tana hannun Amjad, gasu can a compound shida Yaya Asim da mamy" Insaaf ta su Hassan tace "tome kuke jira, kuje Daddyn ku Yana jiranku, karkuji latti a school" Yaran suka fita da gudu suna mata bye bye Amrah ta kalleta tace"ashe kungama final exam dinku jiya? " Insaaf tace" wallahi mungama Anty Amrah, yanzu saura taron graduation da suke hada mana kawai " " to Allah ya tabbatar da Alkhairi " "Amin Anty Amrah" Gidan mamy kenan, inda su Insaaf suke rayuwar su kamar da, har yanzu Allah bai Bata haihuwa ba tun daga kan yan biyu, Amrah kuma ya ranta biyu, babbar itace Hussaina sunan mamy taci, suke kiranta da widad, Sai kuma na biyun namiji, suka saka masa sunan Asim Rayuwar su tana tafiya cikin Jin dadi da kwanciyar hankali Washe Gari da daddare mamy tawuce daki ta kwanta daga Insaaf Sai Asim dakuma yan biyu suna zaune afalo suna shan fruit, Hussain yace "Daddy, idan na girma ko sonake nazama soja, na dinga tarewa widad fada a school" Insaaf da Asim sukasa dariya, Asim yace "A a Hussain, kode yar gida zakuyi ne kaida widad kamar yanda Daddyn widad din yayi?" Hussain bai gane abinda Asim yake nufi ba, Danhaka kai tsaye yace "eh Daddy" πŸ˜‚ Insaaf tayi murmushi, shi kam Hassan cewa yayi "momy, nikam likita nakeso nazama, in dinga yiwa Hussain allura" Gaba dayansu su hudun sukasa dariya, Asim yace "kai, kutashi kuje ku kwanta dare yayi, kuma Karku manta this weekend agidansu Inna zakuyi, Sannan momynku zata tasheku da sassafe ayi muku wanka kuyi ado, zamuje unguwa da mamy, da Maman Insaaf, da Alhaji,(El-Hameed) da Daddy Amjad, da Anty Amrah, dasu widad, duk zamuje kuga kakanku, gobe zai futo daga wani waje daya tafi " Hassan yace"yawwa Daddy, dama bamu taba ganin kakanmu ba, kullum kullum saikace yakusa dawowa" Asim yayi murmushi Yana kallon yaran nasa, kullum Basuda magana saita ina ka kansu yake wanda ya haifi Asim? Basu Bawa yaran labarin irin halin da daddy yayi musu ba, koda yaushe nunawa yaran suke da Asim da Amjad babansu daya, kuma zai dawo yayi tafiya ne, gashi kwanci tashi babu wuya har daddy yayi shekara biyar dinsa zai futo Yayi ajiyar zuciya yace "gobe zaku ganshi insha Allah, idan kakanku yahuta saimu bi Daddy Amjad Yola muje mugano matar Malam, wadda mijinta yayiwa mamanku waliyi ranar auren ta" πŸ˜‚πŸ˜‚ Insaaf tana Jin haka takai hannu ta mintsineshi batare da yaran sun gansu ba πŸ˜ƒ Cikin sauri ta kallesu tace "Hassan, Hussain, go and sleep" Saida sukai kissing din iyayen nasu sannan suka tafi d'akin mamy, dayake acan suke kwana Asim ya kalli Insaaf yadage mata Gira yace "aji dani madam" Bakinta taturo gaba tace "haba Yaya ... Allah kwana biyun nan baka barina nahuta, kullum saika gajiyar dani" "yes ina zan barki ki huta baby, ai saikin Haifa min wasu yan biyun tukunna" daga nan yadauke ta suka shige dakinsu Cikin sauri nabisu zan dauko rahoto suka bugomin kofar agoshi na 😏inajin Asim Yana cewa "haba ya kamata kibarmu haka Amnah, tun ranar danayi hatsari kike bibiyar rayuwar mu, kije kibasu labarin BABBAN YAYA kuma" πŸ€— Ina miqa Godiya tare da jinjina ga : πŸ“šπŸ“˜HAUSA NOVEL GRP INSAAF NOVEL FAN'S INSAAF HAUSA NOVEL AMNAH EL YAQOUB NOVEL PRINCE ABDUL HAUSA NOVEL TASKAR LITTATTAFAN HAUSA ALHUSNA SWEET NOVEL ZAFAFAN NOVELS (Alhusna) Kinada Samari masu yawa? Kinsan hanyar dazakibi kigane wanda yake qaunarki da gaskiya? 'yar'uwa mafi yawan lokaci muna gane masu sonmu ne yayinda muka kwanta jinya kokuma muka shiga cikin wani yanayi, kibiyoni cikin Labarin BABBAN YAYA kiji yanda tsarin yake, soyayya mai tsayawa Arai, zumunci, dakuma karamci, acikinsa ne zakiga yanda qawance yake da tsananin tasiri, kaiiiiii Bana ziga labari inde nice zan rubuta, amma labarin BABBAN YAYA Amnah El yaqoub ta zigashi da kanta, BABBAN YAYA maqura ne, but FOR SALE πŸ€— Labarin kudi ne, bazan iya rubuta labarin BABBAN YAYA a free ba, Karku manta Amnah cede da tazo muku da labaranta abaya,kun karanta DANA SANI, kunji yanda salon soyaiyar Ahmad da Feenah ya kasance, dakuma BURINAH, kowa yasan soyaiyar Amal da Daddy tayi, uwa uba WAZAN ZABA? yanda muketa zuba sharhi atsakanin Haidar da Imran shin waye tauraruwar mu zata zaba? SHALELAN BABA kuwa basai nafada ba πŸ˜…, har private kuke biyoni kuma cewa soyayyar Haneef da Haneefa tayi, haka NI DAKE, kunsan yanda mk ya haukace Akan Baby Nawal, 😊banaso natuno muku nasu salon, nasan kun karanta kunji, DANGI DAYA kam duk wanda yaji ance DANGI yasan Antara masoya dayawa, musanman soyaiyar Nihla da Yaya Abba, to gakuma INSAAF na qarshe, basai natuna muku ba tunda yanzu muka gamashi, to Alhamdulillah insha Allah, nadena ihu Akan comments, idan Kinsayi Labarin BABBAN YAYA natura miki, idan baki biyaba kuma Karki kuskura ki karanta min littafi, zaizo muku bayan nahuta insha Allah. Dan girman Allah masu YouTube channel Karku doramin littafi a YouTube πŸ™πŸ»ban yarda ba, ban amince ba, Kar a doramin littafi na a YouTube, idan da wanda nayiwa laifi Sanadin rubuta wannan labari, please yayi hakuri yayafemin, Nima nayafewa kowa, πŸ™πŸ» Sai mun hadu a BABBAN YAYA TAMMAT BI HAMDULLAH ✍🏻 Amina Muhammad El~Yaqoub Jigawa State A.k.a Amnah El~Yaqoub